HAYATEEM BOOK1 COMPLETE HAUSA NOVEL
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070 1 BismillahirRahmanirRaheem. Fadi da tsawon nisan da dajin yake dashi ya zubawa manyan idanuwansa yana kallan shuka da ganyen hakukuwan da suka cike gurin Wanda babu hanyar wuce a gurin idan ma kace wucewa zakai to sedai Kabi hanyar da adda ko wuqar ringa sare ganye dan Ka ringa ganin gabanka Wanda su hakan ba komai bane a garesu sbd sun saba haka suke rayuwa a cikin ganye da shukoki hakama yawo da wuqa me tsananin kaifi da dafi a jikinsu kaman dole ne kokuma ace al’ada ce me karfin gaske sbd yanayin karni da ake ciki na safarar mutane Ana saidawa a matsayin bayi, Rayuwa ce ta koina zaka iya haduwa Wanda sukafi Ka karfi su raunana rayuwarka suyi safararka zuwa inda zasu siyar a matsayin bawa, Ba iya dan Adam daya ko biyu ko uku koma da yawa ake nuna karfin hakan ba hadda gari sukutum masu safarar basu Bari ba suna cinye gari da karfi su tattara suyi safararsu. ANJOM GHAZ Garin ANJOM GHAZ gari ne dayake zagaye da ruwa masu ya wan…