HALYSAAH HAUSA NOVEL



[4/28, 9:59 AM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: *If you should come across this post plss say a prayer for my late father, Allah ya sabunta masa rahama, ya gafarta masa da duk musulman da suka riga mu gidan gaskiya, Allah ya kyautata makwancinsu gaba daya, ya sa mutuwa hutu ce a garesu, Allah ya yafe masu kurakurrensu, Allah ya bamu guzurin tar da su* πŸ₯Ί

 

 

**All thanks to Allah S.W.T for the chance and privilege to commence this new book, yanda muka fara lafiya Allah ya sa mu idar lafiya*

 

_Hmm ga fa Halysaah, Allah ka bani ikon delivering babu cece ku ce_

 

*This first page goes to all the members of Mayraah Conversation, i love and appreciate you all*πŸ₯°

 

 

 

✨✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

1....

 

 

Tsaye take ta jingina da trunk din bishiya a wani babban garden dake dauke da shukoki iri iri da suka kawata wajen, tsuntsaye sai shawagi suke a garden din happily making a chirping sound as the sun set slowly, the view was so beautiful and breathe taking, duk da yanda ta kafe view din da ido gaba daya hankalinta baya gun, she was just staring at the setting sun absentmindedly, tayi nisa cikin tunanin da take, daga gefenta wata ma'aikaciyar asibiti ce in her mid 40, likitar ta dafa ta tana kallonta cikin kwantar da murya tace "Magariba ya gabato mu je kiyi alwala ko" Kallon likitar kawai take babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda take cewa ba, sai ga hawaye ya fara taruwa idonta tana sauke numfashi a hankali, likitar ta kama hannunta ta jawota jikinta calmly tace "C'mon sweet heart, are you breaking ur promise already?" ta kwantar da kanta jikin likitan hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, likitan ta lumshe ido tana patting dinta duk jikinta a sanyaye, a tare suka juya jin footstep a garden din, ya tsaya daga inda yake bai karaso ba yana kallonsu, likitan ta fara gaishesa cikin girmamawa, zame jikinta tayi daga na likitan ta juya masa baya alamar ko ganinsa bata son yi hawaye na zuba idonta, ji take kamar numfashinta zai dauke kamar ko da yaushe, ta fashe da matsanancin kuka ta dafe trunk din bishiyar dake gefenta, ko amsa gaisuwan likitar bai yi ba ya juya ya fice daga garden din, da sauri likitan ta kamota ganin faduwa zata yi, ta fara kokarin zaunar da ita akan lallausan carpet dake shimfide wajen trying to calm her down tace "Haba kanwata, me yasa baza ki cika min alkawarin da kika daukar min ba?" Muryarta na rawa tace "Kiyi hakuri bazan iya ba wallahi" Rungumeta likitan tayi tana bubbuga bayanta a hankali wani mugun tausayinta na shigarta, tayi attending to different cases in her career as a medical Doctor amma babu wanda ya taΙ“a daga mata hankali ya tsaya mata a rai irin na baiwar Allahn nan, she wish she can take away her pains, she wish she can make her happy once more, she wish she can make her forget the past and face the present, a hankali likitar tace "Halysaah...." khaleesat ta daga rinannun idonta tana kallon likitan, likitan tace "Kiyi hakuri Halysaah, kiyi hakuri" Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, likitan ta daga ta tana rike da hannunta suka bar garden din zuwa babban compound din gidan.

 

 

Few years back!

 

"Talk to Abdul about it, nasan bazai taΙ“a yarda da haka ba, and he will definitely find a way out for u immediately..." Khaleesat ta daga manyan idanuwanta tana kallon kawarta Safiyyah, kamar bazata ce komai ba sai kuma ta sauke idonta a hankali tace "That will be another huge burden Safiyyah, u know how expensive apartment can be in this state, gida da akwai tsada sosai, kuma na fa ce maki ni bazan sake tambayarsa komai ba, ko kuma ince yayi min wani abu...." Safiyyah tace "Cabdi, to in ba ki tambayesa ba kina da wanda zaki tambaya? Balle ma kinsan halinsa lokaci daya tsaf zai juya situation din nan against you, i think gwara kawai ki sanar masa yafi maki kwanciyar hankali" Khaleesat tayi shiru tana nazarin abinda Safiyyah ta ce, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai tace "It's fine Safiyyah, ba sai na gaya masa ba i will cope in sha Allah, after all we have just a year and a half to go" Safiyyah na kallonta ta kamo hannunta tace "Ko zaki dawo wajena sai in gaya masu kawata zata zo ta Ι—an zauna da mu zuwa wani Ι—an lokaci?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Let not inconvenience them Safiyyah, kar ki damu kawai, i will sort my self out...." Safiyyah tace "No, i will talk to Ya Musty about ur current situation khaly, nasan bazai ce a'a ba, matarsa ce dai gagarumar er iska, and do i even care? Ba ki ma san me take min ba yanxu a gidan, duk dare bata girki da ni sai dai in nemi abinda zan ci tunda kinsan Ya Musty night shift yake, ni kuma dama kin san i prefer junk food, kawai sai in hada cornflakes in sha abu na" Khaleesat tayi murmushi tace "Shine kike son in bi ki zuwa gidan a haka ko? You are very funny" Safiyya ta juya ido tace "So what? Naga ai ba kanta zaki zauna ba in kin dawo gidan, Yaya Mustyn nan fa is my cousin brother ko kin manta ne? Saboda haka ko taki ko ta so dole in zauna a gidan har in gama karatuna, very wicked and self centered woman, wallahi kar ki wani damu in dai nayi ma Ya Musty magana kawai ki dauko kayanki ki dawo gidan ko zuwa gobe ne...." Khaleesat tace "Aa gaskiya don't even start that Safiyyah, i will cope with my present situation with time, nasan zan saba gradually, beside it's something that is normal kawai dai ni ce nake damun kai na saboda addinina da culture dina da dai wasu abubuwan da baza a rasa ba, any way... it's fine Safiyyah" Tana fadin haka ta kalli wayarta dake hannunta jin shigowar notification, tace "I think my Lyft is here Sophie, sai gobe in Allah ya kai mu" Safiyya ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk then, take care of ur self, i will stroll home too" a haka suka rabu, Khaleesat ta nufi Lyft din da tayi ordering zai maida ta gida. Khaleesat na kitchen wajen karfe goma na dare ta gama girka Noodles da zata ci for dinner kenan taji alamar an bude kofar parlor, a hankali ta karasa juye Indomie dinta a plate ta dau fork ta saka sannan ta wanke pot din ta ajiye, ta bude fridge ta dau bottle water ta fita daga kitchen din, hanyar dakinta ta nufa direct, dai dai corridor aka bude kofar wani room that is just few steps away from her own room, ko kallon direction din bata yarda tayi ba tana kokarin bude kofar dakinta taji ance "Hi, good evening, we didn't get to meet when i was here in the morning I guess you've already left for school then, you can call me Jay, and i am ur new House mate, I moved in this morning...." Sai a sannan Khaleesat ta juya ta kallesa amma bata ce komai ba, ya gyada mata kai yace "Jay" babu yabo babu fallasa tace "I see" Ganin zata shige daki yace "A minute pls" Ta juya ta sake kallonsa da wani expression, a takaice yace "Ke bahaushiya ce?" Ta Ι—an hade rai tace "I don't know what u are talking about" Yace "Oh ohk, i am asking for a permission..." Ita dai kallonsa kawai take, Ya gyara tsayuwarsa yace "As u can see it's late already now, can i use some of ur portable water and Beverages before i get mine tomorrow if you don't mind?" Khaleesat ta dauke kanta a takaice tace "Ohk" Yace "Alright" Daga haka ta shige dakinta ta kulle kofar ta saka key, ko da ta gama cin Indomie din bata ji zata iya bude kofa ta fita kai plate din kitchen ba, daga karshe kawai ta bar shi a wajen bayan ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta dauro alwala ta fito ta zauna edge din gadon dakin ta dau wayarta, Miss calls din Abdul ta gani har biyu wanda yayi mata tun karfe shidda, ta sauke ajiyar zuciya tana duba agogon wayarta dake nuna mata karfe goma da kusan rabi, meanwhile karfe kusan biyar kenan na asuba agogon Nigeria, bude WhatsApp dinta tayi ta dubasa taga yana online, hakan yasa ta masa WhatsApp call, yana dagawa tayi kasa da murya ta gaishesa a hankali, Bai amsa ba yace "Yanzu kika ga kirana?" Ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Kayi hakuri, yanzu naga kiran wallahi" Yace "You mean tun daxu wayarki baya gun ki kenan?" Tace "Not really, tun dai da na dawo schl nake karatu, in few months time zamu fara exams" Yace "I see, shi ne yasa kika ga ban yi deserving lokacin ki ba don zaku fara exams, ta yaya ma wayarki zai yi ring ki ce baki sani ba in ba rainin hankali ba?" Rasa abinda zata ce masa tayi, don wayar a silent yake kuma ya hanata barin waya a silent on several occasions, to avoid further issues sai bata ce masa wayar a silent yake ba, a hankali tace "Kayi hakuri, wallahi ba haka bane, i am sorry..." Yace "Sorry for ur self, malama so nake ki gaya min kina ina har wayarki rang twice baki ji ba? ur lectures today terminated by 4pm Baltimore time, so ina kika je daga nan?" Ta rufe ido ta bude don ta fara gajiya da tuhumar tasa, After few seconds ta marairaice tace "Ina parlor ne ina karatu, wayar kuma na daki" Yace "Kin fara zaman parlor kenan, when did that start? House mate din taki ta dena shigowa da saurayinta ne gidan?" sai da gaban Khaleesat ya fadi, A hankali tace "Bata nan, taje LA jiya"  Yace "Sau uku kenan ina kiranki a satin nan baki dagawa sai sanda kika ga dama ki biyoni, that nonsense shouldn't repeat it self again, a kanki aka fara karatu ko ni zaki gaya ma karatun Exams?" Shiru Khaleesat tayi lkci daya hawaye ya cika idonta, a Ι—an fusace yace "Baki ji na ne?" Cikin sanyin murya tace "Naji, kayi hakuri hakan bazai sake faruwa ba in sha Allah" Yace "Good, you can go to bed" Tana goge hawayen da yaki tsaya mata tace "Nagode, sai da safe" Shi ya katse call din ta ajiye wayarta gefen gadon ta dora kanta a pillow hawaye na zuba idonta, after a while ta mike ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta dawo ta kashe wutan dakin tayi addu'an bacci ta kwanta....  Washegari Friday da wuri Khaleesat suka gama lectures dinsu, suna zaune a exact spot din jiya ita da Safiyyah dake waya, sosai Khaleesat tayi nisa tunanin da take har bata san sanda Safiyyah ta gama waya ba, dafa kafadarta da Safiyyah tayi ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta shiga, Safiyyah tace "What is wrong Khaleesat, ina ta magana baki ma san ina yi ba, tunanin me kike haka?" Khaleesat ta Ι—an kirkiri murmushi tace "Kawai ina kewar Ummanmu ne da siblings dina" Safiyyah ta girgiza kai tace "Ban yarda ba, there is definitely something that is bothering you" Khaleesat ta kauda zancen tace "Ke da George ne ke waya ko?" Safiyyah tayi kasa da murya tace "Pls gobe weekend ki shirya mu tafi Virginia Leesat, George is throwing a party for his birthday tomorrow, kuma za mu je Beach, don Allah kar ki ce a'a, we need to take a break and rest our brain, ba ko da yaushe karatu ba kamar mu muka kawo boko duniya...." Khaleesat dake ta kallonta tace "Ke yanzu sai ki kama hanyar Virginia Safiyyah??" Safiyyah ta hade girar sama da ta kasa tace "To menene, it's just a 4 hours ride from Maryland, kamar fa ace daga kaduna zuwa kano shi ma in mota bai yi gudu ba, pls for once ki zama social mana Khaleesat, ke baki gajiya da zama guri daya ne a kasar nan? Baki gajiya da karatu? ranan Monday fa za mu dawo in sha Allah, kuma babu wanda zai san mun je wani Virginia, dama Ya Mustapha na riga na gama plan din abinda zan ce masa, ke da ba ma ki da wanda zai sa maki ido kike mis using opportunities haka, da mun koma Nigeria fa shikenan, tafiyar nan maza ne hade da mata" Khaleesat ta girgiza kai tace "Lallai... Ni dai ina baki shawara kar ki je Safiyyah" Safiyyah tace "Bana ma son shawaran, abinda mu goma za mu je" Khaleesat tace "Toh Allah ya tsare hanya ya dawo da ku lafiya" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Baza ki je ba kenan dai?" Ba tare da Khaleesat ta kalleta ba tace "Kema kin san bazan je ba ai" Safiyyah tace "Ke kika sani, mu dai za mu je wallahi" Safiyyah na kai wa nan ta mike tace "Sai ran Monday" Khaleesat na kallonta a hankali tace "Wai tafiya za ki yi? Da sauran time fa Safiyyah" Safiyyah tace "Aa toh me za mu zauna yi a schl bamu da aji? Yau kuma kece ke cewa da sauran time duk son ki da komawa gida da wuri? Ikon Allah" Khaleesat ta kasa cewa komai, ita har ranta take jin ta tsani gidan nata yanzu, she no longer see the home as her comfort zone, and she don't think she can cope staying together with an Hausa Guy under same roof, da ma bature ne ko kadan bazata damu ba kamar yanda ta damu yanxu, har ta taho school bata hadu da sabon Housemate din nata ba da safe, Safiyyah ta Ι—an buda ido ta koma ta zauna tace "Ohh now i remember, wai saboda new House mate dinki? To wai ke meye damuwarki ne da shi? Yayi harkan gabansa kiyi naki ne fa a gidan, ko magana in baki son ya maki you just call the cops a maki iyaka da  shi, just dial 911 and that's all, balle nasan kilan da kyar aka kukuta masa ya taho makaranta kasar nan to kuwa ina zai tsaya bata lkcnsa akan abinda ba shi ya kawo sa ba, don dai in wani Shege ne shi bazai zauna a shared apartment ba a USA, kuma 'ya yan masu kudin nan sun fi iskanci su kuwa talakawa abinda ya kawo su kawai suke yi, kiyi ta kanki kawai shi ma yayi ta kansa, kar kiyi mamaki ta scholarship ya zo kasar ma" Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah ta kyabe baki tace "Tashi mu je gidan, ni banda Ya Musty bazai yarda ba da ba sai in tattaro in dawo gidan naki ba mu zauna kawai" Khaleesat ta marairaice tace "Plss ki sake masa magana ko zai bar ki mana, ai sanda ya hanaki kinga bamu dade da fara makarantar ba" Safiyyah tace "Kar ma ki bata bakinki mutumin nan bazai yarda ba, tashi mu je in raka ki, in House mate din ma yaga kina wani yin abu a tsorace renaki zai yi wallahi, yi zaki yi kamar kema er gari ce kawai sai ki ga ya fara shakkar ki a gidan" Khaleesat ta mike tace "Kar fa muje kiyi ta Hausa, just pretend we are not Hausa" Safiyyah tayi dariya tace "Kece dai is not Hausa, ni kam Bahaushiya ce cikakkiya kuwa" A haka dai suka bar makarantar suka nufi gidan da Khaleesat take.... Khaleesat ta bude handbag dinta ta ciro makulli ta bude kofar shiga gidan suka shiga parlor Safiyyah na biye da ita a baya, Safiyyah na gyada kai jin wani kamshi da parlon yake tace "Da alama bai dade da fita ba ma" Khaleesat dai bin parlon take da kallo ganin duk reading materials dinsa ne saman kujera ya tula a kai, Safiyyah tace "Kinga don Allah ki saki ranki ki ci gaba da harkokin ki Khaleesat, a Maryland fa kike a Amurka ba Kano Nigeria ba, ki dinga abu irin na wayayyu mana pls" Wani kallo Khaleesat tayi mata ta ajiye handbag dinta tace "Ance maki in bature ne ko wani yare ni zan damu, kawai my issue here is about him being a Hausa Guy, har fa tambayata yayi jiya ko ni bahaushiya ce" Safiyyah tace "Ohh kun ma yi magana kenan...." Khaleesat tace "Ni ban kulasa ba kuma ban nuna masa ni Bahaushiya bace, i will just pretend i am from Morocco" Safiyyah ta dinga dariya har da saukowa daga kan kujera tace "Gashi kuwa an ma fi saninsu da fararen mata kyawawa na ajin karshe, tsaf zai yarda daga can kike, kinga da larabci ya zauna daram a bakinki sai kiyi ta zabga larabci nasan ba lallai yana ji ba, daga haka zai kama kansa yayi zaton ke balarabiyar gaske ce... sai ma Abdul yaji kuna gida daya da Bahaushe kilan Baltimore yayi maku kadan wallahi, shi sa nace ki gaya masa kika ki" Khaleesat ta ajiye jakarta bata sake kallon Safiyyah dake ta dariya ba tayi wucewarta kitchen tana tunanin me zata dafa masu dama ko breakfast bata yi ba ta fita daga gidan, tsaye tayi kitchen din tana kallon cartons din bottle water kusan bakwai wanda duk yafi tsada a state din, sai kuma ta juya ta kalli beverages masu yawa da ya ajiye kan cabinet, ta karasa cikin kitchen din ta bude babban fridge zata dau kwai da za ta dafa masu Noodles, kallon fridge din ta dinga yi ganinsa fully stocked with everything, tun daga tsadaddun drinks kala kala, fresh milk, varieties of fruits, with many eggs, muryar Safiyyah taji a bayanta tace "Kai kai kai, shi ya zuba abubuwan nan a fridge Leesah?" Khaleesat ta juya ta kalleta looking speechless, can dai ta dau eggs din da zata dauka ta kulle fridge din ta tafi inda foodstuffs dinta suke shi ma taga kayan abinci ya siyo, Safiyyah ta rike haΙ“a tace "Duk a kudin scholarship din yake facakan nan? Ko dai bashi da hankali ne bai san bin komai ake a sannu a kasar nan ba" Khaleesat dai ta dau Noodles dinta ta bar wajen tana kallon Safiyyah tace "Ga Indomie ki dafa mana, ina son inyi magana da Ummanmu kafin Aunty Sha'awa ta fita kasuwa" Safiyyah tace "Ohk to" Khaleesat ta bar kitchen din ta dau jakarta ta wuce dakinta, WhatsApp dinta ta bude ta shiga contact din makociyarsu Sha'awa tayi mata voice note kamar yanda ta saba a duk sanda take son magana da Ummanta. Sai kusan karfe hudu na yamma Khaleesat ta raka Safiyyah zuwa gun Lyft din da tayi ordering don tun daxu Cousin brother dinta ke kiranta ganin bata dawo gida ba, Safiyyah ta shige motar ta kulle tana daga ma Khaleesat hannu, sai da Lyft din ya bar wajen sannan Khaleesat ta juya tana tafiya a hankali ta nufi apartment dinta, dai dai apartment din taga mota yayi parking a space din da aka tanadar don parking for that apartment, bata karasa ba ta jingina jikin fence din dake inda take tsaye tana kallon motar ta little space din dake between the wooden fence din, taga ya fito daga motar ta bi sa da ido har ya shiga apartment din yana danna wayarsa, ta fi minti biyar tsaye a inda take, daga karshe tana tafiya a hankali ta karasa apartment din ta murda kofar parlon taji ya kulle, hade rai tayi tana kallon kofar, daga karshe da ta gaji da tsayuwa kawai tayi knocking, sau uku tana knocking sannan ya bude kofar, yana ganinta yace "Hi" ita dai ko kallonsa bata yi ba fuskarta babu yabo babu fallasa ta bi gefensa ta shiga parlon, direct gun wayarta dake kan kujera ta nufa ta dauka tare da reading materials dinta dake saman kujeran, har zata dakinta sai kuma ta dawo ta tafi kitchen ta dau goran ruwa daya sannan ta nufi dakin, sai da ta bude kofar tayi masa kallon gefen ido taga he is just busy sorting out some textbooks that were inside a carton he came with, har ta shiga dakin nata bai juya ba balle ya kalli direction dinta....

 

 

07087865788✍🏻

[4/29, 5:07 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: https://chat.whatsapp.com/KVY8hjs3iNq5ntSN4Z5g6V

 

 

 

✨✨ HALYSAAH ✨✨

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

2.....

 

Washegari har karfe sha daya Khaleesat na dakinta bata fito ba duk da yunwan da take ji, tayi tagumi don gaba daya ta ma rasa what is her problem particularly, ta dau wayarta jin shigowar WhatsApp message, tun daxu suke chatting ta VN da Ummanta ta wayar makociyarsu Sha'awa, da taji shiru ta ma zata an maida ma Aunty Sha'awa wayar nata ne, ta bude VN din tana sauraren voice din mahaifiyarta, Addu'a Ummanta ke mata tana mata fatan nasara a karatun ta, sannan kamar ko da yaushe ta sake jaddada mata ta kula da mutuncinta ta kula da kanta, daga karshe ta Ζ™are da cewa za a kai ma sha'awa wayarta don zata fita kasuwa, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayar a hankali sannan ta mike ta dau hijab din sallanta ta saka ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita daga dakin don ta gaji da horan kanta da yunwa ita da ke breakfast da wuri, kitchen ta tafi almost bumping into her new House mate shi kuma yana kokarin fitowa daga cikin kitchen din, komawa baya yayi at the same time yace "Good morning" Bata yarda su hada ido ba ta matsa gefe allowing him to pass, ya fito daga kitchen din yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan ta shiga ciki, tsaye tayi tana kallon littered cups da plates din da yayi amfani da su ya bari a sink din wanke wanke without washing them, ga bowl din fruit salad da shi ma ya ajiye bai sha ba, bin kofar kitchen din tayi da kallon mamaki, to wa ya bari yayi masa wanke wanke? Ta fi minti daya tsaye a inda take da tunani iri iri a ranta, wata zuciyar ta ce mata kawai tayi abinda ya kawota ta fita daga kitchen din ta bar unclean utensils din a yanda ya bar su, amma dai kawai ta jawo liquid wash da sponge fuskarta a daure ta fara wanke kayan wanke wanken kawai, bayan ta gama ta goggoge kitchen din ta hada shayi ta debi cookies a plate sannan ta fita daga kitchen din ta wuce dakinta. Wajen karfe uku Khaleesat ta fito daga dakinta, tun da ta gama breakfast take karatu sai sallah kawai ta tashi tayi da azahar, jin ko ina shiru and to be sure baya gidan ta nufi kofar parlon zata bude taji an kulle da makulli, dakinta ta koma ta dauko makullinta ta bude kofar tana duba garage taga babu motarsa a ciki, komawa cikin gidan tayi ta kulle kofar sannan ta tafi kitchen, tun shekaranjiya take son cin shinkafa da miya amma kasancewar she is not comfortable tun da ya dawo gidan yasa ta hakura da girkawa, yanzu da taga baya nan kawai tayi deciding tayi shinkafa da miyar, bayan ta daura shinkafar, ta fara hada miyar dama tana da sauran chicken thighs a fridge, fitowa parlor tayi da sweeper zata yi shara, ta ajiye sweeper din hannunta to tidy the couch first, dukawa tayi tana kallon takardun Housemate din nata da ta gani, sai kuma ta kyabe baki ta bar su nan yanda ya bari a kan kujeran, share rug din parlon ta fara yi bayan ta dauke makullin da ta gani a kasa, ta dinga juya makullin ganin kamar na Bedroom ne, kafin minti arba'in ta gama girkin da take ta tsaftace ko ina na gidan, ta debi abincinta ta tafi daki da shi, sai da ta fara yin sallahn Asr sannan ta dau wayarta tana dubawa, sosai gabanta ya fadi ganin miss call din Abdul, nan da nan taji abincin ya fita ranta gaba daya, ta zauna gefen gado a hankali tana kallon wayar, ta fi minti goma zaune a haka, she was soo worried, to yanzu me zata ce masa ma in ta kirasa, daga karshe ta daure tayi dialing number nasa, har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai daga ba, duk da yunwan da take ji haka nan taji abincin ya fita ranta, ta tsani duk wani abu da zai sa Abdul ya daga mata hankali, haka tayi forcing din kanta ta ci abincin sannan ta kwanta side din gado, bata san sanda bacci ya dauketa ba a haka.... knocking kofar dakinta da ake yi ne ya farkar da ita daga baccin da take, ta mike zaune da kyar tana murza idonta tana kallon kofar at the same time tana mamakin me zai sa ya dinga bubbuga mata kofa haka, to ko dai bashi da kai ne?? ta jawo wayarta tana duba agogo taga karfe shidda da mintuna, bata yi tunanin ta dade tana bacci haka ba, sake knocking da aka yi yasa ta mike tsaye ta saka hijab fuska daure tace "What is that??" Ta ji yace "Ohk i think i misplaced my keys, just want to know if you saw it while tidying up the parlor?" Sai a sannan ta tuna makullin da ta gani a parlor daxu da take shara, tana tafiya a hankali ta karasa kofar dakinta ta murda key din jiki sannan ta bude door din, tuni har ya bar corridor din ya koma parlor ya tsaya yana jiranta, da alama dawowarsa gidan kenan a lkcn, ta karaso cikin parlon ba tare da ta kallesa ba, shi dai duba message din da ya shigo wayarsa yake with all his attention, ta tafi inda ta ajiye makullin sannan ta dawo ta ajiye masa kan takardunsa dake kan kujera tace "Here" Yace "Ohk" dakinta ta koma ta shiga tana mamakin wai Ohk, ba ma thank you ba kamar irin ya ajiyeta din nan, kwafa tayi ta saka ma kofarta key, bayan Khaleesat ta idar da isha ta sake kiran Abdul bai daga ba, sau hudu kenan tana kiransa tun karfe bakwai bai yi responding ba, yanzu dai tafi tunanin yana bacci don dare ne sosai a can kasar, even at that tasan she is in soup, mikewa tayi ta dau plate din da ta ci abinci daxu ta nufi kofa ta fita daga dakin, a parlor ta ga sabon Housemate dinta yana tattara takardunsa at the same time yana answering phone call taji yana cewa "I am on my way now" Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa ya dau takardunsa da makullin mota ya mike tsaye, ido hudu suka yi for the first time tunda ya dawo gidan, ita dai ta dauke kai kamar bata ma gansa ba ta karaso cikin parlon zata tafi kitchen taji yace "I ate a little out of the food you cook, and...." Yayi pointing takeaway din da ke kan kujera yace "I am taking some to my frnd too" duk wannan abun bai kalli inda take tsaye ba yake magana, sai ita ce ma da ta dinga kallonsa da mamaki babu ko kiftawa, ya dau takeaway din ya nufi kofa cikin hanzari, yace "Good night" Ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle gidan da makulli ta waje, mamaki yasa ta kasa karasawa kitchen din, after some seconds ta tafi kitchen din, da plate din da ya ci abincin, da cup din da ya sha coffee, da bowl din da ya sha fruits salad duk suna ajiye a sink babu wanki, ta jingina da kofar kitchen din ta rungume hannu tana kallon sink din kamar zata fashe don bakin ciki, can ta karasa ciki tana duba shinkafar da ya bar mata, taga da kyar in zai yi spoon uku, gashi duk yayi littering din wajen da shinkafar wajen diba kuma ya bar shi haka, haka nan ta juye er shinkafar da ya rage a karamin bowl, ta wanke duk utensils din, ta gyara ko ina ta goge sannan ta hada shayi ta koma daki da bowl din sauran abincin, zaunawa tayi gefen gado ta dau wayarta tayi dialing number Safiyyah, sai da ya kusa katsewa Safiyyah tayi picking daga daya bangaren tace "Allah da gaske baki da kirki Khaleesah, to ko baki kira ba dai na isa Virginia cikin koshin lafiya" Khaleesat ta Ι—an yi murmushi tace "Dama nasan kin isa lafiya ai, hope you are doing good?" Safiyyah ta tabe baki tace "Oho dai, wannan ba matsalar ki bane" Khaleesat tace "Amma don Allah ina kika ce ma Ya Musty za ki?" Safiyyah tace "Ahaf tsaya wasa, sai kace baki san ni ba, munafukar matarsa da yake ba son zamana a gidan take ba ita ce ma ta kara convincing dinsa, duk zatonsu ina gidanki muna group reading with some of our Coursemate" Khaleesat tayi murmushi tace "To ai shikenan, yanxu yaushe zaki dawo?" Safiyyah tace "Gobe ne birthday din ai, in sha Allah i will be back on Monday" Khaleesat tace "Toh Allah ya kai mu, kinsan mene?" Safiyyah tace "Aa" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi in gaya maki Abdallah ne ya kirani nayi missing call dinsa as i am speaking to you now tun daxu nake  kiransa yaki picking, nasan fushi yayi sosai, ni kuma...." Safiyyah ta dakatar da ita tace "Ke kuma me? Shikenan rayuwa babu uxuri dama?" Khaleesat tayi kasa da murya tace "He warned me times without number kar in sake missing call dinsa Safiyyah, kuma wallahi ina kitchen sanda ya kira wayar kuma na daki ba da gangan nayi missing kiransa ba" Sounding so pissed off Safiyyah tace "Wai don Allah me yasa kika dauki tsoron duniya kika dora ma mutumin nan ne Khaleesat? For how long will things continue this way? Yaushe za ki fara nuna masa ke fa mace ce? yanzu haka za ku yi auren ya maida ki slave a gidansa tunda kin nuna masa kina mugun tsoronsa tun a waje? wannan wani irin gantalallen relationship ne? Gaskiya ina jinjina maki Khaleesat, don wallahi in nice bazan iya ba Allah ma ya gani sai dai duk abinda zai faru ya faru" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "I have no choice nor option Safiyyah...." Tana fadin haka hawaye ya fara gangarowa idonta, a Ι—an fusace Safiyyah tace "To wai ke kadai ce mace a gidanku ne da ya gani? Naga ga Labibah da Lamisah, ina ce sati biyu kika ba Labibah a shekaru, ita kuma Lamisah wata daya, ga kuma yayyinki Samira da salamatu, to wai halan su ba mata bane sai ke??" Khaleesat dai bata ce komai ba tana goge hawayen dake zuba idonta, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai shikenan, but u really need to speak up for ur self Khaleesat, ni dai nasan their worst mistake is sending you to school abroad, aje dai zuwa, ke kuma in har baki waye kin kwatar ma kanki 'yanci daga karshe ba to sorry to say this, wallahi u will live a miserable life in the nearest future Khaleesat, this is just the fact i am saying, na gaji da lamarin so called Abdul din ki" Cike da karfin hali Khaleesat tace "Ki daina cewa haka pls Safiyyah, ke me tayani addu'a ce kan Allah ya kawo min komai da sauki amma ba ki dinga fadin wa ennan maganganun ba...." Safiyyah ta taΙ“e baki bata dai ce komai ba, a hankali Khaleesat tace "Pls ko zuwa gobe da safe ki masa magana ta Whatsapp ki tayani basa hakuri cause nasan bazai daga kirana ba no matter what..." Safiyyah tace "To naji, Allah ya kai mu goben" Khaleesat tace "Ameen" Sallama suka yi, Khaleesat ta ajiye wayarta. Karfe goma saura na safe Khaleesat ta fito daga dakinta rike da wayarta don kar ma Abdul ya kira by mistake tayi missing call dinsa, tun jiya take makale da wayar duk don kar ya kira bata sani ba, kuma sau uku tana kiransa bayan da tayi sallan asuba bai daga ba still, yanzun ma da ta tashi sae da ta kirasa sau daya nan ma no answer, zaune taga new Housemate dinta a Ι—an reading nook da aka tanadar a living Room din studying with a huge textbook dake gabansa, she had no idea ma ya shigo gidan, don bayan da tayi sallan asuba ta fito ta hada shayi ta sha da cookies a nan parlon sannan tayi karatu har zuwa bakwai na safe, daga nan ta shiga daki ta kwanta sai kuma yanzu da ta tashi feeling hungry, sau daya ya kalleta yana ci gaba da duba Textbook din gabansa yace "Good morning" Ta karaso cikin living room din a takaice tace "Ok" Ajiye wayarta tayi kan 1 sitter ta nufi kitchen, Ya daga kai yana kallon direction din da ta bi da harshen turanci yace "In baki yi breakfast ba, ga wani nan ki dauka....." Tsayawa tayi sai kuma ta juya ta kalli Centre table da yake nuna mata,  ledan abinci ne kan table din duk da bata san wani kalan abinci bane a ledan, ta kallesa taga ya ci gaba da karatun da yake, girgiza kai tayi with no interest tace "No, tnx" Daga haka tayi wucewarta kitchen, ta fi minti uku tsaye kitchen din tana tunanin me zata yi, seeing her House mate sitted in the living room yasa ta zama uncomfortable to cook anything, hakan yasa kawai ta dauko kwalin cereals da bowl zata hada cornflakes, wayarta ta ji yana ring a parlor don tun jiya ta cire wayar a silent, bata san sanda ta saki both d bowl and the Cereal din hannunta ba ta fito daga kitchen din within few seconds, House mate dinta ya bi ta da kallo har ta nufi gun wayarta ta dauka da sauri, sai da gabanta ya fadi ganin Abdul ne ke kiranta, babu bata lokaci ta daga call din, zuciyarta na bugawa tayi masa sallama, jin shiru tace "Hello" kallon wayar tayi ta sake maidawa a kunnenta har sannan bata daina cewa Hello ba, House mate dinta dai ya ajiye Textbook dinsa gefe ganin yanda ta rude ya maida duk concentration dinsa akan ta, Khaleesat ta sake kallon Screen din wayar jin shiru Abdul ya ki ce mata komai kuma tana jin maganar mutane a background, marairaicewa tayi ta duka nan kasan living room din ta saka wayar a handsfree tace "I know u can hear me pls, don Allah kayi hakuri, i am making u this promise hakan bazai sake faruwa ba wallahi, don girman Allah kayi hakuri" Sai a sannan yayi magana da husky voice yace "Hold on to ur promise malama, sau biyar kenan kina missing call dina within a short period, are you out of ur senses or is anything wrong with ur brain?" Da sauri ta girgiza kai kamar zata yi kuka tace "Wallahi ina kitchen ina girki san da ka kira jiya, kuma...." Cutting dinta yayi yace "ke, bana bukatar jin komai daga gare ki, none of ur lies and excuses will convince me, naga kamar u are beginning to take me for granted this days.... Kinsan Allah kika sake missing call dina zaki sha mamakina wallahi cause it will take me nothing to be in America...." Hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Amma me yasa baka min uxuri?" Yace "Baza ayi uxurin ba, ni za ki gaya ma uxuri? A kanki aka fara karatu?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Wato ke kin fi karfin ki bude baki ki bada hakuri ko" Kasa cewa komai Khaleesat tayi don tun da ta daga kiransa ta fara basa hakuri bata kuma san wani hakurin yake nufi ba, A takaice yace "Anyway, i called to warn you to stop disturbing me with unnecessary calls, na biyu kuma ki ja ma kawarki kunne she should never come into my DM and tell me nonsense again don zan dau mummunan mataki a kanta, ke kuma duk sanda yayi suiting dina i will call you, don't try calling my line again" Yana kai wa nan ya katse wayar, Khaleesat ta dinga kallon screen din wayar hawayen dake makale idonta ya gangaro, House mate dinta ya Ι—an yi murmushi wanda iyakarsa lips after paying attention to their conversation, mikewa Khaleesat tayi tana share hawayen dake sauka idonta, sai a sannan ta lura da shi a parlon, dauke kai tayi da sauri bayan sun hada ido, gaba daya ta ma mance yana parlon, taji yace "Is that ur Father?" Wani kallo ta jefa masa tayi wucewarta dakinta wasu sabbin hawayen na zuba idonta, ruf da ciki tayi kan gadonta tana kuka har da shessheka, ta kusa minti arba'in kwance a yanda take, zuwa sannan ta dena kukan da take kawai ta lumshe ido, knocking din kofar dakinta da taji anyi at the same time aka bude ne yasa ta mike zaune da sauri don bata san bata kulle kofar ba, hada ido suka yi da new Housemate dinta, yayi dropping ledan hannunsa ya jingina jikin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonta da kyau, calmly yace "Like seriously, Namiji kika kwanta kike yi ma kuka?" Ta wani hade rai ta kauda kanta zuwa wani direction din daban, how did he even know she understands Hausa?? yana juya counter din hannunsa as if counting his words yace "It's... funny" Ta juya ta kallesa har sannan fuskarta a daure tace "Excuse you, why will u barge into someone else's bedroom just like that?" Ya daga kafadarsa yace "Zan yi shisshigi in baki shawara ni dai, run for ur dear life cause u are dating a monster as a boyfriend" Yana kai wa nan ya juya ya fita daga dakin closing the door behind him, Khaleesat ta dafe kanta da yayi mata nauyi, daga karshe ta mike ta kulle dakinta da makulli sannan ta shiga bandaki, karfe sha biyu da yan mintuna ta gama shiryawa don wanka tayi, kallon ledan da ya ajiye mata tayi ta dauke kai sannan ta nufi kofa ta bude ta fita, satan kallon kofar bedroom dinsa tayi ta karasa living room, tana tafiya a hankali ta tafi kofar parlon ta murda taji a kulle an sa makulli, leka windon parlorn tayi taga babu motarsa a garage alamar ya fita, tana tafiya a hankali ta shiga kitchen, ta jingina da kofa tana kallon Cereal da bowl din da ta dauko daxu an ajiyesu kan cabinet din kitchen din, juyawa tayi ta fita daga kitchen din ta koma dakinta, ledan da ya ajiye mata ta dauka ta zauna kan kujeran dake dakin tana duba abinda ke cikin ledan, Breakfast Sandwiches ne sai fresh fruit smoothie a ledan.....

 

 

07087865788✍🏻

[4/30, 5:36 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: https://chat.whatsapp.com/KBwGIidDZY683SzzudJ0zc

 

 

 

✨✨ HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

3.....

 

 

Bayan magrib Khaleesat ta fito living room saboda yunwan da take ji, har sannan bata ji alamar House mate din nata ya dawo gidan ba, gaba daya haka ta wuni ranan babu walwala, all of a sudden yau ta ji a zuciyarta ta fara gajiya da attitude din Abdul da abubuwan da yake mata, da ta tuna Housemate dinta overheard all her conversation with Abdul da kuma maganar da ya gaya mata sai taji wani bakin ciki da takaici ya tokareta at the same time tana wishing that never happened, zaunawa tayi kan kujera ta jinginar da kanta jikin kujeran ta afka duniyar tunanin rayuwarta, after a while ta sauke ajiyar zuciya ta mike tana tafiya a hankali ta shiga kitchen tana tunanin abinda zata dafa ta ci, absently ta fara wanke few utensils din da yayi amfani da shi ya bari a sink sannan ta kunna gas, stir fry pasta ta girka, bayan ta gama ta debi kadan da zata ci ta fita daga kitchen din, dai dai corridor din dakunan ta kusa cin karo da House mate din nata, a firgice tace "Innalillahi...." Sai kuma tayi shiru ta hade rai, ya koma gefe yana kallonta, har ranta taji tsoro don bata san yana gidan ba amma tayi pretending ta hanyar daure fuska, ya daga kafada ya bar wajen ta bi sa da kallon gefen ido.... reading nook dake cikin living room din ta ga ya nufa yana kwashe takardunsa dake kan table, ta dauke kanta ta shiga cikin dakinta ta kulle da makulli, karfe takwas da few minutes ta gama duk abinda zata yi ta dauro alwala sannan kwanta don gobe Monday tana da aji da safe, tana lumshe ido bacci ya dauketa. Cikin bacci Khaleesat taji ana knocking kofar dakinta, ta mike zaune da kyar tana murza ido ta jawo wayarta tana kallon agogo taga karfe goma saura minti biyar, kallon kofar tayi da mamakin dalilin da yasa yake mata knocking by this time, can dai ta daure fuska tace "Waye wannan?" Taji yace "I could use ur help if u don't mind" Bluntly tace "I beg ur Pardon?" A takaice yace "Nayi misplacing makullina again" Da farko rasa ma me zata ce masa tayi don mamaki, she was mute for almost a minutes, taji yace "Hello" Sosai ta hade rai tace "I don't understand kayi misplacing makullin ka?" Yace "Look, ni fita zan yi yanzu idan na fita sai ki kulle gidan" Bata san sanda tace "Idan fita zaka yi ka fita mana, me yasa zaka tambayeni makulli? ko makullinmu a hade yake?" Shiru yayi at first, sai kuma yace "Ta yaya zan fita nace maki ban ga makullin kofa ba" Tace "But our keys are separate isn't it?" Yace "Sai yanzu da kika fada na sani ai, fito ki bude min kofa zan fita" Wani bakin ciki taji ya tokareta, yace "I am waiting at the parlor" Bata tanka sa ba, can tayi tsaki ta sauka daga kan gadonta ta dau hijab ta sa, ta bude handbag dinta ta dau makullinta ta nufi kofar dakin, fuskarta a daure ta bude ta fito ta karasa living room ta gansa tsaye bakin kofar parlon yana jiranta, ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma din wayarsa yake dannawa bai kalli inda take ba, ta karasa ta bude kofar parlon da makullin hannunta tace "You weren't given a needle as key da zai dinga Ι“ata kullum, and i shouldn't be responsible always for someone else carelessness" Shi dai bai ce mata komai ba ya fita without looking at her yace "Na zata ai needle aka bani Housemate" Da ido ta bi sa har ya isa inda motarsa take, wato godiyar da zai mata kenan? Ta gyada kai ta kulle kofar parlon a ranta kuma tayi vow bazata sake masa amfani da makullinta ba sai dai kar ya fita, banda ma rainin hankali me yasa baya misplacing makullin motarsa sai na gida, next time sai dai ya fasa zuwa inda za shi don bazata sake sharing key dinta da shi ba, fuska daure ta koma cikin parlor, sai kuma ta tsaya tana kallon plate din da ya ci abinci ya bari a parlon da container din soft drink ga goran ruwa, tsabar mamaki bata san sanda ta nemi waje ta zauna ba, is this guy okay? After fetching her food without asking for permission he still have the mind to leave the plate for her at the parlor, anyway... she believe he didn't leave it for her, he left it for himself instead, don ko sati daya zai yi bai dawo gidan ba zai dawo ya tarar da plate din at that same spot don bazata daukesa ba, tashi tayi ta tafi daki fuskarta a daure. Da safe Khaleesat ta gama shirin fita makaranta, har a lkcn bata dauke plate din da ya bari a parlon ba, amma fa zuciyarta kawai ta kai nesa don ta tsani ganin abu ba inda ya kamata ba, zata kai cup din da ta sha shayi kitchen taji ta taka makulli a kan ash carpet din parlon, dukawa tayi ta dau makullin tana kallo taga nasa ne, he is just careless, tabe baki tayi ta mike ta ajiye makullin nan kan kujera, ta kalli plate din jiya da ya bari, tsaki tayi ta dauke tare da gwangwanin soft drink din da na ruwa, ta hada da cup din hannunta ta tafi kitchen, bayan Ι—an lokaci ta dawo parlor ta dauki handbag dinta tana duba wayarta, ganin Lyft din da tayi order ya kusa isowa ta nufi kofa ta fita. Wajen karfe sha biyu Khaleesat na zaune tare da Safiyyah warce shigowarta makarantar kenan, Khaleesat na kallonta tace "Kun sha birthday" Safiyyah tace "Oho dai tunda ke baki je ba, yau me ku ka yi a aji?" Khaleesat tace "Nothing much" Safiyyah ta bude handbag dinta ta ciro cake tana mika ma Khaleesat tace "Gashi ba don halin ki ba" Khaleesat tayi murmushi ta amsa tace "Nagode" Safiyyah tace "Kun yi waya da Abdallan ne?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Sophie me kika ce masa ta chat?" Safiyyah ta dau wayarta tayi unlocking cikin few seconds ta shiga DM din Abdul sannan ta mika ma Khaleesat wayar, Khaleesat ta amsa tana duba chat din, it was nothing worth taking personal Safiyyah ta gaya masa a chat din, Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba tana kallon wayar hannunta, Safiyyah tace "Me yace maki halan?" Khaleesat ta mika mata wayarta tace "Nothing, kawai yace min kin masa magana" Safiyyah ta tabe baki tace "Kin dai ga yanda yake amsa min chat din ma kamar wani Ι—an sarki, wallahi Abdallah bai yi deserving dinki ba, u are too good to be Abdul's or to end up with him, Allah ya maki sauyi cikin ruwan sanyi ya kawo maki mafita" a hankali Khaleesat tace "Ki tashi mu je aji" Safiyyah tace "Oh baza ki ce Ameen ba??" Murmushi Khaleesat tayi tace "Wani mafita kenan Safiyyah? Cewa zaki yi Allah ya canza min halayyarsa kawai...." Safiyyah ta tabe baki ta mike tace "Mu je" Khaleesat ta mike suka bar wajen a tare... Khaleesat na sauka Uber din da ya dawo da ita gida ta nufi apartment dinta, dai dai sanda Co-tenant dinta ya fito daga cikin motarsa dake inda aka tanadar domin parking, sau daya ta kallesa ta dauke kai tana ci gaba da tafiyarta toward their apartment, ya bi bayanta yace "I've waited all day long, i forgot some paperwork a cikin gidan gashi zanyi Submitting tun daxu" Ba tare da ta juyo ba tana ci gaba da tafiya tace "Serves you right" Kallonta yake yana biye da ita, ta ciro makulli a jakarta ta bude kofar ta zare makullinta sannan tayi shigewarta ciki ta nufi dakinta da makullin... Bayan Khaleesat ta idar da sallah ta sauya kaya ta fito parlor don daura girki, bata gansa a parlon ba, kuma bata ji alamar ya shiga dakinsa ba, ta nufi tagar living room din tana leka parking space, ganin babu motarsa ta karasa gun kofa ta murda taji a kulle, kallon inda ta ajiye makullinsa daxu da safe tayi taga ya gani har ya dauke, wucewarta tayi zuwa kitchen. Wajen karfe tara na dare Khaleesat ta gama karatun da take ta jawo wayarta ta bude WhatsApp dinta don ganin ko Neighbor dinsu Aunty Sha'awa tayi replying sakon da ta tura mata amma sai taga bata yi reply ba har sannan kuma ta bude message din, ajiye wayar tayi ta mike ta dauke darduman da take zaune kai, ta dau hijab ta saka sannan ta fito parlor zata debi abinci, Zaune taga House mate dinta a parlon yana operating laptop dinsa, without looking at him ta tafi kitchen, after some minutes ta fito, ya daga kai yana dubanta yace "Can i have some of ur food if you don't mind?" Mamaki ma ya bata, har da baza ta tanka sa ba sai kuma ta tsaya tace "Duk na baya da kake diba gaya min kake halan?" Ya Ι—an buda ido yana gyada kai yace "Haka ne kuma fa, i just decided to ask politely today" Bata sake bi ta kansa ba tayi tafiyar ta daki, in har sai tace ya diba to ashe bazai ci ba. Washegari da safe Khaleesat na kitchen tana ma kanta snacks da zata kai school don har yamma suke da Lecture gashi suna da er jarabawan da za su yi ranan da safen, Housemate dinta ne ya shigo parlon, tun jiya da daddare da ya fita sai a sannan ya dawo gidan, har zai tafi dakinsa sai kuma ya tsaya yana kallon Handbag dinta da makulli dake ajiye gefen jakar, karasawa yayi ya dau makullin sannan ya juya ya fice daga parlon gaba daya closing the door gently ya kulle da key, Khaleesat tafi minti sha biyar tana duba makullinta bayan ta fito daga kitchen, tun daga dakinta har parlor zuwa kitchen babu inda bata duba ba amma bata ga alamar makullin ba, she can't even tell ko ta fito da shi parlor, she was so confuse gashi tayi latti, daki ta koma sai da ta birkice ko ina amma babu alamar makullin, how comes will her keys disappear just like that, tunda ta fara karatu a kasar bata taΙ“a misplacing makulli ba banda wani lkci da Safiyyah ta yar mata guda daya, ko gyara dakin da ta birkita bata yi ba ta dawo parlor looking so frustrated, tsaye tayi trying to calm her brain ko Allah zai sa ta tuna inda ta ajiye keys din, ta Ι—aga kai da sauri tana kallon kofar parlon jin ana budewa, House mate dinta ne ya shigo living room din da wasu takardu a hannunsa, sai da ya kulle kofar ya zare makullinsa sannan ya karasa cikin living room din ya ajiye takardunsa kan kujera without looking at her yace "Good morning Housemate...." Bai tsaya yaji amsarta ba yayi wucewarsa daki yana cire jacket din jikinsa, Khaleesat ta bi sa da kallo har ya shige daki ya kulle, zaunawa tayi gefen kujera ta dafe kanta da taji har ya fara ciwo, yanzu ina ta jefar da mukullin nan for God sake gashi lokaci na ta wucewa, after few minutes sai gashi ya sake dawowa parlon, har sannan bai yarda ya kalli direction dinta ba, taga yayi wucewarsa kitchen ya fito rike da ruwan gora ya sake komawa dakinsa ya kulle, wayarta dake jaka ne ya fara ring ta bude jakar ta ciro wayar taga Safiyyah ce, dagawa tayi ta kai kunne Safiyyah tace "Ya baki shigo schl ba har yanzu, duk latti na yau na riga ki shigowa makaranta, ko kin manta muna da test ne" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina sane Safiyyah" Safiyyah tace "Na fa ce akwai tutorial da zaki min kafin mu shiga test din" a hankali Khaleesat tace "Zan taho yanzu" Safiyyah tace "Don Allah ki taho, wallahi ba abinda na sani a course din kema kin sani" Khaleesat ta ajiye wayar bayan Safiyyah ta katse, agogon wayarta ta kafa ma ido, bayan wasu yan mintuna ta mike after gathering courage to do what her mind is telling her, walking slowly ta nufi dakinsa, tsaye tayi tana facing kofar, a hankali ta kai hannu kofar tayi knocking tana turo baki, Yana jin knocking din ya kalli kofarsa, gyada kai yayi letting out a grin, sai da ta sake knocking din sannan yace "Waye wannan?" Exactly yanda take yawan fada, Shiru tayi bata ce komai ba ta kara turo baki, ya mike ya tafi gun kofar ya bude yana kallonta daga sama har kasa da alamar mamaki, tuni ta kauda kai, still keeping a surprise face yace "Madam hope nothing??" Trying to sound a little polite tace "I need you to open the door for me" ya gyara tsayuwa yace "I don't understand, dama a hade makullinmu suke? Where is ur key?" A takaice tace "It's fine, no long talk" Juyawa tayi zata bar wajen, yace "Ko baki ga naki bane?" Ta wani kallesa tace "Banda haka ai da ban zo nan nace ka bude min kofa ba" Yace "Ohh i see, does this mean u are careless too?" Barin wajen tayi ta koma parlor ta zauna, ya gyada kai with smile of satisfaction sannan ya koma daki ya dauko makullinsa ya fito, sai da ya shigo parlon yace "Ta yaya ma zaki yi misplacing a whole bunch of key sai kace allura, this is kind of weird" Daukar handbag dinta tayi ta nufi kofar yana budewa ta fice daga parlon tayi wucewarta without turning her back, ya gyada kai yace "Zaki dawo ai, zan ga ta inda zaki shigo gidan" Kulle kofar parlon yayi still smiling, ko ba komai ya rama abinda ta masa jiya. Safiyyah na kallon Khaleesat tace "To ko ya shige cikin Couch ne makullin?" Khaleesat tace "Ta yaya zai shiga kujera?" Safiyyah tace "Kuma har kitchen din kin duba?" Khaleesat tace "Babu inda ban duba ba fa" Safiyyah tace "Toh kawai kiyi ma agent din gidan magana su baki wani makullin mana" Khaleesat tace "Gani nake kamar dogon process ne hakan, kuma ai biyu ne makullin kika yar min da daya shine na dauko spare key din nake using, to shima gashi ban gansa ba yanzu" Safiyyah tace "Kar ki wani damu kanki, makullin na nan zaki gansa, kawai kin mance inda kika jefar ne, amma definitely it's either in ur room ko kuma parlor, yanzu jira zaki yi sai sanda housemate dinki ya dawo ki koma gidan kenan?" Khaleesat tace "Wani housemate? Shi da ba kwana ma yake a gidan ba, kuma ba shi da exact time da yake zuwa" Safiyyah tace "Kai haba, to a ina yake kwana?" Khaleesat ta zaro ido tace "Kin ji ki da wani tambaya, ta yaya ni kuma zan sani? what is my business with him da zan san inda yake kwana" Safiyyah tace "To kawai mu je gidanmu ki kwana" Khaleesat tace "Kina ganin babu matsala hakan?" Safiyyah tace "Wani irin matsala? To gidanta ne ko na ubanta da za a samu matsala? ta shi mu tafi jare" Safiyyah na gaba Khaleesat na biye da ita a baya suka shigo parlor da sallama, Surayya matar cousin brother din Safiyyah dake zaune parlorn ta daga kai tana kallonsu, Safiyyah tace "Sannu da gida Mom Aslam" Surayya ta ci gaba da danna wayar hannunta tace "Yauwa" Khaleesat ta zauna kan kujera ta gaisheta, Surayya ta amsa without looking at her tana danna wayarta, Safiyyah tace "Ai kin ganeta Mom Aslam, kawata ce kuma Coursemate dita Khaleesat" Surayya tace "Ohk" Safiyyah tace "She will be passing the night here, makullinta ne ya Ι“ata" Surayya ta daga wayarta da ya fara ring ta kai kunne hade da amsa sallama ta mike ta bar masu parlon, Safiyyah ta kalli Khaleesat tace "Tashi mu je ciki" Mikewa Khaleesat tayi ta bi bayan Safiyyah zuwa dakinta, Safiyyah na idar da sallah ta canza kayan jikinta tana kallon Khaleesat dake zaune saman darduma tace "Bari in samar mana abinda za mu ci a kitchen" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Safiyyah ta fita daga dakin... Khaleesat was so uncomfortable a gidan cause it's a home that she is not welcome, ko daga irin tarban da aka mata tasan she isn't welcome, karatun da take ta yi na boko ne ke while din mata lokaci, Safiyyah kuwa tun da suka ci abinci take ta bacci har yanzu da magrib yayi, Khaleesat tayi alwala sannan ta fito ta tasheta, bayan sun idar da sallah Safiyyah tace "Bari in je in ga me waccan matar ta girka" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana ci gaba da azkar dinta, Safiyyah ta fita daga parlon, Surayya na parlor tana ba yaronta Cereal da ta hada masa, Safiyyah ta karasa parlon tace "Aslam yanzu ya tashi ne, ban gansa tun daxu ba" Surayya tace "Ehh" Safiyyah ta Ι—an masa wasa sannan ta wuce kitchen, abinci ne iya cikinta taga Surayya ta ajiye mata a kitchen din, Safiyyah ta fi minti biyu tsaye kitchen din tana kallon abincin, can tayi kwafa ta dau plate ta juye ma Khaleesat kawai ita idan ya so ko cornflakes ne sai ta sha anjima, ta fito kitchen din kenan sai ga Cousin brother dinta ya shigo parlor, gaishesa tayi ta amshi ledan hannunsa yace "Leave it, kije ki ci abincin ki" Tace "Ai ba nawa bane ba ma, kawata zan kai ma, ni sai dai in sha cornflakes tunda abincin iya wannan ya rage" Surayya dai kallonta kawai take, Musty yace "Wace kawarki?" Safiyyah tace "Khaleesat, she lost her house key shine ta zo zata yi spending night din a nan" Musty yace "Oh Allah sarki, ba ayi abincin da yawa bane?" Safiyyah ta karkace masa plate din sosai tana nuna masa tace "Iyakarsa kenan aka bari a kitchen, tun da rana muka dawo kuma" Musty yace "Ohk, me ku ke son ci let me get it yanzu a restaurant" Safiyyah ta Ι—an yi murmushi ta ajiye plate din saman center table kusa da Surayya tace "Bari in tambayi Khaleesar abinda zata ci" Surayya ta bi ta da wani kallo har ta shige daki, Safiyyah na shiga dakin tace "Khaleesat ki fito ku gaisa da yaya Musty nace masa kina nan" Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace "Is it necessary Safiyyah?" Safiyyah tace "Ban gane is it necessary ba, yayana ne fa, kuma nace masa kina nan, ai ya kamata ki gaishesa dai ko" Khaleesat tayi shiru, can ta mike suka fito daga dakin tare, tana tsaye daga jikin kujera ta gaida Musty ba tare da ta kallesa sun hada ido ba, ya amsa da fara'a yana kallonta, Surayya dai fuskarta babu yabo babu fallasa take tura ma yaronta Cereal a hanci maimakon baki ba tare da ta sani ba, Khaleesat ce kadai ta lura da hakan, Safiyyah na murmushi ta kalli Khaleesat tace "Wai yaya yace me za mu ci zai fita yanzu ya siyo mana" Khaleesat taki cewa komai, Safiyyah tayi fari da ido ta fara lissafo masa abubuwan da zai siyo masu, Surayya ta ajiye bowl din Cereal din hannunta kan Centre table ta ciro Aslam daga kekensa tace "Mu je in maka wanka Aslam" Daga haka ta bar parlon tayi wucewarta daki, Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta, Muryar Musty da taji yana mata magana yasa ta daga kai ta kallesa, yace "Su kenan iya abinda Safiyyah ta lissafo za a siyo maku Khaleesah?" Kai kawai Khaleesat ta gyada masa, bayan nan ta juya ta koma dakin Safiyyah jiki a sanyaye.

 

 

07087865788✍🏻

[5/1, 5:20 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨ HALYSAAH ✨✨

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

4.....

 

 

Khaleesat ta zauna gefen gadon dakin Safiyyah duk jikinta a sanyaye, jawo wayarta tayi tana duba agogo taga karfe bakwai har da rabi, sam bata ji zata iya kwana gidan nan ba, tasan probably yanzu House mate dinta na gida, to ya ta iya? Hakan dai zata koma gidan tayi masa knocking, the thought of this made her weak, shigowar Safiyyah dakin yasa ta daga kai, Safiyyah ta rike haΙ“a tace "Kinsan kuwa shegiyar matar nan bata ajiye mana abinci ba, ai ko sai ga yaya Musty kamar an jefosa kuma night shift fa yake yi wallahi, kinga ko ba komai sai ta hadiyi zuciya ta mutu don bakin ciki yau, abincin da na lissafo masa ko rabinsa baza mu iya ci ba kuma kwalelenta sai dai in har shi yayi dubaran siyo mata nata daban, ban taΙ“a ganin me tsinannen hali kamar matar nan ba tirr, ni ai na zata in mutum zai taho wata kasar barin baΖ™in halinsa yake a gida, to ita dai da nata ta taho wallahi" Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace "Lallai kam, kinga ni kuma tafiya zan yi fa, da ma bai siyo abincin ba, yanzu Housemate dina ya kirani yace he is back home" Safiyyah ta bude baki da mamaki tana kallonta, can tace "Ban gane ba, yaushe kika samu number Housemate dinki har ya kira ki? Wallahi ban yarda ba kawai so kike ki tafi, bari ki ji in dai don Surayya ce nima fa zaman hakuri nake da ita a gidan nan Khaleesat, mugun halinta bai da part 2, gwara kawai kiyi zamanki in ma shekara zaki yi a nan babu yanda ta iya tunda ba gidan ubanta bane kuma warmly Ya Musty zai yi welcoming din ki" Khaleesat tace "Sophie ni fa tunda Housemate dina ya dawo bazan kwana a gidan nan ba, dama bani da kayan da zan canza sannan na ma manta na bar kaya a washing machine kin ga bani kadai bace a gidan, may be zai yi laundry shi ma" Safiyyah ta hade rai tace "A takaice me kike nufi kenan? Kina ji ina lissafa ma Ya Mustapha abinda zai siyo mana don walakanci ki ce ke zaki tafi? shima ai bazai ji dadi ba idan ya dawo da abincin yaga kin tafi kuma saboda ke ya fita ya siyo don in dan ta nice sai dai yunwan ya kasheni in bai ga dama ba" Khaleesat ta Ι—an yi murmushi tace "Zan jira ya dawo, sai in tafi da abincin gida kawai" Safiyyah da har ranta ya Ι“aci tayi mata banza ta tafi ta dau wayarta tana dannawa, Khaleesat dai bata sake cewa komai ba, komin fushin Safiyyah ita kam baza ta kwana gidan nan ba, after a while Ya Mustapha ya dawo gidan da abincin da ya siyo masu, Safiyyah ta mike ta nufi kofa bayan ya kirata a waya, Khaleesat ta bi ta da kallo har ta fita sannan tayi murmushi, Safiyyah ta karasa dinning table ta dau abincin da Cousin din nata ya ajiye masu ta koma daki, iya wanda zata ci ta cire ta bar ma Khaleesat duk abincin, Khaleesat tace "Ya zanyi da abincin nan me yawa Sophie?" Ba tare da Safiyyah ta kalleta ba tace "Wannan kuma ke kika sani" Khaleesat bata son jan maganar yayi tsayi kawai ta mike ta dau veil dinta da handbag sannan ta dau ledan abincin tace "Sai mun hadu gobe, thank you so much dear" Safiyyah tace "Kinyi order din ride ne?" Khaleesat tace "Sure" Mikewa Safiyyah tayi suka fito dakin a tare, dai dai fitowar Mustapha parlor shi ma, yana kallonsu da mamaki yace "Ya aka yi kuma?" Safiyyah ta langwabar da kai tace "Her Housemate is back, shine kawai zata tafi gida wai" Yace "Isn't it late?" Safiyyah ta kyabe baki tace "Nima dai haka nace mata" Ya kalli Khaleesat da ta sunkuyar da kanta, yace "Kiyi hakuri ki bari gobe mana Khaleesah, yanzu ai dare yayi...." Khaleesat ta Ι—an yi murmushi ta dago kai cikin sanyin murya tace "Akwai abinda nake son zan yi ne idan na koma gida" Mustapha ya daga kafada yace "While, if you insist...." Ta gyada masa kai tace "Nagode" Safiyyah ta wani harare ta, Mustapha yace "Zan koma aiki ne dama, mu je sai inyi dropping din ki ko" Khaleesat bata yi expecting offer din nasa ba, ta Ι—an kallesa tace "Na riga nayi order din Lyft ai...." Safiyyah ta mata wani kallo tace "Haka kuma you can cancel it ai ko...." Kasa cewa komai Khaleesat tayi, lkci daya ta zama uncomfortable, Mustapha dai kallonta kawai yake, after few seconds a hankali tace "Ohk" in response to Safiyyah, Kofa Mustapha ya nufa, Safiyyah tayi kasa da murya tana kallonta tace "Ke in zaki saki jiki ki saki jiki, a ko da yaushe sai kin nuna ke er.... Ya ma sunan wannan unguwan naku a kano?" Khaleesat ta dinga kallonta, can ta juya ta nufi kofa tana tafiya slowly, Safiyyah ta fara dariya kasa kasa tace "Good night girlfriend" Ko tankata Khaleesat bata yi ba. Yana zaune cikin motarsa yana jiranta har ta karaso, ta bude gaban motar ta shiga, sai kallon entrance din gidan take tana fatan kar matarsa ta fito ta gansu, ya tada motar suka bar garage din, sai a sannan ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tayi fastening seat belt dinta a ranta ta dau alwashin wannan shine zuwanta na karshe gidansu Safiyyah, bayan sun hau saman hanya taji yace "Where do u stay?" Idonta na kan titi ta gaya masa, yace "Co-living kike yi kenan?" Tace "Um" Yace "Menene yasa baki dawo ku zauna gidana tare da Safiyyah ba instead of living alone with a stranger?" Ko rufe baki bai yi ba tace "Ai yawanci ni kadai ce a gidan, my Housemate is not always around" Yace "Ok then" After almost a minute yace "Kema er kano ce?" Tace "Um" Yace "Wani anguwa?" Tayi shiru, sai kuma ta Ι—an kallesa ta gefen ido taga kallonta yake at the same time yana tuki, ta sauke idonta kasa ta gaya masa, she is so uncomfortable with him, Yana gyada kai yace "Ohk, i am also from kano, Sharada to be precise" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, cikin minti 13 ya kawota gida, ya juya yana kallonta bayan yayi parking, daukar ledan abincin tayi tace "Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Wayarsa taga ya mika mata, ta daga kai ta kallesa, yace "Ki sa min digit dinki sai mu dinga gaisawa, in kina bukatar wani abu kuma feel free to ask me anytime" Khaleesat ta sauke idonta, ita da ta sani babu abinda zai kai ta gidansa yau, da kawai dawowarta tayi ta zauna bakin apartment dinta ta jira har sanda Housemate dinta ya ga daman dawowa ya bude mata kofa, muryarsa ya dawo da ita duniyar tunanin da ta tafi ta daga kai da sauri ta kallesa, bata ma san me yace ba taga dae yana kallonta, da kyar tayi stretching hannu ta amshi wayar ta sa masa digit din nata, yayi dialing, ita dai kanta na kasa, wayarta dake cikin jaka ya fara vibrate, yace "Kiyi saving nawa digit din" Tace "Um" Yace "Good night, take care Khaleesah" Tayi karfin halin cewa "Nagode" Daga haka ta bude motar ta sauka, kallon window din kitchen na apartment dinta tayi ganin wuta a kunne, sannan taga mota a Garage, she felt relieved sanin cewar her Housemate is around, ta zaga zuwa gaban apartment din tana jin sanyi na shigarta sosai don sanyi ya fara shigowa kasar, knocking din kofar parlor tayi gently, sai da ta kwankwasa sau uku sannan taji muryarsa yace "Who is there?" Ta kauda kai a takaice tace "Somebody" Yace "Somebody? I am not expecting somebody this late" Ta wani hade rai tace "Ni ka bude min kofa in shiga gida" Yace "Ke wa zan bude ma kofa?" Kin cewa komai tayi cause she is already provoke, yace "Ohk then, i am going back to my room after all i am not a door keeper" Tana jin haka a fusace tace "Don Allah ka bude min" Yace "Ke wa?" Tace "Ban gane ni wa ba?" Yace "Ohh, tsawa ma kike min?" Ta kara marairaicewa tace "Don Allah ka bude mana" Yace "To ai ni ban san wacece ba, baki da suna ne?" Shiru tayi tana kallon kofar kamar zata fashe da kuka, Yace "Ke zan fa yi tafiyata daki in baza ki fadi sunanki in san wa zan bude ma kofata ba cikin daren nan" Ta sauke idonta kasa, after a few seconds ta dake tace "Khaleesat" Yace "Halysaah..." Wani harara ta zabga ma kofar, Kamar yana counting harufan sunan yace "Ha.. lee...saah" A fusace kamar zata yi kuka tace "Sanyi fa nake ji ka ki bude min kofa, ko don ba kai bane tsaye cikin sanyin?" Bude kofar yayi yace "Baki san da sanyin ba kika je kika yi dare a titi?" Ko kallonsa bata yi ba ta kusa bangajesa ta shige parlon fuskarta a murtuke, yace "Wajen saurayinki kika tafi kenan kika yi dare, naga ma shi ya ajiye ki a mota, Allah sa ba me sa ki kukan nan bane dai" Direct dakinta ta nufa without even looking at him abinda ya fada na sinking zuwa cikin kanta, ya bi ta da kallo yace "Ok.... ga Door keeper dinki ya bude maki kofa ko? Tomorrow is another day, better look for ur lost key in ba so kike ki kwana a waje ba next time" Tuni ta bude kofar dakinta tayi shigewarta ta sa makulli tare da jan dogon tsaki. Da safe tunda Khaleesat ta tashi take zaune tana tunanin how today will be like, taje schl din ne ko ta hakura kawai tunda bata da makulli yanzu, zaro ido tayi bayan ta tuna lecture din da za su yi ranan, she just can't miss that class don course din is a bit complicated, mikewa tayi ta shiga bandaki, wajen karfe tara ta fito parlor hoping house mate dinta bai fita ba, don jiya wajen karfe sha biyu da rabi na dare ta fito don saka abincin da bata iya ta ci ba a fridge ta gansa kwance a parlor yana bacci, har ta gama abinda zata yi a kitchen ta fito bai farka ba, tun zuwansa gidan ranan ne rana na biyu da taga ya kwana a gidan, babu kowa parlorn ta karasa kusa da tagan parlon tana leka Garage ko zata ga motarsa taga motar na nan alamar he is around, ajiyar zuciya ta sauke don da ya fita shkkn babu tafiyarta makaranta kenan, kitchen ta tafi ta hado shayi ta debi cookies ta dawo parlon, har ta gama breakfast bai fito parlor ba, sai kallon agogo take don goma ta kusa gashi bata son tayi latti, kuma ita dai bazata taΙ“a masa maganar ya bude mata kofa zata fita ba, goma saura minti goma ya fito parlorn, ita dai bata dago kanta ba tana ci gaba da danna wayarta, taji yace "Good Morning, Halysaah" Without looking at him tana ci gaba da danna wayarta kamar tana ma kanta magana tace "Ok" Ta gefen ido ta bi sa da kallo ganin ya nufi kofa ta mike ta bi bayansa, yana lura da ta biyosa sai ya fasa bude kofar, ya juya yana kallonta keeping a serious face yace "Me ya faru?" Ta kauda kai taki cewa komai, mayar da makullin yayi aljihunsa zai bar wajen ta wani kallesa tace "Ni dai ka bude min kofa zan tafi makaranta" Yana gyada kai yace "Ohhh, ohk kin boye makullinki ne don in zama door keeper dinki dama?" Taki kallonsa don bata ma san me zata ce masa ba, ganin da gaske barin wajen zai yi ta marairaice tace "Makaranta zan tafi fa" Ya juyo yace "Be a good girl and beg politely first....." Shiru tayi tana bin sa da kallo har ya koma cikin parlor ya zauna kan kujera, Ta dake da kyar tace "Please ka bude min. i am going to school" Yace "Ban ji ba" Takaici yasa ta dauke kai taji ranta ya kara Ι“aci, ganin lokacinta kawai take Ι“atawa ta sake juyowa trying to be calm tace "Plss ka bude min kofa i am going to school" Ɗan murmushi yayi ya mike ya dawo bakin kofar ya ciro makullin a aljihunsa yace "Never knew u can be this Obedient" Ita dai bata kallesa ba, ya bude kofar yace "In kika sake yin dare baza ki shigo gidan nan ba sai dai ki kwana bakin Ζ™ofa ko kuma a Garage..." Bata tankasa ba ta fice daga parlon with annoyance almost brushing his shoulders, ya bude baki yana bin ta da kallon mamaki yace "Ohh, is this ur thank you??" Tuni har ta kusa titi abun ta, ta ja tsaki feeling so fed up with him. Bayan Khaleesat sun fito daga aji Safiyyah tace "Kinsan me Khalee?" Khaleesat ta juya ta kalleta, Safiyyah tayi dariya har da kyakyatawa tace "Wai Ya Musty ke tambayata ko kina da saurayi" Sai da gaban Khaleesat ya fadi, Safiyya bata fasa dariyar da take ba tace "Wallahi kuwa, he chatted me up yesternight wajen karfe sha biyu, bari ma in nuna maki ki ga, ni ko nace masa baki da kowa wallahi" Sai a sannan Khaleesat ta kalleta tace "Ban gane bani da kowa ba Sophie?" Safiyyah tace "To kina da shi ne? To in kallon saurayinki kike ma Abdul to ni wallahi kallon Ι—an daba nake masa, ni dai nace ma Ya Musty bakya kula kowa saboda karatu don haka baki da saurayi, kema kin dai san da Ya Musty na da mugun hali da tuni na fesa maki ni da bakina baya shiru, ai ko don wannan er banzar matar tasa zan so ya kara aure, kuma ace kawata ya aura huhuhu za a ga rashin nasiha da jahilci wajena" Khaleesat ta mike tana gyara Veil din jikinta tace "Zan tafi gida sai gobe" Safiyyah ta tsuke fuska tace "Ban gane zaki tafi gida ba daga na kawo maki maganar arziki" Khaleesat tace "Wallahi da na sani babu abinda zai sa in bi ki gida jiya Safiyyah, haba fisabilillah, put ur self in the wife's shoe in kece aka ma haka zaki ji dadi?" Safiyyah tace "Godforbid, her shoes will never size me sef kafin in sa kafata ciki Khaleesat, ai ni bani da mugun hali kamar ta, kina ga fa ko tsayawa ta amsa gaisuwarki bata yi ba ta wani Ζ™ara waya a kunne ta wuce daki ita er iska, sannan bari kiji jiya iya cikina ta ajiye abinci a kitchen bayan nace mata nan zaki kwana kuma ta sani, ni dai wallahi in kika ce baki son yayana nice kawai baki so, Ya Musty bai da wani aibu wallahi, ga arziki ga Ilimi ga kyau, baza ma ki ce ya taΙ“a auren wata er iska ba wai ita Surayya, Ι—an saurayi da shi" Khaleesat tace "In matarsa kike son tura ma haushi ai kema zaki iya aurensa tunda he is ur cousin brother kuma da aure tsakanin ku" Daga haka Khaleesat ta bar wajen tayi wucewarta, Safiyyah tace "Oho dai wallahi ce masa zan yi kin amince sai dai ki mutu, haka kawai kin makala ma kanki Ι—an daba kina kiransa da wanda zaki aura, ki auresa ki ci uwar me da shi, wannan har duka sai ya dinga nakada maki babu me kwatarki in ku ka yi aure" Khaleesat na isa gida taga babu motar Housemate dinta a parking space, jingina tayi jikin entrance din apartment din nasu, gashi ta gaji sosai ga yunwar da take ji, babu wanda ta saba da shi a Neighborhood din balle ta shiga gidansa, balle su turawa basu yarda da hakan ba ma, ta kusa twenty minute a tsaye sai ga motarsa ta hango, sunkuyar da kanta tayi har yayi parking ya karaso kofar entrance din, gefe ta koma without looking at him, tun kan ya karaso kofar apartment din ya sa hannu a aljihunsa yaji babu makullin, ya Ι—an bude ido still yana laluba duk aljihunsa, sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, juyawa yayi ya koma motarsa ta bi sa da ido, ya gama dube dubensa a motar bai ga makullin ba, ai tana ganin yanda yake dube dube tasan kilan ya yar da makullin, shikenan ta shiga uku, she is soo tired, har wani jiri take ji a tsayen da take, dawowa yayi yana kallonta yace "Look Halysaah, i think i left the key at where i am coming from" Ita dai bata ce komai ba kuma bata bari ta hada ido da shi ba, yace "Ko zaki shiga apartment din Neighbor dinmu kafin in dawo" Sunkuyar da kanta tayi still keeping mute, yace "Or ain't you familiar with them?" A takaice tace "Eh" Yace "Ok i will be back as soon as possible" Juyawa yayi ya koma gun motarsa ta bi sa da wani kallo.... Khaleesat na ta tsaye har bayan wani minti sha biyar sai gashi ya dawo, yana kallonta yace "Allah ya taimake ki na gani" Wani kallo tayi masa wato ita Allah ya taimaka ma, yana bude kofar tayi shigewarta ciki ta nufi dakinta ba tare da ta juya ba, sai da ta kwanta na kusan minti sha biyar sannan ta mike a hankali ta shiga bandakinta, bayan Khaleesat tayi wanka tayi sallah tana zaune kan darduma taji yayi knocking kofar dakinta, kallon kofar take bata ce komai ba kuma bata amsa ba balle ta tashi, taji yace "Halysaah" Bluntly tace "Me ya faru?" Jin ya murda kofar dakin ta zaro ido ta mike tsaye da sauri tace "What?" Tuni ta isa gun kofar ta bude tana masa kallon tuhuma, ledan hannunsa ya ajiye mata yace "I got you food, naga kin yi laushi" Ta kalli ledan, ya juya ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya koma parlor, sauke idonta tayi, bayan few seconds ta duka ta dau ledan ta juya ta koma dakin. Khaleesat ta bude abincin da ya kawo mata ta fara ci kenan wayarta ya fara vibrate, mikewa tayi ta bude handbag dinta ta ciro wayar, sosai gabanta ya fadi ganin Abdul ke kiran ta, zaunawa tayi gefen gado tana kallon screen din wayar har sannan gabanta na bugawa, kafin kiran ya katse tayi karfin halin dagawa ta sa handsfree sannan tayi sallama cikin sanyin murya, maimakon ya amsa sai ji tayi yace "Wato all this While ni kike jira in kiraki ko Khaleesat?" Ta sauke idonta a hankali tace "To ai cewa kayi duk sanda kake son magana da ni zaka kirani amma kar in sake in kira ka" Yace "Don nace kar ki kirani sai ki ki kiran nawa? Me yasa baki reason ne?" A sanyaye tace "Kayi hakuri" Yace "In ban hakura ba ya zan yi da ke? Ai saboda baki damu da ni bane yasa kika zama comfortable without calling me all this while, ko da bazan daga ba ai kamata yayi ki kira" Cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" Yace "Yaushe za ku fara jarabawa?" Tace "Probably nan da 6 to 7 weeks" Yace "I can't wait har zuwa nan da sati bakwai ban gan ki ba Khaleesat, idan na samu lokaci zan shigo anytime from now in sha Allah" Shiru Khaleesat tayi as if trying to process what he just said, yace "Hello" Da sauri ta kifta ido tace "Na'am ina ji" Yace "Me yasa kika yi shiru? Ko baki son in zo ne?" Tayi yake tace "Aa ban yi shiru ba network ne, ban ji me kace ba" Yace "Ohk, nace you should expect me any moment from now" A hankali tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen, me kike yi yanzu?" Tace "Abinci nake ci" Yace "Ohk switch to video call" A hankali tace "Toh" Mayafinta ta jawo sannan tayi yanda yace mata.

 

 

07087865788 for more info✍🏻

[5/2, 5:50 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨ HALYSAAH ✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

5......

 

Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta fito parlor daga dakinta, window ta nufa tana leka garage ta ga motar Housemate dinta alamar yana gidan, juyawa tayi ta tafi kitchen zata yi disposing takeaway din da yayi mata daxu, ta window din kitchen din ta hangosa zaune a Lawn din dake bayan kitchen din waya Ζ™are a kunnensa alamar he is making a phone call, komawa baya tayi don kar ya hangota ta window din kitchen din, ta ajiye ledan hannunta a hankali ta juya ta fita daga kitchen din ta dawo parlor, tsaye tayi tana kallon handle na kofar living room din, sai kuma ta tafi gun da ya ajiye takardun karatunsa ta hau bincika Books din da sauri, har ta gama dube dubenta bata ga abinda take nema ba, ta koma kitchen din tana kara lekansa, seeing he is still on call ta dawo da sauri ta tafi corridor din dakunansu, tsaye tayi gabanta na faduwa as if contemplating on whether to do what is on her mind or just forget it, ganin she is just wasting time ta runtse idonta ta bude, sai kuma ta kai hannu handle din kofar dakinsa a hankali ta bude ta shiga ciki zuciyarta na bugawa, bin dakin that was neat and tidy ta fara yi da kallo kafin ta karasa can ciki da sauri, har sannan tana kallon ko ina na dakin, ta ma rasa daga inda zata fara duba abinda ta shigo nema, zagaye dakin ta fara yi tana dube dube with confusion, daya wayarsa dake gefen gado yayi haske alamar shigowar sako, kallon screen din wayar take yi ganin wani matashi kamarsa a shekaru ne a fuskar wayar, ta juya ta kalli Trouser dinsa, gabanta na faduwa ta dauka ta kai hannu aljihun wandon, Dollar ta ciro masu yawa tayi saurin ajiyesu gefen gado, sannan ta duba daya aljihun, zaro ido tayi jin makulli da Counter a ciki, ta ciro da sauri tana kallon makullin taga makullin kofar parlor ne, bata san sanda tayi murmushi ba ta ajiye wandon a inda ta dauka sannan ta juya da sauri, Ζ™amewa tayi a spot din da take ganinsa tsaye bakin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonta daga sama har kasa, kawai ta juya masa baya zuciyarta na bugawa taji kamar Ζ™asa ya bude ta shige ta huta, after some seconds taji yace "Sannu da aiki" Ita dai ta kasa juyowa, she felt so ashame at that moment, she wish this never happened, sai juya makullin hannunta take with shame, Calmly yace "Give me the key" Ta wani turo baki taki juyowa tace "To ba amfani zan yi da shi ba" Yace "Dama in bana nan bincike kike shigowa ki min a daki?" Bata san sanda ta juyo tana kallonsa babu ko kiftawa ba jin abinda yace, sai kuma ta ajiye makullin a gefen gado ta nufi kofa ta bi gefensa ta fice daga dakin ta shiga nata ta tura kofar, nan da nan taji hawaye ya cika idonta ta zauna gefen gado, sai kuma ta Ι—ora kanta saman pillow hawaye na sauka idonta har da shessheka. Karfe bakwai da few minutes Khaleesat na zaune kan darduma, tun da ta idar da sallah take zaune wajen, da ta tuna abinda Housemate din nata yace mata sai taji hawaye ya cika idonta, gaba daya taji ta tsani zaman gidan, kuma bata jin zata iya ci gaba da zama as far as he is here, ta yanke shawaran kawai zata gaya ma Abdul ya canza mata gida kamar yanda Safiyyah ta bata shawara tun farko taki dauka, wayarta dake gefen gado ta dauka jin ana kira, tana dubawa taga Mustapha ne ke kiranta, ajiye wayar tayi gefenta taki dauka har ya katse, ya sake kira nan ma taki dagawa, bayan Ι—an lokaci aka sake kiranta kallon wayar tayi a bit fed up thinking it's still Mustapha sai taga Abdul ne ke kiranta this time around, ta jawo wayar a hankali tayi picking ta kai kunne, sallama tayi masa sannan ta gaishesa, yace "Ya naji muryarki haka?" Tayi shiru tana tunanin ta inda zata fara sanar masa the situation at hand, muryarsa ya dawo da ita tunanin da take, a Ι—an tsawace yace "Ke, baki ji na ne zaki min shiru?" Kasa gaya masa tayi don bata ma san yanda zai fara daukar lamarin ba barin yanda taki gaya masa tun farko, Ta Ι—an yi yake tace "Ina jin ka, kawai muna da wani jarabawa ne gobe, kuma ina jin ciwon kai, and I haven't covered up, shi yasa nake damuwa" Yace "Na ce ki dena stressing kanki da karatu, u are not dull to be studying as if ur life depends on it, read a little and get enough rest, nasan za ki yi passing ko ma me za kuyi gobe" Tana murmushin karfin hali a hankali tace "To" Yace "Kin ci abinci ne?" Ta girgiza kai tace "Ban ci ba" yace "Ohk get something to eat, idan kin gama sai ki kirani ina jiran ki" Tace "Toh" Katse wayar yayi, ta bude WhatsApp dinta tana duba ko Neighbor dinsu ta mata reply taga ta hau WhatsApp din amma still bata yi reply ba, yau kwana uku kenan basu yi magana da Ummanta ba, Dialing din Number Sha'awa tayi ta direct call, har ya katse ba a daga ba, sai da ta sake kira aka daga, sallama Khaleesat tayi mata sannan ta gaisheta, Sha'awa ta amsa tace "Lafiya lau Khaleesah, ya karatu?" Khaleesat tace "Alhamdulillah ya gida ya su Kamilu?" Sha'awa tace "Duu lafiyansu lau wallahi" Khaleesat tace "Su Ummanmu suna lafiya..." Sha'awa tace "Kwana biyu kinyi magana ta wassap kinji shiru ko, to Ummanku dai bata da lafiya amma da sauki yanzu" Nan da nan Khaleesat taji hankalinta ya tashi don dama tun da taji shiru for days tasan ba lafiya ba, don ko bata yi ma Ummanta magana ba ita zata mata ta wayar Sha'awa taji ko tana lafiya, Hankalinta a tashe tace "Aunty Sha'awa tun yaushe?" Sha'awa tace "Ina jin yau kwana uku, ai an ma ce kar a gaya maki, shi yasa ko mayar maki da sakon da kika yi ta wassap din ma ban yi ba, yanzun ma kar ki wani ce zaki kira kowa kiyi ta mata addu'a kawai Allah ya bata lafiya" Khaleesat taji hawaye na sakko mata ta kasa cewa komai, Sha'awa tace "Wai daga ta tashi zata fito daki tayi alwalan magariba shi ne fa ta yanke jiki ta fadi a bakin kofar dakin, duk kwanan nan ina rabata da saka ma kanta damuwa tunda tasan matsalarta na hawan jini, to kinga ai irin haka ake gudu gashi kuma ya faru, Farida ma ta taho daga legas tun jiya ta iso, kar ki wani tada hankalinki don jikin da sauki" Cike da karfin hali Khaleesat tace "Suna asibiti ne yanzu?" Sha'awa tace "Wani asibiti? To har sai da Farida ta zo sannan ta kai ta asibiti jiya in gaya maki, amma duk kwanakin nan tana gida gashi ko taΙ“ata kika yi a daya barin jikinta bata ji wai, ko magana ma in tayi sai kin sa kunne sosai zaki ji, ke abun fa ba kyau, har yanzu hankalinmu a tashe yake, an dai ce kar a gaya maki kar hankalinki ya tashi...." Khaleesat in hankalinta yayi dubu ya tashi a lkcn, ta kalli Screen din wayarta jin kiran ya katse alamar katin ta ya kare, ajiye wayar tayi ta fara rera kuka kamar an sanar mata da mutuwa... Har karfe goma na dare Khaleesat ta kasa tashi daga kan darduman da take, sosai ta shiga damuwa ba kadan ba, a inda take zaune Abdul ya kirata sau biyu amma ta kasa picking call din nasa, karfe goma da rabi taji anyi knocking kofar dakinta, ta juya ta kalli kofar tana share hawayen dake idonta amma bata tashi ba sai ma hade rai da tayi, after a while ya sake knocking still dai bata tanka ba, sai kuma taji yace "Assalamu alaikum" kawai ji tayi ya bude kofar dakin ta juya da sauri daga inda take zaune suka hada ido, daga nan bakin kofar ya tsaya yana kallonta, ita dai taki yarda ta sake hada ido da shi, ya karasa ciki ya tsaya still leaving enough distance between them, calmly yace "Maganar da na maki yasa kike kuka? But i was only pulling ur legs Halysaah, i am sorry about that, was just joking" Wasu hawaye suka cika idonta sai kuma ta fara kuka, bude ido yayi alamar mamaki sosai yana kallonta, can dai ya kwantar da murya yace "Look, do not take my words serious Halysaah ni wasa nake maki wallahi" Ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta tana kuka a hankali, dukawa yayi da mamaki sosai yana kallonta ya ma kasa cewa komai, after few seconds da taji shiru ta Ι—an bude fuskarta don tunaninta ya fita daga dakin, suna hada ido ta daure fuska tace "Ni saboda kai nace nake kuka?" Yace "Toh why are you crying?" Shiru tayi bata ce komai ba wasu sabbin hawayen na cika idonta, Yace "Tell me Halysaah, what is making you cry?" Kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "My mother is sick" Yace "Hasbunallah, what's wrong with her?" bata sake ce masa komai ba tana goge idonta, After few seconds ya sauke ajiyar zuciya yace "Amma ai ba kuka zaki zauna kina yi ba, addu'a zaki mata Allah ya bata lafiya" Nan ma dai bata ce komai ba, ya mike yace "Allah ya bata lafiya" Sai a sannan tace "Ameen" Yace "Are you going back home to check on her?" Ta daga kai ta kallesa amma bata ce masa komai ba, yayi shiru shima, can yace "Are you from kano?" Ta gyada masa kai, Yace "Allah Ubangiji ya bata lafiya, and try getting something to eat for Dinner" Ta sunkuyar da kanta kawai, ya juya ya fita daga dakin ya kullo mata kofar gently. Wajen karfe sha biyu na dare Khaleesat na kwance taji ya sake knocking kofar dakinta, juyawa tayi ta kalli kofar, bayan wasu yan sakwanni ta mike zaune tana kallon kofar, sai da ya sake knocking sannan ta sauka daga saman gadon ta dau hijab dinta ta saka ta nufi kofar ta bude, yace "Are you still crying?" Ta hade rai ta girgiza kai without looking at him, yace "Ok naga baki fito kinyi dinner ba and it's past 12, ki nemi abinda za ki ci kar ki kwanta haka" Ita dai bata ce komai ba, yace "Hello" Daga kai tayi ta kallesa tace "Naji" Yace "Good" Kullo kofar dakin nata tayi ta nufi kitchen tana tafiya a hankali, sai da yaga ta shiga kitchen din sannan ya shiga dakinta yana bin ko ina da kallo, after a while Khaleesat ta fito daga kitchen din with a cup of tea and some cookies, tsaye ta gansa corridor, bayan ta karaso yace "Kin ga nima Ummi na bata da lafiya amma ban zauna ina kuka ba kamar yanda kika yi" Khaleesat bata kallesa ba ta shige dakinta ta kulle kofa, tana gama shan shayin ta koma saman gado ta kwanta, tasan yau da kyar ta iya bacci, she wish she can just see herself in Nigeria, but how?? Wasu hawaye ne suka zubo idonta ta lumshe ido, after a while ta jawo wayarta a hankali tayi dialing number Abdul bayan ta tuna ya kirata har sau biyu daxu bata iya tayi picking ba, har kiran ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, tasan as usual yayi fushi kenan, ko uxuri bazai mata ba, ajiye wayar tayi ta juya zuwa daya side din gadon. Washegari da safe Khaleesat na zaune daki tana ta kokarin kiran Aunty Farida amma baya shiga, har Sha'awa sai da ta kira ita ma wayarta baya shiga, ta rasa wa kuma zata kira, ta kalli agogon wayarta dake nuna karfe goma sha daya ta ajiye wayar tayi tagumi, tun daga daren jiya har yau bata da sukuni, ko schl din ma yau tasan bazata iya zuwa ba, juyawa tayi jin knocking a kofar dakinta, tana dai zaune har sai da ya kwankwasa kofar sau uku sannan ta sauka daga saman gado, walking slowly ta tafi ta bude kofar, Yace "Good morning Halysaah, how was ur night?" Without looking at him tace "Fine" Yace "Ya jikin Mama? Kun yi communicating da su?" Kai kawai ta gyada masa bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, Paper da pen din hannunsa ya mika mata yace "Can i get ur Email Address?" Ta daga kai ta kallesa da mamaki tace "I don't understand" Yace "I mean ur Email Address" wayarsa ne ya fara ring ya mika mata takardan da pen ya daga kiran sannan ya juya ya bar wajen, ita dai ta bi sa da kallon mamaki, can ta juya ta koma daki ta ajiye takardan da pen da ya bata, after some minutes sai gashi ya dawo yayi knocking yace "Can i get the paper" Tasowa tayi ta bude kofar bayan ta dau pen da takardan tace "Why are you asking for my Email Address?" Yace "Ki dae rubuta ki bani" Shiru tayi, sai kuma ta jinginar da paper din jikin kofa ta rubuta sannan ta mika masa ya amsa ya juya ya bar wajen, yana fita da few minutes taji message ya shigo wayarta, ta dau wayar ganin E-mail ne ya shigo ta bude, kallon Image din da ta gani as Email din ta dinga yi babu ko kiftawa, she look shocked and confused at the same time, ta daga kai tana kallon kofar dakinta babu ko kiftawa, dai dai sanda taji sallamarsa, kasa tashi tayi daga inda take zaune, har sai da yayi knocking sau biyu tayi karfin halin mikewa ta isa kofar ta bude tana kallonsa, Yace "I don't know if you find this okay and a good idea" Ita dai bata fasa kallonsa ba looking speechless, Yace "Hope they won't be Mad at this back home Halysaah?" Jin bata basa amsa ba ya gyada kai yace "I guess it's a bad idea, I should have ask for ur opinion first before doing this" Nan da nan hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kanta, yace "Ok it's fine, i will get the ticket cancelled" Daga kai tayi da kyar tana kallonsa hawaye na zuba idonta tace "Thank you so much, i appreciate" Yace "Sure??" Ta gyada masa kai, yace "Ohk, u can order a Lyft that will be taking u to the airport later, ur flight is at 3pm today" Sauke idonta tayi cause she is totally speechless, ya mika mata travelling documents dinta, amsa tayi cike da mamakin how he got them, ya juya ya bar wajen, komawa cikin daki tayi ta kulle kofar tana kallon inda take ajiye travelling doc din nata a dakin, did he come to her room to check ne, to ai throughout babu inda taje, ta karasa gefen gado har sannan jikinta a mugun sanyaye ta zauna, kallon screen din wayarta ta sake yi tana kallon ticket din don ganin abun take kamar a mafarki, tana kara duba taga tun daren jiya ya siya ticket din and kamar yanda yace the flight is by 3pm today, ta ma rasa ko farin ciki zata yi ko kuma wani reaction zata yi, amma da ta tuna she is going back home to see her Mom which was her wish since yesterday sai taji wani farin cikin da tunda take bata taΙ“a jin irinsa ba a rayuwarta, 80% a cikin dari na damuwarta ya ragu cikin lokaci kankani, kallon agogo tayi taga sha daya ya wuce sosai, the weakness she is been feeling since this morning immediately vanished, mikewa tayi tana share hawayenta ta dau medium box din kayanta.... Karfe biyu Khaleesat ta gama duk abinda take, har sallan zuhur tayi, Lyft din da tayi ordering kawai take jira, tana zaune gefen gado xuciyarta fal da tunani kala kala, babban burinta a yanzu bai wuce ta ganta kusa da mahaifiyarta ba, in yaso koma me zai faru daga baya sai ya faru, kallon wayarta tayi taga Safiyyah ce ke kiranta, tun daxu da safe ta kirata amma sbda damuwar da take ciki ko picking bata iya tayi ba, Khaleesat ta daga kiran ta kai kunne, Safiyyah tace "Khalee me yasa baki shigo schl ba yau? Are you okay?" Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Ummanmu ce bata da lafiya Sophie" Safiyyah tace "Subhanallah, amma ya jikin yanzu?" Khaleesat tace "Da sauki" Safiyyah tace "To Allah ya bata lafiya, plss nasan ki kar ki sa ma kanki damuwa kawata addu'a kawai zaki dinga mata, nasan kilan kina nan kina ta kuka ko?" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace "In sha Allah in mun gama lectures zan taho" Khaleesat tace "I am sorry ban kira ki na gaya maki ba i will be leaving for Nigeria by 3pm" Da mamaki Safiyyah tace "Zaki tafi Nigeria? Abdul ne ya siya maki flight ticket?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Uhm" Safiyyah tace "Is it that critical Khaleesat?" Khaleesat tace "To da sauki dai, amma kinsan bazan samu rest of mind ba in ban je ba" Safiyyah tace "To kina airport yanzu ne?" Khaleesat tace "Aa ina jiran Lyft ne yanzu zan tafi" Safiyyah tace "Toh shikenan mu hadu a can kawai sai mu yi sallama, bari in nemi Uber nima" Khaleesat tace "To nagode Sophie" Da haka suka gama wayar, Khaleesat ta mike bayan Lyft dinta ya iso, tana rike da trolley dinta da handbag ta fito daga dakin ta kulle kofa, sanye take da Maroon Abaya sai veil dinta, tana tafiya a hankali ta karaso cikin parlorn, ya ajiye wayar da yake yace "Kin shirya?" Without looking at him tace "Eh" yace "Kin yi ordering ride ai?" Tace "Eh" yace "Ohk" Mikewa yayi ya ciro 1000 Dollars ya mika mata yace "Sort ur self out with this" Girgiza masa kai tayi tace "Aa Nagode" Yace "C'mon, u didn't beg me Halysaah" Ƙin kallonsa tayi kuma taki amsan kudin, ya dau handbag dinta da ta ajiye saman trolley din gabanta ya bude zip din jakar ya sa mata kudin tare da wani farin takarda, ta Ι—aga kai tana kallonsa, ya koma ya zauna yace "Allah ya tsare, my regards to ur Mom and everyone back home, Allah ya bata lafiya" Da kyar tace "Ameen nagode" Yace "Zaki ga digit na rubuta maki a takarda, idan kun sauka Airport sai ki kira number kice masa kun sauka" Ta kasa cewa komai, after few seconds ta dau handbag dinta cikin sanyin murya tace "Nagode " Yace "U are welcome, wishing u a Safe trip" Tana jan trolley dinta a hankali ta nufi kofa, tana bude kofar ta fita ta daga kai tana kallonsa taga Idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, kulle kofar parlon tayi, taga Lyft din dake jiranta ta nufi wajensa. A Airport Khaleesat suka hadu da Safiyyah, Safiyyah na rike da hannunta tace "Tun yaushe ne Umman bata da lafiya?" Khaleesat tace "Jiya Aunty sha'awa ke gaya min" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah Ubangiji ya bata lafiya" Khaleesat tace "Ameen" Safiyyah tace "Lallai Abdul ya fara hankali da yayi tunanin biya maki jirgi kije ki duba Umma, nayi mamaki sosai wallahi" Khaleesat ta Ι—an yi murmushi da iyakarsa lips, Safiyyah tace "Yanzu kwana nawa za ki yi?" Khaleesat tayi shiru at first, sai kuma tace "Sai dai naje tukunna in sha Allah" Safiyyah tace "Toh Allah ya kai ku lafiya, don Allah ki gaida min Umma da jiki" Safiyyah na fadin haka ta jawo handbag din Khaleesat ta saka mata dala dari tace "Plss manage this kawata" Khaleesat ta Ι—an bude baki tace "Haba meye haka Sophie" Sophie bata tsaya ta saurareta ba ta daga mata hannu tana murmushi ta bar ta tsaye wajen, Khaleesat dai ta bi ta da kallo. Khaleesat was more than shock bayan ta amshi boarding pass dinta ganin ticket din Business Class ya siya mata, Business class fa? Kikkifta ido tayi ta sake kallon ticket din sosai to confirm, taga Business class din dai ne still, sosai jikinta yayi sanyi, tana jan kafa da kyar ta shiga jirgin, this is the first time she will be traveling Business class, wata Flight Attendant that gave her all the maximum attention ta yi leading dinta har zuwa Seat dinta a cikin jirgin da fara'a tana welcoming dinta, bayan wani Ι—an lokaci jirgin ya tashi, Khaleesat ta ajiye Amenity kit da aka bata ko duba abinda ke ciki bata yi ba tana bin ko ina na Business class din da ido, the Flight from Baltimore Washington International to Amsterdam Schiphol Airport in North Holland for Layover was smooth and comfortable, duk zuwanta Amurka bata taΙ“a tafiya feeling so comfortable like this ba, bayan few hours aka sauya masu jirgi zuwa Nigeria a nan North Holland, Khaleesat tayi shiru da mamaki jin announcement na cewar Lagos Nigeria jirgin ya nufa, ticket dinta ta sake dubawa taga ashe haka ne a jiki, bayan tafiyar kusan awa bakwai jirgin nasu ya sauka a MMI Airport Lagos.

[5/3, 6:15 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

 

6.....

 

 

Bayan Khaleesat ta dau trolley dinta a cikin airport after going through custom ta tsaya cikin airport din tana tunanin yanda zata yi cause karfe shidda saura ne na asuba, should she check for available flight to Kano? To nawa ne ma a account dinta before she think of doing so, ko dai kawai ta tafi Motor park ta hau mota zuwa kano, dollars din da Housemate dinta ya bata ne ya fado mata a rai don gaba daya ta ma mance, ta bude handbag dinta ta ciro kudin tana kallo, takardan da ya saka mata hade da kudin a jaka ya fadi kasa, ta duka ta dau takardan tana kallon numbers din jiki sai kuma ta mayar cikin jaka tare da Dollars din, masallacin dake cikin Murtala Muhammad International airport ta tafi don yin sallan asuba, tana ta zaune cikin masallacin bayan ta idar da sallah tana azkar dinta, can ta ciro wayarta a handbag ta duba agogo taga karfe bakwai da minti goma, dollars din jakar ta sake cirowa ta kirga taga dala dubu ce, kallon kudin ta dinga yi jiki a sanyaye don bata yi tunanin har haka ya bata ba, ta dau white paper din dake dauke da digit tana tunanin to ko digit dinsa ne wannan din, kati ta siya ta Ussd sannan tayi dialing number a wayarta, sai da ya kusa katsewa aka daga, daga daya side din aka yi sallama ta amsa, amma sai taji kamar ba muryarsa bane, ta dai ce "Ina kwana?" Yace "Hajiya ko kece kika taho daga America?" Tace "Eh" Yace "To barka da isowa Hajiya, ina ta sauraren kiran naki dama tun daxu, kina cikin airport din ne yanzu?" Tace "Eh" Yace "Ohk to gani nan tahowa ba da dadewa ba in sha Allah" Bayan ya katse wayar ta kalli screen dinta, to waye kuma wannan, maida kudin tayi jaka ta ciro nose mask dinta ta saka sannan ta mike ta fito daga Masallacin da trolley dinta with handbag, bayan wasu mintoci sai gashi ya sake kiranta, ta fito outside of the airport, yana hangota ya nufota ya gaisheta da ladabi har da bowing kansa yace "Ya hanya Hajiya?" Ta sauke idonta tace "Lafiya Alhamdulillah" With respect yace "Ga mota can Hajiya, zaki je hotel ki huta zuwa karfe daya na rana don Flight dinki zuwa kano na karfe Biyu ne in sha Allah..." Khaleesat was speechless ta dinga kallonsa babu ko kiftawa cike da mamaki, can kuma ta kalli lafiyayyen motar da ya nuna nata, tuni ya karasa ya amshi trolley dinta ya tafi ya bude booth ya saka, sannan ya bude mata bayan mota yace "Bismillah Hajiya" Sauke idonta tayi kasa taji kafafuwanta sun mata nauyi amma a haka tana tafiya a hankali ta tafi ta shiga back seat sannan ya kulle motar, ya zaga ya shiga driver seat, Hotel me tsada sosai that isn't far away from the airport ya kai ta, sai da ya tabbatar tayi check in har zuwa dakinta sannan ya bar hotel din, tana shiga babu jimawa wata ma'aikaciyar hotel din ta kawo mata lafiyayyen Breakfast, ita dai Khaleesat ba um bare um um, gaba daya kanta ya gama kullewa, tashi tayi ta bude trolley dinta ta dau Shower gel zata yi wanka. Khaleesat na bacci wajen karfe daya da minti ashirin vibration din wayarta ya tasheta, ta jawo wayar a hankali tana duba me kiranta taga mutumin da ya kawota Hotel ne, ta mike zaune sannan tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yayi mata sallama sannan yace "Hajiya fatan kin shirya in taho in dauke ki, flight din naki nan da minti talatin ne in sha Allah" a hankali Khaleesat tace "Toh" Yace "Gani nan tahowa yanzu da izinin Allah" Yana katse wayar Khaleesat ta sauka daga saman gado taje tayi alwala a bandaki, tana idar da sallan Azahar sai ga kiransa, ta dau trolley dinta da handbag ta bar dakin hotel din ta sauko downstairs, yana hangota a Reception din hotel din ya tafi da sauri ya amshi trolley din hannunta, ya karbi makullin dakin ya kai ma Receptionist, sannan suka fita haraban hotel din ya bude mata back seat bayan ya saka trolley dinta a booth, cikin mintuna kadan suka isa MMI Airport, sai da ya tabbatar ta amshi boarding pass dinta sannan yayi mata sallama da murmushi fuskarsa yace "Toh Allah Ubangiji ya tsare Hajiya, idan kun sauka kanon za a karasa dake gida in sha Allah... We will keep in touch" a hankali Khaleesat tace "Toh Nagode, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajjaju, nagode kwarai, Allah Ubangiji ya kai ku lafiya" A haka suka rabu ta nufi Departure lounge walking slowly, bayan kusan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin kano. Suna sauka kano Khaleesat ta fito daga cikin airport gabanta na faduwa, sai gyara nose mask din fuskarta take tana waige waige, yanzu ina ma ta nufa tukun, tasan ko da wasa bazata nufi gida ba dai, wayarta ya fara ring ta duba da sauri gabanta na ci gaba da faduwa, wata lamba ce ke kiranta tayi picking tayi shiru, taji an mata sallama ta amsa, mutumin ya gaisheta yace "Hajiya Hamisu ne ya aiko min lambarki, naga jirgin ku ya sauka yanzu, yace za a karasa dake gida, kina ta ina yanzu?" Tace "Na fito outside of the airport" Tahowa taga mutumin yayi zuwa inda take tsaye bayan ya hangota, nan ya kai ta har motar dake jiranta, motar shigen wanda ta shiga a Abuja ne, mutumin ya bude mata back seat ta shiga tace "Nagode" Yayi bowing kansa yayi mata sallama yace "Allah ya kai ku lafiya" Tace "Ameen Nagode" Drivern dake mazaunin driver ya gaisheta yana tambayarta ya hanya sannan ya tada motar suka fita daga airport din yace "Ina muka nufa Hajjaju?" Khaleesat ta Ι—an yi shiru kamar me nazari, sai kuma tace "Hotoro zaka kai ni" Yace "To Allah ya kai mu lafiya" Suna isa dai dai kofar gidan da ta nuna masa ya tsaya, ya bude motar ya sauka don fiddo mata Trolley dinta a booth, bude motar tayi ita ma ta sauka tana gyara facemask dinta, ta amshi akwatinta a hannunsa sannan tayi masa godiya ta shiga cikin gidan da sauri, Baaba Gaje dake zaune tana tankade garin tuwo ta daga kai tana kallonta, Khaleesat ta Ι—an sauke Facemask dinta tana murmushi tace "Baaba sannu da aiki" Baaba Gaje ta ajiye rariyar hannunta tace "Khaleesatu? Daga ina kuma haka?" Khaleesat ta duka nan gabanta har sannan tana Ι—an murmushi tace "Makaranta" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai ko minti ashirin banyi da dawowa daga gidanku ba kuma ba ace min kina hanya ba" A hankali Khaleesat tace "Baaba ya jikin Ummanmu fa?" Baaba Gaje tace "Kaddai ba a san kin biyo hanya ba kika taho Khaleesatu?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai jikin nata da sauki er nan, shi Awdul din ne ya biya maki kudin jirgi kika dawo?" Khaleesat ta girgiza kai gabanta na faduwa tace "Bai san na dawo ba Baaba" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to bari in kira Parida, ko kuma ke ki kirata da kanki, Gwara da kika yi dubaran zuwa nan kada Salubabben uban nan naki ya sa ki a bakin duniya mu shiga uku, Ga tabarma taho ki zauna ki huta, irin wannan tafiya me nisa haka, naji ance Amurkan har yapi legas nisa ko? Kira Paridan mu ji yanda za ayi" Khaleesat ta zauna gefenta ta bude handbag ta ciro wayarta, duk da yanda gabanta ke faduwa haka tayi dialing din lambar kanwar Ummanta Aunty Farida, Baaba Gaje tace "Auu to ai Parida ba waya a hannunta wai an sace a mota" Khaleesat ta daga kai tana kallonta, Baaba Gaje tace "Abinda zai faru kawai ga garin tuwon nan ki karasa tankade min ga can murhu na dora ruwan tuwo in yayi ki min talgi ki tuka tuwon in ya silala ki kwashe, ga kuma kayan miya can bai dai da yawa ki jajjaga ki kada min miyar kuka, ni kuma sai in koma can Mariri yanzu in sanar ma Ummanku kin zo" Khaleesat tace "Toh Baaba" Mikewa Baaba Gaje tayi ta figi yakunennen gyalenta a igiyar shanyan dake Ι—an karamin tsakar gidan ta yafa tace "Bara inje, dama ina da canjina dari da hansin sai in roke masu Ι—an sahu su kai ni ko Farawa ne sai in karasa Maririn da kafa ta" Khaleesat ta bude handbag dinta amma sai taga Dollars kawai, ta daga kai ta kalli Baaba Gaje tace "Wallahi bani da kudin Nigeria a nan Baaba, amma bari in ciro a POS yanzu sai in baki kudin adaidaita sahun" Baaba Gaje tace "Aa yi zamanki kiyi aikin da na sa ki, minti nawa ne nan da Mariri, kawai dai ga wanke wanke can bakin kwararo ki wanke min har su, ki share tsakar gidan nan, in yaran nan suka dawo islamiyya ki dauraye masu Uniform dinsu, dakin ma na nan sunyi kaca kaca da shi babu kyan gani" Daga haka ta fice daga cikin gidan bayan ta saka slippers dinta, Khaleesat ta cire mayafin abayan jikinta ta dora kan akwatinta sannan ta ci gaba da tankaden da Baaba Gaje ta bar mata, Baaba Gaje makociyarsu ce a can unguwansu Mariri kafin 'ya yanta su siya mata wani Ι—an kararramin gida a nan Hotoro Tsamiyar boka ta dawo tana zaune da jikokinta biyar tana dubasu, zaman mutunci da amana Baaba Gaje suka yi da Mahaifiyar Khaleesat da ta dauki Gajen tamkar uwa. Wajen karfe shidda saura Khaleesat ta gama duk aikin da Gaje ta loda mata sannan ta dora ruwan da zata yi wanka a sauran rushi, zaunawa tayi kan tabarma ta jingina da bango don ta gaji likis, Housemate dinta ne ya fado mata, ta dai yi shiru staring into space, after a while ta sauke idonta a hankali ta mike ta shiga da kwanukan da ta wanke cikin dakin Gaje, dai dai nan Gaje ta shigo cikin gidan da Aunty Farida, Khaleesat ta tafi da gudu ta rungume Aunty Farida cike da murnan ganinta, Aunty Farida na kallonta tace "Ke kuma da wa kika yi shawara kika biyo hanya Khaleesah? Abdul din ne yace ki taho?" Gaje ta daga hannu sama da sauri tace "Aaaa tace bai ma sani ba" Aunty Farida na kallon Khaleesat da mamaki tace "Ban gane bai sani ba??" Khaleesat ta marairaice ta kauda zancen ta hanyar cewa "Aunty ya jikin Ummanmu?" Aunty Farida ta kamo hannunta suka zauna saman tabarma tace "Ai jikin Umma da sauki sosai Khaleesat, gashi har an sallamemu a asibiti, wa yace maki bata da lafiya ne ma tukun?" Khaleesat da har hawaye ya ciko idonta tace "Aunty Sha'awa" Gaje tace "Lahh ha ila, wato Sha'awa bazata dena munafurci ba ko? Wato bazata canxa hali ba ko? Da kaina fa sai da na jaddada mata kar ta gaya maki ko kin mata sako ta wassol don kar hankalinki ya tashi, ashe sai da munafukar ta zaga ta fada maki" Aunty Farida tace "Toh Allah ya kyauta, kwata kwata Sha'awa bazata canza ba" Khaleesat da hawaye ke cika idonta tace "To Aunty ta yaya zan ga Ummanmu yanzu?" Aunty Farida tace "Kar ki damu kiyi zaman ki nan wajen Baaba Gaje, gobe da safe in za mu tafi asibiti sai mu fara biyowa ta nan da Umman tunda asibitin Malam Aminu kano ne" A hankali Khaleesat tace "Toh Allah ya kai mu Aunty" Sai bayan Magrib Aunty Farida ta bar gidan bayan ta ci tuwon da Khaleesat tayi ma Gaje, sosai Khaleesat taji ta samu rest of mind bayan taji jikin Ummanta da sauki, bayan Isha Gaje ta gyara mata Ι—an lungun da zata kwanta a dakin ta daura mata net din sauro tace "Allah dai ya rabaki da cinnaku" ita dai Khaleesat tayi murmushi kawai bata ce komai ba, ita matsalarta ma zafi, ko ya zata yi da zafi yau gashi karamin dakin wani Ι—an mitsitsin window ne kawai ke garesa, su bakwai kuma zasu kwana a ciki, Khaleesat ta gama shirin kwanciya don tayi wanka sannan ta shiga net din ta kwanta, ta amshi maficin da gaje ke mika mata ta cikin net din, tun dawowarta sai a sannan tayi subscription ta shiga WhatsApp dinta, Message din Safiyyah dake tambayarta ko ta isa lafiya kadai tayi ma reply, bata yi mamakin rashin ganin message din Abdul ba don she isn't even expecting his message, ajiye wayar tayi ta gyara kwanciyarta ta lumshe ido, Housemate dinta ne ya fado mata, she have no access to him balle ko godiya ma tayi masa, bata yi tunanin da ta fito zata tafi airport bazai tambayeta phone number dinta ba, ko Airport din ma bata yi tunanin bazai yi offering yace zai kai ta ba, juye juye kawai take yi a net din idonta a rufe, after a while of thinking bacci ya dauketa. Washegari Khaleesat ta gama yi ma Baaba Gaje duk aikace aikacen gidan, ta hura gawayi ta daura ruwa tayi ma kananun jikokinta wanka sannan ta dama kunu, Baaba Gaje ta fita siyo masu kosai a titi, har karfe goma Khaleesat bata ga Aunty Farida sun zo gidan da Ummanta ba, gaba daya ta damu taga Ummanta, Baaba Gaje tace "To ke sai ruwan ya salance zaki je kiyi wankan? Ba fa wani gawayin" Khaleesat tace "Zan yi" Daga haka ta mike ta tafi yin wankan, tana fitowa daga wanka taga takalmin da Aunty Farida ta zo da shi jiya a bakin kofa da wani takalmin daban wanda ko ba a fada ba tasan na Ummanta ne, da sauri ta shiga dakin Baaba Gaje taga Ummanta da Aunty Farida a zaune, tsallake Aunty Farida tayi ta tafi gun Ummanta da gudu cike da farin cikin ganinta ta durkusa gabanta ta rungumeta, Aunty Farida tace "Ko dai baki da hankali ne?" Baaba Gaje tace "Toh da sauki dai kam" Ita dai Umman sai kallon Khaleesat take, gaba daya Khaleesat ta ma mance wai Umma bata da lafiya tsabar farin cikin ganinta, a hankali Umma tace "Meyasa zaki biyo hanya Khaleesah? Abdul din ne yace ki dawo?" Khaleesat ta kamo hannunta cike da damuwa tace "Umma ya jikin?" Umma tace "Naji sauki Alhamdulillah" Khaleesat tace "Aunty Sha'awa tace min ko magana fa baki yi" Baaba Gaje ta rike haΙ“a tace "Oh ni 'ya su, kun ji er iska ko? Wallahi Sha'awa da kyar taga annabi, babu yanda bamu yi da ita ko da wasa kar ta gaya maki ba ashe sai da ta zaga ta fada, har ce mata nayi tace maki tayi tafiya ko da zaki buga nata wassol" Khaleesat ta daga kai ta kalli Baaba Gaje tace "Ni ce na kirata don ina ta magana bata min reply ba" Aunty Farida tace "Ai tsabar munafurci yasa ta gaya maki ba wani abu ba" Khaleesat ta Ι—an yi murmushi ta gaida Aunty Farida, Aunty Farida ta amsa tace "Amma shi Abdul yasan Umma bata da lafiya shine ko kira ya dubata bai yi ba?" Khaleesat ta sauke idonta kasa tace "Ni fa bai san na dawo ba Aunty" Aunty Farida tace "Wai ban gane bai san kin dawo ba, wa ya biya maki kudin jirgin?" Khaleesat ta daga manyan idanuwanta tana kallonsu, Sai kuma a hankali tace "Wani ne ya biya min ba Abdul ba" Umma ta kalleta da sauri tace "Wani?" Da mamaki Aunty Farida tace "Wani a ina?" Khaleesat na kokarin mikewa tace "Neighbor dina ne" Umma ta bude baki tana kallonta, sai kuma tace "Ko baki da hankali ne, waye ya biya maki kudin jirgi Khaleesah?" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Gaje tace "Bude baki zaki yi ki mana bayani dalla dalla, waye shi zai biya maki zunzurutun kudi na jirgin da naji ance ya fi miliyan daya? A ina kika san sa?" Still dai Khaleesat taki cewa komai, Aunty Farida tace "Ke bana son rainin wayo uban wa zaki ma shiru ana maki magana? Ko baki ji tambayar da ake maki bane?" Umma dai kallon Khaleesat kawai take da mamaki, Khaleesat ta koma baya ta Ι—an sunkuyar da kanta a hankali tace "Ni fa nace makocina ne ya biya min, kuma ai gani yayi ina ta kuka Ummana bata da lafiya shine ya biya min jirgi in dawo in dubota" Cikin sanyin murya ta kare maganar, Baaba Gaje tace "Atoh dama ai ko ina ana samun na Allah, Allah ya masa albarka, Bature ne ko?" A takaice Khaleesat tace "Um" don bata son ma a ci gaba da zancen, Baaba Gaje tace "Ko da naji, ai sai baturen dama, wani baΖ™in fata ne zai biya maki jirgi don yana makocinki, ai ko mutuwa uwar taki tayi iyaka ya maki gaisuwa ya kama gabansa, to Allah ya saka masa da alkhairi, abinda ma baturen kudin jirgin ba wani kudi bane a wajensa, ji zai yi kamar naira dubu goma ya kashe fa" Khaleesat na kallon Aunty Farida tace "Aunty yanzu za aje asibitin ne?" Aunty Farida tace "Aa mu har mun dawo daga asibiti sai kuma na gobe in Allah ya kai mu" a hankali Umma tace "Toh da ya biya maki kudin jirgin zuwa wa zai maki na komawa yanzu? Kinsan dai ko hauka kike baza ki bari Abdul yaji wannan batun ba ki ja mana masifa ko?" Sai da gaban Khaleesat ya fadi, a hankali ta sunkuyar da kanta, ita gaba daya ta ma mance ashe biyan jirgi za ayi a koma, nan da nan jikinta yayi mugun sanyi, yanzu ina zata samu kudin ticket din komawa, she became so weak at once, Aunty Farida tace "Toh shi Abdul din baki ce masa Umma bata da lafiya bane?" Khaleesat da har sannan jikinta yake a sanyaye ta girgiza kai tace "Baya nan ne" Daga haka ta mike ta tafi zata shirya don zanin da tayi wanka ne daure jikinta har a lkcn, Khaleesat na cikin saka kayanta da ta fiddo a akwati 1000 dollar din da Housemate dinta ya bata suka fado mata a rai, ta zaro ido lkci daya taji hankalinta ya kwanta har sai da ta sauke ajiyar zuciya, tasan probably in ta canza har da 100 dollar din da Safiyyah ta bata kudaden za su iya maidata Amurka, she felt so relieved, nan da nan walwalarta ya dawo, tana jin Baaba Gaje na tambayar Aunty Farida ko kishiyoyin Ummanta sun shiga dubata yau, Aunty Farida tace "Jiya ma basu shigo dubata ba sai yau Baaba Gaje" Baaba Gaje tace "Shegu matsiyata, so fa suka yi ace ta mutu, to shi Malam Alin ya ku ka Ζ™arke da shi? Ya bada kudin?" Aunty Farida tace "Aa ni fa ban bi ta kansa ba Baaba Gaje, dama me ya tsinana kafin in zo kanon? daxu ma aka turo min sauran kudin adashina da nake jira, duk na siya sauran magungunan" Baaba Gaje tace "Atoh dai bai taΙ“uka komai ba a takaice, shi ma da zaki basa yanxu tsaf zai amshe" Har aka yi azahar su Umma da Aunty Farida na gidan, Umma har tayi bacci ta tashi saboda maganin da take sha, har a sannan da kyar take taka kafarta daya, hannunta dai ya sake ya dawo normal tun a jiya, Khaleesat ta shigo dakin da shinkafa da waken da ta dafa, Baaba Gaje kuma ta shiga makota dubiya, Aunty Farida dai sai bin Khaleesat take da kallo, sosai taga ta kara kyau tayi fresh, duk da dai tana nan a yanda take babu kiba, komawa tsakar gida Khaleesat tayi ta dauko man gyadan da ta soya ta dawo dakin, ta fara zuba ma Umma da Aunty Farida abincin, Umma dake zaune kan darduma tana kallonta tace "Kun fara jarabawan ne?" Aunty Farida tace "Haba dai sun fara jarabawa zata taho? Ai bazai yiwu ba, ko ana haka ne?" Khaleesat dake sauraronsu ta girgiza kai tana Ι—an murmushi tace "Da sauran lokaci bamu fara ba tukun" Aunty Farida tace "To yanzu dai tun kan wani munafukin yasan kina garin nan mu shiga uku yaushe za ki koma Khaleesah?" Khaleesat ta daga kai a hankali tace "Cikin satin nan in sha Allah" Aunty Farida tace "Toh inji dai Abdul din ya rage abubuwan nan nasa da yake maki?" Khaleesat ta ajiye masu abincin a gabansu kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "Babu abinda ya fasa, ni na gaji da halinsa ma yanzu" Umma ta daga kai tana kallonta, Aunty Farida ma kallonta take don bata taΙ“a cewa ta gaji da halin Abdul ba, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya ta fara cin abincin gabanta tace "Na dai gaya maki babu me canza maki shi sai ke da kanki, ke macece ya kamata ace zuwa yanzu kinsan wanene Abdul kinsan kuma yanda zaki zauna da shi" Mikewa Khaleesat tayi without saying anything don ita yanzu taji ko zancen nasa ma bata so har cikin ranta, tun shekaranjiya da yayi fushi har yau bai kirata ba ita kuma as far as tayi masa miss calls har biyu to bata ji zata iya sake kiransa ba unlike before da ta dinga kiransa kenan ko da bazai daga ba, ko kuma tayi ta masa magana ta WhatsApp, to yanzu kam bata ji zata iya ba.....

 

 

07087865788✍🏻

 

*Still on free pages*

[5/4, 8:14 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

 

7.....

 

Kwanan Khaleesat hudu yau a garin kano, kuma har a sannan babu wanda yasan da zuwanta a cikin yan gidansu, ko nan da can bata fita a gidan Baaba Gaje don ma kar tsautsayi ya sa ta hadu da daya daga cikin yan gidan nasu, a kwanaki hudun nan sau biyu Ummanta da Aunty Farida suka zo gidan Baaba Gaje dominta, zuwa sannan Umma ta warware gaba daya tafiyarta ya dawo normal, tun kwanaki biyu da suka wuce ta gama amsan treatment dinta a hospital sai magunguna da take sha kawai, har zuwa ranan kuma Abdul bai kira Khaleesat ba, ita kuwa kawai taji ko a jikinta da ya kira da kar ya kira, there wasn't an atom of disturbance a tattare da ita, ko ta WhatsApp bata yi gigin yi masa magana ba Unlike before da bazata iya hakuri ba sai ta masa, tana bakin murhu tana dafa shinkafa da wake ga turmi gabanta tana Ι—aka yajin da za ayi amfani da shi wajen cin shinkafa da waken, Su Ummanta da Baaba Gaje kuma na can uwar Ι—aka, tunanin yanda zata fara shirye shiryen komawa USA take don suna da wani presentation nan da kwana uku, daxu da safe ta duba available flight da farashinsu online and she is hoping in ta canza dollars din da Housemate dinta ya bata zai isheta ta koma, Khaleesat ta bar daΖ™an yajin da take yi bayan taji Aunty Farida na kwalo mata kira, mikewa tayi ta wuce dakin tana amsawa, tun da ta zo gidan Baaba Gaje ta sakar mata aikin komai, hatta jikokinta ita ke masu wanka kan su tafi makaranta, ita taga kamar har ta Ι—an yi duhu tsabar girki cikin rana da take yi tun zuwanta, Aunty Farida tace "Ana kiran wayarki" nan da nan mood din Khaleesat ya canza ta karasa gun wayar without much interest, duk tunaninta Abdul ne cause she isn't expecting any call from anybody, Number mutumin da ya tarbeta a Airport din Lagos ta gani a gaban Screen din wayarta, ta dinga kallon number bata ko kiftawa, duk da bata yi saving ba amma ta gane nasa ne, daukar wayar tayi ta fita daga dakin ta koma bakin murhun sannan tayi picking ta kai kunne, sallama yayi ya gaisheta da ladabi, tace "Ina yini?" Yace "Alhamdulillahi Hajiya, ya jama'ar gidan?" Tace "Alhamdulillah" Yace "To maa sha Allah, dama na bugo ne inji ko zaki kara kwanaki nawa nan gaba kan ki koma America?" Khaleesat tayi shiru trying to understand why he is asking her that, yace "Hello?" Tace "Ina jin ka, ban gane tambayar bane" Calmly yace "Aa so nake in san ranan da zaki koma ne Hajiya, in ya kama ayi rescheduling din ticket dinki sai ayi hakan in sha Allah" Khaleesat was speechless, a ranta tace Ticket kuma? Kasa cewa komai tayi with surprise, taji ta ma kasa ci gaba da tsayuwa, jin ya sake cewa "Hello" ta kifta ido da kyar ta duka kusa da turmin da take daka yaji tace "Ina ji" Yace "Ina ga a bari duk sanda kika shirya zaki nemeni ta waya ko Hajiya?" Sauke idonta tayi kasa, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, cikin sanyayyen murya tace "Ranan Lahadi nake son zan koma idan Allah ya yarda" Yace "To Maa sha Allah, dama booking din ranan aka maki da zaki taho, flight din karfe daya ne, za ku tashi ta Airport din Abuja in sha Allah" Ita dai Khaleesat ta kasa cewa komai, yace "Sai kin ji ni in sha Allah Hajiya" A hankali Khaleesat tace "Nagode" Khaleesat na zaune dakin Baaba Gaje tana jujjuya shinkafa da waken dake gabanta da cokali, gaba daya ta kasa cin abincin, ita kanta ta rasa dalili, ko tsabar yanda jikinta yayi sanyi ne tun bayan da suka yi waya da mutumin daxu da ya sanar mata da ticket dinta na komawa America sannan tana gama aikin da take ta bude WhatsApp taga ya aiko mata da Flight Ticket dinta which was also business Class kamar dai yanda ta zo, this made her so weak, gaba daya ta ma rasa gane feeling din dake ranta a lokacin, bata taba tunanin Housemate din nata zai mata ticket din komawa ba, Duk Ummanta na lura da sauyawanta lkci guda, Aunty Farida ta gama shafa powder din da take zata leka gidan wata kawarta Maman Fu'ad a nan hotoron, ta dau jakarta da mayafi tana kallon yayarta tace "To sai na dawo Umma" Umma tace "Amma kar ki dade don Allah Farida" Aunty Farida tace "Haba ai yamma tayi bazan zauna ba Umma" Daga haka ta fita daga dakin tayi ma Baaba Gaje dake waje tare da bakuwarta sallama sannan ta fita daga gidan, Umma ta daga kai tana kallon Khaleesat tace "Menene kika saka abinci a gaba kika kasa ci Khaleesat?" Khaleesat ta daga kai da sauri tana kallon kyakkyawan fuskar Ummanta, babu wanda zai ce Umma ce ta haifeta sai dai ma yayi tunanin yayarta ce don kama suke ba na wasa ba kamar an tsaga Ζ™ara, Khaleesat tayi murmushin yake ta kai shinkafa da waken baki tace "Babu komai fa Umma" Umma tace "Yaushe za ki koma? Kuma yaya za ayi da batun kudin jirgi? Har yanzu Abdul din bai san kina nan ba?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Umma ai nace baya nan kuma ba a samunsa ta waya, ranan lahadi zan koma in sha Allah" Umma tace "Ranan Lahadi? To ina za ki samu kudin komawa?" Khaleesat ta gyara zamanta tace "Makocin nawa ai tare ya biya min na zuwa da dawowa" Kallonta Umma ta dinga yi da alamar tuhuma ga mamaki kwance fuskarta, Khaleesat taki yarda ta bari su hada ido sai tura abincin gabanta take, Umma tace "Khaleesah" Da kyar Khaleesat ta daga kai gabanta na faduwa, Umma tace "Meye tsakaninki da wannan mutumi da ya biya maki kudin jirgin zuwa har da na komawa?" Khaleesat ta hadiye sauran shinkafar da ya makale a throat dinta da kyar tace "Wallahi Umma babu komai, makocina ne kawai shi, kuma don yaga yanda na daga hankali baki da lafiya shi ne yasa yayi hakan, ni kaina sai bayan da ya biya min na sani, amma ki yarda dani Umma babu komai tsakanina da shi" Kamar zata yi kuka ta kare maganar, Ummanta ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru, bayan some seconds tace "Toh shikenan, amma dai kinsan in Abdul ya samu labarin nan da matsala ko?" Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba, jin Umma tayi shiru alamar ta fada duniyar tunani Khaleesat ta daga kai a hankali tace "To ai Umma babu wanda yasan na zo kano har yanzu, don haka bazai sani ba" Umma ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "To gudun kada hakan ya sake faruwa kar ki sake yarda ko wata mu'amula ta hadaki da shi makocin naki Khaleesat, ki rufa mana asiri" Khaleesat bata ce komai ba sai kuma ta jawo handbag dinta ta ciro dala dubu dayan da Housemate dinta ya bata ta nuna ma Umma cikin sanyin murya tace "Wannan ma shi ya bani da zan taho" Umma ta dinga kallon kudin duk da bata san ko nawa bane ta dai ce "Ki kula don Allah Khaleesat kar ki ja mana magana kin dai san wanene Abdul kin san kuma waye Babanki" Khaleesat dai tayi shiru, tasan Umma bata san har nawa bane Dollars din in an canza zuwa Naira, ita dai tayi shiru bata gaya mata ba kar ta kara daga mata hankali. Washegari da wuri Khaleesat ta shirya ta saka Nikab dinta ta fita don zata je canza dollar din nata ta dan yi siyayya, bayan ta canza dalolin taga har ya wuce yanda take tunani a Naira, nan ta fara zuwa inda zata siyi waya, ta siya ma Ummanta da Aunty Farida sabbin wayar Android iri daya na dubu dari da hamsin each, Ganin Baaba Gaje ma bata da waya kuma ba iya amfani da Android zata yi ba ta siya mata karamar waya na dubu ashirin, daga nan ta karasa kasuwa tayi siyayyar yan abubuwan da zata koma USA da shi, ta siya ma siblings dinta twins mata sabbin school bag da schl shoe da socks, ta siya masu atamfofi kala uku each da mayafai da takalma masu kyau da inner wears, jikokin Baaba Gaje ma ta siya masu takalma da inner wears gaba dayansu, pharmacy ta shiga da takardan da aka rubuta magungunan Ummanta ta siya mata na wata biyu duk da tsadar magungunan, kusan Azahar ta koma gidan Baaba Gaje ta tarar su Ummanta basu zo ba. Washegari asabar Khaleesat na shanya kayan jikokin Baaba Gaje da ta wanke, Baaba Gaje kuma na shirin fita kasuwa Ummanta suka shigo gidan tare da Aunty Farida da Siblings dinta yan biyu Islam da Noor that are just 11 years old, da gudu suka tafi suka rungumeta suna mata oyoyo, sosai kannin nata ke kama da ita, Khaleesat was so happy seeing her twins Siblings wanda su uku kawai Ummansu ta haifa, Baaba Gaje tace "Basu tafi islamiyya bane?" Umma tayi kasa da murya tana kallon Gaje tace "Sun ma kwana biyu rabonsu da zuwa, ba a biya kudin wata ba" Baaba Gaje tace "Ikon Allah to Alin ca yayi bazai biya ba kenan?" Umma tace "Cewa yayi in dora masu talla kamar yanda yan uwansu ke yi tunda su ba 'ya yan Gwal bane, dama ba fa shi ke biya masu ba wannan karan ne bani da kudi duk jarin ya lalace shine nace su tambayesa" Baaba Gaje tace "To Allah ya kyauta, amma Ali dai haΖ™Ζ™in 'ya ya da kyar ya bari ya jiyo kamshin aljanna balle yaje kusa da ita" Ita dai Khaleesat a sanyaye ta kama hannun kannin nata zuwa dakin Baaba Gaje, tana jin Baaba Gaje  na cewa "Amma de suna zuwa bokon?" Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina fa, islamiyya ma da ya zama dole ba aje ba sae wani boko" Aunty Farida ta girgiza kai cike da takaici tace "Allah de ya kyauta, shi fa bakin cikin bata dora ma yaran talla kamar yanda sauran matansa ke dora ma nasu 'ya yan talla ba yake" Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi don duk sanda ta tambayi Ummanta ko kannen nata na zuwa boko da Islamiyya ta wayar Sha'awa sai tace mata eh suna zuwa, ashe basa zuwa, Umma dai bata ce komai ba suka shiga dakin gaba daya, Baaba Gaje tace "Kun ga bari inje kasuwa in dawo" Su Umma suka mata Allah ya kiyaye ta figi gyalenta ta fita daga gidan, Khaleesat ta fiddo duk siyayyan da tayi jiya, daga Ummanta har Aunty Farida kallonta suka tsaya yi, Aunty Farida ta rike haΙ“a tace "Haka kudin suke da yawa da kika canza? Kuma wa ya aike ki kashe kudi haka mu da muke da sabga a gabanmu Khaleesat? Maimakon ki bada a ajiye maki ko kujeru da setin gado ne da kudaden? Kin de san ko tsintsiya mahaifinki ba lallai ya siya maki da sunan a kai ki dakinki da shi ba ko?" Khaleesat tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Umma dai ta ma rasa abun cewa, Aunty Farida tace "Ni da kin yi shawara da ni duk baza ki yi wannan siyayyan ba, iyaka ki siyi abinda zaki koma can Amurka da shi, in suka tado da maganar aure me garemu da za a kai ki da shi Khaleesah?" Khaleesat na murmushi tace "Allah zai rufa asiri zuwa sannan Aunty" Aunty Farida tace "Yanzu duk kudin sun kare kenan?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Aa, saura dubu dari biyar" Daga Aunty Farida har Umma bude ido suka yi sosai suna kallonta with shock, Aunty Farida ta gyara zama tana zaro ido tace "Har nawa ya baki haka? Ko dai baki da hankali ne" Khaleesat ta kauda zancen ta hanyar cewa "Har fa da kudadena duk na canxa" handbag dinta ta jawo ta bude ta ciro sauran kudaden da suka rage don har wanda Safiyyah ta bata ta canza, ta kirga dubu dari a ciki ta ware, sannan ta kirga dubu dari da hamsin shi ma ta ware, kallonta kawai Umma da Aunty Farida suke, ta ba Aunty Farida dubu dari tace "Aunty kiyi kudin mota da wannan idan zaki koma Lagos sannan ki kara jari" Ta ajiye ma Umma 150k tace "Umma ki rike wannan a biya kudin makarantar su islam da Noor a kuma canza masu Uniform" Umma tace "Ko dai baki da hankali ne Khaleesah? baki ji shawaran da Farida ta kawo bane halan?" Aunty Farida ta mayar mata da 100k din tace "Aa gaskiya ban ga alamar da kan nan ba Umma, ina ga hakoranmu za mu je mu jera mata a gida idan bikin ya tashi...." Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Akwai fa kudade a account dina wanda Abdul ke bani kuma suna da yawa za su isa ayi duk abinda za ayi sannan Aunty" It took Khaleesat almost an eternity to convince her Mother and aunt akan su rike kudin da ta basu, nan kuma bata da wani kudin a zo a gani a account dinta sai miliyan 10 na Abdul da ya ajiye a account din wanda nashi ne ba nata ba, iya kudin foodstuff kawai yake tura mata duk karshen wata sai kuma kudin Uber na zuwa makaranta, sai house rent dinta da yake biya at due time, iya abinda kawai yake mata kenan amma naira biyar dinsa baya bata a matsayin kyauta, instead sai dai ya siya mata kaya masu tsada, monthly kuma yake mata subscription a waya, apart from this bai bata kudi da sunan kudin kashewa, a haka dai ta samu tayi convincing Umma da Aunty Farida suka amshi kudin da ta basu, Aunty Farida na kallon Umma tace "To kinga sai kiyi kaffa kaffa da wayar nan kar su sace maki tunda sun saba maki haka, kin dai ga ba dan karamin kudi aka siyo wayar da shi ba" Umma na kallon Khaleesat tace "To shi Malam din me kika siya masa?" Aunty Farida ta wani kalli yayarta, Khaleesat ma dai kallon Ummanta tayi bata ce komai ba, Aunty Farida ta kyabe baki ta kauda kai, Umma ta kalli Aunty Farida tace "Wai saboda hakki, naga ta siya min waya shima da sai ta nemi abinda ta siya masa kwatankwacin wayar, kuma bashi da wayar shi ma wallahi" Aunty Farida na kallon yayarta da kyau tace "Umma in kinsan zuwa za kiyi ki kyautar da wayar nan da ta siya maki to gwara dai ki bar mata kayanta, ina ce kwanaki can matansa ya siya ma Atamfa yar gadagalle lkcn bikin Salisu ke ya siya maki?" Umma tace "Aa ba ruwanta da wannan Farida, ai ubanta ne, kuma don ta siyi abu ta basa ai ba faduwa tayi ba" Aunty Farida bata sake tanka Umma ba ta fara harhada ma Khaleesat kayayyakin abinci da ta siyo waje daya, Sai kusan la'asar su Umma suka bar gidan kuma har sannan Baaba Gaje bata dawo ba, a boye Khaleesat ta ba Siblings dinta 50k wanda ta saka a karamin jakar Islam tace masu in sun je gida su ba Umma kuma ta ja masu kunni sosai kan daukan sabon wayar da ta siya ma Umma kar su lalata mata. Washegari da safe Khaleesat ta fito wanka wayarta ya fara ring tana dauka taga mutumin nan ne dai, bayan ta daga suka gaisa sannan yace "Hajiya nan da karfe tara da rabi wani driver zai kiraki sai kiyi masa kwatancen inda zai zo ya daukeki ya kai ki airport, don flight dinki zuwa Abuja na karfe sha daya ne, in kun iso Abuja kuma jirgin da zaki bi zuwa Amurka jirgin karfe biyu saura ne" Khaleesat tace "To ba damuwa Nagode" Aunty Farida kadai ce ta zo gidan Baaba Gaje yi ma Khaleesat sallama, Khaleesat bata ji dadin da Umma bata biyo ta ba, duk jikinta yayi sanyi sosai, a haka drivern da zai kai ta airport ya iso, Baaba Gaje ta dinga sa mata albarkan wayar da ta siya mata da abubuwan da ta siyo ma jikokinta, bayan an kai akwatin kayanta cikin mota su Aunty Farida da Baaba Gaje suka rakata har bakin motar, bayan Khaleesat ta shiga motar ta daga masu hannu a sanyaye tana murmushin karfin hali, har cikin ranta bata ji dadin da bata yi sallama da Ummanta ba, a haka suka kama hanyar airport da drivern da ya zo daukarta, suna sauka Abuja karfe daya da minti 40 jirgin su ya tashi. The flight to the United state was so comfortable for Khaleesat in her business class seat, don throughout bacci tayi, karfe hudu saura na asuba jirginsu ya sauka Maryland, It was soo cold in Maryland gashi bata da sweater a kayanta, bayan ta fito da luggages dinta tana duba Uber da zai kai ta gida tana rike da wayar kamar ance ta daga kai taga motar da yayi parking, kallo daya tayi masa sai kuma ta sauke kai kasa, ya karaso har inda take yace "Jirgin ya dade da sauka ne?" Sai a sannan ta kara kallon Sleepy face dinsa, sai kuma ta girgiza kai tace "Aa" Yace "Ohk let me drop you home" Daga haka ya koma gun motarsa ta bi bayansa with both of her luggages, ya bude booth ya amshi daya trolley dinta ya sa a booth, ita ma ta sa dayan, ya zaga ya shiga driver seat, tana jan kafa ta karasa front seat ta bude motar sannan ta shiga tana kallonsa da gefen ido, jinginar da kansa taga yayi da kujeran motar idonsa a lumshe, ta kulle motar gently, after few seconds ta sake kallonsa ga mamakinta sai taga kamar fa bacci yake, kallonsa ta dinga yi, and they seated for almost 3 minutes a haka ita dai bata tashesa ba kuma bata ce komai ba, Vibration din wayarta ne ya sa ya bude ido, ya wara ido ya fara kokarin tada motar, bude jakarta tayi to stop the alarm din da ya sa wayarta ke vibrate, bayan ya ja motar sun bar wajen, still not sounding normal yace "Ya jikin Mama?" Ta sauke idonta tace "Alhamdulillah, You shouldn't have bothered coming tunda akwai Lyft ko Uber" Without looking at her yace "The house key is with me, shi yasa na taho, cause i estimated when u are arriving" Bata sake ce masa komai ba shi ma haka, a haka har suka iso gida yayi parking, ya sake jinginar da kansa da kujeran motar, ita dai ta bude motar gently ta fita, jin fitarta ya sa ya bude ido, shi ma ya sauka daga motar, Entrance din shiga gidan ya nufa ta bi bayansa, Pajamas ne jikinsa sai Jacket da ya saka saboda sanyi, yana isa kofar ya kai hannu aljihu alamar zai ciro makulli, still taga yayi a bakin kofar, ita dai kallonsa kawai take, after some seconds ya juya yana kallonta, zuwa sannan his eyes are very clear gaba daya baccin ya gudu jin babu makulli jikinsa, ko bai gaya mata ba ta fahimci baya tare da makullin gidan, ya Ι—an sosa kai yace "I think.... I think, i left the key at where i am coming from, i am sorry about that Halysaah" Sauke idonta tayi without saying anything, ya juya ya nufi motarsa ta bi sa da kallo, sai da ya isa gun motar ya juyo, da sauri ta dauke kanta daga kallonsa, yace "Mu je in dauko makullin, ba wani nisa zuwa can, kinga it's cold out here baza ki iya tsayawa cikin sanyi ki jirani in dawo ba" Bata yi musu ba ta koma gun motar don yanzun ma sanyin take ji sosai, sai da ya shiga sannan ita ma ta shiga, his car was so warm, ya tada motar suka bar garage din, inda yace mata babu wani nisa taga sunyi tafiyar kusan 15 mins basu kai ba, nan taji gabanta ya fara faduwa, lkci lkci take Ι—an satan kallonsa ta gefen ido, wani unguwa suka shigo wanda ko wani gida da gate dinsa unlike some houses in US, daga karshe taga yayi parking ba tare da ya kashe motar ba yace "Let me get the keys" Bude motar yayi ya sauka ta bi sa da kallo taga gate din kusa da su ya bude ya shiga, tsaf take iya kallon hadadden gidan dake ta cikin gate din don ba irin gate dinmu na gida bane, ita dai sai bin unguwan take da kallo wanda ko ba a fada maka ba kasan na masu hannu da shuni ne a Amurka din, ba a wani dau lokaci ba sai gashi ya fito da wani Huge Dog dake biye da shi yana shisshige masa, wani faduwa gabanta yayi don a duniya tana mugun tsoron kare, ya duka yana patting Dog din yana masa magana at the same time, wani matashi ne dogo just like him ya fito daga cikin gate din gidan sanye da Pajamas shi ma, Khaleesat ta dinga kallonsa as if ta taΙ“a saninsa amma kuma bata san sa from anywhere ba, tana kallonsa tana gyara mayafin kanta kar ma ya kalli direction dinta su hada ido da shi, gabanta kuwa sai faduwa yake kamar mara gaskiya, matashin ya jingina da gate crossing his both legs yana kallon Housemate dinta taji yace "Daga ina kake?" Ƙin basa amsa Housemate din nata yayi instead ya mike yana tura masa Ζ™aton karen don karen tsaf zai ce zai bi sa, Calmly matashin yace "Ina za ka?" Housemate dinta ya kallesa yace "You have any issue with that?" Matashin ya Ι—an kalli motarsa calmly yace "Is that a lady in ur Car?" Housemate dinta yayi kamar bai ji sa ba still pushing the Dog to him, Matashin ya sake kallon motar, Khaleesat tayi saurin kauda kanta, tabe baki yayi yace "Enjoy" Daga haka ya ja karen suka koma cikin gidan, Khaleesat da duk taji conversation din nasu taji ranta ya baci, House mate dinta ya dawo cikin motarsa ya kulle without looking at her yace "Sorry for keeping u waiting Halysaah" Yana fara driving ta hade rai tace "Mene yasa bazaka gaya masa i am just ur housemate ba da kuma dalilin da yasa ka kawo ni nan din?" Housemate dinta yace "Never mind, ba wai yana da hankali bane"

 

 

07087865788✍🏻

[5/5, 6:00 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

8.......

 

 

Har suka isa gida babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu, yana parking a garage ya bude motar ya sauka, ita ma ta sauka tana satan kallonsa, kofar entrance din parlor taga ya nufa without looking at her, hakan yasa tana tafiya a hankali ta bi bayansa, ya bude kofar parlon ya juya ya kalleta, ita ta fara shiga parlorn sannan shi ma ya shiga ya kulle kofar, dakinta ta tafi bayan ta bude kofa ta juya ta kallesa, kwanciya taga yayi a kan 3 seater ya lumshe ido, ta shiga dakinta kawai ta kulle. Washegari da safe karfe takwas da 'yan mintuna Khaleesat ta fito daga dakinta, zaune ta gansa da text books a gabansa alamar he is studying, yana daga kai tayi saurin dauke idonta daga kallonsa, har ta karaso cikin parlon ta tsaya jikin kujera tana wasa da edge din mayafin jikinta, a hankali tace "Ina kwana" Ya ajiye pen din hannunsa yace "Good morning Halysaah" Still bata dago kanta ba kuma bata fasa wasa da gefen gyalenta ba, yace "How was ur trip?" Ta Ι—an kyafta ido tace "Alhamdulillah" Yace "Sorry jiya ban tambayeki jikin Mama ba, i was sleepy hope she is better now?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, tace "She is fine Alhamdulillah" Yace "Hope ur mind is now at rest?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, sai kuma ta Ι—an gyada masa kai, wayarsa ne ya fara ring ya dauka sannan yayi picking ya kai kunne, ta Ι—aga kanta tana kallonsa, taga shiru yayi alamar yana sauraron abinda ake gaya masa a wayar, after few seconds yace "It should be upstairs then" Daga haka ya katse wayar ya ajiye ya daga kai, da sauri Khaleesat ta dauke kanta daga kallonsa, Yace "Hope nothing Halysaah?" A hankali tace "Kawai, i want to appreciate you, thank you so much, Allah ya saka da alkhairi...." Cikin calm voice yace "No, You need not to Halysaah, iya abinda zan yi ma kanwata na maki ai" Cikin sanyin murya tace "To Nagode Allah ya saka da alkhairi" Ya Ι—an yi murmushi yace "To Ameen, so u can be this calm?" Ta wani kallesa, yace "Makarantar zaki tafi baza ki bari ki huta from ur long journey ba?" Ta sauke idonta tace "I am having presentation today" Yace "Ohk then, Allah ya bada sa'a" A hankali tace "Ameen" Ya nuna mata Trolley dinta da ya shigo mata da shi parlon yace "Ga boxes dinki can" Ta kallesu tace "Thank you" Yace "You are welcome" Daga haka ya ci gaba da abinda yake, Sai da ta kai su dakinta sannan ta dawo ta nufi kitchen, Tea kawai Khaleesat ta sha da Cookies sannan ta dauko jakarta zata wuce makarantar, makullin gidan ya mika mata yace "The house key...." Ta tsaya tana kallonsa, sai kuma tace "Ain't u using it?" Ya daga kafada yace "Will sort my self out" Shiru tayi at first, can kuma ta nufesa ta amshi makullin tace "Thank you" Yace "You are welcome" Daga haka ta fita daga gidan ta kullo masa kofar. Khaleesat na tafe tare da Safiyyah dake mata mitar Ya Mustapha yace bata daga kiransa, ita dai Khaleesat tafiyarta kawai take bata ce komai ba, Safiyyah ta tsaya tace "Ohh ga gantalalliya na maki magana ko?" Khaleesat ta tsaya tana kallonta tace "To me zan ce Sophie? Ke kanki kinsan ina da wanda zan aura to menene amfanin in daga wayar Yaya Mustapha? Beside wallahi ko da bani da wanda zan aura ni bazan kulasa ba, ai ana barin halaq ko don kunya" Da wani expression Safiyyah tace "Ban gane ba, as per cewar Surayya cousin sis dinki ce ko kuma kawarki ce? Where did u know her from? Meye hadinki da ita da har za a bar halal don kunya? Can you hear ur self pls? If you are not interested in my cousin brother ba sai kin ta corner corner ba kina kawo zancen da hankali ma bazai dauka ba, meye hadinki da wata Surayya da zaki bar halal don kunya?" Khaleesat tace "Ni dai don girman Allah ki ma bar wannan zancen, Ya Mustapha kuma kiyi ma Allah ki gaya masa i am engage, ni bazan daga kiransa ba" Safiyyah tace "Wallahi bazan fada ba ai kina da baki ki gaya masa da kanki, ke da wa aka yi engaging da zance masa u are engage? Ai as far as i am concern ni ban san wannan batun ba, kawai nasan kina da wanda baki da wani option sai na aurensa, but as time goes on ke kanki zaki san kina da option, za kuma ki ji baza ki iya auren ba sai dai duk abinda zai faru ya faru" Khaleesat ta taΙ“e baki tace "Kin ga ni yunwa nake ji zan tafi gida, sai gobe in mun hadu" Safiyyah bata tanka ta ba ta ci gaba da tafiya ta bar ta tsaye a wajen, Khaleesat ta bi ta da kallo, to wai ma ta yaya zata daga kiran Ya Mustapha, ita a rayuwarta abinda tasan in an mata bazata ji dadi ba ko by mistake ne bata yi ma wani, ita Safiyyah in ita ce a shoe din Surayya ya zata ji, wannan ai son zuciya ne ma kawai, bin bayanta Khaleesat tayi tace "Ni dai tunda ba mu da aji mu je gida pls ki mana girki i am very hungry and at the same time tired from yesterday's journey" A haka ta samu ta lallaba Safiyyah dake jin haushinta suka kama hanyar gidanta, suna sauka daga Uber ta nufi apartment dinta tana kallon Garage taga babu motar Housemate dinta, does this mean a bude ya bar kofar tunda makullin na hannunta, tana murda kofar taji sa a kulle, to ina ya samu key? ko dai magana yayi aka basa wani makullin, bude jakarta tayi ta ciro key ta bude kofar suka shiga cikin living room din tare da Safiyyah dake biye da ita, Safiyyah ta dinga bin parlon da kallo ta lumshe ido tace "Kai amma wannan turaren Housemate din naki ba dai dadin kamshi ba, the perf is so cool" Khaleesat dai bata ce mata komai ba, ta ajiye jakarta da mayafi ta zauna saman kujera tana ciro wayarta a jaka, Safiyyah ta zauna ita ma kan kujera tace "To kun hadu da Abdul din a Nigeria?" Khaleesat tayi shiru cause kawai taji ita ko maganar Abdul ma bata son ana mata yanzu, ganin yanda Safiyyah ta tsareta da ido, a takaice tace "Eh... me zaki dafa mana pls, wllhi yunwa nake ji" Safiyyah ta mike tace "Toh bari in je in ga what is available in the kitchen" Daga haka ta mike ta nufi kitchen, tana shiga bayan few minutes sai ga ta ta fito, tana kallon Khaleesat da mamaki tace "Kee wai Housemate din naki ne ke maku restocking abubuwa a kitchen haka? Look how ur kitchen is stocked up with costly food items, where is he getting the money to buy all this from?" Khaleesat tace "Baza dai kiyi girkin ba kenan in zo inyi?" Safiyyah tayi dariya tace "No wallahi mamaki nake naga abubuwa masu tsada yake siya, don ni dai nasan kudin da Abdul ke turo maki bazai taΙ“a siya maki wnn uban abubuwa dake kitchen din nan ba, anya bazan dawo gidan nan ba kuwa Khaleesat? Kinga wasu tsadaddun cookies da drinks da na gani, even the table water in this kitchen ba na yara bane wallahi, the fridge is full to the brim" Khaleesat taki tanka ta tana danna waya, hakan yasa Safiyyah ta juya ta koma kitchen tana kara jaddada anya bazata dawo gidan ba kuwa, Lafiyayyen girki Safiyyah ke yi a kitchen din komai baja baja malam, Sallah kawai Khaleesat tayi a daki ta dawo ta kwanta kan 3 seater tana danna wayarta waiting for the food to be ready, kiran Abdul ne ya shigo wayar hannunta, sosai gabanta ya fadi lkci daya mood dinta ya canza ta hade rai, ta dinga kallon screen din wayar fuskarta babu fara'a tana jiran sai ya kusa katsewa kafin tayi picking call din, dai dai nan taji alamar ana bude kofar parlon, ta mike zaune tana gyara scarf dinta sai ga Housemate dinta ya shigo parlon, sallama yayi ganinta zaune living room din, ta ajiye wayar hannunta ta fasa picking call din Abdul din ta amsa sallamar House mate din nata, yana cire takalman kafarsa yace "Good evening" Ta sauke idonta tace "Ina yini" Yace "Alhamdulillah, bakuwa kika yi?" Double foot wear da ya gani bakin kofar yasa yayi tambayar, tace "Um she is my course mate" Yace "Good" Daki ya nufa, sai a sannan ta kalli wayarta taga kiran Abdul har ya katse tuntuni, she wasn't bothered at all kuma bata yi attempting bin kiran nasa ba ta ajiye wayar kawai, mikewa tayi ta wuce kitchen, tare suka fito kitchen da Safiyyah bayan Safiyyar tayi dishing masu abincin a plate daya, Safiyyah na bin parlon da kallo tace "Ko dai Housemate din naki ya dawo ne kamshin turaren nake kara ji a parlon" Khaleesat ta dau spoon ta fara cin abincin tace "Ko dai kin san sa ne Safiyyah?" Dariya Safiyyah tayi tace "Ina kuwa na san sa, kawai so nake in gansa ne wallahi, irin wannan kayan alatu a kitchen haka, where is he even getting the money shi da ya zo ta scholarship" Khaleesat dai cin abincin gabanta kawai take taki ce mata komai, Safiyyah ta dau spoon ta fara cin abincin ita ma, basu jima da fara cin abincin ba sai ga shi ya fito daga dakinsa, bai kalli direction din da suke ba ya nufi kofa rike da laptop dinsa, Safiyyah ta bi sa da kallo kamar idonta zai fita ya bi sa, ita dai Khaleesat kallo daya tayi masa ta ci gaba da cin abincinta har ya fita daga parlon ya kulle masu kofa, Safiyyah ta ajiye spoon din hannunta tace "To fa, shi kuma haka yake? Ji wani Ι—aga shoulders da yake ko kallon inda muke bai yi ba, haka yake maki a gidan dama?" Khaleesat tace "You can be funny Safiyyah" Safiyyah ta hade rai tace "No like seriously haka yake feeling kansa? Ko don abincin da yake ajiye maki na yan gayu a kitchen ne ya ja haka? Ta yaya zai wani wuce mu babu ko Hi, ni fa bana son harkan walakanci" Khaleesat tace "Look Safiyyah ni ba shi ya ajiye min duk abinda kika gani a kitchen ba, shi baya ma zaman gidan nan, jifa jifa kawai nake ganinsa, beside ai mun gaisa da ya shigo kina kitchen, to kuma kallon me zai yi mana don zai fita?" Safiyyah zata yi magana wayarta ya fara ring, mikewa tayi ta dauko wayar, ta Ι—an buda ido tana kallon Khaleesat tace "Ke Abdul ne ke kirs" Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta ajiye cokalin hannunta ta dinga kallon wayar Safiyyah, Safiyyah ta rike haΙ“a tace "Ikon Allah, ko ya kiraki baki daga bane? Let me pick dai inji me zai ce" Da sauri Khaleesat ta kamo hannunta zuciyarta na bugawa tace "Safiyyah kar ki ce masa naje Nigeria plss cause bai sani ba wallahi" Safiyyah ta saki baki tana kallonta hangangan, da mugun mamaki tace "Ban gane bai sani ba? To wa yayi sponsoring tafiyar taki? Ina kika samu kudin tafiya" Sosai hankalin Khaleesat ya tashi a lkcn, tana girgiza ma Safiyyah kai tace "Just don't tell him pls, nace maki bai sani ba" Safiyyah da mamaki ya kasa barin ta tace "Ai kiran nasa ma ya katse" Khaleesat taji gaba daya abincin ya fita ranta, sai ga kiransa ya sake shigowa wayar Safiyyah, Safiyyah ta gwalo ido tace "Abdul ne da kirana har sau biyu? Anya lafiya" Khaleesat tayi gathering courage tace "Just pick, in ya tambayeki ni kawai kice masa bani da lafiya yanzu ma kika baro gidana" Safiyyah tace "Ohk" Picking call din tayi ta saka handsfree, ita ta masa sallama ya amsa yace "Ya kike?" Safiyyah tace "I am good" yace "Are you together with Khaleesat?" Babu bata lkci Safiyyah ta sanar masa exactly abinda Khaleesat tace ta gaya masa, ya dan yi shiru at first, sai kuma yace "Tun yaushe ne bata da lafiya?" Safiyyah ta kalli Khaleesat, da sauri Khaleesat tayi mata alamar sati daya da fingers dinta, Safiyyah tace "Yau ina jin sati daya kenan" Daga daya bangaren yace "Sati daya? Me yasa ba a gaya min ba, and what's wrong with her?" Safiyyah tace "Oh ni na zata ai ta gaya maka" Abdul yace "Wani irin rashin lafiya take haka dake hindering dinta from picking calls?" Safiyyah ta wani yamutse fuska jin useless question din da yake yi taki basa amsa tana kyabe baki, ita dai Khaleesat gabanta sai faduwa yake, Yace "Where is she now?" Sounding uninterested with the conversation Safiyyah tace "Tana gidanta mana" Da sauri Khaleesat tayi typing a wayarta sannan ta nuna ma Safiyyah, bayan Safiyyah ta ga abinda Khaleesat ta rubuta tace "Jikin nata dai da sauki sosai fa" A takaice yace "Thanks" Daga haka ya katse wayar, Safiyyah ta ajiye wayarta tace "Tirrrr, ki ji wani magana gatsau gatsau kamar dan daba, ko tashi hankalinsa fa bai yi ba, ni wallahi da ina da yanda zanyi ku rabu rabuwa na har abada da Abdul din nan wallahi yi zan yi, ko kadan bashi da features din miji na gari, babu caring babu tausayi babu affection, so pompous and full of himself always, nonsense and ingredient, wallahi in wani mutumin kirki ne da yanzu hankalinsa ya tashi duk ya birkice min a waya amma kiji yanda yake magana a tsattsaye kamar ubana daga karshe wai Thanks, kamar wanda nayi ma albishir me dadi wai Thanks, ke ki ji fa wai thanks" a hankali Khaleesat tace "Baza ki gane ba Safiyyah, nima naji i am fed up with him, na gaji da halinsa yanzu" Safiyyah ta rike haba da sauri tace "Ke Khaleesat, anya kece ke fadin haka kuwa?" Khaleesat ta wani taΙ“e baki ta jawo abinci ta fara ci tace "Kawai naji na gaji all of a sudden wllhi" Safiyyah ta sako baki tana mata kallon mamaki, can tace "Ni ba wannan ba ma, Khaleesat wa yayi sponsoring flight dinki zuwa Nigeria?" Khaleesat ta daga kai tana kallonta amma tayi shiru, Safiyyah tace "Kin yi shiru, waye ya biya maki kudin jirgi?" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "Housemate dina ne ya siya min Ticket" Safiyyah ta gwalo ido da wani expression na mamaki sosai tace "Ban fahimta ba Khaleesat, Housemate dinki as how?" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Eh shi ne ya biya min ticket din jirgin...." Khaleesat bata boye ma Safiyyah duk yanda aka yi Housemate din nata yayi sponsoring tafiyarta ba, Safiyyah was totally speechless and Surprise, after few seconds tace "Did you know what flight ticket is saying from USA to Nigeria Khaleesat?" Khaleesat tace "I went to Nigeria in business class and came back in Business class Sophie" Buda baki Safiyyah tayi ba tare da ta san tayi hakan ba tana kallon Khaleesat kamar idanuwanta za su fito, a hankali tace "Business class fa kika ce Khaleesat?" Khaleesat ta gyada mata kai, Safiyyah ta fara bin gidan da suke ciki da kallo that is for the average here in America, da wani Expression tace "Business class? To me yake yi a wannan gidan if he is doing this well that he can afford to pay for business class to and fro? Dama ni tun daga irin abubuwan da na gani a kitchen nasan wannan mutumi might be trying to disguise himself for a reason best known to him, idan ba haka ba why share an Apartment bayan zai iya affording shi kadai ya zauna a gidan, beside zai iya samun wanda ma yafi wannan in a more better area" Ita dai Khaleesat kallon Safiyyah kawai take ganin yanda tayi concluding lokaci daya, Safiyyah ta wani juya ido tace "Or did he have any mission here da bamu sani ba?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Daga sanda nayi misplacing makullina ne ya fara kwana gidan nan tunda yasan bani da makulli, amma tun da yayi move in zuwa gidan nan i can count sau nawa ya kwana if i remembered well, baya kwana nan wallahi, ba har na gaya maki ba...." Safiyyah tayi dariya tace "But i am trying to understand me yasa yake zaune a gidan nan, ko dai ya sanki from somewhere ne shine ya dawo nan saboda ke?" Khaleesat tace "Ji fa wani magana, bai san ni a ko ina ba wallahi, ni bamu taΙ“a haduwa da shi ba, ranan da suka fara zuwa gidan i overheard him asking if his housemate is a Male or female, lkcn ina dakina, kilan he is in a haste to settle down ne shi yasa kawai he opt for this, amma bai san ni ba wallahi" Safiyyah dai tayi wani murmushi tace "Ae shikenan we shall see" Sai kusan karfe bakwai Safiyyah ta bar gidan shi ma saboda azababben kiran da Ya Mustapha ke mata ne, tana mita haka ta bar gidan, bayan Khaleesat ta rakata ta dawo tayi sallahn magarib a nan parlon tana zaune saman darduma bayan ta gama azkar ta dau wayarta don dubawa ko Ummanta tayi mata reply, tun Safiyyah na nan suke Voice chat da Ummanta da kannenta, ganin Umma bata yi reply ba ta gane wayar ya mutu don dama Umma tace mata babu caji wayar ta kusa mutuwa, mamakin Abdul kawai Khaleesat ke yi a ranta, duk da ce masa da Safiyyah tayi bata da lafiya amma har yanzu bai kira wayarta ba, ko ta Whatsapp bai mata magana ba, tana cikin wannan tunanin taji an bude kofar parlon, juyawa tayi Housemate dinta ya shigo, sallama yayi ganinta a parlon, ta dauke idonta ta amsa, ya karaso cikin parlon without looking at her ya tafi inda Books dinsa suke yace "Kawar taki ta tafi kenan...." Khaleesat tace "Ina yini" Yace "Good evening Halysaah" Bayan ya gama daukan text books da zai dauka ya dawo cikin parlon yace "Alright Good night" Ta bi sa da kallo, sai da ya nufi kofa ya sake juyowa yace "Sai da safe" Ta sauke idonta tace "Allah ya kai mu lafiya" Daga haka ya bude kofar ya fita tana jin ya kulle kofar da makulli daga waje. Washegari Khaleesat bata da karatun da za su yi a makaranta, don haka har karfe goma bata fito parlor ba tana kwance, ita har sannan fa ta kasa daina mamakin Abdul don har sannan bai kirata ba, tashi tayi daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta shirya, wajen karfe goma da minti arba'in ta fito daga dakinta, kwance taga Housemate dinta saman 3 seater yana bacci, kulle kofar da tayi ne yasa ya bude ido a hankali, walking slowly ta karaso cikin parlon, juyawa yayi bayan ya sake rufe idonsa as if murmuring yace "Good Morning Halysaah" Tace "Ina kwana" Bai bude ido ba bai kuma amsa ba alamar ya ci gaba da baccinsa, ita dai ta wuce kitchen. After an hour Khaleesat ta fito daga kitchen bayan ta gama girkin da take, zaune ta gansa a parlon ya dafe kansa, tsayawa tayi tana kallonsa, ya daga kai suna hada ido ta Ι—an koma baya tace "Is everything okay?"

 

 

07087865788✍🏻

[5/6, 4:37 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

9.....

 

 

Still bai dago kansa ba yace "Tashi na kika yi" Ta Ι—an bude ido tana kallonsa tace "How?" Ya koma ya kwanta ya rufe ido yace "With the noise ur utensils were making in the kitchen" At first kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "To ai ba nan ya kamata ka kwanta kana bacci ba" Ya bude ido yace "Ok u intentionally woke me up kenan?" tace "Ni ban ma san kana parlon ba ai..." Murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba, tana Ι—an kallonsa a hankali tace "I made some breakfast, you can have some" Yace "Ok thanks, baki je schl yau ba?" Tace "Ba mu da lectures" Yace "Ohk, wani school kike?" Shiru tayi tana kallonsa, ya mike zaune yace "University of Maryland Baltimore? Loyola University Maryland? Morgan state University? Stevenson University? Johns Hopkins University?" Tace "Duk kuma a nan garin su ke?" Yace "Ohh, kina gari baki san makarantun dake garin ba?" Ta girgiza masa kai kawai still looking at him, shi dai bai kalleta ba yace "To ke wanne kike zuwa a cikinsu?" Ta sauke idonta tace "Na karshen da ka kira" Ya Ι—an yi murmushi yace "John Hopkins kenan? Buh ni ban taΙ“a ganin ko me kama dake a schl din ba ai" Yayi dariya yace "Just joking kafin ki fara min kuka" Ta wani kallesa, duk wannan abun bai kalli direction dinta ba yana magana ne yana kallon agogon wrist dinsa, yace wani course kike yi?" Tace "Pharmacology" Sai a sannan ya kalleta yace "Really?" Ta gyada masa kai, yace "That's a very good course, year what kike yanzu?" Calmly tace "Year 3" Ya gyada kai yace "Good, Allah ya bada sa'a" Ta sauke idonta tace "Ameen" Yace "Ban yi tunanin makarantar kike ba da na dinga dropping dinki in zan je ai, ko da yake ba lallai sanda zan je kina da Class ba...." Sunan wani lecturer dinsu ya kira mata, kawai ta Ι—an yi murmushi tana kallonsa cause he is one of her favourite lecturer, yace "He took us during our Undergraduate Degree, and Master's degree also, that was 3 years back, and he is still among my Supervisors currently...." Khaleesat dai sai kallonsa take, ta kasa hakuri har sai da tace "And you are still a student till date?" Ɗan murmushi yayi yace "I am a Medical Dr, pursuing my PhD on Cardiology" Khaleesat couldn't stop staring at him, Yace "I have been studying since i was a baby" Tace "Amma lecturer kake son zama?" Er dariya yayi yace "Not at all Halysaah...." Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba tana kallonsa, ya dau wayarsa da ake kira ya mayar ya ajiye yace "Kin ci abincin ne a kitchen naga ban ganki da plate ba as usual?" Ta wani kallesa bata ce komai ba ta juya tayi wucewarta daki, shayi ta sha da cookies a kitchen sanda take girki, bayan ta gama girkin kuma taji bata ma jin yunwan shi sa bata zuba abincin ba, Khaleesat ta koma dakinta da kusan 45 minutes tana duba wani course dinsu ta laptop taji kamar ana knocking din kofar parlor, ta mike ta fito parlorn, tsaye taga Housemate dinta bakin kofar living room din har ya bude kofar, Safiyyah ce ta shigo parlon tana kallonsa tace "Hello" Ya dauke idonsa yace "Hi" Komawa daki Khaleesat tayi, Safiyyah tace "Pls is Khaleesat around?" Yace "Sure...." Dakin Khaleesat ta nufa, shi kuma ya tafi ya ci gaba da karatun da yake a parlor, Khaleesat ta mike tana kallon Safiyyah bayan ta shigo dakinta tace "Why are you looking this way Sophie?" Safiyyah tace "Wallahi kwanan nan zaki ji nayi ma matar can duka a kasar nan" Khaleesat tayi murmushi tace "Me kuma tayi maki again?" Gefen gado Safiyyah ta zauna kana ganinta kasan ranta a bace yake tace "Tun fa da kika je gidan mugun halinta ya ninku akan wanda take min a baya Khaleesat, she is trying all possible best to make the house miserable for me, dama yanzu ta dena ajiye min abinci kwata kwata, cornflakes da Golden morn sai ta boye a dakinta da sunan taje hada ma yaronta ne duk don kar in sha...." Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah ya kyauta, ko zaki dawo nan?" Safiyyah tace "In dawo nan for what reason? ashe ma riba ta ci kenan idan na bar mata gidan, ai we die together with her in that house, babu inda zan dawo wallahi, kawai rabon ta ci duka ne ba wani abu ba" Lkci daya expression din Safiyyah ya canza daga bacin rai ta kamo hannun Khaleesat tana washe baki tace "Kee naga Housemate dinki ido da ido yau, dama haka yake gayen? Wallahi he is so well flavoured komai yaji, ina masa magana ma ko kallona bai yi ba amma ya amsa min cikin girmamawa, wallahi ya burgeni" Tana blushing ta karasa maganar nata, Khaleesat dai ta saki baki ta kasa cewa komai, can ta kalli kofar dakinta da sauri don ta tabbatar a kulle yake kar ace yana jiyo Safiyyah, sai kuma tayi kasa da murya fuska daure tace "Meye haka Safiyyah what if yana jin ki?" Safiyyah tace "Wallahi raina a bace yake amma yana bude kofar kawai na mance da abinda er iskar matar can ta min, a very calm gentleman, yace min Hi nace Hello... kuma kuna Hausa da shi ko turanci ku ke? Ni sai nake ga kamar ba bahaushe bane ba fa" Khaleesat ta hade rai sosai tace "Don Allah ki rufa mana asiri Sophie, What's all this?" Safiyyah tayi dariya tace "Ni dai kinyi girki? Don wallahi yunwa nake ji" Khaleesat ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, a corridor ta gansa zai shiga dakinsa, bai kalli ma wanda ya bude kofa ba yayi shigewarsa daki, Khaleesat ta tafi kitchen ta dibar ma Safiyyah abincin da ta girka, jin alamar har ya fito daga dakin nasa ta dawo parlor ta tsaya sai gashi ya shigo parlon, makullin motarsa taga ya dauka da wani littafi, ya daga kai suka hada ido ta fara kame kame tace "Ain't you eating the food?" Yace "Oh, ok na manta" Kitchen din taga ya nufa ta bi sa da kallo, sai da ya shiga sannan ta bi bayansa zata gaya masa kar ya bar mata plate bai wanke ba, tsaye ta gansa kusa da abincin ya dau spoon ya bude tukunyar sannan ya debi shinkafar kadan ya kai baki, kallonsa kawai take da mamaki, ya juya ya kalleta yace "Bad habit right?" Sake dibar abincin yayi ya kai baki, daga haka ya rufe tukunyar yace "Kinga ni ba yunwa nake ji ba, I am full" Ta dinga kallonsa, bata san sanda tace "Ko in zuba maka ka tafi da shi?" Ya bude fridge ya ciro bottle water yace "Aa in na dawo anjima zan ci" Daga haka ya fita daga kitchen din ya nufi kofar living room ya bude, sai a sannan ya juya, ta dauke idonta, yace "See yah" Fita yayi ya kulle kofar daga waje. Sai wajen karfe shidda na yamma Khaleesat ta raka Safiyyah zata hau Uber da tayi ordering, Safiyyah na kallonta tace "Ya Mustapha dai ya hakura dake, jiya nake gaya masa gaskiya kina da wanda zaki aura a gida, don nima na gaji da damuna da yake yi shi sa kawai na gaya masa, ai ko ina gaya masa yace to shikenan dama tun farko ai da kin gaya masa he will understand" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "To ai kinga gwara haka" a haka suka rabu Khaleesat ta koma cikin gida, har goma na dare bata ji shigowar housemate din nata ba hakan yasa ta gane bazai dawo gidan ba ranan. Washegari da safe ta shirya ta tafi makaranta, bata dawo gidan ba sai kusan karfe hudu na yamma, tana shiga living room ta gane ya dawo gidan da bata nan, bedroom dinta ta wuce bayan tayi wanka tayi sallah ta canza kaya ta fito kitchen zata yi Ι—an wake don shi ne a ranta, bayan ta gama hada duk ingredients din taji an bude kofar parlor, ta dai ci gaba da abinda take, kitchen din ya shigo ya ajiye ledan hannunsa yace "Good evening Halysaah" Tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, Are you baking?" Ta kalli flour din da take kokarin kwabawa tace "No" Yace "What are u using flour for?" Bata yarda su hada ido ba tace "Dan wake" Da mamaki yace "Meye shi?" Ta wani kallesa ganin da gaske jiran amsarta yake tace "Dan waken ne baka sani ba?" Yace "Ban san shi ba" Tace "Toh zaka gansa" Turning stick ta dauko ta fara kwabin danwaken shi dai yana tsaye yana kallo, yace "Hey, why did it change to that color? Ko dai ba flour bane?" Ta Ι—an kallesa amma taki basa amsa, yana ta kallo with astonishment har ta gama kwabin, sannan ta wanke hannu ta fara saka dan waken a ruwan dake tafasa kan gas, shi dai kallonta kawai yake, can yace "To haka ake cin sa?" Tace "Aa da bread ake ci" Sounding amused ya kalli sauran bread din dake a kitchen din yace "Really?" Bata san sanda tayi murmushi ba batare da ta sake ce masa komai ba don taga da gaske ya yarda da Bread za a ci Ι—an waken, he couldn't stop looking at her and the food har ta gama, ya ga ta soya man gyada, sannan tayi dishing din abincin a plate, ta saka eggs din da ta bare a gefe, ta dauko roban yaji, yace "Dama wai wannan abincin ne? To ai na san sa when i was a kid, idan munje wajen Grandma dinmu tana mana" Without looking at him tace "Da ka girma ne ka dawo America ka mance sa kenan" Dariya yayi ya karasa cikin kitchen din yace "Ohk, Can i taste some inji yanda yake?" Komawa gefe tayi bayan ta saka cokali a danwaken, ya dau cokalin ita dai kallonsa kawai take har ya Ι—an juya Ι—an waken ya debi seed biyu ya kai baki, she couldn't stop looking at him yana tauna abincin gently as if trying to figure out the taste, can ya karyar da kai yace "It's nice, i like it, i still remember the taste, it's nice" Murmushi kawai tayi, ya sake diban abincin ya kai baki, tace "To kaje da shi, i will make another one" Yace "Aa bazan iya cinyewa ba ai" Yana fadin haka ya dauko wani plate din ya debi Ι—an kadan a ciki yace "Thank you" Ta karasa ta amsa cokalin a hannunsa ta kara masa Ι—an waken ta saka masa kwai daya, ya kalleta ya Ι—an bude ido yace "Thanks Halysaah, but seriously I can't finish all this" Tace "Eat and remain" Ruwa ya dauka a fridge ya fita daga kitchen din. Khaleesat na idar da sallan Isha'i ta fito parlor zata dafo black tea don tana son tayi karatu har zuwa karfe dayan dare, tunda ta shiga daki daxu da yamma bata sake fitowa ba sai lkcn, bacci ta tarda Housemate dinta yake yi a 3 seater, da mamaki take kallonsa ganin wai bacci yake bayan Isha'i, ita bata ma san yana gidan ba sai yanzu da ta fito, kallon wayarsa dake gefensa tayi ganin yana haske, ta leka screen din taga an rubuta A-jay, kiran na katsewa taga 5 miss calls aka yi masa, kamar ta tashesa sai kuma dai bata yi hakan ba, ta dau wayar kawai tana dubawa taga babu password balle pin a jiki, cire wayar tayi a silent mode sannan ta mayar inda ta dauka tayi wucewarta kitchen, ta gama dafa shayi ta fito parlon kenan taji wayar ya fara ringing loudly, da kyar ya bude idanuwan sa, ita dai ta koma kusa da kofar kitchen din ta makale a jiki, ya Ι—an kalli wayarsa ya jawo yana duba screen din, Ι—aga kiran yayi ya kai kunne yayi shiru har sannan yana lullumshe ido, can ya ja tsaki ya ajiye wayar sannan ya mike zaune, har sannan bai ganta ba ita ma bata bar jikin kofar da ta makale ba, mikewa tsaye yayi daga karshe yana lumshe ido, gani tayi kamar baccin yake yi a tsayen, ta wara ido tana kallonsa with shock , sai da yaga ya kusa faduwa sannan ya bude idonsa sosai, ta kai hannu bakinta saboda dariyar da taji ya taho mata, tafiya yayi ya isa jikin pillar dake parlon ya jingina ya rufe ido, kasa daina kallonsa tayi da mamaki, he stood there for almost 3 minutes yana bacci, ringing din wayarsa ne yasa ya bude ido da sauri as if frightened, kitchen ta shige don bata son yin dariyar da ya taho mata a wajen, sai a sannan ya ganta bayan ta shige kitchen da sauri, ya fara bin parlon da kallo as if trying to understand what was happening, lkci daya idonsa yayi clearing gaba daya ya fara sosa kai, at first bai yi niyyar bin ta kitchen din ba, can kuma dai ya nufi kitchen din, ta ajiye kofin shayin hannunta ta dafe cabinet tana dariya ciki ciki, tana ganinsa ta hade rai tana juya shayinta da cokali as if nothing happened, fridge ya bude ya dau ruwan gora yana kallonta yace "You are still awake?" Ta Ι—an kallesa tace "To karfe nawa ne yanzu da zan yi bacci, as if i am you" Bai ce komai ba ya fita daga kitchen din, murmushi tayi ta bi sa da kallo, daukan shayin tayi ta bi bayansa, taga ya dau makullin motarsa da waya without looking at her yace "Good night Halysaah" Bata san sanda tace "To kar fa kaje kana driving bacci ya dauke ka a kan steering" Bai kalleta ba sai murmushi da yayi kawai ya nufi kofa, ta bi sa da kallo har ya fita sannan ya kulle kofar ta waje, karasawa kusa da window tayi ta Ι—an bude curtain kadan tana kallonsa har ya shiga motarsa a garage yayi reverse, sai da ta daina hangen motarsa sannan ta sake curtain din a hankali, tafi minti uku a tsaye wajen ta jingina da window, daga karshe tana tafiya a hankali ta wuce dakinta bayan ta kashe wutan parlon..... Washegari Khaleesat na sauka daga Lyft bayan ta dawo school taga motar Housemate dinta heading toward the garage, kafin ta karasa apartment din nasu har ya shiga ciki, murda kofar tayi taji a bude ya bar mata alamar ya ganta shi ma, tana shiga parlon yana fitowa daga kitchen rike da Lemon gwangwani me sanyi, ya karaso cikin parlon yace "Are you just coming back from school?" Gaishesa tayi, yace "Good evening Halysaah" Bedroom dinta ta wuce ta bar sa a parlon, it's almost 6pm na yamma kuma Safiyyah ce ta bata masu lkci tana mata bayanin wani course dinsu da tace bata ganewa, wanka Khaleesat tayi ta sauya kayan jikinta zuwa kananun kaya sannan ta saka hijab ta fito parlor, yana parlon har sannan yana operating laptop dinsa, ganin zata shiga kitchen yace "Ki bari ki hutu, zan fita sai na siyo abinci" Khaleesat ta kallesa tace "I am cooking noodles" Yace "Ohk then" Tana fadin haka ta wuce kitchen, Ya mike ya wuce dakinsa da laptop dinsa, cikin mintunan da basu da yawa Khaleesat ta gama dafa noodles din da take, ba da yawa ta dafa ba don bata san ko zai ci ba, zata yi dishing din abincin a plate taji ana knocking kofar parlor, ta ajiye plate din hannunta sannan ta fito daga kitchen din, Housemate dinta ta gani har ya fito shi ma to check on who is at the door, amma ganinta kawai ya juya ya koma dakinsa, karasawa tayi ta bude kofar, lkci daya taji komai ya tsaya mata cak ta dinga kallonsa babu ko kiftawa kamar ranan ta fara ganinsa, Yana kallonta daga sama har kasa yace "Meye kike kallo na haka Malama?" Tayi wani yake zuciyarta na bugawa tana in-ina da kyar tace "Ya Abdul, I.. I.. was surprised, san..nnu da zuwa" Da sauri ta juya ta koma parlon, ya bi bayanta yana duba wayarsa dake vibrate a hannunsa alamar ana kiransa, ita dai ta koma bayan kujera ta tsaya kamar munafuka tana kallonsa zuciyarta na bugawa sosai, kana ganinsa kasan ba a lkcn ya shigo America ba, probably tun daxu ya shigo ya sauka hotel, ya Ι—aga kiran da ake masa ya kai kunne, tana ganin haka ta juya ta nufi corridor din dakunan apartment din tana waige waige, ganin attention dinsa na kan wayar da yake ta bude kofar dakin Housemate dinta ta shiga da sauri ta kulle kofar, Housemate dinta ya juya yana kallonta da mamaki, gaba daya a rude take ta nufesa tana yarfe hannu ta duka kusa da shi, ya mike still looking at her with surprise yace "Are you alright Halysaah?"

 

 

07087865788✍🏻

[5/7, 6:25 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨ HALYSAAH ✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

10.....

 

Khaleesat ta gyada masa kai tana rufe bakinta da hannunta murya can kasa tace "Plss i have a visitor, i want u to plss pretend you are not staying here, just pretend u came to drop some books for ur Female friend living here plssss" Kamar zata yi kuka ta kare maganar tana kallonsa, yayi shiru shima yana kallonta at first, sai kuma yace "As in how Halysaah?" Ta marairaice masa tace "Kawai dai kayi kamar ba a gidan nan kake ba don girman Allah ka rufa min asiri, u know my former housemate mace ce, act as though u are her friend, kayi kamar wajenta ka zo pls, don Allah ka taimake ni" Bata jira cewarsa ba ta mike ta juya da sauri ta fice daga dakin kafin Abdul ya biyo ta, ya bi ta da kallon mamaki baya ko kiftawa, can kawai yayi murmushi ya zauna ya ci gaba da abinda yake yi a Laptop dinsa, parlor Khaleesat ta dawo suka kusa cin karo da Abdul da ya nufo corridor yace "Me kika je yi a ciki? You didn't even get me something to drink" Ta Ι—an yi murmushi a hankali tace "Why didn't you let me know u are coming? Me yasa baka gaya min zaka zo ba?" Yace "Sai na gaya maki in zan zo? Ko ke zaki biya min ticket din jirgin?" Ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "Aa ba haka nake nufi ba, ya hanya?" Yana kallonta daga sama har kasa yace "What is wrong with you, why were you sick?" Ta sauke manyan idanuwanta kasa a hankali tace "I don't know too, but i am much better now, naji sauki Alhamdulillah" Yace "Rashin lafiyar ne yasa kika dena daga kirana all this while?" Ta marairaice masa tace "Don baka san yanda nake ji bane a sannan, let me get you water to drink" Daga haka ta wucesa da sauri, ya bi ta da kallo har ta shiga kitchen, Khaleesat ta jingina jikin cabinet din kitchen din ta dafe kirjinta that was heaving so fast, after few seconds ta sauke numfashi sannan ta dau tray ta bude fridge ta dauko ruwa da lemo da glass cup sannan ta fito daga kitchen, zaune ta gansa a parlon yana danna wayarsa, ta karasa ta duka gabansa ta ajiye masa ba tare da ta bari sun hada ido ba, shi dai tunda ta fito kitchen din yake bin ta da ido, ta zauna kan carpet ta tankwashe kafarta ba tare da ta bari sun hada ido ba tace "Ya su Mumy da Daddy?" Jin yayi shiru ta daga idanuwanta ta kallesa taga kallonta kawai yake, a hankali ta sauke idonta kasa, yace "Duk kwana biyun nan kin canza Baby, you don't look critically ill da har zaki kasa daga kirana, menene yasa kika dena kirana kuma idan na kira ki ki dagawa? Common WhatsApp kin dena min magana yanzu" Ta kasa kallonsa, tana wasa da gefen hijab dinta a hankali tace "To kwanan nan sai kayi ta min fada ta waya baka considering dina, ga kuma course dinmu da wahala ka sani" Ita kanta ta rasa dalilin da yasa hawaye ya cika idonta, He let out a sigh har a sannan yana kallonta, sai kuma ya dagota sitting her down by his side, gabanta ne ya fara faduwa, in da akwai abinda ta tsana kuma take fargaba a rayuwarta bai wuce Abdul ya zo America wajenta ba, duk da yawanci zuwan da yake it's either tare da Mom dinsa or his Dad, amma duk da haka a dar dar take da shi saboda wasu abubuwan da ya tsira wanda a baya baya mata haka, duk zuwansa kasar sai ta kirko wani abu da zai maidata unhealthy wani lkcn har sai an kai ta hospital, ita da tasan zai kamo hanya ya taho da bata fara ce ma Safiyyah tace masa bata da lafiya ba, yana caressing fingers dinta yayi kasa da murya yace "But you know i love you Khaleesah, ke ce kike jawowa nake maki fada a ko da yaushe" Ita dai bata ce komai ba hawayen dake makale idonta ya gangaro bisa kuncinta, ya kai hannu yana goge hawayen a hankali yace "Ohk, but you know i love you so much right?" ta gyada masa kai kawai, a hankali yace "Housemate dinki fa? Is she around?" Sosai taji gabanta ya fadi, taki barin su hada ido tace "No ban sani ba, i saw she had a visitor daxu ya zo nemanta, probably her friend...." Yana kallonta yace "Friend? Namiji kenan?" Khaleesat ta gyada masa kai, lkci daya ya hade girar sama da ta kasa yace "Yaushe ta fara kawo namiji gidan? When did that start?" Khaleesat tayi karfin halin cewa "Dama tana kawowa time to time ai but not frequently, sai in kilan sun kawo mata reading materials ko bata da lafiya sun zo dubata" Yace "Kuma mazan na kwana a nan?" Khaleesat ta hadiye wani abu da kyar tace "Ni ban sani ba gaskiya, tunda ina dakina always a kulle ai" Kallonsa tayi to cut short the conversation tace "Na dafa noodles yanzu bari in kawo maka kar ya huce" Tana fadin haka ta mike da sauri zuciyarta na bugawa, dai dai nan Housemate dinta ya fito daga dakinsa, Khaleesat taji zuciyarta ya kusa shigewa cikinta tsabar kidimewa, tayi saurin dauke kai tayi hanyar kitchen, Abdul ya juya jin an bude kofar daki, hada ido suka yi da Housemate din nata da ya shigo parlon yana tafiya slowly waya kare a kunnensa duk da ba magana yake a wayar ba hannunsa daya rike da wani Textbook, idonsa kuma na kan Abdul, hannu ya daga masa calmly yace "Hello" Abdul ya bi sa da kallo babu ko kiftawa without replying to his Hello, shi dai Housemate din nata yana tafiya calmly ya nufi kofa ya fita daga parlon, tuni Khaleesat har ta shige kitchen hankalinta a tashe ta dafe kirjinta tace "Na shiga uku....." A haka dai ta fara zubo noodles din a plate, cike da karfin hali ta dawo parlon, Abdul dake ta kallonta yace "Who is he Baby?" Khaleesat ta Ι—an yi fari da ido tace "Ni ban ma taΙ“a ganinsa ba sai yanxu, Nancy ya kawo ma littafi ina ga" Abdul ya mike yace "Ta yaya zaki dinga rayuwa under same roof da wani gardi Baby? Yaushe Nancy din ta fara shigo da samari gidan nan? All this while dama yana cikin gidan nan?" A hankali Khaleesat tace "Na fa ce maka ban taΙ“a ganinsa ba, i have never seen him before sai yanzu" Ajiye abincin hannunta tayi cike da karfin hali tace "In dafo maka black tea?" Komawa yayi ya zauna yaki cewa komai, kana ganinsa kasan he is boiling inside, ita dai ta juya tana tafiya kamar munafuka ta koma kitchen, mikewa yayi ya bi bayanta har zuwa kitchen din yace "Ta yaya wani banza can zai dinga shigowa yana kalle min ke anyhow Khaleesah?" A hankali Khaleesat tace "Ya Abdul kar ka manta communal living muke a gidan nan, this is America.... this isn't my apartment alone, bazan iya cewa ga wa enda za su shigo gidan ba tunda ba gidana ni kadai bace" Tsawa ya mata yace "And so what??? An gaya maki bazan iya kama maki hayar gidan ke kadai bane? Banda kince kina tsoron zama ke daya a gida do you think u will be sharing an Apartment with anyone in America? Do u think I can't afford a full apartment for you??" Har jikin Khaleesat ya fara rawa ganin how fiercely he was speaking to her yana huci, ga idanuwansa sun fara sauya launi, sosai take jin tsoron Abdul ita kam, hawaye ya fara gangarowa idonta muryarta na rawa tace "Ka fara kuma ko?" Kamo hannunta yayi fuskarsa a murtuke suka fito daga kitchen din, ta fashe masa da kuka a hankali har suka dawo cikin parlon, cike da fada yace "Ya bazan fara ba naga wani katon banza under same roof with you? Me yasa tun tuni baki gaya min Housemate dinki na shigowa da gardawa cikin gidan nan ba in samar maki other alternative? Me yasa baki da hankali baki da tunani ne ke a rayuwarki?" Zaunawa tayi ta fashe da kuka sosai ta hade kanta da kujera, ya zauna yana huci, ita dai kuka kawai take tana shessheka, after few minutes ya koma kusa da ita ya dagota drawing her closer to him kamshin turarensa ya cika mata hanci, nan da nan ta hadiye kukan da take tana zare ido, Gently yake caressing dinta murya can kasa yace "I am sorry Baby, amma da kin gaya min da na samar maki wani apartment din ai...." Ta fara kokarin komawa baya tana son kwace kanta daga hannunsa, kin saketa yayi a fusace yace "Why do u always act like a Bush gal Khaleesah? Har yanzu rayuwar Ghetto bazai fita a kanki ba? What is the meaning of this nonsense?" Ta ki barin su hada ido, da kyar tace "To ai... This is a promise you made, amma kuma sai ka dinga..." Cikin tsawa yace "So f what if i break the promise? Ko ance maki tsoronki nake ne? Ko kuma wani ne zai aure min ke dama?" Ta marairaice masa kamar zata yi kuka tace "Ni dae bari in kawo maka black tea" zata mike ya fixgota har sae da fado kansa, ya fige hijab din jikinta yace "Naga alamar kin ma maida ni wani gara don kinga ina biye ki" Ta takure waje daya wasu hawayen na taruwa idonta taki yarda su hada ido tana kokarin kwatar kanta daga grip dinsa, skirt karami ne sosai jikinta sai half vest shi sa ma take ta yawo da hijab tun daxu da ta dawo schl, ya sake fixgota sosai jikinsa, kuka ta fara yi muryarta na rawa tace "Don Allah ka bari plss, this wasn't our deal, you are not keeping to ur promise" Kallonta ya dinga yi saboda yanda tayi provoking dinsa, duk da shi bai yi niyyar mata komai ba da ya wuce ya lallasheta amma tsabar yanda ta hasala shi sai ya fara kokarin kissing dinta, Ζ™in yarda tayi tana kiciniyar kwace kanta tana kuka, House mate dinta ne ya shigo parlon a lkcn, ya kalli yanayin da suke da kuma yanda take struggling din kwatar kanta daga jikinsa, direct ya nufi cikin parlorn har inda suke without a second thought ya cakumo Abdul yana kallonsa da kyau "Hey, this is America guy, what sort of molestation is this??" Mikewa Abdul yayi yana kallonsa da wani irin Expression na mamaki, bai yi wata wata ba kawai ya sauke masa fist dinsa a kirji har sau biyu, ya wani cakumosa yace "Are you insane? How dare you??" Khaleesat ta zaro ido ta mike cikin tashin hankali ta riko Abdul tana zaro ido with shock, lkci daya ta kalli Housemate dinta da ya tsaya yana kallon Abdul baya ko kiftawa kuma bai yi attempting rama abinda yayi masa ba, da kyar tace "He is my boyfriend, I don't think u have any problem with this, who are you? And where do you know us from? You have no right to intrude!" Housemate dinta dake kallonta ya sauke idonsa kamar bazai ce komai ba, sai kuma calmly yace "My bad! And i am sorry, i thought u were in danger, i am only here to drop some books, sorry about that plss" Khaleesat ta wani kallesa tace "Do i know u from anywhere that warrant u intruding?" Ya girgiza kai yace "Not at all... I am sorry" Kallon Abdul yayi, bowing his head gently at the same time yace "I am sorry, dude" Daga haka ya ajiye book din hannunsa ya juya ya nufi kofar parlon ya fita waje, that was when Khaleesat realized she was half dressed all this while, dukawa tayi ta fara kuka a hankali ta hade kanta da kujera tana jin kanta na wani irin sara mata, wani kallo Abdul yayi mata yana huci, kawai ya dau wayarsa ya nufi kofa ya fice daga parlon kamar zae tashi sama, ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta, mikewa tayi da sauri ta nufi window tana duba waje taga babu motar Housemate dinta har ya tafi, sae Abdul da ta hango yana tafiya down the street, dawowa parlon tayi tana goge hawayen dake sauka idonta ta dau Hijab dinta ta wuce daki da sauri, har wajen karfe tara na dare Khaleesat ta kasa tashi daga saman darduman da take zaune ga wani ciwo da kanta yake mata, jawo wayarta tayi a hankali, tun daxu take son kiran Abdul amma ta kasa kiransa saboda tsoro, daga karshe tayi gathering courage tayi dialing numbersa har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai Ι—aga ba, tasan ba lallai ya Ι—aga ba dama, ajiye wayar tayi ta kwanta gefen gado wasu sabbin hawayen na zuba idonta. Da safe duk da yanda Khaleesat ke jin ta wani iri kamar zata yi rashin lafiya haka nan tayi shirin makaranta ta saka Facemask dinta sannan ta bar gidan, ta kusa awa daya a makarantar kafin Safiyyah ta shigo, Khaleesat ta zauna gefenta tana kallonta tace "Why are you sitted here Khalee? Is the lecturer not around?" Khaleesat ta sauke idonta bata ce mata komai ba, Safiyyah ta sauke Facemask dinta ganin swollen eyes dinta cike da damuwa tace "Subhanallahi, what is wrong Khaleesat? Kukan me kika yi? Ko jikin Mama ne?" Khaleesat ta girgiza mata kai hawaye na taruwa idonta, hankalin Safiyyah ya tashi tace "Innalillahi, don Allah me ya faru? Is everything ok?" Khaleesat ta girgiza mata kai tana goge idonta a hankali tace "Abdul ne ya zo" Safiyyah ta gwalo ido tace "Abdul kuma?? Yaushe? Kuma me ya maki kike kuka?" Khaleesat tace "He came yesterday evening" Safiyyah tace "Ji jaraba, to me ya zo yi? Kuma me ya faru da ya zo din?" Safiyyah na jefa mata wannan tambayar taji hankalinta ya tashi lkci daya, let it not be what just crossed her mind now, tunda tasan ko wanene Abdul, ta kamo hannun Khaleesat da sauri cikin tashin hankali tace "Ko ya maki wani abu ne? A gidanki ya kwana???" Khaleesat ta girgiza mata kai a hankali tace "A'a" Safiyyah bata san sanda ta sauke wani ajiyar zuciya ba, can tace "Toh meye kuma na kuka don ya zo, ko rashin mutuncin da ya saba ya shuka maki?" Khaleesat na shessheka a hankali tace "He met my Housemate" Safiyyah ta bude baki tace "Kai don Allah, cikin gidan ya gansa? To ke ma dai wallahi baza ki iya karyan kare kanki ba kice masa kawai baΖ™on Housemate dinki ne shi tunda bai san Nancy ta tashi a gidan ba, to sai kika ce masa me?" Khaleesat na gyada mata kai tana goge hawayen da yaki tsaya mata tace "Haka nace masa, amma ai kin sansa kinsan halinsa, he even fought with my Housemate" Safiyyah ta zaro ido tace "Fight? To akan wani dalili?" Khaleesat tace "Kema kinsan yanda yake yi ai Sophie, kawai wai zai yi kissing dina ni kuma naki yarda sai ga Housemate dina ya shigo shine yayi approaching dinsa seeing what he was doing to me, hakan da yayi ne yasa Abdul yayi fada da shi, he hit him so hard" Safiyyah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to Housemate din ya rama ne?" Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace "Bai rama ba, kawai hakuri ya basa" Safiyyah tace "Wallahi in ance min Abdul na shan giya ni bazan musa ba, cause his actions portray that, kawai daga ganin mutum ka fara fada da shi kamar wani Ι—an daba, kuma in banda rainin wayo zai zo me yasa bazai ce maki zai zo ba kawai sai dai ki gansa kamar an jefosa a gidan?" Khaleesat tace "Wai fa ce masa da kika yi bani da lafiya shine yasa ya taso ya taho, da na sani da ban ce kice masa haka ba" Safiyyah ta bude baki tana kallon Khaleesat don ita ma sai a sannan taga da basu ce masa haka ba tunda ba isasshen hankali ke garesa ba, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "To yanzu Housemate din naki fa? Hope he didn't hurt him?" Khaleesat ta fara goge wasu sabbin hawayen idonta tace "Kinsan menene ya dameni?" Safiyyah ta girgiza kai, a hankali Khaleesat tace "Maganganun da na gaya ma Housemate din nawa, meanwhile he was just trying to be protective ganin kamar Abdul molesting dina zai yi, ni kuma abinda yasa nayi masa haka don kar Abdul din ya zargi mun san juna da Housemate din nawa, cause i told him frnd din Nancy ne kuma ni ban taba ganinsa ba" Safiyyah da ta kasa rufe baki tace "Wasu irin maganganu ki ka gaya ma Housemate din naki?" A hankali Khaleesat ta gaya mata duk bakaken maganganun da ta gaya ma Housemate din nata, Safiyyah ta dinga mata wani kallo cike da takaici, can tace "To shi katon banzan da kika fadi bakaken maganganun a kansa hope yayi considering dinki at the end of everything?" Khaleesat ta girgiza kai tace "He walk out on me, na kirasa sau biyu jiya yaki dagawa, kuma har yanzu bai kirani ba" Safiyyah ta ja tsaki tace "In ma ya Ι—aga shi babban Ι—an iska ne, kada Allah yasa ya daga, kuma shi Housemate din naki kun sake haduwa bayan abinda ya faru jiya?" A hankali Khaleesat tace "Shi ma tunda ya bar gidan jiya har yanzu bai dawo ba" Safiyyah tace "To wallahi ki kirasa don mutumin nan yafi karfin walakanci a wajen ki" Khaleesat ta fara wani hawayen tace "I don't have his Number" Safiyyah tace "Ban gane baki da lambarsa ba?" Khaleesat tace "Wallahi, even when i was going to Nigeria kawai hadani yayi da wani mutum ya bani number mutumin amma bai bani lambarsa ba" Safiyyah tayi shiru, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Ki tashi kawai ki koma gida kilan Allah zai sa ya dawo sai ki basa hakuri, Abdul kuma kar ki kuskura ki sake kiransa in ba haka ba in tsine maki wallahi" Duk da bakin cikin da Khaleesat ke ciki sai da ta Ι—an yi murmushi, a haka ta koma gida ta bar Safiyyah a school din bayan Safiyyah tace ta kirata duk abinda ake ciki, in ma Abdul din ne ya sake dawowa gidan ta kirata zata taho..... Throughout ranan Khaleesat bata ga Housemate dinta ya dawo gidan ba har karfe takwas na dare, ta rasa me yasa ta kasa samun nutsuwa hankalinta yaki kwanciya, ko tunanin Abdul bata saka a ranta ba tun bayan barin ta school daxu da safe da Safiyyah tayi encouraging dinta kar ta sake kiransa, but she was so restless ganin Housemate dinta bai zo gidan ba, she wish she had his number ta kirasa, wajen karfe goma saura wayarta ya fara vibrate ta jawo a hankali tana duba screen din taga Safiyyah ce, Safiyyah ta kirata yayi sau 6 daga barinta school da safe har zuwa yanzu, Safiyyah tace "Is he back Khaleesat?" Khaleesat ta girgiza mata kai a hankali tace "A'a bai zo ba" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Kilan sai gobe zai zo gidan, ki kwantar da hankalin ki pls" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace "Plss kar ki wani damu kanki da yawa kawata, hope kin ci abinci?" Khaleesat tace "Na ci" Safiyyah tace "To kiyi kwanciyarki, good night" A haka suka rabu, Khaleesat ta ajiye wayarta ta lumshe ido duk da tasan ba baccin zata yi ba.......

 

 

*Continue making your payment before the end of free pages fanss, in ba haka ba aji shiruuu...*πŸ˜ƒ

 

07087865788✍🏻

[5/8, 6:48 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨ ✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

11.....

 

 

Tun da gari ya waye Khaleesat ta kira Safiyyah tace mata bazata shigo school ba don tana son tayi bacci, Safiyyah tasan sarai bata yi baccin kirki ba kenan daren jiya, har mamakin yanda Khaleesat ta iya saka abu a rai ya dameta take, Safiyyah tace "Shikenan kawata, after our classes zan zo ko da yamma ne in sha Allah" a hankali Khaleesat tace "To Allah ya kai mu, Nagode" Daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar ta koma ta kwanta. Wajen karfe hudu na yamma Khaleesat ta tashi daga baccin da take, bandaki ta shiga ta wanke baki sannan tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tun wayewar gari babu abinda ta ci har zuwa sannan, rabonta da abincin kirki zae yi kwana uku yau tun dai faruwar incident din few days ago, bayan ta idar da sallah ta shirya cikin kaya marasu nauyi ta fito parlor ta tafi kitchen ta hada shayi kawai sannan ta koma dakinta, laptop dinta ta jawo ta kunna zata saka movie ko zata Ι—an samu nutsuwar abubuwan dake damun ta a rai ta hanyar kallon film, daga karshe ma ta fasa kallon ta dauko takardunta ta fara karatu, nan ma taji bata fahimtar komai a karatun, rufe takardan tayi ta kwantar da kanta gefen gado ta lumshe ido with different thoughts running her mind, it's not as if she is disturb don Abdul bai daga kiranta ba ko bai kirata ba, kawai dai bata ma san abinda ke damunta bane in particular, bayan lokaci me tsawo ta sauke ajiyar zuciya ta bude idonta ta jawo wayarta ta bude WhatsApp, status taga Abdul yayi updating few hours ago, ta bude hoton da yasa taga har ya ma koma Nigeria cause a field din kwallo yayi hoton da abokansa dukkansu sanye da jersey, ko kadan bata yi mamakin komawarsa Nigeria ba don zai ma iya abinda yafi hakan, da taji shiru har kwana uku dama ta zargi ya koma, dai dai nan taji an bude dakin that is opposite her's, sosai gabanta ya fadi don tun ranan sae yau Housemate din nata ya zo gidan, ta kalli agogon wayarta taga karfe biyar har ya gota, ta ajiye wayar ta dago kanta, tana ta zaune har bayan 15 mins da shigarsa daki sai kuma ta mike tsaye tana jin jikinta ba karfi ta dau gyalenta tana tafiya a hankali ta nufi kofarta ta bude ta fito corridor, sai kallon kofar dakin nasa take gabanta na faduwa, ta rasa courage din karasawa bakin kofar, she stood der for some minutes daga karshe ta lumshe ido ta bude tana tafiya slowly ta isa bakin kofar nasa ta tsaya, ta kai hannu tayi knocking a hankali kamar tana tsoron kofar, komawa gefe tayi kamar mara gaskiya waiting for his response, jin shiru bai amsa ba ta sake knocking din a hankali, ta jira for like a minute again taga dai ba a amsa ba, babu abinda yayi crossing mind dinta sai ko yana bacci ne, but bacci da yamma haka? handle din kofar ta kai hannu gently without thinking twice ta bude kofar tana kallon cikin dakin with throbbing heart, a edge din gadon dakin ta gansa a duke yana operating laptop dinsa da alamar abinda bai gama ba ranan da ya bar gidan yake karasawa, ya daga kai ya kalleta sai kuma ya ci gaba da abinda yake yi, she felt really really bad, ashe yana ma jin tana knocking din, da tasan yana ji ya kyaleta da bazata fara bude kofar dakin nasa ba, ya mike tsaye yace "Good evening Halysaah" Taki amsawa kuma taki yarda ta kallesa, da kyar tace "Dama kana ji kaki amsawa?" Har muryarta ya fara rawa, ya Ι—an bude ido yace "To na sani ko saurayinki ne Halysaah?" Nan da nan hawaye ya cika idonta ta juya ta bar bakin kofar ta kullo masa dakin ta koma nata, dukawa yayi ya ci gaba da abinda yake yi a laptop, tana komawa daki ta fara kukan da bata san dalilinsa ba, she felt really hurt kuma tayi da ta sanin zuwa dakin nasa, tana nan a yanda take har shidda saura sannan taji yayi knocking kofar dakinta gently, daga kai tayi tana kallon kofar sai kuma ta hade rai, lkci daya ya bude kofar tare da sallama, sai dai daga nan bakin kofar ya tsaya yana kallonta yace "I was trying to finish a power point Housemate, how are you doing?" Ta sauke idonta a takaice tace "It's fine" Yace "Baki je makaranta ba yau?" Ta gyada masa kai looking toward a different direction, yace "Why?" A takaice tace "Ba komai" Yace "Ok, hope everything is okay?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa sai kuma ta dauke kai don kar ma ta fara kukan dake taruwa idonta, bayan like 10 seconds yace "Saurayin da ke maki fada a waya ne guy din nan ko?" Ta kasa cewa komai at first, sai kuma muryarta na rawa tace "Kayi hakuri da abinda ya faru" Ya Ι—an buda ido yace "No it's fine Halysaah, ai ba ma abinda ya faru, but where did you know him from?" Tayi shiru ta kasa cewa komai tana share hawayen idonta, yace "I am intruding ko?" Ta girgiza masa kai kawai, yace "Ohk can we talk if you are comfortable Halysaah" She kept mute Kamar me nazari, can kuma a hankali tace "Ohk" yace "Then meet me at the parlor" Daga haka ya juya ya fita, ko da Khaleesat ta fito parlon bata tarda sa ba a ciki, ta zauna kan kujeran parlon tunani iri iri na yawo a kanta har ta rame a kwana ukun nan, bayan some minutes sae gashi ya fito daga kitchen with a cup of coffee, ya karaso cikin parlon ya zauna yana kallonta yace "You look pale Housemate, are you okay? Ko ya maki wani abun ne?" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta girgiza masa kai a hankali tace "He left immediately u left too" Yace "Oh really? That's weird" Ita dai tayi shiru, ya Ι—an yi murmushi ya ajiye coffee din hannunsa yace "Amma baki ci abinci ba" Nan ma tayi shiru tana kallonsa, yace "Naga kamar its been a while da kika yi girki a kitchen, so me kike ci a gidan?" Ta sauke idonta, he could see tana cikin damuwa sosai, yace "Tun ranan da ya tafi bai dawo ba kenan?" Tace "Um" Ya kalli agogon wrist dinsa yace "Do u mind me taking u out for dinner?" Kallonsa Khaleesat take babu ko kiftawa kuma bata ce komai ba, ya mike yace "Get ready, let me get my car key" Yana fadin haka ya mike ya tafi dakinsa ta bi sa da ido, Khaleesat ta fi minti uku zaune parlon tana contemplating on weather to go out with him or not, what if Abdul bai bar kasan ba kawai old picture yayi uploading a status dinsa? The thought of this sent her quivers all over, Tana cikin wannan tunanin sai gashi ya fito daga dakinsa, yana shigowa parlor ta mike ba tare da ta bari sun hada ido ba ta wuce dakinta, canza kaya tayi ta dau veil dinta ta yafa sannan ta zauna gefen gado tana tunane tunane iri iri, bayan 15 mins da shigowarta dakin taji yayi knocking yace "Baki shirya ba Halysaah?" A hankali ta mike ta dau wayarta ta nufi kofa ta bude ta fita, ta samesa har ya koma parlor yana jiranta, tana isowa parlon yana kallonta yace "Where u contemplating inside the room?" Bata san sanda ta dan yi murmushi ba bata dai ce masa komai ba, yace "To mu je, this is after 6 already" Shi ya fara nufar kofar fita living room din sannan ta bi bayansa, yana tsaye bakin kofar bayan ya fita ya jira har ta fito daga parlon sannan ya kulle kofar yana kallonta yace "Why this much Deodorant Housemate?" Ta wani kallesa tace "Ni nace maka na sa?" Bai bata amsa ba ya nufi garage tana biye da shi a hankali, ita dai bata sa turare yanzu ba sai tun wanda ta saka da tayi wanka daxu, sai in ko kamshin kayanta yaji amma ba dai ita ba, bude mata motar yayi tun bata karaso ba sannan ya zaga ya shiga motar yana jiranta, bayan ta shiga suka bar Garage din, wani babban restaurant sananne ya kai ta a Baltimore, bayan yayi parking ta dinga kallon restaurant din da ta ga an rubuta The Capital Grille, sai da ya fara sauka daga motar sannan ita ma ta sauka, tana biye da shi suka shiga ciki, shi yayi offering dinta seat bayan ta zauna shi ma ya zauna ya dau food Menu dake saman table yana nuna mata na kusa da ita yace "Ki duba abinda za ki ci" Ita dai bata dau Menu din ba, yace "I am talking Halysaah" Without looking at him tace "Ko ma meye zan ci" Yace "Ohk" Tana danna wayarta yayi masu ordering abincin, mamaki Khaleesat ta dinga yi ganin amount of different type of foods that he ordered kamar za ayi karamin feast a wajen, abinci kuma masu tsadan gaske, da yawa cikin abincin da aka kawo masu sai a ranan ta fara ganinsu, duk da dai abincin turawa ne, drink ma ya kusa kala hudu ya siya masu, ta daga kai ta kallesa a karo na farko tace "Su waye za su cinye duk wannan?" Orange Crush ya dauka yana sha bai ce mata komai ba, after a while ganin bata fara cin abincin ba shi kuma sai cin abinda zai ci yake ya daga kai ya kalleta yace "Ko babu abinda kike so a nan ne?" A hankali ta dau Tacos daya, shi ko ya ci gaba da cin abincinsa, Ζ™asa Ζ™asa Khaleesat take kallonsa, ta lura yanda baya wasa da bacci haka baya wasa da abinci, because he didn't even mind she was in front of him abincinsa kawai yake ci sosai, ganin ko kallonta baya yi ta abincin gabansa kawai yake yasa ta Ι—an saki jiki kadan ta fara cin abincin duk da ba sosai ba, ta ci iya abinda zata iya ci ta dau drink tana sha a hankali, sai a sannan ya daga kai ya kalleta after almost finishing his food yace "Ko dai a maki packaging abincin ki ci a gida, naga kamar kina kunyan ki ci abinci cikin mutane, or should i give u privacy?" Tana kallonsa a hankali tace "Privacy in an open restaurant? Ni nace ina kunyan in ci abincin?" Ya Ι—an bude ido yace "Naga u ate just the Tacos bayan ga abinci da yawa a gabanki" Ta sauke idonta tace "Nafi son sa ne" Yana goge lips dinsa da tissue alamar ya koshi yace "Ohk, so now can i talk to you?" Shiru tayi na few seconds, sai kuma ta kallesa a hankali tace "Ohk" Ya karasa shanye drink dinsa yace "A nan America kika hadu da saurayin naki ko a Nigeria?" Khaleesat was silent, sai kuma ta sauke idonta tace "Nigeria" Yace "Ohk, but me kike tunanin yake janyo maku matsala tsakaninku?" Ta girgiza kai tace "Nima ban sani ba" Yace "Saboda ke ya taho nan daga Nigeria or he have a business here?" Ta gyada masa kai tace "Saboda ni ya zo" ya gyara zama yace "Kinga yana sonki kenan, sosai ma kuwa yake sonki, he left everything he was doing and came over just to see you, in na fahimta bai son kiyi sharing apartment da namiji a kasar nan ko?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana wasa da gefen mayafinta, yace "Sure... yana da gaskiyarsa, don ko ni bazan bar budurwata tayi communal living ba" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, Yace "Yanzu dai kiyi kokari ki basa hakuri ku dai daita kanku, ni kuma i will think of another alternative for peace to reign between u and ur boyfriend, sannan shawaran da zan baki shine try all possible best ki dinga nuna masa abinda baza ki yi tolerating ba tun kafin kuyi aure, ya kamata ace akwai mutual understanding tsakanin ku, he look cool though kawai yana da hot temper ne and i notice insecurity na daya daga cikin matsalarku da shi, but you can definitely change him gradually Halysaah, so last maganar da zan maki ina ga ba abinda ya shafeni bane, kawai dai zan tunatar da ke Do's and don't din addininki ta bangaren relationship tsakanin mace da namiji" Khaleesat dai sauraronsa kawai take without looking at him, kuma taki ce masa komai tana kokarin fahimtar abinda zancensa na karshe ke nufi, shirun da taji yayi yasa ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, at the same time ta kalli wa enda yake kallo a cikin restaurant din, 3 Guys ne suka shigo restaurant din gaba dayansu yan Africa, amma daya ne Ι—an Nigeria a cikin su, guys din da ba yan Nigeria ba suka daga ma Housemate din nata hannu alamar girmamawa, and he waved back at them with smile on his face, Khaleesat ta dinga kallon daya mutumin da ya nufo su don ta ma ganesa, su sauran biyun kuma suka tafi yin abinda ya kawo su restaurant din, Mutumin na isowa kusa da table dinsu yana kallon Housemate dinta yace "Done with the power point?" Tuni kamshin turarensa ya cika wajen, Housemate dinta ya daga kai ya kallesa yace "Yau kuma har da kai za a ci abinci a nan kenan...." Yace "Not at all, i am getting some Steak for legend, meanwhile ashe kana nan" Housemate dinta yace "Yea, i came with my friend for Dinner" Khaleesat dai danna wayarta kawai take don mutumin yi yayi kamar bai san da Allah yayi ruwanta a wajen ba, ita ma ko kallon direction dinsa bata yi ba, Housemate dinta ya nuna masa bill dinsu yace "Get the bill cleared" juyawa mutumin yayi ya bar wajen yana tafiya irin ta Ζ™asaita, Khaleesat ta bi sa da kallon gefen ido, he was wearing a Jogger and a white Polo, ta dai ci gaba da danna wayarta, muryar Housemate dinta taji yace "That's my gee Halysaah, we share the same name with him...." Khaleesat ta daga kai without interest tace "Ohk" Yace "Sorry about his attitude, he isn't friendly, but i promise you he is good" Khaleesat tace "Likewise myself" Murmushi housemate dinta yayi sannan yayi excusing kansa ya mike ya nufi gun wanda ya kira da gee dinsa, daga inda take zaune taji mutumin na cewa "Kai kuma ina ka samo waccan yarinyar dake zaune kamar gunki bata iya gaisuwa ba, duk wani harkar raini ka iya ja ma mutane, that was how the other day da ka kawota karfe ukun dare a mota ta dinga kallon mutane kamar statue da aka dasa a gaban motar" Definitely yayi maganar ne ta yanda zata ji, Housemate dinta dake kallonsa yace "Ban gane bata iya gaisuwa ba, ba kai ka sameta a wajen ba, kayi mata magana ne kaga bata amsa maka ba?" Maimakon ya ba Housemate dinta amsar abinda yace sai taji yace "Na kai Legend gun Veterinary daxu" Taji Housemate dinta yace "Hope he is better now?" Mutumin yace "Let me get the bill cleared mu tafi gidan Mike yanxu...." Housemate dinta yace "No kayi tafiyarka zan yi dropping frnd dina first" Taji mutumin yace "Like seriously kai ko wani irresponsible being sae kace friend dinka, why are you stooping your self soo low Jay" Taji Housemate dinta yace "C'mon Ajay, come off it, this is so harsh..." Mutumin da ya kira da Ajay ya tafi ya bar sa gun a tsaye, Dawowa Housemate din nata yayi inda take, tuni ta mike tana gyara gyalenta without looking at him tace "Thanks for the dinner, kawata na kirana zan tafi gida" Housemate dinta yace "Ke kika kawo kanki da za ki koma ke kadai?" Taki kallonsa tace "Ae naga ur responsible frnds are here, so let me get going" Yace "Halysaah" ta daga kai ta kallesa, yace "Jira ni inyi clearing bill dinmu in yi dropping dinki gida" Yana fadin haka daya daga masu aiki a restaurant din ya nufosa da ladabi ya sanar masa anyi clearing bill din su, ya bi A-jay da ya fita daga Restaurant din da kallo, wa enda suka shigo tare na biye da shi a baya. Khaleesat bata yarda ta hada ido da Housemate dinta ba har suka fito daga Restaurant din zuwa inda yayi parking motarsa, sai da ya shiga motar sannan ita ma ta shiga ta zauna tana danna wayarta, bai tada motar ba ya kalleta, speaking calmly yace "Hope you are not offended Halysaah?" Without looking at him tace "Offended at what?" Yace "I don't really know" Ta kada baki tace "Ai ni ban yi kama da someone that isn't responsible ba balle in zama Offended at what a random stranger spew out, out of his ignorance, shi dai da bashi da manner shi ne babban irresponsible being, ai da ya fada a gabana yaji abinda zan gaya masa" Housemate dinta ya bude baki yana kallonta da mamaki looking completely speechless, bai yi tunanin taji abinda Ajay din ya fada ba, bai kuma yi tunanin tana ma da baki haka ba, after few seconds yayi kasa da murya yace "Pls kiyi hakuri Halysaah, bana son wannan yasa ranki ya bace, i purposely brought you out to cheer you up and make you lively don naga kamar kina cikin damuwa, amma ba don a kara bata maki rai ba, plss ignore Ajay's attitude, wani lkcn yana da problem i think today is one of those days" Khaleesat bata sake cewa komai ba but she is trying hard not to cry, ya ci sa'a ba yana tsaye gabanta ya fadi haka ba da tsaff zata mayar masa da baΖ™ar magana dai dai da abinda ya gaya mata a wajen, Housemate dinta ya tada mota suka bar Restaurant din, hakuri ya dinga bata kamar shi ne yayi mata laifi har suka isa gida, direct dakinta kawai ta wuce, after like 40 mins ta fito wanka tana duba sleeping dress din da zata sa taji yayi knocking kofar dakinta, hijab din da tayi sallah ta dauka da sauri ta saka, bai bude kofar dakin ba har sai da taje ta bude tana kallonsa, yace "Sae da safe Halysaah, pls ki kwantar da hankalinki and get some rest, gobe kuma ki je school" ta sauke idonta bata ce komai ba, taji yace "Take care" Sai da ya juya ya bar wajen sannan ta daga kai ta bi sa da kallo cikin sanyin murya tace "Thank you so much, for..." Sai kuma tayi shiru, ya juya yace "For?" Ta langwabar da kai tace "The Dinner" Ya Ι—an buda ido yace "My pleasure Halysaah" A hankali tace "But.... i don't... know, ur name" Yace "Oh really, amma ranan da na fara zuwa gidan nan ai nayi introducing kaina sai dai in kin manta, I am Ahmad Jawwad Yusuf, my frnds call me Jayy" Kallonsa Khaleesat ta dinga yi without blinking, yace "Are you okay with that?" Ta sauke idonta tace "Alright, i really appreciate you" Ya sakar mata murmushi yace "See yah tomorrow" daga haka ya bar wajen ta bi sa da ido har ya fita daga gidan gaba daya sannan ta juya a hankali ta koma dakinta ta kulle kofar.

 

*Make ur payment before the end of free pages, kar a ji shiru*

 

 

07087865788✍🏻

[5/9, 4:49 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

 

12.....

 

Washegari da safe Khaleesat ta gama duk abinda zata yi a gida ta shirya ta tafi makaranta, tana zaune favourite spot dinsu ita da Safiyyah bayan sun fito daga aji, Safiyyah na facing dinta tace "Tsakaninki da Allah ina kika je jiya da yamma da naje gidan baki nan? Ni dai nasan babu inda kike zuwa a garin nan, ba kuma frnds gare ki ba, So where did u go?" Khaleesat da idonta ke kan jotting da tayi a aji tace "To ke meye na zuwa da yamma likis, i was expecting you around 5pm not 7pm" Safiyyah ta amshi takardan hannunta tace "Ina maki tambaya kina min tambaya, ko akwai abinda kika fara boye min ne Khaleesat?" Tagumi tayi tana kallon Khaleesat din da tuhuma, sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kalleta, dariya ta bata amma bata yi ba, kamar dai bazata ce mata komai ba sai kuma ta bude baki tace "Mun fita zuwa restaurant ne da Housemate dina" Safiyyah ta buda baki tana kallonta with surprise, can tace "Waw, really? Housemate dinki fa kika ce?" Sai kuma tayi dariya tana gyara zama idanuwanta kamar za su fito tace "Anya Khalee babu magana a kasa kuwa? Restaurant fa kika ce? How did he convince you har kika bi sa zuwa restaurant?" Khaleesat ta tabe baki tace "Toh meye kuma a kasa? Daga dai ya kai ni restaurant mu ci abinci? Kinsan yaushe rabon da inci abincin kirki a gidan?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "He notice i haven't been eating shi ne yasa har ya kai ni restaurant" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai kece da dora ma kanki abinda Allah bai dora maki ba kawata, akan Abdul din da naga yayi updating status da jersey jiya alamar har ya koma Nigeria ya ci gaba da harkokin gabansa ke kina nan kina neman kashe kanki, wallahi in zaki ajiye lamarin gayen nan a gefe da zai fi maki alkhairi a rayuwarki, very very heartless guy with no conscience, dubi tsabar zuciyarsa ta dutse ne ya gwammace ya kara siyan ticket yayi juyawarsa ya koma Nigeria, Allah ma yasa yayi maki ya jiki zuwan da yayi" Khaleesat dai tayi shiru tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta daga kafada tace "Ga dai Housemate din nan naki duka duka yaushe har ma ku ka san juna? Amma ya gane kina cikin damuwa har da kai ki restaurant for dinner, to this is how a caring and understanding Boyfriend and a Gentleman should be" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace "Ni babban damuwata kar ya sake dawowa kasar ban sani ba Sophie, ce masa nayi Housemate dina frnd din Nancy ne fa, kinsan bai san Nancy bata gidan ba ai har yanzu, to kar ya sake dawowa unexpectedly ya gansa" Safiyyah tace "Abinda zai faru kawai kiransa zaki yi ta yi har sanda ya ga daman daga kiranki, ki basa hakuri ki samu ku shirya, in har ku ka shirya duk wani movement dinsa zaki dinga sani, yanzun ma ai don baku communicating ne all this while shi yasa kawai ya taho kamar an jefosa, banda haka ai duk sanda zai zo yana gaya maki" Khaleesat tace "Haka ne, amma kin san irin zuciyarsa wallahi zan iya kiransa sau goma ma bazai daga ba, ko na masa magana ta WhatsApp bazai yi reply ba" a sanyaye ta kare maganar, Safiyya tace "Bari in kirasa ta wayana yana picking zan ce ya kirani, daga nan in ya kira sai in baki wayar ku yi settling dispute din karyan ku" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, amma tasan hakan kadai shi ne way out, Safiyyah ta ciro wayarta ta fara kiran Abdul, har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa sai gashi ya daga, sallama tayi masa ta gaishesa tace "Pls in ba damuwa ka kirani" Katse kiran yayi sai gashi ya kira tayi picking sannan ta mika ma Khaleesat wayar, Khaleesat ta amshi wayar gabanta na faduwa ta kai kunne, Safiyyah ta tashi ta bar ta a wajen ta koma wani waje ta zauna, a hankali Khaleesat tace "Don Allah kayi hakuri ka saurareni..." Shiru yayi da yaji muryarta, nan da nan hawaye ya cika idonta muryarta na rawa tace "Pls kayi hakuri da abinda ya faru, i promise you hakan bazai sake faruwa ba" Yace "Dama akwai abinda ya faru ne?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "I am asking you, akwai abinda ya faru ne dama?" Ta sunkuyar da kanta tace "Don Allah kayi hakuri, i am truly sorry plss" Yace "Look i am super busy now, idan kin shirya gaya min abinda ya faru kike ban hakuri sai ki kirani ta layin ki anjima" Cikin sanyin murya tace "Toh Nagode" Katse wayar yayi, ta juya tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta kyabe baki ta dawo kusa da ita ta zauna tace "Ya ku ka yi da shi?" Khaleesat ta ja tsaki tana tattara reading material dinta tace "An gaya masa banda ina tsoron kar ya dawo without notice ni zan sake magana da shi ta waya ne" Safiyyah ta bude baki tana kallon Khaleesat tana tunanin yaushe bakinta ya fara budewa haka akan Abdul ne wai, Dariya Safiyya tayi tace "Shi Abdul din naki Khalee?" Khaleesat ta ki bata amsa, har ranta ita fa yanzu tana jin bazata iya ci gaba da tolerating abubuwan Abdul ba, ita kanta bata san daga inda wannan liver din yake zuwa mata ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru but she is not tolerating anymore. Wajen karfe biyu ta koma gida, bayan tayi wanka tayi sallah ta sauya kayanta ta kwanta, sai bayan da tayi la'asar ta shiga kitchen ta jingina da cabinet tana tunanin abinda zata girka, tuwo taji take son ci, kawai daga karshe tayi deciding tayi tuwon since tana da duk ingredients din girka tuwon, kan kace me ta gama girka tuwo da miyar kuka with enough obstacles a ciki, ta gama goge gogen kitchen din sannan ta fito parlor wajen karfe biyar, dai dai shigowar Housemate dinta gidan, ita dai tana tsaye kusa da kitchen, ya juya ya kalleta bayan ya kulle kofar parlon yace "Good evening Halysaah" Tace "Good evening" Yace "What are you cooking with such a nice Aroma" Tace "Tuwo ne" Ya karaso cikin parlon yace "Really, it's been long na ci tuwo fa" Tana kallonsa tace "In kawo maka?" Ya dan buda ido yace "Ok thank you" Juyawa tayi ta koma kitchen din, ya zauna saman kujera hoping ba da yawa zata saka masa ba, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo parlon da plate dauke da tuwo with a diff bowl of soup, tun da ta duka ta ajiye abincin yake kallon bowl din miyan babu ko kiftawa, can dai ya daga kai ya kalleta yace "Wani miya ne wannan Halysaah?" Ta koma gefe tace "Miyar kuka ce" Lkci daya yayi yaΖ™e yana shafa kansa yace "Wow, but bana cin irin miyan, i thought vegetable soup ne, baki yi stew ba?" Ta wani kallesa, a takaice tace "Babu, kuma kayi tasting miyan ne kafin kace baka cin irin sa?" Ya jingina da kujera ya sauke ajiyar zuciya yace "Na ma ci abinci few minutes ago fa" Dukawa tayi ta dau bowl din ta mika masa miyan tace "Taste it first before concluding" Ya dan kalleta yana murmushin dole yace "Ok, where is the spoon?" Tace "Shi ba a cin sa da cokali ai, da hannu zaka sha" Yayi shiru sai kuma yace "Then bari in wanke hannu" Yana fadin haka ya mike, ta koma gefe don basa hanya sannan ta bi sa da kallo har ya tafi bandakin dake parlorn ya wanke hannu sai gashi ya dawo, bayan ya zauna ta mika masa miyan tana kallonsa, shi dai bai yarda ya hada ido da ita ba, tun da ya kai finger ya lasa miyan ya kai baki ya kasa dago kai, ita dai kallonsa kawai take bata ko kiftawa, can dai yana murmushi da kyar ya dago yace "It's sooo nice amma na ci abinci wallahi Halysaah" Duk da dariyar da ya bata ta dake tace "To ai tunda ka sa na zuba sai ka ci ko kadan ne cause i am not throwing it away" Bata jira cewarsa ba ta juye masa miyan a kan tuwon dake plate ta dau plate din ta mika masa tana kallonsa, he was totally speechless and confuse at the same time, tana kallonsa da kyau tace "Karba" Ya kai hannu a hankali ya amsa plate din tuwon, in ya debi tuwon sai ya dangwala miyar kamar yana tsoronsa sannan ya kai baki, sosai ya bata dariya amma fa bata yi ba, instead sai murmushi take, sau uku yana diban tuwon yana ci kuma har sannan yaki yarda su hada ido da ita, kana ganinsa kasan da kyar yake cin abincin, his facial expression says it all, wayarsa ne ya fara vibrate, ya ajiye tuwon da sauri ya fiddo wayar yana kallon screen, sai kuma ya kalleta yace "This is an urgent call Halysaah bari in shiga daki in daga" Kasa basa amsa tayi don kar ma tayi dariyar da take dannewa, ya mike ya nufi dakinsa da sauri don ko jiran jin abinda zata ce bai yi ba, tana ji ya sa ma kofar dakin makulli bayan ya shiga, sai a sannan ta zauna gefen kujera ta rike kanta tana dariya, after some minutes ta mike ta dau plate din tuwon still smiling ta wuce dakinta. Khaleesat na Voice call ta WhatsApp da Ummanta wajen karfe tara da rabi na dare taji Housemate dinta na knocking kofar dakinta, bayan tace ma Ummanta tana zuwa ta ajiye wayar sannan ta sauka daga kan gado ta saka hijab ta tafi ta bude kofar, yana jingine jikin bangon opposite din dakinta idonsa a kulle, yana jin bude kofa ya bude idon da sauri, kana ganinsa kasan daga bacci ya tashi, tun da ya shige daki daxu yace ana kiran wayarsa bata sake ganinsa ba sai yanzu, yace "Zan tafi sai da safe Halysaah, but pls ki dan kulle kofar i can't find my key" Ita dai bata ce komai ba tana kallonsa, he look so sleepy, ya ciro wayarsa dake ta vibrate a aljihu, tsaki yayi after picking yace "Kai dalla ina hanya" Daga haka ya mayar da wayar aljihu ya sake yi mata sai da safe ya juya ya fara tafiya, ta bi sa da kallo har ya isa parlor, jingina taga yayi ta bayan kujera ya rungume hannunsa ya rufe ido, Khaleesat ta sauke idonta sannan ta fito daga dakinta tana tafiya a hankali ta tafi parlon, bude ido yayi da sauri jin tafiya, sai kawai ya nufi kofar fita daga parlon, tace "Since u can't control ur self a ko ina ka samu bacci kake, be it standing, sitting, driving and even walking, then why not sleep over?" Ya dan kalleta jin abinda tace, nan da nan kuwa yaji baccin ya bar idonsa gaba daya, yana mata kallon mamaki at the same time yana sosa kai yace "Yaushe kika ga nake yin duk wannan da kika lissafa Housemate?" Ita dai ta rungume hannu tana kallonsa bata ce komai ba, ya dauke kai yace "I was only meditating ba wai bacci nake ba, in dai kika ga na rufe ido to i am meditating" Yana fadin haka ya nufi kofa ya bude yace "Good night, kar ki manta ki kulle kofar" Daga haka ya fita ya tura mata door din, Ι—an murmushi tayi tana tafiya a hankali ta isa kusa da window ta dan bude curtain din tana lekansa, parking space taga ya nufa ya bude motarsa ya shiga, she is just hoping yana shiga bazai fara wani baccin ba a cikin motar, after few seconds taga ya fara reverse, ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa har ya bar Garage din ya dau hanya, sake curtain din tayi slowly, ta dan tsaya for few minutes sai kuma ta tafi daki ta dauko key dinta ta kulle kofar ta wuce dakinta, sake kiran Ummanta tayi ta WhatsApp, bayan Umma ta daga Khaleesat tace "Ko kin fara bacci ne Umma?" Umma tace "Aa idona biyu ina jiran ki, Abdul ya maki wata magana ne?" Khaleesat tayi shiru jin abinda Umma tace, ta girgiza kai tace "A'a bai ce min komai ba, me ya faru Umma?" Umma tace "Daxu Hasiya Matar Malam Saleh ta zo gidan nan" Sosai Khaleesat taji gabanta ya fadi, Malam Saleh aminin mahaifinta ne, yawanci abubuwa da yawa a bakin matarsa Ummanta ke ji tunda ba gaya mata baban nasu ke yi ba, abu da yawa ma sai dai taji a duniya ba dai a bakinsa ba, Khaleesat tayi karfin halin cewa "Me tace Umma?" Umma tace "Wai ko an tsaida maganarku da Abdul, haka dai tace min" Khaleesat was short of words, lokaci daya jikinta yayi sanyi, sosai maganar ta zo mata a bazata, she could feel her self tearing up, hankalinta yayi mugun tashi cikin lkci kadan, Umma tace "To ina jira dai in ga ko Malam din zai yi min magana, in ba ayi hankali ba kuma in ji a bakin matansa tun da su zai gaya masu ai, kuma kin ce Abdul din bai ce maki komai ba har yanzu ko?" Khaleesat ta goge hawayen da ya gangaro idonta, tana gyada kai da kyar kamar Umma na ganinta amma ta kasa cewa komai, Umma tace "Khaleesah?" Da kyar Khaleesat ta bude baki ta amsa don bata son Ummanta tasan kuka take, Umma tace "Naji kinyi shiru ne" Khaleesat ta dake tace "Ba komai Umma, ina duba wani karatu ne a takarda" Umma tace "To shikenan, kiyi karatun ki ma yi magana washegari ko?" A haka suka rabu, Khaleesat ta ajiye wayar hannunta ta kwantar da kanta saman pillow hawaye na sauka idonta, bata san menene ya sa all of a sudden taji she can't marry Abdul ba unlike before da har cikin ranta tasan bata da option dole ne aurenta da shi, tana kuma masa fatan ya canza wataran, yanzu kam bata jin haka a ranta, instead ji take bazata iya aurensa ba ma, Khaleesat bata yi wani baccin kirki ba daren ranan nan fargabanta daya kar ma yace a daura auren nan take, tasan in har suka ce ma iyayenta haka babu abinda zai hana a daura auren nan sai wani ikon Allah. Da safe Khaleesat ta tashi da ciwon kai sosai, kana ganinta kasan tana cikin damuwa ba kadan ba, haka dai ta shirya ta fita zuwa makaranta, warce take son tayi ma magana ta dan ji saukin abinda ke damunta sai bata shigo school ranan ba, wayarta ta ciro kawai tayi dialing number Abdul cause she can't hold it anymore, kiran na shiga ya katse ya kirata, ta daga ta kai kunne a hankali ta gaishesa, amsawa yayi yace "Ya aka yi?" At first tayi shiru, sai kuma tace "Ba komai i only called to greet you" Yace "Which side of the bed did you wake up from today da kika kirani ki gaisheni?" Tayi masa shiru, yace "ke dai fadi abinda kike so Malama, foodstuffs din ki ne ya kare ko me?" Ta hade rai tace "Yaushe ka siya da har zai kare?" Yace "Bazai kare ba dama mana tunda baki wani cin abinci sai cookies da kayan kwadayi" Ta wani turo baki bata ce masa komai ba, after few seconds tace "Kawai naji a jikina ne kamar da wani abu dake shirin faruwa shi sa na kira ka" Yace "Wani abu kamar me fa?" She was mute bata basa amsar tambayarsa ba, yace "Anyway, ko ma me kika ji a jikin ki haka ne, zan shiga meeting yanzu sai anjima" Katse wayar yayi a nan take, ta dinga kallon screen din wayarta wani tsanarsa na yawo a zuciyarta, a baya duk abubuwan da yake mata bata taba jin tsanarsa ba sai dai haushinsa yanzu kuwa kawai ji tayi ta tsanesa, ta ja tsaki ta mayar da wayarta jaka tana jin wasu hawaye na cika idonta, rashin zuwan Safiyyah makaranta ya sa bata tsaya su gama karatun ranan ba ta kama hanyar gida kawai cike da damuwa, tana jiran Lyft din da tayi ordering sai ga kiran Safiyyah ya shigo wayarta, tun daxu ta kirata bata daga ba sai yanzu ta biyo ta, Khaleesat ta daga ta kai kunne tana jin muryar Safiyyah tace "Baki da lafiya ne?" Da kyar Safiyyah tace "Tun jiya da daddare, na ma zata rasuwa zan yi kawata" Khaleesat ta Ι—an bude ido tace "Me ya sameki?" Safiyyah tace "To ina ma na sani Khaleesat, Allah sa ba poison dina matar nan tayi ba don tun jiya sai yanzu nasan mutanen dake kaina" Khaleesat tace "Subhanallah, kina gida ne yanzu?" Safiyyah tace "Har da karin ruwa kuwa" Khaleesat tace "To bari in taho gidan yanzu" Khaleesat na maida wayarta jaka ta nufi gidansu Safiyyah, bayan tayi knocking kofar Surayya ta bude mata, Khaleesat ta sauke ido ta gaisheta, in ba kasa kunne sosai ba ma baza kasan Surayya ta amsa ba, Khaleesat taji muryar Mustapha na tambayar matar tasa wanene, ji tayi kamar ta juya ta fasa shiga cikin gidan, amma kasancewar a bude Surayya ta bar kofar yasa ta karasa ciki walking slowly, without looking at Mustapha dake parlor ta gaishesa, ya amsa yace "Ya karatun Khaleesat?" Khaleesat tace "Alhamdulillah, ya jikin Safiyyah?" Yace "Alhamdulillah, she is inside her room" Khaleesat ta juya ta nufi dakin Safiyyah, da gasken ruwa ta tarar ake kara mata don ta zata kawai tace mata haka ne don ta zo, Khaleesat ta zauna gefenta da damuwa tace "Sannu Sophie, ya jikin?" Safiyyah tace "Ba sauki Khaleesat, wallahi kilan abu matar nan ta saka min a abinci" Khaleesat tace "Don Allah ki dena cewa hka, kin ga yayanki ai bazai ji dadi ba in kina wnn magana" Safiyyah tace "Wallahi ita ce don lafiya na dawo gida jiya, ni na zata ma na rasu, sai da na farfado naga ba haka ba" Khaleesat tace "Allah dai ya baki lafiya, kin ci abinci?" Safiyyah tace "Ni bazan ci abincinta ba gaskiya tun daxu sai fruit kawai nake ta sha da lemon kwali" Khaleesat tace "Ko in je gida in maki girki? Me kike son ci?" Safiyyah tace "Ko tuwo da miyar kuka ne ki min in kina da ingredient, kawai shi naji nake so wallahi" Khaleesat tace "To ba damuwa, bari inyi sallah sai in tafi in maki girkin" A haka Khaleesat tayi sallahn azahar ta bar gidan bayan tayi ma Surayya da mijinta sallama, Mustapha ne ma ya tambayeta har zata tafi, Shine tace masa zata dawo anjima, Khaleesat na isa gida taga motar Housemate dinta a Garage, tana bude kofar ta shiga parlor ta gansa kwance kan 3 seater yana bacci, har ta kulle kofar bata ga ya bude ido ba, ta nufi dakinta ta shiga ciki ta canza kaya sannan ta fito ta shiga kitchen, tuwon ta dora har zata fara hada ingredient na miyar kukan sai kuma ta fasa taji gwara tayi vegetable soup kawai, ita kanta bata san menene yasa take son yin vegetable soup din ba duk da bata wani son cin miyar ganye she prefer slimy soup, sai da ta gama tuwon sannan tayi ordering lyft da zai kai ta nearest African store da zata iya siyan ingredients din miyan Vegetable.

 

 

*Make ur payment before the end of free pages*

 

_Halysaah is just 500 naira_

 

07087865788 ✍🏻

[5/10, 10:07 AM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6

 

 

 

 

✨✨ HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

 

13....

 

Har Khaleesat ta fita daga gidan zuwa Supermarket Housemate dinta bai tashi ba, bayan ta dawo sai bata gansa a parlor ba alamar ya shiga dakinsa, kafin karfe hudu da rabi na yamma Khaleesat ta gama miyan da take, tayi dishing ma Safiyyah abincin a warmer din da zata kai mata, kan kace me aroma din girkin ya cika gidan, ko tuwon bata ci ba ta tafi dakinta tayi wanka tayi alwala tayi sallan la'asar sannan ta shirya, fitowa parlor tayi ta nufi kitchen, tsaye ta ga Housemate dinta ya jingina da cabinet din kitchen din idonsa a lumshe, ya dora lipton a gas, tace "Bacci kake a kitchen din?" Bude ido yayi ya juya ya kalleta yace "Not at all" Tace "To me kake yi?" Ya dan shafa kansa yace "I am having a terrible headache" Tayi kasa da murya tana kallonsa tace "Ka sha magani?" Ya kashe gas din yace "Zan sha" Tace "To in sa maka abinci?" Yace "What did you cook?" Tace "Tuwo...." Bai jira ta karasa ba da sauri yace "A'a, Alhamdulillah, am full" Murmushi tayi tace "To ai ba miyar kuka bane, vegetable soup ne" Tana fadin haka ta bude masa tukunyar miyar tana kallonsa, bayan ya ga miyar a hankali yace "Ohk, but let me dish the food my self" Ita dai bata ce masa komai ba ya dau plate ta nuna masa inda tuwon yake, kallon dan tuwon da ya zuba ta dinga yi, sai kuma tace "Wannan dan kadan din?" Without looking at her yace "Zai isheni" bata sake cewa komai ba ya zuba miyar a gefe with just one protein ya saka spoon a gefe, sannan ya dau mug ya debi lipton da ya dafa ya dau plate din tuwon yace "Thank you" Bin sa tayi da kallo har ya fita daga kitchen din. Ko da ta fito parlor da abincin Safiyyah ta samesa zaune kan kujera bai fara cin abincin ba, ya daga kai ya kalleta, ta dau handbag dinta dake saman kujera, yace "Are you going out with food?" Tace "Yea, kawata zan kai ma abinci she is sick" Yace "Ohk Allah ya bata lafiya" Tace "Ameen" Daga haka ta fita daga gidan. Har kusan Magrib Khaleesat na tare da Safiyya, sosai jikin Safiyyah yayi sauki sai labari take ma Khaleesat da tayi shiru hankalinta baya kan hirar, da ta tuna maganar da Ummanta tayi mata jiya da kuma abinda Abdul yace mata da ta kirasa daxu sai taji duk duniyar tayi mata zafi babu abinda ke mata dadi a rai, Safiyyah da ta kula da yanayin Khaleesat tace "Wai me ke damun ki ne kawata?" Khaleesat ta kalleta, sai kuma ta dan yi murmushi tace "Bakomai Sophie, kawai na gaji ne sosai har na fara jin bacci" Ba don khaleesat bata son gaya mata damuwarta bane yasa tace mata haka sai don bata son fadin damuwar tata a wnn lkcn, but tasan dole zata gaya ma Safiyyah abinda ke faruwa, Safiyyah tace "To ki kwana a nan mana tunda bamu da lectures gobe, it's already pass 7 yanzu" Khaleesat ta dan bude ido tace "In kwana a ina? A'a ni dai kin ga tafiyata" duk yanda Safiyyah ta so convincing Khaleesat ta kwana gidan, khaleesat ta ki sauraronta tayi sllhn magariba ta kama hanyar gida, dama tun da ta kawo tuwon da tayi ma Safiyyah daxu Mustapha ya shigo har dakin ya diba ta zama uncomfortable zama a gidan, matarsa kuwa ta kasa ta tsare a parlon gidan, ko da ta fito parlorn ita kadai ta samu zaune fuska a murtuke, Khaleesat tayi mata sallama ita dai har ta fita daga gidan bata ji ta amsa mata ba. Khaleesat na isa gida ta kulle kofar parlon ta karasa ciki tana kallon plate din dake saman kujera da yayi covering with another plate, mug din shayin ma na ajiye bai sha ba, ta tafi ta bude plate din tuwon taga bai ci ba, abinda ya fada mata a kitchen ne daxu ya fado mata that he is having headache, ta juya tana kallon kofar dakinsa, tana tafiya a hankali ta nufi dakin tayi knocking gently, sai da ta sake knocking jin bai amsa ba ta Ι—an bude kofar slightly, bacci ta gansa yake yi saman gado, ta sauke idonta kasa, lkci daya ya bude ido yana kallonta, ta Ι—an koma baya kamar mara gaskiya tana kame kame tace "Are you okay?" Kansa kawai ya nuna mata ta karasa cikin dakin ta duka ta side dinsa da damuwa tace "Baka sha maganin bane?" Bai yi responding ba hakan yasa ta kai hannu kusa da forehead dinsa sai dai bata taΙ“a sa ba, amma she could feel he is running temperature, a hankali tace "Should i order an Uber ride sae kaje asibiti?" Ya girgiza mata kai idonsa a lumshe, rasa abinda zata yi tayi, lkci daya taji hankalinta ya tashi, mikewa tayi ta fita zuwa dakinta ta dau karamin towel tayi soaking dinsa da ruwa bayan tayi squeezing ta dawo dakin, ta nufi inda yake kwance ta duka kusa da shi ta dora karamin towel din da ta linke saman forehead dinsa, ya bude idonsa, cikin sanyin murya tana kallonsa tace "In yi ordering ride din?" Ya dafe towel din da ta dora masa a forehead yace "Don't worry Halysaah" ita dai kallonsa kawai take, can ta tuna tana da pain reliever a daki, mikewa tayi dai dai nan taji kamar ana kwankwasa kofa a parlor, ta juya ta nufi kofar ta fita zuwa parlorn, tsaye tayi bakin kofar parlon tana tambayar waye at the same time tana bude kofar, ta Ι—an koma baya tana kallonsa with surprise, shi ma daga sama har kasa yake kallonta hannunsa rike da wayarsa, su biyu ne tsaye bakin kofar, lkci daya ta hade rai tace "How may i help you?" Kai tsaye shi wanda yake mata kallon sama da kasa ya shigo parlon har sai da ta matsa gefe da sauri kar ya bangajeta, shi dayan mutumin dake tsaye bakin kofar calmly yace "Hello, plss is Jay in here? Ahmad Jay...." Mutumin da ya shiga parlon ya juya yana masa wani kallo yace "Kaii wajenta ka zo halan?" Shi wanda ke waje ya Ι—an yi murmushi ya shiga parlon ya sauke kai kasa, amma sai ya tsaya daga bakin kofar bai karasa can cikin parlon ba, shi ko wanda ya fara shigowa har ya nufi hanyar dakunan dake apartment din, da sauri Khaleesat ta nufesa a fusace tace "How will you just barge into someone's apartment without excuse or an explanation?" Juyawa yayi ya kalleta from head to toes, ita kanta bata san me yasa ta tsaya Ι—an nesa da shi ba taki ci gaba da bin sa ba amma bata fasa masa kallon da take masa ba fuska a daure, ya gyada kai ya ci gaba da tafiyarsa kamar yasan dakin, kawai taga ya bude ya shiga ciki, ta juya ta kalli mutumin dake tsaye har sannan a parlor tace "Ku haka ake yi daga inda ku ka fito?" Cikin nutsuwa mutumin yace "We are sorry Madam, location shi Jay din ya tura masa wai bashi da lafiya and here is the location sannan mun ga motarsa a garage din apartment din nan, hope we are in the right place?" Khaleesat tace "Sai bayan kun shigo za ka tambayeni ko kuna right place din?? Where Is it done this way?" Mutumin ya hade hannunsa biyu alamar bada hakuri yace "Kiyi hakuri dai" Yana fadin haka ya bi bayansa ya shiga har cikin dakin shi ma, bin su tayi amma ta tsaya a corridor, ji tayi wanda ya fara shiga dakin da farko na cewa "Jay me kake yi a gidan nan da wannan karamar yarinyar da bata da manners? Is this the reason why ka dena zama 24/7 a gida yanzu? When did u start this useless life? First of all who is the little brat i want to know?" Da wani expression yake kallon Jay dake fama da kansa a kwance yaki basa amsa, shi dai mutumin da ya shigo a karshe na tsaye daga daya gefen Jay yana masa sannu, sai kuma ya kalli Ajay calmy yace "Kaga dai bashi da lafiya yanzu Ajay, all this question isn't necessary now" Da kyar Jay yace "Ka kyale Ι—an iska mana, laifina ne da na tura masa location" Ajay dai sai bin dakin da kallon mamaki yake yi ganin property din Jay duk a dakin, can ya kallesa yace "To ma  menene yasa za ka kirani? in baka da lafiya ita yarinyar ta kai ka hospital mana, ba tare ku ke zama a gidan ba" Mikewa zaune Jay yayi yace "Kai wai did you know how i am feeling? Ka wani zo nan ka isheni da unnecessary surutu, pls get out Ajay, gerrout pls" Khaleesat dake sauraron conversation dinsu ta wani taΙ“e baki ta juya ta koma parlor ta zauna wani mugun haushin mutumin da taji ana kira da Ajay take ji a ranta, taga Abdul ma balle shi, Salem ya mika ma Jay hannu zae taimaka masa ya tashi, Jay yace "Pls kace mata ta kawo min bottle water, or you check the kitchen ka dauko min" Salem ya juya ya fita, Ajay dake taΙ“e baki ya juya ya fice daga dakin shi ma, direct ya nufi kofar fita daga apartment din yayi ficewarsa ya koma can waje ya tsaya jikin motarsa, Salem dai ya bi sa da kallo ya sauke ajiyar zuciya ganin fita yayi, sannan ya kalli Khaleesat ya gaya mata ta dauko ma Jay ruwa, ta mike ta tafi kitchen ta dauko ruwan ta basa, ba a dau lokaci ba sai ga shi sun fito tare da Jay, mikewa tsaye tayi tana kallonsa, Jay ya zame hannunsa a na Salem ya zauna saman kujera ya jinginar da kansa da kujeran ya lumshe ido, a hankali Khaleesat tace "Amma hospital zaku je ko?" Da kyar yace "No, gida za mu je ya min treatment" Khaleesat tace "To Allah ya sauwake, Allah ya baka lafiya" Ya gyada mata kai sannan ya mika ma Salem hannu ya mike tsaye, Khaleesat na son tambayarsa abu amma ta kasa, ganin za su fita daga parlon ta dake tace "Can i get ur digit so i can be checking up on you?" Salem dai ya juya ya kalleta da Ι—an mamaki jin tambayar da tayi, does this mean basu san juna ba kenan tunda har bata da lambarsa, Housemate din nata ya juya ya kalleta yace "Ai zaki gane gidan da muka je ranan da na mance makulli da daddare bayan kin dawo Nigeria, that's our home, zaki iya zuwa at anytime...." Khaleesat dai ta dinga kallonsa, sai kuma yace "Salem give her my digit, ko kuma ka bata nata kar ta kira bata sameni ba" Salem yace "Ohk bari in bata nawa" Khaleesat ta dauko wayarta sannan ta amshi number Salem, bayan ya gama bata suka fita daga parlon tare da housemate din nata, tana tafiya a sanyaye ta karasa gun window ta bude labule tana kallonsu, sae da suka fito Ajay ya shiga motarsa, bayan sun shiga yayi zoom off. Khaleesat ta sauke idonta sannan ta juya a hankali ta koma cikin parlon. Bayan kwana uku Khaleesat sun fito daga aji tare da Safiyyah dake waya, ita dai Khaleesat na tafiya ne amma gaba daya hankalinta na wani gun daban, Safiyyah tace "Wai ya jikin Housemate din naki yanzu? Ko ya dawo ne baki gaya min ba?" Khaleesat ta kalleta tace "Har yanzu ai bamu yi magana da shi ba" Safiyyah tace "To wanda ya baki number sa fa ko har yanzu bai daga kiran naki ba?" Khaleesat tace "Aa ya daga jiya, amma sai yace min he is much better, da na tambayesa ko yana kusa sae yace min a'a yana bacci, kawai ni dai i hope da gasken jikin nasa da sauki..." Safiyyah tace "Shegen mutumi in ba kinibibi ba me yasa zai wani Ζ™i baki lambar Housemate din naki sai na shi, me za kiyi da lambarsa when u have no business with him, in ni ce ke cewa zanyi a'a ba nasa zai ban ba gaskiya, amma fa har yanzu abun na ban mamaki ace duk mutuncin Housemate din nan naki bai taΙ“a requesting phone number din ki ba ko sau daya, ji ma sanda kika je Nigeria, to ko me yasa oho" Ita dai Khaleesat kallonta kawai take bata ce komai ba, Safiyyah tace "To wai ma ba kince har cewa yayi ki je gidan nasu ba, tun jiya nake ce maki mu shirya mu je kin ki, in baki je kin dubasa ba ta yaya zai san kema kin damu da halin da yake ciki, ai ance gaida me gaisheka, beside da bakinsa ya maki kwatancen gidan nasu ai, to me yasa baza ki je ba, da Nigeria muke sai mu ce ai bai kamata ba saboda yan sa ido da yan fassara lamari but this is USA Khaleesat, kuma abu ai kamawa yake for 3 days baki san halin da mutumin nan yake ciki ba gashi ke kanki kina testifying kyawawan halayyarsa, wallahi ki shirya in rakaki mu je ki dubasa da jiki, kuma kafin nan mu fara biyawa ta shopping mall kiyi masa shopping da zaki kai masa, shi ma sae yaji dadi wallahi" Khaleesat tace "Kawai sai in kama tafiya har gidan nasu duba shi? Ai bai ma dace ba sai kace wasu marasa kamun kai Safiyyah, be it in USA still bai dace ba, mu mata ne fa" Safiyyah ta mata wani kallo, can tace "Ai da naki matsalar ya taso haka ya cire kudadensa sama da miliyan goma sha biyar ko fin haka if i am not mistaken yayi solving maki matsalar ki, shi kuma bai da lafiya rai kwakwai mutu kwakwai kince zuwa dubasa rashin kamun kai ne, to rashin dacewa ya wuce zaman da ku ke yi gida daya? Shi wannan me za ki ce masa? Wani lokacin baki ma nazarin maganar dake fitowa bakin ki Khaleesat, in zuwa dubasa bai dace ba to zamanku gida daya ma ai bai dace ba be it in USA" Khaleesat dai sai kallonta take ta kasa cewa komai, can dai tace "Ban gane ba, Miliyan goma sha biyar for what??" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Ohh for what ko? da yake business class ticket din da ya siya maki an gaya maki na wasan yara ne ai, to bari ki ji Business class ticket kusan 5000 dollars ne base on Airline, ki lissafa 5000 ko 4000 dollars kudin Nigeria kiga nawa zai baki" Khaleesat was speechless after realizing Safiyyah is saying the truth, banda dala dubu dayan da ya bata da zata tafi, sannan ga kuma domestic flight ticket from lagos to kano, and from kano to Abuja, bata mance irin hotel din da ta zauna na few hours a garin Lagos ba, sauke idonta kasa tayi bata sake cewa komai ba, Safiyyah ta ja tsaki tace "Wallahi ki ajiye wnn kauyancin naki ki zama wayayyiya ki dinga yin abun da ya dace, komai a rayuwar nan kamawa yake Khaleesat, to wai ku ka zauna apartment daya ba ace rashin kamun kai ba sai don zaki je dubasa bai da lafiya? ni abinda ke daure min kai kenan" Khaleesat dai taki cewa komai with many thoughts running her mind, a haka dai suka rabu kowa ya tafi gida... The next day sai da Safiyyah tasan duk yanda tayi convincing din Khaleesat da dadin baki da masifa da bacin rai, daga karshe Khaleesat ta yarda su je can inda Housemate dinta yace gidansu ne su dubosa amma fa don babu yanda ta iya da Safiyyah ne don har cikin ranta tsoron zuwa anguwan take don unguwa ce na masu kudi a kasar, to in ma sun je su ce me ya kai su? What if iyayensa ko wasu yan uwansa mata na gidan sai su yi yaya kenan? Kasa hakura tayi har sai da tayi ma Safiyyah wannan tambayar, Safiyyah tace "Dai dai kenan in ma iyayensa na gidan, ai ba Nigeria bane nan USA ne, kuma tsaf za su amshe mu hannu bibbiyu su yi farin ciki da zuwan mu don duba Ι—an su muka je yi bai da lafiya" Khaleesat ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, Safiyya tace "Amma ni har raina ina son sanin dalilinsa na dawowa apartment dinki ya zauna bayan ga nasu gidan can, nace da wani abu a kasa kince min ba haka ba, wallahi kilan ya san ki from somewhere Khaleesat" Khaleesat tace "Sai kuma kiyi ai, nace maki bamu taΙ“a sanin juna da shi ba" Safiyyah tace "Ma ji ma gani dai" Sai da Safiyyah ta fara jan Khaleesat zuwa inda za su siya kayan ciye ciye sannan suka yi ordering Uber da zai kai su unguwan, tun da suka shigo Safiyyah ke kallon manyan Gidaje with fascination, Khaleesat kuwa gabanta sai faduwa yake sai addu'a take a ranta, ita banda Safiyyah tayi insisting da babu abinda zai kawota wai duba Housemate dinta, dai dai kusa da gidan Uber din ya tsaya duk suka sauka, Safiyyah dake zaro ido tana kare ma Glass house din kallo tace "Ke kin tabbata nan ne kar mu shiga gidan mutane a kira mana 911 mu shiga uku Khaleesat" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba amma bata tanka ma Safiyyah ba, Khaleesat ta ciro wayarta tayi dialing number Salem ita kanta zuciyarta bugawa yake gaba daya she is afraid, sai da kiran ya kusa yankewa ya daga, sai gashi a mota zai fito daga cikin gidan, sauka yayi daga motar ganinsu, yana kallon Khaleesat da mamaki yace "Ohh you are here, sannu da zuwa...." Gaishesa tayi ta sauke idonta kasa kamar munafuka, ya amsa da fara'a, Safiyyah ma ta gaishesa sannan tace "Dama ta zo duba jikin Housemate dinta ne shi ne na rakota" Yana gyada kai yace "Ohh that's so thoughtful of her, mu je ciki to...." Suna biye da shi suka shiga cikin katon gidan, Safiyyah dai sai gwale ido take tana bin gidan da kallo ta gefen ido, ita dai Khaleesat gabanta sai faduwa yake sosai ko daga kai ta kasa, after walking briefly sai gasu sun iso entrance din shiga parlon gidan, kofar shiga parlon ma kadai sai ka kalla ka sake kalla, Safiyyah ta saci kallon motoci uku dake compound din kuma masu tsada, suna shiga parlon gidan Khaleesat ta hada ido da Ajay dake zaune kan kujera ga different fruits daga gefensa yana kallon abu a wayarsa at the same time yana cin apple dake hannunsa, 3 quarter ne baΖ™i a jikinsa with gray polo, tuni ta dauke idonta tsabar yanda ta rikice bata ma san sanda ta bude baki ta gaishesa ba tana makale bakin kofa, hade rai yayi ya dauke kai ya ci gaba da kallon abinda yake a wayarsa.

 

 

 

07087865788 ✍🏻

[5/11, 5:06 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

 

14....

 

Safiyyah ma dake kallonsa kamar munafuka tana in-ina tace "Good... good evening sir" Without looking at Safiyyah ya amsa yana cin apple dinsa, Salem na kallonsa speaking calmly yace "Ajay sun zo duba jikin Jay ne" Ajay ya ajiye apple din hannunsa, sai kuma ya kai wayarsa kunne alamar bashi da lkcn basa amsa, ganin haka Salem ya juya ya kalli su Khaleesat yace "Bari in masa magana a sama, za ku iya zama ku jira ni, have a sit pls" Daga haka ya nufi stairs, ko haurawa saman bai yi ba Khaleesat ta zaro ido tace "Innalillahi" da sauri ta koma bayan Safiyyah ganin wani jibgegen kare ya nufo su yana haushi, Safiyyah ta dinga buga ma karen jakar hannunta tana koransa ita ma a tsorace, Salem ya dawo parlon da sauri ganin haushin da karen ke yi zai yi attacking dinsu, Ajay ya mike ya nufi karen yana kiransa yace "C'mon Legend" Karen ya juyo da gudu ya dawo gun Ajay da yayi patting din kansa, Salem ya dawo kusa da su yana murmushi yace "Mu je saman kawai tunda tsoron kare ku ke, ai ba abinda zai maku kawai yaga baΖ™in fuskoki ne shi yasa" Khaleesat da jikinta ke rawa ta bi bayan Salem da sauri Safiyyah na biye da ita, a haka Salem yayi leading dinsu har sama zuwa Bedroom din Jay, knocking yayi yana tsaye bakin kofar, Khaleesat sai waige waige take tana ganin kamar karen zai sake biyo su saman, sai da Jay ya amsa ma Salem knocking din da yayi sannan ya kallesu yace "Bari in sanar masa yana da baΖ™i" Daga haka ya bude kofar dakin ya shiga ciki ya kullo, Safiyyah ta rike haΙ“a ta kalli Khaleesat murya can kasa tace "Ke wani tantirin Ι—an iska ne wannan muka gaida a kasa ya mana walakanci haka?" Khaleesat bata tanka ta ba, har sannan kuma bata daina waige waigen da take ba don gani take fa karen nan zai iya biyo su har sama, sai ga Salem ya fito daga dakin yana kallonsu yace "Za ku iya shiga, ni zan Ι—an fita sai na dawo" a hankali Khaleesat tace "Ohk mun gode" Bude kofar dakin tayi still gabanta na faduwa ta shiga cikin massive room din da sallama Safiyyah dake gwale ido na biye da ita a baya, wani Ι—addadan kamshi hade da sanyin Ac ne yayi welcoming dinsu a cikin babban dakin, Housemate din nata na zaune saman makeken gadonsa alamar Salem just woke him up, his room was just something else wajen tsaruwa da haduwa, Khaleesat taki yarda ta hada ido da shi zuciyarta na bugawa ta zauna nan Ζ™asan lallausan carpet din dakin, a hankali yace "C'mon Halysaah, ga gefen gado ku zauna, ko ku zauna kan kujera" Khaleesat bata dago kanta ba tace "I am comfortable here" Ya lura kamar she is frightened, ya kalli Safiyyah dake kallonsa bayan ita ma ta zauna, dan murmushi yayi mata yace "Hello...." Kana jin muryarsa kasan he is still recovering, Safiyyah ta gaishesa da fara'a tana tambayarsa jikinsa, yace "Alhamdulillah, ya karatu?" Tace "Alhamdulillah" Ya kalli Khaleesat yace "Ya kwana biyu Housemate? Hope you are doing good?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa tace "Ya jiki?" Yana murmushi yace "Da sauki, Alhamdulillah" A hankali tace "To Allah Ubangiji ya sauwake ya kara lafiya" Yace "Ameen ya Allah" Safiyyah ta ajiye ledan hannunta kusa da gadon dakin tace "She got you this" Khaleesat ta kalleta, godiya yayi masu gaba daya, sai kuma ya fara kokarin sauka daga saman gadon yace "Bari in kawo maku ruwa" Edge din gadon ya zauna kamar bazai iya tashi ba, Khaleesat tace "Aa mun gode, we are okay" Ya kalleta a hankali yace "To ai ba ke kadai nayi offering ba Housemate" After some seconds ya tashi ya bude portable Fridge din dake dakin ya dauko masu ruwa da tsadaddun lemuka duk ya ajiye masu sannan ya fita daga dakin walking slowly, exactly irin kayan jikin Ajay ne a jikinsa shi ma, Safiyyah ta rike haba tana kallon Khaleesat bayan ya fita, sai kuma tayi kasa da murya tace "Khaleesat kin dai ga arziki ko? Gidansu kenan fa a Amurka ina ga Nigeria kuma?" Khaleesat ta hade rai tace "Pls stop this Safiyyah" Safiyyah ta rufe baki da sauri, sai kuma tayi kasa sosai da murya tace "Kuma haka fa, kar ace da Cctv a dakin mu ji kunya" Khaleesat ta wani kalleta tace "Ki ji kunya dai, tun da mun gaishesa ki tashi mu tafi kawai" a hankali Safiyyah tace "Gaskiya Housemate din nan naki is more than nice and calm, ni har naji yana burgeni wallahi, look how he welcomed us warmly duk da bashi da lafiya" Khaleesat ta daga ido ta kalleta sai dai bata ce komai ba, ita dai Safiyyah sai bin katon dakin take da kallo with fascination, tayi kasa da murya tace "In na samu irin wannan dakin ai mance me ya kawo ni kasar ma zan yi gaba daya, anya ma kuwa student ne Housemate din nan naki" Khaleesat ta hade rai tace "Tashi mu tafi tunda mun dubasa Safiyyah" Safiyyah tace "Amma ai kya jira ya shigo mu yi masa sallama ko, dadina dake a ko ina sai kin nuna halin ki, kamar ana koranmu daga shigowa gida kice mu tashi mu tafi" Budewar kofar dakin ya sa duk suka yi shiru, Housemate dinta ya shigo da sallama ya zauna kan kujeran dakin ya jinginar da kansa da kujeran, sai ga wani chef din gidan ya shigo da wasu tsadaddun cookies ya ajiye masu kusa da su, sannan ya juya ya fita, Jay na kallon Khaleesat yace "Naga kina son cookies sosai Housemate, here are some for you and ur frnd" Bata yarda ta kallesa ba tana wasa da gyalenta tace "I am okay, tafiya ma za mu yi" a hankali yace "So soon? Amma sai kun ci cookies tukun" Khaleesat ta Ι—an kallesa suka hada ido a karo na farko tun shigowarsu dakin, sosai taji gabanta ya fadi tayi saurin sauke idonta, ya kalli Safiyyah yace "In bazata ci ba ke ki ci abunki... Amma ban san sunanki ba kawar Housemate" Safiyya tayi murmushi tana bude cookies din ta dau guda daya tace "Sunana Safiyyah Adam" Yace "Maa sha Allah, it's nice meeting you Safiyyah, i am Jawwad Ahmad, or you call me Jay" Safiyyah tace "Nice meeting you too Jay" ita dai Khaleesat wasa da gefen veil dinta kawai take kanta a kasa, Safiyyah ta bude handbag dinta saboda kiran wayarta da ake yi, tana dubawa taga Cousin brother dinta ne, ta mike tace "Let me pick a call pls" Jay yace "Alright Safiyyah" Kofa ta nufa ta bude ta fita sannan ta kullo masu kofar, ledan da suka shigo dakin dashi ya Ι—an bude yace "You got me all this Halysaah" Khaleesat ta Ι—an kallesa tace "Um" Yace "Ohk thank you so much i really appreciate" Tana kallonsa a hankali tace "Ya jikin?" Yace "I am getting better gradually, daxu sai naji ina sha'awar wannan tuwon da kika yi some days back" Tana kallonsa tace "Na vegetable soup?" Yace "No, wannan da na kasa ci, the dark soup, I can't remember the name" Bata san sanda tayi murmushi ba tace "Ok miyan kuka?" Yace "Shi... kawai naji shi nake son ci sincerely" a hankali tace "Ohk zaka je can gida anytime soon ne?" A hankali yace "Idan na samu lafiya in sha Allah" Ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam idonsa na gun different direction, Ajay ne ya bude kofar dakin, kai tsaye ya shigo ya nufi Jay yana mika masa wayar hannunsa yana kallonsa, ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata kalli inda yake ba, Jay ya amshi wayar yana duba screen din, sauke Ζ™afafuwansa yayi daga kan kujeran da yake zaune ganin wanda ke kan layi, ya kai wayar kunne da ladabi yayi sallama hade da gaisuwa, sai kuma yace "Alhamdulillah Abba da sauki, wayar a silent yake ne shi yasa" Sai kuma ya daga kai ya kalli Ajay jin abinda Abban ke ce masa, a hankali yace "A'a ba haka bane Abba, i do eat... but not much, ba gaskiya ya fada ba" Daga haka yayi shiru bai sake cewa komai ba, after a minute yace "To in sha Allah Abba, Allah ya kara girma" Sai da ya jira Abba ya katse wayar sannan yayi wurgi da wayar saman gadonsa yana kallon Ajay, wani kallo Ajay yayi masa ta gefen ido ya juya ya tafi ya dau wayarsa a kan gadon sannan ya fice daga dakin, Khaleesat ta gama tura ma Safiyyah text din da take na cewa tayi masu ordering Lyft su tafi gida, sai kuma ta daga kai ta kalli Jay, ganin mood dinsa ya canza, a hankali tace "Baka cin abincin ne ko?" Yace "Ki kyalesa mana, i took cereal daxu da safe kuma a gabansa, shi in bai bata min rai ba baya jin dadi a rayuwarsa" Khaleesat tayi shiru kamar bazata ce komai ba, can dai tace "To ai Cereal ba abinci bane, ka dai dinga ci ko kadan ne" Ɗan murmushi kawai yayi bai ce komai ba, tace "Shikenan, za mu koma, Allah Ubangiji ya baka lafiya" Yace "Baza ki bari Salem ya dawo yayi dropping din ku ba?" Tace "Aa, Safiyyah nasan brother dinta ne ke kiranta a waya, kaga tun daxu muka gama lectures bata koma gida ba" Yace "Ohk ni bari in ajiye ku" Khaleesat ta zaro ido tace "Aa kai da baka da lafiya, za mu yi ordering Uber do not worry about us pls" Khaleesat ta mike, yana ganin haka shi ma ya tashi, amma sai da ya dafa kujera for sometime saboda juya masa da kansa ya fara yi, A hankali Khaleesat tace "Pls kar kayi stressing kanka, just lie down and rest" Ya dago kansa yace "No, let me see you downstairs" Juyawa tayi ta nufi kofa, ya bi bayanta, ga mamakinta sai ta ga Safiyyah tsabar samun waje tana zaune parlon dake upstairs tana kallo tana cin cookies ga lemo a gabanta, to a ina ta samo lemun da cookies, Safiyyah ta washe baki ganin Khaleesat sannan ta mike tace "Shikenan mu tafi?" Jay da ta hango ne yasa tayi tsit, Khaleesat ta nufeta suka fara sauka downstairs a tare amma gabanta faduwa yake kar su kara ganin karen daxu, hakan yasa ta bari Safiyyah ta shiga gaba, Jay na biye da su a baya har suka sauko downstairs, ai ko karen na ganinsu ya nufo su da gudu yana haushi, Khaleesat ta juya a tsorace zata koma sama ta ci karo da Housemate dinta dake bayanta, ya rikota da sauri yace "C'mon, are you afraid of dog Halysaah?" Bayansa ta koma zuciyarta na bugawa, Safiyyah kuwa sai kora karen take da jakar hannunta fuska daure, shi dai Ajay na zaune parlor tun da ya kallesu sau daya ya dauke kai ya ci gaba da kallon Football da yake, sai da Jay ya kori karen sannan ya juya da gudu ya koma gun Ajay ya zauna saman kujeran kusa da shi, Jay ya juya ya kalli Khaleesat da ta marairaice ita ma tana kallonsa, ya Ι—an yi murmushi yace "Ba abinda zai maku ai, bai san ku bane shi yasa...." ita dai bata ce komai ba, Jay ya jufi Ajay yace "Ajay ina makullin motana?" Ajay yace "Me zaka yi da makullin mota?" Khaleesat dai tuni ta nufi kofar fita parlon da sauri don ko kallon Ajay bata son yi, Safiyyah kam tana kallon Ajay tace "To sai anjima, Nagode sosai" Yace "Allah ya tsare" sallama tayi ma Jay shima sannan ta bi bayan Khaleesat, Jay yasan bazai basa makullin ba, hakan yasa ya duba aljihun Ajayn ya zaro few dollars sannan ya juya ya bi bayan Safiyyah, duk yanda yayi da Safiyyah ta amshi kudin taki amsa, Khaleesat tuni ta kusa fita daga gidan gaba daya, a haka Safiyyah ta bi bayanta. Safiyyah na kallon Khaleesat bayan sun shiga Lyft har sun fara tafiya ta rike haΙ“a tace "Ke ashe wannan gayen da muka yi misunderstanding da farko da muka shigo gidan yana da kirki sosai, in gaya maki da na zauna parlon nan na sama ni kadai ya zo wucewa ya ganni sai ya tsaya yayi powering min TV, har da kunna min wutan parlon, ya kuma nuna min fridge in dau lemo in sha, wallahi i never expect such kind gesture from him duba da yanda ya amsa mana gaisuwanmu da muka shigo parlon da farko, ashe mun yi misperceiving dinsa ne" Khaleesat tayi kamar ma bata ji abinda Safiyyah ke cewa ba.

 

 

07087865788 ✍🏻

[5/12, 6:46 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6

 

 

✨✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

 

15.....

 

Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune parlor tana duba wani reading material dinta wayarta ya fara vibrate, daukan wayar tayi taga number Salem, ita dai kallon screen din kawai take at first, after some seconds ta daga ta sa Hands-free tayi shiru tana saurare, daga daya bangaren aka mata sallama, muryar Housemate dinta ta ji, ta amsa sallamar tare da gaishesa, yace "Ya kika je gida Halysaah?" Tace "Lafiya lau" Yace "How about Safiyyah?" Tace "Tana can gidansu" Yace "Good, thank you so much for the visit" a hankali tace "Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen Housemate" Daga haka yayi mata sallama ya katse wayar, bata kai ga ajiye wayar ba wani kiran ya sake shigowa ta ga Abdul ne, sai a sannan ta tuna damuwar da take ciki for days now, nan da nan mood dinta ya canza, tayi picking call din ta saka hands free sannan ta ajiye a gefenta tana ci gaba da duba reading material dinta a hankali ta gaishesa, yace "Didn't you see the money i sent to you?" Ta girgiza kai tace "Ban kula ba" yace "To ki duba" Katse wayar yayi ta jinginar da kanta jikin kujera with many thought running her mind.... Washegari da yamma bayan Khaleesat ta idar da sallah tana zaune tayi dialing number Salem, yana fara ring ya daga, bayan sun gaisa tace "Dama abinci ne zan ma Housemate dina yace min yana so, ban san ko zaka iya zuwa karfe biyar sai ka tafi masa da shi ba, that's if you are available and u don't mind doing so pls" Yace "Oops naje Pennsylvania daxu da safe, but za ki iya zuwa gidan ki kai masa ai, he is at home" A hankali Khaleesat tace "Ohk" Yace "Yeah, ki kai masa kawai can gidan" Tace "To nagode" a haka suka yi sallama ta ajiye wayar, Allah ya so bata dora girkin ba don ta san babu abinda zai sake maida ta gidan nan dai, tayi zuwan farko tayi na karshe. Khaleesat na zaune tare da Safiyyah bayan sun gama lectures din su na ranan, Safiyyah tace "Are you checking on ur Housemate even if ta waya ne kuwa Khaleesat?" Khaleesat ta kalleta tace "I don't have his number ai" Safiyyah ta dinga kallonta da mamaki, can ta girgiza kai tace "Ni ban san me yasa kike haka ba, why won't u ask that guy Salem ya baki? It's almost 10 days now da muka je gidan dubasa tunda kika ga har yanzu bai zo apartment dinku ba kinsan kilan ko bai ji sauki bane" Khaleesat tace "There was a time da muka yi waya da Salem din yace zai turo min lambarsa kuma bai turo ba shi sa har yau ban sake masa magana ba naga kamar baya son tura lambar ne, sannan kawai i assume kilan wannan arrogant guy din ne na gidan yayi stopping dinsa from coming to the house, i suspect they are kind of related or something like that" Safiyyah ta tabe baki tace "To ko in raka ki mu sake zuwa dubasa ne?" ko rufe baki bata yi ba Khaleesat tace "I am going no where, sai dai in ke zaki je sai in masa tuwo ki kai masa, dama ranan da muka je yace min yana son tuwo da miyar kuka, but for me babu abinda zai sake maidani gidan nan wallahi" Safiyyah ta dinga kallonta, can tace "Gaskiya zuciyarki kamar dutse yake Khaleesat, wato har ce maki yayi yana son cin tuwo amma kika kasa yi ki kai masa saboda wani banzan dalilinki, gaskiya you are not nice at all sorry to say" Khaleesat ta mike tace "Ki kirani ko ma me zaki kirani amma wallahi bazan koma wannan gidan ba as far as that bossy Man is in the house, kawai sai in kama hanya in sake komawa don yaji dadin kara raina min hankali ya walakanta ni, in dai ke zaki je zan yi girkin in baki, after all kince the arrogant guy is nice to you ai" Safiyyah bata tanka ta ba ta fara danna wayarta kawai, a haka suka rabu ko sallaman kirki basu yi da juna ba, har Khaleesat ta isa gida a lyft bata san sun iso ba, a duk kwanakin nan Allah ya sani Housemate dinta na ranta don babu ranan da zai zo ya wuce bata tunasa a zuciyarta, ba willingly taki zuwa gidan ta dubasa ba kawai wannan mutumin ne bata son ta sake haduwa da, sannan she is afraid of the huge dog in the house, kar ma taje mutumin ya sakar mata karen ta shiga uku, amma a ko da yaushe Housemate dinta yana ranta tana kuma son sanin how he is feeling, a hankali ta bude motar ta sauka duk jikinta a sanyaye ta nufi apartment dinta ta bude kofar ta shiga, turus tayi a living room din ganinsa kwance kan 3 seater yana bacci, juyawa taga yayi with his eyes still close yace "Good evening Halysaah" Sauke idonta tayi daga kallonsa, walking slowly ta karasa cikin living room din ta nufi can kusa da single sitter ta tsaya still looking at him, a hankali ya bude ido ya fara bin parlon da kallo alamar he is looking for her, suna hada ido calmly tace "Good evening" Mikewa zaune yayi trying to recover fully from his sleep yana shafa fuskarsa yace "How are you?" Tace "Alhamdulillah, ya jikin?" Yace "Naji sauki ai" Shiru tayi kamar me tunanin abinda zata ce, can kuma dai tana rike da edge din gyalenta cikin nutsuwa tace "Naga baka zo bane, i thought jikin ne har yanzu...." Ya girgiza kai without looking at her yace "Abbana ne yasa na je Nigeria, we spent 6 days in Nigeria, jiya muka dawo" Yana fadin haka ya daga kai yaga kallonsa take, da sauri ta kauda kanta tana nodding tace "Ohk" Daga haka ta juya ta nufi dakinta kamar munafuka, ya koma yayi kwanciyarsa. After almost an hour Khaleesat ta fito parlor, ta samesa zaune ya gama baccin yana danna laptop dinsa, kanta a kasa ta karasa cikin living room din ta dan kallesa suka hada ido tana kame kame tace "Dama tambayarka zan yi in maka tuwon ne yanzu zaka ci?" Yace "Tuwo kuma? Aa kinga you just came back from school, ki bari next time in sha Allah" Tace "Ohk" Daga haka ta tafi kitchen to make a light dinner, bayan ta gama girkin ta fito parlor, har sannan yana nan zaune, ta Ι—an kallesa tace "You care for some?" Ya kalli hanyar kitchen din sai kuma yace "Let me dish it my self" Daga haka ya ajiye laptop dinsa ya mike ya tafi kitchen din, ita dai tana tsaye ta bi sa da kallo, bayan few minutes ya fito da bowl din pasta din ya zuba very little quantity, with another plate of the pasta, ita dai kallonsa take, ya mika mata na plate din ta sauke idonta ta amsa, ya zauna ya ajiye bowl din nasa, a hankali tace "Wannan ne zai isheka?" Yace "Eh" juyawa tayi zata bar wajen, yace "Bedroom za ki je ki ci abincin kenan" Ta gyada masa kai tayi tafiyarta daki. Wajen karfe tara na dare Khaleesat ta saka hijab dinta jin yana knocking kofarta sannan ta tafi ta bude kofar, yace "Sai da safe Halysaah, i am going home" at first shiru tayi, can kuma a hankali tace "Why are u having two home?" Ya Ι—an buda ido yayi murmushi yace "One is a home, the other... a comfort zone" Ta langwabar da kai tace "U said two same thing ai, A Home is also known as a comfort zone" Dariya yayi yace "Not in my case Halysaah, they are two different thing to me" Shiru tayi kafin tace "So now, which is home and which is comfort zone?" Yayi murmushi yace "Kema dai kamar er jarida, how is ur frnd?" Tace "She is fine" Yace "And ur Bossy boyfriend, hope ya daina saka ki kuka dai yanzu?" Ta wani kallesa zata kulle kofarta da sauri yace "Wait, it's just a harmless question Halysaah" Tace "To da nace maka kuka yake sa ni?" Yace "Ohk, Allah sa kar in zo ina baki hakuri kwanan nan bayan ya saka ki kukan, and before i forget me yasa baki cin cookies dake kitchen?" Tace "Nawa ne da zan ci?" Yayi shiru kamar bazai ce komai ba, can kuma yace "To ki dinga ci daga yau duk abinda kika ga na siya ki dauka idan kina bukata, I didn't buy them all because of my self alone, ko da namiji ne a gidan nan ko wata mace daban in zan siya abu in ajiye zan siya ne in surplus not for only me, kin gane ko? Har bottle water ina siya mana ne mu biyu ba ni kadai ba, after all there is love in sharing" Ita dai idonta na kasa bata ce masa komai ba, Yace "Good night" juyawa yayi ta bi sa da kallo har zuwa parlor, sai kuma ta kulle kofar dakinta a hankali. Washegari Asabar Khaleesat ta gama laundry da take a kitchen, tayi tidying din duk gidan sannan taje tayi wanka ta fito parlor tana tunanin abinda zata girka kafin ta fara karatu cause it's almost 12pm, tun karfe goma Housemate dinta ya shigo gidan ya wuce Bedroom dinsa, ta ma san bacci, ita kam mamakin yanda baya gajiya da bacci take, knocking kofar parlon aka yi, she is expecting Safiyyah dama amma bata yi tunanin da wuri zata zo ba, ta karasa gun kofar ta bude a bit relieve ta samu me taya ta girki, da mamaki ta bi sa da kallo bayan ta koma gefe don da ta ci gaba da tsayuwa wajen taga alamar bangajeta zai yi ya shiga parlon, direct taga ya nufi dakin Jay ya bude ya shiga, kasa rufe baki tayi tsabar mamaki, tana jin sa yana ma Jay bala'i a dakin, ita dai bata ji muryar Jay din ba, Jay ne ya fara fitowa daga dakin, kamar yanda ta zarga kuwa baccin yake, laptop din da ya bari kan kujera da ya shigo daxu ne ya dauka, Ajay na fitowa ya mika masa laptop din, a mugun fusace Ajay yace "What the hell should i do what with it again bayan lokaci ya kure? Kasan implications din da abin nan da kayi zai ja min kuwa?" A karo na farko Jay yace "Kai dalla wayar a silent yake, kuma ni ban san akwai recent aikinka a ciki ba, da bazan taho da shi ba ai" Ajay dai kallonsa kawai yake kamar ya shaΖ™o sa, Jay ya zauna kan kujera ya jinginar da kansa tare da lumshe ido, banda hararan Ajay babu abinda Khaleesat da ke tsaye parlon take yi, lkci daya Jay ya mike yace "Hey let me see you off, wanka zan yi" a takaice Khaleesat tace "And pls Housemate warn him not to ever barge into someone else's apartment like this again, this isn't a shopping Mall da zai shigo kai tsaye" A tare suka juya suna kallonta gaba dayansu, Ajay yayi facing dinta calmly yace "Ke, da ni kike wannan maganar ko wa?" Ta wani kauda kai fuskarta a daure tace "In baka son ayi da kai kar ka sake shiga gidan mutane babu Excuse, after all ba tare muke renting apartment din ba da zaka shigo min gida without notice, idan wajen abokinka ka zo maturely sai ka jirasa a waje, you don't have to push ur way into people's apartment like it's a shopping complex" Ajay that was speechless ya kalli Jay, Jay ya shafa kansa yace "Why didn't u knock and wait for me outside, after all she is saying the truth" Khaleesat tace "Ni in ya sake shigo min gida haka wallahi 911 zan kira masa..." Ajay ya ciro wayarsa a aljihu yana mika mata yace "Call them immediately" Ta jefa masa wani kallo tayi hanyar dakinta, Yana kallonta da kyau yace "I will definitely deal with you" Ita dai tuni ta shige dakinta ta kulle kofar da makulli, Jay na kallonsa yace "Me yasa zaka shigo mata gida kamar tsohon barawo?" Ajay yace "Za kayi bayanin me kake yi da mace under the same roof in America, macen ma da ka kusa haifa, i promise to report you back home, ita kuma i will teach her the lesson of her life" Yana kai wa nan ya fixge laptop dinsa a hannun Jay, Jay dake murmushi yace "Babu abinda ka isa kayi mata don ta gaya maka gaskiya Malam, kai waye da baza a gaya ma gaskiya ba" Tuni Ajay ya fice daga parlon, Jay ya zauna kan kujera ya dafe kansa yana dariya, the incident was just funny to him, kallon kofar dakinta yayi yana mamakin dama wai haka yarinyar nan take amma take ma saurayinta kuka? Mikewa yayi ya nufi dakin nata yayi knocking kofar yace "Halysaah" sai da ya kirata sau uku sannan ta bude kofar a hankali tana leka parlon kana ganinta kasan a tsorace take, dariya yayi yace "Kinsan waye shi da kika masa rashin kunya Halysaah?" Ta wani turo baki tace "To ni ina ruwana da koma wanene shi, saboda me zai shigo min gida kamar wani barawo, where is it done that way? Ni dai wallahi kar ya sake zuwa min gidan nan in ba haka ba in kira 911" Jay dai sai sauraronta yake, can yayi murmushi yace "So dama kina da baki haka amma kike ma saurayin ki kuka?" Khaleesat ta wani kallesa ta hade rai tace "Ni bana son haka" still smiling yace "Ok, sorry" keeping a straight face tace "Ya tafi?" Jay ya juya zai bar wajen yace "Ya tafi mana" Da sauri tace "Plss ni dai kayi masa magana kar ya sake zuwa, if there is anything ai sai ya kira kaje can gidanku ka samesa kawai ba sai ya zo nan ba" Jay dai murmushi kawai yake yace "Ohk" parlor taga ya tafi, ta koma dakinta ta zauna bakin gado, har sannan gabanta faduwa yake, ita kanta bata san inda ta samu courage din gaggaya masa abubuwan da ta gaya masa ba, ko don dama tana jin haushinsa ne yasa ta samu irin wnn courage din oho, bata fito daga dakinta ba sai da tayi sallan zuhur, a hankali take tafiya ta shigo cikin parlorn, gani take kamar zai sake dawowa gidan at anytime, ai ko wallahi yan sanda zata kira masa, Zaune taga Jay a parlon yana danna wayarsa, tana tsaye bayan kujera tace "Did u warn him not to come back plss?" Jay yace "To ke meye damuwarki ba kin masa warning kar ya sake dawowa ba, ai bazai dawo ba" Kamar zata yi kuka tace "Wallahi zai iya dawowa, kuma in ya dawo baka nan ya zan yi?" Dariyar da yake dannewa ne ya taho masa yace "Ina kuwa zan san yanda za ki yi, ke wa ya aike ki yi masa rashin kunya? Da sai ki yi shiru da bakinki har in fitar da shi daga gidan, Laptop dinsa na dauko daga can gida yana bacci ban san akwai aikinsa da zai yi put foward ta email ba, yana ta kiran wayana kuma ina bacci na sa wayar silent, that was what brought him here" Zaunawa tayi kan kujera tace "That doesn't still warrant him ya shigo gidan mutane kai tsaye, ko magana bai min ba ina bude kofa ya kusa bangajeni fa ya shigo parlon, am i a joke to him?" Dariya Jay yayi yana gyada kai yace "This energy u used in attacking him Allah ya baki irin energy din kiyi using ma Boyfriend din ki" Wani kallo Khaleesat tayi masa, shi dai murmushi kawai yake still not looking at her yace "Naga kamar kin damu da abinda kika masa, ko in kirasa ki basa hakuri ta waya komai ya wuce?" mikewa tayi a takaice tace "Allah ya kiyaye" Daga haka tayi wucewarta kitchen, shi dai murmushi kawai yake looking at a different direction, yasan yau da kyar Ajay yayi bacci akan abinda tayi masa. Bayan Khaleesat ta gama girkin da take ta fito parlor tana kallon Jay ganin fita zai yi don har ya shirya yana saka agogon wrist dinsa without looking at her yace "I think sai gobe zan dawo in sha Allah" Ta marairaice amma bata ce masa komai ba, har cikin ranta ta fara jin tsoron kasancewarta ita kadai a gidan, ya Ι—an kalleta yace "Any problem?" Ta hade rai tace "Toh ka bani makullinka idan ka zo goben sai kayi knocking in bude maka kofar" Da mamaki yace "Why?" Tace "So that baza kaje ka ajiye key din recklessly ba wannan mutumin ya gani ya dauka" Yayi dariya yace "To ya dauka yayi me da shi?" Ta nufesa tace "Bani" ba musu ya bata makullin ta amsa sannan a hankali tace "To abincin fa?" Yace "Abinci? Wani iri?" Bata tanka sa ba ta juya ta koma kitchen din, after some minutes sai ga ta ta dawo da plate din rice and stew, ya Ι—an bude ido yace "Wa zai cinye duk wannan?" Tace "Kai mana" Ya zauna sannan ta mika masa abincin, yana girgiza kai yace "It's very plenty" tace "Should i get you water?" Yace "I will appreciate that" kitchen din ta koma ta dauko masa ruwan gora da drink din gwangwani, yace "Thank you Halysaah" dakinta ta wuce, after a while taji yayi knocking kofar dakinta, bayan ta bude yace "Zo ki bude min kofar zan tafi" Makulli ta dauko ta tafi ta bude masa kofar yace "Thank you, see yah tomorrow" ita dai bata ce komai ba ya fita daga parlon ya nufi garage, a hankali ta kulle kofar da makulli sannan ta tafi window ta Ι—an bude labulen tana kallonsa har ya bar garage din after some minutes, Sake curtain din tayi, walking slowly ta tafi kitchen, bude abincin da ya rufe tayi taga kadan ya ci a ciki, Allah yasa yayi spoon hudu, naman ma kawai daya ya ci, kulle abincin tayi ta dawo parlor ta zauna, dai dai nan taji anyi knocking kofar parlon mikewa tayi da sauri tana kallon kofar a tsorace, da kyar tace "Waye??" Muryar Safiyyah taji, lkci daya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta tafi ta bude kofar, Safiyyah tace "Har kin gama laundry din?" Khaleesat tace "Na gama" Safiyyah tace "Housemate din naki ya fita kenan?' Khaleesat tace "Eh" Safiyyah tace "Jiya da daddare da kika gaya min ya zo gidan ta chat wallahi nayi farin ciki, don mutumin na da kirki sosai" Khaleesat bata tanka ta ba, ta koma cikin parlon ta zauna tace "Ban gan ki da laptop dinki ba" Safiyyah tace "Abeg i will use urs, bani da strength din dauko laptop, kin yi girki kuwa? Don yunwa nake ji, wancen er iskar matar faten wake tayi saboda tasan ba na ci, hegiya dama bayerabiya ce ta wajen uwarta ai" Dariya kawai Khaleesat tayi ta mike ta tafi kitchen, abincin ta zubo ma Safiyyah, ita kuma ta dau wanda Housemate dinta ya rage, ta dauko masu ruwan gora da lemon kwali daya....

 

 

07087865788✍🏻

[5/13, 6:21 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

 

16.....

 

Ko da wasa Khaleesat bata ba Safiyyah labarin abinda ya faru tsakaninta da Ajay ba, amma fa bata da rest of mind gani take kamar zai iya dawowa gidan at anytime, upon all her restlessness bata ji tayi da ta sanin abinda tayi masa ba, dama haushi yake bata, Safiyyah na kallonta tace "Ke kwana biyu shiru banji kince ga abinda Abdul yayi maki ba ko dai ya fara canzawa ne? This is so unusual, ko baki gaya min ba in dai ya maki wani abu you are always moody in school, ta haka nake ganewa" Khaleesat na powering laptop dinta ta tabe baki tace "Ni ina naga wannan time din yanzu ga exams a gabana" Safiyyah tace "Atoh dai, wallahi naji dadin da kika fara daukar shawarata kina fita sabgarsa, sauranki abu daya yanzu" Khaleesat ta daga kai ta kalleta, Safiyyah ta gyara zama tace "Saura ki fara mayar masa da magana, in ya gaya maki daya ki gaya masa biyar" Ita dai Khaleesat bata sake ce mata komai ba tana neman softcopy na course din da za su yi studying tare da Safiyyah. Bayan tafiyar Safiyyah... Khaleesat ta wanke utensils da suka yi amfani da sannan ta wuce dakinta, wayarta ta dauka ta shiga WhatsApp don ganin ko Ummanta tayi mata reply din message da ta ajiye mata daxu, wajen karfe goma da rabi tana shirin kwanciya wayarta ya fara ring, dauka tayi taga Abdul ne ke kiranta, ta dinga kallon wayar, tun sanda Ummanta tace mata tana ganin kamar lkci aka tsayar take wani jin tsanarsa a zuciyarta, gashi yaki gaya mata ko da gasken an tsaida lkcn ko ba a tsayar ba don Ummanta ba wai ta tabbatar bane ita ma a gari ta ji, dama tana Nigeria din ne ta san gun warce zata je taji ko hakan ne ko ba haka ba, Ι—aga kiran tayi kafin ya katse ta kai kunne, muryarta kamar me bacci ta gaishesa, ya amsa, a hankali tace "Ya aiki?" Yace "Lafiya lau" Shiru tayi bata sake cewa komai ba, yayi Ζ™asa da murya yace "I don't know, kawai ina missing din ki ne yau, i want to be with you Baby" Ta kauda kai kamar irin yana kusa da ita din nan tace "Um" Yace "Yaushe za ku fara jarabawan?" Tace "Nan da wata daya" A hankali yace "Ohk, sai da safe, naga kamar kin fara bacci" Tace "Um, ina son tashi inyi karatu ne anjima shi sa na kwanta da wuri" Yace "To ci gaba da baccinki, sai mun yi magana" Daga haka ya katse wayar, ta jefar gefenta ta ci gaba da chatting da take da Ummanta. Washegari lahadi Khaleesat na zaune dakinta tana morning Supplications dinta taji ana kwankwasa kofar parlor, wayarta ta jawo tana duba agogo taga bakwai ya wuce, ta daure ta mike tana tafiya a hankali ta fito parlor, bayan ta karasa bakin kofar with calmness tace "Waye?" Taji muryar Housemate dinta yace "Good morning" bude kofar tayi ta koma gefe ya shigo, sau daya ya kalleta yace "How was ur night" Ta kulle kofar tace "Alhmdlh" Materials din hannunsa ya ajiye saman 1 seater sannan ya kwanta kan doguwar kujera, ita dai bin sa tayi da kallo taga har ya kulle idonsa yana gyara kwanciyarsa alamar bacci zae yi, tana tafiya a hankali ta koma dakinta, ta karasa azkar dinta sannan ta kwanta. Har wajen karfe daya na rana Khaleesat bata fito dakinta ba, ta Ι—an juya daga kwancen da take tana kallon kofar dakinta jin ana knocking, kiranta taji Housemate dinta ke yi, mikewa zaune tayi still tana kallon kofar amma bata sauka daga kan gadon ba, Calmly tace "I can hear you" Yace "Are you alright? Naga kamar baki yi breakfast ba ko?" Shiru tayi bata ce komai ba, bude kofar taga yayi, ta gyara blanket din jikinta tana kallonsa, ya tsaya daga bakin kofar dakin yace "Hope nothing?" Ta langwabar da kai tace "Nothing" Yace "To me yasa baki fito kinyi breakfast ba or are you fasting? Beside today is sunday" Ta kauda idonta tace "Kawai dai..." Sai kuma tayi shiru, ya karasa cikin dakin yace "Kawai dai me?" Kamar baza tace komai ba sai kuma dai tace "Ina jin ciwo a kafana ne" Yace "Ciwo a kafa kuma? Yana maki haka ne?" A hankali tace "Once a while" Shiru yayi jin abinda tace, can yace "Then what is the cause?" Ta Ι—an kallesa, sai kuma ta bude hannu alamar bata sani ba, yace "Kun taΙ“a zuwa hospital a kan hakan?" Ta dai yi shiru without looking at him, sai kuma tace "It's fine, i will get better before evening in sha Allah" Ya juya as if trying to diagnose without examination the cause of her leg pain at her age, sau daya ya kalli gaban dressing mirror dinta sai kuma ya juyo yana kallonta yace "Ok i get, Allah ya sauwake..." Ta Ι—an kallesa, yace "Try getting a hot shower, you will feel better" Juyawa yayi ya fita daga dakin, a hankali Khaleesat ta koma ta jingina da pillow, ko tashi tsaye bata jin zata iya a yanzu dai, kilan zuwa can anjima ta Ι—an ji relieve before she can stand up and do anything, kiran Abdul ne ya shigo wayarta ta kife wayar taki dagawa don ko magana bata so, after some minutes ta kalli kofarta jin knocking at the same time ya bude kofar dakin ya shigo ciki rike da cup din hot chocolate, sauke idonta tayi daga kallonsa ya karasa har side din da take ya duka yana mika mata Mug din hot chocolate din yace "Try drinking this, will get u pain reliever now" Ta amshi Mug din without looking at him a hankali tace "Thank you" Yace "You are welcome" Daga haka ya fita daga dakin ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, yana fita kiran Abdul ya sake shigowa wayarta still taki dagawa daga karshe ma tayi silencing wayar, khaleesat na gama shan hot chocolate din ta ajiye cup din a bedside drawer sannan ta koma ta kwanta tayi lamo kan pillow, kamar zata kira Safiyyah daxu wajen karfe sha biyu sai kuma ta fasa hoping the ache will subside, har ta fara bacci Housemate dinta yayi knocking wajen karfe biyu almost 20 mins bayan fitarsa daxu, sai da ta amsa sannan ya bude kofar, ita dai bata juyo ba, ya zaga ta inda take calmly yace "Are you sleeping Halysaah?" Ta bude ido tana girgiza kai, ya ajiye ledan abincin hannunsa da pain reliever da ya siyo mata yace "Baki yi hot shower da nace kiyi ba?" Tace "Zan yi" Yace "Ohk ga maganin sai ki ci abinci ki sha" Ta mike zaune without looking at him, a hankali tace "Thank you" Yace "Zan fita but i will come back around 6pm in sha Allah" Tana kallonsa tace "Toh makullin gidan fa?" Ɗan murmushi yayi yace "Ai a jikin kofar kika bar sa daxu da kika bude min da safe" Tace "Amma baza ka tafi da shi ba ai" Yace "To taso ki kulle kofar" Ta wani kallesa, er dariya yayi yace "Shi fa Ajay nasan yanxu kuma ya mance abinda ya faru tsakanin ku, may be sai ranan da ya kara ganinki zai tuna, but for now i am assuring you ya mance wallahi he is even busy with his upcoming defense, beside you misperceived him, Ajay is more than nice and calm, ba shi da matsala, kawai dai shaidan ne ya saka rashin jituwa tsakaninku tun a ranan da ku ka hadu" Khaleesat dai ta kyabe baki don ko duk jikinta kunnuwa ne bazata taΙ“a yarda da abinda yake fadi ba, Jay yace "Baki yarda ba ko?" Ta buda ido sosai tace "To dama saboda me zan yarda?" Dariya kawai yayi yace "Take care of ur self Halysaah, in kin ci abincin ki sha magani, let me get you bottled water" Daga haka ya nufi kofa ita dai ta bi sa da kallo har ya fita, sai gashi ya dawo mata da ruwan gora mara sanyi ya ajiye a inda ya ajiye mata ledan abinci da magani wato bedside drawer, yace "See yah later" a hankali tace "Thank you, and pls do not mishandle the key" Murmushi kawai yayi ya gyada mata kai ya fita daga dakin ya kullo mata kofar, ta sauke idonta kasa, after some minutes ta dau ledan abincin da ya ajiye mata a hankali tana budewa don ganin abinda ya siyo mata. Karfe shidda saura Khaleesat na zaune kasan dakinta ta kwantar da kanta jikin gado tana voice note da Ummanta, zuwa sannan she is feeling very much better don har ta gyara dakinta ta wanke bandaki tayi wanka, parlor ne dai taji bazata iya gyarawa ba, wajen karfe hudu suka yi chatting da Safiyyah tace mata zata zo karfe bakwai, Khaleesat ta dan yi jim bayan taji kamar an bude kofar gidan, gabanta ne ya fadi bayan Ajay ya fado mata, ta ajiye wayar hannunta a hankali tana kallon kofar dakinta, after few minutes taji an yi knocking kofar dakin, she felt a bit relieved, with calmness tace "I can hear you" Taji muryar Housemate dinta yace "Can i open the door?" Tace "Okay" bude kofar dakin yayi yana daga bakin kofar a tsaye yace "Good evening Housemate, how are you feeling?" Tace "Da sauki" Yace "Are you sure?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, ta dan kwantar da kanta gefen gado tace "It's better than before" Yace "To Allah ya sauwake, where you able to go to the kitchen?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk" Har zai kulle mata kofar sai kuma ya tsaya yace "Ko mu dan yi strolling as exercise, around the neighborhood, it will help you feel much better too" Khaleesat ta daga ido ta kallesa, yace "I will be waiting for you at the parlor, make sure to put on ur jacket cause it's freaking cold outside" Yana fadin haka ya fita daga dakin, Khaleesat dai na ta zaune kamar me nazari, it took her almost 5 mins of deciding kafin ta mike a hankali, veil dinta kawai ta dauka ta yafa ta dau wayarta tana tafiya a hankali ta fito daga cikin dakin, tsaye ta gansa ya jingina jikin pillar dake kusa da study area yana danna wayarsa daya hannunsa rike da jacket dinsa, yana ganinta yace "Are you ready? Where is ur jacket?" Karasawa yayi inda take tsaye yace "It's cold outside" Yana fadin haka ya ajiye mata Jacket dinsa kan kujeran dake kusa da ita yace "Use this, bari in dauko wani" Dakinsa ya koma ita dai ta bi sa da kallo, ba a dau lokaci ba sai gashi ya dawo parlon with another Jacket, ya saka a kan rigar jikinsa yace "Mu je" Ta sauke idonta ta dau Jacket din nasa, Kofar parlon ya nufa ta bi bayansa har suka fita daga parlon, ya kulle kofar ya kalleta yace "Na lura kina son so much perfume ke dai" Ta girgiza kai tace "A'a ni ban sa ba yanzu" Yace "Ohk" A tare suke tafiya with nobody saying anything, tun ba su kai ko ina ba taji tana jin sanyi sosai, hakan yasa ta Ι—an saci kallonsa sannan ta saka jacket din hannunta yace "Ai na zata baza ki sa ba kina forming big gal" Kawai dai tayi murmushi bata ce komai ba, tana jin kamshin turarensa da ya cikata na jikin Jacket din, dai dai yake tafiya da ita to keep same pace with her, slowly suke tafiyar with absolute silence har suka yi nisa away from home, Jay yayi breaking silence din yace "Soon za a fara snow" Tace "In sha Allah kafin nan mun gama Exams dinmu" Zai yi magana wayarsa ya fara vibrate ya ciro a aljihunsa yana duba me kiransa, ta gefen ido ta kalli wayar tasa taga Ajay, yayi silencing wayar ya mayar aljihunsa, ta tabe baki tace "Shi dole sai ya dinga damunka da kira ne as if you are with his kidney?" Jay yayi dariya yace "Kidney ai me sauki ne, cewa za ki yi kamar life dinsa na wajena dai, a rana sai ya kirani sau ashirin in banyi hankali ba" Khaleesat ta kyabe baki sai ga shi ya sake kiran wayar, Jay ya kara ciro wayar yayi picking ya sa Hands-free yana tafiya yace "What again?" Daga daya bangaren Ajay yace"I need ur laptop, zan duba references dinka, na mance zan shiga schl gobe, i am outside with my frnd now" Jay yace "Da laptop din na fita ai, kuma i am not coming back home anytime soon" Ajay yace "Gidan wannan mara kunyan ka koma kenan? Wai are you even okay Bruh? Me kake yi da wannan yarinyar da ya sa kake zama gidanta? Ko iskanci ka fara ne? In ma iskancin zaka yi why with that little local brat pls?" Jay that was trying not to laugh yace "Kai kar ka bata min rai fa" Ajay yace "On a serious note idan baka daina zuwa gidan nan ba i promise you am gonna report you back home kasan karamin aikina ne hakan ko?" Jay yace "In ka fasa, kai duk takurani da kake da yan iskan abokanka a can gida ban kai report ba sai ni da na bar maka gidan for peace to reign shi ne zaka kai karata? To references din ma baza a nuna ba, go and sort ur self out" Yana kai wa nan ya katse wayar ya mayar cikin aljihu, ita dai Khaleesat bata kallesa ba kuma bata ce komai ba amma har cikin ranta take jin Ajay bai mata ba,  she doesn't like him or anything concerning him, ta tsani mutum that is too pompous and proud of himself, Jay yace "Baya karatu fa, in ma wani aiki ne sai dai kai kayi ya gani sannan yayi nasa, har ma nasan yafi naka at the end" Khaleesat tace "To me yasa har yanzu ba a koresa ba daga makarantar?" Dariya sosai Jay yayi yana kallonta yace "Baya karatu doesn't mean he is dull Halysaah, kinsan Genius? That is who Ajay is, he is naturally gifted, he graduated as one of the best medical student during our degree program in this state and masters, kuma kar kice wani karatu yake, mu ne dai sai mun yi karatun za mu wuce" Yana murmushi ya kare maganar, Khaleesat ta wani kyabe baki kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "To ai gwara kai karatun kayi ka wuce, shi kuma banza kawai yake ci" Jay na dariya yace "Ai shi sa na bar masa gidan cause idan na ci gaba da biyesa da abokansa wucewa zai yi ya bar ni, su kansa abokan nasa ina tausaya masu biyesa da suke" Khaleesat tace "Shi ne yasa kake Co-living?" Yace "Yeah, shekaranmu na karshe kenan idan Allah ya yarda so i need much privacy to study very hard to earn my PhD, in kana tare da Ajay ba wani abun arziki da zaka yi in dai bangaren karatu ne, sannan baya barina inyi bacci sosai, nuisance ne shi fa, Ya Subhanallah" Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta sauke idonta, yace "Year nawa kike yanzu?" A hankali tace "Year 3" yace "Kince Pharmacy ko?" Ta gyada masa kai, yace "Kin kusa gamawa kema ai in sha Allah" ita dai tayi shiru bata ce komai ba suna ci gaba da tafiya slowly, ita ce tayi breaking silence din after almost 10 mins da ya biyo baya tace "You know him back home?" Jay ya kalleta yace "Wai Ajay? Yeah he is my favorite, yanzu ma dai kin ga budurwa nake nema masa bashi da mashinshiniya ko daya wallahi" Khaleesat tace "Ashe bazai taba samu ba, ai he is way too rude and full of himself, wacece zata yarda ta auresa in dai ba auren dole aka mata da shi ba, ko makala mata shi aka yi?" Jay dai dariya kawai yake yana kallonta yace "Ya kai Saurayin ki?" Nan da nan mood dinta ya canza, taki ce masa komai tana ci gaba da tafiyarta, yana kallonta yace "Naga kin yi shiru ko compare and contrasting kike yi a zuciyarki? Tell me pls ya kai saurayinki?" Without looking at him tace "Kamar lokacin sallah yayi, and it's getting dark already" Yace "Ke ina ruwanki da sallah tunda ba yi kike ba?" Khaleesat was dumbfounded jin abinda yace, ta kasa kallonsa kuma taki basa amsa still walking slowly, Roadside chair ta hango ta tafi ta zauna, ya karasa wajen yace "Ko har kin gaji ne?" Tace "To da bazan gaji ba, muna ta tafiya for almost an hour now" Yace "Akwai wani Eatry a area din nan, mu je sai mu yi dinner before going back home, the eatry isn't far away from here" Khaleesat tayi shiru, ta san Eatry din da yake magana don sun taΙ“a zuwa da Abdul kuma abincin wajen shegen tsada ne da shi, yace "Let go" Yana fadin haka ya juya ya fara tafiya, hakan ya sa ta mike ta bi bayansa, ya jira har ta iso inda yake sannan suka ci gaba da tafiya a tare har suka isa Eatry din, suna shiga ta kalli Jay that was grinning kamar yaga wanda ya sani a cikin Eatry din, lkci daya ta hango Ajay that was sitted da wata baturiya a cikin eatry din yana mata magana, ga abinci kala kala a gabanta, shi kuma ruwan gora ne kawai a gabansa, Khaleesat ta dauke idonta speaking calmly tace "I think zan tafi gida kawai, dama ba wani yunwa nake ji ba, i will order a Lyft in koma gida" Jay ya riko gyalenta don har ta juya zata fita yace "C'mon Halysaah, so kike ya kara raina ki, kina fita zai yi zaton tsoronsa ne yasa kika kasa shigowa kika fita and he will be very happy, kawai kiyi fuska ki tafi ki zauna" Khaleesat ta tsaya bayan ta Ι—an yi nazarin abinda Jay yace, kuma fa haka ne zai yi zaton tsoronsa take, hakan yasa ta karasa Jay na biye da ita a baya ya jawo mata kujeran dake facing inda su Ajay ke zaune ta zauna, Jay ma ya zauna sannan ya kalli direction din Ajay dake kallonsu babu yabo babu fallasa, Jay ya daga masa hannu with smile all over his face alamar Hi, Ajay ya dauke kai kamar bai taΙ“a saninsa ba a rayuwa, Jay ya daga kafadarsa yana murmushi sannan ya dau menu dake saman table ya mika ma Khaleesat yace "Duba abinda zaki ci" Ta amshi Menu din tana kallo, cikin few minutes Jay ya saka masu order aka kawo masu abincin, duk da Khaleesat tana facing din Ajay ko da wasa bata yarda ta kallesa ba, tayi kamar bata san da shi a Eatry din ba, Jay kuwa cin abincinsa kawai yake with full concentration not minding her in his front, lkci lkci Khaleesat ke kallonsa, ta lura he doesn't joke with food and sleep for anything, dariya ma ita yake bata, ita kam a hankali take cin abincin gabanta, ya daga kai ganin bata wani ci Crab patatoe Chips din gabanta ba yace "Should i fetch some of urs?" Ta wani kallesa tace "Do you have an extra stomach?"  Bai san sanda yayi dariya ba yace "I don't understand an extra stomach?" Tana kallonsa calmly tace "Naga duk kai ka kusa cinye abincin kan table din nan" Jay ya bude ido sosai yace "Har da sharri? Me da me na ci a table din?" Ta tallabi chin dinta tana murmushi tana kallonsa wanda har sai da dimples dinta ya lotsa, Mistakenly ta daga ido suka hada ido da Ajay dake kallonsu babu yabo babu fallasa, nan da nan murmushin dake fuskarta ya bace ta sha kunu, Jay bai ma san tana yi ba don tuni ya ci gaba da cin abincinsa har ma ya diba na gabanta, Khaleesat ta kalli wayarta dake vibrate kan table, sosai gabanta ya fadi ganin Abdul ne ke kiranta, Jay ya daga kai ya kalleta yace "Ba kiran ki ake ba?" A hankali tace "Na sani" Yace "Why are you not picking?" Tayi shiru, sai a sannan ta tuna fa ashe ya kirata severally bata daga kiransa ba, Jay yace "Ko de saurayinki ne?" Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, yace "Ki daga mana kar kiyi laifi" Sauke idonta tayi ta daga kiran a hankali ta kai kunne tare da sallama cikin sanyin murya.....

 

 

 

07087865788✍🏻

[5/14, 5:45 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6

 

 

 

✨✨ HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

 

17....

 

Daga daya bangaren Abdul yace "What is wrong with you these days Khaleesat? Me yake damun ki?" Tunanin abinda zata ce masa ta fara yi, tayi shiru gabanta na faduwa, ita ta ma rasa me yasa take Ζ™in daga kiransa kwanan nan, kawai a zuciyarta take jin bata son waya da shi, Jay ya daga kai ya kalleta jin tayi shiru ga waya Ζ™are a kunnenta, amsar wayar yayi ta zaro ido tana kallonsa da mamaki with fear, ya sa wayar handsfree ya rage volume sannan ya ajiye saman table ya ci gaba da cin abincinsa, a fusace Abdul yace "Wai baki ji na ne, or is something wrong with you?" A hankali Khaleesat tace "Ina jin ka mana, na mance wayar ne a gidansu Safiyyah, i just got it now" Sounding so provoked yace "Ni zaki raina ma hankali? Ke ce zaki bar wayarki tun jiya gidansu Safiyyah?" Khaleesat ta wani kyabe baki ta kauda kai tace "Haka dai kawai bazan ki daga kiranka ba, me yasa baza ka min uxuri ba?" Abdul yace "Wait Khaleesat, where are you getting ur liver from these days? Who is ur vendor? Yaushe kika fara samun courage din mayar min da magana?" Khaleesat tace "Toh ni yanzu me nayi? Nace maka wayar baya wajena and u are trying to create an issue out of nothing, Nan da few weeks fa za mu fara jarabawa, you are only adding more pressure to the one i am already in, ka dinga considering dina mana pls" Jay ya Ι—an daga kai ya kalleta, sai kuma yayi murmushi ya dau ruwan gora ya bude yana sha, Abdul yace "A kanki aka fara jarabawa? What is the big deal ah jarabawan da zaki yi? Ko dai Safiyyah ce ke dora ki akan abinda bazai fisshe ki ba? Safiyyah ce take zuga ki har kika fara samun courage din mayar min da magana ko? Switch to video call now" Khaleesat taji gabanta ya fadi sosai, Jay dai murmushi kawai yake, a hankali Khaleesat tace "Ohk i will, amma kayi hakuri let me dress up first..." A mugun fusace yace "Ki bar shi" Yana fadin haka ya katse wayar, Khaleesat dai tayi shiru tana kallon wayar nata, Jay yace "Ki gama cin abinda zaki ci mu tafi Halysaah, it's pass magrib now zan je inyi sallah" Khaleesat ta daga idanuwanta tana kallonsa, yace "Ko ayi maki takeaway din abincin?" Ta sauke idonta bayan sun hada ido da Ajay da ya mike daga inda yake zaune, Jay ya juya ya Ι—an kalli Ajay yace "Hey man, ka hada har nawa bills din" Ajay yaki kallon direction dinsa kai kace bai san sa ba ma, Jay ya kira daya daga ma'aikatan wajen ta karaso, ya sa tayi masu packaging abincin da Khaleesat bata ci ba, ita dai Khaleesat har sannan taki cewa komai kana ganinta kasan she is a bit disturb, Jay ya bi Ajay da kallo har ya fita daga Eatry din da baturiyar da suke tare, shi bai ma taΙ“a ganinta ba sai ranan duk kwashe kwashen Ajay ne, bayan ma'aikaciyar wajen ta gama packaging abincin, yana kallonta ya tambayeta bill dinsa, nan ta sanar masa Ajay ya hada har nasu ya biya, Khaleesat ta daga kai ta kalli waitress din jin abinda tace, Jay yace "Ok then" Mikewa yayi ya dau ledan abincin Halysaah yana kallonta, ta tashi ta dau wayarta, yana gaba tana biye da shi suka fita daga wajen cin abincin, Lyft din da Jay yayi masu order har ya iso, ya bude mata back seat yana jiran ta shiga, Khaleesat felt somehow hakan da yayi, don duk fitar da suke yi da Abdul bai taΙ“a mata haka ba, yawanci ma shi yake fara shiga sannan ta shiga, bayan ta shiga motar Housemate dinta ma ya shiga, sai da suka kusa gida wayarta ya fara vibrate, ta kasa duba me kiranta sanin kila bazai wuce Abdul ba, Jay dake danna wayarsa ya kalleta yace "Kiran ki ake ai" Bata ce masa komai ba ta kalli screen din wayar sai taga Safiyyah ce ke kiranta, ta daga da sauri ta kai kunne tace "Hello Sophie" Safiyyah tace "Am at the door, nayi knocking shiru" Khaleesat ta Ι—an saci kallon Jay, sai kuma a hankali tace "Ohk na Ι—an fita ne amma ina hanya yanzu" Da mamaki Safiyyah tace "Kin fita? Ban gane kin fita ba, Ina kika je?" Khaleesat tayi shiru, Safiyyah tace "Ko da Housemate din ki?" Khaleesat tace "Um" Safiyyah tace "Hmmm i see, to in dai baku kusa dawowa ba bari inyi tafiyata kawai" Da sauri Khaleesat tace "Aa ki jirani am on my way" Tana fadin haka ta katse wayar, ajiyar zuciya ta sauke don tayi tunanin Abdul ne ya kira Safiyyah shine ta kirata, after some minutes suka isa gida, ta bude side dinta ta sauka daga Uber din, Jay ma ya sauka, Apartment dinsu ta nufa, ta Ι—an rage pace dinta ganin kamar motar Mustapha a vicinity din, shi dai Housemate dinta na biye da ita a baya, sai ga Safiyyah ta fito daga motar Mustapha, da murmushi fuskarta ta nufesu ta gaida Jay, ya tsaya ya amsa mata sannan ya wuce cikin gida, Safiyyah ta kalli Khaleesat tace "Toh ki gaida ya Mustapha, dama girki na tsaya maki na zata har yanzu bakya iya tashi" Khaleesat ta kirkiro murmushi tace "Ohk bari in gaishesa" Zagawa tayi zuwa side din Mustapha taga yanda ya bi Jay da kallo har Jay ya shiga cikin gida, gaishesa tayi kanta a kasa, ya kalleta yace "Who is he Khaleesat?" A hankali Khaleesat tace "Housemate dina ne" Mustapha ya kalli Safiyyah yace "There was a time da kika ce min mace ce Housemate dinta?" Safiyyah tace "Eh wallahi the lady packed out shine shi ya shigo, ai bai wani dade sosai da dawowa apartment din ba" Mustapha ya kalli Khaleesat yace "Me yasa zaki dinga zama gida daya da namiji da sunan Co-living Khaleesat, why not come stay together with ur frnd Safiyyah in my house?" Safiyyah ta wani kallesa, sai kuma ta kyabe baki, sai kace ya gama kwatar mata 'yan ci gun shegiyar matarsa balle ya kwatar ma ita da kawarta, ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba tana wasa da veil dinta, Mustapha yace "Wani yare ne Housemate din naki?" Caraf Safiyyah tayi tace "He is from Tanzania, yaren can kasar yake yi, beside shi baya ma wani zama a gidan once a while yake zuwa yayi karatu kawai" Mustapha ya wani kalleta yace "Ke na tambaya?" Gefe ta koma bata sake cewa komai ba, Mustapha yace "Daga ina ku ke da daddaren nan Khaleesat?" Khaleesat tace "I was sick tun da safe shine muka je ya siya min abinci yanzu" Mustapha dai sai kallonta yake, after some seconds yace "I will talk to my wife, sai ki dawo nan gidana kiyi zamanki tare da Safiyyah har ku gama Exams, i think the exam is by the corner...." Khaleesat tayi murmushi kawai bata basa amsa ba, Safiyyah tace "Mu je in kai maki abincin da na kawo maki ciki" Bude bayan motar tayi ta ciro abincin, Khaleesat tayi ma Mustapha sai da safe sannan suka wuce apartment dinta tare da Safiyyah, nan parlor Safiyyah ta ajiye abincin tayi kasa da murya tana washe baki tace "Ban gane wannan fitar da ku ke yi da Housemate dinki ba Khaleesat? Ina ku ka je?" Khaleesat tace "Abinci fa muka je ya siya min, kuma ba wai lapiyata lau muka je ya siya min abincin ba" Khaleesat ta ajiye ledan abincin hannunta ta zauna gefen kujera tare da sauke boyayyen ajiyar zuciya, Safiyyah dake washe baki tana ma Khaleesat wani kallo tace "To ya aka yi yasan baki da lafiya, kuma how did he know what was wrong with you?" Khaleesat tace "Kinga Sophie wnn ba shine damuwata ba yanzu, muna gidan cin abinci Abdul ya kirani" Safiyyah ta wani yatsine fuska tace "So? Da ya kiraki sai aka yi yaya?" Cike da damuwa Khaleesat ta bata labarin yanda aka yi da kuma call dinsa da ta ki picking tun jiya, Safiyyah tace "Haba, to ko ke fa da kika fara kokarin kwatar ma kanki 'yan ci, ni sai nake ga kamar Housemate din nan naki ne ke baki Liver kike wasu abubuwa yanzu, banda haka yaushe har kika yi bakin gaya ma Abdul magana haka" Tana dariya ta kare maganar, Khaleesat ta dinga hararanta ganin ta ma maida abun joke, Safiyyah tace "In ni ce ke ma bazan kirasa ba wallahi, gwara kawai komai ya ruguje kowa ya huta" Khaleesat tace "Kin manta abinda yayi kwanaki kawai muka gansa kamar an jefosa Sophie? Kinsan yanzun ma ba karamin aikinsa bane sai ya iya kamo hanya ya zo" Khaleesat ta dafe kanta tsabar she is confuse, Safiyyah tayi shiru, can kuma ta kyabe baki tace "Kuma haka ne ba kai ne da shi ba sai ya iya kamo hanya tunda ba su dau kudi bakin komai ba, kawai anjima ki kirasa sai ki kisa abinda zaki ce masa da zai gamsar da shi, kuma kina iya cewa baki da lafiya gantalallen ya kamo hanya, ni dama ya tafka wani tsiya America su kwace visan sa kowa ya huta" Duk da damuwar da Khaleesat ke ciki sai da tayi dariya, Safiyyah tace "Allah kuwa, ban ki ba ya zo ya maki hauka da kaina zan kira masa 911 wallahi" Khaleesat dai tayi murmushin karfin hali kawai, wayar Safiyyah ne ya fara ring ta duba taga Mustapha ke kiranta, turo baki tayi tace wannan mutumi yana takura rayuwata a kasar nan, wai daga cewa zan kawo maki abinci ya zata yawo zani shine fa ya biyoni, kema baki ji ba wai ki dawo gidansa da zama, salon wataran matar ta saka mana guba a abinci mu ci mu mutu gaba daya, yanzu haka fa ko ga maciji bama yi da ita, Ι—an fitar nan da yayi da ni muna nan dake sai ya zamar masa matsala, tana can ta cika tayi fam tana jiransa, ko a jikina kuwa, sai na ma lallabasa ya kai ni ya siya min ice-cream ta yanda zata ga na dawo rike da leda" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, Safiyyah ta mike tace "Bari in je, sai mun hadu Monday in sha Allah" Khaleesat ta rakata bakin kofa a hankali tace "Thank you Safiyyah" Safiyyah tace "No thanks kawata, ki ce ma Housemate dinki na tafi" Khaleesat ta gyada mata kai, a haka Safiyyah ta fita daga gidan, Khaleesat ta kullo kofar a hankali, abincin da Safiyyah ta kawo mata ta dauka ta kai fridge da wanda Housemate dinta ya sa ayi mata takeaway. Khaleesat ta fito wanka kenan taji Housemate dinta na knocking kofarta, ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta nufi kofar ta bude tana kallonsa, yana rike da laptop dinsa yace "Good night Halysaah, i am sleepy" Khaleesat tace "To sai da safe, thank you for the dinner" Yace "No thanks.... kin kira BF din naki?" Khaleesat taki basa amsa, yace "Amma bari in tambayeki, a ina kika hadu da gayen nan ne? Don't know ko na taΙ“a tambayarki kwanaki...." Khaleesat ta jingina da kofa without looking at him tace "Back home" Yana gyada kai yace "I see, ni at first na zata you are not Nigerian, was thinking you are from Niger or Chad, probably Shuwa Arab" Khaleesat ta dinga kallonsa, bata san sanda tace "Why?" Yace "Na ganki kamar Buzuwa" Khaleesat ta sauke idonta bata basa amsa ba, yace "Ok, i will be on my way, good night" Daga haka ya juya ya bar wajen, a hankali ta sauke idonta sannan ta kulle dakinta ta jingina jikin kofar, she stood there for almost 5 mins kafin ta karasa cikin dakin ta cire hijab din jikinta ta ciro sleeping dress dinta ta saka, sanitary pad dinta dake gaban dressing mirror ta dinga kallo, sai kuma ta dauke daga wajen, sai da ta kwanta sannan tayi dialing number Abdul gabanta na faduwa, har ya katse bai daga ba dama tasan ba lallai ya daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, ta bude WhatsApp tayi masa magana ta nan, reply yayi mata yace "I don't have ur time so do not border me" tabe baki tayi ta ajiye wayar ta kashe wutan dakin sannan tayi kwanciyar ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa. Washegari bayan Khaleesat ta gama azkar din da take yi, ta jawo wayarta a hankali, tunda ta tashi jikinta yake a sanyaye don mafarki tayi Abdul ya zo kamar yanda ya zo wancan lkcn still kuma ya sake haduwa da Housemate dinta a gidan, ba karamin daga mata hankali mafarkin nan yayi ba, WhatsApp dinta ta bude bayan tayi deciding zata masa message din ban hakuri duk da bata saka ran reply dinsa ba, cause it won't be funny if her dream comes true, tana shiga WhatsApp din ta ga ya turo mata hotuna kusan biyar tun 3 hours ago, bude message din tayi zuciyarta na bugawa don bata san hotunan menene ba, nan taga har da message yayi mata kafin yayi sending hotunan, ta fara downloading hotunan at the same tana duba message din da ya rubuto mata kamar haka "So now, kina kokarin nuna min cewa i made the mistake of letting you go to America to study right? Kin mance wacece ke ko? kin mance daga inda kika fito, then that is so foolish and stupid of you Khaleesat, amma ina me tabbatar maki idan har kika ci gaba da daukata for granted kamar yanda kike yi kwanan nan sai na sa kinyi da kin sani wallahi" Lkci daya Hawaye ya cika idon Khaleesat, ta sauke idanuwanta kan hotunan da ya turo mata, daya hoto ne da shi yayi mata a bakin kofar dakin Ummanta, yana zaune kan tabarma ta duka gabansa zata ajiye masa ruwa a Cup shine ya dauketa hoton, shekaru hudu da suka wuce kenan, she look so so young and meek a hoton, hoto na biyu kuma tana wajen debo ruwa a nan unguwansu ya zo ranan ya ganta a wajen, ita bata ma san yayi mata hoton ba ga zaninta duk a jike, hoto na uku kuma tana baΖ™in murhu a tsakar gidansu tana juye alalan siyarwan Ummanta a Cooler shi kuma ya zo gidan ranan, duk bata san ya mata hotunan nan ba sai yau da ya turo mata ta gani, hoto na hudu kuma ranan da ya kai ta zata zana Jamb ne, jamb din da bata ma yi amfani da shi ba daga karshe, sai kuma hoton karshe na ranan da zai kawota USA for the first time, looking at all the pictures da kuma looking at her now zaka ga banbanci me tazara sosai, infact the difference is very obvious don a yanzu she looks more beautiful, matured, nourished and well taken care of, yanzu skin dinta har wani glowing yake, in ma ba ka santa ba bazaka taba cewa ita ce a hotunan ba, bata san sanda ta fashe da kuka ba ta hade kanta da pillow tana kuka sosai, but like seriously Abdul bai yi deserving haka daga gareta ba, but did she also deserve irin abubuwan da yake mata? Kuma tun asali haka yake mata, Kuka sosai tayi babu me rarrashinta, bata ma san me take ji a zuciyarta ba a lkcn, she cried profusely for almost 30 mins, daga karshe tayi karfin halin mikewa zaune ta dau wayarta, she don't even know where to start from, Voice note ta fara masa muryarta na rawa trying to tell him she is sorry, amma bata kai ko ina a basa hakurin ba ta fashe da kuka sosai, cikin kuka ta ci gaba da basa hakurin, sai da tayi masa Voice note uku sannan ta ajiye wayar still crying....

 

 

07087865788✍🏻

[5/15, 3:23 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6

 

 

 

✨✨ HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

18.....

 

Wajen karfe goma na safe Khaleesat na kwance dakinta idonta rufe duk da ba bacci take ba, ji tayi ana kwankwasa kofa, kamar bazata iya tashi ba daga karshe dai ta mike ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta saka, tana tafiya a hankali ta fito parlor, ta tagar parlon ta duba ta ga Housemate dinta ne, ta karasa ta bude kofar, Yace "Sorry na tashe ki kina bacci, i forgot the key at home" Ita dai bata yarda sun hada ido ba a hankali tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau, how are you feeling now?" Ta juya going back to the parlor tace "Alhamdulillah" Ya bi ta da kallo sannan ya shiga parlorn, dakinta ya ga zata koma yace "Halysaah" Ta tsaya, after few seconds ta juyo but couldn't let her eyes contact his, shi dai kallonta kawai yake, ya karasa inda take tsaye yace "What happened?" Girgiza masa kai kawai tayi, lkci daya hawaye ya fara sauka idonta, ya dauke kai na 'yan dakiku kafin ya sake juyowa ya nuna mata kujera yace "Sit" Komawa tayi ta zauna, ya zauna shima yana kallonta yace "Tell me what's wrong" Ta sunkuyar da kanta, yace "Are you sick?" Ta girgiza masa kai, yace "Wannan saurayin naki ko?" Ta kasa basa amsa wasu hawayen na sauka idonta, sai kuma ta fashe masa da kuka, mikewa yayi yace "Waye ya hadaki da wannan mutumi ne? Why did u allow him know ur weak point? Why are you always crying because of him? Is he happy making u sad now and then?" Khaleesat dai kuka take a hankali, yayi shiru for almost 2 mins yana jin ransa na baci, can ya kalleta yace "Kee in zaki yi facing study dinki is better you do so, give that ur so called boyfriend space, ur exam is around the corner" Sai a sannan Khaleesat ta daga idanuwanta da suka yi ja ta kallesa, sae kuma ya kwantar da murya yace "Kiyi hakuri Housemate, zan dinga sa ki a addu'ata Allah ya maki mafita, i can't just intrude cause ban san sanda ku ka san juna da shi ba, ban kuma san me ya hada ku ba, i will only include you to my prayers i promise Halysaah" Khaleesat ta gyada masa kai da kyar, sannan ta mike cikin sanyin murya tace "Nagode" Daga haka ta juya ta nufi dakinta, Jay ya koma ya zauna yana mamakin irin son da take ma gayen da har ta kasa rabuwa da shi duk da musguna mata da yake yi a soyayya, bata da aiki sae yi masa kuka, da kanwarsa ce daga ita har saurayin zai hada ya ci ubansu, kuma ya rabata da shi na har abada, tausayinta yaji har cikin ransa don bai san wani irin so bane wannan take masa da har take iya tolerating abubuwan da yake mata, and ya lura the guy is taking advantage of this to hurt her always, mikewa yayi ya tafi kitchen kamar yanda ya zarga yaga alamar bata yi breakfast ba har sannan don kitchen din ma bata shigo ba, fridge ya bude ganin abincin da Safiyyah ta kawo mata jiya yayi mata microwaving dinsa ya hada mata shayi sannan ya kai mata daki, sai da yayi knocking ta amsa sannan ya shiga dakin, tun da ya shigo Khaleesat ke kallonsa har ya ajiye mata abincin, ta sauke idonta a hankali tace "Nagode" kai kawai ya gyada mata, sai kuma ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, karfe sha biyu saura Khaleesat ta jawo wayarta jin yana vibrate, tana duba screen din taga Abdul ke kiranta, ta sauke idonta kasa tayi picking call din ta kai kunne amma bata ce komai ba, yace "Khaleesah...." ta kasa amsawa hawaye ya fara sauka idonta, yace "Can you hear me?" Da kyar tace "Um" Yace "How was you night" tana share hawayen dake sauka idonta tace "Alhamdulillah" Tun daga wannan rana Khaleesat ta fara avoiding duk wani abu da zai hadasu fada da Abdul, she want just nothing but peace with him for her sanity, bin sa kawai take a yanda yake so for peace to keep reigning, in ma bala'i yake mata a waya zata yi shiru ta gama saurarensa sannan daga karshe ta basa hakuri kamar yanda take yi masa da, ranan da bai kirata ba kuwa ita zata kirasa, hakan kuma da tayi ya sa ta samu kwanciyar hankali har take concentrating a karatun ta, amma fa in ta tuna irin kulawar da Housemate dinta ke bata always wanting to make sure she is fine sai taji she isn't lucky having Abdul, ana haka har exams dinsu ya rage some days, ranan Wednesday tana kitchen da safe taji ana kwankwasa kofa, ta fito daga kitchen din don dama she is expecting Safiyyah, ta bude mata kofa, Safiyyah ta shigo tace "Ai na zata zan zo in tarar baki tashi ba?" Khaleesat tayi kasa da murya tace "Aa i am in the kitchen" Safiyyah tace "Ohk, why are you lowering ur voice?" Still  Whispering Khaleesat tace "My Housemate is sleeping" Safiyyah ta sake baki tana kallonta, sai kuma ta rike haΙ“a tace "Ikon Allah gadinsa kike kenan?" Khaleesat ta hade rai tace "Ban gane gadinsa ba, daxu fa ya zo, and dama bacci yake zuwa yayi da safe don yace min baya bacci da daddare" Safiyyah couldn't stop smiling tana kallon Khaleesat, Khaleesat ta wani harareta ta juya ta koma kitchen, Safiyyah ta karasa ta zauna kan kujera har sannan bata daina murmushi ba, sai ga Khaleesat ta fito daga kitchen, still tana magana kasa kasa tace "Ko dai kawai mu je waje ki min gyaran gashin, kinga Hand dryer yana Ζ™ara in ana using dinsa, it's noisy" Safiyyah ta buda baki tace "Ikon Allah, to akwai socket ne a wajen?" Khaleesat tace "Zan sa Extension a kitchen sai mu fito da shi ta window ai zai yi, kuma akwai tap a garden din sai mu wanke gashin ma a nan" Safiyyah dai murmushi kawai take bata ce mata komai ba, yanda Khaleesat tace haka din tayi duk don kar karan Hand dryer ya tada Housemate dinta or any of their noise kamar yanda tace, abinda bata sani ba ashe ba bacci yake ba aiki yake yi a Laptop dinsa a daki, bayan sun isa karamin Garden din dake bayan kitchen Khaleesat ta ajiye duk shampoo da Conditioner din hannunta sannan ta bude gashinta, Safiyyah na kallon gashin tace "Tab, Allah sa Shampoo din da Conditioner su isa dai" Khaleesat ta wani hade rai tace "Ban gane ba, saboda bargo za ki wanke?" Safiyyah tayi dariya tace "To meye banbancin wannan da bargon Khaleesat? Babancinsa kawai wannan akan ki yake, ni naga ma kamar karuwa gashin yake Tabarakallah Maa sha Allah" Khaleesat tace "Ba abinda ya karu yana nan yanda yake" A haka Safiyyah ta fara wanke mata gashin, suka dau time sosai bayan ta gama wankewa ta fara busar mata shi da Dryer, Jay ya shigo kitchen zai yi making Coffee drink ya dinga kallonsu ta window din kitchen, he was confuse seeing her hair, is all that Hair or what? long, full and black, kawai yaji bai yarda gashinta bane, ya juya ya fara yin abinda ya kawo sa kitchen din, Khaleesat ta kasa kunne sosai jin kamar sound a kitchen, ai ko ta jawo mayafinta da sauri ta rufe kanta bayan ta hangosa a kitchen din ya juya masu baya, Safiyyah dai sai kallonta take, Khaleesat ta mike ta isa kusa da window din kitchen din tana kallonsa tace "You woke up early today" Ya juya ya kalleta yace "This is to 12" Khaleesat ta zaro ido don bata san lkci ya wuce haka ba, ashe sun bata lkci sosai wajen wanke gashinta, yace "Me kike yi a nan?" Tace "I am together with my frnd Safiyyah" Ya ci gaba da abinda yake yi yace "Ohk my regards" Juyawa tayi ta koma gun Safiyyah, bayan Drying har Stretching gashin sai da Safiyyah tayi mata, Safiyyah tace "You know what Khaleesat, anjima ki zo can gida sai in maki Kalaba din, i think i can feel my period, i need to go home" Khaleesat ta juya ta kalleta tace "Da gaske?" Safiyyah tace "Wallahi, gwara in tafi gida kar ya zo" Khaleesat tace "Ohk, amma ki bari in dafa mana indomie ki ci tukun ki tafi" Safiyyah tace "Ke bazan ci ba, bari in tafi kawai i am uncomfortable" A hankali Khaleesat tace "To shikenan" Safiyyah tace "Sannan pls Khaleesat nace ma Ya Musty ran sunday zaki zo gidan tunda kinga Monday za mu fara exams, ko 2 days ne sai kiyi kafin matarsa ta fito da baΖ™in halinta gaba daya, kin dai ga bazai ce bamu ji maganarsa ba yace ki dawo gidansa baki dawo ba, even if it's just 2 days come and spend in his house pls" Khaleesat tace "Wallahi ba wai bana son zuwa bane ko kuma ban ji maganarsa ba Safiyyah, bana son issue ne da matarsa, i don't want any problem" Safiyyah tace "I know, shi yasa nace ko kwana biyu ne kawai ki zo kiyi ai bazai ce baki zo ba, ranan Sunday sai ki debi kayanki kala uku ki taho kawai, probably ma daga karshe nima nan gidan zan dawo mu yi karatu tare, ni nasan ba lallai ma kiyi kwana biyun ba matarsa bata kirkiro wata matsala ba, so just chill ba zama zaki yi a gidan ba Likewise myself" Khaleesat tayi shiru kamar me nazari, sau biyu Mustaphan ke mata magana da kansa ta WhatsApp akan dawowar da yace tayi gidansa, iyaka sai tace masa in sha Allah tana nan zuwa before exam, Safiyyah ma tayi mata magana yafi a kirga, ko don Safiyyah zata daure kawai taje tayi kwana biyun a gidan, let it not be as if bata jin magana, a haka ta raka Safiyyah bayan tayi order din Uber da zai maida ta gida, Khaleesat na dawowa parlor taga Housemate dinta ya shirya zai fita, yana kallonta yace "Wai duk gashinki ne wannan ko dai Ζ™arin gashi kike yi Halysaah?" Ta daga idanuwanta ta kallesa bayan tayi realizing ashe ya ganta kenan daxu, sauke idonta tayi tace "Ƙarin gashi kuma?" Yace "Naki ne? Ai na gansa kamar ba naki bane, sorry" Ɗan murmushi kawai tayi without giving him an answer, can yace "Wait, amma ba ki jin zafi na damun ki? I mean baya takura ki gashin? isn't it too much?" Tace "How?" Sounding so serious yace "Ki rage mana, just cut half of it off kema ki huta, sai kiyi azumi uku, wannan ai burden ne Halysaah, it's too much, ji fa sai da kawarki ta zo taya ki wankewa don kema baza ki iya wankesa da kanki ba, all this while ni na zata irin wannan acuci mazan da ku ke yi ne kike daurawa a kanki, i never knew gashin ki ne" Khaleesat tayi murmushi ba tare da tasan tayi hakan ba, can ta kallesa calmly tace "But i am not complaining, kuma ai ba nauyi gashin yake min a kai ba" Ya wara ido yace "Ohh! my bad, haka ne kuma fa, hope you are reading so well for ur exam, kinga in few days time zaku fara, i think monday ko?" Ta gyada masa kai, yace "Wishing you the very best of luck Halysaah" a hankali tace "Thank you" Yace "See ya later" Ta gyada masa kai, daga haka ya juya ya nufi kofa ya fita daga parlon.... Da yamma Khaleesat ta gama shiryawa bayan Safiyyah ta isheta da kira wai taje ta mata kitson, Khaleesat ta dau handbag dinta da mukullin gida bayan Uber din da tayi order ya iso sannan ta fita daga gidan ta kulle, tana hanya kiran Safiyyah ya shigo wayarta, ta daga tace "Ina hanya fa" Safiyyah tace "Allah in baki zo ba sai dai gashinki yayi ta zama haka bani da lokacin maki wani kalaba kuma idan aka fara jarabawa" Khaleesat dai tayi murmushi, tasan kawai Safiyyah so take ta je gidan, karfe hudu da yan mintuna ta isa gidan ta sauka Uber sannan tana tafiya a hankali ta nufi apartment din, tsayawa tayi bakin kofa ta danna bell, lkci daya aka bude kofar, sai da gaban Khaleesat ya fadi ganin Surayya ce ta bude mata kofa, ta sauke idonta tace "Ina yini?" A takaice Surayya tace "Wa kike nema?" Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace "Wajen Safiyyah na zo" Bluntly Surayya tace "To bata nan, sai ki juya ki koma inda kika fito" Khaleesat was just looking at her babu ko kiftawa, sai ga Safiyyah ta fito daga daki fuuu, tana huci tace "Wajenta kika zo da zaki tsaya sauraronta baki bangajeta ba kinyi shigowarki?" Khaleesat ta bude baki tana kallon Safiyyah, wato ta bangaje matar gida ta shigo tsabar neman jifa'i, Surayya ta juya a fusace tana kallon Safiyyah tace "Tunda gidan na ubanta ne ko naki uban sai ta shigo mu ga" Safiyyah tayi cilli da wayar hannunta ta fige dankwalin kanta tace "Wallahi kar ki ga na raga maki daxu saboda yaya, to yanzu baya nan cin kaza kazanki zanyi la'ada waje" Khaleesat was shock, ta kasa rufe baki tana kallonsu, Surayya ta nufi Safiyyah tana kunduma mata zagi kamar dai yanda tayi mata few hours ago a gaban cousin brother dinta, instead sai cousin din ya dinga ba Safiyyah hakuri without taking any action, dama Safiyyah a wuya take, sbda bakin ciki ne ma yasa ta dinga kiran Khaleesat ta zo gidan, Khaleesat ta zaro ido ganin yanda Safiyyah ta finciko Surayya cikin zafin nama, ba ayi wata wata ba suka fara tikar dambe a wajen, Khaleesat ta karasa ciki da sauri tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, meye haka kuke yi Safiyyah? Don Allah ku bari" Yaron Surayya dake kan kujera sai tsala ihu yake, Khaleesat tayi kokarin rabasu taga an cillar da ita gefe har sai da ta kusa faduwa, bata sake gigin zuwa kusa da su ba, ta bude wayarta da sauri ta fara neman number Mustapha, tana kokarin kiransa taga Surayya na harin fixgo wani flower vase zata buga ma Safiyyah a kai, hakan yasa Khaleesat ta tafi da sauri ta dauke Vase din daga inda yake, Safiyyah tayi using opportunity din ta fixge vase din a hannun Khaleesat ta maka ma Surayya a goshi, sai ga jini kuma hakan bai sa sun fasa damben da suke ba, ko da Khaleesat ta kira Mustapha ashe yana hanyar dawowa, cikin few minutes sai gashi ya shigo gidan, sai shi ne ya rabasu bayan sun yi ma juna laga laga, Surayya bata daddara ba tayi kukan kura tayo kan Khaleesat zata cafkota tana cewa "Kika bata Vase ta buga min, wallahi kema sai na ci kaza kazan ki" A nan ne Mustapha ya sauke mata mari ya fincikota yace "Ko kin fara hauka ne Surayya? Me kike son mayar da ni a kasar nan ne?" Ita dai Khaleesat ta tsorata sosai, Safiyyah na huci tace "Shegiya bayerabiyar banza kawai jaka jahila..." Bata rufe baki ba ita ma Mustapha ya kai hannu zai gaura mata mari ta kauce da sauri tana harare harare tana huci, Surayya dake kuka wiwi ta figi Ι—an ta zuwa sama tana cewa "Wallahi sai dai ka zaba ko ni ko Safiyyah a gidan nan yau, in ko ba haka ba ni zan bar maku gidan kayi zaman auren da ita" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ko ba komai dai ta fasa mata kai hankalinta ya kwanta ta kuma ji dadi, Mustapha ya zauna saman kujera ya dafe kai, juyawa Khaleesat tayi sum sum ta fita daga parlon wishing dama bata zo gidan ba kilan da haka bai faru ba, da tasan bala'in da za ayi kenan babu abinda zai fara fitowa da ita daga gida, Safiyyah ta figi dankwalinta zata bi ta, Mustapha ya mata tsawa yace "Kar ki kuskura ki fita daga gidan nan" Safiyyah ta fashe da kuka tana bubbuga kafa tace "Ni wallahi yaya na gaji, na gaji kuma haka, na gajiiii, dubi cin mutuncin da matarka ta min daxu kace in kyaleta, yanzu kuma daga kawata ta zo wajena in mata kitso shikenan sai ta fara kunduma mana zagi ta kamani da dambe??" Yace "Wuce dakin ki nace" Ita dai Khaleesat tuni ta kara gaba ta bar gidan. That same day wajen karfe biyar da rabi sai ga Safiyyah ta zo gidan Khaleesat, Khaleesat ta zauna gefenta bayan sun shigo parlor tana kallonta tace "Ban ji dadin abinda ya faru ba yau Sophie, da na sani da ban je gidan ba ma wallahi" Safiyyah tace "Ai abun duniya ne ya dameni kamar in hadiye zuciya shi sa nayi ta kiranki ki zo daxu, wai fa bayan na gama yi maki gyaran gashi na koma gida matar nan kamar jirana take ta kama zagina ta uwa ta uba a gaban mijinta wai don me zan zubar mata da sauran miyarta dake kitchen, kuma fa kar kice da miya a tukunyar Khaleesat, wallahi ba komai ciki sai wani guntun miya da yayi tsami sai bugawa yake, ni kuma na wanke na dafa indomie na ci kafin in taho nan daxu in maki gyaran gashi, Ya Mustapha ya hanani cewa komai ya bani hakuri na wuce daki, a banza tunda dai shi ma har uwayensa ta zaga, shine bata daddara ba da kika zo zata sake hadamu ta zage ga yan iska sai muyi shiru muna kallonta, ni wallahi so nayi ace ma na cire mata hakora biyu ta dawo wawulo, amma dai a juri zuwa rafi wallahi sai na mata illar gaske kafin in gama karatu a kasar nan, dama tun 3 weeks ago da muka zo muka kawo maki abinci da ni da Y Mustapha ta kara kullatata ta kara tsanata tunda har yau tayi tunanin da akwai wani abu tsakaninki da Mustapha, ko ga maciji fa bama yi da ita a gidan" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Ki dai dinga hakuri plss Sophie wataran sai labari, da ni ce ke ma wallahi bazan dinga biyeta ba a gidan nan" Safiyyah tace "To ai ba kowa ke da matattciyar zuciyar da kare ya lashe irin taki ba, amma wallahi tayi kadan in ki biye mata, tana ce min kule zan ce mata casss don ubanta, an gaya mata ita ta isa ta shiga tsakanina da Mustapha? Cousin dina ne fa, Uwarsa ce ta sha nono ta bar ma uwata, Babansa kuwa Cousin din babana ne halaq malaq, ina ga bai taΙ“a zaunar da ita ya mata bayanin nan dalla dalla bane, kuma ya ci sa'ar bana kai karar abinda matsiyaciyar matarsa ke yi min gida, don wallahi da tuni an dau mataki, amma dai bari mu yi hutu in koma Nigeria" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Zancen gaskiya ke ma fa kina da naki Safiyyah, babu ta yanda za ayi kina zaune da mata ko Ι—an wanke wanken nan da shara baza ki ke taya ta ba a gidan, Abinda fa idan an mana mun san baza mu ji dadi ba to kar mu yi ma wani, she is also human, kuma at times bacin rai ne ke triggering wani mugun halin mutum, kece kika yi triggering din halinta a gidan, babu ta yanda zaki ji dadi wataran kanwar mijinki ta zo gidanki ta zauna bata taya ki aikin komai sai dai in kinyi girki ta deba ta ci ta ajiye maki plate, ki duba wannan lamarin fa, mu mata muna da son kanmu wani lkcn..." Safiyyah ta dakatar da ita tace "Ohh wato goyon bayanta ma kike kenan Khaleesah? you are trying to say duk abinda take min yayi dai dai ko?? To nagode, dama ke baki taΙ“a goyon bayan mutum a duk halin da yake ciki, in dai mutum zai kawo maki damuwarsa to ya kara dulmiya kansa cikin damuwa ne, ni kuma ban taΙ“a kin supporting dinki ba no matter the situation, ko Abdul da nake zagi kullum kamar Ι—a na nake goyon bayanki an gaya maki kema baki da naki baΖ™in halin ne wani lkci? Dama mistake nayi ma na zo gidan nan asirina a rufe da gidan Sandra na wuce da ba a kara bata min rai ba" Tana fadin haka ta mike ta figi jakarta ta nufi kofa kamar zata tashi sama, Khaleesat ta mike tace "Safiyyah" Banza da ita Safiyyah tayi har ta fice daga parlon ta kullo mata kofa, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna, a hankali tace "Ae shikenan"

 

 

07087865788✍🏻

[5/15, 7:17 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6

 

 

 

✨✨ HALYSAAH✨✨

 

 

 

 

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

 

 

 

19....

 

Ranan friday wajen karfe sha daya na safe Khaleesat ta gama Laundry da take a kitchen ta fito, a reading nook din parlon ta tarar da Housemate dinta yana duba textbooks dinsa, cikin few seconds ya dau wanda zai dauka ya dawo cikin parlon yana kallonta yace "Har kin gama kenan" Kai kawai ta gyada masa ta fara tidying din parlon, rana na farko kenan da ta fara ganinsa yayi shiga irin ta Hausa cikin fararen kaya, Taji yace "Hope you are studying well Halysaah" kai kawai ta gyada masa, yace "Alright, till later" Ta Ι—an kallesa tace "Are you Nigerian?" Ya buda ido yace "Why do u ask?" Tace "Kawai nayi zatan ko daga Chad kake, or Niger" Dariya yayi yace "Hope it's fine now tunda kin rama?" Hanyar dakinta ta nufa ba tare da ta basa amsa ba, ya dau makullin motarsa ya nufi kofar parlon, sai bayan da ya fita sannan ta dawo cikin parlon ta tafi gun window ta Ι—an bude drapery din jiki tana leka garage, ganin har ya tafi ta ci gaba da aikin da take yi a parlor. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat na kitchen tana girki at the same time suna waya da Abdul, tun 40 mins ago ya kirata suke magana har sannan, duk kwanan nan dai lafiya suke waya da shi, ya kuma Ι—an rage mata wasu abubuwan da yake mata, he is being a little caring these days, a rana sai su yi waya sau biyu wani lkcn har sau uku har hakan na bata mamaki kamar dai ba shi ba, yanzun ma shi ne yayi encouraging dinta ta tashi ta fara girkin da take yi don bata yi niyyar girki ba, for weeks now kullum Housemate dinta ke masu takeaway na dinner wani lkcn har lunch, this made her soo lazy to go to the kitchen, breakfast dama tea and cookies take ci yawanci ko kuma ta ci da bread idan Housemate dinta ya siyo, wani lkcn ta ci french fries da kwai ko ketchup, kwankwasa kofar parlor taji ana yi, ta Ι—an zaro ido sanin bazai wuce Housemate dinta ba, kilan ya mance makullinsa ko kuma yayi misplacing dinsa as usual, ta kalli wayarta dake ajiye a kan kitchen cabinet har sannan Abdul was on the line kuma a handsfree ta sa wayar, tana Ι—an kame kame tace masa "Can u excuse me pls, i will call u back in the next 2 minutes pls" Abdul yace "Why? Me zaki yi? Is the call hindering you from doing anything?" Da sauri tace "Noo" don bata son tayi laifi, sai kuma a hankali tace "Just want to round up the cooking ne, na kusa gamawa ai" Yace "But my call isn't preventing you from doing so, wayan ba a ajiye yake ba? Continue with ur work kawai" Knocking ta sake ji, ta ma san Housemate dinta ne cause haka yake knocking dinsa, ta kalli wayarta tace "Ohk then" Abdul ya ci gaba da maganar da yake mata, a hankali ta dau wayar ta fita daga kitchen din almost tiptoeing kamar tana tsoron yaji sound din tafiyarta, ta nufi kofar parlon ta bude at the same time tana kokarin yi ma Housemate dinta alamar da yayi shiru ta hanyar dora finger dinta daya a lips dinta, lkci daya taji komai nata ya tsaya cak, a hankali ta zame finger dinta daga lebbenta tana kallonsa bata ko kiftawa zuciyarta na bugawa, ta cire wayar dake kunnenta looking speechless and Surprise at the same time, Calmly yace "Ko in koma ne?" Ta zaro ido cikin in ina tace "No, no, not at all, i... i was just being surprise, sannu da zuwa" Da sauri ta koma gefe zuciyarta na bugawa da karfi, Ya katse wayar dake kare kunnensa sannan ya shiga parlon, ta bi sa da kallo still shocked, gani take kamar she is daydreaming, ta kikkifta idanuwanta ta bude to be sure but still she is still seeing him, har sai da ya karasa cikin parlon ya zauna sannan ta bi bayansa, a hankali ta duka kusa da shi tana yaΖ™en karfin hali tace "Wai dama all this while kana garin nan ne? I am so confuse" Yace "Gashi kin gan ni, in baki yarda ba sai ki taΙ“a ki ji don ki tabbatar" Still feigning smile tace "I am seriously surprise, this is the least thing i expected today wallahi..." Sai kuma ta tashi da sauri tace "Let me get u water" Kitchen ta tafi zuciyarta na bugawa, sai da ta jingina jikin cabinet ta dafe kirjinta a hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku" Tasan at anytime Housemate dinta zai iya shigowa gidan don yamma yayi sosai, cikin hanzari ta bude fridge ta dauko masa ruwan gora da drink with glass cup sannan ta fita da sauri, tana kirkiran murmushi ta durkusa gabansa ta ajiye masa tace "Tun yaushe kake garin nan amma?" Ya dau ruwan goran yana kallo yace "You are buying expensive water now? Sannu er gayu" Tayi dariyar karfin hali tace "Not at all, miyar ma ya kusa yi sai in zuba maka abincin, ko dama shi sa kace sai nayi girki?" Kawai murmushi yayi bai bata amsa ba, ta mike ta koma kitchen, gaba daya she is confuse on what to do, ta fara dube duben wayarta ta tuna ta ajiyesa kan kujera a parlor, fitowa ta sake yi ta tarar Abdul yayi picking din kiran da ake masa ta waya, cikin dubara ta dau wayarta ta nufi dakinta da sauri tana kallonsa ta gefen ido taga attention dinsa na kan wayar da ya fara, bandakinta ta shige ta kulle tace "Na shiga uku" Da ta tuna bata ma da lambar Housemate din nata ta sake jin mugun tashin hankali, yanzu ya zata yi? Da sauri ta fara dialing number Salem, ai ko yana fara ring ya daga, murya can kasa ta gaishesa without waiting for his full reply tace "Plsss how can i get in contact with my Housemate? ina son zan masa magana ne urgently" Salem yace "Ohk, muna ma tare, gashi nan" Bata san sanda ta sauke wani irin ajiyar zuciyar relieve ba, taji muryar Housemate dinta yace "Hello Halysaah, is everything alright?" Ta girgiza masa kai da sauri kamar yana ganinta tace "Plss i am sorry amma kar kace zaka dawo yau, my fiance is around, he just came without notice" Yace "Tohhhh, haka kuma aka yi ashe?" Ta wani turo baki kamar yana ganinta, yayi murmushi yace "Alright Halysaah, keep ur cool, duk sanda ya tafi sai ki sanar min" A hankali tace "Thank you" Yace "Not a problem" Shi ya fara katse wayar, ta kalli screen din sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fito da sauri bayan ta bar wayar a dakinta, har sannan ta tarar Abdul bai gama wayar da yake ba, da alama business call ne, Khaleesat na tafiya a hankali ta tafi kitchen don saka masa abincin da ta girka, har sannan she is shock, babban damuwarta yanzu kasantuwarsu su biyu kadai a gidan, a da bata jin tsoron kasancewa da shi guri daya and that was almost 4 years back, but not anymore, he is complete changed all of a sudden in just a year, da tunanin nan ta fito daga kitchen, ta karasa har gabansa ta ajiye masa abincin, yana kallonta yace "How about ur Housemate, bata nan ne?" Ta Ι—an yi murmushin karfin hali tace "Yeah bata nan" Ta mike ta koma edge din kujera ta zauna kamar bakuwa a gidan, a hankali tace "Ya su Momy da Aunty Hafsah?" Yace "Lafiya lau" Bata sake cewa komai ba, Ya kalli abincin da ta ajiye masa yace "I am full, ki rufe sai dai anjima" A hankali tace "Ok tafiya zaka yi da shi?" Yana dubanta yace "In tafi da shi ina?" Ta kirkiri murmushi tace "A'a ai tambaya kawai nayi" Yace "Na riga nayi lodging out of the hotel, i was in Maryland since morning" Khaleesat was speechless, bata gane yayi lodging out of the hotel ba, to ina zai kwana ko kuma wani hotel din zai kama? kai bata ma yarda ba don in yayi lodge out to ina trolley din kayansa yake, Tana murmushi da kyar tace "To ina akwatin ka?" Yace "Tana cikin mota" Ta hadiye abu da kyar tace "Motar wa?" A takaice yace "Ban sani ba" sunkuyar da kai tayi bata sake cewa komai ba, yace "Ko kina da plans ne yau? Naga kinyi mamakin zuwana da gaske" Ta zaro ido tace "Not at all wallahi, ai kai ma kasan daga schl babu inda nake zuwa, kawai dai nayi mamakin muna ta waya tun daxu ashe kana garin nan" Ya mike yace "To ki dena mamaki tunda ba ke kika siya min ticket din ba" Ta sunkuyar da kanta tayi shiru, dakinta ya nufa yace "Let me take a shower" Khaleesat ta gyada masa kai kawai ta bi sa da kallo, a very tall and masculine guy he is, just like her Housemate, and they are all handsome in their own different ways kamar su suka yi kan su, sai dai ita tafi ganin kyan Housemate dinta ko me yasa, a zahiri duk macen da ta samu Abdul in dai mayyar kudi ce kuma tana son namiji me tsantsan kyau ga kuma qualities na cikakken namiji pertaining to body structure not behavior... to duk walakancin da Abdul zai dinga mata zata jure tayi ta shanyewa don mijin nuna ma sa'a ne shi din, that is if behavior isn't included, amma Khaleesat dai dai da rana daya qualities din nan biyu na Abdul bai taΙ“a dada ta da kasa ba, a haka stepsisters dinta ko ga maciji basa yi da ita all because of Abdul, kiri kiri suke nuna mata jealousy dinsu daga su har iyayensu a fili, ba su kadai ba hatta wasu daga sa'aninta a anguwa sun dena kulata saboda shi, basu san baΖ™in cikin da take kunsa day by day ba, she wish zai koma ma daya daga stepsisters din nata da ita kam ta huta, kwantar da kanta tayi jikin kujera tana jin hankalinta na kara tashi, yana nufin kenan bazai tafi anytime soon ba? kilan ma yace nan zai kwana fa? Sosai hankalinta yayi mugun tashi da tunanin hakan, after a while ta mike a sanyaye ta dau abincin da ta zubo masa ta tafi da shi kitchen ta rufe, ana haka har lkcn sallan magarib yayi bai fito daga dakinta ba, Khaleesat dake ta zaune a parlor kamar bakuwa a gidan ta kalli kofar dakin nata a sanyaye, sai kuma ta tashi walking slowly ta nufi dakin, a hankali tayi sallama sai da ya amsa sannan ta bude, ta samesa zaune saman darduma alamar sallah ya idar yana danna wayarsa, gaba daya dakin ya cika da kamshin turarensa, murmushin karfin hali ta kirkiro ta dau hijab dinta tace "Sallah zan yi" Sai kuma ta juya zata fita yace "Ina zaki yi sallan?" Ta sake juyowa cikin sanyin murya tace "Parlor" Mikewa yayi ya bar kan darduman yace "Pray here, dama kin saba sallah a parlon ne?" Ya koma gefen gado ya zauna still pressing his phone, da kyar ta karasa kan darduman ta fara sallan, bayan ta idar ta dinga addu'ar Allah ya taΙ“a zuciyarsa ya tashi ya tafi ya bar mata gidan ita dai, muryarsa taji yace "Make me a cup of hot chocolate" Ta gyada masa kai tace "To" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita zuwa kitchen, abinda yace tayi ta masa sannan ta koma dakin rike da mug din, bedside drawer ta ajiye masa tace "In kawo maka abincin?" Yace "Aa bazan ci abinci ba, me yasa kike yawo da Hijab kamar matar liman" Tana murmushin karfin hali da kyar tace "Aa ina jiran lkcn isha ne" Yace "Cire Hijab din nan" Ba musu ta cire a hankali ta linke ta ajiye, yace "Ke kin ci abincin ne?" Duk da bata ci ba ta gyada masa kai don gaba daya ta nemi appetite dinta ta rasa, gun reading material dinta ta tafi ta zauna ta kunna laptop dinta tayi kamar karatu take, ya gama danne dannensa a waya ya dau chocolate dinsa ya fara sha, gaba daya Khaleesat bata fahimtar me take dubawa a laptop din gabanta, sun kusa awa daya a yanda suke, ita dai har sannan tana gaban laptop taki tashi, ta gefen ido ta kallesa ganin ya mike daga inda yake zaune, taga sallan isha zai yi, sai da ya idar sannan ita ma ta tashi ta tafi tayi sallan, nan ma babu kalan addu'ar dabata yi ba kan Allah ya taΙ“a zuciyarsa ya koma hotel dinsa, after a while ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye, ya mike ya kamo hannunta yana kallonta yace "Why are you uncomfortable kamar kina tare da stranger a gidan nan ne Khaleesat?" Tayi dariyar yake tace "Stranger kuma Ya Abdul? Ai kai ba stranger bane, kai yayana ne, kuma da ai ka sha kwana gidan nan farkon da na zo kasar, kana kwanciya a parlor ni kuma in kwanta a daki" Yace "Kinsan da haka kike dari dari?" Ta sunkuyar da kanta ganin kallon da yake mata, zuciyarta ya dinga bugawa, har ji take kafafuwanta suna neman kasa daukarta, ya matso da ita dab da shi har tana iya jiyo breathing dinsa, calmly yace "Kinsan menene yasa nake kwanciya a parlor a sannan?" Ta girgiza masa kai without looking at him don she is soo uncomfortable with him drawing her closer to himself, yayi kasa da murya yace "Saboda u were still a baby sannan" Ta daga idanuwanta da kyar ta kallesa amma ta kasa cewa komai, yace "Yanzu kuwa ke ba baby bace, how old are you?" Ta kasa basa amsa, ya Ι—an mata tsawa yace "Tambayarki nake?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "I am 20" yace "To a sannan ina keeping distance between us because i was still grooming you" Ta kauda kai seeing how closer he was coming to her, juyo da kanta yayi yace "Meye haka?" Muryarta na rawa tace "This is against the teaching of islam Ya Abdul, ni ba muharramarka bace" Yace "Oh really? Dama wani ne zai aure ki ba ni ba ashe?" Ta kasa ce masa komai lkci daya hawaye ya cika idonta, duk tsiyar da yake mata da yaga hawaye idonta yake calming down, ya jawota jikinsa yayi kasa da murya yace "Kin zata ke irin matan da zan yi using inyi dumping ne Khaleesat? You are diff from them, ke matar da zan aura ce" Ta kasa basa amsa hawaye na zuba idonta, ita kanta tasan Abdul so na aure yake mata, a shekarun da suka yi tare iyaka yakama mata hannu babu dadi babu kari, amma daga 2 years back labarin ya sauya har bata son ya zo inda take don sai ya mata wasu abubuwa dake damunta, in ya tafi ta sha kukanta kuma ta kan yi kwana da kwanaki bata dawo dai dai ba, amma bai taΙ“a attempting saninta ba, muryarsa ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, as if whispering yace "I have tried Khaleesat, i abstained from doing anything that will distabilize you all this years because i want you to have the best education ta yanda zan iya nuna ki a ko ina as my wife, amma kullum ina jin urge dinki a raina I've tried so many times to ignore the urge, but menene ya rage yanzu? You have just a year and few months to round up, aurenmu kuma ko yau aka ce a daura babu abinda zai hana daurasa, i came all the way from Nigeria because all this days my feeling for you is distabilizing me and making me go nut Khaleesat, so now trust me, relax and keep calm pls baby gal" Khaleesat ta dade bata shiga tashin hankalin da ta shiga a sannan ba, don sarai ta fahimci inda maganarsa ya dosa, kuma lkci daya yake magana yana cire mata hijab din jikinta, common ya taΙ“a ta idan taki ta karfi yake yi mata balle wnn, gashi gaba daya yanayinsa ya canza alamar ya fara fita hankalinsa ma, ta kamo hannunsa jikinta na rawa tace "But kwanakin da suka rage ai basu da yawa ko Ya Abdul, why not be patient pls..." Ya kalleta da idanuwansa da suka kada strictly yace "I can't wait any longer" Muryarsa kadai sai da ya tsoratata hakan yasa tayi gum da bakinta, tana jin zuciyarta kamar zai fito daga kirjinta tsabar tashin hankali, kafin ya rabata da kayanta tayi kasa da murya still holding his right hand tace "Ohk pls ka bari inyi wanka tukun, kai ma ai ka yi" Ya dinga kallonta da idonsa da suka yi ja, ta sunkuyar da kanta trying to control herself kar ta fashe da kuka tace "I won't take long" Saketa yayi ya koma gefen gado ya zauna, tana tafiya da kyar ta nufi bandaki tana kallon wayarta dake gaban dressing mirror, ta Ι—an kallesa, taga bin ta yayi da kallo, ta dake da kyar tace "Zan dau shower gel dina" Gaban mirror dinta ta nufa, dai dai sanda ya fara cire rigar jikinsa da sauri ta dau wayarta da wani Container din lotion da tayi pretending shower gel ne sannan ta shige bandaki ta kulle kofa, tap ta bude jikinta na rawa hawaye na sauka idonta ta fara dialing number Salem, yana fara ring ya daga, da kyar tace "Plss i want to speak to my Housemate plss" Salem yace "Oops wllhi bama tare yanxu" Ko rufe baki bai yi ba tace "Don girman Allah ka turo min lambarsa yanzu" Yace "Ohk let me send you" Yana katse wayar ta dinga kallon screen dinta tana jiran shigowar lambar Housemate dinta, her body was just shaking, ga wani bugawa da zuciyarta yake, cikin few seconds sai gashi ya turo mata lambar, da sauri tayi dialing ya fara ringing amma har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai daga ba, sau uku tana kiransa bai daga ba, ta saki kuka ta durkusa kasan bandakin tace "Na shiga uku" Sake dialing number Salem tayi, yana picking tace "Pls bai daga ba ko zaka..." Salem bai jira jin sauran bayaninta ba yace "Bari in tura maki number Ajay, nasan dama ba lallai Jay ya daga ba don ba ko wani kira yake dauka ba, sai kice ma Ajay ya basa suna tare yanzu" Tana gyada kai da sauri tace "Ohk to Nagode" yana katse wayar sai gashi ya turo mata number Ajay, tayi dialing number da sauri hannunta na rawa, ai kuwa yana fara ringing da few seconds aka daga, da kyar tace "Plsss ina son zan yi magana da Housemate dina ne" Shiru taji yayi as if processing the voice, sai kuma a takaice yace "Waye wannan?" Ta fara shesshekar kuka muryarta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri ka rufa min asiri ka basa ina son zan masa magana" Yace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "I need his help plss" katse wayar taji yayi, hankalinta in yayi dubu ya tashi a moment din nan, ta shiga uku ta lalace, yanzu ya zata yi, ko dai ta kira Safiyyah, number Safiyyah ta duba da sauri tayi dialing amma har ya katse bata daga ba, ji tayi kamar za a bude kofar bandakin tayi saurin tsoma wayar hannunta cikin ruwan da ta fara tarawa a bath tub  a gigice, ashe kunnenta ne ma yaji kamar an taΙ“a kofa amma ba kowa gun kofar, ta ciro wayarta taga screen din yayi baΖ™i, ta dinga yarfe ruwan da ya shiga tana kokarin kunnawa amma yaki kunnuwa, hade kanta tayi da bath tub hawaye masu zafi na sauka idonta....

 

 

*End of free pages, za mu ci gaba da update a payment group*

 

*For continuation of the  book Halysaah, pay 500 into 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah*

 

_And ur evidence of payment via 07087865788_✍🏻

 

 

 

 

*My special thanks to those that have already patronized since the beginning of this book, Thank you so much and i appreciate you*πŸ₯Ί

[5/18, 3:12 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat ta kusa minti sha biyar a bandakin cikin tashin hankali da confusion, banda kuka babu abinda take yi, she can't even think straight tsabar yanda ta shiga tashin hankali, to ko dai kawai ta fita ta gudu ta bar gidan ne, ko kuma taje ta basa hakuri ya rufa mata asiri, ta ma san bazai taΙ“a sauraronta ba, da kyar ta mike daga durkushen da take hawaye sosai na zuba idonta har sannan jikinta rawa yake, gani take kamar the world have come to an end for her, hannunta na rawa ta wanke fuskarta tayi karfin halin bude kofar bandakin a hankali tana leka Bedroom dinta, zaune ta gansa edge din gado yana danna wayarsa, suna hada ido ta bude kofar ta fito, ya dinga kallonta daga sama har kasa, hakan yasa ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa, Mikewa tsaye yayi yana mata wani kallo yace "So you just wasted my time all this while ba wankan kike ba dama?" tears was just rolling down her cheek tana girgiza masa kai muryarta na rawa tace "Don girman Allah kayi hakuri, kar kace zaka...." Dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu, tuni ta ja bakinta tayi shiru tana kallonsa a tsorace ganin yanda lkci daya yanayinsa ya canza, tana ganin ya nufota ta juya zata koma bandakin da gudu yayi saurin fixgota, ta rushe da kuka sosai tana cewa "Don girman Allah kar ka min haka ka rufa min asiri Ya Abdul" Yana mata wani kallo yace "You think i will just waste my time and money coming here at the end in kyaleki da childishness dinki in koma Nigeria? You must be joking, In kika ga na kyaleki yau sai in faduwa nayi na mutu" Zuwa sannan Khaleesat bata ma san kalmomin dake fitowa bakinta ba ta dinga basa hakuri a rikice, ta dai san ko da wasa bazata ce zata yi kokuwa da shi ba, ta ina ma zata fara, da hannu daya in ya riketa ko kwakkwaran motsi bazata iya ba balle ta kwace kanta, Knocking kofar da ta jiyo a kunnenta ne yasa ta zaro ido bakinta na rawa tace "Wallahi Housemate dita ce ta dawo kuma bata da makulli nata ya Ι“ata..." Yace "And so what? Ita zata hanani abinda nayi niyya ne?" Hawaye na sauka idonta tace "Don Allah ka bar ni in bude mata kilan mantuwa tayi, she is not spending the night here" Saketa yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "Remain here, i will open the door for her" Gyada masa kai kawai take zuciyarta na bugawa da karfi, ya dau rigarsa ya saka sannan ya nufi kofa ya fita, a hankali Khaleesat ta sulale kasa tana jin kamar numfashinta zai dauke tsabar tashin hankali, gashi sai knocking kofar parlon ake babu kakkautawa, da sauri ta mike jikinta na rawa ta bi bayansa tana shesshekar kuka at the same time tana tunanin to wa ke kwankwasa kofar Allah Ubangiji ya sa Housemate dinta ne, nan corridor ta makale don tuni har Abdul ya isa kofar parlon zai bude, ya murda makullin ya bude kofar, Khaleesat couldn't believe who she saw standing at the doorstep, ai bata san sanda ta karaso parlon da sauri ba hawaye na sauka idonta, Abdul dake kallonsa daga sama har kasa Calmy yace "How may we help you? Who are you looking for?" Maimakon wanda ke bakin kofar ya basa amsa kawai ya bi gefensa ya shigo parlon yana kallonta yace "Why did you call my line?" Da mamaki Abdul ya juya ya kalli Khaleesat da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta ta lumshe ido, bata san sanda wani relieve ya zo mata ba lokaci daya, ta sake jin muryarsa yace "Me yasa kika kirani?" Ta daga kai ta kalli Abdul ganin irin kallon da yake mata at the same time ya nufo inda take cikin zafin nama, ganin haka ta fara komawa baya cikin rawar murya tana kallon AJ tace "I need you to help me pls" Ko rufe baki bata yi ba taji Abdul ya sauke mata wani wawan mari a kuncinta, AJ could not believe what he just saw cause bude baki yayi at first, ganin ya kara sauke mata wani marin cikin few seconds AJ ya isa gaban Abdul sending him double fist a fuska, he took Abdul unaware don bai gama recover daga fist din ba ya kara masa wasu ukun a jere, kan kace me ya fara punching dinsa kamar an aikosa, Rikicewa Khaleesat tayi da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku plss stop it" Tana matsowa kusa da su zata rike AJ da ya wani hankadata sai da ta fada kan kujera, Dai dai sanda aka bude kofar parlon Jay ya shigo, buda baki yayi ya jefar da wayar hannunsa saman kujera ganin Abdul a hannun AJ kamar ya samu punching bag, AJ gave Abdul no single space to retaliate, dukansa kawai yake kamar suna gidan dambe, Jay ya nufesu da sauri yana kiran AJ, da kyar ya samu nasaran rabasu yana ma AJ tsawa yace "Are you out of your mind Junaid? Are you mad, Meye haka?" Jay bai rufe baki ba Abdul ya koma kansa da fist din da bai samu yi ma AJ ba, ai ko ya kara ja ma kansa wani dukan wajen AJ, Jay that was shock at the attack Abdul just attacked him ya bude baki yana kallonsu, kar AJ yaje ya ma Abdul illa su shiga uku ya sa Jay ya kara rike AJ, Abdul that was beaten blue black ya nufi kitchen kamar mahaukaci vowing to unalive AJ, Khaleesat tsabar shock ko motsin kirki bata yi a inda AJ ya wurgar da ita, Jay na ganin Abdul ya shiga kitchen yasan makami kawai yaje daukowa, ya kalli Khaleesat da sauri yace "Tashi ki tafi daki" Ai kamar jira take ko rufe baki Jay bai yi ba ta mike a guje tayi Corridor ta tsaya tana zare ido, Jay ya fara jan AJ su tafi daki amma AJ yaki yana cewa "Don babansa me yake takama da shi a Nigeria? Who the F is he? Kakkaryasa zanyi in karya banza wallahi, in ya cika shege mu hadu a Nigeria" Jay yaki biye AJ haka dai ya ja sa har corridor zai shigar da shi daki, sai ga Abdul da wuka ya nufo su kamar Ɗan daba, ai ko karasa shigewa dakin basu yi ba Khaleesat ta riga su, tuni Jay ya sa ma dakin Key ya zare makullin ya saka a aljihu don tsaf yasan AJ sai yace zai bude kofar ga makami hannun Abdul, Abdul ya dinga bubbuga kofar saying all sort of abusive words at the same time yana alkawarin sai ya ma AJ illa, AJ ya tafi jikin window ya tsaya yayi crossing kafa yana kallon kofar dakin, Jay dai ya zauna gefen gado looking speechless and confuse, sai kuma ya dafe kirjinsa da ya fara masa ciwo saboda fist din Abdul, ita dai Khaleesat na rakube jikin gado hawaye na sauka idonta tana kuka a hankali, banda bugawa da karfi babu abinda zuciyarta ke yi, taji muryar Abdul na cewa "Ke kuma sai na maki abinda har ki koma ga mahaliccinki baza ki mance ba, i will make sure you become useless and miserable, i promise you this, kasar nan kuma kamar kin bar sa don karatun ki ya zo karshe" Khaleesat ta kara sautin kukanta, Ajay ya daka mata tsawa yace "I will fling you out of this room in baki rufe ma mutane baki a nan ba" Jay ya wani kallesa, ita dai Khaleesat ko kallonsa bata yi ba kukanta kawai take, after a while ko ina yayi tsit a gidan ko tafiya Abdul din yayi oho, da kyar Khaleesat ta mike bayan kusan minti goma zata dau hijab dinta, Jay ya bi ta da kallo, bayan ta saka Hijab din ta juya suka hada ido, sauke idonta da ya kumbura don kuka tayi, sai kuma ta tafi ta dau karamin towel da ta gani gefen gado seeing traces of blood in Jay's lips, bandaki ta tafi ta jika towel din da ruwan dumi sannan ta dawo dakin without looking at him ta duka gabansa ta dafa gadon ta fara goge masa lip dinsa a hankali, AJ ya wani kallesu sai kuma ya tabe baki ya kauda kai yana kallon outside of the window, Jay dake kallonta yace "Thank you Halysaah" Ita dai bata ce komai ba kuma bata yarda ta hada ido da shi ba ta mike ta tafi bandaki da towel din, AJ ya juyo yace "Kai Malam bani makulli in bude kofar nan in fita" Mikewa Jay yayi ya nufi kofar ya fara budewa a hankali, AJ ya bi bayansa incase of necessity, yana bude kofar AJ ya rigasa fita at the same time being very conscious of everywhere in the house, both angle and corner, a haka ya fito parlon Jay ma that was at alert na biye da shi a baya amma fa sai da ya kulle kofar dakin da makulli sbda Khaleesat, and they realized Abdul ya fice daga gidan, AJ ya juya ya kalli Jay yace "Dau wayarka mu tafi gida" Jay yace "You think i can just go and leave her in here?" AJ ya masa wani kallo yace "How sure are you u are safe being in this apartment tonight? Mahaukaci ne fa gayen kuma zai iya dawowa at anytime, it's already dark now" Jay yace "Nasani, but bazan iya barin ta ita kadai gidan nan ba" AJ yace "Are you her family member or something?" Jay yace "Kai da ka taho nan family member dinka ce?" AJ yace "Look Jay, Billah bazan bari ka zauna a gidan nan ba, koma wani taimako zaka mata kayi mata ni babu ruwana amma baza ka zauna a gidan nan ba, i can't risk leaving you here even for 1 second" Jay that was quiet for a while yace "Toh ka tafi, zan biyoka a baya" AJ yace "Kafata kafar ka Malam, kaji nayi rantsuwa bazan bar ka gidan nan ba, dubi kullin da ya dinga maka babu abinda ka tabuka sai sake baki kayi kana kallonsa" A hankali Jay yace "So kake mu hade masa at the end mu zo mu yi abinda za ayi da an sani, ai gwara da na kyalesa kawai kai ba gashi ka basa kashi yanda ya kamata ba, beside in muka ce zamu dokesa tare hakan zai sa mu gigita yarinyar ne" AJ yace "Aa haukatar da ita za mu yi ba gigita ta ba, pls do what ever you want to do ka fito mu tafi gida, ni yunwa ma nake ji" Jay ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Wait for me outside then" Yana fadin haka ya juya ya koma dakinsa da Khaleesat take, AJ kuma ya fice daga parlon ya tsaya nan bakin kofa yana jiransa, bayan Jay ya bude dakin da makulli sai da yayi knocking sannan ya shiga ciki, tsaye ya ganta jikin bangon dakin hawaye na sauka idonta tana shessheka, ya tafi can jikin window ya tsaya yana kallonta, ita dai ta sunkuyar da kanta tana kuka a hankali, Calmly yace "Halysaah" Ta kasa daga kai ta kallesa, yace "Tell me how did you get to know this guy? A ina ku ka hadu? For how long ku ke tare da shi, kuma who is he? Iyayenki sun san da alakar ku?" Sai a sannan ta daga kai wasu hawayen na sauka idonta tana kallonsa, ya sauke ajiyar zuciya yana shafa kansa yace "Where are ur reading material? Suna dakin ki ne?" Kai ta gyada masa kawai, yace "Mu je ki dauka" A tare suka tafi dakinta, bayan yaga inda reading materials din nata suke ya karasa ya dauka har da laptop dinta, ya kalleta yace "Ina wayarki fa?" A hankali tace "Ya fada ruwa" Shiru yayi sai kuma yace "To mu je" Ta Ι—an yi jim tana kallonsa, yace "Mu je mana" ba musu ta nufi kofa ya bi bayanta bayan sun fita ya kullo kofar, ita dai duk a tsorace take sai zare ido take tana ganin kamar Abdul zai sake dawowa gidan at anytime, ganin a tsorace take Jay ya shiga gaba yace "Follow me" Bin bayansa ta dinga yi hawaye na sauka idonta har suka fita daga parlon, har sannan Ajay na tsaye waje, ya juya ya kallesu, Jay ya nufi motarsa ganin Khaleesat ta tsaya yace "Mu je mana Halysaah" tana tafiya a hankali ta ci gaba da bin sa, back seat ya bude ya ajiye laptop dinta da sauran reading material dinta ya kulle sannan ya bude mata front seat, ta sauke idonta ta shiga motar ya kulle, yana kallon direction din AJ yaga har ya nufi gun motarsa ya shiga, zagawa yayi ya shiga driver seat ya tada motar, tuni AJ yayi zoom off, Jay ya bi bayansa. A hankali Khaleesat ta sauko daga motar tana kallon Jay da shi ma ya sauka ya bude back seat ya dauko laptop dinta da takardu ya kulle motar yace "Mu je" Sauke idonta tayi ta fara bin sa a baya walking slowly har suka shiga parlon gidan, ya nuna mata kujera yana kallonta, ta sunkuyar da kai sannan ta zauna, ya ajiye laptop da takardunta dake hannunsa sannan ya wuce sama, ta bi sa da kallo hawaye na taruwa idonta, sai kuma ta fara kuka a hankali tana jin kanta na sara mata, Jay ya tafi dakin AJ yana bude kofar dakin yaji yana wanka a bandaki, hakan yasa ya tsaya bakin kofar dakin don baya son issue, yana ta tsaye da tunani iri iri a ransa har AJ ya fito bandakin, AJ na ganinsa ya dakata da goge gashin kansa da karamin towel yace "Me kake nema a nan kuma?" Jay yace "Ban sani ba" Sai kuma ya karasa cikin dakin that was extra clean, kan kujera ya zauna without looking at AJ yace "We need to talk AJ" Ajay yace "Shi ne sai ka shigo min daki?" Jay yace "Zauna mu yi magana" Ɗan tsaki AJ ya ja yana ci gaba da goge gashinsa yace "Ina jin ka ba sai na zauna ba" Jay yace "I think my Housemate will stay here for a day or 2, before she sort her self out" AJ yace "As per you are her family member or who? Bata da iyaye ne? Ko nan din hotel ne?" Jay yace "Ban sani ba" AJ yace "No i am just asking a harmless question, like naga dai ba daga sama ta fado ba, kuma ba kai ka kawota America ba balle kace zaka samar mata solution, who are you to her? Yayanta ko Ubanta? Wanda muka mata ma Allah ya bamu lada, come off it Jawwad" Jay yace "Ai ba permission din ka na shigo nema ba Junaid, kawai sanar maka nake yarinyar nan zata yi kwana daya zuwa biyu a gidan nan kafin komai yayi settle" AJ yace "Toh ni na haifeka da zaka shigo ka gaya min zaka kawo yarinya tayi kwana biyu gidan nan? Ai sai dai ka kira su Abba ka gaya masu, beside the house is very big with multiple rooms to accommodate her, so ni ina ruwana, i just pray u don't have to explain ur self one day" Jay ya mike ya fice daga dakin banging the door behind him, AJ ya tabe baki yana feshe jikinsa da turaren jiki. Bangaren masu aikin gidan Jay ya nufa bayan ya sauko downstairs, ya basu umarnin da zai basu sannan ya dawo babban parlon gidan, Khaleesat dai na zaune ta jinginar da kanta jikin kujera tayi nisa tunanin da ta fada, ganin komai take kamar a mafarki, sai in taji tana da ta sanin abinda ya faru amma da ta tuna raping dinta Abdul yayi niyyar yi da Ajay bai zo ba sai taji ta nemi da ta sanin ta rasa, amma fa bata da nutsuwa bata da kwanciyar hankali, she was just restless and sick, bata san kuma me zai faru next ba a rayuwarta, muryar Jay ne ya dawo da ita daga tunanin da take ta gyara zama tana kallonsa a sanyaye, ya zauna kujeran dake kallon wanda take zaune yace "Bana son ki sa ma kanki damuwa Halysaah, ki kwantar da hankalinki pls kin ga kina da jarabawa a gabanki" Khaleesat ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara sauka idonta, Yace "Kin yi sallah?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk za a kawo maki abinci sai ki ci kafin mu yi magana" Ta girgiza masa kai tace "Bana jin yunwa" Yace "No, sai kin ci abinci ko ba yawa" Dai dai nan kukun gidan wanda bature ne ya taho da abinci zai kai dinning Area, Jay ya masa umarnin ya kawo parlon sanin abincin AJ na kan dinning din, dawowa kukun yayi Jay ya nuna masa inda zai ajiye abincin, nan ya jerasu a kasan lallausan Centre carpet, ya koma ya dauko sauran, bayan ya ajiye komai ya tafi Jay ya mike yana kallonta yace "Ki sauko ki ci abinci, let me pray" Ta gyada masa kai kawai, ya wuce sama sannan ta sauko kasa a hankali tana duba abincin da aka kawo mata taga duk abincin jajaye ne gashi abincinsu da yawa ita ba iya ci tayi ba duk shekarun da tayi a kasar su. Almost 30 mins after Khaleesat dake ta zaune tana tunane tunane ko abincin ta kasa ci ta daga kai taga Ajay ne ya shigo parlon, sunkuyar da kanta tayi, bai kalli inda take ba yayi wucewarsa dinning Area ya fara cin abincinsa, after a while Khaleesat ta daga kai a hankali jin footstep, taga Housemate dinta ne ke saukowa downstairs, ya karaso har inda take ya zauna kan kujera yace "Kin ci abincin?" Ta gyada masa kai, cook din gidan ya kira ya dauke sauran abincin ya tafi da su, Jay yace "To ki koma kan kujera" Ita dai Khaleesat kanta na kasa bata ce komai ba, har sai da Jay ya sake mata magana sannan ta mike ta koma kan kujeran ta zauna, AJ ya dawo cikin parlon ya tafi reading nook dake parlon, Jay ya bi sa da wani kallo har ya gama kakkabe kakkabensa ya zauna, ko uban me zai yi a can don yasan dai baya ma zuwa nan balle yayi karatun a nan, muryar Jay ya dawo da hankalin Khaleesat jikinta, taji yace "So Halysaah i want to even know what happen first of all at ur apartment today, don ni ban san me ya faru ba, Salem called me yace kin kirani ban daga ba and you sound disturb, and he gave you AJ's number, i rang you back quickly sai kiran bai shiga ba, shine nayi deciding in je can gidan kawai, menene ya faru?" Khaleesat ta sunkuyar da kai don bata ma san me zata ce masa ba, ta yaya ma zata fara cewa raping dinta Abdul ya so yi, muryar AJ suka ji a parlon yace "Allah ma yasa ba rashin kunyan da ta saba yi ma mutane taje tayi masa ba, kawai ta sa na doki bawan Allah a banza" Khaleesat dai bata dago kanta ba, shi dai Jay yayi murmushin da bai yi niyya ba yana kallon direction din da AJ yake, A hankali Jay yace "You are not saying anything Khaleesat" Hawaye ne ya cika idonta, ganin haka Jay yace "Or you don't want to talk about it?" Ta girgiza masa kai hawaye na sauka idonta da kyar tace "Ba haka bane, he tried molesting me" AJ that heard what she said duk da ba kallon direction dinta yake ba yace "He tried molesting you, amma da hannunki ai kika bude masa kofar ba ta window ya shigo ba" Jay ya wani kallesa yace "Stop this please AJ, why are you so wicked and heartless" AJ yayi wata dariyar bosawa, Jay ya dinga hararansa, ita dai Khaleesat hawaye ne kawai ke zuba idonta, tsabar ciwon da kanta ke mata har wani dishi dishi take gani, Cikin kwantar da murya Jay dake kallonta yace "Tell me who he is, and where did you know him from" Ta gyada masa kai tana share hawayen da yaki tsaya mata a hankali tace "Shekara hudu kenan na san shi....."

 

 

 

 

*Don't even know where to start from, the patronage was massiveπŸ₯Ί, thank you soo much for encouraging me fans, Allah ya biya maku bukatunku na alkhairi, Allah ya raya zuri'a, i soo much appreciate ur patronage, marasu auren cikin ku Allah ya baku mazaje na gari, masu aure kuma Allah ya ci gaba da baku zaman lafiya a gidajenku, Allah ya karo maku budi ninkin ba ninki, ya raba ku da iyayenku lafiya* πŸ₯Ί

 

 

_Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta i owe you 500_

 

[5/19, 5:53 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat ta sunkuyar da kanta har sannan bata daina goge hawayen da ya ki tsaya mata ba, she look pained and traumatized, Shi dai Jay kallonta kawai yake waiting for her to continue with what she is saying, jin tayi shiru yace "Halysaah" Ta daga idanuwanta ta kallesa, Calmly yace "I am listening" muryarta na rawa tace "Kawai dai shi ne ke sponsoring dina" Ba Jay da ya kafeta da ido ba yana mata kallon mamaki, har AJ sai da ya juya ya kalleta daga inda yake zaune jin abinda tace, Jay was just speechlessly staring at her, can dai ya gyara zama yace "You mean shi yake sponsoring dinki a kasar nan? Are you related in anyway with him?" Ta girgiza masa kai kawai, da mamaki kawai yake kallonta, after few seconds yace "And ur parent allowed him to sponsor you har zuwa nan America?" Ta gyada masa kai without looking at him, mikewa AJ yayi, yayi wucewarsa sama, Jay ya bi sa da kallo don shi ma ya rasa abun cewa don mamaki, Jay ya maida dubansa kan Khaleesat a hankali yace "Ya kai kudin aurenki ne an sa maku rana?" Ta daga idanuwanta ta kallesa cikin sanyin murya tace "Nima ban sani ba, amma kamar ya kai" Jay yayi shiru for almost 3 minutes with different thoughts running his mind, everything just took him unaware, bai taΙ“a tunanin saurayin nata ne sponsor dinta all this while ba, can ya daga kai ya kalleta yaga ta jinginar da kanta jikin kujera looking so tired and pale, yana son sanin me ya hadata da Abdul, meye ma dalilin haduwarsu, sannan a ina ma suka hadu da shi din, what is this great thing that motivated her parent har suka amince ma stranger da basu hada komai da shi ba ya turo er su har wata kasa karatu, he just don't want to believe it's because of money they did this.... amma ganin yanayinta yasa yayi keeping all the questions to himself for now don baya son ya kara stressing dinta, she is already stressed, mikewa yayi calmly yace "I will be back now" Ita dai ta bi sa da kallo har ya haura sama, wasu hawaye taji na taruwa idonta, kawai so take tayi kuka me sauti ko zata ji saukin abinda take ji a ranta, ta hade kanta da kujera tana shessheka a hankali, Jay na haurawa sama ya tafi dakin da ya sa daya daga worker din gidan ya kara gyarawa, the room was big sai dai bai kai nasa da na AJ ba, kuma babu abinda babu a dakin sai Duvet na saman bed spread, ya bude press din dakin yaga babu a nan ma, juyawa yayi ya fita ya dau hanyar dakin AJ, yana isa ya danna code din bude kofar dakin ya murda yaga bai buduwa, yasan canzawa yayi kenan saboda ya shigo masa dakin daxu, knocking din kofar yayi, after a while AJ ya bude kofar yana kallonsa alamar what happen, Jay ya turasa gefe ya shiga cikin dakin, AJ ya bi sa da kallo yace "Ka dai san bana son haka Jawwad, what are you looking for?" Jay ya kunna wutan dakin that is more brighter yace "Duvet zaka bani, i don't understand dalilin da yasa zaka kwashe kaf duvet din sauran rooms din all to ur self, this is greed" AJ dai kallonsa kawai yake cause he is already angry shigo masa da Jay yayi daki, ganin Jay ya nufi inda duvet dinsa suke yace "Jay me zaka yi da duvet bayan kana da naka a daki?" A takaice Jay yace "I am giving my visitor" AJ ya bude baki yana kallonsa yace "What??? I don't understand, Duvet dina zaka dauka ka kai ma visitor dinka? are you even okay? Can you hear ur self pls?" Jay bai tanka sa ba ya dau na saman gadonsa kawai ya nufi kofa, AJ ya tare kofar on a serious note yace "In ka fita da duvet din nan ka canza min suna yau" Jay ya wani turasa daga bakin kofar har sai da ya kusa faduwa sannan ya fice daga dakin, sai bayan da ya fita ya juya ya kalli AJ da ya bude baki yana kallonsa with shock, Jay yace "Emmanuel" daga haka yayi wucewarsa ya bar AJ da bin sa da kallo, Jay na komawa ya ajiye duvet din kan gadon dakin da aka gyara ma Khaleesat sannan ya sauka downstairs, tana nan zaune yanda ya bar ta idonta a lumshe amma ba bacci take ba, yace "Halysaah" Bude ido tayi da sauri bayan ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, yace "Tashi mu je sama, u need rest" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, ya dau laptop dinta da takardunta yace "Mu je" Sai bayan da ya fara tafiya sannan ta mike a hankali ta bi bayansa, har wani jiri take ji amma a haka ta daure ta bi sa har zuwa sama, ya bude kofar dakin ya shiga tana biye da shi, bayan ya ajiye laptop din hannunsa ya kunna mata na'uran da zai dumama dakin, ya nuna mata hanyar bandaki ita dai kai kawai ta gyada masa, ya ciro wayarsa a aljihu yayi dialing number sannan ya mika mata yace "In case u need anything sai ki kira number da nayi dialing it's my other line" Nan ma dai kai kawai ta iya gyada masa, yace "Good night Halysaah, pls kiyi bacci sosai, do not bother ur self kin ji?" a hankali tace "Toh" kofa ya nufa ta bi sa da kallo sai da ya bude kofar a hankali tace "Nagode" Ya juya ya sakar mata murmushi yace "I gat ur back" Daga haka ya fita ya kullo mata kofar dakin, Khaleesat ta ajiye wayar tasa da ya bata sannan ta zauna gefen gadon dakin a hankali staring at the window absently. Har karfe dayan dare Khaleesat bata ji ko digon bacci ya zo mata ba, tana dai kwance tayi lamo cikin duvet, her heart is soo heavy, har wani zafi take jin yake mata, ga wani zazzabin da taji ya lullubeta, tun da Jay ya bar ta take kuka, gani take kamar duniyar ya tsaya mata ne cak, ta ma rasa wani kalan tunani zata yi, abubuwan da suka faru daxu suka dinga dawo mata abun sai yake mata kamar mafarki, she wish mafarkin ne ma kawai, yanzu babban tashin hankalinta bata san me zai faru a Nigeria ba, bata san next step din Abdul ba, bata san me zai ma iyayenta ba, duk wannan tunanin ya hadu yayi distabilizing dinta, zazzabin da take ji ya karu sosai, tana son tashi taje tayi alwala tayi sallah ko zata samu sukuni amma ta kasa, duk jikinta ciwo yake mata ga ciwon kai kamar kanta zai fashe, da taji azaban yayi mata yawa kamar zata kira Housemate dinta ta tambayesa maganin ciwon kai amma ta fasa don bata san ko bacci yake ba, haka tayi ta juye juye jikinta yayi zafi sosai, yanda taga rana haka taga daren nan that was soo long to her, bacci ko na barawo bai dauketa ba, jin vibration din da wayarsa yayi yasa tayi karfin halin jawowa tana kallon screen taga alarm ne na karfe biyar, ta kashe alarm din tana son tashi don tayi sallah amma ta kasa, daga karshe dai haka tayi karfin hali ta daure ta tafi bandaki ta dauro alwalan, tana idar da sallan taji zazzabin da yafi na baya ya lullubeta gaba daya, kwanciya tayi saman gado ta rufe har kanta da duvet din. Wajen karfe takwas na safe Jay yayi knocking kofar dakinta, tana ji amma ta kasa amsawa, sau uku yana knocking jin bata amsa ba sai ya kira wayarsa dake wajenta nan ma tana kallon kiran amma ta kasa daga hannu ma ta dau wayar, sai da ya katse sannan ya bude kofar dakin da sallama ya shiga, yana kallonta da mamaki ya nufeta yace "Are you Okay Halysaah?" Kai kawai ta girgiza masa, ya duka kusa da ita yace "Baki da lafiya ne? Why didn't you call my line?" Hawaye ya gani idonta, yace "Haba Halysaah, ba nace kar ki sa ma kanki damuwa ba? Did you want to hurt ur self?" Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya fita daga dakin, after some minutes ya dawo da Hot chocolate ya ajiye mata yace "Ki daure ki sha pls, let me get you medicine" Yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo ya ga bata tashi ba still, duk yanda yayi da ita ta tashi ta sha shayin ya bata magani taki tashi, gaba daya ya ma rasa yanda zai yi da ita, can ya kara dukawa kusa da ita yace "Did you have ur frnd safiyyah's number offhand?" Da kyar ta girgiza masa kai, yace "U have her IG handle? Is she active on IG?" Bata ce masa komai ba don ta ma kasa maganan, he look confuse at this point, can dai yace "To zaki iya daurewa ki tashi mu tafi asibiti?" Ta girgiza masa kai, mikewa yayi kawai ya fita daga dakin, downstairs ya sauka don AJ na dinning yana breakfast ga Legend dinsa zaune Ι—an nesa da shi a dinning area din, Jay ya nufesa looking confuse yace "AJ, the girl is seriously sick fa" AJ dake sipping tea dinsa yace "Which girl?" Jay ya masa wani kallo yace "Please be serious AJ, wallahi bata da lafiya sosai" AJ yace "To yanzu daukar ta zaka yi ka kai ta Hospital kenan..." Jay yace "How?? ko tashi fa bata iya yi, plss ko zaka mata allura ta Ι—an samu relieve tukun?" A hankali AJ ya ajiye Mug din hannunsa yana kallon Jay baya ko kiftawa, can ya matsar da shayin gabansa yace "Amma dai don Allah me yasa ka raina ni haka ne Jay? Me nayi maka? Kai me hannunka yake da bazaka mata allura ba sai ni?" On a serious note Ajay ke masa tambayoyin nan looking at him and waiting for his answer, Jay yace "Da gaske fa you are Heartless Junaid, ince maka yarinya ko tashi bata iya yi? Why are you like this pls?" AJ yace "But like seriously kai uban me hannunka yake da bazaka mata allura ba sai ni? Baka fi ni zama likita ba? Wato ni ne Ι—an iska ko?" Juyawa Jay yayi ya bar wajen ya koma sama, yana bude kofar dakin ya ganta duke kusa da kofar bandaki, ya karasa kusa da ita da sauri ganin yanda ta galabaita yace "Did you throw up?" Kai kawai ta gyada masa tana maida numfashi, gun da ya ajiye hot chocolate din ya tafi ya dauko mata yace "Pls ki sha ko kadan ne sai in baki magani" Ta girgiza masa kai, yace "C'mon Halysaah, kadan fa za ki sha" Yana rike da cup din don kar ya sakar mata ta zubar, a haka ta kurbi shayin kadan, sai da yasa ta kara sha sannan ya ajiye shayin ya dauko magani, tana ganin maganin ta fara girgiza masa kai da sauri don har taji wani aman zai taho mata, bude kofar dakin aka yi Jay ya juya, AJ ya gani tsaye bakin kofar yana kallonsu, Jay bai sake kallon inda yake ba ya maida dubansa kan Khaleesat yace "Pls ki daure ki sha Halysaah, ko baki son ki samu relieve?" Kara girgiza masa kai tayi hawaye ya fara sauka idonta, lallabata Jay ya fara yi akan ta sha maganin, AJ ya wani hade rai yace "Kee baza ki amshi maganin da ake baki ba? Wa zaki ba wahala?" Jay yace "Ba ruwanka pls AJ, get out" Ita dai Khaleesat ko kallonsa bata yi ba tana fama da kanta, Jay bai sake takurata kan ta sha maganin ba ya mike yace "Toh ki daure ki hau kan gado ki kwanta, i am coming now" Ta gyada masa kai, ya juya ya nufi kofa, ko kallon Ajay bai yi ba ya fita daga dakin, AJ ya tabe baki ya juya ya koma downstairs. Haka nan Jay ya hado alluran da za mata don saukar mata da zazzabin, sai da ta ga ya dawo dakin sannan ta daure ta koma saman gadon tana ganin jiri ta kwanta, ya tsaya gefen gadon yana rike da alluran yana kallonta, ta marairaice ta girgiza masa kai kawai alamar bata so, ya kwantar da murya yace "To ya kike son in maki Halysaah? Kin ki shan magani" wayarsa dake aljihunsa ya ciro jin yana ringing ganin Salem ke kiransa ya ajiye alluran hannunsa yace "I am coming Halysaah" Fita yayi daga dakin, ya sauka downstairs ya tarar da Salem zaune parlor, bayan sun gaisa Salem yace "Slide dina nake son zaka duba min Jay" Shi dai AJ na zaune yana kallon kwallo ga Legend a gefensa, Jay yace "Ohk, but tunda ka zo pls zaka yi injecting Housemate dita she is sick" Salem yace "Ayya, shi sa ta kira jiya, Allah ya bata lafiya, tana can gidan nata ne?" Jay yace "No, she is upstairs, mu je in nuna maka dakin da take" A tare suka wuce sama, AJ dai kallonsa kawai yake a TV kamar bai san suna parlon ba, Jay bai shiga dakin ba bayan ya nuna ma Salem ya dawo downstairs ya zauna, Khaleesat bata yi ma Salem wani musu ba don ba ma ta da wannan strength din duk da yanda bata son allura haka nan ta bari ya mata, tsabar zazzabin dake jikinta ko zafin shigar alluran bata wani ji ba, Salem yayi mata Allah ya sauwake sannan ya fita daga dakin ya koma downstairs, Jay yace "Thank you, bari in duba maka" Sai bayan kusan minti talatin Jay ya tafi dakin Khaleesat ya sameta tayi bacci, ya sauke ajiyar zuciya ya karasa kusa da gadon ya kai hannu kusa da goshinta sai dai bai taΙ“a ta ba, nan yaji temperature dinta ya fara sauka, juyawa yayi ya dau sauran shayin da ta bari ya fita daga dakin..... Wajen karfe sha daya da rabi Khaleesat na kwance hannunta rike da wayar Housemate dinta, tun 20 min ago ta tashi daga baccin da ya dauketa daxu, she felt a bit relieved now da alluran da Salem yayi mata, sai dai har sannan kanta bai daina mata ciwo ba kamar ta cire ta huta, tayi kokarin ta tashi ma ta tafi bandaki amma ta kasa, she is so weak kamar warce ta dade tana ciwo, hakan yasa kawai ta jawo wayar Jay, da har zata shiga gallery dinsa to while away time amma sai taga it's not proper ta shiga hotunansa, hakan yasa ta shiga wani game da ta gani kawai tana yi daga kwancen da take, bude kofar dakin aka yi ta daga idonta, Jay ne ya shigo dakin AJ dake bayansa yaki karasowa ciki ya tsaya daga bakin kofar, Jay ya nufota yace "Ashe kin tashi, how are you feeling now Halysaah?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Good morning" Yace "Morning Housemate, are you feeling much better now?" Kai kawai ta gyada masa, yace "Ohk bari a kawo maki breakfast, idan kinyi sai ki daure ki sha magani kin ji" Ita dai bata ce masa komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita ya mika ma AJ wayarsa sannan ya sauka downstairs zai kawo mata breakfast, shi dai AJ daga sama har kasa yake kallonta, ta Ι—an saci kallonsa to see if he is still standing by the door ko ya tafi, hada ido suka yi ta dauke idonta tana ci gaba da game dinta da take, after a while ta kara satan kallon bakin kofar taga ya bar wajen, sai ga Jay ya shigo ya ajiye mata tray din breakfast ta dinga kallon plate din baked beans irin na turawa a gefe da soyayyen kwai a gefe, with veggies, sai sausages, ga cup din hot chocolate with few slices of bread a gefe su ma, ita dai tasan ba iya cin wannan abincin zata yi ba, yana kallonta yace "Can you give me ur frnd Safiyyah's Home address?" Ta sauke idonta ta gaya masa address din, yace "Ohk, na ma san area din, i have a frnd there" Ita dai tayi shiru, ya dauko mata maganin da taki sha daxu ya ajiye kusa da ita yace "Pls ki daure kiyi breakfast din, sai ki sha drug din kafin in dawo" A hankali tace "Toh nagode" ya mata murmushi ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Jay ya tarar da AJ zaune a waje gurin shan iska dake compound din yanna danna wayarsa, hakan yasa ya nufesa ya zauna kujeran dake facing dinsa yace "AJ, i think i am confuse at this point, what do u suggest about this young girl's issue?" AJ ya daga ido ya kalli Jay yace "My suggestion is that... ka barta ta tafi duk inda ma zata ka cire hannunka da bakinka cikin wannan case din babu abinda ya shafe ka, a cikin kunnenka kaji tace shi gayen ne ke sponsoring dinta, babu kuma ta yanda zai yi sponsoring dinta without the consent of her parent, kaga they are comfortable with that, so who are you to intrude Jawwad? Baka san komai akan ta ko kan saurayin ba don me zaka zakalkale haka? Tare fa ka gansu, da can baya zuwa America din ya sameta ne a gidan? sai yanzu tasan yana molesting dinta? Girl's can be very cunning fiye da tunaninka, don't start what u can't finish Jawwad" Jay dake ta kallonsa yace "So now what are you insinuating?" AJ yace "Since you are daft kar Allah ya sa ka gane abinda nake insinuating"  Jay dai kallonsa kawai yake, after a while a hankali yace "But duba da abinda ya faru tsakaninka da guy din kasan zai iya hurting dinta idan nace ta koma gidan nan AJ, she is no longer safe in that apartment, ka dai ga ba ma cikakken hankali ke gare gayen ba, ka duba fa wuka yaje ya dauko a kitchen" AJ ya gyara zama yace "Sai kayi mata hanyar komawa gun iyayenta as the good Samaritan that you are from Samaria, kaga in ta koma sai ta gaya ma iyayen nata abinda ke faruwa da abinda selfishness dinsu ya ja mata a kasar mutane, sai su yi sorting kansu a can kawai" Jay yace "Kar kace haka, we know nothing about why they allowed him to sponsor their daughter, we shouldn't judge them har sai mun san dalilinsu AJ" AJ yace "Dalilin banza, babu responsible parent din da za su damka ma kato irin wannan mutumin er su ya kai ta wata kasa da sunan karatu, it doesn't even make sense, sai kace ba musulmai ba, ko da cousin brother dinta ne ma abun bai yi tsari ba balle babu ko wani relationship na jini tsakaninsu, who does that" Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk da haka dai ni bazan yi judging dinsu ba tare da nasan komai ba, let give them benefit of doubt" AJ yace "Sai kayi ta basu ai, ni kam bazan bayar ba" Jay yace "But komawarta Nigeria yanzu bazai yiwu ba AJ, ba shine solution ba, Monday za su fara exams, John Hopkins university take ita ma fa" AJ yayi dariya har da kyakyatawa yace "Tabb, lallai gayen ya kashe kudi ba na wasa ba" Jay dai kallonsa kawai yake, AJ yace "Toh za a fara exams me kake nufi kenan? Naji ka ce apartment din nata is not safe for her anymore..." Jay yace "She will remain here har su gama exam kafin ta koma Nigeria wajen iyayenta" AJ ya wani kallesa da sauri yace "What do you mean? Kana nufin mu zauna gida daya da balagaggiyar yarinya da ba muharramar mu ba kamar wasu jahilai marasu tsoron Allah? Kai da wa za ku yi wannan nonsense din??" Jay yace "Duk yan iskan turawan da kake kawowa gidan nan ka basu daki su zauna dama muharramanka ne ban sani ba?" AJ yace "Turawa kace ai, kuma babu komai tsakanina da su kai ma ka sani, i am only helping most of them tunda ba a garin nan suke ba" Jay ya mike yace "Ita ma haka za mu yi helping dinta tunda ba a garin take ba, take it or leave it" yana kai wa nan yayi wucewarsa inda yayi parking motarsa, Ajay ya bi sa da wani kallo, can yace "Sai dai ku je can ku biya wani apartment din ku zauna tare, babu wanda zai takurani a gidan nan wallahi, dama ai kun saba zama gida daya tare, it's not a new thing, dole ne sae ta zauna gidan nan cikinmu mu ba maguzawa ba" Shi dai Jay ya shiga motarsa ya fita daga compound din ya kama hanyar gidansu Safiyyah....

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

[5/20, 5:24 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Jay na isa unguwan da gidansu Safiyyah yake sai ya mance apartment din da Khaleesat ta gaya masa, hakan yasa ya kira wayarsa dake wajenta, Khaleesat na zaune saman gado har sannan tana playing game da wayar, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallon screen din wayar ganin image din hotonsa da number da yayi appearing, sai taga kamar shi din ne a gabanta take gani, sai da kiran ya katse ta zaro ido bayan tayi realizing bata yi picking ba har ya katse, bayan few seconds ya sake kira, dagawa tayi ta sa handsfree tayi shiru, yace "Halysaah" Tace "Na'am" Yace "I think i forgot the apartment u told me" Gaya masa ta sake yi yace "Thank you" Daga haka ya katse wayar ya ci gaba da driving dinsa, dai dai gaban apartment din yayi parking don motar Mustapha baya nan, yana tsaye bakin kofa yayi knocking gently, after a minute aka bude kofar parlon, komawa baya Safiyyah tayi tana kallonsa da mamaki daga sama har kasa, ya Ι—an mata murmushi yace "Hi Safiyyah" Ta bude ido sosai tana leka motarsa da taga yayi parking thinking may be he is together with Khaleesat, ganin motar ba kowa ciki tace "Hi, good afternoon" Yace "How are you doing Safiyyah?" Lokaci daya tace "Ko dai Khaleesat bata da lafiya ne?" Da damuwa sosai tayi tambayar, Yace "Yeah bata da lafiya" Tace "Wallahi yanzu na gama shiryawa nake son in ci abinci inje gidan naga miss call dinta jiya ina ta kira har yau wayar baya shiga, and i am disturb" Yace "Shi yasa na zo in dauke ki idan ba damuwa so you can be together with her she is sick, probably idan kin mata magana zata ci abinci ta sha magani" Da sauri Safiyyah tace "Sure, bari in dauko gyalena" Juyawa tayi da sauri ta koma cikin gidan, shi kuma ya koma parking space, Surayya dake zaune a parlon ta kasa kunne duk tana jin conversation dinsu kafin Safiyyah ta shigo, Safiyyah ko kallon direction dinta bata yi ba ta tafi dakinta da sauri ta dauko jakarta da gyale sai wayarta sannan ta fice daga gidan, ganin Jay cikin motarsa yana jiranta ta bude gaban motar ta shiga tana cewa "Tun jiya ne bata da lafiyan? Kuma me yasa ta kashe wayarta?" Jay yace "Tace wayar ya fada ruwa ne" Safiyyah tace "Ohk" Sai da suka dau hanya sannan Jay yace "Amma tana can gidanmu fa, can za mu je yanzu" Safiyyah ta juya da sauri tana kallonsa da mamaki tace "Gidanku? Why? What happened?" Calmly yace "Before then za mu fara zuwa apartment dinmu sai ki dau mata kayanta da zata yi amfani da shi, we left yesterday with nothing" Safiyyah bata sake cewa komai ba tunani iri iri na yawo a ranta, to me ya faru? ta yaya Khaleesat da ta sani me shegen taurin kai ta yarda har ta bi sa can gidan nasu? Ko dai rashin lafiyar nata is critical ne haka? Da tunane tunanen nan suka isa apartment din, suka shiga ciki tare da Jay ta nufi dakin Khaleesat shi kuma ya zauna a parlor, bayan few minutes ta fito tace "Kala daya zan dau mata kayan ai ko?" Jay ya mike yace "No, 3 to 4 will be okay" Duk da confusion din da Safiyyah ta shiga bata dai ce masa komai ba ta juya ta koma cikin dakin, ta dau akwati ta saka ma Khaleesat kayanta da duk abinda zata bukata a ciki, tana fitowa daga dakin Jay ya mike yace "Kin dau mata duk abinda zata bukata?" Safiyyah ta gyada masa kai, suka fita daga parlon, duk ta kagu taje wajen Khaleesat ita dae, silently suka yi tafiyar har suka iso gidan, bayan Jay yayi parking ya sauka Safiyyah ma ta sauka, ya fiddo akwatin sannan suka nufi entrance din apartment din Safiyyah na biye da shi, bai ga motar AJ a gidan ba alamar ya fita, suna haurawa sama Jay ya tafi dakin da Khaleesat take yayi knocking, ya mika ma Safiyyah akwatin yace "Zaki iya shiga, zan je inyi sallah" Safiyyah ta amshi box din tace "Ohk" Bude kofar dakin tayi Khaleesat ta dinga kallonta har ta shigo, Safiyyah ta ajiye box din hannunta ta nufeta da sauri tace "Me ya sameki Khaleesat?" A hankali Khaleesat ta sauke idonta ta kasa cewa komai don bata ma san ta inda zata fara ba, sai ga hawaye. Safiyyah na tsaye dakin kusa da window bayan Khaleesat ta bata labarin duk abinda ya faru, tsabar yanda labarin ya kidima Safiyyah kasa ci gaba da zama tayi gefen gadon, Safiyyah tayi shiru for almost 2 minute tana tsaye jikin window tana girgiza kafa, ita dai Khaleesat goge hawayen dake sauka idonta kawai take, can Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya me cike da takaici tace "A baya da nake gaya maki Abdul Ι—an daba ne ba kin maida maganata abun wasa ba? Tunda uwata ta haifeni ban taΙ“a ganin Ι—an iska kamar Abdul ba, yanzu da baki samu lambar kowa ba haka zai lalata maki rayuwa babu digon tsoron Allah a ransa? Ya kashe uban kudin zuwa USA kawai don ya zo yayi lalata? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, amma naji haushi da Ι—an uwan Housemate dinki bai sumar da shi ba an maida sa Airport a haka, tirr da Abdul, tirr da halinsa, i am so happy that things turn out this way, in sha Allahu karshensa ne ya zo a rayuwarki" Khaleesat ta fashe da kuka tace "Sophie ban san next action dinsa ba idan ya koma Nigeria, i am so restless" Safiyyah tace "Next action dinsa? Sai ya koma ya gaya masu uban da ya kawosa USA da Intention dinsa, ke in zaki dena wannan crocodile tears din naki ki dena don ba tausayinki zan ji ba, tunda dai bai samu nasaran lalata maki rayuwa ba ni duk abinda zai faru ma ya dade bai faru ba, kukan uban me kuma kike ma mutane? Ko nasaran da bai samu a kanki bane ya dame ki? Kuma wallahi ya ci sa'ar baki sameni a waya ba don kafin in karaso gidan sai 911 sun riga ni, tuni zan kirasu ince gashi can za ayi fyade, banda iskanci duk karuwansa basu ishesa ba sai ya zo ya kara dake? Gaskiya ki rike Housemate dinki da Ι—an uwan nan nasa da kyau don mutane ne su wallahi, da ba don su ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, don da na kai maki ruwan zafi yafi a kirga zuwa bandaki yanzu" Khaleesat dai bata sake ce mata komai ba tana share hawayen da yaki tsaya mata, Safiyyah ta rike haΙ“a har sannan tana mamakin Abdul, can tace "Kamar irin ya zo wajen matar nan tasa, ni wallahi da yaji suka barbada masa mu ga ta iskanci, shege kawai prostitute" Duk tashin hankalin da Khaleesat ke ciki sai da tayi dariya don ita bata taΙ“a jin inda aka ce ma namiji prostitute ba sai yau a bakin Sophie, Safiyyah tace "Ga dai katon daki an baki, kiyi karatun exams dinki cikin kwanciyar hankali, nima in abun duniya ya isheni in taho nan in sameki kafin dare yayi in koma den dina, don ko da wasa bazan ce ki dawo gidanmu ba ni kaina ban tsira gun tsinanniyar matar Yaya Musty ba kuma yaki kwatar min en ci, da zai bar ni ba nima sai in dawo nan kusa dake ba tunda ba rasa abincin da za su bamu mu ci za su yi ba, wannan dakin ai ya ishemu rayuwar America, bari kiji Khaleesat dama Allah ya riga ya rubuta Abdul ne silan zuwan ki Amurka ki hadu da mutanen arzikin ki, babu me canza haka ko yaki ko ya so dole sai ya kawoki ya hadaki da mutanen arzikin ki tunda Allah ya rubuta haka, iya role dinsa kenan a rayuwarki, kuma Allah ne zai basa ladan hakan bamu ba, ba shikenan ba?" Khaleesat dake ta kallonta ta girgiza mata kai tace "Ni bazan zauna gidan nan ba Sophie" Safiyyah na mata wani kallo tace "Ohk, Apartment din naki zaki koma ki kai ma Abdul din kanki kenan?" Khaleesat ta sauke idonta kasa muryarta na rawa tace "Bazan iya jarabawan ba Sophie, gwara kawai in koma gida, i want to go home, i want to go to my mother" Safiyyah zata yi magana aka yi knocking kofar dakin, Safiyyah ta amsa aka bude kofar Jay ya shigo, kallon Khaleesat yake yace "Kin sha maganin Housemate?" Ta gyada masa kai without looking at him, Safiyyah ta kallesa cike da damuwa tace "Ashe kuma iftila'in da ya faru kenan jiya Yaya Housemate? To Allah Ubangiji ya tsare na gaba, ku kuma Allah ya saka maku da alkhairi ya baku ladan hidimar da ku ke yi da kawata don bata da kowa a garin nan sai Allah sai ni da ku, kuma she is not longer safe in this state don Abdul can be cunning, azzalumi ne mugu, nasan har yanzu yana labe garin nan bai tafi ba, kuma ba imani ne da shi ba ina jin tsoron next move dinsa, Allah kadai yasan sau nawa ya koma apartment din nan yaga babu kowa ciki" Jay dai ya Ι—an yi murmushi yace "She will remain here har ta gama exams dinta in sha Allah" Khaleesat ta kallesa ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "Bazan iya exam din ba, Nigeria nake son tafiya" Safiyyah ta mata wani kallo kamar zata ce in tana da kudin jirgi ta tafi sai dai kuma kawai tayi shiru tana hararanta, Jay ya kwantar da murya yace "Saboda me baza ki iya exam ba Khaleesat, stop saying that pls, in sha Allah zaki yi jarabawan ki lafiya, in kun gama sai ki koma Nigeria" Safiyyah tace "Atoh shi dai na gani, kan wani tantirin Ι—an iska take son lalata future dinta, duka duka fa shekarar karshe za mu shiga yanzu a makarantar" Khaleesat ta sauke idonta hawaye na sauka idonta don tasan baza su gane abinda take nufi ba, Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Try calming her down Safiyyah, and naga tun jiya bata wani ci abinci ba ban san ko tafi son abincin Nigeria ne ba, nasa cook din gidan yayi ordering ingredient din har an kawo, i don't know ko zaki girka mata a kitchen tunda kina nan" Safiyyah tace "To ba damuwa, let me cook for her" Yace "Alright" a tare suka bar dakin Khaleesat ta bi su da kallo hawaye na bin fuskarta. Tunda suka shigo kitchen din Safiyyah ke bin ko ina da kallo don the kitchen is so big and well equipped, irin modernize kitchen din nan, bayan Jay ya fita cook din gidan ya nuna mata ingredients din shinkafa da miya sannan shi ma ya fita, tuni ta hau girkin a kitchen din. Wajen karfe biyar Safiyyah na daki tare da Khaleesat hira kawai take mata kamar ba abinda ya faru, ita dai Khaleesat tayi shiru tana kallonta amma gaba daya hankalinta baya kan hiran, wayar Safiyyah ya fara ring ta jawo jakarta ta ciro wayar ganin Mustapha ke kiranta ta wani turo baki sannan tayi pick ta sa handsfree tace "Ina wuni yaya" Ko amsa gaisuwar bai yi ba yace "Waye ya zo ya daukeki a mota Safiyyah?" Safiyyah ta bude baki tace "Ohh haka matar taka tace maka? to ta manta a jirgi aka zo aka daukeni ba a mota ba, kuma munafurcinta zai kare mata wallahi" Tsawa ya daka mata yace "Ina maki magana kina min maganar banza? Are you okay?" Ta wani murguda baki tace "Toh ba ina hanya bane wai, haka kawai dai babu dalili bazan kama hanya in fito cikin sanyin nan ba yaya, ko ka manta jibi za mu fara exams ne?" Kashe wayarsa yayi, Safiyyah tace "Allah dai ya tsine ma Surayya albarka, kuma wallahi kafin mu gama exam mu bar kasar nan sai na mata abinda bazata taΙ“a mantawa ba a rayuwarta, ko da wasa kuma bazan ma gaya masa abinda ya faru dake ba kar yayi burgan cewa ki dawo gidansa ya kara ma matarsa extra nama" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah ta mike ta dau jakarta da gyale tace "Sai na zo gobe in sha Allahu, saura kar ki karasa cinye abincin ki zauna kina asaran hawayenki akan Ι—an daba, ga lambata na sa maki a waya in da wani abu ko kuma kina bukatar komai kawai ki kirani" Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat ta sauke idonta kasa, Downstairs Safiyyah ta hadu da AJ wanda shigowarsa gidan kenan tana Ι—an murmushi ta gaishesa ya tsaya ya amsa yana danna wayarsa yace "How are you doing" Tace "Alhmdlh ya karatu" Yace "Fine, ya naki" Tace "Muna ta fafatawa dai, to fa mun gode da hidima yaya, Allah ya saka da alkhairi da abinda ku ka ma kawata, Allah ya biya ku" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta jin wai tana masa godiya, ita dai ta ci gaba da godiyar ta ba kakkautawa, Yace "Ameen" Tace "Yaya Housemate din ya fita ne, ni zan koma gida ne yanxu" Sai ga Jay ya shigo parlon from outside, ganinta yace "Ohk zaki koma Safiyyah?" Tace "Eh wallahi yamma tayi amma in sha Allahu zan shigo gobe da safe" Yace "To Allah ya kai mu, mu je inyi dropping dinki" Tuni AJ yayi wucewarsa sama, Safiyyah ta bi bayan Jay suka fita daga parlon tana mamakin inda karen gidan yake bata gansa ba tun daxu, sai bayan da suka dau hanya tace "Yaya Housemate...." Dariya ta ba Jay bai jira me zata ce ba yace "I am Jawwad Safiyyah" Tace "To ni dai don Allah kayi dubara ka amshe wayar da ka ba Khaleesat kar taje ta kira yan gidansu su gigita ta, kaga bamu san ko Abdul din na kasar nan ba ko ya koma Nigeria, in ta kira suka gaya mata wani maganar da kyar ta iya abun arziki a jarabawan nan" Jay yayi shiru cause he reason with what Safiyyah is saying, can yace "Haka ne kuma, i will tell her not to speak to anyone for now, amma bazan iya amsan wayar ba naga kamar it's whiling away her time" Safiyyah tace "To in da kati a wayar don Allah ka kone sa, in da WhatsApp kayi uninstalling dinsa kaga ta haka babu wanda zata ma magana, the exams is just for a few weeks, kamar gobe ne za mu gama" Yace "Sure i will do so Safiyyah" A haka suka isa gidansu ta sauka daga motar ta masa godiya yace "Ki gaida mutanen gidan" Tace "To za su ji" Yayi reverse ya dau hanyar gida hoping Khaleesat bata riga ta ma kowa magana back in Nigeria ba. Washegari da safe Jay yayi booking appointment na ganin likita saboda daren ranan ma Khaleesat dai bata yi bacci ba, yasan dai ba lallai su samu ganin likitan a ranan ba, so he was just helping her to manage her self with the drugs available, da Safiyyah kuma ta zo sai taji ta nemi zazzabin ta rasa dama kadaici ne da damuwa suka mata yawa. Ranan monday da safe Jay yayi dropping din Khaleesat school for her first exam, and he stayed behind har zuwa sanda za su gama don su koma gida tare, kawai shi dai baya son barin ta ita kadai, Jay is trying his very best na ganin Khaleesat ta sake ranta domin tayi karatun jarabawanta da kyau kar ta samu matsala, ga kuma Safiyyah dake encouraging dinta a gefe ita ma, kuma hakan yayi tasiri sosai don ta Ι—an sake ranta tana karatun, AJ dai tun ranan da ya shigo ya ganta zaune a daki har bayan da suka yi Exams uku bata sake saka shi a ido ba, bata san ko yana gidan ba ma ko baya gidan, ita dai 24/7 tana daki, hatta abinci cook din gidan ne ke kai mata sama yayi knocking ta fito ta amsa, in ta gama still shi yake zuwa ya amshi tray din, bayan sati biyu da fara exam dinsu ranan suna da interval Safiyyah ta zo gidan da yamma, abinci ta kawo ma Khaleesat, Khaleesat taji dadi sosai ganin tuwo ne don dama tun jiya take sha'awan tuwon, Safiyyah tace "Kinga ba dadewa zan yi ba yanzu zan tafi kafin mutumin can ya fara kirana kamar Surayya ce ta bar gida" A hankali Khaleesat tace "Baza ki bari anjima kadan ba pls" Safiyyah tace "Wallahi yanzu Ya Mustapha zai fara kirana, bai ma san na fito ba, kuma nayi order din Lyft ma da zai maidani gashi nan ya kusa karasowa nan, tashi ki rakani kofar gida" Khaleesat ta girgiza kai tace "Kawai ki tafi za mu hadu schl tomorrow in sha Allah" Safiyyah tace "Wai ke baki gajiya da zama ke kadai a daki, don Allah ni dai tashi ki rakani kema ki Ι—an yi strolling kafafuwanki" a hankali Khaleesat tace "Baza ki gane ba Sophie, wallahi i am not comfortable staying in this house, na kagu mu gama jarabawan nan in koma Nigeria" Safiyyah tace "Ae ranan Housemate dinki ya gaya min wai kince masa zaki koma apartment dinki nace lallai baki da hankali, Allah ma yasa Abdul bai sake gidan ba" Tana dariya ta kare maganar, sai kuma ta kwantar da murya tace "Kiyi hakuri kawata, nan da sati kadan zaki ga mun gama exams din in sha Allah, ki kwantar da hankalinki pls, yanzu dai tashi ki rakani" a hankali Khaleesat ta sauko daga kan gadon ta dau gyalenta suka fita dakin tare da Safiyyah, suna saukowa downstairs suka tarar da AJ a parlor da Jay, Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta don sai yau taga AJ for almost 2 weeks, ita ta zata ma baya gidan ne, Jay na kallon Safiyyah yace "Are you going soon Safiyyah?" Safiyyah tace "Eh wallahi Yaya Jawwad Lyft dina yana hanya ya kusa" Yace "Alright, ki gaida mutanen gidan" Tace "In sha Allah za su ji" Sallama tayi ma AJ ya amsa mata, sannan ta kama hannun Khaleesat suka fita daga parlon, suna tsaye waje suna jiran karasowar Lyft wata mota ta shiga gidan bayan matukin motar ya fito daga cikin motar ya bude gate, Safiyyah tayi kasa da murya bayan sun shiga ciki tace "Ke kinga wani Ride me suna ride Khaleesat? Su dai da masu kudi kawai suke harkar su a kasar nan, in kin bibiya abokansu ne 'ya yan masu kudi irinsu" Khaleesat dai bata ce komai ba, bayan kusan minti uku sai ga Lyft din Safiyyah ya iso, Safiyyah ta bude bayan motar ta shiga, Khaleesat ta daga mata hannu, Safiyyah na mata murmushi tace "Sai mun hadu a schl  kawata, kiyi karatu da kyau fa" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata sannan ta koma cikin gidan, duk a dar dar take tafiya a babban compound din gidan, har yau ita dai ta kasa sakin jiki a gidan nan gani take kamar a kaya ma take she is so very uncomfortable, a haka ta isa parlon gidan ganin baki biyu dake parlon tare da su Jay wanda da alama abokansu ne Khaleesat ta sauke kai ta gaishesu, suka amsa da fara'a, ita dai ta nufi stairs, daya daga frnds din nasu taji yace "Bakuwa ku ka yi a gidan" AJ dake shan fruit salad yace "Eh, yarinyar wani abokinmu ne a Nigeria ta zo jarabawa" Jay ya saki baki yana kallon AJ da ke ta shan fruit salad dinsa ko ajikinsa, Ita kanta Khaleesat sai da ta Ι—an juya ta kallesa sannan ta wuce sama, abokin na gyara zama yace "Waow, amma da gani da wuri abokin nan naku yayi aure, ya huta abunsa gashi mu duk mun kasa har yanzu" AJ dai ya ci gaba da shan fruit salad dinsa yace "Ai kam ya huta, mu ma da munyi auren da wuri duk da mun haifi kamarta ai"

 

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

[5/21, 6:02 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat na zaune da daddare tana duba course din da za su yi washegari a laptop dinta, sosai take kewan Ummanta tasan kilan tana ta mata magana ta WhatsApp taji shiru, she just pray everything is alright back home in Nigeria, duk in wannan tunanin ya fado mata sai taji ta kasa karatu, haka nan dai ta tsura ma laptop dinta ido, knocking din kofar dakin aka yi ta mike a hankali ta karasa gun kofar ta bude don tasan Jay ne, sau da yawa sai dai yayi mata knocking bai fiye shigowa dakin ba, daga nan bakin kofa yake tsayawa yayi mata duk maganar da zai mata, yana kallonta bayan ta bude kofar yace "Are you sure u are studying for ur next course Halysaah?" Ta gyada masa kai tana kallonsa, ya Ι—an jingina da bangon wajen yace "Erm, sorry about what you overheard AJ saying few hours ago Halysaah, kinga dalilin da yasa nake barin masa gidan shi kadai ya karata kenan, he is a serious nuisance... Kiyi hakuri da abinda yace kin ji Housemate?" Khaleesat ta Ι—an yi murmushi tana wasa da gefen gyalenta kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "Ai ni ban ma san tsoho bane sai yau" Jay couldn't help it but laugh out loud, Khaleesat ta daga idanuwanta tace "Allah kuwa ban san shi tsoho bane, don wanda ya isa haifata ai tsoho ne" akan kunne AJ da ya fito daga parlon dake sama, tsaye yayi yana kallonta, tana hada ido da shi ta kulle kofar dakin gbamm, AJ ya kalli Jay dake ta dariya, can ya juya fuuu ya bar wajen, Jay dai ya bi sa da kallo still laughing, har ransa yaji dadin abinda Khaleesat tace akan kunne Ajayn. Jay na dakinsa wajen karfe goma da rabi yana duba laptop dinsa AJ ya shigo dakin, sau daya ya kallesa ya ci gaba da abinda yake, AJ yace "That brat will not continue staying in this house anymore, ka samar mata wani alternative kawai in ba haka ba in kira gida in fada masu ka kawo mana yarinya tana rayuwa cikin gidan nan" Jay ya daga kai ya kallesa yace "Ni ai na zata har ka kira ka gaya masu, kuma tunda ba gidanka bane baka isa kace bazata zauna ta gama exams dinta ba" AJ yace "Ohk zaka sha mamaki" Daga haka ya fice daga dakin, Jay ya ja tsaki ya ci gaba da abinda yake. Washegari tare Jay ya dauko Khaleesat da Safiyyah ya kawo su nan gida bayan sun gama exams din ranan, bai shiga compound din ba ya tsaya a waje yace "I will be going out now, sai na dawo later" Khaleesat ta sauka daga motar tana kallonsa, a duk sanda baya gidan sai taji gidan duk babu dadi, duk da ko yana nan yawanci yana dakinsa sai in da wani abu ne yake zuwa kofar dakinta ya mata magana, but she prefer him to be at home always ko da baza su ga juna ba, duk sanda ya fita sai ta shiga kadaici wani lkcn har da damuwa, kuma in dai zai fita din sai ya gaya mata zai fita, yau kam she felt relieved tunda tare suka dawo gidan da Safiyyah, yana kallonta yace "Zan kiyi girkin yau tunda ga kawarki sai ta taya ki?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Ohk" Yace "Alright take care" ta gyada masa kai ya ja motarsa ya wuce, ita da Safiyyah suka shiga gidan, Safiyyah tace "Kai na dade banga mutumin me kirki irin bawan Allahn nan ba, he is just extra nice, ni dai Allah ya sa it's what i am thinking" Khaleesat ta kalleta, Safiyyah ta washe maki tana wani murmushi, Khaleesat taki tanka ta, Safiyyah tace "Kinga kamar jiya muka fara exams gashi saura mana course biyu mu gama, baki ga farin cikin da nake ba za mu koma gida" Suna shiga parlon gidan suka ga AJ a zaune da kare a gefensa, sosai gaban Khaleesat ya fadi don tun da ta zo gidan ita dai bata ga karen da idonta ba sai da taji haushinsa wani lkcn, karen ya mike tsaye yana kallonsu AJ ya masa umarnin ya koma ya zauna, tuni Khaleesat tayi wucewarta sama, Safiyyah ta tsaya ta gaida AJ da fara'arta, ya amsa yace "How was ur exam?" Tace "Alhamdulillah, sauran mu kwara biyu, kawai intervals din ne ke da tsayi" AJ yace "Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen" Daga haka ta wuce sama, dakin da Khaleesat take ta shiga, ta rike haΙ“a tana kallonta tace "Ni fa karfin halinki mamaki yake ban Khaleesat, ya kina gidan mutane zaki zo ki wani wucesa babu gaisuwa? Me yasa kike yin haka ne?" Khaleesat ta cire mayafinta without looking at her tace "Don baki ji abinda yayi min bane jiya, frnds dinsa suka zo gidan yace masu ai ni yarinyar abokinsa ce na zo exam" Safiyyah ta kyalkyale da dariya har da kyakyatawa tace "To meye a ciki, in bai fadi haka ba so kike su yi zaton zaman kanki kike cikin maza? Ai nan kare maki mutunci yayi, kinga dai ai abokan za su yi tunanin baban naki ne da kansa ya kawo ki gidan abokansa ki zauna kiyi exams" Khaleesat ta wani kalleta tayi shigewarta bandaki, Safiyyah ta zauna gefen gado tana kyakyala dariya tace "To duka duka shekararki nawa da bazai ce ke 'yar su bace, ni dai ban ga laifinsa ba" Bayan duk sun yi sallah Safiyyah tace "Kin ga ki tashi mu je in taya ki girkin kafin mutumin can ya fara doka min kira yanzu kamar makaho" a hankali Khaleesat tace "Ni kamar ma kar inyi girkin, i don't want to go downstairs" Safiyyah tace "Amma ai ko don saboda Housemate dinki sai kiyi, tunda kika ga haka kilan shi ma yana son cin tuwon da vegetable soup ne" Khaleesat ta marairaice tace "To ai ni i am not comfortable ne, ban ma taba shiga kitchen din ba fa" Safiyya ta mike tace "Mu je, ai ni na taΙ“a shiga har nayi girki" A haka ta ja Khaleesat suka sauka downstairs, da ba don Safiyyah tace kilan Housemate dinta na son cin abincin ba da babu abinda zai sa ma ta yarda tayi girkin, har sannan AJ na parlon amma babu karen a kusa da shi, shi dai wayarsa kawai yake dannawa bai kalli direction dinsu ba, a haka Safiyyah ta ja ta har zuwa kitchen din gidan, after a while suka gama girkin, Safiyyah tayi take away din wanda zata tafi da shi gida tana kallon Khaleesat tace "Ke ba yanzu zaki ci abincin bane naga baki zuba ba?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Sai anjima" Safiyyah ta tabe baki tace "To mu je, Allah dai ya sa Yaya Musty bai kirani ba" Suna fitowa main parlor suka tarar babu kowa a parlon, suka haura sama, kafin su karasa hanyar dakin da Khaleesat take aka bude kofar wani Bedroom din wata mace da bazata wuce 23 years ba ta fito, English dressing ne jikinta amma kana ganinta kaga Hausa Fulani, she is so beautiful, yarinyar ta bi su da kallo da mamaki, Safiyyah na murmushi tace "Hi dear" Yarinyar ta mayar mata murmushin tace "Hlo" Ita dai Khaleesat ta dauke kai tana biye da Safiyyah suka tafi dakin da take, Safiyyah ta kulle kofar ta dora hannu a ka tace "Na shiga uku, ke yanzu Khaleesat me yasa baza ki daina abu kamar warce bata waye ba? Mun ga yarinya ta fito daga daki kika san ko gidansu ne maimakon kice mata Hi kamar yanda kika ga nayi amma kika wani yi shiru kamar kurma kina bin ta da ido?" Innocently Khaleesat tace "To ai naga bamu santa bane" A fusace Safiyyah tace "Gaskiya na gaji da halin ki, ke ko ina sai kin sa an mana kallon en kauye? Ki ga yarinya er gayu wayayyiya abinda kema wayancewa zaki yi yanda nayi ki ce mata Hi, to meye amfanin ilimin in baka iya zaman duniya da kowa ba? Ko Ι—an uwan nan nasa da kike complain a kai kece baki iya siyasar zama da shi ba, ba gashi ni yana kulani ba har da tambayata ya exams, gaskiya ki canza hali Khaleesat, ya ci ace kin yi koyi da ni akan abubuwa da yawa" Khaleesat dai bata tanka ta ba, Safiyyah tace "Duk sai kika sa kunya ya kama ni tsamo tsamo, yanzu zata su kuma wa ennan en kauyen daga ina" Safiyyah ta dau jakarta tana ciro wayarta taga miss calls din Mustapha tace "Ahaf ai na sani" Tsaki ta ja ta fara kokarin order din ride din da zai maida ta gida. AJ ya bude kofar dakinsa jin ana knocking, tana kallonsa daga inda take tsaye ba tare da taje kusa kusa da kofar ba tana Ι—an kame kame tace "Ya Ajay, naga wasu mata ne a gidan, kun yi baki ne?" AJ ya gyara tsayuwarsa yace "Ohk, su nawa?" Ta Ι—an bude manyan idanuwanta tace "Su biyu" Ya gyada kai yace "Good, you saw the fair Slim one that is like yellow pawpaw?" Yarinyar tace "Sure" Yace "To sabuwar budurwar saurayinki ce, all of a sudden ya tattaro ta ya dawo da ita gidan nan suke zama tare, when i said i am reporting him back home he threatened me" The lady look totally speechless and confuse, a hankali tace "Budurwarsa kuma Ya Ajay?" Ya wani hade rai yace "Ina wasa da ke ne balle in maki karya?" Shiru tayi bata ce komai ba ta sauke idonta kasa, yace "She's been in this house for 3 weeks now, ya kai ta school ya dawo da ita" Yarinyar ta sake daga ido ta kallesa, AJ ya daga kafada ya kulle kofarsa, juyawa tayi tana tafiya a hankali ta bar wajen. Har waje Khaleesat ta raka Safiyyah bayan ta takurata ta rakata, sai ma da suka jira Lyft din ya karaso sannan Safiyyah ta shiga ta mata sallama, Khaleesat ta daga mata hannu sannan ta juya ta koma cikin gidan, zaune ta ga yarinyar daxu a parlor, suna hada ido Khaleesat ta sauke kanta sai ta kasa wuce sai da tace mata "Hi, i am Khaleesat" Ido kawai yarinyar ta zuba mata tana kallonta babu yabo babu fallasa kuma babu alamar zata amsa mata, hakan yasa Khaleesat ta fara tafiya ta wuce sama, lkci daya jikinta yayi sanyi ta shiga dakin da take ciki ta kulle. AJ ya fito dakinsa zai sauka downstairs kenan sai ga Jay ya hauro sama fixgosa yayi a fusace yace "Are you out of ur senses Junaid, what did u just do?" AJ yace "Ban gane what did i just do ba, Hadeeyah came, she requested to know the lady she saw in this house, kai kuma baka isa inyi karya saboda kare ka ba tunda ba tsoronka nake ji ba, when i told u to look for another alternative for the brat ai mayar dani mahaukaci kayi" Bude kofar wani daki aka yi sai ga Hadeeyar ta fito da Handbag dinta, Jay ya sake AJ, ya bi ta da kallo yace "Hadeeyah" ko juyawa bata yi ba ta ci gaba da sauka downstairs, ita dai tasan AJ ba wasa yake yi da ita ba balle yayi mata karya, yaushe ma ya sake maka fuska balle ya maka karya, Jay yace "Look Hadeeyah, ko da wasa kika ce zaki ma people back home wannan magana i won't take it likely with you, and that will be the end between me and you, cause u never gave me a listening ear" Sai a sannan ta juyo tace "And so effing what? Wannan ne dalilin da yasa all this days baka da lokacina dama ko Ya Jawwad? I am not surprise" Tana kai wa nan ta sauka ta nufi hanyar fita gidan, Jay ya kalli AJ da ya daga kafada shima yana kallonsa. Jay wasn't even that bordered kamar babu abinda ya faru, amma gaba daya ya fita harkan AJ a gidan, ko kallon inda yake baya yi, ya canza code din kofar dakinsa ta yanda ma bazai shigo masa daki ba, yasan ba lallai ma Hadeeyah ta gaya ma yan gida komai ba, she won't even dare try that, amma still yaki ko da kiranta a waya, dama ita ce me kiran nasa, daga Oxford University take kuma bata ma ce masa zata shigo Maryland ba she just came without notice, ita ko Khaleesat bata ma san abinda ke faruwa a gidan ba amma abinda Hadeeyah ta mata ya tsaya mata a rai. Ranan friday Khaleesat suka yi second to the last exam dinsu, na karshen kuma za su yi ranan talata, gaba daya ta kagu su gama ta bar kasar zuwa sannan hankalinta yayi gida, she just want to go home, duk da tasan Housemate dinta zai ce zai siya mata flight ticket amma gani take she is just a burden to him, for weeks now hidima kawai yake da ita, ya kai ta schl, at times ya jira ta gama jarabawa ya maidota gida, wani lkcn dab da sanda yasan zata fito exam zai koma schl din don daukota, he really tried for her during this period and he is always making sure that she is fine, bata ma san ta inda zata fara appreciating din shi da Safiyyah ba, they where by her side all through, ba don su ba da bazata iya jarabawan ba ma, yau kam tunda ta tashi take jin ta wani iri tana dai kwance da tunani iri iri a ranta, ji take kamar ta jawo monday. AJ na zaune reading nook din dake parlor yana kokarin hada references dinsa a laptop dinsa, ga textbooks kaca kaca a gabansa, gaba daya Jay ya bi ya goge duk wanda ya tura masa ta WhatsApp, infact duk wani abu da Jay yasan AJ zai karu da shi na bangaren PhD da suke sai da yabi ya goge tas, shi da AJ bai nuna masa ma yasan abinda yayi ba, shi yasa ya dukufa tun asuba yake reading nook, Ι—aga kai yayi bayan yayi perceiving din wani turare da ya gauraye ko ina na parlon, he was a bit shock ganin wanda ya shigo parlon tare da wasu mutane biyu suna biye da shi, ya sauke idonsa, he was surprise and shock, sai kuma ya mike ya dawo cikin parlon, ya Ι—an dukar da kansa yace "Sannu da zuwa Abba" Wanda ya kira da Abba yace "Ya karatun? Ina Ahmad?" AJ yace "He is upstairs, Abba surprise visit ka mana" Zaunawa Abban yayi saman kujera yana amsa gaisuwan da ma'aikatan gidan ke masa cike da ladabi sannan ya kalli AJ yace "I just branched to check on u both, daga England mu ke munje wani taro" AJ dai ya sunkuyar da kansa, sai kuma ga wata mata da bazata wuce 50 ba cikin shiga ta alfarma ta shigo parlon da wata yarinya that is 16 years old, AJ dai ya shafa kansa don shi abun ma dariya ya fara basa, ya dai gaisheta ta amsa, yarinyar ta tafi ta rungumesa tace "Ya AJ naga ka zama kato, are you going to the Gym?" Matar da suka shigo tare ta nemi waje ta zauna tace "Allah sa karatun yake" Wani kallo ya mata ta gefen ido ya wuce sama su kuma masu aikin gidan suka tafi dauko bottle water da lemo, direct dakin Jay ya nufa a dai lkcn da Jay ya bude kofar dakinsa ya fito, AJ yayi wata dariyar bosawa yace "Wallahi ga Abba da Aunty a parlor" Jay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa, can yace "Abba da Aunty kuma?" AJ couldn't stop laughing, Jay ya Ι—an leka downstairs yaga da gaske ne, buda baki yayi yana kallon AJ da ya kasa daina dariya, Jay ya sauke ajiyar zuciya ya jawosa yace "Look, let's talk pls Ajay...." Ajay yace "Talk about what? Ba dai baka jin maganata ba, zaka san yanda zaka yi da yarinyar nan yau, kaga ban ma kai report ba sun zo da kansu za su gane ma idonsu rayuwar da ka jefa kanka a Maryland" Jay dai kallonsa kawai yake, AJ ya daga kafada irin ko a jikinsa din nan ya sauka downstairs yana murmushi, Jay ya fi minti biyu tsaye thinking of what yo do, daga karshe dai ya nufi bangaren AJ, yana tura kofar dakinsa yaji dakin a bude, juyawa yayi ya tafi dakin da Khaleesat take yayi knocking, duk da ba bacci take ba amma idonta a kulle, ta bude idonta ta mike zaune sai gashi ya shigo dakin, Calmly yace "Bacci kike ne Halysaah?" Ta girgiza masa kai tace "A'a" yana kallonta yace "Ya na ganki haka ko baki da lafiya ne?" Nan ma ta girgiza masa kai tayi shiru, ya kwantar da murya yace "Gaya min gaskiya, ko dai tunani kike Housemate?" Calmly yake mata maganar kamar ba komai, ta Ι—an yi murmushi cikin sanyin murya tace "A'a" Yace "Good, i think we have visitors a gidan nan yau, i will change you to another room wanda babu wanda yake shiga zuwa har sanda za su tafi, nasan baza su wuce kwana biyu ba bakin za su tafi in sha Allah" Ita dai tayi shiru tana kallonsa, ya sakar mata murmushi, ta sunkuyar da kanta, yace "Alright, ta so mu je ko?" Sauka tayi daga kan gadon ta dau gyalenta, yace "I will bring you all u need to the room afterward" daga haka ya nufi kofa tana biye da shi, direct ya nufi bangaren AJ da ita, ya bude kofar dakin yana kallonta yace "Here" ta sauke idonta tana kallon cikin dakin dake wani kamshi na musamman sannan ta shiga, ko da wasa bata san dakin AJ bane, Jay yace "I will be back soon Halysaah" Ta gyada masa kai, ya jawo kofar sai dai bai kulle ba tunda bai san code dinsa ba yanzu, sai bayan da ya bar wajen yaji dariya ya taho masa, to yanzu ta ina ma zai fara lallaba AJ, kawai yasan ya ma gama kashe AJ, to in ba haka ba bai san way out ba don bangaren AJ ne kadai Halysaah zata tsaya da babu wanda zai san tana gidan tunda babu me zuwa ko kusa da bangaren nasa sanin halinsa, amma kaf din gidan yasan Aunty sai ta bude ta shiga banda part din AJ, downstairs ya sauka da sauri don zuwa gaida su Abba, Khaleesat dai ta kasa daina bin dakin da kallo, komai na cikin dakin fari ne kal har wani kyalli yake tsabar neatness, ita abun yana mata kamar dakin wani important person ne a gidan Jay ya kawota, ta karasa ta zauna gefen gadon a hankali, she just don't know why she is not comfortable with the room. Jay dai na zaune parlor ne amma gaba daya hankalinsa na kan AJ dake ta shan fruit din da aka kawo ma Abba hankali kwance kamar shi aka kawo ma, Aunty kuwa tana dakin Abba dake nan downstairs tana gyara masa, AJ ya mike zai tafi sama, Jay na ganin haka ya mike ya bi bayansa da sauri, bayan sun haura sama Jay yace "Hey let's talk AJ" AJ ya wani kallesa, sai kuma yayi wani dariyar shakiyanci yace "Talk about what? Pls sort ur self out, ka daina ma involving dina a crime din nan da ka aikata, kar a zata tare muka aikata" Jay dai ya fara kokarin danne dariyar da ya taho masa don bai ma san ta inda zai fara masa bayani ba.

 

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

[5/22, 6:50 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Parlon dake sama Jay ya ja AJ zuwa can yace "Ohk now, let me explain Bruh" AJ na girgiza kai yace "I am not interested pls Jay, ni fa bana son ma kana min magana a gidan nan kar ayi zaton tare mu ka kawota" Jay yace "Naji.... bayan yanzu bazan sake maka magana ba, kawai dai na duba naga duk gidan nan dakin ka ne kadai yake da wahalan shiga..." Nan da nan AJ ya hade girar sama da ta kasa yana kallonsa yace "I don't understand, me yasa kake using dakina kake misali? What are you insinuating? What is ur point??" Jay ya shafa sumar kansa a hankali yace "My point is, na kai Housemate dita dakin ka for the meantime before i find a way out, nasan can ne kadai su Aunty baza su ganta ba, tunda dakin ka out of bound ne" Haka AJ yayi dropping jaw yana kallon Jay baya ko kiftawa with shock written all over his face, Jay ya sosa kansa zai yi magana suka ji muryar Hajiya Rukayya warce suke kira da Aunty, ta karaso parlon tace "Jay ka je Abbanku na magana a parlor" Jay yace "To gani nan zuwa Aunty" Ta Ι—an kalli AJ sannan ta juya ta bar parlon, Jay ya sauke ajiyar zuciya yana kallon AJ that was still looking at him ko kwakkwaran motsi baya yi, da alama ya ma kasa cewa komai, Jay yayi patting Ι—in shoulder dinsa yace "I know u gat my back Bruh, you won't love seeing Abba Mad at me" Yana fadin haka ya juya ya bi bayan Aunty yana sauke wani ajiyar zuciya, after almost 15 mins Jay ya dawo sama, zaune ya tarda AJ a parlon dake sama ya tallabi chin dinsa da duk hannunsa biyu yana girgiza kafa, he looks restless, Jay dai ya danne dariyar da ya taho masa da kamar zai juya ya koma downstairs, AJ na ganinsa ya mike ya nufesa a fusace ya fixgosa yace "What offense have i done to you Jawwad? Why my room? Why will u take her to my privacy, my own comfort zone, what sort of nonsense is this plss? Dakina fa? Meye hadina da ita zaka kai ta har Bedroom dina?" AJ was so mad at him, nan da nan idonsa suka sauya launi, Jay yace "To Abba dai na kiran ka, je ka dawo sai ka ci gaba" AJ dai sai kallonsa yake yana huci, can ya turasa ya bar parlon kamar zai tashi sama, Jay ya wara ido yana shafa kansa yana Ι—an murmushi, karkari dai iya abinda zai yi kenan bazai wuce haka ba, kuma ba wani kiransa da Abba yake yi kawai wahala ne bai so yasa yace masa ana kiransa downstairs, dakin Khaleesat ya koma ya dauko mata box dinta da abubuwan da yasan zata yi needing ya kai dakin AJ, Khaleesat ta mike da sauri ganinsa, a hankali tace "But Housemate i am not comfortable in this room" ya Ι—an bude ido yace "Why? Meye da dakin Halysaah?" Tayi shiru bata ce komai ba, Calmly yace "C'mon Halysaah wannan ma ai yafi wancan da kike ciki" Yana murmushi ya kare maganar, ita dai tayi shiru bata ce komai ba, ya ajiye mata kayanta da wayarsa yace "If you need anything just call my line" Ta gyada masa kai, ya nuna mata hanyar bandakin dake babban dakin yace "In zaki yi sallah ga bandaki can" Nan ma dai ta gyada masa kai kawai, ya juya ya fita daga dakin ta koma ta zauna, gajiya tayi da zama tana son kwanciya amma ta kasa kwantawa saman gadon, ita kanta ta rasa dalili, can dai ta zamo kasa a hankali ta kwanta saman lallausan carpet dake dakin ai ko nan da nan bacci ya dauketa, throughout ranan haka Khaleesat ta yini a dakin ita kadai, tun da Housemate dinta ya kawo mata lunch har lokacin magrib yayi bai dawo dakin ba, sai Cook din gidan ne ya kawo mata dinner, tana zaune saman darduma bayan ta idar da sallahn isha taji an bude kofar dakin ta daga kai, sosai gabanta ya fadi ganin AJ, ta sauke idonta daga kallonsa, shi kam ko kallon inda take bai yi ba fuskarsa a murtuke ya tafi ya dau second phone dinsa da laptop, ya bude press dinsa ya dau pajamas dinsa sannan ya fice daga dakin, sai a sannan ta daga kai ta bi sa da kallo tana mamakin abinda ya shigo yi, don bata san me ma ya dauka a dakin ba, har sannan bata kawo cewar dakinsa bane, har ta fara bacci Jay ya shigo dakin da sallama, ta mike zaune daga kwancen da take a kasa, da mamaki yake kallonta yace "Me yasa kika kwanta a kasa Halysaah?" Ta girgiza masa kai kawai, yace "C'mon don't do that pls, ga gado zaki wani kwanta a kasa" Ta kalli gadon tace "Zan kwanta" Yace "Good, hope u need nothing?" Tace "Bana bukatar komai" Yace "Alright then, good night" A hankali tace "Thank you" ya mata murmushi yace "In kashe maki wutan dakin ko a maida maki dim light?" Tace "Dim light" Ya mayar mata wutan mara haske sosai sannan ya juya ya fita daga dakin, bayan fitarsa ta koma tayi kwanciyarta a kasa, ita gani take kamar master bedroom din gidan ne, may be that's why she is not comfortable, wajen karfe dayan dare dakin yayi sanyi sosai amma taki daukan duvet din saman gadon ta rufa, kawai ta lullube da Hijab dinta, she was so cold gashi Safiyyah bata hado mata kayanta da Sweater ba, tana ta kwance ta kasa bacci saboda sanyin da ya dameta sai juye juye take taji an bude kofar dakin, a hankali ta sauke Hijab dinta kasa kadan tana son ganin wanda ya shigo don har kanta ta rufe, taga AJ ne ya shigo, kallo daya yayi mata ya tafi daukar abinda zai dauka, zaro ido tayi bayan ta zargi anya ba dakinsa bane nan kuwa, sai bayan da ya fita taji ya kullo kofar ta mike zaune tana sake bin dakin da kallo with shock, dumin da taji dakin ya fara dauka gradually ne yasa ta gane ya kunna mata heatern dakin, ta koma a hankali ta kwanta sai da dakin yayi dumi sannan bacci ya dauketa..... Washegari da safe Jay na zaune main parlor tare da Abba da Aunty, cikin nutsuwa Abba ke masa magana amma shi gaba daya hankalinsa na sama kan Halysaah don tun da gari ya waye bai je wajenta ba, kawai dai Cook din gidan ne ya kai mata breakfast, AJ ya shigo parlon daga reading nook da yake zaune ya nufi dinning area zai yi breakfast, Abba ya bi sa da kallo, after a while yace "Baka yi breakfast din bane" Jay ya Ι—an kalli AJ, Aunty kanta kallonsa take ita ma, without turning back AJ yace "Ban yi ba" Aunty tace "To ai naga cook din gidan ya kai maka Breakfast din sama daxu" Ko tankata AJ bai yi ba ya tafi dinning ya zauna, Abba na kallon Jay calmly yace "Is he Okay?" Jay ya Ι—an shafa kai yayi kasa da murya yace "I think supervisor dinsa ne bai yi approving Article din da yayi publishing ba tukunna" Aunty tace "To banda abun sa ai ba wani abu bane he should add in more effort to his work kawai" Shi dai Jay bai ce komai ba, haka shi kansa Abba, after a while Jay ya mike ya tafi sama, direct part din AJ ya nufa bayan yayi sallama ya tura kofar dakin ya shiga. Wajen la'asar AJ na zaune parlorn dake sama, gaba daya he look moody, dama jiya da daddare a nan parlorn ya kwana tsabar takaici, har zuwa yanzu yaki ce ma Jay komai a gidan, Jay kuwa ko a jikinsa don ko kallonsa ma baya yi, su biyu ne kadai a gidan don Abba ya fita tare da Aunty da autarta zuwa gidan wani prominent friend dinsa a garin, da yake gobe da safe za su bar kasar zuwa Nigeria, AJ ya gyara zama yana bin Jay da kallo trying to be sure of what he is holding in his hand, he was very shock ya dai bi sa da kallo har yaga ya nufi bangarensa, ya tallabi chin dinsa yana girgiza kafa, sai bayan da Jay ya fito for the first time since yesterday AJ yace "Wallahi i will never forgive you for these Jawwad, i promise you am not forgiving you" Jay dai ya dake bai yi dariyar da ya basa ba, kuma yaki tankasa yayi wucewarsa ya bar sa zaune a gun, da daddare Khaleesat na duba laptop dinta Jay ya shigo dakin da sallama ta daga kai tana kallonsa ya zauna kan kujeran dakin yace "Hope you are better now?" Ta gyada masa kai, yace "Toh Allah ya sauwake, amma ki tabbatar kin sha maganin so that u get enough night rest" Tace "Zan sha" Yace "Alright Good night Housemate, bacci nake ji" Ta Ι—an yi murmushi tana kallon agogo dake nuna karfe goma tace "Ai baka ma yi da wuri ba" Yayi murmushi kawai yace "Saura kar ki kwanta saman gadon yau" A hankali tace "Zan kwanta" Yace "Good" Daga haka ya fita daga dakin, shi kansa yasan tunda ta dawo gidan yake tauye ma kansa bacci, kuma ba wai baccin baya damunsa bane kawai daurewa yake yi, har ciwon kai yake yawan yi yanzu saboda baya bacci sosai, Khaleesat ta kashe laptop dinta ta ajiye sannan ta mike a hankali ta dauko maganin da ya kawo mata daxu ta sha sannan ta kwanta saman gadon, amma fa a dar dar take saman gadon, Jay na isa parlorn dake sama ganin AJ kwance kan kujera yana danna wayarsa yace "Do you care sharing my room with me today?" AJ yaki tankasa yana danna wayarsa, Jay ya daga kafada yayi wucewarsa dakinsa, after like an hour AJ ya mike zaune jin muryar Abbansa, Abba dake kallonsa yace "Is everything Alright Ahmad? Why are you lying down on the Couch?" AJ ya fara sosa kai yace "Eh yanzu zan tafi daki Dad, ban san sanda bacci ya daukeni ba" Yana fadin haka ya mike tsaye ya dau wayarsa ya nufi dakinsa, Khaleesat ta juya jin an bude kofa don ba bacci take ba, yana shigowa dakin kuma ya kulle kofar ya tsaya nan bakin kofar, rufe har kanta tayi da duvet, ya tafi gaban madubi ya tsaya yana tunanin Jay bai taΙ“a cutarsa ba irin na wannan lokacin, sosai abun nan ya tsaya masa a rai, ita dai Khaleesat tana ta sauraren taji ya bude kofar ya fita daga dakin amma taji shiru, hakan yasa ta sauke duvet din kanta a hankali suna hada ido ya watsa mata kallo yace "Meye kike kallona?" Ta wani kallesa, sai kuma ta juya masa baya bata ce komai ba, after almost 5 minutes ya bude kofar dakin ya fice, tsabar yanda bai yarda da neatness din duk dakunan dake gidan ba ya sa ya gwammace ya kwanta a parlor instead of going into any of the room. Da Asuba Jay ya fito dakinsa kenan zai sauka downstairs su yi sallah da Abba, tunda Abba ya zo tare suke sallah amma banda AJ da baya saukowa ayi sallan da shi sai dai yayi shi kadai a sama, Jay ya hadu da Abba yana haurowa sama, Abba yace "This shows baku sallah tare a gidan nan Jawwad, ma'aikatan gidan nan guda biyu duk Musulmai ne, ga ka ga Junaid, amma ace baza ku hadu ku yi sallah ba?" Da sauri Jay yace "Muna yi Abba..." Abba bai ce masa komai ba ya nufi bangaren AJ, Jay ya buda ido sosai, sai kuma ya bi sa da sauri yace "Zan kira maka shi Abba..." Abba yace "Jiya da nace ka kirasa ya sauko?" Jay ya kasa cewa komai, duk tunanin Jay za su ga AJ a Parlor a kwance amma sai yaga baya parlon, nan hankalin Jay ya tashi ya tsaya a inda yake tsaye ya kasa ci gaba da bin bayan Abba, he wish Junaid bai cire code din nambobin kofar dakinsa ba, Abba na tura kofan sai ga AJ da ya shiga bandakin dake parlorn da suka baro yayi alwala ya taho zai dau pray mat, shi ma zaro ido yayi yana kallon Abba kamar yanda Jay ma ya tsaya kallonsa, AJ ya juya suka kalli juna da Jay, tunda Abba ya kunna wutan dakin ya tsaya for like a minute bakin kofar dakin yana kallon Khaleesat dake bacci, sai kuma ya juyo ya fito closing the door gently, Daga AJ har Jay suka sunkuyar da kai a tare kamar munafukai, Abba dai sai kallon AJ yake, after 30 seconds of silence, speaking Calmly Abba dake kallon Jay yace "Abinda ke faruwa gidan nan kenan Jawwad, and you told me nothing about it?" Jay ya kasa cewa komai kuma ya kasa barin su hada ido da Abba, cikin nutsuwa babu fada Abba yace "Magana nake maka Jawwad" Da kyar Jay ya girgiza kai yace "I know nothing about it Abba" AJ ya bude baki yana kallon Jay da yaki kallonsa, Abba ya gyada kai yace "Ohk then, ku mu je mu yi sallah lokaci na wucewa" Daga haka ya juya ya bar su tsaye a wajen, Jay ya bi bayan Abba da sauri, AJ ya bi sa da kallo baya ko kiftawa, tuni har Abba ya sauka downstairs hakan yasa Jay ya tsaya Parlor sai ya tuna tuggun da AJ ya hada masa gun Hadeeyah just 3 days back, bai san sanda dariya ya taho masa ba, sai ga AJ da jikinsa yayi sanyi ya shigo parlon yana kallonsa, hakan yasa Jay ya danne dariyarsa ya hade rai ya sauka downstairs da sauri, AJ ya bi sa da kallo, sai kuma a hankali ya zauna saman kujera ya kai hannunsa baki, ganin abinda Jay yayi masa yake kamar a mafarki, bai taΙ“a shiga shock irin na wannan lokacin ba. Da safe kamar babu abinda Abba ya gani a gidan don bai sake masu maganar baz kuma da alama ko Aunty bai gaya ma ba, Jay ma yasan bazai taΙ“a gaya mata ba, karfe sha daya jirginsu zai tashi zuwa Nigeria don haka har sun gama shirin tafiya Airport, Abba ya kalli Jay yace "Junaid bai sauko yayi Breakfast ba ko an kai masa sama ne?" Jay yace "I don't really know" Abba ya dau wayarsa ya kira AJ, ba a dau lkci ba sai ga AJ ya sauko parlor shi dai ya kasa hada ido da Abbansa, Abba na kallonsa yace "Kayi breakfast ne, naga baka sauko ba" Without looking at his Dad yace "Na yi" Abba yace "Ohk, za mu tafi airport ne yanzu, get ready" a hankali AJ yace "Ohk" Daga haka ya juya ya koma sama, sai da AJ ya fara zaunawa a parlon sama for almost 5 mins, gaba daya jikinsa a sanyaye yake, gashi ya tsani shirun Abbansa don ba alkhairi bane shirun, gwara ace ma fada yayi ta masa ba kakkautawa da wannan basarwan da yayi kamar bai ga komai ba, his next move might not be funny, Jay ya cucesa, bai taΙ“a zaton haka daga Jay ba, to ko yace ma Abba bai santa ba ta yaya zai yarda da shi tunda a dakinsa ya ganta ba dakin Jay ba, ganin bata lkci kawai yake ya mike yana tafiya a hankali ya tafi dakinsa don dauko kayan da zai sa, yana shiga dakin Khaleesat na fitowa daga bandaki da hijab dinta har kasa ta fito wanka, ya wani kalleta daga sama har kasa fuskarsa a daure, ita dai tunda suka hada ido ta dauke kanta bata sake yarda ta kallesa ba tana dai tsaye hanyar shiga bandakin, ya dau kayan da zai dauka ya karasa gaban madubi ya dau tsadadden turarensa ya fice daga dakin, ta wani kyabe baki ta karasa shigowa cikin dakin. Har Abba suka isa Airport bai ce ma AJ komai ba akan daxu da asuba, kuma da alamar babu abinda zai ce masa, he was just speaking about something different in the car, a haka suka rabu normal normal a airport kamar babu komai, AJ yaki jiran Jay ya ja mota ya bar airport din ya kama hanyar gida, dole sai Uber Jay ya samu da zai maida shi gida, ko da ya isa gida ya ga AJ zaune a compound da non alcoholic wine a gabansa trying to use it to calm himself down at the same time trying to figure out wani hukuncin Abbansa zai ce zai dauka a kansa.....

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

[5/26, 9:45 AM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat felt so much relieve after leaving AJ's room, tana biye da Jay ta koma dakin da take, ba tare da Jay ya kalleta ba bayan ya ajiye laptop dinta dake hannunsa yace "Kin ji sanda aka bude kofa da asuba ne?" Khaleesat na kallonsa ta girgiza kai tace "I am not sure, may be ina bacci sannan, banyi bacci da wuri ba" Yace "Ohk" Tace "Why are you asking?" Ya juyo yana kallonta, ya Ι—an mata murmushi yace "Nothing" Tace "But ai frnd din ka yana shigowa ya dau stuffs dinsa wani lkcn" Jay yace "Ohk" Har ya juya sai kuma ya sake dawowa yace "Kince baki yi bacci da wuri, ciwon kan ke damunki har yanzu?" Ta girgiza kai tace "A'a, kawai baccin ne dai bai zo ba" Yace "Ohk" Khaleesat ta bi sa da ido har ya fita daga dakin sannan ta zauna gefen gado a hankali, har cikin ranta take jin kamar ta jawo ranan talata, she is so tired tana bukatar kawai ta ganta kusa da Ummanta, she need her Mom's hug, Jay na fita ya kira ma'aikatan gidan su gyara ma AJ dakinsa, Jay made sure the workers left nothing untouched a dakin duk da babu abinda dakin yayi, amma irin gyaran da aka ma dakin da bandakin ba na wasa bane, sai da ko ina ya dawo yana sparkling tsabar gyara sannan Jay ya koma downstairs, amma still a ranan ma AJ bai kwana dakin ba, yayi kwanciyarsa a parlor kan kujera. Washegari which was monday AJ na zaune usual spot dinsa a compound da Coke din gwangwani a gabansa, har a sannan yaki ce ma Jay komai a gidan, not even Jay hatta ma'aikatan gidan duk ba wanda yake yi ma magana he is just keeping straight face, Jay ya fito daga cikin gida ya karasa har inda yake zaune, ko kallon direction dinsa AJ bai yi ba yana juya counter din hannunsa, Jay na kallonsa yace "Abba wants to speak to you" Yana fadin haka yace "Abba gashi nan" Ya ajiye wayar gaban AJ, Calmly Abba yace "How are you doing Junaid" AJ ya sauke idonsa ya gaida Abba, Abba ya amsa yace "You didn't call to know if we arrived safely" AJ yace "Ayi hakuri" Abba yace "It's fine, yaushe za ku dawo hutu" AJ yace "Ran Thursday zan dawo in sha Allah" Abba yace "What about Jawwad" A takaice AJ yace "I don't know" Abba yace "Hand the phone over to him" Jay ya dau wayarsa sitting in one of the chairs beside AJ yace "Na'am ina ji Abba" Abba yace "Kai yaushe zaka dawo" Jay ya Ι—an yi shiru, sai kuma yace "Probably next week in sha Allah" Abba yace "Ohk Allah ya kai mu, earlier today you said you have something to tell me unfortunately ina tare da baΖ™i a lkcn, so what is it Jawwad" Jay ya Ι—an shafa kansa thinking of where to start, can dai yace "Abba dama it's about the girl u saw yesterday" Abba yayi shiru at first, sai kuma "Ohk, what about her?" Jay yace "Abba ni ne na kawota gidan ba AJ ba, she is a student of John Hopkins also, she is having issue with House rent and she's writing exam, so shine kawai na kawota gidan nan zuwa sanda zata gama jarabawan...." Abba ya dakatar da shi yace "Did you and Junaid birth me or i birth you both?" Jay ya girgiza kai da sauri yace "Billah Abba i am not cooking up stories, believe me, all what i am saying is the truth ai kasan bana maka karya Abba, kawai dai ni na kai ta dakin AJ ne without even his knowledge cause Aunty will definitely see her in the house, part din AJ ne kawai nasan bazata shiga ba, kuma because of this... AJ parlor ya dawo yake kwana, wallahi babu komai tsakaninmu da ita kawai taimako ne, you can even speak to her to confirm ranka ya dade" Abba yace "If she is having rent issue don menene baza ku bata kudin hayan ta biya ba ko kuma ni ku min magana, na menene sai kun kawota nan gida cikin ku ta zauna? Is that ur home training? Dama addininku ya yarje maku da haka?" Jay ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "Kayi hakuri ka gafarce mu Abba, she will be rounding up her exam on Tuesday, and she will leave in sha Allah" Abba yace "Kaga da ba don nasan baza ka min karya ba Ahmad i won't listen to you, da Junaid ne ya tsaya mun wannan bayani bazan yarda da shi ba, and my plan was to start making arrangement na samar masa mace da zan aura masa a kai masa ita can Ζ™asar, tunda ka min wannan bayanin naji na kuma yarda amma daga kai har shi sati biyar na baku kacal ku gabatar min da macen da za ku aura, ita kuma i will send you some money to sort out her House rent" AJ ya daga kai yana kallon Jay bayan yaji abinda Abbansa yace, sai kuma ya mike kamar zai tashi sama ya bar wajen, shi dai Jay was speechless this was the least thing he was expecting to hear from Abba, jin Abba ya katse wayar ya zuba ma screen din ido, ya basu 5 weeks?? jay ya fi minti goma zaune a wajen kafin daga karshe ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya dau wayarsa ya shiga cikin gida. The next day Khaleesat suka gama jarabawansu na karshe and she was so happy amma kuma da ta tuna wasu abubuwa kawai sai mood dinta ya canza, suna zaune tare da Safiyyah a cikin makarantar ganin yanayinta da yanda ta sauya lokaci daya tayi shiru, Safiyyah ta kalleta tace "Why are you like this Khaleesat?" Khaleesat ta daga kai ta kalleta, a hankali tace "I don't have the means of going back to Nigeria Sophie, the burden i am placing on my Housemate is too much ba shi ya kawo ni kasar nan karatu ba, he knows nothing about me, don me zan yi ta dora masa nauyina har haka?" Safiyyah tace "To ya za kiyi Khaleesat, tunda ba ke kika rokesa ya maki ba ai kawai addu'a zaki masa Allah ya saka masa da alkhairi, he is ur God sent Angel, ba gashi with or without Abdul kin gama jarabawanki lafiya ba" Khaleesat ta sauke idonta jin hawaye ya ciko mata, Safiyyah ta hade rai tace "To meye na kuka kuma?" Muryarta na rawa tace "Ni dai bana son yace zai sake kashe min kudi masu yawa in koma Nigeria, i am feeling guilty" Safiyyah ta wani kalleta, can tace "Kya rube a kasar nan kuwa, ke kina da hanyar komawa ne? Ko kuma aikatau zaki nema a kasar ki tara kudin komawa Nigeria? In ba dai kudaden Abdul dake account dinki zaki yi using ki biya kudin jirgi ba" Safiyyah na kai wa nan ta kyalkyale da dariya tace "Ko ya kwashe en kudaden nasa ne?" Ita dai Khaleesat tayi shiru taki ce mata komai, Safiyyah tayi dariyarta me isarta sannan tace "Allah ba batun wasa ba, ya kwashe kudaden nasa ne?" Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace "Suna nan" Safiyyah tace "Miliyan nawa ne ma?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Almost 9.5 Million" Safiyyah tace "To kawai ki siya Ticket abunki tunda dai yasan ba uban wani gareki a kasar ba da zai baki kudin komawa Nigeria ba, bayan shi kawo ki, in nice ke ma har shopping sai nayi na komawa Nigeria a cikin kudin wallahi, ai bazai san kin taΙ“a ba tunda ba shi ke ganin alert ba" Safiyyah na dariya ta kare maganar, ita dai Khaleesat bata tanka ta ba, Safiyya tace "Naji kinyi shiru ko baza ki taΙ“a ba? Wallahi yanzun nan in raka ki shopping mu fatattake kudin" Khaleesat tace "Ai ba nawa bane da zan fatattake su" Safiyyah ta kwashe da dariya tace "To ai sai kiyi ta zama a kasar, dama gulma ce yasa kika kawo maganar ba wani abu ba don nasan Jay kike saka ran ya biya maki ticket" Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take ta kasa ce mata komai, amma ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta, Safiyyah tace "In kuma in ma Ya Musty magana to, don dai Economy class ticket da zai siya mana bazai ce ya gagaresa ba" Da sauri Khaleesat tace "A'a, zan yi amfani da kudin account dina" Safiyyah tace "Atoh dai" Khaleesat ta gaya mata haka ne kawai don bata son taje ta ma Ya Musty magana.... Jay ne ya zo daukansu a schl din as usual, sai da ya fara dropping din Safiyyah sannan ya kama hanyar gida da Khaleesat, daxun nan yaga Abba ya sako masa dala dubu goma wai na House rent dinta, da ya gaya ma AJ sai cewa yayi ya masa transfer din Dala dubu biyar shi ma ya rike dubu biyar din tunda ba su suka kawota kasar ba, shi da Jay bai tankasa ba, Jay dake driving ya Ι—an kalli Khaleesat jin shirun yayi yawa, yaga alamar tayi nisa tunanin da take, sai a sannan ya kula da idonta da yayi ja, a hankali yace "Halysaah" Juyawa tayi ta kallesa trying to look alright ta Ι—an yi murmushi tace "Na'am" Yace "Are you okay?" Tayi yake tace "Na gaji ne kawai" Jay yayi shiru, bai sake ce mata komai ba amma yasan ba gaskiya ta fada masa ba, a Ι—an few months din da yayi da ita har ya gama studying dinta gaba daya, he knows when she is happy, sad, bored, disturbed, and even tired, wannan karan yaga damuwa ne karara a fuskarta, ya dai ci gaba da driving dinsa har suka isa gida, bayan yayi parking ya juya yana kallonta, a hankali yace "Me ke damunki Halysaah?" Duk kokarinta na ganin ta nuna masa ba komai hakan yaci tura, don kawai ita ma gani tayi kuka ya taho mata, Jay ya jinginar da kansa da kujeran motar bai ce mata komai ba, kwana biyu ya huta da kukanta don a sanda ya dawo da ita gidan rana daddaya ne bata kuka don ma Safiyyah na taka mata burki kuma ya ga tana Ι—an jin maganar Safiyyar wani lokaci, sai da tayi kukanta me isanta sannan yace "Sauka mu shiga ciki to" Ba musu ta bude motar ta sauka tana goge idonta, shi ma ya sauka, yana gaba tana biye da shi suka shiga cikin gidan. Khaleesat na kwance da yamma ta shiga Hisnul Muslim dake wayar Jay sai ga kira ya shigo wayar, a hankali ta mike zaune tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren taji yace "Kin tashi?" Tace "Uhm" Yace "Kin yi sallah?" Tace "Nayi" yace "Ohk will you mind going out to the park with me?" Khaleesat tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Ohk, thank you" Yace "You are welcome, i will be waiting for you at the parlor downstairs" Tace "Ohk" After almost 15 mins Khaleesat ta sauko downstairs cikin shiri, sosai kayan jikinta yayi mata kyau sai dai ta rame sosai, shi kadai ne zaune parlon yana jiranta, tun da suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ya mike ya jira har ta iso parlon yana kallonta, a tare suka fita zuwa parking space din gidan ya bude mata motar, ta Ι—an kallesa tayi murmushi tace "Thank you" Ya bude ido yace "No thanks" bayan ta shiga ya kulle motar sannan ya zaga ya shiga driver seat, one of the best park na state din ya kai ta and she love everything about the park, the view was so fascinating and breathe taking, she felt so refresh and relieve taji kamar bata da wani damuwa a lkcn, Jay ya siya masu Wraps da fresh lemonade, wannan karan bata ji kunyar cin abinci gabansa ba, lkci lkci yake daga kai ya kalleta, ita dai ta dinga kallon feral horses dake park din from a far distance, can ta kallesa tace "Su ba a hawansu ne?" Yayi murmushi ya girgiza mata kai yace "Ba a hawa" Tace "And nobody is controlling them?" Yace "Sort of, they are just on their own with no supervision, ko kina son in kai ki inda zaki hau doki ne?" Er dariya tayi ta girgiza masa kai kawai, ya Ι—an kalleta, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki a lokacin, ta kalli wraps dinsa da bai karasa ci ba tace "You are not eating?" Yace "Za ki ci ne?" Tayi murmushi tace "A'a, na koshi, kawai naga baka ci da yawa bane" Yace "Na ci abinci daxu ne, i am full" Ta kalli lemonade din gabansa tace "To in dauka?" Yace "A karo maki wani kenan?" Ta girgiza kai da sauri tace "Aa fa, i just don't want it to waste ne" Ya dauki sauran lemonade din nasa ya ajiye mata a gabanta yana kallonta, ta dau straw din ta fara shan lemonade din a hankali, dauke ido yayi daga kallonta, wayarsa ya fara ring yana dubawa yaga AJ ne ke kiransa, yayi picking ya kai kunne, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, after few seconds Jay yace "Ni sai next week probably, ban gama abinda nake ba, do not book with me" Ajiye wayar yayi bayan AJ ya katse, ya kalli Khaleesat yace "Zaki jira har next week mu tafi Nigeria, or you will leave before then?" Khaleesat tayi shiru at first, a hankali ta sauke idonta tace "Yanda kace" Yana murmushi yace "Ko zaki bi AJ, he is leaving soon, yanzu ma ticket zai yi booking" Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, sai kuma tace "He that dislikes me shi ne zan bi sa?" Jay yayi dariya yace "How will you say he dislikes you Halysaah? He dislikes you shi ne yaje har apartment dinki yayi rescuing dinki? Ke ce dai baki ganesa ba har yanzu, AJ is nice just that yana da son girma ne kuma baya son raini, which i understand him because that's our heritage, kinga ke ko gaishesa baki yi" Tana wasa da straw din lemonade din gabanta tace "To ai nasan ko na gaishesa bazai amsa ba, saboda na taΙ“a gaishesa bai amsa min ba" Jay dai yayi murmushi yace "In kin ci gaba da gaishesa ae zae amsa" Tace "Ur frnd doesn't like me at all, he prefer my frnd" Jay yace "Who told you he is my frnd? AJ is my cousin bro Halysaah" Khaleesat ta daga kai ta kallesa tace "Da gaske?" Yayi murmushi yace "Ba ma kama ne?" Khaleesat ta buda hannu tace "Ni ban wani san yanda fuskarsa yake ba ai, ban taΙ“a kallonsa sosai ba" Jay yayi dariya, a hankali yace "To cousin brother dina ne, His dad is my father's junior bro" Khaleesat tace "To amma dai ka girmesa ko?" Jay na murmushi yace "Not at all, just 3 months ne tsakaninmu, we will clock 34 next year" Khaleesat tace "Shi ne yace ya haifeni?" Jay bai san sanda yayi dariya ba sosai, sai kuma yace "Zolayarki fa yake, but how old are you?" Ta sauke idonta kasa kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "I am 20" Jay ya wara ido yace "Waw, you are still a Baby Halysaah" ta wani kallesa, yana murmushi yace "To ai in AJ mace ne kuma an masa auren wuri ya isa ya haifeki" Yana dariya ya kare maganar, Khaleesat dai taki cewa komai still playing with the straw in front of her, a hankali Jay yace "Are you angry?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma tayi murmushi ta girgiza masa kai still looking at him, Jay ya kwantar da murya yace "U misunderstood AJ, yana da kirki sosai, kuma yana da tausayi, just that he is a no nonsense kuma baya son raini, sannan truly yana da girman kai na sani, but that doesn't make him bad, kuma da kinsan wanene shi zaki san yana ma da saukin kai" Khaleesat ta karasa shan lemonade din gabanta taki ce ma Jay komai, Jay ya kalli agogon wrist dinsa yace "Let go for horseback riding before it gets late" Khaleesat ta zaro ido tace "A'a ni dai bazan hau doki ba" Yana murmushi yace "To mu je dai" Shi ya fara tashi sannan ita ma ta mike suna tafiya a tare, satan kallonsa tayi suka hada ido ya ciro wayarsa yace "Let's take some pictures with this beautiful view" A hankali tace "Ok" Tana tsaye kusa da shi yayi masu hoton da wayarsa, yana kallon hoton da yayi masu ya taΙ“a hancinsa yace "Ya naga hancinki yafi nawa tsayi, ya naga kamar kin fi ni kyau" duk lokaci daya ya jero tambayar yana sake kallon hoton da kyau, ita dai Khaleesat tayi murmushi tace "Uhm is that an irony?" Jay yayi dariya yace "I am serious Halysaah" Wata er Africa ce ta zo wucewa ya mika mata wayarsa politely yace ta masu hoto pls, yarinyar ta amshi wayar zata masu hoton, yanda Khaleesat taji ta uncomfortable kusa da shi, shi ma dai kamar hakan ne cause he left a little gap between them, yarinyar ta masu hotuna masu kyau kuwa, ita kanta yarinyar sai kallon hoton take kafin ta mika ma jay wayarsa tana kallon Khaleesat admiringly tana murmushi tace "You are so Beautiful" Khaleesat ta sauke idonta tace "Thank you" Yarinyar ta daga masu hannu ta bar wajen, bayan Jay yayi mata godiya, kallo daya yayi ma hotunan ya mayar da wayar cikin aljihunsa yace "Let go for horseback riding Housemate" Wani park din ya kai su daban da ake hawa doki, duk yanda yayi da Khaleesat ta hau doki bayan ya biya masu kudi taki wai ita bata iya ba tsoro take ji, daga karshe ta marairaice tace "Ni dai kawai ka bani wayarka in dinga maka video sai kai ka je ka hau" Yayi murmushi kawai ya mika mata wayarsa yace "To ai shikenan" Khaleesat was so impressed with his horse riding skills kamar irin dama ya saba din nan, sai murmushi take masa, mutanen wajen ma suna ta kallonsa, Khaleesat's eyes were glued to him all through, tana yi tana masa video, sai after 7 suka bar wajen, tana kallonsa kafin su shiga mota tace "Where did you learn to ride horse confidently?" Yayi dariya yace "Back home" Tana murmushi tace "To ka taΙ“a zuwa nan ne?" Jay yace "Tab ai nan wajen zuwan AJ ne, kawai dai of recent ne muka dena zuwa" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, sai da ya fara biyawa African Restaurant ya siya mata abinci, ganin leda daya ya mika mata yace "This is for you" Tace "Kai fa?" Yace "No, i am taking tea and bread this night" A hankali tace "Ohk, thank you" Bayan sun isa gida yayi parking, ta juya tana kallonsa a hankali tace "Thank you so much, Allah ya saka maka da alkhairi, i appreciate you" Without looking at her yace "Amma nace ki dena min godiya ko Housemate?" Tayi shiru, ya bude motar ya sauka sannan ita ma ta sauka, yana gaba tana biye da shi har suka shiga gidan, AJay na zaune parlor yana shan fruit salad yana kallon kwallo, ya juya ya kalleta don shi bai ma san bata gidan ba, suna hada ido abinda Jay yace mata daxu ya fado mata, ta sunkuyar da kai, kamar munafuka tace masa "Good evening" AJ ya gyara zama yana kallonta yace "Kin saba gaisheni ne zaki ce min Good evening??" Khaleesat ta Ι—an kalli Jay da ya karasa cikin parlon, Jay yace "Good night Halysaah, if you need anything you call my line" A hankali tace "Thank you" Daga haka ta wuce sama, Jay na kallon AJ yace "Ba don na mata magana ba kana tunanin zata gaisheka ne dama? Ni ne nan na saka ta, sai me kuma in baka amsa ba?" AJ yace "Zamana take a gidan da zata gaisheni" Jay dai yaki tanka masa.

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

[5/26, 9:45 AM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Washegari Wednesday da yamma Jay na zaune parlon dake sama tare da AJ da ya maida parlon wajen kwanansa, don tun da Khaleesat ta kwana dakinsa tsakaninsa da dakin kawai ya shiga ya dau kaya, ko bandakin dake dakin baya shiga, Jay dake kallonsa yace "Yanzu dai zan iya dawowa dakinka kenan tunda ka tashi a dakin?" AJ yayi banza da shi yana ci gaba da hada few kayansa da yake yi a tsadadden box dinsa da zai yi tafiya gobe, Jay yace "To wai kayi booking flight din ne da naga kana hada akwati?" AJ yace "Bana son Airline din da na gani jiya, anjima zan siya Ticket din Turkish Airlines" Jay yace "How many hours connection time for the layover?" AJ yace "Baya wuce 2 to 3 hours, ko ma bazai kai haka ba" Jay yace "Will you mind travelling same plane with my Housemate? I just remembered I will be meeting my Mami at the UK, tare za mu koma Nigeria da ita daga can" AJ yace "Of course I will mind Jawwad, because my OCD will never allow me board the same plane with her, ga Airline kala-kala ka nemi wani ka siya mata ticket mana, what is my business with her da zaka hadani da ita sai kace ni na kawota America, there is this Airline na mance sunansa Economy class ticket dinsu naga is just 600 dollars, you can get her the ticket as the Good Samaritan that you are" Mikewa Jay yayi bai ce masa komai ba ya bar parlon. Wajen karfe biyar da rabi Jay ya kwankwasa ma Khaleesat kofa, bayan ta bude yace "Ba abinda zaki dauka a can apartment din da zaki koma da shi Nigeria Housemate?" Khaleesat tace "Ohk, zan dau wasu kayan" Yace "To ki shirya sai in kai ki can ki dauka" Khaleesat na kallonsa a hankali tace "Pls kar kace zaka siya min ticket ina da kudi a account dina, i will get the ticket" Yayi murmushi yana kallonta yace "To Hajiya me kudi, kudin zai isa ki mana booking har ni da AJ?" Tana murmushi ta fara wasa da gefen gyalenta tace "Sae dai kai kadai, ni ai ban san wani AJ ba" Akan kunnen AJ da ya taho daga parlor zai sauka downstairs, ya tsaya yana kallonta babu fara'a, Jay ya juya ya kallesa yana murmushi yace "Je ki shirya ina jiranki downstairs Halysaah" Juyawa tayi ta tura kofar dakin a hankali, ko da Khaleesat ta sauko downstairs ta tarar da Jay yana jiranta, and it's almost 6pm, ya mike suka fita daga parlon, bayan sun bar compound din a motarsa ya Ι—an kalleta yace "Kinga kin kara tsokanar AJ ko?" Ta marairaice tace "To ni ai ban san yana wajen ba, why is he always eavesdropping?" Jay yayi dariya yace "Ni dai ba ruwana" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, she can't even wait ta dena ganin AJ she is already exhausted with him and his problem, she can't wait to stop seeing him, suna isa apartment dinta abinda ya faru ya dawo mata fresh, kawai sai take ganin kamar trauma din ya dawo mata sabo a kwakwalwarta, lkci daya duk jikinta ya mutu, haka dai jikinta ba kwari ta tafi dakinta ta fara hada kayan da zata hada shi kuma Jay ta bar sa parlor yana jiranta, sau uku Safiyya na zuwa gidan debo mata kayanta kwanaki kuma duk Housemate dinta ne ke kawota, after a while Khaleesat ta gama daukan abubuwan da zata dauka a akwatinta, sauran kayan dakin duk ta haΙ—a su waje daya, ko zata dawo kasar ko bazata dawo ba ita dai bata sani ba, ta kuma bar ma Allah komai, ta gama tidying ko ina a dakin sannan ta fito wajen karfe shidda tana jan akwatinta a hankali zuwa parlor, kwance taga Housemate dinta kan doguwar kujera ya fara bacci, ta tsaya tana kallonsa, sai kuma ta tafi kusa da kujeran still looking at him ta Ι—an tapping din jikin kujeran gently, a hankali ya bude ido sai kuma ya mike zaune yace "Kin gama ne?" Tace "Are you sleeping?" Yace "A'a, kawai na kwanta ne ina wani tunani, it's even time for magrib bari inyi sallah, kema kije kiyi" Bandakin dake parlor ya shiga ita kuma ta koma dakinta, sai bayan wani minti sha biyar din suka bar gidan, tunda suka fito gidan Khaleesat tayi shiru, shi ma kuma bai ce komai ba, amma ya lura mood dinta ya canza, kawai ya sa a rai bazai tafi da ita gida a haka ba, after a while ya Ι—an kalleta yace "Would you mind watching a movie in Cinema tonight?" Khaleesat ta juya ta kallesa, sai kuma ta sauke idonta bata ce komai ba, yace "Ko baki kallo?" Tace "Ina yi, amma ba sosai ba" Yace "To yau za ki yi"  Waje ya samu yayi parking, ya dau wayarsa ya shiga website din Cinema din dake Maryland to check their schedules for that day, yayi selecting movie din da za su kalla, da lokacin da za su kalla sannan ya siya masu ticket aka turo masa ta online, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, yana daga kai tayi saurin dauke idonta daga kallonsa, ya ci gaba da driving dinsa, without looking at her yace "I hope you will enjoy the movie" Ita dai bata ce komai ba har suka isa Cinema din, ya siya masu popcorn and lemonade, sannan suka nufi cikin Auditorium din da za a haska film din da ya siya masu ticket, in some minutes kuma za a fara haska film din, wannan ne zuwan Khaleesat Cinema na farko a rayuwarta duk da a baya babu irin takuratan da Safiyyah bata yi akan su je tare da frnds din Safiyyar amma ita dai bata yarda taje, suna shiga Jay ya fara cin popcorn dinsa kamar abinda ya kawosa kenan, ita dai Khaleesat dama bata wani damu da popcorn ba hakan yasa take Ι—an ci jifa jifa tana kallon film da ake, she is beginning to like the film hakan ya sa ta tattara gaba daya hankalinta kan film din, after almost 35 mins da fara film din ta juya ta kalli Jay taga bacci yake, ta dade abu bai bata dariya haka ba, she couldn't believe he is seriously sleeping abun sa, ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya a hankali, she don't know why she feel relieve a duk sanda take tare da shi, there is never a boring moment with him, gently ta kai hannu kusa da shi ta dauki popcorn dinsa daya, he was still sleeping ta dinga kallonsa maimakon film din da ya kawota ta kalla, idan yana bacci komawa yake so gentle and calm, a nan ne kuma ainahin handsomeness dinsa ke fitowa, if there is the sleeping princess then he will be the sleeping prince, har awa daya da fara film din Jay baccinsa yake kuma ta kyalesa bata tashesa ba, she watched the movie har sai da ya kusa karewa and she really enjoyed every bit of it, ta juya ta kallesa sai kuma ta dau popcorn daya ta matsa dai dai kusa da shi a hankali ta saka masa a baki, da sauri ta gyara zamanta ta maida hankalinta kan movie, ya bude ido, taji yace "What a nice movie" Sai a sannan dariya ya taho mata ta juya ta kallesa tace "Ain't you ashame of saying this?" Yana gyara zama yace "You don't like the movie? But it's nice, i like it" Tana murmushi tace "To in ka gama baccin ka tashi mu tafi, ni na gama kallona" Ya Ι—an shafa kai trying not to smile yace "Wa yace maki bacci nake, i was only meditating duk nasan abinda ake yi ai, ba gashi an kusa gamawa ba" Ita dai murmushi kawai take tace "Naji, tashi mu tafi, a hanya sai ka bani labarin film din don akwai inda ban gane ba" Yayi shiru yaki cewa komai, tana danne dariyarta ta tashi ta dau sauran popcorn dinta da nasa, tashi yayi ya bi bayanta suka fita daga Auditorium din, lokaci lokaci take juyawa ta kallesa don ta tabbatar he is not walking and sleeping at the same time, da sauri ya jawota ta fado jikinsa bayan tayi missing step saboda waige waigen sa da take sai kuma yayi saurin saketa, within few seconds aka yi hakan, ta rufe bakinta da hannu don ba karamin tsorata tayi ba, yace "Yanzu da kin fadi kika fara min kuka kilan har mu kai gida" Ta marairaice tana kallonsa, Softly yace "Alright Sorry Halysaah" Ta juya ta fara tafiya a hankali, a haka suka fita daga cinema din bata sake waigen bayanta ba, yana biye da ita yana kallonta har suka isa gun da yayi parking. Wajen karfe goma suka isa gida bayan yayi parking ta juya ta kallesa a hankali tace "Thank you so much" Ya mata murmushi yace "You are welcome House mate" A haka suka sauka daga motar tana biye da shi suka shiga gidan, kafin ta shiga daki yace "Get me ur travelling documents" Ta kallesa zata yi magana ya daura fingers dinsa biyu a lips dinsa, ta sauke idonta sannan ta juya a hankali ta shiga cikin dakin, after some minutes ta fito ta mika masa, ya amsa yace "Good job, zan tura maki ticket din ta Email dina, sai da safe" A hankali tace "Allah ya tashe mu lafiya" Juyawa tayi ta koma cikin dakin ta kulle kofar, Jay ya tafi parlon sama yaga AJ kwance kan Couch yayi bacci, shi dariya ma yake basa, kawai mutum ya dora ma kansa wahala, juyawa yayi ya wuce dakinsa, wajen karfe sha biyun dare Khaleesat na ta juye juye ta kasa bacci ita kanta ta rasa dalili, message taji ya shigowa wayar Jay dake wajenta ta mike zaune ta jawo wayar tana duba message din taga Email ne ya shigo, tana bude Email din taga ticket din ya turo mata na Turkish Airline, kuma Business class seat, bata san me yasa taji hawaye ya cika idonta ba, ta ajiye wayar a hankali ta koma ta kwanta.

 

 

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

[5/26, 9:47 AM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat na zaune gefen gado tana kallon Jay dake kulle mata akwatunan ta, yana dagowa ta juya a hankali tana kallon window dake dakin, ya dau boxes din biyu yace "Let me get them in the car" Daga haka ya fita daga dakin, ta jinginar da kanta jikin gadon dakin har ya dawo, yana kallonta yace "Hope you didn't forget anything Halysaah" Ta gyada masa kai, yace "Ok, you know what? in dai muka fita kika hadu da AJ thank him and tell him you are leaving" With a smile on his face ya kare maganar yana kallonta, ta sauke idonta tana wasa da fingers dinta a hankali tace "Ohk" Yace "Good gal, mu tafi" Mikewa tayi ta bi bayansa tana rike da karamin handbag dinta walking slowly, suna fitowa walk way din babban corridor din sama sai ga AJ ya taho daga parlorn dake nan sama, Jay ya kalli kayan jikinsa ganin iri daya suka sa kuma tun safe ba wai sun hadu bane kawai coincidence, tunda AJ ya kallesu sau daya ya ci gaba da tafiyarsa, Khaleesat ta Ι—an kalli Jay, ya gyada mata kai sannan ya nufi stairs, ita dai tana tsaye ta jira har AJ ya iso kusa da inda take sannan ta sauke idonta a hankali tace "Good morning, i want to thank and appreciate you for everything, i will be leaving today in sha Allah" Without looking at her yace "Jay dai zaki ma godiya ni me na maki" Ta bi sa da kallo har ya fara sauka downstairs, sai bayan da ya sauka sannan ta tabe baki ta bi bayansa tana tafiya a hankali, parlor ta tarar da Jay zaune yana jiranta, Jay ya bi AJ da kallo yace "Flight din naka na gobe ne amma?" AJ yace "I am leaving for the airport now" Jay yace "Ohk, zaka jira inyi dropping Housemate dina sai in dawo in kai ka airport din?" AJ yace "No, don't bother" Daga haka ya fita daga parlon tare da daya daga workers din gidan wanda da alama shi zai yi dropping dinsa airport din, Jay ya daga kai ya kalli Khaleesat, ya lura tunda gari ya waye jikinta yake a sanyaye, yana kallonta yace "Are you Okay Halysaah?" Ɗan murmushi tayi tace "Sure" yace "Kin gaya ma kawarki yau zaki tafi?" Khaleesat ta gyada masa kai tace "Na gaya mata" Yace "Ok, ita yaushe zata tafi?" Khaleesat tace "Yayanta yace ta bari ranan lahadi" Jay yace "Kin tabbatar baki mance komai ba kuwa a sama?" Ta gyada masa kai, yace "Je dai ki sake dubawa Housemate" Bata masa musu ba ta juya zata koma sama yace "Toh ki ajiye jakar taki mana" Ta dawo ta ajiye jakarta a kan kujera sannan ta wuce sama, Mikewa Jay yayi ya tafi gun jakar ya dauka ya bude sannan ya ciro Dala dubu daya a aljihunsa ya sa mata a jakar ya kulle ya mayar ya ajiye mata ya koma ya zauna, ba a dau lokaci ba Khaleesat ta dawo downstairs tace "Ban manta komai ba" Yace "Good" Mikewa yayi bayan yaji fitar motar AJ don dama jira yake yaji sun fita daga gidan, yana kallonta yace "Mu je, ur Flight is in an hour time in sha Allah" Khaleesat ta gyada masa kai ta dau handbag dinta, tana biye da shi suka fita daga parlon gidan, har gari ya fara duhu, suna shiga motarsa ta mika masa wayarsa dake hannunta kar ta manta, a hankali tace "Thank you so much" Ya amshi wayar sannan ya dauko pin a motar ya cire sim card din cikin wayar snn ya mayar mata yace "Your ticket is on the phone, in kin koma Nigeria sai kiyi SIM card replacement, in kuma baki son wayar sai in sa a kai maki sabo a Nigeria" Tayi murmushin karfin hali tace "Saboda me zance bana so, nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Yace "To ai nasan ku mata da son sabon abu" Ta girgiza masa kai kawai tana murmushi bata ce komai ba, a haka suka bar gidan suka dau hanyar airport da tunani iri iri a ran Khaleesat, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya ga wani daren, ko me zata je ta tarar a Nigeria sai Allah, it's now that reality is dawning on her, bayan sun isa airport Jay ya juya ya kalleta yace "You can sort ur self out ba sai na shiga ciki ba ai ko?" Ta gyada masa kai, da kyar tayi karfin halin cewa "Thank you so much Housemate, Allah ya saka da alkhairi da abubuwan da ka min" Kasa ci gaba tayi saboda hawayen da ya fara sauka a idonta she just can't thank him enough, gani take words aren't enough to thank him, shi dai Jay kallonta kawai yake with surprise, can yace "C'mon Halysaah, to menene abun kuka?" Ta kasa basa amsa ta rufe fuskarta da gyalenta tana kuka a hankali, Jay ya kwantar da murya yace "Pls ki dena wannan kukan, in nasan abinda zaki yi kenan i will have just order either Lfyt or an Uber that will be taking you to the airport" Dena kukan tayi tana goge hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsa, ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido taga Luggages dinta dake booth zai dauko, a hankali ta bude side dinta ta sauka daga motar tana bin sa da kallo, daya daga porters dake wajen ya ba luggages din nata ya shigar mata da shi ciki ya hada masa da tip dinsa, ita dai Khaleesat kallonsa take, ya juya ya dawo kusa da ita yace "Alright safe trip Halysaah, idan kinyi replacing Sim card dinki sai ki min magana ta WhatsApp, my regards to everyone back home" Ta sauke idonta a hankali tace "I will miss you" sai bayan da ta fada haka ita kanta tayi realizing abinda ta fada, sai kuma ta kasa dago kanta, ya Ι—an yi murmushi yace "I will miss you too Housemate, in sha Allah next week i will be in Nigeria too" Bata iya ta kallesa ba ta gyada masa kai kawai ta juya a hankali ta bi bayan porter din da ya shigar mata da luggages dinta zuwa check in counter for her Boarding pass, kasancewar Business class ticket gareta all the processes were smooth and straight for her, daga karshe ta nufi waiting lounge don in 15 mins time za su fara boarding jirgi, tunda ta shiga lounge din take kallon wanda ta gani zaune da mamaki, ta kalli boarding pass dinta sannan ta kalli na hannunsa taga iri daya, wayarsa kawai yake dannawa, ganin bai ganta ba ta juya a hankali ta koma wani wajen daban ta zauna ta inda ma bazai ganta ba, bata sake waigen inda yake ba, iya drink kawai ta amsa a lounge din unlike wasu da ke ta cin abinci duk a cikin kudinsu, gaba daya ta nemi appetite dinta ta rasa saboda damuwa, da ta tuna inda zata sae taji har wani juya mata kanta yake kamar bata da lafiya, ta saΖ™a wancen a ranta ta kwance har daga karshe aka fara boarding din jirgi, sai da Khaleesat ta jira AJ ya fara tafiya sannan ta mike ta bi bayansa walking slowly, Har seat dinta wata Flight Attendance da ke welcoming dinta da fara'a ta kai ta, hada ido Khaleesat tayi da AJ that was sitting few seats away from hers, ta sunkuyar da kanta ta zauna Seat dinta tana mayar da Amenity kit din da aka ajiye mata a gefe, AJ ya kasa daina kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa, he can't even explain what he is feeling at that moment don bai taΙ“a ganin wanda ya gama rena masa wayo a duniyar nan kamar Jay ba, jiya wajen karfe sha biyun dare ya farka ya gansa yana duba masa waya ashe ticket din da ya siya yake dubawa, he felt like just leaving the plane at that moment, after a while kawai ya dauke kai yana kara gyara barrier din da zai sa ko hangota bazai dinga yi ba, Ita ma Khaleesat ko by mistake bata sake kallon direction din sa ba, a haka jirgin ya tashi, Khaleesat bata taΙ“a jin motion sickness ba tun da ta fara tafiya a jirgi amma yau ko don saboda pressure din da ta saka ma ranta ne kawai sai ji tayi as if she wants to throw up tun da jirgin ya daga, ta cire seat belt dinta da sauri ta mike ta nufi Lavatory din jirgin almost running, shi dai ya bi ta da kallo, Flight Attendance din da ta kawo mata Hot towel kafin tashin jirgin ne ta bi bayanta tana tambayar if she's okay, Khaleesat ta gyada mata kai kawai bayan ta fito daga Lavatory din, AJ ya bi ta da kallo har ta koma seat dinta ta zauna sannan ya tabe baki, Flight Attendance din ta duka kusa da ita tana tambayarta ko tana bukatar wani abu ne, Khaleesat ta girgiza kai tana murmushin karfin hali tace "Thank you, i am okay" Matar ta sake tafiya sai ga ta ta dawo da ruwa da orange drink, sai kuma wani drink daban duk a glass daban daban akan tray daya, ta duka tana mika ma Khaleesat ta dauki wanda take so, glass din ruwa kawai Khaleesat ta dauka ta mata godiya sannan ta sanar mata bazata ci abinci ba all throughout the flight don ma kar matar ta sake dawo mata, gani take tana cin abu zata yi aman da bata yi ba daxu, gyara kujeranta tayi ta kwanta ta lulluba da blanket din da jirgin yayi providing for business class passengers, nan da nan bacci ya dauketa, da za su sauka Turkey wajen karfe hudun asuba sai da wata Flight Attendance daban ta zo ta tasheta ta sanar mata jirgi zai sauka, Khaleesat ta mike zaune da kyar don ciwo kanta ke mata, tayi fastening seat belt dinta, bayan sun sauka Istanbul ta bi AJ da kallo har sai da ta daina hangosa sannan ta mike ta dau handbag dinta da waya ta bi bayansa tana tafiya da kyar leaving her Amenity kit behind, jiran awa biyu za su yi a Business Class waiting lounge na airport din kafin a canza masu jirgin da zai kai su Nigeria, ta riga AJ shigowa lounge din kilan masallaci ya tafi, ita ma tana ganin lokacin sallahn asuba yayi ta tafi tayi sannan ta dawo ta zauna a business lounge din, after like 15 mins sai gashi ya shigo, not far away from her ya zauna da ruwan gora a hannunsa, Ita dai ta jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune ta daura handbag dinta a kafarta, she is having a terrible headache a lokacin, after almost 30 mins of sitting wani Ι—an Nigeria ya dawo kusa da ita ya zauna, wanda shi ma daga nan Turkey zai je Nigeria a Business class, kuma jirginsu daya kamar yanda ta ga ticket irin wanda ta amsa bayan sun sauka Istanbul din a hannunsa shima, yana kallonta yayi mata sallama cikin nutsuwa, ta Ι—an kallesa sannan ta amsa, yace "Guess you are coming from America right?" Tace "Uhm" Yana kallon Flight ticket dinta yace "Oops you are having the same name as my Mum, can i call you Jiddah instead of the real name?" Khaleesat dake sauraronsa without looking at him tace "Ohk" Yana murmushi yace "Alright, are you traveling alone Jiddah?" Ta girgiza kai tace "No" Ya buda ido yace "Ohk with who?" Ta kalli direction din AJ, shi ma mutumin ya kallesa suka hada ido don kallonsu kawai Ajayn yake yana jin conversation dinsu, mutumin na murmushi ya tashi yaje ya gaisa da AJ sannan ya koma ya zauna, shikenan Khaleesat ta samu lafiya, don bai sake ce mata komai ba kawai danna wayarsa yake tayi tunda shi dai bai san ko waye Ajayn a gunta ba, daga karshe ma ya tashi ya bar wajen, at last aka fara boarding din jirgin da zai kai su Lagos Nigeria daga Istanbul, Usman ya juya ya kalli Khaleesat da ta mike tana rike da handbag dinta, har AJ ya wucesu sai kuma ya tsaya amma bai juyo ba, ita dai tana tafiya a hankali har ta isa inda yake tsaye sannan ya ci gaba da tafiya tana biye da shi, har jirgi ya tashi Usman dake zaune not far from Khaleesat but close to AJ bai ce mata komai ba, this time around ma dai bacci kawai tayi har zuwa Nigeria. Karfe hudu saura suka sauka Nigeria washegari Friday, ita dai Khaleesat tun da ta ganta Lagos bayan ta gama da Custom da Immigration ta fara tunanin kuma yanda zata yi, to ko dai kawai ta tafi gidan Aunty Farida tunda a nan Lagos take, to ko tace zata je bata da sim din da zata kirata don ba gane anguwan zata yi ba kuma bata da lambarta a kai balle ko waya ne ta ara ta kirata a airport din, sai kuma tayi tunanin kiran Ummanta tunda tana da numberta a kai sai tace ta turo mata number Aunty Farida, gun wata mata warce taga kamar Bahaushiya ce ta nufa, ta gaisheta sannan tace "Don Allah Aunty wayarki zaki ara min in Ι—an yi kira nawa ba caji" Matar ta fara kallonta daga sama har kasa, sai kuma ta bude handbag dinta ta ciro wayarta ta mika mata, Khaleesat ta amsa tace "Nagode" Dialing number Umma tayi ta kira taji a kashe, sosai jikinta yayi sanyi, ta kira har sau uku duk ana ce mata a kashe, a hankali ta zame wayar a kunnenta ta mika ma matar tace "Nagode, wayar ma a kashe yake" sai da matar tayi dialing wayar ta tabbatar eh a kashe din yake, kana ganin matar kasan she is not comfortable giving off her phone, Khaleesat na jan trolley dinta a hankali ta fito daga cikin airport din tana tunanin yanda zata yi, ko dai kawai ta tafi tashan da zata samu mota zuwa kano, since she have some money in her bank account, wani mutumi ne taga ya nufota, ya gaisheta da ladabi yana mata barka da zuwa, sannan ya nuna mata mota yace "Ke mu ke jira ki fito dama" She was looking at him with confusion, can ta kalli motar, shi ko har ya amshi Akwatunanta yayi booth din mota da su, sannan ya dawo ya bude mata back seat, zata yi magana sai ta hango AJ zaune front seat din motar, ta Ι—an yi jim, sai kuma ta fasa cewa komai, ta tafi ta shiga motar, hotel drivern ya kai su kasancewar next available flight to lagos na karfe bakwai na magrib ne, dakin da aka biya mata na downstairs, shi kuma AJ sama taga ya tafi, All this while kuma bai ce mata komai ba, ita dai tana son ce masa ta gode amma bai bar space din hakan ba, ko tsayawa bai yi ba balle tayi godiyan, sai da driver din ya amshi passport din ta da zai mata booking din jirgi tare da AJ zuwa kano sannan ya bar hotel din, bayan Khaleesat ta shiga dakin babu dadewa aka kawo mata lafiyayyen lunch, duk da tana jin yunwa bata iya ta ci da yawa ba she is just restless, taje bandaki ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, bayan ta saka wasu kayan tayi sallah sannan ta dau handbag ta bude zata ciro lip gloss dinta, a nan taga kudin da Jay ya saka mata, ta dinga kallon kudin ko kiftawa bata yi a sanyaye. Karfe shidda da yan mintuna drivern ya sake zuwa ya daukesu ya maida su airport, daga nan kuma suka hau jirgi zuwa garin kano, inda suka sauka airport din Aminu kano karfe tara saura na dare, this time around ma sai da drivern da ya zo daukan AJ ya sauka yayi mata magana tare da kai akwatunanta booth, ita dai tana ta tsaye don taxi kawai ta so dauka da zai kai ta gida, ganin drivern ya bude mata back seat ta karasa jiki a sanyaye ta shiga motar, sai da suka fita daga Airport din drivern ya kalleta ta madubi yace "Ranki shi dade wani anguwan za a ajiye ki?" Khaleesat ta Ι—an kalli AJ dake zaune gaban motar yana danna wayarsa, sai kuma ta kalli drivern tace "Inda zan je da nisa, kar in bata maku lokaci gashi dare yayi, duk inda ka samu kawai ka ajiye ni zan samu abun hawa" Sai a sannan AJ yace "Ce maki yayi sauri yake?" Khaleesat tayi shiru, sai kuma tace "Ni Mariri zan je" Driver yace "Toh Allah ya kai mu lafiya Hajiya" Bayan tafiyar kusan minti arba'in suka iso Maririn, A hankali Khaleesat dake kallon drivern tace "Zan iya sauka a nan sai in karasa cikin layin saboda kar ku shiga baku samu wajen juyawa ba...." Drivern yace "Layin baya bulla ne? In dai yana bulla babu damuwa za mu samu hanya in sha Allah" Tace "Toh shikenan, nagode" Nan ta nuna masa inda zai bi ya shiga unguwan, shi dai AJ kallon ikon Allah kawai yake without uttering a word, haka jama'an anguwan suka dinga bin motar da ya dalle ko ina da haske da kallo, ba ko wani mai mota bane zai yarda ya shiga hanyar nan da motarsa cause driving is uncomfortable there in baka yi hankali ba sai ka goge motarka, gashi gidan nasu can ciki ciki ne, at last dai tace "Kawai in ka samu waje a nan zan sauka, ga gidan can" Drivern yace "Toh shikenan Hajiya" Haka ya samu yayi parking motar, sannan ya sauka zai dauko mata akwatunanta a bayan booth, ta bude motar ta sauka tana kallon kofar gidansu hankalinta ya Ι—an kwanta ganin bata ga Babanta a kofar gidan ba, kan kace me yara yaran anguwan da suka ga ita ce a motar suka taho da gudu ana mata oyoyo, haka dai ta samu ta hadasu da akwatunanta sannan ta zaga zuwa side din da Ajay yake, tana wasa da gefen gyalenta ta kasa kallonsa tace "Thank you so much Allah ya saka da alkhairi" yace "Wanda ya hada ki jirgi daya da ni zaki ma godiya, Jay kenan" Sai a sannan ta Ι—an kallesa, bata dai ce komai ba ta juya tana tafiya a hankali ta bar wajen, godiya tayi ma drivern ta masa kwatancen unguwan da zai shiga wanda a nan zai samu hanyar billa zuwa titi, yayi mata godiya shima ya shiga mota sannan ta nufi cikin gidansu gabanta na faduwa, a hankali tayi raising sack din cement that was use as barrier between the door and inside of the house zata shiga cikin gidan ta ci karo da kanninta da suka fito yi mata oyoyo da gudu bayan yara sun shiga da akwatunan ta, a haka suka shiga cikin gidan tare tana Rungume da su, zazzaune taga kishiyoyin ummanta biyu da 'ya yansu rakacaa a tsakar gidan har a lkcn ba a sauke tuwon dare ba gashi ana neman karfe goma, kananun yaransu ne kawai suka taso yi mata oyoyo da gudu, muryar wata makociyarsu dake zaune cikin gidan taji tana cewa "Ikon Allah sannu da zuwa Amarya ashe dai kina hanya dama" Khaleesat dai kallonta kawai take jin abinda tace, taji kishiyoyin ummanta na cewa "Ai ko dai, kinga mu da muke gidan ma ko gaya mana ba ayi ba balle mu shiga mu fita tahowar nata ya fasu, kinsan haka aka maida mu a gidan, to ga dai ta mun ganta kamar an jefota, mun kuma yi murna" Khaleesat ta gaishesu without waiting for response ta shige dakin Ummanta, zaune ta ganta a bakin kofa Umma dake kallonta cike da damuwa tace "Khaleesat me ya samu wayarki kusan wata daya? Dama kina hanya shine Abdul din bai gaya mana ba?" Khaleesat ta rungumeta a hankali tace "Umma lalacewa wayar yayi" Umma ta dago kanta tana kallonta tace "To shi ya dauko ki a tashar jirgin?" Khaleesat ta sauke idonta tace "A'a" Muryar kawar Ummanta da taji a dakin yasa ta daga kai don bata ma san tana ciki ba, Khaleesat ta gaisheta da murmushi, Mama Salame ta amsa da fara'a tace "Ashe dai kina hanya amarya" Khaleesat tace "Amarya kuma Mama?" Mama Salame tace "Au shi Awdul din bai gaya maki ba dama, ai yau ana saukowa sallan juma'a aka daura auran ku"

 

 

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

[5/26, 9:48 AM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat ta kwala wani karan da ya gigita Ummanta da Mama Salame, Umma ta mike da sauri tana kallonta a kidime, haka ma Mama Salame da tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, menene haka Khaleesah?" kishiyoyin Umma duk suka yo dakin a guje su ma don Khaleesat bata fasa ihun da take kwalawa ba cikin tashin hankali take cewa "Wallahi bana son shi bazan iya zaman aure da shi ba, na shiga uku na lalace, don Allah Umma ku min rai ku rufa min asiri, wallahi bana son sa" Umma dai sake baki tayi tana kallon Khaleesat tashin hankali karara a fuskarta gashi ta kasa cewa komai, daya daga kishiyoyin Umma da ake kira Mama Shatu tana gyara zaninta da ya kusa kwancewa saboda gudun da suka yi tace "Ji wani gulma da kinibibi? Shi Abdul din ne da ya daukeki ya kai ki kasan turai karatu yayi ta kashe kudadensa ne baki so yau? A ajiye batun ubanki a gefe, ke abinda ya kashe maki yau ko kaf kasar da  uwarki ta baro za a siyar za a iya biyansa aka ce maki?" Ita ma daya Co-wive din da suke kira Mama Zubaida tace "A'a rainin wayo mana Shatu, gwara ai a rena mana hankali, don uwarta kasuwa ne nan da zata cika mana gida da Ζ™uwa, wannan ai iskanci ne da walakanci" Khaleesat bata fasa kuka da ihun da take a dakin Ummanta ba tana surutai ita kanta bata san takamaiman abinda take cewa ba tsabar tashin hankali, Kanninta Noor da Islam kuwa har sun fara kuka su ma a dakin, kan kace me har makota sun fara tururuwan shigowa gidan, aka tsaya cirko cirko bakin kofar dakin Ummanta ana salallami, Mahaifinta ne Malam Ali ya shigo gidan yana zazzare ido, shi ma ya karaso da sauri yana tambayar abinda ke faruwa a gidan, Mama Shatu ta tabe baki tace "Wai er da ta fi kowa ce ta sauka yau daga Amurka shine uwar ke sanar mata ai an daura aurensu da shi wanda ya kai ta waje karatu har ta dena ganin kowa da gashi, shine fa ta cika anguwa da ihu da koke koke wai ita bata son auren bazata zauna da shi ba, ga jama'a na ta shigowa an zata gobara muke, wannan ai tsabar sangarci da iya shege ne" Juyawa Malam Ali yayi ya nufi gun da ake ajiye itacen girki da sauri ya suri daya ya dawo ya nufo dakin Umma yana cewa "Ina take..." Matan makota dake tsakar gidan suka hau basa hakuri suna don Allah ya kyaleta, yaki sauraron kowa yana zazzare ido, Khaleesat na hangosa ta tafi bayan Ummanta da gudu tana kuka ta rungumeta, kanninta ma suka yi bayan Umma gaba daya suna kuka, Mama Salame ta tsaya tayi bake bake gabansa tace "Haba haba, haba Malam Ali, meye haka kake kokarin yi?" Yace "Salame ki bar ni dai inci malfar ubanta a wajen, mu zata tona ma asiri? Ni zata ja ma sabon bala'i da fitinan da ya girmeni?" Mama Salame tace "A'a wallahi baza ka doketa da wannan rafkeken icen ba ita ba jaka ba, mu je waje Malam Ali" Ita dai Umma kanta na kasa bata ce komai ba, haka Mama Salame ta samu ta tasa keyarsa ya fita daga dakin tana biye da shi, Mama Zubaida ta rike haΙ“a tace "Ikon Allah, mu muke ganin kinibibi iri iri a gidan nan, to in aka bibiya wani ta kyallara ido ta gani a Amurkan shine zata tona ma uban asirinsa da ke rufe, da can menene yasa ta hakura zata aurensa? Sai ranan da aka daura aure ta nemi tara mana mutan anguwa tace bata san zance ba? Yau ni nake ganin iskanci, to ta tsotsi nonon buzuwa ba dole ta iya makirci da kissa ba" Ita dai Khaleesat kuka kawai take a jikin Ummanta siblings dinta na kusa da ita suna taya ta, Mama Salame ta sake labulen dakin Umma duk don matan dake tsaye bakin kofar su kama gabansu, Umma ta juya tana kallon Khaleesat gaba daya ta kasa cewa komai, zamewa kasa Khaleesat tayi ta hade kanta da gwiwa tana kuka kamar ranta zai fita tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" a sanyaye Umma ta tafi gefen katifar dakin ta zauna ta kasa cewa komai. Karfe biyun dare Umma na zaune kan darduma da carbi a hannunta, Khaleesat ta tsallake kanninta ta fito daga cikin net din da take kwance bayan ta tuna ko isha'i bata yi ba, tunda Mama Salame ta daura mata net tace ta shiga ta kwanta wajen karfe sha daya take kwance duk da ba bacci take ba, don ko bacci barawo bata gani ba, amma tayi shiru cikin net din tunani iri iri na yawo a kanta, gaba daya ta ji kamar hawayenta ma ya kafe, har a lkcn babu maganar da ya hadata da Ummanta, tana jin jiri da zazzabi ta nufi kofa zata fita ta dauro alwala, Umma dai ta bi ta da kallo, bayan ta dauro alwalan ta dawo ta saka hijab dinta ta tada sallah, bayan ta idar tayi nafila raka'a biyu, tana zaune kan darduman ta jingina da bango tayi nisa tunanin da take, gani take kamar a mafarki ake sanar mata an daura mata aure da Abdul amma ta ki farkawa daga mummunan baccin nan har yanzu, muryar Ummanta yaji ta kirata a hankali, Khaleesat ta juya ta kalleta amma ta kasa amsawa, Umma ta mike ta koma kusa da ita ta zauna tana kallonta, cikin sanyin murya tace "Me ya faru kuma tsakaninki da Abdul din Khaleesat? Wani abun ya kara maki? Me yasa kika ce baki son auren?" Khaleesat ta fashe da kuka a hankali tace "Umma wallahi bana son sa, bazan iya zama da shi ba, in aka ce za a kai ni gidansa zan iya mutuwa wallahi, don Allah Umma ku taimakeni ku yi min rai" Umma ta kasa ce mata komai hawaye ya cika idonta ta fara gogewa da hijab dinta, Khaleesat ta daura kanta kan kafadar Ummanta tana kuka me tsuma zuciya tace "Don Allah ku taimakeni Umma, bazan iya ba wallahi" Umma ta rungumeta tana patting bayanta ita ma hawayen na sauka idonta amma bata iya ta ce mata komai ba, they sat there for almost 40 mins, jin tana sauke numfashi a hankali Umma ta gane bacci tayi, a haka Umma ta zauna wajen Khaleesat na jikinta don bata son tashinta har kusan lokacin sallahn asuba. Da safe wajen karfe tara Umma ta shigo dakinta rike da cup din kunu da kosai a roba, ta karasa kusa da Khaleesat dake kwance gefen katifarta ta ajiye mata sannan ta zauna cikin kwantar da murya tace "Ta so ki ci ko kadan ne Khaleesat" Khaleesat dai kallon cup din kunun kawai take, lkci daya hawaye ya cika idonta, Umma dai ta sunkuyar da kai, Islam ce ta shigo dakin rike da paracetamol da Umma ta aiketa ta siyo ma yayar tata, ta zauna kusa da Umma tace "Umma ga maganin na siyo ma Aunty" Umma ta amsa ta ajiye a gefenta tace "Tashi ki je ki karasa min aikin da na sa ki" Islam dake kallon Khaleesat ta mike a hankali ta fita daga dakin, Umma ta maida dubanta kan Khaleesat tace "So kike ki sa ma kanki wani ciwon ne Khaleesat nima ki sa min damuwa? Ki tashi ko kunun ne ki sha" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin rawan murya tace "Ni bazan iya sha ba Umma" a sanyaye Umma tace "Toh ya kike son in maki Khaleesat?" Umma ta kasa ci gaba hawaye ya fara sauka idonta ta dafe kanta, kuka kawai Khaleesat take tana kallon Ummanta, Umma ta dake tana share idonta tace "Ko wajen Nenne zaki sai ki gaya mata ki ji abinda zata ce, ni kin san babu abinda zan iya yi akan lamarin nan Khaleesat" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Umma ta mike a sanyaye ta fita daga dakin don juye mata ruwan wankan da ta dora mata a kan wuta yana ta tafasa, a haka ta ta dawo ta samu ta lallabata ta Ι—an sha kunun sannan ta tafi waje yin wanka, kafin ta fito har Umma ta fiddo mata kayan da zata sa tayi tagumi tana jiranta, karfin hali kawai Khaleesat take amma ji take kamar zata iya collapse at anytime, bayan ta shirya Umma tace "Amma bana son yan gidan nan su san inda zaki, kar su gaya ma Malam" Khaleesat ta jinginar da kanta da bango, a hankali tace "Umma bazan iya zuwa ni kadai ba don Allah ki rakani" Umma tayi shiru, can tace "To zan fita in shiga gidansu Er Lami in jira ki a can, bana son su ga mun fita tare, bayan na fita da minti goma kema sai ki fito" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Umma ta mike ta dau hijab dinta ta saka sannan ta dora nikab ta fita daga dakin, Su Mama Shatu da Mama Zubaida suna ta girka abincin siyarwansu da yaransu za su fita talla da shi, tace masu zata shiga makota sannan ta fita, duk suka bi ta da kallo sun tabe baki, Mama Shatu tace "Ma ji ma gani dai, a sanda ake mana fafa an tura 'ya kasar waje ga namu yaran a zube ai babu bakin cikin da ba a kuntsa mana ba" Mama Zubaida tace "Sun gana tattatse Ι—an mutane rana daya su fito su ce basu san zance ba, ke ina kika taΙ“a ganin anyi haka? Ai na so Malam ya rarrade shegiya jiya da daddare, to dai ba kanta kadai zata ja ma babban magana ba, har shi Malam din" Duk Khaleesat na jin su, ita dai tana zaune ta jinginar da kanta da bango tana sauke numfashi a hankali, bayan minti goma da fitar Ummanta ta tashi da kyar ta fiddo gogaggen Hijab dinta ta saka sannan ta dora Nikab ta fita daga dakin, tunda ta fito suke kallonta, a haka ta nufi hanyar fita daga tsakar gidan tana ji kamar iska zai kadata ta fadi. Gidan da Ummanta tace zata jirata ta nufa, ta samu Ummanta a tsakar gida tana jiranta yan gidan ma duk basa nan, Umma ta taso suka fita daga gidan, tafiyar kusan minti sha biyar ne zuwa gidan Nenne daga gidansu, Nenne ta ajiye tsintsiyar hannunta tace "Dawowa yayi da ita daga inda take karatun don an daura aure?" Umma ta zauna kan tabarman tsakar gidan ta cire Nikab din fuskarta ta gaida Nenne, Khaleesat ta zauna gefen Ummanta, Nenne ta amsa tace "Ai dama nace ko da ta dawo sai ta huta an kintsa ta kafin ayi maganar wata tarewa tunda yace baya bukatar taron komai, amma baza mu dau yarinya haka kawai ace an je kai ta ba" Umma dai tayi shiru bata ce komai ba, a hankali Khaleesat ta cire Nikab din fuskarta ta ajiye, Nenne ta Ι—an duka tana kallonta tace "Lapiya naga idanuwanta sun kumbura haka, me ke faruwa?" Umma ta sauke ajiyar zuciya ta kasa cewa komai, A fusace Nenne tace "Magana nake ku ka min shiru fa? Meye haka aka shigo min da ita da kumburarrun ido" Cikin rawan murya Khaleesat tace "Nenne ni bana son sa, bana son auren..." Nenne ta saki baki tace "Baki son auren kuma?" Khaleesat ta gyada mata kai hawaye wasu na bin wasu a kuncinta, Nenne ta nemi waje ta zauna tace "Atoh dai, ni dama shegen bai taΙ“a kwanta min ba, amma abun dubawa a nan shine na isa da Alin? Ashe ma ba er banza bace ni a gunsa kenan" Nenne ta mike ta shiga dakinta ba a dau lokaci ba ta fito ta dire wani babban ledan hannunta sannan ta bude tace "Kun dai ga duk wata shegiyar kyautarsa da yake kawo min ban taΙ“a amfani da ko daya ba duk na tara masa kayansa waje daya, ga atamfofinsa nan da turarurruka da tarkace, ba ruwana ban yi amfani da su ba, ke ma Zahra'u inda abunsa da kika san ya taΙ“a baki ki tattaro su waje daya, shi Ali ina ma yayi amfani da nasa shi ya sani, sai ya shiga kasuwa da wuri wuri" Ita dai Umma tayi shiru bata ce komai ba, Khaleesat kuwa kuka take a hankali, Cikin sanyin murya Umma tace "Kin mance abinda ke kasa ne Nenne, ai yanzu ba maganar wai abinda ya bamu bane damuwar" Nenne tace "Yo ina ruwana da abinda ke Ζ™asa, ko ina ruwan yarinya da abinda ke kasa? Sai a ma jikata auren dole kike nufi kenan? Ni fa tun asali katon mutumin nan bai min ba sam, ayi mutum ba fara'a ya shigo maka sandan sandan ya fita gansan gansan? A duba fa wannan lamari, da kyar kaga murmushinsa kamar rikakken Ι—an ta'adda da aka kusa yi ma preedom, yo wannan uban kudi na ubansa wa ma yasan ko ta'addancin suke da garkuwa da jama'a, hatta ruwan gidana gansamemen mutumin nan bai taΙ“a sha ba, yanda na ajiye masa haka yake barin min tsiyata bai san yarana mata ruwan gora suke siya min ba ya zata durawa nake, haka zai zauna maka kamar sarki yayi ta danna waya ga gidan er banza ya shigo, to ban isa da Ali ba kannensa mata ma basu isa da shi ba, shi kawai ta kansa yake a rayuwar nan baya duba makomar er da ya haifa a cikinsa, ko dan yaga yaran rakacaa an haifa masa ne ba kwantrol oho, gashi ba jin maganar yayyin uban nasa zai yi ba balle ince ku je ku samesu, in kuma muka ce mu tafi mu kai rahotu gidan yan sanda daga karshe mu za a kulle, to ni Ramatu ya zan yi? Amma dai ba komai zan aika a kira min Alin anjima, hatta batun daurin auren sai jiya da za a daura muke samun labari" A hankali Umma tace "Shi ma Malam din shekaranjiya da yamma suka kirasa suka sanar masa ga abinda suke so za ayi" Nenne tace "Tirrr, duk sun rainamu sun mayar da mu yan iska kawai, na tabbata shi kansa Alin bai taΙ“a rokon Awdul din naira biyar ba balle uban Awdul" Umma ta girgiza kai tace "Bai taΙ“a ba kam, jarabawa ce kawai Allah ya dora mana babu yanda mu ka iya" Nenne tace "A'a har da dai iskanci, ku baku da baki? ke da er taki baza ku iya kwatar en cin ku ba, ita kadai ce mace a gidan? Tun asali dama kin maida kanki gantalalliya a gidan" Umma dai tayi shiru, Nenne tace "Ko kuma kawai ku tafi gida zan daidaici lkcn da zai koma gida da magariba in taho gidan" Umma tace "Toh shikenan Nenne" a haka Khaleesat da Ummanta suka bar gidan bayan Nenne ta dama mata fura da nono ta tilastata ta sha. Khaleesat na kwance dakin Ummanta wajen karfe shidda na yamma, har zuwa sannan ta kasa cin komai tun bayan furan da ta sha gidan Nenne, tun da suka dawo gida take karatun qur'ani don ta rasa me ke mata dadi a duniyar kawai bata son tayi ta daga ma Ummanta hankali yasa ta hakura da kuka sai na zuci kawai da take yi, gaba daya taji duniyar yayi mata zafi, da ta tuna wai fa ita matar aure ce yanzu kuma matar Abdul, sai taji dama kawai Allah ya dau ranta ta huta, bayan taji she is exhausted da karatun qur'anin da take tayi shine ta kwanta gefen katifar Ummanta, tayi nisa tunanin da take jin hawaye na taruwa idonta ta mike zaune tana kallon Ummanta dake gyara kayan su Islam a dakin tace "Umma ina wayarki?" Umma ta kalleta tace "Ko sati ba ayi ba na nemeta na rasa an dauke a gidan nan" Khaleesat tayi shiru tana kallon Ummanta, sai kuma ta jawo handbag dinta a hankali ta bude ta ciro wayar da Jay ya bata duk da babu SIM card a ciki, she just want to do something that will keep distracting her from her worries, har zata shiga game sai kuma ta fasa ta shiga gallery din wayar, ta Ι—an yi jim na few seconds kafin ta bude hotunan, a hankali take flipping tana kallon each and every image of him and AJ, sai a sannan ta lura da kaman da suke yi even though it's not obvious, wani hotansu tare ta tsura ma ido ganinsu cikin shiga ta alfarma irin ta sarauta, ita dai tana ta kallon hoton babu ko kiftawa, sai kuma tayi flipping zuwa next image, haka ta dinga ganin ire iren hotunan, wani taga Jay shi kadai wani taga Ajay shi kadai, ko kuma ta gansu tare, with horses and so many things related to gidan sarauta, kashe wayar tayi a hankali ta mayar cikin jakarta ta ajiye jin muryan Babanta ya shigo gidan, ya Ι—aga labulen dakin Ummanta yana kallonta yace "Ki fita ga Abdul can ya zo yanxu" Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta dinga kallon Babanta bata ko kiftawa, Umma ta juya ta kallesa tace "Ta fita kuma Malam? Dama ana haka? Ai ina ga ba sai ya zo ba sai ya jira har zuwa sanda zata tare ko" Malam Ali da ya bude baki yana kallonta yace "Wato dai duk wani salon dauko min magana kun iya shi Zahra'u, in ya zo ta fita sai aka yi yaya? Addini ne ya haramta hakan ko kuwa shirmen ku? Kuma da kike batun tariya ko gobe yace yana bukatar ta tare mu muna da ja ne dama?" Umma tace "Ai ko muna da ja Malam, tunda baza mu dau yarinya haka kawai mu kai ta dakin miji ba, duka duka ma yaushe ta dawo kasar" Khaleesat ta fashe da matsanancin kuka tana jin kamar zuciyarta zai fashe ta huta, Babanta da ya bude baki yana kallonta yace "Ni kike neman tona ma asiri ko ko ya kike so inyi? Sabon magana za ku ja min ke da uwarki kenan? In ma ba yanzu za a tare ba tunda ya zo ai sai ki fita ku gaisa tunda ba haramun bane, in kun gaisa sai ki dawo cikin gida" Khaleesat taki cewa komai sai kuka take, Ya daka mata tsawa yace "Kar ki ga ina lallabaki don uwarki, zaki tashi ki fita ko sai na rarrade ki da icce" Khaleesat na kuka ta sauka daga kan gadon, Umma da hawaye ya cika idonta ta kauda kanta, Khaleesat ta dau Hijab dinta ta saka ta fita daga dakin tana kuka sosai, Kishiyoyin ummanta dake zaune tsakar gida duk suna sauraron abinda ke faruwa sai tabe baki suke, ganin Malam Ali ya bi bayan Khaleesat, Mama Shatu tace "To rakata wajen nasa zaka yi ne Malam?" Sai kuma ya juyo da sauri yace "Au to" Ya nufi Ι—an karamin dakinsa dake tsakar gidan, Mama Zubaida ta tabe baki tace "Ma ji ma gani dai" Khaleesat na fita kofar gida hawaye na sauka idonta taga motarsa wanda ke dauke da tinted glass yayi parking dai dai inda su AJ suka tsaya jiya, ko saukowa bai yi daga cikin motar ba, hawaye na bin fuskarta ta tafi ta tsaya kusa da motar taki budewa kuma tasan yana kallonta, after almost 5 mins taga ya sauke glass din motar yace "Ni zan sauko in same ki?" Ita dai taki kallonsa, kuma taki cewa komai, after few seconds ta bude gaban motar a hankali ta shiga amma ta ki kulle motar, yace "Sauron unguwan ku zaki cika min a motata, are you in ur right senses?" A hankali ta ja motar har sannan taki yarda ta kallesa ta kulle, gabanta sai faduwa yake don jin muryarsa take kamar ana tsira mata allura a kunne, Lokaci daya ta juya da sauri tana zaro ido ganin ya zuge glass din ya tada motar ya kara volume din sautin da yake ji sannan ya ja motar, a rikice ta fara kokarin budewa motar taji a kulle gam, ta kwala wani azababben kara tace "Na shiga uku na lalace, don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri ina zaka kai ni? Ka bude min in sauka...." Ko kallonta bai yi ba fuskarsa babu yabo babu fallasa yake driving dinsa idonsa na kan hanyar dake gabansa, ta rikosa da hannu biyu cikin gigicewa tana masa magiyan ya bude mata motar, bai yi wata wata ba ya sauke mata wani lafiyayyen back hand slap a fuska, sai da taji dumm na few seconds, lkci daya jin ta da ganinta ya dauke na Ι—an lokaci, duk da haka bata sake sa daga rikon da tayi masa ba tana kururuwan ya bude mata motar, ya fincikota ya jefar kan kujeran motar cikin kaushin murya yace "Kika sake taΙ“a ni sai na wanka maki wani marin" Lokaci daya duk jikin Khaleesat ya mutu saboda shock, ta dinga sauke numfashi da kyar idonta na ganin dishi dishi daga marin da yayi mata tana kallonsa, shi dai driving dinsa kawai yake fuskarsa babu yabo babu fallasa......

[5/26, 9:48 AM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Sai da Khaleesat taga sun bar unguwansu gaba daya sannan reality yayi hitting dinta ta kara fahimtar me Abdul ke da niyyar yi, she felt so helpless at this point, ta jinginar da kanta jikin kujeran motar hawaye masu zafi na sauka idonta ta kasa cewa komai, shi dai driving dinsa kawai yake bai ko kalleta ba, ganin tafiya kawai yake ta juya tana son ko hakuri ne ta bude baki ta basa amma tsoron kar ya sake marinta yasa ta kasa don babu alamar rahama a fuskarsa, ta rufe fuskarta da hijab din jikinta hawaye wasu na bin wani a idonta, tsabar tashin hankali da firgicin da ta shiga a wannan moment din kilan da za a duba jininta za a ga ya hau, bayan tafiyar kusan minti talatin taji ya tsaya cak, da sauri ta sauke Hijab dinta zuciyarta na bugawa tana kalle kallen inda suke, taga dai dai wani eatry ya tsaya, ita dai kallonsa take har sannan hawaye bai daina sauka idonta ba, ya sauka daga motar without looking at her ya kulle, ta bi sa da kallo har taga ya shiga gidan cin abincin, ta fashe da matsanancin kuka tana waige waigen wajen cikin tashin hankali, babban wajen cin abinci ne sosai, ga mutane suna ta kai kawo a gurin, glass din motar ta fara bubbugawa da hannunta amma taga nobody is noticing her, ta fara kalle kallen cikin motar taga bunch of keys da ya ajiye ta dauka da sauri ta fara bubbuga glass din motar da shi da karfi, hakan ya ja attention din wani mutumi da ya fito daga cikin eatry din zai shiga motarsa dake kusa da inda Abdul yayi parking, ita dai bata fasa bubbuga glass din ba tana kuka sosai tana cewa don girman Allah ya taimaketa, da alama baya ganin cikin motar saboda tinted glass din, ya zaga ta gaban motar yana duba ciki, ta dinga kuka tana cewa don Allah ya taimaketa, ba ta damu ko yana jin abinda take cewa ba ko baya ji ita dai kawai ya taimaketa, mutumin ya tafi ya taho da wani security dake wajen, dai dai nan wani soja da ya fito eatry din zai shiga motarsa shi ma ya karasa gun motar kan kace me attention din jama'an dake gurin gaba daya ya dawo kan motar Abdul, Khaleesat bata fasa kukan da take ba duk da ta samu relieve ganin mutanen da suka zagaye motar wasu na kokarin mata magana suna haska cikin motar da fitila, mutane duk suka tsaya aka yi cirko cirko a kusa da motar, ita dai kuka me sauti kawai take kamar ranta zai fita, babu wanda bazai ce sato ta aka yi a lkcn ba, bayan wasu mintuna Abdul ya fito daga Eatry din rike da abinda ya siyo, yana zuwa inda yayi parking yaga jama'a jikin motar ya tsaya yana kallon ikon Allah, Security din dake tsaye wajen don yaga sanda Abdul yayi parking ya shiga eatry din, ya kalli sojan dake tsaye yace "Ga me motar nan ya fito" Da wani expression Abdul yace "What happened?" Sojan yace "Bude motar ta sauko Malam" Abdul yace "Ban gane in bude mota ta sauko ba, matata ce a ciki" Sojan yace "Ai bamu mu sa ka ba, mota kawai zaka bude ta sauko, ba wani abun tashin hankali bane ai" Nan jama'an wajen suka dinga cewa ya bude motar suna hayaniya, Abdul ya bude motarsa da Key din hannunsa daga inda yake tsaye, Khaleesat na jin alamar yayi unlocking din motar ta bude ta sauko da sauri tana kuka, Sojan ne ya fara mata magana yana nuna mata Abdul yace "Waye wannan?" Ta fashe da matsanancin kuka muryarta na rawa tace "Ni ban san shi ba" Kallonta Abdul ya dinga yi da mamaki babu ko kiftawa, hayaniya sosai mutanen wajen suka hau yi sojan na kokarin calming dinsu, Sai kuma ya sake kallon Khaleesat yace "Baki san shi ba? To garin yaya kika shiga motarsa?" Tana shessheka tace "Kawai dauko ni yayi a unguwanmu wallahi, ni ban san shi ba" Tuni matasa yan zaman kashe wandon dake wajen suka fusata suka zagaye Abdul suna dure duren ashar suna kokarin fara mazgarsa, gaban Eatry din ya cika da jama'a an zo kallo wasu har sun fara video, with the intervention of the soldier and the security men da wasu responsible mutanen dake wajen aka saka Abdul cikin motar Sojan don tsaf sun kula matasan za su yi aika aika ne a wajen, wannan opportunity din Khaleesat tayi using cikin dubara ta sulale cikin jama'ar wajen without letting anyone to notice her don gaba daya hankalin mutane ya koma kan Abdul a wajen, a haka ta samu ta tsallaka titi ko waigawa bata yi ta afka wani layi, nan ma tayi ta tafiya da sauri da sauri gabanta na faduwa, duk inda taga alamar hanya ce haka ta dinga bi ba tare da tasan inda zata ba, tafiyar kusan minti arba'in tayi a kafa hawaye na zuba idonta, ko sanin unguwan da take bata yi ba, daga karshe tsabar yanda ciwon kai ya matsa mata ga jiri dake ta kwasarta ya sa ta samu gaban wani gida ta zauna ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka, tana ta zaune for almost 10 mins wani mutumi dake Ι—an nesa da ita yana zaune kofar gidansu ya mike ya nufota, don tun da ta shigo layin ta zauna ya ganta, sallama yayi mata ta dago kanta a tsorace, yace "Baiwar Allah lafiya dai ko?" Ta girgiza masa kai da kyar tana goge idonta tace "Bana jin dadi ne, kuma gida zan je" Yace "Ikon Allah, to ina ne gidan naku?" Without second thought tace "Hotoro" Yace "Hotoro? To bari in samo maki adaidaita sahu sai ya kai ki" Ta gyada masa kai cikin rawan murya tace "Nagode" Ya juya ya bar wajen, bayan wani minti goman sai gashi ya dawo cikin adaidaita sahu bayan yaje har bakin titi ya samo mata adaidaita sahun, ya sauko daga ciki yana kallonta yace "Toh ga adaidaita sahun na samo maki Hajiya" Tace "Nagode" Ta mike da kyar ta dafa adaidata sahun sannan ta shiga ciki, mutumin ya ciro wayarsa ya mika mata yana kallonta yace "Ki saka min lambarki sai inji ko kin isa gida lafiya" Ta girgiza masa kai a hankali tace "Matar aure ce" Mutumin yace "Ohh, na gane to, Allah ya tsare Hajiya, Allah ya baki lafiya, na biya sa kudinsa ba sai kin basa ba" Ta gyada masa kai tace "Nagode, Allah ya saka da alkhairi" yace "Ameen ya Allah" a haka mai adaidaita sahun ya bar layin. Har suka isa hotoro Khaleesat bata san sun iso ba, sai da me adaidaita sahu ya ankarar da ita, dai dai kofar gidan Gaje ta sa ya tsaya, ta sauka tayi masa godiya ta shige cikin gidan, nan gaban Gaje dake zaune tsakar gida ta zuba tana kuka kamar zata shide, Gaje tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Khaleesah? Me ya faru? daga ina kike haka?" Da kyar Gaje ta lallashi Khaleesat tayi shiru bayan lokaci me tsayi, sannan ta fara gaya mata abinda ya faru, Gaje ta saki salati a rikice tace "Mun shiga uku mun lalace, yanzu gidan yan sanda suka tafi da Awdul din kenan?" Cikin kuka Khaleesat tace "Ban sani ba nima" Gaje tace "To kuwa zaman gidan nan bai kama ki ba Khaleesah, yasan bayan gidanku baki da inda zaki taho a kano da ya wuce gidana ko gidan Nenne, wannan fa ba karamin kess bane, Awdul na zuwa nan ya ganki sai ya zata da hadin bakina kika yi abinda kika yi, ya sa yan sanda su kulleni in shiga uku" Cikin kuka Khaleesat tace "Toh ya zanyi yanzu Baaba Gaje?" Gaje ta mike ta figi gyalenta a igiya tace "Ta shi mu je" Jikin Khaleesat na rawa ta mike ta bi Gaje suka fita daga gidan, da kafa suka tafi gidan kawar Aunty Farida da ake ce ma Maman Fu'ad, bayan sun shiga gidan Gaje tayi mata bayanin duk abinda ke faruwa, Maman Fu'ad tunda ta rike haΙ“a har gaje ta gama bada labari bata iya tace komai ba, Gaje tace "Don haka ki rufa mana asiri Sadiyah ta kwana gidanki zuwa gobe a ga abinda hali zai yi" Maman Fu'ad ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat, gwalo ido tayi ganin jinin da ya kwanta idonta tace "Me ya samu idonki?" A hankali Khaleesat tace "Marina yayi" Maman Fu'ad ta saki salati tace "Mari?? Har sai da jini ya kwanta maki a ido? ga lebenki ma a fashe? A'a gaskiya tsinanne ne wannan mutumi" Gaje ta rike haΙ“a tana kallon idon Khaleesat sai kuma ta fashe da kuka tace "Yanzu wannan har mijin aure ne in ba don Ali ya cuceki ba, dubi fa tafin hannunsa a fuskarta?" Maman Fu'ad tace "Da kyar ma in baya shaye shaye wannan, gaskiya duk yanda za ayi a raba auren nan domin ceto yarinyar nan daga halaka, yanxun nan zan kira farida kuwa" Gaje ta rufe bakinta da sauri tace "Ki kirata kice mata me? Rufa mana asiri ba wanda yasan tana nan, ina me tabbatar maki kilan yanzu an tafi da Awdul din police station, kinga ai dole ya kai yan sandan gidansu Khaleesat don wanke kansa su tabbatar matarsa ce, in kuma yayi haka ai za a bazama nemanta ne a gari" Maman Fu'ad tace "Ba komai Gaje, ki tafi kawai ki kyaleta a nan kar su je can gidan naki baki nan" Gaje ta mike da sauri tace "Don Allah ki bata ruwan zafi in kina da shi tayi wanka" Maman Fu'ad tace "Kar ki ji komai Gaje" A haka Gaje ta bar gidan, yanda Khaleesat taga daren jiya wannan daren ma haka ta gansa, ga ciwon kai, ga ciwon ido, ga zazzabi duk ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, she don't even know who to speak to at this point. Washegari karfe tara Gaje ta shigo gidan, tun daga bakin kofa ta fara ba Maman Fu'ad labarin abinda ke faruwa tace "Sadiyah wajen karfe goma suka zo nemanta a gidana wallahi jiya har da shi Awdul din, ni dai jikina sai rawa yake don tare yake da yan sanda, yanxu haka daga can Mariri nake, uwarta na can hankalinta a tashe ko bacci bata yi ba sai koke koke, uban kuma yace da hadin bakin uwar Khaleesat ta gudu, babu kalan tijaran da Awdul bai yi ba jiya, keee abun dai babu kyau, ni dai hankalina ya tashi sosai, ina tsoron kar a gano ni na ajiyeta Awdul ya hadani da hukuma, shine na zo kawai ta shirya tayi hakuri ta koma gida duk abinda Allah yayi dai dai ne" Khaleesat dake jin duk abinda Gaje ke cewa ta fashe da matsanancin kuka tace "Don girman Allah kar ki ce masu ina nan Baaba Gaje, wallahi har duka zai iya min" Maman Fu'ad dai na tsaye da atamfar mutane da zata yanka ta hau kan keke ta kasa cewa komai sai zazzare ido take, ita ma tsoro take kar daga karshe ace ai a gidanta aka boye Khaleesat, ta ina zata fara ma Baban Fu'ad bayani in aka zo tafiya da ita gashi bai gari, Gaje tace "Toh ya kike so inyi Khaleesah, Awdul fa ya maida maganar nan babban magana wallahi, wai kin tozartasa a cikin mutane jiya kin sa an tafi caji opis da shi, ba ki da kowa da zai tsaya maki a lamarin nan sai Allah, Malam Ali na can kamar zai haukace shi ma ya saka uwarki a gaba sai ta fito dake" Khaleesat ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kukan, Gaje ta make hannun Fu'ad dake ta jan yakunannen gyalenta sannan ta ja kujeran tsugunno ta zauna ta rafka uban tagumi tace "Ni dai ban san kuma yanda zan maki ba Khaleesah, ina talaka da ni Awdul yasa a daureni wa zai cece ni, sai ma Kinga kallon da yake min jiya kamar bai yarda da ni ba" Khaleesat ta dago da kyar tana kallon Baaba Gaje hawaye na sauka idonta, Baaba Gaje dai zai zazzare ido take tace "Ni ban ma yarda bai sa CID unguwar nan su kula da shige da fice na ba, yanxu hka sai da na zaga kamar zan je Yan kaba sannan na taho gidan nan" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "Don Allah Baaba Gaje ki min alfarman dauko min jakana a can gidanmu" Baaba Gaje ta gwalo ido tace "Wani jakar?" Khaleesat tace "Karamin jakata, akwai wayata a ciki zanyi amfani da shi" Baaba Gaje tace "Um um Khaleesat, ta yaya zan dauko jaka ana gani na da rana tsaka?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Karamin jaka ne bai da girma, ko a gyalenki zaki iya boyewa don girman Allah ki rufa min asiri ki taimakeni Baba Gaje ki dauko min, har da kudi cikin jakan, zaki ga jakar kusa da akwatina a gefen katifar Umman mu" Maman Fu'ad dai sai baza ido take taji Khaleesat zata bar gidanta amma shiru bata ji ba, can dai tace "To ke ina kika nufa daga gidan nan yanzu?" Khaleesat na share hawayenta a hankali tace "Idan ta dauko min jakar zan san inda zan je in sha Allah" Maman Fu'ad ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, faridan ma bazata kira ba kar daga karshe a gane ita ta ajiye Khaleesat a gidanta ta shiga uku, Da kyar Baba Gaje ta yarda zuwa Mariri dauko jakan don duk a tsorace take, shi ma sai da Maman Fu'ad ta saka baki tunda taji ance in dai aka dauko jaka to za a bar gidanta, shi sa tayi ta lallaba Gaje taje Mariri dauko jakar, bayan kusan awa daya sai ga Gaje da jakar ta kudundunosa a gyalenta, Khaleesat ta amsa jakar ta bude ta ciro wayar Jay dake ciki, ta ga dollars din da ya bata suna ciki har sannan, Call log ta shiga sai kuma ta kalli Maman Fu'ad tace "Don Allah ki ara min wayarki bani da Sim card a nawa" Maman Fu'ad tace "Ai ko babu kati, tunda ga wayar Gaje bari in bada dari biyu a siyo sai ki saka a nata wayar ki kira" Nan duk dubara Maman Fu'ad tayi kar a ga Khaleesat tayi kira da wayarta idan bincike yayi bincike, Gaje ta mika ma Khaleesat wayarta ta fita ta amso mata katin dari biyun da Maman Fu'ad ta dauko ta bada, Khaleesat na saka katin ta fara dialing number Jay, ta kira yafi sau biyar sai dai kiran ya dawo mata alamar bai je ba, bata hakura ba still tayi ta kira baya shiga bata san ko katin ne yayi kadan ba kuma Number sa na Nigeria yake using a can din ma, wasu sabbin hawayen suka fara sauka idonta ta sake shiga call log din wayar tana scrolling slowly, number AJ ta gani shi ma Nigeria Line dinsa, ta Ι—an yi jim tana kallon number, sai kuma tayi dialing tana share hawayen dake zuba idonta, ringing ya fara yi har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan yayi picking, muryarta na rawa tace "Good Afternoon" Shiru yayi, kafin yace "Wacece?" Ta sauke idonta tace "Ni ce" Yace "Ke wa?" Da kyar tace "Plss i want to speak to you" Kawai ta fashe da kuka uncontrollably, shiru yayi for almost 15 seconds, can yace "What happened?" Tana kuka tace "I need to speak to you pls" Ya kara yin wani shirun, can yace "Where are you?" Tace "Hotoro" He still kept quiet for some seconds kafin yace "Address" Katse wayar Khaleesat tayi ta tambayi Maman Fu'ad address din unguwan, Maman Fu'ad ta gaya mata sannan ta tura masa ta message, Gaje dake zaune kan kujera tace "Wanene wannan din da kika kira?" Ita dai Khaleesat tayi shiru wasu hawayen na taruwa idonta, Baba Gaje tace "Gashi idon naki sai kara ja yake yi, wallahi makantar da ke kawai yayi niyyar yi matsiyacin nan" Bayan kusan 35 mins wayar Gaje ya fara ring, Gaje ta mika ma Khaleesat da sauri tace "Ko wanda kika kira ne?" Khaleesat ta amsa tana kallon wayar taga AJ ne ke kira, dagawa tayi yace "I am outside" Khaleesat ta ajiye wayar sannan ta kalli Maman Fu'ad tace "Aunty don Allah kina da Nikab?" Maman Fu'ad tace "Yaushe rabona da Nikab, bani da shi yanzu kam" Khaleesat ta mike tana rike da handbag dinta da wayar Jay ta fita daga gidan, not far away from the house yayi parking, yana jingine jikin motar ya rungume hannunsa looking at a different direction, tana tafiya a hankali ta nufesa tana kallonsa, tana isowa kusa da shi ya juya jin Footstep, ya gyara tsayuwarsa ya dinga kallon idonta babu ko kiftawa, she tried her best na ganin bata fashe da kukan da ya taho mata ba amma ta kasa daurewa ta hade kanta da jikin motar ta fara kuka har da shessheka.

[5/26, 9:21 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Ajay bai ce mata komai ba sai da tayi kukan me isarta don kanta tayi shiru, tana share idonta ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake har sannan, Calmly yace "He did all this to you?" Kai ta gyada masa wasu hawayen na taruwa idonta, yayi shiru for a while kamar me nazari, sai kuma yace "Ɗan kano ne?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "A ina yake a kano?" Muryarta na rawa tace "I don't really know" Zai yi magana Baba Gaje ta leko kofar gidan kamar munafuka tana zazzare ido, Ajay ya Ι—an sauke kansa ya gaisheta bayan sun hada ido da ita, fitowa tayi da sauri tana kalle kallen Unguwan tace "Lafiya lau Ι—an nan, wallahi yarinyar nan tana cikin mummunan masifa, bata da kowa sai Allah, ta dawo daga turai ta tarar an daura mata aure da lafcecen yaron nan Ι—an iska, dama kuma duk mun san Ι—an iska ne muke kauda kai tunda bamu da yanda za mu yi, ashe bai ma yi shawara da ita ba kansa tsaye ya taho ya samu iyayen da ya raina suka daura aure shekaranjiya, to tunda tace bata son auren in dai ba tsinannen mutumi ba ai sai ya kyaleta ga mata kaca kaca a duniya, wani mugun kuduri ne a ransa haka da yasa aka daura auren a gaggauce ko shiri babu? dubi fa abinda ya mata a fuska daga ya dannata a mota taki bin sa, yanxu haka duk ya baza CID a unguwan nan ana nemanta, sai kaga tijaran da yaje ya ma iyayen nata jiya da daddare, shi sa ka gan mu duk a tsorace" Tun da ta fara magana Ajay ke kallonta ko kiftawa baya yi, mamaki ne sosai kwance a fuskarsa, can ya kalli Khaleesat dake kuka kamar Baaba Gaje na dada tunzurata, ya sake kallon Gaje yace "Aure kuma Mama?" Gaje tace "Wallahi da gantalallun igiyoyinsa har uku a kanta yanxu haka, tun jiya ta gudo nan bayan ta samu ta tsere da kyar daga hannunsa" Gaje ta fashe da kuka tana matsar kwalla da gyalenta tace "Wallahi bata da kowa sai Allah, iyayen basu da bakin magana, basu da ta cewa, ni kuma ba kowa bace makociyarsu ce mun yi zaman Mariri tare kuma ni talaka ce, ni ko taimaka mata ne kayi ka kai ta wajen masu kare hakkin Ι—an Adam ta kai masu kukanta su kwato mata hakkinta da ake neman tauyewa" Har sannan Ajay ya kasa cewa komai, can ya bude gaban motarsa yana kallon Khaleesat, Baaba Gaje ta fara tura ta ciki tace "Maza shiga ku je ya kai ki ofishinsu, in ma rike ki za su yi su rikeki ki zauna har sai sun bi maki hakkin ki, amma kar ki ce nasan komai, kar ma ki saka ni a maganar" Khaleesat dai kuka kawai take ta shiga motar, Baba Gaje ta amshi wayarta dake hannunta ta kulle motar gbamm tace "Maza ku je" Ajay dai ya zaga ya bude driver seat ya shiga, Da sauri Baaba Gaje ta koma gate din Maman Fu'ad kamar ba daga kusa da motar ta taho ba, ta makale tana kallonsu har suka fita daga layin, driving kawai AJ yake idonsa a kan titi, gaba daya he look speechlesss, tunda ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba, ita dai Khaleesat ta rufe fuskarta da Hijab dinta saboda hasken rana dake damun idonta kuma tana tsoron kar ace su hadu da Abdul dan motar babu Tint, har sannan bata daina kukan tashin hankalin da take ba, after driving for 20 mins AJ ya kalli wayarsa dake vibrate, Number Jay ne ke kiransa, hakan ya sa ya rage tafiyar da yake ya gangara gefen titi yayi parking sannan ya dau wayar yayi picking ya kai kunne a hankali yace "Jay" Khaleesat ta zame hijab dinta daga fuska jin sunan da ya kira ta juya ta kallesa, Calmly taji yace "I am cool" tambayarsa Jay yayi ko ya bar Kano, AJ yace "Am still around, when are you leaving Maryland?" After few seconds AJ yace "Alright, we will talk later" Daga haka ya katse wayar ya ajiye ya jinginar da kansa jikin kujerar motar ya kafe titi da ido for almost 2 mins, can ya sake daukar wayarsa don duba available flight to Abuja ranan, yaga jirgin karfe uku kuma saura just few seats, National ID card dinta da passport dake motarsa tun ranan da suka dawo US da drivern su na Lagos ya amsa a wajenta don mata booking ticket to kano, ticket ya siya mata immediately na zuwa Abuja sannan ya ajiye wayar, Aunty na nan gidansu na kano sun zo biki shi sa ma bazai fara kai ta can gidan ba, juyawa Khaleesat tayi da kyar ta kallesa tana dafe kanta pleadingly tace "Kanwar Ummata tana Lagos, don girman Allah ka taimakeni i want to go to her plss" Shi dai kallonta kawai yake, Calmly yace "Where in Lagos?" Tace "Zan kira in tambayeta, amma bani da numberta ne" Ya ga alamar gaba daya she is confuse and in fear, yace "Ta yaya zaki kirata baki da numberta?" Wayarsa ta dauka da sauri ta shiga call logs dinsa tana duba number Baaba Gaje, dialing tayi yana fara ring Baaba Gaje ta daga, da sauri Khaleesat tace "Baaba Gaje don Allah number Aunty Farida za a duba a wayarki sai a turo ta wannan layin" Baba Gaje tace "Har kun je wajen kare hakkin Ι—an Adam din?" Khaleesat tace "Ki dai turo min don Allah yanxu Baaba" Baaba Gaje tace "Toh bari in je makota kin san ban san kan wayar ba ai" Khaleesat ta gyada kai da sauri tace "To ina jira" Katse wayar tayi ta jinginar da kanta jikin kujera tana sauke numfashi, wani dishi dishi take gani tsabar kuka, Shi dai Ajay idonsa na kan titi alamar dai kansa ya gama kullewa, ya kalli agogon wrist dinsa yaga karfe biyu ya gota, driving motar ya ci gaba da yi da tunani iri iri a ransa ya nufi wani eatry ya sauka ya shiga ciki, Khaleesat ta dinga bin haraban wajen da kallo sai kuma ta rufe fuskarta da Hijab dinta da sauri zuciyarta na bugawa, incident din jiya ne kawai ke dawo mata a kai as if she is hallucinating, sai taga kamar yanzu incident din ke faruwa yanda Abdul yayi parking ya fita daga mota ya shiga eatry, kan kace me ko ina na jikinta ya fara rawa taji kamar numfashinta zai dauke, ba a dau lokaci ba Ajay ya fito daga gidan cin abincin da leda a hannunsa, yana shiga motar ya ajiye ledan da sauri yana kallonta yace "Me ya faru??" Ta dago kanta hawaye caba caba a fuskarta, sai kuma ta kamo hannunsa gam tace "I just want to leave here plss, don Allah mu bar nan" Gaba daya ta dawo kamar warce ta zauce, ya fara bin area din da kallo tunaninsa ko Abdul din ta gani, can ya sake kallonta bayan ya zauna cikin motar, cikin nutsuwa yace "Look, stay calm.... You are safe" Ya gyara mata kujeran motar a hankali ta yanda zata Ι—an kwanta yana kallonta, sai da ya jira for almost 10 mins yaga ta Ι—an nutsu tana sauke numfashi a hankali, lkci lkci yake kallon agogonsa saboda flight din da yayi booking, after a while ya Ι—an duba fuskarta yaga kamar ta fara bacci, tada motar yayi ya bar wajen, still sai da ya kara tsayawa a pharmacy ya siya mata magunguna, ko kashe motar bai yi ba don kar ta ma san yayi parking, har yaje ya dawo kuma bacci take, ya ja motar ya dau hanyar airport hoping jirgin bazai tashi kafin su isa ba, suna isa airport din bayan yayi parking yaga saura minti sha biyar kawai jirgin ya tashi kamar yanda suka sa a ticket, tapping din kujeran motar yayi gently don har lkcn bacci Khaleesat take, a tsorace ta farka kamar yanda tayi daxu a eatry tana ganinsa kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, ya bude ledan abincin da ya siya ya ciro mata takeaway din ya bata yace "Take a little before ur flight..." Ba musu ta amshi abincin tana kallonsa a hankali tace "Lagos din zan je?" Yace "In kin je zaki gani" Sai da ya hade mata rai sannan ta ci abincin cokali uku da kyar tana hadiyewa kamar magani, ya bude drugs dinta ya bata ta amsa ta sha da ruwan goran hannunta, without looking at her ya mika mata wayarsa yace "Saka min number mutumin nan" Zaro ido tayi tana kallonsa, yace "Ko bakya ji na ne?" Kamar zata yi kuka tace "Kiransa zaka yi?" Yace "Amsa ki sa min number sa nace" Hannunta na rawa ta amshi wayar ta saka masa lambar Abdul don tana da shi a kanta, ya amshi wayar yana kallon number sannan ya ajiye wayar yace "Dama an mashi alkawarin aurenki ne?" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Um, tun shekara hudu da suka wuce" Shiru Ajay yayi yana kallonta, but because of how cautious he is with time kar tayi missing flight dinta kawai ya ciro Eye drop din da ya siya mata ya mika mata ta diga a idonta, tsoro ya sa ta kasa digawa don bata san wani kalan azaba zata ji ba, daga karshe ya fixge eye drop din babu yabo babu fallasa ya diga mata a cikin idon, tuni ya sauka daga motar yana jiran in ta gama kururuwan da take ta sauko, daga karshe ta sauko daga cikin motar tana rufe idon da Hijab dinta, dayan wayarsa ya mika mata wanda ticket dinta ke ciki, daga ita sai handbag din ta da wayarsa ta nufi cikin airport din tana waige waige kamar iska zai kadeta ta fadi, kana ganinta kasan ba dai dai ta ke ba, she is traumatized and stressed, tsoron Abdul kuma ya gama shigarta sosai, shi dai yana tsaye jikin motarsa yana kallonta har ya ga shigarta cikin airport din, komawa cikin motarsa yayi yana duba full name din Abdul ta true caller, wani number yayi dialing yana fara ring aka daga yace "Zan turo maka wata number yanxu, ina son kasa a bincika min location dinsa a cikin garin kano, i will be waiting for feedback" Bayan ya katse wayar ya ajiye ya jinginar da kansa da kujeran motar, yana nan zaune har bayan 20 mins just to be sure bata yi missing flight dinta ba kafin ya bar airport din, Khaleesat ta dinga bin cikin jirgin da kallo kamar idanuwanta za su fito jin anyi announcing za su tashi zuwa garin Abuja, Abuja kuma? Ita wa ta sani a Abuja? Hawaye ne ya cika idonta ta dinga waige waigen cikin jirgin, me yasa ya mata booking ticket din Abuja.

[5/28, 8:42 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat na zaune hall din da jama'a ke jiran Luggages dinsu a Arrival, duk da bata da kayan da zata jira amma rashin sanin inda ta nufa yasa ta zauna wajen tana bin kowa da kallo, tun 15 mins ago jirginsu ya sauka Abuja, daurewa kawai take don wani bacci take ji tare da gajiya, vibration taji a jakarta dake cinyarta alamar ana kiran waya, a hankali ta bude jakar ta ciro wayar da AJ ya bata tana kallon screen din, har ya katse bata daga ba don number kawai ta gani ba ayi saving ba bata san ko ta daga ba ko kar ta daga, kiran wayar da ake ta yi continuously ne yasa tayi picking tayi shiru tana sauraron me magana taji namiji ne, ta amsa sallaman da yayi mata, sannan yayi introducing kansa ya sanar mata shi ne ya zo daukanta Airport, a hankali Khaleesat tace "Ohk" Mikewa tayi ta fita daga Arrival din tana kalle kallen inda yace mata yake a Airport din, sai ga shi ya nufota bayan ya gane ita ya zo dauka, gaisheta yayi da ladabi yace "Babu kaya ko Hajiya?" Khaleesat ta gyada masa kai kawai, yace "Bismillah, Motar na can nayi parking" Tana biye da shi suka isa inda motar yake, ya bude mata back seat ta shiga ya kulle sannan ya zaga ya shiga driver seat, Ita dai Khaleesat ji tayi kawai yana sanar mata sun iso, bata san for how long suka yi tafiyar ba don bacci ne ya dauketa throughout the journey, gyara zama tayi tana kalle kallen compound din gidan da suke ciki, ta kalli Drivern da ya bude mata back seat, ta sauko a hankali tace "Nagode" Gida ne babba irin na zamani, tana biye da shi ya kai ta har zuwa Entrance din shiga babban parlon gidan ya danna bell, ba a dau lokaci ba aka bude kofar wata budurwa ce warce bazata wuce ta ba ta gani tsaye, da ladabi Drivern yace "Bakuwar da na dauko Airport ce Hajiya" Yarinyar ta Ι—an yi murmushi ta koma gefe tana kallon Khaleesat tace "Sannu da zuwa sister, come in" Khaleesat ta shiga parlon yarinyar ta kullo kofar tana nuna mata kujera ta zauna, bayan Khaleesat ta zauna yarinyar na kallonta tace "I am Inteesar" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta tace "Sunana Khaleesat" Yarinyar tace "Welcome Khaleesat, bari in ma Ammin mu magana" Daga haka ta juya ta bar parlon, after a while sai ga ta sun shigo parlon da wata dattijuwa that is in her middle 50, zamowa kasa Khaleesat tayi a hankali tana gaisheta, da fara'a matar da ake kira da Ammi ta dagota tace "A'a, koma kiyi zamanki kan kujera diyata" Khaleesat ta koma ta zauna kan kujeran, Matar ta zauna kusa da ita tace "Sannu da zuwa, ya hanya?" Khaleesat tace "Alhmdlh, ina yini" Ammi tace "Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?" Khaleesat tace "Suna lafiya lau" Ammi tace "Ai na zata tare da Yariman ku ke, ashe ke kadai ce" Ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta tayi shiru tana wasa da gefen hijab dinta, Ammi ta kalli Inteesar tace "Inteesar ki kai ta daki ta huta" Inteesar tace "Ohk" Tare suka tafi dakin Khaleesat na biye da ita, Ammi ta bi su da kallo. Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune daki tare da Inteesar da ta mayar da ita Television, ita dai a hankali take cin fruit salad din gabanta, tun zuwanta gidan in dai ta kalli Inteesar by mistake zata ga kallonta kawai take, da sun hada ido kuma sai Inteesar ta mata murmushi, Khaleesat wasn't bothered da kallon don farkon haduwarsu da Sophie haka ita ma take mata, tayi ta kallonta a makaranta ko gajiya bata yi kuma da sun hada ido sai ta mata murmushi, bayan sun zama best of friends ne Sophie ke gaya mata she is soo beautiful shi yasa bata gajiya da kallonta, sai bayan sun zama kawaye Sophie ta dena mata maganar kyanta, kuma dama da wuya taje waje bata ga mutane na kallonta ba, ba maza ba hatta yan uwanta mata haka suke kallonta, muryar Inteesar taji a hankali tace "You are Beautiful Khaleesat" Khaleesat ta Ι—an kalleta sai kuma ta mayar mata da murmushin da take mata kawai, Inteesar tace "Sosai fa" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "And you too Inteesar" Inteesar tayi dariya tace "A'a gaskiya ba kamarki ba, ni dai ina son mu zama frnds in baza ki damu ba, Ya Prince yace gobe zaki tafi Lagos da safe, don Allah ki bani numberki mu dinga zumunci ta waya, probably baza ki sake dawowa gidanmu ba" Sosai Khaleesat taji wani relieve ya zo mata bayan taji Inteesar tace zata tafi Lagos da safe, dama gaba daya hankalinta yayi gun kanwar Ummanta, Allah ya gani daurewa kawai take amma ita kadai tasan me take ji both mentally and physically, tana cikin tashin hankali sosai but she is trying her best to act normal, Khaleesat tace "Ohk amma nayi misplacing wayana ban yi welcome back, idan nayi zan amshi lambarki gun sa" Inteesar tace "Ohk to ba damuwa, amma zaki dade a lagos ne in kin je?" Khaleesat tace "Zan Ι—an yi kwana biyu a can in sha Allah" Inteesar tace "Akwai sisterna dake aure can, idan baza su dawo gida for New year ba in sha Allah zan je Lagos din so that i will meet with you there" Murmushi Khaleesat tayi tace "Toh shikenan Allah ya kai mu lafiya" Inteesar ta tashi ta bude press ta dauko mata kayan baccinta don dakinta ta kawo Khaleesat, bayan ta ajiye kayan gefen gado tace "You can change to this idan kinyi wanka, i will be back later" Khaleesat tace "Alright, thank you so much" Bayan few minutes da fitan Inteesar Khaleesat ta tashi a hankali ta tafi bandaki, da ta tuna auren Abdul dake kanta tashin hankalinta ninkuwa yake, sai da ta ci kukanta me isarta sannan tayi wanka ta fito daga bandakin, ta gama saka kayan da Inteesar ta bata kenan tana kokarin daure gashinta sai ga ta ta shigo dakin, Inteesar ta wara ido tace "Waow is all that ur hair Khaleesat?" Khaleesat dai ta mata murmushin karfin hali tana ci gaba da daure gashinta, Inteesar that was looking at the hair with fascination tace "Bari in baki Hair net" Hair net dinta ta dauko ta ba Khaleesat, Khaleesat ta amsa tace "Nagode sosai"  Washegari karfe tara da rabi na safe Khaleesat ta gama shiryawa tana jiran Drivern gidan, kayan Inteesar ne jikinta da yake yanayin jikinsu daya babu me cewa ba kayanta bane, tana zaune gefen gadon Inteesar duk da Hijab ne har kasa jikinta amma sanyi take ji sosai, ga AC dake dakin a kashe amma she is shivering, tun da ta tashi da asuba tasan she is not feeling okay, breakfast din ma da kyar ta sha shayi kawai, ko irish din bata ci ba balle bread, she is trying all possible best to look alright don kar ayi cancelling tafiyarta zuwa lagos yau, Mai aikin gidan ce ta Kwankwasa kofa ta sanar mata driver yana jiran ta, Khaleesat ta tashi da kyar ta dau handbag dinta ta fita daga dakin zuwa parlor, nan ta tarar da Ammi zaune, Khaleesat ta karasa ta duka kusa da ita tana mata godiya don sosai suka sake mata kamar da can sun taba saninta, daga karshe dai Inteesar ta bi su har Airport don rakiya, haka kawai jininta ya hadu da Khaleesat, ita kanta Khaleesat don bata cikin nutsuwarta ne amma she so much appreciate Inteesar's care toward her, a haka dai suka rabu kamar sun jima da sanin juna, Khaleesat ta shiga cikin airport din ta amshi boarding pass dinta don Ajay ya tura mata ticket ta Email din wayar da ya bata hade da hoton National ID dinta da yayi snapping tun karfe bakwai na safe, bayan ta amshi boarding pass dinta ta nufi Departure Lounge. Karfe sha biyu saura suka sauka garin Lagos, Khaleesat ta sauka a jirgi da taimakon wata mata don zazzabi ne sosai ya rufeta but she is still pretending to be fine, a haka suka fito Airport din daga Arrival matar na tambayarta za a zo daukanta ne ko Taxi xata hau, Kafin Khaleesat tace komai ta hango wani kamar AJ tsaye jikin wata mota yana danna wayarsa, sai da ta kifta ido ta bude to be sure he is the one she is seeing, ta kalli matar kusa da ita da kyar ta sanar mata yayanta ya zo daukanta, a haka suka rabu da matar, Khaleesat ta nufi inda ta hango Ajay, sae da ta iso kusa da motar ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Ina yini" Calmly yace "Ina wayar da na baki?" Jakar hannunta ta nuna masa tace "Yana ciki, na sa silent ne" Driver seat ya bude ya shiga sannan ya bude mata daya side din motar, zagawa tayi ta shiga ta jinginar da kanta ta lumshe ido, ya tada motar suka bar Airport din, Google map yayi ta using after almost 45 mins ride Khaleesat ta fara gane inda za su, amma kuma sae ko ina yayi mata sabo a area din ko don she is not stabilize ne bata dai sani ba, ta juya ta kallesa shi dai driving dinsa kawai yake with the assistant of his google map, at last suka shigo wani unguwa yayi parking ya dau wayarsa yayi dialing number, muryar Aunty Farida taji bayan anyi picking, Khaleesat taji kamar an yaye mata Ζ™aso tamanin cikin damuwarta jin muryar kanwar Ummanta, bayan few minutes sae ga ta ta fito daga cikin wani gate, tun da AJ ya hangota daga nesa ya fahimci da ita yake waya don kana ganinta ka ga Khaleesat,  yayi driving din motar har zuwa dai dai kofar gidan da ta fito, yana parking Khaleesat ta bude motar da sauri ta sauka da sauran last strength dinta ta nufi Aunty Farida ta fada jikita, Aunty Farida ta rikota da sauri kafin ta kai kasa, wata makociyarta ce ta taimaka mata suka rike Khaleesat suka shiga da ita cikin gidan, shi dai AJ na tsaye kusa da motarsa yana kallonsu har suka shiga ciki, sai kuma ya jingina da motarsa yana kallon yara dake wasa few houses away, wayarsa ya ciro jin yana ringing ganin me kiransa ya daga yace "Ya ake ciki?" Daga daya bangaren mutumin yace "Ranka shi dade sai daxu ya kunna wayar tasa, an kuma duba location din nasa yana cikin garin Abuja yanxu haka" AJ yayi shiru kafin yace "Ohk, i will get back to you nagode" Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa, sai ga Aunty Farida ta fito daga cikin gidan, yayi Ζ™asa da kansa ya gaisheta, ta amsa cikin sanyin murya tace "Sannu da kokari fa, Allah ya saka da alkhairi, mu shiga ciki sai mu yi magana ko" Bai ce mata komai ba ya bi bayanta zuwa cikin compound din, Compound ne me dauke da apartment uku self contain each, AJ ya tsaya daga balcony din apartment din bai shiga ba har sai da Aunty Farida ta kara lekowo ta masa magana sannan ya cire takalmansa ya shiga parlon ya zauna saman kujera yana kallon Khaleesat da ta juya baya kan 3 seater din da take kwance, Aunty Farida ta tafi kitchen dauko masa ruwa, ya ciro wayarsa yana dannawa absentmindedly, Sai ga Aunty Farida ta fito kitchen ta ajiye masa ruwan a kusa da shi sannan ta zauna, da damuwa tace "Sannu da kokari Junaid, Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai" AJ ya daga kansa ya kalleta yace "Amma dai kince bai san inda kike a lagos ba ko Aunty?" Aunty Farida tace "Gaskiya bai san nan gidan ba, tsohon gidan da na baro ne dai ya sani, shi ma wani lokaci ne da ta zo Lagos dubani bani da lafiya, ta zo da kwana uku sai ga shi shima ya zo, to yau wata hudu kenan da barina wancan Unguwan na dawo nan" Ajay dai yayi shiru idonsa a kasa, Aunty Farida tace "Kuma ba unguwa daya bane, shi wancan Unguwan da na baro a Ojota ne, daga can zuwa nan ma tafiya ce me zaman kansa, ba kuma wanda yasan nan na dawo" Ajay yace "Toh shikenan, jikinta da zafi ne?" Aunty Farida tace "Ehh na ji da zafi sosai gaskiya, makociyata da ta rike min ita muka shigo yanzu nurse ce, tace zata rubuta min magunguna in siyo mata" Ajay yace "Ohk, bari zan fita yanzu sai in siyo magunguna da allurai da drip ayi mata karin ruwa" Aunty Farida tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma baka sha ko ruwa ba Junaid" Ajay ya Ι—an yi murmushi yace "Bari in je in dawo dai" A haka ya fita daga parlon ya tafi pharmacy ya harhado mata magunguna da drip da allurai. Wata mace ce warce bazata wuce shekaru hamsin da bakwai ba zaune wani kantamemen parlor cikin isa, mai aikinta na duke gabanta tana yanke mata kumbar kafafuwanta, cikin fada take cewa "Banda ma naci irin naka dama ina kai ina er matsiyata? Er talakawa? Wanda cin yau da kyar na gobe da kyar, ai kai ba class dinta bane ta ko ina, you just stoop ur self so low Abdul, babu wanda ya isa da kai babu wanda zai baka shawara ka dauka, na rasa irin wannan taurin kai naka, tun asali i am against you marrying that poor wretched girl, kuma har gobe ba wai nayi na'am bane kawai bani da yanda zanyi da kai ne Babana, baka jin maganata ko na ubanka balle na yayarka, yanxu ina amfanin kaskantar da kai da matsiyaciyar tayi cikin talakawa yan uwanta a gaban gidan cin abinci, abu har police station, da mutuncinka da iliminka a maka haka? In zaka dau shawarata yanzu gwara kawai ka saketa case ya dawo sabo fil, uban me zaka ci da ita kuma bayan wannan abun da ta maka a idon duniya? Idan yarinya kake so ni duk inda zan shiga zan je in samar maka yarinya karama da ta fi ta komai kuma er gidan arziki ba tsiya ba, kai ko Nijar din ne ma ni sai in shirya inje da kaina in samo maka wata buzuwar er gidan arziki ba talakawa ba, kai ga ma er wata kawata shuwa Arab yanda kaga ita wannan da makale ma ita ma haka take tass da ita, ga gashi, sannan su ba talakawa bane" Wata matashiya ce er shekara 39 dake zaune parlon ita ma ta juya da sauri ta kalli warce ke magana tace "Momy ban gane abinda kike nufi ba? Wai nufinki ya saketa kenan?" A fusace Momyn tace "Toh uban me zai ci da ita idan bai saketa ba Meema? Er talakawa ce fa, a kanta aka fara kyau a duniya ne da bazai rabu da ita ba?" Warce ta kira da Meema ta girgiza kai tace "A'a wallahi Momy, ai idan ya rabu da ita yanzu ma ita da iyayenta ne suka ci riba, duk uban hidimar da yayi mata sai kice ya saketa daga karshe ko tausayinsa ba ki ji ba Momy? Ae wallahi bata isa ya saketa ba, ko don mu kuntata mata yanda ta kuntata ma Abdul baza mu yi fatan ya saketa ba, dole sai ta shigo gidan nan, balle shi ba mahaukaci bane da zae saketan, yarinyar da ya tura har America karatu duk don dai ta zama presentable cikin mutane kar a mana dariya daga karshe ta saka masa da wannan walakanci da tijara haka?" Abdul dake zaune parlon shi ma duk yana sauraronsu ya mike yace "In har aka ga na saketa to bana numfashi ne a duniya, kuma duk inda ma take zata dawo hannuna nan ba da jimawa ba kuwa, a nan ne zata gwammaci bata taΙ“a sanina a rayuwarta ba, i will make life a living hell for her" Momy ta tabe baki tace "Shi dama talaka ai bai gaji abun arziki ba, shi yasa babu ruwana da su ko da wasa, hanyar jirgi daban ta mota daban, kai ne da jajibe jajibenka kasa ubanka ya tafka asaran kusan miliyan dari akan matsiyaciyar yarinyar nan" Tuni Abdul ya fice daga parlon, Meema na kallon uwarsu tace "Ai ki ma dena maganar asaran miliyan dari Momy, don yanxu babu wannan zancen asaran nake ji" Momy dai ta tabe baki tana kallon me aikinta tace "Ke kar fa ki yanka ni inyi mugun bata maki rai yanzu, ya zaki dinga gaftare min naman yatsu" Hakuri mai aikin ta hau bata. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta Ι—an kishingida a 3 seater, hannunta rike da bowl din pepper soup din da Aunty Farida tayi mata, gaba daya ta kasa shan pepper soup din Offals din, don jinsa take kamar magani a bakinta gashi har sannan jikinta babu kwari ga ciwon kai, ta kalli drip din dake hannunta taga ko quarter bai yi ba amma har ta gaji ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, tun da AJ ya kawo magungunan da drip ya ajiye ya bar gidan har sannan bai dawo ba, ga abincinsa Aunty Farida ta zuba a cooler ta ajiye a tray tun daxu tana jiransa, tambayoyi ne da yawa ke yawo a zuciyar Aunty Farida tana son tambayar Khaleesat ko shine ya taΙ“a biya mata jirgi kwanaki da Umma bata da lafiya amma ganin yanayin da Khaleesat ke ciki ta bar duk tambayoyin nan a zuciyarta, Aunty Farida ta kalli Khaleesat tace "Ki daure ko kadan ne ki sha, ko in dama maki custard?" Khaleesat ta girgiza mata kai, dai dai nan aka kwankwasa kofar parlon, Aunty Farida ta mike ta yafa gyalenta sannan ta tafi ta bude kofar ta koma gefe, da sallama Ajay ya shigo parlon yana kallon Aunty Farida yace "Tare da brother dina muke" Aunty Farida tace "To ku shigo mana" a hankali Khaleesat ta gyara zamanta tana kallon Jay babu ko kiftawa, ganinsa ta dinga yi kamar a mafarki, Jay ya sauke kansa ya gaida Aunty Farida ta amsa da fara'a, sannan ya juya yana kallon Khaleesat shi ma babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta tana kallonsa, walking slowly ya karasa har cikin parlon ya duka gabanta yana kallonta, a hankali yace "Are you feeling better now Housemate?" Da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, and truly she felt better immediately, shi dai AJ na tsaye yana kallonsu, haka Aunty farida da ta koma one sitter a sanyaye ta zauna, Jay yayi kasa da murya still looking at her yace "Kiyi hakuri, everything will be okay soon in sha Allah, i promise you" Ta gyada masa kai da sauri with so much hope from his assurance, yana kallon bowl din hannunta Softly yace "Take ur soup" Ba musu ta dau spoon din ta fara shan pepper soup din a hankali, Aunty Farida ta kalli Ajay tace "Baka zauna ba Junaid" Ajay ya sauke kansa ya karasa 2 seater ya zauna, Aunty Farida ta share hawayen da ya cika idonta, da kyar tace "Mu ma duk ba da son ran mu bane abubuwan nan ke faruwa haka ba, ba mu da yanda za mu yi ne kawai, amma babu nagartattun iyayen da za su dau er su su ba Abdul aure"

[5/29, 8:10 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Sai da Jay yaga Khaleesat ta ci pepper soup din me Ι—an yawa sannan ya mike ya koma kusa da Ajay ya zauna, After a while Ajay yayi breaking din silence din da ya ziyarci parlon yace "Iya daukar nauyin karatun ta kawai yayi Aunty?" Aunty Farida zata yi magana wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin Umma ce ke kiranta ta wayar makociyarsu Sha'awa, ta mike ta tafi dakinta don daga wayar, Ajay dai kallon Khaleesat yake kamar yanda Jay ke kallonta don har ta shanye pepper soup din, ta ajiye bowl din kasa tana kokarin disconnecting drip din hannunta ta yanda zata bar cannula din kawai, Jay ya mike yana kallonta yace "What happened? Do u want to ease ur self" Da kyar tana girgiza masa kai tace "I think i want throw up" Ya karasa cikin hanzari yayi disconnecting din mata, ta tashi ta wuce bandakin Aunty Farida da sauri tana toshe bakinta, sai ga Aunty Farida ta fito daga daki, ta kalli inda Khaleesat ke zaune ganin bata nan ta kalli kofar bandaki, zaunawa kan kujera tayi a sanyaye tana kallonsu tayi kasa da murya tace "Yanzu yayata ta kirani wai an zo an tafi da mahaifin Khaleesat" Da mamaki Jay da Ajay ke kallonta, Ajay yace "Kamar yaya kenan?" A sanyaye Aunty Farida tace "Baban Abdul din ne yasa aka je aka tafi da shi" Daga Ajay har Jay kallonta suke with confusion da kuma mamaki, fitowar Khaleesat daga bandaki ya sa Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, bayan Khaleesat ta kwanta kan 3 sitter din Aunty Farida ta juya tana kallonta tace "Ko zaki shiga daki a maida maki drip din?" Khaleesat ta gyada mata kai don ita ma ta gaji da kwanciyar kujeran, Aunty Farida ta mike tace "Bari in ma makociyata magana sai ta sa maki a daki" Daga haka ta fita daga parlon, after some minutes sai ga ta ta dawo da Neighbor dinta Bayerabiya, Khaleesat ta tashi ta koma dakin Aunty Farida, Bayerabiyar ta bi ta ciki ta sa mata drip din, ita dai Aunty Farida na zaune parlor tayi nisa tunanin da take har makociyarta ta fito ta tafi, Aunty Farida ta kalli su Ajay a hankali tace "To abinda yayata ta kirani ta gaya min kenan" Ajay yace "So suke a biya su kudin makarantar da ya dinga biya mata?" Aunty Farida ta girgiza kai tace "Ai ba iya kudin makaranta bane Junaid" Ajay yayi shiru yana kallonta, Jay yace "Bayan makaranta akwai wani abu na kudi da ya hadasu ne?" Aunty Farida tace "Kwarai kuwa.... Shekarun baya Malam Ali wanda shi ne mahaifin Khaleesat dreban babban mota ne, babu garin da baya zuwa da kaya a babban mota a fadin Nigeria, kuma motar tasa ce iyaka idan kana da lodi ya kai maka kayan ka har inda kake so sannan ka biyasa, har Nijar ya sha shiga da kaya daga nan Nigeria ta haka ma ya hadu da yayata Aunty Zahra'u warce ita ce mahaifiyar Khaleesat, don mu yan Nijar ne mahaifinmu har yanzu yana nan da ransa mahaifiyarmu ce dai Allah yayi ma rasuwa shekarun baya, to bayan ya auri yayata ya kawota Kano Nigeria ya ajiyeta cikin matansa biyu, bayan en watanni da auren shine na dawo wajen yayata tunda bata da kowa a Nigeria bata san kowa ba, nan rikona ya dawo hannunta a lkcn ina da shekara goma, tsangwama da kyara babu irin wanda ban sha ba a wajen kishiyoyin yayata, gashi bata iya ce masu komai tunda ita ma ba barin ta suka yi ba, mace ce me hakuri da kauda kai, in zanyi magana ma sai ta hanani, a haka ta samu makaranta ta saka ni tunda a can kasarmu ina karatu aka daukoni aka kawo mata, sai da tayi shekara biyar a gidan sannan Allah ya bata Khaleesat, Mahaifin Khaleesat na da rufin asirinsa sosai don haka bamu rasa komai a gidan ba sai zaman lafiya da kwanciyar hankali daga kishiyoyinta wani lokacin har da uwar mijin, jifa jifa mu kan kai ziyara Nijar gun iyayenmu da yan uwa da abokan arziki, bayan shekaru 12 da auro yayata a lkcn Khaleesat na da shekara bakwai sai abokan Mijin yayata da yan uwa suka dinga zugasa akan ya shiga siyasa ya nemi wani babban mukami zai samu tunda yana da jama'a sosai, kuma ba laifi yayi karatunsa, matansa ma suka dinga zugasa akan ya fito takara, yayata tayi kokarin ganin ta hanasa tunda bai rasa komai ba a sana'arsa ta dreban mota amma ya ki, haka nan ya daga babban motarsa ya siyar har da sabon gidan da ya fara ginawa a nan Ɗan Ladi na sidi, ya daga duk en kadarorinsa ya siyar ya shiga siyasa gadan gadan, duk matansa sai da ya biya masu Hajji suka tafi da mahaifiyarsa, ya kuma canza ma ko wacce kayan daki, ya ba kowa kudi a hannu, kusan mutane goma sha biyu ya biya ma Hajji a lkcn, banda matasan anguwa da ya dinga biya ma kudin makaranta, yayi ta facaka da kudi a karshe dai ya zo ya fadi zabe, duk wa enda suka dinga zugasa suka juya masa baya, Allah ya rufa masa asiri bai amshi bashin banki da wani abokinsa ke ta zugasa ya amsa ba kasancewar da zaben ya gabato bashi da kudi kuma a hannu, bayan faduwarsa zabe aka shiga yanayi na babu a gidan, cin yau da kyar na gobe da kyar ga yayata na da cikin yan biyu, dama gidan da yake haya me tsada tuni ya saki bayan kudin hayan sun kare muka dawo mariri gidan gadonsa da ya bari a walakance don saura kadan ya kyautar lokacin da yake campaign sai gashi gidan ya mana amfani ya rufa mana asiri, makaranta me tsada da yaran gidan ke zuwa duk ya ciresu suka dawo gida suka zauna babu karatu, iyayen basu yi dubaran mayar da su na gwamnati ba, duk muka shiga mawuyacin hali a gidan, sai sanda ya samu mota yake lodin kaya ya kai a biyasa, sanda babu mota kuma sai dai kowa ta ciyar da kanta a gidan, yana kuma fin wata da watanni bai samu ko da karamar mota ba, duk ka zo kofar gida zaka gansa a zaune babu abun yi shi ma duk ya fita hayyacinsa, tuni yayata ta siyar da kayan dakinta ta fara sana'a ina taimaka mata, ta kuma saka Khaleesat a makarantar da zata iya biya don Khaleesat ta taso da kwazo da hazaka ga ta yarinya ce me shiga rai ko don kalan fatarta, don a unguwan ma gidan buzaye ake kiran gidanmu, hatta Mahaifinta kiri kiri yake nuna yafi sonta a cikin sauran yaransa wanda hakan ya ja mata tsana da kyara a gun matansa da yan uwanta, ko sanda yake da mota a hannu tsaraba na musamman yake ma Khaleesat ko da bazai yi ma uwarta ba, ana haka yayata ashe duk cinikin da nake sai ta kwasa ta ba mijinta a boye ban sani ba, ga dai matansa duk da hali na babu da aka shiga a gidan basu bar yayata ba, kullum cikin hada mata tuggu da makirci ake wajen miji da uwarsa, cikin wannan yanayi yayata ta haifi yan biyunta wanda haihuwan da tayi na karshe kenan a gidan, a lkcn matsaloli har sun fi na da, jarin yayata ya karye kuma babu wani abu da zata siyar ta tada jarin, ga jegon yan biyu tana yi ga yunwa wani lkcn sai makota ke zubo abinci a kawo mata, iyayenmu a can Nijar ba masu karfi ba balle su taimaka mana, a haka na bi wata kawata zuwa nan garin Lagos tana siyar da abinci, kafin nan fa nayi aure har na fito, duka auren bai cika shekara daya ba, na auri wani abokin mahaifin Khaleesat, karayar arziki na samun Malam Ali na dinga fuskantar matsaloli gun mutumin da matansa uku wanda daga karshe ya sakeni dama ba saboda Allah yayi auren ba saboda kalan fata ta yayi, ina nan Lagos nake tallafa ma yayata da 'ya yanta uku, don bana son karatun Khaleesat ya tsaya duk da ta samu Foundation sosai sbda makarantar da ubanta ya sa ta ma a sanda yake da rufin asirinsa yafi na sauran yan uwanta tsada, na zo Lagos da yan shekaru yayata ta kirani wataran wai gashi an ba Baban Khaleesat babban mota har zai kai kaya kudu, matsaloli sun fara warwarewa tunda har an biyasa kudin kai kayan kuma kudade masu tsoka gashi har ya siya kayan abinci masu yawa ya ajiye a gida, tace in Maza in dawo gida kawai dama ita hankalinta ba a kwance yake da zamana a lagos ina sana'a ba, a haka ta takurani har sai da na dawo Kano, a sannan Khaleesat na da shekaru sha shidda tana kuma gab da gama secondary don da wuri aka sakata a makaranta, na dawo da wasu kwanaki ranan muna zaune tsakar gida da yamma sai ga mahaifin Khaleesat an shigo mana da shi ranga ranga ko motsin kirki bai yi, wanda duk gaba daya mun zata yana hanyar kudu har ya kusa Lagos, ga dai shi babu ko kwarzanen ciwo a jikinsa kuma wa enda suka

kawosa suka ce ai daga asibiti ma aka taho da shi a can wajajen garin yarbawa, sannan kwanansa uku a asibiti aka sallamosa wasu mutane da suka shaidasa tunda dreba ne suka biya kudi aka sako sa a mota aka dawo da shi Kano, sosai hankalinmu yayi mugun tashi a wannan lokacin, sae da Malam Ali yayi kwana biyu a gida ana ta addu'a da neman taimako kafin ya farfado gaba daya har yana iya magana, nan fa yake sanar mana barayi ne suka kwace Trailer da kayan mutane a ciki bayan sun shaka masa wani farin abu, tashin hankalin da duk muka shiga bazai misaltu ba a lokacin, daga Trailern har kayan cikin trailern ya doshi miliyan dari da tamanin" Shiru Aunty Farida tayi tana goge hawayen dake zuba idonta, Jay that was shock ya kalli Ajay dake kallon Aunty Farida babu ko kiftawa jin zunzurutun amount din da ta kira, Aunty Farida na share idonta ta ci gaba tace "A ranan yan sanda sun kusa goma suka zo a motoci, a haka aka sa ma mahaifin Khaleesat ankwa ana jan sa kamar barawo aka fita da shi yaransa da matansa na kururuwa suna ihu, Khaleesat kadai ce bata motsa daga inda take zaune da littafi a hannunta ba sai hawaye kawai, duk aka cika kofar gidanmu babu masaka tsinke kai kace barawon gaske aka zo dauka, mun shiga tashin hankalin da baya faduwa a wannan rana, kuma duk mutanen da yayi ta biya ma Hajji a sanda yake da hali, da kuma mutanen da ya taimaka ma aka rasa wanda zai bi yaga inda ma aka kai sa, ashe daga kano Abuja aka nufa da shi, bayan dogon binkice aka gano trailern an yasar a wani gari an kuma juye duk kayan cikin trailern, dama me trailer daban, me kaya daban, adadin kayan cikin trailern kuma zai yi na miliyan dari, to ba kowa bane me kayan cikin trailern nan illa mahaifin Abdul, sam ba a yarda babu sa hannun Mahaifin Khaleesat a juye kayan cikin trailern ba, dama kuma yan unguwa na jin haushin ya samu lodi me yawa haka ya tafi kai kayan shi kadai ko yaron mota bai dauka ba, kuma ko wani dreba an san sa da yaron mota daya ko biyu, nan aka yi ta zuga baban Abdul akan kar ya yarda wai dama planning Baban Khaleesat yayi don ya taΙ“a yi ma wani mutum haka da dadewa yace barayi sun kwace kaya a hanya sai yafewa mutumin yayi, kuma wai don yaga Alhaji Musa wato mahaifin Abdul me kudi ne sosai shi yasa zai cucesa yace an sace kaya tunda yanxu ta kare masa bai da komai, kuma wallahi sharri ne ba haka Baban Khaleesat yake ba, bai cin kayan wani baya taΙ“a abu in ba nasa bane, beside bai taΙ“a sanin Baban Abdul ke da kayan ba sai da iftila'in ya faru sannan yaga me kayan, shi dai kawai ance masa ga Lodi zai kai lagos ya kuma amince tunda sana'ar sa kenan kuma kullum fatan samun Lodi yake, ko da babu zugin yan anguwa baban Abdul bai yi kama da mutumin da zai iya yafe kudinsa ba don kana ganinsa kasan bashi da mutunci bashi da kirki, sai da Mahaifin Khaleesat yayi wata uku bamu sa shi a idonmu ba kafin aka dawo da shi kano duk ya rame yayi baki ya dawo kamar ba shi ba, da kyar aka bari muka gansa a fursin da aka ajiyesa na nan kano, ranan duk bamu yi bacci ba bayan mun dawo gida, yayata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa don tun dauke mahaifin Khaleesat dama ta fara alalan siyarwa don mu rufa ma kanmu asiri saboda Ι—an jarin da nake da shi nima duk ya karye bani da komai, kafin ma a dawo da mahaifin Khaleesat kano sau uku muna zuwa gidan Alhaji Musa a Nassarawa GRA domin mu basa hakuri ko zai dubi halin da muke ciki ya taimaka a sake mana Baban Khaleesat amma duk aka mana koran kare, na farko masu gadi ne suka kore mu, na biyu Matarsa ranan ta rako baΖ™inta ta gan mu tayi mana cin mutunci ni da yayata da Baaba Gaje ta sa aka kore mu, na uku kuma Ι—an cikinsa Abdul wanda dama shi kadai ne namiji a 'ya yansa, ana haka aka shiga kotu ko lauya baban Khaleesat bashi da tunda bamu da halin daukan Lauya, rana na farko da aka kawo Malam Ali kotu daga prison ni da Khaleesat da kishiyar yayata Mama Shatu ce muka je kotun don sauraron karan, to a ranan Abdul yaje kotun shi ma a matsayin daya daga lauyoyin mahaifinsa ashe shi ma Lauya ne, sarai na ganesa da na gansa a kotun don ranan karshe da muka je gidansu har ce ma masu gadi yayi in muka sake dawowa su rike mu yan sanda ne za su zo su tafi da mu, zaman kotu da akayi a wannan rana babu wani positive outcome da ke nuni da cewar da nasara a case din, kwata kwata babu alamun nasara tunda Malam Ali ba kowa bane, kuma ba shi da kowa bai da komi, bashi da wanda zai tsaya masa, haka aka dage shari'ar zuwa wani watan shi kuma za a maidasa prison cikin motar da ta kawosa ko belinsa anki badawa, Khaleesat ta dinga kuka sosai a haraban kotun tana kallon yanda aka shigar da babanta motar prison, nima ina rungume da ita ina hawaye, wanda wannan ne ya ja hankalin Abdul da fitowarsa daga kotun kenan zuwa kanta, ba shi ba hatta sauran jama'an wajen kallonta suke, Alhaji Musa babban mutum ne kuma me kudi wannan yasa har da yan jaridu a haraban kotun, wani Ι—an jarida ya nufo mu yana tambayar me za mu iya cewa game da zaman da aka yi yau a kotu, budan bakin Khaleesat cikin kuka sai cewa tayi Allah ya saka ma babanta sharrin da aka masa, ina tunanin a nan ne Abdul ya fahimci er gidan wanda suke Ζ™ara ce Khaleesat, duka duka shekarunta sha shidda a sannan amma duk wanda ya kalleta sai ya sake kallonta, ranan ma tsautsayi yasa ta fito babu Nikab duk da ba a shiga da Nikab amma duk inda zata bata fita babu Nikab, in ma bata sa ba uwarta zata tilastata ta saka, hatta nima bana fita babu shi haka Mahaifiyarta saboda bakin jama'a, kun ji inda Abdul ya fara ganin Khaleesat, a sannan kuma kawai motarsa ya shiga, sai wani Lauya me zaman kansa ya nufo mu, ya ja mu gefe yana kokarin calming din Khaleesat, nan ya tambayeni me ya faru, me ya kawo mu kotu, nayi briefing din masa komai nima ina kuka, ya tambayeni zuwa yaushe aka daga karan, na sanar masa, yace to in basa lambata in sha Allah anjima zai kirani yaga abinda za ayi akan case din kuma mu kwantar da hankalinmu, ko wayar bani da shi a sannan, instead sai na basa Address din unguwanmu Mariri, ita dai kishiyar yayata na zaune karkashin bishiya tayi tagumi, a haka muka bar kotu ranan rai babu dadi muka koma gida, bayan kwana biyu ranan da yamma wajen karfe shidda muna zaune tsakar gida ko wacce na fafutukar abinda zata dora ta ciyar da kanta da yaranta, don yanzu kowa takai takai a gidan, kishiyoyin yayata har sun sake 'ya yan su maza kanana suna fita almajiranci suna ciyar da kansu, matan kuma a dora masu talla su tafi can bakin kasuwa, yayata dama ina taimaka mata muna sana'a a gida, kudin waec din Khaleesat ne dai muka kasa hadawa gashi saura kwanaki kadan a fara, kamar daga sama sai ga Mahaifin Khaleesat ya shigo gidan kamar an jefosa, Khaleesat ce ta fara ganinsa ta tafi da gudu ta rungumesa, duk muka mike tsaye a tsorace muna kallon ikon Allah baki bude, yayata tayi karfin halin tunkararsa tana tambayarsa daga ina yake haka, kar dai gudowa yayi daga gidan yari, Baban Khaleesat yace kawai shi dai ce masa aka yi an bada belinsa daxu da rana, sai gashi kuma aka daukosa aka kawo har gida aka ajiyesa, tsabar mamaki duk muka kasa cewa komai a tsakar gidan, yayata ta kama hannunsa hawaye cike idonta ta kai sa dakinsa don shi ma duk a firgice yake kana ganinsa kasan ba karamin wahala ya sha ba, sai a sannan yaran gidan suka fara ihu suna murnan dawowan mahaifinsu suna ta tsalle tsalle, sauran matan duk suka bi bayan yayata zuwa dakin Baban Khaleesat"

[5/30, 7:48 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat na zaune hall din da jama'a ke jiran Luggages dinsu a Arrival, duk da bata da kayan da zata jira amma rashin sanin inda ta nufa yasa ta zauna wajen tana bin kowa da kallo, tun 15 mins ago jirginsu ya sauka Abuja, daurewa kawai take don wani bacci take ji tare da gajiya, vibration taji a jakarta dake cinyarta alamar ana kiran waya, a hankali ta bude jakar ta ciro wayar da AJ ya bata tana kallon screen din, har ya katse bata daga ba don number kawai ta gani ba ayi saving ba bata san ko ta daga ba ko kar ta daga, kiran wayar da ake ta yi continuously ne yasa tayi picking tayi shiru tana sauraron me magana taji namiji ne, ta amsa sallaman da yayi mata, sannan yayi introducing kansa ya sanar mata shi ne ya zo daukanta Airport, a hankali Khaleesat tace "Ohk" Mikewa tayi ta fita daga Arrival din tana kalle kallen inda yace mata yake a Airport din, sai ga shi ya nufota bayan ya gane ita ya zo dauka, gaisheta yayi da ladabi yace "Babu kaya ko Hajiya?" Khaleesat ta gyada masa kai kawai, yace "Bismillah, Motar na can nayi parking" Tana biye da shi suka isa inda motar yake, ya bude mata back seat ta shiga ya kulle sannan ya zaga ya shiga driver seat, Ita dai Khaleesat ji tayi kawai yana sanar mata sun iso, bata san for how long suka yi tafiyar ba don bacci ne ya dauketa throughout the journey, gyara zama tayi tana kalle kallen compound din gidan da suke ciki, ta kalli Drivern da ya bude mata back seat, ta sauko a hankali tace "Nagode" Gida ne babba irin na zamani, tana biye da shi ya kai ta har zuwa Entrance din shiga babban parlon gidan ya danna bell, ba a dau lokaci ba aka bude kofar wata budurwa ce warce bazata wuce ta ba ta gani tsaye, da ladabi Drivern yace "Bakuwar da na dauko Airport ce Hajiya" Yarinyar ta Ι—an yi murmushi ta koma gefe tana kallon Khaleesat tace "Sannu da zuwa sister, come in" Khaleesat ta shiga parlon yarinyar ta kullo kofar tana nuna mata kujera ta zauna, bayan Khaleesat ta zauna yarinyar na kallonta tace "I am Inteesar" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta tace "Sunana Khaleesat" Yarinyar tace "Welcome Khaleesat, bari in ma Ammin mu magana" Daga haka ta juya ta bar parlon, after a while sai ga ta sun shigo parlon da wata dattijuwa that is in her middle 50, zamowa kasa Khaleesat tayi a hankali tana gaisheta, da fara'a matar da ake kira da Ammi ta dagota tace "A'a, koma kiyi zamanki kan kujera diyata" Khaleesat ta koma ta zauna kan kujeran, Matar ta zauna kusa da ita tace "Sannu da zuwa, ya hanya?" Khaleesat tace "Alhmdlh, ina yini" Ammi tace "Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?" Khaleesat tace "Suna lafiya lau" Ammi tace "Ai na zata tare da Yariman ku ke, ashe ke kadai ce" Ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta tayi shiru tana wasa da gefen hijab dinta, Ammi ta kalli Inteesar tace "Inteesar ki kai ta daki ta huta" Inteesar tace "Ohk" Tare suka tafi dakin Khaleesat na biye da ita, Ammi ta bi su da kallo. Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune daki tare da Inteesar da ta mayar da ita Television, ita dai a hankali take cin fruit salad din gabanta, tun zuwanta gidan in dai ta kalli Inteesar by mistake zata ga kallonta kawai take, da sun hada ido kuma sai Inteesar ta mata murmushi, Khaleesat wasn't bothered da kallon don farkon haduwarsu da Sophie haka ita ma take mata, tayi ta kallonta a makaranta ko gajiya bata yi kuma da sun hada ido sai ta mata murmushi, bayan sun zama best of friends ne Sophie ke gaya mata she is soo beautiful shi yasa bata gajiya da kallonta, sai bayan sun zama kawaye Sophie ta dena mata maganar kyanta, kuma dama da wuya taje waje bata ga mutane na kallonta ba, ba maza ba hatta yan uwanta mata haka suke kallonta, muryar Inteesar taji a hankali tace "You are Beautiful Khaleesat" Khaleesat ta Ι—an kalleta sai kuma ta mayar mata da murmushin da take mata kawai, Inteesar tace "Sosai fa" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "And you too Inteesar" Inteesar tayi dariya tace "A'a gaskiya ba kamarki ba, ni dai ina son mu zama frnds in baza ki damu ba, Ya Prince yace gobe zaki tafi Lagos da safe, don Allah ki bani numberki mu dinga zumunci ta waya, probably baza ki sake dawowa gidanmu ba" Sosai Khaleesat taji wani relieve ya zo mata bayan taji Inteesar tace zata tafi Lagos da safe, dama gaba daya hankalinta yayi gun kanwar Ummanta, Allah ya gani daurewa kawai take amma ita kadai tasan me take ji both mentally and physically, tana cikin tashin hankali sosai but she is trying her best to act normal, Khaleesat tace "Ohk amma nayi misplacing wayana ban yi welcome back, idan nayi zan amshi lambarki gun sa" Inteesar tace "Ohk to ba damuwa, amma zaki dade a lagos ne in kin je?" Khaleesat tace "Zan Ι—an yi kwana biyu a can in sha Allah" Inteesar tace "Akwai sisterna dake aure can, idan baza su dawo gida for New year ba in sha Allah zan je Lagos din so that i will meet with you there" Murmushi Khaleesat tayi tace "Toh shikenan Allah ya kai mu lafiya" Inteesar ta tashi ta bude press ta dauko mata kayan baccinta don dakinta ta kawo Khaleesat, bayan ta ajiye kayan gefen gado tace "You can change to this idan kinyi wanka, i will be back later" Khaleesat tace "Alright, thank you so much" Bayan few minutes da fitan Inteesar Khaleesat ta tashi a hankali ta tafi bandaki, da ta tuna auren Abdul dake kanta tashin hankalinta ninkuwa yake, sai da ta ci kukanta me isarta sannan tayi wanka ta fito daga bandakin, ta gama saka kayan da Inteesar ta bata kenan tana kokarin daure gashinta sai ga ta ta shigo dakin, Inteesar ta wara ido tace "Waow is all that ur hair Khaleesat?" Khaleesat dai ta mata murmushin karfin hali tana ci gaba da daure gashinta, Inteesar that was looking at the hair with fascination tace "Bari in baki Hair net" Hair net dinta ta dauko ta ba Khaleesat, Khaleesat ta amsa tace "Nagode sosai"  Washegari karfe tara da rabi na safe Khaleesat ta gama shiryawa tana jiran Drivern gidan, kayan Inteesar ne jikinta da yake yanayin jikinsu daya babu me cewa ba kayanta bane, tana zaune gefen gadon Inteesar duk da Hijab ne har kasa jikinta amma sanyi take ji sosai, ga AC dake dakin a kashe amma she is shivering, tun da ta tashi da asuba tasan she is not feeling okay, breakfast din ma da kyar ta sha shayi kawai, ko irish din bata ci ba balle bread, she is trying all possible best to look alright don kar ayi cancelling tafiyarta zuwa lagos yau, Mai aikin gidan ce ta Kwankwasa kofa ta sanar mata driver yana jiran ta, Khaleesat ta tashi da kyar ta dau handbag dinta ta fita daga dakin zuwa parlor, nan ta tarar da Ammi zaune, Khaleesat ta karasa ta duka kusa da ita tana mata godiya don sosai suka sake mata kamar da can sun taba saninta, daga karshe dai Inteesar ta bi su har Airport don rakiya, haka kawai jininta ya hadu da Khaleesat, ita kanta Khaleesat don bata cikin nutsuwarta ne amma she so much appreciate Inteesar's care toward her, a haka dai suka rabu kamar sun jima da sanin juna, Khaleesat ta shiga cikin airport din ta amshi boarding pass dinta don Ajay ya tura mata ticket ta Email din wayar da ya bata hade da hoton National ID dinta da yayi snapping tun karfe bakwai na safe, bayan ta amshi boarding pass dinta ta nufi Departure Lounge. Karfe sha biyu saura suka sauka garin Lagos, Khaleesat ta sauka a jirgi da taimakon wata mata don zazzabi ne sosai ya rufeta but she is still pretending to be fine, a haka suka fito Airport din daga Arrival matar na tambayarta za a zo daukanta ne ko Taxi xata hau, Kafin Khaleesat tace komai ta hango wani kamar AJ tsaye jikin wata mota yana danna wayarsa, sai da ta kifta ido ta bude to be sure he is the one she is seeing, ta kalli matar kusa da ita da kyar ta sanar mata yayanta ya zo daukanta, a haka suka rabu da matar, Khaleesat ta nufi inda ta hango Ajay, sae da ta iso kusa da motar ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Ina yini" Calmly yace "Ina wayar da na baki?" Jakar hannunta ta nuna masa tace "Yana ciki, na sa silent ne" Driver seat ya bude ya shiga sannan ya bude mata daya side din motar, zagawa tayi ta shiga ta jinginar da kanta ta lumshe ido, ya tada motar suka bar Airport din, Google map yayi ta using after almost 45 mins ride Khaleesat ta fara gane inda za su, amma kuma sae ko ina yayi mata sabo a area din ko don she is not stabilize ne bata dai sani ba, ta juya ta kallesa shi dai driving dinsa kawai yake with the assistant of his google map, at last suka shigo wani unguwa yayi parking ya dau wayarsa yayi dialing number, muryar Aunty Farida taji bayan anyi picking, Khaleesat taji kamar an yaye mata Ζ™aso tamanin cikin damuwarta jin muryar kanwar Ummanta, bayan few minutes sae ga ta ta fito daga cikin wani gate, tun da AJ ya hangota daga nesa ya fahimci da ita yake waya don kana ganinta ka ga Khaleesat,  yayi driving din motar har zuwa dai dai kofar gidan da ta fito, yana parking Khaleesat ta bude motar da sauri ta sauka da sauran last strength dinta ta nufi Aunty Farida ta fada jikita, Aunty Farida ta rikota da sauri kafin ta kai kasa, wata makociyarta ce ta taimaka mata suka rike Khaleesat suka shiga da ita cikin gidan, shi dai AJ na tsaye kusa da motarsa yana kallonsu har suka shiga ciki, sai kuma ya jingina da motarsa yana kallon yara dake wasa few houses away, wayarsa ya ciro jin yana ringing ganin me kiransa ya daga yace "Ya ake ciki?" Daga daya bangaren mutumin yace "Ranka shi dade sai daxu ya kunna wayar tasa, an kuma duba location din nasa yana cikin garin Abuja yanxu haka" AJ yayi shiru kafin yace "Ohk, i will get back to you nagode" Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa, sai ga Aunty Farida ta fito daga cikin gidan, yayi Ζ™asa da kansa ya gaisheta, ta amsa cikin sanyin murya tace "Sannu da kokari fa, Allah ya saka da alkhairi, mu shiga ciki sai mu yi magana ko" Bai ce mata komai ba ya bi bayanta zuwa cikin compound din, Compound ne me dauke da apartment uku self contain each, AJ ya tsaya daga balcony din apartment din bai shiga ba har sai da Aunty Farida ta kara lekowo ta masa magana sannan ya cire takalmansa ya shiga parlon ya zauna saman kujera yana kallon Khaleesat da ta juya baya kan 3 seater din da take kwance, Aunty Farida ta tafi kitchen dauko masa ruwa, ya ciro wayarsa yana dannawa absentmindedly, Sai ga Aunty Farida ta fito kitchen ta ajiye masa ruwan a kusa da shi sannan ta zauna, da damuwa tace "Sannu da kokari Junaid, Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai" AJ ya daga kansa ya kalleta yace "Amma dai kince bai san inda kike a lagos ba ko Aunty?" Aunty Farida tace "Gaskiya bai san nan gidan ba, tsohon gidan da na baro ne dai ya sani, shi ma wani lokaci ne da ta zo Lagos dubani bani da lafiya, ta zo da kwana uku sai ga shi shima ya zo, to yau wata hudu kenan da barina wancan Unguwan na dawo nan" Ajay dai yayi shiru idonsa a kasa, Aunty Farida tace "Kuma ba unguwa daya bane, shi wancan Unguwan da na baro a Ojota ne, daga can zuwa nan ma tafiya ce me zaman kansa, ba kuma wanda yasan nan na dawo" Ajay yace "Toh shikenan, jikinta da zafi ne?" Aunty Farida tace "Ehh na ji da zafi sosai gaskiya, makociyata da ta rike min ita muka shigo yanzu nurse ce, tace zata rubuta min magunguna in siyo mata" Ajay yace "Ohk, bari zan fita yanzu sai in siyo magunguna da allurai da drip ayi mata karin ruwa" Aunty Farida tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma baka sha ko ruwa ba Junaid" Ajay ya Ι—an yi murmushi yace "Bari in je in dawo dai" A haka ya fita daga parlon ya tafi pharmacy ya harhado mata magunguna da drip da allurai. Wata mace ce warce bazata wuce shekaru hamsin da bakwai ba zaune wani kantamemen parlor cikin isa, mai aikinta na duke gabanta tana yanke mata kumbar kafafuwanta, cikin fada take cewa "Banda ma naci irin naka dama ina kai ina er matsiyata? Er talakawa? Wanda cin yau da kyar na gobe da kyar, ai kai ba class dinta bane ta ko ina, you just stoop ur self so low Abdul, babu wanda ya isa da kai babu wanda zai baka shawara ka dauka, na rasa irin wannan taurin kai naka, tun asali i am against you marrying that poor wretched girl, kuma har gobe ba wai nayi na'am bane kawai bani da yanda zanyi da kai ne Babana, baka jin maganata ko na ubanka balle na yayarka, yanxu ina amfanin kaskantar da kai da matsiyaciyar tayi cikin talakawa yan uwanta a gaban gidan cin abinci, abu har police station, da mutuncinka da iliminka a maka haka? In zaka dau shawarata yanzu gwara kawai ka saketa case ya dawo sabo fil, uban me zaka ci da ita kuma bayan wannan abun da ta maka a idon duniya? Idan yarinya kake so ni duk inda zan shiga zan je in samar maka yarinya karama da ta fi ta komai kuma er gidan arziki ba tsiya ba, kai ko Nijar din ne ma ni sai in shirya inje da kaina in samo maka wata buzuwar er gidan arziki ba talakawa ba, kai ga ma er wata kawata shuwa Arab yanda kaga ita wannan da makale ma ita ma haka take tass da ita, ga gashi, sannan su ba talakawa bane" Wata matashiya ce er shekara 39 dake zaune parlon ita ma ta juya da sauri ta kalli warce ke magana tace "Momy ban gane abinda kike nufi ba? Wai nufinki ya saketa kenan?" A fusace Momyn tace "Toh uban me zai ci da ita idan bai saketa ba Meema? Er talakawa ce fa, a kanta aka fara kyau a duniya ne da bazai rabu da ita ba?" Warce ta kira da Meema ta girgiza kai tace "A'a wallahi Momy, ai idan ya rabu da ita yanzu ma ita da iyayenta ne suka ci riba, duk uban hidimar da yayi mata sai kice ya saketa daga karshe ko tausayinsa ba ki ji ba Momy? Ae wallahi bata isa ya saketa ba, ko don mu kuntata mata yanda ta kuntata ma Abdul baza mu yi fatan ya saketa ba, dole sai ta shigo gidan nan, balle shi ba mahaukaci bane da zae saketan, yarinyar da ya tura har America karatu duk don dai ta zama presentable cikin mutane kar a mana dariya daga karshe ta saka masa da wannan walakanci da tijara haka?" Abdul dake zaune parlon shi ma duk yana sauraronsu ya mike yace "In har aka ga na saketa to bana numfashi ne a duniya, kuma duk inda ma take zata dawo hannuna nan ba da jimawa ba kuwa, a nan ne zata gwammaci bata taΙ“a sanina a rayuwarta ba, i will make life a living hell for her" Momy ta tabe baki tace "Shi dama talaka ai bai gaji abun arziki ba, shi yasa babu ruwana da su ko da wasa, hanyar jirgi daban ta mota daban, kai ne da jajibe jajibenka kasa ubanka ya tafka asaran kusan miliyan dari akan matsiyaciyar yarinyar nan" Tuni Abdul ya fice daga parlon, Meema na kallon uwarsu tace "Ai ki ma dena maganar asaran miliyan dari Momy, don yanxu babu wannan zancen asaran nake ji" Momy dai ta tabe baki tana kallon me aikinta tace "Ke kar fa ki yanka ni inyi mugun bata maki rai yanzu, ya zaki dinga gaftare min naman yatsu" Hakuri mai aikin ta hau bata. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta Ι—an kishingida a 3 seater, hannunta rike da bowl din pepper soup din da Aunty Farida tayi mata, gaba daya ta kasa shan pepper soup din Offals din, don jinsa take kamar magani a bakinta gashi har sannan jikinta babu kwari ga ciwon kai, ta kalli drip din dake hannunta taga ko quarter bai yi ba amma har ta gaji ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, tun da AJ ya kawo magungunan da drip ya ajiye ya bar gidan har sannan bai dawo ba, ga abincinsa Aunty Farida ta zuba a cooler ta ajiye a tray tun daxu tana jiransa, tambayoyi ne da yawa ke yawo a zuciyar Aunty Farida tana son tambayar Khaleesat ko shine ya taΙ“a biya mata jirgi kwanaki da Umma bata da lafiya amma ganin yanayin da Khaleesat ke ciki ta bar duk tambayoyin nan a zuciyarta, Aunty Farida ta kalli Khaleesat tace "Ki daure ko kadan ne ki sha, ko in dama maki custard?" Khaleesat ta girgiza mata kai, dai dai nan aka kwankwasa kofar parlon, Aunty Farida ta mike ta yafa gyalenta sannan ta tafi ta bude kofar ta koma gefe, da sallama Ajay ya shigo parlon yana kallon Aunty Farida yace "Tare da brother dina muke" Aunty Farida tace "To ku shigo mana" a hankali Khaleesat ta gyara zamanta tana kallon Jay babu ko kiftawa, ganinsa ta dinga yi kamar a mafarki, Jay ya sauke kansa ya gaida Aunty Farida ta amsa da fara'a, sannan ya juya yana kallon Khaleesat shi ma babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta tana kallonsa, walking slowly ya karasa har cikin parlon ya duka gabanta yana kallonta, a hankali yace "Are you feeling better now Housemate?" Da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, and truly she felt better immediately, shi dai AJ na tsaye yana kallonsu, haka Aunty farida da ta koma one sitter a sanyaye ta zauna, Jay yayi kasa da murya still looking at her yace "Kiyi hakuri, everything will be okay soon in sha Allah, i promise you" Ta gyada masa kai da sauri with so much hope from his assurance, yana kallon bowl din hannunta Softly yace "Take ur soup" Ba musu ta dau spoon din ta fara shan pepper soup din a hankali, Aunty Farida ta kalli Ajay tace "Baka zauna ba Junaid" Ajay ya sauke kansa ya karasa 2 seater ya zauna, Aunty Farida ta share hawayen da ya cika idonta, da kyar tace "Mu ma duk ba da son ran mu bane abubuwan nan ke faruwa haka ba, ba mu da yanda za mu yi ne kawai, amma babu nagartattun iyayen da za su dau er su su ba Abdul aure"

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

 

 

 

Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buΙ—e a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍

 

‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!

MG’s Beauty Lounge ya buΙ—e da kwalliya, tsafta da Ζ™amshi irin na sarauniyar zamani!

 

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

 

Gyaran gashi da kitson zamani

 

Kwalliyar Sallah mai Ι—aukar ido

 

Wanke Ζ™afafu da pedicure mai sanyaya rai

 

Kayan gyaran fata na gaske

 

Lalle mai kyau da salo na zamani

 

Tura-turai, humra, incense da Ζ™amshi masu daΙ—i

 

Shirin amare da na musamman

 

 

Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.

Zo ki ji daΙ—in wanke Ζ™afa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da Ζ™amshi – komai a wuri guda mai kyau.

 

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

 

Tambaya/Booking:

WhatsApp: 08062991549

Kira: 09016108092 / 08064532391

 

Ki zo ki gani da idonki – ki ji daΙ—in sauyin MG’s Beauty Lounge.

Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge

[5/30, 8:55 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: *Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga me kasuwar garin Dutse Hajiya Aunty Zahrah da Hajjaju Sadiya Chamo Ex in-law, Hajiya Nafeesah Mom twins da Ummu Zainab Maman Ramla, Aunty Maryam Dan Ladi nasidi kema na gaisheki da katon murya, Hajiya Jumare da Hajiya Asmy me kayan amare, Oum Nabeelah, Mardiyyah, Uwar Janan, Halysah GarbaπŸ˜‚ i hail you all with respect yan Palace*

 

Manyan Membobin _❤‍🩹Khaleesat's Citadel_❤‍🩹

*Su Meenah parrotπŸ”, Oum Noor, Nafeesah Jawwad, Rukayya, Fidomashi, Siyam, M manal, Mrs Barrister, Shanono Esq, Ummilos, Na'imatu, Zulaiha, Ummu Abdrhm,  Khaleesat Haiydar is saying a big thank you to you all for ur support always, Allah ya bar min ku*πŸ₯°

 

 

Aunty Farida ta numfasa a hankali tace "Da yake Abdul shi kadai ne namiji gun mahaifinsa, mahaifin ya dauki son duniya ya dora masa kuma bai jin maganar kowa sai nasa, duk abinda Abdul yake so shi mahaifinsa ke so, bayan yaga Khaleesat a kotu babu tantama zuwa yayi ya samu uban ya nuna yana sonta zai kuma aureta, wannan dalili yasa babu bata lokaci suka janye kara a kotu suka bar maganar miliyan dari da sharadin Malam Ali zai ba Abdul auren er sa Khaleesat, mu dai har yau bamu san ko da wata yarjejeniya da aka yi a kotun ba ko babu, mun dai san an janye kara kawai kuma duk muka yi farin ciki sosai da hakan, burin mu kawai Malam Ali ya dawo gare mu ko da bazai tsinana mu da komai ba amma mu dinga ganinsa a tare da mu a matsayin kantangar gida, balle duk mun san yayi ma iyalansa hidima dai dai gwargwado ya kuma kyautata masu yanda ya kamata, jarabawa ce kawai ta fada masa, bana mantawa Khaleesat ta shiga damuwa sosai a lkcn tana ta koke koke wai ita bata son Abdul tun ma bata san kalansa ba bata gansa ba tace bata sonsa bazata iya aurensa ba, mu kam idonmu duk ya rufe da son ganin an wanke Malam Ali daga laifin da ake zarginsa da shi, ni da uwarta muka yi ta bata baki muna kwantar mata da hankali muka ce ko tafi son a maida mahaifinta prison ne, ko don mahaifinta bazata hakura ba ta amince da bukatar Abdul na son aurenta don case din ya mutu gaba daya, gashi tun bayan dawowar Malam Ali yayi ta rashin lafiya ko kudin kai sa asibiti babu, duba da hakan ne ma yasa muka yi ta karfafa ma Khaleesat gwiwa muna bata baki, a haka dai muka samu muka lallabata ta fara hakura, nan kishiyoyin Ummanta suka fito da baΖ™in cikinsu da hassada a fili tunda su ma ai suna da 'ya ya mata sa'annin Khaleesat da ma wa enda suka girmeta amma shine Abdul zai ce sai Khaleesat, nan fa duk suka hau gaba sosai da yayata saboda Ι—an mai kudi ya ga Khaleesat yace yana so, ranan farko da Abdul ya fara zuwa unguwan cewa yayi shi bazai shigo da motarsa layin ba ta fito bakin titi ta samesa, gashi daga gidan zuwa bakin titi akwai tafiya sosai, haka nan uwar ta lallabata ta shirya ta saka nikab dinta kannenta biyu suka rakata har bakin titin ta samesa, a ranan kuma ya bata babban waya ya kuma hadata da dubu hamsin, ba ma ita ta amsa ba don nuna masa tayi bata so shine ya ba kannenta yayi tafiyarsa, da kudin aka samu aka biya mata waec dinta tunda ba mu da yanda za mu yi, a kaf tarihi ban taΙ“a jin wanda yake neman yarinya da isa da gadara da walakanci kamar Abdul ba, for almost 2 months in Abdul zai zo unguwan mu sai dai dole ta fito titi ta samesa shi bazai shiga layin da motarsa ba, watarana ne ya kira bata da lafiya shine da ya tashi zuwa dubata da yamma ya shigo layin a karo na farko tunda ya fara zuwa gurin ta, daga nan kuma ya dena cewa ta fito bakin titi in ya zo sai dai ya karasa ciki da motarsa, ya kai ya kawo har cikin gida yana shigowa, tun a wannan lokacin Abdul baya raga ma Khaleesat, fadan yau daban na gobe daban, bashi da fahimta bashi da uxuri, ga nuna isa da gadara abinda yace yake so dole shi zata yi, haka nan yarinyar nan ke hakuri da halinsa duk don saboda mahaifinta, rana daddaya ne baya sa ta kuka, sai dai ni da uwarta mu yi ta bata hakuri muna ganin duk me sauki ne tunda har yana sonta kuma yaji zai aureta ya zauna da ita wataran zata canza sa da kanta, ni dai a sanda na fara sarewa da lamarin Abdul jikina yayi sanyi shine watarana da ya daga hannu ya mareta har sai da shatin yatsunsa ya kwanta fuskarta, mu dai har yau bata gaya mana me tayi masa da yayi mata haka ba don a cikin motarsa hakan ya faru, nan jikin uwarta ma ya fara sanyi kan lamarin har ta samu Mai gidanta ta gaya masa amma Malam Ali yayi ta kakkarewa har da cewa duk wanda ma ya kara tada maganar Allah ya isa, ana haka har ya biya mata jamb ya kai ta da kansa ta zana don fara jami'a tunda waec dinta ya fito kuma sakamakonta yayi kyau sosai, kawai rana daya kwatsam ubansa ya kira mahaifinta wai ga abinda Abdul yace yake so, wato zai tura Khaleesat Amurka tayi karatu a can, duk kawaicin da yayata take wannan karan sai da ta nuna bata amince da hakan ba, don ana ta bin su a yanda suke so ba hakan ke nufin bamu da ta cewa akan lamarin Khaleesat ba, ba Yayata ba har kakar Khaleesat Nenne ta nuna rashin amincewarta a wannan bukatar tasu, babu ta yanda za a dau yarinya karama haka da ko mallakan hankalinta bata gama yi ba ace za a tura ta har Amurka da sunan karatu, in haka ne kawai a daura auren mana sai ya kai ta duk inda ma zai kai ta tayi karatu, in ko ba haka ba babu inda er ta zata je da sunan karatu sai dai duk abinda zai faru ya faru, a nan dai laifin Mahaifin Khaleesat ne da ya dau tsoron duniya ya dora ma Abdul da mahaifinsa ba kuma tsoron komai ba sai tsoron kar su sake maidasa inda ya baro wato prison, dama tunda ya baro can ya dawo gashi nan gashin nan dai kamar ya Ι—an samu matsala a kwakwalwarsa, yau lafiya gobe akasin haka, ya dawo kamar ba Malam Ali ba, a lokacin duk ya gigice yayi ta bala'i wai ina ne ba a tura yaro karatu a zamanin yanxu, yarinya me shekara sha bakwai ce za ace ma yarinya, inda yake shiga ba nan yake fita ba, hakan ya zame masu bacin rai sosai da mahaifiyar Khaleesat har sai da ta bar gidan ta koma gidan Mahaifiyarsa warce ita ma yaki sauraronta, haka nan Malam Ali ya dau Khaleesat ya damka ma Abdul ba tare da amincewar uwarta ba ya kai ta karatu Amurka, Shiru Aunty Farida tayi tana kallon su Ajay dake kallonta duk suna sauraronta, a hankali tace "Tun daga sannan shi yake sponsoring komai nata a Amurka, cin ta da shan ta, da suturanta komai dai shi ne, sai san da ya ga dama ne yake bari ta zo hutu Nigeria, mu tsakaninmu da ita dama sai sanda muka ganta ko kuma muyi magana ta WhatsApp, gashi yaki a daura auren nasu wai sai ta gama karatun wanda wnn ne ke kara daga mana hankali, a haka ake ta rayuwar bamu da kwanciyar hankali, a ko da yaushe fatanmu shine ayi ayi auren don duk wasu iyaye nagari baza a same su da kwanciyar hankali ba ace yau er su budurwa bata gabansu, kusan kullum sai uwarta ta zubda hawaye kan wannan lamari sanadiyar hakan har sai da hawan jini ya kamata, ace bata da iko da er ta sai dai abinda Abdul da ubansa suka tsara gashi mai gidanta ya dau tsoron duniya ya dora masu sai jan sa suke kamar rakumi da akala.... ko wata biyu ba ayi ba ranan yayata ta kirani take sanar min sun kawo kudin auren Khaleesat, duk muka yi farin ciki sosai da hakan, muka yi fatan Allah ya sa hakan alkhairi ne a rayuwar Khaleesat tunda mu ma mun fi son ayi auren kowa ma ya huta, kawai ranan juma'an nan da ta wuce sai ga kiran yayata wai an daura auren Khaleesat da Abdul, nace mata ban gane ba, Khaleesat din ta dawo ne? Sannan dama ana daura aure haka ba shiri? Nan take gaya min ai mahaifin Abdul din ne ya kira Baban Khaleesat da yamma likis yace ga bukatarsu gobe juma'a, babu bata lokaci kuma aka daura auren kamar yanda suka bukata washegarin, nace mata to shikenan Allah sa hakan shine mafi alkhairi, zuwa satin da za a shiga zan shigo kanon tunda tace Khaleesat din ma na Amurka bata dawo ba, ban kuma san komai dake faruwa ba sai ranan Lahadi da kirani, mun yi waya da kai babu dadewa sai ga yayata ma ta kirani tana kuka" Ajay ya sauke idonsa kasa, Calmly yace "Amma dai baki ce mata tana nan ba har yanxu ko?" Aunty Farida ta girgiza kai tace "Ai tunda muka yi waya kace kar in nuna ma kowa nasan inda take wallahi ban nuna ma yayata nasan komai ba, ita kanta har yanxu bata san inda Khaleesat take ba, Nasan Baaba Gaje bazata gaya mata ba ita ma" Ajay ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan, yanxun ma kar ki nuna tana wajenki, in sha Allah za mu ga yanda za ayi, in ma kudin baban nasa da abinda ya kashe mata na makaranta za a mayar masu wannan ba matsala bane in sha Allah" Aunty Farida ta gwalo ido jin abinda yace, ko dai bai ji amount din da ta kira bane da kyau, a hankali tace "Kudaden ne da yawa ai Junaid, miliyan dari fa banda abinda zai ce ya kashe mata na makaranta da bamu sani ba" Ajay yace "Bazai dai ce ya kashe mata sama da miliyan dari a makarantar ba, mu ma duk makarantar muke ai, in ma yace haka miliyan dari biyu ba abu bane da muke fatan zai gagara a mayar masu, so kawai kar ki ce ma kowa tana wajenki, we will see how things will go in sha Allah" Ita dai Aunty Farida tsabar yanda jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai, dama tun da ya sakko daga mota jiya taga kalansa take ta kallonsa tana mamakin inda Khaleesat ta samo shi, hatta wanda ya kira Ι—an uwansa bata ga yayi kalar tsiya ba shima, Shi dai Jay yayi shiru bai ce komai ba idonsa akan buhun shinkafa biyu da babban jarkan man gyada da carton din taliya dake parlon Aunty Farida, kana gani kasan food vendor ce, Ajay ya mike yana kallon Jay alamar ya tashi su tafi, Jay ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yana kallon Aunty Farida a hankali yace "Bacci take ne?" Ajay ya wani kallesa sai kuma yayi ficewarsa daga parlon, Aunty Farida ta mike tace "Bari in duba ta" Dakinta ta nufa Jay ya bi ta da kallo, after few seconds sai ga ta ta fito tana kallonsa tace "Ehh bacci take" Yace "Ohk, amma Drip din na raguwa kuwa?" Aunty Farida tace "Eh yana sauka" Mikewa yayi yace "Toh shikenan, sai anjima Aunty, kilan zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Aunty Farida ta Ι—an yi murmushi tace "Toh Allah ya kai mu Jawwad, mun gode sosai" Murmushin ya mayar mata ya nufi kofa, har ya fita ya sake juyowa yace "Amma Aunty ki Ι—an dinga duba drip din idan ya kare sai kiyi ma makociyar taki magana ta cire" Aunty Farida tace "Ina sha Allah, mun gode Jawwad" Daga haka ya fita daga parlon ya nufi kofar gida, cikin mota ya tadda Junaid har ya tada mota, ya karasa ya bude front seat ya shiga ya zauna ya jinginar da kansa da kujeran motar ya lumshe ido ya bude, saukansa kenan daga America ko hutawa bai yi ba balle ya ci abinci, yayi wanka kawai suka taho gidan Aunty Farida da Ajay, har suka isa gidan Cousin sister din parent dinsu dake Banana Island babu wanda yace komai a cikin motar, it's almost 7pm tsabar traffic din Lagos da ya rike su a hanya, bayan Ajay yayi parking Jay ya sauka daga motar ya nufi entrance din shiga gidan Ajay na biye da shi, a parlor suka tarar da Hajiya Fatima warce suke kira da Ummi, ta amsa gaisuwar da suka mata ta bi su da kallo, Ajay dai ya nufi sama, Tana kallon Jay tace "Baka ci abincin da aka ajiye maka ba Jawwad, ina ma ku ka je haka sai yanxu ku ke dawowa?" Jay ya shafa kansa a hankali yace "Wajen wani abokinmu" Daga haka shi ma ya wuce sama, ta bi sa da kallo. Wajen karfe tara na dare Ajay ya gama saka pajamas dinsa, Jay ya ajiye mug din tea dake hannunsa yana kallonsa Calmly yace "So now what is ur suggestion Ajay, gaba daya kai na ya kulle akan issue din nan, that guy have evil in mind shi yasa ya saka aka daura auren tun bata dawo ba, he have a different plan, abinda kayi masa a USA na ransa har yanzu.... He married her immediately just to deal with her, I don't think he still loves her, he married her to take revenge" Ajay yace "Dama ai ba saboda Allah ya sa aka daura auren ba, akwai abinda yake nufi da hakan, ashe ma karamin Ι—an iska ne shi ban sani ba tun da bai yarda da kansa ba, da ya yarda da kansa bazai dinga kashe waya ba" Jay yace "Kamar ya?" Ajay yace "Na karbi numbersa na sa a duba min location dinsa, his location was showing Abuja on Sunday, tun sunday din har zuwa yau bai sake kunna wayarsa ba, kuma baya location din da aka gansa bayan na sa an je can" Jay ya bude baki yana kallonsa, can yace "Ban gane ka sa an je can ba, what are you trying to do? Plss ni bana son wannan dabancin naka Ajay, ni na zata fa ka shiryu, is that why u were busy shouting ku hadu a Nigeria on that very day? No pls ka girmi haka yanxu Prince, why spare ur precious time for a tout like him, don ni wallahi kallon tout nake ma gayen, sannan kar ka manta barrister ne shi kamar yanda kanwar mamarta ta gaya mana, definitely yasan plan dinka a kansa da yasa ka dage ku hadu a Naija, kaga bazai bar wayarsa a kunne ba kuwa" Ajay yace "Ai sai dai bai kunna wayarsa ba amma wallahi duk sai ya janye batancin da yayi min a parlon nan ranan, ya zata ana zagina a tafi scot free? I will so deal with him" Jay ya tabe baki yace "Yanxu dai that aside, meye abun yi" a takaice Ajay yace "Abun yi kawai a makasa a kotu ya fadi duk abinda ya kashe a biyasa ya saketa taje tayi rayuwarta, cause in har ta zauna zaman aure da mutumin nan zai iya kasheta har lahira, don prisoner zai mayar da ita kawai" Jay yayi shiru at first, can yace "But Ajay bamu san ko anyi a rubuce kan cewar an basa aurenta a madadin kudin da mahaifinta zai biya mahaifin Abdul din ba, sannan gayen nan Barrister ne, kana ganin zai bari ayi wannan yarjejeniyar babu sa hannu or anything of such ta bangaren shari'a?" Ajay yace "Su na ma iyayenta kallon talakawa marasu galihu da basu da wani say shine za su tsaya wani yarjejeniya? Ai masu arziki ke yarjejeniya, bayan sun san har a tashi duniya iyayen nata ba samun hanyar biyan miliyoyin kudin nan za su yi ba? Ai hankalinsu da tunani ma bazai je kan wata yarjejeniya ba cause they just assume sun samu yarinyar sun gama kuma ba wani abu da zai gifta ya hana hakan, so now we are taking this case to court, da bakinta zata ce ma alkali bata auren a kotu, iyaka ace ta biyasa abinda ya kashe mata na karatu sannan tayi masa wani auren ba shikenan ba" Jay yayi murmushi yace "Case din babanta da shi mahaifin Abdul din fa?" Ajay yace "We will reach der also" Jay yace "I just hope the agreement isn't in written form, but before mu je kotu nawa ne a account din ka Ajay?" Dariyar da Ajay bai yi niyya ba yayi yana shafa kansa, can ya kallesa yace "Why are you asking me that silly question Jay?" Jay yayi murmushi yace "Let me know first cause the money in my bank account isn't more than that amount" Ajay yace "200M?" Jay yace "Ban sani ba" Dariya sosai Ajay yayi yace "Na raina capacity dinka Bruh, meye kuma 200M a account dinka? Na zata account dinka ya doshi 1 Billion yanxu, Ohhh i remember baka wasa da investing fa, sannan kai Momy's boy ne har account din Momy ajiye kudi kake, Allah sa 200M din ma baya account dinta" Jay yaki tanka sa, Ajay yace "Kasan me, yanxu 600M or more ya kamata ace mun ajiye aside for this case cause I don't trust that stupid guy zai iya tripling kudin a kotu, i will get some more money from dad, Billah i am doing all this for the sake of humanity not because of that little brat, in don ta ita ne bazan yi ba, infact in don ta ita ne ba ruwana a case din ma" Jay dai danna wayarsa kawai yake bai ce komai ba don hankalinsa gaba daya yayi kan drip din da aka sa ma Khaleesat, yasan zuwa yanxu dai ya ci ya kare. Abdul na zaune gidan wani cin abinci tare da abokansa biyu da ke sauraronsa, Abdul yayi sipping energy drink din gabansa ya ajiye ya ci gaba da magana yace "I am still trying to gather more informations about the guy, kuma duk inda take yanxu da taimakon guy din taje can don bata da kowa a cikin garin kano or anywhere da zata je sai wajen sa, all of a sudden fa kawai naga yarinya ta canza attitude tana min wani sabon kalan raini, at first na zata naughty frnd din nan nata Safiyyah ce ke zugata duk da ita ma sai nayi maganinta don nasan da hadin bakinta a abubuwan nan da ke faruwa, i will fish her out too, ashe wai er ficiciyar yarinyar nan maza take kulawa a kasar suke bata liver take min raini, Billah sai na kauda gayen nan a doron kasa this is a promise i am making, sai dai uwarsa ta haifi wani, zai san gonata ya shiga sannan zai san bai daki banza ba, ba a dukana a ci gaba da rayuwa lafiya, he said we should meet in Nigeria ko? nasan yanxu shi ma yana bibiyan inda zai sameni, i don't want to be taken unaware shi yasa nake kashe wayata don nasan definitely zata basa lambata, idan na gama shirya masa tuggu zan bude wayar yayi tracking dina ya zo ya sameni inda nake, wallahil Azeem sai na kawar da shi kuma babu abinda zai faru, ita kuma duk inda take zata shigo hannuna nan ba da jimawa ba kuwa, sai dai in ban cika Abdallah Musa ba" Abokinsa Aminu yace "Toh kai baka ga fuskar guy din bane?" Abdul yayi wani murmushi yace "Ai ni yanxu ban damu da naga fuskarsa ko ban gani ba, burina in ga na aika sa barzahu, kun yankar mana ticket din da nace?" Aminu yace "But ta yaya zaka samu informations din wanda baka taba sani ba, baka da lambarsa ba, baka san komai kansa ba, baka san wanene shi ba, baka ma san inda yake a Nigeria ba ko kuma wanda ya san sa, How will that be possible Abdul?" Abdul yayi wani irin murmushi yana bubbuga kafarsa da kasa a hankali, sai kuma ya karyar da kai yace "Na zata you will be among people that will never underate my capacity and intelligence Aminu, ai ina da lambar wayarta ko? Kuma ni nayi mata registering sim card din, toh abokina dake aiki a kamfanin network din sim da take amfani na ba phone number dinta ya duba min duk calls dinta ya kuma turo min numbers din da take waya da su frequently a America, he just sent them to me few minutes ago" Yana kai wa nan ya mike yana wani murmushi yace "Let go" Dariya kawai abokan nasa ke yi, suka tashi duk suka fita daga eatry din.

[6/2, 1:05 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Wajen karfe goma na dare Khaleesat na zaune dakin Aunty Farida da fruits a gabanta ta kasa sha, ita dai Aunty Farida na zaune opposite dinta ta zuba mata ido don har ta gaji da ce mata ta sha fruit din, ga abinci ma taki ci, tun tuni makociyar Aunty Farida ta shigo ta cire mata drip din bayan ya kare, ta daga kai ta kalli Aunty Farida a hankali tace "Aunty su Housemate dina sun tafi ne?" Aunty Farida tace "Waye kuma Housemate din ki?" Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, Aunty Farida tace "Junaid din ne Housemate din ki?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Wanda suka zo tare" Aunty Farida tace "Ohk, tun daxu ai suka tafi kina bacci, ta yaya ya zama Housemate din ki?" Khaleesat na juya fruits din gabanta a hankali da fork tace "Gida daya muke da shi a America" Aunty Farida ta Ι—an buda ido da confusion tace "Gida daya kuma? Kamar yaya? Amma ba kin ce makociyarki mace bace?" Khaleesat tace "Eh daga baya ta tashi daga apartment din, shi ne shi ya dawo gidan" Aunty Farida tace "Ikon Allah, shi kuma Junaid din a ina kika san shi?" Khaleesat tace "Cousin brothers ne ai, dalilin Housemate dina na san shi" Aunty Farida ta kafe ta da ido, Khaleesat ta sauke kanta bata boye ma Aunty Farida duk abun da ya faru tun daga dawowar Housemate apartment dinta, yanda ya biya mata kudin jirgi to and fro ta dawo Nigeria ta duba Umma, irin zaman da suka yi da shi da kirkin da yayi ta mata, har zuwa lkcn da Abdul ya zo kasar a karo na biyu da kuma abinda ya faru tsakaninsa da Ajay, da yanda suka maidata gidansu har ta gama Exams, babu abinda ta boye ma Aunty Farida hawaye na zuba idonta, Aunty Farida ta kasa cewa komai sai kallonta kawai take jiki a sanyaye, after almost a minute Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tayi tagumi don she is just speechless bata san ma me zata ce ba, amma ta fahimci wani abu a labarin da Khaleesat ta bata..... Washegari wajen karfe goma na safe Jay ya bude kofar dakin Ajay ya samesa tsaye yana buttoning din shirt dinsa ya gama shiryawa, Jay ya jingina da jikin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonsa calmly yace "You know what Ajay?" Ajay ya dau face cap dinsa ya saka, yana kokarin daura agogonsa a hannu yace "All ears" Jay yace "I think we shouldn't say anything to Abba akan kudin da muka yi magana jiya" Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace "Why?" Jay yace "Kasan zai yi querying dinmu about what we are using that huge amount of money for, i think gwara in amshi kudi wajen Mamina kawai, cause you know i can't lie to Abba idan yayi insisting akan abinda za mu yi da kudi haka, zan iya gaya masa me za muyi da kudin if he insist" Ajay ya masa wani kallo daga sama har kasa yace "Sannu saint, ita Mamin ce bazata yi querying dinka akan me zaka yi da huge sum of money din ba?" Jay yace "Yeah, but i know how to convince her" Ajay yayi wani murmushi yace "Mamin ce zaka yi convincing, i see" Bai jira amsar da Jay zai basa ba ya dau makullin mota da wayar sa ya bi gefensa ya fice daga dakin ya sauka downstairs, Jay ya bi sa da kallo, after a while ya jawo kofar dakin ya kulle sannan ya bi bayansa, Ummi dake zaune parlor ta bi su da kallo ganin alamar fita za su yi tace "Ina kuma za ku da safen nan?" Without looking at her a takaice Ajay yace "Bar beach" Ummi tace "Dama ana zuwa Bar beach da safe?" Ajay yace "Eh" daga haka ya fice daga parlon, Ummi ta kalli Jay tace "Wai Beach za ku?" Jay ya Ι—an sosa kansa yace "A'a sai da yamma, yanxu dai kawai yawo za mu yi a gari" Ummi ta tabe baki tace "Ai shikenan, traffic ma kadai ya isheku, Mami ma suna hanya yau in sha Allah, sun ma kusa sauka" Jay ya sauke kansa yace "Eh haka tace min" Ummi tace "To sai kun dawo" Jay yace "Allah ya sa" Daga haka ya fita daga parlon, ya tarar da Ajay a mota yana jiransa, yana shiga motar Ajay yace "Ko ina ruwanta da inda za mu, ni bana son sa ido a rayuwata, shi yasa bana sauka gidanta a garin nan, i hate what i don't like" Jay yace "Ikon Allah, what's wrong with her asking us where we are going?" Ajay yace "That's very wrong, we are not kids da zata dinga tambayar mu inda za mu idan za mu fita, ko Abba baya controlling din mu yanda matar nan take yi, i don't think i am going back to that house zan je in kama hotel kawai" Jay ya girgiza kai yace "Kai fa matsala ne da kai kamar gidan haya, ni ban ga wani abu ba don ta tambayemu inda za mu da safe, it's normal ai" Ajay ya kallesa yace "To ni ba kai bane da ake controlling yanda aka ga dama a family, kai da kaga za ka iya sai ayi ta controlling dinka Jawwad" Jay bai sake ce masa komai ba, Ajay ya ja motar suka fice daga gidan. Da sallama Safiyyah ta daga buhun dake makale kofar shiga compound din gidansu Khaleesat, Mama Shatu da Mama Zubaida ne tsakar gida ko wacce na zaune bakin murhunta ana girka abincin talla hayakin icce duk ya cika ko ina na gidan, Mama Zubaida sai mita take an siyo masu jikakken icce, gaishesu Safiyyah tayi suka amsa ana mata wani kallo kasa kasa, Safiyyah ta tsaya suka gaisa da Labiba dake wanke robobin da za a zuba abincin siyarwa, sannan ta nufi dakinsu Khaleesat ta daga labulen ta shiga da sallama, zaune ta tarar da Umma ta jingina da bango hannunta rike da carbi ga kawarta Mama salame da wata Zaliha makociyarsu sai Sha'awa ita ma makociyarsu zaune dakin ko wanne yayi jigum, zaunawa Safiyyah tayi tana kallon Umma ko gaisheta bata yi ba ganin yanayinta tace "Umma baki da lafiya ne?" Umma tayi karfin halin cewa "Sannu da zuwa Safiyyah" Safiyyah ta gaisheta sannan ta gaida sauran mutanen dake dakin, ta sake maida dubanta kan Umma kan tace komai Mama Salame da ta san kawar Khaleesat ce ita tayi kasa da murya tace "Tsakaninki da Allah Sapiya baki san inda kawarki Khaleesah take ba?" Safiyyah ta zaro ido tace "Kamar yaya Mama?" Sha'awa ta gyara zama tace "Ae tun ranan asabar rabon da a saka Khaleesat a ido, daga ta dawo kasar waje ta tarar an daura mata aure da audallah washegari Asabar aka nemeta aka rasa, babu inda ba a shiga neman Khaleesah ba amma babu ita babu labarinta, jiya jiya yan sanda suka zo suka tafi da Malam Ali" Safiyyah da ta shiga wani shock jin wai an daura ma Khaleesat aure da Abdul ta ajiye jakarta a gefe ta dafe kirji tace "Wani Abdul din aka daura mata aure da?" Sha'awa na gyara barkakken zaninta tace "Audullah saurayinta dai da kika sani, ranan juma'an nan da ta wuce aka daura masu aure, tana dirowa kasar aka sanar mata shine ta gudu har yau babu ita babu labarinta, gashi an tafi da Malam Ali an kullesa" Safiyyah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mikewa tayi tsaye ba tare da tasan tayi hakan ba tsabar shock din da ta shiga maganganun Sha'awa na yawo a kanta, hawaye ne ya cika idonta tana girgiza kai ta kasa cewa komai, ina jin bayan Khaleesat da tayi bakin cikin auren da aka daura mata da Abdul idan aka cire su Jay babu wanda yayi bakin ciki kuma irin Safiyyah, don ji tayi kamar an aza mata katon dutse a kirji tsabar bakin cikin wannan labarin, kawai ta fashe da kuka cike da tausayin kawarta, Abdul fa?? Housemate din Khaleesat ne ya fado mata a rai, nan Safiyyah ta dinga rera masu kuka kamar ita ce Khaleesat din, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana kunduma ma su Mama Shatu da Mama Zubaida zagi tana cewa "Wato har sararin kunna rubabbun murhun ku kuka samu a gidan nan baku dubi bala'in da ake ciki ba, ai in dai Ι—a ne kowa ma ya haifa wallahi, yanda ku ke nuna halin ko in kula da abinda ya samu Ι—a na ku ma dai kun haifi 'ya yan nan naga, shegu masu fararen kafafuwa tunda Ι—a na ya auro ku yake shiga bala'i sinka sinka a duniya amma saboda baku da imani da tausayi ko wacce ta zauna bakin shegen murhun ta" Mama Zubaida ta kauda kai tana tabe baki tayi kasa da murya tace "Sai kuma yunwa ta kashe mu saboda yan sanda sun zo sun dauki Malam" Ita dai Mama Shatu sai juya miyarta take kar ya kone taki ko kallon inda Nenne take, Nenne na huci ta nufi dakin Umma ta dage labulen tana kallon cikin dakin tace "Saka dogon hijabi da rike carbi ba shine mafitarki ba Zahra'u, duk inda kika tura yarinyar nan waya kawai zaki buga masu ki ce ta dawo tun lamari bai lalace mana gaba daya ba, in ko ba haka ba wallahi sai a wanke daya daga kanninta a ba ma Awdul din tunda abinda yayi ta shi yayi su, in jar fata da gashi irin ta buzaye ne su ma duk suna da shi, babu abinda zata gwada masu sai shekaru tunda ta basu shekaru bakwai, don bazan zuba ido a karo na biyu Ι—a na ya koma fursin ya tagayyara ba, Allah kadai yasan nawa na kashe wajen shige shige har Allah ya bamu mafita a wancan lokacin da aka kullesa, tun asali bata san bata son Awdul din ba sai bayan da ya kashe mata uban dukiya da bazai lissafu ba? Wace masifa ku ke son ja ma Ι—a na ke da er ki a garin kano? Shi kadai fa ya rage min namiji sai mata, wallahi ki fito da ita Zahra'u in ya so su riketa a sake min Ι—a na, nasan har da hadin bakin makirar tsohuwar can Gaje, yanxu kuma zan kama hanya in tafi Hotoron duk inda ku ka boye Khaleesah sai kun fito da ita baza ku kara ja min salalan tsiya ba, sha'awa taso ki rakani gidan tsohuwar banzan can Gaje" Da sauri Sha'awa ta mike ta figi baΖ™in gyalenta ta fita daga dakin ta bi bayan Nenne dake huci suka fita daga compound din gidan, Mama Zubaida da Mama Shatu suka saki guda a tare bayan Nenne ta fita, Mama Shatu ta kyalkyale da dariya tace "Ana yi muna hura murhu, ma ga dai karshen wannan dirama me dadin kallo a gidan nan, su buzuwa sai a koma dajin da aka shiga aka nemo maganin farin jini ayi ma Malam bayanin lamari ya kwabe, ba dai 'ya yanmu bane munana masu baΖ™in jini, maji ma gani dai" Umma dake jin duk abinda suke cewa ta jinginar da kanta da bango hawaye na sauka idonta Mama Salame na bata hakuri, Safiyyah dai jingina tayi daga bango a inda take tsaye hawaye na zuba idonta ita ma, ganin abun take kamar a mafarki wai an daura auren Khaleesat da Abdul, to amma ina Khaleesat zata tafi tun ranan Saturday ita da tasan Khaleesat ko kawaye bata da su a kano, Housemate ne ya fado mata, ta dau jakarta da sauri tana share hawayenta ta fita daga dakin Umma, Umma ta bi ta da kallo hawaye masu zafi na bin idonta daga ranan asabar zuwa yau har ta rame, ko abinci bata iya ci ta kira Aunty Farida yafi a kirga akan ta zo gareta ko zata ji saukin radadin da take ji a zuciyarta, Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi Safiyyah da wani kallo suna tabe baki har ta fita daga compound din, Mama Zubaida ta matsa kusa da Mama Shatu da yake murhunsu kusa da kusa yake, tayi kasa da murya tace "Kin ga ki hakura da dafa waken nan da kika ce don gaskiya zai bata mana lokaci ga waje da nisa, gwara mu je a kara kada hankalinta taji ta tsanesa da auren kuma taki dawowa, in ya kama a kadata ta shiga duniya duk sai mu ce ayi, kudi ne dai zai yi kuka ba wani abu ba, kinga daga karshe in ma Labiba ko Lamisah duk wanda yace a basa duk daya ne a wajen mu babu banbanci, babu abinda zata gwada masu sai farin fata da uban gashi kamar na doki, in idanuwa ne su ma suna da shi, sannan suna da hancinsu dai dai gwargwado, tun asali kece kika yi ta makon fiddo kudi da ba a kai ga haka ba ma wallahi" Mama Zubaida ma tayi kasa da murya tace "Wallahi ban taba zaton aikin mutumin na ci haka ba Shatu, kinsan Malaman Jabu sun yi yawa yanzu sai dai ka kai masu kudinka su yi cefanen gidansu, shi sa kika ga ina ta ja da baya naki sakin kudi dama jarina ba jarin arziki ba, kinsan tun bayan rasuwar Malamin nan da yayi mana aiki kan Parida naki sakewa da Malamai don asaran kudi kawai mutum yake shi din dai ne malami gangariya amma mutuwa ta dauke mana shi kwatsam, gashi har yau duk uban kyan parida babu mashinshini tana can tana tuwo tuwo a Legas tana aiko ma yayar kudi kuma in sha Allahu a haka zata kare ga dai kyan da diri da komai amma babu mashinshini, to in anyi duniya don manzon Allah haka Khaleesar ma zata kare, amma yanxu tunda muka samu sabon Malamin nan naga aiki da cikawa kema kin san fiddo kudi bazai kara min wahala ba, ba gashi har na sa an amso min adashina ba daxu, in sha Allah sai mun karkato da hankalin Abdul kan 'ya yan mu, ko Labisah ko Labibah, ba dai kyau suke takama da shi ba wai su buzaye, to wallahi sai dai su ga ana aure....." Shiru Mama Zubaida tayi ganin Salame ta fito daga dakin Umma ta ci gaba da juya miyarta with serious face, Safiyyah na fita kofar gida ta ciro wayarta a jaka don tana da number Housemate, tayi dialing numbersa gabanta na faduwa tana hoping yasan whereabout din Khaleesat, jin Khaleesat take a ranta kamar er uwarta ta jini, she can't imagine halin da take ciki yanxu, yana fara ring Jay dake mota tare da Ajay ya daga wayar ganin Safiyyah ke kiransa yayi picking ya kai kunne calmly yace "How are you Safiyyah?" Da kyar Safiyyah tace "I am fine, ina kwana?" Yace "Lafiya lau, kin dawo Nigeria kenan?" Ta gyada kai da kyar tace "Pls tambaya nake son in maka Ya Jawwad" Jay yace "Ina jin ki Safiyyah" Safiyyah tace "Don Allah kasan whereabout din Khaleesat, wai tun Saturday ta bar gida har yanxu ba a san inda take ba, yanxun nan na zo gidansu nake samun labarin" Hawaye na zuba idonta ta kare maganar, a hankali Jay yace "Halysaah?" Lkci daya Ajay ya juya ya kallesa, sai kuma ya fixge wayar ya katse ya ajiye, Jay dai kallonsa kawai yake, can yace "Kawarta ce fa" Ajay yace "And so? Assignment din announcing whereabout dinta aka baka ne? Me yasa baka da sirri ne kai?" Jay yace "But it's nothing, kawarta ce kuma tana sonta sosai, nasan bazata gaya ma kowa komai ba" Ajay ya dau wayar jin ya fara ringing, yayi rejecting call din Safiyyah sannan ya saka wayar a silent ya zura a aljihunsa yace "Dama ka saba tona ma mutane asiri kayi ruining plan dinsu ai" Jay yace "Bani wayata malam" Calmly Ajay yace "Bazan bayar ba" Dai dai sanda Ajay yayi parking a kofar gidan Aunty Farida ya kashe motar ya sauka ya bar Jay a ciki. Nenne na isa kofar gidan Gaje tare da Sha'awa er rakiyarta suka ga yan sanda biyu kofar gidan Gaje da motarsu, ga yan unguwa sun tsaya cirko cirko ana salallami, Nenne ta ja burki inda take tsaye tana gwaggwale ido sai ga wata er sanda ta kado keyar Gaje sun fito daga cikin gidan, Gaje na rusa kuka cikin rudewa take cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wallahi ban san inda take ba tsakanina da Allahn da ya halicce ni, in nasan inda take Allah ya tsine min albarka, Al-qur'anin Allah babu abinda na hada da ita ba dangin iya ba na Baba haduwar gidan duniya ne kawai, don manzon rahama ku min rai ban hada komai da ita ba" Er sandar tace "Amma ai an ganta ta shigo gidan ki ranan asabar da daddare, iya gaskiyar ki kadai ne zai cece ki a wannan case din aki kai ki furson, in kuma kika ce zaki ci gaba da karya zaki ga illar karya kuwa" Cikin tashin hankali zufa na keto ma Gaje ta ko ina tace "Wallahi zan fada gaskiya ku tsaya ku saurareni, tsakanina da Allah ta zo gidana da daddare wajen karfe goma tace in rufa mata asiri amma bata gaya min abinda ke faruwa ba, ni kuma da na tashi sai na kai ta gidan wata er dakina Sadiyah Chamo, Sadiyah ce ta bata mafaka a gidanta ta kwana, kashegari kuwa ta kira wani gingimemen mutumi a wayarta ya zo da katuwar motarsa ya dauketa suka tafi inda ban sani ba, idan na maku karya a wannan zance kada Allah yayi min rahama" Er sandar tace "Ina gidan Sadiyar yake?" Jiki na rawa Baba Gaje ta nuna hanyar gidan Maman Fu'ad, er sandar tace "Shiga mota mu je ki nuna mana gidan" Gaje ta rushe da kuka tana cewa "Na shiga uku na lalace ni Al-haqqatu na ja ma kaina masifa a garin kano" Bayan mota aka bude ma Gaje tana kuka ta shiga er sandar ta dago mata yakunannen gyalenta dake jan kasa ta dora kan cinyarta sannan ta shiga bayan motar ita ma, tuni Nenne ta juya sum sum tun ba a lura da ita ba ta shige wani layi, sai juyawa sha'awa tayi taga gefenta wayam babu Nenne.....

 

 

Next update at night in sha Allah.

[6/2, 8:30 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: A hankali Khaleesat ta Ι—an bude curtain din dakin Aunty Farida tana leko cikin parlon ta hada ido da su gaba daya, sauke idonta tayi ta shigo parlon walking slowly ta tafi ta zauna kan kujera kanta a kasa, tun da taji sallama ta tashi ta tafi dakin Aunty Farida don saka Hijab dinta, gaishesu tayi still not looking at them, Jay ne kawai ya amsa yana kalllonta calmly yace "How are you feeling now Housemate?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa a hankali tace "I am much better now" Kallon Ajay tayi suna hada ido ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini?" Yana danna wayarsa yace "Fine" Aunty Farida ta shigo parlon daga kitchen ta ajiye masu tray din Can drink da ruwa da taje dauko masu, sannan ta zauna kan kujera tana kara gaishesu, Jay yace "Ya me jiki" Aunty Farida tace "Da sauki, abinci ne dai bata ci har yanxu" Jay ya daga kai ya kalli Khaleesat, sauke idonta tayi ta dau plate din abincin da Aunty Farida ta zuba mata not long ago, ta bude murfin ta ajiye sannan ta dau spoon ta fara cin abincin a hankali, Aunty Farida na kallonsu tace "Bari in kawo maku abinci" Ajay ya kalli Jay, Jay yace "A'a mun yi breakfast Aunty, mun gode" Aunty Farida tace "To ai rana tayi yanzu" Bata jira taji me zai ce ba ta tafi kitchen zata zubo masu abincin, ita dai Khaleesat a hankali take cin abincin hannunta, mikewa Ajay yayi, Jay ya sa hannu a aljihunsa ya ciro wayarsa, Ajay yace "Zan yi waya a waje" Daga haka ya fita daga parlon kafin Aunty Farida ta fito daga kitchen, Jay yayi murmushi bai dai ce komai ba, bude wayarsa yayi yaga miss calls din Safiyyah har shidda, yayi dialing number dinta ya saka handsfree, yana fara ring Safiyyah ta daga kamar jira take, yayi kasa da murya yace "Can you hear me Safiyyah?" Tace "Ina jin ka, plss ba a san inda Khaleesat take bane tun ranan asabar, kuma ni nasan bata da inda zata je a garin kano" Yace "Where are you at now?" Da sauri tace "Nima a kano nake ai, jiya da yamma na dawo daga Maryland shi ne na zo gidansu yau nake samun labari she is away from home tun ranan Saturday after receiving the news of her marriage with Abdul, wai Abdul fa aka daura mata aure da" Safiyya na kai wa nan ta fashe da kuka, Jay yace "I mean are you at home or where?" Cikin kuka tace "A'a yanxu na baro gidansu, ina bakin titi ma haka, i am just confuse, Khaleesat bata da kawaye bata zuwa ko ina, i don't know where she will be now, i am disturb don Allah in kasan inda take kar ka boye min plss Ya Jawwad trust me" Calmly yace "Look, this should be confidential Safiyyah, i trust you are saying nothing to anybody about this...." Da sauri Safiyyah tace "Na rantse babu wanda zan ce ma komai Ya Jawwad, trust me, i am also not in support of the fruitless marriage" Jay yace "Ohk, here is ur frnd speak to her....." Mikewa yayi ya mika ma Khaleesat wayar, ta amshi wayar tana kallon screen din dama tun jiya take wishing ace Sophie na kusa da ita ko ba komai zata dinga Consoling dinta tana karfafa mata gwiwa da bata assurance, lkci daya hawaye ya cika idonta cikin rawan murya tace "Sophie" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Khaleesat, i am so happy you are safe and sound, dama fatana kenan, plss kina ina haka yanxu in taho don Allah" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Bana kano Sophie" Da mamaki Safiyya tace "To kina ina?" Khaleesat ta daga kai ta kalli Housemate dinta dake kallonta, sauke idonta tayi da kyar tace "Ina Lagos" Safiyyah tace "Lagos wajen wa? Ko wajen Aunty Farida?" Khaleesat tace "Um" Safiyyah tace "Amma Umma bata san kina nan ba" a hankali Khaleesat tace "Bata sani ba" Safiyya ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "Pls kar ki tada hankalinki kinji kawata, i know ur Housemate won't allow u do that, kuma in sha Allah babu zaman aure tsakaninki da Abdul don bai yi deserving din ki ba, i can't imagine what he will turn you into, in Allah ya yarda bazai ci nasara akan ki ba, Allah zai raba auren cikin gaggawa, shi kadai yasan mugun Intention din dake ransa akan ki shi yasa yayi haka, amma Allah ya fi sa" Khaleesat dai gyada mata kai kawai take hawaye na sauka idonta ta kasa cewa komai, Housemate dinta ya mike ya nufeta ya amshi wayar a hannunta ya koma ya zauna yace "Safiyyah" A sanyaye Safiyyah tace "Na'am Ya Jawwad, Please kawata bata da wanda zai tsaya mata akan issue din nan, ba da intention me kyau ya saka aka daura auren ba wallahi, mugu ne azzalumi, har abusing dinta yana yi" Jay dake sauraronta yace "In sha Allah we will try our very best ki taya mu da addu'a" Safiyyah tace "In sha Allah, but how can i be reaching her?" Yace "Don't you have her aunt's number" Safiyyah tace "Sure ina da shi, i will be calling her ta wayar Aunty Farida" Jay yace "Keep this confidential pls Safiyyah" Safiyyah tace "Trust me Ya Jawwad, i now have rest of mind knowing my frnd is safe" Da haka suka yi sallama ya ajiye wayar, Khaleesat ta ajiye plate din abincin hannunta don ta kasa ci, iya spoon uku kawai ta iya yi, tuni Aunty Farida har ta ajiye ma Jay abincin da ta zubo ta nemi waje ta zauna, sai da ta jira suka gama waya da Safiyyah sannan ta kallesa tace "Ina Junaid din ga abincin na zuba maku" Jay yace "Aunty bamu dade da cin abinci ba da gaske" Aunty Farida tace "Ai ko in baku ci ba bazan ji dadi ba, haka jiya ku ka bar min abincin ku ka ki ci, yanxu fa karfe biyu da rabi ake nema kuma breakfast kace kawai ku ka yi" Jay dai murmushi kawai yake, can yace "Toh zan ci Aunty" Tace "To ko kai fa, ina Junaid din kayi masa magana ya shigo ku ci" Jay na shafa kansa yace "Ai shi ya ci snacks a mota bazai ci abincin ba na sani, bai fiye cin abinci da rana ba" Aunty Farida tace "Ikon Allah to saboda me?" Jay yace "Haka yake, iya breakfast da Dinner kawai yake yi" Aunty Farida tace "Iko sai Allah" Jay na kallon abincin da Khaleesat ta rage ya mike ya dauko yace "Zan ci wannan kar mu bata abincin Aunty" Aunty Farida tace "Don Allah ka ajiye ka debi abinci ga plate nan Jawwad" Yace "Aunty wannan fa ya isheni ba iya cinyewa zan yi ba ma" Spoon din ya dauka ya fara cin abincin, Khaleesat dai kallonsa kawai take, Aunty Farida tace "Ai shikenan" Karfe uku da yan mintuna Ajay da Jay suka bar gidan, Jay ne ke driving din idonsa akan titi yace "To ya ku ka yi da Lauyan?" Ajay yace "He said we should meet in kano" Jay ya Ι—an kallesa yace "Zuwa gobe kenan?" Ajay yace "Sure, tomorrow in the morning za mu tafi kano" Jay bai sake cewa komai ba har suka isa gida, yau dai traffic din da Ι—an sauki, bayan Jay yayi parking ya juya yana kallon Ajay yace "Please since gobe za mu tafi kano ka bar maganar hotel da kace zaka koma" Ajay yace "Ai matar ne ta fiye takura da sa ido" Jay yayi dariya bai dai ce masa komai ba suka sauka zuwa cikin gidan, Ummi na zaune parlon Hadeeyah na kwance kusa da ita da daura kanta a saman cinyar Ummin, ba tare da Ajay ya kalleta ba ya gaisheta a takaice zai wuce sama Hadeeyah ta gaishesa ya amsa yana haura stairs, Jay ya zauna parlon ya gaida Ummi ta amsa tace "Sai yanxu? Ko dai ba Bar beach din ku ka je ba?" Jay ya Ι—an buda ido yace "Mun fasa" Yana magana ne yana kallon Hadeeyah da ta hade rai tana danna wayarta kamar bata gansa ba, Ummi ta kalleta tace "Ke baki ga yayanki bane" Hadeeyah na ci gaba da danna wayarta tace "Oh, ok, Good evening" Jay yace "Ya hanya?" Tace "Lafiya lau" Ummi na kallonsa tace "Mami tana sama" Jay ya mike yace "Ohk" Sama ya wuce, Hadeeyah ta bi sa da kallon gefen ido har ya fara hawa stairs, bayan ya tafi Ummi na kallon Hadeeyah tace "Fadan ku ka sake yi kenan?" Hadeeyah ta Ι—an yatsine fuska taki cewa komai tana danna wayarta, Ummi ta kyabe baki tace "Kun fi kusa dai" Jay na bude kofar dakin da yasan Maminsa na ciki ya sameta zaune tana waya, ya karasa ya zauna kusa da ita yana kallonta yayi mata side hug ya jinginar da kansa a shoulder dinta a hankali yace "Mami" Mami tayi ma warce suke wayar sallama ta ajiye wayar hannunta tana kallonsa tace "Ina ka je tun safe Son? I was thinking zaka zo airport kayi picking din mu" Jay ya Ι—an kalleta yace "Karfe nawa ku ka iso Mami?" Tace "Karfe sha daya da rabi na safe" Jay yace "Mun fita ne da Ajay, Ummi bata gaya maki ba" Mami tace "Kaga da ubansa ne zai sauka Lagos duk abinda yake yi barin sa zai yi ya tafi ya taro sa, amma kai uwarka ta sauka Lagos ya ja ka kun tafi gantali" Jay bai ce mata komai ba, Mami na kallonsa tace "Duk karatun ne yasa ka fada haka? Are you okay?" Jay yace "Stress din tafiyar da nayi zuwa Nigeria ne" Mami tace "Nasan shi zai zugaka ku dawo Nigeria kar ka biyo min ta UK" Jay ya Ι—an hade rai yace "Ya fa riga ni dawowa Nigeria Mami, ni ba jiya na dawo ba, shi kuma ai tun last week yake Nigeria" Mami ta tabe baki bata ce komai ba, Jay ya mike ya nufi kofa yace "Zan je inyi wanka" Mami tace "Dama gobe ka shirya mu tafi Bauchi ban san gantalin da yake jan ka ku ke yi a Lagos ba, kai da ko ance ka sauka Lagos baka taba yarda sai gashi saboda Junaid na lagos kai ma ka zauna a lagos, to gobe za mu tafi Bauchi kuma Hadeeyah ma a can zata yi hutu" Jay ya juya ya kalleta yace "Mami ni ban gama abinda nake yi ba, kawai ku yi tafiyar ku" Bai jira me zata ce ba ya fice daga dakin. Wajen karfe biyar da rabi Jay da Ajay suka sauko downstairs, dakin dake kasa suka nufa don Mami na ciki tare da wata bakuwarta warce suka hadu da dadewa a Saudia suna zumunci sun zama kaman en uwa, jin Mami ta shigo Lagos sai matar ta taho gidan gaida Mami tunda ita ma a Lagos din take, Ajay ya zauna kan 1 sitter dake dakin ya gaida Mami sannan ya gaida frnd dinta, Jay ma ya zauna ya gaida kawar Maminsa, matar me suna Hajiya Batula ta amsa da fara'a tana kallonsu sai kuma ta kalli Mami tace "Wanne ne son din naki a ciki Hajiya?" Mami tayi pointing Jay tace "That is my son" Matar na kallon Jay tace "Maa sha Allah, ai kuwa ga kama na gani" Shi dai Ajay danna wayarsa kawai yake bai dago kansa ba, Jay ya mike yace "Mami za mu je Gym ne" Mami ta kallesa tace "Da yamman nan ga uban traffic din Lagos ne zaka je Gym?" Jay yace "Ai ba nisa Gym din" Hajiya Batula tace "Nan Area din ma ai da Gym ba sai sun je da nisa ba" Jay ya kalli Ajay yace "Mu je" Mikewa Ajay yayi ya nufi kofa Jay ya bi bayansa suka fice daga dakin, Hajiya Batula tace "Amma Ι—an uwansa ne wannan din ai ko, naga suna yanayi sosai" Mami tace "Eh Cousin dinsa ne" Hajiya Batula tayi kasa da murya tace "Ko dai shi ne Ι—an sarkin dai?" Mami ta tabe baki tace "Shi ne" Hajiya Batula tace "Ya sunansa?" Mami tace "Sunansu daya Ahmad amma Junaid ake kiransa" Hajiya Batula tace "Ikon Allah, shi kam Jawwad babu ruwansa..." Cike da takaici Mami tace "Ni babban bakin cikina yanda har yanxu Jawwad bai san ciwon kansa ba, hakan na ci min tuwo a kwarya wallahi, controlling dinsa kawai yake yana bin sa, ko a America din ma Junaid din ne ke juyasa" Hajiya Batula tace "A'a gaskiya bai san ciwon kansa ba naga alama, shi ko kishi baya yi, kuma gaskiya Mai martaba ya nuna son kansa a fili karara nada Ι—an sa da yayi Yarima me jiran gado a maimakon Jawwad, ina ce Jawwad din ya girmi Ι—an sa?" Mami tace "Ya basa watanni har uku" Hajiya Batula ta rike haΙ“a tace "Amma in tambayeki mana Fulani, bayan rasuwan mahaifin Jawwad wato me martaba Sarki Ahmadu Yusuf shi brother din nasa wanda shi ne sarkin yanxu bai nemi rikon Jawwad a gabansa ba?" Mami tayi shiru, can tace "Cikin Jawwad na da wata bakwai mahaifinsa me martaba ya rasu aka nada kaninsa wato mahaifin Junaid, dama su uku ne gun babansu Sarki Yusuf Ibrahim, daga Mahaifin Jawwad wanda shi ne babba sai Mahaifin Junaid sannan Maimuna warce nake gidanta yanxu suna kiranta da Ummi...." Hajiya Batula tace "Ikon Allah, to amma...." Shigowar Ummi dakin ne yasa Hajiya Batula tayi saurin canza topic din tace "Yanxu goben za ki koma Bauchi kenan Hajiya?" Mami tace "In sha Allah" Ummi ta ajiye plate din hannunta tace "Sannun ku, gashi nan kaza na tsaya gasa maku" Hajiya Batula na murmushi tace "Allah sarki, sannu da aiki" Ummi tace "Bari in kawo maku drinks din, a can parlor mai aikin ta ajiye" Daga haka ta fita daga dakin, Mami tace "Da ma kin ci gaba da maganar ki, ita ma ai bata so Junaid din da aka nada Yarima me jiran gado ba" Hajiya Batula tace "To ke sai kika zuba ido aka yi hakan Fulani? In uban Jawwad din bai mutu ba a ina kanin nasa zai samu har yayi sarauta? Kuma shine bazai yi kara ya nada Ι—an yayansa da ya mutu ya bar masa sarautan Yarima me jiran gado ba sai ya nada Ι—an cikin sa?" Mami tayi wani murmushi tace "Ni fa ko a jikina hakan da aka yi, Jawwad is doing fine beside shi mulki ma baya gabansa, as far as my son is okay, i think da a nada sa Yarima da kar a nadasa duk daya..." Hajiya Batula tace "To halan Junaid din kadai sarkin ya haifa?" Mami tace "Wani Junaid? Amaryarsa da suke kira da Aunty na da Ι—a me shekara 29, ita in son samu ne ma a nada Ι—an ta Yariman ai" Hajiya Batula ta rike haΙ“a tana kallon Mami. Ajay yayi parking kenan bayan sun dawo gida wajen karfe bakwai na dare ya kalli Jay zai yi magana wayarsa ya fara ring, ya dauka yana duba me kiransa ganin number wani abokinsu ne da kamar bazai yi picking ba kawai sai kuma ya daga ya kai kunne, after few seconds of listening to what the frnd was saying ya zaro ido yace "What???" Kallonsa Jay yayi da sauri don intonation din da yayi using ya nuna ba lafiya ba, Da kyar Ajay ya cire wayar a kunnensa yana kallon Jay dake kallonsa shi ma babu ko kiftawa, Nan da nan Jay yaji hankalinsa ya tashi don babu inda mind dinsa yaje immediately sai gun Khaleesat, Ya fixge wayar hannun Ajay yace "What's happening plss?" Ajay ya kasa cewa komai tsabar yanda ya girgiza, Jay ya shiga call logs din wayar da sauri yaga Adams abokinsu ne ya kira nan yaji hankalinsa ya Ι—an kwanta don yasan ba abu bane da ya shafi Khaleesat, dialing number yayi amma har ya gama ring ba a daga ba, a hankali Ajay yace "Salim aka harba" Jay bai san sanda ya ajiye wayar hannunsa ba yace "What? Harbi kuma? Is he dead?" Ajay ya dau wayarsa shi ma ya kara dialing number Adams amma har ya katse bai daga ba, available flight to kano ya fara dubawa immediately.....

[6/3, 9:01 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Washegari sai da rana Ajay da Jay suka samu ganin Salem a hospital din da aka yi admitting dinsa, iya kafadarsa ne kadai aka nannada ma bandage alamar a nan aka harbesa amma duk kamanninsa ya canza alamar ya ci duka ba na wasa ba, Jay ya zauna kujeran dake kusa da gadon yana kallon Salem that was in pain yace "Hasbunallah, How did this happen Salem?" Shi dai Ajay na tsaye ya rungume hannu shi ma yana kallon Salem ganin yanda aka canza masa kama, ya ma kasa cewa komai, Salem dake kishingide jikin pillow da kyar don ko iya motsa kafadarsa daya baya yi ga duk jikinsa yayi tsami yayi karfin halin cewa "Ban san su ba suka yi attacking dina" Jay yace "Har gida suka same ka?" Salem ya girgiza kai yace "I stayed out late yesterday in wudil naje gurin wani abokina, he insisted i stay till the next day amma saboda ina da abun da zanyi washegari da safe a kano sai naki kwana a garin muka yi sallama da shi, bayan na kusa unguwan da nake da zama sai na lura da wata mota na biye dani a baya amma ban yi tunanin komai ba na zata ya shigo layin ne bai san hanya ba shine yake bi na ko nima fita zanyi daga unguwan mun fita tare, bayan na shigo layin mu babu kowa saboda dare yayi tun kan ma in sauko daga motata in shiga gida in bude gate sai nake ma motar alama da hannu ya tafi gaba zai samu hanya, sai kawai matukin motar ya fito ya nufo ni, duk da haka ban wani damu ba na zata direction zai tambayeni, na tsaya har ya iso dai dai gabana ban ankara ba kawai sai jin saukan naushi nayi ta ko ina a fuskata ina kokarin defending kai na sai sauran mutane ukun dake cikin motar suka fito su ma suka hau dukana ta ko ina at the same time they were asking me about a girl i know nothing about, wai inyi providing dinta ko su kashe ni" Da wani expression Jay ke kallonsa, sai kuma ya mike da sauri ya dafa gadon da Salem yake kai yace "A girl?" Salem ya gyada kai da kyar yace "Wai Khaleesat, ni ban ma taba jin sunan ba wallahi, suka yi ta dukana wai sai na fadi inda take ko su harbeni" A tare Ajay da Jay suka kalli juna, Salem yace "Kashe ni suka yi niyyar yi banda Allah ya rufa min asiri kururuwan da nake yi wani soja dake kusa da gidanmu ya fito da bindiga, da wani makocina da ya fito da adda, kafin makota na su fito ne suka min harbi har biyu daya ya sameni a kafada daya kuma bai sameni ba ya sami gate, sojan da makoci na suna fitowa suka shige motarsu suka tsere, ni wallahi ban taba jin sunan yarinyar da suka ambata ba ma" Aunties din Salem biyu ne suka shigo ward din da sallama, Ajay ya gaida su sannan ya fita daga ward din ya tafi haraban asibitin ya zauna, after almost 10 mins Jay ma ya fito, inda Ajay ke zaune ya nufa ya zauna bai dai ce masa komai ba, Ajay yayi breaking silence din yace "He is tracking me, ni yake nema ba Salem ba, but tana da number Salem a wayarta ne?" Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Yawanci shi take kira ya bani waya if there is anything she wants to tell me, ko number ka ma ai Salem ne ya tura mata, instead cewa zaka yi he is tracking the both of us tunda nima ta kira layina ai ranan, but how did he get Salem's line?" Ajay yayi murmushi yace "Definitely layinta ya sa a duba masa numbers din wa enda take waya da, and he is using that to track us" Jay ya mike yace "We need to take down our sim card AJ, decidedly zai samu information mun shigo kano since we are in his list, sannan i think before anything ya kamata mu fara fighting for her innocent father's release tunda ita Halysaah yanxu bai san inda take ba and she is safe where she is, but the Man needs help" Ajay yace "No, i don't think she is safe with her aunt, although aunt din tace bai san inda ta koma ba amma as far as yana da number wayarta zai iya sakawa ayi tracing din inda take ita ma" Jay ya juya yana kallonsa yayi shiru, he just realize of course hakan zai iya faruwa cause ya daina underrating Abdul yanxu, Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "That guy is something else Ajay, duk wata salon mugunta ya sani adding it to his career skills, ina jin kawai a duba mana if there is flight zuwa Niger republic a biya masu kawai su tafi can da aunt dinta har zuwa sanda za mu gama da Case din dad dinta, in the other hand shi kuma mun yi sue dinsa requesting for divorce for her" Ajay yayi shiru, can yace "But what if she is needed in court?" Jay yace "For now her lawyer will represent her, in ma an bukace ta a court we will sort that out" Jay yace "I think that's cool, amma ya kamata mu je gidan su gun mahaifiyarta" Ajay dai kallonsa kawai yake, can yace "Is that necessary?" Jay yace "Of course, kasan aunt dinta tace mana the mother is not medically fit, kada wannan damuwar yayi weighing dinta down" Ajay yace "Sai mu je a matsayin su wa?" jay ya mike yace "Human right" Abdul na tsaye rike da takardan da mahaifiyar sa ta mika masa daga shigowar sa parlor idonsa na kan takardar yana karanta content din jiki, Meema yayarsa ma na zaune parlon tana kallonsa fuskarta dauke da bacin rai karara, wani murmushi Abdul yayi ya cukuikuye takardar ya jefar kan kujera, Mahaifiyar sa dake ta kallonsa ta tabe baki tace "To yanxu menene amfanin wannan tozarcin da kaskantar da kai da ake yi? Sam kace kai baza ka ji maganata ka dau shawara ta ba Abdallah?" Meema ta katse ta tana kallonta a fusace tace "Haba Momy ta yaya kike son ya ji maganarki bayan uban kudin da ya kashe ma tsinanniyar shegiyar yarinyar? Ai jin maganar ki ba nasa bane wallahi, kuma don an kawo masa sammaci ba shi ke nufin ya hakura zai saketa ba, kotu ce kawai za a shiga ayi ta gwabzawa, kuma in sha Allahu duk inda kafafuwana za su shiga sai na shigar da su don Abdallah yayi nasara a wannan case din, bazan taΙ“a bari a tozarta min kanina ba ga mari ga tsinka jaka bazai taΙ“a yiwuwa ba wallahi, alamar koma waye ya zugata ta yarda aka yi karansa zai iya biyan ko nawa aka ce ya biya a kotu, kai jama'a amma yarinyar nan anyi babbar er iska butulu, dama ni tun asali ban goyi bayan da yace zai kai yarinyar nan Amurka ba ina jiye masa tsoron kar idonta ya bude, to gashi nan bayan karatun har da karuwanci ta dinga yi da manyan kasar nan tunda gashi har ta samu wanda zai tsaya mata da lauya ya biya makudan kudin da aka kashe mata kilan yace har da miliyan 100 da ubanta ya salwantar, abun arziki dai bai amshe mu ba a family din nan, ban ga laifin ki da baki son talakawa ba Momy, shi yasa nima bana son su na tsane su" Momy dai girgiza kafa kawai take tsabar takaici da bakin ciki ta kasa cewa komai, Meema ta kalli Abdul daka safa da marwa a parlon yana Ι—an murmushi tace "Ka kwantar da hankalin ka Abdul, as far as ina numfashi kuma uwar mu na numfashi ko don ka rama duk abinda yarinyar nan tayi maka za mu shiga mu fita har sai kotu ta baka ita, in sun san wata ai basu san wata ba, koma waye ke taka mata baya daga karshe kashe kudadensa kawai zai yi a banza don sai ta shigo gidan nan mun ci ubanta da izinin Allah, banda kaddara me ma zaka yi da er gagurumin barawo kuma makaryaci, daga basa dukiya ya kai Lagos yace an kwace mota" Sama Abdul ya wuce kamar zai tashi sama, Momy ta bi sa da kallo cikin bacin rai tace "Kai Allah Ubangiji ya tsine ma mutanen nan albarka, yanda suka sa Ι—a na a damuwa Allah ya saka duk zuri'arsu a damuwa, ita kuma yarinya Allah ya kasheta ma duk mu huta, tun da lamarin nan ya faru ko abincin kirki Abdallah yaki ya zauna ya ci a gidan nan, in ya fita tun safe sai dare muke ganinsa gaba daya ba shi da sukuni akan er talakawa, wannan wani irin iftila'i ne ya same mu" Meema tace "Tashi tsaye kawai za mu yi ayi abinda ya kamata Momy, gidan nan ai kamar ta shigo sa ne in sha Allahu, da bakinta zata ce ita ta hakura a kai ta gidan mijinta kawai, kuma ta shigo nan ta same mu muna jiranta" Daga haka Meema ta mike ta bi bayan Abdallah. Jay na zaune tare da Ajay a office din lauyansu suna sauraron sa, lauyan yace "He is trying to re-litigate a case already resolved in court, don an riga an rufe case din a kotu tunda yace ya yafe, har lauyoyinsa sun yi filing notice of discontinuance kuma kotu tayi approving sannan ta kulle case din ta yi releasing debtor dinsu from any further liability, but like seriously ban san wani irin lauya bane Ι—an sa, don har da written confirmation of debt forgiveness da suka yi a kotu duk yana nan, why let them arrest the man again? Ko dai Ι—an nasa bai gaya masa consequences din hakan da yayi bane cause this is pure abuse of process and malicious prosecution" Jay yace "To yanxu meye abun yi Barrister?" Lawyern ya ajiye pen din hannunsa yace "Za mu yi Filing motion to dismiss the already forgiven case, and we will plead abuse of process, sannan muyi Raising estopped from pursuing the debt again in near future, just that za mu yi presenting  documentation of the original debt forgiveness and court records to the court, wannan ma ai sun yi breaching court order ne kuma hakan laifi ne me zaman kansa" Ajay yace "That is because suna ganin ba shi da wanda zai tsaya masa ko shekara nawa zai yi a kulle, his family have no voice to do so, that was why the breached the court order for their selfish interest" Lauyan yace "Babu matsala in sha Allah za mu shigar da kara kotu, and the man will be bailed out while the case is going on, they will even have to pay him damages...." Bayan la'asar Ajay yayi parking a kofar gidansu Khaleesat, dai dai inda yayi parking ranan da suka yi dropping dinta da daddare, a bayansu kuma wata mota ce ita ma tayi parking, Guard uku ne suka fito daga cikin motar dukkansu suka yi tsaye jikin motar da suka sauka, shi dai Jay kallon unguwan kawai yake, Ajay ya bude mota ya sauka, ya jingina da motar ya rungume hannunsa, Jay ma ya sauko sannan ya zagayo inda Ajay yake tsaye yace "Where is the house?" Ba tare da Ajay ya kallesa ba yace "Gashi nan kana kallo" Jay ya kalli gidan dake opposite dinsu, wani almajiri ne ya zo wucewa Ajay ya kirasa, yaron ya taho da sauri Ajay yace "Shiga cikin gidan can kace ana sallama da Maman...." Sai kuma ya kalli Jay alamar ya fadi sunan, Jay na kallon almajirin yace "Kace ana sallama da Maman Halysaah" Almajirin yace "Toh" Da sauri ya nufi gidan, Ajay yace "Meye kuma Halysaah? How is that even a name? In zaka kira sunanta na asali kawai ka kira" Jay na kallonsa yace "Meye sunan nata na asali?" Ajay bai kallesa ba har sannan yace "Ka fi ni sani ai, tunda ka fi kusa da ita" Jay ya Ι—an yi murmushi bai sake ce masa komai ba, Nenne ce ta leko kofar gidan tana zazzare ido kuma bata yarda ta fito waje ba, tana yin ido hudu da su Jay sannan ga wasu samudawa da ta gani har uku tsaye jikin wata motar ta juya ta koma cikin gidan da sauri har tana tuntube, sai ga Mama Zubaida tana gyara gyalenta da ta yafa akan daurin kirjin da tayi, Mama Shatu na bayanta tana kokarin saka hijabinta ta bai bai, tsaye duk suka yi daga cikin gidan suna leko su Ajay da samudawan dake jikin mota a tsaye, Mama Shatu tayi karfin halin cewa "Ina wuninku?" Jay ne ya karasa har inda suke tsaye, shi dai Ajay na rungume da hannunsa yana kallon ikon Allah, Jay ya gaishesu duk suka amsa kamar munafukai suna gwale ido, Jay yayi kasa da kai yace "Mahaifiyar Halysaah mu ke son gani" Da sauri Mama Zubaida tace "A'a to ku shigo mana, Bismillan ku ai tana ciki, fakewa kawai suka yi da cewar bazata iya fitowa ba bata da lafiya, lafiyarta lauz ku shiga har dakin ku sameta" Duk tunaninsu an zo tafiya da Umma ne kamar yanda aka zo aka tafi da Malam Ali, Jay ya juya ya kalli Ajay dake jin duk conversation din su daga inda yake tsaye, ko ba a gaya masa ba yasan stepmom din Khaleesat ne matan, ya kulle motarsa yana kallon wa enda ke tsaye jikin mota yayi masu alamar da cewar za su fito in 5 mins sannan ya karasa har inda Jay ke tsaye yana jiransa su shiga gidan, su Mama Zubaida kuwa har sun koma tsakar gidan sun tsaya cirko cirko suna jiran su ga yanda za a shigo a fitar da Umma, da hannu suka nuna ma Jay da Ajay hanyar dakin Umma, Jay ne yayi sallama bakin kofar dakin, shi dai Ajay na tsaye a gefe yana kallon white t-shirt dinsa to be sure ruwan taΙ“on da yayi gaja gaja a compound din bai fallatsar masa a jiki ba, Mama Shatu da Mama Zubaida a tsakar compound din suke zubar da duk wani ruwan da suka yi aiki haka ma yaransu, sun maida compound din kamar na mahaukata, gashi simintin da aka masa duk ya dagargaje ya kusa komawa kasa, shi yasa in suka zubar da ruwa sai ya cabe, kudaje sai safa da marwa suke ta ko ina, ga kwanuka gaja gaja, igiyoyin gidan kuwa duk an rataye kaya, Ajay na ganin Jay ya shiga dakin Umma shi ma ya shiga ciki da sallama, dukawa Jay yayi daga bakin kofar ya gaida Umma da Maman Salame dake dakin, Ajay ma yayi hakan ya gaishe su, ganin haka Maman Salame ta tashi da sauri ta shimfida masu darduma a kan ledan dakin tana masu sannu da zuwa, duk tunaninta ita ma zuwa aka yi za a tafi da Umma amma sai bata ga alamar hakan a tattare da su ba duba da yanda suka yi gaisuwa cikin girmamawa, Jay ne kawai ya zauna kan darduman Ajay kuwa ya kasa zama ga wani zafi da yake ji a duk jikinsa, ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan goshinsa, Mama Salame ta dau mafici ta mika masa, ya Ι—an yi murmushi ya amsa yace "Nagode" Mama Salame ta dage labulen dakin tana cewa "Yau mun fi sati biyu basu kawo wutan ba, ance tiranspoma tayi bindiga" Nenne dake makale kofar bandaki rike da buta ta dinga leka dakin Umma bayan Maman Salame ta daga labulen, haka su Mama Zubaida da suka ji shiru ba a taso keyar Umma an fito da ita ba, Jay na kallon Umma dake zaune don ko ba a gaya masa ba yasan ita ce mahaifiyar Khaleesat duba da kalan fatarta sannan babu ta inda Khaleesat ta bar ta, ba karamin kama Khaleesat ke yi da mahaifiyarta ba a nan ta samo asalin kyanta, Yayi kasa da murya yace "Ya jikin Umma?" Cikin sanyin murya Umma tace "Alhamdulillah da sauki" Ajay ma yayi mata ya jiki ta amsa tana kallonsu gaba daya don jira kawai take taji me ke tafe da su, in ma cewa za su yi tafiya suka zo yi da ita dama a shirye take tunda hijab dinta na jikinta, shiru ne ya biyo baya a dakin, don Jay bai san ta inda zai fara introducing kansa ba ma, haka ma Ajay da yayi shiru zafi na neman hallaka sa, after few seconds Ajay yayi karfin halin breaking silence din a hankali yace "Makaranta daya mu ke tare da Jidderh a can America, so kawarta ta sanar mana abinda ke faruwa shi ne muka nemi ta bamu address mu zo nan duba ki" Sosai hankalin Mama Salame ya kwanta jin abinda Ajay yace, Mama Salame tace "Allah yayi maku albarka, kuma mun ji dadi mun kuma gode da zuwan da ku ka yi" Jay ya kwantar da murya yace "Kiyi hakuri Umma kuma ki kwantar da hankalinki, muna tabbatar maki in sha Allah komai zai wuce nan ba da dadewa ba, don za ayi duk abinda ya kamata, mahaifinta ma in sha Allahu za mu yi abinda ya dace a sakesa a yan kwanakin nan, ita kanta Halysaah zata dawo gida in sha Allah" Maman Salame ta daga hannu sama cike da farin ciki tace "Alhamdulillah ya Allah, gaskiya mun ji dadin jin hakan daga gare ku, don bamu da wanda zai tsaya mana sai Allah, Alhamdulillah" Ita dai Umma kanta na kasa hawaye na zuba idonta, Ajay yace "Zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Mama Salame tace "To Allah Ubangiji ya kai mu goben lafiya, mun gode, mun gode" Mikewa Ajay yayi ya kara yi ma Umma sallama sannan ya fita daga dakin kar yayi suffocate, heat wan finish prince, don in akwai abinda baya shiri da shine zafi, baya son zafi ko yaya yake, Nenne na ganin Ajay ya fito daga dakin Umma ta sake komawa cikin bandaki da sauri, su Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi sa da kallo har ya fita daga compound din, to su waye wannan kuma su da suka baza ido da kunne su ga an fito da Umma tana kuka, bayan fitar Ajay da few minutes sai ga almajirai suna shigowa gidan da buhun shinkafa biyu, carton din taliya biyu, carton din indomie biyu, manyan gallon na manja da mangyada, da carton din maggi duk kuma aka dinga dire su a kofar dakin Umma, daga Nenne har su Mama Zubaida haka suka saki baki suna kallon ikon Allah, Maman Salame ta taso zuwa bakin kofa tana kallon kayan abincin da mamaki tace "Ikon Allah, har da uban hidima haka??" Jay ya ajiye ma Umma 100k yace "Gashi Umma ayi cefane da wannan, in sha Allah gobe za mu shigo da izinin Allah" Bai jira cewar Umma that was speechless and shock ba ga hawayen dake sauka idonta kawai ya fita daga dakin.....

[6/6, 5:08 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Jay na fitowa dakin Umma, Nenne dake tsaye tsakar gida bayan ta fahimci ba yan sanda bane ta rushe da matsanancin kuka ta nemi er kujera ta zauna tana kallonsa tace "Da wannan uban kudaden da ku ka kashe na siyo kayayyakin abincin nan ai da belin Ι—a na ku ka yi, wallahi maraya ne ba shi da kowa, in ba wani ikon Allah ba sai dai ya rube a can, wancan karan ni kadai nasan wahalan da na sha na ganin an sako sa, babu inda kafata bata shiga ba wallahi, na dinga bi gida gida ina neman taimakon kudi" Jay ya kwantar da murya yace "In sha Allah za mu yi bakin kokarin mu na ganin an sako sa kaka, ki kwantar da hankalin ki" Nenne na matsar kwalla da gefen haΙ“ar zaninta tace "Ɗan nan ina hankalina zai kwanta Ι—a na na can furson? In dai daga gidan radio da talabijin ku ke ni dai na amince ku zo ku dau muryata da fuskata in nemi taimakon al'ummar musulmai ku watsa ni duniya ta gan ni ina jawabi, kilan gwamna ma in ya gani yaji tausayina ya saka baki a sakar min Ι—a na" Jay yace "Ba sai anyi haka ba Kaka, ina tabbatar maki nan ba da dadewa ba zai dawo gida in sha Allah" Nenne tace "To daga ina ku ke? Ko dai kungiyar kare haΖ™Ζ™in en Adam ne" Jay ya Ι—an yi shiru, Mama Zubaida da Mama Shatu dai sun yi cirko cirko a tsakar gida suna gwale ido suna kallon Jay, Jay yace "Makarantar mu daya da Halysaah a can Amurka, shi ne muka samu labarin abinda ya faru mu ka zo" Nenne ta mike da sauri tace "To ai yau kusan sati daya kenan ana neman ta ko sama ko kasa, wallahi bamu san inda take ba, ita uwar ta na daki tana jimamin ta, ni kuma ina nan ina jimamin Ι—a na, haka muka raba abun, amma tun da yarinyar nan ta samu labarin daurin aurenta da annoban nan Awdul ta shiga duniya, wallahi bakina da nata tace min bata son sa bazata iya auren sa ba, tun da uwata ta haifeni ban taΙ“a ganin inda ake auren dole ba" Nenne na kai wa nan ta fasa sabon kuka, Jay dai ya ma rasa abinda zai ce mata, beside baya ma son yayi magana gaban su Mama Zubaida da suka wangale kunnuwa suna saurare, kawai ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu ashirin din da yayi saura, yaje har gaban Nenne ya mika mata da ladabi yace "Ga wannan Kaka, in sha Allah za mu shigo gobe" Nenne ta daga hannu da sauri tace "A'a, gwara ku hada kawai ku kai furson a sako min Ι—a na, don yafi min ko wani kudi a duniya" Jay yayi murmushi yace "Ki amsa kaka, na maki alkawarin za a sako sa nan ba da dadewa ba in sha Allah" Nenne ta amshi kudin da hannu bibbiyu tana sa masa albarka cikin rawan murya tace "In ma Allah ya sa kun zo gobe ba ku sameni a nan ba ku sa a raka ku gidana babu nisa daga nan" Yana murmushi yace "In sha Allah Kaka" Daga haka yayi mata sallama sannan ya fita daga gidan su Mama Zubaida suka bi sa da kallo babu fara'a ko wacce da abinda ke yawo a ranta, Nenne ta kulle kudin a habar zaninta ta soke tace "Dama gobe da asuban fari zan je gun Malam Na ta'ala, Allah ya sa in samu kwale kwalen da zai tsallakar da ni da sassafe" Dakin Umma ta nufa tace "To ke Salame kike ko wa? Ki fito mana ki shigar mata da dukiyar nan dake bakin kofa kar a faki ido a sungume mata wani abun, kayan abinci ai dukiya ce me zaman kanta a yanxu, Allah kadai yasan dubu dari nawa suka kashe wajen siyo kayan abincin nan...." Maman Salame ta fito daga dakin Umma ta fara shigar da kayan abincin ciki, Mama Shatu ta shige dakinta fuska a murtuke, Mama Zubaida ma ta tabe baki ta shige nata dakin ta sako tsumman labulenta dake rataye da kyauren dakin. Jay na fita waje ya tarar da Ajay cikin mota yana zaune a kujera me zaman banza ya kwantar da seat din kujeran idonsa a lumshe, Jay ya bude driver seat ya shiga yana kallon Ajay jin yanda ya kure AC din motar gaba daya, Ajay ya gyara zamansa yana kallonsa, Jay dai yayi murmushi ya fara driving motar Ajay ya nuna masa hanyar da suka bi suka fita ranan da yayi dropping Khaleesat, motar dake bayan su ma ya bi su, Ajay sai sake kare ma unguwan kallo yake with distress har suka isa main road, bayan sun hau saman titi ya kalli Jay yace "In za a samu gida ko na 30M zuwa 50M ne a siya pls su bar wannan vicinity din" Jay yace "I think that will be okay idan anyi releasing mai gidan but not now" Ajay yace "Duk daya ne Bruh, plss kayi ma Salisu magana a fara duba gidan daga yau zuwa gobe, that house isn't healthy for a living thing, ta yaya me rai zai dinga rayuwa a gida irin wannan? This is so pathetic, or am i exaggerating pls?" Jay yace "But haka kawai baza mu yanke decision without the release of the head of the House ba, so kake mu kara triggering saurayin nata bayan har yanxu ba mu yi achieving ko abu daya ba, we are following everything step by step Ajay, we will reach der in sha Allah" Ajay bai sake cewa komai ba, amma da gaske hankalin sa ya tashi kwarai ganin condition din cikin gidan most especially the compound, in ba dole ba shi kam babu abinda zai sake kai sa gidan nan, it's not about the house structure or where it's located but the hygiene of the house, sai kace cikin prison, ji yake kamar har ya kamu da cholera don har wani zazzabi zazzabi ya fara ji, ya kai hannu ya rage Ac din motar, shi dai Jay driving dinsa kawai yake. Washegari da yamma haka nan suka sake komawa gidan bayan Lauyan su yayi requesting su tambayi matan Malam Ali ko da akwai wani written debt forgiveness document kuma original one din da kotu ta bashi bayan masu karansa sun janye karar, cause in dai babu takardun to sai dai ayi case din biyan bashin da yake bin Alhaji Musa amma ba dai su yi karan sa ba, Bayan Ajay yayi parking ya juya yana kallon Jay yace "Zan jira ka" Er dariya Jay yayi yace "Toh ai da baka biyo ni ba kayi zaman ka a gida kawai" Bai jira cewar Ajay ba ya sauka daga cikin motar ya nufi cikin gidan, yau ma dai kamar jiya ba su kadai suka zo unguwan ba don securities da suka biyo su har sun fi na jiya tunda basu san ko Abdul na da Spy a unguwan ba, infact bazai ma rasa ba, definitely za a basa labarin wasu sun zo gidan su Khaleesat jiya, so they are not loosing guard by any means, and they are never going to let him take them unaware, A takaice Jay ya gaida Kishiyoyin Umma dake zaune tsakar gidan sun yi rashe rashe da su, yau ko murhu basu kunna ba don dawowar su kenan daga wajen Malamai, tun asuban fari suka bar gida sai yanxu suke dawowa, duk suka bi Jay da kallo, Jay dai yana tafe yana kallon Islam da Noor dake ma Umma wanke wanke a tsakar gidan don ko ba a gaya masa ba yasan siblings din Khaleesat ne duba da pheomelanin din su, a tare suka gaishesa ya sakar masu murmushi yace "How are you?" Murmushin kawai suka yi basu ce masa komai ba Islam na wanke wanke Noor na mata dauraya, Jay ya isa har kofar dakin Umma yayi sallama, Umma da ta gama gyara dakinta kenan ta saka turaren wuta na tsinke ta amsa sallaman sa, a kullum in zaka shigo dakin Umma a haka zaka tarar da shi fes fes, duk da ba komai bane a dakinta don ta siyar da komai nata amma kullum a gyara zaka same dakin da turaren tsinke, Jay ya shiga dakin Umma na kallonsa tace "Sannu da zuwa" Tabarma ta dauko ta shimfida masa don bata yi tunanin zai dawo yau kamar yanda yace mata jiya ba, Jay ya zauna yana murmushi ya gaisheta, Umma ta zauna kan dardumanta ta amsa gaisuwar sa, har a sannan zaka ga damuwar dake tare da ita alamar karfin hali kawai take, sai kuma ta mike tace "Bari in kawo maka ruwa" Ruwa ta debo masa a cup din stainless ta karaso ta ajiye masa a gabansa sannan ta koma ta zauna, yace "Nagode Umma" Ɗan murmushi kawai tayi, Mama Zubaida da Mama Shatu suka yi tsit a tsakar gida ko wacce ta kasa kunne ko zata ji abinda ake cewa a dakin Umma, Ajay ne ya shigo gidan duk suka zuba masa na mujiya, sau daya ya kallesu ya dauke kai ya nufi dakin Umma, yau dai tsakar gidan a bushe yake bai yi gaja gaja da ruwa ba da yake basu yi girkin siyarwa ba, Islam na tsaye bakin kofar dakin Umma bayan ta shiga da kayan wanke wanken da suka yi da twin sis dinta, Ita kuma Noor na share inda suka yi wanke wanke, Idan Ajay ya kalli Noor sai ya kalli Islam, ya amsa gaisuwar da Noor ke masa tana rike da tsintsiya, yana isa bakin kofar dakin Umma ya ja dogon hancin Islam don ita ce ke mugun kama da Khaleesat har bakinsu iri daya ne, murmushi tayi tana kallonsa yace "How are you?" Ta sauke idonta bata ce komai ba yanda dai Khaleesat ke yi, da sallama ya shiga dakin Umma, Jay ya daga kai yana kallonsu don bai yi tunanin zai shigo ba, Umma ta amsa sallamansa, ya zauna daga gefen Jay sannan ya gaisheta, Umma ta amsa da murmushin karfin hali tana masa sannu da zuwa, after some seconds Jay ya fara magana a hankali yace "Umma akwai wasu takardu na yarjejeniyar kotu na yafiyan bashin da aka yi ma Mai gidan nan, Allah yasa kun san in da takardun suke ana bukatarsu ne" Umma tayi shiru, can tace "To, amma wallahi ban sani ba sai dai ko a duba dakinsa ko suna nan" Jay yace "Eh a duba Umma, Allah ya sa a gani" Umma tace "Ameen" Mikewa Umma tayi ta fita daga dakin, Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi ta da kallo har ta shiga dakin Malam Ali, after almost 8 mins sai ga Umma ta fito da wasu takardu wanda bata san ko na menene ba dai zata kai masu su duba ko akwai wanda ake nema a ciki, a haka ta wuce Kishiyoyinta da idanuwansa duk ke kanta, ta koma dakinta ta mika ma Jay takardun sannan ta koma kan dardumanta ta zauna, Jay ya dinga duba takardun daya bayan daya, yaga har da takardun makarantar Malam Ali, ashe har Degree garesa a Agriculture, kafin nan kuma sai da yayi diploma, yana ta dai duba tulin takardun har daga karshe yaga wasu takardun da yake saka rai na yarjejeniyar yafiyar da aka yi ma Malam Ali a kotu na biyan bashin Mahaifin Abdul ne, ya mika ma Ajay shi ma ya amsa yana duba takardun, Jay ya kalli Umma yace "Ina jin wannan ne takardun da muke nema" Umma tace "To Alhamdulillah" Jay yace "To za mu koma, duk yanda ake ciki za mu dawo in sha Allah" A hankali Umma tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma sai dai akwai wata uwar dakina da bata ji ba bata gani ba yan sanda suka tafi da ita shekaranjiya har yanxu ba a ma san wani caji ofis din aka kai ta ba" Ajay dake kallonta yace "Ko Baabar nan ta Hotoro?" Cike da karfin hali Umma tace "Ita, wallahi bata ji ba bata gani ba aka je aka tafi da ita" Ajay yayi shiru yana kara mamakin stupidity din Abdul, he don't think that guy is okay in anyway, after some seconds ya kalli Umma a hankali yace "Za mu bincika inda aka kai ta mu yi bailing dinta in sha Allah" Umma ta share hawayen da ya kawo idonta ta kasa cewa komai, Jay yace "Ki kwantar da hankalin ki Umma, in sha Allah komai zai wuce da izinin Allah" Cikin rawan murya Umma tace "Allah ya sa" Jay ya kalli Ajay, tsabar tausayin Umma kawai yaga gwara su gaya mata gaskiyar inda Khaleesat take ko zata Ι—an samu sukuni a ranta, Jay ya sauke idonsa a hankali yace "Sannan Umma akwai maganar da zan gaya maki yanxu, amma don Allah kar ki gaya ma kowa har zuwa sanda za mu gama abinda muke" Ajay ya juya ya wani kallesa don har ya gano maganar da Jay zai gaya ma Umma, Umma na share idonta tace "To in sha Allah" a hankali Jay yace "Halysaah na Lagos, amma don Allah ba ma son kowa yasan hakan Umma, ko makusantan ki kar ki gaya ma tukun....." Umma da zuciyarta ke bugawa tace "Lagos kuma? Wajen wa a Lagos?" Jay yace "Tana wajen sister din ki ne, amma mun ce mata kar ta nuna maki tana wajenta har sai sanda komai ya dai daita, shi yasa ma har yanxu bata gaya maki ba" Umma tayi shiru, amma fa ji tayi wani nutsuwa ya zo mata, lkci daya kuma taji hankalinta ya kwanta kamar an yaye mata kashi saba'in na damuwar da take ciki, Umma tace "In sha Allahu babu wanda zai ji hakan daga gare ni, yanda ku ka tsaya mana ku ma Allah Ubangiji ya tsaya maku haka, Allah ya saka maku da alkhairi..." Umma ta kasa ci gaba hawaye masu zafi na sauka idonta, A haka Ajay da Jay suka fita daga dakin Umma za su koma Office din lauya din su da takardun hoping shi ne kotu zata bukata, yau ma dai Ajay ji yayi kamar zafi zai kashesa a dakin Umma amma haka ya dinga daurewa har suka fita daga dakin sannan ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan da yayi, ya kalli Islam dake zaune bakin kofar dakin Umma da takardan makaranta a hannunta alamar karatu take, Noor kuma na hura gawayi a can gefe, ya saka hannu a aljihu ya ciro kudaden da bai san ko nawa bane ya mika ma Islam yana kallonta yace "Ku raba ke da er uwarki" Islam taki amsan kudin, ya hade rai yace "C'mon collect it" Jay dake kallonta shi ma ya sakar mata murmushi yace "Karba mana cutie" Islam ta kalli Noor amma still taki amsan kudin, Ajay ya zare mata ido yace "Kee, amsa nace" A hankali ta kai hannu ta amshi kudin, Ajay da Jay suka fita daga compound din, Kishiyoyin Umma suka dinga kallon uban kudin da aka ba Islam kamar idanuwansu za su fito ko kiftawan kirki basa yi, Islam ta tashi ta shiga dakin Umma da kudin a hannunta, Mama Zubaida ta mike ta ma Mama Shatu alamar su shiga daki, duk suka shiga dakin Mama Shatu sannan suka sake labule, Mama Zubaida ta rike haba tace "Anya kuwa Shatu baza mu san yanda za mu yi Abdul ya samu labarin abinda ke faruwa a gidan nan ba? Ni wallahi ban yarda wa ennan samarin basu san inda Khaleesat take ba, kina fa ganinsu kin ga 'ya yan masu kudi, dubi suturan da suka sa wa, ji motocinsu, sannan kalli fatarsu kalan ta yan hutu, in fa muka yi sake Shatu bakin ciki ne zai kashe mu a gidan nan muna ji muna gani" Mama Shatu tace "Ke ma dai wallahi kin fiye gaggawa, sai kace kin manta me Malamin yace mana, duka duka ba yau muka kai masa kudin ba, to mu zuba ido ya fara aiki mana tukun" Mama Zubaida tace "Duk da haka dai gwara mu ma mu dinga yin namu ta bayan fage Shatu, kada mu sakankance mu bar malami da aiki shi kadai, ya kamata tun wuri mu san yanda za mu yi mu ankarar da Abdul abinda ke faruwa a gidan nan, don gaskiya na sha jinin jikina da wa ennan zaratan samarin, ke ki ga tulin kudin da suka ba Islam, sannan kalli uban kayan abincin da suka jibge jiya daga karshe don walakanci aka biyo mu da kwano uku uku da taliya bibbiyu da man gyada da manja, sai maggi leda bibbiyu ga mayunwata, ke kiji wai yau Zahra'u ce da tsam mana kayan abincin da aka jibge mata, bayan haka Allah kadai yasan nawa suka bata a daki tunda ba gaya mana zata yi ba, ga Nenne ma a gaban mu aka bata rafar kudi yan dubu dubu, anya bamu shiga uku ba Shatu? Ni fa jikina yayi sanyi hankalina ya tashi, meye hadin su da Khaleesat din da har suke wannan hidima haka a kanta, mu ga 'ya yanmu a zube har yau babu mataya sai talla suke, ni fa wallahi ko tsirara zan yi yawo gwara inyi da dai Zahra'u da zuri'arta su ji dadi a duniya" Mama Shatu tace "Yanxu dai Gwaska za mu samu ya raka mu gidan su Abdul din tunda yace yasan gidan uban sa, nasan Abdul din zai taka ma yan iskan burki har ma ya bamu makudan kudi fallasa asirin abinda ke faruwa da mu ka yi" Mama Zubaida tace "Atoh dai tun wuri my gaya masa abinda ke faruwa, zuba ido ba namu bane wallahi, amma sai dai jibi kenan za mu je gidansu Abdul din don Gwaska ya tafi dambatta daxu uwarsa ke gaya min yaje kai kaya can" Mama Shatu tace "Ai jibin kamar gobe ne, kin ga gobe dama mu gama girkin mu da wuri mu tafi inda wannan matar ta mana kwatance daxu a gidan Malam" The next day wajen karfe biyar da rabi na yamma Sha'awa tayi sallama bakin kofar dakin Umma dake yi ma yan biyun ta gyaran gashi, babu kowa gidan don duk yan matan gidan basu dawo talla ba, kananun yaran kuma sun tafi gantali, tun Sha'awa bata shigo dakin Umma ba take cewa "Umma yanxu Ladingo ke sanar min an sako Gaje, wai daxu taje unguwan taga ana ta shiga gidan yi mata jaje" Umma ta sake gashin Noor ta mike da sauri tace "Da gaske Sha'awa?" Sha'awa tace "Wallahi kuwa Ladingo bazata min karya ba Umma, tace Gaje dai ta dawo gida ga yan unguwa na ta tururuwan shiga yi mata jaje tun daxu" Umma ta jawo Hijab dinta tace "To bari in je gidan Allah ya sa da gaske ne dai" Sha'awa tace "Da ina da kudin mota ai da mun je tare Umma, kusan kwanan ta biyar fa a kulle, don ma akwai kanwarta da zata kula da jikokinta tunda uwarsu na can Libiya ta tafi aikatau, ubansu kuma yayi watsi da su, banda haka da yaya makomar jikokin nan nata fisabilillahi?" Umma bata tanka ta ba ta gama saka hijab dinta ta daura nikab ta dau purse zata fita, Noor da Islam suka marairaice wai za su bi ta, ganin in ta tafi su kadai zata bari a gida yasa tace su saka hijab gaba daya, haka nan duk suka saka Hijab suka fita daga dakin Umma na biye da su, kusan kullum sai Umma taje gidan Gaje sau biyu ta duba ko ta dawo amma sai taga akasin haka sai dai ta samu kanwarta Iya a gidan, jiki a sanyaye take juyawa ta koma gida don Iya na ganinta take fara masifar ita ta saka er uwarta a uku, Umma zata fita gidan tare da yan biyunta sai ga su Mama Shatu da Mama Zubaida sun shigo wujiga wujiga da su, kana ganin fuskokinsu kasan a gajiye suke likis, ga wuyan hijabinsu duk yayi jagab da zufa, kafafuwarsu kuwa kamar wa enda suka dawo daga gona, Umma dai tayi masu sannu da zuwa kawai ta fita daga gidan su Islam na biye da ita, ai ko tana isa gidan Gaje taga da gaske an sako Gaje, Gaje na ganin Umma tayi kamar bata taΙ“a saninta ba a duniya, yanda take amsa gaisuwa da jajen masu shigo mata haka ta amsa ma Umma kamar ranan ta fara ganinta, ita dai Umma na zaune tayi shiru ta ma rasa me zata ce, su Islam na zaune gefenta, Gaje bata sake kallon direction dinta da yaranta ba, duk wanda ya shigo haka take sanar masa yanda Maman Fu'ad ta ci amanarta tace ma yan sanda ita bata taΙ“a ganinta ba ma balle wata Khaleesat, In tayi bayanin sai ta rushe da kuka tace "Ban taΙ“a tunanin Sadiyah zata min butulci haka ba duk alakar da ke tsakanin mu wai bata taΙ“a gani ba, kaji tsoron Allah kaji tsoron mutumin yau kawai, duk kyautata ma yarinyar nan da nake amma ta barni ni kadai raina a cikin matsalar da na tsoma kaina" Ita dai Umma tayi tagumi tana sauraron duk abinda Gaje ke cewa.

[6/9, 7:26 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Sai bayan da aka yi sallan Magrib Umma ta bar gidan Baaba Gaje da yan biyun ta, kuma har ta bar gidan Gaje bata nuna ta taΙ“a saninta ba don casually ma take amsa mata kamar yanda take ma kowa da ya shigo mata jaje, Umma dai a sanyaye ta baro gidan, tana isa gida taga mutane tsattsaye a kofar gida kowa da abinda ke fitowa bakinsa, sosai taji gabanta ya fadi gashi ta kasa fahimtar akan me ake ta surutu haka, can dai ta dubi wata makociyarsu dake tsaye wajen tace "Munnira me ke faruwa?" Munnira tace "Wallahi Umman su Khaleesah nima fitowa ta kenan da naji hayaniyar tayi yawa, amma wai kamar wasu mutane ne da ba a san ko su waye ba suka shiga gidan naku suka yi aika aika, ance a katuwar mota suka zo...." Umma ta kasa cewa komai tana kallonta, da kyar take jan kafa tana rike da su Islam ta shiga gidan har sannan gabanta bai daina faduwa ba, Su Mama Shatu da Mama Zubaida ta gani tsaye da 'ya yan su duk sun yi cirko cirko a tsakar gidan da makota ana ta maida magana, tsakar gidan dai cike yake da jama'a kowa na fadin albarkacin bakinsa, Umma ta dake tace "Wai me ke faruwa ne a gidan?" Mama Zubaida ta wani kalleta a walakance tace "Ina kuwa za mu san me ke faruwa tunda mu dai muna zazzaune sai ga wasu kattin gardawa sun kusa goma babu annuri a tare da su sun shigo mana gida da makamai suna tambayar dakin Malam, basu tsaya iya dakin Malam ba hatta sauran dakunan gidan nan sai da suka shiga..." Sai a sannan Umma ta lura da bakin kofar shiga dakin Malam Ali, gaba daya yayi kaca kaca da takardun da ta mayar daxu bayan su Jay sun dau wanda za su dauka, har kayan cikin dakin sai da aka watso su waje har da er katifarsa da akwatin kayan sakawan sa da butar alwalansa, Umma ta juya tana bin tsakar gidan da kallo taga har dakinta an fito da kaya an yi watsi da su waje, da kyar Umma ta karasa kofar dakin Malam Ali ta leka ciki taga basu bar komai ba, dama ba wasu abun kirki ke cikin dakin ba, can ta juya tana kallon Kishiyoyinta amma ta ma rasa me zata ce, Mama Shatu ta kyabe baki tace "Ni takaicina dakunan mu da suka shiga wai ina takardun da Malam ya ba mu ajiya, ni ko nace mu muka san wasu takardu mu da bamu yi karatu ba ta yaya Malam zai bamu takardu mu ajiye ai sai dai ko ya ba er sa da aka kai turai karatu daga karshe tayi ma wanda ya kai ta karatun butulci wai bata son sa kuma, amma ina mu ina ajiyar takardu mu da muke jahilai" Umma bata tanka ta ba ta duka tana tattara takardun dake watse bakin kofar su Islam suka je suna tayata, a haka duk ta maida kayan Malam Ali cikin dakinsa, su Mama Zubaida sai hararanta suke, can Mama Shatu ta kyabe baki tace "Mu dai mun san ko ma wani takarda suke nema bazai wuce yana da alaka da er ki ba kilan kotu za a shiga, tun da kika haifi yarinyar nan muke shiga jarabawa munana a gidan nan, ko kuma muce tunda aka auro ki, mu da bamu san wani talauci ba balle wahalar rayuwa, daga auro ki karayar arzikin da ba a taΙ“a yin irinsa a tarihi ba ya samu Malam, sannan gashi sanadin er da kika haifo ga abinda ya samu Malam a karo na biyu, daga ke har 'ya yanki babu wani abun alkhairi a tare da ku sai masifa, ina ma Malam zai yada kwallon mangwaro ya huta mu ma mu huta ki tattara ki koma can kasar ku ki auri buzu Ι—an uwanki" Sha'awa dake tsakar gidan wanda tana daga cikin mutanen farko da suka shigo bayan Mama Zubaida da Mama Shatu sun kurma ihu, amma fa sai da gardawan suka fita sannan suka samu bakin ihun neman agaji su da yaransu, Sha'awa tace "Haba Mama Shatu, wannan wani irin magana ce kike yi haka don kin ga Ummansu Khaleesah bata tanka ku a gidan nan, wannan ai cin fuska ne, kar fa wataran ku kureta ayi dauki ba dadi a gidan nan, don mai hakuri bai iya fushi ba wallahi" Wani zagi Mama Shatu ta kundumo mata a fusace, Sha'awa ta rama tace "Wallahi ba dai ubana ba, sai ko in naki uban me gyaran keke dake kabari" Ganin fada na kokarin kaurewa a tsakar gidan Umma da wasu mata suka fitar da sha'awa dake kunduma ma Mama Shatu zagi ta uwa ta uba, ga su Labeebah na kokarin dambe da Sha'awa dake zagar masu uwa su ma duk aka rirrike su, a haka dai aka fitar da Sha'awa dake gyara daurin zaninta da ya kusa faduwa gashi babu komai kasan zanin, tana huci take cewa "Shegu en kutumar uba masu bin bokaye, ko jiya sai da aka bani labarin kun je wajen wani boka na kuma san warce ta raka ku, kun ga kuwa Umman Khaleesah ta fi ku ko a wajen Allah tunda bata san hanyar zuwa gun Malamai ba" A haka dai aka fitar da Sha'awa daga gidan, Umma dai jiki a sanyaye ta tafi kofar dakinta ta tarar su Islam suna ta maida kayan cikin dakin da aka watso waje bayan sun kunna er fitilar dake ba dakin hasken, Noor na kallon Umma tace "Umma kinga babu kayan abincin a inda suke" Umma ta kalli inda Maman Salame ta ajiye mata kayayyakin abincin da su Jay suka kawo taga wayam, tsayawa tayi tana kallon wajen babu ko kiftawa tsabar mamaki yasa ta kasa cewa komai, muryar Nenne taji a tsakar gidan cikin fushi tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, meye haka aka cika gidan nan kamar ana taron farin ciki? Ku yan unguwan nan tsabar munafurci da gulma bakwa tashi shigowa sai iftila'i ya faru sannan ku bi ku cika ma mutane gida ko wacce da warin jikinta, farin cikin iftila'in ku ke ko menene haka? Doo Allah duk ku fita ku ba mutane waje mu ji da daya, ai ba kanmu farau ba, en iska kawai magulmata" Rai bace ta nufi dakin Umma hannunta rike da jarkar manja daya hannun kuma rike da tocilan ta, ta tsaya daga bakin kofa tace "Zahra'u me suka dauka a dakin Alin da suka zo?" Umma da ta zauna gefen katifar ta tace "Shigowa ta kenan nima Nenne, na je gidan Baaba Gaje an sakota daxu da yamma" Nenne ta kalli kayan da su Islam ke shigarwa daki tace "Har dakin naki suka shiga ne? To ni Usama ce min yayi iya dakin Ali suka shiga suka watso kayan ciki, ke kuma wa ya watso naki tsummokaran waje?" Mama Shatu tace "To shi da ya sulale ya gudu ya bar gidan ta yaya zai ce iya dakin Malam suka shiga? Ai babu dakin da basu shiga ba a gidan nan yau, mu ma duk mayar da namu kayan mu ka yi, hatta babban jarkan mangyada da na siya jiya sun dauke, iya shi suka dauka a dakina, Ita kuwa Zubaida kwashin adashin da aka kawo mata suka dauke" Nenne ta fara matsar kwalla cikin rawan murya tace "Lallai na ga abinda ya isheni bai ishi Ubangijina ba, to yan fashi Awdul din ya aiko mana wannan karan? Don dai duk mun san yafi karfin wani kudin adashin da bai taka kara ya karya ba balle wata jarkan mangyada, Allah mun gode maka da wannan rantsattsiyar jarabawan da mu ke ciki mun gode maka Allah, Alhamdulillahi ya Allah, Ina ga in ba tattarawa muka yi muka hakura da zaman birni mu koma kauye gaba daya ba muna cikin mummunan hatsari a Mariri gashi ba mu da gata, kar wataran cikin dare mun saki baki muna bacci su babbake mu, su babbake banza tunda babu me tsaya mana" Ita dai Umma tayi shiru bata ce komai ba, Nenne na kallonta tace "Su kuma samarin da suka sha uban fararen kaya suka zo mana nan suna kwambo dama yaudarar mu suka zo yi bamu sani ba, sun zo nan sun gama cika mana baki sai gashi tunda suka karkade wandonsu suka fita bamu sake ganin keyar su ba, to ina amfanin karya? har da ce min za a saki Ali kwanan nan ashe duk yan iskan gari ne makaryata bamu sani ba" Umma dai kallon Nenne kawai take, Nenne ta mika ma Islam jarkan manjan hannunta tace "Ba ruwana, wahalan da nake ta sha kan Ali ko shi ya halittoni duniya ai sai haka, kai kenan kullum ayi ta garkame ka kamar kasungumin barawo, sai kace wanda yayi ma Allah wani saΙ“on da bamu sani ba, saura kadan kwale kwalen da na hau jiya zan je nema masa taimako ya kife da mu banda Allah ya tsare, to ina dalili bayan ba shi kadai na haifa ba, in ya kasheni sauran su yi yaya? ke ungo amsa ki mika ma uwarki ta tsiyaya min manja, nawa ya kare" Islam tace "To ai an kwashe kayan abincin gaba daya Nenne" Nenne ta gwalo ido tana kallon direction din da aka ajiye kayan abincin taga wayam, bude baki tayi tana kallon Umma tace "Zahra'u ina kayan abincin? Ko kasuwa ki ka kai kika siyar? Fatarar taki ta kai haka Zahra'u?" Umma tace "Saboda me zan kai kayan abinci kasuwa in siyar Nenne, daga zuwa gidan Baaba Gaje in dawo nima na tarar an kwashe kayan abincin" Nenne ta ajiye jarkan hannunta a kidime ta saki salati tana tafe hannu tace "Baki kulle dakin bane Zahra'u?" Umma tace "In zan fita ai ina sa ma dakina kwado, to fasa kwadon aka yi, ga makullin ma a jakata" Nenne ta juya ta fita daga dakin dai dai shigowar Usama wani almajirin Malam Ali dake tare da shi tun yana da arzikinsa, kuma har yanxu dai yana tare da shi, Nenne na haska sa da tocila tace "Yauwa Usama kace iya wani daki mutanen suka shiga a gidan nan?" Usama yace "Iya dakin Alhaji kawai suka shiga" Nenne bata sake cewa komai ba ta nufi dakin Mama Zubaida don yafi kusa da ita, tana dage labulen dakin ta fara haske hasken tocila, sai kuma ta duka karkashin gadon karfen dake dakin ta hango carton din indomie biyu an tura su can ciki, ta kwalo ma Usama kira ya karaso da sauri tana haska masa karkashin gadon tace "shiga ka jawo min kwalayen taliyar yaran can" Ai ko ya shiga ya kwaso su ya fito da su, Nenne ta shiga cikin dakin tana duba bayan kyaure nan ma taga Babban jarkan man gyada ta sa Usama ya fiddo waje, ta gama duba dubenta a dakin bata ga wani kayan abincin ba sannan ta nufi dakin Mama Shatu, a bayan kyaure taga buhun shinkafa daya da quarter an lullube da zani, ta kwalo ma Usama kira shi ma ta saka ya kinkimo su ya fitar waje, a dakin Mama Shatu still taga kwalayen taliya da na maggi da jarkan manja duk ta sa Usama ya fiddo su waje, Nenne na kallonsa tace "Kwashe su ka mayar dakin Zahra'u Usama" Yace "To Nenne" Sai a sannan Nenne ta juya tana kallon su Mama Shatu da suka yi wuki wuki da ido ko wacce na kokarin diban ruwan alwala a buta, Nenne tace "An dai yi asara duniya da lahira, barayin banza barayin wofi, tirrr da halin ku, wato ga sabon jarin kayan abinci kun samu ko, tunda Zahra'un ta maida kanta er wahala warce bata san ciwon kanta ba, da ban ce a tsam min manja ba shiru zata yi maganar ta bi rariya ta bar ku da haram, ko zama da ku kadai ya isa ya dinga jefa Ali a masifa iri iri, ai ba kyau zama da jahilai shine kawai bai gane ba" Daga haka ta juya ta koma dakin Umma. Khaleesat na bakin pampon dake compound din Aunty Farida tana wanke wanke, ita kadai ce a gidan gaba daya don duk sauran tenant dake gidan sun fita aiki, Aunty Farida kuma ta tafi kasuwa, juyawa Khaleesat tayi jin an bude gate, ta mike tsaye tana kallonsa, murmushi ya sakar mata ya rufe gate din ya karaso cikin compound din shi ma yana kallonta, ta sauke idonta a hankali tace "Sannu da zuwa" Yace "Good morning Halysaah" Ɗan murmushi tayi ta sunkuyar da kai ta gaishesa sannan ta juya ta tafi ta bude masa kofar shiga parlon Aunty Farida tana kallonsa, yace "Aunty fa? ina ta kiran wayarta no response" Khaleesat tace "Eh ta bar wayar a gida ne ta tafi kasuwa" Ya kalli plastic chair dake veranda din Aunty Farida yace "Let me seat here ba sai na shiga ba, i just came to check on you" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "I really appreciate Housemate" Yace "To ki zauna mana" Ta kalli second chair din dake wajen sannan ta zauna, sake gaishesa tayi da ladabi tana kallonsa, yace "Lafiya lau Halysaah, how is ur body?" Tana wasa da gefen karamin veil din jikinta tace "Naji sauki" Yace "To amma naga kin rame, baki cin abinci ne?" Tayi shiru, yace "Baki ci ko?" Ta Ι—an yi murmushi tace "Ina Ι—an ci kadan" shiru ne ya biyo baya for almost 30 seconds, ta Ι—an daga kai ta kallesa taga kansa a kasa, ajiyar zuciya ya sauke calmly yace "Everything will be alright soon in sha Allah Housemate" Nan da nan hawaye ya cika idonta, da kyar tace "But i don't know my mom's condition, i am really worried" Jay yace "Don't worry, Umma tasan kina nan, mun je can gidanku da Ajay, i assure you everything is fine back home do not worry ur self pls, yanxu dai we are working on clearing ur dad first before anything, soon in sha Allah he will be free from the debt" Hawaye na sauka idonta tace "To amma ni bazan iya zama da Abdul ba tsoron sa nake wallahi, kawai torturing dina zai yi yayi revenging abinda nayi masa, i am afraid" Jay yace "Do not be Housemate, we won't allow that happen in sha Allah, we will go to any extent na ganin hakan bai faru ba" Khaleesat dai tayi shiru tana share hawayen idonta, after some seconds yace "Baki tambayi Ajay ba?" Ta daga kai tace "Na zata tare ku ke yana waje" Jay yace "Not at all yana kano, bai ma san nayi tafiya ba, i took an early morning flight, zuwa 12 noon kuma zan koma kano in sha Allah, i just came to check on you" Khaleesat na kallonsa cikin sanyin murya tace "Nagode sosai, kuma naji dadi" Ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe sha daya saura yace "I will be leaving for the airport now kar inyi missing flight dina, kafin Ajay yayi noticing i am not home ya fara damuna da kira" Khaleesat tace "Ko ruwa baka sha ba, ko in kawo maka shayi? Kilan ma baka yi breakfast ba ko?" Da damuwa tayi tambayar tana kallonsa, Yace "No i am okay Housemate" Wayarsa ne ya fara ring ya ciro yana kallon screen din yayi murmushi sannan ya nuna mata screen din taga Ajayn ne ke kiransa, mayar da wayar yayi aljihunsa sannan ya fiddo 100k ya mika mata yace "In case you need anything Halysaah" ta girgiza masa kai tace "A'a Nagode, bana bukatar komai wallahi" Mikewa yayi ya ajiye mata kudin a kafarta ya fita daga balcony din yace "Take care of ur self Housemate, idan na sake samun lkci ko zuwa nan da few days ne zan dawo in sha Allah, my regards to Aunty Farida" Khaleesat ta mike tana kallonsa ta kasa ce masa komai wasu sabbin hawayen suka cika idonta, ya daga mata hannu kawai ya nufi gate don bai ma son ganin hawayen nata, tana kallonsa har ya fita sannan ya rufo gate din, parlon Aunty Farida ta shiga ta zauna kan kujera ta rufe fuskarta tana rera kuka tana shessheka..... Bayan few weeks na zirga zirga a cikin garin kano, da kuma zuwa court lauyan su Jay yayi Succeeding na amsan Bail din Malam Ali, afterward suna sa ran kotu tayi dismissing claim din Alhaji Musa saboda previous debt forgiveness dake kasa, a kuma yi masa imposing monetary sactions for abuse of process, all this weeks Jay da Ajay where so cautious of der movement in kano and they were at alert In case of necessity ko kadan basu ba Abdul chance din yi masu ba zata ba cause sun san bazai rasa informant a unguwan ba, ranan da suka yi dropping din Malam Ali a gida bayan kotu ta bada bail dinsa farin ciki gun iyalinsa da wasu yan unguwan ba a cewa komai barin ma Umma, sai shigowa gidan ake ana taya sa farin ciki, shi ko Malam Ali har kasa ya duka cikin ladabi yana gode ma Jay da Ajay, shi dai Ajay ya juya ya koma jikin motarsa ya tsaya ya rungume hannu, ga motar escort dinsu a bayan motar tasa, Jay har ya gaji da ce ma Malam Ali ya dena masu godiya, Calmly yace "Don Allah Baba ka dena mana godiya, mu saboda Allah muka yi..." Malam Ali na gyada kai yace "To... to...to wannan gaskiya ne, Allah Ubangiji ya maku albarka, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara daukaka, Nagode Nagode" Duk a birkice yake godiyan, Mama Shatu ta dauko tabarma ta shimfida tace "Taho ka zauna ka huta ko zaka dawo seti Malam, naga duk a firgice kake" Nenne ce ta shigo unguwan bayan wani almajiri yaje har gidanta ya sanar mata Malam Ali ya dawo, mayafin nata ma a baibai ta yafa ga dankwali da ta kima a kan mayafin tana hade hanya ta taho gidan Ι—an nata, bata kula da Ajay a kofar gidan ba ta shige ciki da sauri, Ajay ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihunsa yana duba me kiran sa, gyara tsayuwarsa yayi yana kallon screen din wayar babu ko kiftawa ganin Aunty Farida ke kiransa, haka kawai yaji zuciyarsa ta harba don Aunty Farida bata kiransa all this while, in ma da wani abu shi ne ke kiranta, ya kalli Jay da ya fito daga cikin gidansu Khaleesat, har sannan ya kasa daga kiran Aunty Farida.

[6/10, 6:29 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Jay ya karasa har inda Ajay ke tsaye yace "I think we can take our leave now, nan da friday sai a basa makullin sabon gidan, we just hope he will accept it" Shi dai Ajay bai ce masa komai ba don bai ma san me yake cewa ba, ganin yanayinsa Jay yace "Are you alright Bruh?" Jin Ajay bai basa amsa ba ya kalli wayar hannunsa that was still vibrating yace "Who is calling you?" Ajay ya sake kallon screen din sannan yayi picking dab da kira na biyu zai katse, kunne ya kai wayar yayi shiru yana sauraron yaji abinda Aunty Farida zata ce, muryar Khaleesat yaji a hankali tace "Good evening, Plss can i speak to my Housemate?" At first shiru Ajay yayi, can babu yabo babu fallasa yace "About?" Khaleesat ta girgiza kai murya can kasa tace "Ba komai, kawai dai ina son zan masa magana ne" Jay dai kallon Ajay kawai yake don bai san da wanda yake wayan ba, a takaice Ajay yace "Don't you have his digit?" Bai jira cewarta ba ya katse wayar ya mayar aljihu, Jay yace "Who is that?" Banza Ajay yayi masa ya bude driver seat ya shiga ya tada motar fuskarsa a daure, Jay ya daga shoulder sannan ya zaga ya shiga gaban motar shi ma bai sake kulasa ba, Ajay ya ja motar suka bar anguwan motar  bayansu na biye da su. Bayan sallahn magariba Malam Ali na zaune tsakar gida tare da Nenne da duk matansa sai yaran gidan gaba daya, Nenne ce kadai zaune kan kujera er tsugunno, sauran duk kan tabarma suke a zaune kowa na jiran jin dalilin zaunar da su da Nenne tayi, Umma dai na kusa da bakin kofar dakinta da su Islam da Noor a jikinta, Nenne tayi gyaran murya tace "Da farko dai nayi farin ciki ainun da dawowan Ι—a na daga furson a karo na biyu, ina rokon Allah ya sa iya bakin wahalarsa kenan sannan muna fatan yayi zuwan karshe kenan, wa ennan samari da suka zo suka tsaya mana kuma har suka kubuto da Ali Allah Ubangiji ya masu albarka don da farko na zata makaryata ne kawai en neman suna, duk da dama inda naje ance min za a roki Allah ya kubutar da Ι—a na, nafi tunanin ma rokon Allahn da aka yi ne kawai hakan ta faru ba wai don samarin nan ba, mun dai gode koma ya ya ne, sannan shawaran da zan bada shi ne muyi bulaguro mu koma kauye gaba dayanmu na en shekaru kafin komai ya lafa, mu ma hankalinmu zai fi kwanciya da hakan don Alhaji Musa da tsinannen Ι—an sa ba barin mu za su yi mu zauna lafiya ba, duk da kotu ta wanke Ali amma Allah kadai yasan wani sharrin za su billo da shi don mutane ne wa enda babu Allah a ransu, wallahi sai su iya sa wa duk a kona mu cikin dare muna bacci, kunga ance zaman lafiya yafi zama Ι—an sarki shi sa cikin rufin asiri mu tattara komatsanmu ko zuwa gobe da magariba ne Ali ya mana shatan katuwar tirela mu koma kauyen mu" Mama Zubaida da Mama Shatu da suka saki baki suna kallon Nenne kusan a tare suka ce "Kauye kuma Nenne?" Nenne na kallonsu da kyau tace "Kwarai kuwa kauye, don dama can ne asalinmu, na gaji da tsallaka kogi cikin kwale kwale zuwa neman ma Ali taimako wataran inje in kife, gwara tun da sauran mutuncinmu mu bar garin nan" Mama Zubaida na girgiza kai tace "Inaaa, ai bazata saΙ“u ba gaskiya, sai dai ni a bar ni a nan in ci gaba da kasuwancina ina rufa ma kaina da 'ya ya na asiri, akan matsalar da buzuwar matarsa da er ta suka jawo baza a cucemu a mayar da mu riga ba, bazai ma taΙ“a yiwuwa bane gaskiya" Mama Shatu ta cafke tace "Sai dai ya tattara matarsa da 'ya yanta su kuma kauye Nenne, amma mu kam muna nan tunda ba mu ko 'ya yanmu muka jawo magana ba, dama mu ke ciyar da kan mu balle mu ji tsoron zamu rasa abinci" A fusace Nenne tace "A yaushe ku ka fara ciyar da kan naku munafukan Allah? ba sai bayan da ku ka tsiyace sa da fararen kafafuwan ku ba tukun? Ai ko Alhamdulillah kowa zai ma Ali shaidan kula da iyalinsa banda jarabawan shegun mata da Allah ya hadasa da, ku ne nan ku ka ja masa karayar arziki, dama ance min dukkanin ku babu alkhairi a tare da shi gwara ma Zahra'u, wallahi ce min aka yi in dai zai rabu da ke da Zubaida to arzikinsa zai dawo kaca kaca har fin na Ι—a, Zahra'u ce kadai matarsa ta arziki aka ce min, da zai ji ta nawa ma duk ya sallameku in ga inda za ku koma idan ba kauyen ba, ke Zubaida kin manta kauyen da uwarki da ubanki suke sai sati sati ake kawo ruwan pampo? Kin manta ko wutar lantarki ba a ja maku har yau a kauyen ba? Kauyen da muka je na dawo ina ta amai da gudawa watana daya a asibiti amma har kina da bakin kushe namu kauyen da babu abinda babu? To wani Ι—an iskan ne ma yace Rano kauye ce tukunna? Sannan ke shatu baza ma a kira garin iyayenki da kauye ba sai dai ace daji, haka nan muka dawo kano maguzawan mayu suka kamani da kyar aka samo kaina ba don Allah yayi da sauran shan ruwana a duniya ba da tuni na rasu wallahi" Shi dai Malam Ali yayi tagumi yayi shiru bai ce komai ba don tun kan Nenne ta kawo wnn shawara dama yake jin gwara ya koma garinsu don bai san da me Alhaji Musa da Ι—an sa za su billo ba kuma, shi dai bai yarda kotu zata wankesa akan kudaden nan masu yawa ba gani kawai yake dadin baki su Ajay suke masa, Nenne tace "Yau ga samun waje kai, ita Zahra'u me yasa bata kushe shawarata ba sai ku masu fararen kafa, ko da yake ita ta guduwan er ta da ta shiga duniya ma take, mu bar ta taji da wannan ma" Mama Shatu tace "Wace er ta? Ai wallahi ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Zahra'u tasan inda er ta take, mu dai ne kawai aka rena ma wayo aka raina mana hankali" Mama Zubaida tace "To ai ba ma sai kin rantse ba Shatu, kwarai kuwa Zahra'u tasan inda Khaleesat take" Nenne dai sai kallon Umma da ko kallon kishiyoyin nata bata yi ba take, a hankali Nenne tace "Lallai biri yayi kama da mutum, na kuma yarda da maganarku don Zahra'u da na sani da har yanzu tana nan kan darduma sanye da dogon hijabi tana rike da carbi tana kuka ba dare ba rana duk ta fita hayyacin ta, kawarta Uwar Salame da makociyarku sha'awa me daddawa su yi ta shigowa suna dannarta su zazzauna kusa da ita kamar me takaba, amma ina lura da ita yau kusan sati uku kenan tana ta harkar gabanta kamar babu abinda ya faru, nima dai ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba tasan inda Khaleesah take" Malam Ali ya gyara zama yana kallon Umma cikin lallami yace "Kiyi ma girman Allah Zahra'u ke da er ki ku rufa min asiri yanda Allah ya rufa maku, duk inda er nan ta tafi kiyi masu waya ta dawo ta amshi auren mijinta hannu bibbiyu, dama Allah ya riga ya kaddara Abdul ne mijinta  mu din banza ne za mu canza hakan? don girman Allah ta rufa min asiri, ina cikin tashin hankali har yanxu wallahi don ban san kuma da me Alhaji Musa da Ι—an sa za su dawo min ba, rufin asirina shi ne na damka masu Khaleesah kawai, in har suka kasheni wallahi banza kawai za su kashe tunda ba galihu ne da ni ba, tunda aka maida ni furson din nan nake rashin lafiya me tsanani, yanzu haka maganar da nake yi kirjina kamar an aza min katuwar dutse, ku yi min rai ke da er ki" Kamar zai yi kuka ya kare maganar, Nenne na matsar kwallan da babu tace "In wani abu ya same ka dama da Zahra'u da er ta zan yi kuka wallahi, don su ke kokarin salwantar min da kai ta karfi da yaji" Umma da hawaye ya cika idonta tace "To wai ta yaya zan san inda Khaleesah take ni ba waya ba balle ku yi tunanin tana kirana? Ko kun ga ina zuwa wani waje daga cikin dakina ne?" Mama Zubaida tace "Na rantse da wanda raina ke hannunsa Zahra'u kinsan inda makirar er ki take, don haka sai dai ki rena ma wani hankali amma ba mu ba, duk abinda ya samu mijinmu dama har karshen duniya mun yi ta ja ma ke da 'ya yanki Allah ya isa kenan, banda samun waje ita Khaleesah har tana da ta cewa da har zata bude baki tace bazata zauna da Abdul ba? Da me tafi Abdul din banda rufa mata asiri da yayi zai aureta? Mutumin da ya maida ta fess ya maida ta mutum ya kashe mata dukiya babu adadi don butulci da samun waje tace ita bata son sa kuma a ina aka taΙ“a tafka wannan iskancin? Wallahi ba a samu wanda zai ci ubanta bane shi yasa ta samu waje da yawa" Umma tace "Tun da har kuke tunanin nasan inda take kuma baza ku rasa sanin inda take ba ai, kilan ma za ku fi ni sani, don haka sai ku je ku fito da ita ku kai ta gidan Abdul din" Umma na kai wa nan ta mike ta shige dakinta, Mama Shatu tayi kasa da murya tace "Al-qur'an tasan inda take, da bata san inda take ba wallahi da har yau bata dena koke koke ba kilan har sai tayi rashin lafiya, kuma ni na ma fi zargin tana wajen kanwarta ne a garin Legas wallahi, in da ba haka ba ai da tuni mun ga Farida a gidan nan kamar an jefota amma gashi kusan sati uku har yau shiru Farida bata zo ba" Mama Zubaida tace "Ahaf ai mu ba yara bane" shi dai Malam Ali sai zazzare ido yake, Nenne tayi kasa da murya tace "Gaskiya na yarda da maganarku, don nima ina ta mamakin me yasa har yau farida bata zo ba, ita da ko tari yayarta tayi zata hawo mota ta kamo hanyar kano, amma ace an rasa Khaleesah yau sati uku shiru bata kamo hanya ba, ai da alamar tambaya" Malam Ali ya share zufar goshinsa duk da sanyin da ake shi ma yayi kasa da murya yace "To yanxu meye shawara? Ko ni zan shirya in tafi Lagos din ne?" Sosai hankalin Umma dake tsaye bakin kofarta daga cikin daki ya tashi don duk tana jin abinda suke cewa, Mama Zubaida tayi kasa da murya tace "Ai ban ma yarda da shiga dakin da tayi ba kilan er uwar zata kira, ko da yake bata da waya, kawai ina ga a gaya ma...." Mama Shatu ta Ι—an tsunguli Mama Zubaida alamar tayi shiru, lkci daya Mama Zubaida tayi tsit, Nenne ta mike tana kallon Malam Ali tace "Mu je daga gefe mu yi shawara Ali" Mikewa Malam Ali yayi ya nufi can hanyar fita daga compound din Nenne na biye da shi, Mama Shatu ta mike tayi ma Mama Zubaida alamar su shiga ciki, suna shiga daki Mama Shatu tace "Ke ya muna neman maganar auren nan ya rushe gaba daya ko zai hakura yace a basa Labeebah ko Lamisah amma kike basu shawaran su je Lagos?" Mama Zubaida tace "Wallahi gaba daya na sha'afa kinsan kwakwalwar tawa, kuma kece kika kawo maganar Khaleesah, tun asali ma bai kamata mu ce komai ba gashi yanxu mun karkato da hankalinsu zuwa Lagos, sai fa Malam ya iya shiryawa ya kama hanyar Lagos wallahi" Mama Shatu tayi shiru, can tace "Ai ko in yaje lagos din nan shikenan tsarinmu ya lalace don taso keyarta zai yi su dawo kano ya mika ma Abdul ita, kinga shikenan mun tashi a tutar babu mun kai ba malamai kudadenmu a banza, tunda duk mun san Abdul din na sonta kuma hannu bibbiyu zai amsheta su fara rayuwar aure" Mama Zubaida tace "Toh kuwa ina ga da kaina zan kira Farida ince mata in har tasan Khaleesah na wajenta to tayi maza maza su bar gidan don Malam zai kama hanyar lagos tare da Abdul" Mama Shatu tace "A'a bari in shiga dakin Zahra'u in gaya mata hakan, tunda ga Nenne da Malam can sun kebe bamu san maganar da suke ba" Bata jira cewar Mama Zubaida ba ta fita zuwa dakin Umma, Zaune ta tarar da Umma bakin katifarta abun duniya ya isheta gashi babu waya hannunta, kuma in tace ta fita daga gidan ta amshi waya a makota tasan dole za a zargeta, kuma daxu da safe suka yi waya da farida ta wayar Mama Salame take sanar mata jibi za su Nijar da Khaleesat,  Mama Shatu na kallon Umma tayi kasa da murya tace "Zahra'u, ga can Nenne da Malam suna shirya yanda za a tafi legas wajen Farida gobe da asubar fari, in dai kinsan Khaleesah na wajenta wallahi kiyi maza ki buga mata waya su bar gidan su tafi wani wajen, a ajiye batun kishi a gefe abinda baza ka so ma danka ba kar ka so ma Ι—an wani, don duk mun san Abdul ba mutumin kwarai bane, kuma a zamanin nan an dena auren dole, mu ma ba a mana dole ba don haka baza mu yi ma 'ya yan mu ba" Mama Shatu na kai wa nan ta juya ta fice daga dakin, Umma ta mike gabanta na faduwa ta Ι—an leka tsakar gidan taga Nenne da Malam Ali tsaye a can lokon tsakar gidan suna magana kasa kasa.... Jay ya fito daga kitchen hannunsa rike da mug din shayi yana juyawa a hankali, Step Mom din Ajay ce zaune parlon cikin shiga ta alfarma, a ranan ta sauka gidan tare da jakadiyarta sun dawo daga kaduna, Jakadiyarta na dinning area tana yanka mata fruit, Jay ya tsaya dai dai inda yake don bata san ya fito daga kitchen din ba, da wani kallon tsana kawai yaga take bin Ajay dake haurawa sama hannunsa rike da laptop dinsa, after few seconds Jay ya ci gaba da juya shayin hannunsa yana kallonta, tana jin sound din cokali ta juya da sauri tana Ι—an murmushi ta hau canza channel din TV, shi dai Jay ya karasa cikin parlon bai sake kallonta ba, Jakadiyarta ta taho ta ajiye mata fruit din da ta gama yankawa cikin ladabi take sanar mata ga kayan marmarin, Cike da isa Aunty ta dau Apple ta fara ci, ta Ι—an kalli Jay ganin sama zai wuce shi ma tace "Gobe Abbanku zai shigo wani taro" Jay yace "Mun yi waya da shi" Daga haka shi ma ya wuce sama, ta wani taΙ“e baki ta bi sa da kallo, Jakadiyar da ta zube gefenta cikin girmamawa tayi kasa da murya tace "Ranki shi dade, Allah ya ja zamaninki, daxu na jiyo mana wani labari Allah ya sa zaki yi maraba da wannan labarin" A takaice Aunty tace "Labari akan me?" Jakadiyar ta gyara zama tace "Akan Yarima" Aunty ta ajiye Apple din hannunta ta ba jakadiyar gaba daya attention dinta tace "Me kika jiyo?"

[6/11, 8:28 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Har mahaifin Abdul ya gama bambamin da yake yi a parlon Momy kamar zai ari baki bata ce masa komai ba illa rungume hannu da ta yi tana zaune kan kujera tana girgiza kafa fuskarta babu fara'a, Meemah dake zaune parlon ita ma dai bata ce komai ba fuska a murtuke, Alhaji Musa yayi bala'in sa me isarsa sannan ya juya zai bar parlon a fusace, sai kuma ya sake dawowa yana huci yace "Ina wawan Abdallan yake? Ina yake yaga abinda rashin tunaninsa da rashin daukan shawarar sa ya ja min" Momy ta tabe baki ita ma cike da takaici tace "Ai Alhaji yau kwana uku curr rabonsa ma da gidan gaba daya, kuma ba a samun sa a waya, ya kashe wayar" Rai bace Alhaji Musa yace "Duk shi ya ja min wannan bala'i ina zamana, wa yace masa dama ana harkar arziki da talaka? Sam ai ba a shige ma talaka duk yanda yake kuwa, tun asali zuri'ar da yake son in hada da wancan barawon mutumi ba wai nayi na'am da hakan bane, kawai bani da yanda zan yi da Abdallah ne" Momy ta gyara zama zuciyarta na tafarfasa tace "Atoh dai, har na gaji da nanata wannan sentence din da kayi Alhaji, ai ba a abun arziki da talaka don tun asali dama a tsiyace ya zo duniya kuma a tsiyace zai koma, kana zaman zaman ka gashi Abdullah ya ja maka asaran makudan kudi har da su taran kotu, wai kai da aka zalunta kai ne kuma da biyan tara saboda rashin adalci, ai Abdul bai kyauta mana bai duba mana ba, ace shi bazai dau maganata a matsayina na uwarsa ba? Babu yanda banyi discouraging dinsa kan tsinanniyar yarinyar nan ba na nuna masa ba ajinsa bace yaki saurarata wallahi, kyanta ne kawai ya rudesa wato kyan Ι—an maciji, har tayin er aminiyata nayi masa amma firr yaron nan yaki, to ga dai abinda ya ja mana" Meemah tace "Ni duk ba wannan ba Momy, kawai so nake in san wasu 'ya yan shegun ne suka tsaya mata haka har suka maida case din kotu? Sannan ga auren ma suna kokarin kotu ta rabasa ta karfi da yaji, kun ga kenan mun tashi a tutar babu, kuma babu tantama duk yanda aka yi ma su suka boye yarinyar, su waye en iskan nan ne?" Alhaji Musa na safa da marwa a parlon yace "Don kotu ta kori karar nan ba shi ke nufin na bar wannan mutumi da ya salwantar min da dukiya ba, mu zuba mu gani da shi, sai na lahira ya fi sa jin dadi wallahi" Daga haka ya bar parlon kamar zai tashi sama, Momy ta sauke wani ajiyar zuciyar takaici tana girgiza kai tace "Abdallah bai duba mana ba wallahi, ya kaskantar da mu a idon duniya kawai, wai yau talaka ne ya ci nasara a kan mu a kotu, this is a big slap to us, kuma ko uban menene dalilinsa na dinga kashe waya ba a samun sa oho? Ni taran da aka ci Alhaji ne ma yafi Ζ™ona min rai wallahi, ga mari ga tsinka jaka, ki sake kiran wayarsa kiji ko zai shiga" Meemah tace "Baza fa a samesa a waya ba Momy, mu da ganin Abdallah sai ya cika burin dake ransa kema ai kin san halinsa, gwara ma ki saka ma ranki salama mu bi sa da addu'a kawai" Momy ta kalleta tace "Wato kin san inda yake kenan?" Meemah tace "Ke dai kawai ki bi sa da addu'a Allah ya basa nasaran abinda ya saka a gaba Momy, amma shegiyar yarinyar nan ai kamar ta shigo gidan nan ne babu me hana hakan, don baza mu yi biyu babu ba" Momy ta tabe baki tace "Har ga Allah ni so nayi kawai ya hakura da er matsiyatan nan Meemah, kada tsautsayi ma yasa a hada iri da ita mu shiga uku, hada iri da talaka ai ci baya ne Meemah, don ni har cikin raina naki jinin talaka wallahi balle in hada zuri'a da su" Meemah tace "To ai dama bama fatan a hada iri da ita Momy, personally bazan ma bar hakan ya faru ba trust me, kawai ta shigo gidan ta gane Allah daya ne, ke kuma ki fara masa fafutukar wani auren da wuri wuri" Momy dai tayi shiru, can ta tabe baki tace "Allah ya sa ya saurareni to" Meemah tace "Haba dai zai saurareki, da kaina zan masa magana, a samar masa yarinya dai dai class dinsa" Momy tace "To ai shikenan, yanxu tracing din matsiyaciyar yarinyar ya sa a masa kenan?" Meemah tace "Ko ma dai menene mu dai mu zuba ido mu bi sa da addu'a kawai Momy" Mikewa Momy tayi tace "Bari in je in lallaba babanku, na dade ban ga ransa ya baci irin haka ba, haba ai abun da bacin rai, wai ace talaka yayi nasara akan ka a kotu bayan kai ne me gaskiya ai abun da ciwo" Daga haka ta wuce sama, Meemah ta dau wayarta tayi dailing number da take samun Abdul da shi ta tashi ta shiga dakin dake parlon. Da asuba ko sallah ba ayi Malam Ali ya fito da er jakar da yake tafiya da shi bayan ya mulke jikinsa da basilin saboda sanyin da ake, bin dakunan matan nasa yayi duk ya kwankwasa masu kofa, Mama Zubaida da Mama Shatu suka fito suna kallonsa da mamaki suka ce "Lafiya Malam?" Mama Zubaida tace "Ko tafiya kauyen ne ya taso?" Shi dai bai tanka su ba ya dinga goge takalminsa da yayi Ζ™ura, Umma ce karshen fitowa ita ma ta tsaya tana kallonsa ta kasa cewa komai don tasan manufarsa, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya tsabar yanda hankalinta ya tashi, Nenne ce ta shigo gidan yafe da zaninta tana ganin Malam Ali tace "Yauwa ko sallah kar ka jira kayi idan kaje tashar kayi a can Ali, ga er soyayyiyar nama da gurasa na kullo maka ka ci a hanya" Mama Shatu tace "Tafiya zai yi ne Nenne?" Nenne tace "Babu ruwan ku, ku dai ku yi masa fatan Allah ya kiyaye hanya" Malam Ali ya amshi kullin nama da gurasan da Nenne ke mika masa, yana kallon matan nasa yace "Toh sai Allah yayi min dawowa" Mama Shatu tace "To ai shikenan, Allah Ubangiji ya tsare Malam" Mama Zubaida ma tace "Allah ya tsare duk da muna da hakkin ka sanar mana inda zaka je da asuban fari Malam" Nenne tace "Bazai sanar ba Zubaida, uban me sanin inda za shi zai kara maki?" Mama Zubaida ta juya ta koma daki, Mama Shatu ma ta tabe baki ta koma dakinta, Nenne ta kalli Umma tace "Wato ke ce isasshiyar da bazata yi masa Allah ya kiyaye ba ko Zahra'u" Shi dai Malam Ali tuni har ya fice daga gidan, Nenne na nuna Umma tace "Mugun abun ku zai kare maku da ke da er ki wallahi, babu wanda ya isa ya salwantar min da Ι—a na lokacinsa bai yi ba" Daga haka ta bi bayan Malam Ali da sauri zata rakasa bakin titi ya samu adaidaita sahun da zai kai sa tasha. That same day bayan an idar da sallahn asuba Jay ya shigo parlorn Mai martaba da sleepy face ta dalilin kiran da yayi masa, ganin irin zaman da Abba yayi kamar yana fadarsa ya gane serious issue Abban zai yi discussing da su kenan, ya kalli Ajay dake parlon zaune shi ma alamar kiran sa Abban yayi, Aunty ma na zaune parlon, Jay ya sauke kansa ya karasa kusa da Ajay ya zauna kasan lallausan carpet din parlon, dabi'ar Abba ne sai ya iya minti biyar zuwa goma kamar me nazari kafin ya fara magana in ya tara ku, Jay ya sunkuyar da kansa ya lumshe ido, Ajay ya Ι—an kallesa sanin sai ya iya bacci a haka, ai ko yaga baccin yake, Ajay ya Ι—an tunkudesa da elbow dinsa, Jay ya bude ido da sauri yana gyara zama, shi dai Abba kallonsu kawai yake, At last Abba yayi gyaran murya cikin nutsuwa yace "First of.... Ina son sanin zaman me ku ke har yanxu a garin nan baku karasa gida ba?" Duk suka yi shiru babu wanda yace komai kansu a kasa, Calmy Abba yace "Ohk take ur time, amma kuyi kokari ku je gida kafin hutun ku ya kare, Secondly.... maganar da nayi da ku a Maryland naji babu wanda yace min komai a kai har yanxu, ga lokacin da na baku ya cika, nayi maku uxurin mantuwa shi yasa nake tunatar da ku yanxu..." Nan ma duk suka yi shiru babu wanda yace komai, shi ma Abban yayi shiru yana kallonsu yana jiran amsa a duk sanda suka shirya, sun san shirun da Mai martaba yayi amsarsu yake kira ko da zai dau 10min ko fin haka ma kafin su basa amsan he won't mind zai jira su patiently, sanin halin Abban nasa yasa Ajay ya daga kai, Softly yace "Ayi hakuri ranka shi dade ba mantawa muka yi ba, in sha Allah we are working on that very soon" Mai martaba yace "Is that so?" Ajay ya sauke kansa don kalman Abba na nufin bai gamsu da abinda yace ba kenan, Shi dai Jay yaki dago kai, a hankali Ajay yace "A gafarce mu a Ι—an kara mana lokaci Abba..." Aunty da har ta fahimci maganar da ake ta Ι—an yi gyaran murya ta nemi permission din magana gun Mai martaba, ya gyada mata kai alamar ta fadi abinda zata fada, cikin nutsuwa tace "In na fahimci maganar da ake ranka shi dade, magana ce akan su fito da matan aure duba da yanda shekarunsu ke gaba ba baya ba, wannan magana kuma ba sabuwar magana bace don an fi shekara 3 ana yin ta amma babu wani progress, a takaice basa daukar maganar da muhimmanci, to amma dai ina ga ka Ι—an sha'afa ne ur Highness, don shi Jawwad ai akwai maganar sa da Hadeeyah a kasa duk da ba wai maganar tayi karfi bane kuma wannan hadi, hadi ne me kyau da zai kara karfafa zumunci don mahaifiyar Hadeeyah jininka ce kuma ita ta kawo wannan shawara duk da Fulani wato mahaifiyar Jawwad uwar dakinta ce tun asali, shi kuma Junaid a yanda na lura da shi zai fi maraba da zabin ka garesa duba da nature dinsa da rashin choice dinsa, don haka shi Jawwad a tsaida maganar sa da Hadeeyah kawai ina ga hakan zai fi, shi kuma Yarima i think we should get him a princess from neighbouring states, ko ni zan iya jagorantar hakan don arranged marriage zai fi suiting dinsa duba da nature dinsa, kuma ina son a bar komai a hannuna ranka shi dade..." Ajay ya daga kai ya kalleta zai yi magana mai martaba ya dakatar da shi, Ajay ya sauke kansa, Speaking Calmly Mai martaba dake kallon Ajay da Jay yace "Za ku iya tafiya, Allah yayi maku albarka" Sai a sannan Jawwad ya dago kai ya kalli Aunty dake Ι—an murmushi ganin Mai martaba yayi na'am da shawaranta, tuni Ajay har yayi disappearing daga parlorn fuska a murtuke, Jay ya mike shi ma ya bi bayan Ajay yana tafiya a hankali, bai taΙ“a sanin baya son Hadeeyah da aure ba sai yau da Aunty ke bada shawaran a tsaida ranan aurensu da ita, yasan kuma duk abinda Aunty tace kamar Abba ya aikata hakan ya gama ne, kawai yaji hankalinsa yayi mugun tashi yaji wani zufa na keto masa, dakinsa ya shige ya kulle da makulli ya jingina da kofar ya lumshe ido zuciyarsa na bugawa, Ajay na shiga dakinsa shi ma ya kulle da makulli ya zauna gefen gado ya dafe kansa da hannu biyu, this is not the first time da Aunty ke kasalanda akan duk abinda ya shafesa gashi Abbansa baya basa listening ears ko me Aunty tace masa kawai haka za ayi abun nan komin munin abun, at this point he felt he is of no importance to his father, he felt dejected, and it's been like this for so many years, he have no one to stand for him, a hankali ya juya yana kallon wayarsa dake vibrate, Number Aunty Farida ya gani a gaban screen din wayar, ya kalli agogo yaga karfe shidda da minti biyar na safe, request din Khaleesat na jiya da ta kirasa ya tuna, hakan yasa har kiran ya katse bai daga ba knowing she might be the one calling, kiran ya sake shigowa ya kalli screen din nan ma bai daga ba har ya katse, sau hudu kiran na shigowa continuously, hakan yasa ya maida attention dinsa kan wayar ya Ι—an yi jim with different thought running his mind, ganin kiran ya katse an sake kira making it the 5th time of calling yasa ya dau wayar ya daga ya kai kunne yayi shiru waiting to hear who is on the line, a hankali ya mike jin abinda Aunty Farida ke ce masa ta wayar, bai san sanda ya zame wayar daga kunnensa ba rate din heartbeat dinsa na karuwa, da sauri ya nufi kofarsa ya bude ya fice daga dakin ya murda kofar dakin Jay yaji a kulle, knocking ya dinga yi non stop kafin Jay ya bude kofar da mamaki yana kallonsa yace "What is it?" Ajay ya shiga dakin yana shafa gashin kansa da wani expression yace "He tracked her to Lagos" Still Jay yayi a inda yake tsaye ko kwakkwaran motsi baya yi yana kallon Ajay, Ajay ya ja numfashi sannan ya zauna kan kujeran dakin ya lumshe idanuwansa ya jinginar da kansa jikin kujeran trying to calm himself, Jay was speechless and shock at the same time, da kyar ya ja kafa ya zauna gefen gadonsa ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi, kamar an tsikare Ajay ya mike yace "Book us ticket to Lagos" Daga haka ya fice daga dakin.

[6/12, 8:02 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Aunty Farida ta share hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsu Ajay da kyar tace "Wallahi ban san ko har su nawa bane a motar, ban ma san ya motar take ba tunda ina cikin gida sanda abun ya faru, yaran makota dake diban ruwa a bakin rijiyar tare da ita ne suke cewa kawai suna diban ruwa sai ga motar ta shigo street din, wasu mutane suka sauka a motar suka ja ta zuwa cikin motar suka tafi da ita, a sannan an idar da sallahn subahi kenan kun ga gari bai waye ba ai" Ajay was speechless, bai taΙ“a zama confuse haka a rayuwar sa ba don ya ma rasa abun cewa, likewise Jay dake jingine jikin mota tun da suka iso unguwan dama shi bai ce komai ba, Ajay ya daga kai after some seconds ya kalli Aunty Farida a hankali yace "Amma yana da number ki ne Aunty?" Aunty Farida tace "Ba shi da wannan number tawa gaskiya sai tsohon layi na, kwanaki Maman Khaleesat tayi rashin lafiya sai na tafi kano dubata to a hanya na yar da wayata, da na zo kano sai na siya sabon layi kafin inyi welcome back din tsohon layin, to har yanxu ban yi welcome back din ba" Ajay yayi shiru yana nazari, Aunty Farida na hawaye tace "Tsautsayi yasa ta fita deban ruwan yau, amma tunda ta xo wallahi ni ke diban ruwana bana barin ta dibar min tunda har yanxu gata nan ne dai bata dawo dai dai ba, wani lkcn ma da daddare idan na dawo kasuwa nake yi tunda ana wahalar ruwa a season din nan don yawanci rijiyoyi kafewa suke yi sai ana bari ruwan na taruwa sannan a diba, gashi ba a samun wuta balle a samu ruwan pampo, a jiyan nayi girki me yawa ne na wani biki duk sai na gaji ban deba ruwan da daddare ba, da na tashi kuma sai nake jin zazzabi, kun ji dalilin fitarta ta debo mana ruwa kenan" Ajay ya jingina da motarsa ya lumshe ido ya bude, gaba daya Ζ™ansa ya gama kullewa, bai yi zaton Abdul ya wuce yanda yayi zatonsa ba, the guy is really something else ko wani salon tactics na mugunta ya san sa gashi har yau yaki kunna wayarsa balle a san inda yake, ko by mistake baya kunna layin, shi dai Jay dama bai taΙ“a underrating Abdul ba dai dai da rana daya duba da irin actions din da ya dinga portraying, kawai dai tracing din Halysaah har zuwa Lagos is the least thing da yayi zaton Abdul zai yi, tunda bashi da access da Aunt dinta, but like seriously how did he even find his way, bayan bashi da active line din Aunty Farida sannan bai san unguwan da take ba, ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yana tunanin ta inda za su fara billo ma wannan lamari, tunda dai babu ta yanda za su ce yayi kidnapping Halysaah da ke a matsayin matarsa ta sunna. Khaleesat na zaune at the far end of the large room ta hade kanta da gwiwa, zuwa sannan ta hakura da kukan da take don ba ma ta da strength din kukan amma tana jin zuciyarta na mata zafi ga wani azababben ciwon kan da take ji da kishin ruwa da ya dameta, tafi awa sha biyu zaune a dakin ba ci ba sha, don tunda aka shigo da ita har zuwa sannan babu wanda ya sake zuwa dakin, infact bata ji motsin kowa a gidan ba alamar ita kadai ce a ciki, bandakin dake cikin dakin take shiga tayi alwala ta fito tayi sallah duk da ba sanin lokaci tayi ba kawai tana amfani da instinct dinta ne, at this point in time tasan bata da wani sauran gata sai wajen Allah, domin kuwa tasan Abdallah ne kawai zai sa a zo ayi mata irin wannan daukan, wasu hawaye masu zafi suka zubo idonta tana tausayin rayuwarta, all she could remember vividly was that tana bakin rijiyan dake kusa da gidansu Aunty Farida tana diban ruwa wasu mutane biyu suka zo a mota, lokaci daya kuma suka yi leading dinta zuwa motar tasu, at first turje masu tayi ta fara kokarin raising alarm tana ihu, yaran dake bakin rijiyan duk suka gudu suka shige gidajensu, tana kururuwa daya mutumin ya rufe fuskarta da wani Handkerchief da sauri, taji ta shaΖ™i wani abu kamar dust, lkci daya kuma ya cire handkerchief din a fuskarta, daga nan kuma ko kokarin ihun bata sake yi ba cause she became weak, ita dai tasan all through the ride she was conscious but not fully, gashi ta kasa tabuka komai don duk jikinta ya mutu, kanta yayi mata nauyi idonta suka dinga juya mata.... Da sauri Khaleesat ta dago kanta ta mike tsaye jin ana Ζ™oΖ™arin bude kofar dakin ta waje da makulli, gabanta ya dinga bugawa da karfi idonta na kan kofar har ya bude ya shigo, she wasn't expecting anyone but him dama, ta sauke kanta bayan sun hada ido, wasu sabbin hawayen suka fara zuba idonta, muryarsa taji ya daki kunnenta cike da isa da gadara yace "Har yanxu Body guards din naki basu biyo bayanki bane? Ai yaci ace sun iso zuwa yanxu don naga It's almost 12 hours now, how comes basu zo cecen ki ba duk capacity din su" Sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kallesa cikin rawar murya tace "Ka ji tsoron Allah...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da matsanancin kukan takaici, shi dai yana tsaye yana kallonta da wani murmushin mugunta kwance fuskarsa, ta dago kai da sauri jin yana takowa har zuwa inda take tsaye, mannewa tayi da bango tana jin kamar bangon ya tsage kawai ta shige gabanta na bugawa da karfi, sai da ya zo dab da ita cikin kwantar da murya yace "Me kika ce?" Ta girgiza masa kai da kyar gabanta na ci gaba da faduwa muryarta na rawa tace "Kaji tsoron Allah Ya Abdul, kaji tsoron...." Bata rufe baki ba taji saukan lafiyayyen mari a fuskarta wanda sai da taga taurari, ta dafe kuncinta tana kallonsa babu ko kiftawa, cikin husky voice dinsa yace "You still have the guts to repeat what u just said saboda baki da kunya ko? Ni zaki gaya ma in ji tsoron Allah? To tsoronki zan ji ko tsoron uban ki dake Mariri idan ban ji tsoron Allah ba?" Da kyar Khaleesat ta dake tace "Ka zageni amma kar ka sake zagar min uba" Still bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani wawan marin a other side of her face, this time around sai da dakin ya juya mata don ba marin wasa yayi mata ba, ya fixgota yana mata wani irin kallon da ya gigitata don tuni idonsa yayi jajur yana huci yace "Ina magana kina mayar min how dare you poor wretched girl?" Ta fashe da matsanancin kuka tana jin dama Allah ya dau ranta kawai ta huta a wannan lokacin, zata durkusa kasa ya hadeta da bango yace "Yau ina body Guards din naki dake goya maki baya kina min iskanci? Tell me where they are today? Da aurena a kanki kike hulda da wasu banzayen gardawa saboda ke jahila ce warce bata san me take ba" Tana kuka sosai bata san sanda tace "To wai ana aure dole ne dama Abdul? Nace bana son auren, bana son ka, gwara kawai ka kasheni duk mu huta" Da karfi ya bugata da bango har sai da taji numfashinta ya dauke na few seconds, yana mata wani mugun kallo yana huci yace "Dama ke baki san aurena wajibi ne a gare ki ba ko kina so ko ba kya so? Dama shi ubanki bai gaya maki hakan ba ko mantawa kika yi saboda kin fara bin maza? Wallahil Azeem kin ji rantsuwar musulmi ko? Duk ranan da kika sake yunkurin guduwa ko kuma yin wani silly act to rayukan twin siblings din ki za su zama fansar aurena idan kika kuskura kika min jakanci, ko kina so ko baki so lallai dole ki zauna da ni ko kuma in salwantar da ran kanninki i am promising you this Billahil Azeem, kuma babu abinda zai faru don tamkar na kashe banza ne daga ke har iyayenki babu abinda za ku yi, su kansu Body guards din naki ba kyalesu nayi ba don sai na dau revenge din intruding da suka yi a sabgata, i will teach them a lesson kina ji kuma kina gani" Khaleesat ta kasa cewa komai don sama sama kawai take jin numfashinta kalmansa na cewa zai salwantar mata da siblings dinta ya sa jikinta ya fara rawa, ya juya cike da isa ya tafi ya bude closet din dakin wanda duk kananun shegun kaya ne yace "All this are your wears, in kin yi sallah kin shirya ki zo ki sameni a dakina which is 3 rooms away from this, ina jiranki at exactly 7pm and this is just 6:30pm" Yana kai wa nan ya fice daga dakin yana rike da key din dakin, a hankali Khaleesat ta sulale kasa tana sauke numfashi tana jin wani abu ya tsaya mata cak a zuciya, gashi ba ta ma da strength din da zata yi kuka sosai ko zata ji relieve don tun jiya rabonta da abinci, she was just weak and helpless, ga idonta da taji ya fara ciwo saboda marin da yayi mata don dama ba warkewa idon yayi gaba daya ba lkci lkci tana jin yana damunta, tsoro da fargaban kada ya sake dawowa dakin yayi mata fiye da abinda yayi mata yasa Khaleesat tayi karfin halin mikewa da Ι—an sauran strength din ta da ya rage tana tafiya da kyar ta shiga bandakin dake cikin dakin ta tara ruwan pampo tana sha ko zata ji saukin abinda take ji a zuciyarta, bayan ta sha ruwan ta dinga kallon fuskarta da yayi ja ta madubi, a hankali ta zame kasan bandakin ta jingina da tile din bangon hawaye masu zafi na zarya a fuskarta, tafi minti goma a haka lokaci daya ta yunkura ta mike bayan ta tuna time din da ya bata kar ya sake dawowa, she wish akwai makulli a jikin kofar bandakin don da kulle bathroom din kawai zata yi in ma mutuwa ne tayi a haka don yafi mata kasancewa da Abdul, cikin rashin kuzari ta cire hijab dinta da kayan baccin dake jikinta ta fara wanka da shower gel din dake bandakin, komai na bukatar mace akwai a banΙ—akin everything is just set, after a while ta gama wankan ta wanke bakinta ta fito sanye da dogon hijab dinta with different thoughts running her mind, tunda ya bar kofar dakin a bude ko dai ta samu ta lallaba ta fita and find a way for her self, duk da tasan Abdul will never be that stupid da zai bar kofa a bude har ta samu ta fita, infact in ma ta fita daga building din gidan tasan definitely akwai mai gadi a bakin gate kuma babu ta yanda zai bar ta ta fita, kilan ma Abdul din ya sanar masa in zata fita kar ya bude mata gate, but still ita dai burinta ta samu ko daki me makulli ne ta shige ciki ta kulle kofar sannan ta bar key din a jiki yanda ko spare key idan aka saka za a bude kofar bazai budu ba sbda key din da ta bari a jiki, da wannan tunanin ta nufi kofa gabanta na faduwa ta bude kofar dakin a hankali zata fita suka kusa cin karo da shi, rikicewa tayi ta juya da sauri zata bar bakin kofar ya fixgota, bakinta na rawa tace "I am very thirsty" fuskarsa babu wani rahama yace "Follow me" Bata iya ta masa musu ba tunda taga kiris yake jira ya mareta a ko da yaushe, at every slight opportunity marin ta kawai yake, tana biye da shi zuciyarta na bugawa suka shigo Main parlor din gidan, karshen haduwa gidan ya hadu amma ita ko lura da hakan bata yi ba don ta kanta kawai take, tana biye da shi ya kai ta har kitchen din gidan, ya juya ya kalleta a takaice yace "Gashi nan ki dafa abinda zaki ci don bani da time din fita in siya maki komai tunda kina da hannun girki, after that ki dafa min lipton ki kai min dakin da nace" Ita dai Khaleesat na rakube jikin kofar kitchen din gaba daya hankalinta baya jikinta, taga yayi ficewarsa ya bar mata kitchen din, ta bi sa da kallo har ta dena ganinsa, ta zame kasa ta hade kanta da gwiwa cikin rawan murya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" ta kusa minti biyar a haka kafin ta yunkura ta mike tana goge hawayen da yaki tsaya mata, tana tafiya a hankali ta nufi kofar parlon ta murda taji a kulle kuma babu makullin a jiki she wasn't surprise don tasan dole zai kulle gidan, haka duk sai da ta bi dakunan dake gidan ta murda su taji a kulle kuma babu makullansu a jiki, a sanyaye hawaye na bin fuskarta ta koma kitchen din, duk da rabonta da abinci tun jiya amma ko yunwan bata ji tsabar tashin hankali, kawai jikinta ne yayi weak taji strength dinta duk ya kare, wnn yasa ta Ι—an hada shayi kadan a cup zata sha, shi ma dai ta kasa sha don bata da appetite, haka nan ta zubar ta dau black tea din da yace ta dafa masa ta fito daga kitchen din, dai dai san da ya shigo parlon, sunkuyar da kai tayi rate din heartbeat dinta na karuwa cause he is just wearing short and singlet, cike da karfin hali tace "Ga tea din" Babu yabo babu fallasa taji yace "A nan nace ki bani tea?" Ita dai bata ce komai ba amma kana ganinta kasan a mugun tsorace take, tana hade hanya ta nufi inda yace ta kai masa shayin yana biye da ita a baya, da ace tashin hankali da fargaba na kashe mutum ya ci ace ya kashe Khaleesat a wnn moment din, a bakin kofar dakin ta tsaya cikin rawan murya tace "Ga tea din" Wani tsawan da ya kidimata yayi mata don bata ma san sanda ta shige dakin ba ta je ta ajiye masa Mug din tea din a kasa tana waige waige, ya shigo dakin ya tura kofar fuska a daure yace "Cire Hijab din nan, kuma yau ya zama first and the very last day da zaki min yawo da Hijab a gida" Ta durkusa kasa ta fashe masa da kukan tashin hankali tana kallonsa, ya mata tsawa yace "Are you daft?" Cikin kuka tace "Wallahi sallah nake son inyi ne kayi hakuri" Darduma ya nuna mata a takaice yace "Je kiyi" Jiki na rawa ta mike ta tafi kan darduman ta fara sallah jikinta na rawa, tayi raka'a ya fi sha biyar ita kanta bata sani ba, kawai daga bayanta taji ya fixge hijab din, tun bai karasa cirewa ba ta fara kokuwa da shi ta rike hijab din gam tana kiran Ummanta cikin rikicewa, amma da yayi mata wani riko da hannu daya sai da ta gane Allah daya ne, don ko kwakkwaran motsi kasawa tayi, tana ji tana gani ya fixge hijab din ya jefar da ita kan gado rokonsa ta dinga yi da duk kalman da ya fito bakinta tana cewa "Ina rokon ka da girman Allah kayi hakuri Yaya Abdul, don Allah ka min rai kayi hakuri, in kana yi ma darajan iyayenka kayi hakuri, wallahi ban gama sallan da nake ba...." Ya gama kare mata kallo at the same time yana surveying every bit of her beautiful and breathe taking body, komai yayi masa yanda ya kamata, ashe asalin kyanta na boye all this while bai sani ba, yayi tarayya da mata iri iri amma bai taΙ“a ganin mace that is so beautiful while naked kamar ta ba, iya haskenta kadai ya isa ya rikita mutum, tuni idanuwansa suka sauya launi ya cire singlet dinsa yana kallonta kasa kasa yace "In ma kika yi taurin kai kece a wahale don that isn't stopping me in anyway Baby gal, just relax and i won't be rough" Kara gigicewa Khaleesat tayi tana rokonsa at the same time tana kokarin sauka daga kan gadon ya fixgota ya mayar da ita saman gadon yana kallonta cikin husky voice dinsa yace "Do not allow me give you a dirty slap...." Bata ma san me yake cewa ba still zata sake sauka taji ya danneta kan gadon, roughly ya fara exploring dinta kamar ya samu er hannu....

[6/13, 9:19 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Ko minti uku Abdul bai yi da fara taΙ“a ta ba Khaleesat taga ya koma gefe lkci daya, da sauri ta mike tana komawa baya har sannan bata dena kukan da take tana basa hakuri ba cikin rikicewa, after some seconds ya juya ya kalleta da rinannun idonsa, suna hada ido ta kara rikicewa muryarta na rawa cikin kuka take cewa "Don girman Allah kayi hakuri, i am begging you please kayi hakuri" Ya jefa mata wani kallo ya mike kamar zai tashi sama ya nufi kofa ya fice daga dakin, ganin hakan tayi kamar a mafarki ta kasa ko kwakkwaran motsi, kamar ance ta sauke kanta taga jinin da ya Ι“ata farin zanin gadon da take kai, ta dinga komawa baya a hankali tana kallon jinin babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa at the same time, and she realize daga jikinta yake fita, lokaci daya ta tuna rabonta da period tun a Maryland almost a month and some days, from nowhere taji relieve ya zo mata, ta jingina da jikin gadon hawaye masu zafi na sauka idonta, tafi minti biyar a hakan ganin zata ci gaba da soiling zanin gadon ta sauka ta dau hijab dinta ta rungume, har sannan jikinta bai daina rawa ba, tana ta tsaye a dakin tana tunanin yanda zata yi, ta kalli kafarta jin period din yana gangaro mata, ajiye hijab dinta tayi ta shiga bandakin da ke cikin dakin, after few minutes ta fito ta dau hijab dinta ta saka, tana kallon zanin gadon da ya baci ta fara Ζ™oΖ™arin cirewa a hankali har ta cire gaba daya, bude kofar dakin taji anyi ta mike tsaye da sauri zuciyarta na bugawa tana kallonsa, ya wani harareta yace "What are you using that for?" Bakinta na rawa tace "A'a wankesa zan yi ne" Yace "Ajiye bana so, zo ki fitar min a daki" Ta sunkuyar da kanta babu musu ta ajiye zanin gadon a gefen gado ta nufi kofa a tsorace kamar munafuka, amma ta kasa bin gefensa ta fita daga dakin saboda fargaba, gashi he is blocking the way, ta fi 30 seconds tsaye zuciyarta na bugawa ta kasa fita, shi dai kallonta kawai yake babu yabo babu fallasa, da kyar tace "Zan wuce" Ganin kallon da yake mata bata sake cewa komai ba haka nan ta raΙ“a ta gefensa ta fita daga dakin, kallon inda ta tsaya yake don nan din ma dai sai da tayi staining dinsa da jini, ita dai tuni har ta shige dakin da aka fara ajiyeta ta tafi bandaki da sauri tana jin maranta na kullewa, ita da ko ciwon mara bata yi sai dai wani lkcn tayi ciwon baya ko kafafuwanta su rike shi ma kawai na 'yan awanni ne, ta samu dai ta wanke jikinta ta fito tana dukawa sbda ciwon da take ji a mara, a haka ta bude closet din da ya nuna mata tana duba ko zata ga pad, amma taga babu alamarsa, ta fara tunanin yanda zata yi gashi tana jin alamar saukan period din nata a jikinta, ita ko da kyalle ne idan ta samu zata iya manage da shi, amma duk dube dubenta bata ga alamar akwai kyalle ko dankwali a closet din ba, duk kananun kaya ne, she was so confuse and in pain at the same time, ta rasa yanda zata yi, sai da tayi sahu ya fi a kirga zuwa bandaki ta wanke jikinta ta sake fitowa, kuma a haka ba heavy flow take ba a ranan farko, ko zama ta kasa yi ciwon mara ya addabeta, hawaye ya fara sauka idonta ta karasa kusa da gadon dakin ta durkusa ta daura kanta saman gadon ta lumshe ido trying to endure the pain she is feeling, tafi 20 mins a haka taji budewar kofar dakin, da sauri ta dago kanta daga gefen gadon har sannan tana duke, ta kallesa gabanta na faduwa, ya shigo dakin ya ajiye ledan hannunsa yana mata kallon sama har kasa a takaice yace "Me ye ma'anar hakan?" Muryarta na rawa tace "I am having cramps" Yace "Yaushe kika fara cramps? Is this also among ur lies?" Ta sunkuyar da kanta wasu sabbin hawayen na sauka idonta, yace "Bazan sake fita gidan nan da daddaren nan ba saboda ke, after all mate din ki ne ke enduring labor pain" Ita dai bata ce masa komai ba har ya fita daga dakin, sai a sannan ta dago kanta with tears rolling down her face, ta kalli ledan da ya ajiye, rarrafawa tayi zuwa gun ledan ta bude taga Sanitary pad ne, daya ledan kuma abinci ne da ya siyo mata a eatry da bottle water, ta daure ta mike tsaye da kyar bayan ta cire pad daya ta bude closet ta dau sabon underwear dake ciki ta tafi bandaki, bayan ta gyara jikinta ta wanke hijab dinta da yayi staining a bandakin sannan ta fito, rigan bacci wanda ya Ι—an fi sauran mutunci ta dauka ta saka, ya saukar mata har kusa da gwiwa, kasa cin abincin da ya siyo mata tayi, haka nan ta bude ruwan goran ta sha sannan ta dau pillow ta ajiye a kasan dakin ta dau duvet din saman gado ta kwanta tana jin ciwon cikinta na tsananta, ita rabonta da ciwon mara tun ranan farko da ta fara period, haka nan hawaye yayi ta zuba idonta, har ta samu bacci ya dauketa taji budewar kofa, taki bude idonta tayi lamo a inda take bugun zuciyarta na tsananta, ya zagayo har inda take ya duka gabanta, hannu ya kai forehead dinta hakan yasa ta bude ido da sauri, magani ya mika mata da ruwa a hannunsa ta sauke idonta sannan ta daure ta mike zaune ta amshi maganin da ruwan hannunsa ta sha, ajiye sauran ruwan tayi a gefenta har sannan ta kasa kallon idonsa, taji yace "Meye da gadon da baki hau ba?" Kai kawai ta girgiza masa yace "Get on the bed now" Tashi tayi ta koma gefen gadon ta zauna, kana ganinta kasan a tsorace take, ya dau pillow da duvet din ya ajiye mata saman gadon, kwanciya tayi ta lulluba da duvet din ta kulle idonta, tana ji ya fita ya kullo mata dakin, ta bude idonta da sauri taga ya kashe mata wutan dakin, hawaye taji na gangarowa ta gefen idonta, gradually taji ciwon maran ya fara subsiding after almost an hour of taking the drug he gave her, daga nan kuma bata san sanda bacci me nauyi ya dauketa ba, wajen karfe ukun asuba yunwa ta farkar da ita, ta mike zaune tana bin dakin da kallo har wani rawa jikinta yake saboda yunwa don rabonta da abinci tun shekaranjiya ga kuma maganin da ta sha babu komai a cikinta, zamowa tayi daga kan gadon tana laluba ledan abincin da ya kawo mata taga ya dauke, rasa yanda zata yi tayi, tana ta zaune a haka kawai taji ya bude kofar dakin hannunsa rike da wayarsa da ya kunna fitila, shigowansa na uku kenan zuwa dakin amma duk bata sani ba tana bacci, haskata yayi da wayarsa ya karaso cikin dakin ya kunna switch din fitila, ita dai ta sunkuyar da kanta kamar munafuka tana jin zuciyarta na throbbing, yace "Me kike yi a nan?" Sai a sannan ta daga kai da kyar ta marairaice amma bata ce komai ba, ya daure fuska yace "Nace me kike yi a nan?" Da kyar tace "I am hungry" Yace "Me yasa baki ci abincin da na kawo maki jiya ba?" A hankali tace "Na kasa ci" Juyawa yayi ya fita daga dakin, ta lallaba ta koma saman gadon ta kwanta tayi lamo, after almost 10 mins sai gashi ya dawo dakin da abincin bayan yayi microwaving din mata, nan kan bedside drawer ya ajiye mata abincin da ruwan gora, bata jira yace mata komai ba ta mike zaune tana sunkuyar da kai kamar mara gaskiya ta kai hannu ta dau abincin, shi dai yana tsaye yana kallonta, a hankali ta fara cin abincin har sai da ta ci rabi sannan ta kallesa cike da karfin hali tace "Na koshi" Yace "Cinye sa" Bata masa musu ba ta ci gaba da cin abinci har sai da ta cinye, amma fa da kyar ta dinga turawa, ta ajiye plate din a saman beside drawer, juyawa yayi ya fice bayan ya kashe wutan dakin, Khaleesat ta koma ta kwanta tayi lamo kan pillow, ta ma rasa wani tunani zata yi at this point, ta goge hawayen da taji yana gangaro mata, ba ita ta koma bacci ba sai da aka yi sallan asuba. Wajen karfe bakwai na safe ta fito daga wanka daure da towel tana tafiya a hankali ta bude closet din dakin tana tunanin abinda zata saka, kana kallon fuskarta kasan tana cikin damuwa me tsanani, fargabanta yanxu idan ta gama period ya kenan? Ta ina zata fara nema ma kanta solution yanxu, what next? ta fashe da kuka a hankali tana jin kirjinta na mata zafi, ta jingina da closet din tayi kukanta me isanta tana tausayin rayuwarta, daga karshe ta goge hawayenta a sanyaye ta dau wata riga wanda har kasa ne amma it's transparent, ajiyewa tayi gefen gado ta cire hair net din dake kanta tun shekaranjiya, tana tafiya a hankali ta karasa gaban madubin dakin, turarurruka iri iri ne da mayuka, da man kai, ta dau turaren jiki kadan ta shafa sannan ta shafa ma kanta man gashi don tana barin sa ya kara kwana daya a haka bata shafa mai ba duk tangling zai yi barin dama cukuikuyesa kawai tayi cikin Hair net din Aunty Farida, ita ma Aunty Farida haka gashinta yake, infact dukkansu har Umma da su Islam duk texture din gashinsu daya, tana cikin shafa ma gashinta oil aka bude kofar dakin, still tayi a inda take gabanta ya fara faduwa, taki yarda ta kalli direction dinsa, da kyar ta ajiye oil din hannunta ta dau Hair net zata mayar da gashinta ciki, taga ya amshe net din a hannunta ya juyo da ita yana kallonta, ta sunkuyar da kanta kirjinta na heaving shi dai kallonta kawai yake, short ne kadai jikinsa shi ma da alamar he just took his bath, ya jawota jikinsa ya daura goshinsa saman gashinta at the same time yana shafa dogon baΖ™in gashinta a hankalin, Khaleesat ta runtse ido zuciyarta na bugawa, murya can kasa taji yace "Why did u change ur mind abou me? It's all my fault right?" Jin bata ce komai ba ya dago kanta yana kallonta, kawai jin bakinsa tayi a nata bayan ya lumshe idanuwansa, tsoron turje masa take yi don bata san me zai biyo baya ba idan tayi hakan, jikinta ya dinga rawa kamar me zazzabi hawaye na sauka idonta tana girgiza masa kai amma ta kasa cewa komai kar ya mareta kamar yanda ya saba, a haka ya ja ta zuwa saman gadon dakin yana sarrafata, he made sure he romanced her deeply to the extent that sai da ya birkice mata kamar ba shi ba, daga karshe kuma ya kyaleta kar ya kasa controlling kansa gashi tana period, amma fa sosai ya iya kai zuciyarsa nesa kafin ya kyaleta ya koma can edge din gadon yayi rub da ciki tare da lumshe idonsa, everything about Khaleesat is just perfect for a Man, laushin jikinta kadai ya isa ya kara gigita mutum, Khaleesat ta koma daya side din gadon a hankali take kukan takaici faduwar gabanta ya tsananta, juyawa yayi ya kalleta after some minutes yaga yanda dogon gashinta ya rufe duk fuskarta tana kuka, sai kuma ta zamo a hankali daga saman gadon ta kife kanta da jikin gadon tana shessheka, ji tayi ya dafata ta juyo a firgice tana komawa baya don bata san sanda ya zagayo ba, ya sa hannu biyu ya maida duk gashinta zuwa gefen fuskarta yana kallonta, tuni ta daina kukan da take saboda tsoro, ta sunkuyar da kanta kirjinta na heaving, jawota yayi jikinsa ya rungumeta ya lumshe ido, ita dai tayi tsit tsabar firgici, a haka ta dinga jin bugun zuciyarsa tana jikinsa, they were like that for 3 mins daga karshe taga ya mike a hankali ya fita daga dakin ta bi sa da kallo tana share sabbin hawayen dake sauko mata a fuska, throughout ranan haka Khaleesat tayi ta zama a daki sai dai ya kawo mata abinci, da ta tuno abubuwan da Abdul yayi mata daxu sai ta firgita, sai ya zama kamar tana hallucinating ne, hakan ya dinga sa mata ciwon kai taji kamar zazzabi zai rufeta, saura kadan panic attack ya kamata a dakin banda Allah ya takaita mata, gaba daya yanxu tunanin menene makomar rayuwarta take, shikenan haka zata hakura tayi zaman aure da Abdul ta ci gaba da shanye duk bakin cikin da zai kunsa mata a zaman aurensu bata da me tsaya mata tunda shi din mijinta ne? Did she even have a way out with the way things turn out to be all of a sudden? Is this going to be the beginning of a new era a rayuwarta? Shikenan irin rabuwar da zata yi da su Housemate dinta kenan? Kilan ma ba lallai ta sake ganinsu ba a rayuwarta? Shikenan haka Abdul zai ci gaba da caging dinta a gidansa ga threatening din kashe mata siblings da yayi idan taki zama da shi? Duk wa ennan tunanin suka sa ta dinga kuka tana tausayin sabuwar rayuwar da take kokarin fadawa, don tasan Abdul na gane ta gama period bazai daga mata kafa ba and that is the end of her, kuma shikenan dole ta zauna tayi zaman aure da shi ko da yankan naman jikinta zai dinga yi kuwa don azabtarwa, tunda Ummanta ta haifeta tana jin bata taΙ“a shiga irin wannan tashin hankalin da take ciki ba a wannan lokacin, tana jin alamar zai shigo dakin take goge fuskarta ta langwabe a zuwan ciwon ciki take.... Cikin wannan yanayin Khaleesat tayi kwana uku a gidan tare da Abdul, a wannan kwanaki ukun kuwa duk da halin da take ciki a haka yake sakawa taje tayi masu girki a kitchen wai shi baya son abincin restaurant, Khaleesat bata taΙ“a fatan kar period dinta ya dauke ba kamar irin wannan lokacin, she wish she will keep on flowing continuously like the woman with the issue of blood amma tasan dole ya dauke nan da kwana biyu don bata wuce 5 days in tana period, sosai hankalinta ke kara tashi idan ta tuna hakan, yau tunda gari ya waye tayi wanka ta saka pad take kwance kan gado saboda azababben ciwon kan da take, all these pass days bata wani samun baccin kirki da daddare tsabar damuwar da ta saka ma kanta da tunane tunane, daga karshe dai haka ta daure ta fita zuwa kitchen da kyar don dora breakfast kafin ya fito daga dakinsa kamar yanda yayi mata umarni 2 days back, tana fita parlor ta leka compound din gidan taga babu motarsa alamar ya fita, ta murda kofar parlon taji a kulle kamar yanda tayi tunani, Zaunawa tayi kan kujera ta dafe kanta hawaye masu zafi na zuba idonta, after a while ta mike tana shesshekan kuka ta wuce kitchen din, tana cikin hada breakfast taji alamar shigowar motarsa gidan, after a while aka bude kofar parlon, Ζ™asa kunne tayi jin kamar muryar mace take ji a parlor, can kuma taji tsit, ita dai ta ci gaba da abinda take yi jiki babu kuzari har ta gama ta tsaftace kitchen din sannan ta juya zata fito ta kusa cin karo da wata mace in her late 30's zata shigo kitchen din, daga sama har kasa matar dake tsaye kofar kitchen din take mata wani irin kallo da za a iya kira da kallon kaskanci, ita dai Khaleesat tunda ta kalleta sau daya ta sunkuyar da kanta ita kanta bata san sanda ta gaisheta ba don duk ta rude gashi kuma taga suna kama da Abdul duk da bai taΙ“a nuna mata wani nasa ko da a hoto ba, a walakance matar tace "Da ban kwana ba zaki gan ni munafukar Allah, Er gidan matsiyata ma ci amana.... A gidan ubanki kika san ni da zaki gaisheni?" Sai a sannan Khaleesat ta sake daga kai tana kallonta da mamaki cause kalmomin matar kawai a bazata suka zo mata, bata san sanda tace "Ki zageni amma banda iyayena...." Bude baki Meema tayi da mamaki tana kallonta ganin guts dinta, kafin tace komai Khaleesat ta bi gefenta zata fice daga kitchen din wanda saura kiris ta bangajeta wajen fitan, cikin zafin nama da bacin rai Meema ta fincikota ta dawo da ita gabanta sannan ta sauke mata wani wawan mari ta shakota tana kokarin kai ta kasa ta nakadi banza, Khaleesat ta kwala wani kara, dai dai isowan Abdul wajen, lkci daya yanayinsa ya canza don a kan idonsa yayar tasa ta sauke ma Khaleesat mari sannan ta shakota tana kokarin dukanta, cikin daga murya yace "Zo ki fita ki bar min gidana Amina, how dare you? Me tayi maki zaki mareta haka? Baki da hankali ne? Get out of my house pls, fita ki bani waje" Sake baki Meema tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, cikin zafin nama ya tafi ya bude kofar parlon kirjinsa na sama da kasa yace "Ki fita nace Amina kar in rama mata" Cikin karfin hali Meema ta dafe kirjinta da hannu daya tace "Abdallah ni kake cewa in fita a gidanka?" Ya jefar da wayar hannunsa yana huci ya nufeta kamar zai kai mata duka cikin daga murya yace "Na ce ki fita din ko gidanki ne? Get out of this house before i loose my control Amina, gerrout" Ita dai Khaleesat makalewa tayi jikin kofa jikinta na rawa, sum sum sum Meemah ta karasa ta dau handbag da karamin travelling bag dinta don dama daga airport yaje ya daukota saukanta garin kenan, ta nufi kofar fita parlon sannan ta juya tana kallonsa da mamaki tace "Abdallah ni kake daga ma murya kake cewa in fita in bar gidanka akan wancan matsiyaciyar? Har kake ikirarin zaka kai min hannu? Ni din Abdallah?" Da karfi yace "Duk nayi, fitaa ki bar min gidana malama" Fita tayi daga parlon ya bi bayanta kamar zai tashi sama ya tafi ya bude mata gate din gidan, ta fita yayi banging gate dinsa ya kulle, har ya dawo parlon Khaleesat na makale jikin kofa ita tsabar yanda ta tsorata ma ko digon hawayen marin da Meemah tayi mata babu a idonta, ya karasa kitchen din yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, sai a sannan taji hawaye ya fara zuba idonta.

[6/14, 9:16 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Juyawa Abdul yayi ya fice daga kitchen din ba tare da yace mata komai ba ya dau wayarsa ya nufi dakinsa, Khaleesat ta bi sa da kallo tana goge hawayen dake zuba idonta har ta dena hango sa, jingina tayi da kofar kitchen din ta kai hannunta fuskarta dai dai inda Meemah ta mareta don sai a sannan ta fara jin zafin marin, fashewa tayi da kuka tayi me isarta kafin ta fito daga kitchen din tana tafiya a hankali ta tafi ta zauna kan 1 seater dake parlorn tana share hawayen da yaki tsaya mata, abubuwan da Abdul yayi ma Meemah ne suka dinga dawo mata a kai don hakan yayi mugun shock dinta, but she just don't want to believe senior sister dinsa yayi harrassing haka har da koranta, to ko dai ita ce Aunty Aminan da suke ce ma Meemah don taga sosai suke kama da ita, tana ta zaune parlon bayan wani lokaci sai gashi ya fito daga dakinsa, sunkuyar da kanta tayi tana wasa da fingers dinta, ya karaso cikin parlon yace "Kin yi breakfast din ne?" Da Authoritative voice yayi tambayar yana kallonta, hakan yasa ta Ι—an rikice kamar mara gaskiya ta girgiza masa kai with fear all over her face, sai kuma ta mike da sauri ta nufi kitchen ya bi ta da kallo har ta shiga ciki, shayi rabin cup ta hada sannan debi Irish kadan a plate don tension yasa ta rasa appetite dinta gaba daya , sai kuma ta tuna shi ma bata basa breakfast din ba, tunanin ko ta kai masa parlor ta fara yi don a kwanaki ukun nan Bedroom dinsa take kai masa breakfast din kamar yanda ya umarce ta, kamar munafuka ta makale jikin kofar kitchen din tana kallonsa tana son tambayarsa ko ta kawo masa breakfast din nasa parlorn amma ta kasa don bata san me zai ce ba kar yayi mata masifa, wayarsa kawai yake dannawa bai ma san tana wajen ba, juyawa tayi a hankali ta koma kitchen din a sanyaye ta hada masa breakfast din ta fito da shi parlor,  jikin kujera ta tsaya a hankali tace "Ga breakfast din nan" Daga kai yayi ya kalleta, gabanta ya dinga faduwa ta sauke idonta daga kallonsa, jin bai ce komai ba yasa ta karasa har gabansa ta duka ta ajiye masa breakfast din, yace "Ke ina naki?" Taki barin su hada ido tace "Yana kitchen" Yace "Dauko" Mikewa tayi ta tafi ta dauko nata ta dawo tana kallonsa, yace "Ajiye ki ci a nan" Bata masa musu ba kanta a kasa ta zauna gefensa da ya nuna mata ta fara tuttura irish din kamar dole tana satan kallonsa ta gefen idonta, a hankali taga ya jawota jikinsa taji gabanta yayi mugun faduwa, calmly yace "I am a monster to you right?" Da sauri ta girgiza masa kai zuciyarta na bugawa, yace "Gashi nan, kin maida ni dodonki" Ita kanta bata san sanda hawaye ya cika idonta ba, yayi kasa da murya yana zame hulan kanta yace "Now tell me what u want from me, tell me what's on ur mind.... amma before then ki sani bazan taΙ“a rabuwa da ke ba saboda ina son ki Khaleesat, rabuwa dake will be the last thing i will do on earth no matter what, You know i love you genuinely from onset, i loved you wholeheartedly and i gave u the best of everything I could, i loved you even before you become the woman you are today, i love you since when u were just a 15 year old teenager tun baki girma ba, yea i know about my flaws but loving you is all that matters, not in the sense that abubuwan da nake yi are right, i am obsessed with you Baby, may be you can change me in ur own way...." Khaleesat ta rufe idonta tana jin kamar ta fashe da kuka, jin kalamansa take kamar ana soka mata mashi a kirji, Ya dora forehead dinsa a nata murya can kasa yace "Why not give me a chance and forgive my flaws Khaleesat?" Bude idonta tayi hawaye suka hau zarya a idonta, har cikin ranta taji bata son jin maganganun da yake mata, a hankali yace "Forgive me, i know i wronged you in all ways, but don't forget ina sonki, ina kuma sonki ne saboda Allah, they are many beautiful ladies out der buh i chose you Khaleesat" Lokaci daya gaba daya tunaninta ya tafi kan Housemate dinta, kasa daurewa tayi ta fashe da matsanancin kuka, ya daura kanta a saman shoulder dinsa patting her softly, ta dinga kuka kamar an aikota, shi dai bai ce mata komai ba, sai da tayi kukan me isarta sannan ta hakura don kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, ya daga kanta yana kallonta taki yarda su hada ido, breakfast dinta ya ajiye mata a kusa da ita, ba musu ta fara ci a hankali da tunani iri iri a ranta, muryarsa taji ya daki dodon kunnenta "Yaushe zaki gama period?" Gabanta yayi mugun faduwa, ta ajiye cup din shayin dake hannunta ba tare da ta kallesa ba, a hankali tace "Ai ban dade da farawa ba" Yace "Yau kwana hudu da farawan ki" Da kyar ta dake tace "A'a, uku ne.... first day din ai bana yi sosai..." Yace "Saura kwana nawa ki gama kenan?" Sosai gabanta ke bugawa, ta sunkuyar da kanta cike da karfin hali tace "Kilan nan da kwana uku ko hudu" Jin bai ce komai ba ta daga kai a Ι—an tsorace ta kallesa, taga kallonta yake without blinking, sauke idonta tayi tana wasa da karamin cokalin dake cikin mug din shayinta, ya dauke shayin ya mayar gefe, taga ya kai hannu shoulder dinta zai sauke siririn hannun rigar dake jikinta, sosai hankalinta ya tashi amma bata ce masa komai ba gabanta na ci gaba da faduwa, ya sauke rigan gaba daya yana kallon bare chest dinta, hawaye ne ya cika idonta taki yarda su hada ido, can dai tayi karfin hali muryarta na rawa tace "Toh baka sha shayin ka ba zai huce" Yayi kasa da murya yace "Wa ennan zan sha... "  Momy ce tsaye parlor tana kallon Meemah dake rusa kukan bakin ciki uwa er yarinya, ga trolley dinta a gefenta, bacin rai ne karara kwance fuskar Momy da idanuwanta suka Ζ™ankance tana huci, mai aikin gidan ce ta shigo parlon rike da bowl din pepper soup din da tayi ma Momy, cikin ladabi ta risina tace "Hajiya ga farfesun nan ya kammala" a fusace Momy ta figi throw pillow ta jefa mata tace "Don ubanki wuce ki ban waje ke da farfesun, baki ga magana nake bane zaki shigo min parlor kai tsaye, yau ga jahilar mata kai" a tsorace mai aikin ta juya da sauri ta bar parlon ta koma kitchen ta kullo kofar, Momy tace "Na kusa daina daukan tsinannun masu aikin nan don sun isheni haka kuma, na kori wancan shegiyar da ta shigo min parlor da yan uwan Alhaji da suka zo daga kauye babu izinina yanxu kuma an kawo min wannan jakar da ko kwana biyu bata yi ba ta fara nuna halayyan dabbobi" Ita dai Meemah kuka kawai take tana fyace hancinta da handkerchief, tsabar kuka idonta har sun suntume, Momy ta kara kankance idanuwanta tana kallon Meemah tace "Shi Abdallahn ne yayi maki haka Meemah?" Meemah ta hadiye wani abu da ya tokare mata wuya don bakin ciki tace "Momy da kin ga tijaran da Abdallah yayi min akan yarinyar nan ko, hmmm, ki bari kawai Momy, Momy kare bazai ci abinda Abdul yayi min ba, bayan zagi da cin mutunci wai ni ya kora a gidansa, kora irin ta walakanci" Momy ta zauna kan kujera with disbelief, duk da AC dake aiki a parlorn sai zufa take yi dama ga ta narkekiya, tana gyara zama tace "Ko dai ya sha wani abu ne Meemah??" Cikin rawan murya Meemah tace "Babu abinda ya sha wallahi Momy don lafiyan Allah ya dauko ni a airport muna ta hira, tare fa da ni duk aka yi tracking yarinyar nan tunda akwai wani tsohon saurayina wanda aikinsa kenan, amma wai yau akanta Abdallah zai min irin wannan tijara haka tun ba aje ko ina ba, duka duka fa kwananta yau hudu da shiga hannunsa, amma ya rufe ido ya zazzageni ya ci min mutunci ya koreni" Momy tayi wani murmushin takaici tana girgiza kafa tace "Kin ga abinda nake ta gudu kika kasa ganewa kenan ai ko? Dama ance duk abinda babba ya hango yaro ko uban me zai hau bazai taΙ“a hangowa ba wallahi, ba ya kwana da ita ba dole ki ga abinda yafi haka ai, babu yanda banyi in lalata batun auren nan ya hakura ba amma sam Meemah kika ki bani hadin kai ki ka koma bayan Abdallah, har da bin wasu malamanki da basu taka kara sun karya ba duk don yarinyar ta shigo hannunsa, to ai ta shigo kuma kin ga abinda ya biyo baya daga shigowarta, to wallahi zai kai ya kawo wataran Abdallah yace bai san mu ba akan yarinyar nan, ni na haifesa ba wani ya haifar min shi ba sarai nasan abinda zai iya aikatawa" Meemah ta dinga kallon Momy babu ko kiftawa don ita sai yanxu ta kara fahimtar dalilin Abdul nayi mata irin wannan mugun tijara kan yarinyar da yake ta ikirarin zai koya ma lesson idan ta shigo hannunsa, sarai kuwa ya kwana da ita dole ya birkice haka ya haukace kanta, dama buzaye da aka sani da mugayen asiri, Meemah tayi wani murmushin takaici tace "To kuwa yanda nayi ruwa nayi tsaki har sai da yarinyar nan ta shiga hannunsa to haka zan yi har sai ya rabu da ita a kwanan kuwa ba da jimawa ba" Momy ta kwado ma sabuwar me aikinta kira, matar ta taho a guje har sai da tsantsin tiles ya kwasheta sbda ruwan dake kafarta sai ga ta a kasa timmm, A fusace Momy tace "Wallahi tallahi kika kuskura kika illata min tiles sai na cire cikin kudin albashinki, yau naga er iskar mata kawai, kullum na kiraki sai kin azabtar min da tiles saboda kauyanci? Wannan wace irin mata Adama ta kawo min haka da sunan me aiki?" Har kasa mai aikin ta zube tana ba Momy hakuri, cikin tsawa Momy tace "Miko min wayata dallah ki fita ki bamu waje, er kauyen banza" Mai aikin ta kalli wayar dake kan center table dab da inda Momy ke zaune, ta karasa da sauri ta dau wayar ta mika ma Momy, Momy ta warce, mai aikin ta bar parlon, Momy ta mika ma Meemah wayar tace "Dubo min lambar Godiya, glasses dina yana daki" Meemah ta amshi wayar ta dubo number aminiyar Momy sannan tayi dialing ta mika mata, a kashe suka ji wayar, Momy tace "Tayi tafiya me muhimmanci kenan, bari zuwa anjima in sake kiranta" Meemah da kanta ya gama kullewa tace "Tabddi jam, lallai nayi babban kuskuren da ban taΙ“a yin irinsa ba Momy, sai ma fa kinga kayan dake jikinta da naje gidan, tana kitchen tana soye soye" Momy dai tayi shiru tana girgiza kafa don bakin ciki da takaici, can tace "Dauko min gyale da jaka a daki, ina zaman zamana kin janyo min kashe kudin da banyi budgeting ba Meemah, duk ke kika ja min wannan masifa da kika ki jin maganata wallahi, in hada iri da matsiyata akan wani dalili? A farko dai na hakura na zuba masa ido da yaki jin maganata, amma yanxu kuwa wallahi sae ya rabu da yarinyar nan, babu dalilin da zai sa in hada zuri'a da ita, ga kuma rashin adalcin da aka yi ma Alhaji ga asara ga biyan tara" Tashi Meemah tayi ta tafi dauko ma Momy gyalenta da handbag, all this while dama ita ke ta shiga malamai don Khaleesat ta shiga hannun Abdul Momy ko bin ta kanta bata yi tunda dama ba son auren take ba, Momy na ficewa daga gidan da driver dinta Meemah ta tafi dakinta da wayarta tayi dialing number Malamin da tasa yayi mata aiki. Runtse ido Khaleesat tayi bayan taji duk maganganun da Abdul yayi, yana rungume da ita saman gadonsa kamar zai maidata jikinsa, it's past 8pm na dare, jin taki cewa komai s hankali yace "Khaleesat" Bude idonta tayi wasu hawaye masu zafi suka silalo fuskarta tace "Um" Yace "Say something" Still tayi shiru hawaye na zuba idonta don bata ma san me zata ce masa ba at this point, ya dago kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace "Say something pls" Da kyar muryarta na rawa tace "Ban san me zan ce ba" Yace "Say anything" Shesshekan kuka ta fara yi masa tana jin zafi a zuciyarta, me kuma yake son ta ce masa, tunda yace bazai taΙ“a rabuwa da ita ba ko me zai faru, meaning dole ko tana so ko bata so haka zata ci gaba da rayuwa da shi a matsayin mijinta, so me yake son ta ce, ta dai dake da kyar har sannan muryarta na rawa tace "Kawai alfarma daya zan nema wajenka" Murya can kasa yace "Say it Khaleesat" Tayi karfin halin cewa "I don't want you to hurt anyone because of me...." Kasa ci gaba tayi tana kuka a hankali, ya dinga kallonta don sarai yasan su wa take nufi, Calmly yace "Ohk u mean ur Body Guards that sue me?" Ita dai kuka kawai take, Ya Ι—an yi wani murmushi yace "I don't think i will leave dem cause they started everything first, they intruded in what wasn't der business, basu baki labarin harbin da aka yi ma wani dake da alaka da su ba, I mean Salem..." Khaleesat ta daga kai da sauri ta kallesa hawaye na sauka idonta gabanta na faduwa, lkci daya ta tuna sanda Aunty Farida ke sanar mata Ajay yace mata an harbi wani abokinsu a kano, yana wani murmushi yace "To su ma ana nan ana targeting din su, amma in kince in kyalesu i will do that under 2 condition..." Khaleesat dai kallonsa kawai take ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi, yace "The first condition is that.... zaki yi magana ta waya da su ki gaya masu ke za ki zauna da mijin ki they should back off, sannan ki gaya masu su janye karan da suka kai kotu..." Bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba, ya dinga kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Baza ki yi ba kenan?" Muryarta na rawa tace "Ban ce bazan yi ba" Wayarsa ya dauko ya mika mata yana kallonta, da kyar tace "Bani da number ai" Yace "Amma aunt dinki na da shi ai... Call her and ask her to send you the number" Ta girgiza masa kai tana jin kamar numfashinta zai dauke sbda rikicewan da tayi bayan ya fadi conditions dinsa, cikin kuka tace "Bani da numberta offhand" Yace "Ni ina da shi, i will call her now sai ki gaya mata ta turo maki number daya daga cikinsu, and mind you kada ki kuskura ki ce mata komai, number kawai zaki yi requesting ta turo maki" Ta fashe masa da kuka sosai tace "Why are you doing this plss Ya Abdul" Yace "Ohk, i will revenge and nothing is gonna stop me, i promise you this, shi abokinsu da aka harba ai yayi surviving, i hope they survive too....." Tana kuka sosai tace "No plsss..." Wayar ya dauka yayi dialing number din Aunty Farida yana fara ringing ya mika mata yana kallonta.

[6/17, 7:43 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Har Aunty Farida ta Ι—aga kiran Khaleesat bata amshi wayar da Abdul ke mika mata ba hawaye na zuba idonta, lkci daya ya hade rai yana mata wani irin kallo, babu shiri ta amshi wayar hannunta na rawa, a sanyaye tace "Aunty" Cikin rikicewa Aunty Farida tace "Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, hankali tashe Aunty Farida tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Khaleesat kina ji na? Don Allah kiyi magana, Hello Khaleesat" Khaleesat ta kasa ce mata komai hawaye masu zafi na sauka idonta, kiris ya rage ta fashe mata da matsanancin kuka a wannan lokacin, Abdul ya fixge wayar yayi a hannunta ya katse yana mata wani mugun kallon da ya tsorata ta sosai yace "Are you daring me?" ta fashe masa da kukan da take dannewa tana girgiza masa kai, a fusace yace "Ohk then, since abinda kika zabar masu kenan to ina me tabbatar maki zan aikata hakan nan ba da jimawa ba kuwa, sannan bayan nayi zan sanar maki, don bani da imanin kyale duk wani mahalukin da yace zai shiga hurumina, i don't mind sending that person to his early grave, and mind you.... i will so deal with them yanda in their next life baza su kara shisshigi akan abinda bai shafesu ba, if you think i am bragging watch and see, bani da conscience...."  Khaleesat ta girgiza masa kai cikin karfin hali tace "Duk ba sai ka masu komai ba, zan yi abinda kace" Wayar ta amsa a hannunsa ta cire a Flight mode din da ya saka sannan ta sake dialing number Aunty Farida, yana fara ringing Aunty Farida ta daga da sauri tace "Khaleesat, kina ji na Khaleesat?? Hello" Khaleesat ta dake ta hadiye sauran kukanta cike da karfin hali tace "Na'am Aunty" Cikin tashin hankali Aunty Farida tace "Kina ina Khaleesat?" A hankali Khaleesat ta daga kai ta kalli Abdul taga ya wani murtuke fuska yana kallonta kamar bai taΙ“a fara'a ba a rayuwarsa, ta sunkuyar da kanta wasu sabbin hawayen na zubo mata cikin sanyin murya tace "Aunty Number Ahmad za ki turo min yanxu plss" Aunty Farida da duk ta rude tace "Ahmad kuma Khaleesat? Wanene Ahmad? Kina ina ne yanxu?" Shi dai Abdul wani devilish look kawai yake mata, tayi kasa da murya tace "Aunty Number Junaid zaki turo min" Da sauri Aunty Farida tace "To bari in turo maki yanxun nan" Katse kiran Aunty Farida tayi cikin rawan jiki ta tura ma Khaleesat number Ajay, number na shigowa Abdul ya amshe wayar a hannunta yana kallon number for almost 5 seconds, can yayi wani murmushi ya mayar mata da wayar, cike da isa yace "Kirasa ki gaya masa abinda nayi instructing din ki" It took Khaleesat almost 30 seconds kafin ta iya dialing number Ajay, shi ma saboda irin kallon da Abdul ke mata ne, exactly irin kallon da yake mata in zai gaura mata mari, cikin muryarsa dake tsoratata taji yace "Kika kuskura kika yi magana da wata muryar da ba normal voice dinki ba zaki sha mamaki wallahi, and immediately he picks just go straight to ur point, do not give him a breathing space to say anything to you, go straight and tell him kin hakura zaki zauna da mijinki, kin ji me nace maki?" Ita dai bata ce masa komai ba hawayen takaici na zuba idonta, sai da kiran ya kusa katsewa Ajay ya daga, ta Ι—an kalli Abdul da bai fasa mata wani irin kallo ba, da kyar ta daure tace "Hello, good evening....." Mikewa Ajay yayi jin muryarta, bata jira ya gama processing ba ta ci gaba a hankali tace "Dama ina son in ce maka ni na hakura zan zauna da mijina, and i appreciate all what you've done for me kai da Yaya Jawwad, thank you so much" Ajay ya juya ya kalli Jay da shigowar sa dakin kenan, as if counting his words yace "Come again!" Yana fadin haka ya saka wayar a handsfree sannan ya nufi Jawwad yana kallonsa, Khaleesat ta kalli Abdul, sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "Cewa nayi ni na hakura yanxu, zan zauna da mijina, and thank you for all what you've done for me...." Wasu sabbin hawaye suka hau zarya a fuskarta tana ji kamar ta fashe da kukan dake cin ta, Abdul ya fixge wayar a hannunta ya katse sannan ya kashe wayar gaba daya, Ajay ya kalli Jay that looks speechless and shock at the same time, lkci daya ya jefar da wayarsa saman gado, cikin nutsuwa yace "Nayi da na sanin bata lokacina akan yarinyar nan, i regret wasting my very precious time...." Jay ya ma rasa me zai ce, walking slowly ya karasa gaban window din dakin yana kallon Ajay that was boiling from inside, a hankali yace "Look Ajay, i think those words are not coming from her heart, sakata yayi ta fadi hakan pls mu yi mata uzuri, she is forced to say all what she said, ba mu san situation din da take ciki ba let consider that plss" Ajay ya masa wani kallo yace "Billah na cire hannuna a lamarinta kaji na rantse Jay, i have nothing to do with her case again, after all i was just doing it just for the sake of humanity not because of her, ko kasheta yake ya kamata ta gaya mana haka? Mu zata dauka for granted? Beside she spoke confidently meaning she is okay with what he asked her to say, i am leaving this state first thing tomorrow morning, so unfortunate i waste my time on the brat, don taga mun yi stooping kan mu so low shi yasa ta dauke mu for granted" Yana kai wa nan ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Jay ya lumshe ido ya bude don bai san me zai sake ce masa ba da zai sa ya sauraresa, kuma tunda har ya rantse magana ta kare, ya zare hannunsa kenan babu abinda zai sa ya sake involving kansa, zaunawa yayi gefen gado ya dafe kansa da yaji ya masa nauyi, at the same time letting out a sigh, kalmomin Khaleesat ne suka dinga dawo masa kai, he felt really disappointed in her too, but can kasan zuciyarsa tausayinta ne ya mamayesa ya kuma yi mata uxuri, ya rasa menene yasa shi shiga yanayin da ya shiga a wnn lkcin, da kyar dai daga karshe ya mike ya fita daga dakin yana tafiya a hankali. Daren ranan nan Khaleesat bata yi baccin awa biyu ba cikakke, da bacci barawo ya saceta zata farka a firgice, bata taΙ“a jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Abdul ya sa tayi ma su Housemate dinta ya tsaya mata ba, gashi ko digon hawaye yaki fita idonta, her heart is just heavy, but did she have a choice? In bata yi hakan ba yayi ma su Housemate dinta wani mugun abu ai bazata taΙ“a yafe ma kanta ba, tunda har yake ikirarin ba shi da imani babu abinda bazai iya aikatawa ba, tasan kuma sarai zai iya aikatawa din, tunanin sabuwar rayuwar da take kokarin fadawa take, is she going to survive this at all? Is this not going to be her end? A ranta taji kilan lokacin mutuwarta ne ke tinkarota, sai a sannan taji hawaye masu zafi for the first time a idonta, ta kai hannu a hankali tana sharewa ta juya tana kallon Abdul dake baccinsa hankali kwance, dai dai nan alarm din wayarsa ya kada, ta juya da sauri tayi backing dinsa tana goge hawayen da ya fara zubo mata sosai, after some seconds taji alamar ya tashi yana karanto addu'an tashi bacci, ita dai hawaye kawai take, sai da taji yayi sallah ya fita daga dakin sannan ta mike zaune tana kuka a hankali. Nenne ta bude hannu tana kallon su Aunty Farida cikin nutsuwa tace "To kun ga ai baza mu shiga hurumin Allah ba, ko akwai me tsaurin idon da zai shiga a cikin ku? Allah Ubangiji ne kadai yasan daliliin da ya maidata hannun mijinta cikin ruwan sanyi babu tashin hankali, to don me za mu shiga hurumin da ba namu ba? A'a gaskiya banda ni tunda ni dai nasan wanene Allah, kuma shi kadai yasan hikimarsa ta yin hakan, da yasan Khaleesah zata cutu hannun Awdul da bazai fara basa sa'ar sungumeta ba don bamu fi sa sani ba, ko ba komai Ι—a na zai samu kwanciyar hankali ya ci gaba da sabgogin rayuwarsa kamar ko wani Ι—an adam, mu mun yarda da kaddara mummuna ko kyakkyawa tunda mu musulmai ne, kuma duk abinda Allah yayi mu din banza za mu ce don me, domin haka nake cewa Allah ya bata zaman lafiya da mijinta, Ι—an halayyarsa da yake yi mara kyau Allah ya gyara sa ya dena, ai babu wanda bai da taΙ“on wani mugun abu a rayuwar nan, in sun dawo kano mu kuma sai mu je ganin daki mu sa albarka, duk sanda ya bar ta ta zo ta gaida mu a Mariri sai ta zo bakinta alekum, shi kuma Ali Allah ya sa karshen wahalarsa kenan a duniya" Wani irin kallo Aunty Farida ke ma Nenne zuciyarta na tafarfasa, Umma dai kanta na sunkuye bata ce komai ba amma ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta, Mama Zubaida tace "Amma dai Nenne ai ya kamata a bibiyi halin da take ciki, an taΙ“a tarewa haka kawai a zo a sungumi yarinya a mota da asuba ba a san ko shi din ne ba ko ba shi ba amma duk a rasa me bibiyar hakan, wannan ai abun dubawa ne, tun da mu dai har yanzu bai ce mana shi ya dauketa ba" Nenne tace "To er bakin ciki, shi din ne ya sungumeta ba kowa ba aniyarki ta bi ki, kuma ai halaliyarsa ya sunguma ba wata ba, duk wanda ya sake cewa zai bada shawara a wannan lamari idan ban sa Ali ya sallamesa ba shegiya uwata da ubana suka haifeni, kwata kwata bakwa neman ma Ι—a na sauki a rayuwar nan, burin ku kawai tashin hankali ya kashe Ali ku huta ni kuma in shiga uku, ita uwar da ta tsugunna ta haifi yarinyar bata da bakin magana sai ke me baki kamar ta dorinar ruwa?" Mikewa Mama Zubaida tayi ta shige dakinta, Mama Shatu ta kyabe baki tace "To Allah ya kyauta, in ya dawo mana da gawar ta ai sai mu zauna mu yi zaman makoki ba shikenan ba" Nenne tace "Sai dai ki ga gawar er ki Labeebah amma ba Khaleesah ba, kuma bakin cikin da ku ka kasa boyewa ne zai kashe ku ke da Zubaida" Mikewa Umma tayi hawaye cike idonta ta shiga dakinta, Nenne ta kyabe baki ta mike tana kallon Aunty Farida tace "In Ali ya dawo ki ce masa nace ya zo ya amshi tuwo da miyar taushe zan ajiye masa, wallahi wata guda zan yi ina masa girki ya marmaro" Daga haka ta fice daga gidan, Aunty Farida tayi tagumi hawaye cike idonta.

Meemah ta shigo parlon Momy ta zauna tana Ι—an murmushi, ta jira har Momy ta gama wayar da take yi da aminiyarta godiya sannan tace "Momy na samesa a waya" Da sauri Momy tace "Ya daga kuma?" Meemah tace "Eh ya daga bayan yaga text din da na tura masa kenan" Momy na gyara zama tace "Toh Alhamdulillahi nagode ma Allah, sai yace maki me?" Meemah tace "Kema kinsan dole zai taho ai, amma tsorona daya kada ya kira Daddy kuma ya daga waya yace masa ba haka ba" Momy tayi wani murmushi tace "Bazai daga ba, tunda na riga na gaya masa abinda ke faruwa ai" Meemah ta sauke ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah, in ya samu flight yau za mu iya ganinsu a gidan nan" Momy tace "Me zai hana ya samu jirgi, ai da sauran lokaci dole zai samu" Mai aikin Momy ce tayi sallama tana makale jikin kofar parlon duk da a bude yake amma bata shiga ba, hannunta rike da tray me dauke da plate din gasasshen kaza da lemon kwali biyu, Meemah ce ta amsa sallaman tana mata wani kallo tace "Tun da kika ga kofa a bude ba sai ki shigo ba, kin wani raΙ“e jikin kofa kamar munafuka, don Allah ki dena wannan kauyancin yana damun mu a gidan nan" Momy ta hade rai tana kallonta har ta karaso ta ajiye plate din, cikin ladabi tace "Ga kazar ta kammala Hajiya" Momy tace "Kalan Hijabin nan naki na daga min hankali a gidan nan, kar ki sake saka min shi, in yar wa zaki yi to ki yar bana son shi kwata kwata yayi kalar talauci" Mai aikin ta dukar da kai tace "Toh Hajiya in sha Allah bazan sake sa shi ba, kiyi hakuri" Fita tayi daga parlon da sauri, Momy ta dau plate din tulin kazar da aka ajiye mata ta fara ci tana cewa "Ai dama tunda aka ce min zai taho da ita hankali na ya kwanta, don dama taho da ita shi ne me wuyan...." Meemah tayi murmushi ita ma ta dau yankan kaza daya tana ci tace "I trust you Momy" Khaleesat ta saka Hijab dinta har kasa tana harhada wasu daga kananun kayan dake cikin closet din dakin kamar yanda Abdul ya umarceta tayi, absentmindedly take aikin don tayi nisa a tunanin da take, bude kofar dakin yayi ya shigo, ita dai bata juya ba tana ci gaba da abinda ya sakata, ya karasa har bayanta ya tsaya, taki juyowa gabanta na faduwa, juyo da ita yayi yana kallonta ta sunkuyar da kanta, yace "Me ya sa baki son ki saki ranki har yanxu? Always looking worried" A hankali ta daga kanta ta kallesa amma bata ce komai ba, yace "Kin gama hada kayan ne?" Girgiza masa kai tayi, yace "To gama" ta juya ta ci gaba da abinda take, shi dai yana tsaye yana kallonta, pad ta dauko a karshe zata saka cikin karamin trolley din yace "What are you using that for? Ba yau zaki gama ba?" Taki kallonsa zuciyarta na bugawa tace "Amma ban gama ba ai" Bata jira me zai ce ba ta saka a akwatin sannan ta kulle ta mike tsaye, kamo hannunta biyu yayi yana kallon cikin idonta, speaking slowly yace "Promise me you won't act silly har mu isa kano Khaleesat" Ta rasa dalilin da hawaye ya cika idonta, shi dai kallonta kawai yake, after some seconds yace "If you try anything silly, zaki yi matukar mamakin abinda zan yi, i promise you" Da kyar tace "Toh, amma plss ina son inyi waya da Safiyyah, i am missing her" Yace "Baza ki yi waya da Safiyyah ba, amma idan muka isa kano zan fara kai ki gidanku ki gaishesu sannan mu tafi gidanmu" Ita dai bata ce komai ba hawaye na zuba idonta, a haka suka bar gidan zuwa airport tunda yana da hoton National ID dinta a wayarsa. Da yamma suka sauka garin kano, driver din gidansu har ya iso airport din yana jiransa, Drivern ya bude ma Khaleesat back seat bayan ya gaisheta, kanta a kasa ta shiga motar, kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai gashi ta kara zagbewa gaba daya, Abdul ya shiga ta daya side din, sannan drivern ya shiga motar ya tada suka bar airport din, sai bayan da suka fita daga cikin airport Abdul ya gaya ma drivern inda zai fara kai su, sun yi nisa sosai da tafiyar Abdul ya juya ya kalli Khaleesat da tayi nisa cikin tunanin da take, hannunta ya saka cikin nasa wanda hakan ya dawo da ita reality, ta Ι—an kallesa, yayi kasa da murya yace "Are you hungry?" Girgiza masa kai tayi, ya jawota zuwa jikinsa yana kallonta, ita dai bata ce masa komai ba zuciyarta na bugawa, a haka suka isa Mariri wajen karfe biyar da rabi na yamma, Drivern na parking daga opposite din gidansu Khaleesat Abdul ya bude motar ya sauka, jiki a sanyaye Khaleesat ta sauka daga motar, ta ma rasa ko farin ciki zata yi ko akasin haka ganinta a kofar gidansu, Abdul ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidan sai a sannan hawaye suka cicciko mata ido, Noor ce ta fara hangota tana hura gawayi ta taso da gudu ta rungumeta, sai a sannan sauran en gidan duk suka juya suna kallon Khaleesat, Umma dake zaune bakin kofar dakinta ita ma ta dinga kallonta, Mama Zubaida da Mama Shatu suka taΙ“e baki suna kallon juna, Aunty Farida dake gyara dakin Umma ta fito da sauri jin sunan wanda Noor ta kira, Khaleesat ta tafi ta rungumeta ta fashe da matsanancin kuka, Farin ciki wajen Aunty Farida ba a cewa komai don duk tunanin su Ajay ne suka dawo da ita gida, sallaman Abdul yasa duk suka juya suna kallon hanyar shigowa gidan da mamaki, nan da nan fara'ar Aunty Farida ya bace, su Mama Shatu ne kawai suka amsa masa sallaman, ya karaso cikin compound din, Aunty Farida ta saki Khaleesat ta tafi ta zauna kusa da Umma fuskarta babu yabo babu fallasa, Mama Zubaida ta mike da sauri ta shimfida masa tabarma ita da Mama Shatu na masa sannu da zuwa, ya zauna kan tabarman yana kallon Umma ya gaisheta, Umma ta amsa tace "Sannu da zuwa" Aunty Farida ta mike ta shige dakin Umma, Abdul ya gaida su Mama Zubaida dake ta washe baki, duk suka amsa da fara'a, Ita dai Khaleesat na durkushe kusa da Ummanta kanta a kasa, Abdul ya kalli Umma yace "Baba baya nan ne" Umma tayi karfin halin cewa "Eh bai dawo ba" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Malam Ali ya shigo gidan da rabin buhun dankalin Hausa a hannunsa, ajiyewa yayi ganin Abdul da Khaleesat, yace "A'aa, ikon Allah, baki mu ka yi yau a gidan" Abdul ya tashi ya tafi har inda Malam Ali ke tsaye ya gaishesa, Malam Ali ya amsa yana kame kame, ya tafi da sauri ya dauko tabarma ya kara shimfida ma Abdul yace "Yi zaman ka a nan, bari in zubo mana ruwa a buta lokacin Magariba yayi" Da sauri ya tafi ya dauko butoci biyu ya tafi zai debo ruwan, Umma ta mike ta shige dakinta, Khaleesat ta bi bayanta, Nenne ce ta shigo gidan da sallama tace "Allah me hikima, sannunku da zuwa Awdul" Abdul ya gaisheta, ta jawo kujera ta zauna tana facing dinsa tace "Lafiya lau wallahi, ya iyayen naka, ina kokarin daura sanwa kenan sai ga wani almajiri da gudu ya zo ya sanar min ai kun zo, kasan Ι—an albarka ne almajirin nan duk wani abu da ke faruwa a gidan Ali kamar kiftawan ido yake rugowa ya sanar min, ni kuma in ina da er dabino kwara uku in basa la'ada, nayi farin cikin ganin ka wallahi, ina matar taka, in ji tare ku ke?" Yace "Tare mu ke" Sai ga Malam Ali da ruwa a butoci yace "Ai ina jin tana dakin uwarta" Nenne tace "Kai kuma lafiya? ina zaka da butocin ruwa ko karfe shidda bai yi ba?" Malam Ali yace "Au? To to bari a ajiye, na zata magariba ta yi" Da sauri ya koma ya ajiye butocin ya dawo, Nenne tayi kasa da murya tana kallon Abdul tace "To Awdallah, ka dubi girman Allah ka rike amanar da muka baka, yanxu kai ne uwarta kai ne ubanta, duk ta kuskure maka ka kawota wajena ni zan san yanda zan yi da ita, kuma albarkacin auren da ya shiga tsakaninka da jikata ka kara ba Mahaifinka hakuri ya yafe ma Malam Ali komai ya wuce a wajensa don girman Allah, don yanxu kam duk mun zama daya tunda ga aure har ya shiga tsakani, Allah Ubangijin ya baku zaman lafiya ya kauda duk wata fitina ya kawo zuri'a dayyaba" Abdul yace "In sha Allah Kaka" Nenne na murmushi tace "To madallah, gashi ko tuwon dare ban yi ba balle in zubo maka" Yace "Ba komai, can gidanmu za mu wuce yanxu yamma tayi" Nenne tace "Gaskiya kam, bari in fito maka da ita ku tafi, go slown hanyar nan bata da kyau" Tashi Nenne tayi ta nufi dakin Umma, kuka kawai Khaleesat take Umma tayi tagumi tana kallonta ta ma rasa abun cewa amma daurewa kawai take ita ma hawayen bai zubo mata ba, don bakin ciki Aunty Farida na jingine jikin bangon dakin ita ma ta kasa cewa komai, a haka Nenne ta shigo dakin ta same su, taΙ“e baki tayi tace "Ta so ki fita mijinki na waje na jiranki" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana kuka kamar ranta zai fita, Nenne tayi kasa da murya tace "Wato a yanda kanwar uwarki ke zube ba mashinshini shekara da shekaru haka kema kike son ki zauna mana tunda kyau kawai gare ku amma babu farin jini, banda samun waje ki samu miji zankadede kamar Awdul amma son zuci irin taki da na uwarki da kanwarta bazai sa ku yi farin ciki da hakan ba, in a baya Awdul Ι—an iska ne dama Allah ya taΙ“a halittar da bai shiryar ba in yayi niyya? Daga yanda Awdul ke magana a kintse na gane ya shiryu wallahi, to ko kawota da yayi ta gaishemu kadai ya isa mu shaida shiriyarsa, wallahi ku dinga jin tsoron Allahn da ya halicce ku, duk wanda burinsa ya raba aure to tsinuwar Allah ne zai tabbata a garesa, kuma in sha Allahu Khaleesat tayi aure kenan mutuwa kadai ne zai rabata da mijinta tunda duk mun san yana sonta, tashi ki fita gun mijinki ku tafi munafuka kawai, duk da can baki san baki son shi ba sai da ya aika ki kasar turawa idonki ya bude a can" Cikin kuka Khaleesat tace "Ni wallahi bana son sa, bana son sa, bazan iya zama da shi ba" Nenne tace "Aikin banza, to uban me ya rage kuma bayan ya kwana da ke? Ai duk rashin son da kike masa dole ki zauna da shi tunda ya kwana dake yau kusan satin ki daya a gidansa ba kuma ajiye ki zai yi yana kallo kamar hoto ba tunda shi ba Ι—an iska bane, kuma gidan Ali ba Obalande bane da za a tara masa fararen zawara har biyu a gida, Farida ma kadai ta ishemu, tashi ki fita ki bani waje ko in tafi in kira maki Ali yanxun nan ya fitar min da ke, tun da uwata ta haifeni ban taΙ“a ganin er da bata son kwanciyar hankalin ubanta ba sai ke" Umma ta share hawayen dake zuba idonta tana kallon Khaleesat tace "Ta shi ki je Khaleesah, Allah ya maki albarka, Allah kuma ya baku zaman lafiya" Mikewa Khaleesat tayi tana kuka sosai ta fita daga dakin Ummanta, Nenne tace "Atoh dai, iya addu'ar da za mu yi mata kenan a matsayin mu na rikakkun musulmai, tun da muka ga haka to Allah ne kadai ya san hikimarsa nayin hakan, kuma dama an gaya min aurenta da Awdul aure ne me kyan gaske in har zata kwantar da hankalinta, gashi mun shaida yana son ta, kuma ta dalilinta arzikin ubanta duk zai dawo har ma ya fi na da, wallahi haka aka ce min, kawai dai babba ba a son yayi ta surutu ne shi sa nake jan bakina nayi shiru" Har suka bar gidan da Abdul hawaye ne kawai ke zuba idon Khaleesat, dubu talatin ya ba kishiyoyin ummanta ko wacce 15k, ya ba Islam 50k, Nenne ya bata 20k, Malam Ali kuwa bai amsa kudinsa ba sai ajiye masa Abdul yayi kan tabarman dake bakin kofar dakinsa, babban tashin hankalin Khaleesat yanxu period dinta da ya dauke, don kafin su taho kano a dari dari tayi sallahn Azahar kar ya shigo ya ganta,  tasan yau dai Ζ™aryar ta ya kare kawai, a haka suka iso gidansu Abdul bayan sallan magrib, Driver na shiga babban compound din da mota Khaleesat taji gabanta ya tsananta faduwa, bayan yayi parking a space din parking Abdul ya sauko daga motar yana kallonta, da kyar ta iya saukowa daga motar zuciyarta na bugawa sosai wanda ita kanta bata san dalilin hakan ba all of a sudden, ya fara tafiya tana bin sa har suka isa entrance din shiga parlorn gidan....

[6/18, 7:34 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat na tafiya a hankali ta shiga parlon tana karanto addu'o'i a ranta don irin faduwar da gabanta yake yi isn't normal, ga tsikar jikinta sai tashi yake, she was so uncomfortable and restless at the same time, Abdul ya kulle kofar parlon ya kalli mahaifiyarsa dake zaune cikin parlor ita da kanwarta Aunty karima da Meemah, ko wannensu da bowl cike da farfesun kayan ciki a hannu, Khaleesat ta sunkuyar da kanta ganin gaba dayansu zubo mata ido suka yi suna kallonta fuskarsu babu yabo babu fallasa, amma kana kallon kwayar idanuwansa babu abinda zaka gani sai tsantsan kiyayyarta, da kyar ta karasa tsakar parlon kamar zata harde ta fadi, ta duka kasa cikin sanyin murya ta gaishesu gaba daya, instead Momy sai ta dauke kai tana kallon Abdul tace "Flight din sai na dare ka samu kenan Babana, bayan tun sassafe Meemah tayi maka text" Aunty Karima ta hau kwalo ma mai aiki kira ta zo ta karo mata farfesu, Abdul bai ce ma Momy komai ba ganin babu wanda ya amsa gaisuwar Khaleesat cikinsu ya kalleta yace "Ta shi mu je" Khaleesat ta Ι—aga kai ta kallesa amma bata tashi ba ga zuciyarta sai bugawa yake, Momy tace "Ta tashi ku je ina? Wacece ita din tukunna?" A takaice yace "Matata ce" Aunty Karima ta gyara zama da mamaki tace "Ikon Allah, ita ce er gidan barawon da yayi ma Alhaji sata har na miliyan dari kenan?" Meemah tace "Kwarai kuwa gashi kin gane ma idonki, ita ce dai er matsiyatan da Abdul ya makale ma saboda rashin sanin darajan mahaifinsa bai dubi rashin kirkin da aka yi ma Daddy a kotu akan hakkinsa ba ya koma ma yarinyar, dama yawon ta zube uwarta ta shigo yi Nigeria shi ne ta hadu da ubanta bayan sun yi watsewarsu ya aureta...." Katse ta Abdul yayi a fusace yace "Idan kika ci gaba da voicing gibberish zaki sha mamakin abinda zan maki a nan Amina, bridle ur tongue" Aunty Karima ta bude baki da mamaki tace "Amina kai tsaye? Ko ka fara shaye shaye ne Abdul? Akan shegiyar yarinyar nan kake nema kayi ma yayarka rashin kunya?" Abdul ya kalleta yace "Kar ki sake sako min baki tunda ba dake nake ba, stay out of anything that concerns me, Momy ce dolen ki ba ni ba" Momy tayi wani murmushi tace "Rabu da su Babana, take her inside ta huta, sannunku da zuwa" Tana fadin haka ta tashi ta taho kusa da Khaleesat ta dafa ta tace "Welcome my daughter, ku je sama kin ji" Da kyar Khaleesat ta mike tsaye duk jikinta a sanyaye ta bi bayan Abdul, Momy ta koma ta zauna ta bi ta da kallon gefen ido, har ta ga sun haura sama sannan ta kalli su Meemah tayi kasa da murya tace "Sam baku da hankali baku da tunani, haka muka yi da ku daxu?" Meemah da ke huci tace "Ni matsala ta kinsan ban iya pretending bane Momy, wallahi ban iya ba ko nace zan yi" A fusace Momy tace "To in kin san ruguza min plan za ki yi ki ja min asara to tun wuri ki tattara ki tafi gidan Suwaiba bana son hauka, duk ba ke kika ja mana wannan bala'i ba? da sa hannun ki fa abubuwan nan suka faru, ai wallahi sati daya yayi ma yarinyar nan yawa a gidan nan in dai ni na haifi Abdallah, don haka duk wanda bazai iya abinda nace yayi ba to ya bar gidan nan kawai kar ya ja min asara" Aunty Karima tace "Toh Momy kar kuma fa yace zai koma can gidansa da ita, kin san babu me sa shi babu me hanasa idan yayi niyyar yin abu" Momy tace "Ku dai ku zuba min ido kawai ku ga ikon Allah, ance maku ni mahaukaciya ce warce bata san abinda take yi ba irin ku? Ai ni ba yarinya bace nasan me nake yi" Mikewa Momy tayi tana tafiya gansan gansan ta nufi staircase, Meemah ta kyabe baki tace "Wallahi ji naki zuciyata bazata iya wani pretending ba akan shegiyar yarinyar nan me kamar sadaka yalla, ban taΙ“a jin tsanar mutum a duniya irin yanda na tsaneta ba, Abdul bai taΙ“a min kalan tijaran da yayi min akan ta ba, kuma fa a gabanta yayi min haka tana ji tana kallo" Aunty Karima ta sauke ajiyar zuciya tace "Nima ba gashi yayi min ba Meemah, fatan mu kawai komai ya zo karshe cikin gaggawa, mu yi yanda Momy tace kawai" Khaleesat ta dinga bin dakin da Abdul ya kawota da kallo wanda babu tantama dakinsa ne, a hankali ta zauna saman kujeran dakin tana kallonsa yana cire agogon wrist dinsa alamar zai shiga bandaki yayi alwala, abinda aka yi mata a parlor ne kawai ke yawo a kanta, tayi nisa tunanin da take yi sai gashi ya fito daga bandakin yana kallonta yace "Shiga kiyi alwala" Sosai gabanta ya fadi ta daga kai tana kallonsa, ta dake tace "Ai ban gama ba" Wani tsawan da ya gigitata ya daka mata, yana mata wani mugun kallo yace "Kar ki raina min hankali, is it going to take u forever to finish ur period? Karya kike yi kin gama" Tsabar yanda ta tsorata jikinta har bari yake ta ma rasa me zata ce masa, yace "Idan na dawo masallaci i will check for my self" Daga haka ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, hawaye ya fara zarya a idonta, wannan moment din take ta tsoro gashi ya zo kuma babu yanda ta iya, shesshekan kuka ta fara yi cikin tashin hankali, bayan ya fita da kamar minti biyu taji an bude kofar dakin, ta juya da sauri gabanta na faduwa, Momy ce ta shigo dakin ta sakar mata murmushi ta nufota tace "Ya sunanki daughter? Mu sai yace mana Khaleesat, ni dai nace Khaleesat ai ba sunan yanka bane" Khaleesat ta sauke idonta zuciyarta na bugawa a hankali tace "Sunana Hauwa" Momy tace "Maa sha Allah, ashe uwata ce, welcome to the family my dear, taso mu je kiyi sallah" Khaleesat felt a bit relieve da gesture din Momy toward her, ta mike tsaye Momy ta kama hannunta suka fita daga dakin, can bangarenta ta tafi da ita har cikin Bedroom dinta sannan ta nuna mata bandakin dake dakinta tace "Ki shiga ciki kiyi alwala, amma kafin nan let's do a mother and daughter talk first my dear" Khaleesat ta daga kai tana kallon Momy, Momy ta nuna mata kan kujera tana mata murmushi tace "Get sitted Mamana" Khaleesat ta zauna kan 2 seater dake dakin Momy ta zauna gefenta tana facing dinta tace "Kar ki boye min komai mamata, ki daukeni tamkar mahaifiyarki, ki gaya min gaskiya wani abu ya shiga tsakaninku da Abdul ne tun bayan da ya dauke ki?" Sosai Khaleesat taji tambayar yayi mata nauyi a kai, hakan yasa ta kasa kallon Momy ta sunkuyar da kanta kawai, Momy ta kwantar da murya tace "Akwai dalilin da ya sa nake tambayarki haka ne Mamana, kar ki ji kunya ki boye min komai, open up to me" Girgiza mata kai kawai Khaleesat tayi ba tare da ta bari sun hada ido ba, Momy ta kamo hannunta tace "Kar fa ki ji kunyata ki boye min komai mamana, gaskiya zaki gaya min" a hankali Khaleesat tace "Gaskiya na gaya maki Momy" Momy ta dinga kallonta kamar dai bata yarda ba, can tace "To saboda me? Anya kuwa gaskiya kike gaya min Mamana?" Khaleesat bata dago kanta ba tace "Period nake yi ne" Momy tace "Toh kin gama yanxu?" A hankali Khaleesat tace "Daxu na gama" Momy ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "To naji dadin jin hakan mamana, don nasan irin daukan da Abdul ya tafi ya maki bayan dawowar ki daga makaranta, hakan bai ba iyayenki daman yi maki duk abubuwan da ya kamata su maki ba a matsayinki na budurwa kafin ki tare gidan mijinki, basu samu daman yi maki shirin xuwa gidan miji ba, amma tunda ya kawo ki nan in sha Allah zan maki duk abinda ya kamata diyata...." Ita dai Khaleesat tayi shiru har sannan bata dago kanta ba, Momy ta mike tace "Ta shi mu je bandaki ki ga...." Khaleesat ta mike tsaye ta bi bayan Momy har zuwa bandakinta, Momy ta nuna mata wani babban flask tace "Kin ga wannan flask din? To zaki dinga tsiyayan ruwan ciki ki sirka da ruwan zafi a pampo ki dinga tsarki da shi" Momy ta dauko wasu Ι“akakken sabulai dake nannade a leda ta mika mata tace "Sabulan nan su ma tsarki zaki dinga yi da ko wannensu, in kin yi sai ki ajiyesa inda kika ga na dauko yanzu don naki ne" Momy ta nuna mata wani roba dake rufe a bandakin shi ma tace "Wannan ma diba zaki yi kiyi tsarki da shi, kin ji?" A hankali Khaleesat tace "Toh Momy" Momy ta dauko wani kwalba dake boye a cikin bandakin, Khaleesat dai bin ta kawai take da kallo ta bude flask din ta tuttule abinda ke cikin kwalban, sannan ta mike tace "Yauwa mamana, duk ki tabbatar kinyi amfani da su yanda nace, sai kiyi alwala ki fito" A hankali Khaleesat tace "Toh Momy" Daga haka Momy ta fito daga bandakinta ta shimfida ma Khaleesat darduma, sannan ta zaune kan kujera ta jirata har ta fito daga bandakin, Momy ta mike ta nuna mata darduman tace "In kin idar da sallan kar ki fito, kiyi zamanki zan kawo maki abinci" Khaleesat tace "To Momy" Daga haka Momy ta fita daga dakin ta kulle da key ta tafi da makullin tana Ι—an murmushi, a corridor ta hadu da Abdul ya taho daga dakinsa bayan ya shiga bai ga Khaleesat a ciki ba, Momy tace "Har ka dawo masallacin Babana?" Yace "Na dawo, tana ina ne Momy?" Momy ta ja kunnensa tace "Yanxu abinda kayi ma yayarka ya kamata Babana? Kasan ta fa wani lokacin ba hankali ya ishi yayar taka ba, da sai kayi hakuri ka kyaleta da halinta kawai" Ya hade rai yace "Dukanta fa take kokarin yi Momy? A ina ta san ta ko kuma me tayi mata da zata zageta kuma ta nemi ta doketa??" Momy ta kama hannunsa suka shiga dakin baΖ™in dake kusa da su tana kallonsa tace "Ai na mata fada sosai Babana, yanxu ma haushin abinda kayi mata ne yasa tayi abinda tayi a parlor amma kayi hakuri kaji Babana" Yace "Naji, ina Khaleesat din take?" Momy tace "Bazan fa baka matar ka ba sai zuwa jibi in ma zaka cire ido a kanta ka cire, tun da baka bari iyayenta sun gyarata yanda ya kamata ba to ni zan gyarata" With confusion Abdul yace "Gyarata kamar yaya Momy?" Momy tace "Ka taΙ“a ganin inda aka dau mace budurwa aka kai ta gidan miji haka nan? To fin karfin iyayenta da kayi kuma suna shakkar ka shi yasa suka baka ita haka babu yanda suka iya maka, amma a al'adar mu ta Hausa babu inda ake yin haka, ni kuma kaga bazan baka ita ba sai nayi mata duk abinda ya kamata na gyarata, in kuma rashin kunya zaka yi min to yi Babana, Khaleesah dai bazan baka ita ba sai zuwa nan da jibi in sha Allah, zan mata duk abinda ya kamata a matsayin ta na 'ya ta" Abdul ya kasa cewa komai yana kallon Momynsa, Momy tace "Mu je ka ci abinci" Bata jira cewarsa ba ta fita daga dakin, bin bayanta yayi ya fita amma duk tsaurin idonsa sai yaji nauyin ce ma uwar tasa komai, haka nan Momy ta dauko masa abincinsa da ta hada masa da kanta ta jera masa su a dinning sannan ta koma kitchen zata hada abincin Khaleesat, Abdul ya zauna kujeran dining amma ya kasa cin abincin, shi fa bai yi niyyar ma kwana gidan da Khaleesat ba don irin burin da ya ci a kanta yau ai sai Allah, nan da nan yaji ransa ya baci, ya mike ya shiga kitchen ya samu Momy ta sa mai aikinta ta jera ma Khaleesat abinci a tray, don irin abin da ta hada mata har ya fi na Abdul, Momy na kallon mai aikin tace "Tafi ki kai mata bangarena ki jirani ina zuwa" Mai aikin ta fita daga kitchen din da tray din, Abdul na kallon Momy a fusace yace "Toh wai menene yasa Meemah zata ce min Daddy ba shi da lafiya critically bayan ma ashe baya kasar?" Momy tace "To ai ganin likita yaje a Amurka, ko bai gaya maka bane? Karfe hudu na yamma jirginsu ya tashi, shi yasa kaji nake cewa baka taho da wuri ba don duk zatona zaka tarar da shi" Abdul yayi shiru yana kallon Momy, Momy tace "Ni dai bari in je wajen diyata, kar ka wani huce kan Meemah don ba ita ta hanaka matarka ba" Daga haka Momy ta bar sa tsaye a kitchen din, tsaye ta tarar da Mai aikinta a bangarenta tana jiranta don kofar a kulle yake, Momy ta bude mata suka shiga ciki, Mai aikin ta ajiye abincin gaban Khaleesat, Momy na kallon mai aikin wanda ranan ne ranan farkon da ta shigo mata daki tace "Toh fita ki ban waje...." Mai aikin ta fita da sauri ta kullo kofar, Momy tayi murmushi tana kallon Khaleesat tace "Ga abinci nan Mamata" Momy ta tafi ta dauko handbag dinta ciro wani kulli ta dawo kusa da Khaleesat ta bude kullin ta barbada mata abinda ke ciki a farfesun kayan cikin dake cike a bowl tace "Maza ki shanye har romon kin ji" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Momy ta tafi ta zauna kan kujera tana murmushi ta dau remote ta kunna TV din dakin, a hankali Khaleesat ke shan farfesun tunani iri iri na yawo a kanta, to yanxu kenan hakuri kawai zata yi da auren Abdul, since gaba daya family dinta sun nuna sun yi accepting auren, sannan ga Mum dinsa ma ta ga tana sonta, kilan zaman aure da Abdul a kaddarar rayuwarta yake, she should just accept it with good faith, most important of all gashi mahaifiyarsa na sonta, his sister won't be an issue tunda mamansa na sonta, kawai ta saka ma ranta salama ta amshi auren tunda haka Allah ya kaddara mata, Housemate dinta ne ya fado mata, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, da sauri ta sunkuyar da kai kar Momy ta gani cikin dubura ta dinga goge hawayen tana jin wasu masu zafi na sakkowa, sai da Momy ta tabbatar ta ci abincin sosai, sannan ta umarceta da taje tayi wanka ta tabbatar ta sake tsarki da duk abubuwan da ta nuna mata a bandaki, kafin Khaleesat ta fito Momy ta dauko mata kayan bacci da inner wears, Khaleesat ta shirya tayi sallan isha'i, Momy bata tashi barin dakin ba sai kusan karfe tara da rabi, bayan ta sa Khaleesat ta kwanta kan gadonta sannan ta kashe mata wutan dakin ta bata remote din Ac a kusa da ita, tayi mata sai da safe ta fita daga dakin, har ta kulle kofar ta sake budewa ta shiga tana kallon Khaleesat tace "Ko tashi kika yi zaki kama ruwa cikin dare kiyi tsarki da abubuwan nan fa Mamana kar ki manta" Khaleesat tace "Toh Momy" Momy ta kara mata sai da safe sannan ta fita ta kulle kofar da makulli ta sauka downstairs, Abdul kadai ne zaune parlor yana kallon kwallo amma kana ganinsa kasan ransa a bace yake, Momy tana kallonsa tace "Sai da safe Babana" Ciki ciki ya amsa mata, ta juya ta koma sama zuwa dakin da su Meemah suke, duk suka dinga kallon Momy bayan ta shigo, Aunty Karima tace "Ya dai Momy duk ta yi?" Momy tayi wani murmushi tace "Tun yaushe kuma" Meemah tace "Alhamdulillahi, shi Abdul din fa?" Momy tace "Shi ai dama a miyar shinkafa aka ce na zuba masa maganin, sai ruwan lipton, na kori mai aikin taje bakin pampo tayi wanke wanke shine na samu duk na zuba masa nasa" Meemah tayi murmushin mugunta tana gyara zama sanin Momy bata bin malaman banza, kai in malami yace zai amshi kasa da 1M a wajenta ma bata yarda da ingancin aikinsa ba, inda ake aikin da gaske take zuwa, ko da kuwa miliyan biyar zata kashe bata kyashi don tasan aiki na gaske ake mata.

[6/19, 8:55 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Washegari da safe bayan Khaleesat ta shirya cikin tsadadden Abayan da Momy ta bata, Momy ta gama hada mata shayin da take yi cikin cup tace "To zo kiyi breakfast din kar ya huce Mamana" Khaleesat bata ce komai ba ta karasa ta zauna kan darduman da aka jera mata breakfast din, Momy tayi murmushi tace "Idan farfesun bai isheki ba sai ki bude warmer ki Ζ™ara, dankalin ma akwai saura a warmer in bai ishe ki ba" Ita dai Khaleesat kai kawai ta gyada mata, tana juya shayin gabanta a hankali da spoon din ciki, Momy ta koma kan kujera ta zauna tana kallonta tace "Duk da ma ina lura jiya baki wani ci abincin da aka kawo maki da yawa ba, ko maganin cin abinci zan sa a samo maki mamana" Khaleesat tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba ta dau shayin tana kallon ciki, sai tayi tunanin lipton din ne kilan ya fashe a cikin ruwan shayin, sipping din shayin tayi kadan ta ajiye sannan ta fara cin irish din, Momy dai kallonta kawai take kasa kasa, Bude kofar dakin aka yi Momy ta juya, ganin Abdul tace "Sai yanxu ka tashi Babana" Bai ce mata komai ba ya karasa ya zauna saman kujera, Khaleesat ta Ι—an kallesa taga kallonta yake, sauke idonta tayi a hankali tace "Ina kwana" Ya kauda kai yace "Lafiya" Momy tace "Ka tashi kaje kayi breakfast din ka" Yace "Momy za mu je shopping ne, bata zo da kaya ko daya ba" Momy na kallonsa tace "To wanda ka gani a jikinta yanxu kai ka siyo mata?" Shiru Abdul yayi yana kallon Momy, Momy tace "To har na tura ma Meemah kudi su je su yi mata siyayya ita da Karima tunda kai baka da Ζ™ara" Mikewa Abdul yayi ya nufi kofa ya fice daga dakin, Momy ta bi sa da kallon gefen ido, sai da Momy taga Khaleesat ta gama cin abinda zata ci na breakfast din sannan ta mike ta fita ta kira mai aikinta ta fitar da sauran abubuwan da Khaleesat ta rage, bayan mai aikin ta fita Momy ta bude bayan labulenta ta dauko wani karamin jarka ta kawo ma Khaleesat tace "Wannan tsumi ne Mamana, daga yanxu har zuwa dare nake son ki shanyesa gaba daya" Ita dai Khaleesat kallon jarkan take, Momy tace "Kin ji ai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Toh Momy" Momy ta dauka ta mayar bayan labule sannan tace "In zaki yi kallo sai ki kunna TV abun ki, bari in je zanyi bakuwa ban san ko ta iso ba" Khaleesat tace "Toh" Momy ta fita daga dakin ta kulle da makulli tana rike da makullin ta sauka downstairs don aminiyarta godiya ta kirata ta sanar mata tana hanya, tana shigowa parlor taga Abdul zaune dinning area da breakfast din da Khaleesat ta rage a gabansa, da karfi Momy ta kwala masa kira, ya juya yana kallonta, ta karasa wajen da mugun sauri tace "Banda abun ka ba ga naka a kitchen ba Abdul me zaka yi da wanda aka rage? Ko har kaci wannan din ne?" Abdul dake kallonta yace "Ban ci ba, amma menene idan na ci?" Momy ta kwalo ma mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da sauri Momy ta kunduma mata wani ashar tace "Nan nace ki ajiye sauran abincin er iska kawai er neman jidali? Me yasa ke dakikiya ce? Wallahi zan kore ki fa a gidana na gaji da maganar da kike sa ni kamar kanwar uwarki, yau ga shegiyar mata kawai" Abdul ya kalli Momy yace "Ni fa nace ta kawo min nan, beside what is wrong with the food da bazan ci ba?" Momy ta mata tsawa tace "Dauka ki wuce ki ban waje guntuwar banza kawai" Mai aikin na ba Momy hakuri ta dauke jiki na rawa ta tafi kitchen da breakfast din, Momy ta kalli Abdul dake kallonta, yace "I want to understand meye da abincin da bazan ci ba Momy?" A takaice Momy tace "Kayan gyaran mata mana? Ko kai na mace ne?" Bata jira cewarsa ba ta bar wajen ta shige kitchen ya bi ta da kallo, Tuttular da shayin tayi a sink sannan ta juye sauran irish din da kwai da farfesun duk ta cakudesu waje daya tace "Gasu nan ki kai ma karnuka, in kuma kwadayin ki ya ja ki kika ci ke kika jiyo" Mai aikin ta risina ta amsa tace "Toh Hajiya" Sai da Momy ta jirata har ta dawo bayan ta kai ma karnukan can cage dinsu sannan Momy ta dau breakfast din Abdul ta kai masa kan dining din tace "Ga naka nan"  Daga haka ta juya ta bar wajen, dai dai shigowar Godiya gidan, da fara'a Momy ke mata sannu da zuwa Abdul ya dauke kai kamar bai ganta ba don ya tsani matar with passion, tun asali dama baya gaida ta, Haka Momy ta ja ta zuwa sama tana cewa "Mu je ki ga surkar tawa ku gaisa" Da ido Abdul ya bi su har suka haura sama, Momy na isa kofar dakinta ta bude da makulli suka shiga, Khaleesat dake gyara gadon Momy ta mike tsaye tana kallonsu, Momy na murmushi ta kalli godiya tace "Kin ganta" Da fara'a sosai Godiya tace "Maa sha Allah, ai ko ga ta kamar balarabiya Maa sha Allah, sannu amarya, ya sunanki?" Momy na murmushi tace "Sunan Baabata gareta, Hauwa sunanta" Khaleesat ta zame kasa ta sauke idonta ta gaida Godiya, Godiya ta karasa kusa da ita ta dafata tare da Ι—agota ta zaunar da ita gefen gadon Momy tace "Lafiya lau diyata, ya bakunta?" Khaleesat bata ce komai ba kuma bata dago kanta ba, Momy na kallon Khaleesat tace "Kin sha tsumin da nace ki sha kuwa?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Na sha" Momy tace "To maa sha Allah, Allah ya maki albarka Mamana, zuwa anjima sai ki kara sha kin ji" Khaleesat tace "To" Bayan few minutes Momy da Godiya suka fita dakin, Momy ta sake kulle kofar da makulli sannan ta cire makullin suka tafi wani daki dake sama, bayan sun shiga Momy ta kulle kofar tana kallon Godiya tayi murmushi tace "Duk tayi amfani da abubuwan babu gardama godiya, iya na jarkan nan ne kawai ya rage yanzu" Godiya ta zauna gefen gado tace "To madallah, shi ma Abdul din duk kinyi yanda aka ce kiyi da na sa?" Momy tace "Kwarai kuwa" Godiya tayi wani murmushi ta bude handbag dinta ta ciro wani babban laya bakikirin da shi ga er karamar kwado a jiki ta mika ma Momy tace "To aikin karshe kenan wannan Hajiya, Malam ya ce ki samu inda kika san baza a taΙ“a tono sa ba ki binne a cikin gidan nan" Momy ta zauna gefenta tana murmushi ta amshi layan tace "To laya nawa na binne gidan nan ba a tono ba godiya, ai wannan karamin aiki ne a wajena don ba sabon abu bane" Godiya tace "Yauwa, bayan kin binne Malam yace ki basa yarinyar kawai, wallahi yace min in har ta wuce sati biyu Abdul bai rabu da ita ba to bazata wuce sati biyar ba a gidansa" Fara'ar fuskar Momy ya bace tace "Har sati biyar Godiya? Ni da yace min sati daya kacal a waya" Godiya tace "Halan bai gaya maki irin abubuwan dake Ζ™an dan ki bane? Da yaya ma aka samo kansa har asirin nan yayi tasiri? Ai abubuwan Ζ™an Abdul sun fi karfin wani asirin wallahi kiji in gaya maki" Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "An taΙ“a gaya min haka da dadewa wallahi, don ni akwai malamin da yace min ma yanda asiri ke cin ubansa shi sai an wahala asiri zai ci sa" Godiya tace "To wallahi Malam sai da ya tura masa aljanu don ma ki ji Hajiya, aikin nan sai da Malam ya hada da wasu malaman don aiki ne me wahalan gaske yace min wallahi" Momy tace "To ni fargabana kada fa in mika masa yarinya ace asirin nan bai ci ba abinda muke gudu ya afku mu shiga uku Godiya" Godiya tace "Sai kace yau Malam ya fara maki aiki? Ai da aikin bai yi ba kinsan bazai boye mana ba, sai dai ya kara mana lokaci yayi wani sabon aikin fa, dama yace in na yarinyar ya ci shine zai sa na Abdul din ma yayi tasiri sosai" Momy tace "Haka ya ce kam" Godiya tace "Don haka zuwa gobe ki basa ita kawai su tafi an gama aiki sai jiran result, kuma ina me tabbatar maki zaki sha mamaki" Momy na murmushi tace "Toh shikenan godiya, nagode sosai, zan tura masa cikon dubu dari biyar dinsa anjima" Da yammacin ranan bayan Momy taga Abdul ya fita gidan tayi maza ta aiki mai aikinta kasuwa saboda tayi amfani da daman ta haΖ™a rami a garden din gidan ta binne layan da Godiya ta kawo mata, bayan mai aikin ta tafi Momy ta zaga zuwa garden din gidan ta samu spot me kyau ta fara haΖ™a rami da wuka, bayan ta haka yayi zurfi yanda take so sannan ta jefa layan ta mayar da Ζ™asan wajen ta dau wani dutse ta dora dai dai wajen don kada a ga alamar an tono kasa, tap ta bude don wanke hannunta da wuΖ™an da tayi using, Khaleesat ta karasa bakin window din dakin Momy jin Ζ™aran bude ruwan pampo, in ta gaji da zaman dakin dama jikin window take zuwa ta tsaya tana kallon waje, ta tsaya jikin window din tana ta kallon Momy dake ta wanke hannunta bayan ta wanke wuΖ™an, bayan ta gama ta kara komawa kusa da dutsen tana seta sa da kyau ta yanda ko da wasa baza a ga tonannen Ζ™asa ba, sai kuma ta mike ta fara tsinko doddoya dake Garden din, sannan tayi using wuΖ™an hannunta ta yanki pumpkin leaves isasshe bayan ta gama ta bar garden din tana rike da ganyayyakin hannunta, babu abinda Khaleesat ta kawo a kai don tunaninta ganye Momy taje diba a garden din, Momy na kai ganyayyakin kitchen sai ga su Meemah sun dawo daga shopping din da ta aikesu su yi ma Khaleesat, dariya Momy ta dinga yi a parlor ganin wasu shegun abayoyi masu saukin kudi da suka kwaso ma Khaleesat irin wanda ake dinkawa a kano, ga wasu shegun dogayen riguna su ma masu arha, hatta inner wears da suka siyo duk very low quality ones ne, babu wani abu na arziki da suka siyo ma Khaleesat, Momy na ci gaba da dariya tace "Duk maida su cikin ledojin kawai na yafe ganin wannan tarkace haka karima, amma baku da kirki yaran nan" Aunty Karima na dariya ta maida kayan cikin leda ta kulle tace "Su ne dai dai er talakawa ai Momy, da so kika yi ki ga abayan dubu hamsin zuwa sama? Ai ita Meemah ma en gwanjo ta so mu je muyi selecting mata kawai" Dariya kawai Momy take, ita kuwa Meemah danna wayarta kawai take don duk wani abu da ya shafi Khaleesat ko kadan baya bata dariya, she just can't wait taga irin rabuwan da Abdul zai yi da Khaleesat don shine babban abinda ke gabanta yanxu. Wajen karfe takwas da rabi Momy na zaune parlor da Abdul tana ta yi masa hira, shi dai wayarsa kawai yake dannawa baya responding kamar ma bai san me take cewa ba, Momy ta kwalo ma mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da gudu tace "Na'am Hajiya?" Momy tace "Zaki ga Kankana da na yanka a kitchen ki dauko ki kai ma Mamata a sama"  Mai aikin tace "To Hajiya" Juyawa tayi ta koma kitchen sai ga ta ta dawo rike da bowl din kankanan tana kallon Momy cikin ladabi tace "Amma Hajiya dakin a kulle yake" Momy tace "A'a a bude yake tun daxu, ki je ki kai mata" Bayan mai aikin ta tafi ta kai water melon din ta dawo ta tafi kitchen ta ci gaba da aikin da take, Momy ta dau wayarta tace "Bari in inyi waya da Alhaji, daxu na ga kiransa ina kitchen wallahi" Shi dai Abdul bai ce mata komai ba har ta shiga dakin dake downstairs ya bi ta da kallo... Bayan minti biyu ya mike ya nufi stairs direct ya tafi bangaren Momy, yana bude kofar dakin Khaleesat dake zaune saman darduma bayan ta idar da sallah ta gama duk addu'o'in da zata yi ta juya ta kalli kofar, sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido da Abdul, ya karasa cikin dakin babu yabo babu fallasa yace "Ta shi mu je shopping...." Khaleesat da gabanta ke faduwa ta nuna masa ledan da Momy ta kawo mata daxu duk da bata duba kayan ciki ba cikin sanyin murya tace "Ai Momy ta sa an min shopping din, ka gan su can ma" Ya hade rai yace "Kee... Get up nace, i am not asking for ur opinion" Ta sauke idonta ta mike tsaye da kyar ta dauke darduman tana linkewa, sosai taji hankalinta ya tashi, a ranta ta dinga addu'an Allah ya kawo Momy dakin immediately, fixge darduman hannunta yayi ganin it's taking her a whole eternity to fold, ya ajiyesa saman kujera sannan ya kama hannunta suka nufi kofa fuskarsa a daure suka fita daga dakin, Khaleesat dai bin sa kawai take a tsorace, downstairs suka sauka har sannan yana rike da hannunta, babu kowa a parlorn sai mai aiki dake goge goge a dining area, ya dau makullin motarsa da ya bari kan center table, Khaleesat ta marairaice masa cikin rawan murya tace "Ya Abdul Momy fa bata sani ba, kar ta shiga dakinta taga bana nan, kaga babu dadi haka" Wani kallon da yayi mata yasa tayi shiru zuciyarta na bugawa, bata sake gigin ce masa komai ba har suka fita parlorn gidan zuwa parking space, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta bayan ya sa ta shiga motarsa ya shiga driver seat, mai gadi ya bude masa gate ya fice gidan da motar. Momy ta fito parlor tana kallon Mai aikinta tace "Naji kamar fitar mota, waye ya fita?" mai aikin tace "Alhaji karami ne ya fita" Momy tace "Shi da wa?" Mai aikin tace "Shi da matarsa" Shiru Momy tayi don bata yi tunanin zai ce zai tafi da Khaleesat yau ba, don so tayi taga yanda za su kwashe, shi yasa ma ta basa hint din dakinta a bude yake, ta zata can din kawai zai bi ta ko kuma ya kai ta dakinsa, Momy ta sauke ajiyar zuciya, ganin mai aikinta sai kallonta take ta hade rai tace "Lafiya kike kallona haka munafuka?" Da sauri mai aikin ta juya ta bar wajen, Momy ta juya ta koma daki amma fa zuciyarta ya kasa nutsuwa sam sam, gani take kamar Abdul zai yi tarayya da Khaleesat, duk da malaminta bai taΙ“a mata aiki bata ga result me kyau ba amma a wnn case din sai take Ι—ari Ι—ari kada abinda suke gudu yaje ya afku dama ga Godiya tace aikin me wahala ne, ai kuwa da ta shiga uku ta lalace, number Godiya tayi dialing ta zauna gefen gado tana jiran tayi picking. Hawaye kawai Khaleesat take tana dafa shayin da Abdul ya sa ta dafo masa a kitchen, ita ta ma riga tayi give up yau don bata da wani dubaran da ya rage mata in ba so take ta fusata Abdul ya doketa ba, she will just accept her kadr with good faith, gwara tayi accepting dinsa kawai a mijinta tunda haka Allah ya kaddara mata, goge hawayenta tayi tana tafiya a hankali ta tafi kai masa lipton din dakinsa, tana bude kofar ya ajiye wayar hannunsa yana kallonta, kanta a kasa ta karasa har inda yake ta duka ta ajiye masa black tea din, ta mike zata bar wajen ya jawota ya zaunar da ita gefensa yana kallonta, ita dai bata bari sun hada ido ba zuciyarta na wani irin bugawa, ya dago kanta suka hada ido, sauke rigar baccin jikinta yayi slowly yana kallonta babu ko kiftawa, ta sunkuyar da kanta bugun zuciyarta ya tsananta sosai, tana ji tana gani ya cire duk abinda ke jikinta yana kare ma each and every part of her body kallo, bata sake yarda sun hada ido ba, a hankali ya kwantar da ita, ta runtse idonta da sauri jikinta na rawa ganin inda yake kokarin kai bakinsa, after some seconds Khaleesat ta bude idonta a hankali tana kallonsa jin bai yi abinda yayi niyya ba, taga wani wajen daban yake kallo babu ko kiftawa, after some seconds ta ga ya mike ya nufi kofa ya bude, fuska daure yake kallonta babu yabo babu fallasa yace "I need my privacy....." Khaleesat ta mike zaune da kyar tana kallonsa, lokaci daya jikinta yayi sanyi, ta jawo Hijab dinta da ya cire tun zuwansu gidan ta saka sannan ta dau kayan baccinta ta nufi kofa, bata bari ta hada ido da shi ba ta fita daga dakin taji ya kulle kofar da makulli, juyawa Khaleesat tayi tana kallon kofar.....

 

[6/20, 7:35 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Da Asuba Khaleesat na zaune kan gado ta dafe kanta da yayi mata nauyi sosai, tun karfe uku da rabi bacci ya kaurace mata, bayan tayi sallahn nafila ta kai ma Allah kukanta shine take ta zaune saman gado tana tunanin rayuwarta, in 3 weeks time za su yi resuming school wanda shekarar su na karshe kenan za su shiga a makarantar but unfortunately tasan baza a koma da ita ba, ko kadan bata saka ran zata koma John Hopkins ba dama, but it's really hurtful don duk shekarun da tayi a makaranta zai tashi a banza kenan, ta goge hawayen da ya gangaro mata jin ana kiran sallan asuba ta sauka daga saman gadon, sai da ta dafa bango sbda juya mata da kanta ke yi, tun da ta tashi daxu take jin jikinta kamar ba ita ba, she can't even understand how she is feeling, sai da ta koma ta zauna na yan mintuna sannan ta tashi tana tafiya slowly ta wuce bandaki, wanke bakinta tayi sannan ta dauro alwala ta fito daga bandakin, bayan ta idar da raka'atanil fajr tayi sallan asuba, har karfe bakwai na safe Khaleesat na zaune kan darduma duk da ta idar da azkar din ta, in tayi wannan tunanin tayi wancan a haka dai har ta mike daga karshe tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta bude ta fita daga dakin, bata karasa parlon ba ta tsaya tana kallon Abdul dake kwance saman 3 seater idonsa a lumshe yana sauraron karatun qur'ani ta wayarsa dake gefensa, duk tunaninta bacci yake ganin yanda ya lumshe ido, har zata juya ta koma dakinta taga ya bude ido yana kallonta, ta sauke idonta ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali ta duka kusa da shi cikin sanyin murya tace "Ina kwana" Yace "Lafiya" Bata sake cewa komai ba kanta a kasa, after some seconds ta mike zata bar wajen, calmly yace "I need breakfast, ban ci abinci da daddare ba" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma tace "Toh...." Juyawa tayi ta nufi kitchen don ganin me zata girka, doya da kwai tayi deciding tayi don shi tagani available a kitchen din, wajen karfe takwas ta gama komai ta kai har gabansa a parlon ta durkusa ta ajiye, ganin bread a kan dining table ta mike ta tafi ta dauko sannan ta dawo ta ajiye masa tana kallonsa a hankali tace "Gashi na gama, in hada maka shayin?" Without looking at her yana danna wayarsa daga kwancen da yake yace "Ohk" Hada shayin tayi bayan ta gama ta koma gefe tana kallonsa a hankali tace "Na gama" Ajiye wayarsa yayi ya sauko daga saman kujeran, shayin ya dauka yana sha, ba tare da ya kalleta ba yace "Ke ina naki shayin?" Shiru tayi bata ce komai ba, jin tayi shiru ya daga kai ya kalleta, sunkuyar da kanta tayi, sai kuma ta mike ta nufi kitchen, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo da cup da tea spoon, ta duka kasa ta fara hada shayin nata, ya kalli madaran da ta zuba a shayinta ya dau wani spoon ya kara mata madaran, ita dai bata bari sun hada ido ba, a plate daya ya dibar masu doyan ya fara ci, ita dai juya shayinta kawai take a hankali, after some minutes ganin bata fara cin doyan ba ya daga kai ya kalleta yace "Ko a baki za a baki?" Ta Ι—an yi murmushin karfin hali ta dau fork ta fara cin doyan a hankali, da ta kallesa sai su hada ido, kana ganinta kasan she is not comfortable a wajen don ya riga ya sa mata tsoronsa a zuciya, daga karshe ta ajiye fork din hannunta a kan tray, ya daga kai ya kalleta, a hankali tace "Na koshi" Bai ce mata komai ba, ta koma gefe tana shan shayinta slowly, after a while Abdul ya mike ya koma saman kujera, ta tashi ta dau sauran abincin ta kai kitchen, sai da ta wanke utensils da suka yi using sannan ta fito daga kitchen din, magana take son yi masa amma tana tsoro, ya kalleta tayi saurin sunkuyar da kai kamar munafuka tana wasa da yatsunta, yace "Me ya faru?" Ta karasa ta duka daga gefensa a hankali tace "Dama pls ina son zan yi magana da Safiyyah, ka taimaka ka kira min ita ta wayarka" A takaice yace "Bazan kirata ba, kanwar baabarki ce Safiyyar?" Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi, ta sunkuyar da kanta tayi shiru bata ce komai ba, yace "Tafi ki bani waje" A hankali ta mike a sanyaye ta wuce dakinta, goge hawayen da ya taru idonta tayi ta zauna gefen gado, after a while ta share hawayen da ya ki tsaya mata ta mike ta cire hijab din jikinta ta linke ta ajiye sannan ta shiga bandaki, brush tayi sannan tayi wanka, ganin abubuwan wanke gashi a bathroom din ta wanke gashinta ta tsane da karamin towel sannan ta dau wani towel din ta daura ta fito,  tana tsaye gaban madubi tana shafa man gashi taji an bude kofar dakin, da sauri ta juya gabanta ya fadi sosai ganinsa, kana ganinsa kasan daga wanka ya fito shi ma, cikin dubara ta gyara daurin towel dinta tana jin zuciyarta na bugawa ta ci gaba da oiling gashinta, ya karaso har inda take tsaye ya tsaya a bayanta yana kallonta ta madubi, ita dai ta kasa dago idonta tana jin saukan numfashinsa a bayanta, ta ajiye oil din hannunta a hankali don duk ta daburce, shi dai yana tsaye dab da ita yana kallonta ta madubi, ya kai hannu zai yi loosening din towel din kirjinta, juyowa take son yi da sauri kamar zata yi kuka cause bazata iya ganin kanta ta madubi a yanda yake ganinta ba, yaki barin ta juyo hakan yasa ta runtse idonta zuciyarta na bugawa, bai fasa kallonta ta madubin ba har ya cire towel din jikinta ya jefar saman gado, he kept his eyes glued to her cause he just can't stop admiring her bare body any time he set his eyes on her, gaba daya taki yarda ta bude idonta, bata ankara ba kawai sai jin su tayi a saman gado, bata san sanda ta bude ido ba ta fashe da kuka tana turasa a tsorace ganin yau kai tsaye kawai far mata yake kokarin yi babu bata lokaci, ita kanta bata san inda ta samu courage din turasa ba duk da tsoronsa da take, da mamaki yake kallonta yana sauke numfashi, ganin kiciniyar sauka take yi daga saman gadon tana kuka, cikin kakkausan murya yace "I will give u a dirty slap" Danneta yayi yanda ko motsin kirki bazata iya ba balle tace zata sauka daga saman gadon, ta dinga masa kururuwa tana kokarin kwatar kanta don bata taΙ“a tsorata ta gigice da lamarin nan ba irin yau, duk yanda Abdul ya so cimma burinsa a wnn moment din hakan ya faskara, kawai ya tuna ita ba irin matan da ya saba mu'amala dasu bane, he couldn't have his way no matter how hard he tried, he was so confuse as at how intact she is even though he knows she is a virgin, hakan yasa ya fara romancing dinta roughly to make his way more slickier, cause he was determined in fulfilling his mission today, wani wawan marin da yayi resetting dinta back to default ya sauketa mata don duk da yanda ya danneta she is still struggling so hard to free her self under him, Khaleesat taji kamar numfashinta na yi mata gardama, at this moment tasan babu me kwatar ta hannunsa sai Allah, she was so weak and in severe pain hakan bai hanata struggling ba cikin kuka take cewa "Don girman Allah ka rufa min asiri Abdul, wallahi mutuwa zan yi bazan iya ba, it's soo painful...." Ya kara sauke mata wani marin cause he is seriously trying to find his way by all means, Gaba daya Abdul komawa yayi kamar bai taΙ“a tarayya da mace ba a wnn lkcn, ya koma kamar Amateur da ta mance inda zai bi, duk wani dubaransa was fortile, he was really frustrated and vexed, Ganin how helpless she was ga numfashinta na neman daukewa ya rungumeta gam jikinsa yana kallon fuskarta da tafin hannunsa ya kwanta ta dalilin marin da yayi mata, lumshe ido yayi yana sauke numfashi kamar wanda yayi tsere, saukan hawayenta ya dinga ji a kirjinsa ya lumshe idonsa zuciyarsa na bugawa, after almost a minute yayi kasa da murya da kyar, yana shafa dogon gashinta yace "I am sorry Khaleesat, i am sorry" Ita dai hawaye kawai take tana sauke ajiyar zuciya, tana jin wani azaba in between her, they were like this for almost 5 mins, Abdul ya saketa ya koma can karshen gadon ya dafe kansa dake sara masa, ga wani azababben ciwon mara da yake ji, da kyar ya mike ya dafa bango na Ι—an lokaci kafin ya nufi kofa ya fice daga dakin, Khaleesat ta takure cikin duvet tana sauke ajiyar zuciya hawaye wasu na bin wani a idonta, bata san lkcn da baccin wahala ya dauketa ba a haka. Karfe sha biyu saura taji hannu a forehead dinta, bude idonta da suka kumbura tayi a hankali don sosai kanta yayi mata nauyi, suna hada ido ta sauke idonta, Calmly yace "Ta shi ki shirya mu tafi shopping" Da kyar ta mike zaune tana kara rufe jikinta da duvet, sai kuma ta fara jawo towel din da ya cire mata daxu, shi dai bai ce mata komai ba yana kallonta, har cikin ransa he felt bad ganin yatsunsa kwance a fuskarta, cikin dubara ta daura towel din sannan ta mike tsaye lkci daya ta duka kasa da sauri tana runtse ido, yana kallonta yace "What?" Lokaci daya hawaye ya idonta, cikin rawan murya tace "Bazan iya ba, zafi nake ji sosai" Ya hade rai yace "Zafin me?" Ta kasa kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "Me na maki da za ki ji zafi?" Ita dai bata dago kanta ba gabanta na faduwa, mikewa yayi ya fice daga dakin ta bi sa da kallo, after a while Khaleesat taji fitar motar sa a gidan, ba karamin daurewa Khaleesat tayi ba ta tafi bandaki, sai da tayi sit bath sosai sannan taji ta samu sukuni, tayi wanka ta dauro alwala ta fito. Karfe biyu saura tana tafiya a hankali tana dingishi ta fito parlor, ledan kayan da Momy ta bata ta gani a parlon, ta karasa ta bude ledan sai a sannan taga irin kayan da su Meemah suka siyo mata, a hankali ta daure ledan ta dau kayan walking slowly ta koma dakinta da su ta ajiye ta dawo parlon ta tafi kitchen don daura girki... Momy dake zaune parlor tana kallon Meemah da wani expression tace "Bacci fa kika ce Meemah??" Meemah ta ajiye gyalen jikinta tace "Wallahi kuwa Momy" Momy tace "To baccin me take wajen karfe sha dayan safe??" Meemah tace "In kin tambayeni in tambayi wa?" Momy ta gyara zama tace "Toh baki tafi dakin kin dubo ba?" Meemah tace "In lafiyarta qlau ai kinsan taso ta zai yi ta fito ta gaisheni barin ma da nace masa kin bani sako in bata, sai ce min yayi magani ta sha tana bacci" a hankali Momy tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Meemah tayi wani murmushi tace "Kinsan Allah Momy, kawai jikina ni tun asali ya bani ba lallai irin wannan asirin yayi tasiri lokaci daya ba, bance bazai yi tasiri ba amma sai ya gama moreta tukun, kin ga in rabo ya shiga kafin nan kuma ai mun shiga uku mun lalace, hada iri da talaka ya tabbata" a fusace Momy tace "Ke dai a rayuwarki baki taΙ“a furta alkhairi sai sharri Amina? Asirin kusan miliyan biyun kike ce min ba lallai yayi tasiri ba? Ko kina hauka ne?" Meemah tace "A'a ni bance bazai yi tasiri ba Momy, cewa nayi..." Momy ta dakatar da ita rai bace tace "Bana son ki sake saka min mugun bakin ki a lamarina, ki tashi ki ban waje kar in yi mummunan bata maki rai wallahii" Mikewa Meemah tayi ta kyabe baki tace "Shi Abdul din da duk mun san yanda idonsa ke kan mata ne kike tunanin zai bar yarinyar nan su kwana gida daya babu abinda ya shiga tsakaninsu?" Wani zagi Momy ta kunduma mata tace "Baza ki tafi ki ban waje ba, me mugun alkaba'i kawai, duk ba ke kika ja mana wannan bala'i ba?" Meemah na tabe baki tayi tafiyarta sama, Mikewa Momy tayi ta fara zaga parlor tana jin zufa na keto mata duk da Ac dake kunne, sai kuma ta dau wayarta ta wuce sama da sauri. Wajen karfe hudu da rabi Abdul ya dawo gida, Khaleesat ta idar da sallah tana zaune kan darduma ya shigo dakin ya ajiye shopping bags din hannunsa, ta mike a hankali tana kallonsa tace "Sannu da zuwa" Yace "Ki duba ko akwai abinda ba a siya ba" Tana kallon bags din ta karasa inda ya ajiyesu tana duba tsadaddun Abayan da ya siya mata kala kala, da takalma da handbags, irin dai quality din da yake siya mata a baya, duk wani abu da zata bukata sai da ya siyo mata, har da tsadaddun turaruka iri iri da man gashi, da na shafawa, kallon lube din da ta ciro a siyayyan ta dinga yi don at first tayi zaton na shafawa a fuska ne, sosai gabanta ya faΙ—i ta Ι—an kallesa taga kallonta yake, da sauri ta dauke kai zata ci gaba da ciro sauran abubuwan da ya siyo ya mika mata hannu alamar ta basa lubricant din, ta mika masa ba tare da ta bari sun hada ido ba, juyawa yayi ya dau ledan kayan da Meemah ta kawo daxu ya fitar da shi daga dakin, a hankali Khaleesat ta zauna gefen gado nan da nan hawaye ya cika idonta, bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba tana tuna azaban da ta sha daxu.

Wajen karfe takwas da rabi na dare Khaleesat ta gama dafa ma Abdul tea din da ya sa ta ta dafa masa, gaba daya tun daga sanda ya dawo har zuwa yanxu bata da sukuni a gidan, tana sanye da hijab ta karasa har inda yake zaune a dakinsa yana karatun Alqur'ani, ta durkusa ta ajiye masa shayin, zata mike ya jawota jikinsa bayan ya rufe qur'anin, yayi kissing goshinta yana kokarin cire mata hijab din har dai ya cire, lkci daya jikinta ya fara rawa tana son kwace kanta, Ζ™in saketa yayi ya riketa gam, tun tana ganin abun kamar wasa tunda a zaune yake, har sai da ta gansu saman gado ya rabata da komai na jikinta sannan idonta yayi clear, ihun da ta dinga masa tana kuka tana kokuwa da shi bai sa ya fasa abinda yake yi ba, upon yayi using lube da ya siyo amma kamar daxu yanxun ma dai bai iya yayi mata komai ba, after a while ya sake ta, fuskarsa a daure yace "Fita" Ta sauka kan gadon da sauri ta dau hijab dinta ta saka ta fice daga dakin jikinta na rawa, zaunawa yayi gefen gado ya rike kansa da yayi masa nauyi yana sara masa. Throughout washegari Abdul bai bi ta kanta ba a gidan, ta dai gaishesa da safe ya amsa babu yabo babu fallasa, amma hatta breakfast da tayi bai ci ba balle lunch, sosai taji guilty conscience na damunta don tana tsoron kamun Allah, tunda tayi karatun addini tasan kuma meye aure, amma yanxu ita kanta tasan ba intentionally bane taki basa hadin kai, kasa daurewa tayi wajen karfe uku na rana jiki a sanyaye ta samesa a parlor ta durkusa daga gefensa a hankali tace "Don Allah Ya Abdul kayi hakuri idan nayi maka laifi" Shiru tayi don ita kanta tasan she sounds stupid, Babu yabo babu fallasa yace "Laifin me?" Ta sauke idonta ta kasa cewa komai, Yace "Ohk kinsan ma abinca kike yi kenan" Ta girgiza masa kai da sauri, kallonta kawai yake don duk yau ji yayi kamar an dauke masa sha'awarta, unlike before da ko me zata yi feeling din nan nata dai na nan a ransa, kawai ji yayi baya ma son ganinta kawai, Calmly yace "Tashi ki bani waje" A hankali ta mike ta bar parlon. Da daddare bayan magrib yana kwance parlor ya kunna karatun Alkur'ani ta wayarsa yana saurare, tun da Khaleesat ta fito zata je daukan abinci a kitchen ya bi ta da kallo, har ta fito daga kitchen din ta wuce dakinta da abincin, ya mike zaune, after a while sai ga ta ta sake fitowa ta kai plate din kitchen, hijab ne har kasa a jikinta, still da ta fito haka ya bi ta da kallo, ita dai ta gefen ido kawai take kallonsa har ta koma dakinta, Bayan isha'i ya bude kofar dakinta, sosai ta tsorata ganinsa, suna hada ido ta sunkuyar da kanta don dama zaune take kan darduma ta idar da sallah, Yace "Make me a cup of tea" A hankali tace "Toh" Jiki a sanyaye ta tashi taje ta dafo masa tea din ta kai masa dakinsa, haka kawai gabanta ya dinga faduwa ganin kallon da yake mata, ta dai ajiye cup din tea din sannan ta fita ta koma dakinta ta kashe wuta ta kwanta ta shige cikin duvet, banda faduwa babu abinda gabanta yake yi, har ta fara bacci ta ji ana cire duvet din jikinta ta mike zaune a tsorace tana kallonsa kamar zata yi kuka don ya kunna dim light a dakin, yace "Nan wai wayo kika yi kika zo kika kwanta da wuri?" Sunkuyar da kanta tayi zuciyarta na bugawa bata ce masa komai ba, ya xauna gefenta ya jawota jikinsa a hankali, yayi kasa da murya yace "Kar ki manta you are my wife legally Khaleesat, why are you making everything seems hard for us both?" Kuka ta fara yi a hankali, yana magana kamar me rada yace "You just have to stay calm and relax plss, i promise i won't hurt you Khaleesat, the lube will help, jiya kin ki sakin jiki shi yasa bai yi ba" Khaleesat dai kukan tashin hankali kawai take bata ce masa komai ba tana kallon lube din da ya ajiye saman gado, kwantar da ita yayi taking off her nighty ya fara bi da ita gently kamar yanda yace, duk yanda Khaleesat ta saka ma ranta yau dai zata daure kawai tayi hakuri yayi abinda zai yi amma yana fara taΙ“ata ta fara masa kuka da karfi tana turjewa, tsabar feelings dinta da yake ji yau duk bai ma san tana yi ba, banda lallabata da bata hakuri babu abinda yake yi yana bi da ita a hankali, don burinsa kawai yayi accomplishing mission dinsa yau ya maida ta mace, amma me? even with the help of so much lube hakan yayi seeming impossible, magiya ya dinga yi mata kamar zai mata kuka yake rokonta she should let him pls don gani yake kawai don taki sakin jiki ne, sosai yake rokonta as if his life depend on what he is trying to do, ita banda kukan azaba babu abinda take tana kokarin kwace kanta tana turasa da duk sauran karfinta, mari ya sauke mata a fusace ya shakota yana huci yace "Is all this among ur plan??" Kasa magana tayi saboda shaΖ™eta da yayi da karfi, ya wani turata har sai da ta fadi kasan dakin, yana huci ya sauka daga saman gadon ya nufeta yace "Ni xaki raina ma hankali? Ni zaki dinga dauka for granted?" Cikin kuka tana komawa baya ta dinga cewa "Don girman Allah kayi hakuri, wallahi bani bace Ya Abdul, nima ban san me yasa haka ba" Ya dagota da karfi yana kallonta da idanuwansa da suka yi jajir yana wani irin numfashi yace "Saboda kin saka a ranki baki son aurena baki son zama da ni shi yasa baza ki bani hakkina ba?" Jikinta na rawa ta dinga girgiza masa kai tace "Wallahi a'a, don girman Allah kayi hakuri...." Wurgata yayi da karfi har sai da ta buga da bango, ya juya ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Ζ™asa motsi Khaleesat tayi tana ganin duk dakin na juya mata, yana fita dakin da minti goma taji fitar motarsa a gidan, kuka Khaleesat ta dinga yi sosai ko ina na jikinta na mata ciwo a dakin, ta fi awa daya kwance inda ya wurgata, ji take kamar bazata iya tashi ba ga azaban da take ji a Ζ™asanta, da kyar ta rarrafa zuwa bandaki daga karshe, bayan ta gyara jikinta ta fito ta kwanta nan kasan dakin tana kuka a hankali ga wani azababben ciwo da kanta yake mata, tashi zaune tayi ta jingina da gado tana tunanin what exactly will be the problem, don ita ta riga tayi give up din Abdul a matsayin mijinta, ko dai tana da wani ciwo ne da bata sani ba a wajen, if not ko yanda yayi using lube din nan should have been enough, to ko ce masa zata yi su je asibiti don ya dena zargin hanasa take yi, bazata so Allah ya kamata da laifin hana mijinta kanta ba, hawaye masu zafi suka dinga sauka idonta, she wish zai bata listening ears ya saurareta yasan she is not doing this purposely, sai wajen karfe daya da rabi na dare taji shigowar motar Abdul, gabanta ya dinga faduwa tana kwance kasan dakin har taji alamar ya shiga dakinsa, mikewa tayi da kyar ta saka hijab dinta tana dingishi ta fita daga dakinta, tsaye tayi tana kallon kofar dakinsa gabanta na faduwa don bata san me zai ce zai mata ba idan ta shiga dakin, daga karshe tayi shahada ta bude a hankali ta shiga gabanta na faduwa, wanka taji alamar yake yi a bandaki, ta dinga kallon wrist watch dinsa da wayoyinsa da sauran ledan Prophylactic dake ajiye gefen gadon, sosai jikinta yayi sanyi ta dinga kallon prophylactic din, taji hawaye masu zafi na sauka idonta, bayan few seconds ta juya a hankali ta fita daga dakin, wasu sabbin hawaye na sauka idonta ta koma dakinta ta kwanta saman gado tana shesshekan kuka.

[6/23, 2:54 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Wajen karfe bakwai Khaleesat ta fito daga dakinta tana tafiya a hankali, duk da zazzabin da ta tashi da shi yau haka nan ta daure ta fito,  tana hangosa kwance kan kujera yana danna wayarsa sai da gabanta ya fadi sosai, ta sauke kanta ta karasa har inda yake kwance ta durkusa cikin sanyin murya ta gaishesa, wayarsa kawai yake dannawa yaki kallon direction dinta balle ya amsa gaisuwarta fuskarsa a daure, bayan kusan minti daya ta mike jiki a sanyaye ta juya ta wuce kitchen, hawaye taji ya cika idonta ta kai hannu tana gogewa sannan ta fara preparing breakfast, bayan kusan minti arba'in ta fito daga kitchen din zata tambayesa ko ta kawo masa breakfast din yanxu duk da yanda gabanta ke faduwa, amma sai bata gansa a parlon ba, hakan yasa ta juya ta koma kitchen din ta dauko breakfast din ta kai dinning table ta ajiye, zata tafi dakinta kenan sai gashi ya fito daga nasa dakin har ya shirya alamar wanka yayi, tana kallonsa a hankali tace "Na gama preparing breakfast din" Banza yayi mata ya wuce ta, ta bi sa da kallo har ya shiga parlor, a sanyaye ta bude kofar dakinta ta shiga hawaye na taruwa idonta, ta zauna gefen gado tana goge hawayen a hankali, lamo tayi kan pillow tana shesshekan kuka, tunani iri iri ne ke mata yawo a rai, me ke faruwa da ita ne? Ko tana da wani ciwo ne da bata sani ba, who is she going to talk to about this? Hawaye taji na zubo mata sosai, how is she going to explain to Abdul that this isn't her fault? Ta yaya zata fahimtar da shi ya gane? Tafi awa daya kwance tana saΖ™e saΖ™e a ranta, a hankali ta mike zaune jin alamar fitar motarsa daga gidan, da kyar ta mike daga karshe ta tafi parlor tana tafiya a hankali, dinning area ta nufa ta duba taga bai taΙ“a komai ba a breakfast din da ta ajiye masa, ta juya a sanyaye ta koma parlor ta zauna ta jinginar da kanta da kujera hawaye na sauka idonta, after a while ta tashi da kyar ta fara gyara gidan sannan ta hada shayi ta dawo parlorn ta zauna amma ta kasa sha saboda damuwa, daga karshe kawai ta koma dakinta. Wajen karfe uku taji ya dawo gidan, ita dai tana ta zaune dakinta bata fita ba, bayan kusan minti biyar ya bude kofar dakin nata, kallo daya yayi mata yace "You have Visitors" Daga haka ya juya ya bar wajen, tayi jim tana tunanin su waye visitors din, mikewa tayi ta dau veil din Abayan dake jikinta ta rufe kanta sannan ta fito parlor tana tafiya a hankali, buda ido tayi ganin Aunty Farida da Nenne da step mothers dinta zaune a parlor, da gudu ta tafi ta fada kan Aunty Farida ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Nenne ta hade rai tana kara hakikancewa kan kujera tana kallon TV da aka kunna a parlon, Aunty Farida ta dago kan Khaleesat tana kallonta ganin yanda ta rame, a hankali tace "Ya kike Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Lafiya lau Aunty, Ummana fa? Me yasa baku zo da su Islam ba?" Aunty Farida tayi kasa da murya tace "Ke baki gaida su Nenne ba" Sai a sannan Khaleesat ta tuna da sauran mutanen parlon, zamowa Ζ™asa tayi a hankali tana kallon Nenne tace "Ina yini Nenne?" Nenne tace "Akan me zaki ce min ina wuni ni da nake er banza mara mutunci a idonki? Ita Faridar da kika makalewa kina shigewa jikinta da an biye ta tata da bata kashe auren nan har lahira ba? Da an biye ta Farida da Zahra'u idan kin ganki a wannan gida haka Allah ya tsine min albarka, to sai me don kin gan ni kin kauda kai kinyi kamar baki ganni ba da sauran matan ubanki? Ai babu komai" Khaleesat ta hade rai ta gaida su Mama Shatu dake zaune fuska duk babu walwala suka amsa mata babu yabo babu fallasa suna kare mata kallo, Nenne ta gyara zama cikin bacin rai tace "Banda matan ubanki da suka takura aje a san inda kike a ga halin da kike ciki sannan ni da na amshi sabon lambar Awdul wajen Farida nayi ta doka masa kira har yaje ya dauko mu ya kawo mu kin zata akwai wanda zaki gani a gidan nan ne? Ita farida Allah Allah take ta koma Legas ta ci gaba da tuwo tuwonta a can, uwarki kuma ba sanin ciwonki tayi ba balle ta samar mana hanyar zuwa ganin halin da kike ciki, amma me? haka nan albarkacin Ali nace dole dole sai naje naga halin da kike ciki, haka nan na uzura ma Awdul da kira yaje ya dauko mu, kuma Alhamdulillahi ga ki nan har wani haske kika kara alamar kina cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya da mijin ki, to meye zaki yi kamar baki taΙ“a sanin mu ba daga abun arziki dai" Mama Zubaida tace "To ai sai a zaga damu cikin gidan mu sa albarka tunda Allah bai yi mu za mu kawo amarya ba" Nenne tace "A'a, ba bin kwakkwafi da tsegumi ya kawo mu ba kaman en iska, tunda dai yarinya na cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya dama mu hakan ne kadai fatan mu, don haka babu me shiga mata ko ina a gidanta, in ma ce maku aka yi ku yi hakan don wata mugun manufa taku to baza ayi ba, don ni ban yarda da yanda ku ka dage sai an zo gidan Khaleesah ba tunda ni ba yarinya bace, dama kuma Ali yace ko minti sha biyar kar mu yi, da mun samu ganinta mu kamo hanya mu dawo tunda mu ba iyayen banza bane" Mikewa Khaleesat tayi ta tafi kitchen ta bude fridge ta dauko ruwa da drinks ta daura kan tray ta kai masu parlorn ta ajiye, ita dai Aunty Farida sai bin ta da kallo take don kana kallon fuskarta tasan akwai damuwa, gashi tana son kebewa suyi magana da ita amma tana gudun fitinar Nenne, Nenne na kallon Farida tace "Karfe nawa yanxu?" Farida tace "Uku da minti goma" Nenne na gyara mayafinta tana kallon Khaleesat tace "Toh kitchen za ki kai ni mu gana ko kuwa? in mun gama magana sai kije ki ce masa za mu koma ba zama muka zo yi masa ba" Aunty Farida ta dake ta mike tace "Kafin nan bari in Ι—an yi magana da ita Nenne" Nenne ta kalleta da sauri tace "Ai ba kashe aure ya kawo mu ba Farida, in baza kiyi mata magana a gabanmu gaba daya ba to ki rike maganar ki kawai don ba alkhairi bane, haka kawai baza ki ja yarinya ki keΙ“e da ita ki kitsa mata tsiya da salon kashe aurenta ba" Aunty Farida ta dinga kallon Nenne, Nenne ta mike tana rike da babban jakarta tana kallon Khaleesat tace "Kai ni kitchen din" Khaleesat taji kamar tayi kuka bayan Nenne ta hana Aunty Farida tayi mata magana, rai babu dadi ta nufi kitchen Nenne na biye da ita a baya bayan ta jaddada ma farida a kunne kar ta bari su Mama Zubaida su shiga ko ina na gidan, su Mama Shatu da Mama Zubaida sai tabe baki suke, Nenne ta tura kofar kitchen din bayan sun shiga, tana kare ma kitchen din kallo tace "Maa sha Allahu kai kaji waje sai kace daki uku a hade, kuma iya girki kawai ake yi a nan?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Nenne ta zauna kasan tiles din kitchen din ta zuge jakarta tana kallon Khaleesat tace "To kin tsaya min kerere a kai" Dukawa Khaleesat tayi a gabanta tana kallonta, Nenne ta fito da wasu kulle kulle har Ζ™ashi biyar, ta dinga kwancesu daya bayan daya cikin nutsuwa, murya can kasa tace "Kin ga wannan?" Khaleesat dai kallon kullin da Nenne ke nuna mata kawai take, Nenne na magana a hankali kamar tana tsoron wani ya ji tace "Cikin ruwan wanka zaki dinga diba kadan kadan kina zubawa kiyi wanka, duk wani mugun abu da mutum zai maki ko kuma yayi maki to da izinin Allah zai koma kansa da zuri'arsa, sharrin zai lalace na har abada, Wnn kuma a kunu zaki dinga zubawa ki sha kayanki ke kadai, wannan girki zaki dinga yi maku da shi gaba daya ku ci, ba wani mugun abu bane kawai saboda zaman lafiyanku da kwanciyar hankalin ku babu kuma Ι—an iskan da zai iya shiga tsakaninki da mijin ki, sai ki ga kanku ya hadu kuna ma juna nutsattsen soyayya bakwa son laifin juna, wnn na hayaki ne shima duk wani mugun abu idan an maki zai karye ya koma kan me shi da izinin Allah, da kyar aka tsam min wallahi, kin dai gansa Ι—an mitsitsi ko Ali ban dibar ma ba tunda naga bashi da yawa na kawo maki ba don halin ki ba, wannan na karshen shi kuma na sha ne da wanka, in kinyi wankan sai ki kada shi ko cikin ruwan shayi ne ki dinga shan abun ki" Ita dai Khaleesat tayi shiru tana ta kallon abubuwan da Nenne ke mata bayaninsu sinka sinka cikin nutsuwa, Nenne ta gyara zama fuskarta a daure tace "Wallahi in kika sa nayi asaran lokacina da en kudadena kika ki amfani da wannan abubuwan da na shiga kauyuka takanas na samo maki to in na maki Allah ya isa sai ya bi ki tunda ni ba baiwar buzuwar uwarki bace, duk ita ya kamata ta maki wannan abun amma gantalalliyar bazata yi ba, dama kuma sari nasan ke da ita bakwa amfani da duk wani abun taimako da nake baku, wani lkcn matsalarku ce ma ke shafan Ι—a na yayi ta wahala a duniya, to wannan in ma kinki yi wallahi kanki kika cuta don dangin Awdul ba mutanen arziki bane duk mun sani, kuma ba lallai su barki ki zauna lafiya a gidan mijin ki ba barin yanda suka dau Ζ™aran tsana suka dora ma ubanki saboda shi talaka ne, to ni dai gashi nan albarkacin ubanki na maki wannan wahala, haka nan na shiga wani kauye duk mayu na fito da kyar, to ya rage naki kiyi ko kar ki yi, in ma baki yi ba Allah ya isa" Khaleesat dake kallonta tace "Toh in ya gan su sai in gaya masa na menene su?" Nenne ta saki baki tana kallonta, a fusace tace "Ke dai sokuwa ce mahaukaciya, to uban wa yace maki a gabansa za ki yi? Yau naga bala'i, wannan wace irin shashashar yarinya ce? dama ba sai ya fita ba zaki yi maza kiyi duk abinda zaki yi kafin ya dawo? Ni da ban yi boko ba ma nafi ki hankali da wayo? wannan wace irin jaraba ce Zahra'u ta haifar ma Ali? To ki kwasa ki nuna masa tunda baki da seti" Khaleesat ta wani hade rai ta kauda kai, Nenne tayi kasa da murya tace "Ae sai ya fita duk zaki yi komai cikin sirri, yanxu boyewa zaki yi inda ko da wasa bazae gani ba" Khaleesat tace "Toh ae zae ji warin hayakin kuma, sannan ni bama ni da abun yin turaren wutan ai" Nenne tace "To dama ai shegen a gantale ya dauko ki bai bari duk mun shirya maki turaren wuta ba da sauran abubuwan da ake kai mata da su gidan miji, yanxu dai nasan shi zai maida mu gida ina da manyan robobin turaren wuta har biyu da na ajiye maki zan basa turaren da kasko ince ya tsaya gun masu siyar da gawayi a bakin hanya ya siya maki ko leda uku ne ya taho maki da shi, sai ki dinga hurawa a kaskon tunda ga AC a parlon nan da nan zai kama maki in kika hura" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba, Nenne tace "To shikenan ki maida ni mahaukaciya ina kokarin taimakon rayuwarki" Khaleesat tace "Na ji" Nenne tace "Yauwa to, yanxu gasu nan maza ki je ki boye inda bazai gan su ba kwata kwata" Khaleesat ta amsa ta nemi waje a nan kitchen din ta boye, Nenne tace "Yauwa to haka ake yi, yanxu maza tafi ki ce masa zamu tafi kar ya ga mun zaune masa a gida, dama ni wnn abubuwan yasa nayi ta doka masa kira yau kwana uku kenan, har Allah yayi ya zo ya dauke mu" Mikewa Khaleesat tayi ta fita daga kitchen din Nenne na biye da ita murya can kasa tace "Ko ruwan gidansa mu dai bamu sha ba balle yace" Khaleesat na tafiya a hankali ta nufi dakin Abdul, knocking tayi tana jiran ya amsa, after almost a minute ya bude kofar, ta sunkuyar da kanta tace "Za su tafi" juyawa yayi ya koma dakinsa, hakan yasa ta dawo parlor, Nenne na kallonta tace "Kin gaya masa?" Kai ta gyada mata ta tafi kusa da Aunty Farida ta zauna a kasa, Su Mama Shatu kana ganin fuskokinsu kaga bakin ciki da hasadda karara a kwance, bayan kusan minti biyar Abdul ya fito daga dakinsa yana murmushi yace "Har za ku koma Kaka?" Nenne tace "Wallahi kuwa Awdul, ai dama ba zama za mu yi ba, ni dai nayi farin cikin ganin jikata cikin kwanciyar hankali dama duk haka muke so" Shi dai bai ce komai ba, Nenne ta mike tace "Don haka yanxu sai ka maida mu gida kawai" Abdul yace "Toh naga ko abinci bata baku ba ai" Nenne tace "A'a mu muka hanata don duk a koshe mu ke, ruwan ma in ka lura ai bamu sha ba" Shi dai murmushi kawai yayi, a haka Nenne ta kada keyarsu Mama Zubaida da Mama Shatu suka fita daga parlon, Ita dai Khaleesat na biye da su duk jikinta a sanyaye, Aunty Farida ce last din fita a parlorn, tana kallon Khaleesat tayi kasa da murya tace "Za ki ga sako na ajiye maki bayan throw pillow din kujeran da na zauna, kar ki damu kafin in koma lagos zan samu lokaci in zo ni kadai kin ji?" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Bayan Abdul ya bude motarsa ya kalli Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi ganin su Aunty Farida za su tafi, yace "Mu je sai mu yi dropping din su mu dawo" Nenne dake kokarin shiga bayan mota ta dakata tace "Toh ai babu waje a motar, a ina zaka dora ta Awdul?" Aunty Farida tace "Sai ta shiga gaban motar Nenne ni in koma baya" Nenne tace "A'a babu ruwana wallahi, a irin narka narkan jiki na Shatu da Zubaida mu uku ma ya muka kare a baya balle kin shigo cikinmu Farida? Ko dai a cinyar su zasu dora ki?" Shi dai Abdul murmushi kawai yayi, Khaleesat tace "Toh ni sai in zauna a bayan" A fusace Nenne tace "To ke dole sai kin bi mu ne kamar en matan amare? Kawai don na zo gidanki sai in koma gida da ciwon jiki? ni wallahi in da matsi a mota ma bana shiga, da mun sani da bamu taho da Zubaida ba don duk ita ta cika waje..." Abdul ya kalli Khaleesat yace "Don't worry, ki koma ciki kawai" Hawaye ne ya cika idonta tana kallonsa, Aunty Farida ta yi ma Nenne wani kallo ta shige gaban motar, Nenne ta kyabe baki ta shiga bayan motar tana hararansu Zubaida da su ma duk suka shiga motar kuma babu warce tayi gigin gogan jikin Nenne a cikin motar, Nenne tace "To duk ku sauka Khaleesah ta fara shigowa ta dawo kusa da ni tunda ba wani auki gareta ba, ku ne abun tsoron dama" Babu musu duk suka sake sauka daga motar suka koma gefe, Nenne na kallon Khaleesat tace "Ba sai kin yi kuka ba, shigo ki matso kusa da ni mu ga adadin wajen da zai rage, in ya kama wata sai ta hau adaidaita sahu" Khaleesat ta goge idonta ta karasa ta shiga cikin motar ta matsa kusa da Nenne, space din da ya rage a motar tsaf zai dauke su Mama Zubaida, Nenne ta tabe baki tayi kasa da murya tace "Duk fa wari suke, in Farida ta shigo nan ai jikina za su rakube in ta shakan wari su cuce ni, in de ba kusa dani Faridan zata dawo ba, kuma Zubaida duk ta fi warin, banda akwai turare da AC a motarsa ai da mun ji kunya" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba su Mama Zubaida suka shigo motar Nenne na yatsine yatsine, a haka suka bar gidan. Sai kusan karfe biyar suka isa Mariri, bayan Abdul yayi parking dai dai kofar gidansu Khaleesat Nenne ta bude motar ta sauka tare da Khaleesat, su Mama Zubaida ma duk suka sauka da Aunty Farida suna ma Abdul godiya sannan suka shiga cikin gida, Nenne na gyara gyalenta tace "To Allah yayi maka albarka Awdul mun gode, amma dai zan yi maza in karasa gida akwai sakon Khaleesat da zan dauko in bata tunda Allah ya kawo ku ta tafi da kayanta kawai" Yana zaune driver seat ba tare da ya juya ba yace "Toh Kaka" Tana kallon Khaleesat tace "Mu je ki taho da sakon" Khaleesat bata ce komai ba ta fara bin Nenne zuwa gidanta, bayan sun yi nisa Nenne tace "Ai kinga shegen bai ce bari ya karasa gidan nawa da mu a motar ba, gaba daya baya ganin mutuncin gidana dama" Ita dai Khaleesat tayi kamar bata ji me tace ba, har suka isa gidan Nenne Khaleesat na gaisawa da mutanen anguwan, Nenne tace "Munafukai, sun yi mamakin ganin ki haka ai, kinsan duk ca aka yi kin shiga duniya kin gudu, sai daga baya kuma aka ji kina gidan mijin ki" Murmushi kawai Khaleesat tayi, bayan sun shiga gidan Nenne ta dauko turaren wutan ta saka su a katon leda da kasko biyu sannan suka fito, suna isa kofar gidansu Khaleesat Nenne ta saka ledan a bayan motar Abdul tana cewa "Kaga har mun dawo Awdul, dama turaren wutan ne ba wani abu ba, don haka ku yi maza ku tafi kar Magariba ya tarar da ku a hanya" Yace "To Kaka" Khaleesat na kallonsa tace "Zan shiga in gaida Ummata" Bata jira cewarsa ba ta shiga cikin gidansu ya bi ta da kallo, ko minti uku bata yi da shiga dakin Ummanta ba sai ga Nenne, tana tsaye bakin kofar dakin bayan ta dage labule tace "Abun kuma ba hauka bane ai, taso ki fita yana jiran ki..." Khaleesat ta daga kai tana kallon Nenne, Nenne tace "Ae sai yayi mana kallon mutanen banza marasu hankali, taso nace ki fita kar ki ja mana reni" Umma na kallon Khaleesat tace "Ku je Khaleesat, kin ga yamma tayi" Fuska a daure Khaleesat ta mike ta fita daga dakin, Nenne ta rakata har bakin motar Abdul, tana shiga gaban motar yayi ma Nenne sallama ya ja motarsa ya bar wajen, har suka isa gida ana kiraye kirayen magrib bai ce mata ba, ita ma bata ce masa komai ba, bayan yayi parking ya sauka motar ita ma ta sauka, tana tafiya a hankali ta bi bayansa suka shiga gidan, Kitchen ya shiga direct, har zata wuce dakinta ta tuna sakon da Aunty Farida tace ta bar mata kan kujera, ta karasa inda Aunty Farida ta zauna ta dauke throw pillow din wajen ta dinga kallon Dollars din dake ajiye da wayoyi biyu, daukan 1000 dollars din tayi wanda Jay ne ya bata da zata dawo Nigeria, ta dau wayoyin biyu, daya na Ajay daya na Jay, lkci daya jikinta yayi sanyi hawaye suka cika idonta, muryar Abdul taji a kanta yace "What's that?" Da sauri ta boye hannunta a baya tana kallonsa tsabar yanda ta gigice.

[6/24, 6:29 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Abdul ya zagayowa ya tsaya gabanta yana kallonta ya mika mata hannu yace "Give me what you are hiding" Sosai gabanta ya fadi tana kallonsa ta kasa cewa komai, tsawan da ya gigitata ya daka mata yana mata wani kallo, lkci daya hawaye ya cika idonta ta mika masa wayoyin da kudin hannunta, amsan su yayi yana kallon su, ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa, Calmly yace "Who gave you this?" Kasa dago kanta tayi hawaye na zuba idonta tana jiran jin saukan mari at anytime, juyawa yayi ya bar wajen ya nufi dakinsa yana rike da wayar da dollars din, Khaleesat ta bi sa da kallo har ya shiga dakin, taji kafafuwanta sun kasa daukanta tsabar yanda ta tsorata, da kyar ta karasa ta zauna gefen kujera tana jin bugun zuciyarta na karuwa, tana goge hawayen dake sauka idonta.... Abdul na shiga dakinsa ya zauna gefen gado ya ajiye dollars din yana jujjuya wayoyin hannunsa ganin iri daya ne with different colors, kuma duk a mace suke babu caji, Exactly irin second phone din da yake using ne, ya mike ya tafi yayi plugging din wayar Jay da chargern sa, sannan ya koma ya dau kudaden ya kiraga yaga 1k dollar ne, ya ajiye su saman gadon yana kallonsu, jin za a tada sallah a masallaci ya shiga bathroom dinsa, bayan ya fito zai tafi masallaci ya kulle Bedroom din nasa da makulli, har sannan Khaleesat na zaune parlor ta kasa motsi a inda take zaune, tana ganinsa ta mike tsaye a tsorace tana kallonsa, ko kallonta bai yi ba ya nufi kofa ya fita daga parlon, a sanyaye ta tafi dakinta hawaye na sauka idonta zata je tayi alwala ita ma. Abdul na dawowa masallaci bayan ya bude dakinsa ya shiga ya dau wayar Jay ganin har yayi caji ya kunna kansa, ya cire wayar jikin chargern ya dauko wayar Ajay ya jona, sannan ya koma gefen gado yana duba wayar tunda babu lock jiki, gani yayi ba Sim card a wayar, ya dai ci gaba da dube dubensa, babu inda bai shiga ba a cikin wayar yana bincike but bai ga komai ba don babu any form of Media a wayar, messages ma ko daya bai gani ba, bayan ya shiga Email yaga Business class flight ticket da Jay ya siya mata da zata dawo Nigeria, ya dinga kallon Ticket din for almost 30 seconds, sosai fa yayi mamaki ba kadan ba, fita yayi daga Email din ya shiga Gallery din wayar hoping zai samu hoto a ciki, a nan ne ya ga Hotunan Jay, wanda duk yawanci tare zaka gansu da Ajay, Zooming pic din Jay yayi yana kallonsa with full concentration, sai kuma ya koma kan Ajay shi ma ya dinga kallonsa baya ko kiftawa, at once ya gane da shi ne suka samu Encounter a Amurka, but sai ya ga Ajay looks familiar, where did he know him from? mikewa yayi da sauri ya dauko wayarsa ya shiga Instagram dinsa yayi Searching sunan da yake tunanin ya san sa da shi a Instagram, amma sai yaga account dinsa is locked, komawa yayi ya zauna ya kasa dena kallon hoton Ajay babu ko kiftawa, can ya kara duba hoton Jay yayi Zooming dinsa yana kallo, kawai bai san me yasa yaji yafi jin tsanar Jay ma akan Ajay, mikewa yayi ya dauko wayar Ajay don har ya Ι—an yi caji, babu lock a wayar hakan ya sa ya shiga, nan yaga Ticket da aka siya mata from Kano to Lagos, iya shi kadai ya gani a wayar babu hotuna, babu WhatsApp, babu komai, hatta sim card babu a wayar, fita yayi daga dakinsa ya tafi dakin Khaleesat ya sameta tana sallah, tun da taga yanda ya tsaya mata a bakin kofa taki idar da sallan da take yi da wuri kamar me Tuhajjud, muryarsa taji cikin tsawa yace "Idan baki sallame sallan nan da kike yi continuously ba zaki ga abinda zai faru yanxu" Sosai jikinta yayi sanyi, haka nan ta daure ta sallame sallan tana ji kamar bango ya tsage ta fice daga dakin tsabar tsoronsa, duk da yanda gabanta ke faduwa haka ta hade rai taki kallon direction dinsa barin da ta ga both wayar Jay da Ajay a hannunsa, ya karaso cikin dakin yana mata wani kallo cikin daga murya yace "Wayoyin su wanene wannan??" Still taki kallonsa, wani tsawa yayi mata yace "Are you stupid? Are you Mad? Ina maki magana kina kallon wani direction din daban?" Sai a sannan ta kallesa, har sannan fuskarta a daure yak, amma Allah ya gani daurewa kawai take, yace "I am asking you whose phones are this?" A takaice tace "My Housemate and his Brother....." Ya dinga kallonta babu ko kiftawa, she just realized she said her Housemate to him, ta kallesa a sanyaye, ganin kallonta yake yi baya ko kiftawa, ta sauke idonta a hankali tace "I mean...." Ya girgiza kai yace "No, you mean ur Housemate, dama Housemate dinki ne ranan da na je kika min karya? Dama gida daya ku ke tare da wannan katon banzan da na gani?" Gani tayi shiru fa ba nata bane, don shirun nata duka kawai zai ja mata, in ma maganar tayi ba hakan zai hana ya doketa ba in yayi niyya, ta wani hade rai duk da mugun faduwan da gabanta ke yi, a takaice tace "Eh, he is my Housemate, Nancy moved out of the apartment shi ne shi ya shigo, and i have no choice but to live with him, tunda bana son in dinga bothering dinka da Expenses, kuma naga in just few months za mu yi hutu, dama nufina idan mun yi hutu sai in ce maka ka canza min wani apartment din since a sannan ne zaka yi renewing house rent dina" Kallonta kawai Abdul yake yi babu ko kiftawa, ita dai ta kasa kallonsa gabanta na faduwa tana expecting ta ji saukan mari at anytime a cheek dinta, Calmly yace "So, shi ne kike zaune gida daya da shi ku ke rayuwa, ku yi sharing same kitchen, same parlor and same corridor, if coincidentally kin fito daki shi ma ya fito sai ku kusa karo da juna ko? Ki fito babu hijab ya gan ki haka, ki fesa turare ki zo ki wucesa yana jin kamshi, in ma ya kama ki zauna ku yi hira da shi, in kinyi girki ya diba ya ci" Sai a sannan Khaleesat ta kallesa tace "I don't mind if you believe me or not... But shi baya kwana gidan, karatu kawai yake zuwa yi ya tafi don suna da gidansu a Amurka" Abdul ya dinga kallonta, sai a sannan ya tuna abubuwa masu tsadan da ya dinga gani a kitchen sanda yaje, tun daga kan bottle water, cikin nutsuwa yace "Shi ne dalilin da ya sa kika fara min wasu stupid attitude kenan? Kin samu wanda yake siya maki duk abinda kike so a gidan har ma ya Ι—ebe maki kewa, To bari ki ji, ko duk jikina kunnuwa ne bazan taΙ“a yarda babu wani intimacy da ya hada ki da shi, ke kika san me kike basa da yasa yake siya maki abubuwa masu tsada yake ajiye maki a kitchen, sannan har ya cire kusan 5000 dollars ya siya maki Business class ticket kawai don ki dawo Nigeria...." Nan da nan hawaye ya cika idon Khaleesat, ta mike tsaye tana kallonsa tace "Ko me zaka fada bazan ce maka ba haka bane, amma put this at the back of ur mind, ba kowa ke da halin son taΙ“a warce ba muharramarsa ba kamar ka, kuma shi bai dau kudin Business class ticket wata tsiya ba shi yasa ya siya min, akwai difference sosai between you and him" Kallonta Abdul ya dinga yi da mugun mamaki, bata ankara ba sai jin saukan tagwayen mari tayi a fuskarta, ta fashe da kuka tace "Iya mari kawai?? ka kasheni mana ka huta kawai Abdul...." Ya fizgota da karfi yana huci yana kallonta da idanuwansa da suka yi jajir yace "Ni kike comparing da wani Ι—an iska matsiyaci can??" Cikin kuka tace "May be if i do that you will change ur terrible ways, he made me realize i am dating a monster because of his kind attitude toward me, babu komai tsakanina da shi amma shi din mutum ne me kirki da sanin darajan Ι—an Adam da sanin ya kamata, he always make sure i am fine, baya barina da damuwa komin kankantar sa, kuma ko da kuskure bai taΙ“a saΙ“a min ba a duk zaman mu da shi a America, kyawawan halayyarsa da irin yanda yake interacting yasa naji i am fed up with ur attitude, all this made me realize you are enslaving me ba sona kake ba, why not treat me the way he is treating me idan har sona kake da gaske? Bani da daraja da mutunci a idon ka, kullum cikin duka da cin mutunci nake a wajenka tun sanda baka aureni ba, iyayena ma basu da mutunci a wajen ka, to menene yasa baza kayi releasing dina zuwa inda za a ga mutuncina da na iyayena ba kuma a san darajata? Is it my father's fault da kaddarar sa ta zo a yanda take? Ku kan ku kun san bai ci kudin mahaifinka ba, bai salwantar masa da kayansa don son rai ba, ba ku tunanin ko ba ta sanadin mahaifina ba sai kun yi asaran kudaden nan tunda ku ma a kaddarar ku hakan take? Kuma meye zaka  daga min hankali a kan su bayan kace baza ka sakeni ba kuma kowa yasan igiyar auren nan a hannun ka yake? Duk cikin rashin lissafin naka ne yasa kake kishi da su bayan ka ri ga ka aureni??" Turata yayi har sai da ta bugu sosai da bango sannan ya juya ya fice daga dakin kamar zai tashi sama. Wajen karfe dayan dare Khaleesat dake kwance taji an bude kofar dakinta, da kyar ta bude idonta da yayi mata nauyi tsabar kuka da ciwon kai, tana ta kwance a yanda take bata juya ba duk da bata ga ya kunna wutan dakin ba, duvet din jikinta ya sauke kasa ya jawota kusa da shi yayi kasa da murya yace "Kinsan da igiyata a kanki kike da effrontery din kawo min maganar wani katon banza can har kike comparing dinsa da ni? What wrong have i commit to you da kike ganin shi yana da halayya masu kyau wanda ni bani da shi" Khaleesat taji zuciyarta na mata wani zafi jin useless question din da yake tambayarta, tayi kamar bacci take taki motsawa, yayi kasa da murya yace "Khaleesat..." Still tayi kamar bata jin sa, duk da idonta a rufe yake she could feel the tears accumulating in her eyes, kiranta ya sake yi a hankali jin bata amsa masa ba ya juyota zuwa jikinsa yana kallonta cikin duhun, ya dora goshinsa kan nata yayi kasa da murya yace "But you know i love you so much Khaleesat, da bana son ki bazan yi wasting shekaru kusan biyar a kanki ba, i gave you the best of everything i can kema kin sani" Bata san sanda ta turasa ba tsabar wani tsanarsa da take ji a rai jin abinda yake cewa, ta mike zaune muryarta na rawa tace "Duk saboda kana sona kake dukana kake marina kamar jaka? Shi ma duk cikin so ne? Plss ka koma ka fahimci menene kalmar so...." Sauka ta fara kokarin yi daga kan gadon tana shesshekan kuka, ya rikota da sauri yaki barinta ta sauka, ta fashe da matsanancin kuka sosai tana jin zuciyarta na mata zafi saboda bakin ciki, ya rungumeta gam a jikinsa, a hankali yace "Kiyi hakuri, amma Allah ya sani ina son ki, in ma baki yarda ba i owe you no explanation tunda Allah shi ya sani, kuma today should be ur first and last warning Khaleesat.... I mean in ur life do not ever ever dare compare me with any stupid guy born of a woman, kar ki sake kawo min zancen wani Ι—an iska ko shi wanene a kunne na, sannan bazan yi taking zaman da ku ka yi tare da shi and whosoever da kuma alakar ku personal ba because you are my wife now, duk wannan ya zama pass and shi ne looser, kuma har abada babu wata alaΖ™a da zai sake hada ki da shi don ubansa har duniya ta nade kuwa, ba wai ban ji zafin alakar da kika yi creating da su a America bane a raina, fadin zafin da naji ma is just an understatement wallahi, amma considering the fact that you are my wife yasa nayi letting bygone to be bygone, so let me keep using that to calm my self kar in masu abinda ke raina...." Wani mugun tsanarsa ne ke karuwa a ran Khaleesat jin kalmomin da ke fitowa bakinsa, wasu hawaye masu zafi suka dinga sauka idonta tana tausayin kanta da irin monster din da Allah ya bata as miji, kokarin kwace kanta take yi a jikinsa zata sauka daga kan gadon yaki saketa yace "Ohk bokare min za kiyi don ina baki hakuri? But i said i am sorry, and i promise i won't hurt you again, na dena dukan ki...." Ƙin ce masa komai tayi tana kuka a hankali, ya kwantar da ita kirjinsa yana shafa gashinta a hankali yace "Billah ina son ki Khaleesat, duk abinda kika ga ina maki saboda ina son ki ne, but kin ki bani hakkina saboda ke akwai wani plan din a xuciyarki, probably ma su suka koya maki haka" Daga kai Khaleesat tayi ta kallesa tsabar bakin ciki bata san sanda tace "Ai ba kowa ne bashi da aikin yi kamar ka ba" Shiru yayi yana kallonta babu ko kiftawa, ita kanta shirun tayi gabanta na faduwa don bata san sanda kalman ya fito bakinta ba, Instead sai ji tayi yayi kasa da murya kamar me rada yace "Where is the Lubricant?" Sosai gabanta ya fadi jin abinda yace, yana rungume da ita jikinsa ya bude bedside drawer kamar yasan nan din ta ajiye kuwa, ya laluba ya dauko, shesshekan kuka ta fara yi zuciyarta na bugawa, yayi kasa da murya yace "Kinsan tsinuwar Allah kike tara ma kanki kuwa?" Cikin kuka tace "To ai ba ni bace" Yace "To waye?" Muryarta na rawa tace "Wallahi ban sani ba" Cikin kwantar da murya yace "Promise me today will be different plss Baby" Ta kasa cewa komai hawaye masu zafi na sauka idonta ga faduwan da gabanta yake yi, gently ya fara cire kayan baccin jikinta yana kallon kwayar idonta cikin duhun dakin, a wannan dare Abdul bai yi bacci ba tsabar bacin rai, sai dai bai hantareta ba bai zageta ba, bai kuma doketa ba, haka ya mike ya fice kawai ya bar mata dakinta ya koma nasa, ya shiga bandaki ya sakar ma kansa ruwan sanyi duk da mugun sanyin da ake a garin, bayan ya fito ya saka Pajamas dinsa ya kunna karatun qur'ani a wayarsa ya kwanta amma ko rintsawa bai yi ba har asuba. Tunda Khaleesat ta idar da sallan asuba take zaune kan darduma bayan ta gama azkar dinta, gaba daya jikinta a sanyaye yake, zuwa yanxu kam sosai lamarin nan ya fara bata tsoro, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya tsabar yanda abun ya tsaya mata a rai, kawai tayi deciding tayi amfani da abubuwan da Nenne ta kawo mata zuwa anjima, sai da gari ya waye sosai sannan ta mike tana tafiya a hankali ta fita daga dakin zuwa parlor, sosai gabanta ya fadi ganinsa zaune a parlon da cup din shayi a gabansa, ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa ta tafi ta durkusa Ι—an nesa da shi a hankali tace "Ina kwana" Maimakon ya amsa sai ji tayi yace "Meye nake perceiving a cikin kitchen kamar maganin gargajiya?" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, shi ma kallonta yake fuskarsa babu yabo babu fallasa, rasa me zata ce masa tayi tana wasa da fingers dinta, a fusace yace "Bakya ji na ne?" Bakinta na rawa da kyar tace "Nenne ce ta kawo min" A takaice yace "Na menene?" Ta sauke idonta tace "Magani ne kawai, dama ta saba bani in dinga amfani da shi a gida" Mikewa yayi yace "Mu je ki bani su" Ta shi tayi kamar munafuka ta nufi kitchen din ya bi bayanta, ita kanta taji kamshin itatuwan da ta shiga kitchen din, ta bude inda ta ajiyesu ta dauko, ya mika hannu, ta karasa ta basa, yace "Ba a min amfani da irin wa ennan abubuwan a gida" Kai kawai ta gyada masa, fuska daure yace "Kin ji me nace maki? Kar ki sake amsa idan ta baki" A hankali tace "Na ji" Juyawa yayi ya fice daga kitchen din ya koma parlor ya zauna, ya ajiyesu nan kasan tiles, tana fitowa daga kitchen yace "Get ready za mu fita, kuma kar ki bata min lokaci" Cikin sanyin murya tace "Toh" Dakinta ta tafi, bayan kusan minti talatin sai ga ta ta fito cikin shiri, dai dai nan shi ma ya fito daga dakinsa rike da wayarsa da car key, yana gaba tana biye da shi suka shigo parlor, ya dau ledan magungunan da Nenne ta kawo mata ya nufi kofar fita daga parlon ita dai tana biye da shi a baya, a booth dinsa ya saka ledan magungunan, sannan ya zaga zuwa driver seat, ita ma ta shiga front seat, bayan ya gama warming motar ya fita daga gidan. A sanyaye Khaleesat ta fito daga Office din Dr Mariya with different thoughts running her mind, ta Ι—an juya ta kalli Abdul da ke bayanta shi ma ya fito office din likitan, Ζ™in kallonta yayi, hakan ya sa ta ci gaba da tafiyarta slowly, sai ga Dr Mariya ita ma ta fito daga Office din zata masu rakiya zuwa parking space, hira suke yi kawai da Abdul suna tafiya a tare, ita dai Khaleesat na can gabansu, har dai suka fita daga reception din hospital din suka karasa parking space, Dr Mariya na kallonta tana murmushi tace "To amarya plss inji labari opposite of this kin ji? There is nothing wrong with you, In kinyi amfani da duk shawararin da na baki komai zai tafi dai dai in sha Allahu, hakuri kawai za ki yi it's always like that dama, Allah Ubangiji ya bada zaman lafiya, in dai na samu lokaci zan zo har gida mu gaisa" a hankali Khaleesat tace "To Nagode Aunty, Allah ya kawo ki lafiya" Dr Mariya na murmushi tace "Ameen" Sai kuma ta kalli Abdul tace "To Barrister ku gaida gida, ina kuma tabbatar maka in sha Allah matsalar ta zo karshe tunda kaga mun dade ina magana da ita, kuma hopefully ta dau duk abinda nace mata" Yace "Thanks for your time Dr" Zagawa yayi ya shiga driver seat, Khaleesat kuma ta shiga front seat, ya tada motar suka bar hospital din, har suka yi nisa bai ce mata komai ba, ita ma dae shiru tayi tana ta tunane tunane, sae da taga unguwan da suka shigo tayi realizing gidansu ya kawosu, bayan yayi parking ya sauka motar, ita ma ta sauka, booth ya tafi ya bude ya ciro ledan da Nenne ta kawo mata, da mamaki tana kallonsa tace "Ina zaka kai wannan?" A takaice yace "Momy zan kai ma, naga tana dealing da irin abubuwan nan, she can use it if she want, ke dai baza kiyi amfani da su ba a gidana" Khaleesat ta marairaice masa tace "Noo pls, ni dai gwara kayi disposing dinsu don Allah" Fuska daure yace "Bazan yi disposing din su ba" Bata san dama haushinta ne fal zuciyarsa ba bayan Dr Mariya ta dubata ta tabbatar masa lafiyarta qlau babu wani abu da yake hindering passage dinsa, everything is normal, kawai hadin kai taki basa, Khaleesat ta sunkuyar da kai a sanyaye bata sake cewa komai ba, ya nufi entrance din gidan nasu, tana tafiya a hankali ta bi bayansa har suka shiga parlorn gidan, da mamaki Momy ke kallonsu tace "A'a, daga ina ku ke da safen nan, sannun ku da zuwa" Abdul ya zauna ya gaisheta, ta amsa tana kallon Khaleesat da ta zauna kasan carpet tana gaisheta, Momy ta amsa da fara'a sosai fuskarta tana welcoming dinta, Momy na kallon Abdul tace "Amma ba daga gida ku ke ba ko" Yace "Eh, daga asibiti mu ke" Da mamaki Momy tace "Asibiti kuma, waye ba lafiya?" A takaice yace "Bata ji dadi bane, amma da sauki" Momy na kallon Khaleesat tana murmushin karfin hali tace "Allah sarki, sannu Mamana, Allah ya kara lafiya" Sai kuma ta kalli Abdul tace "Ko wajen Dr Mariya ku ka je?" Yace "Eh" Mikewa yayi ya ajiye mata ledan magungunan kusa da ita yace "Kakarta ce ta kawo mata wnn jiya, ni kuma kin san bana son irin abubuwan nan na gargajiya shi ne na kawo ko zaki yi amfani da su ke" Momy tayi kuri da ido tana kallon ledan da mamaki, sai kuma ta dauka ta bude da sauri, lkci daya ta saita kanta tana murmushin karfin hali tace "Allah sarki, ai kam nasan halin ka baka san itatuwa, zan ko yi amfani da su dama nawa sun kare tas" Ita dai Khaleesat kasa dago kanta tayi, Momy was shock har cikin ranta amma tayi karfin hali take wayancewa, can ta kalli Khaleesat tace "Amma baki fara amfani da su ba ko" Khaleesat ta girgiza kai ba tare da ta kalli Momy ba tace "A'a jiya ta kawo min banyi amfani da komai ba" Momy tace "To to, hakan yayi" Ta kalli Abdul tace "In dai an samu wasu a dinga kawo min kawai" Mikewa yayi yace "Za mu koma Momy" Momy tace "Da wuri haka? To wai ka koma aiki ne?" Yace "Ban koma ba tukun" Momy tace "Toh shikenan, Allah ya tsare nima in sha Allahu ina nan shigowa in kawo mata turarrukan wuta da na jiki" Shi dai bai ce komai ba ya nufi kofa, Khaleesat ta mike tana yi ma Momy sallama, Momy duk fa a rude take ta gyada mata kai kamar kadangariya tace "To Mamata, sai na shigo, ku gaida gida, maza bi sa ku tafi" Daga haka Khaleesat ta bi bayan Abdul da har ya fita daga parlon, Momy ta dau wayarta har tana tuntube ta shiga dakin dake downstairs ta fara kiran Dr Mariya don family Dr dinsu ce for long, Dr Mariya na dagawa suka gaisa da Momy cikin fara'a, Momy tace "Yanxu Abdul ya zo min da matarsa yace daga asibiti suke, naga duk ba shi da walwala nasan yana da zurfin ciki bazai gaya min ko menene ba, shi ne na kira inji lafiya dai ko Dr? Ko juna biyu gareta? kinsan dama yace bai son haihuwa da wuri, in dai juna biyu ne da ita gwara in yi dubara in dawo da ita wajena don ni dai ina son ganin jikana, kar yaje ya bata wani abu da zai lalata cikin taje ta sha" Dr Mariya tayi dariya sosai, bata boye ma Momy komai ba tayi mata bayanin dalilin zuwansu Asibiti, Momy ta sauke wani irin ajiyar zuciya ba tare da tasan tayi hakan ba, sai kuma ta bige da cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kinsan yarinya ce fa, duka duka Allah yasa tayi shekara ashirin, har da yarinta abun nata dae" Dr Mariya tace "Wallahi nima haka nace masa don dae in kwantar masa da hankali kar ya dinga jin haushinta, amma shekara ashirin ai ba yarinya bace Hajiya, aka ma er shekara sha biyar aure ta zauna balle er shekara ashirin, ni dai na bata shawarwari Allah ya sa tayi amfani da shi, kar tun yana hakuri da ita hakurinsa ya kare a fara samun matsala gaskiya" Murmushi kawai Momy take tana Allah Allah su gama waya da Mariya ta kira Godiya, daga karshe Momy tace "To Allah ya sa ta dau shawaran naki Dr, kuma zan yi ma yayarsa magana ita ma taje gidan anjima ta kara nutsar da ita in sha Allahu" A haka Momy suka yi sallama da likitan, Momy tayi wani dariya tana girgiza kai sannan ta fara dialing number Godiya, aikin miliyan biyu ai ba wasa bane, sun dade suna waya da Godiya a waya, daga bisanni suka yi sallama, Momy na ta murmushi ita kadai bayan Godiya ta sake jadadda mata Malamin yace lokacin ma da ya dibar masu za ayi sakin baza a kai haka ba, don gab ake da yin sakin cikin kwanan nan kuwa, Meemah da ta shigo dakin ta tarar Momy na waya ta zauna duk tana sauraron conversation dinsu har suka yi sallama tace "To shikenan Momy yanxu haka zai saketa ba mu ci ubanta ba na huce haushin abinda yayi min a kanta?" Momy tace "Ke wa ke ta wani cin ubanta? Ance maki shi ne a gabana sai kace wata yarinya? Ni dai in na samu Abdul ya rabu da ita an gama min komai, kuma hakan kadai ne a gabana yanxu ba shashanci irin naki ba, ke kinsan menene hada iri da talaka kuwa? Ke kiji matsiyaciyar kakarta har ta fara shige shigen malamai tana kawo mata asiri banda Allah yasa Abdul din ya gani, to karyarsu ta sha karya wallahi, cikin kwanan nan zai kora masu ita bayan ya saketa" Mikewa Meemah tayi ta fita daga dakin don kwata kwata ba haka ta so ba ita, so kawai tayi a bar ta tayi ma Khaleesat dukan mutuwa ko zata jin sanyin abinda Abdul yayi mata a kanta.

[6/25, 8:35 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Bayan Khaleesat sun koma gida tayi wanka sannan ta canza kaya tayi sallan azahar ta fito ta dora lunch a kitchen, tana ta zaune parlor bayan ta gama hada komai na girkin tayi tagumi tayi nisa tunanin da take bata san sanda ya fito daga dakinsa ba, ya karaso parlon yana kallonta yace "Burden din mutane nawa ne a kanki da kike tagumi haka" Juyawa tayi ta kallesa tana gyara zamanta amma bata ce masa komai ba, tunda suka dawo gidan sai yanxu yake mata magana bayan ya gama cika da batsewan sa kenan, Yace "I am asking you" Shiru tayi still bata ce komai ba, ya zauna kan kujeran dake facing dinta yace "Mutane nawa kike ciyarwa da kike tunanin yanda za ki yi?" Bata san sanda tayi murmushi ba tana wasa da fingers dinta, kamar bazata ce komai ba, sai dai a hankali tace "Ba ina son zan yi magana da frnd dita Sophie ba kace bazan yi ba" Yana kallonta yace "Kiyi magana da ita ki ce mata me?" A hankali tace "Babu komai, i am just missing her kawai" Wayarsa dake hannunsa ya cire ma lock sannan ya mika mata yace "Speak to her in my front" Amsan wayar tayi ta shiga contact dinsa ta duba number Safiyyah sannan tayi dialing, yana kallonta yace "Sa a handsfree" Ba musu Khaleesat ta saka kiran a Handsfree, yana fara ring Safiyyah ta daga, a hankali Khaleesat tace "Sophie" Safiyyah tace "Omg Khaleesat? Wallahi I've been expecting your call for so long kawata amma shiruu, Ya Allah, number Abdul din ne wannan?" Khaleesat ta Ι—an kalli Abdul da ya kafeta da ido tace "Um, nasa ne" Lkci daya har Safiyyah ta gane wayar a handsfree yake sanin wanene Abdul, a hankali tace "Ohk then, ki gaida min shi sosai pls, but can i come over in gan ki if he will permit that pls?" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "I will speak to him about it" Safiyyah tace "Alright dear, take care of ur self, i will be waiting for ur feedback" Khaleesat tace "In sha Allah" a haka suka yi sallama, safiyyah ta kalli wata aunt dinta dake kusa da ita cike da bakin ciki tace "Wallahi nasan yana gefenta shi yasa ban tofa nawa ba, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Her marriage and Abdul is the worst thing that have happened to me last year, yanxu shikenan ta zama matarsa duk guje mata hakan da na dinga yi, ba irin addu'an da ban sa ta akan Allah ya rabata da Abdul ba, nayi ta mata sha'awan Housemate dinta amma Allah ya riga ya kaddara Abdul ne mijinta, dubi yanda take min magana kina jin muryarta kinsan tana cikin damuwa da matsin rayuwa, gashi karshen watan nan za mu koma school ban kuma ga alamar zai bar ta taci gaba ba" Safiyyah ta fara matsar kwallan bakin ciki, ita dai tana jin babu wanda ya kai ta bakin ciki da auren Khaleesat da Abdul, Abdul ya amshi wayarsa da Khaleesat ke mika masa bayan tayi sallama da Sophie, a hankali tace "Thank you" ajiye wayar yayi yace "Sai hankalin ki ya kwanta yanxu tunda kin yi magana da kanwar Baabarki ko" Cikin sanyin murya tace "Plss ina neman favour din ka barta ta zo wajena don Allah, i am missing her so much" A takaice yace "Baza ta zo ba, in barta ta zo ta ji dadin zuga ki kamar yanda ta saba? you think i don't know saboda tasan wayar a Handsfree yake shi yasa tayi composing words dinta without saying anything silly yanxu, duk ba ita bace ta fara ruining tunanin ki, very stupid girl" Khaleesat dai kallonsa kawai take hawaye cike idon ta, kawai tayi deciding tayi masa maganar abinda ya tsaya mata a rai all this while, hoping Allah zai sa yayi considering din request din nata, cike da karfin hali tace "Amma don Allah Yaya Abdul kar kace bazan koma makaranta ba, we are resuming end of this month kuma kasan wannan shekaran kadai ya rage min plss kar ka bari inyi asaran shekarun da nayi a baya, kayi considering expenses din karatun plss, in kuma zai yiwu kawai a min transfer ba lallai sai can kasar ba..." Hawaye na sauka idonta ta kare maganar tana kallonsa, ya mike yace "You think i am stupid da zan bari ki kara komawa America ki ci gaba da karatu? to ai kai ki can ma da nayi tun farko i deeply regret doing so, nayi da na sanin kai ki karatu America da har ya bude maki ido, kuma tunda ba kudin ki ko kudin wani naki aka kashe ba all this past years ina ruwanki da asaran da za ayi? How is the lost going to affect you da kike nagging akan expenses din? Ina ce kudina ne sai ko kudin mahaifina? So babu ruwanki, na gwammace inyi asaran duk abinda na kashe maki da dai ki koma kasar nan, kuma kika kuskura kika sake kawo min maganar karatu sai nayi mummunan saΙ“a maki wallahi, kuma bari kiji, common University din kasar nan ma baza ki yi ba balle na wata kasar don babu inda aka ce lallai lallai sai kinyi karatu, at first nayi tunanin kina da kamun kai da nutsuwa ne shi yasa confidently na kai ki America, amma sai kika tafi kina rayuwa da wani Ζ™aton Ι—an iska a gida daya without my knowledge, ya kai ya kawo ko kudi na tura maki sai kiyi kamar baki gani ba for days tunda kin samu Ι—an iskan dake siya maki abubuwa, not even one guy, kattin maza har biyu kika je kina mu'amala da su a can, ko wanne kuma ke kika san abinda kike basa da yake kashe maki kudi, so ko da kuskure kika sake kawo min maganar karatu wallahi sai na maki abinda har ki koma ga Allah baza ki manta ba" Yana kai wa nan ya dau wayarsa ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Khaleesat ta bi sa da kallo hawaye masu zafi na sauka idonta. Har dare Khaleesat na dakinta abun duniya ya taru ya mata yawa, wajen karfe sha biyun dare har ta fara bacci taji an bude kofar dakinfa, a hankali ta bude idonta, wutan dakin taga ya kunna sai kuma ya kashe, ita dai tana kwance bata juyo ba, ya karaso inda take kwance ya cire duvet din jikinta ya cire hulan kanta yana shafa dogon gashinta ya kai fuskarsa kusa da nata murya can kasa yace "You gave me Neither lunch Nor dinner today, saboda kinfi karfin a gaya maki gaskiya ko?" Ita dai bata ce komai ba duk da tana jin sa, dagota yayi zaune ya rungumeta yace "Then let me have you since you are not giving me what u cook" Bai jira abinda zata ce ba ya fara kissing dinta, Sosai Abdul ya bata lokaci wajen romancing dinta irin yanda yasan zai gigita ta, in ba ita ba ma babu warce ya taΙ“a romancing har haka, ko lube din bai dauko ba yau don baya ganin zasu bukace sa ma, a wannan moment din Frustration dinsa yafi na kullum don sosai ya kai zuciyarsa nesa bai kai mata hannu ba, yana wani irin huci ya fixgota da karfi yace "Why are you doing this to me Khaleesat? Why are you frustrating me?" Kasa ce masa komai tayi jikinta na rawa hawaye na zuba idonta, ta gaji da ce masa ita bata san abinda ke faruwa ba, cikin daga murya jikinsa na rawa yace "Ki bani amsa? Me na maki kike wahal dani kike cutata haka?" Khaleesat dai ta kasa ce masa komai jikinta na rawa don tsoron magana ma take ya gaggaura mata mari, yana wani irin huci ya turata yace "Ki jika abun ki ki sha" Yana fadin haka ya sauka daga saman gadon ya saka Pajamas dinsa ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Khaleesat dai ta jawo duvet ta rufe jikinta har sannan zuciyarta na bugawa ta fashe da matsanancin kuka, bayan kusan minti goma taji fitar motarsa a gidan gaba daya. Da yammacin ranan Momy na parlonta da Godiya sai ga Abdul ya shigo kamar an hankado sa, Momy na kallonsa tace "A'a Babana, sannu da zuwa" Juyawa yayi ya fice daga parlon ganin Godiya, Momy ta Ι—an zaro ido tana kallon Godiya sai kuma ta mike da sauri ta tafi kusa da kofar ta bude tana leka corridor taga bangaren Abbansa ya tafi, ita ta dade bata gansa cikin irin wannan yanayin ba ma, ta kulle kofar ta dawo tana kallon godiya tace "Anya Godiya Malamin nan ba maye bane kuwa, kin ga dama yace Abdul zai zo yau gashi kuma ya zo din kamar an jefosa" Godiya tayi wani dariya tace "Ke ma dai wallahi sai kace yau Danger ya taΙ“a maki aiki da zaki yi mamaki? Yanxu dai sai ki tashi kije ki dora masa girkin da ya fi so da maganin" Momy tace "Ikon Allah, in dai kana da kudin ka zaka ga aiki da cikawa kawai, yanxu ki dubi yanda ya shigo mana a firgice kamar mara lafiya" Godiya tace "Ina kuwa lafiya dama an hanasa angwancewa da amarya, sai kace baki san maza in suka kwallafa rai kan wannan lamari ba" Suka kwashe da dariya gaba daya har da kyakyatawa, Momy tace "Toh yanxu zan tura cikon aikin nan na karshe, yaushe zaki koma wajensa mu je tare in masa godiya" Godiya tace "Nan da kwana uku in sha Allah, kin ga bari in tashi in tafi mai gidana na hanyar dawowa yau" Momy tace "Haka fa kika ce, toh shikenan sai mun yi waya dai kawai" A haka Momy ta raka Godiya har gun motar ta sannan ta dawo cikin gidan ranta fari Ζ™al, bangaren Alhaji ta nufa ta tarar da Abdul kwance a parlor idonsa a lumshe, zaunawa tayi gefensa tana kallonsa cikin kwantar da murya tace "Babana baka da lafiya ne?" A takaice yace "Hutawa nake yi Momy, i need privacy pls" Momy tace "Toh shikenan, bari in sa a daura maka favorite din ka, ina Mamata fa?" Shiru yayi yaki ba Momy amsa, Momy ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kullo kofar, sai a sannan tayi wani murmushi ta koma bangarenta zata dau maganin da Godiya ta kawo mata wanda zata zuba a cikin girkin abinda Abdul ya fi so, sai da ta kori mai aikinta can compound sannan ta fara girka masa Pounded yam da Vegetable soup, cikin miyan ta zazzage duk maganin da kyauta ta kawo har kala uku, wajen karfe bakwai ta gama ta dau abincin ta kai masa dining table ta ajiye, dama iya cin sa kawai ta girka wato malmala daya kuma ba babba ba, miyar ma Ι—an tsut yanda zai cinye gaba daya, sai bayan isha Abdul ya ci abincin da Momy tayi masa, ya bar ma mai aiki ta kwashe sannan ya wuce sama zuwa dakinsa, Momy ta fito dakin Meemah kenan ta bi sa da kallo har ya shiga dakinsa sannan ta bi bayansa, tana shiga dakin tace "Wai lafiya Babana? Ko dai akwai wani matsalan da kake boye min ne" a takaice yace "Ba komai, zan shiga wanka" Yana fadin haka ya fara cire kayan jikinsa, Momy tace "To ka ci abincin?" Yace "Na ci" Momy na murmushi tace "You like it?" Yace "Miyan yayi dadi, but it's little" Tana murmushi tace "To maa sha Allah, amma ai ya isheka dai" Yace "Ya isa" Tace "Toh je kayi wankan ka nima bari inje in ci abinci" Fita tayi daga dakin ya shiga bandaki, Momy na zaune parlonta tana cin farfesu dake cike cikin bowl din hannunta Abdul ya shigo, kallonsa tayi ganin yanda ya shirya sai zuba azababben kamshi yake, tace "Har zaka tafi Babana" Yace "Eh, sai da safe" Tace "To ko in zuba maka farfesun ka kai ma Mamata" A takaice yace "A'a ni ba gida zan kwana ba" Momy tayi murmushi tace "To Allah ya tsare Babana" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga gidan. The next 10 days a gidan Abdul was a living hell for Khaleesat, gaba daya Abdul ya sauya mata a gidan ya dawo kamar wani monster, dukanta da yace ya dena sai dai bai samu slightest opportunity din yin hakan ba, kawai ya maida ta punching bag dinsa a gidan barin in ya zo gareta bai samu biyan bukata ba, kuma bai fasa zuwa mata da bukatar tasa ba amma as usual sai dai kawai ya doketa ya fita bai cimma burinsa ba, kwata kwata ya dena cin abincin gidan, ya dena kwana sai sanda ya ga dama, duk wani ingredients din girki ya dena siyowa sai dai tayi ta cin indomie, hatta bottle water ma da ya kare yaki siyowa, kuma ko Satchet water yaki siya ya ajiye, sai dai ta sha ruwan pampo, gaba daya Khaleesat ta fita hayyacinta a gidan ta dawo kamar ba Khaleesat ba, ga karyewa da gashinta ya dinga yi sosai saboda tsananin damuwa, kana ganinta kasan tana cikin jarabawan rayuwa, bata da aiki sai kuka sai kuma addu'a da sallan dare, gaba daya ta maida duk lamarinta ga Allah, kullum haka take kwana ta tashi da zazzabi amma ina taga fuskar ce masa bata da lafiya, sai dai tayi ta daurewa a haka, in ma ta gaya masa don ya zagi iyayenta ba komai bane a wajensa, in zazzaΙ“in ya rufeta sai dai ta kwanta har sai sanda zata ji dama dama sannan ta daure ta tashi. Ranan Friday tana dakinta a kwance ko breakfast bata yi ba har kusan karfe sha biyu da rabi, zuwa yanxu ta gaji da cin indomie da ma tana da dakakken yaji sai ta dinga yin ko shinkafa da mai da yaji ne amma babu, indomie duk ya fita a kanta bata iya ci ko ta dafa, gashi haka take dafasa babu yaji balle albasa, bude kofar dakin nata yayi ta mike zaune da sauri tana kallonsa gabanta na faduwa, kamar zai fasa mata dodon kunne taji yace "Ina Cufflinks din da na bari a parlor shekaranjiya?" Sauka tayi daga kan gado, ita dai ta gyara parlon ta goge ko ina jiya da yau amma bata ga wani Cufflinks dinsa ba, a hankali tace "Toh bari in duba a parlon" Wani mugun kallo yake mata hakan yasa ta raΙ“a tabi ta gefensa ta fita daga dakin zuciyarta na bugawa ta tafi parlor tana dudduba Cufflinks din, da alama masallaci zai je don yin sallan juma'a, babu ta yanda za ace iya Cufflinks din da yake tambayarta yake da shi a gidan, amma sbda neman hanyar da zai musguna mata yake shi yasa zai saka ta gaba ta fito da abinda bata gani ba, kuma rabonsa da gidan tun shekaranjiyan, tana cikin dube dube a parlon shi kuma yana tsaye fuskarsa a murtuke alamar he is loosing his patient aka bude kofar parlon, Momy ce ta shigo da Cousin sis din Alhaji Musa, warce suke kira da Ummu, Yau kwanan Ummu uku a Nigeria daga Dubai inda take aure da yaranta duk a can, kuma a yau zata koma Dubai shi ne ta sa a kawota ta ga matar Abdul kafin a kai ta airport, duk da Abdul yaje ya gaisheta san da ta zo, Khaleesat da duk a rude take ta kalli Abdul a hankali tace "Wallahi ban gansa ba da nake gyaran parlorn jiya da yau, kilan ka sha'afa ko a daki ka bar su ne ka manta" Bata rufe baki ba ya sauke mata wani gigitattcen mari yana huci ya fixgota yace "Ni zaki gaya ma a daki na bar su?" Ta dafe kuncinta hawaye cike idonta tana girgiza masa kai, nan da nan fuskarta yayi ja, ko minding uwar sa da Cousin sis din Babansa da suka shigo parlon bai yi ba, duk suka yi cirko cirko baki bude suna kallon ikon Allah, cikin tsawa yace "Baza ki fito min da shi ba sai na maki dukan tsiya a nan?" Tana shesshekan kuka tace "Nace maka ni ban ga wani links din ka ba wallahi...." Bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani wawan marin, Momy da taji ranta yayi fari tass cikin kwantar da murya tace "Subhanallahi, Babana ka bi a hankali, hakuri ake Babana" Ummu ta jefar da handbag dinta kan kujera ta nufesa cikin bacin rai tace "Abdallah?? kana hauka ne kake marin mace haka don uban ka?" Momy ta wani hade rai tana kallon Ummu, Abdul yaki ko kallon Ummu dake masa magana, ya wani haure Khaleesat a mugun fusace har sai da ta fadi kasa, Wani Mari Ummu ta sauke masa a fuska, cikin fushi tace "Ashe kai jahili ne shashasha ban sani ba?" Juyowa yayi yana kallon Ummu da mamaki baya ko kiftawa, Momy ta dinga huci tana kallon Ummu ita ma, nan da nan idanuwanta suka kankance don bacin dai, tunda ta haifi Abdul bata taΙ“a marinsa ba haka ma ubansa sai gashi yau an maresa a gabanta, Abdul dake kallon Ummu kamar me counting din words dinsa yace "Ummu akan wannan jakar yarinyar kika mareni??" Ummu tace "Na mare ka din, zaka rama ne? Wawa kawai mahaukaci ka saka yarinya karama haka a gaba kana duka? Tarbiyar da aka maka kenan? In na san abinda zan zo in tarar a gidan ka kenan uban me zai kawo ni?" Abdul da idanuwansa suka sauya launi ya kalli Khaleesat yace "Ki je... na sake ki" Yana fadin haka ya dau makullin motarsa ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Khaleesat ta bi sa da kallo babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda yace ba, Momy ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tace "To Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" Sai kuma ta kalli Ummu tace "Ke kuma Muhusina kin ci darajar Musa banda haka da babu uban da zai hanani rama ma Ι—a na marin da kika masa don tunda na haifesa ban taΙ“a marinsa ba haka ma ubansa, kuma Abdul yayi min dai dai hukuncin da ya dauka, dama me ake da auren er gidan talakawa er gidan matsiyata? Ai ba class din mu bace ita, kuma duk bama goyon bayan wannan tsinannen auren, kawai irin wannan rana muke ta jira gashi Allah ya kawo mu cikin ruwan sanyi, Alhamdulillah Allah na gode maka, Allah na gode maka, yau zan yi bacci cikin farin ciki da kwanciyar hankali burina ya cika, effort dina kuma bai tashi a banza ba" Momy na kai wa nan ta nufi kofa tana tafiya gansan gansan farin ciki fal a ranta mara misaltuwa tana murmushi ta bude kofar parlon, Khaleesat ta bi Momy da kallo with shock ko kwakkwaran motsi ta kasa tsabar mamaki, maganganun Momy suka dinga yawo a kanta kamar a mafarki, Ummu ta zauna gefen kujera ta dafe kanta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai a sannan Khaleesat taji hawaye masu zafi na silalowa fuskarta, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta har kasa ta fito.....

 

 

[6/26, 9:27 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat na fitowa parlor suka hada ido da Ummu dake kokarin kiran Alhaji Musa da wayarta cikin bacin rai, sunkuyar da kai Khaleesat tayi tana goge hawayen dake ta zuba idonta, Ummu tace "Zo ki zauna tukunna diyata" Khaleesat tayi shiru bata ce mata komai ba don har cikin ranta bata ji zata iya zama a parlon ba kamar yanda Ummu ta umarceta, amma kar tayi disrespecting matar duba da tsaya mata da tayi sanda Abdul ke ci mata mutunci yasa kawai ta duka kasan carpet kanta a kasa, Sau uku Ummu na kiran wayar Dad din Abdul, daga karshe ya daga kiran, cikin fushi ta fara koro masa abubuwan da ta zo gidan Abdul ta tarar da kuma abinda Abdul ya aikata daga karshe, Alhaji Musa dake ta sauraronta ya jira har ta gama, sannan yayi gyaran murya yace "Ai ina ganin Muhusina wannan ba issue bane da zaki shigar da kanki farat daya, ke da ba ma a kasar kike ba zuwa kawai kika yi, i don't think it's proper kiyi involving kanki sama ta ka, it's not done that way, alright? kuma tunda kika ga ya saketa definitely yana ganin hakan shi ne dai dai so meye zaki damu kanki, ko mu iyayensa we are not in the rightful place to question his act, okay? decision dinsa ne, so just stay out of what u know nothing about Muhusina, ba naji kin ce flight din karfe biyu gare ki ba? Ko kin daga tafiyar taki ne?" Kasa cewa komai Ummu tayi tsabar mamaki, kana ganinta kasan she is speechless, ita dai Khaleesat kanta na kasa don ba handsfree Ummu ta saka wayar ba balle ta san abinda Dad din Abdul ke cewa, a hankali Ummu tayi ending call din ta ajiye wayar a gefen kujera don ba ma ta da amsan da zata ba Ι—an uwan nata, sosai jikinta yayi sanyi, yanxu dama Family din Alhaji Musa basu canza ba daga yanda ta san su tun tale tale, don ita sai tayi shekara aru aru ba a ganta a Nigeria ba in ba muhimmin abu bane ya kawo ta, Momy ce ta bude kofar parlon fuskarta a murtuke, ashe all this while tana kofar gida tana jiran ganin Khaleesat ta fito ta bar gidan amma shiru shiru bata ga ta fito ba, Momy na kallon Khaleesat tace "In dai ba gidan ubanki bane ko na uwarki nan din tunda har ya furta ya sake ki ai kya fito ki kama gabanki, ko zaman ubanki kike yi har yanxu? Da wani abinda kika zo gidan da shi ne kika yi waya a zo da mota a kwashe maki ko yaya?" Ummu ta kalli Momy tana girgiza kai cike da takaici tace "Ki ji tsoron Allah Hajiya, ki ji tsoron haduwar ki da Allah, ke ma fa kina da yaran nan mata...." A mugun fusace Momy ta karaso cikin parlon ta dakatar da ita tana nunata da Ι—an yatsa tace "Kin ga wannan family issue ne ki cire bakin ki a abinda bai shafeki ba Muhusina don ke bare ce a wannan Ι“angaren, kuma ba ke kika haifar min Abdul din ba da kike neman cusa kai abinda ya shafi rayuwarsa, who are you to even interfere? Ko Musa kin zata ya isa ya hana Abdul abinda yayi niyyar zai yi ne? To wallahi ki cire bakin ki da idonki akan abinda ya shafi zuri'ata, 'ya ya mata kuma dama ko wani shege ya haifa ai, meye a ciki" Momy na kai wa nan ta kalli Khaleesat cikin daga murya tace "Baza ki tashi ki san inda dare yayi maki ba ko sai na kira su Meemah sun fitar min da ke daga gidan nan??" Mikewa Khaleesat tayi bata bari sun hada ido da Momy ba ta nufi kofa tana tafiya a hankali, Ummu ta kasa cewa komai tana kallon Momy tana girgiza kai, sai da Khaleesat ta fita daga compound din gidan gaba daya sannan ta fara share hawayen dake sauka idonta, tunanin yanda zata koma gida bata da ko sisi ta fara yi, tafiya me nisa tayi har ta iso titin da zata samu abun hawa, daga karshe bayan jiran kusan minti sha biyar ta samu wani adaidaita sahun da zai kai ta Mariri a dubu biyu da dari biyar, in taje gida sai ta basa kudinsa, har Khaleesat ta isa gida hawaye ya ki tsaya mata a ido, ita kanta bata san yanda take ji a ranta ba game da abinda Abdul yayi mata, farin ciki take ko akasin haka har sannan ta kasa ganewa a zuciyarta, but she was deeply hurt and pained, daurewa kawai take kar ta fashe da kuka a adaidaita sahun, bayan ya tsaya dai dai kofar gidansu ta sauka tace "Za a kawo maka kudin yanxu, nagode" Daga haka ta shiga cikin gidansu, a tsakar gida ta tarar da kishiyoyin Ummanta sun gama abincin siyarwansu na yamma yara za su fita da shi talla, ta gaishesu ba tare da ta bari sun hada ido da su ba direct ta nufi dakin Ummanta, duk suka bi ta da kallo, Aunty Farida da fitowar ta daga bandaki kenan zata yi alwala don lokacin sallan La'asar yayi ta ajiye butan hannunta ta bi Khaleesat da kallo ita ma duk da Khaleesat bata ganta ba, Khaleesat na shiga dakin Ummanta ta fada jikinta ta fashe da kuka a hankali, Kasa cewa komai Umma tayi tana kallonta da mamaki, sai ga Aunty Farida ta shigo dakin ita ma, sosai gabanta ya fadi ta tsaya nan bakin kofa tana kallon Khaleesat, da kyar Umma ta dago kanta cike da karfin hali tace "Me ya faru?" Khaleesat ta kasa cewa komai tana kuka sosai, Umma da nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta ta rungumeta bata sake ce mata komai ba ta bar ta tayi kukan me isarta, cikin sanyin jiki Aunty Farida ta karasa cikin dakin ta zauna gefen katifa tayi shiru, Umma ta goge idonta tana patting Khaleesat a baya a hankali trying to calm her amma bata hanata kukan da take ba, sun fi minti biyar a haka sai ga Mama Zubaida ta dage labulen dakin tace "To Ι—an sahu dai na ta jira a mika masa kudinsa a kofar gida" Magana take amma idonta na kan Khaleesat da Umma, tsabar gulma yaron makota me adaidaita sahun ya aiko cikin gidan amma tayi karaf ta mike bayan yaron ya sanar masu ta nufo dakin Umma taki barin yaron ya karasa, don tun shigowar Khaleesat suka baza kunnuwa ko za su ji wata magana amma shiruu basu ji ko tari ba a dakin Umma, Aunty Farida ta dau handbag dinta ta fita daga dakin ta sake labulen daga hannun Mama Zubaida dake rike da shi, sannan ta fita zuwa gun mai adaidaita sahun, sai a sannan Umma ta iya daga kan Khaleesat, suna hada ido Khaleesat ta sauke jajayen idanuwanta, Umma tayi karfin halin cewa "Me ya faru Jiddah?" Khaleesat ta sauke idonta wasu hawayen na zuba idonta tace "Yace ya sakeni" Hawayen dake makale idon Umma ya zubo tana kallon Khaleesat babu ko kiftawa, Khaleesat ta rufe fuskarta jikin Umma ta fara wani sabon kukan, Umma ta rungumeta sosai, cikin rawan murya tace "Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ki, kiyi hakuri kin ji?" Kai kawai Khaleesat ke gyada mata tana shesshekan kuka, a haka Aunty Farida ta dawo dakin ta same su, Aunty Farida ta zauna gefen Umma tana kallonsu, Da kyar Umma ta kalleta tace "Wai sakin ta yayi" Ƙasa cewa komai Aunty Farida tayi tsabar yanda ta girgiza, ta dinga kallon Umma babu ko kiftawa, nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta, after a while ta goge hawayen dake zuba idonta ta fita ta dau buta tayi alwalanta ta dawo ta tada sallah, Umma ta dago Khaleesat da tayi shiru a jikinta, sai taga bacci take, Khaleesat ta bude ido a hankali, Umma tace "Kin yi sallah ne?" Girgiza mata kai Khaleesat tayi, Umma tace "Ki je kiyi alwala kiyi sallah" Khaleesat ta mike tana tafiya a hankali ta fita daga dakin. Khaleesat na idar da sallah Aunty Farida na kallonta tace "A zubo maki abinci?" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Na koshi" Daga haka ta mike ta hau saman gadon Ummanta ta kwanta, nan da nan bacci me nauyi ya dauketa, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya iya cewa komai a dakin, suna ta zaune har kusan karfe shidda, ita dai Aunty Farida tana rike da Al-qur'ani tana karatu silently a ranta, su Islam suka dawo hadda wanda suke zuwa har ranan friday, Umma ta sa su je su hura gawayi su dora girki, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana cewa "To Zubaida sai ki dau na annabawa don kin tafka asara lafiyayye yau, almajirai na mugun wasa suka hamΙ“are Suwaiba tallan da kika dora mata ya kife a kasa, su kuma suka tsere, sanin azaban da zaki mata ta taho ta sameni tana kuka kamar ranta zai fita, yanzu haka tana can gidana nace tayi zamanta, ga robobin tallan da faranti nasa an kwaso maki kayanki, ko roba daya bata siyar ba suka hambare farantin" Mama Shatu ta saki salati tana kallon Mama Zubaida da ta nemi waje ta zauna jin abinda Nenne ke cewa, Nenne ta kwashe da dariya har da kyakyatawa tace "Yaran layi kuwa duk suka wawushe abincin da ya zube a kasa suka loda ma cikin su" Daga haka ta nufi dakin Umma ta dage labulen tace "Zahra'u kina da er kuka ko kubewa ki tsam inje in Ζ™ada miya" Umma bata yarda sun hada ido da Nenne ba tace "To bari in duba maki, Ina wuni" Nenne tayi mitsi mitsi da ido tace "Wacece wancan kuma a kwance kan katifarki?" Umma dai bata ce komai ba ta tashi zata dauko ma Nenne kubewa busasshe, Aunty Farida ta gaida Nenne ba tare da ta kalleta ba, Nenne na kallon Khaleesat tace "Wai wa nake gani kamar Khaleesah a kwance?" Aunty Farida ta ajiye Qur'anin hannunta still bata kalli Nenne ba tace "Ita ce" Nenne ta shigo dakin tace "Wato ni dai shikenan kun nuna mata banda matsayi da har zata shigo unguwan nan ta karasa gidana ta gaisheni ko? In ma bata je ta gaisheni don Allah ba ai sai tayi don ubanta Ali tunda ni na haifesa har ya haifeta" Daga Umma har Aunty Farida babu wanda yace ma Nenne komai, Nenne tace "Mijin ne ya kawota? Shi ma ai shegen ne tunda ba karasawa yake yi gidana ya gaisheni ba, banda kaddara a ina za mu san sa har mu aura masa Khaleesat mutumin da baya ganin mutuncin mu, kana masa magana yana amsa maka cikin gadara da yanga wai shi Ι—an Alhaji Musa, waye bai san satan da ubansa ya zabga a gwamnati ba kafin ya koma kasuwanci, ko don muna kauda kai?" A takaice Aunty Farida tace "To sakin ta yayi..." Nenne ta juya ta kalli Aunty Farida na en sakwanni, can tace "Ban ji me kika ce ba Parida?" Aunty Farida da har hawaye ya kawo idonta tace "Sakinta Abdul din yayi" Nenne ta kasa motsi a inda take tsaye, a hankali tace "Sakin aure ko sakin me?" Aunty Farida dai bata tanka ta ba, ita dai Khaleesat na kwance tayi backing din Nenne bayan surutunta ya tasheta daga baccin da take, Nenne ta saki wani salati muryarta na rawa tace "Wato dai Ι—an nawa ne ba a son a ga ya zauna lafiya a gidan duniya kamar yanda kowa yake zaune" Fita tayi ta koma tsakar gida ta rushe da kuka sosai tace "Allah ya isa tsakanina da Zahra'u da er ta, babban burin su a duniya su ga Ali ya tagayyara, babban burinsu su ga Ali cikin mawuyacin hali cikin tashin hankali, banda haka ko dukanta da zaginta Awdul ke yi a gidan bazata hakura ta zauna ba albarkacin ubanta? Shi ne har zata amshi sakin da yayi mata hannu bibbiyu ta dawo mana gidan nan domin shari'arsu da Ali ya dawo sabo?" Mama Zubaida da Mama Shatu tuni suka mike tsaye jin abinda Nenne ke cewa, cikin kuka Nenne tace "Ban taΙ“a ganin er da burinta taga ubanta a walakance ba, kun ga ai ta dawo taga yanda za ayi da uban nata ko furson din za a mayar da shi ko hukuncin rataya za a yanke masa, ni dai na shiga uku na lalace, Allah ya hada Ali da mata da 'ya yan da basa tausayinsa kuma su za su yi ajalinsa, yanxu in Khaleesat er arziki ce da yace ya saketa ba sai tace babu inda zata je ba tunda bautar Allah take??" Malam Ali ne ya shigo gidan da er taliyar Hausa da ya siyo cikin Bacco bag, Nenne na ganinsa ta rushe da sabon kuka tace "Wallahi ta kashe auren ta dawo taga yanda za su yi da kai Ali" Malam Ali ya tsaya yana kallon Nenne, Nenne na fyace majina tace "Ga ta can dakin uwar a kwance tana jiran taga da wace motar za a zo a kwashe ka, dama wallahi tun da muka je gidan da parida nasan za a samu babban matsala don babu alkhairi a ran Parida, kuma in bata yi hankali ba daga ita har Zahra'un sai dai su koma kasar su, duk wanda baya son kwanciyar hankalin Ι—a na to kwanciyar hankalina ne baya so wallahi" Malam Ali dai ya nemi tabarma ya zauna ya kasa cewa komai, Mama Zubaida tace "Ikon Allah, kuma abinda ya faru kenan ni Zubaida? Aure wata daya da yan kwanaki amma har an yi saki? Yanxu zawarawa har biyu garemu a gidan nan kenan?" A fusace Nenne tace "Ta zauna tayi ma uban wa zawarci a gida? Ai ko taki ko ta so sai naje na ba Awdul hakuri ya maidata dakinta don kaf zuri'armu babu wanda ya taΙ“a zawarci sai in mutuwa mijin yayi, to ko bakin halinta bai isa ya sa ya korota ba bai shirya ba, Khaleesah ce duk wani mummunan bakar maganar da ya zo bakinta take yaΙ“a ma mutum, ko kuma in ka gaya mata abinda bai gamsheta ba tayi maka wani kallon walakanci da kaskanci da tula tulan idanuwanta, wani lkcn kana mata magana tayi maka banza wannan duk mun san halinta ne ba wai sharri ba, ga nukurci kamar er sarkin kutare, to ai ba ko wani namiji bane zai dau wannan, don haka zan je in basa hakuri ya dubi girman Allah ya maidata dakinta..." Mama Shatu tace "Toh ko samun sa kika yi ai sai yayi niyya zai maidata Nenne, in zai iya ai bazai fara sakin ta ba" Wani zagi Nenne ta kundumo mata a fusace, dai dai nan aka rafka sallama a kofar gida, Malam Ali ya mike tsaye yana kallon hanyar fita gidan, Nenne tayi tsit zufa na keto mata, can ta fara kuka a hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Zahra'u dai bata zo mana pamily da alkhairi ba, kun ga har an zo tafiya da shi" Mama Zubaida ce ta yafa gyale ta nufi hanyar fita daga compound din, wani mota taga anyi parking a kofar gidan, mutumin dake tsaye kusa da motan ya nufota yana kallonta, Mama Zubaida ta gaishesa har da risinawarta, ya amsa yace "Mai gidan na ciki kuwa?" Mama Zubaida tace "To Allah ya sa dai lafiya Malam" Mutumin yace "Eh to, ni Dreban Alhaji Musa ne, an bani sako ne in kawo ma mai gidan" Mama Zubaida tace "To ni mai dakinsa ce, ni ce uwar gidansa, ko zan iya karba in mika masa, don baya jin dadi ne" Mutumin yace "To ba damuwa" Hannu yasa a aljihu ya ciro Envelope ya mika mata, ta amsa yayi mata sallama ya koma zai shiga mota, Mama Zubaida ta koma gidan tana juya takardan ita kanta sai da gabanta ya fadi don irin wannan in an kawo ai sammaci yake nufi, Nenne na ganin Envelope din hannun Mama Zubaida ta rushe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, shi kenan Ali a haka zai kare kenan ni Zainabu? wani takardan kotun aka sake kawo masa kenan?" Malam Ali ya amshi Envelope din hannun Mama Zubaida ya yage ya ciro takardan ciki ya warware, "Ni Abdallah Musa, na saki er ku Hauwa saki daya, biyu, uku" content din dake jikin takardan kenan, Shatu ta amshi takardan hannunsa tun da tayi karatun primary, tana duba takardan ta karanto abinda ke jiki amma fa da kyar tana in ina, Nenne ta tsaida kukan da take bayan taji Shatu ta karanto rubutun jikin takardan tace "Ji tsinanne la'ananne matsiyaci? saki har uku kamar warce ta kashe ubansa ko uwarsa? To Allah Ubangiji ya tsine masa albarka, dama banda kaddara uban me Khaleesat zata ci da Ι—an barawon Gwamnati? ubansa barawon gwamnati shi kuma Ι—an daba, Ai mu wannan sakin abun farin ciki ne a gare mu gaba daya tunda ba na'am muka yi da auren ba, kuma ko yau Khaleesat ta fita sai ta samu mijin nuna ma tsara da ya fi sa komai wallahi, bakin cikinmu daya zawara da ya maida ta, dama kullum da fargaban aurenta da shegen nake don har raina bana son sa babu yanda na iya ne kawai, banda jarabawa wasu iyayen kwarai ne za su dau er su su ba tsinanne irin Awdul? Khaleesah sai dai kawai tayi hakuri don cuta kam Ali ya cuceta, ya cuci Rayuwarta, don duk shi ya ja mata wannan masifa, da suka ce maka er ka suke so bayan an fito da kai furson in kai uba na gari ne sai ka cije kace sam baka yarda ba sai dai a maida ka furson din ka mutu a can, amma saboda tsoron azaban duniya ba na lahira ba ka zabi ka sadaukar da erka don samu encin kanka, to gashi nan bayan ya rabata da budurcinta ya sako mana ita, dama auren sha'awa kawai yayi da ita, Allah ya isa bamu yafe masa ba wallahi" Nenne na kai wa nan ta fashe da kuka ta jawo kujera er tsugunno ta zauna tana rera kuka sai kuma tace "To yanxu ko zuwa za muyi mu basu hakuri ya dubi girman Allah ya maidata tunda malamai sun ce saki uku a madadin daya yake"  Wajen karfe goma na dare Aunty Farida ta zauna gefen Khaleesat dake zaune da cup din kunun da Umma ta dama mata tunda ta kasa cin abinci, Aunty Farida tace "Baki shanye kunun bane?" Khaleesat ta dau cup din ta ci gaba da shan kunun a hankali, Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba tana kallon buhun abubuwan da ita da Umma suka hada zata kai ma Khaleesat gobe, don da gobe zata je wajenta, tun daga dakakken yaji, kubewa busasshe, kuka, kanwa, su citta da kanumfari, gyadar miyar, har da garin danwake da sauran abubuwa da yawa duk su ne a cikin buhun, ga turaren wuta da suka siya mata masu kyau, Aunty Farida ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat da ta kasa shanye kunun hannunta, a hankali ta jawota jikinta, soothingly tace "Kiyi hakuri Daughter, Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, kar ki saka komai a ranki kin ji?" Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida bata sake ce mata komai ba don ita bata ma son ta tambayi abinda ya hadasu don mayar da maganar bacin rai kawai zai kara masu, Ita dai Umma na zaune kan darduma Islam na bacci a jikinta, Maman Salame ce tayi sallama ta shigo dakin tana kallon Umma tace "Wani labari ne wannan nake ji a garin nan Zahra'u?" Umma dai tayi shiru tana kallonta, Maman Salame ta zauna kan tabarma tana kallon Aunty Farida da Khaleesat dake gefenta tace "Farida" Aunty Farida ta Ι—an yi murmushi tace "Ina yini Maman Salame" Maman Salame tace "Wai da gaske ne? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Farida tace "A ina kika ji Maman Salame?" Maman Salame tace "Ga labari nan ya baza Mariri? Dawowata daga Wudul kenan kusan mutane biyar suke gaya min haka a hanya tun ban karasa gida ba, wallahi buhun hannuna kawai na ajiye bayan na shiga gida na yo nan" Aunty Farida tace "To Allah ya sa mu dace" Maman Salame tana kallon Khaleesat cike da tausayinta tace "Garin yaya haka Khaleesah?" Khaleesat ta sauke idanuwanta bata ce komai ba, Maman Salame tace "To Allah Ubangiji ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, in kuma auren bai kare ba Allah ya kaddara za ki koma sai ki ga an koma" Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai saki uku ne Maman Salame" Maman Salame ta kasa cewa komai tana kallon Aunty Farida, kana ganinta kasan sosai jikinta yayi sanyi, ita dai Umma babu abinda tace a dakin, bayan kusan minti goma Maman Salame ta mike a sanyaye tace "Toh Allah ya sa mu dace, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu duka, sai na shigo da safe in sha Allah" Umma tayi mata sallama, Maman Salame ta fita daga dakin rai babu dadi, sarai Umma tasan kishiyoyinta ne suka baza labarin a garin, don ko Nenne bazata gaya ma kowa wannan labarin ba ita da ta tsani tonan asiri, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya don exactly tunanin da Umma take yi ita ma shi ne a ranta, Khaleesat ta kalli Aunty Farida a hankali tace "Aunty kina da number Safiyyah?" Aunty Farida tace "Ina da shi" Khaleesat tace "Ina son zan kirata ne" Aunty Farida tace "Babu kati a wayar, kuma yanxu dare yayi, ki bari gobe da safe sai kiyi magana da ita" Khaleesat ta gyada mata kai sannan ta mike tayi kwanciyarta saman gadon Umma, yaron Mama Shatu ne yayi sallama bakin kofar dakin Umma ya daga labulan yace "Wai Babanmu yace Khaleesat ta je" Umma da Aunty Farida dai sai kallon yaron suke, ya juya ya bar bakin kofar, Khaleesat ta mike zaune bayan taji abinda step brother dinta yace, tun dawowarta gidan ita ko haduwa da baban nata bata yi ba, ta sauka daga saman gadon tana gyara hulan kanta ta fita daga dakin Umma ta bi ta da kallo taji hawaye na taruwa idonta, Khaleesat na tafiya a hankali ta karasa har bakin kofar Babanta don yana zaune kan tabarma shi kadai a bakin kofar nasa, dukawa tayi daga gefen tabarman ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya ta gaishesa, maimakon ya amsa sai taji a hankali yace "Kiyi hakuri Jiddah, i failed you as a father, i caused you all this, but everything happened because I am a nobody, everything happened because...." Shirun da taji yayi ya sa ta daga kai ta kallesa taga hawaye a idonsa, bata san sanda ta fashe da kuka ba, yace "I am sorry for failing you daughter, albarkacin biyayyan da kika min baza ki taΙ“e ba in sha Allah, my wish for you since u were born was to give you the best of everything i could amma Allah bai nufa hakan ba kaddara ta fada min...."

[6/27, 8:51 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Washegari da safe har karfe goma saura Khaleesat bata tashi baccin da take ba, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya tasheta don duk sun san bata yi wani baccin kirki ba daren jiya, daga wayewar gari zuwa lokacin mutanen da suka shigo dakin Umma yi mata Allah ya kyauta da abinda ya faru sun fi goma, don gaba daya labarin ya gama bazuwa garin, Aunty Farida ta kalli Umma bayan wata makociyarsu da ta shigo jajen ita ma ta fita, a fusace tace "Don Allah ki dena tanka masu Umma, ki nuna ke baki ma san jajen uban me suka shigo yi maki ba, wallahi banda ke in ban ci kaza kazan mace ba ta sake shigo mana dakin nan ace ba ni ba, wannan ai iskanci ne" Umma tace "To ya kike son inyi Farida? kinga ai muna mutunci sosai da su shine har ya sa suke shigowa, duk warce kika ga ta shigo dakin nan to muna mutunci sosai ne da ita, kin ga ai bazan masu rashin mutunci ko wani abu ba, wanda ya yaΙ—a labarin a garin ai shine vabvan munafuki ba wanda ya shigo jajenta maka ba, kuma naga dai ba kan Khaleesat farau ba mutuwar aure" Aunty Farida ta mike tace "Ban taΙ“a ganin inda ake shigo ma mutum jajen mutuwar aure ba sai a garin nan, kuma wannan ba komai bane banda salon gulma da munafurci" Daga haka ta fice daga dakin zata duba ruwan zafin da ta dora kan wuta, Umma ta kalli Khaleesat da tayi backing dinsu tana bacci, ta kai hannu ta dafata, tayi kasa da murya tace "Har yanxu baccin dai Khaleesat?" Juyowa Khaleesat tayi tana murza ido, sai kuma ta mike zaune, Umma na kallonta tace "Jiya da daddare baki ci abun kirki ba, ki je ki wanke baki ki zo ki karya, ga wainar shinkafa na sa an amso maki tun daxu, kar ya huce" Khaleesat ta jawo hijab dinta ta saka sannan ta sauka daga kan gadon, ta tafi gun akwatinta da ta dawo da shi daga America ta duΖ™a ta bude jakar ta ciro Shower gel dinta da sponge, sai toothpaste da Brush, Umma dai kallonta kawai take har ta mike zata fita daga dakin Umma tace "Tunda wanka za kiyi kice Farida ta juye maki ruwan zafin, tana waje" Khaleesat tace "To Umma" Daga haka ta fita daga dakin Umma ta bi ta da ido, Khaleesat bata ko kalli inda kishiyoyin Ummanta suke ba da dukun dukun din zannuwan jikinsu kamar masu yin kuli kuli, ta jira Aunty Farida ta juye mata ruwan zafi a bucket ta surka mata sannan ta kai mata har bandaki, bayan ta shiga wankan Aunty Farida ta dora wani ruwan ta koma dakin Umma, Mama Zubaida ta taΙ“e baki tana murmushi ta kalli Mama Shatu tace "To kuma yanxu ko da uban me za ayi mana takama?" Mama Shatu ta kwashe da dariya tace "In kin tambayeni in tambayi wa? Ba ke kike kokwanton maganar Malam ba da yace auren karkari ayi wata daya ya sakota, to kin dai ga kwalliya ta biya kudin sabulu, sai ki dena cewa kinyi asaran kudin ki, ji yanda hankalinki ya tashi ranan da muka je gidan da Nenne kin ga katon gida ta shiga dakin can ta fito ta shiga wancan ta fito kin zata watayawa take a gidan, ni dama ina kallon kwayar idonta nasan ubanta take ci a gidan, sam ban ga alamar kwanciyar hankali ba don duk a firgice na ganta" Mama Shatu ta sauke ajiyar zuciya ta rike haΙ“a tace "Ohhh.... Ba karatu a Amurka, ba Miji, ga zawarci, wannan asara da yawa take ni Aisha, wannan shi ne ga koshi ga kwanan yunwa, an ga samu an ga rashi, ina Zahra'u zata saka ranta ta ji dadi" Mama Zubaida tace "Ke baki ga haka ya korota daga ita sai kayan jikinta ba, ko er jakar hannu da ake saka waya fa bata taho da shi ba, dama a haka ya dauketa, kuma kinga ko tsinke ba a kai mata ba dama" Duk suke kwashe da dariya har da kyakyatawa, Mama Shatu tace "Sai a dawo a ci gaba da alalan da aka watsar, don ita kanta Faridan Allah ya sa Ι—an zaman da ta dawo suka yi ba a cinye jarin nata ba, nan nan a gabanmu aka yi ta hade haden garin Ι—anwake da su kuka da kubewa za a kai ma Khaleesat ashe ashe korota zai yi, ni anjima ma zan shiga a tsam min garin danwaken don naga da yawa suka yi" Tana dariya ta kare maganar, Mama Zubaida tace "Ae wallahi ko tsirara zan yi na gwammace inyi da dai Zahra'u taji dadi da 'ya yanta, in ke kin manta irin cin Ζ™ashin da Malam ya dinga mana bayan ya aurota ni ban manta ba, duk muka zama bora a gidan nan, baya ganin kowa sai Zahra'u tunda da asirinsu na buzaye ta shigo gidan, banda dai dama tun asali idonmu ya bude da Malamai ai da tuni ya sake mu tun bai samu karayar arziki ba, hatta kayan dakin da ya siya mata sai da na zaga na koma kasuwa na tambaya aka ce min nata duk yafi namu tsada, gashi yaranta su ne 'ya yan so barin Khaleesat din nan ai mun sha bakin ciki iri iri Shatu, Ita fa har Umra tayi sannan ga Hajji, mu kuwa iya Hajji kawai muka je mu ka yi tsabar ya maida mu 'yan iska" Mama Shatu ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ki bar tuna min wannan takaicin Zubaida, banda a tsaye muke ai da wani labarin ake yanxu ba wannan ba, haka mu ma muka yi ta hadata da Malam da taimakon asiri, amma shegiyar bata yi zuciya ta koma kasar su ba da ya fara cin ubanta a gidan, in sha Allahu yanxu ta fara ganin bala'i ita da zuri'arta su da jin dadi ko farin ciki har abada, hatta yan biyun nan ya kamata mu fara miΖ™a sunansu yanxu kar lokaci ya kure, don naga wani farin jinin jama'a da suke da shi, duk inda suka shiga sai an tankasu ayi ta nan nan da su" Shigowar Nenne gidan yasa suka yi shiru, duk suka gaisheta ta amsa ba tare da ta kallesu ba ta nufi dakin Umma da er ledanta a hannu, duk suka taΙ“e baki suna bin ta da kallo har ta shiga dakin, Umma da Aunty Farida suka gaida Nenne bayan ta shigo dakin, Nenne ta amsa bayan ta ajiye ledan hannunta tace "Ina Khaleesar take?" Aunty Farida tace "Ta shiga wanka" Nenne tace "Atoh dai, dama ina zata tsaya bakin cikin shege ya kasheta, harkar gabanta kawai zata ci gaba da yi kamar babu abinda ya faru, da auren wannan gansamemen mutumin da rashin aurensa ai duk daya, kuma mu muka cusa mata shi ba sonsa take ba wallahi, yanxu banda ni da ku waye yasan tayi wani gantalallen aure ko da wani ya fito yana son ta, banda dai gulma tayi ma jama'ar Mariri katutu, ai kawai ce ma Ali zan yi ya siyar da gidan nan da nawa gidan mu koma ko Rijiyar Lemo ne" Dukawa tayi ta kwance ledan da ta ajiye tace "Gashi nan, kasuwa na aiki almajirina ya siyo min kayan ciki me kyau nayi mata farfesu ta sha ta mance abinda ya dameta, saki ai ba kanta farau ba, mu ma duk ai an taΙ“a sakin mu, uban Ali saki nawa ne bai min ba, sai da igiya daya ya rage mana sannan muka nutsu muka zauna har mutuwa ta raba" Wata mata ce tayi sallama bakin kofar dakin Umma, Umma ta amsa mata, matar ta shigo tana gyara yakunannen gyalenta, ganin Nenne ta duka har kasa ta gaisheta, Nenne ta amsa tana rufe farfesun da ta kawo ma Khaleesat kar matar ta barbade farfesun da gyalenta, Bayan matar sun gaisa da Umma tace "Ashe abinda ya faru kenan Ummansu Khaleesah?" Nenne ta juya ta kalleta tace "Me ya faru?" Matar ta langwabar da kai cikin rashin jin dadi tace "Mutuwan auren Khaleesah Nenne" Nenne ta mike tsaye tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, mutuwar auren wace Khaleesar? A ina kika ji auren Khaleesah ya mutu? Na shiga uku na lalace, wato matan Mariri baza ku canza halin ku na tsugudidi ba ko? To daga ke har wanda ya gaya maki kun ci kaza kazan ku yan iska kawai shegu, tashi ki fita ki ba mu waje, sai dai ki ga mutuwar aure a dakin ki ko na uwar ki, kaji min mata dai munafuka, uban mutuwan auren Khaleesah, fita ki bamu waje" Da sauri matar ta fita daga dakin ta saka takalmi wari da wari ta bar bakin kofar, Nenne na huci ta kalli Umma tace "Ke kuma Las spika ki ka dauka kike shelan an saki Khaleesah?" Aunty Farida ta tabe baki tace "Ina fa Nenne, mu ma kawai gani muka yi ana ta shigo mana tun da gari ya waye, wai an zo Jaje, wa enda suka fitar da labarin ai su ne babban munafukai" Nenne na share zufan goshinta tace "Shatu da Zubaida kenan, babu me fitar da zancen nan sai su" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, kafin ta fito dama su Mama Shatu duk sun shige dakunan su da sauri bayan sun ji abinda Nenne tayi ma matar da ta fita daga gidan, nan tsakar gida Nenne ta tsaya babu abinda ta manta bata gaya masu ba, zagi kam sun sha har sun gode Allah, Allah ya isa shima tayi masu kwando kwando, daga karshe tace "Kuma in har Ali ya dawo gidan nan anjima bai dau matakin fitar masa da sirrin gida da ku ka yi ba wallahi sai dai ya zaba ko ni ko ku, da dai in zauna da surkai magulmata munafukai gwara in sallame ma duniya Ali in shi bazai sallama maku ba, to ai ita Khaleesar ta samu mashinshini har tayi auren ta fito, ku kuma da naku 'ya yan ke zube kaman gwanjo babu mataya fa? Dama nace ma Ali in har bazai bada su sadaka ba to ni a dena nuna su ace jikokina don kunya nake ji, ko kuma in tattara in bar masa Maririn in har bazai samar ma narka narkan 'ya yanku mafita ba, yanxu in na Jera da Labeebah ba sai ace ita ta haifeni ba, sannan kwata kwata basa wuni a gidan nan ban san inda suke zuwa ba, sai mutum ya shigo sau dari bai gan su sau biyu ba" Khaleesat ta fito daga bandaki tana rike da Shower gel dinta ta nufi dakin Umma, Nenne ta bi ta a baya tana cewa "Kin fito Khaleesah, mu je ga farfesu can na maki" Sai da suka shiga dakin sannan Khaleesat ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace "Kar fa ki ce zaki sa damuwar shegen a ranki kin ji? Allah ne ya dubemu ya rabu dake cikin aminci bai maki wata illa ba, dama kuma ance min uwarsa har tsafi take yi, kinga hada zuri'a da irin wannan mutane ai abun tsoro ne, kar ki saka komai a ranki, rabuwan shi ne mafi alkhairi a gare ki dama an gaya min" Khaleesat dai ta zauna gefen gadon Umma tana shafa cream dinta, Nenne na kallon Umma tace "Ke kuma duk wanda ya shigo maki jaje baki koresa ba Allah ya isa kema, ai mutum daya na shigowa kika rufe ido kika koresa komawa zai yi ya sanar ma sauran, shikenan babu wanda zai sake shigo maki, ni kin ga tafiyata inje in nemi abinda zan ci da rana" Daga haka ta fice daga dakin. Bayan Azahar Khaleesat na zaune kan darduma da qur'ani a gabanta tana karantawa a zuci, sai ga Safiyyah ta shigo dakin Umma da sallama, Khaleesat ta rufe Al-qur'anin ta daga kai tana kallonta tana murmushi, ji tayi kamar all her worries are gone ganin Safiyyah, Safiyyah ta ajiye handbag dinta ta zauna edge din katifar dakin tana kallon Khaleesat a sanyaye, gaba daya ta kasa ce mata komai, Khaleesat ta mayar da Al-qur'anin Aunty Farida gefe sannan ta mike ta koma kusa da Safiyyah ta zauna tana kallonta har sannan murmushin fuskarta bai Ι“ace ba tace "I miss you so much" Hawaye ne ya zubo ma Safiyyah a ido don kawai ta kasa daure hakan, Khaleesat ta sauke idonta kasa, sai ga hawayen ita ma a idonta, rabonta da zubda hawaye tun jiya a gaban Abbanta, bayan kuma ta shigo ta kwanta bata sake yarda tayi kuka ba duk da kusan yanda taga rana haka taga daren ga zafin da zuciyarta ya dinga mata, Safiyyah ta rungumeta tace "It's fine Khaleesat, Allah ya saka maki abinda yayi maki" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Safiyyah ta goge idonta don taga alamar kukan da take ne yasa Khaleesat kuka, Safiyyah ta dago kanta tana kallonta tace "Su Umma fa?" Khaleesat tace "Sun je gaisuwa ne anyi rasuwa dazu a unguwan" Safiyyah tace "Allah sarki, Allah ya ji Ζ™an musulmi" Khaleesat tace "Ameen, ya su Mama fa?" Safiyyah tace "Duk suna lafiya lau, tace in gaisheki, bayan mun gama waya daxu tace in kira mata ke, na sake kiran wayar Aunty Farida naji a kashe" Khaleesat tace "Ehh babu caji ne, ta bada a kai mata wajen caji" Safiyyah tayi shiru, bata son yi ma Khaleesat maganar da zai kara sa taji ciwo a ranta, amma duk da haka calmly tace "Saki nawa yayi maki?" Khaleesat ta buda manyan idanuwanta tace "Kawai ce min yayi ya sakeni" Safiyyah taji bakin cikin ba saki uku yayi mata ba, don ita ba kukan bakin cikin sakin da yayi take ba, a'a bakin cikin mayar mata kawa bazawara da yayi ne babban bakin ciki da takaicinta shi ne yasa har ta zubda hawaye, a gida ma kukan da tayi kenan don taji ciwon abun sosai, Khaleesat ta kalli inda Aunty Farida ta ajiye Envelope din da Drivern gidan su Abdul ya kawo tace "Ga ma can takardan ya aiko" Safiyyah ta juya ta kalli Envelope din, mikewa tayi ta dauko ta dawo ta zauna ta ciro takardan ciki, ita dai Khaleesat kallonta kawai take don har sannan bata duba abinda ke jikin takardan ba, daga Aunty Farida har Umma babu wanda yace mata saki uku ne, jiya kuma da Nenne ke ta hayaniya a tsakar gida bayan an kawo takardan Khaleesat na kwance duk bata san abinda ake ba don abubuwan da suka dameta daban, Safiyyah ta kalli Khaleesat da sauri tace "Saki uku ne ai a takardan" Khaleesat ta amshi takardan a hankali tana dubawa, after some seconds ta kalli Safiyyah tace "Wannan ai ba rubutun sa bane" Safiyyah ta hade rai tace "Do we care?? Ba dai shi aka kawo mana ba, kinga ai da shi za mu yi aiki, don da kika ce saki daya ne sai da gabana yayi mummunan faduwa don matsiyacin zai iya dawowa yace ya maida ke mu shiga uku, amma tunda ga takarda an rubuta saki uku a jiki shikenan an wuce wajen, Alhamdulillah" Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah ta ajiye takardan ita ma tana kallonta, can a hankali Safiyyah tace "I don't understand you Khaleesat, ko dai bakin ciki da sakin da Abdul yayi maki ki ke? Kin yi give up kan cewa zaki zauna zaman har abada da shi ne? Pls let me know first so that i will watch my words" Khaleesat tayi murmushin takaici tace "Dukan yau daban, na gobe daban, zagi, hantara cin mutunci, living with hunger...." Kasa ci gaba Khaleesat tayi ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza kai, Safiyyah ta rungumeta tace "Allah ya saka maki, Allah ya saka maki cikin gaggawa, in sha Allahu sai yaga karshensa tun ba aje da nisa ba, in sha Allah sai hakkin ki yayi tormenting dinsa har karshen rayuwarsa, komin lalacewan gidanku baza a doke ki ba balle a zage ki ko a hantare ki, uwa uba a bar ki da yunwa, In anyi duniya don manzon Allah sai Allah ya nuna ma Abdul iyakansa, wato punching bag ya mayar dake a gidan, kalli yanda kika rame kalanki ya disashe kamar ba ke ba, dubi yanda duk kika fita hayyacin ki, wallahi hakkin ki bazai taΙ“a barin Abdul ba, ki kwantar da hankalinki ki cire ko wani damuwa a ranki ki dau hakan a kaddarar rayuwarki" Kai kawai Khaleesat ke gyada mata hawaye masu zafi na zuba idonta, Sosai Safiyyah ta dinga bata words of encouragement tana kwantar mata da hankali, har Khaleesat taji sanyi sosai a ranta, taji ta samu relieve din abubuwan da suka tunkushe mata a rai tun jiya, a haka Umma da Aunty Farida suka dawo suka samesu, Umma ta ajiye masu Ι—anwaken da ta siyo a makota sanin Khaleesat na son Ι—anwake, ba laifi Khaleesat ta ci Ι—anwaken me yawa tare da Safiyyah, dama duk yau ta kasa cin komai, ko farfesun da Nenne ta kawo mata kaΙ—an ta iya ci, amma sai ga shi ta ci Ι—anwaken sosai, sai kusan karfe shidda na yamma Safiyyah ta bar gidan, with the relieve that tayi consoling kawarta tunda gashi har tana dariya ta baro ta, sallan magrib kawai Safiyyah tayi ta jawo wayarta tayi dialing number Housemate, wanda rabon su yi magana tun sanda ya gaya mata abinda Khaleesat tayi masu shi da Ajay.

[6/30, 11:27 AM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Jay na zaune dakinsa wajen karfe tara na dare yana rike da mug din coffee da yake ta stirring for almost 5 minutes now ya kasa sha, ya daga kai jin an bude kofar dakin, Ajay ne ya shigo ya nufi inda Laptop dinsa yake, shi dai Jay kawai bin sa yayi da ido har ya kunna laptop din ya duka yana dube dube a cikinsa, after almost 2 minute ba tare da Ajay ya kallesa ba yace "Resend me those files u sent yesterday via Email" Jay bai ce masa komai ba, hakan yasa Ajay ya juya yana kallonsa, mikewa yayi ya nufesa, ya cire masa head warmer din kansa ya saka a nasa kan yace "Hey is everything Okay? Me yasa baka fito ka ci abinci ba?" Jay ya mike ya fixge Head warmer dinsa sannan ya koma ya zauna yace "Kai dai ba ka ci ba, cire min Jacket dina Ajay, I can't remember dashing you the Jacket...." Ajay na gyara Jacket din jikinsa ya koma ya ci gaba da abinda yake yi a laptop din Jay, after a while Jay ya ajiye Mug din hannunsa, speaking slowly yace "I spoke to Safiyyah not long ago"  Ajay ya kallesa yace "Wacece haka?" Jay yace "My Housemate's friend" Banza Ajay yayi masa ya ci gaba da duba abinda yake yi a laptop, calmly Jay yace "And she...." Ajay ya dakatar da shi sounding pissed off yace "Plss Jay, i am not interested, do not provoke me this night, banda file da nake nema a laptop dinka baza ma ka gan ni a dakin ka da daddaren nan ba" Jay ya mike yace "Whether you are interested or not, Safiyyah ta gaya min gayen ya saki Halysaah" Ajay ya juya ya kalli Jay babu ko kiftawa, after some seconds ya maida idonsa kan laptop din gabansa sai dai bai ci gaba da operating laptop din ba, Jay ya karasa kusa da window din dakinsa ya bude drape din ya rungume hannunsa yana kallon tiny snow din dake zuba kasa, Ajay yace "What did you expect? Were you expecting less? He's satiated his craving, and that is all that he is after, yayi satisfying Lust dinsa" Yana kai wa nan ya rufe Laptop din kawai ya nufi kofa ya fice daga dakin, shi dai Jay da ido ya bi sa kawai, can ya sauke wani ajiyar zuciya ya karasa ya rufe kofarsa da Ajay ya bari a bude. Khaleesat na zaune gaban Coal pot wajen karfe sha biyun rana tana ta fifita gawayin da ta hura zata dora girkin rana at the same time tana gyara waken farantin dake cinyanta, Ummanta ce zata dora girkin don Aunty Farida ta fita kasuwa shi ne ta amshi girkin tace zata yi, shinkafa da wake da mai da yaji ne za su yi da rana, babu kowa a gidan sai ita da Umma don su Mama Zubaida da Mama Shatu sun tafi gidan biki ko girkin siyarwa basu yi ba ranan, Umma ma gidan Nenne take shirin zata je ta kai mata kubewan da ta tambayeta ranan friday, Ι—aga kai Khaleesat tayi jin sallaman Safiyyah a compound din su, ta dinga kallonta bata ko kiftawa don bata ce mata zata dawo yau ba, Safiyyah tayi murmushi ta karasa har inda take sannan ta dau kujeran tsugunno da ta gani a tsakar gidan ta zauna tana kallon Khaleesat tace "Sannu da aiki" Khaleesat ta Ι—an bude ido tana murmushi tace "You didn't tell me you were coming today Safiyyah" Safiyyah tace "Eh nima ban zata zan zo yau ba, dama ranan Monday ko Tuesday nace maki zan dawo ai" Umma ce ta fito daga dakinta, Safiyyah ta gaisheta da ladabi, Umma ta amsa da fara'a tace "Ya su maman ku?" Safiyyah tace "Sun ce in gaishe ku Umma" Umma tace "Allah sarki, to ina amsawa, bari in je gidan Nenne in dawo yanxu" Safiyyah tace "To sai kin dawo Umma" A haka Umma ta fita daga gidan, Khaleesat ta dora ruwan girkin ta ajiye waken da ta gyara sannan suka shiga dakin Umma da Safiyyah, Safiyyah na kallonta tace "Don Allah ki daure ki dinga cin abinci Khaleesat, kin ga yanda kika rame kamar ba ke ba kuwa" Murmushi kawai Khaleesat tayi tace "To ni dama kiba gareni Sophie?" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Even though, yanxu raman tayi yawa wallahi, ji fa sai idanuwa da dogon hanci kawai" Dariya kawai Khaleesat tayi bata ce mata komai ba, Safiyyah na kallonta tace "Ba dadewa zan yi yau ba Khaleesat, aikoni aka yi wajen ki" Da mamaki Khaleesat ta dinga kallonta, sai kuma tace "Wajena kuma? Wa ya aiko ki" a hankali Safiyyah tace "Ur Housemate" Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta dinga kallon Safiyyah babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Sai dai kiyi hakuri, ni dai na gaya masa abinda ya faru, And...." Sai kuma Safiyyah tayi shiru, Ita dai Khaleesat kallonta kawai take don ta kasa cewa komai tana jin hawaye na taruwa gradually a idonta, a hankali Safiyyah tace "He sent me money for ur flight ticket back to America, and you tuition fee for this semester, ya ce zai samar maki wani apartment din for the one year that is remaining for us...." Hawayen dake makale idon Khaleesat ya zubo, ta kasa ce ma Safiyyah komai, bata san sanda ta fashe da kuka ba sosai, ita dai Safiyyah tayi shiru tana kallonta cause she wasn't expecting less, sai da Khaleesat tayi kukanta me isarta sannan tana girgiza kai muryarta na rawa tace "I don't think za a bari in koma in ci gaba da karatu Sophie" Safiyyah tace "Ban gane ba? Saboda me baza a bar ki ba?" Khaleesat na goge idonta da kyar tace "Saboda Abdul ma da aka bari ya kai ni karatu babu yanda za mu yi ne hakan ta faru, we had no choice then, dalilin haka har sai da Ummata ta samu hawan jini, kin ga yanxu kuwa ai babu wani hujjan da zai sa a sake barin wani ya ci gaba da sponsoring dina a wata kasar" Safiyyah tace "I don't understand Khaleesat, yanxu me kike nufi? So kike kiyi asaran shekarun da kika yi a makarantar kenan?" Hawaye na zuba idon Khaleesat ta girgiza mata kai tace "A'a Sophie, but iyayena za su ji tsoron sake yarda wani ya dau dawainiyata try to understand me" Safiyyah tace "Zan jira har Umma ta dawo daga gidan Nenne in mata magana, ke kam bani da sauran magana dake, cause haushi zaki ci gaba da bani idan na biyeki, banda haka ta yaya ga dama ta samu amma kina neman misusing opportunity din, did you even know what you are saying?shekara daya kacal fa ya rage maki Khaleesat? Dropout kike son ki zama ko me? Ai wani abun mutum ba shi yake bargaining ma kansa hakan ba, you never bargained for all this Khaleesat, situation ne kawai, kina tunanin har a tashi duniya akwai ranan da Yaya Jawwad zai bude baki yace ai ya dau nauyinki a makaranta? Kina ganin Jawwad yayi kama da mutumin da zai maki gori wataran? Ai wallahi daga shi har Cousin dinsa sun girmi hakan, they are too classy for that, Kin zata kowa mahaukaci ne mara aikin yi kamar Abdul? Haba wallahi har kin bata min rai, ban taΙ“a tunanin zaki nemi kiyi turning down din offer dinsa ba, shi fa taimako kawai yayi saboda yana da halin yin hakan, duba da kin kusa gamawa kuma yasan duk abinda ya sameki, amma sbda rashin tunani irin naki kina neman gwalesa, i was thinking zaman da kika yi da Abdul zai sa ki Ι—an canza wasu tunaninki marasu ma'ana, ko kuma in ce Childish tunani" Ita dai Khaleesat hawaye kawai take sosai ta kasa ce ma Safiyyah komai, tasan duk bayanin da zata mata bazata taΙ“a fahimtar ta ba, Safiyyah ta ciro wayarta ta fara dannawa bata sake ce ma Khaleesat komai ba don da gaske ta Ι“ata mata rai, after a while Khaleesat ta mike zata je ta wanke wake ta zuba a ruwan da to dora kan wuta, bayan ta gama wanke waken ta zuba ta rufe tukunyar tayi tagumi tana zaune gaban Coal pot din, a haka Umma ta shigo gidan ta sameta, Khaleesat ta sauke hannunta daga tagumin da tayi tana kallon Umma da ta nufota, tace "Umma kin dawo" Umma tace "Na dawo, ina Safiyyar?" Khaleesat tace "Tana ciki" Umma tace "Shi ne kika bar ta ita kadai" Khaleesat tace "Yanxu na fito in zuba wake ne" Aunty Farida ce ta shigo gidan da abubuwan da ta siyo a kasuwa, Umma tayi welcoming dinta sannan ta karasa dakinta ta shiga ciki da sallama, Safiyyah ta amsa tana mata sannu da zuwa, Umma ta cire Nikab da hijab dinta ta linke tace "Bata baki ko ruwa ba?" Safiyyah tayi murmushi tace "Umma ni ke nake jira ma tafiya zan yi" Umma ta zauna tana kallonta tace "To gani Safiyyah, lafiya dai ko?" Safiyyah tace "Lafiya lau Umma" Kafin Safiyyah ta ce komai Aunty Farida ta shigo dakin, Safiyyah ta gaisheta tana murmushi, Aunty Farida ta ajiye kayan hannunta tana amsa gaisuwan Safiyyah da fara'a, Umma dai kallon Safiyyah take tana jiran jin abinda zata ce, Babu bata lokaci Safiyyah ta fara yi ma Umma bayanin duk yanda suka yi da Housemate din Khaleesat, ita dai Aunty Farida na tsaye ita ma tana sauraron bayanin Safiyyah, Umma ta Ι—an yi murmushi bayan Safiyyah tayi shiru tace "Allah sarki, mun gode sosai da kulawan sa, amma dai ki maida masa kudinsa Safiyyah, don ko babanta ma bana jin zai yarda, Abdul ma da ya kai ta karatun ba mu da yanda muka iya ne Safiyyah, Allah ya amfana abinda ta samu" Safiyyah was speechless, Aunty Farida ta dinga kallon Umma jin abinda tace, can tace "Allah ya amfana abinda aka samu kuma Umma? Shikenan fa tayi asaran karatun gaba daya idan bata karasa ba, kamar ka fara gini ne fa ya ruguje har kasa ya rage Foundation, ai kin ga kuwa baza kace Allah amfana abinda aka samu ba" Umma ta kalli Aunty Farida tace "Farida kin fi kowa sanin ban taΙ“a goyon bayan fitar Khaleesat karatu waje ba tun asali, daga ni har mahaifinta babu yanda muka iya ne, don haka Khaleesat bazata koma Amurka da sunan karasa karatu ba, ashe ma bamu dau darasin abinda ya faru a baya ba kenan" Aunty Farida bata sake ce ma Umma komai ba ta hau fiddo abubuwan da ta siyo a kasuwa, Ita ma Safiyyah tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, Umma na kallon Safiyyah tace "Ki masa godiya kawai ki mayar masa da kudinsa Safiyyah, Allah ya dubi niyyarsa na alkhairi ya saka masa, ba wai ni kadai ba, hatta Mahaifinta ma ba yarda zai yi ba Safiyyah, cutar da ita da muka yi da farko ma da muna da wani dubaran da baza ayi haka ba, kin ga in mu iyayen arziki ne ai baza mu yarda ayi na biyu ba" Aunty Farida ta mike tace "To shi Umma ce maki yayi da wata manufa zai biya mata kudin karatun har kike tunanin za ayi na biyu? Shi fa Abdul duk abinda yayi yana da manufar yin hakan duk mun sani, ba haka kawai ya dauketa ya kai ta karatu ba...." Umma ta dakatar da ita tace "Ban ce shi wannan bawan Allahn yana da wata manufa ba amma dai kam Khaleesat bazata koma Amurka ba Farida" Aunty Farida bata sake tanka Umma ba ta fitar da albasan da ta siyo zata je ta shanya a bakin kofa, Safiyyah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya a hankali tace "Toh shikenan Umma, ni zan koma gida, dama abinda ya kawo ni kenan" Umma tace "To ki gaida mutanen gidan Safiyyah mun gode kwarai, shi ma ki yi masa godiya don Allah" Safiyyah tace "To Umma" Jiki a sanyaye ta mike ta fita daga dakin, Aunty Farida ta dau hijab dinta da ta rataye a igiya tayi ma Safiyyah alamar su je waje, ita dai Khaleesat na zaune inda take bata tashi ba don duk taji conversation din Safiyyah da Ummanta, Aunty Farida na fita kofar gida da Safiyyah tace "Safiyyah kar ki yarda ki gaya masa abinda Umma ta ce, ki bari Babanta in ya dawo anjima zan samesa in yi masa magana" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya tace "To Aunty, don Allah ki yi convincing dinsa shi ma, It will be very sad idan aka ce bata karasa karatun nan ba, shekara daya fa kawai ya rage mana" Aunty Farida tace "In sha Allah zan yi bakin kokarina, kuma Khaleesat zata ci gaba da karatun ta" Safiyyah tace "To Aunty, gobe da safe zan kira ki sai inji yanda ku ka yi da Baba" Aunty Farida tace "To babu damuwa, ki gaida gida" a haka suka rabu Aunty Farida ta juya ta koma cikin gida... Khaleesat ta gama girkin da take bayan ta kashe gawayin tayi alwala ta shiga dakin Ummanta, tana idar da sallah ta kwanta, gaba daya taji damuwarta ya dawo sabo fil maganar Housemate dinta da Safiyyah ta kawo mata, Umma na kallonta tace "Baza ki ci abincin bane yanxu?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Sai anjima" Ita dai Aunty Farida linke kayan su Islam take don tun bayan tafiyar Safiyyah bata ce ma Umma komai kan maganar da Safiyyah ta kawo ba sanin Umma bazata taΙ“a fahimta ba. Bayan Magrib Aunty Farida ta samu Malam Ali yana zaune kofar dakinsa, bayan sun gaisa yace "Amma ba Lagos kika zo gaya min zaki koma ba Farida?" Murmushi kawai Aunty Farida tayi don in akwai abinda ya tsana zamanta Lagos yayi fadan har ya gaji, ta kauda tambayar da yake mata tace "Magana na zo mu yi kan Khaleesat" Yayi shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace "To ina sauraron ki" Cikin nutsuwa Aunty Farida ta sanar masa batun da Safiyyah ta zo da shi daxu da rana, Malam Ali ya girgiza kai yace "Ashe ban daddara ba kenan Farida, na yi tunanin duk mun dau darasi kan abinda ya faru wanda duk nafi kowa laifi a ciki...." Aunty Farida ta kwantar da murya tace "Ae wancan issue din da wannan ba daya bane Malam, shi fa Abdul da isa da gadara ya turata karatu Amurka kuma babu yanda muka iya haka duk muka sallama masa domin zaman lafiyanmu da naka, Abdul da manufarsa na tura ta karatu, shi ko wannan bawan Allahn babu wata manufa a ransa, saboda Allah zai biya mata ta karasa karatun kar tayi asaran shekarun da tayi, iya shekara daya fa ya rage mata Malam, ka san muhimmancin karatun nan balle ka kushe komawarta America ta karasa, in kowa zai kalubalanci haka ai banda kai Malam, don Allah ka duba wannan lamari, kuma shi wannan bawan Allahn da ya ce zai dau nauyin shekara dayan da ya rage mata su ne fa suka dau maka lauya har aka wanke ka a kotu aka kashe maganar bashin ka da Baban Abdul...." Malam Ali yayi murmushi yace "Ai nayi appreciating hakan da suka min kuma kullum ina saka su a addu'ata, amma babu zancen komawar Jiddah America karatu Farida, kiyi hakuri a bar batun nan gaba dayanta, we shouldn't be a bad parent for the second time saboda son abun duniya, tayi hakuri in Allah ya hore min sai in biya mata tayi Jamb ta nemi ko BUK ko Northwest, duka duka shekarunta nawa suke? Ai lokaci bai kure mata na karatu ba Farida, kuma ko aro ne zan nema in biya mata in sha Allah, don haka bana son a sake tada zancen ci gaba da karatun ta a America" Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, after a while tace "To shikenan, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi" Yace "Ameen" Mikewa tayi ta bar wajen rai babu dadi. Washegari wajen karfe tara Aunty Farida ta gama shirin da take, Umma dake kallonta tace "Ina za ki ne?" Aunty Farida na dora Nikab dinta kan Hijabin jikinta tace "Ba nace maki zan je gidan Abida ba shekaranjiya" Umma tace "Shi ne zaki mata sammako?" Aunty Farida tace "Jiya tace min bata da lafiya ne, kuma ina son in dawo da wuri in wanke kai na" Umma ta tabe baki tace "To sai kin dawo" Ita dai Khaleesat juya kokon gabanta take a hankali tana sha ga dumamen tuwo shi ma a gabanta, da kyar take shan kokon, dumamen kuwa ta kasa ci, dama jiya da daddare ma bata wani ci tuwon ba, Aunty Farida tayi ma Umma sallama ta fita daga dakin. Nenne na gyara daurin dankwalinta tayi kasa da murya tace "To ke banda abun ki ai Zahra'u Jahila ce Parida, matar da har yau bata da wayewa kanta a murfi yake kamar matar kauye, ita ta wani san maki muhimmancin karatu kina ganin mata haka kara zube, gashi sai yanda kazaman kishiyoyi suka yi da ita sun mayar da ita Bora? Ai bari ki ji Parida, Zahra'u a yanxu dai ita daga tuwo sai bautan Allah kawai ta saka a gaba, babu ruwanta da wani ci gaba na duniya ko kyale kyalin duniya, ta riga ta amince ta kare rayuwar ta a haka in dai zata ci tuwo tayi bautar Allah, shi yasa kullum zaki ganta rike da carbi a kuturin dakinta da ko Ceiling din arziki babu, ni bana ma jin Zahra'u na yi ma Ali addu'an Allah ya dawo masa da arzikinsa don in tayi hakan gani zata yi kamar ta butulce ma Allah, duk tunaninta fa haka Allah ya so ganinsu cikin baΖ™in talauci, gani zata yi in tayi ta ma Allah magiyan ya yaye masu talauci kamar butulci tayi bata gode da ni'imarsa ba tunda tana samun tuwo ta ci, to irin tunanin yayarki kenan Parida, in ba haka ba ta yaya zaki dinga yi ma er cikinki bakin cikin karasa karatu ta taimake ku a rayuwa ta cire ku daga kangin talauci? shikenan kuma don kai jahili ne sai ka rasa sanin abinda ya kamata? Har wani kwambo fa take da jahilcin ta da rashin wayewa, ki bar ni da su kawai zan yi maganinsu daga Alin har Zahra'un, da can uban me yasa suka bari aka kai ta Amurkan in har da tsoron Allah a lamarinsu daga ita har Alin? Wato sai yanxu suka zama iyayen kirki masu tsoron Allah ko? To zan yi maganinsu gaba daya, in dai karatu ne kamar Khaleesah taje Amurka ta karasa in har ina numfashi, Allah ya kai mu anjima da yamma, Alin ai zai dawo daga zaman kashe wandon da yake yi a kasuwa, zan je har gidan in samesa inji ko na tauye masa karatunsa duk da talauci na, in de ni na amince taje to ko wani Ι—an iska ma kar ya amince" Nenne na kai wa nan ta mike ta jawo kofar dakinta ta kulle da kwado, sannan ta dau mayafinta sabo dake rataye saman igiya ta yafa, ta dau handbag dinta ta saka makullin kofar a ciki, ta zura takalmanta ta nufi kofar fita daga gidan tana taku dai dai don sabuwar atamfa ce a jikinta, Aunty Farida ta bi ta da kallon mamaki tace "Wai fita zaki yi ne Nenne?" Ba tare da Nenne ta juyo ba tace "To me zan maki, anguwa har uku zan je yau da kika gan ni, bazan zauna a banza ki bata min lokaci ba, in ba gulma ba ganinki nake yi a gidana, ni dai in kin gama zaman kin fito ki ja min kyauren gidana kar almajirai su shiga su min sata" Daga haka Nenne ta fice daga gidan, murmushi Aunty Farida tayi ta mike ta nannade mata tabarmanta ta ajiye sannan ta daura nikab dinta, bin bayanta tayi da sauri don jadadda mata kar tace ita ta zo ta gaya mata maganar don tasan tsaf sai yayarta ta kullace ta.

[6/30, 6:59 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Wajen karfe shidda na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Ummanta tana yanka mata alaiyahu a cikin roba, stepsisters dinta Labeebah da Lamisah na can zaune su ma daga bakin kofar dakin Mama Shatu da kawayensu sai hira suke suna shewa duk sun cika tsakar gidan kai kace gidan biki ne, Mama Shatu da Mama Zubaida su ma suna tsakar gidan don da su ake hiran da kawayen 'ya yan nasu, magana daya biyu sai su kwashe da dariya, yawanci kuma duk habaici suke jefa ma Umma da Khaleesat, ita dai Umma tana zaune gaban Coal pot tana kwashe tuwon masara da ta gama tukawa, Aunty Farida kuma ta tafi Hotoro tun bayan la'asar da su Noor, Nenne ce ta shigo gidan rataye da jakarta a kafada, lkci daya gidan yayi tsit, a takaice Nenne ta amsa gaisuwan da su Mama Zubaida da Lamisah da kawayensu ke yi mata ta nufi gun Umma tace "Zahra'u Alin ya dawo ko be dawo ba?" Umma ta gaida Nenne sannan tace "A'a bai dawo ba tukun Nenne, sannu da zuwa" Nenne tace "Kin gan ni nan daga Sheka nake daga can na tafi Ɗan Agundi, ni ce har Na'ibawa yau, tun safe na bar gida sai yanxu nake dawowa 'yan adaidaita sahun kano dai sauransu yawo da bindiga kawai...." Murmushi kawai Umma tayi tana ci gaba da kwashe tuwon da take yi, Nenne ta jawo kujera ta zauna tace "Gidan Katime me Aya na tafi a Sheka, in gaya maki me Aya dai kafafuwanta sun mutu murus Zahra'u, ko tashi bata iya yi, babu yanda ban yi da matar nan ta rage cin nama ba amma taga kamar bakin ciki nake mata don mijina baya kawo min, to yau ni da ban ci nama ba gani da kafafuwana biyu rass, ita kuwa duk sun mutu, wai tana ganina ina taku dai dai na shigo gidan sai ta fashe da kuka, ni dai bata ban tausayi ba wallahi, sai kinga yanda take mana fafa da nama lokacin, kullum kya ji kamshin tafashen nama a gidanta, mu sai dai mu watsa er daddawa a miya" Umma na girgiza kai tace "To Allah Ubangiji ya bata lafiya" Nenne tace "Ba batun Allah ya bata lafiya ba, ai duk kafafuwan sun rube, da kyar in baza ace za a yanke mata su ba tunda ko motsa su bata iya yi " Su Mama Zubaida gaba daya kunnuwansa na kan labarin da Nenne ke ba Umma, Malam Ali ne ya shigo gidan da sallama, Nenne ta juya tana kallonsa, can ta mike ta nufesa tace "Yanxu Ali baza ka hakura da fita kasuwar nan ba tun da ba wani abu kake yi a can ba sai zama cikin rana da iska? Ka dubi yanda duk kayi bakikirin kamar baka taΙ“a haske ba a rayuwarka Ali, tunda ba aikin fari gareka ba balle baΖ™i a kasuwar ka hakura da zuwa mana" Gaisheta kawai yayi ya dau buta zai debi ruwa ya fita waje ya zauna ya jira Magariba, Nenne ta tabe baki tace "To wajen kai da matar ka Zahra'u na xo" Umma ta juya tana kallon Nenne jin abinda tace, Shi ma ya tsaya yace "To lafiya dai ko?" Nenne tace "A ina lafiyar take, ba sai kun nemi zaman lafiyar za a zauna lafiya ba, labari na samu wai masu kare hakkin 'yan Adam sun zo gidan nan sun ce za su ci gaba da daukar nauyin karatun Khaleesat a Amurka saboda tausayin abinda tsinannen mutumin nan Awdul yayi mata, to amma wai saboda kai da Zahra'u yan bakin ciki ne sai ku ka gwalesu ku ka koresu, da wanne ku ke son yarinyar ta ji fisabilillahi? Da mayar da ita bazawara da aka yi tana da karancin shekaru ko kuma da asaran karatun ta da kuke kokarin yi mata? In ita Zahra'u jahila ce bata yi karatun boko ba kai ma Jahili ne Ali? Ina ne ban shiga nayi aikatau ba don kayi karatu? To wallahi ko karshen bangon duniya ne sai Khaleesat ta koma ta karasa karatun ta tunda har aka ce za a dau nauyinta babu ko sisin ku, to ina ma ku ka ga ko sisin" Malam Ali dake ta kallon uwar tasa yace "A ina kika ji wannan zancen Nenne?" Nenne tace "Labarin duniya na buya ne dama? Ina zaune yan Mariri suka zo suka tsegunta min har unguwan da naje yau...." Mama Shatu ta kalli Mama Zubaida da ta saki baki tana sauraron Nenne, Mama Zubaida ta kasa daurewa ta gyara zama cikin kwantar da murya tace "Amma Nenne na farkon ma ba a wanye lafiya ba shi ne za a sake na biyu? Dama gashi duk garin nan kallon makwaita masu son abun duniya kawai ake mana, ko ina sai zaginmu ake tun da aka samu labarin sakin walakancin da aka yi ma Khaleesat, ana ta cewa ubanta ne ya ja mata, A rayuwar nan yanxu fa in ba iyayenka ne za su yi maka dawainiya ba duk wanda yace zai dau dawainiyar ka sama ta ka to da wani abu da yake hangen zai samu a gare ka ne, Khaleesat fa 'ya mace take ba namiji ba Nenne, kuma ba komai ke rudar maza akanta ba sai kyanta da kalan fatar ta sun ga buzuwa, shi kenan saboda son abun duniya sai a zuba ido har sai yarinyar nan ta lalace tukunna, Abdul ya gama nasa ya samu abinda yake so ya sako mana ita sai kuma yanxu ace ga wani ma ya zo wai zai ci gaba da daukar nauyinta? Haba sam batun nan babu tsari a cikinta, shikenan ita kuma haka ta zama kamar Tasi...." Nenne ta kundumo wani zagi tace "Toh duk wanda ya fasa fadin abinda ke ransa akan Khaleesah Allah ya tsine masa albarka, kuma in de karatu ne kamar tayi ta gama sai dai bakin ciki ya kashe duk wani shege wallahi, ko ma ina za a kai ta a kai ta ni na amince ta je, ai ita tasan tarbiyyar da muka yi mata in ma ta gantalar da tarbiyar ita da Allah, kuma gobe gobe zan sa a kira min baΖ™ar kawar tata ta zo in gaya mata uban Khaleesah ya amince koma waye zai dau nauyinta ya dauka, taje can ta ci gaba da karatun ta, ai gwara tayi nesa da mu ko bakin cikin dake damunta a rai zai ragu, mu kanmu in tana ganinmu takaici da bakin ciki take don ba mu da wani babanci da Awdul a wajenta tunda mu muka ja mata komai, gwara ta koma ta gama karatunta ta dawo da kwalinta don bazata tashi a tutar babu ba, shi kansa Awdul din yana samun labari an samu wanda ya maidata Amurka ta ci gaba da karatu sai bakin ciki ya kusa kashe shegen, a nan kuma zai san ba a banza Khaleesah take ba farin jininta ya shahara" Nenne na huci ta juya ta kalli Umma tace "Ke kuma Zahra'u halan tallan alalen ki ke da niyyar dora mata da kike mata bakin cikin komawa ta karasa karatun? To kamar yanda kike takama kina da iko da ita nima haka tunda ni na haifi ubanta, ban ga shegen da ya isa yace bazata koma ta karasa karatun ta ba" Ita dai Umma bata ce ma Nenne komai ba, Malam Ali dai na tsaye rike da buta a hannunsa yana kallon uwarsa, can dai yace "Amma dai Nenne sam babu tsari ace mun sake barin yarinyar nan ta bar kasar nan da sunan wani zai dau nauyinta bayan duk abinda ya faru, me kike son jama'an gari su ce a kaina? Sannan nace duk sanda na samu kudi zan nema mata Jami'ar garin nan tayi, ba wasu shekaru gareta ba balle ace lokaci zai kure mata" Nenne ta kallesa da sauri tace "A gidan uban wa zaka samu kudin? Mutanen garin in sun fasa fadin abinda za su fada a kanka Allah ya tsine masu albarka, kai bari kaji Ali bana bukatar ra'ayinka ko shawararka a yanxu saboda kai ma sanda ka bi ra'ayinka ka yarje ma Awdul ya kai ta kasar waje babu wanda ka saurara ko kaji shawaransa, don haka ni ma yanzu wallahi bazan saurare ka ba Amurka ne sai Khaleesat ta koma ta karasa abinda ta fara in sha Allahu, in kuma nuna ma duniya zaka yi ni er banza ce a gareka to Bismillah" Kofar gida kawai Malam Ali ya fita da butansa a hannu, Nenne ta kalli Khaleesat tace "Maza ki hada akwatinki ki tsaya cikin shiri, in sun biya maki kudin jirgin ki kama gabanki kije kiyi abinda zai taimaki rayuwarki, zama gidan nan kadai ya ishi mutum ya fada cikin mummunan damuwa, gida kamar na 'yan sansanin gudun hijira, ga lafta laftan mata suna yawo suna doyi a cikinsa, ai ko mutum matsiyaci ne ya kasance dai yana da tsaftarsa dai dai gwargwado, amma gidan nan ga talauci ga kazanta, ina bawa zai iya rayuwa a nan idan ba dole ba" Nenne na kai wa nan ta kama hanya tayi tafiyarta, Khaleesat ta daga kai ta kalli Umma da ta bi Nenne da kallo, Mama Shatu ta mike tana kallon Umma tace "Muddin kika ce baza ki bude baki kiyi magana ba to kina ji kina gani za a mayar maki da er ki karuwa Zahra'u, wata birkitacciyar tsohuwa can kamar Nenne ce zata yanke ma er da kika haifa hukuncin abinda ya shafi rayuwarta? Ita ta tsugunna ta haifar maki er? Mu meyasa ba a mana iko akan namu yaran ba? Saboda an san baza mu dauka ba mu ba yan iska bane, to kuwa wallahi Nenne na dab da kai ki ta baro ki, mata me tabin Ζ™waΖ™walwa zaki yarda ta yanke hukunci akan 'er ki? ai in ita Khaleesar ta bude baki tace bazata je ba babu uban da zai tilastata ta je wallahi, waye bai san Nenne da kwadayi da son abun duniya ba kamar tayi sata?" Muryar Nenne suka ji ashe tana makale bata tafi ba tana jiran jin abinda za a ce, Nenne ta dinga kwalo ma Malam Ali kira, sai gashi ya shigo da sauri yana kallonta yace "Lafiya Nenne? Ai magana ta wuce yanda kika ce haka za ayi" Mama Shatu tayi wuri wuri da ido daga inda take tsaye, Mama Zubaida ta mike ta lallaba ta dau kwandon kwanon wanke wankenta ta shige daki ta sako labule, Nenne ta rushe da matsanancin kuka tana kallon Malam Ali tace "Ali yau sai dai ka zaba ko ni ko Shatu a gidan nan, kawai ka zaba ko ni ko ita, ni Shatu zata kalla ta kira me tabin Ζ™waΖ™walwa wato mahaukaciya er macukule? Ni zata ce ma me kwadayi da son abun duniya? Tunda nake me na taΙ“a zuwa gun almajirin ubanta dake bara a bakin danja nace ya bani? Me na taΙ“a rokon uwarta me shanyayyen kafa? Bata san ina labe ban tafi ba duk ina jin abinda take cewa, cin mutunci da zagi sai wanda ta manta ne bata min ba Ali, har tana gaya ma Zahra'u ni na haifar mata er da zan yanke mata hukunci akan ta? Me nayi ma Shatu da har zata yi mugayen kalamai haka a kai na? Naga dai kullum ci gabanka da na iyalan ka shi ne burina, fadi tashi babu wanda bana yi akan kai da iyalinka, amma daga karshe sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, tsofe tsofe da ni Shatu tace min me son abun duniya?" Kuka sosai Nenne take tana share idonta da gyalen jikinta, Malam Ali na kallon Mama Shatu da tayi tsuru tsuru yace "Shatu ki tafi gida, sai na neme ki" Mama Shatu ta gwalo ido tace "Ban gane in tafi gida ba Malam, wani gidan zan tafi?" Malam Ali yace "Gidan iyayenki, ki je na sake ki" Mama Shatu ta zabura tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ka sake ni fa kace Malam, na shiga uku na lalace" Labibah ta mike tana huci tace "Gaskiya Baba sai dai mu bi Baabarmu mu ma" Nenne tace "Shegiya ku bi ta mana, yunwar cikin ku kadai ma ya isheku ai" Malam Ali na kallon Mama Shatu dake rusa kuka yace "Kar in dawo in sameki a gidan nan" Daga haka ya fice daga gidan, Nenne ta bi bayansa tana goge idonta ita ma ta fita, sai a sannan Mama Zubaida ta fito tana salati tana kallon Mama Shatu dake kuka wiwi, Umma tsabar yanda jikinta yayi sanyi ta ma kasa cewa komai daga inda take zaune, Mama Zubaida na kallon Umma tace "Ke kam kinyi asara wallahi Zahra'u, ko wani bala'i ta dalilin ke da tsinannun 'ya yan ki yake faruwa a gidan nan, gashi yau saboda ke da er ki an saki Shatu, sam babu alkhairi a tare dake da zuri'ar ki Zahra'u" Umma ta juya tana kallon Mama Zubaida sai dai bata ce komai ba, Khaleesat ma ta daga kai tana kallonta, Mama Shatu na kuka sosai tace "Kuma in sha Allahu asirin da kike yi zai kare maki a gidan nan Zahra'u, yanda kika yi sanadiyyar tsinkewar igiyar aurena daya ke da er ki wallahi sai nayi sanadin naki igiyar kema, ko tsirara zan yi yawo kuwa, Ni saki daya aka min ke ukun gaba daya za a maki, kuma kamar Ali ya maida ni ne don yanxu na fara auren sa wallahi" Don mamaki Umma ta ma rasa abun ce masu ganin yanda suka juya zancen lokaci daya, yau ga fadan karfin hali tana gani kiri kiri, biyesu ma bata lokaci ne kawai a wajenta ga makota na jin su, tsam ta mike tayi shigewarta daki, Khaleesat ta mike ta bi bayanta. Washegari da sassafe Umma da Aunty Farida suka fito tsakar gida suka tarar da Mama Zubaida da Mama Shatu a tsaye suna jiran fitowarsu za a je ba Nenne hakuri, ko wanne da Hijab dinsa har kasa don sanyi ake sosai, duk abinda suka yi ma Umma jiya hakan bai sa tace bazata bi su zuwa gidan Nenne ba, Su ma din sun san ta dalilin Umman sai Nenne ta iya hakura ta sa Malam Ali ya maida Mama Shatu shi yasa Mama Zubaida da kanta ta samu Umma ko kunya babu tayi mata magana wajen karfe biyar din asuba, Mama Shatu dama a makota ta kwana ranan don sae da Nenne ta dawo ta korata har da watsi da en tsummokaran ta, sae kusan hudun asuba Shatu ta dawo gidan daga inda ta kwana, a haka duk suka kama hanya zuwa gidan Nenne da asuban. Ranan Thursday da safe Khaleesat na zaune dakin Umma tana kallon Aunty Farida dake ta jera mata kayanta da aka amso wajen guga a cikin akwati, ita dai Khaleesat har sannan ta rasa gane me take ji a ranta, farin ciki take ko akasin haka duk ta kasa ganewa, babban damuwarta yanxu bata san da idon da zata kalli Housemate dinta ba idan ta koma America, sannan gani take kamar babban burden kawai zata zame masa a can din tunda ita ba komai gare iyayenta da za su tallafa mata da shi ba idan ta koma, Ι—an kudin dake account dinta ba wani kudin kirki bane kuma da shi ta siya sabon waya with new sim card, sai few abubuwan da tasan zata bukata a can kasar, sauran kudin dake account dinta ko dubu dari da hamsin bai karasa ba, duk wannan tunanin yasa take damuwa sosai a ranta, Aunty Farida ta daga kai tana kallonta kafin ta rufe zip din jakar tace "Baki manta komai ba dai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Aunty Farida tace "A Airport din za ku hadu da Safiyyah goben?" A hankali Khaleesat tace "Eh" Aunty Farida ta kulle zip din tace "Gwara ki saki ranki kiyi abinda ke gaban ki Khaleesat, ki cire duk wani damuwar dake ranki kar ki je ki samu matsala a karatun ki, shi kuma Jawwad Allah ya saka masa da mafificin alkhairi...." Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, Aunty Farida ta mike ta dauko daya akwatin don hada few foodstuffs din da suka siyo mata da Umma wanda zata iya shiga Amurka da shi, a hankali Khaleesat tace "Toh Aunty ta yaya za a maida masa kudinsa dake account dina?" Aunty Farida ta daga kai ta kalleta, can tace "Kudin wa? Ko Abdul?" Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida ta saki baki, can tace "Wai dama har yanxu kudaden nan nasa na account din ki?" Khaleesat ta gyada mata kai, shiru Aunty Farida tayi kamar me nazari, after a while tace "Ki ci gaba da ajiye kudin kawai Khaleesat, duk sanda ya dawo ya bukaci kayansa sai a basa, ko Umma kar kiyi ma maganar kudin for now, bana son a samu delay a tafiyarki don yanxu sai su iya cewa sai an maida masa kudadensa, kuma hakan zai iya ja maki delay...." Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Aunty Farida ta ci gaba da hada foodstuff din da take a akwati.

[7/1, 1:11 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Wajen karfe uku na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Umma Aunty Farida na combing din mata dogon gashinta bayan ta wanke mata shi da Shampoo da Conditioner, har wani sheki baΖ™in gashin nata yake yi bayan Aunty Farida ta shafa mata man gashi, tun daga wajen wanke gashin Aunty Farida ke ta mata fadan ta bar gashinta ya kakkarye saboda banzan da tayi da shi ta dena kula da shi, ita dai Khaleesat bata ce mata komai ba don har sannan basu san irin zaman da tayi a gidan Abdul ba, don ma abun ya tsaya iya kakkaryewan gashi, har bata son tuna experience dinta a gidan Abdul hakan yana traumatizing dinta, su Mama Zubaida da Mama Shatu dai na bakin murhu suna girka abincin siyarwansu na yamma, suna yi suna kuskus a bakin murhun, lkci lkci sai su kalli direction din su Khaleesat, ita dai Aunty Farida dama ko kallo basa isanta a gidan, a da dai ta biye su har dambe sun sha yi amma yanxu bata da wannan time din, kallon stark illiterates kawai take masu, wasu mata biyu ne suka shigo gidan babu ko sallama, sun yi shiga ta alfarma sun sha gwala-gwalai suna taku cikin isa, at the same time suna bin ko ina na gidan da kallo cike da kyama gashi dama su Mama Zubaida sun yi gaje gaje da ruwa a tsakar gidan ranan, Khaleesat ta dinga kallonsu haka Aunty Farida da ta ajiye comb din hannunta, Mama Zubaida ta mike tace "Sannun ku da zuwa ko dai batan hanya ku ka yi ne, in gidan Hajiya Samira matar Alhaji Bala ku ke nema can karshen layi za ku karasa sai ku yi tambaya a nuna maku gidan, amma ba nan bane" Momy ce ta shigo gidan tana tafiya gansan gansan da Drebanta a bayanta yana biye da ita, mayafin nata ma ko yafa shi bata yi ba, gashi ta sha wani tsadadden baΖ™in glass no respect, Khaleesat ta dinga kallonta babu ko kiftawa, lkci daya taji gabanta ya fadi sosai, ta juya ta kalli Aunty Farida, sai ga Meemah ita ma ta shigo gidan tana yatsine fuska, ita ko mayafin ma babu a hannunta, Aunty Farida ta dake tace "Bayin Allah lafiya? Daga ina haka, babu ko sallama" Daya daga matan da suka shigo da farko tana ma Aunty Farida wani matsiyacin kallo tace "Ba shi ya kawo mu ba, a irin wannan bolan za ayi maku sallama?" Umma ta fito daga dakinta don tana jin duk abinda ake cewa, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsu, Mama Shatu da Mama Zubaida dai sai zazzare ido suke kamar wa enda suka yi ma sarki karya, Momy ta karaso har tsakiyar compound din tana tafiya cikin isa da gadara, fuskar nan nata babu ko digon mutunci tace "Zuwa nayi in ji ko shegiyar er ku tana da gadon Abdul ne, Ko kuma shi ma satan da ku ka yi ma ubansa kuke da niyyar za ku yi masa, in kuwa babu gado to yanxun nan ba sai anjima ba a maido mana kudadensa dake account din er ku..." Umma ta kalli Khaleesat nan da nan hankalin Umma ya tashi sosai, Aunty Farida tace "Ikon Allah, shi ne sai anyi wannan zuga haka kamar za ayi yaki?" Meemah ta matso har gaban Aunty Farida tana mata matsiyacin kallo tace "Yakin ne ai, ko kin ga alamar da sassauci muka zo? sanin halin familyn na ku na sata wanda ku ka gado a gun Malam me dattin hula ya sa mu ka yo tattaki a mayar mana da kudaden mu tun wuri, ai kowa yasan sata da cin amana shi ne tambarin gidan nan, don haka tun wuri ba a jiyo kan mu ba a maido mana Miliyan goman Abdul, kun zata bulus za ku ci ga banza ta fadi ko? To Sponsoring din matsiyaciyar er ku da ya dinga yi da kudinsa ma ai ba yafewa yayi ba sai kun biyasa a lahira wallahi, kawai babban farin cikin dake saka ni nishadi idan na tuno shi ne karewar da zata yi as dropout din John Hopkins university, don ko kaf zuri'arku za ku siyar baza ku samu kudin biya mata ta ci gaba da karatun a kasar Amurka ba, da yau ta gama John Hopkins sai bakin ciki ya kasheni, amma Alhamdulillah a dropout zata kare, Abdul kuma ya yar da kwallon mangwaro ya huta" A fusace Momy tace "Ke Meemah tsayuwa cikin kangon bolan nan ne ke burge ki da baza kiyi abinda ya kawo mu mu fita ba, ko so kike Cholera ya kama mu? Ina ke ina cacar baki a irin wannan gida" Aunty Farida tayi wani murmushi tana kallon Meemah tace "Sai dai kuwa bakin cikin nan ya kashe ki don kina ji kina gani Khaleesat zata gama karatu a makarantar da kike fada, Allah ya ji Ζ™an ki in Advance" Cikin tsawa Meemah tace "Keee, ki iya bakin ki, kar ki gan ni tsaye a wannan bolan gidan a gabanki kiyi zata ni sa'ar yin ki ce, don wallahi inda na bi da kafata ma baki isa ki bi ba har duniya ta nade, ni ba sa'ar ki bace ta ko wani angle, banda Abdul yayi downgrading dinmu ya kaskantar da darajan da Allah yayi mana ina mu ina hada hanya da matsiyata talakawa irin ku balle har aje ga auratayya? Ke ki duba irin wajen da ku ke rayuwa wanda ko karen gidanmu baza mu bari yayi rayuwa a cikin wannan hali ba, To wallahi ki iya bakin ki ni ba sa'ar yin ki bace, ba karamin aikina bane in sa a shafe babin ki a duniya" Tun kan Aunty Farida ta mayar ma da Meemah amsa Umma ta hanata, cikin fushi Aunty Farida tace "Kamar yaya in yi shiru Umma, gidanmu fa suka zo suka same mu kuma ki ce inyi shiru? ashe ma karyar arziki suke in don saboda miliyan goma za su yi wannan uban zugan kamar masu bibiyan miliyan 50 har su tsaya suna kumfar baki suna tada jijiyoyin wuya akan 10M, uban wani ya saka ya tura mata kudin a account dinta da har za su zo nan suna gaya ma mutane maganar banza, ko kuma rokonsa tayi ya saka mata kudin, su arzikin ma wallahi da gani taka haye suka yi, da can su ma matsiyata ne" Meemah ta mika ma Momy handbag dinta tana huci zata cakumo Aunty Farida, Momy ta dakatar da ita tace "Ke me ya kai ki, ki taΙ“a ta ki ce kin taΙ“a wa? Salon ta goga maki Ζ™ashin tsiyarsu kike kokarin dambe da ita? Yanzu wannan har Class din damben ki ce in ba rashin wayo irin naki ba Meemah? Ai ba a dambe da talaka matsiyaci" Umma ta kalli Khaleesat tace "Ta yaya za ki fiddo kudaden a account din ki Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Sai naje banki, bani da Atm card, kuma kudin bazai fita lokaci daya ba...." Momy na mata matsiyacin kallo tace "Sai ki tashi ki tafi bankin ai don wallahi kudaden nan baza su kwana a account din ki ba yau, da niyyar ki kin ci bulus tunda ubanki ne ya nema masa kudin ba" Khaleesat ta daga kai ta kalleta, ita har sannan ta kasa daina mamakin matar nan, kai tunda aka haifeta ma ita ba a taΙ“a shayar da ita ruwan mamaki yanda mahaifiyar Abdul ta shayar da ita ba, yau sati daya da sakin da Abdul yayi mata amma kullum in ta tashi sai ta zauna tayi mamakin uwarsa ganin abun take kamar Drama, ba ayi ranan da zai zo ya wuce da Momy bazata fado mata ba, bata taΙ“a san akwai mutane irin Momy a rayuwar nan ba, muryar Mama Zubaida taji tace "Ai ba zama zaki yi kina zazzare ido ba kamar barauniya, tashi za ki yi ki kama hanya ki tafi banki ki fiddo masu da kudadensu tunda ba gadon Abdul din gare ki ba kuma ba kudin tsohon ki bane, duk wani abu na rashin gaskiya dake da uwarki da kanwarta gaba ku ka basa ba baya ba, banda haka ta yaya za kuyi shiru da makuden kudadensa har Miliyan goma a account dinki? So ku ka yi ku danne kudin ko yaya? Don ma kun samu masu hakuri da kawaici da wasu ne idan ba a zo da motar yan sanda an tafi da ku ba ku ce bani ba, wannan ai rashin gaskiya ne da rashin tsoron Allah kiri kiri, duk kun yi mukus da bakin ku za ku cinye miliyan goma ga banza ta samu" Aunty Farida ta juya tana kallon Mama Zubaida, sai kuma ta nufeta tana cewa "Zubaida idan ban zubar maki da hakora a gidan nan yau ba ki ce bani ba, don kaza kazan ki akwai tsinannen da ya sako bakin ki? Uwarki muka yi ma rashin gaskiya ko ubanki?" Mama Zubaida tayi wani shewa tana tafe hannu tace "To yau kika saba Farida? Ai ke fitsararriya ce dama mara mutunci mara kunya shi yasa ga ki har yau duk kyan ki kin rasa mashinshini sai dai kiyi tuwo tuwo a garin legas kina hadawa da karuwanci, waye bai san wannan ba?" Aunty Farida zata cakumo Mama Zubaida Mama Shatu ta shige tsakaninsu tace "Ke yanxu Farida Zubaida sa'arki ce zaki dinga zaginta haka ta uwa ta uba don kawai tana kishiyar yayarki? Daga dai ta fadi gaskiya banda Ι—an Adam baya son gaskiya?" Aunty Farida tayi wani wurgi da Mama Shatu sai ga ta a kasa timmm, tuni Mama Zubaida ta shige dakinta ta kulle kofarta da sakata tana cewa "Haka kawai ki shafa min bakin jini irin na ku? Allah ya sauwake in yi dambe dake Farida, ku je can ku ji da rashin sa'ar ku a rayuwa, ku kenan daga wannan iftila'in sai wannan bala'in, ko wani fitinar duniya a kan ku ya kare, daga wannan sai wannan, Allah kadai yasan laifin da ku ka tafka a kasar ku, kilan ma ta zina aka sami ke da yayar taki, ga bakin jini da rashin sa'ar ku ya shafi Malam ya talauce" Da kafa Aunty Farida ta hambare uban miyan da Mama Zubaida ke yi na abincin siyarwanta, miyar duk suka malale kasa, shinkafar ma dake cikin kwando ta kifar da shi a kasa tana zagin Mama Zubaida ta uwa ta uba, Mama Shatu ganin yanda aka yi watsi da kayan sana'an Mama Zubaida ya sa ta ja bakinta tayi shiru ta tafi gun nata miyan ta zauna tana cewa "Hakuri kawai za kiyi Farida, hakan ba dadi kam" Momy ta rike haΙ“a tace "Alhamdulillahi da na yi iya bakin kokarina na ganin ban hada iri da gayyar tsiya ba, ku kuga wannan tsiya haka kamar 'yar tasha, ga talauci ga tashanci, Abdul ya so ja mana abun fade a dangi Allah ya takaita min abun, kuma ba dai kun ce kudade na banki ba, to zuwa yau da daddare in ga alert din Miliyan goma, in kuwa ba haka ba gobe da sassafe za ku gan ni a gidan nan ba kuma zuwan lumana zan yi ba, ai shi ramin karya kurarre ne, kuma ko kwabo daya yayi ciwon kai a kudaden nan wallahi sai an daure er ku..." Momy na kai wa nan ta bude handbag dinta ta ciro takarda dauke da account details dinta ta jefa ma Khaleesat sannan ja tawagarta suka yi waje tana cewa "Haka kawai Meemah zata ja min bala'i ta hada Ζ™ashi da wannan iri na fitina, irin tsiya, to kiyi dambe da ita ki ce kin yi dambe da wa? Kina ganin yarinya kamar mahaukaciya, A'a wallahi Allah ya maki tsari" A haka duk suka fita daga compound din, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma komawa dakinta tayi tayi tagumi ranta ba dadi, ita kam ta gode Allah da jarabawa iri iri, daga wannan sai wannan, Khaleesat ta dau takardan da Momy ta jefa mata ta juya ta shiga dakin Umma hawaye na zuba idonta, Aunty Farida kuwa bata fasa zage su Mama Zubaida da Mama Shatu a tsakar gida ba, Mama Zubaida taki fitowa kuma taki tanka Aunty Farida, Mama Shatu kuwa tayi tsit kamar bata san da wa Aunty Farida take ba, daga karshe bayan Aunty Farida tayi masu wankin babban bargo ta shige dakin Umma tana huci, Umma ta daga kai tana kallonta tace "Yanxu ban isa ince ki bari ki bari ba Farida?" Aunty Farida ko tanka Umma bata yi ba ta dau Hijab dinta ta saka tana kallon Khaleesat tace "Ki tashi ki shirya mu tafi bankin" Mikewa Khaleesat tayi tana goge idonta ta dau hijab dinta ta saka, a haka suka kama hanyar banki da Aunty Farida, amma suna isa bankin suka tarar an tashi aiki sai ran Monday don karfe hudu har da rabi a lokacin, Aunty Farida na kallon Khaleesat bayan sun fito bankin tace "Goben karfe nawa ne tafiyar naku?" A hankali Khaleesat tace "Flight din karfe daya zuwa Abuja, daga Abuja kuma jirgin yamma ne" Aunty Farida tace "Kuma bazai yiwu a daga tafiyar ba Khaleesat? Kinga banki dole fa sai Monday idan Allah ya kai mu" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, ita kanta she is just confuse bata san yanda zata yi ba. A haka suka koma gida kusan karfe biyar da rabi, Umma na kallonsu tace "An tashi a banki ko?" Aunty Farida bata ce komai ba ta cire hijab dinta ta nemi waje ta zauna, Khaleesat ta zauna tana kallon Umma tace "Banki sai ranan litinin, sun tashi yau" Umma tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Kema kin san bai amshi kudinsa ba me yasa zaki yi shiru har na sati daya Khaleesat? Yanxu da kinyi magana tun yaushe za a san yanda za ayi a cire kudin a mayar masa kayansa, yanxu rashin mutuncin da suka zo suka mana makota na ji ina amfanin sa?" Aunty Farida tace "A'a ta min maganan kudin fa ranan Alhamis, a lkcn ma tayi zaton yau ne tafiyar ashe gobe ne, kuma kema kinsan Khaleesat bazata taΙ“a ko biyar a kudin nan ba tunda ba nata bane, kawai dai dama matsiyata ne yan iska daga Abdul din har iyayensa" A hankali Khaleesat tace "In ma an cire kudin an basu bazan iya tafiya babu kudi a account din ba, don baza a bari in shiga kasar ba, they wilk see i am not financially capable idan babu kudi a account dina, shi yasa ma ya bar kudin a account din all this years" Aunty Farida tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, haka ma Umma da ta rafka tagumi tun shigowarsu, after a while a hankali Umma tace "Ni tsorona kar su dawo goben da suka ce bamu san kuma da me za su zo mana ba" Aunty Farida ta mike tace "Sai su zo su amshi babu tunda su yan iska ne" Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma na kallonta a hankali tace "Kiyi hakuri Jiddah, wataran duk hakan zai zama labari, Allah ya bamu ikon cin jarabawan mu, in ma kin koma makarantar in ma baki koma ba duk yanda Allah yayi dai dai ne" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata ta mike ta dau tsintsiya zata yi gyaran dakin Umma tana goge hawayen dake sauka idonta....

[7/2, 6:55 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat har ta fara bacci wajen karfe goma da rabi Aunty Farida ta tasheta tana mika mata sabuwar wayarta dake vibrate, mikewa tayi zaune tana gyara hulan kanta ta amshi wayar taga Safiyyah ce ke kiranta, Ι—agawa tayi ta kai kunne, daga daya bangaren Safiyyah tace "Ko har kin fara bacci ne" Khaleesat tace "Um, da wuri na kwanta ne" Safiyyah tace "Ayya sorry for waking you up, dama Housemate din ki ne yace in tambayeki wani account zai maki funding, cause nasan definitely Abdul ya amshi kudinsa dake account din ki ko?" Khaleesat tayi shiru ta kasa ce ma Safiyyah komai, har sai da Safiyyah tace "Hello" a hankali Khaleesat tace "Ina jin ki Sophie" Safiyyah tace "To naji kin yi shiru" Khaleesat ta daga kai ta kalli Aunty Farida dake kallonta, goge hawayen dake makale idonta tayi cikin sanyin murya tace "Daxu Mom dinsa suka zo za su amshi kudin, ni kuma bazan iya transfer ba kuma bani da Atm card, shi ne ta ajiye min account number wai in tura masu kudin yau, and today is Friday, mun je banki sun tashi, yanxu tace zata dawo gobe da safe idan ban tura mata kudin ba" Safiyyah dake ta sauraron Khaleesat cikin bacin rai tace "Allah ya sauwake, ke kiji wani tsiya don girman Allah, akan miliyan tara ne ko goma uwar ta kamo hanyar gidan ku da kanta? Can you imagine fa? A'a gaskiya sai yanxu nake sake tabbatar da su Abdul were once poor in this life, all of a sudden kawai Allah ya basu arziki sama ta ka, nobody can change this my perspective wallahi, banda tsiya meye kuma miliyan Goma a irin yanda suke show casing arzikinsu, what is 10M to them? wannan ai abun kunya ne a garesu, Ke kuma maimakon ki kirani tun daxu ki gaya min shi ne kika yi shiru? Yanxu ba don Housemate dinki yayi reason cewar dole sai da sufficient fund a account dinki za ki iya tafiya ba da shiru zaki yi kenan sai gobe da za mu tafi ki gaya min? Allah ya sauwake, ita kuma uwar Abdul wallahi matsiyaciya ce er wahala, har ta iya kamo hanyar Mariri akan kudin da ba ita ta bada ba, in kin bibiya ma Ι—an nata bai sani ba ta kamo hanya, ki min sending shegen account din nata da ta bar maki" Daga haka Safiyyah ta kashe wayarta, Khaleesat ta jawo handbag dinta tana goge hawayen da ya taru idonta, ta bude jakar ta ciro takardan account details din da Mom din Abdul ta bar mata, tura ma Safiyyah account din tayi ta message sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta koma ta kwanta, ita dai Aunty Farida bata ce komai ba don duk ta fahimci conversation din nasu. Washegari Khaleesat na idar da sallan asuba kiran Safiyyah ya shigo wayarta, tayi picking call din ta kai kunne, a hankali tace "Good morning Safiyyah" Safiyyah tace "How was ur night?" Khaleesat tace "Alhamdulillah" Safiyyah tace "Na tashi yanzu naga Housemate dinki ya tura min receipt din 10M da ya tura a account din da kika turo min jiya, he sent the receipt via my WhatsApp, ba ki yi activating WhatsApp dinki ba da sai in tura maki ki tura masu, sai su san su ne matsiyata" Kasa cewa komai Khaleesat tayi hawaye ya fara sauka idonta, Safiyyah tace "Ko kuma bari in tura ma Aunty Farida receipt din kawai since she is on WhatsApp" Khaleesat ta gyada mata kai da kyar tace "Nagode" Safiyyah tace "Kuka kike yi ko? Kina da aiki, ni dai sai anjima, make sure ki fito gida da wuri kin san Flight dinmu zuwa Abuja karfe daya ne" Daga haka Safiyyah ta katse wayar, Umma na kallon Khaleesat tace "Wai me ya faru?" Khaleesat na share hawayen da yaki tsaya mata tace "Ta ce ya tura masu kudin ne, zata tura ma Aunty Farida receipt" Shiru Umma tayi ta rasa abun cewa, kana ganinta kasan jikinta yayi sanyi sosai, Aunty Farida dake zaune kan darduma tace "Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi ya kare sa sharrin masu sharri, Allah ya mayar masa da dubban abinda ya kashe maki, yanda ya rufa maki asiri Allah ya rufa masa shi ma" a hankali Umma tace "Ameen ya Allah"  Mikewa Khaleesat tayi don dama ta gama azkar din da take yi, ta kwanta kan gadon Umma har sannan hawaye yaki dena sauka idonta. Da safe wajen karfe tara Aunty Farida na bude WhatsApp dinta taga Receipt din da Safiyyah ta tura mata, tana kallon Khaleesat tace "Yanxu ta ya za a tura masu receipt din su gani Khaleesat?" Umma tace "Ba kina da number Abdul din ba? Ki tura masa ta WhatsApp din kawai" Khaleesat dake cin wainar da Umma ta sa aka siyo mata ta daga kai ta kalli Umma, sai kuma ta girgiza kai a hankali tace "A'a Umma kar a tura masa, ba sun ce za su zo da safe ba, in sun zo sai a nuna masu receipt din" Umma tace "Saboda me? Ba kudinsa bane kuma shi ya aiko su karbar masa?" Aunty Farida ta kalli Umma tace "Suka aiko kansu dai Umma, don Abdul dai a yanda yake ji da kansa bazai ce a zo a amsar masa miliyan goma ba, dama sun san da kudin kuma kilan sun san bazai ce zai amsa ba shi yasa suka taho su amsa" Khaleesat tace "Shi yasa nace kar a tura masa receipt din, don nasan ba shi yace su zo ba" Umma tace "To ko ma dai yaya ne ai kudinsa ne, ni bana son su sake dawo mana nan su mana tijara makota na ji shi yasa nace a tura masa kawai, idan yaso sai yayi ma uwar tasa magana tunda zai ga a account dinta aka tura kudin ai, tonan asirin bai ishe mu bane da har za mu sake yarda su dawo gidan nan" a hankali Khaleesat tace "Umma ni bana son abinda zai sake hadamu magana da shi balle har yace zai dawo da wata magana kuma" Aunty Farida tace "Ya dawo da wani magana? Saboda ba shi da hankali zai dawo da wata maganar? Ai yanxu ba mu da abinda zai sake hadamu da shi da ya wuce kudin nan nasa, saki uku ya aiko maki balle ace zai dawo da wata magana" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya tace "Aunty ba fa shi ya aiko da takardan sakin nan ba, ba rubutunsa bane, iya saki daya yayi min" Daga Aunty Farida har Umma kallonta suka dinga yi, a hankali tace "Shi yasa bana son a tura masa receipt din balle har hankalinsa ya dawo kan mu..." Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya bayan kusan minti daya tace "To Allah ya kyauta, yanxu su suka rubuto takardan suka aiko kenan? To su dai suka sani Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu da ke baki daya, idan sun kwaso kafa sun sake dawowa sai a nuna masu receipt din" Umma dai bata ce komai ba don bata ma san me zata ce ba.

Meemah na bacci Momy ta shigo dakinta wajen karfe goma na safe ta tasheta tana mika mata wayar hannunta, Meemah ta amshi wayar tana kallon screen din, sai kuma ta kalli Momy tace "Kudin suka sako?" Momy ta tabe baki tace "Gashi kuwa kina gani, nima yanxu naga alert din ashe tun daren jiya aka sako" Meemah tace "To a gidan uban wa ta samu ta turo bayan tace bata yin transfer kuma bata da Atm card" Momy tace "Ke baki ga sunan wanda ya turo kudin ba? Ai ba ita bace ta turo" Meemah ta kara kallon wayar da kyau taga sunan namiji, taΙ“e baki tayi tace "To wai ke Momy da nake ce maki iskancinta ta dinga yi da maza a Amurka kin zata wasa nake? Ai ba abun mamaki bane don kin ga ta samu wanda ya turo miliyan goman, harkar iskancinta kawai ta dinga yi a Amurka da 'ya yan masu kudi, kuma karya take babu miliyan goman nan a account dinta wallahi, to dai gashi nan daya daga farkanta ya turo kudin nan take" Momy tace "Oho dai koma wa ya turo kudin ta matse masu can, ni dai ba na amshi kudin Ι—a na ba, da ban yi haka ba har a tashi duniya in dai Abdul ne wallahi bazai yi maganar kudin nan ba, kin ga da shikenan sun ci bulus, to ni da na haifesa ba asararriya bace da zan yarda ya bar masu makudan kudaden nan" Meemah tace "Wallahi Momy ni so nayi mu ce sai sun biya kudin sponsoring dinta da Abdul yayi, ke kinsan nawa Abdul ya kashe akan yarinyar nan kuwa? Wallahi idan na fara maki lissafi sai kin rike baki don mamaki, kudade ne ba na wasa ba da, duk kanta dukiyarsa ya dinga tafiya kamar kin masa baki, yaushe rabon kiji Abdul ya siya wani asset nasa ya ajiye? Tun da ya hadu da tsinanniyar yarinyar nan ya dena yi ma kansa komai sai dai yayi mata, ranan a gabana ya siya mata Abaya har biyu ko wanne dubu dari da hamsin, nayi masa magana ya nemi ya min rashin kunya cikin jama'a, handbag din nan shegiya sai Abdul ya siya mata na dubu kusan dari har fin haka, komai designer yake siya mata, suturu kam yayi mata ba iyaka, to wai ko monthly allowance da yake tura mata a kasar Amurka in kika ji sai hankalin ki ya tashi, uwa uba a zo kan kudin makarantar ta da House rent" Momy tayi mitsi mitsi da ido cikin bacin rai tace "Don Allah ki bar wannan maganar don raina baci yake Meemah, su je kawai Allah ya isa, ni da nake uwarsa ma sai ya ga dama yake siya min abu, to yanxu ko ce masu muka yi su biya a ina suka ga kudin biya Meemah? Ko gidan da suke ciki suka ce za su siyar wallahi karkari yayi dubu dari biyar, kai ni dubu dari biyar din ma bazan siya wannan kangon ba wallahi, kin ga kuwa gwara a bar zancen kawai, baki ji yanda raina ya baci ba wallahi, kawai Allah ya isa zan ta ja masu a kan uban kudin da Abdul ya kashe ma yarinyar kuma ba wai don bani da kudin maka su kotu ba...." Meemah tace "Ko kuma mu je duk mu kwaso kayan da ya dinga siya mata da jakunkuna masu tsada" Momy tace "Ki ci uwar me da su? Kema dai wallahi, shekara 38 ban san yaushe zaki yi hankali ba Meemah, Allah ya isan dai shi ne dai dai su, don babu abinda za mu ci da kayanta, tunda muka samu miliyan goman ma ai mun gode Allah" Meemah ta tabe baki ta koma ta kwanta tace "Kuma kin san wani abu Momy, da Abdul yana kasar nan har yanxu zai fa iya waiwayanta idan asirin ya sakesa, don wallahi masifaffen so yake ma shegiyar ke har yanxu baki gane ba, ji fa kafin su bar kasar yanda ko magana baya yi ma mutane a gidan nan, kullum zaka gansa babu walwala" Momy ta hade rai tace "Ni kuma ga er iska sai in sakankance har asiri ya sakesa ko? Ai da gangan na sa uban ya tafi da shi business trip din da za shi china, da biyu na takura uban su tafi tare don naga take takensa, ga sabon tijaran da na lura zai fara mana, kuma ko ba komai ai kinga za su dade a can kan su dawo, ni kuma kafin nan na sa anyi aiki sosai ya mance da wata shegiya wai ita Khaleesat a duniyar nan, sai kuma in tanadar masa mata er gidan mutunci, yana dawowa sai biki kawai" Meemah tace "Da dai yafi kam, yana dawowa yayi aure, ki sama masa yarinya dai dai class dinsa ba er talakawar da ya nace ma ba, ni wallahi ban zata talaucin iyayen yarinyar nan ya kai haka ba, har muka dawo gida na kasa cire view din gidan a idona, wannan ko karen gidanmu aka ajiye a gidan nan ai sai yayi rashin lafiya a bar mu da kashe makudan kudi zuwa veterinary balle ace mutum, to yanxu da bai rabu da ita ba haka wataran abu zai kama ki kwashi kawayenki da abokan business aje gidansu yarinyar? Misali ace ubanta ko uwarta wani ya mutu, haka za a kwasa aje masu gaisuwa wannan gidan?" Momy tace "Ai Abdul ya so ja min abun kunyan da bazai taΙ“a goguwa ba, ya so tona min asiri a idon duniya amma Allah ya rufa min asiri ya takaita abun, da irin rainin da Abdul zai ja min sai Allah wallahi, to ni dai tunda na samu aka rabu lafiya ai sai su bi wani sarkin kuma" Meemah tayi dariya tace "Kuma da bai saketa ba fa sai ya iya canza masu wani gidan don ba hankali garesa ba, tunda don yayi ta ma shegiyar yarinyar bauta Allah ya halitto sa" Wani shegen kallo Momy tayi mata sannan ta juya ta fita daga dakin. Khaleesat na durkushe gaban Umma dake mata addu'an Allah ya kai ta lafiya, ya bata sa'an karatun ta, ita dai Khaleesat kanta na kasa duk jikinta a sanyaye, a hankali Umma tace "Ki kula da kanki don Allah, duk da na yarda dake Jiddah amma ki kara taka tsantsan, kar ki mance tarbiyar da muka maki, kuma ki rike addu'a da azkar, Allah ya kare min ke ya tsare ki duk inda zaki shiga..." Nenne ce ta bude labulen dakin a fusace tace "Yau naga jaraba wajen Zahra'u, sai me motar yayi zuciya ya ja motarsa ya wuce ne ko yaya? Duk daren jiya da wayewar garin yau baki sakata gaba da duk wani zancen da zaki mata ba sai yanxu da motar da zai kai ta iyapot ya iso, haba Zahra'u ya ki ke haka ne? Ko dai maidata ciki za kiyi?" Aunty Farida ta wani kalle Nenne tace "To kyauta zai kai ta airport din da bazai jira ba, naga dai kudi zata basa Nenne" Nenne tace "Ai ba motar ubanta bane da zata shanya sa a rana don zata basa kudi, kuma shi ba boyi boyinta bane da zai ta tsayuwa yana jiranta a rana kamar Ι—an iska, tunanin ku kenan 'yan Adam, don zaka ba mutum kudi sai aka ce ka walakantasa? Ka ki darajasa?" Aunty Farida taki tanka Nenne, Umma na kallon Khaleesat tace "Tashi ki je Jiddah, Allah ya tsare ya kai ku lafiya" A hankali Khaleesat tace "Ameen Umma" Daga haka ta mike ta dau handbag dinta don duk an fitar da akwatunan ta kofar gida, Nenne na kallon Umma tace "In ji dai duk an saka mata doya da dankalin da na kawo mata a akwatin nata?" Da sauri Aunty Farida tace "An saka komai" Nenne tace "Wake da su albasa da garin masara da na alkama fa?" Aunty Farida tace "Har su an sa" Nenne tace "To mu je" Khaleesat ta bi bayan Nenne suka fita daga dakin, Aunty Farida ta kara tura doya da dankalin da Nenne ta kawo da su garin alkama da Masara a bayan kyaure ta boye yanda Nenne bazata gani ba ko ta dawo dakin, daga nan ta bi bayan su, kasa daurewa Umma tayi ta mike ita ma ta fita, su Mama Zubaida da Mama Shatu na tsaye tsakar gida duk suka bi Khaleesat da kallo, Kana ganin fuskokinsu kasan babu farin cikin komawa Amurka da Khaleesat zata yi, Yaron Mama Zubaida ya nufo Khaleesat da gudu yana mika mata kudin hannunsa yace "Wai gashi inji Ummanmu da Mama Shatu ki sha ruwa a hanya" Nenne ta karbe kudin a hannun yaron ta kirga taga dubu biyu ne, sokesa tayi jikin haΙ“ar zaninta tace "Ta gode" Daga haka ta kalli Khaleesat tace "Mu je" Khaleesat tayi ma kishiyoyin ummanta sallama sannan ta bi bayan Nenne suka fita daga gidan Aunty Farida na biye da su, a kofar gidan Khaleesat ta kara sallama da Babanta don bai fita kasuwa ba ranan yana jiran tafiyarta, kasa hada ido tayi da shi yana mata addu'a da fatan alkhairi, Nenne ta bude mata bayan motar tace "Ni dai shiga don Allah, tun jiya basu san da addu'an su ba sai yau da kike sauri salon jirgi ya tafi ya bar ki" Khaleesat ta shiga motar Nenne ta kulle, haka kawai Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, ta daga masu hannu kawai sannan drivern ya ja motar suka bar kofar gidan. Ko da Khaleesat ta isa airport ta tarar Safiyyah na ta jiranta don tun daxu ta iso airport din, Khaleesat ta amshi boarding pass dinta suka nufi Departure Lounge, bayan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin Abuja, inda a nan za su hau jirgin da zai kai su kasar America.

[7/3, 9:23 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Tun da suka sauka Amurka wajen karfe hudu na asuba gaba daya walwalar Khaleesat ya bace, ta dawo so silent kamar mara lafiya, cikin rashin kuzari ta dinga yin komai har suka gama da custom da Immigration, Safiyyah na kallonta tace "Wai duk sanyin ne yasa kika dawo haka? Naga mood din ki ya canza all of a sudden, are you okay?" Khaleesat tayi murmushin karfin hali ta girgiza mata kai kawai tana gyara Jacket din jikinta don tun a kasar da suka yi transit duk suka saka Jacket din su saboda sanyi, Safiyyah na kallon wayar hannunta ganin kiran Mustapha for the 4th time tace "Shi kuma wannan daga sauka ko kashe jirgin ba ayi ba ya fara doka min kira kamar jira yake, kilan kewan fadan da muke yi da matarsa kullum yake yi, bai san i came fully ready for her ba, don this time around bazan sake tolerating nonsense dinta ba wallahi" Khaleesat dai murmushi kawai tayi bata ce mata komai ba har suka fita daga Arrivals, Safiyyah tace "I don't want us to stress ur Housemate, naga message dinsa tun muna Abuja yana tambayar karfe nawa za mu taso kuma a ina za mu yi transit, kilan da na gaya masa zai iya estimating time din da za mu iso ya zo yayi picking din mu daga airport cikin azababben sanyin nan da ake, shi yasa kawai ban masa reply ba kar muyi inconveniencing dinsa" Khaleesat ce ta fara hango Ya Mustapha tsaye jikin motarsa kafin Safiyyah ma ta gansa tayi kasa da murya tace "Sai kin ga yanda ya addabi Dad din mu wai an koma makaranta naki dawowa, sai kace zaman jin dadi nake yi a gidansa da shegiyar matar nan tasa" Khaleesat ce ta fara gaida Mustapha bayan ya iso inda suke tsaye, ya amsa da fara'a yace "Ya hanya Khaleesah?" Khaleesat tace "Alhamdulillah" Safiyyah ma ta gaishesa ya amsa sannan suka nufi motar sa gaba daya, ya amshi trolley dinsu ya saka a booth din motar yace "Kun ji sanyin America ko, don ma yau babu snow" Khaleesat dai tayi murmushi, Safiyyah ta bude mata back seat tana kallonta, Khaleesat ta shiga sannan Safiyyah ta zaga ta bude gaban motar ta shiga ita ma, Mustapha ya tada motar bayan sun bar Airport din ya kalli Safiyyah yace "Amma dai Khaleesat won't be going to her apartment now, zai fi kyau mu je can gidana idan ta huta sai ta koma Apartment dinta anytime she is ready" Safiyyah tace "Dama gidan ka zaka kai mu gaba daya mana, cikin sanyin nan ta ina zata je ta fara gyaran apartment dinta ga gajiyar hanya" Ko da wasa Safiyyah bata ba Mustapha labarin abinda ya faru da Khaleesat ba, ita dai Khaleesat tayi shiru a bayan motar tana tunanin another new life that she is going to begin in America with her burden on people's shoulder, shikenan ita kuma daga wannan ya dau responsibility dinta sai wannan ya dauka, sosai tunanin nan ke kara kashe mata jiki, gashi rayuwar America ba dai tsada ba, kawai tasan takura Housemate dinta zata yi da burden dinta, a haka suka isa gidan Mustapha da tunani iri iri a ranta, bin unguwan ta dinga yi da kallo don bata san unguwan ba, sati biyu da fara exams dinsu Last semester Safiyyah ke gaya mata Mustapha ya amshi wani apartment da ya fi wanda suke ciki girma za su tashi a gidan da suke, ita dai har suka bar America bata san gidan da suka koma ba, bayan Mustapha yayi parking suka sauka a motar Safiyyah ta bar sa da shigo masu da kayansu ta kama hannun Khaleesat zuwa cikin gidan, ita dai Khaleesat bin ta kawai take, upon yanda ta tsani duk abinda zai hadata da gidan Mustapha saboda matarsa sai gashi yau saboda rashin option da choice ya sa ta amince da zuwa gidansa babu ko musu, zaune suka tarar da matarsa a parlor ta sha uban rigan sanyi ga daurin dankwalin ture kaga tsiya da tayi da zaninta, sosai jikin Khaleesat yayi sanyi ta rakube jikin kujera tana kallonta ta gaisheta, amma matar nan ta dinga kallon TV tana cin popcorn kamar bata ji Khaleesat ba, Safiyyah dama ko kallonta bata yi ba ta nufi hanyar dakinta ta murda taji a kulle kuma babu makulli a jikin kofar, tsaye tayi fuskarta babu yabo babu fallasa tana jiran Mustapha ya shigo gidan, bayan yan sakwanni sai gashi ya shigo parlon da akwatuna biyu, Safiyyah tace "Yaya ina makullin dakina?" Ya karasa ya murda kofar yaji a kulle, ya dawo parlor yana kallon Surayya yace "Surayya ina makullin dakin can yake?" Sai a sannan Surayya ta juya ta wani kallesa tana ci gaba da cin popcorn din hannunta tace "Makullin daki? Ban gane Makullin daki ba, Ajiyar makulli aka bani da za a tambayeni?" Safiyyah dake ta kallon Ya Mustapha tana huci tace "Kai dama yaya da ka wani ishi Daddy da kira cewar mun koma makaranta in dawo a saman roofing din gidan nan kake da niyyar ajiyeni tunda gashi an dauke makullin dakin an boye? Wannan ai iskanci ne da walakanci, mutum yayi dogon tafiya haka ya dawo kuma yaga an dauke masa makullin daki?" Mustapha ya karasa kusa da Surayya da sauri yace "Ke Surayya ko dai Aslam yana wasa ya cire Makullin dakin ne a jikin kofar?" Surayya taki ko kallonsa, Safiyyah ta wani tsuke fuska tace "Aslam ne tsayinsa zai kai har ya cire makulli a kofar daki? Ai sai dai Uwar Aslam, kuma Allah ya so ban bar komai da za a sace min a dakin ba sai takardu, tunda an saba min satan dama" Mikewa Surayya tayi tana mata wani tsinannen kallo tace "Keeee, in kina cin kasa ki kiyayi ta shuri, wallahi ki iya bakin ki don ni ba sa'ar ki bace ki kiyaye ni, in kika yi wasa za ki sha mamakina yanxun nan" Safiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Osheyy ancient of days, ashe dai ke ba sa'a ta bace, ai sai yau kike gaya min nake ji, kuma in kin fasa bani mamaki sunanki ba Surayya ba, shege ka fasa tsakanin ni da ke" Fada Mustapha ya fara yi yana cewa "Meye haka? Ko kuna hauka ne? Wannan wani irin iskanci ne? A gaban nawa ku ke wannan rashin hankalin?" Magana yake yi at the same time yana kai kawo yana dube duben makullin dakin Safiyyah a parlon, Ita dai Khaleesat na rakube jikin kujera taji kanta har ya fara mata wani azababben ciwo, banda rashin option me zai kawota gidan nan ita kam, tunanin hakan yasa ta ji hawaye ya cika idonta, Safiyyah sai girgiza kafa take tana hararan Surayyah da ta koma ta zauna tana cin Popcorn dinta tana gyara daurin ture kaga tsiyan dake kanta tana kara cokarosa gaba, Mustapha ya karasa inda Aslam ke kwance yana bacci a parlon ya fara tashinsa yana tambayarsa makullin dakin Safiyyah, yaron da ko shekara biyu bai karasa ba, a fusace Surayya tace "Wallahi kar ka tada min yarona Mustapha, shi yasan maka wani makulli da zaka tashesa yana bacci" Mustapha ya juya ya kalleta yace "Surayya in ke kika dauke makullin nan ki fito da shi bana son rainin hankali" Surayya ta wani hararesa tace "Kar ka bata min rai this early morning, in dau makulli inyi uwar me da shi? Plss do not provoke me Mustapha" Tana kai wa nan ta mike ta figi yaronta dake bacci ta nufi dakin ta da shi, Mustapha ya kasa cewa komai ya bi ta da kallo yana rike da waist dinsa, can ya juya ya kalli Safiyyah dake masa wani mugun harara kamar zata kwadesa, karasawa yayi kusa da ita yace "Look Safiyyah...." Katse sa tayi a fusace tace "Babu abinda zaka gaya min Yaya, Don't tell me anything, dama don matarka ta min wannan walakancin ya sa ka dage sai na dawo an koma makaranta, wallahi ni dai Daddy zan kira a samar min wani gidan da zan zauna in karasa final year dina kawai in peace, don bazan iya zama da wannan devil wife dinka a gida daya ba" Kamar zata yi kuka ta kare maganar, Mustapha bai iya yace mata komai ba, can dai ya nufi hanyar dakinsa don daki uku ne a gidan, yana shiga dakin ya dau duk abinda zai bukata ya fito da shi parlor ya ajiye yana kallon Safiyyah yace "Ga bedroom dina can ku shiga" Safiyyah na jin haka ta figi hannun Khaleesat zuwa dakin nasa, da sauri Surayya ta fito daga dakinta don bata kulle kofar dakin ba saboda ta dinga jin abinda za ace a parlon, tana kallonsa da wani irin mamaki tace "Ban gane ga Bedroom dinka can su shiga ba Mustapha, turakar namu za su shiga kake nufi ko me?" Safiyyah ta kwashe da wani dariya har da kyakyatawa ta ja Khaleesat suka shiga dakin sannan tayi banging kofar ta kulle, Surayyah zata yi magana Mustapha ya Ι—aga mata hannu fuska a murtuke alamar baya son jin komai sannan ya fice daga parlon zai shigo da sauran akwatunan su Safiyyah, Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi ta dinga kallon Safiyyah tace "Haba Sophie, this isn't proper mana, why not mu zauna a parlor har san da za a ga makullin dakin naki, dakinsu ne wannan fa" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Ai ba kowa ne Ι—an iska mara zuciya kamar ki ba Khaleesat, kuma wallahi ina dakin nan babu inda zan je har sai ranan da ta fito min da makullin dakina...." Khaleesat ta kasa cewa komai don da gaske she is shock, sai ga Mustapha yayi knocking kofar dakin sannan ya ajiye masu hand luggage dinsu yace "Me za ku ci yanxu?" Safiyyah na zaune gefen gadonsa fuskarta babu walwala irin ita an bata mata din nan tace "Kawai shayi da cookies kafin gari ya waye" Yace "Ohk" Juyawa yayi ya fita daga dakin ya kullo masu kofa, har sannan Surayyah na tsaye inda take a parlor ta kasa motsin kirki, ta bi sa da kallo har ya shiga kitchen zai hado masu shayin, bata san sanda ta fashe da kuka ba tana rufe bakinta ta nufi dakinta da sauri, Mustapha ya dawo dakin nasa da Cup din shayi biyu da cookies ya ajiye masu ya fita.... Khaleesat na idar da sallan Asuba ta kwanta kasan carpet din dakin Mustapha don dakin da dumi saboda room heater dake kunne, amma hakan bai hanata dinga jin sanyi ba saboda wankan da tayi, babu yanda Safiyyah bata yi da ita ta kwanta saman gado ba amma Khaleesat taki tace kasan carpet din ya isheta, wayar Safiyyah ya fara ring, ta mike ta dauko handbag dinta ta ciro wayar, kallon Khaleesat tayi tace "Housemate dinki ne ke kira" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah ta zauna gefen gado sannan tayi picking call din tayi masa sallama tare da gaishesa, daga daya bangaren yace "How are you, naga baki yi replying message da na maki ba tun jiya" Safiyyah tace "Kawai bana son inyi stressing dinka ne probably kace zaka zo picking din mu a airport" Yace "Kuna ina yanxu?" Safiyyah tace "Muna gidan yayana, ga Housemate din ka nan, let me give her the phone...." Calmly yace "Ohk..." Safiyyah ta mike ta tafi inda Khaleesat ke kwance ta durkusa tana mika mata wayar, Khaleesat ta kasa amsan wayar, har sai da Safiyyah ta kai mata wayar kunne, daga daya bangaren Khaleesat taji yace "Halysaah...." Kasa ce masa komai tayi, lokaci daya taji hawaye masu zafi sun fara sauka idonta, a hankali yace "Can you hear me?" Muryarta na rawa da kyar tace "Uhm" Shiru yayi, after some seconds yace "I will come over later in sha Allah" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, kashe wayarsa yayi, ta ajiye wayar wasu hawayen na sauko mata, ita dai Safiyyah bata ce mata komai ba. Karfe takwas na safe Safiyyah ta fito daga dakin Yaya Mustapha zata je kitchen ta duba menene available da zata girka masu ita da Khaleesat, ga mamakinta sai taga an ajiye makullin dakinta kan Centre table din parlon, dariya ma abun ya bata, ta karasa ta dauki makullin sannan ta koma dakin ya Mustapha da sauri ta kulle kofar, dariya ta dinga babbakawa Khaleesat na kallonta, tana nuna ma Khaleesat makullin hannunta tace "Kin ga er iskar ta ajiye min makullin kan Centre table saboda taga na tare dakin mijinta, ashe karamar er iska ce ita ban sani ba? ai wallahi boyewa zan yi inyi kamar ban gani ba don ni kam naga dakin zama..." Safiyyah na fadin haka ta bude zip din akwatin ta ta cusa makullin ciki, Khaleesat dake ta kallonta ta girgiza kai tace "Don Allah tunda har ta ajiye maki makullin kiyi hakuri mu koma dakin ki Sophie" Safiyyah tace "Wallahi bazan koma ba for now, next time in ance ta boye min makulli bazata boye ba, ba tace ita er iska bace ni kuma zan nuna mata er daba ce ni, ina nan dakin sai naga abinda ya ture ma buzu nadi" Murmushi kawai Khaleesat tayi bata ce komai ba, Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace "To ni ba na manta ke buzuwa bace" Khaleesat tace "A'a ni bafillatana ce, babana bafillatani ne" Safiyyah tace "To Umma fa?" Murmushi kawai Khaleesat tayi bata ce mata komai ba, Safiyyah ta nemi waje ta zauna tace "Ke kiji rashin kunya kiri kiri ta ajiye min makulli kan Centre table da taga ba sarki sai Allah, to da menene nufinta da ta boye makullin in koma garage da zama ko me?" Knocking kofar dakin aka yi Safiyyah ta mike ta bude taga Mustapha tsaye ya shirya alamar zai fita aiki yace "Zaki fito ki yi maku breakfast ne?" Safiyyah tace "Har yanxu duk jikina ciwo yake min wallahi Yaya" Yace "Toh bari ayi maku order" Ta gefen ido Safiyyah ke kallon Surayya da ta fito parlon daga dakinta idonta akan Centre table wato tana duba makullin da ta ajiye, Surayyah ta kalli Mustapha tayi mitsi mitsi da ido tace "Mustapha bayan Aslam ya tashi bacci na tambayesa makullin shi ne ya dauko min wani toy dinsa ashe ciki ya zura, na samu da kyar na ciro makullin sannan na fito na ajiye mata kan Centre table 30 minutes ago, to kaga dai yanxu babu makullin kan Centre table din sannan bata fito daga dakin ka ba, me hakan ke nufi??" Mustapha ya kalli kan Centre table din, can ya kalli Safiyyah da ta hade rai tana rike da waist dinta yace "Safiyyah kin dau makullin ne?" Safiyyah ta wani kallesa tace "Ban gane na dau makullin ba Yaya" Cikin daga murya Surayyah tace "Wallahi in baki fito min daga dakin miji ke da shegiyar kawarki ba duk abinda na maku ku kuka ja ma kan ku a gidan nan" Safiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Toh ni kuma dakin yayana ne, ita kuma Khaleesat dakin yayan kawarta ne, kin ga kuwa baki isa ki ce mu fito ba bayan bamu da wani dakin da za mu zauna in mun fito" Rungume hannu Mustapha yayi yana kallonsu ya kasa cewa komai, Surayya ta yo kan Safiyyah a fusace Mustapha ya tareta yace "Kee baki da hankali ne??" Safiyyah tayi wani shewa tace "Ka kyaleta dai ta zo ta taΙ“a ni zan nuna mata da sabon dabanci na dawo daga Nigeria, wallahi sai na tuge mata gashin kanta gaba dayansa, ta zo ta taΙ“a ni ta ga ikon Allah" Khaleesat dai tayi tagumi duk jikinta a sanyaye tana jin su, Surayyah ta fashe da kuka tace "Wallahi Mustapha zan bar maka gidan nan kai da Safiyyah ku zauna don bazan ci gaba da zama da matsiyaciyar ba a gida daya, sai dai ka zaba ko ni ko ita a gidan nan" Safiyyah tace "Ke din banza, minti nawa ne ya canza ki amma ni bazai taΙ“a canza ni ba tunda jininsa ce ni, ke kuwa tsaf zai iya sakin ki ya auro wata" Surayya tayi wani kukan kura zata cafko Safiyyah, Mustapha yayi saurin riketa ya ja ta zuwa dakinta yana masifa kamar zai ari baki, Safiyyah ta koma daki ta dinga babbaka dariya har da rike ciki, Khaleesat dai sai kallonta take ta kasa cewa komai, after a while Mustapha ya sake knocking dakin, Safiyyah ta fito ta wani kauda fuska tana jiran jin abinda zai ce, nan ya fara lallabata yana cewa "Pls Safiyyah in dai kin san kin dau makullin kiyi hakuri ki kyaleta ki koma dakin ki, don ni zaki yi ai ba don ita ba, kin ga i am almost late for work, don Allah in kin dau makullin kiyi hakuri ko koma dakin ki" Safiyyah taki cewa komai tana girgiza kafa daya, haka ya dinga lallabata daga karshe ta kallesa tace "Na ji, amma wallahi ka ja mata kunne da kyau ta fita sabgata a gidan nan idan ba haka ba za mu yi batattciya da ita, don jahilci zan dinga nuna mata iri iri wallahi" Mustapha yace "Na ji, i will talk to her" Juyawa Safiyya tayi ta koma dakin, shi dai ya koma parlor ya tsaya yana jiran yaga fitowar Safiyyah. Khaleesat felt relieve bayan sun koma dakin Safiyyah, sai sannan ne ma ta samu bacci ya dauketa don kasa bacci tayi a dakin Mustapha. Wajen karfe uku da rabi na yammacin ranan Safiyya ta dau wayarta dake ringing sai kuma ta kalli Khaleesat tace "Housemate din ki ne, kilan ya zo ne, tun daxu yace in tura masa location ta WhatsApp" Tana fadin haka tayi picking call din ta kai kunne tare da yi masa sallama, after few seconds tace "Ohk to" Daga haka ta katse wayar tana kallon Khaleesat tace "Yana waje" Ita dai Khaleesat ta kasa dago kanta ga wani faduwa da gabanta yayi.

[7/4, 8:51 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Safiyyah ta gama saka Jacket dinta da neck warmer tana kallon Khaleesat da ta kasa tashi daga inda take zaune tace "C'mon Khaleesat, yana fa waje yana jira, and the weather is very cold outside, don Allah ki tashi mu je" Da kyar Khaleesat ta tashi tana jin bugun zuciyarta na tsananta ta dau Veil din Abayan jikinta ta yafa kanta a hankali, gaba daya jikinta a sanyaye yake don bata san ta yaya zata fara hada ido da Jay ba, Safiyyah na kallonta tace "Baza ki saka rigar sanyin ki ba?" Khaleesat ta girgiza mata kai kawai, Safiyyah tace "Saboda room heater ne fa yasa kike jin kamar ba sanyi sosai a garin, amma wallahi azababben sanyi ake a waje idan kika fita" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba don bata ma san me Safiyyah ke cewa ba, duk tunaninta ita dai da wani idon zata kalli Housemate dinta, Safiyyah ta tabe baki ganin Khaleesat taki tanka mata kamar ma bata san me take cewa ba, Safiyyah ta nufi kofa Khaleesat ta bi bayanta tana tafiya a hankali kamar mara lafiya, a haka suka fito parlor, Safiyyah bata ko kalli Surayyah dake zaune parlor tana ba yaronta abinci ba ta nufi kofar fita, ita dai Khaleesat na bin ta a baya walking slowly fuskarta dauke da damuwa, Surayyah ta bi su da wani shegen kallo har suka fita daga parlon, Khaleesat na hada ido da Housemate dinta dake jingine da motarsa ya rungume hannunsa taji wani kuka na neman taho mata from no where, amma ta dake ta sunkuyar da kanta tana biye da Safiyyah har suka iso dai dai inda yake tsaye, sau daya ya kalli Khaleesat ya dauke idonsa ya mayar kan Safiyyah dake gaishesa, ya amsa gaisuwanta da murmushi fuskar sa yace "Ya hanya?" Safiyyah tace "Hanya Alhamdulillah" Ita dai Khaleesat gefe ta koma ta tsaya har sannan ta kasa hada ido da shi tana wasa da veil dinta, nan kuma daurewa kawai take kar ta fashe da kukan dake cin ta, bayan sun gama gaisawa da Safiyyah, ya juya ya kalli Khaleesat for the second time, calmly yace "Housemate" Kamar jira take ta fashe masa da kuka sosai, ya sauke idonsa yayi shiru, after some seconds... walking slowly ya karasa har inda take tsaye yayi kasa da murya yana kallonta yace "Ina Jacket din ki?" Ta kasa cewa komai tana kuka a hankali tana girgiza masa kai, cire tsadadden rigar sanyin jikinsa yayi yana kallonta ya zaga ta bayanta yace "Wear this, the weather is cold" Ta gyada masa kai kawai wasu hawayen na sauka idonta ta amshi Jacket din nasa ta saka, lokaci daya kamshin turarensa da ta dade bata ji ba ya cikata ta ko ina ga kuma warmth din jikinsa from the Jacket, ji tayi kamar an yaye mata duk wani damuwar dake tunkushe a ranta, Ita dai Safiyyah na tsaye tana kallonsu, har cikin ranta take jin tausayin Khaleesat don tana jin ta ne kamar er uwarta ta jinin, Jay ya cire neck warmer din wuyansa ya daura mata kan Jacket din, ita dai Khaleesat ta kasa barin su hada ido, taji daddaden kamshin turarensa na kara mata wani irin nutsuwa da relieve, Ya juya ya kalli Safiyyah yace "Za mu je tare da ke can apartment din nata yanxu ko?" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk, let me get her luggages" Daga haka ta juya ta koma cikin gida, ya bude ma Khaleesat gaban motarsa yana kallonta, ita dai ta kasa hada ido da shi wasu hawayen na taruwa idonta ta shiga motar ya kulle gently, after some minutes Safiyyah ta fito da akwatin Khaleesat guda biyu ya bude booth ya saka a ciki, Safiyyah tace "Let me get the rest" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan ta dauko sauran kayan su ma ya amsa ya saka a booth, Safiyyah ta shiga back seat sannan ya zaga ya bude driver seat ya shiga, the ride was so silent ga snow da aka fara yi, after almost 20 minutes suka iso sabon Apartment din da Jay yayi renting ma Khaleesat, parking yayi a garage din apartment din yayi shiru, sai kuma ya jinginar da kansa da driver seat ya lumshe ido bayan ya tuna makullin apartment din na can gida ya bar sa, after some seconds ya Ι—an shafa kansa yace "Sorry... i think na mance makullin apartment din a can gidanmu" Reverse ya fara yi bayan ya fita garage din ya dau hanyar gidansu, ita dai Safiyyah tayi murmushi kawai bata ce komai ba, dai dai sanda wayarta ya fara vibrate ta duba taga Mustapha ne ke kiranta, hade rai tayi, tayi silencing kiran sannan ta kife wayar a cinyarta, wato ya dawo yaga bata gida shi ne zai fara doka mata kira, Jay na isa gidansu yayi parking a waje ya juya ya kalli Khaleesat da tayi nisa tunanin da take, yace "Let me get the keys Housemate" Bata bari sun hada ido ba ta gyada masa kai kawai, ya bude motar zai fita, ta kalli snow din dake sauka sai kuma ta kallesa, da sauri ta fara kokarin cire Jacket dinsa dake jikinta tace "Should i give you the Jacket? Naga akwai sanyi" Ya juya ya kalleta, sai a sannan suka hada ido all this while, taji kamar kasa ya bude ta shige tayi saurin sauke idonta, ya Ι—an yi murmushi yace "Don't worry, i will get another one idan na shiga gida yanxu" Daga haka ya sauka daga motar ya shiga gidansu. Bayan kusan minti goma sai ga shi ya fito daga cikin gidan yana sanye da wata rigar sanyin, Khaleesat dai kallonsa kawai take, ganin ya tsaya bakin gate din gidan nasu yana kallon direction daban yasa ta kalli direction din da yake kallo, sunkuyar da kai tayi bayan ta hango Ajay yana tahowa tare da katon karensa Legend yana rike da Leash din karen, Safiyyah tayi kasa da murya tace "That is Ajay, and ya kamata ki gaishesa gaskiya Khaleesat" Khaleesat ta Ι—an kalli Safiyyah, a hankali tace "Baza ki gane ba Sophie wallahi kunya nake ji" Safiyyah tace "To ya za ki yi? Dole dai haka zaki ajiye kunyan ki sauka ki gaishe sa, ni dai nasan baxai taΙ“a barin Jay yayi duk wannan hidimar da yayi maki shi kadai ba, tunda kan su a hade yake, nasan dole Jay zai yi shawara da shi before anything, Kuma tare za su yi komai..." Khaleesat ta kasa cewa komai amma har cikin ranta she is so ashame of speaking to him, har yau maganganun da Abdul yasa tayi masa ta waya na yawo a kanta, Safiyyah ta hade rai ganin Ajay ya kusa inda Jay ke tsaye tace "Pls Buckle up kiyi abinda ya dace Khaleesat, ni na tsani wannan halin kauyancin da kike yi wallahi, to meye a ciki gaishesa fa kawai zaki yi, ai ko ba komai kokarin da shi ma yayi maki ya kamata ki gaishe sa, abinda ya faru ya riga ya faru so forget that and do the needful" Jiki a sanyaye Khaleesat ta kai hannu zata bude motar, amma Ajay ko kallon inda suke bai yi ba ya wuce Jay dake tsaye yana jiransa yayi shigewarsa cikin gida, Jay ya bi bayansa, a sanyaye Khaleesat ta fasa bude motar ta juya tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "He is still angry at what you did to them, nasan zai huce definitely" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, after some minutes sai ga Jay ya fito daga cikin gidan ya bude driver seat ya shiga yace "Sorry for keeping u waiting, makullin apartment din na aljihun jacket dina ne, and Ajay wore the Jacket out for a walk" Safiyyah na murmushi tace "It's fine" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, wajen karfe biyar da rabi suka iso sabon Apartment din, ya kashe motar yana kallon Khaleesat a hankali yace "This is ur new apartment Housemate, i hope you will love it" Daga haka ya bude motar ya sauka, Safiyyah ma ta sauka tana kallon gidan tana murmushi don sama da kasa ne, Khaleesat ta goge hawayen dake makale idonta sannan ta sauka daga motar, bude masu kofar apartment din Jay yayi ya jira suka fara shiga sannan shi ma ya shiga, yayi switching din light din parlon da Heater, Safiyyah na murmushi tana bin parlon da kallo ganin yafi na tsohon Apartment din girma tace "Waow, this is soo beautiful" Jay ya zauna kan kujera yana duba wayarsa dake vibrate alamar kira, Safiyyah ta bude kofar da ta gani a parlor taga kitchen ne, ita dai Khaleesat na tsaye bayan kujera tana kallon Jay ta kasa cewa komai, Safiyyah ta fito daga kitchen din ta nufi sama zata duba dakunan gidan, after some seconds Jay ya gama sending message din da yake a wayarsa ya juya suka hada ido da Khaleesat, sauke idonta tayi tana wasa da gefen Veil dinta, Calmly yace "Housemate" Da kyar tace "Um" Ya mike ya dawo gabanta ya tsaya yana kallonta, a hankali yace "You like the new apartment?" Ta gyada masa kai tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba, bai sake ce mata komai ba don yana kallon fuskarta yasan kuka zata fara masa, Safiyyah ce ta sauko downstairs tace "Ya Jawwad wallahi gida yayi kyau Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya saka da alkhairi yasa kafi haka, my frnd is really grateful ba ma ta da bakin yi maka godiya shi yasa nake magana on behalf of her, mun gode sosai, Allah Ubangiji ya kare ka da sharrin mahassada, thank you so much Housemate we are really grateful" Ɗan murmushi yayi bai ce mata komai ba, Khaleesat ta goge hawayen da taji ya silalo idonta, Safiyyah tace "Toh ni zan tafi yanxu, yayana sai doka min kira yake, ya kirani yafi sau goma ban dauka ba" Jay yace "Ohk, to bari in yi dropping din ki" Da sauri Safiyyah tace "A'a wallahi ba sai ka ba kanka wahala ba Yaya Jawwad, har nayi order din Lyft gashi nan zuwa" Yace "Ohk then, my regards to everyone back home Safiyyah" Safiyyah na murmushi tace "In sha Allah" Sai kuma ta kalli Khaleesat tace "Toh mu je ki rakani kawata" ta kama hannun Khaleesat suka fita daga parlon, suna barin apartment din Safiyyah ta kalleta tace "If you like kar ki dena wannan kukan ki bude baki kiyi masa godiya sosai, shi yasa ma nace ki rakani don nasan halinki in kika fara kuka ba lallai ki masa godiya ba, in mutum yayi kukan sau daya ba shikenan sai ya rungumi kaddara ba yayi abinda ya kamata yayi move on, amma ke kiyi ta kuka kamar me takaba, i understand you are lost of words amma kiyi composing kanki kiyi appreciating dinsa plss, wallahi ban taΙ“a ganin mutum with kind heart like Jawwad ba, kuma shi tsakani da Allah yake abun sa ba don komai ba" Khaleesat ta fashe da kuka muryarta na rawa tace "I don't know where to begin Safiyyah, ban san ta inda zan fara masa godiya ba, i am just confuse" Safiyyah ta rungumeta tana patting bayanta a hankali tace "I understand Khaleesat, i understand you, nasan you are confuse, but just start from anywhere, tell him anything that means appreciation zai fahimce ki" Khaleesat ta gyada mata kai hawaye masu zafi na sauka idonta, a haka Lyft din Safiyyah ya karaso, Khaleesat ta kamo hannunta da kyar tace "Thank you for everything Safiyyah, thank you for always being by my side through thick and thin, thank you for being supportive, nagode Allah ya saka da alkhairi" Tana magana hawaye na zuba idonta, Safiyyah ta hade rai tace "C'mon Khaleesat, ni kar ki sake min godiya, don na dauke ki tamkar sister din da bani da ita ne, i care so much about you" Safiyyah ta zame hannunta ta bude bayan motar ta shiga ta kulle kofar sannan ta daga ma Khaleesat hannu, kai kawai Khaleesat ta gyada mata tana share hawayen da yaki tsaya mata sannan ta juya tana tafiya a hankali ta koma Apartment din, tana bude kofar parlon Jay ya juya ya kalleta sai kuma ya ci gaba da danna wayarsa, walking slowly ta nufesa har inda yake zaune ta durkusa kasa tana kallonsa, Kafin tace komai ya dakatar da ita ba tare da ya kalleta ba yana magana softly yace "I don't want ur thanks Khaleesat, bana bukata, ba don ki gode min nayi duk abinda nayi ba, nayi ne saboda Allah, nayi ne saboda kinyi deserving in yi maki, so bana bukatar godiyan ki pls, instead ki gode ma Allah" Khaleesat ta kasa cewa komai kanta a kasa hawaye na zuba idonta daurewa kawai take kar ta fashe masa da kuka, ya mike yace "Let me show you round the house before i leave" Tana goge fuskarta ta mike ta fara bin sa tana tafiya a hankali, kitchen ya fara kai ta, ita dai tana tsaye daga bakin kofa take bin kitchen din da kallo, hatta foodstuff duk ya siya mata, fridge din kitchen din ma was fully stocked up, ga cookies kala kala a kitchen din saboda yasan tana son cookies, ta kasa daurewa bata san sanda ta kamo hannunsa ba muryarta na rawa tace "Ban san ta inda zan fara maka godiya ba...." Ya Ι—an bude ido cause he never saw that coming, lkci daya yayi saurin janye hannunsa daga nata, yana murmushin karfin hali yana komawa baya ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "Nace maki bana bukatar godiyan ki, let me show you other places" Daga haka ya fita daga kitchen din, ta jingina da kofar kitchen din bayan ya fita tana kuka a hankali, sai da tayi me isarta sannan ta fito daga kitchen din tana jan kafa da kyar, tsaye ta gansa dai dai staircase yana danna wayarsa alamar ita yake jira, yana ganin ta fito daga kitchen din ya mayar da wayar aljihunsa ba tare da ya kalleta ba yace "The rooms are upstairs" Sai da ta karaso har inda yake sannan ya fara haura stairs din ta bi bayansa, ya fara nuna mata spare rooms guda biyu, sannan ya bude kofar nata dakin, calmly yace "Ur room" Ita dai tana tsaye bakin kofa tana kallon dakin babu ko kiftawa, ba abinda babu cikin dakin nan na comfortability, duvets ma manya hudu duk sababbi cikin case dinsu ta gani a dakin, the room look so beautiful sai wani sparkling yake, a hankali ta juya ta kallesa ya sauke idonsa bai dai ce mata komai ba, sai kuma ya juya ya bar bakin kofar dakin ya sauka downstairs ta bi sa da kallo, jingina tayi da kofar dakin for almost 5 mins tana kallon cikin dakin, a hankali ta juya ta bar bakin kofar dakin ta fara sauka downstairs cikin rashin kuzari, tsaye ta gansa bakin kofar fita daga parlon, yana ganin ta sauko yace "I will take my leave now Halysaah, amma dai sai jibi zaki shiga school, cause i see you look stressed" Ta gyada masa kai a hankali, yace "Ohk, here are the apartment key" Ta karasa ta karbi bunch din makullan da yake mika mata, sai kuma ta kallesa tace "Baka cire spare key ba?" Yace "A'a ki ajiye su kawai a wajen ki" Ta gyada masa kai kawai bata ce komai ba, ya bude kofar parlon without looking at yace "Text me ur Skin care set via WhatsApp" Yana fadin haka ya fita daga parlon yace "Good night Halysaah" Tana kallo ya kulle kofar parlon, after some minutes ta ji alamar tafiyar motarsa.

[7/6, 5:55 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat ta dade rabon da tayi bacci peacefully babu abinda ke damunta a rai kamar yanda tayi daren jiya, bayan tayi sallan asuba ta sake komawa baccin don garin akwai sanyi sosai, karfe takwas da yan mintuna na safe vibration din wayarta ya tasheta daga baccin da take, ta jawo wayar a hankali tana duba me kiranta duk da tasan bazai wuce Safiyyah ba, ai ko taga ita ce, picking din kiran tayi ta kai kunne murya can kasa tace "Sophie" Safiyyah tace "Nasan kina nan kina bacci ko?" Khaleesat tace "Um, Good morning" Safiyyah tace "Morning, amma baza ki shigo school ba yau?" A hankali Khaleesat tace "Sai gobe in sha Allah" Safiyyah tace "To Allah ya kai mu, ni dai gani har na shigo school din, amma fa gobe akwai get together da za mu yi na manta ban gaya maki ba, just few of us, ba mu wuce mu sha biyar ba duka, the time is 5pm prompt" Khaleesat tace "Cikin sanyin nan za ku yi get together Sophie?" Safiyyah tace "So? Kin ga alamar sanyi na hindering daily activities din mutane a kasar nan ne in dai ba snow bane yayi mugun yawa? Beside ai ba a open space za ayi get together din ba, it will take place at one of our Course mate House" Khaleesat tace "Toh ai shikenan" Safiyyah tace "Ban gane ai shikenan ba, banda ke za ayi get together din kenan kike nufi?" Khaleesat tace "Kema kin san bana son gathering ko ya yake Sophie, me yasa kika yi tunanin har da ni za ayi bayan kinsan bazan je ba" Safiyyah tace "Plss for once ki zama Social or should i even say Civilised Khaleesat, ko ba komai idan kika zo za kiyi nishadi ki mance duk wani damuwar ki na Nigeria kiyi freshen up din Ζ™waΖ™walwar ki for this semester, amma kawai kiyi ta zaman gida ke kadai kullum kamar me wani cuta, kin ga wannan shekara dayan da ya rage mana so nake ki waye ki fara yin abubuwa irin na wayayyu ta yanda babu wanda zai raina ki babu wanda zai san daga wani irin background kika fito, yanxu fa ba da bane a gareki Khaleesat don ke kin ma tsallake matsayin da mu bamu zo ba ma, don haka use this last opportunity in USA ki zama wise ta yanda babu shegen da zai raina ki" Khaleesat dai idonta a lumshe yake don har ta ci gaba da baccin ta, Safiyyah tace "Hello" Khaleesat ta bude ido da kyar tace "We will talk later Sophie" Safiyyah tace "Tun da ina gaya maki gaskiya ba dole kice we will talk later ba, kuma ko kin ki ko kin so sai mun je get together din nan da ke don yanxu ba da bane" Daga haka ta katse wayar ta, Khaleesat ta gyara kwanciyarta ta rufa da duvet zata ci gaba da bacci, ita kanta tasan bashin baccin da bata yi a Nigeria ne take biya....  Sai kusan karfe uku na rana Khaleesat ta tashi daga bacci, bayan tayi wanka tayi sallan azahar ta sauka parlor don yunwa take ji sosai, kunna heater din parlon tayi don parlon yayi sanyi kamar fridge, ta karasa ta tsaya jikin window din parlon ta daga labule tana kallon beautiful Neighborhood din ta, ko ina fari tas saboda snow din da aka yi sosai daren jiya da bai gama narkewa ba, after some minutes ta sake drape din windan a hankali ta nufi kitchen, shayi ta hada ta debi cookies ta dawo parlorn ta zauna, bayan ta gama ta kai plate din da cup kitchen ta wanke sannan ta koma sama don harhada textbooks dinta da reading materials, gaba daya sauran kayanta na tsohon Apartment dinta duk ta gansu a dakin alamar Jay ne ya kwaso mata su daga old apartment din nata, ta gama hada kan reading materials dinta, ta fara gyara kayan sawanta a press din dakin kenan taji an danna bell din gidan, ta Ι—an yi jim to be sure a apartment din take jin karan bell din, after some seconds ta fita daga dakinta ta sauka downstairs bayan an sake danna bell din, ta karasa har bakin kofar ta bude a hankali tana duba waye a bakin kofar, yana kallonta calmly yace "Good evening Halysaah" Ɗan murmushi tayi ta koma gefe don basa hanyar shigowa, yace "A'a kawai ki shirya, za mu je kiyi shopping abubuwan da kike bukata, i will wait for you inside in the car" Shiru Khaleesat tayi tana kallonsa, ganin zai koma motarsa tace "Amma ai ba abinda zan bukata yanxu, don naga akwai komai a gidan" Yace "For ur personal use Halysaah, beside ai babu cleaning agents a gidan, i forgot to get them..." Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, yace "I am waiting at the garage" Daga haka ya juya ya koma garage ta bi sa da kallo kafin ta rufe kofar ta juya ta nufi sama a sanyaye, bayan minti sha biyar ta sake saukowa downstairs tana sanye da jacket dinta, tana fita waje taji wani azababben sanyi duk da Jacket din jikinta, ta kulle gidan tana rike da makullin ta nufi motarsa, bude front seat din tayi ta shiga ta kulle, yace "Akwai sanyi ko?" Tana kara takurewa waje daya tace "Sosai, ni ban ma san akwai sanyi haka ba" Yayi murmushi ya kara dumin motarsa yace "Kina cikin gida da room heater ya za ayi ki san akwai sanyi" Murmushi tayi tana juya makullin hannunta ta Ι—an kallesa a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya Halysaah, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Hope you are comfortable in the new house?" Ta gyada masa kai tana kallonsa, yace "Good to hear that..." Tada motar yayi suka bar garage din, bayan sun dan yi nisa da tafiyar a hankali tace "Yaya Junaid fa?" Sai a sannan ya kalleta yace "Ajay yana gida, he is under the weather, baya son irin season din nan" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Ya kika baro su Umma and Aunty Farida?" Tace "Mun yi chatting dasu jiya da daddare, Umma tace tana son ta maka magana if you are around" Yace "Ohk to idan mun koma gida sai in kira ta" Khaleesat bata sake cewa komai ba, jifa jifa dai take kallonsa, shi kam ya maida hankalinsa kan driving din da yake, Wani babban Shopping mall ya kai su, bayan yayi parking sun shiga ciki ya dau shopping cart yana turawa, zata amsa cart din a hannunsa yayi murmushi yace "No, don't worry Halysaah, i will do the wheeling and u do the shopping" Ta sauke idonta bata ce komai ba, gun cosmetics ya fara kai su yace "Ki dauki duk abinda kika san za ki bukata a nan Housemate..." Ta Ι—aga kai ta kallesa, ya Ι—an bude ido yace "Look Halysaah, i want you to be free and open with me, kar ki saka komai a ranki ko kiji nauyin tambayar wani abu da kika san kina da bukata, assuming i don't have the means ai bazan ce zan yi ba Halysaah, so feel free plss Housemate, haka jiya nace ki turo min Skin care set din ki ba ki turo ba, ni ina maki duk abinda nasan zan ma kanwata ne ko er uwa ta, so ki dau duk abinda kika san kina da bukata yanxu" Ita dai idonta na kasa bata ce komai ba, ya mika mata katin kudinsa yace "Ko in baki katin in jira ki a mota?" Ta Ι—an kallesa sai kuma ta girgiza masa kai a hankali tana murmushin karfin hali tace "A'a" yace "Then shop all you need Housemate" Cikin sanyin murya tace "Ohk, Thank you so much" Shi dai murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba, few abubuwan da tasan zata yi needing take dauka a wajen cosmetics din tana ajiyewa a cart din da yake tura mata, amma idan ta dau abu daya sai ya kara mata biyu a kan wanda ta dauka, ita dai sai dai ta kallesa, ta dau set din Cream din shafawanta da shower gel, nan ma yayi doubling mata su ya zuba a cart, a hankali tace "Ina da saura fa" Bai ce mata komai ba, ta ci gaba da tafiya, tana kallon pad amma ta kasa dauka kawai ta wuce, shi ma kuma bai ce mata komai ba yana wheeling cart din har dai suka gama da bangaren cosmetics, ya nufi gun cleaning agents tana biye da shi abaya, duk shi ya dinga daukan abubuwan da yasan zata bukata a gida, sai bayan minti talatin suka fito daga shopping mall din ya zuba duk abubuwan da suka siya a booth din motarsa, maimakon su nufi gida sai taga ya kai ta wani babban store din Africa yace "I didn't get much cooking ingredients for you cause i am not good at that, so mu shiga sai ki dau duk me zaki bukata na girki...." Ta kallesa tace "To ai ko fara amfani da wanda ka siya ban yi ba" Yace "I know, zan Ι—an yi tafiya ne Housemate, so i want to be sure you have enough of everything" Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, yace "Mu je" Daga haka ya sauka daga motar, jiki a sanyaye ita ma ta sauka ta bi sa zuwa cikin store din, Spices din girki da su seasoning, albasa, irish, dankalin hausa, doya, eggs, all kind of peppers, tomatoes, da dai duk wani mahadin girki suka siya a store din, sannan ya kara mata frozen chicken da turkey, sai beef, bayan ya biya kudaden suka bar store din, yana driving Khaleesat ta kallesa cikin sanyin murya tace "Thank you so much, Allah ya sa kafi haka" Yayi murmushi kawai, sai kuma ya dau wayarsa dake vibrate yana dubawa, ganin Ajay ne ke kiransa yayi picking ya kai kunne yace "How are you feeling?" After some seconds ya ajiye wayar, Khaleesat tace "Is he sick?" Yace "Yeah, i told you he is under the weather" Khaleesat ta yi shiru, Jay ya kalleta yace "Ko mu je gidan ki dubasa?" Ta Ι—an buda ido, sai kuma tayi murmushi a sanyaye tace "Bazai kulani ba ai" Jay yayi dariyar da bai yi niyya ba yace "Saboda me bazai kula ki ba?" Ta sauke idonta tace "Jiya ma da ka je dauko makulli ai yayi kamar bai gan mu ba a mota" Jay yace "Jiyan nan ma da ku ka gansa ba shi da lafiya, sai da nace kar ya fita yaki saurarana, bayan ya fita kuma aka fara snow" A hankali Khaleesat tace "To Allah ya basa lafiya" Jay yace "Mu je can gidan za ki gaishesa?" Tayi shiru don har zuciyarta tana fargaban kar ya shareta, Jay yace "A bari next time ko?" Ta sauke idonta a hankali tace "To mu je, amma idan bai kulani ba ai shikenan" Jay yayi murmushi yace "Idan bai kulaki ba kema sai ki sharesa" Khaleesat ta Ι—an kallesa suka hada ido, murmushi tayi har sai da dimple dinta ya lotsa tana kallonsa, ya dauke idonsa ya maida dubansa kan titi yana ci gaba da driving dinsa gently. Kusan karfe biyar da rabi suka isa gidan, Jay yayi parking a compound ya kashe motarsa ya Ι—an kalleta yace "I can see you are tensed?" Ɗan murmushi tayi tana wasa da fingers dinta bata ce komai ba, ya bude motar yace "To mu shiga" A hankali ta bude motar ita ma ta sauka, ta bi Jay da kallo har ya dau hanyar entrance din babban gidan nasu, ta bi bayansa tana tafiya slowly, bayan ya bude kofar parlon sai da ya jira har ta iso, ta sunkuyar da kanta ta shiga parlon sannan shi ma ya shiga, sosai gabanta ya fadi bayan wasu memory sun dawo mata, memory that is so disturbing to her, tana tafiya a hankali ta karasa har cikin parlon ta zauna kan kujeran da ta zauna ranan da Jay ya kawota gidan da daddare, ta daga kai ta kalli Reading Nook din da Ajay ya zauna a ranan da daddare, sauke idonta tayi tana wasa da fingers dinta, Jay ya karaso cikin parlon yana kallonta yace "Give me some minutes" Ta gyada masa kai ya nufi stairs ta bi sa da kallo har ya haura sama, Jay na tafiya sama ya karasa bangaren Ajay ya bude kofar gently yana kallon cikin dakin nasa wanda babu haske sosai don Drape din dakin very thick one ne saboda sanyi, Jay ya shiga ciki ya kunna dim light din dakin yana kallon Ajay, kwance yake saman gado yayi rub da ciki yana bacci, har wani hucin zafi dakin yake tsabar yanda ya kure room heater, Jay ya karasa kusa da gadon yana kallonsa, lallai yanxu ya kara tabbatar da bai da lafiya, Ajay ne har za a bude masa daki a kunna wuta a shigo bai sani ba, ai duk baccin da yake kana taΙ“a kofar dakinsa yake tashi tun kafin ka shigo masa, Jay ya juya ya fita daga dakin ya jawo kofar gently amma bai kulle ba, ya koma downstairs yana kallon Khaleesat yace "Mu je sama Housemate, yana bangarensa" Mikewa tayi tana kallonsa ta nufesa, Jay yace "And before i forget, kiyi masa godiya he paid for ur new apartment" Khaleesat tayi shiru tana kallonsa amma ta kasa cewa komai, jiki a sanyaye ta bi Jay suka haura sama zuwa bangaren Ajay, Jay ya tura kofar dakin Ajay gently ya shiga sannan ya kalleta yayi mata alamar ta shigo, ta dake tana tafiya a hankali ta shiga dakin, haka kawai taji gabanta na faduwa, dakin nan nasa dai ne da tayi kwanaki biyu a ciki sanda take gidan, kallo daya tayi ma Ajay dake kwance kan gadon sannan ta kalli Jay, Kan lallausan farin carpet din dakin ta durkusa, Jay ya nuna mata kujera alamar ta zauna ta girgiza masa kai kawai, kamar yanda ta san dakin har yanxu komai na cikinsa fari ne kal, ga wani irin kamshi da dakin yake, amma fa ji tayi tana jin zafi saboda room heater din da ya kure, Jay ya karasa har inda yake kwance ya duka yana kallon fuskarsa ya janye Head warmer din da ya Ζ™ima a kai, calmly yace "Hey...." A hankali Ajay ya bude idonsa yana kallonsa, hade rai yayi cikin muryar bacci yace "Gerrout Jay, meye na shigo min Bedroom" Jay ya mike tsaye yana kallonsa yana murmushi yace "Kai baka shiga na mutane?" Ajay ya jawo pillow dake gefensa da kyar ya jefa masa yace "Gerrout Jawwad, i want to be alone, i think i am running temperature, i am feeling sleepy, can i speak to my dad? I want to speak to Ammi too" Jay yayi murmushi don yasan duk sumbatu yake kamar yanda ya saba in bashi da lafiya, Jay ya duka yana kallonsa yace "Should i get u a Cup of Coffee? And some drugs?" As if murmuring Ajay ya lumshe ido yace "Yess pls, but don't come back" Jay yace "To ta ina za a miko maka Coffee din?" Ajay bai bude ido ba yace "Drink it for me Jay" Jay yayi dariya yace "Ohk, amma an zo duba ka" Ajay ya bude idonsa da kyar yace "Don Allah ka fita, leave my room pls Jawwad" Sai kuma ya juya zai jawo wani pillown a fusace ya wurga ma Jay kawai suka hada ido da Khaleesat dake ta kallon ikon Allah, juyawa Ajay yayi da sauri ya kalli Jay amma tuni Jay ya nufi kofa trying not to laugh out loud ya fita daga dakin, Khaleesat ta bi Jay da kallo taji kamar ta tashi ta bi sa, Ajay ya kasa juyowa, yana kokarin tuna abubuwan da ya fada da Jay ya tashesa bacci.....

[7/7, 9:34 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat dai har sannan tana durkushe inda take a dakin ga gabanta sai faduwa yake, lkci lkci take satan kallon Ajay, bayan kusan minti biyu ya mike zaune daga kwancen da yake ya sauke kafafuwansa kasa yana facing bangare daban na dakin, he still can't recall all what he said to Jay bayan ya tashesa a bacci, after some seconds ya jawo head warmer dinsa ya saka, ya daure ya mike tsaye ya juya, hada ido suka yi ta sauke idonta a hankali, ya hade rai yace "What happened?" Girgiza kai tayi ba tare da ta kallesa ba tana wasa da farin carpet din da take durkushe tace "Kawai gaisheka na zo in yi ne" A takaice yace "Gaisheni for what? Do we have any agenda?" Sai a sannan ta daga kai ta Ι—an kallesa tace "And i want to say thank you for the apartment you got me" Kofa ya nufa yace "Karya yake maki, meye hadina dake zan biya maki apartment, ki dai je ki masa godiya...." Bata san sanda ta bi sa da wani irin kallo ba har ya fice daga dakin, can ta wani murguda baki ta mike ta nufi kofa, har zata fita sai kuma ta tsaya bayan ta hango wani abu a gaban mirror din dakin nasa, tana tafiya slowly ta karasa har gaban madubin tana kallon Hair ribbon dinta dake ajiye, ta dau ribbon din tana jujjuyasa tana kallonsa, wanda da alama sanda tayi kwana biyu a dakin ne ta manta shi, kofa ta nufa ta fita daga dakin tana rike da ribbon din nata, tana isowa dai dai stairs ta hango Ajay downstairs yana tsaye gaban Jay sai bala'i yake masa kamar ubansa, Jay dai na zaune yana kallonsa keenly yana cin chocolate din hannunsa, can dai Jay yace "Where is ur rod Ahmad? Ka mance baka sakko da bulalan ba ai" Ajay na masa wani kallo yace "Seriously kar ka sake min haka bana so, i did all what i did because of you not her, kawai don kar burden yayi maka yawa nayi ba don komai ba, meye na zuwa kace mata ni na biya mata apartment? Did i send you message? Upon how i warned you not to tell her amma sai da kaje ka fada, to yanxu riban me ka ci da kaje kace mata na biya mata gida?" Jay yace "Ashe dai lafiyarka qlau all this while Junaid? Where did u get this strength from all of a sudden?" Khaleesat dai ta taΙ“e baki ta fara saukowa downstairs, tana saukowa Ajay ya nufi stairs din fuskarsa a daure zai koma sama, Jay ya bi sa da kallo yana cin chocolate din hannunsa, Khaleesat ma ta bi sa da kallo kafin ya haura sama tace "Sai anjima, and thank you for everything, Allah ya kara budi" Ya wani juya ya kalleta yace "Kee kar ki sake min godiya, ko kinga ina wasa da ke ne?" Kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "Tunda kayi abinda zan maka godiya ai dole zan maka godiya, inda baka yi ba ai bazan maka godiyan ba, wishing you quickest recovery" Ɗan murmushi Jay yayi ya mike yace "It's getting dark, mu je inyi dropping din ki Housemate" a hankali Khaleesat tace "Ohk" daga haka ta bi bayan Housemate dinta ta bar Ajay tsaye bakin stairs din ya bi su da kallo har suka fita daga parlon.... Jay ya kalli ribbon din da take juyawa a hannunta bayan ya tada motarsa yace "Where did you get that from?" Ta kalli ribbon din tace "A dakinsa na gani" Jay yayi shiru yana kallon ribbon din, sai kuma yace "Kuma na ki ne?" Ta gyada masa kai tana kallonsa, ya amshi ribbon din yana kallo babu ko kiftawa, sai kuma yace "How did it get there?" A hankali tace "Sanda ka kai ni dakin nayi kwana biyu" Jay bai sake cewa komai ba ya mayar mata da ribbon din without looking at her, ya fara driving zai fita daga compound din nasu, bayan sun bar gidan calmly yace "Where did u see the ribbon in his room? Ko shi ya baki?" Ta girgiza kai tace "A'a, kawai hangosa nayi a gaban mirror din dakin" Jay yayi shiru bai sake cewa komai ba yana driving dinsa with calm, a haka har suka iso apartment din nata, bayan ya kashe motar ya sauka ita ma ta dau makullin apartment dinta ta sauka, Jay ya zaga ya bude booth zai fiddo shopping din da yayi mata, kawai bag din cosmetics dinta ya mika mata yace "Go with this, i will get the rest" ta Ι—an duka ta amsa sannan ta nufi kofar apartment din ta bude ta shiga ta kunna wutan parlon, sai da Jay ya tabbatar ya ajiye mata duk siyayyan da suka yi a inda ya kamata a kitchen din, wanda zai zuba fridge duk ya zuba mata, sannan yayi tidying din ko ina a kitchen din, ita dai tana tsaye jikin kofa tana ta kallonsa, yana juyowa ta sauke idonta ta juya a hankali ta bar kofar kitchen din ta koma parlor, bayan ya fito parlor yana kallonta yace "Ki turo min account details din ki let me send you Money for transportation to school" Ita dai Khaleesat kallonsa kawai tayi bata ce komai ba, yace "I am waiting, zan tafi ne" Ta sauke idonta tace "Ai akwai kudi a account din" Yace "Halysaah" Ta daga idanunta ta kallesa, yace "Turo min details din ki yanxu" Shiru tayi tana kallonsa, sai kuma tace "Ai bani da number ka" Yace "Oh, na manta, ina wayar naki?" Tace "Yana sama" Yace "To dauko" Sama ta wuce ya bi ta da kallo, sai kuma ya dauke idonsa ya zauna kan kujera, after some minutes sai ga ta ta dawo parlon, ta karaso har gabansa ta mika masa wayar, ya amsa without looking at her yayi dialling numbersa a wayar sannan ya mika mata yace "Save it" Ta amshi wayar, ta Ι—an yi jim kamar tana tunanin sunan da zata yi using tayi saving number nasa, after some seconds kawai ta saka My Housemate, ya mike yace "Turo min details din yanxu, zan tafi" Tura masa bank details din nata tayi, bayan yaga shigowar message din nata yace "Alright then zaki ga alert anjima, if there is anything just ping me via WhatsApp" a hankali tace "Ohk" Yace "Good night?" Sai da taga ya nufi kofa ta kasa daurewa cikin sanyin murya tace "Ka ce zaka yi tafiya?" Juyowa yayi ya kalleta yace "Sure Halysaah..." A hankali tace "Gobe zaka tafi?" Yace "Yeah that was my plan initially, but i think if Ajay is still sick zan yi postponing tafiyar zuwa Wednesday or Thursday" Khaleesat ta gyada masa kai, yace "Or is there anything Housemate?" Ta girgiza masa kai a hankali tace "Zaka dade ne?" Yace "I am going to UK, cousin sis dinmu ce bata da lafiya zan je in duba ta, idan naga she is much better zan koma Nigeria da ita" Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, after few seconds a hankali tace "Allah ya bata lafiya" Jay yace "Ameen, but do not worry Housemate, Ajay is around if there is anything nasan zai yi idan yaga bana nan" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a babu komai, i am okay, Allah ya kai ka lafiya" Jay yace "Ameen, amma idan ban tafi gobe ba we will meet in school in sha Allah" Kai kawai ta gyada masa, yayi mata murmushi yace "Good night" Tace "Thank you very much Housemate, Allah ya saka da alkhairi" Ya dora finger daya a lips dinsa yana kallonta da kyawawan idanunsa, sauke idonta tayi, ya juya ya fita daga parlon, ta karasa window din parlon ta tsaya tana kallonsa ta Drape har ya bar garage din da motarsa sannan ta sake drape din a hankali ta juya, after some minutes tana jan kafa ta karasa ta kulle kofar parlon. Washegari Khaleesat ta fito lecture Hall saboda message din da Jay yayi mata ya shigo school din yana jiranta, dama ba lectures suke ba suna tutorial na wani course dinsu ne kawai ta ce ma Safiyyah tana zuwa sannan ta fito, exact spot din da yake jiranta sanda take exam ta hango sa zaune, gaba daya attention dinsa na kan wayarsa da yake dannawa, yanda yayi keeping serious face ya fito da ainahin handsomeness dinsa, sam bashi da wata makusa, he is just the real definition of handsome, everything about him is just perfect, tun daga nesa Khaleesat take kallonsa bata yi realising ba sai ganinta tayi har ta iso inda yake zaune, ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike ya mayar da wayarsa aljihu yace "Good Afternoon Halysaah" ta sunkuyar da kai tana Ι—an murmushi don sai ta ganta er karama a kusa da shi, yace "Hope ba lectures ku ke ba?" Ta girgiza kai tace "A'a" Yace "Ohk, my flight is in 2 hours time in sha Allah" Ta daga kai tana kallonsa a sanyaye, suna hada ido ta sauke idonta tace "Ya Junaid yaji sauki kenan?" Jay yace "Yeah he is better, shi ne ma yace in tafi..." Khaleesat bata sake cewa komai ba, yace "Kin yi lunch ne?" Duk da bata yi ba ta gyada masa kai alamar tayi, yace "Ohk ke da Safiyyah?" Tace "Um" Yace "To shikenan, i came to tell you i am leaving, take care of ur self Housemate, kuma kiyi concentrating a karatun ki, if there is anything just ping me via WhatsApp" A hankali Khaleesat tace "Dadewa zaka yi kenan?" Yayi murmushi yace "Bazan dade ba in sha Allah, nasan dai daga can definitely za mu je Nigeria" Khaleesat ta kasa kallonsa don sai taji kamar hawaye na neman ciko mata a ido, ta dake tace "To shikenan, Allah ya kai ka lafiya, ya tsare" Yana kallonta yace "Ameen" Taki barin su hada ido tace "Muna karatu ne da su Safiyyah zan koma" Yace "Ohk" Tace "Sai anjima" Bata jira cewar sa ba ta juya zata bar wajen tun kan hawayen da ya cika idonta ya zubo, Calmly yace "Halysaah" kin juyowa tayi, ya zaga har gabanta ya tsaya yana kallonta, ta kasa kallonsa tana goge hawayen da ya fara zuba idonta, shiru yayi yana kallonta, after some seconds ya dauke idonsa a hankali yace "But you have Safiyyah here Housemate...." Ta gyada masa kai tana murmushin karfin hali, yace "In sha Allah bazan dade ba i promise" Nan ma dai kai kawai ta gyada masa, yace "Ko za ki rakani Airport din?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, still tana murmushi ta girgiza masa kai, bai yi wani insisting ba bayan ya tuna Ajay ne zai yi dropping dinsa a airport din, dai dai nan wayarsa dake aljihunsa ya fara vibrate, ya ciro wayar yana duba me kiransa, ganin Ajay ne yayi picking ya kai kunne, after few seconds ya katse wayar yana kallonta yace "Mu je to ki rakani, our car is somewhere around here" Ta gyada masa kai suka fara tafiya gun motar, tun daga nisa ta hango Ajay dake tsaye jikin mota yana jiran Jay, wayarsa ce a hannunsa yana dannawa with his full attention, Khaleesat ta Ι—an kalli Jay, sai a sannan taga kaman da suke yi da Ajay, Jay ya kalleta speaking slowly yace "Ko zaki koma daga nan?" A hankali tace "Ohk, Allah ya kiyaye hanya" Yace "Ameen" Kamar ance Ajay ya daga kai yayi ido huda da su, Jay ya dauke idonsa yana kallon Khaleesat yace "I will drop you a WhatsApp message idan na isa, just go" Ta gyada masa kai, ta Ι—an kalli Ajay suka kara hada ido, sai kuma ta kasa tafiya, murya can kasa tace "Ko dai kawai mu je gun motar sai in gaishesa tunda ya gan mu?" Ba tare da Jay ya kalleta ba yace "Ohk" a haka suka karasa gun motar, Khaleesat na kallon Ajay da ya ci gaba da danna wayarsa tace "Ina yini?" Jay ya zaga ya bude front seat ya shiga ya kulle motar, ita dai tana tsaye don Ajay bai amsa gaisuwan ta ba bai kuma kalli inda take ba, after some seconds ya daga kai ya kalleta yace "Idan kika gaishe da Jay ya wadatar, ni ki dena gaisheni" Tana kallonsa tace "Saboda me" Ajiye wayarsa yayi yana kallonta da mamaki, can yace "Na fara wasa da ke ne?" Still tana kallonsa tace "To ai kar watarana kace bana gaishe ka shiyasa nake gaishe ka yanxu, once again thank you for the new apartment" Yace "I will slap you idan baki fita a gabana ba" Tayi masa wani kallo ta juya ta fara tafiya, ya bi ta da kallon mamaki, ta sake juyawa suka hada ido don kallonta kawai yake, ta zumbura baki tayi wucewarta, sai da ya dena hangota ya bude driver seat ya shiga ya fara balbale Jay da bala'i yana cewa "Ka ga ka dena hadani da yarinyar nan Jay, don na lura tun da taje ta san menene aure ta karo wani rashin kunya na musamman" Dakatar da shi Jay yayi fuska daure yace "Pls bana son hayaniya Junaid" Tada motar Ajay yayi ya fara driving, after some minutes ya juya ya kalli Jay yace "What happened? Wa ya bata maka rai?" Jay na danna wayarsa yace "Never Mind" Ajay bai sake ce masa komai ba ya ci gaba da driving din da yake. Murmushi Khaleesat tayi ta bude handbag dinta ta saka wayarta ta mike tace "Ai kuma sai kiyi, naga dai ba dole bane sai naje wani get together ko?" Safiyyah ta rike Abayan jikinta rai bace tace "Wallahi dole ne Khaleesat, wai don Allah me yasa kike haka ne? Me yasa kike da taurin kai haka? Sai yaushe zaki waye ki fara abu irin na mutane wayayyu? Wallahi na fara gajiya da halin ki, babu wanda ya isa ya baki shawara ki dauka kike nufi ko me?" Khaleesat tayi dariya tace "Yau nake ganin ikon Allah, duk saboda nace maki bazan bi ki ba? To naji zan je amma ni ko minti talatin bazan yi ba a wajen" Safiyyah da fuskarta ke daure har lokacin tace "Naji, mu tafi gidan naki mu shirya" Khaleesat tace "Meye da kayan jikina da bazan je da shi ba?" Safiyyah tace "A'a wallahi a gan ki tun safe da kaya anjima kuma a sake ganinki wajen get together da shi? Ni ma ga kayana da zan canza cikin jakan laptop dina, bari in mana order din Uber mu tafi gidan naki" Khaleesat dai ta tabe baki bata ce mata komai ba, Safiyyah ta gama order din ride din sannan ta mike har sannan tana rike da Khaleesat, Khaleesat tace "Ikon Allah, to ki sakeni mana ko guduwa zan yi?" Safiyyah tace "Na san maki?" Dariya kawai Khaleesat tayi a haka suka tafi inda za su jira Lyft dinsu, wajen karfe hudu suka isa apartment din Khaleesat, sai da suka yi sallan azahar sannan suka shirya, Safiyyah har da make up, Khaleesat dai ko powder bata yarda ta shafa ba, Safiyyah ta kyaleta da baΖ™in halinta don lallabata take kar ta canza mind dinta, a haka dai suka bar gidan wajen karfe biyar saura.

 

 

[7/8, 9:34 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Tun da suka iso gidan Coursemate dinsu Clara da aka yi organizing Get together din Khaleesat ta nemi waje a parlon ta zauna tayi isolating kanta totally daga cikin mutane don sun tarar har an fara taron ana ta nishadi, yawanci duk turawa ne sai few Africans da kuma student from other Continent, simple girke girken turawa da snacks iri iri ne a parlon sai drinks with so many chocolate, sannan ga tea with cookies, tuni Safiyyah ta shige cikin Coursemate dinsu ana ta shagali dama duk ta saba da su unlike Khaleesat da ba kowa take hulda da shi a department din nasu ba, lokaci lokaci Khaleesat ke kallon Safiyyah don a rayuwa idan akwai abinda ke saka Safiyyah farin ciki da nishadi bai wuce Chilling da partying with friends ba, har mamakinta Khaleesat take ko gajiya da harkar party bata yi, tana son life sosai ba kadan ba, bata ki a gayyaceta wani partyn gobe ba tsaf zata je, Khaleesat dai wayarta kawai take dannawa tana yi tana kallon agogo don dama tace minti talatin kawai zata yi, sai ga Safiyyah ta nufo tana washe hakora da glass din wine ta mika mata tace "Haba Khaleesat ki tashi ki shiga cikin jama'a mana ayi shagali da ke, sai tambayata suke if you are okay, ke in baki kunyata mutum ba baki ji dadi ba, ni dai ga glass din wine na kawo maki" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "A'a ni bazan sha ba, thank you" Safiyyah ta hade rai tace "Ke Non-alcoholic wine ne fa, sai kace ban san abinda nake ba, it's non alcoholic" Khaleesat tace "Na sani, kawai bana sha ne, kema kinsan drink ba wani damuna yayi ba" Safiyyah ta kyabe baki ta juya ta koma cikin yan ajin su, ba iya Coursemate dinsu kadai bane a wajen har da few masters student, wa enda suke Pursuing masters dinsu a course din da su Khaleesat ke Degree din sa, tun da Khaleesat suka shigo parlon dama ta lura da wani mutumi dake zaune shi ma yayi isolating kan sa a gefe yanda ita ma tayi, shi ma kuma wayarsa kawai yake ta dannawa da glass din wine a hannunsa, tana ganinsa ta gane bahaushe ne amma ta fuske a inda take a zaune, lokaci lokaci yake kallon direction dinta, kawai mistakenly ta daga kai suka hada ido da shi, ta maida kanta kasa tana danna wayarta with full concentration, mikewa yayi ya nufota har sannan yana rike da glass din wine, tana ganin alamar ya nufo inda take taki dago kanta har ya karaso wajenta, jingina yayi da bango daga gefen inda take zaune yana kallonta yace "Good evening" Ba tare da ta dago kanta ba a takaice tace "Ohk" Ya mayar da wayarsa aljihunsa yana kallonta yace "African?" Ta girgiza masa kai kawai, yace "But Safiyyah is your friend" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa a karon farko babu yabo babu fallasa tace "So???" Ya Ι—an bude ido yana murmushi yace "Safiyyah that i know is from Africa, Nigeria precisely" A takaice tace "I don't know what you are talking about pls, because Safiyyah is my frnd doesn't mean we have to be from the same continent" Fuska daure ta kare maganar ta, calmly yace "Not at all, you sound provoked, sorry if u feel offended..." Mayar da wayarta tayi jaka with the intention of leaving the house gaba daya, sai ga Safiyyah ta nufo su da plate din cake a hannunta zata kawo mata, tana ganinsa tace "Ohh Aymaan, i didn't even notice you here, ashe ka zo" Ya gyada mata kai yace "Yeah, good evening Safiyyah" Tana murmushi tace "Evening Aymaan" Yace "Ya sunan kawar taki ne?" Safiyyah na murmushi tace "Ohh, her name is Khaleesat" Ya gyada kai yace "Ta ce min daga wani Continent din daban take not Africa, i saw she was sitted alone, shi ne na zo nan so we while away time together, but she took it personal, i think i wilk take my leave" Yana fadin haka yayi murmushi ya fara tafiya zuwa inda yake zaune, Safiyyah ta kalli Khaleesat tayi kasa da murya tace "Na shiga uku, yanxu kenan baza ki taΙ“a canzawa ba  Khaleesat, ke baza ki koyi siyasa ba a rayuwar nan? Meye ne don ya zo ya sameki? kin zata cewa zai yi yana son ki? Ai shi kuma Aymaan ba haka yake ba, Masters dinsa ma yake shi yasa baza ki wani san sa a department din ba, he is the son of the Deputy governor of a state in Nigeria" Khaleesat ta wani kalleta tace "So??" Safiyyah tace "Maida wukar, nan da kika gansa ma ba lafiya garesa ba, chronic ciwon zuciya yake battling with, you think he have time for any relationship aside friendship? Beside iyayensa ma sun masa aure yana da mata haka da kika gansa, kawai don ya gan ki zaune shi ne ya zo to keep you company amma ba wani abu ba, kuma da aka yi inviting dinsa get together din ma yace bazai zo ba, nasan Nora ce ta takurasa ya xo, ita wai son sa take kamar zata yi yaya, ko me zai yi da baturiya, ke kuma ki sha kurumin ki ba cewa zai yi yana son ki ba he is Married..." Khaleesat dai bata ce komai ba, can ta kalli Aymaan din taga ya koma inda yake zaune yana danna wayarsa kawai sai taji wani iri a can kasar zuciyarta, sai take jin kamar bata kyauta ba yanda tayi shunning dinsa kamar jiransa take dama, Safiyyah ta tabe baki ta mika mata plate din cake din hannunta tace "Ni dai ga shi, kuma ki taso za mu yi hotuna, in shi ma din baza kiyi ba sai mu ji...." Khaleesat ta amshi plate din ta ajiye duk da ba ci zata yi ba amma kawai jaraban Safiyyah ne bata so yasa ta amsa. Haka nan Khaleesat babu yanda ta iya ta tashi za su yi hotuna da Coursemate dinta, yawancin su duk shakkar interacting da ita suke don ko murmushinta baka gani a department balle dariyarta, bata kuma kula kowa sai dai gaisuwa shi ma sama sama saboda Safiyyah, tunda Safiyyah kowa nata ne, yawanci duk hotunan da suka yi Ayman yana ciki shi ma kuma sai da aka je aka gayyatosa ya zo ayi pictures, daga karshe ya mika ma wani abokinsa wayarsa yace yayi masu hoto da Safiyyah, ita dai Khaleesat na tsaye gefe kamar bata ma san abinda suke yi ba nan kuwa slightest opportunity take nema da zata fita daga parlon ba tare da Safiyyah ta lura ba, abokin yayi masu hoto da Safiyyah tana washe hakora as usual, sosai kuma hoton yayi kyau, sai kuma ya mika ma Safiyyah wayar tasa yace "To yi min da kawarki, Khaleesat ko?" Safiyyah na murmushi ta amshi wayarsa da yake mika mata tace "Eh, her name is Khaleesat..." Komawa yayi kusa da Khaleesat ya tsaya yana kallonta yace "Let take a snap Khaleesat" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, amma da ba don abinda Safiyyah ta gaya mata a kansa ba da babu abinda zai sa ta tsaya wani yin hoto da shi, fuskarta babu yabo babu fallasa take kallon Safiyyah da ta saita waya zata masu hoton, Safiyyah ta wani kankance ido tana kallonta alamar ta saki ranta mana, kamar irin uwarta din nan haka tayi mitsi mitsi da ido tana kallonta, Khaleesat bata sanda tayi dariya ba don ba karamin dariya Safiyyah ta bata ba, Safiyyah tayi using wannan Opportunity din tayi snapping dinsu pictures kusan biyar tare da Aymaan, shi dai Aymaan kallon Khaleesat yake don bai zata tana dariya ba, abokansa biyu ma suka yi joining hoton, da wasu turawa, a haka Safiyyah ta gama masu pictures din ta mika masa wayarsa, yayi murmushi yace "Thank you Safiyyah" Safiyyah tace "Bari in sa maka numberna ka min sending pictures din pls" Ya bata wayar yace "Alright" Take away Safiyyah tayi ma Khaleesat ganin bata ci komai ba a wajen, Khaleesat dake ta kula da agogo tana ganin karfe bakwai da kusan rabi tayi ordering ride da zai maidata gida ba tare da Safiyyah ta sani ba, ride din na isowa cikin dubara tayi sneaking ta bar parlon without letting Safiyyah notice her. Wajen karfe goman dare sai bayan Khaleesat ta gama duk abinda zata yi tayi shirin kwanciya sannan ta bi miss calls din Safiyyah da tayi mata kusan hudu tun daxu, Safiyyah na dagawa tace "Sannu kin kyauta Khaleesat, da kince min zaki tafi ai ba hanaki zan yi ba, sai ma kilan in samar maki motar da zai maida ke gida, amma ba sai kin sulale kin tafi ba" Khaleesat tace "Uhm ke din ce baza ki hana ni ba?" Safiyyah tace "Ke kika jiyo kuma, da na sani ma da ban taho da ke ba wallahi, ba wani amfanin da zuwan ki yayi, Coursemate dinmu sai cewa suke me yasa kike haka baki da walwala ko kina battling da wani ciwo ne da yake sa kike haka" Khaleesat tayi dariya tace "To kun gama party din ko har yanzu kuna can kuna yi? Ko dai till dawn ne party din? Ya Mustapha bai yi ta kiran ki ba?" Safiyyah tace "Ban sani ba" Daga haka ta katse wayarta, Khaleesat tayi murmushi ta bude WhatsApp dinta, sosai gabanta ya fadi ganin message din Housemate dinta ya shigo, dama saboda shi ta kunna data ta shiga WhatsApp din nata, sai taga hoto ya turo mata kawai, ta kalli time din da ya turo ta ga tun karfe tara ya mata sending image din kuma iya shi kawai babu wani sako, ta shiga DM dinsa sai taga yana ma online, ta fara downloading hoton, lokaci daya ta mike zaune daga kwancen da take tana kallon hoton da ya turo mata babu ko kiftawa, ta cire duvet din jikinta tsabar yanda ta girgiza da wannan hoto, hoton da Safiyyah tayi mata da Aymaan ne tana dariya, ta kasa daina kallon hoton with confusion, to a ina yaga hoton nan? How did he get it? Wani kyau na musamman tayi a hoton saboda dariyar da take, shi kuma Aymaan dake gefenta ya kafeta da ido shi ma yana murmushi a hoton, ajiye wayar tayi don gaba daya kanta ya gama kullewa, to ko dai Safiyyah ta dora a status ne tunda yana da numberta, ko kuma yasan Aymaan ne? da sauri ta dau wayar tana kokarin duba status din Safiyyah, ai kuwa ta ga ita ce ta dora kusan duk pictures din da suka yi a get together din, hotunan da ta dora sun kusa 15 a status, sauka tayi daga WhatsApp din tayi dialing number Safiyyah yana fara ring ta daga, Khaleesat tace "Safiyyah me yasa zaki dora har da nawa hotunan a status din ki?" Safiyyah tace "Ban gane ba? Is there anything wrong don na dora hoton ki a status dina?" Khaleesat da taji ranta yayi mugun bace tace "Then why will u upload har da wanda muka yi da wannan mutumin nan?" Safiyyah tace "To fa" Sai kuma da sauri tace "Ohhh sorry wallahi na mance the situation on ground bari in je in goge Khaleesat, wallahi na manta" Khaleesat tace "Yanxu gashi Housemate dina ne ya min fowarding hoton wanda muka yi da mutumin fa" Cikin sanyin murya Safiyyah tace "Ni wallahi mancewa ma nake kina iddah ne, bari in je in goge yanxu, to amma dai ghost viewer ne Housemate din nan naki don ni bana ganin ya bude status dina kuma yana budewa wani lkcn... Let me go and delete them" Katse wayar Safiyyah tayi, Khaleesat taji kamar tayi kuka saboda bakin ciki da takaici, ita irin dariyar da tayi a hoton ne ma yafi kona mata rai, nan kuma ba a san Safiyyah ce ta bata dariya ba, can dai ta sake shiga WhatsApp ta shiga Dm din Housemate dinta taga yana online har sannan, ignoring hoton da ya turo mata tayi ta tura masa Good evening, hope ka isa lafiya? Har bayan minti goma bata ga yayi reply ba kuma yana online din, gaba daya duk jikinta yayi sanyi, after another 5 mins tayi deciding ta kirasa ta WhatsApp call, har call din ya katse bai daga ba, kuma tana ganinsa online, kashe datan ta tayi, ta ajiye wayar a sanyaye ta kwanta, amma ta kasa bacci har kusan karfe sha biyun dare, daga karshe ta mike zaune ta kara jawo wayar ta kunna data ta hau WhatsApp, har sannan taga bai mata reply ba kuma yayi uploading status din abun kwallo 30 minutes ago, taji hawaye ya cika idonta ta kashe datan ta ajiye wayar ta koma ta kwanta tana goge idonta. Washegari wajen karfe goma na safe Khaleesat ta gama shiryawa zata tafi school, duk da sai karfe biyu suke da lectures ranan amma taji gwara kawai ta tafi schl din, har sannan she is moody tun da ta bude WhatsApp dinta bayan da tayi sallan asuba taga har sannan bai mata reply ba bata sake hawa WhatsApp din ba, tana zaune parlor tana jiran Lyft din da tayi ordering, ta bude handbag dinta ta ciro wayarta ta kunna data ta shiga WhatsApp, bayan messages dinta sun gama shigowa still dai bai mata reply ba, ta bude voice note din Aunty Farida bayan ta saurari abinda ta ce mata, ta mayar mata da reply, WhatsApp call Aunty Farida tayi mata don tana online, ta daga bayan ta kara gaisheta daga daya bangaren Aunty Farida tace "To Khaleesat in Jawwad din shi baya nan ki hada mu da Junaid mana" A hankali Khaleesat tace "To ai ba wai muna haduwa bane a schl Aunty, inda nake daban inda suke daban" Aunty Farida tace "Ya naji muryarki haka, lafiya dai ko?" Khaleesat ta Ι—an yi yake tace "Ba komai, kawai dai akwai sanyi ne kuma gashi zan fita school yanxu" Aunty Farida tace "Kuma rigunan sanyi biyu kawai ki tafi da shi ko?" A hankali Khaleesat tace "Eh, amma Ya Jawwad ya bani wani" Aunty Farida tace "Toh shikenan, ko Junaid din ne ki hada mu da shi, kinga ba dadi har yanzu bamu ce masu komai ba ba ayi masu godiya ba, kuma duk laifin ki ne, tun yaushe muke ta bin ki, Babanki ma sai da yayi magana daxu" Khaleesat tace "To zan hada ku idan mun hadu Aunty, Umma fa?" Aunty Farida tace "Umma tana lafiya" Khaleesat tace "To shikenan, zan tafi schl yanxu sai anjima" Aunty Farida tayi mata sallama, sannan Khaleesat tayi ending call din, status taga Housemate dinta yayi uploading tun karfe tara na safe, ta bude status din, kallon hoton dake status din ta dinga yi babu ko kiftawa don lkci daya ta ganeta, ta kalli caption din da yayi mata hoton, next photo din ma na yarinyar ne tare da shi kuma da alamar new pictures ne ba old ones ba, da har zata fita daga WhatsApp din sai kuma tayi screenshot din hotonsa da Hadeeyah, ta shiga DM dinsa taga yana ma online, sending masa hoton tayi sannan a kasa ta rubuta ur sick Cousin? After few minutes taga ya mata reply yace Halysaah... Bata mayar masa da reply ba, ta tafi zata duba last picture din status din nasa taga ya goge duk hotunan daga status din nasa, ajiye wayar tayi for almost 5 mins, can ta dauka zata fita daga WhatsApp din sai ga WhatsApp call dinsa ya shigo, har ya katse bata daga ba, daga karshe ta kashe data dinta ta saka wayar cikin handbag dinta. Har Khaleesat ta isa school bata san ta isa ba don gaba daya hankalinta baya jikinta, ta sauka daga Lyft din tana tafiya a hankali kamar mara lafiya, all through lectures dinsu na ranan kawai gata nan gata nan ne a hall, ko sanin abinda ake koyarwa ma bata yi ba, ta rasa menene ya tsaya mata a rai haka, bayan sun fito lectures din Safiyyah na kallonta tace "Wai har yanzu fushi kike akan hoton da na dora Khaleesat? Kin san fa bazan yi hakan da gan gan ba, don Allah kiyi hakuri, wallahi yayi escaping mind dina ne situation din dake at hand, ko fada Housemate din naki yayi maki ne?" Khaleesat ta girgiza kai trying to sound ok tace "A'a ni fa kaina ne ke min ciwo amma ba wani abu ba, gida ma nake son zan tafi yanxu" Shiru Safiyyah tayi trying to be sure of wanda take hangowa nesa da inda suke zaune, can ta kalli Khaleesat....

[7/9, 9:08 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Sau daya Khaleesat ta kallesa ta dauke kai bayan tayi convincing kanta ba wajensu yake tahowa ba, Safiyyah tayi kasa da murya tace "Ni ban ma taΙ“a ganinsa a school din nan ba sai yau, gwara Housemate dinki shi dama ya saba zuwa ya same mu a nan sanda muke Exam, he is coming toward us fa" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba amma can kasan ranta ita ma tayi mugun mamakin ganinsa a department dinsu, how did he even know spot din da suke zama da Safiyyah, sai kawai tayi assuming hanya ce ta biyo da shi ta nan din, har ya iso inda suke zaune Khaleesat bata daga kai ba but she is surprise, Safiyyah na kallonsa tana murmushi tace "Good afternoon Ya Junaid" Ba tare da ya kalleta ba yana kallon different direction yace "Evening, can you excuse us... I want to have a word with ur Coursemate" Safiyyah dai bata fasa kallonsa ba tana gyada kai tace "Sure, why not...." Sai kuma ta dau jakanta ta mike tana kallon Khaleesat tace "Zan je wajensu Nora, if you are looking for me ina can..." Khaleesat ta gyada mata kai kawai, daga haka Safiyyah ta bar wajen, ita dai Khaleesat mamaki ma yasa ta kasa kallon Ajay dake tsaye kanta, he wants to have a word with her? To me zai ce mata da zai biyota har department din su, duk da under same faculty suke amma ko da wasa bata taΙ“a haduwa da shi a school ba in ba few days ago ba da suka shigo da Jay, ta kalli wayar da yake mika mata fuskarsa babu yabo babu fallasa, she was surprise, why is he giving her his phone? bata amshi wayar ba ta daga kai ta kallesa a karo na farko, ganin yanda ya daure fuska ya sa ta mika hannu ta amshi wayar tana kallon screen din, sosai gabanta ya fadi ganin hoton da suka yi da Aymaan jiya a get together, ta dinga kallon hoton babu ko kiftawa, gashi ba hoto daya ba ba kuma biyu ba, can ta kalli a ina yaga hoton sai taga a Instagram ne, bata san sanda ta gyara zama ba zuciyarta na bugawa sosai, Instagram kuma? Me ya kai hoton Instagram? ta shiga uku, ita da ko a screen din wayarta bata taΙ“a saka hotonta ba balle aje ga WhatsApp ko kuma facebook uwa uba Instagram, gaba daya hankalinta yayi mugun tashi ta kasa cewa komai, da kyar ta daga kai ta kallesa ta ga wani irin kallo yake mata, ta sauke idonta gabanta na ci gaba da faduwa ta kasa cewa komai, fixge wayarsa yayi daga hannunta yace "So you came back fully prepared to party in Baltimore Right? You came back to mingle with jobless guys following them to party up and down, Har kin ma mance abinda ya same ki, but wait... Baki taΙ“a zuwa islamiyya bane ko kuma kin je kin yi skipping classes? Ko kuma bayan mijin da kika ce a kyaleki kina son zama da shi ya sake ki baki zauna kin tambayi makusantan ki what next ba? Kawai saboda kina jin kanki on a different level yanxu shi yasa kika kama hanya kika tafi cikin kattin banza masu shaye shaye da sunan get together, har ki tsaya gefen wannan crook guy din ayi maku hoto kina dariya" Khaleesat ta kasa daurewa ta fashe da kukan da tun safe take son yi bata samu kwakkwaran reason din yin sa ba, shiru yayi yana kallonta irin kallon mamakin nan, after a minute ya zauna inda Safiyyah ta tashi amma bai ce mata komai ba, ita kuma bata fasa kukan da take ba kamar an aiko ta, tayi me isarta don kanta ta hakura ta fara goge idonta tana sauke ajiyar zuciya, sai a sannan ya kalleta yace "Ohk i understand, kin dawo America ne kiyi abinda ranki yake so ba kuma kya bukatar wani yace zai yi questioning din ki ko kuma yayi correcting din ki" Wani sabon kukan ta fara yi kamar ana tunzurata, ya mike trying to control himself yace "Get up" ganin taki tashi ya hade rai yace "Baza ki tashi ba?" A hankali ta mike tana ci gaba da goge hawayen dake zuba idonta tana shesshekan kuka, babu yabo babu fallasa yace "Mu je" Bata masa musu ba ta fara bin sa har sannan tana goge hawayen idonta, after almost 10 minutes walk suka iso inda yayi parking motarsa, yana bude motar ta daga kai ta kallesa a hankali tace "Ni ban ce ma Safiyyah zan tafi ba" Ya mata wani irin kallo yace "Baza ki ce mata ba, get in the car" Bata ce komai ba ta zaga ta bude gaban motar ta shiga, bata taΙ“a shiga motarsa a America ba sai ranan, har suka isa Apartment dinta babu abinda yace mata, bayan yayi parking without looking at her yace "Leave my car" Sauke idonta tayi, ta bude motar a hankali ta sauka ta kulle masa tana kallonsa tace "Don Allah tunda ka san sa kayi masa magana ya goge hotona a Instagram" Ya jefa mata wani kallo yace "Zan gaura maki mari, ni na hada ku nayi maku hoton da zan ce masa ya goge?" Daga haka yayi Reverse yayi zoom off daga Neighborhood din, wasu sabbin hawaye suka cika idonta ta juya tana tafiya a hankali ta nufi kofar apartment dinta ta bude ta shiga, zaunawa tayi a parlor ta fara tunanin to ko shi ma Housemate dinta ya ga hoton ne a Instagram bayan status din Safiyyah, bata taΙ“a jin haushin Safiyyah irin yau ba, Allah kadai yasan mutane nawa ne suka ga hoton nan daga jiya zuwa yau, ta goge idonta ta bude handbag dinta ta ciro wayarta ta fara kiran Safiyyah, yana fara ring Safiyyah ta daga tace "Ya tafi ne in fito?" Trying to be calm Khaleesat tace "Kin ga Safiyyah kije kiyi ma wannan mutumin magana ya cire hotona a Instagram, who does that? Ta yaya daga hoto zai je yayi posting a Instagram kamar mun san juna from anywhere da shi? Meye hadina da shi da zai min haka? Har wani dogon magana muka yi da shi da har zai dau hotona tare da shi yayi posting a Instagram dinsa?" Muryarta na rawa ta kare maganar, Safiyyah tace "Innalillahi, Instagram yayi posting hotunan? Kinsan ni ba wani damuwa da IG nayi ba, kuma fa Aymaan ban taΙ“a ganin yayi posting mace a Instagram ba, sai gashi yayi posting na ki, amma how did you know his Handle da har kika ga yayi posting din ku?" A fusace Khaleesat tace "Ina ruwana da wani handle dinsa, kawai daga haduwa ko maganar minti daya ban yi da mutum ba ya kama hotona yayi posting duk duniya su gani, is he even okay? Ko ba shi da hankali ne? To wallahi ki je kiyi masa magana ya goge min hotona" Safiyyah tace "Ni ma dai nayi mamaki gaskiya, wallahi ban taΙ“a ganin yayi posting mace ba sai gashi yayi posting din ki, kar dai shi yasa Ajay ya zo wajen ki yau? Don definitely za su iya sanin juna kilan ma suna following juna, kinsan akwai association na Nigeria student a makarantar mu dole ma za su sun san juna, Ι—an Deputy governor ne fa Aymaan, he is also popular on IG" Takaici ya sa Khaleesat ta katse kiran ta jefar da wayarta kan kujera, wani mugun haushin Aymaan da Safiyyah ta dinga ji a ranta, da tana da numbersa babu abinda zai hanata kiransa ta gaggaya masa magana, ko an gaya masa ita irin wa ennan matan ne da har zai yi posting din ta duniya su gani, Abdul ne ya fado mata, nan da nan jikinta yayi mugun sanyi, don babu uban da ya kai sa zama active a Instagram gashi da uban followers, wa ma ya sani ko yasan Aymaan din, sosai taji hankalinta ya tashi ta jinginar da kanta da kujera wasu hawayen na zuba idonta, bata taΙ“a jin Safiyyah bata kyauta mata irin yau ba, da kyar ta mike ta dau jakarta da waya ta wuce sama. Meemah ce ta shigo dakin Momy tana mika mata wayar hannunta hankali tashe tace "Momy kin gane wacece wannan kuwa?" Momy ta ajiye bowl din farfesun hannunta ta amshi wayar tana kallon screen din, can ta kalli Meemah tace "Wannan ba er matsiyatan can bace? Khaleesat take ko wa" Meemah ta zauna gefen gado har sannan fuskarta dauke da tashin hankali tace "Ita ce Momy, ita da Aymaan" Momy ta ajiye wayar ta dau bowl din farfesunta ta ci gaba da ci tace "Waye kuma Aymaan?" Meemah tace "Aymaan din kuma kika manta yau Momy, Muhammad Aymaan Ι—an mataimakin gwamna fa" Momy ta kalleta tace "Wai tsohon saurayin ki Muhammad?" Meemah ta hade rai tace "Tsohon saurayi fa kika ce Momy, Aymaan din ne tsohon saurayina?" Momy tace "To in ban ce maki tsohon saurayin ki ba ya zan ce, yaron da ba Ι—aga kiranki yake ba yanxu, yaushe rabon ki da shi? kin ga kuwa ai sai in ce tsohon saurayin ki Meemah, dama ai a titin Instagram din ku ka hadu da shi, ba sai da na dinga hada maki da rokon Allah ba kika samu sassaucin son sa da kika dora ma kanki, dama su biyu zuciyarki ta makale ma da shi da wani Ι—an sarki yake ko wa shi ma kullum sai kin isheni da zancensa bana ma tunanin kina da numbersa, duk samarin ki a Instagram din ku ke haduwa kuma a can ku ke rabuwa, ni na taΙ“a ganin wannan wahala" cike da damuwa Meemah tace "Wallahi mace ce ta shiga tsakaninmu da Aymaan Momy, amma ai ya so ni kamar ran sa, ki tuna har fa kano ya sha zuwa wajena" Momy ta tabe baki tace "Amma ai ba gidan ubanki yake zuwa ba sai dai yace ku hadu gidan cin abinci ko wani wajen, bai taΙ“a biyo ki yaga gidan ku ba, shekara kusan takwas ana abu daya in da gaske son naki yake me ya hanasa fitowa har yau, ni dama tun da Malam Tasi'u yace min bazai fa aureki ba na hakura da kashe kudina a iska, amma ai na kashe kudi kan wannan Aymaan din, bayan Malam Tasi'u ma akwai wani malamin da yace min mu hakura ba auren ki zai yi ba bata maki lokaci kawai yake, kuma uwarsa ma a tsaye take kyam" Meemah tace "Momy duk ba wannan ba, a ina yasan yarinyar nan har suka yi hoto tare? Kinsan shi ma a Amurka yake kuma makarantar su daya amma ya gama degree dinsa tuntuni in dai ba masters ya koma yi ba, kuma wnn hoton daga gani a Amurka aka yi sa" Momy tace "Atoh kika san ko tsohon hoto ne, dama ai kin ce iskanci ta dinga yi a Amurkan don haka ba abun mamaki bane don kin ga hotonsu tare, yanxu kuwa ai sai dai tayi karuwancinta da yan Mariri" Meemah dai ta kasa cewa komai amma kana ganinta kasan hankalinta ya tashi sosai, Momy ta kalleta tace "Ai kun ma fi shekara biyu baku yi waya da shi ba ko?" Meemah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Yanxun ma ina ganin hoton na kirasa bai daga ba, amma ni abinda ya bani mamaki duk yanda yake da mace fa baya posting dinta ko a WhatsApp balle har Instagram" Momy tace "Ɗan wani gari ne ma?" Meemah tace "Gusau" Momy tace "Abdul ya san sa ne?" Meemah tace "Oho, shi wannan ana sanin cikinsa ne, ni ban san ko sun san juna ba, kuma ai Abdul bai san ni da Aymaan ba tunda kinga ba wai ya taΙ“a zuwa gidanmu bane Aymaan din, sai dai su san juna a Instagram amma ba a sarari ba" Meemah ta kara Zooming din hoton da kyau tana kallon tsadadden Abayan jikin Khaleesat ga wani kallo da Aymaan ya kafeta da shi, ita kuwa tana dariya with her beautiful set of teeth, Meemah ta fice daga wajen hoton ta sake dialing number Aymaan amma har ya katse bai daga ba, mikewa tayi ta nufi kofa, Momy ta tabe baki tace "To ke banda abunki me zai yi da er talakawa aka ce maki, in kin bibiya hoton ya dade, yanxu kuwa ina taga hanyar zuwa Amurka, ai uwarsa ma ta fi mu Ζ™in talakawa bari ki ji in gaya maki, a zamanin yanxu dai ko wani me kudi ya waye baya yarda ya hada zuri'a da talaka, yanxu kwarya tabi kwarya kawai, haka abun yake" Ita dai Meemah ta fice daga dakin tana sake dialing number Aymaan with confusion. Tana zaune usual spot din da suke zama a school tana jiran Safiyyah da taje kai ma wani coursemate dinsu laptop dinsa, tun daxu take zaune wajen tana danna wayar hannunta with full concentration, lkci daya ta dakata da abinda take yi a wayarta jin wani kamshin turaren da ta sani ya doki hancinta, waige waigen wajen ta fara yi suna hada ido bata san sanda ta saki wayar hannunta ba zuciyarta na bugawa tana kallonsa babu ko kiftawa, he was the least person she is expecting to see in her life, lkci daya taji wani courage ya zo mata ta dau wayarta fuskarta a daure ta mike da nufin barin wajen, ya fixgo gyalen jikinta yana kallonta da kyau yana murmushi yace "You think i will let you just like that Khaleesat? Har kin samu masu ci gaba da sponsoring din ki an dawo dake America, ga shi har ana hoto dake ana dora ki a Instagram, u snapped a picture together with Aymaan har yayi posting din ki duniya ta gani, ko wani Ι—an iskan gaye kin sani a Amurka and they are all ready to go through any mile for you, to ki sani na maida aurenmu da ke, you are still my wife...." A firgice Khaleesat ta farka daga baccin da take ta mike zaune jikinta na rawa, tun da uwarta ta haifeta bata taΙ“a mummunan mafarki irin wannan ba, ta sauka daga saman gadonta har sannan jikinta na rawa, bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba tana ganin abun kamar ba mafarki bane gaske ne, ba karamin tashin hankali ta shiga ba ta fara karanto duk addu'an da ya zo bakinta tana kuka, duk yanda ta so ta samu nutsuwa hakan ya gagare ta, she was really shock, da kyar ta daure ta dauko wayarta ta kunna data hannunta na rawa, kawai taji she wants to speak with her Housemate, tana bude data taga Aunty Farida ta ajiye mata sako, ta shiga DM dinta taga hoton da suka yi da Aymaan ta turo mata tana tambayar wanene shi, kuma me yasa zata yi hoto da shi.... Tashin hankalin Khaleesat ya ninku akan wanda take ciki da, she was so confuse and shock, gashi jikinta sai rawa yake, a ina kuma Aunty Farida taga hoton nan, ta shiga uku, shikenan kilan Abdul ma zai gani kenan mafarkinta ya tabbata ya zamto gaskiya? Ta fashe da matsanancin kuka tana jin zuciyarta kamar zai fito tsabar tashin hankali, ko reply din Aunty Farida bata yi ba ta fita daga WhatsApp din ta fara dialing number Housemate dinta da sauri, ta kirasa har sau biyu bai daga ba, rasa yanda zata yi tayi tana kuka, can kawai ta fara dialing number Safiyyah har sannan jikinta bai dena rawa ba, yana fara ring Safiyyah tayi picking, cikin rawan murya Khaleesat tace "Safiyyah baki ce ma mutumin nan ya goge hotona a Instagram ba dama??" Safiyyah tace "A'a na masa message ta WhatsApp he is not online fa, na kuma kirasa bai yi picking ba, kuka kike yi ko me? Haba Khaleesat sai kace warce tayi wani mugun abu? Get together fa kawai muka je aka yi hoto ba wai club ba, kuma shigar ki ta mutunci kika yi fa, Aymaan kuma left a reasonable distance tsakanin ku balle ace ko manne maki yayi a jiki" Khaleesat taki bata amsa tace "Kina da number Ya Junaid pls?" Safiyyah tace "Eh kamar ta numbersa Jawwad yayi min fowarding receipt din 10M da aka tura ma su Maman Abdul" Da sauri Khaleesat tace "Don Allah ki turo min yanxun nan" Safiyyah tace "Ohk bari in duba, amma ni dai wallahi ban ga abun damuwa ba don kawai Aymaan ya daura hoton ki a Instagram, sanannen Celebrity ne shi fa, kawai don bama Instagram ne shi yasa baza mu sani ba, kuma kawai don dai kina Iddah ne da ace kin gama so what?? Ai kin isa ne yasa ya dora ki" Khaleesat ta katse wayarta don bata son ta gaya ma Safiyyah magana she is just controlling her self all this while, ba a dau lokaci ba sai ga Safiyyah tayi mata fowarding number Ajay, Khaleesat tayi dialing number da sauri, gaba daya zafi ta dinga ji duk da uban sanyin da ake har da snow, don Ajay na dropping dinta daxu babu dadewa aka fara snow shi ne har ta kwanta bacci tayi wnn mummunan mafarkin, sai da ta kira sau biyu sannan Ajay ya daga, ta kasa daurewa ta fashe masa da kuka muryarta na rawa tace "Don girman Allah idan kasan mutumin nan ka taimaka min kayi masa magana ya cire hotona a Instagram page dinsa, wallahi ni ban san sa ba pls talk to him" Tana kuka sosai ta kare maganar, Ajay dake sauraronta kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Ni na ajiye ki a gefensa aka yi maku hoton da zan masa magana ya cire?" Ta kara fashe masa da matsanancin kuka tace "Na shiga uku, don Allah ni dai ka taimake ni wallahi ban san waye shi ba" Ajay ya ki cewa komai daga karshe ma ya katse wayarsa, ta mike ta koma kan gado ta dinga rera kuka, ita babban tashin hankalinta ace Abdul ya ga hoton nan, tsaf attention dinsa zai iya dawowa kanta kuma ba da good Intention zai dawo ba, tana rayuwarta low key gashi Safiyyah ta ja mata fitina, ji tayi kamar zazzabi na neman rufeta tsabar tashin hankali, ta kwanta saman gado tana sauke ajiyar zuciya hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, ta kusa awa daya a haka daga karshe tayi karfin halin tashi ta tafi bandaki zata yi alwala don yin sallan magrib, ko da ta fito ta kasa yin sallan ta kwanta ta lulluba da duvet saboda rawan sanyin da take, ba karamin kidimar da ita wnn mafarkin da tayi yayi ba, after like 15 mins ta ji ana danna bell din gidan, ta mike zaune da sauri har lkcn tana rawan sanyi, gaba daya a tsorace take kamar mara gaskiya, after some minutes aka sake ringing bell din gidan, ta fara tunanin ko dai Housemate dinta ne ya dawo, tunanin hakan yasa ta daure ta sauka daga saman gadon ta fita daga dakin, har a sannan kuma snow bai dena zuba ba.....

[7/10, 8:55 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat na isa kofar parlon ta bude a hankali tana kallon wanda ke tsaye bakin kofar, sauke idonta tayi ta koma gefe ta tsaya, babu yabo babu fallasa yana kallonta yace "Me yasa kika kira wayana kina kuka kamar ni na aike ki? Why didn't you call Jay kiyi masa kukan sai ni?" Ta daga jajayen idanuwanta ta kallesa, ji tayi wasu hawayen sun cika idonta ta sunkuyar da kanta, after some seconds ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, da kyar tace "Ni dai in ka san sa kayi masa magana he should delete my pictures off his phone plss, Aunty Farida ma fa sai da ta turo min hoton, ni kuma wallahi ban san sa ba" Yace "Baki san sa ba kika tsaya gefensa kina washe hakora ku ka yi hoto?" Ta fashe masa da kuka ta juya da sauri ta bar wajen ta koma cikin parlor ta kwanta kan kujera tana rera kuka, tsabar mamaki da haushi yasa ya kasa cewa komai ya bi ta da kallo, ya tsani unnecessary kukan mace a rayuwarsa, ya kuma lura bata da aiki sai kukan banza tun da ya santa a haka ya santa da kuka, how is Jay coping interacting with her this way, shi ba shi da irin wannan patient din, parlon ya shiga ya kulle kofar, ya saka hannunsa a aljihun Jacket din jikinsa cause he is already cold kawai Ι—an tsayuwar da yayi a waje, ya karasa har inda ta kwanta take kukan ya hade rai yace "Don't you dare call my line again kina kuka, ni ban aikeki ki bi silly friend dinki zuwa party har ayi maku hoto da wani namiji ba, stop stressing me with ur troubles pls, i am not Jay" Ta dakatar da kukan da take ta wani kallesa ta hade rai tace "Ni ba party muka je ba, get together ne, ka dena cewa party" Wani kallo yayi mata, ta kauda kanta tana goge idonta, ya kalli Heater din parlon sai kuma ya tafi ya kunna, ta bi sa da kallo ganin ya nufi window din parlon ya bude drape din yana kallon snow dake sauka waje sosai, he was just imagining how he managed to get here in this snowstorm, mikewa tayi a hankali tayi wucewarta sama, ya juya ya bi ta da kallo. Wajen karfe takwas da rabi Khaleesat ta fito daga dakinta tana leka downstairs daga corridor din da take tsaye, taga yana zaune har sannan a parlon ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa a lumshe, ta zata ma ya tafi, after some minutes ta sauko downstairs tana kallonsa, har sannan bai bude idonsa ba, tana tafiya a hankali ta nufi window tana duba waje taga it's still snowing outside, dawowa parlor tayi ta tafi kitchen, after a while ta fito da cup din tea biyu ta tafi har inda yake zaune ta tsaya tana kallonsa, a hankali tace "Ga shayi" Bude ido yayi, sai kuma ya gyara zama yace "Did i send you message?" Ta wani kallesa, sai kuma tace "To ai naga kamar sanyi kake ji tunda gashi ka kasa tafiya" Ya kalleta yace "Zan juye maki shayin a baki in baki matsa gabana ba, ba ke kika fito da ni cikin sanyin ba? Kin zata idan Jay yana nan zan saurare ki ne? Ai shine wahalalle dama" Tace "Ni ban fito da kai cikin sanyi ba, tunda ba cewa nayi ka zo ba ai, kawai kiranka nayi nace kace mutumin nan ya cire hotona a Instagram, amma ban ce ka zo ba" Kallonta ya dinga yi, at this point kamar he is lost of words, ta juya ta koma kitchen ta ajiye cup daya ta fito ta wuce sama tana rike da cup din nata shayin, still ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, Khaleesat na gama shan tea din ta kwanta ta rufa da duvet ta lumshe ido tana addu'an Allah ya sa kar ta kara mafarkin da zai firgitata kamar daxu, kamar warce ta tuna abu ta bude idonta a hankali, ta jawo wayarta tana dubawa ko Housemate dinta ya biyo kiranta bata sani ba, amma sai taga bai biyo kiran ba, har ta ajiye wayar sai kuma ta sake dauka a hankali ta kunna data dinta tayi login WhatsApp, tun call din da yayi mata da safe bata daga ba bai kara mata magana ta WhatsApp din ba, and he uploaded a status not long ago, sauke idonta tayi ta kashe datan ta ajiye wayar ta gyara kwanciyarta, nan da nan mood dinta ya canza, duk yanda ta so tayi bacci kasawa tayi, sai juye juye take har kusan karfe sha dayan dare, mikewa zaune tayi daga karshe ta cire duvet din jikinta ta dau Jacket dinta ta saka sannan ta bude kofar parlon a hankali ta fita, tsaye tayi a corridor din sama tana kallon Ajay dake kwance kan 3 seater idonsa a lumshe don wutan parlon a kunne yake, ta fi minti biyu tsaye tana kallonsa, sai kuma ta juya ta koma dakinta ta dau one out of the new duvet Jay got for her, ta cire farin duvet din daga pack dinsa sannan ta fito daga dakinta ta sauka downstairs, tana tafiya a hankali ta isa har inda yake kwance, gida biyu ta linke soft duvet din ta rufa masa a jiki, ba wai hannunta ya taΙ“a sa bane but she could feel he is running temperature, tana rufa masa Duvet din ya cire daga jikinsa ya wurgar ba tare da ya bude ido ba yace "Gerrout Jay...." Sai kuma ya fara kokarin juyawa a kan kujeran sai ga shi a kasan carpet ya fadi timm, rufe bakinta tayi da sauri, ita kanta bata san meyasa dariya ya taho mata ba don da har jikinta yayi sanyi after noticing that he is running temperature, amma wannan reaction din nasa yayi mugun bata dariya, cikin magagi yake cewa "Bana son haka Jawwad, why are you stressing me, gerrout pls, i think i caught a cold, can you help increase the room heater before getting out" Sai kuma ya bude ido a hankali yana dafe kansa da yayi masa nauyi cause bai ji Jawwad na responding ba, ita dai kallonsa kawai take da mamaki, he look so shock ganinta, ya fara bin parlon da kallo, sai kuma ya kalleta ya hade rai yace "Kee, fita ki ban waje" Bata san sanda tayi dariya ba tace "Ai to bani na fadar da kai kasa ba, ni kawai bargo na kawo maka, and you heavily fell down on the Carpet" Ya kara daure fuska yace "Get out of my sight, am i a joke to you?" Ta wani juya kai, sai kuma ta nufi stairs tana waigansa har ta haura sama ta shiga dakinta, sai a sannan ta fara dariya tana mamaki shi kuma haka yake, har bayan minti talatin Khaleesat bata yi bacci ba tana dai zaune dakinta, after a while ta mike a hankali ta kara fita daga dakin nata tana leka downstairs, bata gansa kwance a parlon ba, hakan yasa ta fara saukowa downstairs, ta kalli duvet din da ya ajiye saman kujera da makullin gidan, sai kuma ta kalli bakin kofa ta karasa can ta murda kofar taji a kulle, window ta tafi tana leka Garage taga babu motarsa, ta dawo parlon ta dau makullin gidan tana kallo taga ya cire guda daya a ciki, she felt somehow ganin bashi da lafiya kuma still ya bar gidan a haka gashi snow din raguwa kawai yayi, ta fi minti biyu a tsaye after a while ta dau duvet din zata koma sama taji vibration din wayarsa, dube dube ta fara yi amma bata ga wayar kan kujera ba, daga karshe sai karkashin kujeran taga wayar, kilan sanda ya fadi daga kan kujeran shi ne wayar ya shige karkashin kujeran, screen din wayar ta dinga kallo ganin Jay ne ke kiransa, tayi silencing wayar ta wuce sama tana rike da wayar da duvet, sau uku Jay na kiran wayar, ita dai ta ajiye wayar gaban madubi tayi kwanciyarta. Washegari ta idar da sallan asuba bayan ta gama azkar dinta zata kwanta wayar Ajay ya fara vibrate gaban madubinta, ta dinga kallon wayar sai kuma ta karasa can tana duba screen din taga Jay ne still ke kiransa, ta juya ta koma saman gado tayi kwanciyarta, wajen karfe tara na safe ta gama shiri zata tafi school, tana tsaye gaban mirror din dakin tana kokarin daure gashinta sai ga Jay ya sake kiran wayar Ajay, ta dinga kallon wayar babu ko kiftawa sai kuma ta daga wayar ta sa handsfree bata ce komai ba, daga daya bangaren Jay yace "Why were you not picking ur calls Bruh, hope baka fita jiya ba cause naji anyi snow sosai, how are you doing?" Khaleesat dake sauraronsa ta sauke idonta tace "Good morning, he forgot his phone" Shiru Jay yayi daga daya bangaren for almost 10 seconds, can yace "Halysaah..." Tace "Good morning" Yace "Morning, where did he forget his phone?" Tace "In my apartment" Shiru Jay yayi bai ce komai ba, after some seconds a hankali yace "Ohk then" Daga haka ya katse wayar, Khaleesat ta dinga kallon screen din, sai kuma ta ajiye wayar tana kallonsa, sai bayan kusan minti daya ta iya ci gaba da gyara gashinta. Bayan Khaleesat ta gama abinda take ta saka wayar Ajay a jakarta zata tafi school da shi incase yaje zai amsa a department dinta, bata nuna ma Safiyyah komai ba da suka hadu a school duk da har sannan she is still very much angry at her, Safiyyah na kallonta tace "Yanxu dai sai hankalin ki ya kwanta don naje na duba na ga Aymaan ya cire hoton naku a account dinsa, ko wa yayi masa magana oho, ni kuma gashi bai min reply din WhatsApp message dina har yanzu ba" Khaleesat tace "Toh in ba dai he is irresponsible ba ta yaya zai dau hotona bai san ni ba yayi posting a account dinsa? Bai ma dau matarsa da muhimmanci ba in dai haka ne, who does that?" Safiyyah tace "Atoh, nima dai haka naji aka ce yana da mata amma ban sani ba ban kuma tabbatar ba" Khaleesat ta kalleta baki bude, Safiyyah tace "Wallahi kuwa, haka naji ana cewa, kuma wai yana da ciwon zuciya, ni dai bai min kama da me ciwon zuciya ba kuma ban ma yarda da wnn labari ba, kinsan yan mata na jin haushinsa saboda sai wanda ya ga dama yake kulawa shi yasa aka masa wannan sharrin, amma ki kalli mutum lafiyayye kamar sa a wani ce ciwon zuciya, gashi da son zuwa club" Khaleesat ta ma rasa abinda zata ce ma Safiyyah, kawai ta kauda kai don lamarin Sophie ya fara bata tsoro, the way she is saying it kamar bakinta da bakinsa suka yi magana ya gaya mata yana da ciwon zuciya kuma yana da mata, Safiyyah tace "Ni dai tashi mu je mu ci abinci yunwa nake ji, kilan ma haushin an sa shi ya cire hoton ne ya sa yayi banza da ni ta WhatsApp kuma na kirasa yaki picking, dama an masa shaidan girman kai and he is way too pompous of himself, bazai wuce Housemate dinki ya san sa ba shine yayi masa magana ya sauke hoton, dama ni fa sam gayen bai min ba ga wani jijji da kai da yake wai shi Ι—an gidan Deputy sai kace Ι—an vice president, deputy governors da ba a ma san da zamansu ba a Nigeria, gani yake yafi kowa a haka fa, kina kallon idonsa kinsan bazai rasa shan drugs ba" Khaleesat tace "Amma dai yanxu idan Abdul yaga hoton nan me kike tunani Safiyyah?" Safiyyah ta mike tace "Waye kuma Abdul? Pls mu je mu ga abinda za mu siya mu ci yunwa nake ji wallahi" Har Khaleesat ta bar school ranan bata ga Ajay ya zo amsar wayarsa ba, hakan kuma yasa taji a ranta he is sick. Mamaki abun ya ba Khaleesat ganin har ta dawo school Housemate dinta bai kirata ba ko kuma yayi mata magana ta WhatsApp, wayar Ajay ma bai sake kira ba, sai dad dinsa da ta ga ya kira wayar har sau biyu, da daddare taji zuciyarta ya kasa daurewa kawai tayi ma Housemate din nata magana via WhatsApp, ta gaishesa sannan ta tambayesa ya jikin cousin dinsa, after almost 15 minutes yayi mata reply da Alhamdulillah, daga nan kuma bai sake cewa komai ba, she was taken aback, haka nan ta ajiye wayarta kawai ta kwanta tana jin wani iri a zuciyarta. Bayan kwana biyu Khaleesat da Safiyyah suna zaune a wajen department dinsu, Khaleesat na yi mata explaining wani course dinsu da tace bata gane ba, Murya can kasa taji Safiyyah na cewa "Ji gantalallen Aymaan din can, he is coming toward us, kar ki dago kanki" Khaleesat bata dago kai ba, ta ci gaba da bayanin da take ma Safiyyah, har ya iso inda suke zaune, calmly yace "Good evening Safiyyah and Khaleesat" Safiyyah ta washe baki tace "Hi Aymaan, how are you doing ya kwana biyu?" Yace "Lafiya lau, ya karatu?" Safiyyah na washe hakora tace "Alhamdulillah, tun ranan bamu sake haduwa ba sai yau" Yana kallon Khaleesat yace "Good evening Khaleesat" Ba tare da Khaleesat ta kallesa ba fuskarta babu fara'a tace "Ohk" Ya kalli Safiyyah yace "Naga kamar kawar taki a fusace take" Safiyyah tayi dariya da iyakarsa fuskarta tace "Ai bata ji dadin abinda kayi mata bane, duk da na fahimtar da ita ba da wata manufa kayi hakan ba, kuma ta fahimta, ita tsoronta ma kar matarka ta ga hoton" Yana kallon Safiyyah yace "Ke kika min auren?" Safiyyah tayi dariya tace "To ai kaga za a sa maku ido kuma shi yasa ta damu" Yace "Ohk in nasan haka ne ai da bazan sauke hoton ba, don wani guy that is full of himself i think saurayinta ne ya sameni yayi min magana about it, yasan ni, na sansa a kasar nan amma ba mu taΙ“a ma juna magana ba, had i know ban cire hoton ba in ga abinda zai yi" Safiyyah ta kwantar da murya tace "Kaga Aymaan Khaleesat fa matar aure ce babu wani boye boye...." Aymaan yayi wani murmushi without letting Safiyyah to go further yace "Ban yarda ba, shi wanda ya min magana in cire hoton zan nuna masa ba aurenta yayi ba ai...." Khaleesat ta daga kai fuska daure tace "Pls delete my pictures off your phone Mr man, don ban san ka ba, ban hada komai da kai ba ban kuma ga dalilin da yasa zaka yi posting dina ba, no sane person will do such, plss take my pictures off ur phone matar aure ce ni" Tana kai wa nan ta tura ma Safiyyah Laptop dinta ta mike ta figi handbag dinta ta bar wajen ko waigawa bata yi ba, Aymaan ya bi ta da kallo yana Ι—an murmushi, Safiyyah tayi tagumi don har ta gaji da ce ma Khaleesat ta koyi siyasa da iya zaman duniya, da faram faram ya kamata ta samu ta rabu lafiya da Aymaan amma ga abinda tayi, Aymaan ya gyada kai yace "We shall see then" Safiyyah ta kallesa tace "Kasan tana da aljanu ne fa Aymaan kuma abun har ya taΙ“a brain dinta, da sauki ma basu tashi a nan ba, don wallahi duka take kuma in ta fara famfala gudu da kyar ake kamota, shi sa kullum zaka ganta babu fara'a ni kadai nake iya zama da ita wallahi, wanda kuma yasa ka cire hoton ba saurayinta bane believe me..." Aymaan yayi wani murmushi yace "Nima su gareni, kin ga dai dai kenan" Daga haka ya juya ya bar wajen, Safiyyah ta kara rafka wani tagumi. Khaleesat na isa gida wajen karfe biyar zata bude kofa taji kofar a bude, ta kalli parking space taga babu mota a nan, tura kofar tayi a hankali ta shiga parlon, zaune ta gansa ya kunna TV yana kallon kwallo, ko juyowa bai yi ba har ta karasa cikin parlon tana kallonsa, ya mike without looking at her yace "Bani wayata" Tace "Ya jikin?" Sai a sannan ya kalleta yace "Nace maki bani da lafiya ne?" Tace "A'a kawai na gane idan baka da lafiya surutu that is not comprehensible kake yi a bacci....." Tana murmushi ta kare maganar tana kallonsa.

[7/11, 8:44 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat ta bi sa da kallon gefen ido ganin ya nufi kofa, sai kuma ta juya tana kallonsa, fita ta ga zai yi daga parlon, da sauri tace "Ka jira in dauko maka wayar yana sama" Tuni ya fice daga parlon without looking at her, tafi minti biyu tsaye tana kallon kofar da mamaki, does this min yaji haushin abinda ta fada kenan? To ai ita ba da wata manufa ta fadi hakan ba, tana ta tsaye parlorn with surprise, can dai ta taΙ“e baki ta karasa ta zauna kan kujera ta bude handbag dinta ta ciro wayarta tana duba pdf da aka mata sending a school na wani course dinsu, after a while ta mike ta tafi sama don yin sallah ta canza kayan jikinta sannan ta dawo downstairs ta girka abinda zata ci, Khaleesat bata sauko downstairs din ba sai kusan karfe biyar da rabi na yamma don tana sallah bacci ya dauketa saboda sanyin garin, tana gyara hulan kanta bayan ta sauko kasa zata shiga kitchen taji anyi knocking kofar parlor at the same time aka murda kofar, juyawa tayi da sauri after realizing ashe a bude ta bar kofar bayan Ajay ya fita daxu, kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa kuma ko kwakkwaran motsi bata yi a inda take tsaye tsabar yanda ta tsorata, ya kullo kofar yana tsaye daga nan bakin kofar yana kallonta yana murmushi with calm yace "Good evening Khaleesat" Khaleesat ta sauke idonta gabanta na wani mugun faduwa, her common sense didn't give her the go Ahead to be rude or anything of such to him, can dai ta kallesa with calm in her voice tace "Why will you badge into my House just like this?" Ya Ι—an yi murmushi yana sauke hulan jacket din jikinsa yace "That was because u left the door open..." Cikin kwantar da murya tace "But that doesn't warrant you to badge in" Ya daga hannu sama yace "My bad, sorry about that beautiful Khaleesat" Zaunawa tayi kan kujera bata sake cewa komai ba faduwar gabanta ya tsananta, yana bin apartment din da kallo keenly yace "Such a nice apartment, Communal living kike, ko ke kadai ce a duk apartment din nan?" Ba tare da ta kallesa ba calmly tace "Co-living" Ya karaso cikin parlon tayi masa kallon gefen ido gabanta na faduwa sosai, zaunawa yayi gefenta yana kallonta yace "Sorry i came unannounced, banyi tunanin kina da fahimta haka ba, na zo gidanki ba tare da izinin ki ba and u are not mad at me, i even badged in but u are still calm...." Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace "It's fine... How did you get to know my apartment?" Yana gyara zama yana wani murmushi yace "Gane apartment din ki har wani wahala zai min a Baltimore ni da na damu dake?" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, tasan babu tantama bayan ta fito school ne daxu ta hau Lyft shi ne ya biyota without her knowledge, bin parlon ya dinga yi da kallo yace "But seriously i really love this ur apartment, it's big and fine, ko ke da Safiyyah ku ke sharing?" Ta girgiza masa kai, can kasan zuciyarta kuwa tunanin next move din da zata dauka take yi, yana kallon sauran gashinta da basu gama shiga hulan kanta ba tunda tana cikin saka hulan ya shigo parlon, ya kai hannu zai taΙ“a gashin da mamaki yace "Are all this ur hair??" Da sauri ta matsa gefe tace "Noo, i won't welcome that" Ya buda ido yace "I am sorry Dear, you've got a beautiful soft black hair" Ita dai bata ce komai ba, Yana kallonta speaking calmly yace "Tell me more about ur self pls Khaleesat" Ta kirki murmushi tace "Kaga yanxu fita zanyi zan tafi supermarket in yi shopping, and it's almost late" Yayi er dariya yana kallonta da kyau yace "Duk salon korana ne wannan dear?" Tace "Not at all, assuming zan kore ka ai kana shigowa zance ka fitar min a gida, kawai zan je in yi siyayya ne yanxu don gobe ba da wuri zan dawo gida daga schl ba" A hankali yace "Alright, dress up sai mu je shopping din" Tayi karfin halin mikewa tsaye sai kuma ta kallesa tace "But plss respect my privacy, ka jira ni in sauko" Yayi wani murmushi yace "Baki da matsala my dear" Bata sake cewa komai ba ta nufi stairs har sannan gabanta na faduwa sosai, ga wani takaici da take ji a ranta don wata er doguwar riga ne kawai a jikinta that is not even cloth enough, a haka dai ta haura sama yana bin ta da kallo, tana shiga dakinta ta kulle dakin da makulli hawaye ya cika idonta ta tafi ta dau wayarta da sauri, number Housemate dinta tayi dialing bayan few seconds ya fara ring amma har ya katse bai daga ba, zaunawa tayi gefen gado tana goge hawayen dake sauka idonta tana tunanin yanda zata yi, bata sake dialing number Housemate dinta ba instead tayi dialing number Ajay, a cikin daya daga jakunkunan da take fita school taji vibration din wayar tasa, ajiye wayarta tayi ta daura kanta kan pillow ta fashe da kukan takaici, after some minutes ta mike tana goge hawayen da yaki tsaya mata, ta dau handbag din da wayar Ajay ke ciki, ta ciro wayar tana dubawa taga ya ma kusa shut down, cikin jakar da ta dawo da shi daga school ta saka wayar sannan ta dau nata wayar tayi ordering Uber, ta saka wayarta ma cikin jakar, ta canza kayan jikinta sannan ta saka hijab ta fito daga dakin ta kulle ta sauka downstairs, yana tsaye parlorn hannunsa rike da can drink da ya shiga kitchen dinta ya dauko a fridge yana sha, ya bi ta da kallo yace "The weather is cold outside dear, ina jacket din ki?" Without looking at him tace "I will be fine" Yace "Ohk then, mu tafi?" Tace "A'a zan Ι—an yi abu a kitchen in fito tukunna" Yace "Ohk, take ur time" Kitchen dinta ta nufa ya bi ta da kallo har ta shiga ciki, kulle kofar tayi ta tsaya a kitchen din tana jiran Uber dinta at the same time zuciyarta na tafarfasa tana goge hawayen takaicin dake sauka idonta, after a while ta fito daga kitchen din without looking at him tace "Na gama" Mikewa yayi yana gyara jacket dinsa yace "You look cute dear, ko dai in baki jacket dina, its freaking cold outside fa" Tace "Kar ka damu" Daga haka ta nufi kofa ta fita, shi ma ya fito sannan ta kulle kofar da makulli, motarsa da yayi parking ya nufa yana nuna mata yace "There is my car" Ta kallesa tace "Ga Uber da nayi order can" Ya juya ya kalleta yace "Why? Cancel the order, da mota na zo ae" Tace "I can't cancel it" Bata sake sauraronsa ba ta nufi uber din without looking at him, ya bi ta da kallo with astonishment, dariya yayi yace "Whatt? Like seriously.... this little girl played me" jingina yayi da motarsa ya rufe baki yana murmushi yana kallonta yana gyada kai har ta shiga uber din, wato shi zata yi ma wayo, gaskiya tana da wayo, gyada kai yayi ya shiga motarsa ya tada sannan ya bi bayan uber din da ta shiga.... Khaleesat na lura da yanda yake bin uber din da ta shiga a baya, sai kusan karfe bakwai ta isa gidan, ta bude Uber din ta sauka ta nufi cikin gidan da sauri, sai gashi shima yayi parking, ko kashe motar bai yi ba ya sauka ya bi ta yana kiranta, amma tuni ta shiga gidan zuciyarta na bugawa, hakan yasa ya tsaya ya bi ta da kallo har sannan yana murmushi yana gyada kai, sai da ya kare ma babban gidan kallo sannan ya juya ya koma motarsa, Khaleesat tana hardewa ta isa har kofar shiga gidan tana jin gabanta na faduwa sosai don gani take kamar ya biyota har cikin gidan tunda ba juyawa tayi ba balle ta gani, bubbuga babban kofar parlon ta dinga yi hawaye cike idonta, amma shiru ba a bude ba, sai a sannan ta lura da madannin kararrawan gidan, ta danna da sauri hannunta na rawa, sau uku tana danna bell din kafin aka bude kofar after almost 5 minutes, ta fashe masa da matsanancin kuka tana kallonsa, Da mamaki yake kallonta daga sama har kasa yace "Me ya faru?" Taki ce masa komai tana rusa masa kuka, bai san sanda yayi mata tsawa ba sounding so apprehensive yace "Can't u speak out? Tell me what is it? Me ya faru?" Cikin kuka tace "He followed me to my apartment" Ya bude ido sosai yace "Who?" Tace "Wannan mutumin nan" Da mamaki yake kallonta babu ko kiftawa yace "Ur apartment?" Ta gyada masa kai hawaye na zuba idonta tace "Ya biyoni har nan gidan ma a cikin motarsa" Yace "Nan gidan??" Tace "Eh, yana waje ban san ko ya shigo ba ma...." Ya cire takalman kafarsa ya saka wasu dake bakin kofar sannan ya fito daga parlon ta bi sa da kallo tana goge hawayen idonta ta jingina da bango, Ajay na fita can waje ya dinga bin Neighborhood din nasu da kallo don babu alamar ko mota daya a waje, sannan kuma babu kowa cause the weather is sooo cold kuma gari yayi duhu, ya juya ya koma cikin gida, har ya iso entrance din shiga parlon kallonsa take, ya hade rai yace "Shiga ciki" A hankali ta juya ta shiga cikin parlon ta cire takalmanta ta karasa ciki ta zauna kan kujera har sannan gabanta bai dena faduwa ba, shi dai Ajay na tsaye bakin kofar parlon gaba daya mamakin Aymaan ya gama cikasa, har ya fara tunanin irin matakin da zai dauka kansa, lkci lkci Khaleesat take kallonsa, after some minutes ya karaso cikin parlon yana kallonta fuska daure yace "Ta yaya ya san apartment din ki har ya je?" Muryarta na rawa tace "Nima wallahi ban sani ba" Ya wani hade rai yace "Kee, kar ki kuskura ki min kuka a nan, don't stress me with your silly cry...." Ita dai bata ce komai ba, yace "Da ya je apartment din naki sai aka yi yaya?" A hankali tace "Ni na manta ban kulle kofar ba da ka tafi daxu, kawai da yayi knocking sau daya shine ya bude kofar ya shigo da yaji sa a bude, and i told him i am going out for shopping yace to zai kai ni, bayan mun fito sai naki shiga motarsa dama nayi ordering Uber, shi ne ya biyo bayan motar da na shiga har muka zo gidan nan" Ajay yace "Da ya je apartment din naki ur common sense bai gaya maki ki kira masa cops ba immediately, ni ranan saboda rashin kunya ba cewa kika yi zaki kira min 911 ba??" A hankali tace "To ba wayar yana sama ba, kuma ai mantawa nayi da cops, i was confuse" Jinginar da kanta tayi jikin kujera bata sake cewa komai ba cause she is already tired, a hankali ta jawo handbag dinta ta bude ta ciro wayarsa ta mika masa tana kallonsa, taga direction din da yake kallo daban yana nazari, ajiye wayar tayi a gefenta, after a while ya juya yana kallonta a takaice yace "Go upstairs" Ta Ι—an bude ido tana kallonsa tace "Upstairs?" Ya mata wani kallo yace "Gidan za ki koma yaje ya same ki a can?" A hankali tace "A'a i tot za mu koma gidan tare" Yace "Sai ki zo ki daukeni mu tafi" Daga haka ya nufi stairs, ta wani bi sa da kallo, shi dai komai masifa, sai kuma ta zumburo baki ta kauda kai, har bayan awa daya Khaleesat bata ga ya sauko downstairs ba, tayi ta zama a parlon har ta gaji gashi bata yi sallah ba, bata ji alamar da workers ko daya a gidan ba cause everywhere is so silent, jinginar da kanta tayi da kujera don ta gaji ga wani ciwo da kanta yake mata and she is very hungry, ta lumshe ido tana zaune a haka bacci ya dauketa, cikin bacci taji muryarsa ta bude ido da sauri ta gyara zama, yana kallonta yace "Oh baki tafi saman ba?" Ta hade rai tace "To ni nasan inda zan je a saman?" Yace "Baki san inda Jay ya saba ajiye ki ba?" Kin cewa komai tayi, after some seconds ta daga kai ta kallesa taga hararanta yake, ta mike ta dau handbag dinta ta bar masa wayarsa a kan kujeran, juyawa yayi ya koma sama ta bi bayansa tana tafiya a hankali, tsaye ta gansa a corridor fuskarsa babu yabo babu fallasa, sau daya ta kallesa har zata tafi dakin da ta taba zama a gidan sai kuma ta saci kallonsa tace "Ina zan je?" Yace "Ban sani ba" Juyawa tayi ta dau hanyar bangarensa, ya bude baki da mamaki yana kallonta yace "Kee" kasa daurewa tayi har sai da tayi dariya don ba karamin dariya abun ya bata ba, ta dake tace "To ba kace inda Housemate dina ya ajiyeni ba, ae can zan je" Shi tsabar mamaki ma rasa abinda zai ce mata yayi, can yace "To tafi ki ga ikon Allah" Ta wani kallesa ta juya ta nufi dakin da ta zauna sanda take exam, tana shiga dakin ta kulle kofar, the room was neat amma kana gani kasan an dade ba a zauna a ciki ba, sosai dakin yayi sanyi kamar kankara, tayi dusting gefen gadon sannan ta zauna tana takurewa waje daya, bayan wani Ι—an lokaci ta mike da sauri bayan ta tuna bata yi sallah ba, ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito, Heater din dakin ta kunna amma yaki yayi function, a haka dai ta tada sallah bayan ta idar tana zaune saman darduman taji knocking a kofar dakin, tana ta kallon kofar sai kuma ta mike ta tafi ta bude kofar tana kallonsa, a takaice yace "The workers in the house are yet to resume, you can go to the kitchen and sort ur self out, this is the only help i can render" Daga haka ya juya ya bar bakin kofar ta bi sa da kallo, sai kuma ta kulle kofar ta koma ta zauna ta takure waje daya don sanyi take ji sosai gashi bata zo da Jacket ba, duk da yunwan da take ji ta gwammace ta hakura don bazata iya zuwa kitchen ba, har ta kagu gari ya waye a san yanda za ayi da Aymaan ta koma gidanta, amma duk da haka ita dai ta tsorata da wannan apartment din ita kadai a cikinsa, mikewa tayi ta kwanta saman gadon bayan ta kakkabe, ta lulluba da second of the bedsheet don biyu ne a kai amma duk da haka sanyi ta dinga ji kamar bata rufa ba, a haka bacci ya dauketa, wajen karfe goma Ajay yayi knocking kofar dakin, ta bude idonta a hankali don restlessly take baccin saboda sanyi, still dai bata juya ba, ya shiga cikin dakin, ya nufi gun room heater din shi ma ya kunna yaga bai yi ba, ya fi minti daya tsaye dakin, sai kuma ya juya ya fita, dakin Jay ya nufa ya bude ya shiga ya dauko white duvet dinsa, sannan ya fito ya koma dakin da Khaleesat take, sai da ya fara duba tagogin dakin to be sure they are locked, sannan ya rufa mata duvet ya juya ya fita ya kullo kofar, kamshin turaren Jay ya cikata gaba daya, nan da nan ta nemi baccin da take yi ta rasa, and she felt so warm, a hankali ta jawo wayarta tana kallon call logs dinta don har sannan Jay bai biyo kiran da tayi masa ba a apartment dinta, ta kunna data dinta ta duba WhatsApp taga nan ma bai ajiye mata message ba, and she even saw him online, sauke idonta tayi, nan da nan taji hawaye na taruwa idonta ta fita daga WhatsApp din ta shiga contact dinta ta goge numbersa da tayi saving daga wayarta, sannan ta ajiye wayar ta rufe har kanta da duvet din tana kuka a hankali, wajen karfe sha daya saura ta zamo kasa a hankali ta dalilin sharp pain da take ji a abdomen dinta, tana durkushe for almost 10 mins daga karshe ta mike da kyar ta shiga bandaki, sosai gabanta ya fadi ganin period dinta ne, ta kasa fitowa daga bandakin, at last dai ta jawo kafa ta fito tana tafiya a hankali, to yanxu ya za ta yi, ta kalli white bedsheet da duvet din Jay dake saman gadon, ba wai ta fara flow sosai bane amma tasan dai hakan zai iya faruwa ko zuwa anjima, a hankali ta durkusa kasan dakin, bata ma damu da sanyin da take ji ba, ta jawo wayarta tana tunanin yanda zata yi, ko dai tayi order din Uber zuwa apartment din nata, amma dai tsoron komawa gidan kuma take, tana jin alamar saukan period din ta mike a hankali, duk jikinta a sanyaye ta nufi kofa ta bude ta fita, ta dade tsaye corridor kamar mara gaskiya daga karshe dai tayi gathering courage ta karasa har bangaren Ajay, tsaye tayi jikin kofarsa kamar tana tausayin kofar tayi knocking gently, Ajay dake danna wayarsa ya juya yana kallon kofar, ta sake knocking a hankali, ya mike zaune ya jingina da gadonsa ya ajiye wayarsa ya rungume hannu yana kallon kofar, idan yace bai gaji da yarinyar nan ba yayi ma Allah karya, daukar wayarsa yayi, yayi dialing number Jay fuska daure, after some seconds Jay ya daga, Ajay yace "Wai yaushe ma kace zaka dawo ne?" Jay yace "Gobe zan tafi Nigeria" Ajay yace "Na gaji da wannan brat din da ka bar ni da ita a kasar nan, you know i have anger issues, I can't tolerate her anymore wallahi..." Jay dake ta sauraronsa yace "To ka iya ajiyar ribbon for more than 2 months, me ribbon din ce baza ka iya ajiyewa under your watch ba?" Shiru Ajay yayi, Jay yace "Hang up pls, Mami tana kirana" Ajay ya kalli screen din wayarsa don daga can bangaren Jay ya katse wayar, ajiye wayar Ajay yayi idonsa akan screen din ko kiftawa baya yi, after almost a minute yace "What is he talking about, meye ma ribbon?" A hankali ya dau wayarsa ya shiga Google yayi typing ribbon.....

[7/13, 1:42 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Ajay ya ajiye wayar hannunsa bayan ya ga abinda google ya bayyana masa a matsayin ribbon, kamar zai sake kiran Jay kawai ya fasa ya ja tsaki ya jingina da gadonsa kalmomin Jay na ci gaba da yi masa yawo a kai, sai kuma ya kalli kofar dakinsa don har sannan Khaleesat bata dena knocking continuously ba, kamar bazai tashi ba sai kuma ya tashi daga karshe ya nufi kofar, bude kofar yayi fuska daure yana kallonta without saying anything, ta Ι—an koma baya taki barin su hada ido a hankali tana wasa da fingers dinta tace "Don Allah dama gida nake son ka kai ni pls...." Ya dakatar da ita yace "Sai na kai ki? Baki san hanyar gidan ba, ko ni na kawo ki?" Ta daga kai ta kallesa ta ma rasa abinda zata ce, ya wani murtuke fuska yace "Ni ba Jay bane da kike ma iskanci iri iri kina controlling din sa" Juyawa tayi a hankali ta bar bakin kofar yayi banging kofarsa ya kulle, ya koma ya dau wayarsa har yayi dialing number Jay sai kuma ya katse kiran ya ja tsaki, Khaleesat na komawa dakin da take ta dau handbag dinta da wayarta sannan ta fita daga dakin, tana tafiya a hankali ta sauka downstairs ta nufi kofar fita daga babban parlon sai taga kofar a kulle, duk kokarin da tayi na ganin ta bude kofar ta kasa budewa gashi bata ga makulli a jiki ba, ta fi minti biyu tsaye bakin kofar tana jin tana flow a hankali, ta juya ta kalli hanyar sama, komawa tayi tana tafiya kamar bata so ta nufi bangarensa, jingina tayi da bango kamar bazata kwankwasa kofar ba sai kuma dai tayi knocking din kamar tana tausayin kofar, Ajay da har ya kashe wutan dakinsa ya kalli kofar babu ko kiftawa, sai kuma ya gyara kwanciyarsa bai motsa daga inda yake kwance ba, Khaleesat ta fi minti biyar bakin kofar bata kuma fasa knocking din da take ba, cire Duvet din jikinsa yayi ya jefar gefe sannan ya sauka daga kan gadon fuska daure ya nufi kofar ya bude yana kallonta at the same time cutting her a serious warning yace "Ki ka sake knocking din min kofa zan maki walakanci wallahi, why are you such a nuisance? Pls get out before i loose my temper" Khaleesat dake kallonsa ta wani hade rai tace "To ta window kake son in fita daga gidan bayan kofar parlon a kulle yake??" Yace "Ki bi ta roof ma ba window ba" Yana fadin haka zai kulle kofarsa tayi saurin shiga cikin dakin kamar zata fashe da kuka ta nufi tsakar dakin ta tsaya tace "Kasan dalilina na cewa zan tafi gida ne? Kawai kayi ta ma mutum masifa baza ka tsaya kayi considering dinsa ba ka basa listening ears, kawai haka nan zan taso cikin daren nan in ce zan tafi gida? Ni ban ce sai kai ka kaini ba ka zo kawai ka bude min kofa inyi tafiyata...." Magana take amma gaba daya hankalin Ajay na kan dakinsa da ta shiga kai tsaye, he look shock irin he didn't see that coming, he ignored her ailment that he understood immediately, ya Ι—an yi calming din kansa yana kallonta yace "Saboda kin ga ranan ya shigo dake nayi persuading kaina ban yi reacting ba sai kika yi zaton public room ne wannan? An gaya maki ko shi Jay din yana shigar min daki anyhow? Baki da hankali ne or are you out of ur mind? Come and get out before u push me to the wall, kuma kar ki kuskura ki taka min carpet dina da wannan kafafuwan naki, wannan filthy dakin da kika shiga kika kwanta duk Ζ™ura da datti common sense dinki bai gaya maki ki share dakin ki goge ba sannan kiyi changing bedsheet, sannan zaki shigo min daΖ™i ki kakkabe min duΖ™ kuran da kika kwasa a jikinki ki cuceni, plss come and get out before i loose my temper...." A fusace ya kare maganar yana kara bude mata kofa da kyau ta yanda zata zo ta fita, Khaleesat ta wani taΙ“e baki tace "To ai sai kaje ka bude min kofar parlor" Tsawa yayi mata yace "Baza ki fice min daga daki ba?" Ta fashe da kuka ta nufi kofar tace "To kasan me yasa zan je gida ne, ko ba saboda urgent issue bane" Yace "Ke kika san urgent issue din, get out of my room" Ganin he is damn serious don gaba daya mood dinsa ya canza tun da ta shiga dakin yasa ta fita daga dakin tana kallonsa tace "Don Allah ka bude min kofar parlon before it's too late" Banging kofar dakinsa yayi ya kulle, Khaleesat ta dinga kallon kofar, after a minute sai gashi ya fito, ya saka takalmin da yake yawo da shi a gidan, ta bi sa da kallo sai kuma ta bi bayansa tana hararansa, downstairs ya sauka ya tafi ya bude mata kofar parlon, tana tafiya a hankali ta karasa bakin kofar sannan ta fita tana kallonsa, kulle kofar parlon yayi, Khaleesat taji wani sanyi don iya Hijab ne jikinta babu rigar sanyi, walking slowly ta fita daga compound din gidan gaba daya wani mugun sanyi ke shigarta, sai yanxu ta kara tabbatar da Ajay mugu ne kuma ba shi da conscience, ta ciro wayarta taga ko zata iya order din ride, tana ta tsaye a Neighborhood din bayan ta duba ride din, after almost 5 minutes taga hasken fitilar mota daga compound din gidan, dauke kai tayi har ya fito da motar, taga yayi parking inda take tsaye, ta wani kallesa, fuska daure yace "Do not waste my time Malama" Ta wani tura baki ta bude front seat, sai dai kuma tsoro take kar ta zauna ta Ι“ata masa motar ta shiga uku, haka dai ta shiga sai bata sake jikinta gaba daya a zaune ba, tana shiga ya ja motarsa, har suka isa apartment dinta bai ce mata komai ba, bayan yayi parking murya can ciki tace "Nagode" Daga haka ta sauka daga motar ba tare da ta kallesa ba ta nufi kofar apartment dinta ta bude da makulli ta shiga ciki, bata kulle kofar ba ta tsaya jikin window ta Ι—an bude labule kadan tana lekawa taga ko ya tafi, haska inda ta zauna taga yana yi da wayarsa, ta zaro ido ta juyo hijab dinta da sauri sai taga bata yi stain ba, ta sake kallonsa taga ya gama haske haskensa ya kashe fitilar wayan, ta ma san kilan ya gane me yasa tace zata dawo gida, turo baki tayi saboda kunyan da taji, tana ta tsaye jikin window har bayan minti biyar bata ga yayi Reverse ba, ita kuma so take taga tafiyarsa sannan ta kulle kofarta da makulli don saboda zuwan da yayi daxu ya bar mata kofa a bude Aymaan ya fado mata gida kamar barawo, bude motar taga yayi after almost 10 mins ya fito, sai da taga ya nufo kofar apartment din sannan ta ruga sama da sauri ta shige dakinta... Ko da Khaleesat ta shiga bandaki taga hatta kayan jikinta ma bai yi stain ba, pad din da ta siyo tun daga Nigeria ta dauka a cikin akwatinta, bayan ta gama gyara jikinta ta fito ta canza kaya sannan ta saka rigar sanyinta ta kwanta, wajen karfe dayan dare Khaleesat ta farka daga baccin da ya dauketa a firgice duk da bata dade tana baccin ba ta mike zaune zuciyarta na bugawa, mafarki tayi wai Aymaan ya zo yana ta bubbuga mata kofa, dama kuma har tayi bacci hankalinta na kan kofar parlor ko ya tafi ya kulle mata kofar ko a bude ya bar mata oho, a hankali ta sauka daga kan gadon ta bude dakinta ta fita corridor tana leka downstairs, kwance ta gansa kan kujera idonsa a lumshe ya maida wutan parlon zuwa dim light, a hankali ta sauka downstairs din yanda bazata yi making sound ba, after some seconds ta koma sama ta dauko masa duvet, tana dawowa parlon ya bude ido, ta koma baya tana kame kame tace "Duvet ne, naga akwai sanyi sosai yau...." Ya nuna kansa yace "I should use ur duvet? Me? Ke da kika iya shiga daki duk Ζ™ura da datti comfortably ki kwanta shi ne zaki kawo min duvet din ki i should use saboda nayi hauka, ai duk macen da zata iya zama comfortably cikin daki me datti da Ζ™ura without cleaning it, kuma ta dinga yawo a gida babu takalmi a kafarta to babu kalan kazantar da bazata aikata ba, shi yasa taku ta zo daya da Jay, bird of the same feathers, ba gwara in kwanta sanyi ya kasheni ba da inyi amfani da abinda ya fito daga dakin ki, kujeran nan ma don sabbin furnitures ne yasa na kwanta" Khaleesat ta wani kallesa, sai kuma ta juya ta koma sama da duvet din, kuma sabo ne ko amfani da shi bata taΙ“a ba a ledansa ma ta ciro yanxu, can kasan ranta ta dinga ce ma kanta Allah ya kara mata, tsaki ta ja bayan ta shiga daki ta kulle kofarta da makulli tayi kwanciyarta. Washegari wajen karfe bakwai Khaleesat ta fito daga dakinta, bata gansa a parlon ba, hakan yasa ta sauka downstairs ta tafi kofar ta murda taji a kulle, ta leka garage taga babu motarsa, tabe baki tayi ta wuce kitchen don dama da yunwa ta kwana, sai wajen karfe goma ta gama duk abinda take ta bar gidan zuwa school, har suka gama lectures bata sake fuska ba ranan, tun Safiyyah na jan ta da magana har ta gaji ta kyaleta, bayan sun fito department Safiyyah na kallonta tace "Is there any problem Khaleesat? Naga gaba daya yau mood dinki babu kyau" A takaice Khaleesat tace "Nothing" Safiyyah tace "Ke dai ki gaya min gaskiya, kila ma haushina kike ji ban sani ba ma" Sai a sannan Khaleesat ta kalleta tace "Saboda me bazan ji haushin ki ba Sophie? Kawai kin ja Ι—an iska mara kamun kai ya shigo rayuwata ina zaman zamana, you caused me all this wallahi" Safiyyah tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Wai Aymaan? Wallahi ban san Ι—an iska bane Khaleesat, kin ji na rantse, na zata yana da kamun kai ne yanda nake ganinsa sumi sumi a department" Khaleesat tace "To jiya wajen karfe shidda na yamma sai gashi a apartment dina unfortunately na bar kofa a bude kawai ya fado min cikin parlor kansa tsaye" Bude baki Safiyyah tayi tana kallon Khaleesat ko kiftawa babu with shock, a hankali tace "Apartment din ki kuma Khaleesat? Na shiga uku, sai aka yi yaya?" Khaleesat taki bata amsa don takaici, Safiyyah ta hade rai tace "To kuwa sai nayi masa hauka, uwarsa yaje nema maki a gida ko an gaya masa kowa shege ne kamar sa?" Kallonsa kawai Khaleesat take daga nesa har ya nufo inda suke zaune, Safiyyah kuwa ko lura da shi bata yi ba rai bace take cewa "To ke baki kira masa Cops ba? don Allah ki gaya min sai aka yi yaya da yaje apartment din naki? Yau ga mahaukaci kai" Juyawa Safiyyah tayi ganin shadow din mutum a gabansu, yana kallon Khaleesat da kyau yace "Kara ta kika kai gun wancen garan don ya min me? Me kike tunanin zai iya min? Muscles dinsa na banza har ni zai nemi ya daka? Who did he think he is? Me yake takama da shi? Sarautar tasu da bata taka kara ta karya ba ko me? Sannan naga kamar yana mance a America mu ke not Nigeria, ni zai nuna ma dabanci bai san course dinsa nayi a Nigeria ba?" Safiyyah ta mike tace "Look Aymaan, ita fa Khaleesat ba irin wa ennan shegun matan da kake tunani bane gaskiya, ka bar ganinta sakaka a Amurka, yarinya ce ita me mutunci da ta san ciwon kanta, kuma harkar duniya bata gabanta wallahi, wannan get together din ma ni na ja ta don dole taje ba wai ra'ayinta bane shi yasa throughout ta kebe gefe daya a wurin u saw that too, shi kuma wanda kake kira da gara fiance dinta ne, ba wai shisshigi yake yi ba, sannan sarautarsu kuwa ta taka kara ta karya don gidansu a nan Amurka ma ba ko wani shege bane a Nigeria ke iya mallakan irin wannan babban gidan a wata kasar, kai kuma naga hayan apartment kake a Amurkan, Sannan iyayen Khaleesat basu fara turata wata kasa karatu ba sai da suka tabbatar da mijinta a hannu, kuma shi ma a kasar yake, ka ga ai baza kace masa gara ba" Aymaan na mata wani kallo yace "Ke ki iya bakin ki kar ki ja ma kanki matsala a rayuwarki, Fiance din banza, a ina Fiance ya zama miji? ranan daurin aure ma an fasa balle common Engagement, shi da Engagement din yake takama dama?" Safiyyah tayi wani shewa tana rike kugu tace "Na ga kamar ba zaman lafiya kake so ba Malam, to wallahi idan baka fita harkar kawata ba a kasar nan a gaban idon ka zan kira maka 911 in lafta maka sharrin da babu me fitar da kai sai Allah, kamar yanda ka fada nan ba Nigeria bane tuni za ayi mana maganinka wallahi, kuma Unguwan da take tsaf za a bincika surveillance camera a ga sanda ka shiga apartment dinta ta yanda za a tabbatar ba sharri aka maka ba..." Aymaan ya gyara tsayuwa yana kallonta da kyau yace "Really?? dama ke mahaukaciya ce ban sani ba?" Safiyyah tace "Dawanau ce ni karewa, wallahi idan baka yi hankali da mu ba a kasar nan zaka ga jahilci tsantsa, ai ni da nake ganin ka sumi sumi a makaranta ban san gogaggen dan iska bane kai sae yanxu, to banda Ι—an iska waye zai fada apartment din mutum kamar gidan ubansa? Ashe dama ciwon Ζ™waΖ™walwa gare ka ake yada jita jitar ciwon zuciya gare ka?" Har ya daga hannu zai wanka mata mari sai kuma ya rike fist dinsa ya cije hakora yana kallonta yana huci, Safiyyah tayi wani dariya tace "No slap me, try it plss, mare ni mana.... wallahi rabon ayi deporting dinka back to Nigeria a cikin jirgin ruwa ne ke tunzura ka, try slapping me ka ga ikon Allah" Yace "Daga ke har kawar taki zan yi maganin ku wallahi...." Daga haka ya juya kamar zai tashi sama ya bar wajen, Safiyyah tace "Ni wallahi da aka ce min babanka Deputy ne sai da kunya ya kamani ranan na rufe fuska, na zata Ι—an vice president ne kai irin wannan jijji da kan da kake ashe common Deputy ne ma da ba a san da ku ba a Nigeria, kuma in ka fasa maganinmu baka cika namiji ba wallahi, dama ana ganinka an ga kwararren Ι—an shaye shaye Ι—an codeine, ban san wani tsautsayin yasa har mu ke gaisawa da kai ba banda nima dai gantalalliya ce bani da kamun kai"

[7/13, 1:42 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat tsabar yanda ta zama shock kasa cewa komai tayi a inda take zaune kamar ruwa ya cinye ta, ta shiga uku ita kam ga kuma wani da yafi Abdul tashanci, Safiyyah na huci tace "Ta shi mu je, don dai ban san yanda ake yi bane a kasar nan, da Nigeria ne ai daga nan police station na nufa in je in kai report, to su nan ban san ko ana haka ba" Ita dai Khaleesat ta kasa tashi don duk jikinta yayi sanyi kamar an watsa mata kankara, Ganin Khaleesat taki tashi Safiyyah tace "Ki tashi mu tafi don Allah kar ya sake dawowa" Khaleesat ta kalleta tace "In tafi ina? Am not going anywhere Safiyyah, haka kawai in koma apartment dina ya bi ni can?" Safiyyah na huci tace "Kuma fa haka ne" Khaleesat ta dafe kanta da yayi mata nauyi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Safiyyah tace "Wannan fa kamar ya fi Abdul zama Ι—an daba, ni wallahi ban san haka yake ba da ko hanyar da ya bi a makarantar nan ma bazan dinga bi ba, in ba dai in danna 911 yanxu su taho ba gaskiya" Khaleesat ta wani kalleta tace "Su taho su yi maki me? Kar kiyi dialing ki bari sai na bar nan tukunna" Safiyyah ta koma ta zauna tayi tagumi, Khaleesat ta bude handbag dinta duk jiki a sanyaye ta ciro wayarta, ta fi second talatin ta kasa dialing number Ajay don ta tsani masifarsa ita kam, but did she have a choice? Haka kawai ta koma Apartment dinta Aymaan ya bi ta ko kofar a kulle yake ya balle ya shigo mata ta shiga uku, ita sai yau ma ta kare masa kallo kana ganinsa kaga someone on drug shi yasa idonsa suka zama kamar me sexy eyes ashe tsabar shan kwaya ne, Safiyyah ta kalleta tace "Dole dai wancan mara mutuncin za ki kira, don ni wallahi bana son Ajayn nan gwara Housemate sau miliyan, ki ji fa ranan har da korata saboda kawai zai maki magana sai kace bai san yanda muke da ke ba, ya maida ni kamar wata bare ranan, abinda Housemate dinki bazai taΙ“a yi ba kenan yace in tashi wai zai maki magana, tun daga ranan na kullacesa a raina wallahi, ashe haka yake da baΖ™in hali ban sani ba, nace masa good afternoon wai ya amsa da evening tsabar rainin hankali, pls i don't like him" Khaleesat tace "To ina da wanda zan kira bayan shi ne?" Safiyyah tace "Yaushe Housemate din naki zai dawo ne? Gaskiya we are missing him yayi maza ya dawo" Khaleesat tace "Oho" Daga haka tayi dialing number Ajay, sai da ya katse ta sake kira sannan ya daga, taji yace "What again Madam?" Hurriedly yayi tambayar as if in a haste to cut the call, ta sauke idonta a hankali tace "Zuwa yayi ya same mu a department ni da Safiyyah" Ajay yayi shiru, sai kuma yace "Sai aka yi yaya?" A sanyaye Khaleesat ta gaya masa abubuwan da ya zo ya fada da kuma yanda suka yi da Safiyyah daga karshe, Ajay dake ta sauraronta yace "Kin ga wannan kawar taki me shegen rawan kai sai ta ja maki bala'in da baki yi tunani ba a rayuwarki, who sent her to exchange words with him? Duk ba ita ta kai ki inda kika hadu da gayen ba? And meye kike son in maki da kika kirani yanxu?" Khaleesat ta katse wayarta ta ajiye, Safiyyah dake ta kallonta tace "What is he saying?" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, sai ga wayarta ya fara ring ta duba taga shi ke kiranta, Safiyyah ta taΙ“e baki tace "Allah sarki Housemate gaskiya yana kokari da wannan Ajay din ashe haka yake? Wallahi yanda kika san Malamin islamiyya haka nake ganinsa ni dai yanxu, kullum a fusace yake, ki daga kar ya katse, ni yanxu na gaya ma Mustapha wannan magana ai zai gano na tafi Party bayan ce masa nayi baki da lafiya zan je apartment din ki daga schl ranan" Khaleesat tayi picking call din ta kai kunne taki cewa komai, yace "Kashe min waya kika yi?" Tace "To me zan yi idan ban kashe ba, kawai kayi ta ma mutum masifa kullum" Yace "Sai ki je kiyi sorting self din ki out" Daga haka ya katse wayarsa, Safiyyah tace "Tirrr, anya wannan zai iya zama da mace kuwa? Ina ga a world din da ya tashi iya maza ne kawai suka yi surrounding dinsa, amma sam bashi da sympathy wa mace, kawai tashi zaki yi mu tafi gidan Yaya Mustapha don nima ban baki goyon bayan zuwa apartment din ki ba, Aymaan drugs din da yake sha basa gaya masa gaskiya" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, gaba daya taji zaman America din ma ya fita kanta har ma da karatun, shikenan ita daga wannan sai wannan a rayuwarta, hawaye taji ya cika idonta, Safiyyah tace "Ke kuma matsalata dake kenan, komai sai kice kuka kamar wata er yaye, Meye abun kuka kuma? Ni fa ina da strong mind yanda bakya zato" Ita dai Khaleesat goge hawayen idonta kawai take don ta gaji kuma haka, Safiyyah ta tabe baki ta koma gefe, haka suka zauna for almost 10 minutes a wajen kowa da tunanin da yake a ransa, murya can kasa Safiyyah tace "Kin ga kuma gashi can zuwa, wannan mutumi dai bashi da alkibla" Khaleesat ta daga kai tana kallon inda Safiyyah ke kallo, lkci daya ta dauke kai fuskarta a daure, A hankali Safiyyah tace "Ni dai kinga tafiyata...." Daga haka ta dau handbag dinta kamar munafuka ta bar wajen kan Ajay ya karaso, har Ajay ya iso wajen Khaleesat bata sake kallon direction dinsa ba, Yana kallonta yace "Rashin kunyan ki har ya kai ki dinga katse ma mutane waya yanxu?" Ta wani kallesa amma taki cewa komai, sai kuma ta kauda kai, yace "Ba magana nake maki ba?" Bata fuska tayi tana shirin kukan da ya tokare mata a makogwaro yace "Sai dai kiyi ma kanki kuka ba ni ba, and in case u don't know.... work load dake kaina yafi karfin duk wani kananun issues din ki, Jay ne yake iya combining both ni kam bazan iya ba, i will be taking you home ki zauna can har sanda Jay zai dawo ku ci gaba daga inda ku ka tsaya, i don't have much time to be fighting with a tout because of you" Ita dai bata ce komai ba, ya hade rai yace "Baza ki tashi ba?" Mikewa tayi without looking at him, ya juya ya bar wajen ta fara bin bayansa tana hararansa, can apartment dinta ya fara kai ta, bayan yayi parking yace "Kar ki bata min lkci ki shiga ki dauko duk abinda zaki bukata for now, don't waste my time" Bude motar tayi ta sauka ta nufi apartment din, sai da ta Ι“ata kusan minti ashirin a cikin gidan bata fito ba, patient dinsa ya kare ya dau waya zai kirata kenan ya ga motar da ya tsaya dai dai apartment din, kallon motar ya dinga yi don ya gane motar waye, wanda ke cikin motar na ganin motarsa sai yayi gaba ya wuce apartment din yana driving slowly, Ajay ya dinga kallon motar da mamaki, wato uban fist din da yayi masa banda frnds dinsu sun shiga tsakani bai ishesa ba kenan, few a cikin abokan Aymaan are also his frnds shi yasa matter din ma bai yi escalating ba har suka shiga tsakaninsu suna ba Ajay hakuri, amma fa Aymaan ya sha kulli kafin abokan su yi intervening, haushin hakan yasa yaje ya samu su Khaleesat a department dinsu, sai kuma yanxu gashi ya sake biyota gida, Ajay ya gyada kai, ya ci sa'a ba a Nigeria suke ba, wayarsa ne ya fara ring ganin Jay ke kiransa ya daga, daga daya bangaren Jay yace "Yarima me yasa baza kayi respecting title din da kake holding ba pls, why are you like this? menene ya kai ka fada da Aymaan? A America ku ke fa ba Nigeria ba Bruh" Ajay dake sauraronsa yace "Ai ba mu yi fada ba, kilan dai nan gaba za mu yi, don sai na karya masa hannu in bai yi hankali ba, dama naga ba shi da Stamina bugu daya ya tafi kasa don haka karyasa ba wahala zai min ba..." Jay ya ja tsaki yace "Can you hear ur self plss? I will report you to Abba in dai baza ka dena wannan abun da kake yi ba, kai bini bini ka kai fist kamar wani Ι—an dambe? who does that pls, haba wannan zubar da class dinka kake wallahi" Ajay yace "To wa ya jawo? Ba kai da wannan brat din bane ku ka ja har nake fada? Da baka bar ni da ita ba hakan zai faru ne?" Jay yace "A'a dama can hannunka kaikayi yake, stop using us to cover ur foolishness, sannan ni ban bar ka da ita ba because i know she is old enough to care for her self with no supervision kai ne dai ka maida care dinta hannunka voluntarily for reasons best known to you, Kuma ni ba gashi nayi ma Aymaan din magana ba kuma ya fahimce ni, amma kai komai sai ka sako hargagi ciki kamar jira kake ka fara dambe" Shiru Ajay yayi, kawai sai yayi ignoring wasu daga maganganun Jay yace "Ohk, kayi masa magana shi yasa naga motarsa yanxu a kofar apartment dinta ko?" Jay yayi shiru, sai kuma yace "Kai me ya kai ka apartment dinta?" Ajay ya katse wayarsa ya ajiye, sosai yaji Jay ya bata masa rai, and he was boiling from inside, ji yayi kamar ya ja motarsa yayi tafiyarsa ya bar ta da faith dinta a gidan tunda dama ba idea dinsa bane dawowarta America, har ya fara reverse amma kuma sai ya kasa tafiya, ya sake kallon direction din da Aymaan ya bi yaga babu motarsa alamar ya tafi, Jay ya dade bai Ι“ata masa rai kamar haka ba, kawai ya dau wayarsa ya shiga contact dinsa ya danna masa block sannan ya ajiye wayar, sai ga Khaleesat ta fito daga apartment dinta, ko kallonta Ajay bai yi ba har ta gama saka duk abubuwan da ta dauko a back seat don taga bai bude booth ba babu kuma alamar zai bude, bayan ta kulle seat din ta bude front seat ta shiga motar ta kullo kofar a hankali, ita ma bata kallesa ba kamar yanda shi ma bai ko kalleta ba ya fara reverse din motar. Har suka isa gidan ba abinda yace mata ita ma haka, yayi wucewarsa ciki ya bar ta da kayanta, haka nan ta dauka kayan bit by bit tana shiga da su gidan, har sannan yana tsaye parlor waiting for her to finish, sai da ta gama shigo da kayan babu yabo babu fallasa yace "Meet me in the kitchen" Daga haka ya nufi kitchen din ta bi bayansa, Utensils da aka kebe a kitchen din ya nuna mata wajen da suke a takaice yace "That is a no go area, duk ma me zaki taΙ“a a kitchen din nan banda su" Yana kai wannan ya fice daga kitchen din ta dinga kallon Utensils din ba ma sae an gaya mata ba ta gane iya shi ke amfani da su, can ta tabe baki ta juya ta fita, bayan ta kai duk abubuwan ta dakin da ta sauka jiya taji wayarta dake jaka na vibrate, ta dau jakan ta bude ta ciro wayar, sosai gabanta ya fadi ganin number Housemate dinta, duk da tayi deleting number amma tsaf yana kanta don special digits ne bbu wahalan haddacewa....

[7/14, 8:35 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat ta zauna gefen gadon dakin tana kallon screen din wayarta, zata yi picking call din ya katse, it took her almost 2 minutes before returning the call amma har ya katse bai daga ba, ta dinga kallon wayar waiting to see if he will call back amma har bayan minti goma bai kira ba, hakan ya sa ta ajiye wayar a hankali ta mike ta fara gyara dakin, ta sauka downstairs tana dube duben inda zata ga abun shara da goge goge na gidan, har ta fidda rai da samu sai gashi ta gani a under stair storage din gidan, bayan ta gama gyaran dakin da take ciki da Babban corridor din sama sai kuma ta sauko downstairs ta fara gyaran babban parlon hade da goge goge, it took her almost 2 hours kafin ta gama aikin gidan gaba daya, kitchen kuma bata ga abinda zata gyara ba cause it was very neat and tidy alamar yana gyarawa a ko da yaushe, ta maida Household cleaners din da tayi amfani da su a under stair storage din da suke sai gashi yana saukowa downstairs ya canza kayan jikinsa, yi yayi kamar ma bai san me tayi ma gidan ba ya dau makullin motarsa da ta ajiye saman Centre table ya nufi kofa ya fita daga parlon, tabe baki tayi ta tafi sama don ta gaji sosai ba kadan ba, sai da tayi gyaran gidan sannan ta kara tabbatar da girman gidan. Khaleesat na zaune a daki da laptop dinta a gabanta tana studying wani course dinsu da za su yi test dinsa ranan monday, it was a Saturday afternoon, ta juya ta kalli wayarta dake vibrate, sau uku kenan Safiyyah na kiranta taki picking don tasan me zata ce, can dai ta jawo wayar tayi picking ta kai kunne tayi shiru, daga daya side din Safiyyah tace "Haba mana Khaleesat don zaki koya min abu sai kiyi ta min walakanci gashi test za mu yi ranan Monday, is it fail that you want me to fail?" Khaleesat ta sauke wani ajiyar zuciya tace "To ya kike son inyi Sophie? i said u should be coming kin ki" A fusace Safiyyah tace "A'a wallahi bazan zo wannan gidan ba kinji har na rantse, haka kawai in zo ya koreni, shi ba wai kara garesa ba balle ince zai ji kunyan korata, gaskiya bazan zo ba don zan iya zaginsa idan ya koreni" Khaleesat tayi dariyar da bata yi niyya ba tace "Wai ban gane ya kore ki ba, why will he do so bayan yasan wajena ki ka zo" Safiyyah tace "In dai baza ki zo school din ba shikenan kawai i will look for another person to teach me, ni kinsan ba gane lectures nake a aji ba sai in an min bayani dalla dalla gani ga mutum" Khaleesat dai tayi shiru tana jin ta, Safiyyah tace "Sai anjima don Allah...." Khaleesat ta Ι—an yi murmushi tace "To let me see if i will be able to come, kin ga karfe biyu da rabi yanxu fa, da tun jiya sai ki gaya min ai, kina school ne?" Safiyyah tace "Eh mana, tun 12 na shigo schl ai" Khaleesat tace "Ohk, i will be coming now" Katse wayar tayi, ta sauka daga kan gadon ta canza kayan jikinta ko rigar sanyi bata sa ba don sanyin ya ragu sosai yanxu, ta dau backpack dinta bayan ta saka laptop ciki ta kashe wutan dakin ta fito, downstairs take leke daga passage way din da take tsaye, ta ga Ajay zaune parlon da wasu turawa biyu alamar frnds dinsa ne ga wine a gabansu, she can't even remember the last time da suka hadu a cikin gidan da shi, it is more than a month now da take gidan amma zata iya kirga sau nawa suka yi crossing part da shi a gidan, yawanci yana bangarensa take fita school da safe, kuma daya daga ma'aikatan gidan ne ke dropping dinta sannan ta gaya masa sanda zai je ya daukota kamar dai yanda aka basa instruction yayi, in kuma aka dawo da ita gidan bayan ta gama lectures zata ga babu motar Ajay a compound alamar ya fita, tunda a daki take zama bata sanin sanda yake dawowa gidan, the next day kuma the same process will repeat it self, girki kuwa tunda tayi sau uku da shi taga duk bai ci ba don ko kusa da abinda ta dafa baya zuwa kawai sai ta dena sai dai tayi nata ita kadai, but tayi noticing anyi restocking foodstuffs irin na Africa a kitchen din probably because of her, don ita duk wani ciman turawa ba damunta yayi ba, may be yayi noticing hakan ne yasa ya siyo mata irin wanda take so, gyaran gida kuma tunda workers din are around iya dakin da take ciki kawai take gyarawa, tana saukowa downstairs ta gaida friends dinsa sannan ta kallesa shi ma ta gaishesa, bai amsa gaisuwan ba without looking at her yace "Ina za ki je?" Ta sauke idonta tace "Zan shiga school" Still not looking at her yace "Ki yi me a school on a Saturday?" Ta Ι—an kallesa, sai kuma tace "Tutorial zan ma Safiyyah" Sai a nan ya juya ya kalleta yace "As per the lecturer you are in John Hopkins ko? to baza ki je ba" Tayi shiru tana kallonsa, ya hade rai yace "Ko baki ji me nace ba?" Bata fuska tayi tana kallonsa, ya ci gaba da maganar da yake da friends dinsa, tana jan veil din jikinta tace "To zata iya zuwa nan?" A takaice Ajay yace "Baza ta zo, leave this parlor Madam" Ta wani tura baki ta juya ta koma sama, tana komawa daki ta kira Safiyyah, a hankali tace "Sophie i met the door locked kuma no one is around...." Safiyyah ta katse ta tace "Har workers din gidan?" Khaleesat tace "Kawai ki nemi wanda zai maki Tutorial din Sophie, ranan Monday before the test zan sake yi maki" Safiyyah tace "Ai shikenan, dama ban saka ran za ki zo ba, in ma Ajayn ne ya hanaki shi ya sani don ko a jikina wallahi, dama tun ranan farko da muka je duba Housemate dinki da na fara ganinsa sam bai kwanta min a rai ba naji tsoronsa, wai don Allah yaushe Housemate din ki zai dawo ne abu almost 2 months yanxu, ko dai anyi awarding dinsa doctorate Degree dinsa ne shi ne ya tafi yayi wasu abubuwan a Nigeria? shi kuma wancan uztaz din ko anyi cancelling work dinsa ne yake sakewa daga farko?" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, magana Housemate din nata yake mata balle tasan sanda zai dawo? Kuma kullum da damuwan hakan take kwana take tashi a ranta, ta rasa gane me yasa communicating din da baya yi da ita ya tsaya mata sosai a rai har yake damunta, well... may be he have his reasons, she is not even judging him, but deep down she knows she misses him so much, she misses everything about him, wani lkcn in ta kasa hakuri takan dake zuciyarta tayi masa magana ta WhatsApp, zai kuma yi mata reply amma casually, in yayi mata haka kuma bata iya daurewa sai tayi kuka, last maganar da tayi da shi almost a week ago ta tambayesa yaushe zai dawo, kawai yace mata soon and that was how the conversation ended, after that basu sake magana ba har yau, dama kuma ita ke yi masa, Safiyyah tace "Ni dai sai anjima, ina ta maki magana zaki min shiru katina na tafiya" Daga haka ta katse wayarta, a hankali Khaleesat ta ajiye wayar hannunta a gefen gado. Few weeks later Khaleesat na zaune ranan friday ita kadai a haraban department dinsu, Voice call suka gama da Aunty Farida ta WhatsApp bayan ta turo mata wasu videos da ta kasa fahimta sai kawai ta kira Aunty Faridan don tana online, tunda suka gama wayar Khaleesat ta kasa kwakkwaran motsi a inda take zaune, she looks so confuse and shock at the same time, kamar ance ta daga kai ta ga Aymaan da wata yarinya suna tafiya, yarinyar na ta masa labari da turanci, bata yi kama da er Nigeria ba duk da kana ganinta kasan er Africa ce yarinyar, Khaleesat ta sauke idonta tana kallon wayar hannunta har suka wuce ta, sai ga Safiyyah ta fito daga Hall din karatu da Backpack dinta a hannu, tana isowa kusa da Khaleesat ta zauna tace "Ke baki ga Aymaan ya wuce ba yanxu?" Khaleesat dai tayi shiru don har sannan bata yi recovering daga shock din da take ciki ba, Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace "Ni wallahi naji haushi da ya Musty ya neme sa wai har da basa hakuri akan abinda muka masa, me muka masa in ba cowardliness irin na Musty ba? Abinda ma shi ne ya nuna mana halin jakanta, tunda uwata ta haifeni ban taΙ“a ganin matsoraci kamar Ya Musty ba, ni da nake mace ma na fi sa dakakken zuciya, wai ka samu namiji kamar ka kana basa hakuri, wallahi ban so ace case din nan ya mutu da wuri ba na so ayi ta gwabzawa, na tsani in ga an shashantar da Case me zafi irin haka, bayan hakurin da Ya Musty ya basa naga kamar yana shakkar Ajay ma, kinsan na gaya maki frnd dina Sulaiman ya gaya min ashe narka masa duka Ajay ya so yayi aka maza aka shiga tsakaninsu, amma duk da haka ya sha kulli wajen Ajay, to duk har da hakan ya tsoratasa ya kama kansa da mu, amma nasan zai fake da cewa Ya Musty ne ya basa hakuri, kuma yaga Ajay ya daukeki daga apartment din ki ya maida ki gidansu, kinga ai dole ya tsorata da lamarin, Allah ya sa dai Housemate din ki ma bai ba Aymaan din hakuri ba don daga yanda ya sameni yayi min magana ta WhatsApp sanda abun ya faru har da bani lefi wai me yasa zan yi ma Aymaan rashin kunya wallahi babu tantama shi ma Housemate din naki ya basa hakuri, ni fa na tsani in ga maza suna baya baya da case din tashin hankali kamar wasu mata, shi yasa Ajay ya burgeni da ya nuna masa hauka, wo koma yaya ne dai can ta matse masa shege, ai kinga bai sake bi ta kanmu ba a school din nan, kaiii mun ga jalala ashe lafiyarsa qlau mutumin, sannan bai taΙ“a aure ba sai yawon iskanci..." Shiru Safiyyah tayi ganin hankalin Khaleesat gaba daya baya jikinta, Safiyyah tayi kasa da murya ta kamo hannunta tace "Me ya faru kawata? Is anything the matter? Naga lafiya na bar ki naje dauko Backpack dina, why the sudden change of mood? Ko Aymaan din yace maki wani abu ne?" Khaleesat ta kasa ce ma Safiyyah komai, sai ga hawaye cike idonta, Safiyyah ta dire jakar hannunta a kasa tace "Subhanallahi, don Allah me ya faru? Me Aymaan din yace maki mu kira Ajay yanxu" Khaleesat na goge idonta cike da karfin hali tace "I spoke with Aunty Farida now" Safiyyah ta zaro ido tace "Me ya faru?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Kawai ce min tayi Housemate dina yaje can gidanmu jiya" Safiyyah ta wani kalleta, can tace "Don Allah ji yanda kika sa gabana ya fadi na zata mutuwa aka yi a gidan naku, to don ya je gidanku sai ki fara kuka? Ko dai dama akwai abinda ke damunki kike son kiyi kukan amma sai yanxu kika samu sarari?" Khaleesat ta girgiza mata kai, wasu hawayen na taruwa idonta tace "Gida wai ya siya ma Abbana" Safiyyah ta bude baki da mamaki tana kallon Khaleesat, can ta dafe kirji tace "Gida fa Khaleesat?" Khaleesat ta kasa cewa komai wasu hawayen na sauka idonta, ta bude wayarta ta shiga chat dinsu da Aunty Farida ta tsaya dai dai wajen videos din ta mika ma Safiyyah wayar, Safiyyah was speechless for almost 2 minutes bayan ta gama kallon videos din gidan, wato gida ne har gida irin na zamani that is well furnished, a hankali Safiyyah tace "I am short of words too Khaleesat, wallahi ban san me zan ce ba, but just know that ur Housemate is one in a million Khaleesat...." Khaleesat ta fashe da kuka, Safiyyah ta rungumeta soothingly tace "It's something to be happy about ba kuka za ki yi ba, yanda ya saka iyayenki farin ciki Allah Ubangiji ya dawwamar da shi cikin farin ciki na har abada, Allah ya saka masa da mafificin alkhairi, ya biya masa duk bukatansa na alkhairi, yanxu kina komawa gida sai ki nutsu ki kirasa" Cikin kuka Khaleesat tace "Ko na kirasa baya picking" Safiyyah tayi shiru, can tace "May be he have his reasons Khaleesat, just compose a text for him sai ki tura masa ta WhatsApp, and i will also thank him via WhatsApp on ur behalf, duk wani abun farin cikin ki nawa ne nima...." Ita dai Khaleesat ta kasa cewa komai but she is soo emotional, ta kasa daina kukan da take, a haka driver ya zo daukanta, Safiyyah ta rakata har inda yake parking ta bude mata back seat tace "Don Allah kar ki je gida kina wannan kukan, wannan ai abun farin ciki ne ba na bakin ciki ba da zaki yi ta kuka har haka" Khaleesat ta gyada mata kai kawai tana share hawayenta, Safiyyah ta daga mata hannu tace "Anjima zan kira ki in sha Allah" Nan ma dai kawai kai Khaleesat ta gyada mata a haka drivern ya ja motar suka bar wajen. Bayan sun isa gida Khaleesat ta bude kofar parlor ta shiga da sallama can kasa, kanta a kasa ta gaida Ajay da ta gani zaune parlor da Salem, sannan ta wuce sama, sau daya Ajay ya bi ta da kallo sai kuma ya dauke kansa, after some minutes yana kallon Salem yace "I am going up to get some rest, will you still be around?" Salem yace "Ohk i will wait har ka sakko" Mikewa Ajay yayi ya dau wayarsa sannan ya saka House Slippers dinsa ya wuce sama, kofar dakin da take ciki ya tsaya yayi knocking, Khaleesat da ta kwanta gefen gado ta dora kanta saman pillow feeling so emotional ta mike zaune tana kallon kofar, yana bude kofar ta fara goge sauran hawayen idonta, ya shigo closing the door behind him yana kallonta yace "What happened?" Sauke idonta tayi bata ce komai ba, yace "Ba kya ji na ne?" Girgiza masa kai tayi a hankali tace "Ba komai" Yace "Bakomai zaki shigo ma mutane gida kina kuka?" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, yace "Sake kula ki yayi a school din ne?" Ta daga kai ta kallesa ta girgiza masa kai cikin sanyin murya tace "A'a, kawai kaina ne ke min ciwo" Daga sama har kasa ya kalleta sannan yace "Kukan ya baki magani" Daga haka ya juya ya fita daga dakin.... Wajen karfe biyar Khaleesat ta farka daga baccin da ya dauketa tun bayan da Ajay ya bar dakin, da yake ba sallah take ba, mikewa zaune tayi ta jawo handbag dinta a hankali ta bude ta ciro wayarta, number Housemate dinta da bata kara saving ba har sannan tayi dialing hoping he will pick her call today, amma har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, to yanxu me ma zata ce masa ta WhatsApp, words failing dinta kawai za su yi in ma tace tayi masa magana ta can, bata ma san ta yaya zata fara ba, Ι—aga kai tayi ta kalli kofar dakin jin ana knocking, sai da aka sake knocking din sannan ta sauka daga kan gadon tana tafiya a hankali ta tafi ta bude kofar, daya daga workers din gidan ne rike da tray din abinci, mamaki tayi don tun zuwanta gidan babu worker din da ya kawo mata abinci har daki, infact ita ce ma ke girka abinda take ci a gidan, ta dai amshi tray din cikin sanyin murya tace "Thank you" Sannan ta juya ta koma daki, bayan ta ajiye tray din ta bude plate din dake rufe a kai taga Jollof rice ne yana tiriri alamar yanxu aka gama girkin, ga wani aroma me dadi na tashi, ta bude wani plate din taga full chicken laps biyu anyi grilling dinsu, sai kuma bowl din veggies da dressing dinsu a gefe, with 2 bottles of water and a glass cup da can drink, still a kan tray din taga maganin ciwon kai, a hankali ta dau spoon ta goge sa da tissue din da aka yi wrapping dinsa sannan ta fara cin abincin, kuma sosai abincin yayi dadi, ya kuma yi yaji kamar a Nigeria aka yi, ta dai ci abinda zata ci ta ajiye sauran for dinner. Washegari still haka aka kawo mata breakfast har daki, bacci ma take tunda ba school zata je ba ta sauka kan gadon ta saka hijab sannan ta bude kofar, bayan ta amshi tray din ta kulle kofar dakin ta tafi ta ajiye breakfast din don sai ta fara wanka.... Wajen karfe biyar din yammacin ranan Ajay na parlor tare da Salem aka bude kofar parlon, tun da ta shigo Ajay ke kallonta da wa enda ke biye da ita a baya, wato jakadiyarta da aminiyarta Hajiya Usaina, sai er aminiyarta da bazata wuce 25 years ba, Salem ya mike tsaye yana welcoming dinta da ladabi, ta amsa masa sama sama without looking at him, sai da ta zauna parlon bayan jakadiyarta tayi saurin gyara mata throw pillow sannan Ajay ya gaisheta, ta amsa cike da isa tace "Daga Massachusetts Boston mu ke, mun je convocation din Afrah a Havard University, we will be passing the night here before leaving for Nigeria tomorrow" Ajay dai bai tanka ta ba, ya gaida aminiyarta warce convocation din er ta suka je a Havard din, Afrah dake ta kallonsa ta gaishesa, ya amsa without looking at her sannan ya mike ya nufi sama, shi dai Salem ya juya ya fita daga parlon, Ajay na haurawa sama direct dakin da Khaleesat take yayi knocking sannan ya bude kofar.

[7/15, 9:49 PM] khaleesat Haiydar πŸ“š✍️: Khaleesat dake karatu da Laptop dinta ta juya tana kallonsa, a takaice yace "Don't look at me that way, ki dau duk wani abinda zaki bukata yanxu zaki koma dakin Jay don muna da baki a gidan...." Ko rufe baki bai yi ba aka bude kofar dakin, ta madubin dakin yake kallonta don tsayuwa tayi bakin kofa tana kallon Khaleesat with mouth agape, Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Ina yini...." Aunty ta karaso cikin dakin da mamaki tana kallon Ajay tace "Junaid? Wacece wannan kuma?" Ba tare da Ajay ya juya ya kalli inda take ba a takaice yace "Kanwar Salem" da wani expression Aunty tace "Kanwar Salem? Me take yi a gidan nan? Kuma a cikin daki zaune a saman gado?" Sai a sannan Ajay ya juya, looking at her in the eyes yace "The apartment she was staying was sold out yesterday, and she is homeless, so she is here for today before moving to her new apartment tomorrow...." Aunty tace "Da iznin wa kayi hakan? Dama gidan ka ne nan din da zaka yanke hukunci kanka tsaye kamar me gidan? I can't remember his Highness saying this house is urs in anyway Junaid, baka da right, sannan iyayenta da suka turota karatu basu nema mata wani alternative ba sai kai sarkin Hausawan Nigeria dake Baltimore? Beside ban ga ta inda take kama da Salem ba, Salem da yake baki me ya hadasa da wannan farar yarinyar? karya kake yi daya daga matan banzan da kake iskancin ka da su ne a kasar nan, ka zata duk bamu san abinda kake yi ba ne?" Calmly Ajay yace "You can say whatever, kawai dai ni dai i also can't remember Abba saying we are to share this house with you and ur visitors, saboda ni da Jawwad Abba ya siya gida a garin nan ba don kowa ba, don haka ban ga dalilin da za ki dinga zuwa da wasu mutane can babu notice ba ki maida mana gida gidan saukan baki, kaf Massachusetts babu hotels da dole sai kin taho Maryland za ki samu masauki? Beside all this... u are not even in the rightful place to tell me what to do and what not don da sunana da na Jawwad Abba ya siya gidan nan, don haka babu ruwanki da duk wanda zan kawo gidan, since you can't do without intruding, ki zo kiyi intrusion dinki in peace kiyi tafiyarki without questioning me...." Aunty da ta bude baki tana kallonsa tace "Zagin nawa da ka saba zaka yi Junaid? Ni kake gaya ma bakaken magana? Rashin kunyan da ka saba yi min zaka yi a nan ma?" Ajay yace "Whatever, all i know is that u can't just be appearing in here without notice tare da wasu mutane can kina inconveniencing din mu kina sa mana ido" Wani murmushi kawai tayi ta kalli Khaleesat sannan ta juya ta fita daga dakin, gaba daya jikin Khaleesat yayi sanyi ta kasa motsi a inda take, after few seconds ta sauka daga kan gadon tana kallon Ajay da ya kafe ma dressing mirror ido yasan fitar da tayi Abba zata je ta kira, cikin sanyin murya Khaleesat tace "Why will u speak to her that way Ya Junaid?" Ya dakatar da ita fuska daure yace "Ba ruwanki Malama, kin san ta ne?" Khaleesat ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, ya juya ya fice daga dakin yana birkita gashin kansa, ga wani zafi da yake ji, where is he even going to start explaining this to his dad for the second time, gashi Jay baya gidan just him and the lady in the house, wani bayani zai yi ma Abba da zai yarda da shi? Ι“angarensa ya nufa ya zauna gefen gado ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi, in mahaifiyarsa ce ai sai dai su kashe su rufe tare da ita without her involving his dad in this issue, infact baza ma ta so wani yaji ba, he felt soo emotional, Aunty na komawa downstairs ta zauna kan kujera ta jawo jakarta ta ciro wayarta, Hajiya Usaina dake kallonta tace "Ya naga ranki a bace Fulani?" Aunty tayi wani murmushin takaici tace "Bari dai inyi waya da mai martaba tukunna Usaina" Tana fadin haka ta tafi dakin da take sauka ta tarar da jakadiyarta a ciki tana ta faman goge goge duk da dakin fess yake, zata fita Aunty ta mata alamar ta ci gaba da abinda take, sannan ta zauna kan kujera tayi dialing number mai martaba tana girgiza kafa at the same time tana fatan Allah ya sa ya samu damar daga kiran don zuwa yanxu dai tasan yana Ι“angarensa shi kadai, ai ko babu jimawa ya daga kiran, bayan sun gaisa cikin ladabi da kwantar da murya tace "Allah ya taimake ka ya ja zamaninka, mun iso Maryland babu dadewa yanxu" Daga daya bangaren yace "To maa sha Allah fulani..." Ta kara yin kasa da murya tace "Amma Allah ya ja zamaninka ban ji dadin abinda na zo na tarar a gidan nan ba" Shiru Mai martaba yayi bayan yaji me tace, don tana fadin haka babu abinda ya fado masa sai abinda ya gani dakin Ajay kwanaki da ya sauka Baltimore, Jin Mai martaba yayi shiru Aunty tace "Ko kana tare da baki ne ranka shi dade babu sararin mu yi magana?" Calmly Abba yace "Ina sauraron ki" Aunty ta gyara zama tace "Mace na zo na tarar a dakin Yarima cikin wani yanayi mara dadin fade, hankalina yayi matukar tashi ranka shi dade, na dimauce ba kadan ba da abinda idona ya gane min, ban ji dadin hakan ba ko kadan wallahi, kuma da alama ba wannan bane karo na farko, ya saba yin hakan, Allah Ubangiji ya shirya mana su kawai" Mai martaba yayi shiru don sosai yaji abinda ta fada ya dake sa don har sai da ya jingina kansa da kujeran da yake zaune, tayi kasa da murya tace "Amma ba komai ranka shi dade kar hakan ya sa kaji babu dadi a ranka ko kuma ka damu, in sha Allahu idan na dawo sai mu san abun yi, mu san inda za mu billo ma lamarin don baza mu zuba ido a ci gaba a haka ba, kaga wannan big slap to our faces ne idan aka samu labarin abinda yake yi a kasar nan, hakan zai zubar mana da reputation din masarautarmu ne kawai, shi yasa kwanaki nace maka a samu yarinya me hankali da nutsuwa er manya a aura masa ko da kuwa ba er gidan sarauta bace, sai naga kamar hakan bai gamshe ka ba tunda baka ba maganar tawa muhimmanci ba na lura baka son yi masa dole ne, ni kuma abinda yasa na kawo wannan shawaran shi ne saboda shi Yarima ba kula yan matan yake ba a gida Nigeria" Cikin nutsuwa mai martaba yace "Bangaren nasa kika je?" Aunty ta Ι—an fara kame kame tace "Ehh can na je ranka shi dade, gani nayi tunda muka shigo gidan ga dai motarsa amma shiru bamu gan sa ba, da yake kwanaki ai ya Ι—an yi zazzabi saboda weather sai nayi tunanin to ko baya jin dadi ne, sai na karasa bangaren nasa, shi ne fa idona yayi mummunan gamon nan" Mai martaba yace "If possible try conversing with the lady u saw ki ji er wace jaha ce a Nigeria, ina son sanin background dinta, just Converse with her Fulani...." Aunty tayi shiru bayan taji me Mai martaba yace, can tace "Ranka shi dade ai ba er Nigeria bace matar, baturiya ce fa, kuma irin tsofaffin turawan nan, da kyar ma in bata haifesa ba" Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace "Na fahimta" Aunty tace "Yanxu dai idan na dawo za mu tsara komai ur Highness, ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu anyi na karshe, we will put a stop to this soon, kuma ko makusantan ka na fada don Allah kar ka gaya ma wannan magana, don ba magana bace da ya kamata ace ya fita" Mai martaba was quite, don tunanin da yake yi ma shi daban, daga karshe Aunty tayi masa sallama ya katse wayar, tana kallon jakadiyarta dake zaune kasa tayi murmushi tace "Mace na samu a dakin baΖ™i, amma ban san tun yaushe take zaune gidan ba ya dai ce min jiya ta zo gidan, sannan babu cin mutuncin da ya mance bai min ba" Jakadiya ta kara bajewa a kasa tace "Ja'iri, gaskiya ya kamata wannan karan ki dau mummunan mataki akan sa ranki shi dade kar ki dau lamarin da wasa, abubuwan da yake maki sun isa haka, duk baya ganin mutuncin ki kuma wannan abu na saka ni damuwa uwar gijiyata, yanxu dai kamata yayi ki kira daya daga ma'aikatan gidan ku kebe ki tambayesa ki ji tun yaushe ya ajiye yarinyar a gidan nan..." Aunty tayi wani murmushi tace "Kin kawo shawara kuwa...." Mikewa tayi ta fita daga dakin Jakadiya na jero mata kirari.... Bayan wani lokaci Ajay ya fito dakinsa ya tafi dakin da Khaleesat take, without looking at her yace "Ina jiran ki downstairs" Daga haka ya fita daga dakin, har zai sauka kasa ganin su Aunty a parlon ga uban kayan ciye ciyen da aka baje masu a tsakar parlon, sai kawai ya tsaya a corridor, a hankali Khaleesat ta mike tsaye ta dau Hijab dinta ta saka ta bude kofar dakin ta fito, yana jin alamar ta fito ba tare da ya juya ba yace "Mu je, kuma ban ce ki ce zaki gaida kowa Downstairs ba" Daga haka ya fara sauka kasa tana biye da shi a baya jiki a sanyaya, tun da suka sauko Aunty da kawarta da Afrah ke kallon Khaleesat, Ajay dai ko kallonsu bai yi ba ya nufi kofa Khaleesat na biye da shi ita ma bata yarda ta kalli direction din su ba, gun motarsa taga ya nufa ya bude ya shiga, ta karaso gun motar ganin bata shigo ba ya daure fuska yace "Baza ki shigo ba?" A hankali ta bude seat din ta shiga, yana kallonta yace "Haka kika fito baki dauko komai ba?" Tayi shiru, sai kuma tace "Ai baka ce min in dau komai ba" Tsaki ya ja ya bude motar ya fita ya koma cikin gidan, ita dai ta bi sa da kallo, dakin da take ya koma ya dau laptop dinta da charger sai wayarta shima da Chargern sa sannan ya fita daga dakin yayi locking kofar yanda ba wanda zai bude ya sauka downstairs, nan ma su Aunty suka bi sa da kallo, Afrah kamar idanuwanta za su bi sa har compound din.... Har Ajay ya isa apartment din Khaleesat bai ce mata komai ba, ita ma dai tayi shiru da tunani iri iri a ranta, kana ganinta kasan duk a sanyaye take, bayan sun sauka motar ya nufi entrance din shiga apartment din ya ciro makullin a aljihunsa ya bude ya shiga parlon, ta bi bayansa. Jay na zaune gaban mai martaba kansa a kasa yana jin duk abinda yake cewa, Cikin nutsuwa mai martaba ya ci gaba da cewa "I am so disappointed in you Ahmad, kana kallon abinda Ι—an uwan ka ke yi amma ka kasa gaya min, i am really disappointed, even if you can't tell me directly there are other ways to approach me and i will understand you, to yanxu kana tunanin rufa masa asiri kake yi yana aikata sabo kenan?" Jay ya dago kansa a hankali, after few seconds murya can kasa yace "Abba ba abinda ku ke tunani bane, i promise you Junaid is doing nothing that is against the teaching of Islam, ba ma shi da lokacin da yake kula mata balle har yayi wani doguwar mu'amala da su, ka yarda da ni Abba bazan maka karya ba" Mai martaba dake kallonsa yace "Na je Maryland na ga mace a dakinsa, Auntynku ta je jiya and same thing happened, ta yaya zan yarda da maganar ka Ahmad? What sort of silly coincidence is that?" Jay yace "A gafarce ni Abba, amma nasan ba a dakinsa Aunty ta ga mace ba sai dai a dakin baki, shi Junaid wani irin mutum ne wanda idan yaga mutum stranded be it namiji ko mace bai ki ya ajiye ko ma waye a gidan ba har zuwa sanda mutumin zai yi sorting kansa out, you can confirm this from the workers of the house, wallahi halinsa kenan ba wai don ya hada komai da wa enda yake taimaka ba, Abba kasan bazan maka karya ba wai don in rufe laifin da kake tunanin Ajay ya aikata don in nayi hakan nima Allah bazai bar ni ba, Billah i am telling you nothing but the truth Junaid ba shi da hadi da koma wacece Aunty ta gani a gidan nan" Abba yayi shiru, after a while yace "Na ji, kuma na yarda, but i am afraid hukuncin da na tsara a kansa bazai masa dadi ba, but he still have to accept it cause hakan kadai ne zai sa in samu nutsuwa da kwanciyar hankali" Jay sai kallon Abba yake, a hankali yace "Wani hukunci kenan Abba?" Abba yace "Na yanke hukunci zan masa aure and he just have to accept ko ma wacece matar, you are not excluded also, duk da kai akwai maganar ka da Hadiyah....." Jay ya kwantar da murya yace "Don Allah kayi hakuri Abba, we have just few months remaining da muke saka ran za mu gama karatun nan da muke yi, bamu yi tunanin za mu kawo har warhaka bamu gama ba, plss Abba a saurare mu har zuwa sanda za mu gama, in just 2 to 3 months" Abba yace "Kwanaki ma haka ku ka min dadin bakin nan, kun maida ni kakan ku" Jay yace "Kayi hakuri Abba, mun san ka bamu dama sosai and this will be the last in sha Allah" Murmushi kawai Mai martaba yayi yana kallonsa, kowa yasan sa a mutum mai magana daya, amma ga yara sai juyasa suke yanda su ke so, after a while Abba yace "Yaushe zaka koma Amurkan?" Jay ya sunkuyar da kansa yace "Watan da za mu shiga in sha Allah" Abba yace "Allah ya kai mu" Khaleesat na zaune saman darduma wajen karfe shidda na yamma, tun da tayi sallan la'asar take zaune kan darduman take karatu a laptop dinta don in a month and few days time za su fara Spring semester exams din su, wayarta taji yayi vibrate alamar shigowar text, ta jawo wayar tana duba text din taga number Ajay, "Come out" iya abinda ya tura mata kenan, ta ajiye wayar ta mike ta dau Hijab dinta ta saka, tunda ta dawo apartment din nata kusan kullum zai zo wani lkcn ya gama zamansa a motarsa da yake parking a garage sai kuma yayi ordering ride ya bar motar tasa a garage din ya tafi, wani lkci kuma ya shigo parlon nata bazai dai dade ba zai fita, kuma ba wai magana yake yi mata ba, da ta lura bai son magana iyaka kawai ta gaishesa ta koma ta ci gaba da abinda take, wani lkcn ma sai ta dawo school zata ga alamar ya zo apartment din idan taji kamshinsa a parlor, duk ta lura for security purpose yake hakan, har ma da barin motarsa da yake yi a garage din apartment din, don ko da ya zo da safe ya dau motar ya tafi inda za shi to zai maida nan yayi parking da yamma sannan yayi ordering ride da zai kai sa gida, and she really appreciate all this that he is doing for her safety, don farko da ta dawo gidan kusan kullum sai tayi kuka gashi bata iya bacci da daddare don gani take kamar at anytime Aymaan zai iya zuwa gidan, gradually kuma ta hakura barin da ta ga Ajay na yawan zuwa gidan, amma fa duk wannan abubuwan ba shi ne yasa bata tunanin Housemate dinta ba, babu ranan da zai zo ya fadi bata yi tunaninsa ba, wani lkcn har da kukanta ta rasa dalilin hakan, zuwa yanxu kam ta ma hakura ta dena masa magana ta WhatsApp din tana ganin kamar takurasa take maganar da take masa duba da yanda yake amsa mata kamar baya so, tana bude kofar apartment din bayan ta sauka downstairs taga ledojin dake ajiye bakin kofar, sai kuma ta kalli garage ta gan sa zaune cikin motarsa, sai da ta fara shiga da ledojin parlor sannan ta fito ta nufi gun motarsa tana kallonsa ta gaishesa, ya bude motar ya sauka ya amsa without looking at her ya kulle motarsa, sai kuma taga ya nufi lyft din da ke jiran sa, tana tsaye tana kallo har ya shiga sannan ta juya ta koma apartment dinta ta kulle kofar da makulli, kayan shayi ta gani a ledojin da ya kawo mata, gwangwanin madara manya biyu, milo biyu, kwalayen sugar, Lipton, coffee powder, da kuma chocolate, har da bread manya uku da cookies iri iri, kilan ya shiga kitchen ne yaga babu madara shi ne ya siyo mata, kuma lokaci ne bata samu ba tana ta son zuwa taje tayi shopping din kayan shayin.... Bayan kwana biyu Khaleesat na isa school Safiyyah dake zaune lecture hall ta dinga mata wani kallo tace "Wai don Allah baza ki dena yafa manyan mayafan nan ba kina kunyata ni Khaleesat, kin fa gama wannan kadararren iddan ba wai baki gama ba, ko sau biyu za ki yi masa iddan ne?" Murmushi kawai Khaleesat tayi tana kallonta tace "Ni na ce maki na gama?" Safiyyah tace "Ai shi yasa na tambaya ko sau biyu za kiyi don ina nan ina taya ki lissafi wallahi kin gama, duk na kagu inga kin fara cin gayu kina zuba zawarcin ki son ranki, ai yanxu kuma ba da bane kin shiga wani level daban" Khaleesat tace "To bakya lissafi dai dai kuwa..." Safiyyah tace "Wallahi ina yi sai dai in kece bakya lissafin" Khaleesat bata tanka ta ba ta nemi waje ta zauna don yanxu wani sabon gayu Safiyyah ke ji a makarantar ita ga final year student, ko ta zo da mayafi sai ta saka a jaka tayi ta yawo da hula kawai kamar er Enugu, ko kuma tayi azababben English dressing ta daura karamin dankwali a kai, ita dai har ta gaji da yi mata magana ta zuba mata ido, a tare suka koma apartment din Khaleesat ranan don danwake Safiyyah tace zata masu, sai kusan yamma likis Safiyyah ta bar gidan shi ma Mustapha ne ya isheta da kira, Khaleesat na kitchen ta gama wanke duk Utensils din da Safiyyah taki wanke mata tana goge gogen kitchen din taji an bude kofar apartment din, dama tasan dole zai zo tun da taga ya mance charger dinsa a parlor alamar da taje school ya zo apartment din daxu, a hankali take wanke hannunta a pampon kitchen din trying to be sure of what she is perceiving, gently tayi patting hannunta jikin towel din kitchen din tana goge ruwan hannunta, sai kuma ta juya, sai da numfashinta ya tsaya for some seconds tsabar yanda gabanta ya fadi, yana jingine jikin bango kusa da kofar shiga kitchen din ya rungume hannu yana kallonta, ta sunkuyar da kanta, sai kuma ta nufi kofar kitchen din zata fita zuwa parlor, hannunta ya kamo yana kallonta with smile on his face, bata san sanda ta fashe da kuka ba zata kwace hannunta ya jawota kusa da shi murya can kasa yace "Halysaah" Hawaye kawai ke zuba idonta ta kasa kallonsa, slowly ya rungumota jikinsa murya can kasa yace "I am sorry" Bude kofar parlon aka yi, Jay yayi saurin saketa amma tuni Ajay ya shigo, sau daya ya kallesu sai kuma ya sauke idonsa ya tafi ya dau charger dinsa ya juya ya fita daga parlon....

 

Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

 

 

 

 

[23/07/2025, 1:50:42PM] Khaleesat Haiydar πŸ“š ️: https://chat.whatsapp.com/I5vo38MH2jH8pDvzVF0Q4w

 

 

 

Khaleesat ta bi Jay da kallo ganin ya nufi parlor, kana ganinsa zaka gane shi ma bai so abinda yayi ba don bai yarda ya sake hada ido da ita ba, kamar bai san sanda ma yayi hakan ba, ganin ya zauna a parlon ta sauke idonta daga kallonsa, sai kuma ta juya ta koma kitchen, Jay yayi dialing number AJ amma har ya katse bai yi picking ba, bai yi zaton zai shigo parlon ba don har yana ce masa kar ya bata masa lokaci, ya mike ya tafi window din parlon yana duba garage amma sai yaga ya tafi don babu motarsa a garage din, komawa yayi ya zauna ya cire face cap dinsa, Khaleesat na fitowa kitchen ya maida face cap din without raising his head, ita dai kanta a kasa ta karaso parlon tana rike da bottle water da glass cup ta duka gabansa ta ajiye masa, still not looking at him a hankali tace "Sannu da zuwa" Sai a sannan ya Ι—an kalleta, ganin ba kallonsa take ba with calm in his voice yace "How are you Halysaah?" Cikin sanyin murya tace "Alhamdulillah, ya hanya?" Yace "Cool" Tana wasa da fingers dinta tace "Yaushe ka dawo?" Har sannan bai cire idonsa a kanta ba yace "Not less than an hour ago Housemate" A hankali tace "Ya su Mama da mutanen gida?" Yace "They are all good Halysaah, ya karatu? In few weeks time za ku fara Spring semester exams ko?" Ta gyada masa kai, shi dai kallonta kawai yake, can yace "How is Safiyyah?" Ta kwantar da kanta saman gwiwowinta har sannan tana jin kamshin turarensa na tashi a jikinta tace "She left not long ago" Sai kuma ta daga kai ta kallesa, sauke idonsa yayi daga kallonta, ita ma ta sunkuyar da kai tace "What should i make for you? Daxu danwake Sophie tayi mana and it's finished, should i make you pasta or rice?" Yace "No don't worry Housemate, Ajay made some food for me back home" Ta Ι—an bude ido tana kallonsa tace "Can he cook?" Kawai yayi murmushi wanda iyakarsa lips bai bata amsa ba, sai kuma ya nuna mata trolley din da ya shigo da shi parlon yace "I got you some stuffs, hope you will love it" Shiru tayi tana kallon akwatin, yace "Check them" Ta sauke idonta sai kuma ta mike ta bude akwatin, tsadaddun Abaya ta fara cin karo da tana bude akwatin, ta daga kai ta kallesa suka hada ido ya sakar mata murmushi, sauke idonta tayi ta rufe akwatin kawai, cikin sanyin murya tace "Thank you soo much, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara budi" Yace "Ameen Halysaah" Still bata dago kanta ba a hankali tace "And i also want to appreciate you for what you did to my parent, Allah Ubangiji ya sa kafi haka, Allah ya biya maka duk bukatun ka na alkhairi...." Bai tanka ta ba yana kallon agogon wrist dinsa ganin bakwai saura yace "I will take my leave now Housemate, it's late already" Ita dai bata ce komai don sai taji babu dadi da yace zai tafi, ya mike yana kallonta yace "Kina da lectures gobe ne?" A hankali tace "Sai karfe daya na rana" Yace "Ohk, i will come before then in sha Allah, Aunty Farida ta bada sako a kawo maki, yana mota kuma Ajay ya tafi da motar" Ita sai a sannan ma ta tuna ashe Ajay ya shigo gidan fa, ta kallesa tace "Ohk, but how are you going back home tunda ya tafi da motar? Kayi order din Uber ne?" Jay yace "Ohh, na ma manta" Komawa yayi ya zauna yana danna wayarsa yace "Let me order the ride now" Ita dai tayi shiru tana kallonsa babu ko kiftawa, har ya gama order din ya daga kai suka hada ido, sunkuyar da kanta tayi tana jan yatsunta tace "Toh baza kayi sallah ba kafin ride din ya karaso?" Yace "Ohk bari in yi alwala" Mikewa yayi ya nufi bandakin dake parlon, ita ma ta tashi ta tafi sama dauko masa darduma, bayan Jay ya idar da sallah Khaleesat na kallonsa daga bayan kujeran da take tsaye tace "Or should i make you tea?" Yace "My ride is waiting Outside Housemate" Ta gyada masa kai kawai, tana biye da shi a baya har suka fita daga apartment din, ta rakasa har gun Lyft din dake jiransa, yana kallonta kafin ya shiga motar yace "Sai na zo gobe, take care of ur self" Ta gyada masa kai don har cikin ranta take jin da ma kar ya tafi, sai yanxu ta kara tabbatar da irin missing dinsa da tayi, memories dinsu tare na old apartment dinta ya dinga dawo mata a kai, and she misses every bit of those moment, she wish it's gonna happen again, a hankali ta juya bayan ya shiga Lyft din tana tafiya kamar mara lafiya ta koma apartment dinta ta kulle kofar. Jay na komawa gida ya bude kofa parlor ya tarar da Legend zaune bakin kofar alamar shi yake ta jira, tun da ya dawo gidan daxu bayan Ajay ya daukosa a airport Legend ke ta tsalle kansa yana haushi kamar zai rungumosa wanda hakan ke nuni da yayi missing dinsa ba kadan ba kuma ya bi sa har daki yana wagging tail dinsa yana kada kai alamar farin ciki ya nemi waje ya zauna a dakin, kafin su fita daxu kuwa sai da Jay ya kullesa a Cage dinsa don bin sa ya so yi yana ta haushi, Jay ya kalli Ajay dake zaune parlorn yana danna wayarsa ko dago kai bai yi ba, dukawa Jay yayi gaban Legend yana patting kansa ya bude steak din da ya siyo masa a hanya ya ajiye masa a pack din sannan karen ya kyalesa ya maida hankali kan Steak din, Jay ya mike ya karasa cikin parlon yana kallon Ajay yace "Didn't you see my call?" Ba tare da Ajay ya kallesa ba yace "I didn't" Jay bai sake ce masa komai ba ya nufi kitchen, bayan wasu yan mintoci ya fito yana kallon Ajay yace "Where is the food you said you made?" Still not looking at him Ajay yace "Nayi zaton can zaka kwana ae, i gave all the food to the workers" Kallonsa kawai Jay yake, can ya juya ya koma kitchen din to make a cup of tea for him self, ko kafin ya fito kitchen din Ajay ya bar parlon. Washegari wajen karfe sha daya Khaleesat ta sauko downstairs jin ana danna bell, bayan ta tambayi waye ta bude kofar parlon, gaishesa tayi tana kallonsa, ya amsa da murmushi, zata amshi ledan hannunsa yace "Don't worry Halysaah" Juyawa tayi ta koma cikin parlon, ya bi bayanta, bayan ya ajiye ledan yana kallonta yace "Sakon Aunty Farida da tace a kawo maki" Khaleesat ta karasa ta dau ledan ta kallesa tace "Thank you so much" Kitchen ta tafi da shi ta duba taga cin cin ne me yawa aka yi packaging sai alkaki da dublan, a wani ledan kuma ta ga kayan kamshi na dafa shayi, sai flour, kuka da kanwa, da dakakken yaji me yawa, tana gani ta gane saboda danwake aka aiko mata, Ι—an murmushi tayi sai kuma ta dau take away a kitchen ta dibi cin cin din da su alkaki ta saka a wani ledan ta dawo parlor da shi, dukawa tayi gefensa da ledan, yana kallonta yace "What's that?" Tace "Cin cin ne da alkaki da Aunty Farida ta bada a kawo, i fetch some for you" Ya Ι—an bude ido yace "No, ta bamu namu ni da Ajay, it's at home wannan naki ne" Ta wani kallesa tace "Ban yarda ba" Yace "I am serious, har da tea spice da grounded pepper duk ta bamu" Khaleesat tayi murmushi tace "To na yarda" Mikewa tayi ta maida cin cin din kitchen, sannan ta fito tace "I made you some food in kawo maka yanxu?" Yace "I had breakfast before leaving home Halysaah" Ɓata fuska tayi tana kallonsa, yayi murmushi ya sauke idonsa yace "Ohk... amma kadan zaki zubo min ba da yawa ba" Juyawa tayi ta koma kitchen din, ba a dau lokaci ba ta kawo masa shinkafa da stew din kaza da tayi, yana kallon abincin yace "Wannan ai yayi yawa" Tace "Eat and remain" Shi dai murmushi kawai yayi, ta koma kitchen ta dauko masa ruwa da glass cup ta ajiye masa, yace "Karfe nawa kika ce kina da lectures?" Tace "Karfe daya" Yace "Ohk to ki shirya idan na gama sai inyi dropping dinki nima zan shiga school din" Tace "Ohk, nagode" Sama ta wuce ta bar sa a parlon. Ko da Khaleesat ta sauko downstairs wajen karfe sha biyu da rabi ta gansa kwance kan 3 sitter idonsa a lumshe, murmushi tayi cause this is one of the part she misses so much about him, ta dafa bayan kujeran a hankali ta duka tana kallon innocent face dinsa, zagawa tayi tana tafiya a hankali ta tafi gun Vase din artificial flower dake parlon ta zari daya ta dawo gabansa ta duka dai dai fuskarsa ta kai flower din a hankali moving it back and forth his face, cikin bacci ya kai hannu fuskarsa da sauri ya kauda kai, hakan bai sa ta dena abinda take ba, yana kokarin mikewa zaune ya kusa cin karo da ita banda tayi saurin matsawa baya, ta dinga kyalkyala dariya tana kallonsa, murmushi yayi ya jinginar da kansa da kujeran yace "See this girl, wa yace maki ban ga sanda kika sauko ba, i just pretended i was sleeping" Tana dariya tace "Wallahi baka gan ni ba, you were sleeping" Shafa kansa yayi still smiling ya mike tsaye yace "I am waiting for you at the garage, amma ni dai nasan ba bacci nake ba i was just meditating..." Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo tana murmushi, ta kalli wayarsa da ya bari kan kujera without noticing, sai da ta jira har ya fita daga parlon sannan ta duka kusa da kujeran ta dau wayar taga babu lock, miss calls ta gani guda hudu na wani number da aka yi saving with Hadiyah tare da text message dinta, call logs din duk yawanci miss calls dinta ne, amma kuma yana picking wasu call din nata, Khaleesat ta dinga kallon number, can ta shiga cikin message din da ta turo masa, "You should have at least pick, just wanted to know if you've arrived safely" shine content din message din, A hankali Khaleesat ke strolling text messages din taga inda Hadiyah ta turo masa "I love you so much Baby, and i want to spend forever with you" Da bai mayar mata reply ba sai ta sake tura masa uhmm, sai ya mata reply da "Love yah 2" Fita daga messages din Khaleesat tayi without going any further, tana kokarin clearing duk inda ta shiga don kar ya gani kawai taga kamar hoton da suka yi a park da shi among many other apps da ya bude a ranan, tayi tapping zata shiga hoton kawai ya nuna mata wajen is locked, ta fi minti biyu durkushe a wajen rike da wayar don gaba daya jikinta yayi sanyi ko motsin kirki ta kasa, can dai ta mike a hankali ta dau jakar laptop dinta ta nufi kofa walking slowly, kafin ta bude kofar ya riga ta budewa har sai da ya ci karo da ita, komawa baya yayi da sauri, ita kuma ta dafe kanta, Ya shigo parlon yana kallonta da damuwa yace "Hope u are not hurt? I am sorry i should have knock" Ta girgiza masa kai kawai ba tare da ta kallesa ba, yace "Are you sure you are okay Housemate?" Zame hannunta tayi daga fuskarta tana kallonsa, a hankali yace "Sorry Halysaah, i forgot my phone shi ne na dawo dauka..." Mika masa wayar tayi ya amsa yana kallonta, ita dai ta sauke idonta, bude mata kofar yayi ta fara fita sannan shima ya fita, ta mika masa makullin apartment din ya amsa ya kulle sannan suka nufi motarsa har a lkcn bai daina waigawa yana kallonta ba to be sure she is okay har suka iso garage, ita dai bata sake yarda ta kallesa ba, ya bude mata gaban motar yana kallonta, Ι—an murmushin karfin hali tayi still not looking at him murya can kasa tace "Thank you" Sannan ta shiga motar, tana shiga ya daga mata veil dinta da ya fito waje ya daura kan cinyarta yana kallonta, sae a sannan ta daga manyan idanuwanta ta kallesa ya sakar mata murmushi, ita ma murmushin tayi har sai da dimple dinta ya lotsa ta sunkuyar da kai tana wasa da gefen veil dinta, ya kulle motar ya zaga ya shiga driver seat yayi igniting motar, bayan sun yi nisa ya Ι—an kalleta murya can kasa yace "Are you sure you are okay Halysaah?" Khaleesat ta Ι—an bude ido tace "Sure..." Don tabbatar masa da hakan tayi kokarin creating conversation tace "Ya Junaid fa?" Jay ya maida dubansa kan titin gabansa yace "Ba kuna magana da shi ta waya ba" A hankali Khaleesat tace "A'a, sai if there is something important" Without looking at her yace "Something important like?" Tace "May be idan ya kawo min abu apartment" Yace "Abu kamar me?" Khaleesat ta juya ta kallesa tace "Grocery shopping" Jay ya gyada mata kai yana ci gaba da driving dinsa, har suka isa school babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu, ita kam Khaleesat ta tafi duniyar tunanin da take.....

 

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

 

 

https://chat.whatsapp.com/I5vo38MH2jH8pDvzVF0Q4w

 

 

 

Bayan Jay yayi parking a school din ya juya yana kallonta, zata bude motar ta sauka yayi kasa da murya yace "Halysaah" Ta juya tana kallonsa, yace "What happened? Why the sudden change of mood?" Khaleesat ta Ι—an bude ido, sai kuma tayi murmushin karfin hali ta girgiza kai tace "Ba komai fa" Yace "Are you sure?" Ta sauke idonta tace "Sure" Yace "Yaushe za ku gama lectures din?" Tace "Lecture daya kawai za mu yi" Yace "Zuwa 3pm kun gama kenan?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk, i will pick you then" A hankali tace "To Nagode" Murmushi kawai yayi mata yana kallon idonta, ta bude motar ta sauka ya bi ta da kallo, sai kuma ya dau wayarsa, Lkci daya ya gane ta shigar masa wayar cause yasan yana da miss calls din Hadeeyah da message a gaban screen, swiping yayi ya bude wayar yaga alamar ta shiga har cikin message din bayan call logs dinsa, jinginar da kansa yayi a hankali jikin kujeran motar with different thoughts running his mind. Har Khaleesat suka gama lectures bata ga Safiyyah ta shigo school ba ranan, tana zaune inda suka saba zama tana ta kokarin kiran Safiyyah tun daxu amma numberta baya shiga, lkci lkci take bin inda take zaune da kallo as if wanting to figure out something, at some point she became confuse and afraid at the same time don wasu memories that are not welcome in her heart ne suka hau dawo mata kai, Student sai harkan gabansu suke a vicinity din babu ma wanda yake kallon inda take zaune, tana kokarin tashi ta bar wajen kawai sai ga kiran Safiyyah ya shigo wayarta, Khaleesat ta koma ta zauna tayi picking call din ta kai wayar kunne, Safiyyah tace "Kin ga ban shigo school ba shine ko ki kirani matar nan?" Khaleesat tace "I have been trying ur line tun daxu baya shiga, hope you are fine? Why are you not in school today?" Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace "Ke da ba sai dai in kira ki ince maki Surayya ta rasu yau ba" Khaleesat tace "Me ya faru?" Safiyyah tace "Ni dai wallahi har na fidda rai da ita in gaya maki kawata" Khaleesat ta hade rai tace "Don Allah ki gaya min me ya same ta?" Safiyyah tace "To wani azababben zazzaΙ“i ne ya damke ta har tana suma, sai ga Surayyan ki har da kamo hannuna yau tana neman agaji duk ta ruda ni, yanxu haka tana can an bata gado a asibiti, ni kuma ina gida saboda Aslam shi yasa ma ban shigo school yau ba, Aslam din da ko kusa da ni bata bari ya zo, kinga in ni mayya ce ai yau da babu abinda zai hanani cinye mata Ι—a" Khaleesat tace "To Allah ya sauwake, Allah ya bata lafiya, wani asibitin ne?" Safiyyah tace "Oho ni dai ba an bar ni da baby sitting ba, Housemate dinki fa? Wallahi naji haushi da bazan samu zuwa in masa sannu da zuwa ba, ai sai ya zata ma walakanci ne ya dawo naki zuwa" Khaleesat tayi murmushin da bata yi niyya ba tace "Ni dai sai anjima, har mun gama lectures din" Safiyyah tace "Don Allah ni dai in ya je apartment din naki anjima ki kirani ki gaya min, ko goyo Aslam ne sai inyi in taho, kin ga ba dadi ace ban masa sannu da zuwa ba har zuwa yanxu" Khaleesat ta dake don bata son tayi dariya tace "Till we speak Sophie, sai anjima...." Safiyyah tace "Ke dalla ba cewa zan yi ina son sa ba, kowa yasan Housemate ai naki ne duk wanda yace zai maku shisshigi ma ai sai dai ya mutu, kilan ma har ya tambayi baba aurenki baba kuma ya basa bamu sani ba" Bude baki Khaleesat tayi a bit shock, don she never saw those words coming from Safiyyah, Safiyyah tayi dariya tace "Atoh, mu ba mu ki gobe a daura auren ba ma wallahi, Uztax Ajay sai ya bada sadakin yayansa, shi kuma Housemate kawai ya tare a nan apartment din naki Ajay da Salem su rakasa, in kayan mata ne sai in debo maki na Surayyah don a kitchen ma take jerasu don in gani, Ghana must go dinsu ake aiko mata daga gida, kin ga kawai sai in debo maki kina da gwangwanin madara da yoghurt abun ki, yanda dai zaki dawo babu banbanci da warce bata taΙ“a aure ba" Khaleesat bata san sanda ta katse wayarta ba ta kife a kafarta kamar warce taji wani mugun abu daga bakin Safiyyah, tafi minti goma zaune a yanda take kamar an dasa ta, taji wayar hannunta ya fara vibrate, a hankali ta juya wayar taga number Housemate, at first ta kasa daga call din nasa, sai da taga ya kusa katsewa sannan tayi picking ta kai kunne tayi shiru kamar munafuka, daga daya bangaren yace "Are you done Halysaah?" Ta gyada masa kai tace "Um" Yace "Ohk, i am waiting for you" A hankali tace "To" Sannan ta katse wayar ta mayar cikin jakarta, ta mike ta fara tafiya zuwa inda zata samesa. Har ta shiga motarsa bata yarda ta hada ido da shi ba, shi dai kallonta kawai yake, Bayan ta kulle motar a hankali tace "Ina yini" Calmly yace "Lafiya lau Halysaah, ya lectures din?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Frnd din ki ta tafi ne ita?" Khaleesat ta girgiza masa kai tace "Bata zo schl yau ba, matar brother dinta bata da lafiya" Yace "Allah ya bata lafiya" Daga haka ya fara driving zuwa gidanta, sai da suka kusa apartment din nata ya kalleta speaking slowly yace "Do you mind going out for dinner with me later Housemate?" Sai a sannan Khaleesat ta dan kallesa, suna hada ido ta sauke idonta a hankali tace "Alright" Yayi mata murmushi ya ci gaba da driving dinsa, Yana parking gaban apartment dinta ba tare da ta kallesa ba tace "Thank you so much" Yana kallonta yace "You are welcome Housemate..." Ta bude motar ta sauka sannan ta Ι—an kallesa suka hada ido, murmushi tayi ta daga masa hannu sannan ta juya ta nufi apartment dinta, shi dai ya bi ta da kallo har ta shiga. Tun da Khaleesat ta ga karfe bakwai na yamma yayi ta zama tense, ta rasa dalilin da yanxu kuma take jin nauyin Housemate din nata sosai, duk da ba yau ta saba fita dinner da shi ba, amma yau gaba daya sai take jin wani nauyi na musamman, har lkcn kuma bata shirya ba tana dai zaune saman darduma after praying, karfe bakwai da minti goma kiransa ya shigo wayarta, ta jawo wayar a hankali tayi picking ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yace "I am on my way now Halysaah" A hankali tace "Ohk, Allah ya kawo ka lafiya" Sai bayan da ta ajiye wayar ta mike ta fara duba kayan da zata sa, har ya iso apartment din nata after 15 minutes bata gama shiryawa ba, sai da ya jirata for another 10 minutes sannan ta fito, ta gansa tsaye jikin motarsa ya rungume hannu yana jiranta, sauke idonta tayi har ta karaso inda yake tsaye, yayi mata murmushi yana kallonta ya bude mata front seat, ita dai taki yarda su hada ido ta shiga motar, yana kallonta yace "Housemate" Sai a sannan ta daga idanuwanta ta kallesa, kamar me rada yace "You look cute" Rufe fuskarta tayi da veil dinta tana murmushi, ya kulle motar ya zaga ya shiga driver seat. The ride was silent, tunanin da take yi daban a ranta shi ma haka, bayan sun isa wajen cin abincin after offering her a seat ta fara zama sannan shi ma ya zauna opposite dinta, ya dau menu din eatry din yana mika mata yana kallonta, ta sauke idonta tace "I am okay with anything u order" Yace "Are you sure? Ke da baki son abincin turawa ni kuma nafi son sa" Murmushi tayi tace "Zan koya ci" A hankali yace "Really?" Ita dai bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, yayi masu order din abincin irin wanda yasan she can cope with, bayan an kawo abincin ta dau lemonade dinta tana sipping a hankali, kamar ance ta daga kai taga kallonta yake, murmushi yayi ya dau nasa lemonade din yana sha yace "Naga kin yi kyau ne sosai" Khaleesat ta kasa kallonsa tace "Kai ma haka" Yace "Ni da baki kalla ba ta yaya kika san haka" Tayi murmushi ta daga idanuwanta tana kallonsa, kashe mata ido yayi slowly, ta boye fuskarta tana dariya a hankali, A haka suka fara cin abincin, amma ta kasa sakin jiki ta ci, shi kuma sai ya tsallake nasa abincin ya dau na gabanta, ta tallabi chin dinta tace "Ko in hada maka dukka ne?" Yace "Ke ma zaki iya daukan wanda kika ga yayi maki a nawa ai, it's called sharing..." Ta wani kallesa, sannan ta ci gaba da cin abincinta a hankali, har ta mance rabon da ta jita so happy and lively irin haka, gani tayi yayi exchanging abincinsa da nata, ta daga idanuwanta ta kallesa bata dai ce komai ba tayi murmushi, ya buda ido yace "Naji naki yafi dadi ne" Yana fara cin nata sai kuma taga ya mike ya dawo kusa da ita ya zauna da abincin yana kallonta yace "I think i can see the food more clearly from here..." Khaleesat dai kallonsa kawai take don gaba daya kamshin turarensa ya cika ta, ya bude pizza dake kan table din, kawai gani tayi ya dau slice daya ya kai mata baki yana kallonta babu ko kiftawa yace "Here...." She couldn't look at him in the eyes, at the same time she was a bit shock at his action, murya can kasa taji yace "Take Halysaah...." A hankali ta bude bakin ya bata pizzan, duk wani abu da yaga ta ki ci sai ya dauka ya kai mata baki, she was so shy, daga karshe ta girgiza masa kai cikin sanyin murya tace "I am full" Yana kallonta yace "Are you sure?" Ta gyada masa kai ta dau lemonade dinta tana sha, shi dai kallonta kawai yake, ta mika masa sauran lemonade din don shi ya shanye nasa, yayi murmushi ya amsa yayi sipping kadan ya ajiye sauran, after some seconds yace "I will like to discuss something with you Housemate, something that's bothering me, may be zaki bani shawara..."  Khaleesat ta kallesa a hankali tace "Ohk...." Amma haka kawai taji gabanta yana faduwa, Calmly ya fara magana yace "You know i am an only child right?" Khaleesat tayi shiru tana kallonsa don bata san da haka ba, yayi murmushi yace "Yeah, my dad was late before i was even brought to the world" Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi tana kallonsa, ya ci gaba yace "Junaid's Dad was my father's younger brother, and he inherited the throne after my father's demise who was then a king...." Khaleesat ta sauke idanuwanta cikin sanyin murya tace "Allah Ubangiji yayi masa rahama, ya gafarta masa" Jay yace "Ameen, i was partially raise together with Ajay, don Mamina couldn't let go of me gaba daya, so lokaci lokaci nake zuwa emirate din, wani lkcn inyi hutu a can, Ajay also lost his Mom when he was just 3 years old" Khaleesat ta dinga kallon Jay ta kasa cewa komai, Jay ya Ι—an yi murmushi yace "Yeah, it's still not easy for him till date, but Alhamdulillah on his behalf" A hankali Khaleesat tace "Allah ya gafarta mata, Allah ya sa ta huta" Jay yace "Ameen, so now kinsan me yake faruwa Housemate?" Khaleesat ta girgiza masa kai, yace "I have this cousin sister Hadiyah...." Sosai gaban Khaleesat ya fadi don tsaf ta haddace sunan nan a zuciyarta, saura kadan tace masa ma bata son zancen amma ta dake zuciyarta tunda shawara yace yake son ta basa, Ι—an farin cikin da take ciki na wnn moment din taji ya fara fading gradually, Jay ya Ι—an yi shiru sai kuma ya daga kai ya kalleta directly in the eyes yace "A gida ake son hada mu aure da ita, Mamina, Mom dinta, my late father's senior sisters, infact all the family members, ya kai ya kawo har sun kai maganar gaban Mai martaba yanxu, kinsan mata idan suna son abu... At first Ajay aka so hadata da and he bluntly turn down the offer..." Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, A hankali yana kallonta yace "I think all this explanation isn't necessary Halysaah, kawai a takaice i want to refuse the offer too nan ba da jimawa ba for reasons known to me alone, but i don't know where to start from Halysaah, I don't know how everyone is going to take this, but deep down i don't think Mamina zata tilasta ni aka abinda bana so, she is always after my happiness and comfort, nasan bazata min dole ba...." Khaleesat was mute, don bata ma san me zata ce ba, amma jikinta kan yayi sanyi sosai ba kadan ba, ji tayi ya kamo hannunta murya can kasa yace "Kin yi shiru Housemate, say something pls" Kasa kallonsa tayi, idonta a kan hannunsa dake nata tana jin heartbeat dinta na karuwa, a hankali ta zame hannunta daga nasa tana murmushin karfin hali cikin sanyin murya tace "Amma baka tunanin hakan da zaka yi zai ja issues a family din naku?" Jay yace "I don't care, as far as Mami is in support of me i really don't care ko me za ace, idan naga ran Mami ya bace da decision dina shine kadai hankalina zai tashi, cause i love my mom so dearly...." Khaleesat still couldn't look at him in the eyes, after some seconds a hankali tace "Menene yayi triggering din canza decision da kake kokarin yi all of a sudden, bayan a farko ka riga kayi masu accepting zaka aureta?" Jay ya Ι—an yi murmushi yana kallonta, kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Look at me in the eyes Halysaah" Khaleesat felt like she is melting cause his intonation was something else, gaba daya ta kasa kallonsa, underneath his breathe yace "Look at me Halysaah" Da kyar tayi karfin halin daga manyan idanuwanta ta saka cikin nasa....

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

 

Ur evidence 07087865788

 

 

https://chat.whatsapp.com/I5vo38MH2jH8pDvzVF0Q4w

 

 

Tun kan Jay yace komai Khaleesat ta kasa ci gaba da kallonsa ta sunkuyar da kanta tana jin kamar ta nutse a wajen, bata taΙ“a jin tana kunyarsa ba kamar wannan lokacin, ta kasa gane wani irin kallo ne wannan yake mata da yake sa ta kara jin kunyarsa, shi ko bai fasa kallonta ba yana admiring kunyanta, she became so uncomfortable lokaci daya a wajen, taji Ι—an composure din nata na neman guduwa ya bar ta, yayi kasa da murya yace "Halysaah..." Bata yarda ta sake kallonsa ba, speaking with calmness yace "Ban taΙ“a sanin akwai lokacin da zai zo inji wata daban nake so ba Hadiyah ba, i never saw that coming, and i can't help it...." Shiru Khaleesat tayi har sannan taki yarda su hada ido, a hankali yace "Kin yi shiru Housemate" Tayi murmushin karfin hali, sai kuma ta fara kame kame tace "To ai ni ban ma san me zan ce ba, the issue is too big for me to give out any advice, it's ur family matter, or better still kawai kayi addu'an abinda yafi zama alkhairi a gare ka, just pray about it, pray for the best...." Yace "Is that all u have to say, ke da ake neman shawara a wajen ki" Tayi shiru for the second time, sai kuma ta samu kanta da cewa "To idan zaka iya masu adalci sai ka hadasu duk biyun ai ba haramun bane" Bata san sanda furucin ya fito bakinta ba, sai kuma ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake babu ko kiftawa, sunkuyar da kanta tayi da sauri, a hankali yace "Haka kike ganin yafi?" A takaice tace "Nima ban sani ba" Yace "But you suggested it" Kin cewa komai tayi tana wasa da edge din veil dinta, shiru Jay yayi kamar wanda ya fada duniyar tunani, after a while Khaleesat ta daga kai ta kallesa, suna hada ido ta dauke nata idon, slowly yace "Ohk then, i will think about that, but..." Kafin ya karasa Khaleesat ta dau handbag dinta tace "I think hadari ne a garin, kar ruwa ya sauko" Yace "Yea akwai hadari, i can perceive it too" Mikewa tayi without looking at him, yace "To saurin me kike sai kace a kafa zaki koma gidan" Ta Ι—an yi yake tace "Gobe fa akwai jarabawan da za mu yi kuma ko karatu ban yi ba" yace "Ai ke Genuis ce...." Khaleesat dai bata ce komai ba amma taki komawa ta zauna, a hankali yace "Kin kawo Suggestion kuma kina fushi da Suggestion din naki Housemate" Khaleesat ta zaro ido tana kallonsa, bata san sanda tace "Ban gane ba" Murmushi yayi ya mike yace "To mu je kar ruwa ya sauko" Sosai ta sha jinin jikinta da furucinsa ta kasa motsawa a inda take tsaye har ya wuce ta, after clearing the bills ya dawo kusa da ita yana kallonta yace "Let go Housemate, ko baki koshi bane let's place another other" Ta wani kallesa, dariya yayi yace "To mu je in ba dai wani abincin kike son ci ba" Kamar warce aka zare ma laka take biye da shi a baya tana tafiya a hankali har zuwa gun motarsa, ko da suka fito an fara yayyafi amma ba da yawa ba, ya bude mata front seat bayan ta shiga ya kulle motar ya zaga ya shiga mazaunin driver, yana fara driving wayarsa ya fara vibrate, Khaleesat ta kalli screen din wayar, Hadiyah ta gani, ta dauke idonta, ya kai hannu yayi silencing wayar gaba daya sannan ya kifar ta yanda ma bazai dinga ganin hasken wayar ba, ita dai bata sake kallon inda wayar yake ba, the ride back to her apartment was silent, ga yayyafin da ake sosai, ko wannensu da tunanin da yake a ransa, ita kam gaba daya farin cikin da take ciki as at 15 mins ago duk ya bace kamar bata yi sa ba, kawai taji zuciyarta ya tunkushe babu abinda yake mata dadi a rai, sai da suka kusa gida ya Ι—an kalleta a hankali yace "Amma idan kun gama Exams za ki je Nigeria ko?" Khaleesat tayi shiru, ita har tana da choice din cewa zata je Nigeria ko bazata je ba, abinda ba ita zata ma kanta kudin jirgin ba, murya can kasa taji yace "Kin yi shiru Housemate..." Murmushi tayi ta buda masa hannu alamar ita ma bata sani ba, yace "Za ki je in sha Allah, ko 2 weeks sai kiyi kafin ayi resuming  summer and final semester din ku...." A hankali tace "To Allah ya kai mu" Yace "Ameen" Ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna takwas da rabi yace "Idan nayi dropping din ki zan je wajen abokina ne da ya shigo garin nan daxu, he will be leaving early tomorrow, ko mu je dake ku gaisa? He is looking forward to meet you" Khaleesat ta girgiza masa kai a hankali tace "Ruwa ake yi, kuma ina son zan yi karatu" Shiru yayi idonsa akan titi, can yace "Ohk then, may be some other time sai ku gaisa, he is my very good frnd, a Nigerian also" Khaleesat dai bata ce komai ba, duk ta kagu ta ganta a apartment dinta taje tayi sallah ta kwanta ko zata samu nutsuwan da ta rasa ga zuciyarta dake a tunkushe, dai dai garage din apartment din nata yayi parking yana kallonta yace "But cikin ruwan nan zaki fita Halysaah, kar ruwa ya taΙ“a ki kiyi mura" Khaleesat ta kirkiri murmushi tace "The rain is not heavy ai" Yace "Give me the key idan na bude sai ki sauko..." Bude jakarta tayi ta ciro makullin ta mika masa ya amsa yana kallonta, sai kuma ya sauke ido yace "Before then i have something little for you" Ita dai kallonsa kawai take har ya dauko wani karamin box a nan cikin motar ya bude yana mika mata, kallon zoben dake cikin box din yana ta kyalli kawai take, sai kuma ta kallesa taga kallonta yake, yayi murmushi yace "Haska da wayarki ki gani, i hope you will love it" A hankali Khaleesat ta ciro wayarta a handbag dinta ta ajiye handbag din gefe, sannan ta kunna fitila tana haska siririn diamond ring din dake wani kyalli, sauke idonta tayi ta ma rasa me zata ce, ya ajiye mata a cinya sannan ya bude motar ya fita cikin ruwan, da ido ta bi sa har ya isa kofar apartment din ya bude, jiki a sanyaye ta dau box din zoben ta kashe fitilar wayarta sannan ta bude motar ta sauka, zuwa sannan ruwan ya fara karfi, yana tsaye bakin kofar yana jiranta har ta karaso ya mika mata makullin apartment din yana kallonta yace "Good night Halysaah" Hawaye ya gani idonta, ta amshi makullin zata yi magana ya daura fingers dinsa a lips dinsa ya girgiza mata kai sannan ya juya ya koma gun motarsa ta bi sa da kallo tana son ce masa ko zai yi spending night din a apartment din nata because the rain is getting heavy, amma tuni ya bude motarsa ya shiga, a hankali ta dinga goge hawayenta, ta shiga parlon ta kulle kofar ta wuce sama, gefen gado ta zauna ta kife kanta da pillow wasu hawaye masu zafi na zuba idonta, bata san da ta fashe da kuka ba bayan ta tuno maganar da yayi mata na Hadiyah, tafi minti goma a haka taji an danna bell din gidan, mikewa zaune tayi ta kalli wayarta da ke hannunta, dawowa kuma yayi cikin ruwan nan, sai a sannan ta tuna ta bar Handbag dinta a motarsa, ko jakar ya kawo mata, ta kalli agogon wayarta dake hannunta, sai kuma ta mike ta bude kofar dakinta a hankali ta sauko downstairs, sake danna bell din aka yi making it the 3rd time, ta karasa har bakin kofar ta bude a hankali, kiris ya rage numfashinta bai dauke ba bayan tayi ido hudu da wanda ke tsaye bakin kofar, bata gama recovering daga matsanancin shock din da ta shiga ba kawai taga ya shigo parlon yana kallonta, wani kara tayi duk da babu me jinta saboda ruwan da ake, ya tura kofar speaking calmly yace "Listen to me Khaleesat" Bata sake yarda ta hada ido da shi ba tsabar rudewa sai ta nufi kitchen maimakon ta gudu sama, shi dai ya bi ta da kallo yana tsaye inda yake, sai da ta shiga kitchen din taga babu makulli jikin kofar, hannunta na rawa ta shiga call log dinta tana neman number Ajay tayi dialing, don tasan tsayawa kiran Housemate dinta ma will be a waste of time, he might not even see the call balle yayi picking, jikinta na rawa ta dinga addu'an Ajay ya daga kiran, rikicewa tayi ganin sa a kitchen din ya biyo ta, ya karasa har gabanta ya amshe wayar hannunta yana kallonta ya kashe wayar gaba daya ya ajiye saman cabinet din kitchen din, cikin sanyin murya yace "Listen to me Khaleesat, i promise you I am not here to hurt you" Kuka kawai Khaleesat take ta rakube jikin bango har lkcn jikinta na Ι“ari tana kallonsa, he look so lean kamar ba Abdul din da ta sani ba, sai dogon hancinsa da haske da ya kara, daxu tana zaune department dinsu a schl taji exactly kamshin turaren da yake using wanda hakan sai da ya sa ta tsorata ta rasa nutsuwarta, does it mean bibiyanta yake ta yi kenan all this while? How did he even know her apartment? Ta shiga uku ta lalace, Muryarsa taji a hankali yace "Kiyi hakuri na shigo maki apartment without permission Khaleesat, i know it's not right, bani da courage din tare ki a hanya don ban san yanda zaki yi reacting ba cikin mutane, i have no choice shi yasa har kika gan ni a nan this late, kiyi hakuri don Allah" Sai a sannan Khaleesat ta samu kwarin gwiwan hade rai ganin how calm and soft he was speaking to her, cike da karfin hali tace "Pls i don't want to report you to the cops, ka fita ka bar min apartment dina tun wuri" A mugun tsorace ta dake take masa maganar, instead sai taga ya sauke idonsa, a hankali yace "Zan fita, amma kafin nan ina son kiyi hakuri ba don ni ba kar ki sanar ma bodyguards dinki i badged into ur house, plss kar ki gaya masu Khaleesat.... Ni ba tashin hankali bane ya kawo ni i promise you.... nasan you are soft Khaleesat, ke mace ce me raunin zuciya sannan ke me yafiya ce, i am not using ur good characters to blackmail you Khaleesat, i am just saying the fact about you, ki dubi girman Allah da soyayyar da kike yi ma ma'aiki ki yafe min sannan ki tsaya ki saurareni ko na minti biyar ne...." She was so shock ganin ya duka a gabanta ya sauke idanuwansa daga kallonta cikin muryarsa da baya fitowa sosai yace "Ki duba alkhairina gareki ki saurareni ba don halina ba Khaleesat, i am begging you to pls give me a listening ear, na maki alkawarin ba dadewa zan yi ba zan fita...." Khaleesat ta dauke idanuwanta daga kallonsa tana jin hawaye na zuba idonta, alkhairansa da yace ne kawai ke ringing a kanta amma duk da haka ta dake zuciyarta, cikin rawan murya tace "Ni dai don Allah ka rufa min asiri ka fita in kulle apartment dina bani da lokacin sauraron ka ko na minti daya wallahi, i am begging you plss ka fita" Kamar zai mata kuka yace "Baza ki saurareni ba kenan Khaleesat?" Muryarta na rawa tace "In saurareka akan me? Bani da lokacin sauraranka, ka tashi ka fita before it's too late" Cikin sanyin murya yace "To zan fita, amma kiyi hakuri kar ki gaya masu i am here, i came with a pure intention not otherwise, plss do not tell them i am here" Duk don ta samu ya fitar mata a gida tace "Na ji, ka tashi ka tafi" Mikewa yayi ya juya ya nufi kofar kitchen din ta bi sa da kallo hawaye masu zafi na zuba idonta, sai kuma ta bi bayansa da sauri don tabbatar da fitan zai yi ko akasin haka, yana sa takalmansa dake bakin kofar parlon, Khaleesat ta karasa window da sauri ganin haske a labulen parlon, tana dubawa taga motar Ajay yayi parking a garage, ta juya da sauri ta kalli Abdul, zuciyarta na bugawa tace "My call went through, kuma gashi ya xo..." Abdul ya bude labulen dai dai sanda Ajay ya fito daga motar, kallonta Abdul yayi and she could see the panic in his eyes, ita kanta jikinta rawa yake don ko kadan bata son ayi wani tashin hankali a gabanta, muryarta na rawa tace "Ni ban san ta inda zaka fita ba, just go upstairs before he comes in...." sama ya nufa, within a blink of an eye ta dena hangosa, ta karasa tsakar parlor da sauri zuciyarta na bugawa ta zauna hawaye na zuba idonta, dai dai sanda Ajay ya bude kofar parlon, tsaye yayi bakin kofar yana kallonta, ita dai taki yarda su hada ido da shi wasu hawayen na zuba idonta, ya karasa cikin parlon still looking at her yace "Why did you call my line?" Kin cewa komai tayi tana goge sabbin hawayen dake sauko mata, ya hade rai yace "Kee, baki ji na ne? Me yasa kika kirani?" Muryarta na rawa tace "Nima ban sani ba" Tana fadin haka ta fashe da kuka sosai tana kallonsa, ya cire takalmansa going closer to her yace "Ban gane baki sani ba, What happened?" Tana shesshekan kuka ta bude masa hannu alamar ita fa bata sani ba, bin parlon ya dinga yi da kallo, nan taji gabanta ya fara faduwa sosai, cikin rawan murya tace "May be i was just hallucinating...." Sai kuma ta rakube jikin kujera ta kwantar da kanta tana wani sabon kukan, shi dai kallonta kawai yake, can ya zauna kan kujera that is near to her yace "What did you see?" A hankali tace "Abubuwa da yawa" Ya dinga kallonta kafin yace "Abubuwa kamar me?" Ta bude masa hannu alamar bata sani ba, yace "Ina wayarki? And why did you switch off the phone after calling me?" Ta fara kalle kallen parlon a hankali tace "Nima ban sani ba ai" Yace "Ina kika ajiye wayar da kika kirani?" Hanyar kitchen ta kalla tayi shiru, ya kalli kitchen din sannan ya mike ta bi sa da kallo zuciyarta na tsananta bugawa har ya shiga kitchen din, sai gashi ya fito yana rike da wayarta dake a kashe, tuni ta lumshe ido da sauri don kar ma su hada ido yayi mata wani tambayar, ya karasa har gabanta, ita dai idonta na lumshe tana sauke ajiyar zuciya a hankali, dukawa yayi gabanta ya kai hannu forehead dinta to feel if she is running temperature, amma yaji temperature dinta is normal, kawai with the way she is breathing zaka gane a tsorace take, ta bude ido a hankali tana kallonsa, sai kuma murya can kasa tace "Bacci nake ji" Yace "Why won't you hallucinate, wani kika ba ma contract din ya dinga maki Azkar din ki?" Ta sauke idonta bata ce komai ba, mikewa yayi ya koma kan kujera ya zauna yana Ζ™are ma parlon kallo, a hankali ta mike ta kwanta saman dogon kujera ta takure waje daya tana jiran taga ya tashi ya tafi, shi dai Ajay bai ma san wani tunani zai yi ba, ta kirasa yana jin kukanta a background and before you know it kuma yaji an kashe wayar gaba daya, he tried reaching her but to no avail, tunani ya fara yi ko tana da jinnu ne, ya sake juyawa ya kalleta, ita dai idonta a lumshe yake, a haka bacci ya dauketa bata sani ba. Khaleesat bata yi minti sha biyar tana bacci a kan kujeran ba ta farka a gigice bayan tayi mafarkin Ajay ya ga Abdul a gidan ya kamasa yayi ta duka, kawai daga karshe ya harbesa da bindiga, rikicewa tayi bayan ta fado daga kan kujeran ta dinga nanata "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" jikinta na rawa, Sai bayan da ta tabbatar mafarki ne ta daga kai har lkcn jikinta na rawa tana kallon Ajay da ya durkusa gabanta yana tofa mata addu'o'i, jinginar da kanta tayi jikin kujera tana jin hawaye na zuba idonta, after almost 10 minutes, speaking calmly yace "Ta shi ki tafi sama kiyi alwala ki kwanta" Make masa kafada tayi tana shesshekan kuka tace "A'a ni tsoro nake ji, zan kwanta a nan" Tana fadin haka ta mike ta sake kwanciya kan kujeran, shi dai kallonta yake, tun da bacci ya dauketa yake tsaye jikin window din parlon yana son tafiya amma bai tafi ba, kuma har lokacin ruwa ake, and before he know it 15 minutes into her sleep ta farka cikin firgici, Khaleesat ta dade bata ji irin wannan tsoron dake zuciyarta ba, yanxu idan ya ga Abdul a gidan nan me zata ce? Ko dai kawai ta gaya masa gaskiya, to amma idan ta gaya masa kuma ya kamasa da duka har ya aiwatar da abinda ta gani a mafarki ba, Da tunane tunanen nan wani baccin ya sake awon gaba da ita bata sani ba, cikin baccin taji an rufa mata duvet, ta bude ido da sauri sai kuma ta mike zaune tana kallon duvet din da ya rufa mata don parlon yayi sanyi sosai, tana zaro ido bata san sanda tace "A ina ka dauko?" Yace "Ban sani ba" Tsoronta kar yaje ya shiga dakin da Abdul yake, ta koma ta kwanta a hankali tayi lamo, Ajay ya tafi ya ci gaba da tsayuwarsa a jikin window din parlon yana duba wayarsa ganin Jay ke kiransa ya maida wayar aljihu. Karfe daya da rabi Khaleesat ta kara farkawa a bacci, ta cire duvet din jikinta tana kallon Ajay dake zaune kan one sitter ya jingina kansa da kujeran idonsa a lumshe, amma tana mikewa zaune ya bude ido, ta fara sosa kai taki barin su hada ido tace "Fitsari zan je in yi" Bai ce mata komai ba, ta mike tsaye tana tafiya a hankali ta wuce sama, waige waige ta dinga yi kamar munafuka a corridor din dakunan sannan ta bude one of the 3 rooms dake sama, taga Abdul baya ciki, ta dai san baya dakinta tunda har Ajay ya shiga dakin ya dauko mata duvet, dakin dake kallon nata ta bude a hankali, ta gansa kwance kan carpet at the far end of the room yana bacci, ta shiga uku ta lalace, how did she find her self in to this mess, duk don saboda tausayi, a hankali ta jawo kofar ta kulle har da makulli sannan ta cire makullin ta tafi dakinta da shi ta ajiye a handbag dinta, bayan kusan minti 7 Khaleesat ta sauko downstairs rike da darduma da Hijab don alwala tayi bayan ta tuna bata yi sallan isha'i ba, shi dai Ajay bin ta da kallo yake, ta shimfida darduman ta sa Hijab din sannan ta tada sallan, bayan ta idar tayi sallan Nafila, ta dade zaune kan darduma, lkci lkci take satan kallon Ajay don idonsa biyu har sannan, ganin ta fara jin bacci ta mike a hankali ta koma kan kujera ta kwanta ta rufa da duvet, a nan ne bacci ya dauketa wanda bata sake farkawa ba sai safe, don har gari ya fara wayewa, ta mike zaune da sauri don yaushe rabonta da makara haka, kalle kallen parlon ta dinga yi ganin Ajay baya parlon ta mike tsaye ta nufi window tana leka garage taga babu motarsa, ta fi minti biyu tsaye jikin window din sai kuma ta juya ta wuce sama bayan ta dau dardumanta da hijab, tana idar da sallah ta fito da makullin dakin da Abdul yake ta bude kofar dakin tana tsaye daga bakin kofa ta hade rai tana kallon cikin daki, yana zaune kan carpet, alamar tun bayan da yayi sallah yake zaune a haka, hade rai tayi tace "Ka zo ka fita don Allah" Mikewa yayi ya nufo kofar ta matsa ta basa hanya fuskarta daure, yana kallonta yace "Good morning Khaleesat" Ƙin amsawa tayi waiting for him to go downstairs, cikin sanyin murya yace "Nagode da rufa min asiri da kika yi" Yana fadin haka ya nufi downstairs, ita dai ta bi sa da kallo, sai kuma ta bi bayansa to be sure he is leaving, ko da ta sauka downstairs taga har ya bude kofar apartment din, tana tsaye tana kallonsa har ya fita ya kullo mata kofar, ta karasa ta saka ma kofar makulli, ta jingina da kofar letting out a sigh of relief.....

 

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

 

 

 

We sell all kind of children school shoes, school bag, Lunch box, Readymade for children.... Atamfa, Lagos laces, veils, Handbags, shoes, lafaya, jewelries, kitchen items e.t.c.....

All at affordable prices

 

Akwai adashin kayan kitchen, kayan yara and atamfa with laces if interested....

 

 

 

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM

 

 

 

Wajen karfe tara Khaleesat ta sauko downstairs bayan tayi shirin tafiya makaranta, zaunawa tayi kan kujera ta jinginar da kanta jikin kujeran tana jin kanta na mata ciwo, banda suna da test da baza ma taje schl din ba don har a lkcn she was still stunned at what happen yesterday, gaba daya a dar dar take cikin gidan, ko appetite din yin breakfast bata da shi, ganin it's almost 10am ta ciro wayarta a jaka tayi ordering Uber da zai kai ta school din, bayan ya iso ta mike ta dau jakarta ta nufi kofa, tana isa school taga Safiyyah bata iso ba, kiranta ta fara yi a waya amma baya shiga, dab da za su fara test din sai ga Safiyyah, bayan sun fito Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Kawai daga na Ι—an sake ma yaro fuska uwarsa bata da lafiya shine ya kai ni ya baro Khaleesat" Khaleesat ta kalleta amma bata ce komai ba, Safiyyah ta gyara zama tace "Gaba daya ya lalata min jakunkuna da jambakin uwarsa, duk ya goggoga, daga in shiga wanka in fito, ai ko ni dai na dokesa in ma uban ya kullace ni shi ya jiyo, jakunkuna na masu shegun tsada sai kace uwarsa ce ta siya min" Khaleesat dai ta Ι—an yi murmushi kawai without saying anything, Safiyyah na kallonta da kyau tace "Me kuma ya faru na gan ki haka?" Khaleesat ta bude jakarta ta ciro zoben da Housemate ya bata ta mika mata, Safiyyah ta amshi box din ta bude, zaro ido tayi with awe tace "Oh my God, who got u this Khaleesat? diamond ne fa, don Allah wa ya baki, kamfanin Forevermark fa...." Ganin Khaleesat taki bata amsa Safiyyah ta hade rai tace "Don Allah ki min magana, where did u get this from?" A hankali Khaleesat tace "My Housemate gave me" Mikewa Safiyyah tayi baki bude tana zaro ido tace "Don't tell me he proposed to you?" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Ko ba propose ba, he just gave me as a gift Sophie" Safiyyah tayi wani Ζ™ara tace "Omg, wallahi proposing yayi maki amma saboda sense is far from you kinga ai baki gane ba, ya salam luxury brand ne fa Forevermark, to da ya baki me kika ce masa? Kuma ta yaya ya baki, kuna zaune ne ko kuna tsaye sanda ya baki?" Safiyyah ta koma ta zauna kusa da Khaleesat looking so excited tace "Don Allah how did u react da ya baki?" Khaleesat tace "Bai ma jira nayi masa godiya ba kawai ya wuce" Safiyyah tace "A apartment din ki ya baki?" Khaleesat tace "A'a, he took me out for dinner yesternight, bayan da muka dawo shi ne ya bani a mota" Safiyyah ta kyalkyale da wani shegen dariya tace "Yanxu fa sai kice har yanzu baki gane Housemate dinki is in love with you ba ko? Duk sai kice he is just being kind ko?" Khaleesat ta wani kalleta, Safiyyah na dariya tace "Ae ba abun mamaki bane kice baki gane yana sonki ba har yanxu, amma wallahi Housemate dinki na bala'i son ki kawata, don wannan care din is extra ordinary, ko kanwarsa da suka fito ciki daya bazai dinga yi mata irin wannan hidimar da yake maki ba, kai budurwar da saurayinta zai mata haka ma ba karamin musulmin sonta yake ba,  yan mata nawa ne yanxu ko Naira biyar baya hadasu da samarinsu kuma a haka wai aurensu za ayi, ke dai wallahi you are very lucky om earth, Allah ya kashe ya baki kawai, ni kuma zan baki shawara kar kiyi misusing privilege din nan, cause it's a privilege to you wallahi, bai duba wai kin taΙ“a aure ba kawai shi tsakani da Allah yake son ki a zuciyarsa, come to think of who he is, daga gidan sarauta fa ya fito, in zaki ajiye kunya ki nuna masa kema kina sonsa to zai dai fi maki, you are not a kid Khaleesat, kinsan sonki Jawwad yake, so me tsanani kuwa" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Kinsan me Sophie?" Safiyyah na kallonta tana washe baki tace "Ina jin ki" After some seconds Khaleesat tace "Abdul came to my apartment yesterday night" Mikewa Safiyyah tayi ba tare da tasan ta yi hakan ba a tsorace, tana kallon Khaleesat with shock all over her face tace "Waye kuma Abdul? Did you have another frnd that is Abdul by name da ban sani ba?" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta, cikin sanyin murya tace "Abdul dai guda da kika sani" Safiyyah tace "Na shiga uku na lalace, Abdul tsohon mijin ki wai kike nufi?" Khaleesat ta kasa ce mata komai, Safiyyah ta koma ta zauna tana kallonta da wani expression tace "Ta yaya yasan apartment din ki Khaleesat? Kuma me yaje yi maki a apartment? Don Allah ki min bayani yanda zan gane, i am lost...." Khaleesat ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Wallahi ban san ta yaya yasan apartment dina ba Sophie, ni kaina i am still shock up till now, ko breakfast na kasa yi saboda tsoro, yanda kika san an jefo sa" Safiyyah ta maida jakarta gefe tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ji min shege Ι—an iska, to wai uban me yaje maki a apartment din, tell me what happen da yaje, ke kuma da yaje kofa kika bude masa ya shigo?" Khaleesat tace "Bayan Housemate dina yayi dropping dina a gida ya tafi ana ruwa, after like 10 mins sai aka danna bell, to na mance jakana a motar Housemate i was thinking shi ne ya dawo ya kawo min jakar, da na sauka downstairs sai na bude kofa kawai, ashe Abdul ne" Safiyyah da tayi mitsi mitsi da ido tana sauraron Khaleesat tace "Go on, ina jin ki, sai aka yi yaya?" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "I was very shock and afraid bayan na bude kofan ya shigo, shi ne na shiga kitchen da gudu dama wayata na hannuna nayi dialing number Ya Junaid, sai gashi ya biyoni kitchen din ya karbe wayar" Buda baki Safiyyah tayi tana kallonta da firgici a fuskarta, cikin sanyin murya Khaleesat ta gaya mata duk abubuwan da Abdul yace mata a kitchen din bayan da ya sameta a ciki, da kuma yanda Ajay ya zo gidan duk bata boye mata komai ba.... Safiyyah na girgiza kai tace "Amma kin bani mamaki Khaleesat, yanxu shi Abdul har wani abun tausayi ne shi da zaki boyesa a apartment dinki? Abdul fa???" A hankali Khaleesat tace "Ce min fa yayi in tuna alkhairansa gare ni Sophie, kuma he look afraid also baya son Ajay ya gansa, shi ne yace in rufa masa asiri" A fusace Safiyyah tace "Wani shegen alkhairin yayi maki da zaki tuna? Harrassing dinki da ya dinga yi ko kuma gorin da yake lafta maki da walakanta ki da yake yi? Nan nan ranan kika bani labarin zaman ukuban da kika yi a gidansa kafin ya sake ki, da yanda ya bar ki da kwalin indomie ko albasa babu balle tarugu, marukan da ya dinga maki da zagin cin mutunci ne alkhairin da zaki tuna game da shi? Mutumin da ya ci mutuncinki ya sake ki bayan ya samu abinda yake so a wajenki har shi ne abun tausayi Khaleesat? Yanxu kina nufin kika boye Abdul har washegari a apartment din ki kika bar Ajay da gadin ku? Ikon Allah, Gaskiya baki taΙ“a bani tsoro irin yau ba Khaleesat, i fear who no fear you, me yake damun ki ne haka?" Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi tana kallon Safiyyah tace "Safiyyah kar ki manta this is America, we are not in Nigeria, Ya Junaid na lura temper dinsa a kusa yake, yana da zuciya sosai, what if yaje ya masa wani illa wajen dukansa don nasan definitely bazai kyalesa ba idan ya gansa a gidan, kina tunanin idan yayi masa wani abu za a kyalesa ne a kasar nan? dole doka zai yi aiki a kansa, kuma duk saboda ni sai haka ya faru Sophie??" Safiyyah ta wani kalleta tace "Sannu me hangen nesa, da duk baki san da hakan ba kika doka masa kira? Why did you call him at the first place idan ba don ya zo ya fitar maki da Abdul ba?" Hawaye ya cika idon Khaleesat tace "Ai a sannan ban san da wani Intention ya zo min gida ba, kinga if he just came to harm me wannan daban ne, amma he meant no harm he was even afraid, banda haka ai bazai rokeni kar in gaya masu ya zo gidan ba" Safiyyah tayi wani murmushi tace "Maa sha Allah, kinga shawara daya kawai Abdul ya koma Nigeria ya bada sabon sadaki a kara daura maku aure kije can ku karata, tunda yanxu kam ya tuba kuma har kin yarda da tubansa kina mugun tausayinsa a rai, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a masu yawa" Khaleesat ta hade rai tace "Come off it Safiyyah, ni nace maki i am ready to accept his repentance? Ko sake daura min aure aka yi da shi ba sai dai a kai gawata gidan ba, how will I forget what i went through so soon Safiyyah, wallahi kawai kalman alkhairi da ya furta ne da kuma irin sigar da naga ya zo min yasa na rufa masa asiri, ni ba butulu bace bazan ce Abdul bai min abubuwan Alkhairi ba a rayuwata, in ba don shi ba yaushe har ma zan zo kasar nan in hadu da su Housemate dina? I lacked nothing tun da Abdul ya kawo ni kasar nan karatu, don har nafi wasu da iyayen nasu ke daukar nauyinsu, kinga bazan ce Abdul bai min wani abun alkhairi ba, kuma bazan taΙ“a iya biyansa abinda yayi min ba, ki fahimce ni plss Sophie, ba wai nace ya kamata in sake kulasa bane, don wallahi ko ganinsa bana son yi don hakan na fama min ciwon dake zuciyata..." Safiyyah ta tabe baki tace "Tun da kin rufa masa asiri kin ga yau ma nasan yana can bakin apartment din naki yana jiran ki, hauka ake zan rufa ma Abdul asiri idan ni ne a shoe din ki? Abdul fa? Ai ko duk alkhairan duniya yayi min wallahi bazan rufa masa asiri ba sai dai Allah ya yafe min kawai, Monster in form of human ne fa Abdul, gaskiya kin ci amanar Junaid, kin cuce sa, kuma da ya kuskura yasan abinda kike boyewa a gidan nasan ko ciki daya ku ka fito da shi bazai sake barin wata alaΖ™a ta hada ku ba har abada, kuma bazai taΙ“a yafe maki ba, in kina tsoron kar Ajay ya masa illa me ya hanaki kiran 911?" Khaleesat dai tayi shiru tana bin inda suke zaune da ido, Kawai ganinsa suka yi a gabansu, ta rike numfashi tsabar yanda tayi shock tana kallonsa babu ko kiftawa, Safiyyah da ita ma ta gwalo ido tana kallonsa da mugun mamaki ta mike tana huci tace "Kai bawan Allah lafiya muna zaune zaka tsaya mana a kai, ko dai batan hanya kayi ne?" Sau daya ya kalli Safiyyah sannan ya mika ma Khaleesat wayoyin dake hannunsa guda biyu yana kallonta, daya na Jay daya na Ajay, Khaleesat ta wani hade rai tace "Abdul kaga bana son muyi creating scene a nan, kindly stay away from me, are you even okay? Meye zaka dinga bibiyata?" Safiyyah ta figi jakarta tana kokarin ciro wayarta tace "Idan ban kira maka 911 ba Allah ya tsine min albarka...." Tana ciro wayar ya fixge daga hannunta yana kallonta da kyau yace "Wajen ki na zo da zaki kira min 911 Malama?" Safiyyah ta kundumo wani zagi tana kallon Khaleesat tace "Kin dai ga crook din da kika ji tausayi har kika boye a apartment din ki kar Ajay ya gansa ya jibgesa ko, kin taΙ“a ganin inda shedan ya tuba dama? Shey u can see the useless monster you are pitying har da boyesa kar a dokesa?" Abdul na mata wani kallo yace "Hey watch your tongue, idan ba haka ba i will teach you a bitter lesson Billah, Ajay kika kirasa ko? To ya zo ya dokeni tunda ni statue ne, ina ga shi ko gidan dambe bai taΙ“a zuwa ba, ki je ki tambayi wanene ni a Lagos..." Khaleesat ta maida box din zobenta cikin jaka sannan ta mike ta amshe wayar Safiyyah dake hannunsa, ta dau jakar Safiyyah da nata ta fara janta su bar wajen, banda zagi babu abinda Safiyyah ke kunduma ma Abdul idonta rufe tana cewa "Munafuki kawai algungumi, wato saboda ka san tana da tausayi shi ne ka dawo sumui sumui da kai kamar na Allah zaka kara yaudaranta ka cuceta, har kana cewa ta rufa maka asiri, to kuwa sai na tona asirin nan naka wallahi, shegen duka za ayi maka da zai sumar da kai, in ka farfado ka siya ticket ko koma gida kayi jinya, tsabar baka samu daman ci gaba da musguna ma kawata ba har da rama sai da kayi kamar me ciwon Aids, to wallahi in baka fita harkar Khaleesat ba sai nayi maka abinda har ka koma ga Allah bazaka manta ba, mugu azzalumi kawai" Gaba daya attention din mutane ya dawo kansu a wajen, Abdul yayi wani murmushi yace "Sai kinyi regretting duk kalaman nan naki wallahi, sai na sa an lalata maki rayuwa i promise you this...." Khaleesat dai ta samu ta ja Safiyyah suka bar wajen gaba daya, banda rawa babu abinda jikinta yake yi don tsoro, Safiyyah ta warce hannunta tana kallonta a fusace tace "Kin dai ga Ι—an iskan da kike tausayi ko? ashe da sabon salo kawai ya dawo don ya samu attention din ki, ke kuma ga sarkin masu tausayi, to kuwa rabon a karyasa yasa ya dawo Amurka don wallahi Ajay karyasa kawai zai yi" Khaleesat ta zauna ta rufe fuskarta da hannunta tana kuka a hankali, gaba daya ta gama tsorata, ta ma rasa wani irin tunani zata yi, zaman apartment din nata ita kadai ya fara bata tsoro kuma, can ta kalli Safiyyah dake ta bambami cikin rawan murya tace "Sophie ko dai in ma Ya Musty magana da kaina ki dawo apartment dina da zama tunda exams za mu fara? Wallahi bazan iya zama ni kadai ba kuma a gidan nan Sophie, i am afraid..." A fusace Safiyya tace "Ai baki zama afraid ba tunda har kika iya boye kasungumin Ι—an daba a gidanki ya kwana, Abdul har abun yarda ne bayan duk mun san Ι—an iska ne shi? Wani dadin baki zai maki har ki yarda da shi? Kin dai ga abinda yayi min ai yanxu, dama kuma me hali baya taΙ“a fasa halinsa" A hankali Khaleesat tace "To ko dai in yi ma Ajay bayanin abinda ya faru jiya kar ya zo ya gano yaji haushina? Wallahi i am so confuse Sophie" Safiyyah tace "To nima naji haushin ki balle Ajay da yayi gadin ke da Abdul ku ka sharbi baccin ku? ai wallahi kin cuce Ajay kuma sai Allah yayi masa sakayya" Khaleesat ta goge hawayen gefen idonta tace "To amma sai dai inje can gidan nasu in masa magana ko? Don kar yaje yayi misinterpreting dina ta waya idan na kirasa, i want to explain to him ta yanda zai gane" Safiyyah tace "Dama ai gwara ki samesa face to face kiyi masa bayani, sannan kar ki kuskura ki ce masa a gidan Abdul ya kwana don daga nan zai fatattake ki ya kora ki, ko ya hadaki da karensa ya kora ki, inda Ajay ke burgeni kenan wallahi, no nonsense Man kike ji, sam baya daukan wargi, tsayayyen namiji kenan, kawai ce masa zaki yi kin shiga kitchen zaki zuba abinci sai kika ga kamar Abdul a jikin window din kitchen dinki yana kallonki, shi ne duk kika rude kika kirasa jiya da daddare, daga baya kuma kika ga wajen wayam ba kowa, amma da ya zo sai baki gaya masa hakan ba tunda baki tabbatar ba kin zata hallucination kawai ki ke yi don dama kanki na ciwo jiyan, sai ki ce masa yau kina department muna zaune ni da ke kawai sai ga katon a gabanmu, ashe jiya shi din dai kika gani a jikin window, kinga ai maganata tayi making sense akan ki ce masa ai boyesa kika yi a daki jiya...." A hankali Khaleesat tace "To bari inyi order din Uber zuwa gidan" Safiyyah tace "Sannan idan kin je gidan ki fara masa godiyan gadin ki da yayi jiya ya hana kansa bacci, don nasan ba hankali gare ki ba kina iya zuwa ki fara maganar da ya kai ki kanki tsaye...." Khaleesat ta ciro wayarta za tayi order din Uber da zai kai ta gidansu Ajay, kafin tayi order din ta kalli Safiyyah tace "Ko zaki rakani mu je mu biyu?" Safiyyah ta rike haΙ“a tace "Wa?? Ni? Salon inje ya koro ni mutumin da ba kirki ne da shi ba, a'a wallahi bazan je ba, ko kadan bai taΙ“a burgeni ba dama ni, tun farko tamu bai zo daya da shi ba don na tsani mutum fitinanne, da dai Housemate ne sai in bi ki mu je, kuma banda ma yafi Housemate zafi me zai sa ma a sako sa cikin wannan case din, to tsorona muna iya sako Housemate yaje ya fara ba Abdul din hakuri kinga ai lamari ya lalace kenan, babu dai yanda muka iya Ajayn zaki je ki sama duk da mugun halinsa, ayi mutum ace bai son mutane kullum yayi ta daure fuska yana fushi shi kadai" Khaleesat na kallon Safiyyah cikin sanyin murya tace "Ko dai kawai in gaya ma Housemate in kyale Ya Junaid din?" Safiyyah ta wani hade rai tace "Wani Housemate, hakuri kike son ya tafi ya ba Abdul din kenan yanda zai ji dadin ci gaba da iskancinsa, ai karki kuskura ki gaya ma Housemate he won't help matters at all, gwara Ajay no nonsense, tsaf zai mana maganin Abdul, amma Housemate ai har durkusawa sai ya iya yi ya ba Abdul din hakuri yanda suka yi ma Aymaan shi da Ya Musty, Ajay ai shi ne namiji" Khaleesat dai bata ce mata komai ba tayi order din ride din, Safiyyah ta zaro ido tana kallon hannun Khaleesat tace "Ina zoben naki? Mun shiga uku ko dai Abdul din ya kwace?" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Ga fa shi nan a jaka" Safiyya tace "Atoh, don ni yanda na gansa wujiga wujiga anya karayar arziki bai fada masu ba kuwa, kamar wanda yake yunwa duk ya rame sai idanuwa da hanci, da kyar idan ba talauci a tattare da shi" Khaleesat dai bata tanka Safiyyah ba, Safiyyah tace "To ki saka zoben mana, ko jere zaki yi da shi a gaban madubi?" Khaleesat ta bude ido sosai tace "Ina zan je da zan saka zobe Sophie?" Safiyyah tace "Ke dai kin ki wayewa a rayuwarki Khaleesat, ba don gayu ya siya maki ba dama?" Warce jakar tayi ta ciro box din zoben tace "Dalla ki saka" Khaleesat tayi murmushi ta amshi zoben ta saka tana kallonsa admiringly, cif ya zauna mata ta kalli Safiyyah dake ta murmushi ita ma kamar bakinta zai yage tace "It's sooo cute, gaskiya Housemate is so romantic, har na hango kun yi aure, wallahi kashe ki zai yi kawai da soyayya, in soyayya ne a bar ma Housemate kawai, in kuma kwato hakki ne a bar ma Ajay" Dariya sosai ta ba Khaleesat, kawai ta mike bayan ta maida wayarta da empty box din zoben cikin jaka, Safiyyah ta rakata har zuwa inda Lyft dinta ke jira, ta bude motar ta shiga, hannu ta daga ma Safiyyah dake ta murmushi tana kallon zoben yatsanta dake ta kyalli, a haka Lyft din ya bar wajen, tun da suka kama hanya Khaleesat ke ta waige waige to be sure babu motar dake bin su a baya, don ita kam yanxu duk a tsorace take, tunda har Abdul ya iya gano apartment dinta to babu kuma abinda bazai iya yi ba, har dai suka isa bata ga alamar ko wani mota dake biye da su a baya ba, ta sauka daga lyft din tana tafiya a hankali ta shiga compound din, it's almost 4pm na yamma, motar Ajay ta fara gani a parking space din gidan, sannan ta ga motar Jay ma alamar duk suna gidan, walking slowly ta karasa har entrance din parlon dai dai sanda aka bude kofar parlon, ta Ι—an koma baya tana kallon Housemate dinta dake kallonta da mamaki, cikin dubara ta boye zoben finger dinta da veil dinta kar ya gani, tana kirkiran murmushi a hankali tace "Good evening" Yace "Evening Housemate, come in" Ta sauke kanta kasa ta bi bayansa har zuwa cikin parlon, ta zauna kan kujera shi ma ya zauna yana kallonta hoping all is well don sai yaji gaba daya hankalinsa ya tashi ganinta a gidansu, jin tayi shiru yana kallonta yace "Hope all is well Housemate?" Tana murmushi tace "Alhamdulillah, babu komai, Ya Junaid yana nan? I came to greet him" Jay yayi shiru yana kallonta, after some seconds yace "Yeah, he is upstairs" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Ohk, i want to meet him" Jay ya gyada mata kai yace "He is at the parlor upstairs, ki samesa a can" A hankali tace "Sai na je sama?" Jay ya mike yace "He is there, ni zan fita yanxu...." Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, ya Ι—an yi murmushi ya nufi kofar fita parlon ta bi sa da kallo har ya fita, bayan fitarsa da kusan minti goma Khaleesat ta mike, walking slowly ta tafi sama, tsaye tayi Ι—an nesa da parlon dake sama tana kallon Ajay dake kallon kwallo a Tv, ga grapes a gefensa yana sha, ko lura da ita bai yi ba, he was so engrossed in the football match he was watching.....

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

 

 

 

https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM

 

 

Khaleesat ta sauke idonta daga kallonsa ganin for almost 2 minute bai lura da ita ba kallon ball kawai yake da duk attention dinsa, ta Ι—an yi kasa da murya tayi masa sallama, juyawa yayi da sauri suna hada ido ya gyara zamansa don kishingide yake saman kujeran, nan da nan yayi keeping straight face ya ci gaba da shan grape dinsa idonsa a kan TV, tana tafiya a hankali ta karaso cikin parlon ta tsaya jikin kujera trying to gather up courage tace "Good evening..." Ya Ι—an kalleta, sai kuma yace "Yes?" Ta Ι—an langwabar da kai tana kara rungume handbag dinta tace "Ina son zan maka magana ne pls" a takaice yace "I am busy as you can see...." Ta kalli football din da yake kallo, a hankali tace "To shikenan, sai anjima" Tana fadin haka ta juya zata bar parlon yace "Ke.... awa daya zaki yi using kiyi min maganar ne, say what u want to say in few seconds i am listening" Tayi shiru tana kallonsa, after few seconds ta zagayo ta zauna kan 1 sitter tana kallonsa, har a sannan kusan duk hankalinsa na kan TV din kamar baya son missing kwallon da yake kallo, bayan kusan minti biyar ya juya ya kalleta, shi har ya mance tana wajen, yace "Kee fadi abinda ya kawo ki and stop staring at me that way" Tace "To ai naga kallo kake" Yace "Ido ke ji ko kunne? Ina ruwanki da kallon da nake yi?" Ɗan taΙ“e baki tayi, ita shi yasa bata ma son abu yana hadata da shi, komai sai yayi masifa, ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Dama Abdul ne ya biyoni school yau..." Lokaci daya ya juya ya kalleta, ta sunkuyar da kai, can yace "Waye Abdul?" Ta Ι—an kallesa taga kallonta yake, tayi karfin halin cewa "My ex" Shiru ya sake yi, after some seconds yace "In zaki min bayani in details ki bude baki kiyi min and stop wasting my time" Ta Ι—an saita kanta ta yanda zata fara koro masa duk abinda Safiyyah tace ta gaya masa, tayi inhaling numfashi sannan ta fara masa bayanin exactly yanda Safiyyah tace tayi, ya rage volume din TV, yana sauraronta attentively amma ba kallonta yake ba, har ta kai aya tana kallonsa, bai ce komai ba for almost a minute as if yana processing duk bayanin nata a kansa, still not looking at her yace "So now what did you want me to do?" Shiru Khaleesat tayi don bata san me zata ce ba, can taji yace "Saki nawa yayi maki?" Ta sauke idonta a hankali tace "Kawai ce min yayi ya sakeni, bayan da na dawo gida kuma aka aiko takarda daga gidansu da saki uku a jiki, amma ba rubutunsa bane" Ajay ya wani kalleta yace "Rubutun ki ne kenan?" Sunkuyar da kanta tayi, ya sauke idonsa kan zoben hannunta dake kyalli, ta Ι—an saci kallonsa taga he is still looking at her, dauke kansa yayi bai sake cewa komai ba na Ι—an lokaci, sai kuma taji yace "So what did you want me to do now da kika zo kika gaya min?" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kallesa, lkci daya jikinta yayi sanyi, yace "Ko nan gidan kike son ince ki dawo?" Ta girgiza masa kai tace "A'a, i will cope in sha Allah, kawai na gaya maka ne" Sai kuma ta mike a hankali tace "Nagode, i am going back home" Ya watsa mata wani kallo yace "Are you okay? Ina maki magana zaki mike tsaye? Ni nace ki tashi?" Ta sunkuyar da kanta sai kuma ta koma ta zauna, nan da nan taji hawaye ya cika idonta, da ta sani kawai da Housemate dinta ta gaya ma duk da Safiyyah tace kar ta gaya masa, Ajay ya dau grape dinsa yana ci yace "Shi Guardian din naki me ya hanaki gaya masa sai ni? Baki fi kusa da shi ba a kaina zaki tsallakesa ki zo ki sameni? Am i ur Bodyguard?" Jin tayi shiru ya juya ya kalleta, hawaye ya gani a idonta, ta kai hannunta tana goge hawayen, bai sake cewa komai ba idonsa a kan grape din gabansa, after almost 30 seconds ya kalleta yace "Ya ma kike da suna, Yaushe zaku fara exams?" Bata dago kanta ba cikin sanyin murya tace "In less than a month time" Yace "Amma kinga silly frnd din nan taki wataran sai ta jefa kanta masifar da bazata iya fita ba, har ke sai ta jefa cikin matsala, shi tout din ta tsaya take exchanging words da saboda rashin kamun kai...." Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Ajay bai sake cewa komai ba a parlon yana nazarin how to tackle the issue, shi ya dade bai ga Ι—an iska kamar Abdul ba, amma zai yi maganinsa, shafa kansa yayi still thinking of where to start from, a yanxu dai baza su fara cewa ta zauna a gidan nasu ba don Mai martaba went on a trip to Toronto, kwanansa hudu kenan a can kuma basu san ko zai biyo ta Amurka ba, infact zai ma biyo don in dai ya taho overseas komin nisan inda yaje da Amurka dole sai ya zo Maryland in har suna kasar to check on them, so they won't take the risk of accommodating her in the house, assuming the semester isn't late da kawai sun mata applying for On-campus residence halls a cikin makarantar ta zauna, Ajay ya daga kai yana kallon Cousin brother dinsa Mukhtar that was coming towards the parlor, Mukhtar yayi kasa da murya yace "Tare mu ke da Mai martaba...." Ajay bai san sanda ya mike tsaye ba dai dai sanda yayi ido hudu da Abbansa dake biye da Mukhtar a baya, Ζ™amewa yayi a inda yake tsaye with surprise, what a bad coincidences this is, Mai martaba ya shigo parlon with a broad smile on his face yayi kamar ma bai ga Khaleesat ba, Ajay ya sauke kansa kamar wanda ruwa ya cinye a wajen, at first ya ma rasa abun cewa, can kuma yayi karfin halin cewa "Barka da zuwa ranka shi dade....." Khaleesat ta daga kai tana kallon Mai martaba sai kuma ta sunkuyar da kanta ta zamo kasan carpet ta gaishesa cikin sanyin murya, sai a sannan mai martaba ya kalleta still smiling ya amsa gaisuwarta, Mukhtar yayi offering masa kujera ganin bai zauna ba, Mai martaba yace "I am fine Mukhtar..." Sai kuma ya kalli Ajay da ya kasa kallonsa har sannan yace "Ina Jawwad?" A hankali Ajay yace "I think he went out just now..." Mai martaba yace "Ohk" Mikewa Khaleesat tayi da niyyar barin parlon, Mai martaba ya kalleta yace "No yi zamanki yarinya, ya sunanki?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta koma ta zauna a hankali tace "Sunana Jiddah" Yayi nodding kai yace "Maa sha Allah, ke er Nijar ce?" Khaleesat ta Ι—an yi murmushi tana wasa da gyalenta tace "A'a, er Nigeria ce" Mai martaba yace "That's good, Nigeria wani state?" Tace "Kano" Ajay dai yaki daga kansa yana jin zufa na karyo masa a forehead, can kawai ya juya ya bar parlon yana tafiya a hankali, Mai martaba ya zauna saman kujera still looking at Khaleesat yace "Karatu kike a kasar nan Jiddah?" Khaleesat tace "Eh karatu nake" Yace "That's good, wace makarantar?" A hankali Khaleesat tace "John Hopkins university..." Mai martaba na jinjina kai yace "Maa sha Allah, kano a wani unguwa iyayenki suke?" Khaleesat tace "Muna mariri ne" Shi dai Mukhtar na ta tsaye a parlon yana mamakin yanda Mai martaba ya tsaya ya bada lokaci yana conversing da Khaleesat bringing her down to his level, Ita kanta Khaleesat bata yi tunanin sarki bane shi duk zaton ta ko dai brother din babansu ne shi din, Mai martaba yace "Maa sha Allah Jiddah, Allah ya bada sa'an karatu" Tace "Ameen Abba Nagode" Mikewa tayi zata bar parlon ya kalli Mukhtar yace "A bata dala dubu biyar Mukhtar" Mukhtar ya Ι—an risina kai da ladabi yace "To ranka shi dade" Khaleesat na kallon Mai martaba a hankali tace "Abba Nagode, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara girma" Daga mata hannu kawai yayi with smile, sannan ta mike ta bi bayan Mukhtar, tun basu fita parlon ba sai ga Jay ya shigo, kasa karasowa yayi bayan yayi ido hudu da Khaleesat ga Mai martaba zaune a parlon, can ya kalli Mukhtar da ya daga masa hannu alamar gaisuwa, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam ya sunkuyar da kai walking slowly, a hankali tace "Sai anjima" Murmushin karfin hali kawai yayi mata without saying anything, ta bi bayan Mukhtar suka bar parlon, Jay ya karasa har cikin parlon ya zauna kasan carpet yana gaida Mai martaba da ladabi, Mai martaba ya amsa yace "Ina Ahmad din?" Jay ya mike ya bar parlon zai kira Ajay, ba a dau lokaci ba suka dawo tare, shi dai Ajay ya kasa hada ido da mahaifin nasa, ya zauna kan carpet gefen Jay, sae kuma yayi karfin halin cewa "Ya hanya ranka shi dade?" Cikin nutsuwa Mai martaba yace "Alhamdulillah...." Daga haka mai martaba bai sake cewa komai ba, Jay da Ajay ma duk suka yi shiru kamar masu jiran hukunci a gabansa, after a while Mai martaba ya kalli Ajay yace "Ita ce yarinyar da za aje gidansu kenan..." Ajay ya Ι—aga kai yana kallon Abban nasa, can ya Ι—an sosa kai yana murmushin karfin hali yace "Abba ai budurwar Jawwad ce, wajensa ta zo ba wajena ba" Mai martaba ya kalli Jay da bai dago kai ba, Can Abba yace "Budurwar Jawwad kuma na gan ku zaune tare a parlor" Ajay ya gyara zama yace "Ranka shi dade abinda na fada gaskiya ne, ba wajena ta zo ba wajensa ta zo" Mai martaba ya kalli Jay, cikin nutsuwa yace "Jawwad" Jay ya dago kai amma ya kasa hada ido da mai martaba, jin mai martaba yayi shiru yasan bayani yake jiran ji daga garesa, hakan yasa ya fara magana with calm yace "Gaskiya ya fada Abba, haka ne..." Mai martaba yayi shiru na kusan minti daya kafin yace "Ita Hadiyar fa?" Jay ya kasa cewa komai, Mai martaba sam bai yarda da abinda suka ce masa ba don gani yake kamar Jay is covering for Ajay, after some minutes cikin hikima Mai martaba yace "Ko hakan yasa kake ta jan maganar Hadiyah?" Jay ya gyada masa kai still not looking at him, Mai martaba ya numfasa speaking with calmness yace "So ta yaya zan yarda da ku yanxu? Don na fara kokonton ka yanxu Jawwad, a da dai baka min karya amma yanxu ka fara" Jay yayi karfin halin cewa "Allah ya taimake ka, believe me ba karya nayi maka ba" Mai martaba yace "Ai shi ne nake tambayarka ta yaya zan yarda da hakan? Yanxu nema maka auren yarinyar zan sa ayi idan na koma Nigeria so i can clear away my doubt?" Jay ya daga idanuwansa ya kallesa, a hankali yace "Da zan yi farin ciki da hakan ranka shi dade"  Mai martaba yace "To batun Hadiyah fa?" Jay ya rasa abinda zai ce, after few seconds yace "I will be glad idan aka amince min na janye daga batun auren Hadiyah" Mai martaba ya Ι—an yi murmushi yace "Ai bazan maka dole ba Jawwad, ya rage naka kayi ma iyayenka mata bayani su bar maganar Hadiyah tunda kana da yarinyar da kake so da aure, don waΖ™a a bakin me ita tafi dadi, in kuma kaga zaka hadasu su biyun it's fine, as far as zaka yi adalci... By so doing iyayenka mata baza su dau lamarin da zafi ba tunda duk sun saka ran auren ka da Hadiyah" A hankali Jay yace "But i am afraid za su yi shunning batun idan na kai masu ranka shi dade" Mai martaba yace "Not when i am alive Jawwad, duk abinda kake so shi zan maka in sha Allah" A hankali Jay yace "Allah ya kara girma ranka shi dade...." Mai martaba ya kalli Ajay yace "Kai kuma ina sauraron ka har yanzu" Mikewa Mai martaba yayi ya bar parlon, bayan tafiyarsa suna ta zaune kamar wa enda aka yi planting a wajen sai dai ko wannensu akwai abinda yake tunani a ransa, Ajay ya Ι—an kalli Jay sai kuma yayi breaking silence din yace "Allah ya sanya alkhairi me mata biyu" Jay ya wani kallesa, Mikewa Ajay yayi zai bar wajen Jay ya sa masa kafa sai gashi timmm ya fada kan kujera, juyowa yayi ya hade rai yana kallon Jay da ya fara dariya, yaushe rabon su zauna waje daya a gidan, har magana ma sama sama suke yi... Jay ya dakata da dariyan da yake, sai kuma yayi kasa da murya yace "So what did you think about all this?" Ajay yace "About what?" Jay ya juya ya kallesa bai ce komai ba, Ajay yace "Getting married to ur Ward?" Jay dai kallonsa kawai yake, Ajay ya Ι—an yi murmushi yace "All this while ka zata wataran zan so ta ne da kake creating attitude a gidan nan? Saboda me ma zan so ta? Dama shi son haka yake very cheap? Ai ba class dita bace yarinyar nan, i like nothing about her most especially her silly cry, duk abinda nake mata saboda kai nake mata, if not because you bazan taΙ“a saninta from anywhere ba, ba ma abinda zai sa nayi crossing path da ita, so chill bruh.... Just that har na fara hango maka challenges din da zaka yi facing a wannan familyn naka, considering the fact that ta taΙ“a aure, sannan she is a nobody, familynka kuwa basa son someone that is a nobody not to talk of bazawara, kaga you have to tighten up ur belt kayi facing all the up and downs that will approach you.... Wishing you the very best of luck" Yana kai wa nan ya mike ya nufi dakinsa, Jay dai ya bi sa da kallo, sai kuma Ajay ya tsaya sannan ya juya yace "In addition, tsohon mijinta na bibiyanta yanxu haka, that was why she was here earlier on" Daga haka Ajay yayi tafiyarsa Bedroom dinsa ya bar Jay da ya mike tsaye jin abinda Ajay yace. Ajay na shiga dakinsa ya tafi jikin window ya tsaya yana kallon Neighborhood dinsu, everywhere was so silent and calm as usual, sai kuma ya sauke idonsa ya juya ya tafi ya dau wayarsa ya koma jikin windon ya tsaya, number Khaleesat yayi dialing, yana fara ringing tayi picking, yace "Where are you?" Khaleesat dake cikin Lyft tace "Ina cikin mota" Yace "Za ki ina?" Kallon wayarta tayi jin shigowar kira taga Jay ne ke kiranta, ta maida wayar kunne a hankali tace "Gidansu Safiyyah zan je" Yace "Ohk, remain there idan kin je, do not go back to ur apartment...." Yana kai wa nan ya katse wayarsa, Khaleesat tayi picking call din Jay don bai katse ba har sannan yace "Kina ina Halysaah?" Tace "Ina hanya" Yace "Kar ki koma apartment din ki, wait for me somewhere, i will be on my way now" A hankali tace "Dama gidansu Safiyyah zan je" Yace "Ohk to ki je, zan same ki a can" Tace "To Nagode" Katse wayar tayi ta mayar cikin jakanta, wai yau ita ce zata kai kanta gidansu Safiyyah yau saboda rashin choice, to ya zata yi, ko zaginta Surayyah tayi ai sai dai kawai ta bata hakuri in dai zata barta ta zauna a gidan, a haka ta isa gidan, bayan ta sauka Lyft ta nufi kofar apartment din ta danna bell......

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

 

07087865788

 

 

 

πŸ—£️ HADJIBS DATA SERVICES

 

Barkan ku da zuwa HADJIBS DATA SERVICES

Wannan wuri ne da muke:

 

πŸ“Œ Siyar da data (MTN, Airtel, Glo, 9mobile)

πŸ“Œ Siyar da airtime cikin sauki (VTU)

πŸ“Œ Biya kudin DSTV, GoTV, Startimes

πŸ“Œ Biya wutar lantarki (NEPA/PHCN)

πŸ“Œ Siyar da WAEC Scratch Cards

πŸ“Œ Reseller Wallet System zaka iya siyarwa da riba

πŸ“Œ Dama ga masu so su fara sana'a a wayarsu

 

Kawai zaku bude account dinku ku fara sana'ar ku cikin sauki.

 

πŸ–±️ Shiga: https://hadjibsdata.com.ng

 

πŸ“² App Ι—in mu yana nan a Play Store da App Store.

 

Idan kana da tambaya ko bukatar taimako, tuntubi admin kai tsaye, 07017133099.

 

 

Safiyyah na bude kofa ta washe baki tana kallon Khaleesat tace "Wallahi na zata wasa kike da kika ce kina hanya, shigo ciki mana" Khaleesat ta Ι—an yi murmushi ta shiga parlon, Safiyyah ta ja ta zuwa Bedroom dinta tace "Ni kadai ce a gidan, ko ina suka tafi oho, ni sai nake ga kamar fa ciki Surayyah tayi, in ko haka ne zan kama kaina in dena biyeta a gidan nan kar taje ta haifi kyakkyawa kamar ni..." Khaleesat ta cire veil din jikinta tace "Sallah zan yi" Safiyyah tace "Kin ci abinci a can kuwa?" Khaleesat tace "Abinci kuma?" Safiyyah tace "Ko da yake waye zai baki gida duk maza, bari inje in dafa maki noodles kafin ki idar da sallahn" Mikewa Khaleesat tayi ta shiga bandaki, Safiyyah kuma ta fita zuwa kitchen, bayan Khaleesat ta idar da sallah Safiyyah ta shigo dakin da indomie da kwai da ta dafa mata ta ajiye, Khaleesat ta kalleta tace "Thank you" Safiyyah tace "Naga duk kinyi wani sanyi, ko dai koran ki Ajayn yayi?" Khaleesat tayi er dariya tace "Saura kadan dai ya kore ni" Safiyyah ta kankance ido tace "Fitinanne, to sai aka yi yaya? Did u meet Housemate in the House?" Khaleesat tace "Eh na gansa" Sai kuma ta jawo handbag dinta ta bude ta ciro kudin da Mai martaba ya bata, Safiyya tace "Wa ya baki wannan kuma?" Khaleesat tace "I think their uncle, ya zo ya same mu a gidan ne, shi ne ya bani da zan tafi" Safiyyah ta Ι—an bude ido tace "Ko dai babansu?" Khaleesat tace "Babansu kuma? babansu fa Sarki ne, a'a ba babansu bane" Safiyyah ta amshi kudin tana kirgawa tace "Atoh, dama sai dai ko uncle din nasu, amma ina sarki yaga lokacin tsayawa dake har ya baki kudi, da sarki ne ai kya gansa da guards dinsa kuma yaushe ma zai tsaya maki magana, dogarawansa ma baza su bari ba, amma fa ke Hajiya ce kinsan nawa kudin nan in an canza a Naira?" Khaleesat tayi murmushi ta fara cin indomie din gabanta, Safiyyah tace "Wallahi kudade ne masu yawa, har karamin gida sai ya iya siya maki a maririn ku, yanxu ya ku ka yi da Ajay din bayan kin gaya masa abinda ya faru?" Khaleesat tace "Ai bamu gama magana ba Uncle din nasu ya zo, but after i left the house ya kirani yace kar in koma apartment dina, Housemate dina ma ya kirani...." Safiyyah ta hade rai tace "Ba nace kar ki sako Housemate a ciki ba? Shi fa Abdul namiji fitananne ne kawai zai iya dealing da shi, shi kuma Housemate dinki ba mutum bane me son hayaniya" Khaleesat tace "Kilan Ajay din ne ya gaya masa...." Safiyyah ta mike jin ana danna bell tace "Kilan sun dawo daga gantalin da suka je" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba Safiyyah ta mike ta fita daga dakin, ba a dau lokaci ba ta dawo tace "Ban ga kowa a bakin kofar ba kuma, ko dai kunne na ne yaji kamar an danna bell?" Khaleesat ta ajiye fork din hannunta tace "Kuma kin bude kofar?" Safiyyah tace "Haba dai sai kace ni ce ke, ta peephole na duba mana" A hankali Khaleesat tace "Ban san me yasa gabana ke ta faduwa ba Sophie, Abdul can be cunning kar ace ya fa biyo ki yaga gidan nan baki sani ba" Safiyyah tayi wani dariya tace "Saboda yana shan codeine sai ya biyo ni gidanmu, ai yasan ni ba ke bace hauka tuburan zan masa wallahi, to ya biyo ni akan me?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, taji abincin ma ya fita ranta, Safiyyah tace "In zaki ci abincinki ki ci, idan su Ya Musty sun dawo zan sa ya duba surveillance camera din bakin kofar mu ga wani shege ne ya danna bell" After a while Khaleesat ta tura abincin gabanta don ya isheta ga baccin da take ji, Safiyyah dai chatting kawai take da wayarta, Khaleesat ta dau kudin da Safiyyah ta ajiye mata ta cire dala dubu biyu a ciki ta ajiye mata kusa da ita, Safiyyah ta hade rai tace "Meye wannan?" Khaleesat bata kalleta ba tace "Na baki" Safiyyah tace "Inyi me da shi? A'a bana so wallahi, ki ajiye kudin ki kawai zai maki wani amfanin" Khaleesat bata tanka ta ba ta mike tayi kwanciyarta gefen gado ta lumshe ido, cikin dubara Safiyyah ta jawo handbag dinta ta mayar mata da kudin ciki sannan ta ajiye. Wajen karfe shidda da rabi Safiyyah ta tashi Khaleesat dake bacci ta dalilin wayarta dake vibrate, Safiyyah tace "Ana kiran ki a waya" Khaleesat ta mike zaune ta jawo wayar ta duba taga Housemate ne ke kiranta, daga kiran tayi ta kai kunne, daga daya bangaren yace "I am outside Halysaah" A hankali Khaleesat tace "To" Veil dinta ta dauka Safiyyah ta rakata zata bude mata kofa, Khaleesat ta riko hannunta da sauri tace "Ki fara duba waje kafin ki bude mana" Safiyyah tace "Ke dai matsoraciya ce wallahi, shi Abdul din ai ba Ι—an iska bane da zai zo ido na ganin ido, baki ga kamar barawo ya shige maki gida ba ranan da daddare" Bude kofar tayi Khaleesat ta makale a bayanta gabanta na faduwa, bayan ta hango motar Jay ta Ι—an sauke ajiyar zuciya, Safiyyah na washe hakora tace "Yau dai Allah yayi za mu gaisa da shi" Khaleesat ma murmushin tayi suka fita zuwa gun motarsa a tare, yana ganin Safiyyah ya sauko daga motar, ya rungume hannu yana kallonta yace "Good evening kawar Housemate" Safiyyah ta tuntsire da dariya tace "Welcome Yaya Housemate, sai yau Allah yayi za mu hadu tunda ka dawo" Yace "Amma ai ina ce ma kawarki ta gaisheki" Safiyyah tace "Wallahi bata taΙ“a gaya min ba" Jay ya Ι—an kalli Khaleesat dake kallonsa, ta sauke idonta da sauri bayan sun hada ido, murmushi yayi yace "Gaskiya ban taΙ“a cewa ta gaishe ki ba, it's not her fault..." Safiyyah tayi dariya tace "Wai don ka kareta ko, ai nafi ka sanin wacece Housemate dinka" Jay na murmushi yace "Ya mutan gidan?" Safiyyah tace "Duk lafiya lau suke, yanxu take gaya min uncle dinku gave her much money a taya mu yi masa godiya plss, ranan kuma ta nuna min diamond ring da ka siya mata, Allah ya saka da alkhairi Yaya Housemate, Allah ya bar ku tare" Khaleesat ta bude baki tana kallon Safiyyah with shock, Jay dai yayi murmushi yace "Our father... not uncle Safiyyah" Daga Safiyyah har Khaleesat kallon Jay suka yi, Safiyyah ta bude ido sosai tace "Kana nufin Mai martaba da kansa? That's surprising, Allah ya kara masa girma....." Jay na murmushi yace "Ameen" Ita dai Khaleesat tayi shiru tana tunanin yanda yayi ta hira da ita a parlon kamar random person babu wanda zai yi tunanin sarki ne, Safiyyah tace "To ni zan koma ciki Housemate" Jay yace "Alright Safiyyah, thank you so much" Tana murmushi ta juya ta koma cikin gida, shi dai Jay kallon Khaleesat yake, sai kuma ya bude mata front seat, ba musu ta shiga motar ba tare da ta kallesa ba, ya zaga ya shiga driver seat yana kallonta yace "Kin ci abinci ne?" Kai ta gyada masa, jin bai sake cewa komai ba ta daga idanuwanta ta kallesa, zoben hannunta taga yana kallo baya ko kiftawa, tayi saurin boye hannun a bayanta kamar ta nutse don kunya, yayi murmushi yana kallonta a hankali yace "Wai yaushe kika fara jin kunyata Housemate? I am only admiring the ring, it look soo cute in your finger" Taki daga kai ta kallesa, ita kanta ta rasa gane wannan sabon kunyan nasa da take yi, ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallonta babu ko kiftawa, tunda taji yayi shiru tasan kallonta yake hakan yasa ko da wasa bata yarda ta dago kanta ba balle su hada ido, murya can kasa taji yace "Me yasa ni baki gaya min Ex dinki yaje wajenki a schl ba sai Ajay?" Shiru tayi jin tambayar da yayi mata, can ta dan kallesa, still speaking slowly yace "Why?" Tace "Ae ko an kira ka baka picking call dinka..." Yayi shiru yana kallonta kafin yace "Yaushe kika kira ban yi picking ba?" Ta langwabar da kai tace "Anytime i call, you don't pick" Jay ya sauke idonsa kasa, after some seconds yayi kasa da murya yace "I promise i won't do that again, i will prioritize ur call from henceforth yanda nake prioritizing na Mami da me martaba" Khaleesat ta daga kai suka hada ido, tayi saurin dauke idonta daga nasa, yace "Me yace maki da ya sameki a school din?" Khaleesat tace "Safiyyah ce ta kulasa suka yi exchanging words" calmly Jay yace "Do not worry Halysaah, i will bring an end to ur fright about ur Ex Husband very soon in sha Allah, i promise you this, zaki samu kwanciyar hankali fiye da yanda kike tsammani" Khaleesat ta kallesa, cikin sanyin murya tace "But i don't want you to confront him pls, he can be cunning" Jay ya Ι—an yi murmushi yace "I am not confronting him Halysaah, kawai dai zan yi abinda zai yi cutting duk wani Intention din da yasa ya dawo yake bibiyan ki, i will put a total stop to that, kuma babu yanda ya iya haka nan zai hakura ko ba don Allah ba...." Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, After some seconds tace "Amma yanxu i will prefer inyi ma brother din Safiyyah magana to let me stay in their home har sanda zan gama exams, don bazan iya zama a apartment dina ni kadai ba kuma, i am very afraid" Jay yace "Kar kiyi inconveniencing dinsu Housemate, and I don't want you to be a burden to them considering the high cost of livelihood in this state.... ki zauna a apartment dinki kawai, i will be there also, i will be there to protect you...." Khaleesat tace "Zaka dinga zuwa kamar sanda muke former apartment dina?" Yayi murmushi yana kallon kwayar idanuwanta yace "Sure, anything for you Halysaah" Sosai taji hankalinta ya kwanta, cikin sanyin murya tace "To Nagode" Yace "Lokacin sallah ya kusa, can we go home now" Tace "Let me get my handbag" Gyada mata kai yayi, ta bude motar ta sauka, ya bi ta da kallo har ta shiga apartment din, after some minutes sai ga ta ta fito daga gidan da handbag dinta da waya, ta shiga motar ta rufe tana kallonsa taga kallonta yake.... Khaleesat na zaune dakinta wajen karfe takwas da rabi na dare suna WhatsApp call da Aunty Farida, gaba daya jikinta a sanyaye yake ga faduwar da gabanta yake ta yi jin abinda Aunty Farida ke gaya mata, labarin biyota da Abdul yayi har sabon Apartment dinta da kuma cikin makaranta take ba Aunty Farida, a nan ne Aunty Farida ke sanar mata ai yaje Mariri ma yafi a kirga few weeks ago kawai gaya mata ne bata yi ba don bata son daga mata hankali, Cikin sanyin murya Khaleesat tace "To Aunty ya aka yi yasan ina America ne?" Aunty Farida tace "In kin tambayeni in tambayi wa Khaleesat? Kilan ko bincike yayi a unguwan aka gaya masa, kinsan babu abinda yan unguwan nan baza su yi ba akan kudi, dama kuma ga tsegumi ya masu yawa, in kuma ba a unguwan ya bincika ba kilan shi ma yaga hotonki da wannan mutumin da ya dora ki a Instagram" Khaleesat kamar zata yi kuka tace "Toh me yake so kuma a guna Aunty da yake bibiyana ne?" Aunty Farida tace "Mutumin da yana zuwa cewa yayi ya maida auren ku, Allah ya so Nenne ta zo ranan sai abinda ta manta ne bata gaya masa ba ta kusa tara masa yan unguwa, kuma tace ai kin gama iddansa tun wani shekara in ma yau ya farka bacci tun sanda ya sake ki to yaje ya duba calendar yaga yau shekara nawa da yayi sakin, Nenne ta sille sa tas, ni ai shi yasa hankalina bai wani tashi ba, da dai baki idar da iddansa bane shine babban tashin hankalinmu gaba daya, amma da baki da hakkinsa ai kinga Allah ya kada hankalinsa sai bayan da kika gama ya waiwayo ki, yana sake zuwa inda kike ki kira masa hukuman kasar kawai su ja maki layi da shi...." Khaleesat dai ta kasa cewa komai, Aunty Farida tace "Dama in kika ga ya hakura da bibiyanki ai sai in wani auren kika yi tunda babu tsoron Allah a ransa, ban taΙ“a ganin mara kunya ma irin sa ba, babu kunya babu tsoron Allah fa ya zo ya marairaice ma Babanki wai ya maida ke, ya zo gidan nan yafi sau goma wallahi, to Allah na tuba ko da ace baki gama iddansa ba da ba sai dai mu makasa a kotu ba akan ki koma gidansa, shi Ι—an iska, danginsa matsiyata marasu mutunci" Khaleesat taji hawaye ya cika idonta tace "Toh Aunty ni tsoro nake kar ya sake cewa zai daukeni kema kinsan halinsa fa" Aunty Farida tace "A American zai dauke ki saboda ba shi da seti?" Khaleesat dai tayi shiru gabanta na faduwa don har yanzu bata mance yanda aka dauketa aka kai masa ita ba, tunanin hakan yasa hawaye ya fara zuba idonta, Aunty Farida tace "Yanxu dai ki kwantar da hankalin ki tunda kin ce Jarabawa za ku fara, su Junaid ma baza su bari ya cutar dake ba in sha Allahu, kiyi ta addu'a kina neman tsari daga sharrinsa, in sha Allahu Allah zai kare ki" Khaleesat ta gyada mata kai cikin sanyin murya tace "To Aunty" a haka suka yi sallama da Aunty Farida tana goge hawayen da yaki tsaya mata, kiran Safiyyah ne ya shigo wayarta tayi picking ta kai kunne, Safiyyah tace "Khaleesat kin san wa yayi ring din bell daxu kuwa?" Sosai gaban Khaleesat ya fadi tun kan Safiyyah ta gaya mata, Safiyyah tayi wani dariya har da kyakyatawa tace "Wallahi shi ne in gaya maki, Abdul ne ba wani ba, gashi nan an duba Camera na gansa, to da na bude kofar uwar me zai min ne? Wato ban taΙ“a ganin Ι—an iska mara aikin yi kamar sa ba, ki ji har yayi locating inda nake saboda rashin aikin yi, to me zai min da Allah bai min ba?" Cikin rawan murya Khaleesat tace "Kin dai ga abinda nake gudu ko, wallahi da baki kulasa ba Safiyyah, ba kowa ake musayar yawu da ba" Safiyyah tace "Wallahi ba abinda ya isa yayi min da izinin Allah, shi kuma yaya Musty idan ya gama bambamin fadan da yake yana cewa ina dauko masa magana a kasar nan sai ya daukeni mu tafi mu kai ma Cops report, sai an gano Abdul duk inda yake ya fadi abinda ya zo yi a apartment dinmu wallahi..." Tana kai wa nan ta katse wayarta, knocking din kofar dakin Khaleesat taji ana yi, ta juya ta kalli kofar har sannan zuciyarta na bugawa ta mike ta dau hijab dinta ta saka ta tafi ta bude kofar, sauke idonta tayi bayan sun hada ido, yana kallonta da damuwa ganin hawaye idonta yace "Are you crying Halysaah? Me ya faru?" Kamar jira take ta jingina da kofar dakin ta fashe masa da kuka dama ta kwana biyu bata yi ba, nan da nan ta rikitasa a wajen.....

 

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

 

*Ur evidence 07087865788*

 

 

 

https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM

 

 

 

Juyawa Jay yayi ya sauka downstairs don bai son yayi abinda zuciyarsa ke tunzura sa yayi a wannan moment din, yasan in ya ci gaba da tsayuwa yana sauraron kukanta a wajen the case will be totally different, sai da Khaleesat taga ya sauka kasa sannan ta dena kukan da take har lokacin tana jingine da kofar tana goge idonta a hankali, juyawa tayi ta koma dakinta ta dau laptop dinta ta zauna kan gado zata yi karatun wani course dinsu amma ta kasa karatun, sai kuma tayi tagumi tana kallon screen din laptop din babu ko kiftawa, after a while ta maida Laptop din gefe ta sauka daga kan gadon ta nufi kofa ta fita daga dakin, walking slowly ta fara sauka downstairs tana kallonsa, zaune yake kan kujera idonsa a wayar hannunsa, ya juya yana kallonta jin foot step dinta, har ta karaso karshen staircase din, ta sunkuyar da kai ganin kallon da yake mata, mikewa yayi ya nufeta yayi kasa da murya yace "Halysaah... " Ta daga idanuwanta ta kallesa amma bata ce komai ba, yace "Why are you crying?" Kamar bazata ce komai ba sai kuma ta jingina da bango ta rungume hannunta tace "Ba sai kace min inyi hakuri ba amma ka wani tafi...." Murmushi yayi yace "To ai ban san ta yanda zan fara cewa kiyi hakurin bane ta yanda zaki gane da gaske nake baki hakurin, shi yasa na tafi" Ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, can ta juya zata bar wajen, ya dakatar da ita yace "Halysaah" After some seconds ta juyo fuska a daure, ya Ι—an yi murmushi yace "Mu je parlor in baki hakurin to" Ta wani turo baki ta kara rungume hannunta, yana murmushi ya juya ya koma parlon, sai kuma ta bi bayansa, ya jira har ta karaso ta zauna kan kujera, sannan ya zauna same kujeran leaving some space between them yana facing dinta yayi kasa da murya yace "Now tell me, why were you crying Halysaah?" Ta sauke idonta a hankali tace "I just can't understand why Abdul is still after me..." Jay yayi shiru yana kallonta babu ko kiftawa, can yayi kasa da muryarsa yace "But mun gama maganan nan just few hours ago ai Housemate, i told u i will put a stop to that soon, i promise you this, kina gama jarabawa idan mun koma Nigeria komai zai zo karshe in sha Allah" Muryarta na rawa tace "Why not now? Ai bazai daina bi na ba, and i want to concentrate fully on my exams...." Jay yayi shiru yana kallonta, ya sauke idonsa with calmness in his voice yace "Are you sure you will want that now?" Ta gyada masa kai looking so confuse tace "Ya fa je har gidanmu a can kano so many times, sannan daxu muna gidansu Safiyyah sai da yaje gidan fa ya danna bell and left immediately...." jay ya daga idanuwansa yana kallonta da mamaki yace "Really?" Ta marairaice masa tace "Aunty Farida ta gaya min yana ta zuwa gidanmu, pls kawai we should report him to authorities don ya fita hanyata, ni wallahi tsoronsa nake ji, he can be so cunning...." Jay was quiet for almost a minute, sai kuma ya daga kai suka hada ido don kallonsa take, ita ta fara dauke idonta, har zai kamo hannunta sai kuma bai yi hakan ba ya fara kokarin kara barin enough distance tsakanin, yayi kasa da murya yace "Do you want to get married Khaleesat?" Shiru Khaleesat tayi tana kallonsa babu ko kiftawa don tambayar tasa ya zo mata a bazata, shi dai kallonta kawai yake yana jiran amsarta, a hankali tace "Aure kuma?" Jay yace "Yeah" Tana son tambayarsa aure da wa amma ta kasa, nan da nan jikinta yayi sanyi don babu inda tunaninta ya tafi sai ko yana da wani da zai hadata aure da, speaking slowly yace "Aure ne kawai zai sa ya hakura ya dena bibiyanki Halysaah, in kuwa ba haka ba bazai hakura ba ko da an hadasa da hukuma he will only change his tactics..." Hawaye taji ya fara taruwa idonta, sai tayi da ta sanin sauko ta samesa a parlon, kilan da bai gaya mata wannan magana ba, ganin hawaye a idonta cikin sanyi yace "Baki shirya auren ba ko Housemate?" Ƙin ce masa komai Khaleesat tayi tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba a wajen, ta rasa me yasa ta zama heartbroken all of a sudden da jin furucinsa, was it because that wasn't what she was expecting or wanting, she still can't tell, Jay ya sauke idonsa daga kallonta, after some seconds yace "To kiyi hakuri, i shouldn't have brought this suggestion up, may be you have other plans than marriage ko" Ita dai bata ce komai ba tana goge hawayen dake sintiri a fuskarta, ya jinginar da kansa da kujera bai sake cewa komai ba, tayi karfin halin cewa "Ai baka ce min da wanda zan yi auren ba" Ya girgiza mata kai still not looking at her yace "A'a, naga ba aure bane plan dinki na gaba, i am sorry i came up with the idea, kawai ina ganin kamar hakan kadai ne mafita... I am sorry" Tana girgiza masa kai still trying not to cry out loud tace "Ni bani da wani plan wallahi, kawai burina Abdul ya fita rayuwata ya kyaleni, duk wani abu da zai tabbatar da hakan i will welcome it wholeheartedly, as far as he will stay far away from me" Jay ya kalleta a hankali yace "To nace aure kin fara kuka ai Housemate" Ta girgiza masa kai tace "In hakan ne best solution i will welcome it, kawai dai ban san da wanda zaka hadani bane" Jay dai kallonta kawai yake amma ya kasa cewa komai, ita kuwa sai goge hawayenta take without looking at him, yayi kasa da murya yace "I don't know ko za kiyi turning down din wanda zan hada ku Halysaah, bazan so in maki dole ba, ko kuma nauyina yasa ki amince bayan ke ba hakan kika so ba a ranki" Khaleesat ta girgiza masa kai cikin karfin hali tace "I won't... as far as it's ur choice i will never turn it down, i trust ur choice, and i know it will be the best for me, nasan baza ka min zabin da bazai yi favouring dina ba, i know this..." Magana take amma Allah yasani karfin hali kawai take, she was very very heartbroken deep inside her and she can't even say why, Jay dai bai fasa kallonta ba yana tunanin what he is about to voice out and how she will react to it, jin shirun nasa yayi yawa ta daga idanuwanta da har sun fara ja suka hada ido, kamar me rada yace "Za ki iya aurena Halysaah?" His question almost took away her breathe cause it hit her unexpectedly, she was stunned into silence at the same time paralyzed with surprise, she couldn't stop staring at him with wide eyes, shi ma kallonta yake babu ko kiftawa kamar yanda take kallonsa, and she realize they've been staring at each other for almost 30 seconds, da sauri ta dauke gaze dinta daga idonsa zuciyarta na bugawa, cikin dubara ta fara kokarin mikewa zata bar masa parlon, yana gano abinda zata yi yayi saurin rike hijab dinta yana kallonta murya can kasa yace "Ba inda za ki je without giving me my answer Halysaah" Boye fuskarta tayi jikin kujera da sauri taki yarda su sake hada ido tana jin kamar ta nutse cikin kujeran, ta dade bata ji irin wannan kunyan da take ji a yanxu ba, yana kallonta yace "Halysaah" Taki dago kanta tana kara shigewa cikin kujeran tace "Uhm" Yayi kasa da murya yace "Look at me plss" kamar zata yi kuka tace "Uhm ni bazan iya ba" Gaba daya ta gama narkar da shi a wajen, ya duka gabanta yana kallonta as if he is whispering yace "Pls say something Halysaah, i want to hear you say something" Khaleesat dai taki yarda ta dago kai su hada ido da shi, she can't even explain what she is feeling at the moment, slowly yace "To tashi ki je ki kwanta, sweet dreams Dear, I love you so much...." Sake gigitata yayi da kalamansa, ta fara kokarin mikewa daga kan kujeran tana rufe fuskarta da Hijab din jikinta, saboda saurin da take ta bar wajen ta take dogon hijab din jikinta kiris ya rage ta fadi har zai rikota kawai ya hana kansa yin hakan, tayi regaining balance dinta within a twinkle of an eye har ta isa staircase ta wuce sama da sauri ta shiga dakinta ta kulle kofa ta jingina jikin kofar tana sauke ajiyar zuciya kamar warce tayi tseren gudu...

Daren ranan Khaleesat bata yi baccin kirki ba, she can't even explain her emotions, da gari ya waye har karfe sha daya na safe ta kasa sauka downstairs gashi karfe takwas suke da class ranan, har ta gaji da kiran da Safiyyah ke ta doka mata tun daxu, da sauri ta juya jin ana knocking kofar dakinta, ta kasa tashi ta bude kofar, ita kanta bata san kunyanta ya kai haka ba sae yanxu, da kyar ta mike jin an sake knocking kofar, ta dau veil dinta ta yafa kamar sabuwar amarya ta karasa bakin kofar, nan ma sai da ta tsaya for almost 30 seconds kafin tayi karfin halin bude kofar kanta a sunkuye, yana tsaye bakin kofar calmly yace "Good morning Housemate" Still not looking at him cikin sanyin murya tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau, baki da lectures ne?" Kanta a kasa tace "Ina da" Shi dai kallonta kawai yake ganin wani sabon kunyansa da ta tsira kuma, ya Ι—an yi murmushi ya mika mata karamin tray din hannunsa yace "Here.... Idan kin gama sai inyi dropping dinki a school din" Iya abinda yake mika mata kawai ta Ι—an kalla sannan ta amsa, shi dai kallonta kawai yake ta juya ta koma cikin dakin sannan ta kulle kofar, Hot chocolate da cookies ta gani a saman tray din, ta zauna saman carpet din dakin da breakfast din a gabanta, bayan Khaleesat ta gama sai da ya kira wayarta sannan dai ta karasa shirinta ta dau handbag dinta da tray din breakfast dinta ta sauka downstairs, yana zaune parlon ta samesa, kanta a kasa ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, bayan ta wanke utensils din ta fito daga kitchen din ta tsaya bayan kujera tana wasa da fingers dinta a hankali tace "Na gama" Mikewa yayi ya dau makullin motarsa yace "Ohk mu je" Kofa ta nufa yana biye da ita a baya zata bude kofar taji a bude yake ta fita sannan shi ma ya fita, ta tafi garage ta jirasa ya kulle apartment din, as usual shi ya bude mata door din motar bayan ta shiga ya kulle, sannan ya zaga ya shiga driver seat ya tada motar ya fara Reverse, sai da suka dau hanya yace "We saw our dad off to the airport in the morning, na san kilan bacci kike lokacin da na fita" A hankali Khaleesat tace "Ya koma Nigeria kenan?" Jay yace "Yeah in sha Allah" Khaleesat tace "Toh Allah ya kai su lafiya" Jay yace "Ameen" duk wannan maganar da take taki yarda ta kallesa balle har su hada ido, ya Ι—an yi murmushi kamar bazai ce komai ba sai kuma yayi kasa da murya yace "Ko sai mun yi auren zan cire maki wannan kunyan naki?" Wani sabon kunyan ne ya kara lullebeta a motar, ta kauda kanta kamar zata yi kuka tace "Ni dai bana so" Yana murmushi ya gyada kai yace "Za ki yi bayani" Gaba daya Khaleesat ta zama so uncomfortable a motar, Allah Allah take su isa makaranta ta sauka, shi dai lokaci lokaci yake kallonta yana kara admiring din irin kunyarta, can dai yayi murmushi yana gyada kai, suna isa makarantar bayan yayi parking Khaleesat ta bude motar, a hankali yace "Halysaah" Bata fita ba amma kuma bata kallesa ba tana dai jiran jin abinda zai ce, taji yace "To kalleni mana" Ta girgiza masa kai still looking outside, yayi kasa da murya yace "Please" Ta marairaice tace "Bazan iya ba" Yace "Please" Shiru tayi tana jin kamar ya hadata da wani gagarumin aiki kallonsa da yace tayi, da gasken gaske kunyarsa take ji yanxu, a hankali tace "Don Allah nayi latti fa" Yace "To me yasa baza ki kalleni ba" Cikin sanyin murya tace "Zan kalle ka anjima" Yace "A'a ni yanxu nake so" Shiru tayi tana Ι—an murmushi tana kallon wajen motar, shi dai kallonta kawai yake, sai da tayi gathering buhun courage sannan ta dake ta Ι—an juya a hankali ta kallesa suka hada ido, she could see nothing but her love in his eyes, sai yanxu ta kara fahimtar irin kallon da yake mata tun bayan dawowarsa daga Nigeria, kallon so ne tsantsarta yake mata, ya kashe mata ido daya yana murmushi yace "I love you" Ta rufe fuskarta da mayafinta da sauri, sai kuma ta bude motar cikin hanzari ta sauka ta kulle without turning back ta bar wajen ya bi ta da kallo, Jay was sitted in the car for almost 15 mins ya kasa tafiya, nan kuma duk tunanin inda Khaleesat zata zauna har ta gama Exams dinta yake don shi dai yasan a yanxu dai bazai iya zama under the same apartment with her ba, he just can't, a sanda suka zauna gida daya he had no feeling toward her, ganinta yake just as his normal Housemate and nothing more, babu komai game da ita a ransa har ma sanda suka samu encounter din farko da Abdul a apartment din, he is just being kind and nice to her as a Housemate sannan kuma matsayinta na er uwarsa musulma from Nigeria, ko a sanda ya biya mata kudin jirgi taje duba Ummanta yayi hakan ne kawai saboda shi yasan girman mahaifiya don baya wasa da tasa, but outside of their apartment bayan abubuwa sun faru tsakaninta da Abdul ya maidata gidansu he gradually started developing feelings for her from nowhere, shi kansa bai san ta yaya ba amma yafi tunanin tausayinta da ya saka a rai ne ya ja hakan, he can't even say how everything happened all of a sudden and he fell deeply for her tun period din da suke Exams dinsu, yanxu kuma bazai ce zai kai ta gidansu ta zauna ba don baya fatan wani family member dinsa su sake ganinta a gidan, Ya jinginar da kansa jikin kujeran motarsa ya lumshe idanuwansa cause he is so confuse, yasan yanxu kam ba Ι—a bane and he won't risk staying in the same apartment with just the both of them inside, yeah she need him to protect her from her Ex amma zuciyarsa bazai jure zama gida daya da ita ba don yasan lallai na ukun su Shaidan zai zama, and getting another apartment for her is not even an option, bude ido yayi jin wayarsa na vibrate yana dubawa yaga Ajay ne ke kiransa, picking call din yayi ya kai kunne kafin Ajay yace komai yace "Are you at home?" Ajay yace "Did you come across my debit card?" Jay yace "Tare muke amfani da card din... Are you home now cause i need to speak to you Ajay" Ajay dake sauraronsa yace "Bout what?" Jay ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "I will be home now, kar ka fita ka jira ni" Yana fadin haka ya katse wayar ya tada motarsa ya kama hanyar gidansu......

 

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda*

 

Ur evidence 07087865788

 

 

 

 

https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM

 

 

Ajay na cin strawberry dake gefensa idonsa a kan movie din da ake yi a TV, Jay ya dinga kallonsa kafin ya fixge remote ya kashe Tvn, Ajay ya juya ya kallesa yace "Wai kunne ke ji ko ido? Ina fa sauraronka Jawwad" Jay yace "If you are not giving me ur attention i will leave this parlor, tun daxu ina magana hankalin ka na wani waje daban, what's all this pls" Ajay ya tabe baki, sai kuma ya juya yana kallonsa direct in the eyes yana ci gaba da cin Strawberry dinsa yace "Oya be fast pls" Mikewa Jay yayi zai bar parlon Ajay ya fixgosa yace "Kai matsala ta da kai kenan banzan zuciya, ba gashi ina sauraron ka ba" Jay yace "Kar ka rena min hankali mana Malam" Ajay dai ya ci gaba da cin fruit dinsa yace "Ka kashe Tv din ai, i am listening" Jay ya koma ya zauna, for peace to reign yasa Ajay ya maida hankali yana sauraron maganar da Jay ke yi masa, can ya Ι—an yi murmushi ya jawo grapes dinsa zai fara sha yace "This is weird... All of a sudden sai ka ji bazaka iya zama gida daya da ita ba, why is that? Meye dalilin ka? Da ba apartment daya kake zaune da ita ba some months ago, ko ni ban san gida daya ku ke ba sai ranan da baka da lafiya, meye kuma ya canza ra'ayin ka all of a sudden...." Jay yace "To yanxu bazan zauna ba, period! in zaka kawo Suggestion din yanda za ayi ka kawo ina sauraron ka...." Ajay yace "Ai ni dalilin hakan nake son sani" Jay yace "Ni dai babu ruwan ka da dalilina kawai solution nake nema, just tell me yanda kake ganin ya kamata ayi.... Tunda kaga we are not going to make the mistake of accommodating her again in this House" Ajay yayi shiru, kamar bazai ce komai ba can dai yace "Kai din dai ya kamata ka zauna a apartment din tare da ita, that's the only solution for now tunda jarabawa za su fara, ko da za a samar mata sabon Apartment definitely sai ya bi ta can din ma kamar yanda ya gano wannan, da mun san haka kawai da a cikin makaranta aka biya mata accomodation to avoid all this, wannan wawiyar kawar tata mara hankali kuma will just worsen the situation idan aka ce taje can gidansu ta zauna, beside no one loves being inconvenience in this state...." Jay ya sauke ajiyar zuciya, after a while ya fixge remote din da Ajay ya dauka yana kokarin kunna TV alamar ya gama maganarsa, Ajay yace "Na fa baka solution din da ka zo nema, ka bar ni in ci gaba da abinda nake yi" Jay yace "I told you staying in the apartment with her isn't an option Ajay, kaga kenan har yanxu babu solution" Ajay yace "Wai saboda kana gudun ka ci gaba da rungumeta ne yasa ka kasa zama gida daya da ita? To ai wannan norms ne a wajen ku tunda iya runguma ce kawai..." Jay ya dinga masa wani kallo, Ajay yayi murmushi yana gyara zama yace "Ko kuma kawai ka kira gida a daura maku auren, ko ni sai in rakaka ka tare a can apartment din kawai" Jay yace "What is this u are saying?" Ajay yayi dariya yana shan grape dinsa bai ce masa komai ba, Jay dai kallonsa kawai yake, can Ajay ya daga kafada yace "Or better still idan kanwar Baabarta na da Passport kawai ka nema mata visa idan Allah yasa an bata sai ta zo ta zauna da ita har ta gama jarabawan....." Jay yayi shiru kamar me nazarin abinda Ajay yace, after some seconds yace "What if ba a bata visa din da wuri ba, sannan before Everything is process kasan zai Ι—an dau lkci may be kafin nan ma sun fara jarabawan" Ajay yace "To ni iya shawaran da zan iya badawa kenan, ban san kuma yanda zaka yi ba, stop stressing me with ur problem plss" Jay yace "Why not stay in the apartment with her, har zuwa sanda kanwar Mom dinta zata zo" Ajay ya daga kai ya kallesa, can yace "Wa zai zauna a apartment din?" Calmly Jay yace "Kai....." Ajay ya ajiye fruit din hannunsa yace "Amma ka ma raina min hankali Jay, ni ne zan zauna da ita a apartment din ga ni Bodyguard ko? Can you even hear ur self? kawai sai in koma apartment dinta in zauna gadin ta saboda ni bani da aikin yi, in da gaske neman me gadinta kake ka sa Salem ya koma apartment din da zama mana tunda ya gama masters dinsa, after all she was sharing an apartment kafin ka santa a kasar nan, so yanxu ma zata iya sharing da Salem as her Housemate" Jay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa, har ransa yaji zafin abinda Ajay yace wai ya hada Khaleesat da Salem a gida daya, duk da ba wai Salem na da wani mugun hali bane amma yaji haushin hakan sosai, har Salem din da bai masa komai ba sai da yaji ya fara jin haushinsa a zuciya, mikewa yayi ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Ajay ya taΙ“e baki ya ci gaba da shan fruit dinsa ya jawo remote ya kunna TV.

Khaleesat na zaune tare da Safiyyah bayan sun gama lectures wajen karfe shidda saura na yamma, ita dai sai kallon Safiyyah dake bata labarin yanda Mustapha yace zai nemi Abdul duk inda yake ya basa hakuri don shi baya son fitina a kasar mutane, cikin bacin rai Safiyyah ke bata labarin tana cewa "Mustapha Ι“ata mana sunan family kawai zai yi a zata mu coward ne matsorata, abun duk ya dameni wallahi, har da cewa in na sake kula Abdul zai kira babana ya gaya masa, ni kuma tsoron old Man dina nake wallahi...." Ita dai Khaleesat kallonta kawai take ba don tana sauraron abinda take cewa ba, infact gaba daya ma bata san me take cewa ba, kawai memories din jiya da daddare ne ke dawo mata a kai, ko karatun ma yau bata san abinda aka yi ba sunan ta zo school ne kawai, kana ganinta kasan she is in a very happy mood today, Safiyyah tace "Wai yau naga sai fara'a kike kamar warce aka biya ma kujeran mecca, meye sirrin kawata, wallahi na zata idan na shigo school zan ga idanuwanki sun kumbura don kuka tunda aikin ki kenan, amma naga sai farin ciki kike kina nishadin ki, yau har da kula Coursemate dinmu a Hall kamar ba ke ba" Khaleesat tayi murmushi tana wasa da zoben hannunta tace "To saboda me zaki ga idona ya kumbura don kuka?" Safiyyah tace "Akan issue din Abdul mana, ai nasan halin ki sai ki iya kwana kina kuka" Khaleesat ta taΙ“e baki har sannan tana murmushi tace "That was then, I don't have time for that now Safiyyah, ni fa na ma dena tsoron nasa yanxu, kuma ba abinda ya isa yayi min...." Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace "Nagode tawan, don Allah a wani kasuwan kika siyo liver din nan naki me shegen kyau?" Khaleesat bata san sanda tayi dariyan ba ita ma tace "Allah da gaske i am not afraid of him any longer Safiyyah" Safiyyah tace "Ko ke fa, yanzu tun asali da haka kike ai babu me taka ki kawata, amma naji dadin wanda ya siyar maki da liver din nan har kika samu kwarin gwiwa...." Shiru Safiyyah tayi ta daga kai tana kallon Abdul that is coming toward them, tuni Khaleesat ta hade rai bayan ta gansa ita ma, ta fara tattara reading materials dinta a jaka, ta dau jakar tana kallon Safiyyah tace "Mu je Sophie" A tare suka mike Safiyyah na taΙ“e baki, Khaleesat na fara tafiya Abdul ya riko veil dinta yana kallonta yace "Don Allah ki bani minti biyar mu yi magana Khaleesat" Ta juya ta kallesa fuskarta a murtuke tace "Let go of my veil Abdul" Yayi kasa da murya yace "Plss Khaleesat, i want to say one or two words, don Allah ki bani lokacin ki ba don ni ba" Fixge veil dinta tayi a fusace kafin ta bar wajen kawai taga ya shige gabanta yana mata magiya yace "Don Allah fa nace maki Khaleesat, ko minti biyu ne ki bani" Safiyyah dai ta koma gefe tana wani dariya kamar taga wawan zama, lallai Abdul ya zama abun dariya yanxu don tsakaninsa da Allah ya marairaice ma Khaleesat, Khaleesat ta juya tana jin zuciyarta na tafarfasa zata bi daya direction din taji ya riko hannunta this time around, bata san sanda ta juyo ta sauke masa mari a fuska ba, cikin fushi tace "Baka da hankali ne Abdul?" a hankali ya sake hannunta don bai ma san hannunta ya rike ba, yana kallonta calmly yace "I am sorry Khaleesat, I didn't mean to...." Tuni ta juya ta bar wajen kamar zata tashi sama, Safiyyah da ta saki baki hangangan ta bi Khaleesat da kallo, slapping Abdul was the least thing da tayi zaton Khaleesat zata iya yi a rayuwa, Safiyyah ta kalli Abdul da ya zauna inda Khaleesat ta tashi ya rike kansa, bin bayan Khaleesat tayi har sannan ta kasa rufe baki with shock, ita kuwa Khaleesat ta sha kunu Kamar bata yi komai ba tana ta tafiyarta, bayan sun yi nisa a hankali Safiyyah tace "Khaleesat?? Did you just slap him?" Without looking at Safiyyah tana ci gaba da tafiyarta tace "He asked for it, don me zai rike min hannu, ko bashi da hankali ne" Safiyyah da ta bude baki tace "Don Allah wa ya koya maki haka? Dama kin iya haka all this while kike maida kanki rubabbiya ake taka ki yanda aka ga dama? I still can't believe your action Khaleesat, Omg" Khaleesat ta tsaya ta ciro wayarta dake vibrate, number Housemate dinta ta gani dama kuma she was expecting his call don shi yace ta jira zai zo ya dauketa, tayi picking call din ta kai kunne, after some seconds tace "Eh mun gama tun daxu" Safiyyah dai kallonta kawai take da mamaki har ta gama wayan, sannan Khaleesat ta kalleta tace "He came to pick me, mu je sai yayi dropping din ki tunda hanya daya ne" Safiyyah ta rike haΙ“a tace "Ni fa na kasa yarda marin Abdul kika yi da gaske, don da bana wajen aka yi ko jikina kunnuwa ne bazan yarda ba, ko ni duk fitina ta bazan yi gigin marin Abdul ba wallahi" Khaleesat ta hade rai tace "Ni dai don Allah mu tafi, kawai yayi ta bibiyata a makaranta yana daga min hankali for what reason? babu komai fa tsakanina da shi yanxu don me bazai bari inyi rayuwata irin na kowa ba, i am fed up with this" Hawaye ne ya ciko idonta ta fara gogewa tana ci gaba da tafiya, Safiyyah dai tayi shiru tana bin ta, don yau kam Khaleesat ta goge mata hadda tasss, a haka suka karasa inda Housemate yayi parking motarsa, yana ganinsu ya sauko daga kujera me zaman banza, Safiyyah na washe baki ta gaishesa ya amsa da murmushi fuskarsa yace "Ya lectures din? Ko kuma ince revision, since exams is around the corner" Safiyyah tace "Alhamdulillah Yaya Jawwad" Juyawa yayi ya kalli Khaleesat, ganin mood dinta nan da nan fara'ar dake fuskarsa ya bace, ita kuwa Safiyyah sai gwale ido take bayan ta hango Ajay zaune driver seat, shi kuwa dama tun da ya hangosu da Khaleesat ya toshe kunnensa da ear pod yana kallon gabansa, Housemate na kallon Khaleesat ya bude mata back seat, cikin sanyin murya ta gaishesa sannan ta shiga motar, ya kalli Safiyyah yace "Tun da hanya daya ce ki shiga mu ajiye ki ko?" Safiyyah na kirkiran murmushi ta girgiza kai tace "A'a akwai wata Coursemate dinmu da nake jira akwai reading material dina a wajenta" Jay yace "Alright Safiyyah sai anjima" Daga haka ya bude front seat ya shiga, Safiyyah ta daga ma Khaleesat hannu sannan ta jefa ma Ajay harara duk da ko kallon inda take bai yi ba, ta juya tayi wucewarta, Allah ya rabata shiga mota daya da fitinannen nan, kila ma tana dosana kugunta a kujeran motar zai ce ta fita, in ya mata haka kuma tsaf zata masa rashin kunya ita kam, to ina dalili, gwara da ta kama kanta taki bin su.... Bayan sun bar school din Jay ya kasa daurewa ya juya yana kallon Khaleesat yace "What happened Housemate?" Khaleesat ta girgiza masa kai alamar ba komai, yace "No there is something, why are you Moody? Tell me pls, wa ya bata maki rai?" Kamar Khaleesat bazata ce komai ba, sai kuma ta sauke idonta tace "He still followed me again today" Ta madubin mota Ajay ya kalleta jin abinda tace, Housemate yace "Sai me ya faru kuma?" Khaleesat tace "Rike min hannu yayi wai in tsaya in sauraresa ni kuma na maresa nayi tafiyata" Ba Housemate dinta ba, Hatta Ajay sai da ya bude baki yana kallonta ta madubi, Jay was totally speechless yana kallonta, can ya juya ya kalli Ajay, Ajay yace "Kika maresa? Saboda baki da hankali zaki maresa? Ana kokarin protecting dinki by all means kina kara jawo ma mutane aiki? nasan wannan baΖ™ar kawar taki ce zata zuga ki ta koma gefe tana kallo, dama kuma nace idan kika ci gaba da mu'amala da ita sai ta ja maki bala'in da yafi karfin ki don ban ga alamar tana da seti ba yarinyar nan, kina er mitsitsiyar ki zaki daga hannu ki mari gabjejen mutumi haka ko tsoron tsayinsa baki ji ba, da kika maresa sai ta fara hailing din ki ko..." Kuka Khaleesat ta fara yi a motar kamar jira take, Jay ya juya ya kalli Ajay yace "Look Ajay, no one is above mistake, we all make mistake, don haka ba gigitata zaka yi ba, she is frustrated shi yasa tayi hakan, so we shouldn't blame her...." Ajay ya wani kallesa sannan ya maida dubansa kan titi bai sake tofa nasa ba a cikin motar, Jay ya kalli Khaleesat dake kuka, cikin kwantar da murya yace "Ki kwantar da hankalin ki Housemate, babu abinda zai maki in sha Allah, i am giving you assurance, marinsa da kika yi kuma baki yi kuskure ba shi ya ja ma kansa" Ta gefen ido Ajay ya kallesa bai dai ce uffan ba, Ita dai Khaleesat kuka kawai take a hankali har suka isa apartment dinta, sauka tayi daga motar ta nufi kofar apartment din ta bar su cikin motar. Jay ya kalli Ajay yace "You are not suppose to scold her that way, she is already frustrated, cikin kwantar da murya ya kamata ayi mata gyara, beside ita yarinya ce fa har yanzu" Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace "A'a, sha'awar gado ce" Jay bai sake ce masa komai ba a motar, bayan kusan minti daya ya kallesa yace "Ka shiga ciki... let me get some food from the restaurant for her, kai nasan zaka yi sorting kanka out, there is everything available at the kitchen" Ajay yace "Wait pls, ni kaji nace maka na amince da tsarin ka ne da kake wannan bayanin?" Jay yayi shiru yana kallonsa, can yace "Pls ka daina maido da magana baya Ajay, i tot we are done with all this, nayi ma Aunty Farida magana daxu tace bata da passport, but getting a passport isn't an issue, Visa ne babban damuwan yanxu, kasan baza a samu da wuri haka ba" Ajay yace "Yanzu me kake nufi? Shikenan ni sai inyi inconveniencing din kaina in takura rayuwata just to please you? Bayan ka fi kowa sanin ba ko ina nake zama comfortably inyi rayuwa ba, You know how irritating everything can be to me, why not consider me?" Jay yace "I will make the apartment very Comfortable for you to stay, beside i will be coming around too, wata daya ne fa an gama exams din...." Ajay yace "To wai ba na baka shawaran kawai kayi ma mai martaba magana a daura maku aure ba? What are you still waiting for?" Jay yace "Me yasa kake mantawa da Mamina ne? I didn't birth my self, har yanxu fa Mami bata san komai kan wannan maganar ba, i need to speak to her about it face to face ta yanda zata fahimce ni... After their exams dama tare za mu koma Nigeria, so i can speak to Mami" Ajay ya Ι—an yi murmushi ya shafa gashin kansa bai dai ce komai ba, Jay dake ta kallonsa yace "Meye ma'anar hakan?" Ajay ya daga hannu da sauri yace "Nothing..... Just wishing you luck" Jay bai sake cewa komai ba kuma bai fasa kallon Ajay ba, after some seconds yace "Ban taΙ“a nuna ina son abu Mami taki abun ba ko da bai mata ba, she is after nothing but my happiness, bata da kowa sai ni, farin cikina shi ne first priority dinta, kuma kai ma kasan da wannan, you can attest to that" a hankali Ajay ya jinginar da kansa jikin kujeran motar keeping silent.....

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

Ur evidence 07087865788

 

 

 

 

_We sell all kind of spices like grand masala, 7 mixed spice, all purpose spices, Mandy spices, biryani, pepper soup spice, ginger mix, Curry, suya spice and tsire mix all at affordable prices_

 

_Siyan daya ko sari, contact +234 803 298 6552 for more info_

 

 

 

https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM

 

 

Wajen karfe sha daya na dare Khaleesat na zaune saman gadonta tana karatu a laptop din gabanta, ba sosai take gane karatun ba saboda yunwan da take ji, abincin da Housemate dinta ya siyo mata daxu Ι—an kadan ta ci a ciki don bai mata dadi ba, tayi tagumi tana kallon slide din gabanta, kofar dake kallon nata taji kamar an bude, ta juya tana kallon nata kofar, after almost 5 mins ta sauka daga saman gadon ta dau hijab dinta har kasa ta saka sannan ta nufi kofa zata je kitchen ta hado shayi, dama tun daxu ta kasa fita ne don kar ta hadu da Housemate dinta a parlor, don yanxu wani kunyansa kawai take ji, a hankali ta bude kofar ta fito corridor tana tiptoeing, tana fara sauka downstairs ta tsaya da mamaki tana kallon Housemate dinta dake kwance 3 sitter idonsa a lumshe, duk da ba wuta me haske bane kunne a parlon amma tsaf take iya ganinsa, juyawa tayi ta kalli dakin dake kusa da nata with confusion, ko dai kunnenta ne yaji kamar an bude kofar dakin? Lokaci daya taji gabanta yayi mugun faduwa bayan Abdul ya fado mata a rai, kaddai Housemate dinta mance kofar yayi a bude yayi bacci, tana cikin wannan tunanin zuciyarta na bugawa aka bude kofar dakin dake kallon nata, wani kara ta kurma a mugun tsorace tun ma bata ga wa zai fito daga dakin ba, Jay ya mike da sauri yana kallonta, sai kuma ya nufeta da mamaki yace "What happened Housemate?" Tana hada ido da Ajay da ya fito daga dakin shi ma yana mata kallon mamaki ta durkusa wajen ta fara kuka tana jin har lkcn zuciyarta bai dawo dai dai ba, tuni Jay ya karasa inda ta durkusa yana kallonta yace "Me ya faru?" Tana kuka a hankali ta daga idanuwanta ta kallesa tace "Tsoro ya bani ai, ni na zata fa ya tafi daxu..." Ajay yaji kamar yayi ball da ita ta gangara downstairs tsabar yanda ta bashi haushi, don shi kansa sai da ihunta ya juya masa kai, Jay dai kallonta kawai yake ya kasa cewa komai ma, Ajay ya fara saukowa downstairs fuska daure yace "Tashi ki ban waje kar inyi ball dake a nan, silly gal" Turo baki tayi tana goge idonta ta basa hanya yayi tafiyarsa downstairs ya bar su a wajen, ta Ι—an daga kai a hankali ta kalli Jay dake ta kallonta ya ma rasa me zai ce, boye fuskarta tayi da hijab din jikinta tana lekosa ta Ι—an space din da ta bari a hankali tace "Kayi hakuri, ni wallahi ban san a gidan nan zai kwana ba shi ma, na zata ya tafi tun daxu" Murmushi yayi mata, calmly yace "It's fine Halysaah, you need something?" Ta gyada masa kai, a hankali tace "I want to take tea" Yace "Ohk, let me get you some, ki koma dakin ki" Tana murmushi cikin sanyin murya tace "Thank you" Daga haka ta juya ta koma sama zuwa dakinta, shi kuma ya sauka downstairs Ajay ya bi sa sa kallo har ya shiga kitchen, kwafa yayi ya dau remote ya kunna TV, after some minutes Jay ya gama hada mata tea ya debar mata cookies a plate sannan ya tafi sama, Ajay ya taΙ“e baki ganin yanda ya maida kansa Boy Boy dinta kawai, alhalin ko 5% din treatment din nan baya yi ma Hadiyah, Jay na kai mata shayin sama yayi knocking ta fito ta amsa amma ta kasa kallonsa, cikin sanyin murya tace "Nagode sosai" Kai kawai yayi mata nodding, slowly yace "Good night Halysaah" Ta juya ta koma cikin dakin ta kulle kofar. Washegari wajen karfe tara na safe Khaleesat ta sauko downstairs bayan tayi wanka ta shirya duk da bazata je school ba ranan, kallonsa ta dinga yi yana kwance saman kujera ya rufe fuskarsa da karamin towel ya kife wayarsa a kirji, karasawa tayi har inda yake kamar tana son gano wani abu, lokaci daya ya cire towel din fuskarsa suka yi ido hudu, komawa baya tayi with shock tana Ι—an zare ido tace "Ohh, I tot it's my Housemate" Ya mike zaune yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Kin taΙ“a ganinsa da wannan kayan? Ko kuma ina wasa dake ne?" Ta Ι—an langwabar da kai tace "To ai dai bazan san ba shi bane, since you are having the same height and complexion with him" Yace "I could slap you idan baki fita a gabana ba Malama" Ta wani taΙ“e baki ta nufi kitchen, irish ta diba ta fere wanda zata yi using, tana yanke yanken veggies da zata soya kwai da shi a ranta tana mamakin Why Ajay is in the house instead of her Housemate, kawai daga jiya zuwa yau ya mata masifa sau biyu, turo baki tayi ta ajiye wukan sai a sannan ta zaro ido ta dau irish dinta ta zuba a man gyada da ta dora don har ta manta da man gyadan, rufe baki tayi da hannunta jin fire alarm din kitchen din ya dau ruri, gaba daya ta mance da shi, don in dai zata yi soye soye wani lokacin lullubesa take da Shower cap dinta ta yanda bazai yi detecting komai ba balle ya fara tona mata asiri yana ruri, ta juya ta fito daga kitchen din tana kallon Ajay kamar munafuka tace "Don Allah ka zo ka min stopping din alarm din ya dena" Ajay yace "A'a ki dai kona masu gida ni ina ruwana, kin zata a Nigeria kike ba" Ta marairaice tace "Don Allah mana, kaga it's very loud fa" Ko kallon inda take bai sake yi ba, ta juya ta koma kitchen din tana kallon inda smoke alarm din yake, ita bata ma san ya ake kashewa yayi shiru ba, ta rage abun girkin zata sake komawa parlor ta masa magana ta kusa cin karo da shi zai shigo kitchen din, komawa gefe tayi tana kallonsa har yayi silencing smoke alarm din sannan ya fita daga kitchen din, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da girkin da take yi, bayan ta gama ta fito daga kitchen din dama iya wanda zata ci da Housemate dinta kawai tayi, tana kallon Ajay tace "Housemate dina fa?" Bayansa ya nuna mata alamar gashi ya goya shi, juyawa tayi ta wuce sama ya bi ta da wani kallo, tana shiga dakinta ta dau wayarta ta zauna gefen gado tayi dialing number Housemate dinta, yana fara ringing ya daga, in his calm voice yace "Good morning Halysaah" Ta Ι—an yi murmushi kamar yana ganinta ta fara wasa da gefen duvet dinta a hankali tace "Good morning" Yace "How was your night?" Tace "Alhamdulillah, naga baka nan" Yace "Yea i went to get something, i will come over later" Tace "I made some breakfast for you" Yace "Really" Tayi shiru bata ce komai ba don har ranta ta so ya ci breakfast din, yace "Ohk give me 30 mins zan dawo sai in ci" Tayi murmushi har sai da dimples dinta ya lotsa tace "Toh Allah ya kawo ka lafiya" Katse wayar tayi sannan ta mike ta fita daga dakin ta koma downstairs, bata ko kalli Ajay ba tayi wucewarta kitchen ta ajiye ma Housemate dinta nasa breakfast din ta dau nata ta fito, hada ido suka yi ta sauke idonta har zata wuce sai kuma ta Ι—an kallesa tace "There is everything available in the kitchen, idan kana son kayi making breakfast for ur self" Ya juya ya kalleta yace "Kee, ki shiga hankalin ki, ni ba Jay bane" ita dai tayi tafiyarta sama bata ce masa komai ba. Da yammacin ranan Khaleesat na kitchen tana stew taji an danna bell, fitowa parlor tayi amma ta kasa karasawa gun kofar gabanta na faduwa, kaddai Abdul ne ya biyota, tunawa da tayi Ajay na gidan sai kuma taji hankalin ta ya kwanta, amma dai bata karasa gun kofar ba tana tsaye inda take, sama ta kalla ganin Ajay na saukowa downstairs, bai kalli inda take ba ya nufi kofar ya bude, Safiyyah ta koma gefe ganinsa ta fara kame kamen yafa mayafinta tace "Yaya Ajay ina wuni" A takaice yace "Lafiya" still kuma bai bata hanya ba, yana tsaye bakin kofar, Ta Ι—an sosa kai tace "Kwana biyu nace ko laifi nayi maka da ban sani ba Yaya Ajay" Kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace "Kin taΙ“a Ι—aga hannu ke kin mari namiji da har kika zuga kawarki tayi hakan?" Safiyyah ta gwalo ido ta cire handbag dinta a kafada tace "Na rantse da Allah ba da sanina tayi haka ba, ta yaya zan zugata? yanxu ma wallahi zuwa nayi zan mata fadan abinda tayi bata kyauta ba, ita Khaleesat bata jin magana kwata kwata ne, ko ni bazan daga hannu in mari lukeke irin Abdul ba, i am trying my best in dinga sakata a hanya amma abun yaci tura, ka tambayeta wallahi ni bani nace ta maresa ba" Ajay yace "Daga ke har ita za ku san yanda za ku yi da shi duk ranan da ya cafke ku a kasar nan..." Yana kai wa nan ya juya ya bar bakin kofar, Safiyyah ta tura masa maki, sai kuma ta shiga parlon tana gwale ido, ganin Khaleesat a tsaye a parlon sai kuma ta washe baki, suka zauna a nan parlon Khaleesat na tambayarta daga inda take ganin uban gayun da ta ci, kasa kasa take bata labarin Birthday din karen wani coursemate dinsu da taje da yanda masu karnuka ke ta zuwa da nasu ita kuma bata da ko mage balle kare, can tace "Da na sani na su Housmate na ara na tafi da shi wallahi" Khaleesat don takaici ma ta kasa ce mata komai sai kallonta take, Safiyyah tace "Har hotuna fa sai da muka yi da karnuka gwanin ban sha'awa in gaya maki" Khaleesat ta taΙ“e baki ta mike ta tafi duba stew din da take yi, bayan ta fito ta ajiye ma Safiyyah drink din da ta dauko mata ko zaunawa bata yi ba Safiyyan tace "Me jarababben nan ke yi a gidan ki, ina Yaya Housemate din mu?" Khaleesat bata san sanda ta fashe da dariya ba don Ajay yana bakin stairs a tsaye, kamar Safiyyah ta sani ta juya da sauri tana ganinsa ta sinne kai kamar munafuka, dai dai nan Housemate ya shigo parlon, Yana shigowa Ajay ya nufi kofa ya fice alamar dai shi yake jira dama, Safiyyah ta gaida Housemate da fara'arta tana masa sannu da zuwa, ya amsa ya karaso ya zauna parlon yana kallonta yace "Social function kika je ne haka" Tayi dariya har da tafe hannu tace "Eh wallahi birthday din karen wani coursemate din mu na je" Jay yayi murmushi yace "To sannu da dawowa" Tace "Shi ne nace bari in biyo ta nan, kwana biyu ban san me nayi ma Cousin dinka ba sai yayi ta Ι—aga min hanci idan ya gan ni...." Jay ya shafa kansa yace "Don't mind him, wani lokacin haka yake" Safiyyah ta taΙ“e baki tace "Gaskiya abun nasa ba kyau..." Jay ya Ι—aga ido ya Ι—an kalli Khaleesat dake tsaye parlon tana kallonsa kamar ranan ta fara ganinsa, suna hada ido ta tura masa baki ta juya tayi wucewarta kitchen ya bi ta da kallo, duk Safiyyah na kallonsu tana Ι—an murmushi, sai kuma ta rataye jakarta a kafada still smiling tace "To ni zan koma gida Housemate, kafin yayana ya fara kirana" Jay ya maida dubansa kanta yace "Kin jima da zuwa ne?" Tace "Ai ko minti goma ban yi ba, Cousin dinka ne ya bata min mood dina don ban ji dadin abinda yayi min ba, kawai albarkacin ka ya ci yasa na danne zuciyata, har fa da ce min ni nake zuga Khaleesat a America, abun nan ya min ciwo wallahi" Housemate na murmushi yace "Kiyi hakuri, but kinsan me Safiyyah.... Don Allah ko da kun sake haduwa da shi a school kar ki ce zaki yi wani sa'insa da shi" Safiyyah tace "Wai Abdul?" Yace "Eh" Tace "Ai tun da yayana ya hanani ban sake ba wallahi, ko zagina yayi iyaka in kira masa 911 kar yaje ya min wani mugun abu, amma na dena kulasa" Yace "Good...." Mikewa yayi yace "Let me talk to your frnd in the kitchen" Tana Ι—an murmushi tace "Ohk" Kitchen ya nufa bayan ya shiga ya kulle kofar ya jingina jiki ya rungume hannu yana kallon Khaleesat dake goge goge a kitchen din bayan ta gama stew din da take yi, ta kasa juyawa ta kallesa, a hankali yace "Weldone Halysaah" Ta Ι—an yi murmushi kawai, yace "Let drop off your friend at home" Ta gyada masa kai alamar to, yana kallonta yace "Sai mu je park daga can ko?" Sai a sannan ta Ι—an kallesa, sai kuma tayi murmushi ta juya masa, shi dai kallonta kawai yake, after some seconds a hankali yace "Get ready ina jiran ki" Daga haka ya bude kofar kitchen din ya fita, Tsaye ya tarar da Safiyyah tana jiran su fito ta kama gabanta don bata gane irin wannan kallon da taga suna ma juna ba, Jay yace "Ki jira ta shirya sai mu yi dropping dinki a gida" Komawa tayi ta zauna tana murmushi tace "Ai ko Nagode, bari in maza inyi cancelling ride dina" Yace "Idan ta shirya ku sameni a Garage" Safiyyah tace "Toh" Fita yayi daga parlon, Khaleesat na fitowa kitchen Safiyyah ta gaya mata abinda Housemate dinta yace, a tare suka tafi dakin Khaleesat, Safiyyah ta zauna gefen gado tace "I wish i have freedom like you in this country...." Khaleesat tayi murmushi tana duba kayan da zata sa tace "Yanxun ma ai abinda kika ga dama kike yi, gashi har da zuwa birthday din Dog" Safiyyah tace "A'a wallahi, kinsan da yanda na fito yau kuwa, ni da ma ayi sacking Mustapha a wajen aiki su tattara su koma Nigeria" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba, tana fiddo kayan da zata canxa Safiyyah tace "Waow, dadina dake in kika so akwai fashion, kina sa wannan kaya ai har ku dawo gida Housemate bazai gaji da kallonki ba" Khaleesat tace "To bazan sa ba" Zata maida kayan Safiyyah ta tare press din dakin tayi bake bake a wajen tace "Ke dalla wasa fa nake maki" Da kyar Safiyyah ta lallabata ta saka kayan daga karshe, bayan nan still tayi forcing dinta ta Ι—an yi mata light make up a fuska, Safiyyah ta koma gefe ta rike haΙ“a tana kallonta tana nazarin ace ita Allah ya ba kyan Khaleesat irin abubuwan da zata yi a duniya ai sai Allah, can ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace "Kullum kika yi sallah ki dinga gode ma Allah Khaleesat, he created you differently, wallahi you are so beautiful...." Khaleesat ta wani kalleta, sai kuma ta tsaya gaban madubi tana duba abinda zata goge a fuskarta, just eye pencil da powder kadai Safiyyah ta shafa mata, sai lip gloss shi ma lightly, ta ma rasa abun gogewa a fuskar tata, cause there is nothing special, a hankali Safiyyah dake ta kallonta tace "Ji fa lips dinki wani ba sai ya rantse kin shafa jan baki ba kawata, wallahi ki dinga addu'a idan zaki fita don nasan mutane ne daddaya basa tanka ki a zuciya idan kika fita suka gan ki, duk da dai nan kasar kowa ma da hasken sa" Safiyyah ta zaro ido tace "Lahhh, mun bar Housemate dinki a garage tun daxu fa" Khaleesat ta marairaice mata tace "Ni wallahi kunya nake ji Sophie, i am not comfortable with the dress and the make up" Safiyyah tace "Naga jaraba, idan ku ka yi auren haka zaki dinga kunyar tasa?" Khaleesat ta bude baki tana kallon Safiyyah ta ma kasa cewa komai, Safiyyah ta fixgo hannunta bayan ta tayata daukan handbag dinta ta ja ta suka fita daga dakin, har suka fito daga apartment din Khaleesat taki sakin jiki, Safiyya ta karΙ“e makullin apartment din a hannunta tace "Tafi ki shiga mota zan kulle gidan" Khaleesat taki tafiya, haka kawai aje bata kulle kofar da kyau ba Abdul ya samu hanyar shiga gidan, Safiyyah ta gama kulle kofar ta juya tana kallon Khaleesat tace "Don Allah ki dena yin abu kamar yan unguwan ku mana, America fa ne nan" Khaleesat ta kai hannu handle din kofar ta murda taji sa a bude, wani kallo tayi ma Safiyyah ta kwace makullinta ta kulle kofar da kyau, Safiyyah tace "Oho na zata ya kullu, mu je" Tunda Khaleesat ta nufi garage Housemate ke kallonta babu ko kiftawa, Safiyyah da taya bera bari ta bude mata front seat tana murmushi, Khaleesat ta wani kalleta sannan ta shiga motar ba tare da ta bari sun hada ido da Jay ba, Safiyyah ta koma bayan motar ta shiga, he wants to compliment her amma yayi shiru saboda Safiyyah, ya fara driving yana kallonta lokaci lokaci, daga karshe ya kasa hakuri yace "You look beautiful Halysaah" Safiyyah dake bayan motar ta fara blushing kamar ita aka ce ma haka, tana Ι—an murmushi tace "Nima na gaya mata wallahi, amma ta zata am just pulling her legs, nace mata kyanta na daban ne a cikin kyawawa, duk mijin da ya aureta ya more a rayuwa, ko bacin rai yake ya kalleta zai ji ransa yayi fari Ζ™al, kuma ace ta samu miji me kyau kamar yanda dae kake din nan, waiiiii Allah kadai yasan yanda kids din ku za su zama don kyau..." Khaleesat taji da ma kawai hakura tayi da fitar nan gaba daya tsabar kunya, shi kam Jay murmushi kawai yake idonsa akan titi yana driving, Safiyyah ta bude jakarta ta ciro wayarta ganin Mustapha ke kiranta ta danna wayar a silent a fusace ta mayar cikin jaka, Jay ya kalli Khaleesat yayi kasa da murya yace "Wani park din kike son mu je?" Karaf a kunne Safiyyah, tace "Park za ku je Yaya Housemate" Yace "Yeah Safiyyah" Safiyya tace "To aje da ni mana don Allah sai in zama photographer" Khaleesat ta dafe kanta, Jay na murmushi yace "To nawa za a biya ki for the Job?" Ta kyalkyale da dariya tace "Haba, ko er lemonade ne kawai a siya min" Yana dariya yace "To an gama, amma baza a kira ki a gida ba?" Tace "A'a ba wanda zai neme ni wallahi" Ko da suka isa park din Safiyyah taki yarda ta zauna kusa da su Khaleesat wai za su yi inconveniencing dinta tana son ta nutsu tayi enjoying ambience din wajen da kyau, Khaleesat tasan duk scope din barin ta daga ita sai Jay ne yasa Safiyyah tace haka, shi ko Jay yaji dadin hankalin da Safiyyah tayi a nan, hotuna tace zata fara masu kar yamma yayi sosai, dadi kamar zai kashe Safiyyah ganin azababben kyan da hoton da ta fara masu yayi, can ta karasa inda suke tsaye tace "Ba fa wanda zai tsaya a space din nan da ku ka bari a tsakaninku gwara ku cike sa kawai" Khaleesat ta wani kalleta, Shi dai Jay Murmushi kawai yayi, Safiyyah tace "Ka Ι—an matsa kusa da ita kadan Yaya Housemate so that the space won't make the picture look somehow" Slowly ya matsa kusa da Khaleesat yana kallonta yana murmushi, Khaleesat ta ganta er karama a kusa da shi ga daddaden kamshin turarensa da ya cika ta, tuni Safiyyah ta koma baya da gudu ta ci gaba da daukan hoton da take tana washe baki, farin ciki kamar ya kasheta, haka ta dinga controlling dinsu wajen daukan hotunan, tace su koma can, tace su dawo nan, ta tabbatar tayi masu hotuna masu bala'in kyau, har dai daga karshe Jay yace mata ya isa ita ma ta shigo su yi hoton, zai ba wata er Africa dake wajen wayarsa ta masu hoton har Safiyyah amma Safiyyah taki shiga tace "A'a kar in bata maku hoto ina baΖ™a da ni" Dariya Housemate yayi haka dai ya lallabata ta shigo aka yi masu hoton su uku, Safiyyah na murmushi tace "Amma fa tunda nake daukan hoto ban taΙ“a daukan wanda ya dauku kamar hotunan nan da na maku ba wallahi" Jay na murmushi yace "Dollar nawa za a baki to?" Dariya tayi ta tattara lemonade dinta da tacos da ya siya mata tace "Wannan ma da aka siya min Allah ya amfana" Daga haka ta kara gaba ta bar masu wajen, Jay was amaze at how Safiyyah snapped the pictures so well, ya kasa daina kallon Khaleesat a hoton, the pictures where so beautiful, Khaleesat tun da ta kalli hoto daya ta kasa ci gaba da kallon sauran ta koma ta zauna kawai, after a while ta daga ido ta Ι—an kalli Jay taga kallonta yake, da sauri ta maida kanta kasa, a hankali yace "Halysaah" Bata dago kanta ba still tace "Uhm" Yace "Me yasa baki sakin jiki da ni yanxu? You weren't like this before, ko don nace zan aure ki?" Sunkuyar da kanta tayi alamar kunya, yace "To meye amfanin zuwa nan tunda baza ki saki jikin ki ba, i want us to have a quality time together amma kiyi ta sunkuyar da kai...." Tana murmushi a hankali tace "To ai kunya nake ji" Yace "To kalleni zaki dena jin kunyan" Taki dagowa tayi shiru, yace "Halysaah" Tace "Ni bazan iya ba" Bai sake ce mata komai ba, ganin haka ta daga idanuwanta ta kallesa taga kallonta yake, murmushi yayi mata murya can kasa yace "You are specially made Halysaah" Rufe idonta tayi tana murmushi a hankali tace "Thank you" Yace "Kin dai ji me kawarki ta ce ko?" Khaleesat ta daga ido ta kallesa tace "Me ta ce?" Yayi kasa da murya yace "We will make beautiful Babies together...." Khaleesat ji tayi wani azababben kunya ya rufeta, yana murmushi yana kallonta yace "Ni ko guda daya kika bani me kama dake i will appreciate..." Kamar zata yi kuka tace "Ni dai mu tafi gida" Yace "A'a sai kin ban labari, kina ban labari ko daya ne sai mu tafi" Shiru tayi, sai kuma tana wasa da straw din drink din gabanta tace "Wani irin labari?" Yace "Ko ma wani iri ne, ko kuma ki bani labarin yanda ku ka hadu da Funny frnd dinki Safiyyah" Khaleesat tayi murmushi ta dago kai tace "Ohk...." Babu bata lokaci ta fara basa labarin farkon haduwarta da Safiyyah a school, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawan kirki baya yi, everything about Khaleesat is just beautiful and breathtaking, tsakaninta da Allah take ta basa labarin Sophie ashe ko sanin abinda take cewa bai yi ba ya kafeta da ido with many imagination running his mind, daga bada labarin Safiyyah kawai ta saki jiki a wajen, dama kuma haka yake so... kamar yanda ya so hakan ne ya faru don they had a wonderful time together, labari sai wanda ta manta ne bata basa ba a kan experience dinta a America tun daga shekaran da ta zo har zuwa yanxu, wani yayi dariya, wani yaji tausayinta wani ya ga wautan ta, babu abinda ya kara burgesa da ita tana basa labarin sai turancin ta, she was so vocal, duk da timidness dinta she was very outspoken kamar ba a unguwan nan da gidansu yake ta tashi ba, he never knows she speak so well sai yau, yayi kasa da murya yace "You know what Halysaah?" Ta girgiza masa kai tana kallonsa, a hankali yace "I love you so much" Rufe fuskarta tayi da sauri tana murmushi... Sai wajen karfe bakwai suka bar park din, sai da suka fara dropping Safiyyah a gida before heading home, Jay na parking Khaleesat ta kalli motar Ajay dake parking Space, can ta kalli Jay tace "Is he waiting for you?" Jay yace "I don't think so, kinsan yana da aboki a Neighborhood din nan shi ma PhD yake, the frnd is at the far end of this street, External defense dinsu is around the corner...." Khaleesat tace "Ohk har da kai?" Jay yace "Yea in sha Allah, period din exam din ku ne Defense dinmu" A hankali tace "To Allah ya baku nasara" Yana murmushi yace "Ameen" Tace "To a ina zaka yi parking since he is occupying the space?" Yace "Zan je gida in dawo anjima" A hankali tace "To ni kadai a apartment din?" Yace "Ga motar Ajay kina gani, ai yana ciki kenan" Shiru tayi tana kallonsa, ya mata murmushi yace "Mu je in raka ki ciki to" A tare suka sauka daga motar ya rakata har cikin apartment din, yana kallonta calmly yace "Can i go now?" Jingina tayi da bango a kusa da shi ta langwabar da kanta kawai ta marairaice tana kallonsa, ya sauke idonsa daga kallonta trying to calm his self down, a hankali yace "I need to go Halysaah, ki kulle kofar" Daga haka ya juya ya fita daga parlon without looking at her, ta bi sa da kallo kafin ta kulle kofarta....

 

 

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment  07087865788 πŸ‘ˆπŸ», it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

 

 

 

 

Bayan Khaleesat tayi karatun da zata yi ta kashe laptop dinta ta ajiye sannan ta saka hijab ta fito daga dakin don tun da ta dawo bata ci abinci ba gashi har karfe goma ya wuce, downstairs take leke ko zata ga Housemate dinta, Ajay ta gani yana danna wayarsa, hannunsa rike da Can din soft drink, tana ta tsaye a corridor din don da ba don yunwan da take ji ba komawa dakinta kawai zata yi ta hakura da abincin, after a while ta fara saukowa staircase din trying not to make any sound, tun daga nesa take kallon screen din wayarsa ganin kamar hoton da suka yi da Jay daxu a park, tsaye tayi tana ta kallon wayarsa da mamaki, after some seconds taga ya fita daga hoton kasa gane inda ya samu hoton tayi, tasan dai Jay bazai tura masa pictures din ba, to kaddai a status Housemate dinta ya dora hoton, ta shiga uku, sosai taji gabanta ya fadi, lokaci daya Ajay ya juya bayan yayi sensing kamar mutum na tsaye bayansa, ta Ι—an koma baya kamar munafuka tana kame kame tace "Kitchen zan je dama" Ajiye wayarsa yayi ya juya da kyau yana kallonta da mamaki, ta langwabe kai sai kuma ta nufi kitchen din da sauri tana Ι—an waigen sa, ko da ta fito bata gansa a parlon ba, bayan ta koma daki ta ajiye shayin hannunta ta dau wayarta da sauri ta bude WhatsApp dinta, status din Housemate dinta ta bude taga hoton amma ya rufe fuskarta with the caption "Halysaah" da yayi ma hoton, to amma wanda ta gani a wayar Ajay fuskarta a bude yake, ta dinga kallon hoton duk da fuskarta a rufe yake, bata san sanda murmushi yayi escaping lips dinta ba don sun yi kyau sosai, har ta ajiye wayar sai kuma ta dauka tayi masa reply din picture din tace "What if gal frnd dinka ta gani" ajiye wayar tayi ta dau cup din shayin da ta ajiye tana juyawa a hankali, taji wayarta yayi vibrate alamar shigowar message, daukan wayar tayi taga ya mata reply yace "Ke ba Gal frnd dita bace? Ai ke zabina ce, ita kuma zabin iyayena" Hmm kawai ta mayar masa sannan ta kashe data dinta ta ajiye wayar, lokaci daya duk jikinta yayi sanyi tana maimata zabin iyayensa da yace a ranta, duk yunwan da take ji haka nan ta neme sa ta rasa shayin ma bata wani sha sosai ba, bayan ta gama shirin kwanciya ta dauro alwala ta fito sannan ta kashe wutan dakin ta kwanta, wayarta taji na vibrate ta jawo wayar a hankali tana dubawa taga Housemate dinta ne ke kiranta, sai da ya kusa katsewa tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, yace "Why did you go offline Halysaah?" Ta Ι—an yi murmushin karfin hali tace "Na je nayi alwala ne zan kwanta" Yace "Ohk, kina da class gobe ne?" Ta Ι—an yi shiru, duk da bata da shi tace "Eh ina da...." Jay yace "Yaushe?" Tace "Da safe" Yace "Ohk, na tsaya wani aiki ne a system dina shi yasa ban dawo ba, may be we will meet in school tomorrow in sha Allah" Tace "Allah ya kai mu" Yace "Ameen, Good night Halysaah, naga kamar kin fara jin bacci ko?" Cikin sanyin murya tace "Uhm, sai da safe" Yace "Allah ya kai mu lafiya" Daga haka ya katse wayar sa, Khaleesat ta ajiye wayar hannunta ta juya ta lumshe ido. Da safe Khaleesat na saukowa downstairs taga parlon soo tidy, kamshi sai tashi yake ta ko ina via diffuser da ta gani a parlon, makalewa tayi jikin staircase tana ta kallon parlon, ai kuma ta shiga uku da gori, after a while ta nufi kitchen, ta window din kitchen din take kallonsa don karamin garden ne a waje, entrance din garden din yana ta wajen Garage, tunda ta zo apartment din bai fi sau biyu ta shiga wajen ba, press up yake yi a wajen, juyawa tayi ta kalli Yoghurt da diff kind of berries da granola da nuts sai kiwi and apple dake ajiye kitchen din, nan ta gane parfait zai hada, har zata hada masa wata zuciyar tace ta kama kanta tayi abinda zata yi ta fita, noodles ta dauko zata dafa, tana cikin dafa noodles din ta daga kai taga ya fita daga garden din, bayan ta gama girkin ta fita daga kitchen din zuwa dakinta, after almost 20 mins ta sake saukowa downstairs ta shiga kitchen din, har sannan fruits din suna wajen, ta Ι—au karamin bowl ta fara tsinkar different berries din wajen ta yanda bazai gane ta taΙ“a masa ba, tana wankesu a sink ta fara sha, da sauri ta juya tana kallon kofar kitchen din tayi ido hudu da shi, ita kanta bata san dalilin da yasa ta fara dariya ba, ta ciro berry din da ta kai baki tace "Wanke maka su zan yi fa, so that i can help you dice them" Tana fadin haka ta ajiye bowl din hannunta ta dau wuka zata fara fere Kiwi fruit dake wajen, taji yace "Zo ki fita ki ban waje" Ta Ι—an kallesa tace "I want to help you wash them...." Tana ganin kallon da yayi mata, ta ajiye wukan ta wanke hannunta a sink sannan ta ajiye masa bowl din Berries din da ta diba a kofar sauran fruits din, kofa ta nufa ta bi gefensa ta fita daga kitchen din ya bi ta da kallo yace "Ke da baki iya gyaran gidan da kike ciki ce zaki wanke ma mutum abinda zai ci" Khaleesat ta juya ta kallesa dama tasan sai yayi maganar nan, tace "Tun da kai ka gyara ba shikenan ba, ai don ina zuwa school ne...." Yace "You are dirty dai Malama, do not use school to cover ur untidiness" Yana fadin haka ya karasa cikin kitchen din, ta tsaya bakin kofar tana kallonsa taga ko da Liquid wash zai wanke fruits din karewar tsafta, sai da ya fara tura bowl din Berries din da ta diba zuwa can far end of the kitchen yanda bazai dinga ganinsa a kusa da shi ba sannan ya fara wanke fruits din a sink, bayan gishiri har da Venegar yayi using wajen wanke fruits din, a ranta tace to ai wannan ba sabon abu bane kowa na yi, ita tsakaninta da Allah take jiran taga ya zuba liquid wash wajen wanke fruits din, amma taga bai yi hakan ba, tana ta tsaye jikin kofar kitchen din har ya gama hada lafiyayyen parfait dinsa, ta shiga kitchen din ta dau bowl din Berries dinta da ya gantalar gefe daya ta ajiye kusa da shi ta kallesa, ko kallonta bai yi ba, can ta ga ya jawo sauran Yoghurt da ya rage ya tsiyaya mata a bowl din ya ci gaba da abinda yake yi, dariya ya bata amma ta dake bata yi ba, tana ta kallon rich parfait dinsa da yaji fruits da Granola da Nuts, tana kallo ya dau zuma ya tsiyaya a kai, dai dai nan aka bude kofar parlor, ya ajiye zuman hannunsa ya karasa kofar kitchen din don ganin wanda ya shigo, da sauri Khaleesat ta kai hannu ta lakaci honey din da yoghurt, akan idonsa don har ya juyo ya dawo cikin kitchen din, komawa baya tayi da sauri, bai ko kalleta ba ya dau spoon yayi scoping dai dai inda ta saka hannu sannan ya ajiye spoon din a sink, ita dai bata san ya aka yi ba kawai ganin bowl din parfait din tayi ya kife a kasan kitchen, ya koma baya yana kallon parfait babu ko kiftawa, tun tana daurewa har ta kasa ta dafe base cabinet din kitchen din ta tuntsire da dariya kamar an aikota, Ajay dai kallon Parfait din kawai yake a kasan kitchen din, after some seconds ya shafa kansa trying not to laugh too, don dariyarta kadai ya isa ya saka mutum yayi dariya bai yi niyya ba, irin dariyar muguntar nan kawai take yi, ita kuwa ba abinda ya bata dariya ganin bai tsam mata ba gashi duk sun tuntsire a kasan kitchen, kuma shi ya kifar da kayansa da alama, kawai ya juya ya fice daga kitchen din ta bi sa da kallo tana kyalkyala wani sabon dariya, sai kuma ya sake dawowa yana kallonta yayi kasa da murya yace "Kin ga idan ina abu a kitchen kika sake shigo min i will fling you out of this window, ai ni ban san ke mayya bace" Yana fadin haka ya sake ficewa daga kitchen din, Khaleesat dai bata fasa dariyan da take ba, da ta kalli bowl din da ya Ι—an tsiyaya mata zallan yoghurt sai ta kalli rich parfait dinsa dake kasan kitchen a kwance, sai ta kara kwashewa da dariya, ta dade abu bai bata dariya kamar haka ba, tayi dariyarta ma'ishi sannan ta fara gyara kitchen din, sai kuma ta fara jin tausayinsa don duk effort dinsa bai sha ko spoon daya ba, gwara ita ta Ι—an lasa zuma da yoghurt, the incident was so funny to her, haka duk ta kwashe fruits din da granula dake kasa tayi disposing a shara, bayan ta gama goge kitchen din ya dawo fess ta fito parlor taga Housemate dinta zaune a parlon yana danna wayarsa, tana murmushi ta karasa cikin parlon ta zauna sannan ta gaishesa, ya daga kai ya kalleta ya amsa, bata sake cewa komai ba, shi ma haka, after a while yace "Ba kince zaki school da safe ba?" ta langwabar da kai tace "Kawai fasawa nayi" Juyawa tayi ta kalli Ajay dake saukowa downstairs fuskarsa babu yabo babu fallasa yana rike da makullin motarsa, ta bi sa da kallo trying not to start another laugh har ya fice daga parlon, sai kuma ta kalli Jay ta fara basa labarin abinda ya faru a kitchen, she couldn't hold her self anymore ta dinga kyalkyala dariya har da saukowa daga saman kujera, shi dai Jay kallonta kawai yake, sai kuma ta dena dariyar da take tace "Isn't it funny?" Jay yayi murmushi wanda iyakarsa lips yace "It is, sai yace maki me?" Tace "He was very shock too, nasan da ya san abinda zai faru kenan da ya debar min, Allah ne ya kamasa, ga shi yayi stressing kansa ya gyara gidan nan gaba daya yau" Tana dariya ta kare maganar, Jay yace "Gaskiya ne, amma baza ki je school ba me yasa kika ce min za ki je?" Shiru tayi, sai kuma tace "Kawai da gari ya waye na canza mind" Jay yace "Ohk" Wayarsa ne ya fara vibrate ya mike yace "Zan fita sai anjima" Khaleesat na kallonsa tace "Kayi breakfast ne?" Yace "Nayi" Tace "Ohk, byee" Juyawa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita.... Khaleesat na kitchen da yamma bayan ta dawo school taji an bude kofar apartment dinta, sosai taji gabanta ya fadi don dama tunda ta dawo taga ba kowa apartment din take a tsorace, sai da taji muryar Ajay a parlon sannan hankalinta ya kwanta, jingina tayi jikin cabinet din kitchen din tana kirga kwanakin da taga Jay last, after a while ta kashe wutan girkin don ta gama, ta dan leka parlon taga Ajay da wani abokinsa ne bayerabe yana gwada masa abu a Laptop dinsa da alama shima Phd yake yi, fitowa tayi daga kitchen din ta gaida abokin ya amsa yana kallonta, sai kuma ya kalli Ajay yace "Is she ur sister" a takaice Ajay yace "Yeah" Yana ci gaba da nuna masa abinda yake nuna masa, da broken English abokin yace bazai basa ita ya aura ba, Ajay ya daga kai ya kalli Khaleesat yace "Ke dalla malama wuce ki ba mutane waje" Khaleesat ta kallesa da mamaki don ita dai ba tsayuwa tayi a parlon ba, sama ma zata wuce, Femi na kallon Ajay yace "I am very serious Prince, i will marry her as far as una go give me, she's very beautiful, is she Halfcast?" Ajay yace "Meet Jay about that Femi" Femi ya gyara zama yace "Jay no get joy at all, he isn't as straight as you" Ajay yace "He will listen, since it's about you marrying his sister..." Femi yayi dariya sosai yace "I will definitely visit Bauchi soon be that" Ajay dai bai sake ce masa komai ba.

A kwana a tashi lokacin Exams din su Khaleesat ya matso don satin da za su shiga za a fara jarabawan, tun ranan da ta mari Abdul har zuwa yau bata sake ganin ko giftawarsa a school din ba, ita dai har sannan hankalinta yaki kwanciya don gani take kawai jira yake ta koma Nigeria before doing anything to her, sosai tayi da ta sanin marin da tayi masa, she wish bata yi hakan ba, da kawai ignoring dinsa ta dinga yi since he is not harming her, da ta tuna sati biyu kawai za su yi suna jarabawan sannan ta koma Nigeria sai taji jikinta yayi sanyi sosai, During all this time haduwanta da Jay ya ragu sosai ba kadan, ko apartment din nata sai in zai kai mata abu yake zuwa kuma ba dadewa yake yi ba, but tayi masa uxuri tunda yace mata su ma a wannan period din ne External defense dinsu may be he is concentrating on that and also giving her space to concentrate on her own studies too, amma abinda ke bata mamaki kafin taga Ajay da laptop ko wani abu da zai nuna karatu yake sau daya to ta gansa da remote din TV da bowl din fruit yana ci yana kallon football ko wrestling sau goma, gashi kamar baya bacci, abokansa kuwa in suka xo baya shigowa da su apartment din.... Ranan Friday Khaleesat na school tare da Safiyyah suna studying course din da za su yi exams dinsa ranan Monday, hadari ne sosai a garin, Khaleesat tace "Mu je apartment dina sai mu ci gaba da karatun a can ko?" Safiyyah tace "Tabb, ni ce zan je apartment din ki wannan Uztaz din na nan? Ni har yanxu kin ki gaya min dalilin da yasa suka yi switching da Housemate din ki" Khaleesat na kallonta tace "To ta yaya nima zan sani, na tambaye Housemate dina yace kawai sbda he is busy because of his upcoming defense ne baya samun time sosai he is always in the Library" Safiyyah tayi dariya tace "Shi kadai zai yi defense din? Shi ma Ajay ba defense din zai yi ba ko ba lokaci daya za su yi bane? Ni har na gano dalilin da yasa yaki zama a apartment dinki wallahi" Khaleesat tace "Meye dalili?" Safiyyah tayi dariya tace "Gaskiya na kara respecting Housemate dinki, wallahi iya da addini da sanin ya kamata, kinga a baya ai babu komai tsakaninku shi yasa ku ke zaune kowa na harkar gabansa a tsohon Apartment din ki, iyaka kuyi mutunci, yanxu kuwa da ya fara son ki yana tsoron kada shaidan yayi using Opportunity din zaman ku gida daya ya cuce ku, kinga hakan bazai haifo Ι—a me ido ba, gaskiya yaya Housemate iya da addini" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba sai ma murmushi da tayi kawai, Safiyyah tace "Abinda ya guje ma kenan kawai ba wani abu ba, don shi zuciya ba shi da Ζ™ashi, shi kuma Ajay masifarsa da fitinarsa kadai ma bazai sa ya shiga harkar ki ba a gidan, shi fitinarsa ma zai iya zuke mutum wallahi" Khaleesat na maida wayarta cikin jaka tace "Sai ka masa abinda baya so yake masifa ai, he just love being on his own kar a shiga harkarsa that's all, but he is kind, caring and down to earth, sai da muka zauna yanxu na gane haka" Safiyyah ta saki baki tana kallonta, can ta gyara zama tace "Ikon Allah, yau ke kike yabon Ajay da kanki, to me da me yayi maki da kika ga he is caring and kind zaman ku a apartment din naki" Khaleesat ta daga ido ta kalleta, can tace "Kilan baza ki yarda ba idan na fara gaya maki wallahi" Safiyyah tace "Ai ina jin ki, gaya min yanda aka yi kika gane hakan in ga ko zai yi convincing dina..." Wayar Khaleesat ya fara vibrate a jaka, ta bude jakar ta ciro wayar, Safiyyah ta leka screen din don ganin me kiranta, sae kuma ta riΖ™e haΙ“a tace "Ikon Allah"

 

 

 

_Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda Ur evidence_

07087865788

 

 

*Hakika duk wacce ta Bari aka barta abaya ita taso domin mu mata da ado da kwalliya aka  sanmu.                                  Assalamualaikum, barkanmu dai Yan uwana ma masu albarka, ayau na zo maku da batun  sababbin kayan da na kawo Mana masu matukar kyau da kuma inganci,oum eman collection 🀝😍, takawo maku jakunkuna da takalma,hadi da abayas da kuma sarkoki masu matukar kyau da kuma sauki,07018872587               Ena amare da uwayan gida masu capacity's toh duk wacce ta yarda da tacika mace da wacce takeso ta zamo ma abociyar kwalliya toh ta garzayo gunmu domin hadewarki cikin ado da kwalliya kedai nemeni a wannnan number domin kisami kayayyaki masu kyau da kuma quality akan kudi kalilan hajiyata 07018872587 ngd 🀝 ado da kwalliya shine takenmu*