𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 1
𝘼𝙢𝙗𝙞𝙩𝙞𝙤𝙣
& 𝙨𝙪𝙘𝙘𝙚𝙨𝙨
𝙈𝙪𝙝𝙖𝙢𝙢𝙖𝙙
𝙛𝙪'𝙖𝙙 𝙟𝙖𝙙𝙙𝙖
"Hustle until you no longer need to introduce yourself,push your self because no one else is going to do it for you". Kalamansa na qarshe kenan da tarin mayan attajiran da sukayi meeting na qarshe dasu wanda keson saka share dinsu cikin sabon kamfanin da kwanaki bakwai suka rage masa ya budeshi. Kalamai ne da suka dauki hankulan mutanen dake wajen,wanda dasu aka kammala zaman.
Sanda
yake sallama dash fiye da rabin hankalinsa yana kan wayarsa da tun dazun ya
lura tana haske. Sai da gurin ya rage saura shi daya da hudu daga cikin guard
dinsa da wannan karon dasu yayi tafiyar wadanda ke nesa da inda yake,ya miqa
hannu a nutse yana jawo wayar gami da fesar da iska me dumi daga bakinsa. Cikin
kowanne motsi yana jin farinciki na yadda al'amuran bude kamfanin ke gudana da
dukkan wani haske qyalli da kuma alamu na nasara,bai taba qwallafa rai akan
wani abu kaman haka ba,baisan me yasa dukka tunaninsa da hankalinsa suka raja'a
wajen son ganin cikar wannan mafarkin nasa ba. Tunda yazo samu cikakken zama na
awa biyu cur ba,saidai idan dare yayi ya wafci wasu awanni ya tilastawa kansa
kwanciya ya huta. Kowanne minti idan ya shude da amfaninsa a wajensa,ko baya
din dama shi mutum ne me girmama lokaci tare da bashi muhimmanci qwarai.
Sunan
farouq kawai daya gani ya sakashi gyara zama yana furta
"Ya salam" Qasa qasa fuskarsa nason fidda wannan
sihirtaccen murmushin nasa da ba kasafai ake samun dacen ganinsa ba. Wani sirri
ne kwance cikin murmushinsa dake qara masa haiba da kwarjini da fitar asalin
kyan da ubangiji ya huwace masa. Yasan zayasha qorafi ne kawai wajen farouq
din......don yace masa zai kirashi har baisan adadi ba......hakanan bazai ma
iya tuna awar qarshe da sukayi waya ba.
"Hala baka da wani abu me muhimmanci cikin rayuwarka
sama da business dinka?" Kalmar da farouq ya fara jera masa kenan.
Boyayyen murmushi ya saki yana daga dogayen qafafunsa ya aza saman dunqulallen
table din gabansa me azabar kyau. Wani irin shaquwa da fahimtar juna ce
tsakaninsu dake sanyasu iya fahimtar mode din juna koda basa kallon fuskokin
juna. Yasan zaiji fiye da haka ma a bakin farouq din,don muryarsa a dake take
da alama har kan fuskarsa akwai alamu na qosawa
"Idan ka cire ku family na.......tabbas ba abinda ya
fishi muhimmanci cikin duka kaf rayuwata".
"Aurenka da yarinyar su a wanne muhalli ka
sakasu?....." Ya sake masa tambayar kansa tsaye cikin salo na kaiwa maqura
da son masa titsiye.
"Aure?....yarinya?" Ya maimaita maganar har ga
Allah cikin son neman qarin haske.
"Eheeennn" Farouq ya fada a taqaice,cikin ransa
yana jin rainin hankalin jadda yana neman fin qarfin tunaninsa muddin ya gaya
masa ya manta da lamarin auren dake gabansa.
"Mmtsewww......au" Fuad ya furta wani siririn
murmushi yana sake qwace masa. Sai a yanzun kwanyar tayo masa tariyar karatun
baya na abinda ya baro a nigeria. Kusan gaba daya sabgar ta shafe daga
tunaninsa,abinda ya sanya a gaba ya mamaye tunanin komai daga kansa.
"Am sorry......kasan halin......"
"......halin mijin aljana.......zata sakashi ya aikata
fiye da haka ma,saidai alhmdlh.....duk abinta a wannan karon munci
qarfinta,kuma in sha Allah dan uwana bazai mutu babu aure ba". Dariya
sosai ta qwace ma fu'ad din ganin yadda farouq din ke maganar very
serious,abinda ya jima baiyi ba,ya rasa abinda yasa suka damu da auren
nan......ya fuskanci gaba dayansu murna suke dashi.....ya karanci dukkaninsu
sun daukeshi serious kuma da gaske suke lamuran baki daya.....ciki harda MAAMAH
duk da akwai qatotuwar ayar tambaya a kanta......don ya sani,koda yaushe ita
ungulu bata jewar banza.
"Ka duba email dinka na sauke maka saqo......ka duba
urgently"
"Alright" Ya amsa masa suna katse wayar dukansu.
Yasan tsaf
xaya iya mancewa idan bai duba saqon yanzu ba kaman yadda farouq ya buqata. Don
haka kanshi tsaye ya bude email dinsa. Baibi takan sabbin saqonni da ya fahimta
kaman akwaisu ba,kanshi tsaye ya bude saqon farouq din.
Daya bayan
daya yake bin hotunan daya turo da kallo ba don yana fahimta can can ba. Hotuna
ne na style readymade na kayan maza masu azabar kyau da aji da wani fitaccen
kamfanin fidda readymade suturu ke samarwa. Company ne da sanya suturar data
fits daga cikinsa sai wane da wane......sai mutanen da suka amsa sunan shegu ne
su ta fannin kudi da dukiya.
A idanu
kayan sunyi kyau,saidai shi baisan me zaiyi dasu ba,don haka ya jawo daya wayar
tashi ba tare daya dauke dubansa daga kan hotunan kayan ba ya dannawa farouq
din kira.
"Am coming" Abinda yaji farouq din ya fara fadi
kenan da alama yana magana da wasu ne daga gefe
"Have you seen it?" Idanunsa ya lumshe kadan
sannan ya budesu
"Yes I have.....but bansan me zanyi dasu ba......hala
ka fara preparation na bude garment company ne?". Wani qululun takaici ya
tsayewa farouq a wuya,seriously mutumin nan da gasken gaske yake ya fara
mantawa da cewa aure zaiyi. Duka ya sakar masa ragamar komai a hannunsa ba tare
da damuwa ko tambayar ya ake ciki ba ko meke faruwa ba.
"Na rantse da Allah sa'arka daya baka kusa
dani......shin wai ka manta yarinyar mutane da zaka aura wadda ka kaiwa
sadaki?,in all likelihood ka samu memory formation right?" . Wannan karon
ma saida sautin dariyarsa ya isa har kunnen farouq
''Calmdown mana dude......abun yayi zafi ne har haka?"
"Yama fi haka zafi" Ya fada yana jin ya tuqewa
halin fu'ad din.
"To am sorry......amma dai ka sani......ina da abubuwa
masu muhimmanci da yawa a gabana.....kai din kuma wakili nane a ko ina......duk
abinda ya dace ka zartar ka zartar....na baka wuqa da nama" Ya fada
calmly,don bayason ya sake tunzura farouq din,tunda yana ganin yana iya bakin
qoqarinsa a abinda shi a nasa ganin baikai muhimmanci da suke bashi ba. Dan
shurun da farouq din yayi da yadda ya sauke numfashi ya tabbatar masa fushinsa
ya sauka,dama ko can basa wani dogon fushi da juna,da farouq ya zazzage abinda
ke cikinsa shikenan,shine dama me yawan kauda kai.....zaka jima kana masa abu
amma miskilancinsa bai bari ya nuna maka har kasan kana masa ba daidai ba,har
sai sanda ya gama taraka tukunna.
"Kayi magana dasu abdulghafar......for now ya kamata su
sassauta tsaronsu akan yarinyar"
"For what reason?" Fu'ad ya maida masa kanshi
tsaye yana gyara zamansa sosai saman lallausar kujerar da yake zaune akai.
"Ina ganin kaman ya kamata ta sake.....duk da dama dole
ka bata security da guard,ko don yanayin halin tsaro da qasar ke ciki,sannan
zuwa yanzu ta zama part of us......wanda duk xai d'amfara da sunanmu dole a
bashi tsaro"
"Forget about it farouq......she's gonna be able to do
what you....." Sai kuma ya fasa qarasawa yana jan siririn tsaki. Shi sam
sam koda sau daya bai taba jin wani abu da yayi kama da yarda ko gasgata
yarinyar ba.....akwai abubuwa da yawa da uake suspecting a kanta,wanda ya sake
qaruwa tun daga lokacin data bayyanar masa a mazaunin ZABIN MAAMAH.
"Do you have concern about her actions?" Farouq ya
tambayeshi yana tattara masa hankalinsa.
"Manta kawai......mu ajiye wannan,baka tambayeni akan
komai ba dude?". Yayi maganar calmly kaman zancan business din yafi bashi
peace akan batun auren.
"Akan komai?,akan business dinka?,wannan shine kadai
damuwarka?"
"Wani abu daban daya kamata na damu dashi sama da
haka?". Numfashi sosai farouq yaja,yana tsoron yadda fu'ad gaba daya baya
bawa harkar nan muhimmanci,yana tsoron faruwar wani abu......careless din yayi
yawa har haka,yana jin kamar ya kashe wayar kawai,to amma ya sani wannan shine
abu na qarshe da zaiwa fu'ad ya bata masa rai,ya tsani a kashe masa waya sam
sam.
Yadda yake
masa bayanin nasarorin da sauran abinda ya rage ya sake bashi tabbacin business
dinsa shine gaba da komai. Sunyi magana har ta kusan awa guda kafin su yanke
sadarwar dake tsakaninsu.
Sanda yake
qoqarin minimizing email din idanunsa suka sauka kan wani sabon adreshin email
din dake dauke da sabbin saqonni guda uku,kamar zai share ya wuce sai baiyi
hakan ba,ya danna ya budeshi ya fara bin saqonni da kallo.
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 2
Kallon farko
zaka fahimci ya bada dukka hankalinsa akan abinda yake ganin gilmawarsa cikin
wayar tasa. Saqonni ne kusan guda uku,kala daban daban,saidai kuma kowanne saqo
daya yakeson isar masa.
_mr muhammad jadda,You hereby warned to stop all activities
related to lunching your company_ saqon farko kenan.
A nutse ya
sauke idonsa zuwa ga email na biyu
_Not heeding this warning may put your personal and
professional assets at risk_ . Sake matsawa yayi zuwa saqo na uku shima still
dai kakkaifan jan kunne ne zalla a cikinsa.
_Ignoring this warning may lead to financial losses and
reputational damage_ still dai qasansa shima wani saqonne
_Proceed with caution,as this may have unintended
consequences_.
Tsam
yayi da ransa,yana sake bin saqonnin daki daki yana bitarsu. Wannan wanne irin
barazana ce haka me girma?,daga wanne sashe ta bullo?,su waye keda alhakin
aiwatar da hakan?.
Ya jima da
sani......ba sanin jiya ko kuma yau ba.....sana'arshi sana'a ce dake dauke da
tarin hamayya gogayya da kuma abokan adawa na sarari dana boye,wani irin
matsayi ne da Allah ya bashi wanda bai taba tunanin samuwarsa a qananun shekaru
irin nashi ba. Akwai tarin mutanen da suka fishi jimawa cikin harkar.....saidai
har yanzu basu samu irin nasibin daya samu ba.
Gyara
zamansa ya sakeyi da kyau yana furzar da iska daga bakinsa. Ya sani,zai iya
bincike akan ainihin adreshin,saidai kuma yasan zai wahala ya iya reaching
komai akai koda yaso samun haka. Beside ma,isn't the first time daya fara samun
ire iren wadannan saqonnin,wanda daga qarshe yake cimma daga wanne waje suke?.
Ba abinda ya taba girgizashi ko ya daga masa hankali kwata kwata,amma kuma
hakanan yaji wannan saqon ya tsaye masa a rai. Bai sani ba.....ko don saqon
yazo masa ne a daidai sanda yake da burin aiwatar da abinda ya qwallafawa ransa
na cikar burinsa?.
Yadda yake
a tsaye a siffa da zati me taba zuciya,haka zuciyarsa take a tsaye. Ba komai ke
bashi tsoro ko firgitashi ko sanyashi yaja baya akan abinda ya fuskanta ya kuma
qudira zai aiwatar ba.....don haka wannan saqon ma sai ya sanyashi cikin sahun
sauran saqonni marasa muhimmanci,wadanda ba komai bane a ciki face zallar
barazana maras muhimmanci a wajensa.
"Hasbiyallahu wa ni'imal wakil,hasbiyallahu la'ilaha
illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ya furta a
nutse,take taji zuciyarsa tana sake samun nutsuwa da aminci.
Komai ya
tattare yana duba lokaci,cikin jikinsa yake jin ya gaji,yana buqatar cikakken
hutu kafin gobe,so samu yabar qasar nan da kwanaki biyar,to amma ya fahimci zai
wahala dama ta bashi hakan.
Sanda
suke takawa da guard dinsa zuwa mazaunin motocinsa guda biyu kira ya shigo
wayarsa. A gajiye ya zura hannunsa a side pocket dinsa ya zaluqota. Taku biyu
baya sukayi dukkaninsu,wanda wannan kuma sabonsu ne,don basu tsaiwa a waje
muddin zai amsa waya,saidai idan shine ya buqaci hakan.
Sosai ya
zubawa sunan ido yana kallonsa,yayin da zuciyarsa ta cika da wasi wasi da saqe
saqen abinda kunnuwansa zasu iya jiye masa daga bakinta. Yaci gaba da irga
bugawar da wayar keyi,wanda yake jinsa kamar daidai da bugawar
numfashinsa. Ko a tarihi,ko kuma a
labari yana kyautata zaton shi din yana cikin mutane sahun farko da idan
labarinsu zai fita a kundin littafin al'ajabi zai ja hankalin mutane da dama.
Kiran uwa na daya daga cikin kiran dake sanya dukkanin yaro
alfahari.......kiran uwa na daga cikin kiran da kowanne yaro ke fatan gani a
kowacce rana.....kiran uwa kira ne dake iya juya zuciyar kowanne yaro daga
baqinciki zuwa farinciki.....amma banda su......banda tasu
mahaifiyar......banda kuma nasu kiran wanda ba komai a cikinsa face zallar ko
kwanto da didibniya tsakanin lalubo alkhairi ko sharrinsa.
Yana daga
cikin motor qafafunsa suna waje ya zauna,yana qoqarin lalubo nutsuwarsa da
yakan rasa a duk sanda kiranta ya riskeshi ya daga wayar.
Alamun
daga kiran ya sanyata sake hada nutsuwarta waje daya,gami da dagawa hajja
furaira hannu wadda ke lissafo mata tsare tsare na abubuwan da suka shirya
gudanarwa a wata shimfidaddiyar farar takarda.
Tsit
wajen yayi,bakajin motsin komai da kowa,abinda zai sanya wanda ke nesa irin
fu'ad din xaya dauka ita kadai ce wanze a dakin.
"Barka da warhaka" Ya furta da muryar nan tasa
dake da tasirin kwarjini me yawa da haiba a ciki.
"Barka kade.....ina fata kana lafiya?" Ta masa
tambayar data zamo abu mafi dadewa baiji ba daga bakinta. Duk da zuciyarsa ta
kasa yarda haka siddan tayi kiransa amma ya hadiye wannan.....ko yaya yaji
dadin tambayar cikin ransa koda kuwa da manufa aka yita
"Alhamdulillah.....Allah yasa kuma hakan" Dan
murmushi ta saki,zuciyarta tana ayyano nesanta zuwa kusa da ita.
"Lafiyarmu qalau,sai shirye shirye da muke yi gadan
gadan". Bai wani fahimci shirye shiryen da take magana a kansu tashin
farko ba......har sai data dora da nata bayanin.
" Na kiraka ne don na shaida maka.....ina buqatar wasu
kudade da zan qarasa duk hidimomin da suka ragen.....ta bangaranka da kuma
bangaren ita kanta amaryarka......don kasan hidimar biki ba qaramin abu
bane,......bare ni da zan aurar da dan fari......kuma ita kanta yarinyar ya
kamata ace ita,danginta da dukkan wani dage da jibi da ita yasan cewa tabbas da
gaske mamallakin diamond company zata aura.......banason harkar qaranta......ya
kamata duniya kanta ta shaida d'ana zaiyi auren fari".
Kusan koda
yaushe fitar kalmomin bakinta suna zame masa tamkar makaranta ne......ya jima
da sanin maamah din macace me son izza da nuna isa.......ya dauka wani tsohuwar
dabi'a ce a tattare da ita.....amma xuwa yanzun ya sake amanna mutuwa ce kadai
zata iya samun nasarar rabata da wannan halin.
"Me ake buqata?" Ya tambayeta kai tsaye.....don
shima da nashi plan din. Zuwa yanzu yana kallon komai ne tamkar a tafin
hannunsa ake shiryashi,abinda ya rage masa ya sani kuma kadanne da bayajin zai
zame masa me wahalar riska.
"Kudi nakeso ka sakamin......sannan ka sakawa
amaryarka......kamar million......."
"Kiwa saddiq magana......zan gaya masa ya saka miki
adadin abinda kike buqata" Ya yanke bayanin da taso yi masa da adadin
kudaden da duk da yasan ya jima da fin qarfinsu........amma kuma ana nemansu ne
a muhalli da gurbin da babu buqatar yawan wannan adadin.
Murmushi
ta saki tana jin wani dadi yana ratsa zuciyarta,tun a yanzu tana sake samun
tabbacin nasarar dake bibiyarta,tana kuma fara jin qamshi da dadin da uwa keji
a yayin da take gwada girman izzarta akan yaranta suke kuma bibiyarta sau da
qafa akan duk wani buri ko quduri nata
"Allah yayi maka albarka" Ta fada tana murmushi.
Kalmar ta dinga masa amsa kuwwa cikin kunnuwansa,sai ya dinga jin kamar ba daga
bakin maamah ta fito ba. Idan yace bazai iya tuna ranar data fadi wannan kalmar
a kansa baiyi qarya ba.
A hankali
sai yaji kaman zuciyarsa tana rugujewa. Inama ace ta fadi kalmar ne domin
cancanta da kamatar ta fadeta a kansa?,bawai don duniya ko wani abu dake
cikinta ba?,bawai don son rai ko biyan buqatar rai ba.
Da wannan
murmushin dake sake yalwata saman fuskarta a kowacce rana ta ajjiye wayar saman
table din gabanta. Qasaitaccen table ne da yazo cikin set na kayan furniture
din da aka qawata sabon gidan nata data riga kowa tarewa a ciki. Gida ne datake
jin zata kece biki na alfarma a ciki......zata daga sunanta da kuma martabarta
a idanun qewaye dama duniya gaba daya.
"Kowanne motsinsa sai ya dangantani da saddiq hamza
kibiya" Ta fadi tana duban idanun hajja,har cikin ranta tana jin wata wuta
tana ruruwa tare dason gaggautowar ranar da zata saka kakkaifar wuqarta ta
yanke wannan alaqar da tafi mata kama da baqar alaqa.
"Hanzarin na mene mariya?,saurin me kikeyi ne?,saura
kwanaki nawa duka duka?" Hajja ta bata qwarin gwiwa tana cike da kwadayi
da son jin abinda ya faru tsakaninta da fuad din.
Kai maamah
din ta jinjina tana son dawo da walwalarta kaman daxun.
"Bai tsaya jin koma nawa nake buqata ba......kawai yace
nayi magana da saddiq,shima zai masa magana na karbi abinda zan karba
din......kinga zan karbi kaso biyu kenan......da nawa dana yarinyar can,zan san
mata wani abu a ciki ne kawai.....sai na cire abinda zan cira a ciki.......zan
ware na boka donshi kansa yawan kudin dana qara masa akan wanda ya buqata na
fahimci ya qara masa azamar aikin nan.....hajja" Ta qarash da kiran
sunanta da wani irin sauti dake nuna gajiya da zallar zaquwa.
"Inaso yayimin aiki irin aikin da bai taba yin irinsa
ba tunda ya fara harkan nan......inason yayimin kalar aikin da ba fuad
ba......ko tsuntsun gidan fu'ad sai ya zama me biyayya a gareni........inason
yayimin aikin da sabreena zata koma tamkar bawa da ubangidansa a
hannuna........bansan me yasa yarinyar ke yimin kwarjini ba,bansan me yasa
nakeji wani abu daban ba idan ta kalleni......inason dukka wadannan abubuwan su
shafe daga idanuna".
Wani
murmushi dake dauke da tarin boyayyun ma'anoni da rufaffun qudurori dake amsa
kuwwa da amon nawa burin yana sama da naki hajja tayi,sannan ta harde qafarta
tana cewa.
"Dukka wannan qanqanin aiki ne a wajensa,kuma ko iya
haka aka tsaya zaki bawa wani labarin zafin aikinsa......isassun mata kawai ke
iya aiki dashi,matan manya da iyayen manyan mutane irinki,saboda daga sadakin
aikinsa kawai zaki fahimci ba gama garin boka bane.....don haka ki rubuta ki
ajjiye.....dukkanin wadannan burirrika naki tamkar sun gama cika ne......saidai
banji share dita a wannan kasafin naki ba".
Rausayar
da kai maamah tayi tana sakin murmushin jin dadi. A qasan ranta tana mamakin
son kudi tsantsa irin na hajja din,duk kuwa da cewa lullube take cikin wadata
me tarin yawa.......saidai wadatar yaranta idan kaf idan aka hadesu batakai
kaso daya cikin ukun abinda fuad ya mallaka ba shi kadai......amman duk da
hakan bata raina kudi komai qanqantarsu(tabbacin zuciya ta zarme da yawa dason
abun duniya,Allah ka kiyashemu).
"Baki da dukkan wata damuwa hajja,kina da million uku a
ciki,kafin alqalami ne kawai......kuma somin tabi,nan gaba kadan ke zaki dinga
bada wannan adadin a matsayin taki kyautar"
"Qwarai da gaske kuwa mariya" Hajjan ta fada kanta
tsaye tana duban idanun maamah da wani irin confidence daya sanya maida
hankalin maama duka a kanta. Wannan ya sanya ta sassauta kaifafa harshenta da
nuna dukkanin qwarin gwiwar dake kan fuskarta.
"Yaronki ai yarona ne mariya...ni nasan bani da
haufi....ba zaki taba butulcemin ba" Ta sake yiwa kalamanta ado da wasu
kalmomin
"In sha Allahu" Maamah ta amsa tana rausayar dakai
har yanzu murmushin na saman fuskarta,ta kuma jawo wayarta tana fadin
"Bari na nemi musaddiq ya nemo yaron can,don da zafi
zafi ake dukan qarfe......gobe nakeso muyi sammakon tafiya hado dukka ayyukan
dama sauran bayanai......bikin nan da gaske tahowa yakeyi,kwana shida kacal ya
rage......inason tasan da zaman kowacce doka qa'ida dama sharadi kafin ta samu
lasisin karbar igiyoyin auren d'ana a kanta". Da wani kallo hajja ta bita
kawai ba tare da tace komai ba.....saidai kuma can cikin wani saqo na zuciyar
magana ce me yawa nauyi da kuma dogon xangon da bazai yiwu baki ya furtata ba.
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 3
Daure da
babban towol da kuma da kuma wani babba data lullufe jikinta kirif tun daga
saman kanta take takowa daga cikin toilet din dake manne da falon tana dawowa
cikin ainihin falon daya zama sansaninta a yanzu.
Nan din
wani kebantaccen guri ne cikin gidan nasu,da asalinsa ya zama muhalli ne na
mahaifinsu,wanda tun bayan shudewarsa ba wanda yake ta'ammali da wajen,don
gidan nasu ya wadaci kowa,kawai sai saman inda falon nasa yake ya zama wajen da
akan bude ne kawai a share,sai idan wani taro ya tashi kuma cikin gidan sannan
akan zauna a ciki har ayi a gama.
A yanzun
saman ya zama kusan nata,tunda aka fara mata aikin gyaran jikin ko qasan gidan
bata saukowa. An killace muhallin da komai da zata buqata,kaman yadda aka ajiye
mata cima kala kala wanda sam basu taba birgeta ba koda qanqani. Hasalima ita a
yanzu cin abinci ya zame mata daya daga cikin horon da mamma bahijja keyi mata.
Koda kuwa ta kauda kai ta kuma kafe akan ba zataci ba,mamman bahijjan data
tsaya a bigiren da akan buqaci uwa saita nemo wani abu daban ta bata,takance
"Aure zakiyi fa sabreena,gidan miji zakije,anata gyaran
fata amma can cikin ko oho?,kinsan yadda yunwa ke kassara ni'imar mace
kuwa?" A duk sanda ta furta hakan sai sabreen taji kaman wani abu ya shaqe
mata wuya. Wai halan basu kula kuma basu lura da dukkan komai?,sunata magana
akan auren da ba komai a cikinsa face zallar rudani?,rarrabuwar burika da kuma
tarin biyan buqatar rayuka masu yawa a cikinsa?.
A
yanxun data dawo daga dauraye jikinta da tayi daga gyaran jikin da kullum
kwanan duniya takeji kaman ana mannawa fatarta wuta.....duk inda ta gifta kota
zauna wani irin fitinannen qamshi take barwa gurin. Wani irin mayen qamshi me
matuqar naci da mannewa jiki dama dukkan wani abu da mutum zaiyi mu'amala
dashi.
Qawatattun idanun nan nata da a yanzun suka koma rusunannu ta daga a
nutse tana duban me gyaran jikin dake faman gyara wutar da zata sake turareta
da ita. Ta zama wata kurmar qarfi da yaji,magana na mata wahalar
gaske,kwanyarta da nazarinta harma da dukka tunaninkan da takan raba dare tana
yinsu.....dukkansu sunfi ta'allaqa da kuma rinjaye akan YAYA WASAN ZAI
KAYA?......wa zata fuskanta cikin fuskoki muryoyi dama ruhikan dake zagaye da
wannan game din?.
Idan ta
tuna da mariya maamah.......tana jin wani abu sosai qasan ranta......jikinta
kuma yana bata wani lamari me nauyi da batasan mene shi ba,amma kuma wani sashe
na zuciyarta yana gaya mata ita din ba komai bace......tayi ganganci ne ma
kawai data kutso kanta cikin rayuwarta......batasan wacece sabreen ba da gaske
da bata aikata hakan ba.......bata kuma san meye da meye zata iya aikatawa ba.
Motsawar sunan muhammad fu'ad kawai cikin kwanyarta shine abinda yafi sanyawa
wani tsagi na zuciyarta damuwa.........lalata dukkan wata alaqa da kuma
dangantaka cikin aurensu shine abu mafi sauqi da zata iya aiwatarwa......to
amma kuma saki fa?.....A HANNUNSA YAKE!,amsar da akowacce rana take qara yawan
adadin fargabarta.
Lumshe
ido tayi taja iska sosai cikin huhunta sanda muryoyi biyu suka sauka a tsakiyar
kanta
"Turaren ya hadu kona miqo miki ki zauna akai da
kanki....." Cewar basudaniyar me gyaran jikin,yayin da nata maganar ya
cakuda dana mamma bahijja data miqa mata wani bowl na tangaran
"Bata din.....kafin hayaqin ya gama bin jikin ki saiki
qoqari ki shanye wannan". Dara daran fararen idanunta ta daga tana kallon
mamma bahijja kafin ta maida dubanta kan abinda take miqo mata,itama ita take
kallo wannan ya hanata katabus na musanta mata,sai kawai ta miqa hannu ta
karba,saidai kuma data fakaici ta juya,saita maidashi daga gefanta ta ajiye.
Sanda
tururin hayaqin ke ratsa sassan jikinta haka kowanne lungu da saqo na zuciyarta
ke qoqarin bata mafita a lamarin dake tunkarota nan da kwanaki biyar masu zuwa.
Zuwan mamman bahijja ya zame mata wani babban katanga daya hanata aiwatar da
kowanne shiri da zai nesantata da auren.....duk da tarin bayanan da kawu yayi
mata na ba inda zata shiga a duniya ta iya tserewa me jadda........saidai ta
dauki.maganar tasa a wasan yara ne.
Koshi
waye.....ko kuma da meye yake taqama tayi imanin saidai idan bata sakashi cikin
plan dinta ba.....
"Adda baki sha bafa" Muryar huda da ke zaune
gefanta ta fada,wadda kusan kowanne shirye shirye da ita ake aiwatar dashi.
Maida
idanunta tayi ta sake lumshewa muryar huda na dawo mata,ta fahimci dari bisa
dari ba wani me adawa da auren,kusan kai tsaye ma zata iya cewa dukkaninsu
maraba suke da abun,duba da irin walwalar da suke ciki gaba dayansu.
"Ki nutsu sabreen.......ki nutsu.....karkiyi abinda
zargi zai dawo kanki......karkiyi abinda su mamma bahijja xasu kasa karbarki da
wankeki daga laifi duk sanda kika kammala da wancan game din kika dawo
musu" Wata murya daga can qasan zuciyarta ta soma gaya mata.
Idanunta
ta bude ta aza kan huda har sai da hudan tadan sha jinin jikinta. Sunyi mata
farin sani,daga kallonta kawai suna iya karantar umarni da kuma hani,amma ga
sabanin tunaninta sai tayi mata nuni data miqo mata abun. A hanzarce kuwa ta
ajiye littafin hannunta ta miqe ta dauko ta miqa mata.
Tsure
abun tayi da kallo wanda batasan da meye da meye aka hadasu ba,to amma koda
meye aka hada din,ta tabbatar mamma tana asarar kudinta ne kawai,don haka ta
kafa kai ta soma kurba a hankali gardin abun yana ratsa kunnenta duk kuwa da
bakinta ba taste,haka zuciyarta a quntace take.
*******Doguwar tafiya,hawa da kuma sauka,kutsawa cikin
surquqi dukka ba damuwar maamah bane. Fatanta da burinta ta dangana ga mutumin
data miqawa al'amarinta gaba daya,ta kuma sanya hope me yawa a kansa.
A yanayin
data ganshi a yau ya sake saka mata tabbacin samun cikakkiyar nasara. A
hargitse yake yau din cikin zafin ayyukan mutanen da suka zabi ya zame musu
abun dogaro kuma hanyar samun duniyarsu ba tare da damuwa da meye makomarsu ta
lahira ba?.
Bayan shafe
shafensa da buge bugensa,ta hautsina dukkanin kayan aikinsa da yayi,ya kalleta
da jajayen idanunsa qananun ainun dake cike da rashin tauhidi da kuma zallar
sabo fajirci da fasiqanci. Dubane daya sake tabbatar mata ba rahama ko tausayi
ko misqala zarratin a cikin ransa
"Akwai tarin sarqaqiya......akwai tarin
qalubale......akwai al'amura da yawa da zasu iya wanzuwa ko su biyo
baya........ita din taurarinta nada tsananin haske da wahalar kutsa kai a
cikinsu........tana da wahalar sha'ani na gaske......tabata kuma abune da zai
iya zuwa da nasara da akasin haka.......kaman zan iya cewa KINYI KUSKUREN
ZABINTA.......to amma kuma ba wani tauraro da zai iya shiga nasa taurarin sai
natan......tamkar itace mahadi masarrafi kuma barin nasa
taurarin......taurarinta sune abokan tafiyar nasa.........sunyi matuqar dacewa
da juna.......wanda hakan shine zai bada damar tafiyar umarninmu da haninmu a
kansa......kusan komai nasu suna matuqar kamanceceniya dana juna......ITACE TA
DACE DA CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMI GUSHEWAR AKASIN DA NAKE
HANGOWA......saidai na gaya miki.....kamar akwai alamun KUSKURE DA
NADAMA.......akwai babban waqeee'a......juyewar komai da lullubewar mayanin
duhu bisa faifan qaddara".
Tunda ya
fara maganar gabanta ke wani irin faduwa. Hajja da suka gama sauraron bayanan a
tare ta dora hannunta a kafadar maamah da zummar yin magana da ita da neman
qarin bayani......saidai da sauri maamah ta zame hannunta daga
kafadarta......tayi nisan da batajin zataji kira......zuwa yanzu nasara take
nema ta kowacce fuska,ta kuma kowanne yanayi......bata buqatar tsaiko fashin
baqi ko qarin bayani a yayin da take dab da cimma nasararta........bayan kuma a
baya ya bata tabbacin ta wannan hanyar ce kawai nasara zatazo mata babu ko
kwanto
"Amma dai akwai hasken nasara ko dan kadanne?".
Kansa dake cike da wasu irin gasussuka ya jinjina ba tare daya koda dubi
idanunta ba. Cikin samun qwarin gwiwa tace
"Nasara duk nasara ce komai qanqantarta,baa canza mata
suna daga nasarar dai,hakanan daga qaramar nasara ake cimma babba......ayimin
komai da ake da iko a kansa.......a
sakamin yarinyar a tafin hannuna kafin samuwar fu'ad.......itace
tsanin......ita zan fara mallaka don ta zama hannuna tsani na kuma idona zuwa
ga wancan babban burin nawa!". Ta fadi muryarta na raunana tana tsoron jin
akasin abinda zuciyarta ke muradi.
"An gama!" Ya fada da wata kakkaurar murya maras
dadin amo. Saita sauke ajiyar zuciya tana yi relax ganin yadda ya soma maida
hankali akan aikinta.
Boyayyar
ajiyar zuciya hajja itama ta saki. Ba haka taso lamarin ya kasance ba,taso tana
kuma so taji cikakken fashin baqi da qarin bayani daga bakinsa.
Wacce irin sarqaqiya ce?
Wanne irin duhu ne?.
Wani irin baqin lullubin mayafi ne haka?.
Wacce nadama ce zata biyo baya?.
Meye kuskure a cikin zabin nata?.
Dukka
wadannan amsoshin tana buqatar saninsu ne don tasan daga ina zata dasa nata
harsashin?. Daga ina tata TAFIYAR zata fara?. Ta wacce fuska zata saita tata
DUNIYAR?,ta aza duniyar SHALELENTA?.
Bata data
cewa ko wani motsi,ta sani cikin aikinsa ba shishshigi,ke me rakiya kuma baki
data cewa......hakanan baki da damar yin komayya kiyi tambaya akan aikin daba
naki ba.....wannan kadai ya kashe mata jiki,ta zurfafa a cikin saqe saqe har ya
kammala aikin maamah,ya kuma shaida mata su wuce zasu tadda komai cikin motarsu
da qarin bayani.
Bata sake
gasgatawa da imani da zancansa ba saida suka samu komai a mota a ajjiye kaman
yadda yace. Ta sake tsinkewa da lamarin aikinsa,inda da wani suka je
wajen.....ko akwai gilmawar dan adam ta wajen sai tace an ajiye musu ne.
"Kings abun mamaki hajja?,kullum mutumin nan sake
dauren kai lamarinsa yakeyi" Ta fada tana juya kayan tsatsubar dake
hannunta.
"Kina zaton gurin qaramin mutum na kawoki......amma
mariya?,me yasa kikaqi tambayarsa dukka qalubale da matsalolin daya hango
miki?" Hajja tayi tambayar da tafi tsaya mata a rai.
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 4
A nutse ta
daga kai tana kallon hajjan
"Na tsani matsala ko akasi hajja......musamman a wannan
matsayin da nake kai a yanzu......me zanyi da ita ballantana na buqaci sharhi a
kanta?,bana buqatar dukkan wani jawabi da zai alamta min FADUWA ko MATSALA akan
cikar burina a yanzu.......inaji a jikina da raina cewa......zan iya kauda
kowacce matsala da zata tunkaro muddin na samu nasarar tsallake wannan matakin
da muke kai a yanzu......da qwanjina....da kuma fikirata". Jinjina kai
kawai hajja keyi.......tanason taji wanne tanadi da tsari tayi akan hakan?,amma
kuma bataso ta zafafa tambaya akai har maamah ta zargi wani abun,saita
tattarewa ranta komai tana jiran lokaci.....domin kuwa ta san cewa qwace goruba
a hannun kuturu ba abu bane me wahala ba.
********Abune sananne a wajen kowa......sharar biki da yawan
maganarsa a bakunan mutanen mu ya ta'allaqa da suna da sharar iyali dangi ko
zuri'ar da za'a gudanar da bikin diyoyinsu. Hakan itace ta kasance akan
MUHAMMAD FU'AD JADDA mamallakin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES.
Daga
qishin qishin zuwa samun tabbacin tasowar maganar aurensa,wanda tabbacin ya
samu ne daga yadda farouq musaddiq saddiq da uban family alhaji hamza kibiya
sukewa bikin shiri na gasken gaske.
Daga
abokansu saddiq maganan ya fara yaduwa,kafin kace meye wannan labarin ya fara
kewaye kowacce kafar sada zumunta.
Duk da a
qurataccen lokaci labarin ya fasu.....to amma labari ne me dumin gaske daya
bawa mutane da dama mamaki.......ya girgiza zukata da zuciyoyin 'yammata da
dama......musamman yaran masu kudin da suke kwana su tashi da mutuwar
sonshi......suke kuma da qaqqarfan hope din samun shiga a wajensa kodon matsayi
da mahaifansu ke dashi......walau na dukiya ko na siyasa......ko kuma
kasancewarsu abokan kasuwancin gold da diamond dinsa.
A gefe
guda kuma wajen 'yammatan da suka hada duk wata sura kyau da isa.....wadanda
sukasan basu da wani tsanin isa zuwa gareshi......saidai sunyi mutuwar murus
akan mayatacciyar soyayyarsa......abun ya sake bude musu topic of
discussion......qarqashin kowanne posting na labarin bikin dake dauke da
qawataccen IV na bikinsa da aka qawata da zallar ruwan gold,yake kuma wani irin
sheqi da daukan idanun da zai gaya maka bikin ba na yaro bane......tarin cincirindon
comments ne da mabanbantan kalamai masu yawan gaske. Da yawansu suna fatan
inama zasu samu hotunan amaryar?,ina free wedding pics da sauransu,saidai ko
daya basu samu ba face kunji kunji da shaidar zur daga wasu daga cikin
commentators na qarya,sai luguden labba da tsabar kyan IV din bikin da aka
kashesu dashi.......sai videos na lefen da aka samu wadda ta qwarewa gulma da
munafurci ta ba bajesu dashi......abinda ya sake hura wutar tattaunawar.
Sam
wadanda ake abin dominsu basusan anayi bama......daga angon har amaryar ba
ma'abota social media bane........idan kaga ta qulla abota da waya to akwai
sabon mission a gabanta........data gama ta ajiye wayar dama layukan da tayi
aikin dasu,wani ta karya ta zubar.......wani kuma sai bayan wani
zamanin.......yayin da oga fu'ad sam sam ayyukansa basa ma bashi damar tunawa
da wani media......koda WhatsApp dinsa idan ka ganshi akai wani abune ya kama
da lallai yake da buqatar hawa yayi a can din.
Koda yana
free ma ko yana annual leave dinsa.......yanayin tsaro da dukka rayuwarsa ke
buqata ya sanya ya sake nesa nesa da duk wani harkoki irin wadannan......don
komai nasa a matakin rayuwar daya taka yanzu yana buqatar privacy.
A daren
da ya rage ayyuka sosai......abu daya tak ya rage masa ya kammala yabar qasar.
Yana zaune saman bean bag chair,daga gefansa ruwan wolfberry ne me dumi yake
sipping yana kuma chewing berries din idan sun shigo bakinsa.
Haka kawai
yayi shaawar shiga yaga me duniya ke ciki don duka schedule dinsa na yau ya
kammalasu. Da wani personal account yake amfani,wanda bai taba ba baya kuma
wallafa komai a ciki bare ka iya gano waye mamallakinsa. Akwai account na
company dinsa kala daban daban dake qarqashin kulawar ma'aikatansu dake kula da
wannan fannin,so amma ko su baya bi ta kansu tunda yayi imanin zasuyi handling
dinsa ya dace da abubuwan da ya kamata ace an sanya din.
"Ya salam" Ya fada yana miqewa daga relaxing din
da yayi cikin bean bag din yana kallon yadda hotunan katinan daurin auren ke
shawagi cikin media. Da farko ma bai fahimta ba,saidai daga bisani da suka yita
jeho masa ire iren posting din.....kamar sunayi da gayya sunsan shike da
alhakin abun har sai da hankalinsa yakai. Shuru yayi yana sauka gami da furzar
da iska daga bakinsa. Yasan aikin mutum uku ne wannan farouq saddiq da
musaddiq,sai amna ta hudunsu.
Kamar jira
akeyi ya gani kira ya shigo masa,a nutse ya jawo yana dubawa......farouq
ne,kusan tun randa yace ya zaba kaya bai sake barin wayarsa yadda za'a sameshi
ba sai yau,sai ya katse kiran,ya koma ya laluboshi video call.
Ta signal
ya shiga,amintaccen app din da mafi yawan manyan mutane ke ta'ammali dashi
saboda samun cikakken tsaro.
Shigan
farko ya daga,fuskarsa ta fito tarwai kaman yana gabansa.
"Hey...." Ya fada qasa qasa yana duban fu'ad
"Don't tell me baka ma taso ba?" Yayi masa
tambayar yana tsuke fuska tare da bata fara'ar fuskarsa
"Zuwa ina kuma dude?.....bakaga abinda kuka jawo
ba?,baka ga abinda ke trending ba?" Ya masa tambayar shima hana dan bata
fuska kadan.
Kai farouq
ya jujjuya hagu da dama yana yarfar da hannu
"Am asking you seriously fa.....where are you?"
"Ask media users......farouq,you take it very serious
fa.....wannan fa auren ba wani abu bane da za'a damu dashi har haka ba.....ba
wani babban abu bane da zai zama ya yada ko ina ba......it's just a
temporary......."
"Kai kasan wannan......mu bamu sanshi ba......in fact
ma idan ka matsa da yawa zan fiddo komai.....just ka dauko hanya gobe
kawai......if not,bazan gaya maka abinda zai faru ba". Datse kiran farouq
din yayi,abinda ya sanya fu'ad sakin murmushi ba tare daya motsa daga inda yake
ba. Da alama farouq din a qufule yake dashi sosai,shi yasa yayi masa abinda
yafi tsana kashe masa kira. Ya kasa fahimtarsa ne,shi sam baiga me yasa zai
damu da abinda baida wani muhimmanci ba,baiga abun daurawa kai hidima har haka
ba......already sun gama diban kudin komai da komai uban da 'yar,daurin aure
kuwa ko aike yayi cikin ma'aikatansa za'a daurashi,gidan da zai ajeta ko ba
yanzun ba zai iya bada umarnin tarewarta idan ya gama sabgogin gabanshi,for god
sake zai bata lokacinsa ne da ranshi akai?.
Bai sake
bi takan farouq ba don yasan fushinsu da juna ba wani abu bane me dorewa ba.
Saidai yadda farouq din yace idan bai dawo ba washegari baisan me zaya faru
ba,yana tsaka da ayyukansa da yake sanya ran sune na qarshe kiran anni ya
sameshi.
Abdul_haleem daya daya cikin guard dinsa ya miqawa folder din
hannunsa,ya koma gefan table din da yake ajiyar takardun ya zauna yana daga
wayar.
Cikin
nutsuwar nan tata da ko yaushe take qara mata kima da kwarjini tayi masa
sallama cikin tsantsar kulawa da qauna irin ta uwa da d'a. Kaman ko yaushe
shima,cikin tausasawa da matuqar bada kima ya amsa mata sallamar.
"Barka da warhaka anni......anni ayyuka sun sani
gaba,ayimin afuwa" Yayi riga malam masallaci wajen fada. Murmushi ta saki
cikin nutsuwa tace
"Anyi maka Muhammadu........ya aikin?,fatan komai yana
tafiya daidai?"
"Alhamdulillah anni.....komai alhamdulillah,saidai muna
buqatar qarin addu'a" Ya furta maganar jerin saqonnin daya gani shekaran
jiya suna fado masa. Ba'a raina kaidin maqiyi,kuma abokin adawa ko wanda bai
sonka ba'a rainashi komai qanqantarsa.
"Kullum a cikinta muke,ba abinda zai faru in sha Allah
sai alkhairi......amma nayi zaton samun baquncinka a yau......tuntuni mun sauka
a sabon gida.....duka duka jibi ne daurin auren nan......ga baqi a gidan kowa
kai yake tambaya". Hannu ya sanya ya shafi sumarsa,har yanzu ya gaza gano
abinda yasa suka daukaki sabgar nan haka.....har wani taron gayyar jama'a anni
itama tayi kenan bayan ta maamah?.
"Jibi din zan shigo in sha Allah anni"
"Anni jibi yayi kusa.....gobe ko yau ya
kamata....private jet ne,baida buqatar samun wani issue ko ya kawo excuse"
Ya jiyo muryar farouq daga gefe tana shigo masa.
Murmushi ya
saki da sautinsa ya gaza boyuwa,wato zuwa yayi ya hadashi da anni kenan?.
"Bani shi anni please" Ya fada da sauri,bata ce
komai ba ta miqawa farouq wayar tana murmushi. Drama din fu'ad da farouq babu
me shiga,idanma kace zaka shiga din kunya zakaji.
"Definitely idan ka samu dama saika shiga tsakanina da
anni......ka canza hali wallahi" Ya fada yana dan daure murya.
"Kome zaka fada ka fada.....ina nan ina jiranka"
"Kaci gaba da jira.....at last idan bakayi wasa ba kai
zan daurawa auren nan da yarinyar......tunda naga ka damu da lamarin ta da
yawa" Daga haka ya katse kiran yana dariya ciki ciki. Yasan ya kunno
farouq din,don ba wanda zai rabashi da fannah dinsa sai Allah.
Haka
kawai ya samu kansa dason cika alqawarin daya yiwa anni,ya maida hankalinsa
qwarai kan qoqarin kammala abubuwan da suke gabansa don ya samu isa nigeria
kaman yadda ya alqawarta.
Hannu
anni ta miqa tana karbar wayarta daga wajen farouq dake mita. Duk da mitar da
yakeyi din saidai ya kiyaye dukkan wani abu da zai saka anni ta fahimci akwai
lauje cikin nadi.....boyayyen manufa da qudurin data hana fu'ad damuwa da
dukkan wani lamari daya shafi auren.
"Anni kina sauqaqa masa da yawa........hatta da friends
dinmu gobe zasu iso.....amma ace shi yana can neman kudi?.....har yau ya kasa
sanin kalmar hutu a rayuwarsa?.....ta yaya zai kula da diyar mutane?"
Murmushi anni ta sake,yadda farouq din keta mita ke bata dariya
"Banda abinka farouq.....na tabbatar ya fika damuwan ya
iso fa.....sannan tunda kaga haka din ba yadda zai taho dinne,da yau gobe da
jibin dukka na Allah ne,kuma kaman yau ne.......ina da saqo ma da nakeson ka
miqawa d'iyata...." Anni ta fada tana yunqurawa ta miqe.
"Ina amna ta shiga ne?" Farouq ya tambayi anni
dake qoqarin bude wani side na wata qawatacciyar cupboard ta daban dake cikin
aljannar duniyar bedroom din nata.
"Tana bangaren beauty spa"
𝘿𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖 𝙩𝙖
𝙣𝙖 𝙠𝙪𝙙𝙞 𝙣𝙚.
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 5
"Okay" Ya fadi kawai a taqaice,don ita kanta yadda
yaga alamun ta dauki bikin kamar yafi yadda kowa a gidan ya dauka.
******A duk bugawar daqiqa,wucewar kowacce saa da kuma
bugawar agogo sake kusantar da ita kawai yakeyi zuwa ga duniyar mamakin abinda
ke shirin faruwa da ita. Sannu sannu taga gidan ya fara cika da baqin fuskokin
da da yawansu ta manta da kasancewarsu ahalinta. Wasunsu tun ana taron alhinin
rasa mahaifinsu mamallakin gidan gaba daya,yau sai gasu da daya da daya suna
bullowa da sunan halarta taron bikin da tayi imanin ba wani bane ya gayyacesu.
Dondai
mamma bahijja ba wata mu'amala ke tsakaninsu ba,hasalima ba sanin kaso casa'in
da tara a cikinsu tayi ba. Ba sanin jiya ko yau ta yiwa duniya ba,ta
sani....kusan mafi rinjaye a cikinsu sanin waye yake shirin aurenta shi ya
kawosu bikin,bikin da babu wani abu guda daya da take da masaniyar ita ko mamma
bahijja ta tsarayi,koda an tsara din ta tabbatar aikin kawu rufa'i ne,wanda ya
kasa zaune ya kasa tsaye,komai yana gaba gaba a kai,hakanan ya saki kudi anata
hidima cikin gidan.
Yanayin
yadda ya saki bakin aljihunsa ya dasawa sabreen qaqqarfan yaqinin kudade ya
samu ko ya karba daga wajen mutanen daya sadaukarwa da ita. Bata cewa da kowa
komai ba,amma tana karance da kowanne motsi na cikin gidan. Yadda bibo tayi uwa
tayi makarbiya,a rana takan hauro saman da zummar dubasu har babu adadi,saman
da a baya sai da akasha dambarwa da ita kafin ta daga qafan kasancewarta a
can,sai da sukayi baram baram da kawun,ya wanke mata zanin mutuncinta tas tare
da buga mata gori nau'i daban daban,yau din sai gata tana zarya tsakanin
hidimar da ba tata ba bata kuma shafeta ba.
Sanye take
da wata simple dubai gown me rangeamen nauyi da sassauqan ado me daukan
hankali,cotton ce me yankakken hannu da ya tsaya iya damtsenta,sai siririn
mayafinta data maidashi tamkar dankwali ta yane sassalkan gashinta dake zube
gadon bayanta ba tare data daureshi da komai ba. Cikin jikinta sam babu
qwari,tana jin kamar iska zata iya dibanta ta kayas da ita,hakan kuwa ta sani
baya rasa nasaba da qauracewa abinci da tayi akan yadda ta saba cin abinci,duk
da dama can ita din ba ma'abociyar cin abincin bace.
Ta samu
huda ta dafa shinkafa da wake,sai miya da soyayyen kifi daban. Goshinta ta dafe
tana zama,kanta tun jiya yake sara mata bayan data jiyo mamma bahijja na magana
da qannen mahaifiyarta da kuma kawu Abdul Hakeem,tana shaida masa jibi gobe
kenan shine ranar daurin aurenta bayan sallar juma'a.
"A zuba miki adda?" Huda ta tambayeta cike da
fatan ta amsa cewa zataci din. Hannuwan huda da sukasha lalle tabi da kallo. Ko
nata hannuwan farare suke sidik da zara zaran yatsunta dake dauke da dan baqin
lalle dan kadan saman farcenta,ragowar lallen data yiwa adon yatsunta wata biyu
baya da suka shude.
"Zuba......amma kada kisa miya.....mai zaki saka da dan
maggi kadan" Ta yiwa huda bayani a taqaice tana zare idanunta daga sashen
da suke. Sauka idonta yayi kan wayarta dake ajiye wadda a qalla ta kusa kwana
biyu a wajen. Sam bata da sha'awarta ma don batajin zuwa yanzu tana da wani
uzuri da ita. Jib,ayshatu,qannenta da sauran mutanen da takejin sun Ta'allaqa a
wuyanta kadai zuciyarta ke mata amsa kuwwar ta nemesu.......tayi sallama da
kowannensu.....saidai kuma wani sashen daban yana bata qwarin gwiwar bata da
buqatar hakan!. Tana ji a rai zuciya dama jikinta tamkar wani gajeran balaguro
ne kawai zatayi daga tata duniyar zuwa wata duniyar,balaguron da bai wuce
misalin qifatawar idanu daga rufewar zuwa budewar ba. Bataji kwata kwata cewa
wai auren zai zama wani dogon aiki da zata kasa yakiceshi cikin qanqanin
lokaci. A yanzun zata zubawa komai da kowa idanu.....kwadin me
kwadayi......burin me buri......da tsarin me tsari a kanta ya kwanta.....sannan
ne ita kuma zata aiwatar da nata shirin hankali kwance( nikam nace
uhmmm....qaddara dai ta rigayi fata🥺😊).
Da plate
huda ta dawo,wanda tsara zuba abincin gwanin sha'awa. Sabreen tasan duka tayi
ne don taci,ta jera soyayyen kifin saman shinkafa da waken,sannan ta mata roban
yaji da magi daban. Da kallo kawai tabi plate din,don tasan yafi qarfinta koda
duniya ma tana kwance bare yanzu da wani abu waishi abinci baya burgeta.
Sallamar
kawu rufa'i da sautin muryarsa kadai ya sanya abincin data sanya a bakinta ya
tsaya mata cak a maqogaronta,sauran na bakinta kuma taste dinsa ya canza
mata,har tana jin ba zata iya taunawashi ba,har sai data tattara dukkan
juriyarta sannan ta tauna ta turashi zuwa maqogaronta wanda ta samu ya wuce da
qyar,sai kawai ta yanke hukuncin ajiye abincin. Idanunta ya sauka kan kawun
sanda take ajiye plate din a qasa,wanda yake jaye da wata mini luxury luggage
me azabar kyau da kuma daukan idanu. Koda bakasan me duniya ke ciki ba,koda
bakasan darajar abinda yake janye dashi ba tabbas zata fahimci luggage ne me
tsada da madaukakiyar daraja.
Wajen zama
mamma bahijja tayi masa tana sanya nadra ta ajiye masa drink da ruwa.
"Ya hidima ya kuma shirye shirye?" Kawun ya furta
da muryar dake nuni da zallar farincikin da yake ciki
"Alhamdulillah.......ai kune da hidima,tunda mu nan ba
abinda zamuyi" Kai kawu rufa'i ya girgiza yana satar kallon sabreen da
tunda ta gaidashi bata sake koda kallon sashen da yake ba.
"Allah ya yiwa yarinyar nan taurin kai
bahijja......idan kinga abubuwan da sukaso gabatarwa zakisha mamaki......har
yanzu quruciya ke dawainiya da ita,inda tasan girman matsayi da darajar mutumin
da zata aura,na rantse miki saita qare rayuwarta tana godemin.....attajirin
matashin da babu irinsa a wannan qarnin da muke ciki?" Dan murmushi kasan
momma bahijja tayi,adan zamanta ta fahimci kawun yana sa son abun duniya
"Duk bama wannan ba rufa'i,indai har bincikenku ya
tabbatar da nagartarsa ai magana ta qare.....dukiya wannan wani abune na daban
ai"
"Habawa.....idan ana batun nagarta ma da dattako har
ayi magana wadannan dattijan?"
"To alhamdulillah.....haka akeson ji...."
"Yanzu haka ma aike ne......saqo ne na musamman daga
surukarta......kaya ne tace a kawo mata da zata sanya a gobe kenan"
"Tofa.....ikon Allah,kuma dai?,basa gajiya?"Momma
bahijja ta fada duba da irin kudaden da aka narkar,tun daga dukiyar aure har
izuwa batun lefen dasu kansu har yanzu basu gama sanin komai da komai dake
cikin akwatunan ba. Tana qara ganin girman qaunar da suke gwadawa sabreen din,a
gefe guda har ranta tana jin tamkar sabreen din tayi sa'ar inda zata rayu cikin
qauna da kulawa.
"Wai wai.....ma sha Allah" Momma bahijja ta furta
tana daga lafiyayyen applique lace da kudi suka koka qwarai wajen siyensa. Daga
qasanshi kuma wata bazin ce data amsa sunanta sai super Sheraton da iya ado da
gayu da kashema kai kudi irin na momma bahijja bata taba katarin ganin irinta
ba. Daga qarshe set ne na banguls earrings da sarqa da zobensu duka na danyen
gold me matuqar daraja(nikam nace masu abu da abinsu).
Ko
qwaqwqqwaran motsi sabreen batayi ba ballanta ta daga kanta ko zata nuna alamun
tasan bidirin da akeyi,har sanda hadiyya tayi sallama tana shigowa falon da
guntuwar fara'arta.
Sunan
kayan kawai ya gaya mata darajar abinda aka sako a ciki saidai hakan bai dadata
da qasa harta daga kai ta basu darajar kallo ba,don batajin zata iya rabasu a
jikinta. Komai daya fito daga hannunsu duhu yake mata,baya mata haske ko
kadan.....musamman da take kyautata zaton kayan sun fito ne daga hannun waccar
matar maras daraja. Still shigowar hadiyya bata sakata daga kai ta dubeta. Can
qarshen zuciyarta danqare da mamaki,yadda kudi ke iya sauya dabi'un mutanen
duniya cikin qanqanin lokaci,duk da wannan karatun ta jima da
haddaceshi......kusan shi ya zama sila na sauyawar DUNIYARTA.
Hadiyyan ta
sauya kamar ba ita ba,abinda bata taba tsammanin zaya faru nan kusa ba. Bata
zaqe da yawa ba wanda tasa tasirin karatu ne wala'alla da salon
gogewa......hakanan kowanne taku kadan tana yunqurin kutsa kai jikinsu ne.
Hadiyya ita
ta qarasa daga kayan matsanancin mamaki yana sake kasheta. Hidima sosai suke
gwadawa sabreen din kaman rijiyar kudi garesu. Ba wanda yakai me kudi sanin
darajar kudi,saidai ga wadannan bataga alamun hakan sam daga garesu ba.
"Gashi zakiyi magana da surukarki" Momma bahijja
ta fada tana sauke wayarta daga kunne gami da miqawa sabreen. Dan turus tayi
tana sauke fararen idanunta akan fuskar momma bahijja din. Muddin wannan matar
ce sam bata da sha'awar wata magana da ita. Komai nata bisa gadara ne iko izza
da kuma nuna qarfin dukiya,don me zata zauna tana gwada mata tata izzar bayan
ba ita ta gayyaceta cikin rayuwarta ba.
Idanu
sunyi yawa a kanta,don haka ta sanya hannu ta karba tana kauda fuskarta daga
kallon idanuwan.
Sallamarta
kadai ya gaya mata ba wadda take zato bace,cikakkiyar sallamar data saukar da
duk wani zafi da zuciya da kuma halshenta suka dauka,saita amsa mata a nutse
matuqa
"Kina yini lafiya diyata?" Anni ta fada daga nata
bangaren jin sabreen din tayi shuru. Karon farko sai taji nauyin matar ya
saukar mata,batasan me yasa a iya waya kawai takejin girma da kwarjininta
ba......shin itace asalin mahaifiyarsa ko yaya?.....itadin wacece a
wajensa?,waccan ma wacece a wajensa?. Iya wannan tambayoyin da bata da amsa
kadai suna sakata a jikinta tana jin tabbas akwai wani gagarumin abu birne a
qasa.....duk da zuciyarta tana gaya mata ba wani babban abu bane da zai gagari sarrafawarta
ba.
"Barka da yamma.....lafiya alhamdulillah" Ta hade
gaisuwar da amsar tambayarta.
"Ma sha Allah"
"Naga saqo,na gode" Tayi hanzarin fada,don a cikin
ranta takejin bai kyautu ba har sai ta magantu.
"Ba komai......inaso ne kawai kiyimin alfarmar sanyasu
a duk sanda zaki shigo ahalinmu" Tayi maganar a tausashe cikin kuma nuna
kulawa,kulawar data bayyana kanta sosai cikin sautin muryarta
"In sha Allah" Ta sake amsa mata
"Ina fatan hakan ba takura?"
"Ba komai....in sha Allah"
"To alhamdulillah......ina roqon ubangiji ya tattara
dukkan alkhairanku ga junanku......ya kauda kowacce irin fitina da abunqi a
tsakaninku". Batasan me yasa ma......amma har tsakiyar qirjinta taji
saukar addu'ar......batayi kuskure ba idan tace kunnuwanta itace mutum ta farko
data fara jin addu'ar daga bakinta,sai taji labbanta sunyi nauyi bare su
tallafeta ta amsa.....yayin da anni tayi zaton kunya da kawaici suka hanata
amsawar......a haka tace ya baiwa momma din wayar.
Zuciyarta
tayi nisa qwarai da zurfi wajen tunani,har batajin ma meke wakana cikin
falon,sai kawai ta yanke nesanta kanta dasu ta hanyar komawa daki kaman yadda
ta maida hakan dabi'arta.
Bata
jima cikin duniyar dakin data maida mazauninta ha nadra ta shigo dauke da
wayarta a hannu.
"Ana kiranki" Ta fada tana miqa mata wayar. Kamar
tace mata ta koma da ita sai ta fasa,ta saka hannu ta karba tana daga kwancen
tana duba me kiran.
Sunan data
gani ya sanyata miqewa ta zauna sosai babu shiri,hannunta na gaggawa wajen amsa
kiran ta sakashi a kunnenta
"Kicemin kun dawo titi don Allah,kicemin ayshatu ta
warke"
"Na warke adda......na samu sauqi" Muryar yarinyar
ya saukar mata a kunne. Wani hawaye me sanyi ne ya kubce mata,kullum da lamarin
yarinyar take kwana take kuma tashi,daga yadda taji muryarta tasan cewa tabbas
lafiya cikakkiya ta samu a gareta
"Muna cikin sabon gidanmu yanzu aunty.....na gayawa
titi bazan yarda na fara ganin kowa ba sai ke".
"Yanzu kuwa zaki ganni ayshatu" Ta bata amsa kai
tsaye kaman ta manta a wanne yanayi ita din take.....kaman ta manta rabonta da
taka qasar waje wasu kwanaki ne masu yawa.
Da wani irin
excitement ta ajiye wayar,ta zura qafafunta qasan gadon da hanzari zara miqe da
nufin shiryawa,sai kuma ta dakata cak saboda dawowa hayyacinta da tayi.
Tayi
imanin wadannan mutum mutumin har yanzu suna tsaye a qofar gidansu suna
gadinta,yawan mutanen dake kai kawo a gidan bai sanyasu sun tafi ba......don ko
dazu ita iya jiyo baqin tsagin abbansu suna tambaya a kansu.
"Saina fita kota halin qaqa wannan karon......ko meye
zai faru saidai ya faru" Ta fadi tana qarasa saukowa,ta kuma fito kai
tsaye zuwa ga falon tana nufar doguwar veranda din dake saman wanda tacan zata
samu hanyar gangarawa qasa ta koma ainihin dakinsu.
_DUNIYA TA na kudi ne_
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 6
Page 06
Batasan gidan ya fara daukan mutane ba sam sai data sauko
din. Gomayyar idanuwa sukayi kanta caaa ana qare mata kallo. Kowa da nashi
tunanin cikin ranshi,wasu na kallon tsantsra kyan data qara saboda gyaran jiki
na musamman data samu tsahon kwanaki daga wajen qaararriyar me gyaran
jiki......wasu kuma na mata kallon sha'awa suna fadin inama su ko 'ya'yansu
keda wannan sa'ar ta auren irin mijinta?,yayin da wasu nasu kallon na bin
qwaqwafi ne hassada da tarin tambayoyin ta yaya KARUWAR GIDA.....WADDA TA GAMA
RABA MUTUNCINTA WA MAZAN TITI TA SAMU BABBAN MUTUM.IRIN MUHAMMAD JADDA DIN?.
Miskilanci
da shariya kusan cikin jininta suke,don haka tayi kaman bata gansu ba ta wuce
dakinsu kai tsaye.....ballantana kusan dukansu tana cike dasu. Ba wanda yabi
takan rayuwarsu.....qaqa suka kwanta qaqa zasu tashi?,amma sai gasu yanzu zube
da sunan sunzo auren yarinyar da basusan yaya ta girma ba?,me taci har takai
wadannan shekarun?.
A gaggauce
ta shirya cikin wata luxury Egyptian abaya datayi masifar karbarta,wadda inda
cikin nutsuwarta da hayyacinta take itama ya kamata ace taga yadda rigar ta
karbeta.
Tun daga
nesa kana iya ganin mugun kyan da fatarta tayi,wani irin haske da glowing kawai
takeyi,saika rantse da Allah diyar wani hamshaqin ce. Qaramar handbag kawai ta
dauka ta jefa wayarta a ciki da dan canjin da zata riqa saboda mota,ta fito
daga dakin a nutse tana isowa falon,daidai sannan momma bahijja ta shigo
rungume da dinkakkun atamfofin da tasa aka dinkawa su haneefa duk da tarin
suturunsu.
"Ina zuwa kuma?" Momma din ta jefa mata tambayar
tana kallon yadda take komai a gaggauce. Batasan da wanne harshe zata yiwa
momma bayanin aysha da muhimmancinta a wajen ta,don haka a taqaice tace
"Dubiya zani momma...."
"Zuwa ina?.....kuma dubiya a irin wannan lokacin?"
Kai ta langabe kadan tana fargabar kada momma din ta hanata fita,don a irin
wannan lokacin ita kadai takejin zata hanata fitar ta hanu
"Ba niss momma.....ba jimawa zanyi ba".
"Nadra ta rakaki,kuma kada ki wuce awa daya" Ta
fada tana qarasawa tana zube dinkunan hannun nata saman kujera.
Mayafi kawai
ta figowa nadra,ta sanya wasu plate shoe nata sannan suka fito. Sam bata damu
da yadda idanuwa keci gaba da binta da kallo ba,har wasu na qoqarin gaisawa da
ita,a haka ta doshi qofar gidan nasu tana tsara yadda zata kaya tsakaninta da
qedarun da aka tsaida a qofar gidan.
Tana
takawa zuwa qofan tana jin fargabar yau dame zasu zo mata?,don dai yadda takeji
a ranta yau koda sama da qasa zasu hade sai ta fita.......don ba wani mahaluqi
daya taba saka mata dokar zama cikin gida har haka tsahon rayuwarta......sai
yau gashi sama ta ka wani mutum can da baisan ciwonta ko darajarta
ba......yanason yayi amfani da giyar kudi ya yiwa rayuwar karan tsaye.
Tana
tura qofar yana riqeta kana aka qarasa budeta. Fuskar kakkauran mutumin ta
bayyana har abun yana bawa sabreen mamaki. Bata taba kawowa a lokacin irin
wannan zata sameshi tsaye bakin qofar ba kamar wanda aka tsaiguntawa zata
fita......waisu basa zama?,ko basa hutawa da jiddin suna tsaye suna gadin duk
wani motsinta.
"Good evening madam" Abdulgaffar ya furta cikin
matuqar girmamawar nan da suka saba mata magana da ita saidai kuma a dabarance
yana matse kowacce hanya da zata iya rabawa ta fice daga gidan.
Ta gama
karantar motsinsa kaf.......bata wani damu da gaisuwarsa ba ta azawa fuskarta
wani irin halakakken bacin rai da kuma d'aurewa
"Kiramin boss dinku" Ta bashi umarni nakai tsaye
da wani irin sauti da babu wasa ko kadan a ciki. Tanaso ta gwada musu girman
abinda zata iya aikatawa.......tanaso ta gwada musu basu ba......koda boss
dinsu ma bata daukeshi da wani tarin muhimmanci ba.
"Bani da connection dashi......idan zan kirashi saina
jira anyimin iso kafin na samu magana dashi......amma ga jordan zai kira miki
shi" Abdulgaffar yayi mata bayanin cikin girmamawa yana matsawa da baya.
Can
qasan ranta mamaki yake kamata,wanne irin girman mulki da izzar kudi gareshi da
har yaransa ma ba kowa da kowa keda daman magana kai tsaye dashi ba
"Good evening madam.......kiyi haquri ki jira
kadan,yanzu in sha Allah zai amsa" Jordan ya fada yana rusuna mata. A
ranta tanaso ta gaya musu ne a fili
"Qattin banza.....kun zauna kuna yiwa mutum qwaya daya
bauta saboda yana da dukiya" Abinda zataso gaya musu kenan ganin yadda
jordan ke lalubar muhammad fuad jadda cikin girmamawa.
A
lokacin yana tsaka da hada duk wasu muhimman abubuwa nashi da kanshi,ba tare da
ya bari hidiminsa ya masa ba wato me sunan malam. Akwai wasu abubuwan da da
kanshi yake yinsu,duk da tarin hadiman dake gareshi. Yana sanye da fara qal din
t.shirt me laushi Vshape neck,hannunta iya dantsensa wanda hakan ya sanya
murdaddun damtsensa dake nuna girman daga qarfe da yakeyi suka bayyana,wandon
jikinsa ma farinne duka duka tsahonsa iya qaurinsa,sai lausasan fararen
flip-flops masu tsananin haske da taushi.
Cikin
kowanne irin yanayi tsarinsa na dabanne,kai tsaye zaka iya cewa gayu ya ratsa
jikinsa da gasken gaske.....koda kuwa
bacci zai shiga zaka sameshi neat....komai nashi kuma completed kai kace ba
bacci zai kwanta ba. Yadda yake a nutse cikin wani irin tsari haka komai nashi
yake kasancewa,waya.yake amsawa wadda ya sakata a hands free ya ajiye saman
wani zagayayyen kujera me siffar qwallo dake a gefe. Kadan ya kalli wayar,sai
ya fahimci kiran jordan keson shigowa amma yana buqatar izinin haka,don haka ya
katse wancan kiran ya bawa kira jordan din dama
"Barka da wannan lokaci sir" Jordan yayi maganar
cikin girmamawan data bata ran sabreen,ta cika fal da mamakin wanne irin ban
girma ne haka kaman yana a gabansa?,ya kasa miqewa da dukka tsahonsa ya amsa
wayar.
"Yauwa Jordan......ya akayi?" Ya tambayeshi kai
tsaye. Sai daya dan daga idanu ya kalli sabreen din da idanunta ke cike tab da
fushi,sannan qasa qasa yace
"Madam daka tura a yiwa aiki ce keson magana dakai
sir"
"Madam?" Ya tambaya yanason tuna abun don ba komai
yake baiwa muhimmanci ba
"Eh sir....."
"Bata wayar" Ya umarceshi kai tsaye don ya tuna
inda zancan ya dosa.
"Ka matsa a wajen idan ka bata" Ya sake fadiwa
jordan don bayason yayi involving yaransa cikin abinda bai shafesu
ba.....hakanan yana ganin ba girmansa bane su fahimci komai ba.
Kaman ba
zata karba wayar ba don tana jin kamar ta zuba a qasa data nema magana
dashi......saidai kuma girma da martabar inda zataje din ya shafe komai a
idanunta,don haka ta sanya nadra ta karbo wayar daga hannunsa sannan ta karba a
hannun nadra din,ta taka a nutse tana dan komawa ciki duk da jordan ya matsa
daga inda zai iya jinta.
A kunnenta
ta kara wayar,saidai har kusan shudewar mintuna guda tim ba wanda ya cewa da
dan uwansa komai.
𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀 𝐓𝐀
𝘓𝘪𝘵𝘵𝘢𝘧𝘪𝘯 𝘬𝘶𝘥𝘪
𝘯𝘦
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 7
Tana
tsananin buqatar ta fita,ta kumayi imanin wadannan gumakan ba wanda zai musu
magana suji sai wanda ya turosu.....tana jin kuma faduwar fara yin magana
dashi. Sanda taji ya motsa da bisa alamun ajiye kiran zaiyi,a nutse ta bude
baki ta soma magana dashi da qaramar muryar nan tata me wani irin tone
"Ban kasance daya daya daga cikin hajojin kamfaninka ba
ballantana ka sanya min masu tsaro na......'yantacciyar d'iya ce kamar
kowa,hakanan mutum ce dake da nata tsarin da qa'idojin da ba komai take jurewa
ba......ka yiwa wadannan gumakan magana da suyi gaggawar matsawa subar qofar
gidanmu". Tsayawa yayi cak da abinda yakeyi,ya harde hannayensa a qirji
yana sauraronta da muryar dake nuna tamkar gargadinsa kawai takeyi kai tsaye.
Idanunsa ya
lumshe kai tsaye na sakanni sannan ya budesu,yana ci gaba da jin qaramin
sautinta dake magana cikin yanayi na tsiwa har sai data qarasa maganarta.
"Bakisan waye ni ba.....i can't tolerate it,dole ki
koyi manners......bawai na zama dani kawai ba,manners akan komai ma,tabbas kina
buqatar tarbiyya,Your attitude needs a serious adjustment.....and im not going
to put up with anymore nonsense,I won't tolerate any more of your nonsense,its
time to get in line" Yayi furucin harshly muryarsa cike da seriousness.
Din din din da taji wayar nayi shi ya tabbatar ya yanke kiran. Ta sauke wayar
daga kunnenta tana jin wani irin daci yana taso masa tun daga cikin maqogoranta
har zuwa saman harshenta. Tabi wayar da kallo ranta yana mugun baci,tana jin
maganganun daya gasa mata suna yawo cikin kunnuwanta.
Tana jin
kamar tayi cilli da wayar ko zata samu sauqin radadin dake cisgar
zuciyarta......to amma saita tuna idan tayi hakan bata kyautawa ainihin me
wayar ba,wanda shima da alama komai nasa yana yine bisa tsoro da kyakkyawan bin
umarni ba tare da sabawa ba.
"Kai mishi wayarsa" Tace da nadra tana miqa mata
wayar,sannan ta miqe tana gyara jakarta tabi bayan nadra zuwa qofar gidan,tana
jin yau saita nuna masa iyakarsa ta hanyar fita,idan yaso ya tashi duniyar a
yau kowa ya huta.
Nadra ta
rigata isa,ta bashi wayar dake ringing,yana duba me kiran yayi hanzarin dagawa
tare da matuqar rusunawa yana fadin
"Hello sir" Idanunshi suna sauka kan sabreen,sai
ya miqe yana sauraron umarni daga wayar yana kuma kallon sabreen wadda ke
tafiya cikin tsananin fushi,har kuma ta samu nasarar sanya qafafunta a qofar
gidan.
"......idan naga sabanin haka ka kuka da kanka"
Qarshen maganarsa kenan data jawo hankalinsa zuwa ga sabreen wadda ta dauki
hanyar barin layin sosai bata tsaya koda waiwayarsa ba ballantana wayarsa da
yakeyi,tana jin bata da lokacinsu gaba dayansu.
Da sassarfa
abdulgafar ya jefa wayar a aljihunsa ya juya da sassarfa yabi bayanta. Daga
yadda yau boss din ya masa magana ya tabbatar akwai magana a qasa. He's
speaking seriously,yasan abinda ya fada da gaske yake.
"Madam.....ah.....am,madam sorry......listen
please" Ya furta bayan ya cimma bayanta. Nuna ma tasan yana biye da ita a
wajenta bata lokaci ne,bata da lokacin batawa ta saurareshi daga shi har boss
din nasa
"Madam please ki tsaya ki saurareni,am going to loose
my job.....please listen to me". Maganar ya taba mata zuciya........yanzun
nar rashin imaninsa yakai ace ya kori mutum bakin aikinsa saboda wani abu daban
ya faru?. Daga yadda yake maganan kawai ya gaya mata da gaske yake fadi,don
haka tadan sassauta tafiyar ba tare data kalleshi ba tace
"Ina jinka"
"Please madam ki koma gida.....kiyi haquri ba yadda
muka iya.....haka boss ya tsara......"
"Wannan kuma bazai yiwu ba,idan baka da abun fada ka
koma yafi maka sauqi" Daga hakan taci gaba da tafiyanta. A nutse take
ratsa layin,yayin da idanun 'yan sanya ido ya soma yin caa a kanta. Ba yadda
zaka kalleta ita da abdulgaffar din kace ba body guard dinta bane,saboda yake
take mata baya yana maida takunsa duk inda ta dauke ba tare da sunsan abinda ya
sanya ya biyota ba,take tsegungumi suka fara tashi,masu rade radi akan irin
mijin da zata aura a yau suka samu tabbacin hakan
Da alama
zazzafa ce itama tamkar boss din nasu,ya hanga ya hango babu wani sauran abinda
ya rage masa illa ya kira oga farouq,don haka yana biye da itan yayi
kiransa,yayi kuma bayani a taqaice.
"Turawa hood location ta watsapp...zaizo da mota ya
kaita.....idan yazo din give me a call.....zanyi magana da ita" Yayi
maganar haushin fu'ad yana kamashi.
A ganinsa
tunda batu ake na aure koma meye ya kamata ya ajiyeshi a gefe,batun aure ya
wuce wasa.....ya kuma wuce tunanin mutum.
Wani irin
aiki ne da ake yinsa da umarni da kuma doka. Iya tsaiwar da tayi tana jiran
ababen hawan da batasan dalilin da yasa duk wanda ta tsaida sai ya wuce
ba.....wanda qwarewar aiki irin na abdulgaffar ya sanya yake musu alama me nuna
gargadi kan tsaiwar tasu,take suke wucewa abinsu.
A hankali
motar ta rage gudu tana qarasowa gabansu,wanda tun kafin takai ga qarasowar
abdulgaffar ya ganeta. Motocin da dukka suka jibanci familyn muhammad jadda da
kuma gidan alhj hamza kibiya ba boyayyu bane,don hatta da plate number dinsu na
dabanne da wani irin kebantaccen tsari na daban.
Bai bari
motar ta qaraso gabansu ba ya kirayi farouq din,sai komai yazo a daidai,isowar
motar gabansu da kuma matsawa da yayi daura da ita ya saka wayar a handfree
yadda idanunta zasu iya ganin wayar
"Ranki ya dade......Allah ya taimakeki,tuba muke,kunyi
magana da boss yana cikin fushi ne.......ayi mana alfarma kiyi haquri,ga driver
da mota nan ya iso,ki shiga ya kaiki duk inda kikeso,tuba muke,tuba muke"
Ya maimaita har sau biyu yana hade tafukan hannayensa guri daya.
Batasan me
ysaa ba,amma sai taji tasss ta sauka daga fushin da takeji. Yanayin maganarsu
dama komai nasu ba daya bane,batasan kuma waye ba......sannan batasan nasabarsa
dashi ba.....amma da iya lafuzan bakinsa kadai ta tabbatarwa kanta yasha banban
dashi tako ina.
Batace
komai ba ta soma takawa tana nufar motar da tuntuni suka wagale mata qofar suna
tsaye suna jiran isowarta,tadan dubi security din kadan ta kauda kai tana tabe
baki. Su kuma a haka rayuwarsu zata qare?,basa da aiki sai ta'ammali da murda
murdan garadan da babu rahama akan fuskarsu?,idan kuma suna tsaye sai kace
gumaka?,wacce irin rayuwa zata shiga ne?. Da wannan tambayar ta shiga cikin
motar suka maida murfin suka rufe.
Duk da
yadda ranta yake a bade,zuciyar kuma bata tare da komai amma hakan bai hanata
fahimtar banbancin inda ta shigo ba. A hankali ta kalli wani sashe na
motar,cikin ranta tana jin zallar tsagwaron banbanci. Batayi kuskure ba idan
tace tsahon rayuwarta bata taba tsammanin da gaske akwai mota irin wannan a
nigeriar mu ba,cikin motar bai mata kama da komai ba saida wani qawataccen
madaidaicin falo na alfarma,idan ba yaye labulen window din kayi ba zata ko dan
jirin motsin motar kadan ba saika tsammaci cikin wani killataccen falon kake.
Taja numfashi a boye tana saukeshi,duk da ita kadaice a nan amma saita killace
ganinta. Bangare daya zuciyarta tana bugawa da samun tabbacin lallai da gasken
da kawun ke fada su din ba qananun mutane bane......amma ta yaya suke bibiyan
rayuwarta?,me yasa sai ita?,me suke tunanin tana dashi wanda zata iya basu?.
Amsar dai kamar kowane lokaci.....hasashen kaman na kowanne lokaci shine AKWAI
WANI ABU A QASA.
Da wani
irin makirin narkakken murmushi ta maida murfin qawataccen akwatin ta rufe
bayan ta gama ganin suturar alfarmar da aka tsumata da wasu tsatsube tsatsube
na musamman da suke a mazaunin matakin farko na fara tunkarar shirin data yiwa
rayuwar mutum biyun.......sanadin wato sabreen.....da kuma maqasudin wato
muhammad fu'ad.
"Komai yayi hajja........suturar million biyu kam baa
kashe kudinsu a banza ba.......yanzu zuwaira za'a aika?.....inajin kamar nayi
tattaki naje nakai Mata da kaina,don inaso ta fahimci muhimmancin sanya suturar
nan" Tayi zancan da wani irin muhimmanci cikin sautinta,tana tuna bayanan
bokan da bata dana biyunsa a yanzu haka
_".......tana sata a jikinta ta fara zuwa hannu fa
hajja......hakanan shi Kansa fu'ad kallon farko da zaiyi mata da suturar zai
jarabtu da sonta,abinda zai bada damar gudanar da aikinmu cikin sauqi,zai karbi
komai daga hannunta yaci ya kuma sha ba tare da wani matsala ko tangarda
ba"_
Murmushi
hajja ta saki tana dora qafarta daya saman daya
"Tafiyar zuwaira ita daya yana nuna aiken bame daraja
bane,hakanan zuwanki da kanki zai jefa shakku a idanun mutanen da hankulansu ke
kanmu irin aminatu hamza kibiya......wannan saqon babbar aminiya kuma
amintacciya ya kamata ta isar dashi" Murmushi me sauti ya qwacewa
maamah,ta bawa hajja hannu suka tafa tana fadin
"Allah yabar mutum da nasa.......bari na yiwa usama
magana" Ta fadi tana dauko wayarta dake ajiye gefe ta fara lalubar number
wayar usaman.
Zuwanta
wajen aysha da dawowarta....farincikin data samu na ganin yarinyar ta dawo
cikin cikakken hayyacinta da wata lafiya data sanya kumatunta cikowa shine ya
haifar da sakewar fuskarta,ya kuma saka mata farincikin da ta kusa mantawa da
abinda ke tunkararta a gobe.
Kallon masu
kallo da idanun masu sanya idanu tun daga qofar gidansu da lafiyayyar motar ta
ajiyeta bai dadata da qasa ba,har zuwa sanda ta isa tsakar gidan,ta kama
matakala tana haurawa zuwa saman nasu.
Tana sanya
qafarta sukayi kacibus da momma dauke da tray da lemuka da ruwa akai.
"Yauwa yanzu nake shirin kiranki......kina da baqi suna
qasa,ki hanzarta ki samesu" Ta gaya mata tana rabata zata wuce
"Baqu momma?,su waye?,daga ina kuma?"
"Kinga duka wadannan tambayoyin ki adanasu idan kinje
kyayi musu.....me lalle ma ke take jira tunda kika fita". Ambaton sunan me
lalle saiya fara dagula mata lisssafi,bayan dirje fatar da aka dameta dashi na
kwanaki kusan goma yanzu kuma wani me lalle ne na daban zata zauna yi?,salon a
bata mata hannu da qafar da bata shirya diga musu komai ba?.
Ganin
momma tayi gaba har tana gangarawa qasan stairs din ya sakata itama ta laqume
dukka tambayoyinta tana wucewa ciki. Zuciyarta fal da saqe saqe ta sauya abayar
jikinta zuwa wata sassauqar doguwar Riga cotton me gajeran hannu data zauna
daidai jikinta,ta dauki qaramin hijab daya tsaya mata iya kafadu ta maqala ta
juyo tana saukowa.
Dukkansu
su biyun suka amsa mata sallamar idanunsu a kanta
"Tubarkalla ma sha Allah" Zuwaira da tayo rakiya
ta qarfi da yaji don ba haka Hajja taso ba ta furta kyan sabreen yana bugar da
ita. Duk yadda take jin hira da yadda aka tsara komai bata taba kawowa kyan
yarinyar yakai haka ba,ta dauka maamah din nada tsananin wayo......zata dauko
yarinyar da bata da cikakken siffa gudun juyewar reshe da mujiya. A iya sanin
data yiwa halittar 'ya'ya maza masu jarabtuwa da kyakkyawar mace komai
kamewarsu kuwa. Sanda suka iso gidan batayi tunanin gidan masu matsakaicin
qarfi da gata irin wannan yana qunshe da kyakkyawar sura har haka ba,taci gaba
da qare mata kallo yadda shape me qirar Coca-Cola ya fita sosai ta cikin rigar
ta wajen qugunta.
Duk kallon
da zuwaira ke qare mata hankalinta baikai ba,saboda hankalinta daya tafi akan
hajja da suka fara hada idanu. Ta yaya zata manta fuskar matar?,bayan tana a
wajen sanda sukazo da tallar qazamtacciyar hajarsu?,kuma kusan itace tafinta a
wajen matar dake iqirarin mahaifiya take a wajensa.
Yadda
sabreen din ta tsareta da idanu tana zama a dosane a hannun kujera irin yadda
takeyi idan zuwan mutum magana ko mu'amala dashi baiyi mata ba
"Sannu ko?" Hajja ta fada tana qaqaro murmushin
dole. Wani irin kishi me girma ya sauko mata akan Sabreen din. A haduwarsu da
suka taba yi qwaya biyu hankalinta bai taba kaiwa kan sassanyan kyan da
yarinyar ke dashi ba. Wani irin halakakken kyau dake boye a kowanne sashe da
kuma halittarta. Anya wannan ba kuskure bane?,idan har tayi saken daya fadawa
sonta rabasu kuwa zai zama abu me sauqi kuwa?.
Tabbas
bata taba kula da wannan kyan ba,wanda inda tasan dashi tana da dukkan makaman
da zata rusa tafiyar........a yanzu bayan komai yayi nisa ta yaya zata katse
wannan wasan da bata taba ganin abinda maamah ta ciwa buri a kansa har haka ba.
"Yauwa sannu" Sabreen ta maida mata da salon yadda
tace da ita. Haka kawai taji ba zata iya gaida matar ba,tun a waccar ranar duk
wata kima martaba da kuma mutunci da ake ganin dan adam me girma da shekaru
nasu duka su biyun suka kwaranye mata.
"Ya gida ya shirye shirye?" Hajjan ta sake
dauriyar fada yadda sabreen din ke shan qamshi yana qara qona mata rai,amma
duka wannan ba komai bane......tasan s nan kusa zata fahimci wace ita?kuma su
waye su.
"Alhamdulillah" Ta sake amsa musu. Kai tsaye hajja
ta gabatar da abinda ya kawosun,da dukkan alamu sun nuna ba'a maraba dasu ata
nan din
"Saqone daga mamarki" Hajja ta fadi tana
turawa zuwaira akwatin,ita kuma tana
sadar dashi xuwa ga sabreen dake binsu da idanu.
𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐓𝐀
𝘭𝘪𝘵𝘵𝘢𝘧𝘪𝘯 𝘬𝘶𝘥𝘪
𝘯𝘦
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 8
Page 8
Duniya ta
Sai data qarewa akwatin me ruwan gold kallo,sannan a nutse
ta aza kallonta akan hajja,don tayi yaqinin itace jagorar tafiyar kamar wancan
karon.
Kallon
kallo ne dake nufin ina buqatar qarin bayani. Da yake hajja din 'yar gari ce
har ta fahimci ma'anar kallon,ta saki wani qaramin murmushi sannan tace
"Kusan duk inda akace ana arziqi tsiya guduwa
takeyi.....lallai ba shakka kina cikin matan da sukazo duniya a sa'a da har
tarihi zai baki daman kasancewa matar muhammad jadda.......wannan suturan ta
lashe miliyoyin kudi.....kuma an tanadeta ne kawai saboda ki sanayata a ranar
da za'a miqa ki zuwa gidan fuad,wannan shine burin uwar mijinki da kuma umarni
na farko da takeso ki fara dauka cikin tafiyar ku......lallai ne muddin kika
kasance me biyayya ina miki busharar keda sunan talauci kinyi adabo.... Aiki ne
na qididdgaggun watanni,amma ribarsa zaki ci gaba da cin gajiyarta har qarshen
rayuwarki data zuri'arki". Idanu ta lumshe a nutse sannan ta budesu. Tana
jin wani murmushi yana taso mata daga qasan zuciyarta amma kuma batason
bayyanarwa hajja dashi. Shin sun dauka ita din wawiya ce da har zata aminta da
komai daya fito daga garesu?,sunyi tsammanin shirunta galaba ce a tare dasu?,ko
sauraro da dakonta a kansu suna tsammanin alkhairi ne?.
Zamowa tayi
a nutse daga saman kujerar ta zauna a gabansu gaba daya tana langwashe qafarta.
Idanunta tsakiyar na hajja ta soma magana da nutsuwar nan tata dake qarawa
maganarta kwarjini da fahimta a muryar me sauraro
"Ina zaton aikin data nema daga gareni zaya tsaya ne
kawai iya kan danta.......aiki kawai tace zanyi mata na wata uku ko
hudu......bata da hurumin komai cikin rayuwata.....kama daga cima ko
sutura......" Ta tsaya iya haka tana maida numfashin bacin rai. Ranta ya
fara dugunxuma na ganin yadda suke qoqarin maida rayuwarta tamkar gare gare
tsakanin uwa da d'anta da suka zamo tsatso daya......abinda sam ba zata lamunta
ba kenan,ita tayi mata......danta ma yayi mata?,shin ummeeenta su ta haifawa su?.
A
mamakance hajja ke binta da kallo,bata taba zaton haka daga gareta ba,kallon
hajjan ya isheta hakanan,dom haka ta miqe cikin rashin damuwa tana gyara
lullubin kanta tace da ita
"Ki gaya mata damuwarta ta tsaya iya kan aikinta
kawai......indai tace zata hada da shigar da rayuwar sabreen......komai bazai
tafi yadda take tunani ba.....ni din tamkar wahainiya nake a wasu
lokutan.....sawun keke da gane gabansa yake da wahala koda a wajen
gwanaye".
*MAAMAH*
Idanunta ta
runtse bayan hajja ta jera mata dukkan wadannan bayanan da sabreen ta aiko mata
dasu ba tare data rage komai a ciki ba.....koda ta manta wani abun zuwaira dake
gefe tana taso mata dashi. Ta bude idanunta cikin bacin rai tana duban akwatin
da iya shi daya kawai kudi ta zuba masu yawa,banda kayan banda kuma aikin da
akayi akan kayan.
"Yarinya ce qarama tabbas.....amma na yarda da gaske
tana da hadari........tana kuma da wasu boyayyun abubuwan da bamusan dasu
ba......iya kalmominta na yau sun sake zaburar dani akan dole na ninka shirina
a kanta......amma ba wannan ba.......asarar data sani nayi tun a matakin farko
yafi damu na....."
"Kada ki damu.......akwai mataki na biyu da nayi imanin
ba zata tsallakeshi ba......saidai shi na biyun bangare daya ya
qunsa.......bangaren cusa soyayyarta a zuciyar fuad ya saraya,saidai a samo
masa wata hanyar ta daban". Ajiyar zuciya maamah ta saki tana jin
sassaucin tashin hankalin dake sauko mata
"Wannan dinma wahalar da nayi a kansa bazai tafi a
banza ba.....koda bataso sai tayi amfani dasu,ta hanyar da takeso ko ta hanyar
da bataso bata kuma shirya mata ba". Daga haka ta jawo akwatin ta cusashi
qasan lafiyayyen gadonta.
𝙈𝘼𝙁𝘼𝙍𝙄𝙉
𝙏𝘼𝙁𝙄𝙔𝘼𝙍......
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
Tamkar jira
akeyi su kammala sauka daga jirgin,wayarsa dake riqe hannun daya daga cikin
guard dinsa da tun tafiyar zuwa yanzu shike da alhakin riqe masa ire iren
wadannan kayan nasa.
"Sir.....oga farouq" Ya sake matsowa kadan bayan
fuad yana fadi cikin rusunawa. Baice komai ba ya miqa masa hannun shi kuma ya
dora masa wayar,ya dawo da wayar fuskarsa yana duban kiran farouq din yana ci
gaba da takawa yana fita a wajen.
Boyayyen
murmushi ya saki,tun jiya ya kashe wayarsa dama duk wani hanya da farouq din
zai sameshi,yasan tabbas idan ba haka ya masa ba bazai shafa masa lafiya ba,zai
birkita masa lissafi ne kawai.
"Idan baka da niyyar dawowa ne malam ka yiwa mutane
magana.......awa uku kadai suka rage awannin daurin aurenka su cika......amma
still ace baka iso ba?".
"Who told you dude?.....mu hade a Bristol,banason
hayaniya" Daga haka ya kashe wayar ya miqa masa yana magana dashi ya tura
masa number dakin da yayi booking already. Yana da gidajen da zai iya sauka a
cikin su,saidai sam sam baya shaawar ya sauka a can din gudun kada a cimmasa a
dameshi da damuwa.
Abinda
bai sani ba yayi gudun gara ne,don kusan mafi yawan abokansu da sunzo ne don
farouq a Bristol din sukayi masauki.
Sanda saqon
yakai wayar farouq shafa kansa kawai.yayi,yaci alwashin sai ya rama wasa da
hankalin da fuad din yayita yi masa. Ya ajiye wayar yana kiran musaddiq kan ya
fiddo mota yanason kai yakai ga fitowa su ruskeshi a can.
Yayi
mamakin ganin motocin jadda har guda biyar a wajen suna jiran isowarsa. Bai
gama wannan mamakin ba farouq ya fito cikin daya daga cikinsu yana qoqarin rufe
wayarsa ya jefata a aljihu.
Wani kallo
me kama da harara ya watsama fuad din wanda ya jingina kawai jikin daya daga
cikin motocin yana kallon qarewar fushin farou a kanshi. Ya sani shi ko farouq
din babu me iya fushi da dan uwansa.....duk wani abu da daya daga cikinsu zai
fadi burga ce kawai da cika baki,da zarar sunyi face to face yake wucewa tamkar
bai faru ba.
Koda ya iso
duka yakai masa ya goce yana wannan tsadajjen murmushin nasa
"Haka kawai ka nakasani bayan banyi komai ba?" Ya
furta murmushin yana shimfide a fuskarsa
"Sa'arka daya wallahi......yau babbar rana ce"
Farouq ya fadi yana buda masa murfin motar da kansa. Sai daya shiga sannan yabi
bayansa,yana zama wayarsa kuma ta dauki tsuwwa ya ciro yana amsata.
Tunda suka
taho a hanya farouq ke amsa wayoyin mutane iri iri. Yana ankare dashi amma
baice komai ba,ko a iya haka ya samu alama da shaidar lallai gayyar jama'a
farouq din yayo.
"Kada kacemin tsayawa kayi ka batawa kanka lokaci
kayita kiran mutane?" Yayi maganar yana tabe baki cikin rashin bawa abun
muhimmanci. Wani kallo ya watsa masa
"An gaya maka kowa irinka me wai?,kai abinda ka dauka
daban.....yadda mu muka dauka......aure komai lalacewarsa sunansa
aure.....barema ba lalataccen koda na bariki ne".
"K'nnnnn" Kawai ya fada yana zamewa gami da yin
relaxing sosai jikin motar
"Nidai muyi mu qarasa,bacci ne a ido na,kwanakin duk da
nayi acan ba wani bacci na samu ba".
" Mutuwa zakayi ba bacci ba" Farouq ya fada cikin
harzuqa. Kallo daya ya yiwa farouq din ya lumshe idonsa yana cewa
"Allah ya baka haquri" Daga haka bai sake cewa
komai ba kaman yadda bai kuma bude idonsa ba har sukaje.
Da
lallausan farin towel ya fito daga toilet din dakin daya zame masa masauki
daure a qugunsa. Ya qarasa gaban madubin dakin yana duban yadda farouq ya zube
masa duk wani kayan shafawarsa. Duddubasu yayi kawai ya ajiye yana mamakin
yadda farouq ya dauki auren nan serious. Sai ya jawo stool ya zauna akai yana
kallon kyakkyawar fuskarsa ta cikin madubi gami da sanya qaramin towel yana
tsane ruwan kansa. Koda ya gama sai ya aje towel din,ya soma lalubar wayoyinsa.
Sunyi da larab zai kirashi don ya tabbatar an gama design na hall din dake
cikin kamfanin inda za'a gabatar da taron budeshi a jibi kaman yadda ya tsara.
Gajiya yayi
da dube dubensa,sai ranshi ya bashi farouq ya kwashesu. Qaramin murmushi ya
saki,yasan zai aikata,kuma duk zaiyi hakanne don ya tilastashi shiryawa. Duk da
abun ba wani muhimmanci gareshi ba a wajensa.....amma farouq ya tattara duka
lokacinsa akan komai dason ganin komai ya tafi daidai din,ya qarasa gaban
madubin ya sake zama yana bude lotion dinsa na dindindin ya fara shafawa. Yana
tsaka da taje sumarsa me tsananin daukan hankali aka murda handle din aka
turo,bai motsa ba don yasan mutum daya ne zai masa haka.
Ta cikin
madubi ya hangoshi ya shigo. Sai ya samu kansa da dan qare masa kallo. Yayi
kyau cikin wata irin danyar shadda dake nuna nauyin kudaden da aka narkar domin
siyenta,aka kuma keta alfarmar nera tare da nuna mata iyakarta wajen tsara mata
dinkin jikinta.
Farar
hula ce saman kanta da aka yiwa nadin farin rawani,wanda aka saki jelar rawanin
ya zubo ta qirjinsa daga gefan kafadarsa ta dama. Iya abinda ya iya gani
kenan,amma fadin yadda shigar ta qarawa farouq din kwarjini ma ba'a magana.
"Kayi kyau ango" Ya fada da sigar zolaya yana
maida idanunsa saman mirror table din yana aje comb din hannunsa tare da
lalubar hair spray.
"Kaima yanzu zakayi naka kyan.....don komai namu iri
daya zai kasance". Da sauri ya daga kai ya kuma juyo gaba daya yana
dubansa hadi da fiddo sexy eyes dinsa sosai zuwa waje,abinda ba kasafai ya fiya
yi ba
"Wanne irin rigima ne wannan farouq?,kafi kowa sanin
banason manyan kaya basu dameni ba......for god sake zakace babban riga zan
saka harda wani qarin rawani kamar nine zan jagoranci sallar juma'a na yau
din?".
Watsa
hannuwansa farouq yayi
"Kai ka sani" Ya fada a gajarce yana nufar inda
kayan suke ya soma ware masa.
𝐃𝐮𝐧𝐢𝐲𝐚𝐭𝐚
𝐧𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐧𝐞
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 9
Page 9
Duniya ta
Tsaye yayi
ganin da gaske farouq din yake,daga qarshe baida wani zabi illar amsar kayan
daya dinga yi da daya da daya yana sanyawa.
Komai
nashi fari ne qal yayi amfani dasu,tun daga undies har zuwa complete suturar
jikinsa. Qerarren handmade half shoe din me ainihin tsada da kyau gami da
daukan idanu dan asalin qasar italy,da agogon rolex me asalin daraja da ya samu
ado daga wani yanki na gold din da kamfaninsa ke sarrafawa.
Gurin saka
rawanin akaso asha daru,amma shigowar ahsan cousin din farouq ya raba gardaman.
Shi ya karba ya nada masa shi tsaf saman kansa
"Ya subhanallah......ya Allah,na taba ganin wanda
rawani ya yima kyau kaf tsayin rayuwata kuwa irinka?.....amma ban taba ganinsa
dashi ba farouq" Ya maida tambayar kan farouq sanda fuad ke tsaye gaban
madubin yana kallon yadda fuskarsa ta fita fes kamar an sauya masa ita. Wani
annuri shi kansa yaga tana futarwa wanda bai taba gani ba,da gaske manyan
sutura suna qarawa mutum kwarjini,karon farko yaji manyan kaya suna sake
burgeshi.
"Lokaci yayi" Yaji farouq yana fada ba tare da
yaji amsar da ya bawa ahsan ba.
"Ya
salam" Ya fada sanda suke yo tattaki shi da farouq da ahsan zuwa ma'ajiyar
motoci na Bristol din. Yawan matasan masu jini a jika daya gani kowa cikin
shigar fararen kaya da babbar riga ya bashi mamaki. Abokan da da yawa ya manta
dasu,wasu kuma haduwa tayi wahala,saidai kowa a cikin su yana cikin jerin sahun
matasan da suke wasa da kudi som ransu saboda samun cikakken sukuni da arziqin
rayuwa. Parking lot din ya cika gaba daya da motocinsu,ta wannan tana wane
wannan,a haka ya qaraso gurinsu da natsattsen takun nan nasa kamar namijin talo
talo.
Daya
bayan daya yake basu hannu suna gaisawa,wasu su zolayeshi wasu suyi masa
qorafi. Da yawansu bashi da abun cewa,musamman yadda yaji gabbansa sunyi sanyi
da ganin mutanen da farouq din ya tara masa duk kawai dondai su shaida daurin
auren da bai gama gamsuwa da yiwuwarsa ba. Ba wanda shigar fuad din bata dada
da qasa ba,don ya dace da shigar ainun,harma tafi karbarsa sama da farouq din.
A nan suka
kashe wasu mintuna kusan sha biyar ana rudu irin na abokai,gaba daya wajen ya
dumame da qamshin turaruka masu tsananin tsada,daga bisani suka fara shiga
motocinsu suna tashi daga wajen. Convoy sosai suka hada da jerin gwanon motoci
masu tsayi,kusan daurin auren sanannen labari ne daya karade kowa,don haka duk
inda zasi gifta sai ya zamana kamar suna sake bada sanarwar afkuwar abun. Duk
inda suka gifta saisun wafci hankula da kyawun motocin,kowanne traffic suka je
ba jinkiri ake daga musu qafa motocinsu su wuce tas,don haka basu wani kashe
lokaci sosai a hanyar ba suka isa inda suka nufa.
Bai sake
ji a jikinsa komai da gaske bane sai sanda suka isa alu avenue dake
nasarawa,masallacin alfurqan inda acan aka tsaida don shaida daurin auren.
Jikinsa yayi wani irin sanyi sosai,yana ganin da gasken gaske komai yake wakana
lallai.
"Ya salam.....ya subhanallah" Kawai yake fada a
ranshi. Irin taron dafifin al'ummar daya gani bai taba zaton zai samu irinsu a
gurin ba........manyan mutanen daya samu a wajen bai taba koda kawowa zai
samesu a wajen ba.....duba da ba wani mutum daya daya gayyata da bakinsa.
Manyan 'yan kasuwar duniya daga qasashen duniya daban daban......manyan 'yan
siyasa da qusoshin gwamnati......shugaban qasa da attajirai gami da duk wani me
fada aji,don kusan kowa qarin martaba ne a tare dashi halartar daurin auren.
Basu ma
kai ga samun damar isa cikin masallacin ba saboda yawan al'ummar dakeson
ganinsa tare dayi masa fatan alkhairi. Baisan iya dadin yawan manyan mutanen
daya jima bai gani ba amma yau daurin auren ya tattarasu waje guda
ba.....baisan kuma adadin su nawa ya gaisa dasu ba,har zuwa sanda kunnuwansa
suka jiye masa ta lasifiqan cikin masallacin data fito waje tana fadin.
"Mun shaida daurin auren matashin attajirin dan kasuwar
gold MUHAMMAD FUAD JADDA da amaryarsa
AMEENATU AHMAD MU'AZZAM".
"AMEENATU?.....why?. Me yasa aka sanya mata wannan
sunan?" Ya furta can qasan ransa. Ta yaya zai zamana tana da suna me
matuqar martaba da mutunci a idonsa irin wannan?,why..... Full name din da aka
kirata dashi bai tuna masa komai ba sai kawun nata rufa'i,ranar daya samu fill
details nashi da wannan sunan ya sameshi. Ya saki siririn tsaki yana jin ranshi
yana baci. Inda mutane sunsan ko su waye su da basu bata kudadensu ba wajen
siyan ticket na jirginsu sun cika jingim wajen shaida daurin auren ba,ya sake jan
qaramin tsaki yana juyawa tare da neman nesanta kansa da hayaniyar wajen,guard
dinsa da duk hautsinewar wajen basu yarda sun matsa ba suka biyoshi a baya.
Can wajen
motocinsu ya koma,sai daya shiga ya zauna sannan yace musu
"Don't.....karku gayama kowa ina ta nan idan ba farouq
bane ya tambaya".
"Yes sir" Suka amsa a matuqar ladance suka maida
murfin suka zuge masa.
Rawanin
duka da babbar rigar ya cire ya ajiye gefe,sannan ya koma ya zauna sosai yana
nazarin wajen ta cikin motar. Abinda ya lura dashi,bawai farouq kadai ba,hatta
da abba ya dauki abun very serious,yaga mutanensa a wajen har baisan adadinsu
ba......haka anni,yaga familynta sosai,tamkar tana auren farouq ne,sai ya maida
idonsa ya kulle yana son tuno waye da waye ya gani daga bagaren maamah?.
Bai samu
nasarar kaiwa qarshen tunaninsa ba knocking da aka yiwa glass din motar ta
sakashi bude ido,ya ganshi farouq ne,yana daga kwancen ya danna remote ya bude
mass murfin.
Dubansa
yayi sanda yake qoqarin shigowa
"Reception zamu wuce.... Already wasu sun fara yin
gaba,musaddiq da saddiq tun dazu suna ta wajen". Shi sai a sannan ya tuna
ma.baiga kowa cikin su ba,ason ranshi farouq din ya barshi ya koma masauki ya
kwanta ya rama baccin dake.kansa,ya kuma rage hayaniyar mutane da yakeji har
cikin kansa,saidai kuma ya sani koda yace zai masa bayani ma farouq din ba
fahimtarsa zaiyi ba,yadai fadi abu daya
"Ina fatan daga can duk wata hidima ya qare baku
qirqiri komai ba kuma......don bazan iya jure zuwa wajen komai ba".
" Wanda baisan halinka bane zai wahalar da kansa shirya
wani abu......walimar.ma saboda cika sunna ne da neman albarkar auren"
Farouq ya amsa masa yana daga kiran abokinsa da yake gaya musu sun isa wajen
"Muma muna dab......ka jirani" Yace yana sauke
wayar. Siririn murmushi kawai fuad ya saki,farouq.....farouq..... Idan ba
farouq babu shi.......kaman yadda yasan idan babu shi babu farouq din.
Tunda
momma bahijja ta tilastata tayi wanka,ta kuma shirya cikin wata sabuwar atamfar
Hilton wax. Cikin kayan da momma ta zare cikin lefen ta bayar aka dinka ba tare
da sanin sabreen din ba. Tun tana shiryawa taji shigowar uncle abdulhakeem da
tun jiya suka iso suka kwana a tahir guests palace. Zancan duka ya shafi
aurenta ne,wanda duk kalma daya da zata fita daga bakin uncle din nata sai taji
kanta ya wani sara mata. Zazzafan mutum ne da ta jima bataga mutum me zafi da
kafiya akan gaskiya ba irinsa. Ta jima tana tunanin idan ta kammala deal dinta
ta tashi matsawa daga gurbin da take zuwa wani ta yaya zata bacewa idanunsa?,ta
kuma zullewa duk wata tuhuma tashi?. Taji ya ambaci sunan su huda da nadra da
tafi sati tana tunanin ina za'ayi da rayuwarsu?,amma tasan tayi kadan ta tsaya
gabansu ta musu wannan tambayar,bata kuma samu jin abinda suke cewa ba
sanadiyyar hayaniyar yan tafiya daurin auren data qaru. Ta gama shiryawar taji
wani zazzabi ya sauko mata bayan ciwon kanta daya dinga gaba gaba saboda
tunanin data matsawa kanta dashi,sai kawai ta lallaba can gadonsu nadra dake
qarshe ta haye can ta qudundune.
𝐃𝐮𝐧𝐢𝐲𝐚𝐭𝐚
𝐧𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐧𝐞
𝟎𝟖𝟏𝟖𝟕𝟐𝟓𝟓𝟖𝟔𝟐
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 10
Page 10
Can cikin
tsakiyar kanta maganganun mutane ke mata yawo sanda motar ke tafiya cikin
nutsuwa saman lafiyayyar kwaltar dake shimfide a kanta. Muryoyin mutane daban
daban da sukayi mata fadan shiga gidan miji wai a cewarsu
"Allah yasa dai ki iya zama......don zaman aure daban
da zaman bariki,zaman gidan miji daban da yawon bariki" Muryar bibo kenan
da nata salon fadan da yafi kama da turun mutuwa
"Da dadi ba dadi kiyi haquri ki zauna......Allah yasa
mutuwa ce zata raba,kiji kiqi ji,ki gani kiqi gani" Muryar daada kenan
wadda ta kama hannuwanta tana fada muryarta a sanyaye. Ko da can ba zatace ga
wani mummunan abu da daada ta taba musu ba,ita dai barta da shariya da rashin
shiga lamari da sabgar kowa cikin gidan. Idan ka ganta kuwa a ciki to tabbas
abu yaci tura,amma bibo da yaabi koda dan wani akeyi suna iya ara su yafa tun
usul.
"Mommaa......nadra.....haneefa.....huda" Sunayen
data iya kirawa momma kenan sanda take yunqurin sakata a cikin motar da zata yi
musu jagora zuwa inda zasuje.
"Ina sane dasu......kuna su din ba nauyinki bane"
Ta amsa masa a tausashe.
Ta cikin
lafayar jikinta take iya hangen yadda motar ke tsala gudu abinta,amma saboda
lafiyar motar da irin tsarin da akayi mata zaka rantse ba gudun takeyi ba.
Ta maida
idanunta ta lumshe,wasu hawaye da batasan sanda suka taru ba suka biyo kuncinta
suka diga bayan hannunta dake ajiye saman cinyarta. Har yanzu dai ta kasa
gasgata abinda take gani,har yanzu ta kasa gasgata abinda kunnuwanta da
zuciyarta ke nanata mata.
Da gaske
mutumin nan yaci galaba a kanta da dukka tsarikansa.....da gaske shike da
nasara ba ita ba.......da gaske ya cinye wasan a wannan gabar.....saidai kuma
hakan baya nufin zaita nasara kenan a kanta,hakan baya nufin ta fadi kenan har
abada.....lallai zata canza labarin......zata canza qaddarar da dukkan
iyawarta.
"Gidan mamarshi zamu fara shiga.......sai gidan
riqonsa,kamar haka matar data shigo dazu tace ko?" Daada ta fadi tana dan
duban momma bahijja da hannun sabreen yake cikin nata.
"Eh haka ne" Ta amsa mata idanunta sauke kan
faffadan sabon gate din gidan maamah dake nuna zallar dukiyar dake narke cikin
gidan.
A nutse
jerin gwanon motocin suka cusa kai makekiyar harabar gidan data kasance
mafarkin maamah na shekara da shekaru,gidan daya dauki hankula da bakunan
dukkan jama'arta dake hulda da ita. Gidan da a cikin ranta ita kanta ta gamsu
da dukiyar daya lashe,amma zuciyarta bata gama nutsuwa da hakan ba saboda har
yanzu gidan alhj hamza kibiya da iyalinsa yafi nata girma yalwa da kuma
tsari,ba tare data duba yawan da suka darata dashi ba,da kuma yawan al'umman da
gidan ke dauka suke riqo a yanzu haka.
Tunda motar
ta tsaya a parking lot na gidan gabanta yake wani irin faduwa,ta maida idonta
ta lumshe tana sauraren bugun da zuciyarta keyi da bata taba jin irinsa ba,sai
taji bugun har kusa da maqogoronta. Sake runtse idanunta tayi sanda momma
bahijja ke fadin ta fito,tana jin bugun zuciyar na sake daduwa amma kuma ta
rasa me ya kamata ta karanta?,wacce addu'a ce ta dace da irin wannan yanayin da
takejin kanta a ciki?.
Riqon
hannunta da momma din tayi shine ya sassauta mata abinda takeji kadan,ta sake
riqe momma din itama da kyau ba tare tasan ta yadda zata gaya mata abinda
takeji cikin qirjinta ba.
A dan
hanzarce ta shigo dakin nata,sannan ta maida qofar ta kulle ta kuma murza key.
Da dan hanzarin still ta isa gaban madubin nata dake manne da wasu lafiyayyun
lockers. Ta murza daya daga ciki ta bude ta,sannan ta saka hannu ta ciro baqar
ledar dake a ciki ta dora saman madubi. Ko ina a jikinta amsawa yakeyi da wani
irin doki da son fara aiwatar da nata aikin,a yau batasan sau dubu nawa tana
addu'ar samun wannan sa'ar ba......batasan sau nawa ta roqi samun nasara a
wannan ranar ba,nasarar da indai ta rasata kamar wadancan kwanakin ta tabbatar
komai zaizo mata da wahalar gaske.....batasan kuma ta yadda zata tari abun ba.
Kusan leda
shidda ce,kowacce sai data kunceta sannan ta saka hannu ta fara ciro kayan
ciki. Kusan tarkace ne a idanun me kallo,amma a wajen maamah gwara rashin
million dubu da rasa daya daga cikin kayan. Wasu kwalabe ne masu dauke da wani
irin baqin abu a ciki,wani kuma kore kore ne,saidai yana da dan qamshi qamshi
kadan a ciki mara qarfi. Ta bude kowanne ta tsiyaya cikin tafin hannunta,ta
kuma mulke hannun nata da kyau kamar yadda aka umarceta da tayi,sannan ta maida
komai muhallinsa kamar bata taba komai ba cikin dakin.
Gaban
madubin ta tsaya tana qoqarin controlling kanta da daidaita nutsuwarta. Idanun
ta fes cikin fuskarta tana maganar zucci da kanta da kanta,wanda batayi wani
nisa ba knocking din da ake mata ya isa kunnuwanta. Adan fusace tace tambaya
don bata buqatar doguwar mu'amala da kowa har sai wadda tayi shirin saboda ita
ta iso
"Zuwaira ce" Ta bata amsa a tsanake.
"Sun iso,suna falon qasa sun......."
"Gani nan" Ta tari numfashin zuwairan ba tare data
jira sauran bayaninta ba. Ba sauran bayaninta take da buqatar ji ba,tunda taji
abinda take buqatar jin,ta waiwaya tana zura takalmanta data cire tare da
kallon tsadajjen mayafin data lullube jikinta dashi ta tabbatar ya zauna a
jikinta......ya sanyata tayi kwarjini da wata irin kamala da sam zai wahala ka
kawo wani abu me muni a kanta. Kyanta ya bayyana.....kamanninta da musaddiq
sosai,yanayin jin dadin da kulawar data samu wadda take rainawa ta sake sanyawa
jikinta ya murje sosai,hutu da quruciya sun bayyanar mata.
Murmushi ta
sakarwa kanta da kanta,sannan ta juya a hankali tana fita a dakin.
Tun daga
saman stairs din take raba idanunta tana son hangota. Bata wani sha wahala
ba,ta hangeta zaune saman lallausan carpet din da aka qawata tsakiyar falon
dashi. Qafafunta a tanqwashe suke,kanta a qasa cikin shigar laffayar da tazo
mahadin lace din da aka zauna akyi dukka adon jikinsa da hannu(handmade
lace),kamar yadda lafayar jikinta itama duk wani zare da duwatsun jiki da hannu
aka gameshi. Abune na masu dashi,ba wani cikar jama'a masu yawa ko cinkoso,kowa
yana zaune a nutse,yayin da gaisuwa ke wakana tsakaninsu momma da jama'ar da
suka samu cikin falon.
Da wani
irin kirki na gasken gaske saman fuskarta,faffadan murmushi da fara'a me nuna
tsantsar maraba da baqo ta iso rukunin kujerun tana furta
"Lale maraba......sannunku da zuwa......sannunku da
qoqari" Da murmushi a fuskar momma ta amshe maraban tana duban maamah tsaf
tare da karantar yanayinta.
"Bari na zauna kusa da diyata" Ta fadi tana zama
kujerar dake kusa da sabreen din.
Gaisuwa
akayi cikin mutunci dason nuna ainihin zallar kirkinta,suka gabatar mata da
amanar sabreen tare da dan qaramin jawabin girmama kowa ga sabreen din
"Itama diyata ce ai tunda yarona take aure,kuma in sha
Allah zakuyi alfahari da hada alaqa damu,Allah ya bada zaman lafiya,shi kuma
Allah ya tayashi riqo" Maamah ta furta cikin zaquwa da gajiya da bayanan.
So take kawai ta isa ga muradinta.
"Am nace ba.....idan ba damuwa inason ganin diyata a
kebance,minti biyar don Allah" Maamah ta fada tana murmushi. Ba tare da
tunanin komai ba ko kawo komai ba momma bahijja tace
"Bismillah mana......haba hajiya ai diyarku ce"
Daada ta fadi yadda momma din ta karbi sabreen yana burgeta.
Duk da
tayi gaba zuwaira ke mata jagora zuwa wani daki na daban a saman benen.....amma
saita dinga jin wani irin yanayi yana bibiyar gabobinta.
Kasa zama
tayi,tana a tsaye sanda taji zuwaira taja musu qofar ta fice.
"Zauna mana.....ki yaye wannan lullubin kan
naki......don fahimtata nakeso kiyi sosai tamkar yau ne karon farko da kika
fara fahimta ko haddace wani abu a rayuwarki" Tayi maganar cikin jerarrun
kalmomin da kana jinsu zakasan ko meye zata fada yana da matuqar muhimmanci a
wajenta.
Sai data
fara janye lullubin nata baya,sannan ta sulale a wajen ta zauna. Tana jin kamar
babu wani sauran qwarin gwiwa daya rage mata a rayuwa,duk da yadda take kokawa
da zuciyarta da qoqarin qarfafawa kanta gwiwa.
"To alhamdulillah.......komai ya kammala,kuma komai
yazomin da sauqi fiye da yadda nayi zato ko kuma tsammani........ina fata baki
manta meye manufar aurenmu ba?" A nutse sabreen din ta daga kai sannan ta
zube mata idanunta saman fuskarta. Kallonta tayi na second kusan goma sannan ta
gyada kai
"Da kyau.....da farko abinda zan fara gaya miki shine
abinda na maimaita miki a baya.......qaidar contract dina na farko shine
sirri.......inason sirri,don muddin aikin nan ya fita daga da'irar sirri zuwa
wata da'ira ta daban.....to tamkar kin wargaza rayuwarki da hannunki
ne......bayan taki rayuwar da kika wargaza kuma......kin wargaza ta 'yan uwanki
suma...." Daga ma maamah hannu tayi da hanzari tana zare idanunta daga
kanta
"Ki tsaya iya kan ameenatu kawai......huda,nadra da
haneefa,tabasu ko sako sunansu cikin sabgarki da ameenatu tamkar ganganci
ce"
"Da kyau!" Maamah ta furta tana sakin
murmushi,abubuwa biyu zuwa uku suna jan hankalinta. Gyara zamanta tayi tana ci
gaba da murmushi
"Ashe ameenatu ce....abu yayi kyau..ameenatu ta
bata,wata ameenatun zata gyara,wannan abun yayimin dadi.......qwarin gwiwarki
da rashin sarewarki ya burgeni......kariyar da kike bawa qannenki tana da
yawa,kuma ita dai ta isa ta bani yaqini da tabbacin ba zaki bari a samu failure
ba ko don saboda su......."
"Shiga maganarki kai tsaye" Sabreen ta fadi mata
tana kauda kanta zuwa wani sashe na daban. Idanu maamah tadan zuba mata har
yanzu tana murmushi,sai kuma ta miqa hannu ta zaro wata paper da abun rubutu ta
ajiye a gabanta.
"Inaso ki rubuta adadin kudaden da kike da burin
mallaka a rayuwarki......ni kuma zan mallaka miki su a madadin sadakin
aikinki,zan kuma qara miki kwatankwacinsu muddin komai yayi daidai".
Fararen
manyan idanunta ta daga ta watsawa maamah su,karon farko da idanun suka yiwa
maamah din wani kwarjini da bata taba jin irinsa ba. Murmushin da ya subuce
kuma a fuskar sabreen ya sanya mata kokwanto
"Ki fadi magana me muhimmanci saboda mutanen dake zaman
jiranki a qasa" . Maganar tata tadan daure mata kai,a nata ganin ba wata
magana da zata zama me muhimmanci a wajen sabreen sama da maganar kudin
aikinta,wanda take ganin shi kadai ya isa ya bata azama akan aiwatar mata da
komai. To amma akance......shi yaqi dan zamba ne,don haka ta gyada kai
𝗗𝘂𝗻𝗶𝘆𝗮𝘁𝗮
𝗻𝗮 𝗸𝘂𝗱𝗶 𝗻𝗲
𝟬𝟴𝟭𝟴𝟳𝟮𝟱𝟱𝟴𝟲𝟮
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶𝗕̶𝗢̶𝗢̶𝗞 ̶𝟮
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 𝟭𝟭
𝗣𝗮𝗴𝗲
𝟭𝟭
"𝗡𝗮𝗷𝗶
𝗱𝗮𝗱𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗶𝗸𝗮
𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗺𝗲 𝗹𝘂𝗿𝗮
𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶,𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻
𝘇𝗮𝗶 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶
𝘆𝗮𝘇𝗼 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝘂𝗾𝗶........𝗮𝗶𝗸𝗶𝗻𝗮
𝗺𝗲 𝘀𝗮𝘂𝗾𝗶 𝗻𝗲
𝗶𝗱𝗮𝗻 𝗸𝗶𝗻𝗯𝗶
𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝗻𝗮𝗰𝗲
𝗺𝗶𝗸𝗶,𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻
𝘄𝗮𝘁𝗮𝗻𝗻𝗶 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗻
𝗺𝗮 𝗸𝗶𝗻𝗮 𝗶𝘆𝗮
𝗸𝗮𝗺𝗺𝗮𝗹𝗮𝘄𝗮
𝗸𝗶 𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗮𝗯𝗶𝗻𝗸𝗶,𝗮𝗸𝘄𝗮𝗶
𝗻𝗮 𝘀𝗮𝘄𝗮 𝗮 𝗮𝗯𝗶𝗻𝗰𝗶,𝘀𝗮𝗶𝗻𝗮
𝗿𝘂𝘄𝗮𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗸𝗮,𝘀𝘂
𝗸𝗲𝗻𝗮𝗻 𝗱𝗮 𝗻𝗮𝗸𝗲
𝗱𝗮 𝗯𝘂𝗾𝗮𝘁𝗮𝗿
𝗮 𝗸𝗼𝘄𝗮𝗰𝗰𝗲 𝗿𝗮𝗻𝗮
𝗸𝗼𝗱𝗮 𝘀𝗮𝘂 𝗱𝗮𝘆𝗮
𝗻𝗮𝗰𝗶𝗻 𝘆𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗮
𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻𝘀𝗮,𝗻𝗮
𝘄𝗮𝗻𝗸𝗮𝗻 𝗸𝘂𝗺𝗮
𝘆𝗮 𝗸𝗮𝘀𝗮𝗻𝗰𝗲
𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗿𝘂𝘄𝗮𝗻
𝘄𝗮𝗻𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮,𝗶𝗱𝗮𝗻
𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗺𝘂 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻
𝘀𝗮𝘂 𝗱𝗮𝘆𝗮 𝘁𝗮𝗸
𝗮 𝗿𝗮𝗻𝗮 𝗺𝗮 𝘆𝗮
𝘄𝗮𝗱𝗮𝘁𝗮𝗿. 𝗜𝗻𝗱𝗮𝗶
𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗺𝘂
𝗶𝗻𝗮 𝗺𝗲 𝗺𝗶𝗸𝗶
𝗮𝗹𝗯𝗶𝘀𝗵𝗶𝗿 𝗱𝗶𝗻
𝗸𝘄𝗮𝗻𝗮 𝗰𝗮𝘀𝗮'𝗶𝗻
𝘄𝗮𝘁𝗮𝗻𝗻𝗶 𝘂𝗸𝘂
𝗸𝗮𝗰𝗮𝗹 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶
𝘇𝗮𝗶 𝘀𝗮𝘂𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗶𝗱𝗮𝗶
𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝗻𝗮𝗸𝗲𝘀𝗼......𝗱𝗮𝗴𝗮
𝗿𝗮𝗻𝗮𝗿 𝗸𝗶𝗻 𝘇𝗮𝗺𝗮
'𝘆𝗮𝗻𝘁𝗮𝗰𝗰𝗶𝘆𝗮.....𝗮𝗸𝘄𝗮𝗶
𝗸𝗮𝘆𝗮𝗻 𝗮𝗶𝗸𝗶𝗻,𝗴𝗼𝗯𝗲
𝗯𝗮𝘀𝗮𝗶 𝗷𝗶𝗯𝗶
𝗯𝗮 𝘇𝗮𝗻 𝗮𝗶𝗸𝗼
𝗮𝗺𝗶𝗻𝘁𝗮𝗰𝗰𝗶𝘆𝗮𝘁𝗮,𝗸𝘂𝗺𝗮
𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘁𝗮𝘆𝗮𝗸𝗶
𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗻𝗮 𝘄𝗮𝗱𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻
𝗸𝘄𝗮𝗻𝗮𝗸𝗶𝗻 𝗮
𝗺𝗮𝘇𝗮𝘂𝗻𝗶𝗻 '𝘆𝗮𝗿
𝗮𝗶𝗸𝗶 𝗵𝗮𝗿 𝗸𝗶
𝗸𝗮𝗺𝗺𝗮𝗹𝗮 𝗮𝗶𝗸𝗶𝗻𝗸𝗶
𝗸𝗶𝘆𝗶 𝗴𝗮𝗯𝗮........𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮
𝘇𝗮𝗸𝗶 𝘇𝗮𝘂𝗻𝗮
𝗱𝗮 𝗳𝘂𝗮𝗱 𝗸𝘂𝗺𝗮
𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘇𝗮𝗯𝗶𝗻𝗸𝗶
𝗻𝗲.......𝘀𝗮𝗶𝗱𝗮𝗶
𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘇𝗮𝗻 𝗴𝘂𝘁𝘀𝘂𝗿𝗮
𝗺𝗶𝗸𝗶 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗻
𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗵𝗮𝗹𝗮𝘆𝗲𝗻𝘀𝗮
𝗱𝗼𝗻 𝗸𝗶 𝗸𝗶𝘆𝗮𝘆𝗲
𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶
𝘆𝗮𝘇𝗼 𝗺𝗶𝗸𝗶 𝗱𝗮
𝘀𝗮𝘂𝗾𝗶......"
"𝗕𝗮𝗯𝘂 𝗯𝘂𝗾𝗮𝘁𝗮"
𝗧𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮
𝘁𝘀𝗮𝘆𝗲,𝘀𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻
𝘁𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗲 𝘁𝘀𝗮𝘆𝗲
𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗴𝘆𝗮𝗿𝗮
𝗹𝘂𝗹𝗹𝘂𝗯𝗶𝗻𝘁𝗮.
𝗪𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝗺𝗮𝗺𝗮𝗸𝗶
𝗸𝗲 𝗵𝗮𝗷𝗶𝗷𝗶𝘆𝗮
𝗱𝗮 𝘇𝘂𝗰𝗶𝘆𝗮𝗿𝘁𝗮
𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗸𝗲
𝘀𝗮𝘂𝗸𝗼𝘄𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮
𝘀𝗮𝗺𝗮𝗻,𝗯𝗮𝗻𝗱𝗮
𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮 𝗾𝗮𝗿𝗳𝗲𝗻
𝘀𝘁𝗮𝗶𝗿𝘀 𝗱𝗶𝗻
𝘄𝗮𝗹𝗮 𝗮𝗹𝗹𝗮 𝘇𝗮𝘁𝗮
𝗶𝘆𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗱𝗲𝘄𝗮.
𝗔𝗻𝘆𝗮 𝗸𝘂𝘄𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻
𝗱𝗶𝗻 𝗨𝗪𝗔 𝗖𝗘?,𝗨𝗪𝗔
𝗖𝗘 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗵𝗮𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗿
𝗯𝗶𝗹'𝗮𝗱𝗮𝗺𝗮?,𝗸𝗼
𝗸𝘂𝘀𝗮 𝘂𝘄𝗮 𝗰𝗲
𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗶
𝗷𝗶𝗻𝘀𝗶 𝗸𝗼 𝗵𝗮𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮
𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗯𝗮𝗻?. 𝗕𝗮𝘁𝗮𝘀𝗮𝗻
𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗯𝗶𝘆𝗲 𝗱𝗮
𝗶𝘁𝗮 𝗯𝗮 𝘀𝗮𝗶 𝗱𝗮𝘁𝗮𝗷𝗶
𝗺𝘂𝗿𝘆𝗮𝗿𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮
𝘁𝗮𝗸𝗲 𝘁𝘀𝘂𝗴𝘂𝗻𝗻𝗮𝘄𝗮
𝗴𝗮𝗯𝗮𝗻 𝗺𝗼𝗺𝗺𝗮
𝗯𝗮𝗵𝗶𝗷𝗷𝗮 𝗱𝗼𝗻
𝘁𝗮𝘀𝗮𝗻 𝘁𝗮 𝗾𝗮𝗿𝗮𝘀𝗼.
𝗕𝗮 𝘇𝗮𝘁𝗼 𝘁𝗮 𝘁𝘀𝗶𝗻𝗰𝗲𝘁𝗮
𝗮 𝗴𝗮𝗯𝗮𝗻𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗻𝗮
𝗳𝗮𝗱𝗶𝗻
"𝗟𝗮𝗹𝗹𝗮𝗶
𝘆𝗮𝗿𝗼𝗻𝗮 𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗰𝗲,𝗻𝗮𝘆𝗶
𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻𝗰𝗶𝗸𝗶
𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗺𝘂𝗻 𝘀𝘂𝗿𝘂𝗸𝗮
𝗶𝗿𝗶𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻....𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗺𝗶𝗸𝗶 𝗮𝗹𝗯𝗮𝗿𝗸𝗮"
𝗧𝗮 𝗾𝗮𝗿𝗮𝘀𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮
𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗮𝘇𝗮 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻𝘁𝗮
𝘀𝗮𝗺𝗮𝗻 𝗸𝗮𝗻 𝘀𝗮𝗯𝗿𝗲𝗲𝗻
𝗱𝗮 𝘀𝗶𝗴𝗮𝗿 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮
𝗮𝗹𝗯𝗮𝗿𝗸𝗮.
𝗬𝗮𝗺𝗺𝗺𝗺
𝘁𝗮𝗷𝗶 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻
𝗮𝗯𝘂 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗯𝗶𝗻
𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘀𝗮𝘀𝗵𝗲
𝗻𝗮 𝗷𝗶𝗸𝗶𝗻𝘁𝗮.
𝗖𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲
𝗵𝗮𝗿𝗯𝗮𝘄𝗮 𝗷𝗶𝗻𝗶
𝗱𝗮𝗸𝗲 𝘇𝗮𝗴𝗮𝘆𝗮𝘄𝗮
𝗴𝗮 𝗷𝗶𝗷𝗶𝘆𝗼𝘆𝗶𝗻𝘁𝗮
𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝘀𝗮𝗾𝗼
𝗱𝗮 𝘀𝗮𝘂𝘆𝗲 𝘀𝗮𝘂𝘆𝗲
𝘀𝘂𝗸𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗮 𝗮𝗳𝗸𝘂𝘄𝗮
𝗱𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻
𝘀𝗮𝘂𝗿𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮
𝗴𝗮𝗴𝗴𝗮𝘄𝗮 𝗺𝗲
𝘆𝗮𝘄𝗮𝗻 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲
"𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝘆𝗮𝘆𝗶
𝗺𝗶𝗸𝗶 𝗮𝗹𝗯𝗮𝗿𝗸𝗮"
𝗧𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝗺𝗮𝗶𝗺𝗮𝗶𝘁𝗮
𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 𝘀𝗮𝘂
𝘂𝗸𝘂 𝗱𝗼𝗻 𝘁𝗮𝗻𝗮𝘀𝗼𝗻
𝗮𝗱𝗮𝗱𝗶𝗻 𝘀𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗶𝗻
𝘀𝘂 𝗰𝗶𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗳𝗶𝗻
𝘁𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗲 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻
𝗻𝗮𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝘀𝗮𝗺𝗮𝗻
𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮
"𝗔𝗺𝗲𝗲𝗻 𝘆𝗮
𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵......𝗮𝗺𝗲𝗲𝗻
𝘆𝗮 𝗿𝗮𝗯𝗯𝗮𝗹 𝗔𝗮𝗹𝗮𝗺𝗶𝗻"
𝗠𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲𝗻 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻
𝗸𝗲 𝗮𝗺𝘀𝗮𝘄𝗮 𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶.
𝗛𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻
𝘁𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗲 𝗱𝗮𝗴𝗮
𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮,𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮
𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝘄𝗮𝗻𝘁𝗮
𝗱𝘂𝗸𝗸𝗮 𝗯𝗶𝘆𝘂𝗻
𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗼𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗻𝗮
𝗳𝘂𝘀𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮𝗿𝘁𝗮
"𝗧𝗮𝘀𝗵𝗶 𝗸𝗶
𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻𝗸𝗶......𝗱𝗮𝗴𝗮
𝗻𝗮𝗻 𝗸𝘂 𝗸𝗮𝗶𝘁𝗮
𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻𝘁𝗮 𝗸𝗮𝗶
𝘁𝘀𝗮𝘆𝗲......𝗱𝗮𝗴𝗮
𝗯𝗮𝘆𝗮 𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗵𝗶
𝘆𝗮 𝗿𝗮𝗸𝗮𝘁𝗮 𝗶𝗻𝗱𝗮
𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗰𝗲 𝘁𝗮𝗷𝗲
𝗱𝗶𝗻.....𝗸𝗶𝗻𝗷𝗶 𝗱𝘂𝗸𝗸𝗮
𝗯𝗮𝘆𝗮𝗻𝗮𝗶𝗻𝗮
𝗸𝗼?" 𝗦𝗮𝗺𝘂𝗻 𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮
𝘁𝗮𝘆𝗶 𝗱𝗮 𝗴𝘆𝗮𝗱𝗮
𝗺𝗮𝘁𝗮 𝗸𝗮𝗶 𝗱𝗮
𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝗺𝘂𝗴𝘂𝗻
𝘀𝗮𝗻𝘆𝗶𝗻 𝗷𝗶𝗸𝗶
𝗱𝗮 𝗯𝗮𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗯𝗮
𝗷𝗶𝗻 𝗶𝗿𝗶𝗻𝘀𝗮
𝗯𝗮,𝘀𝗮𝗶𝘁𝗮 𝗷𝗮𝘄𝗼𝘁𝗮
𝘁𝗮 𝗿𝘂𝗻𝗴𝘂𝗺𝗲𝘁𝗮
𝘁𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝘀𝗮𝗸𝗲
𝗺𝗮𝘁𝗮 𝘄𝗮𝘀𝘂 𝗮𝗱𝗱𝘂'𝗼'𝗶𝗻,𝗮𝗯𝗶𝗻𝗱𝗮
𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝘁𝗮𝗷𝗶
𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶
𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝘀𝗮𝗿𝗮𝘄𝗮,𝘁𝗮𝗸𝗲
𝗰𝗶𝘄𝗼𝗻 𝗸𝗮𝗶 𝘆𝗮
𝘀𝗮𝘂𝗸𝗮𝗿 𝗺𝗮𝘁𝗮.
𝗦𝗮𝘂𝗸𝗲
𝗹𝗮𝗯𝘂𝗹𝗲 𝗮𝗺𝗻𝗮
𝘁𝗮𝘆𝗶 𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗼
𝗻𝗮 𝗯𝗮𝗯𝘂 𝗮𝗱𝗮𝗱𝗶,𝘀𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻
𝘁𝗮 𝗺𝗮𝗶𝗱𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗮𝗻𝘁𝗮
𝗸𝗮𝗻 𝗮𝗻𝗻𝗶 𝘁𝗮𝗻𝗮
𝗻𝗮𝗿𝗸𝗲 𝗳𝘂𝘀𝗸𝗮
𝗸𝗮𝗺𝗮𝗿 𝘇𝗮𝘁𝗮
𝘀𝗮𝗸𝗶 𝗸𝘂𝗸𝗮
"𝗔𝗻𝗻𝗶 𝗱𝗮𝗿𝗲
𝗳𝗮 𝘆𝗮 𝗿𝗶𝗴𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶,𝗵𝗮𝗿
𝘆𝗮𝗻𝘇𝘂 𝗯𝗮𝘀𝘂
𝘀𝗵𝗶𝗴𝗼 𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮
𝗯𝗮.....𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘆𝗮𝗮
𝗺𝘂𝘀𝗮𝗱𝗱𝗶𝗾 𝘆𝗮𝗰𝗲
𝘀𝘂𝗻 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻
𝗺𝗮𝗮𝗺𝗮𝗵....𝗱𝗮𝗴𝗮
𝗰𝗮𝗻 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘀𝗮𝗶
𝗻𝗮𝗻". 𝗔 𝗻𝘂𝘁𝘀𝗲
𝗮𝗻𝗻𝗶 𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮
𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮
𝘇𝗮𝗿𝗲 𝘄𝗮𝗿𝘄𝗮𝗿𝗮𝘆𝗲𝗻
𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻𝘁𝗮 𝗱𝗮
𝘁𝗮𝗸𝗲𝘆𝗶 𝘁𝗮 𝗺𝗮𝗶𝗱𝗮
𝗸𝗮𝗻 𝗮𝗺𝗻𝗮
"𝗠𝗲 𝗸𝗶𝗸𝗲
𝗰𝗶 𝗻𝗲 𝗻𝗮 𝗯𝗮𝗸𝗮
𝘆𝗮𝗻𝗮 𝘇𝘂𝗯𝗮 𝗮𝗺𝗻𝗮?,𝗰𝗶
𝗱𝗮 𝘇𝘂𝗰𝗶?,𝘆𝗮𝘆𝗮𝗿𝗸𝗶
𝗰𝗲 𝗳𝗮?,𝗵𝗮𝗿 𝘀𝗮𝗶
𝗸𝗶𝗻 𝗴𝗮𝗷𝗶 𝗱𝗮
𝗴𝗮𝗻𝗶𝗻𝘁𝗮 𝘄𝗮𝘁𝗮𝗿𝗮𝗻𝗮.....𝘄𝗮𝘁𝗮𝗾𝗶𝗹𝗮
𝗱𝗮𝗿𝗲 𝗻𝗲 𝘆𝗮𝘆𝗶
𝗺𝘂𝘀𝘂 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝘄𝘂𝗰𝗲
𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮,𝗮𝗺𝗺𝗮
𝗸𝗼𝗺𝗮 𝗺𝗲𝘆𝗲 𝗻𝗮𝘀𝗮𝗻
𝗵𝗮𝗺𝗺𝗮𝗻𝗸𝘂 𝘇𝗮𝗶
𝗸𝗮𝘄𝗼𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗯𝗯𝗮𝘀
𝗸𝗼𝗱𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮
𝗻𝗲" . 𝗧𝗮𝘆𝗶 𝗺𝗮𝗴𝗮𝗻𝗮𝗿
𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝘀𝗼𝗻 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗿𝘄𝗮
𝗱𝗮 𝗮𝗺𝗻𝗮 𝘁𝘂𝗻𝗮𝗻𝗶𝗻
𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶,𝗱𝘂𝗸 𝗱𝗮
𝗶𝘁𝗮𝗺𝗮 𝘁𝗮𝘀𝗼
𝗾𝘄𝗮𝗿𝗮𝗶 𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗼
𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮𝗻,𝗱𝗼𝗻
𝗮𝗸𝘄𝗮𝗶 𝗺𝗮𝗴𝗮𝗻𝗴𝗮𝗻𝘂
𝗺𝗮𝘀𝘂 𝘆𝗮𝘄𝗮 𝗱𝗮
𝘁𝗮𝗸𝗲𝘀𝗼 𝘁𝗮𝘆𝗶
𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮.
"𝗔𝗺𝗺𝗮 𝗮𝗻𝗻𝗶
𝘆𝗮𝘂𝘀𝗵𝗲?,𝗻𝗶 𝗸𝗼
𝗴𝗼𝗯𝗲 𝗻𝗲 𝗴𝗮𝗻𝗶
𝗻𝗮𝗸𝗲𝘆𝗶 𝘁𝗮𝘆𝗶
𝗻𝗶𝘀𝗮"
"𝗦𝗮𝗶 𝗸𝗶𝘆𝗶
𝗳𝗶𝗳𝗳𝗶𝗸𝗲 𝗸𝗶𝗷𝗲
𝗮𝗶 𝘀𝗮𝗿𝗸𝗶𝗻 𝗴𝗮𝗿𝗮𝗷𝗲"
𝗦𝗮𝗱𝗱𝗶𝗾 𝗱𝗮𝗸𝗲
𝘀𝗵𝗶𝗴𝗼𝘄𝗮 𝗿𝗶𝗾𝗲
𝗱𝗮 𝗹𝗲𝗱𝗮 𝗮 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻𝘀𝗵𝗶
𝗱𝗮𝗸𝗲 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗲
𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗺𝗯𝗮𝗿𝗶𝗻
𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗯𝗮𝗯𝗯𝗮𝗻
𝗸𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶 𝗱𝗮
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘀𝗵𝘂𝗵𝘂𝗿𝗮
𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗳𝗶𝗱𝗱𝗮
𝘀𝘂𝘁𝘂𝗿𝘂 𝗻𝗮 𝗺𝗮𝗻𝘆𝗮𝗻
𝗺𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲. 𝗝𝘂𝘆𝗮𝘄𝗮
𝘁𝗮𝘆𝗶 𝘁𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗲𝘀𝗵𝗶
𝘁𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝗯𝗮𝘁𝗮
𝗿𝗮𝗶,𝘀𝗮𝗶 𝘁𝗮 𝘁𝘀𝘂𝗸𝗲
𝗯𝗮𝗸𝗶 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶
𝘁𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝘇𝗮𝘂𝗻𝗮
𝗯𝗮 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮𝘁𝗮
𝘀𝗮𝗸𝗲 𝗰𝗲𝘄𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶
𝗯𝗮,𝗱𝗼𝗻 𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗻
𝗺𝘂𝗱𝗱𝗶𝗻 𝘁𝗮𝗰𝗲
𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝗺𝗮𝗴𝗮𝗻𝗮𝗿
𝘇𝗮𝘀𝘂 𝘆𝗶𝘁𝗮 𝘀𝗮'𝗶𝗻𝘀𝗮
𝗻𝗲 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗱𝗮
𝘀𝗮𝗱𝗱𝗶𝗾,𝗱𝗮𝗴𝗮
𝗾𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗮𝘁𝗮
𝗸𝘂𝗸𝗮.
"𝗔𝗻𝗻𝗶 𝗸𝗲𝘆
𝗻𝗮 𝘀𝗮𝘀𝘀𝗮𝗻 𝗕𝗕
𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾,𝘆𝗮𝗰𝗲
𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗮 𝗺𝘂𝘀𝘂
𝗸𝗮𝘆𝗮𝗻 𝗻𝗮𝗻 𝗮
𝗰𝗶𝗸𝗶,𝗵𝗮𝗺𝗺𝗮
𝘇𝗮𝗶𝘇𝗼 𝘆𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗿𝘆𝗮".
𝗪𝗮𝗶𝘄𝗮𝘆𝗮𝘄𝗮
𝘁𝗮𝘆𝗶 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗯𝗮𝘄𝗮
𝗮𝗺𝗻𝗮 𝘂𝗺𝗮𝗿𝗻𝗶
𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗺𝗮𝘁𝗮 𝗻𝘂𝗻𝗶
𝗱𝗮 𝗶𝗻𝗱𝗮 𝘁𝗮 𝗮𝗷𝗶𝘆𝗲𝘀𝗵𝗶.
"𝗕𝗮 𝗶𝗻𝗱𝗮
𝘇𝗮𝗸𝗮𝗷𝗲 𝗳𝗮 𝘀𝗮𝗶𝗸𝗮
𝗸𝗮𝗺𝗺𝗮𝗹𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗿𝘆𝗮𝘄𝗮
𝗻𝗮 𝗿𝗮𝗸𝗮𝗸𝗮 𝗸𝗮
𝘆𝗶𝘄𝗮 𝗮𝗻𝗻𝗶 𝘀𝗮𝗹𝗹𝗮𝗺𝗮......𝗱𝗼𝗻
𝗯𝗮 𝘇𝗮𝗸𝗮 𝗵𝗮𝗻𝗮𝗻𝗶
𝗸𝘄𝗮𝗻𝗰𝗶𝘆𝗮 𝗱𝗮
𝘄𝘂𝗿𝗶 𝗯𝗮 𝘆𝗮𝘂......𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮
𝗻𝗮 𝗴𝗮𝗷𝗶 𝗱𝗶𝗻𝗻𝗮𝗻
𝗯𝗮𝗰𝗰𝗶 𝗻𝗮𝗸𝗲
𝗯𝘂𝗾𝗮𝘁𝗮 𝗺𝗲 𝘁𝘀𝗮𝗵𝗼.....𝗸𝗼
𝗳𝗮𝗻𝗻𝗮 𝗵𝗶𝗱𝗶𝗺𝗮𝗿𝗸𝗮
𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝗮𝗺𝗶𝗻
𝗷𝗶𝗻 𝗺𝘂𝗿𝘆𝗮𝗿𝘁𝗮"
𝗙𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗮𝘆𝗮
𝗿𝗶𝗾𝗼 𝗳𝘂𝗮𝗱 𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮
𝗸𝗲 𝗾𝗼𝗾𝗮𝗿𝗶𝗻
𝘄𝘂𝗰𝗲𝘄𝗮 𝗸𝗮𝗶
𝘁𝘀𝗮𝘆𝗲 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻
𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻 𝘆𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮.
𝗪𝗮𝗶𝘄𝗮𝘆𝗼𝘄𝗮
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗹𝗶
𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻
"𝗗𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗶
𝗸𝗮𝘀𝗼.....𝗸𝗮 𝗮𝘇𝗮𝗺𝗮
𝗸𝗮𝗻𝗸𝗮 𝗵𝗶𝗱𝗶𝗺𝗮𝗿
𝗱𝗮 𝗸𝘄𝗮𝘁𝗮 𝗸𝘄𝗮𝘁𝗮
𝗯𝗮𝘁𝗮 𝗱𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗶
𝘁𝘂𝘀𝗵𝗲 𝗸𝗼 𝗸𝘂𝗺𝗮
𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶.....𝘄𝗮𝗶
𝘄𝗮𝗶𝘁 𝗺𝗮......𝘁𝘂𝗸𝘂𝗻𝗻𝗮
𝗸𝗮𝗻𝗮 𝗻𝘂𝗳𝗶𝗻
𝗻𝗶 𝘇𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗮
𝗮 𝗴𝗮𝗯𝗮 𝗸𝗮𝗸𝗮𝗶
𝗰𝗮𝗻 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻?"
"𝗪𝗮𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶
𝘄𝗮𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶 𝘀𝗮𝗶𝗸𝗮
𝘀𝗵𝗶𝗿𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗻
𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗮𝗻𝗴𝗼,𝗸𝘂𝗺𝗮
𝘀𝗮𝗶𝗻𝗮 𝗸𝗮𝗶𝗸𝗮
𝗵𝗮𝗿 𝗰𝗶𝗸𝗶" 𝗬𝗮𝘆𝗶
𝗴𝗮𝗴𝗴𝗮𝘄𝗮𝗿 𝘆𝗮𝗻𝗸𝗮𝗿
𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮 𝗱𝗮
𝗿𝗮𝗻𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮,𝗱𝗼𝗻
𝗿𝗮𝗻𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮𝗿
𝗰𝗲 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗶 𝘆𝗮𝘀𝗮𝗻
𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗮 𝗳𝘂𝗮𝗱
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗮𝗯𝗶𝗻𝗱𝗮
𝘆𝗮𝗸𝗲𝘀𝗼 𝗱𝗶𝗻
𝗯𝗮 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮 𝗷𝗮𝗻
𝘇𝗮𝗻𝗰𝗲 𝗯𝗮,𝗸𝗮𝘀𝗮𝗻𝗰𝗲𝘄𝗮𝗿
𝗱𝘂𝗸 𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶
𝗿𝗮𝗻𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮 𝗮
𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝘀𝘂 𝘆𝗮𝗻𝗮
𝗾𝗼𝗾𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗳𝗶𝗱𝗱𝗮
𝗱𝗮𝗻 𝘂𝘄𝗮𝗻𝘀𝗮
𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗿𝗮𝗻𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮𝗿.
𝗜𝗱𝗮𝗻𝘂
𝘆𝗮 𝘇𝘂𝗯𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮,𝗸𝗮𝗺𝗮𝗿
𝘇𝗮𝗶𝘆𝗶 𝗺𝗮𝗴𝗮𝗻𝗮
𝘀𝗮𝗶 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘆𝗮
𝗳𝗮𝘀𝗮,𝘆𝗮 𝗷𝘂𝘆𝗮
𝘇𝘂𝘄𝗮 𝘀𝗮𝘀𝗵𝗲𝗻
𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻
𝘆𝗮𝗻𝗮 𝘁𝗮𝗸𝗮𝘄𝗮
𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗻𝘂𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮𝗿
𝗻𝗮𝗻 𝘁𝗮𝘀𝗮. 𝗖𝗮𝗸
𝘆𝗮 𝘁𝘀𝗮𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗯
𝗱𝗮 𝘇𝗮𝗶 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗮,𝗺𝘂𝗿𝗺𝘂𝘀𝗵𝗶
𝗺𝗲 𝗾𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻
𝘀𝗮𝘂𝘁𝗶 𝘆𝗮 𝘀𝘂𝗯𝘂𝗰𝗲
𝗺𝗮𝘀𝗮,𝘆𝗮 𝘄𝗮𝗶𝘄𝗮𝘆𝗮
𝘆𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗶 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾
𝗱𝗶𝗻
"𝗪𝗮𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶
𝘆𝗮𝗿𝗼𝗻 𝗻𝗮𝗻 𝗸𝗮
𝗿𝗮𝗶𝗻𝗮𝗻𝗶 𝗱𝗮
𝘆𝗮𝘄𝗮,𝘄𝗮𝗶 𝗸𝗮
𝗺𝗮𝗻𝘁𝗮 𝗸𝘄𝗮𝗻𝗮
𝗱'𝗮𝗶 𝗱'𝗮𝗶 𝗵𝗮𝗿
𝗯𝗮𝗸𝘄𝗮𝗶 𝗻𝗮 𝗯𝗮𝗸𝗮.....𝘁𝘂𝗸𝘂𝗻𝗻𝗮
𝗺𝗮 𝘄𝗮𝗶 𝘄𝗮𝘆𝗲
𝘆𝗮𝗰𝗲 𝗺𝗮𝗸𝗮 𝗵𝗮𝗸𝗮
𝗻𝗮 𝘁𝘀𝗮𝗿𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶
𝗻𝗲?,𝗮𝘂𝗿𝗲𝗻 𝗱𝗮𝗻𝗮
𝘁𝘀𝗮𝗿𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮
𝗱𝗮𝘂𝗿𝗮𝘄𝗮 𝘀𝗮𝗶
𝗿𝗮𝗸𝗮𝘁𝗮 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻
𝘁𝗮𝗿𝗯𝗶𝘆𝘆𝗮 𝗱𝗮
𝘇𝗮𝘀𝘂𝘆𝗶?"
"𝗚𝗶𝗱𝗮𝗻 𝘁𝗮𝗿𝗯𝗶𝘆𝘆𝗮?"
𝗙𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻
𝘆𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮
𝗱𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗱𝗮𝗿𝗶𝘆𝗮𝗿𝘀𝗮,𝗱𝗼𝗻
𝘁𝘂𝗻 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗻𝗮𝗻
𝗵𝗮𝗿 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘇𝗮𝗶
𝗯𝗮𝗿𝗼 𝗳𝘂𝗮𝗱 𝗱𝗶𝗻
𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻𝘀𝗮
𝗯𝗮𝘆𝗮𝘀𝗼𝗻 𝘆𝗮𝗴𝗮
𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗮𝗯𝘂 𝗺𝗲
𝗸𝗮𝗺𝗮 𝗱𝗮 𝘄𝗮𝘀𝗮
𝘀𝗮𝗺.....𝘆𝗮𝗻𝗮𝘀𝗼𝗻
𝗶𝗱𝗮𝗻𝗺𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮
𝗱𝗮𝘂𝗸𝗮𝗻 𝗮𝗯𝘂𝗻
𝗮 𝗺𝗮𝘇𝗮𝘂𝗻𝗶𝗻
𝘄𝗮𝘀𝗮 𝘀𝗼 𝘆𝗮𝗸𝗲
𝘆𝗮𝗷𝗶 𝘀𝗼𝘀𝗮𝗶
𝗮 𝗿𝗮𝗻𝘀𝗮 𝗮𝘂𝗿𝗲
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗿
𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗺𝗮𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻𝗰𝗶.
"𝗧𝗼 𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗯𝗮
𝗹𝗶𝘀𝘀𝗮𝗳𝗶 𝘆𝗮𝗹𝗹𝗮𝗯𝗮𝗶"
𝗬𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗻𝗮
𝗷𝗮𝗻 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻𝘀𝗮
𝘀𝘂𝗻𝗮 𝗾𝗮𝗿𝗮𝘀𝗮𝘄𝗮
𝗰𝗶𝗸𝗶.
𝗗𝗮𝗴𝗮
𝗾𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲 𝗱𝗮𝗶
𝗱𝗼𝗹𝗲 𝗶𝗱𝗮𝗻𝘂
𝘆𝗮 𝘇𝘂𝗯𝗮𝘄𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾
𝗱𝗶𝗻,𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘄𝗮𝗻𝗸𝗮
𝗱𝗼𝗻 𝗱𝗮𝗺𝗮 𝘀𝗮𝗯𝗼𝗻𝘀𝗵𝗶
𝗻𝗲 𝗱𝘂𝗸 𝗱𝗮𝗿𝗲,𝗯𝗮𝗿𝗲
𝘆𝗮𝘂 𝗱𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝘀𝘂𝗸𝗮
𝘄𝘂𝗻𝗶 𝘇𝗶𝗿𝗴𝗮
𝘇𝗶𝗿𝗴𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝗯𝗮𝗯𝘂
𝗴𝗮𝗶𝗿𝗮 𝗯𝗮𝗿𝗲
𝗱𝗮𝗹𝗶𝗹𝗶 𝗱𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾
𝘆𝗮 𝗮𝘇𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮.
𝗬𝗮𝗷𝗶 𝗱𝗮𝗱𝗶𝗻
𝗷𝗶𝗸𝗶𝗻𝘀𝗮 𝘀𝗼𝘀𝗮𝗶,𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾
𝘆𝗮 𝗳𝗶𝗱𝗱𝗼 𝗺𝗮𝘀𝗮
𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶. 𝗞𝗮𝗺𝗮𝗻
𝗱𝗮𝘇𝘂 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝘆𝗮
𝗱𝗶𝗻𝗴𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗮
𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶
𝘆𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗿𝘆𝗮𝘄𝗮,𝘀𝗮𝗶
𝗴𝗮𝘀𝗵𝗶 𝘆𝗮 𝗳𝗶𝘁𝗼
𝗳𝗲𝘀 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗼𝗹𝗶𝘃𝗲
𝗰𝗼𝗹𝗼𝗿,𝘆𝗮𝘆𝗶
𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝗵𝘂𝗹𝗮
𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗹𝗳 𝗰𝗼𝘃𝗲𝗿
𝘀𝗵𝗼𝗲 𝗱𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗮𝗻
𝗽𝗮𝗹𝗲 𝘀𝗮𝗴𝗲 𝗱𝗮𝘆𝗮
𝗱𝗮𝗰𝗲 𝗾𝘄𝗮𝗿𝗮𝗶
𝗱𝗮 𝗼𝗹𝗶𝘃𝗲 𝗰𝗼𝗹𝗼𝗿
𝗱𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗶
𝗶𝗿𝗶𝗻 𝗺𝗮𝘁𝗰𝗵𝗶𝗻𝗴.
𝗗𝗮𝗴𝗮 𝘀𝗵𝗶 𝗵𝗮𝗿
𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝘀𝘂𝗻𝘆𝗶
𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗯𝗮𝗹𝗮'𝗶𝗻
𝗾𝘄𝗮𝗿𝗲𝘄𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻
𝗶𝘆𝗮 𝗵𝗮𝗱𝗮 𝗰𝗼𝗹𝗼𝗿
𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝘀𝘂𝘁𝘂𝗿𝗮𝗿
𝗱𝗮 𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘇𝗮𝘂𝗻𝗮
𝗮 𝗷𝗶𝗸𝗶. 𝗗𝘂𝗸 𝗱𝗮
𝗮 𝘆𝗮𝗻𝘇𝘂 𝘀𝗵𝗶
𝗯𝗮𝗶𝗱𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻
𝗹𝗼𝗸𝗮𝗰𝗶𝗻,𝗱𝗼𝗻
𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮 𝗽𝗿𝗼𝗳𝗲𝘀𝘀𝗶𝗼𝗻𝗮𝗹
𝗰𝗹𝗼𝘀𝗲𝘁 𝗼𝗿𝗴𝗮𝗻𝗶𝘀𝗲𝗿
𝗱𝗮𝗸𝗲 𝘁𝘀𝗮𝗿𝗮
𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗸𝗮𝘆𝗮𝗻
𝗱𝗮 𝘇𝗮𝗶𝘆𝗶 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶
𝗱𝗮𝘀𝘂 𝗻𝗮 𝘁𝘀𝗮𝗵𝗼𝗻
𝘀𝗮𝘁𝗶𝘁𝘁𝗶𝗸𝗮,𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮
𝘆𝗮 𝗮𝗷𝗶𝘆𝗲𝘀𝘂
𝗻𝗲 𝗮 𝗱𝘂𝗸𝗮 𝗴𝘂𝗿𝗮𝗿𝗲𝗻
𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗶𝘆𝗮
𝘇𝘂𝘄𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘀𝗮𝘁𝗶
𝗸𝗼 𝘀𝗮𝗺𝗮 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗸𝗮,𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲
𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗮𝗹𝗯𝗮𝘀𝗵𝗶𝗻𝘀𝗮
𝗱𝗮𝗯𝗮𝗻 𝗸𝗼𝗱𝗮
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘄𝗮𝘁𝗮𝗻𝗻𝗶
𝗯𝗮𝗶𝘆𝗶 𝗮𝗶𝗸𝗶𝗻𝘀𝗮
𝗯𝗮. 𝗦𝗮𝗶𝗱𝗮𝗶 𝗱𝘂𝗸
𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝗱𝘂𝗸
𝗿𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗺𝘂
𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮 𝘆𝗮 𝗵𝗮𝗱𝗮𝘄𝗮
𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮 𝗱𝗿𝗲𝘀𝘀𝗶𝗻𝗴
𝘁𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗮𝘁 𝗱𝗮𝘆𝗮
𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗸𝗲 𝗴𝗮𝗻𝗲𝘄𝗮.
𝗬𝗮𝗮𝗮𝗻 𝗵𝗮𝗹𝗶𝗻𝘀𝗮,𝗺𝗮𝘆𝗲
𝗻𝗲 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗶𝘆𝗮
𝘁𝘀𝗮𝗿𝗮𝘄𝗮 𝗷𝗶𝗸𝗶
𝗮𝗱𝗼 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘄𝗮𝗻𝗰𝗶
𝘆𝗮𝗸𝗲 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝘁𝗮𝗸𝗮
𝗺𝘂𝗵𝗶𝗺𝗺𝗶𝘆𝗮𝗿
𝗿𝗮𝘄𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻
𝗳𝘂𝘀𝗴𝗮𝗿 𝗵𝗮𝗻𝗸𝘂𝗹𝗮𝗻
'𝘆𝗮𝗺𝗺𝗮𝘁𝗮𝗻 𝗱𝗮𝗸𝗲
𝗾𝘂𝗹𝗮𝗳𝘂𝗰𝗶𝗻𝘀𝗮.
"𝗠𝗮 𝘀𝗵𝗮 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵....
.𝗽𝗲𝗿𝗳𝗲𝗰𝘁 𝗺𝗮𝘁𝗰𝗵"
𝗙𝘂𝗮𝗱 𝗱𝗶𝗻 𝘆𝗮
𝗳𝗮𝗱𝗶 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗮𝗳𝗮
𝗴𝗮𝗯𝗮𝗻 𝗯𝗮𝗯𝗯𝗮𝗻
𝗿𝗶𝗴𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘀𝗵𝗮
𝗮𝗶𝗸𝗶. 𝗦𝗵𝗶 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮
𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻
𝗸𝗮𝗹𝗹𝗼𝗻𝘀𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲,𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮
𝗸𝗮𝘆𝗮𝗻 𝘀𝘂𝗸𝗮
𝗮𝗺𝘀𝗵𝗲𝘀𝗵𝗶 𝗺𝗮𝘁𝘂𝗾𝗮
𝘀𝘂𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝘀𝘂𝗿𝗮
𝗱𝗮 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗷𝗶𝗻𝗶𝗻
𝗱𝗮 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝘆𝗮
𝗯𝗮𝘀𝗵𝗶.
𝗡𝗲𝗺𝗮𝗻
𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝘇𝗮𝗺𝗮
𝘆𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮𝘆𝗶,𝘀𝗮𝗶
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗯𝗮𝗻𝘇𝗮
𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶,𝘆𝗮 𝗳𝗶𝗱𝗱𝗮
𝘄𝗮𝘆𝗮 𝘆𝗮 𝗸𝗶𝗿𝗮
𝗮𝗯𝗯𝗮.....
"𝗔𝗯𝗯𝗮 𝗺𝘂𝗻
𝗴𝗮𝗺𝗮,𝗼𝗸𝗮𝘆 𝘁𝗼"
𝗠𝗮𝗶𝗱𝗮 𝘄𝗮𝘆𝗮𝗿
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗮𝗹𝗷𝗶𝗵𝘂𝗻𝘀𝗮
𝘆𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗲
"𝗦𝗮𝗶𝗸𝗮 𝘁𝗮𝘀𝗼
𝗺𝘂𝗷𝗲 𝗮𝘆𝗶 𝗺𝗮𝗸𝗮
𝗳𝗮𝗱𝗮𝗻 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻
𝗮𝘂𝗿𝗲". 𝗬𝗮 𝗳𝘂𝗿𝘁𝗮
𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮𝗻𝗻𝗲
𝗱𝗮𝗿𝗶𝘆𝗮𝗿𝘀𝗮.
𝗗𝗮
𝗸𝗮𝗹𝗹𝗼 𝘆𝗮𝗯𝗶
𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻
𝗴𝗮𝗹𝗮𝗹𝗮 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶
𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗮𝗻𝘀𝗮.
"𝗞𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗮
𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗶𝘆𝗮𝗸𝗮𝗻𝗸𝗮
𝗳𝗮......𝗳𝗮𝗱𝗮 𝗰𝗲
𝗺𝗮𝗸𝗮 𝗮𝗸𝗮𝘆𝗶
𝗺𝘂𝗻 𝗿𝗮𝗯𝘂?" 𝗬𝗮
𝗳𝗮𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗷𝗶𝗳𝗮𝗻
𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗿𝗮
𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘁𝘂𝗻𝗶
𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗶 𝗾𝗼𝗳𝗮,𝗱𝗼𝗹𝗲
𝘆𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗲 𝗵𝗮𝗿
𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗿𝗮𝗻𝘀𝗮
𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗷𝗶𝗻 𝗮𝗯𝘂𝗻
𝘆𝗮 𝗶𝘀𝗮 𝗵𝗮𝗸𝗮.
𝗦𝗵𝗶 𝘀𝗮𝗺 𝗯𝗮𝗶
𝗸𝗮𝘄𝗼 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝗮𝗯𝘂𝗻
𝘇𝗮𝗶 𝗷𝘂𝘆𝗲 𝗯𝗮,𝗱𝗮
𝘁𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗮 𝗺𝗮 𝘇𝗮𝗶
𝗯𝗮𝗿𝗶 𝗮𝘆𝗶 𝗵𝗮𝗸𝗮
𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶?,𝘁𝗮𝗯𝗯𝗮𝘀
𝗱𝗮 𝗿𝗮𝗻𝗮𝗿 𝗱𝗮𝘆𝗮
𝗱𝗮𝘂𝗸𝗼 𝘄𝗮𝗻𝗰𝗮𝗻
𝘁𝘀𝗼𝗵𝗼𝗻 𝗻𝗮𝘁𝗮
𝘇𝗮𝗶 𝗸𝗶𝗿𝗮 𝗺𝗮'𝗮𝗶𝗸𝗮𝘁𝗮𝗻𝘀𝗮
𝘀𝘂 𝘀𝗵𝗮𝗶𝗱𝗮 𝗮
𝗱𝗮𝘂𝗿𝗮 𝗮𝘂𝗿𝗲𝗻
𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗮 𝘄𝘂𝗰𝗲
𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻,𝘆𝗮 𝘁𝗮𝘁𝘁𝗮𝗿𝗮
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘁𝗮𝗳𝗶𝘆𝗮𝗿𝘀𝗮
𝘀𝗮𝗶 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮
𝗴𝗮𝗺𝗮 𝘂𝘇𝘂𝗿𝗼𝗿𝗶𝗻𝘀𝗮
𝘁𝘂𝗸𝘂𝗻𝗻𝗮,𝗵𝗮𝗸𝗮
𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾
𝗱𝗶𝗻 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗿𝘂𝘄𝗮
𝗱𝗮 𝘁𝘀𝗮𝗸𝗶 𝘆𝗮
𝗺𝗮𝗶𝗱𝗮 𝗹𝗮𝗺𝗮𝗿𝗶𝗻
𝘄𝗮𝗻𝗶 𝘀𝗲𝗿𝗶𝗼𝘂𝘀.
𝗤𝘄𝗮𝗾𝘄𝗾𝘄𝗮𝗿𝗮𝗻
𝗺𝗼𝘁𝘀𝗶 𝗸𝗮𝘀𝗮
𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮
𝗮𝗯𝗯𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝗺𝗮𝘀𝗮
𝗻𝗮𝘀𝗶𝗵𝗮 𝗴𝗮𝗺𝗶
𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗻𝘁𝗮
𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗵𝗮𝗹𝗮𝘆𝗲𝗻
𝗺𝗮𝘁𝗮 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮
𝗮𝗸𝗲 𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗱𝗮𝘀𝘂
𝗹𝗮𝗳𝗶𝘆𝗮,𝗸𝘂𝗻𝘆𝗮
𝗱𝗮 𝘁𝗮𝘂𝘀𝗮𝘆𝗶𝗻
𝗮𝗯𝗯𝗮𝗻 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝘀𝗵𝗶
𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲
𝗯𝗮𝘆𝗮𝗻𝗶𝗻 𝗱𝗮
𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲𝗻 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲.
𝗬𝗮 𝘀𝗮𝗻𝗶,𝗯𝗮𝘆𝗮𝗻𝗮𝗶
𝗻𝗲 𝗺𝗮𝘀𝘂 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶
𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗳𝗮 𝗴𝗮 𝗺𝘂𝘁𝘂𝗺𝗶𝗻
𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗮
𝗱𝗮 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲𝗻 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲
𝗮𝘂𝗿𝗲 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻
𝗻𝗮 𝗺𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲.....𝗮𝘂𝗿𝗲
𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻
𝗻𝗮 𝗸𝗼𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗸𝗼𝘄𝗮,𝗯𝗮𝘄𝗮𝗶.𝗺𝘂𝘁𝘂𝗺
𝗶𝗿𝗶𝗻𝘀𝗮 𝗱𝗮 𝗯𝗮𝗶𝗷𝗶𝗻
𝘀𝗵𝗶 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮
𝗱𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗮𝗸𝗸𝗲𝗻
𝗹𝗼𝗸𝗮𝗰𝗶𝗻 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮
𝗯𝗮 𝗯𝗮𝗿𝗲 𝗻𝗮 𝘄𝗮𝘁𝗮.....𝘄𝗮𝘁𝗮𝗻
𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗸𝗶𝗹𝗹𝗮𝗰𝗲𝘁𝗮
𝗻𝗲 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗱𝗼𝗻
𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗶𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗯𝗶'𝘂𝗻𝘁𝗮.......𝘆𝗮
𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗻𝘂𝗻𝗮 𝗺𝗮𝘁𝗮
𝗴𝗶𝗿𝗺𝗮 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘄𝗮𝗻
𝗮𝗱𝗮𝗱𝗶𝗻 𝗸𝘂𝘀𝗸𝘂𝗿𝗲𝗻
𝗱𝗮𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗳𝗸𝗮
𝗮 𝗿𝗮𝘆𝘂𝘄𝗮𝗿𝘁𝗮.
"𝗞𝗮𝗱𝗮 𝗸𝘂
𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗯𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗮
𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗺𝗮𝗿𝗶𝘆𝗮
𝗯𝗮" 𝗔𝗻𝗻𝗶 𝘁𝗮
𝗳𝗮𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮
𝘀𝘂𝗸𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗲 𝘆𝗮𝗻𝗮
𝗺𝘂𝘀𝘂 𝘀𝗮𝗹𝗹𝗮𝗺𝗮𝗿
𝘀𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗳𝗲,𝗾𝗮𝘀𝗮
𝗾𝗮𝘀𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗷𝗶𝗳𝗮𝗻
𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗿𝗮.
𝗝𝗶 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗻
𝘆𝗮 𝗷𝗮𝘄𝗼𝘀𝗵𝗶
𝘆𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗴𝗲𝘀𝗵𝗶
𝗱𝗮 𝗸𝘆𝗮𝘂,𝗱𝘂𝗸
𝗻𝗮 𝗺𝗲𝘆𝗲 𝘇𝗮𝗶
𝘀𝗮𝗸𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗶𝘆𝗮𝘆𝗲
𝘇𝗮𝗺𝗮𝗻 𝗱𝗼𝗴𝗼𝗻
𝗷𝗮𝘄𝗮𝗯𝗶𝗻 𝗱𝗮
𝘀𝗮𝗺 𝘀𝗵𝗶 𝗯𝗮𝗶𝗱𝗮
𝗮𝗹𝗮𝗾𝗮 𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶?.
Duniyata na kudi ne
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 12
Page 12
Har qasan
ranta takejin wata izza tana mamayarta sanda take takowa inda yake zaune yana
jiran fitowarta. Kansa a qasa,baima dagashi ba ballantana ya qarewa ginin daya
zuba kudi da kudinsa akayi kallo.
Burinsa daya yayi ya fita ya wuce inda zaije ya kwanta ya huta,don ya
gaji matuqa......ga bikin bude company nan da kwana uku a gabansa,gobe da jibi
dinma ya tabbatar baida hutu saboda baqinsa zasu fara sauka kuma. Har bayason
kallon komai na gidan,yana tuna masa yadda ta dinga uzzurawa kowa da kalar a
siya kaza a saka mata kaza,bayan komai a rubuce yake a hannun kamfanin da ya
bawa kwangilar ginin.
"Zaku wuce kenan?" Ta tambayeshi bayan sun gaisa
ba tare data damu ta tambayeshi komai ba. Kansa ya gyada a hankali,ta gyara
zamanta tana kiran sunansa kai tsaye
"Muhammad.....inaso ka bani hankalinka da kyau,magana
zan maka me muhimmancin da itace ta biyu a rayuwarka da zan sakeyi maka
ita". Baice komai ba bai kuma motsa ba,illa dai kawai ya tattara
kunnuwansa yana jiran DA WANNE ZATA ZO?.
"ka san wa na aura maka?.....zabin raina" Ta masa
tambaya da amsa gaba daya. Yanayin datayi maganar ya sakashi daga fararen
idanunsa masu tarin kwarjini ya dan kalleta,akaci sa'a itama shi take kallo,sai
ta jinjina masa kai
"Eh......itadin zabi na ce,saba mata wulaqantata ko
tozartata tamkar ni mahaifiyarka mariya ka yiwa hakan.......ina me baka umarni
ka riqeta kayi mu'amala da ita kamar yadda kowanne namiji yake mu'amala da
matarsa da yakeso.......zan iya komai akan cusguna mata muddin kayi......idan
nace komai kuwa ciki harda fushi dakai me tsanani". Bai shirya ba a wannan
karon ya daga kansa da sauri ya sake kallonta
"Wacece ita?......meye shirinta?.......dame ta
shigo?" Sune tambayoyin da har a cikin mota yakai maimaitawa cikin ransa.
Cikin kowanne jijiya dake kai jini zuwa zuciyarsa cike yake qyamar yarinyar da
qaqqarfan zargi a kanta,baya shinshino alkhairi ko qwaya daya a kanta,ta
kowacce fuska ITA DIN SHARRI CE.
Tun daga
ranar daya fahimta itace zabin maamah data fara saukar masa da zazzafan umarni
da maganganu a kanta.....tun daga ranar daya fahimci ita dince dai wannan wadda
tayi fashin online wa kamfaninsa kudaden da ko namiji me taurararriyar zuciya
da tsananin taurin kai iyakarsa kenan......tun a wancan ranar ya sake
tabbatarwa kansa akwai wasu abubuwan ma masu yawa da bai sani ba a
kanta.....amma koma meye.....koma mene zai tabbatar ya koya mata darasin rayuwa.......zai
sauya mata DUNIYARTA da kalar horon da ba zata sake gigin aikata irin rayuwarta
ta baya ba......zai sakata tasan meye ainihin TARBIYYA GIRMAMAWA KUNYA DA
GASKIYA.
Tsaiwar motarsu shine abinda ya fincikoshi daga duniyar tunani zuwa ta
zahiri. Ya waiwaya yadan dubi farouq dake qoqarin baiwa guard din da sukazo
dasu umarnin yadda shigarsu zata kasance. Ko sau daya farouq bai katse masa
tunanin ba ko ya sako masa hira. Wani irin mutum ne daya karanceshi ya kuma
fahimceshi sosai,yasan babu yadda zai shiga wajen mahaifiyarsa bai fito da
guzurin damuwa ba,shiga lafiya da fita lafiya duka tamkar sa'a ce a
wajensu,wannan ya sanya bai fiya masa katsalandan akan kowanne yanayi yaga ya
fito dashi ba.
A nutse
ya dinga bin tsarin ginin da kallo. Baisan inda farouq ya samo gidan ba,don
basa cikin gidajensa sam sam,saidai kuma ya cika da mamakin yadda tun daga
farfajiyar gidan ta zama sak irin yanayin ginin da yake so,kuma zabinsa.
"Alhamdulillah" Farouq ya furta yana dubansa,shima
shi din ya kalla,yaja numfashi kadan sannan yace
"Shikenan?,hankalinka ya kwanta?,saika wuce gida ka
kwanta" Murmushi kadan farouq ya saki,ya miqa hannu bayansu. Kyakkyawan
bamboo basket ya fiddo,wanda aka yiwa wani irin ado da tsari,can qasan ransa
yana jin tsoro sosai kan yadda yake ganin rashin baiwa komai daya shafi auren
muhimmanci daga wajen fu'ad din. Baya jin tsoro akan zaiyi wani maras kyau
ba......saidai bashi da tabbaci ko guarantee din zaiyi komai daidai.
"Ga tsarabar amarya" Ya fada yana ajiye basket din
a tsakaninsu. Harara ya watsawa farouq din sannan ya fara yunqurin bude murfin
motar,sai daya fice din sannan yace masa
"An gaya maka harda ni a wannan wasan yaran?"
"Please mana fu'ad,waye ya gaya maka ana shiga wajen
amarya haka?,take it.......it's sunnah fa" Baiko waiwayeshi ba ya fara
nufar hanyar dake nuni da shine ainihin qofar shiga gidan gaba daya.
"Aurenma sunna ne kuma jihadi zanyi".
"Jihadin daukan fansa?" Ya fada a ransa a fili
yana dariya qasa qasa. Murfin motar ya balle shima ya biyo bayansa duk da baida
niyyar shiga cikin gidan don duka ba tsarinsu bane,a qasan ransa yana fata da
addu'ar Allah yasa reshe ya juye da mujiya.
Dab da
bakin kyakkyawar qofar ya dukansu suka tsaya kamar wadanda aka yiwa umarni,a
nutse farouq ya sunkuya ya ajiye basket din sannan ya dago yana duban tsakiyar
idanun fu'ad. Koda baiyi magana ba fu'ad din ya fahimci magana yake gaya masa
da idon. Farouq ya cancanci kowacce girmamawa da qauna,don haka sai ya sunkuya
kawai ya dauki basket din yaci gaba da takawa
"Muhammad" Yau farouq din ya kirashi da zallar
sunansa da ya jima da manta rabon da yaji ya kirashi dashi. Waiwayowa yayi suka
hada idanu.
"Don Allah......kayi dukkan abinda ya dace,ka riqeta
yadda ake riqe kowacce macen aure". Idanu fu'ad ya lumshe yana budesu
lokaci guda,shima nasa idanun cikin na farouq
"Banyi maka alqawarin zaman aure irin na kowanne miji
da mata ba......ban maka alqawarin cewa zataji dadi kaman kowacce mace
ba.......amma zan kyautata idan ta kyautata.......manufar aurendai kuma banajin
zata canza,dole tayi wannan karatun,saidai shima zaizo a duk yanayin data zabi
yazo" Daga haka ya juya yana shigewa don bayason farouq ya sake neman
karyashi da kowacce kalma daga bakinsa.
Ba zata
iya cewa ga yanayin data wanzu a ciki ba tunda su momma bahijja da sauran
mutanen da basufi ashirin ba suka juya suka barta a gidan da suke fama jaddada
kyau da tsaruwa da kuma dukiyar dake ciki wanda babu daya a ciki da yayi mata.
Ko bayan wucewarsun shuru ne yaci gaba da wanzuwa cikin gidan,jifa jifa tana
jin tamkar haushin kare daga dan nesa kadan daga inda take. Ko sau daya bata
janye mayafin kanta ba,saima qara duqunquna da tayi tana daga zaunen saboda
yadda azababben zazzabi yake sake sauko mata. Wani irin tsoro mara misali yana
saukar mata,kalar tsoron da bata taba jin irinsa ba. Empty takejin
kwanyarta,kaman an kwashe komai dake ciki an zuba tsoro da rashin nutsuwa,sai
muryar matar dake da sunan surukarta a yanzu wadda keta mata kai kawo ita da
dukkan dokokinta cikin tsakiyar kanta tamkar ana mata bita kada ta mance.
"Assalamu alaikum warahmatullah" Ya furta qasa
qasa yadda baya zaton akwai wanda zai jishi,saidai don kawai yasan sallamar
wajibi ce a musulunci koda babu kowa cikin gida,Ko ina da haske tarwai tamkar
rana,ba wani qwai da yake a kashe. Da idanu yake bin parlor din da kallo,wani
tsari me kyau da ya dace da ra'ayinsa tamkar dashi farouq yayi shawara wajen
tsarin gidan,tun daga kan color na paint dana furniture din.
A nutse yaci
gaba da takawa cikin parlor din hannunsa zube a aljihun shaddarsa. Bai tsaya ba
sai daya isa tsakiyar parlor din,ya aza basket din hannunsa saman wani dan
qaramin table dake tsakiyar falon.
Juyawa
yayi yana ci gaba da bin kowanne makunnin fitila dake falon yana kasheshi daya
bayan daya,har sai da hasken daya rage
kawai dake farfajiyar gidan wanda ke ratsowa ta lafiyayyun curtains din da aka
zagaye falon dashi.
Sai daya
tabbatar ba wani sauran abinda ya rage sannan ya sauya akalarsa zuwa upstairs
da yake kyautatan zaton a can ne sashensa yake.
Stairs na
farko kadai ya taka wayarsa tayi qara. Ya dakata ya sanya hannunsa a aljihunsa
yana cirota da niyyar kasheta gaba daya,don a matuqar gajiye yake,baya buqatar
duk wani abu da zaiyi disturbing nasa. Sanda ya bude da nufin kashewar saqo ya
cika screen na wayarsa.
*_welcome home mr jadda,Its strongly warning Cease all
preparation,Stop all activities,good night,have a nice night_*.
Maimaita
karanta saqon yayi kusan sau uku,zuwa yanzu ranshi ya fara baci,ya kuma hango
zallar rainin wayo daya fara shiga cikin lamarin. Koma su waye suna bibiye da
duk wani motsi nasa kenan?. A irin wannan saqon da suke aike mishi,ya tabbatar
inda suna da ikon cimmasa da tuni sun cimmasa din.
Da baya ya
dawo ya zauna saman daya daga cikin kujerun falon wadda tafi kusa da stairs
dinsa. Mutum uku ya nema,ya aike musu da komai,sannan ya saka binciken cikin
schedule dinsa na gobe,ya kashe wayar ya jefa a aljihu ya miqe a nutse yana
wucewa saman.
Babban
parlor ne da akayi masa wani tsari na musamman,wanda ke dauke da dining area
well designed,sai dakuna bedroom biyu da Master room guda daya dake da
lafiyayyen balcony da zai baka daman ganin gidan gaba daya gaba da baya.
Abinda ya
bashi mamaki komai nasa an jera masa,kayanshi da komai nasa,abinda farouq kadai
bai taba ba abinda ya shafi dakin sirrinsa dake wancan gidan nasu.
Master
bedroom din ya zaba,ya tura ya shiga yana rage hasken fitilun,ya qarasa a
hankali ya zauna daga bakin sofa bed ya ware hannayensa dake saman cinyarsa
yana karanto addu'o'in wanzuwa cikin sabon muhalli
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 13
Page 13
yana sauke
dubansa akan ko ina. Bai jima ba ya shafa duka addu'o'in sannan ya miqe. Har
cikin ransa yana jin gidan yayi masa,komai ma na gidan kuma ya dace da
tsarinsa,tabbas farouq din dan uwa ne kuma amini ne na gaske.
Bathroom
ya shige kai tsaye,ya hada ruwa me dan dumi kadan bame yawa ba,don garin an dan
fara zafin da ake sanya rai zai kaimu zuwa ga damuna. Sosai yayi wanka,ruwan
dumin ya ratsashi,ya hada da alwala ya fito.
Wasu
milk color pajamas ya sanya masu tsananin taushi na kamfanin Ralph Lauren,gray
color da suka fidda haskensa da kuma wani kwantaccen kyau nasa daya
mallaka,idanunsa sunyi laushi sosai saboda tsananin gajiya,don a daddafe yayi
wuturi kadai ya wuce saman gadon.
Sasai
yaja numfashi yana furzarwa sanda gabbansa suka samu sakewa sosai cikin
tattausan gadon da aka lullube da luxury bedsheet dan qasar italy kamfanin
feretti. Sosai yaja qamshin da yakeyi har can cikin cikinsa sannan ya fesar da
iskar waje.
Qamshi......qamshi yana daya daga cikin abinda ke matuqar burgeshi a
rayuwa,shi yasa yawa yawan gift din da yake samu suna da alaqa da abu me
qamshi,walau turare body mist ko makamancin hakan......farouq ya dade da sanin
wannan,shi ya sanya ya saka company din da sukayi aikin shirya gidan suka
tsumashi da qamshi.
"Ko zata iya tsaftace gidan ya zauna a haka?" Ya
raya a ranshi,sai ya tabe baki yana juyawa zuwa barin hannunsa na dama gami da
jan qaramin tsaki.
"Ruwanta tayi tsafta ruwanta kada tayi" Ya raya a
ranshi. Abu daya ya sani shi din zamansa a gidan bame tsaho bane,don zuwa yanzu
dole ya fara tabbatar da tsaiwar company dinsa na abuja da za'a bude kafin ya
sakar musu. Wani abu kadan yaji ya taba ransa daya tuna yawan massages da yake
samu na barazana akan company din
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ya furta murya
qasa qasa
(Shin kinsan qarfinta kuwa?,kisan aikin da take yiwa me
yawan ambatonta?,damuwa gareki?,ciwo ne?,ka maqiya suka sakaki a gaba?,ki
kamata qamqam ki hada da salatin annabi kisha kallo,Allah ya bamu dacewa yayi
mana maganin damuwoyinmu ameen).
*******Ba zata ca ga sanda wahalallen baccin dake cike da
mugun zazzabi ya dauketa ba,ita dai ta bude idanunta ne kawai ta ganta kwance
daga bakin gadon,wanda ta tabbatar da tayi mugun juyi cikin baccinta ba abinda
zai hanata fadowa.
Tsoro
gaba daya ba dabi'arta bane,amma kuma tun a jiya ta fuskanci yana neman samun
wajen zama cikin zuciyarta da ruhinta. Tsoron abu guda kawai zata iya cewa ta
fahimta.....girman gidan data tabbatar yafi qarfin zaman mata hudu ma da
iyalinsu.....alamun motsi da shigowar motarsu dama fitar da motar ta
sakeyi,daga haka bata sake jin komai ba amma kuma tsoron bai saketa ba.
Idanunta
ta maida ta lumshe. Ba ciwon kan zuwa yanzu,ba kuma zazzabin,saidai tana fatan
rufe idanunta da tayi dinnan ta budesu ta samu komai ya koma mafarki......komai
ya shafe tamkar bai faru ba. Saidai inaaa.....akace qaddara ta rigayi fata,koda
ta bude komai yana nan kamar yadda yake,agogo naci gaba da tafiya ba tare daya
koma baya ko na second guda ba,wannan shi ya bata tabbacin babu abinda zai
canza din,don haka ta yunqura ta miqe da wata irin kasala tana sauka daga saman
gadon.
Qofa
guda daya da tafi kama data bandaki ta nufa. A hankali ta shiga kamar me tsoron
wani abu kada ya kamata idanunta nabin kowanne sashe na bandakin da kallo.
Komai
luxury ne kuma designer daya sanyashi yasha banban da toilets da dama. Sai data
bata lokaci tana qoqarin tantance komai,sannan ta isa sashen wanka dake dauke
da jacuzzi da bathtub,ta soma zare kayan jikinta. Ko ina na jikinta ya mata
nauyi,sam ba dadi saboda nuqurqusar zazzabi,uwa uba kuma akwai rashin sabo na
kwanciya ba tare da tayi wanka ba,don haka yanzun kai tsaye taji wankan tafi
buqatar yi kafin komai.
Sanda ta
isa ga closet dinta kuwa sai taji gaba daya ta raina duniyarta ta baya,duk
yadda taso abun kada ya burgeta amma hakan bai samu ba,dolen dole ma ya
burgeta,komai a jere a tsare tamkar wani hamshaqin boutique daya amsa sunansa
ta fannin saida komai da komai. Sai yanzu ta fahimci maganar da hadiyya takeyi
bayan sun dawo daga gidanta,suturu ne da batasan iya sanda zata kammala sakesu
ba,kusan komai ya cakude,kayanta na gida da wadanda ta taras a nan,bata ma iya
ganin natan kwata kwata,duk yawa ta suturarta kuwa sun boye tsaf cikin closet
din. Batason ta wahalar da kanta da yawa don bata da wannan energy din,dole ta
zabi atamfa kawai riga 3quater da straight skirt ta saka.
*******Tun daga daren jiya data dawo daga gidan maamah din
wato mariya,bata samu wani cikakken lokaci daya haura mintuna talatin ba cikin
tunani ba. Kowanne motsi da zatayi yana motsa mata da tsananin kwadayin cikar
burinta,wato wanzuwar jininta cikin jinin mamallakin kamfanin sarrafa gold da
diamond din. Ta sani......akwai wasu tsauraran hanyoyi daya kamata ace an
sharesu fetal kafin takai ga haurawa izuwa nata bigiren......to amma
shin.....mallakar fu'ad a hannun mariya kamar yadda takeso zai iya zama mataki
kuma mabudin tata nasarar?.
Amsoshi
guda biyu ne wato eh da kuma a'ah. Eh idan har tayi nata aikin akan hajiya
mariya tazo hannunta.....ita din zata zame mata tsani na mallakawa tata
shalelen fu'ad. Aah idan har ta gaza samun mariya a hannunta ko kuma fu'ad ya
gagara zuwa hannun mariya kamar yadda take buri......shin me zai hana tayi nata
aikin itama daga gefe?,tayi amfani da tata basirar?. Wannan tunanin kadai ya
sanyata yankar asubahi,bata kuma tsaya a ko ina ba sai a gaban babban bokanta
wato BAHAGO.
Maida
foldable basket din me zip tayi ta rufe gami da zuge zip din,sannan ta maida
idanunta kan zuwaira dake zaune a gabanta
"Ina fatan kin riqe dukan baya naina......don a haka
nakeso su shiga kunnuwanta tamkar ni nake bayanan......bana buqatar mantuwa
ballantana ganganci ko kuma kuskure zuwaira.......zaki zauna kuma a iya
matsayinki na 'yar aiki kawai" Kai zuwaira ta jinjina mata. Taji dadin
wannan matsayin sosai da maamah ta dauka da danqa mata,ta wannan hanyar kawai
zata nunawa hajja qarfin mulki da isarta akan maamah din. Saidai kafin tace
komai anyi knocking daga waje
"Waye ne?" Ta tambaya cikin qosawa,don ta fara
gajiya da yawan baqin da suketa zuwa ganin gida. Jiya a daren bata kwana da
kowa ba cikin gidan,tun a daren kowanne baqo ta sanya aka dinga dibansu ana
kaisu gida,na wani garin tunda asuba aka debi hanya dasu.
"Nice......baquwa kikayine tace na gaya niki"
"Baquwa kuma?" Ta tambaya a mamakance,don bata
tsammanin samun baquncin kowa a wannan lokaci,hasalima ta gayawa malam Sa'adu
kada a sake bari kowa ya shigo,koda sun shigo ta barwa masu aiki sallahu ko
waye a gaya masa tana hutawa ne.
"Wacece baquwar?" Ta tambaya kai tsaye cikin bacin
rai
"Hajiya harira" Yarinyar ta amsa mata kai tsaye
"Shigo da ita" Itama ta bada amsa kanta
tsaye,saidai kuma can cikin ranta tana mamakin abinda ya kawota,don a jiya sun
rabu ne tanata mata tsiya,ba zata kuma ganinta ba sai ta huta da kyau.
"Kada dai ace har kin watstsake hutun kuma ya
qare?" Maamah ta fada tana tsokanarta. Wani murmushi ta saki mai nuna
alamun akwai damuwa.
"Ina naga ta hutu mariya?,matsala ta tasomu gaba tun
cikin daren jiya?". Idanu maamah ta fiddo tana matsa mata wajen zama
"Subhanallah.....ni wallahi har kin sanya gabana ya
fadi......matsala ko yaya take banson jin koda sunanta,me kuma ya faru?".
Baki ta tabe tana zama kafin ta bata amsa
"Waini harira za'a gwadawa iya shege?.wai qanin
mahaifin laila ne yazo yakeson gwadamin qaramin shege ne shi.....lallai lallai
wai ya bada laila.....aure nan da wata guda me zuwa". Ido maamah tadan
fiddo a mamakance
"An gaya masa a ina yanzu ake hakan?,ya akayi kika bari
yayi wannan bunqasar hajja?". Kai ta girgiza irin kana cike da tsananin
takaicin nan
"Ki barni dashi......zan gwada masa tawa iyawar indai
harira nake.....shi yasa kika ganni gab da takewar rana.....ajiyar laila
nakeson kawo miki".
"Laila ai d'iyata ce.....wannan bazai zama matsala
ba".
"Shege ne fiye da yadda baki zato,shi ya kusan zamemin
matsala zamanin zamana da abbansu.......inda zai yiwu kuma ba
takura.....kiyimin wannan alfarmar ki ajemin ita gidan fu'ad,don na tabbatar a
can dinne ko daga qiyama ubansa zai dawo bai isa ya shiga da sunan koda ganinta
ba ballantana daukota......wadannan qedarun sun isheshi".
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 14
15
Da farko
maganar taso yiwa maamah din banbarakwai,amma koda ta tuna wacece hajja a wajen
ta da kuma tata fafutukar da suka gama yi tare suke ma kuma kanyin sai taji
wannan din ba komai bane.....ai rama halasci sai dan halak,banda ma plan din da
take dashi batajin zai zama wani abun damuwa don laila zata zauna gidan. Ta
tabbatar bata da matsala da laila,ko ita din tana iya zama me sanya musu idanu
akan plan dinsu.
"Kada ki damu hajja,ni ba abinda bakiyimin ba,kinfi
qarfin haka a wajena.....hakanma qarin samun tsaro ne,don yau nakeson tura
zuwaira ta zauna dasu ta dinga sakamin ido akan komai". Murmushin qasan
zuciya hajja ta saki,bahago shu'umi ne fiye da yadda take zato,ya gaya mata,ya
sake gaya mata dama ba damar musu......mariya ba zata iya musanta mata ba.
"Na gode sosai mariya....Allah ya saka da alkhairi ya
qara zumunci". Kai ta girgiza tana murmushi
"Ba wannan tsakaninmu,kinfi qarfin komai a
wajena......ko yau tana iya shiryawa sai zuwaira ta biyo ta dauketa su wuce,don
banason magariba tayi basu isa gidan ba" Ta fada tana daga wayarta ta duba
lokaci. So samu ace tun da safen nan ya karya da breakfast din yarinyar da zai
zama lullube da makamanta,to amma sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade
ba'aje ba.
Da wani
irin farincikin samun nasara ta isa gida. Ta samu laila din zaune a falo tana
kallo. Kusan tunda ta kammala karatu aikinta kenan. Hajja tayi tayi a samar
mata aiki ta fara tace sammm ita ba zata iya yawo a gari kowacce safiya
ba,hasalima ba zata iya barin baccin safe ba,idan ta barshi waye zaiyi mata
shi?.
Sai
data sha ruwa sosai da lemo,sanyinsa ya sanyata ta fara dawowa hayyacinta
sannan ta maida dubanta kan laila dake matse matsen waya.
"Mansura ta kawomin kayan nan kuwa?" Kai laila ta
girgiza alamun a'ah ba tare data dauke idanunta daga kan wayarta ba. Hotunansa
ke matuqar jan hankalinta,kullum kwanan duniya ta kalleshi kota tuna dashi sai
taji kaman bata tare da nutsuwarta.
Tsaki
hajja taja ta jawo wayarta tana mita ita daya
"Yarinyar nan inajin sai taje gidansu tayi kwana biyu
sannan zata shiga hankalinta". Dab da kiran data mata zai shiga sai gata
ta shigo. Niqi niqi dauke da kaya wanki a wanke a goge a hannunta. Mansura daya
daga cikin surukan hajja da suke rayuwa gida daya,suke kuma karban duk wani
mulki isa da izza tata hannu bibbiyu don ba yadda suka iya,an dauresu da duk
wani zaren sihiri da zai bata damar mallakarsu kamar yadda ta mallaki
mazajensu.
Ko
sallamarta bata amsa ba sai harara data jefeta dashi
"Uban me kika tsaya yi?,na baki wanki tun bayan asuba
da kadan amma sai yanzu zaki gama don bakisan muhimmancin kayan ba?" Bata
amsa mata ba saboda nauyin kayan har sai data zubesu.
"Kiyi haquri hajja,sai dana sallami yara suka wuce
makaranta,abbansu ya fita kasuwa sannan....."
"Sannu dadi 'ya'ya dadi miji,bakisan aikina gaba yake
da nasu aikin ba su duka?,kada ki sakemin irin wannan?"
"Kiyi haquri" Ta fada kanta a qasa,saita janye
kallonta daga kanta tana sake jan tsaki
"Laila tashi ki kwashe kayan nan ki zuban a
wardrobe". Sai sannan ta cire kanta ta kalli kayan
"Kai.....gaskiya hajja sunyimin nauyi bazan iya
ba.....saidai a barsu a nan,zuwa anjima idan na tashi na kwashesu daya bayan
daya". Tsaki hajja din ta sake ja ta maida dubanta ga mansura din
"Kwashesu kikai min wardrobe,kuma bance ki zauna ba
bare ayimin bincike a daki". Itadai batace komai ba ta tsugunna ta kwashe
ta wuce dasu.
"Zaki ajiye wayar nan muyi magana ko sai na
fasata?" Hajja tayi maganar da daga murya,abinda ya sanya laila kashe
wayar ta ajiye agefe,sannan ta juyo wajen hajja
"Gani" Sai data dire cup din hannunta sannan tace
"Kaman yadda nasha gaya miki ina da plan ina da tanadi
a kanki.....tanadina ba kowa bane face muhammad fu'ad jadda.....mamallakin
jadda diamond chore resources.....dan qawata mariyah"
"Ahhhhhh" Laila ta fada tana fidda idanu cikin
tsananin mamaki da kuma gigita. Wani abune da bata taba kawoshi cikin kanta
ba,hasalima batasan akwai qawance har haka tsakanin momynta da mahaifiyarsa ba
"Wasa kikemin hajja?" Ta fada tana kallonta sosai
gudun ganin samu da rashi
"Na taba wasa irin wannan dake?" Maimakon ta amsa
mata saita daka wani irin tsalle tayi kanta ra ruqunqumeta.
"Wayyo Allah mamana......i love you so much
mamana......you fulfill my dream"
"Kinga shashasha zata karyani......da Allah zauna muyi
magana dake don gidansu zaki koma da zama na wani dan lokaci" Ido ta sake
watsowa waje,tana jin komai kaman cikin shirin film ko labarun hikaya
"Serious?"
"Ubanki" Ta fada tana watsa mata zagi da yatsu
biyar,saita saki dariya ta koma tana zama din kamar yadda hajja ta umarta. Baki
ta daga zata watsawa mansura kira sai gata ta fito
"Yauwa saiki wuce ki tafi,ki rufen qofa.....ki gayawa
madeena nan da minti talatin ta dafamin madara ta kawomin,wallahi kuma aka wuce
haka sai ranta yayi mummunar baci". Kai a qasa ta amsa mata ta juya tana
ficewa. Sai data fita din sannan ta maido hankalinta ga laila
"Kina jina ko?"
𝙎𝙖𝙗𝙧𝙚𝙚𝙣
Sake duban
lokaci tayi,sha biyu saura na rana. Tunda ta farka tayi wanka da sallolinta
bataji motsin kowa ba,don hatta securityn dake aikin kula da gidan bakajin
motsin kowa,sanin da sukayi cewa hayaniya da motsi me qarfi na daya daga cikin
abinda boss din nasu bayaso. Uwa uba ma su dake first gate bata yadda na ciki
kamarta zai iya jiyosu. Bawai yunwa takeji ba,amma a jikinta takejin ya kamata
ta sawa cikinta koda ruwan dumi ne. Kaman ba zata fito din ba amma ta miqe,ta
lalubi mayafi ta lullube jikinta sannan ta sanya plate shoe dinta na jiya ta
fara nufar qofa ba tare da tasan takan gidan ba ko kuma daga inda zata fara ba.
Rufaffen
hallway din ta soma ratsawa,wanda aka qawatashi da wani irin wall led light na
musamman,da wasu irin qananu masu haske da suka sake fidda ainihin kyan wajen.
Tattausan runner carpet ne shimfide duka tsahon wajen tsakanin kowanne qofar
daki zuwa na dan uwansa an qawatashi da wasu irin nature frames masu daukan
hankali. Daga bangon dake facing naka kuma,babban console mirror ne da zai baka
daman ganin kusan dukka jikinka har kusan cinyoyi. Akwai plants masu kyau data
gani cikin flower vase masu wani irin daukan hankali,bata sani ba masu kyau ne
ko ma decoration. Guri ne daya cika da hasken da koda allurarka idan ta fadi
zaka iya tsugunawa ka dauka,ko ina fes da wani irin matsanancin tsaftar da babu
qura ballantana ka saka ran samun wani abu waishi datti saman lafiyayyen
marbles din dake lullube kuma shimfide a qasan wajen. Duk zuqar iska guda daya
idan tayi da qamshi take kai mata har hanjinta,qamshin da sam bata da tabbacin
daga ina yake fesowa ya karade kowacce iska dake kai kawo a wajen duk kuwa da a
rufe hallway din yake.
Idanunta
kafe akan staircase din dake gabanta. Batasan ina bane bata kuma fatan sani,nan
din inda aka ajiyeta ma kawai tana jin ya isheta harta kammala abinda zatayi
tabar cikin rayuwarsu,fatanta daya shine idan ta isa staircase din ta samu wata
qofar tsakanin hagu da dama cikin dan lugu biyu da take ganin alamunsa.
Ajiyar
zuciya ta sauke sanda take dab da bakin stair case din,akwai wasu qofofi hagu
da dama,saidai ta daman tafi mata kama da qofar da zata sadaka da wani gurin.
Solid wood
door ne me qofar biyu data dace da kalan gidan gaba daya dake bata kalan gold
and off white,dayan pivot door ne wanda tafi kyautata zaton wani gurin na daban
zai sadaka dashi,don haka ta nufi hannun damanta,ta sanya hannu ta murda handle
din ta bude qofan a hankali kamar me tsoron wani abu.
Wani irin
tsararren parlor ne da kana kallonsa zakasan ilimi hankali da dukiya duka sunyi
amfani. Well designed parlor me wani irin sassanyan yanayi me jan hankali.
Babban swarovski crystal chandelier din dake tsakiyar falon ce kawai a
kunne,amma duka fitilun dake zagaye da falon a kashe suke,saidai duk da haka
hakan bai hana fitar ainihin kyau da tsaruwar falon da aka qawata da kujerun
qasar Italy.
Kutsa kai
taci gaba dayi cikin falon kamar me tsoron sautin takunta,tako ta ina tsarin
gidan yana dada kwance mata kai. Wani irin tsari dake da matuqar sha'awa da
daukan hankali. Idanunta suka fada daya sashen falon.
Glass door
ne da zai baka damar hangen wani guri da aka qawata da wani irin shuke shuke
masu launika daban daban masu daukan hankali. Wajen yafi mata kama da qaramin
lambun da zai taya mazaunin falon debe kewa. Ta sake wurga idonta.....ba wata
qofar a nan data mata kama da qofar kitchen,sai wata qofar shigen qofar farko
data bude.
Ita ta nufa
kai tsaye,tana jin yadda qafafunta suke nutsewa cikin lallausa Italian Versace
carpet daya dace ta kowacce fuska da kalar tsarin falon.
Steps hudu
masu fadi ta soma cin karo dasu,wanda ta nan zata taka ta sauka cikin wani
falon na daban da yasha banbam dana farko ta kowacce fuska. Furniture din ciki
girma da tsari,saidai kusan komai nacan akwaishi anan,illa na wannan falon yafi
na wancan yawa da girma. Rukunin kujeru biyu ya dauka saboda girmansa.
Sabanin
wancan falon,wannan tafkekiyar tv plasma din da tafi qarfin Wall wooden TV
stand din aka girketa samanta ce a kunne. Saudi qur'an ce kunne,saidai kuma
sautin karatun sam baya fita. Lullube kowanne bango yake da tsadaddun curtain
masu wani irin kwarjini da haiba,kowanne maqale jikin Drapery hardware,abinda
zai baka daman ganin qifofin da sukayi saura ta wajen banda yalwataccen dining
area da aka yiwa ado na musamman da roman shade curtain da zai baka daman
kallon wani sashe na kitchen da glass door ya rabasu.
Qaramin
tsaki taja tana janye kallonta daga kallon kowanne tsari na parlor din. Finally
bayan ta gama duk bulayin ta samo kitchen din da qyar,don haka ta taka a nutse
tana hawa steps din da zai sadata da dining din zuwa kitchen din.
Sak tayi
canma tana kallon kitchen din,don wata aljannar duniyar ce da bata san ta ina
zata fara ba. Komai a kitchen din baqonta ne,ba wani abu da zatace ta masa
farin sani idan ka debe kayan amfani na yau da kullum da kowanne kitchen ake
samu. Ya qawatu sosai da custom cabinets da aka sarrafa da wani irin gogaggen
katako datayi imani badai daga qasar nan ba,yabi sauran kayan cikin gidan yazo
ne daga wata qasar daban.
Tunaninta
ya dawo da baya,shin yaushe duka suka samu wannan kudin?,a ina?,da har aka samu
daman zuba mata wannan uwar dukiyar cikin gidan?. Anya kuwa bayan mutunci da
kawun ya saida mata ba hada harda 'yancin jere ga kowacce diya budurwa ba?.
Iya wannan
tunanin ya sake sanyawa taji komai na gidan ya fice mata a rai,baya kuma
burgeta ballantana taba haskenshi. Taja qafafunta da sukayi mata nauyi tana
nufan gas glass stove din tana fatan ta kunnashi daidai kama kowanne. Sai data
bata lokaci shi kansa wajen gane kansa sannan ta saki ajiyar zuciya. Taja da
baya tana baza ido don hango inda zata samu koda ganyan shayi ne,don dama cimar
bata wuce haka. Daga can ta hango wata qofar,ta taka zuwa wajen tana addu'ar
Allah yasa ta samu abinda takeso,don duka ta gwada duba cabinets din bata samu
komai ba aciki,da alama shi kam banda kayan kitchen din da aka jera ba'a taba
komai ba.
Cikin sa'a
ta tadda yalwataccen guri da yafi mata kama da store saidai na musamnan. Don ba
abinda yake zube a qasa hatta kuwa da buhunhuna da kwalaye,kusan duka wajen
shima an masa kanta sosai kamar kanti ko shago,an saka komai a bangarensa
daidai da kwalayen maggi kuwa. Daga gefe babbar freezer ce wadda batabi ta
kanta ba,don ko sha'awar budewa bataji ba,to ta bude taga me?,ba wannan ne a
gabanta ba.
Bangaran
spices na tea ta nufa,ta bude ta debi kowanne daidai yadda zai isheta,daga
wannan ba abinda ta qara ta dawo ainihin kitchen din,ta bare tukunya daya,ta
nufi sink ta kunna famfo ta debi ruwa,sannan ta dawo ta kunna gas stove din ta
dora bayan ta zuba komai.
Minti
goma tsaf ya tafasa,ta soma duba mazubin da zata juye ta wuce dashi,don sam
batason zamanta kitchen din.
Tea set
ne kala kala,ta rasa ma wanda zata dauka. Taja qaramin tsaki still,komai na
gidan ya fiya fi'ili da feleqe,tunda ta tashi komai ma sai tasha wahala take
laluboshi,iya yau kawai.....neman kitchen da dafa tea ya zame mata
alaqaqai?,ina ga sauran rayuwarta cikin gidan.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 15
16
Qarshe dai
wani Wedgwood tea set din qasar chaina ta dauka ruwan sararin samaniya,ta juye
duka ta zuba sugar a mazubin sugar din sannan ta dauka tray na set din cak tana
wucewa ciki dashi.
A yanzun
tafi fahimtar hanyar da take komawa ba kamar dazu ba. Tabbas duk yadda takai
gason ta kushe komai ta kasa,duk.yadda takeso komai kada ya burgeta a gidan
hakan ya gagara,dole ta sallama saidai still zuciyarta na gaya mata
"Allah yasa da kudin halal akayi komai"
(😂 yarinya tunda dai kin fara mora ai magana ta
qare).
Bata tashi
tunawa da personal wayan da ta bata ba sai data kusa kammala shan tea din.
Qarar wayar ya Haifa mata da wata irin faduwar gaba. Wayace data jaddada mata
cewa ta bata ita ne kadai saboda personal use dinta,bata bata ita don ta kira
kowa ba sai ita kadai. Hannu ta tura qasan inda wayar ta fada tun a jiya da
zazzabi ya kamata,ta duba fuskar wayar sunanta ya bayyana baro baro
𝙈𝙖𝙧𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪
𝙖𝙙𝙖𝙢 shine sunan data zabi ta sanya mata saman
number. A zahiri tana qoqarin hana kanta daga wayar ne,don bata da buqatar jin
muryarta kwata kwata.....amma a badini sai taji kamar ana tilastata daga wayar.
Can qasan zuciyarta ta dinga jin bata da wani sauran sukuni saina daga wayar,a
sanyaye ta latsa ta kuma kara wayartata a kunneta
"Amarya.....ina fatan kin tashi lafiya?" Sai da
taja wani nannauyan numfashi tana qoqarin daidaita kanta kafin ta furzar da
iskar a hankali a kuma sirrance
"Ina kwana?" Ta fada da sassanyan murya. Murmushi
maamah ta saki,da gaske aikinta na jiya ya ratsata yadda takeso,ta tabbatar
banda haka bataga alamun zata samu gaisuwa wajen yarinyar ba koda na minti daya
ne
"Lafiya lau....ya baqunta?" Batasan wacce kalar
amsa zata bata ba,don haka ta zabi tayi shuru. Itama shirunta ba shine
damuwarta ba,isar saqonta zuwa ga kunnuwanta shine damuwarta don haka ta dora.
"Zuwa anjima kadan zan aike miki da me aiki da kuma
'yar 'yar uwata......zata zauna daku nadan wani lokaci ne.....me aiki zatayi
aiki ne kadai da umarninki,da tayaki abinda kike da buqata......amma kula da
muhammad da dukkan abinda zaici ban dorawa kowa ba yana wuyanki......kada ki
damu da wanzuwarsu.....dukansu sunsan da tafiyar.....saboda haka ba buqatar
boye boye wajen gudanar da aikinki,kiyi komai kawai gaba gadi. Abu na gaba
muhammad bame sauqi bane.....kada ki sanya rai koki damu da rashin cin abincinki
a zangon farko......kawai kici gaba da dafawar.....kici gaba da shiga
lamarinsa.....kici gaba kuma da dukka qoqarin ki na ganin yaci yasha
din.....yana da tsananin miskilanci......yana kuma da tsantsamin da sai kin
zama me tsananin tsafta kafin ki samu abinda kikeso.....ina fata kin
fahimta?". Can qasan ranta suya sosai zuciyarta takeyi. Tanajin maganganu
na taso mata da ya kamata ta maidawa maamah.....amma sai takejin kamar biyayya
wa umarninta ya zame mata tilas ne kawai,ba buqatar musu ballanta jayayya
"Kin jini?" Ta sake tambaya don tabbatar da taji
komai din
"Eh naji"
"Yauwa.....saikin sake jina ko?,idan akwai tambaya ko
wani abu daya shige miki duhu......qofa a bude take". Kasa cewa komai
tayi,sai kawai ta sauke wayar daga kunnenta tana ajeta gefe tare da binta da
kallo.
Shawarwari
kala kala zuciyarta ke bata game da wayar,wata zuciyar na cewa ta zare layin ta
karyashi ta yar,wata nace mata ta kashe wayar ta wurgar a dustbin,wata kuma na
gaya mata ta sakata a silent tayita kira ba'a dagaba,amma daga qarshe ji tayi
ko guda daya ba zata iyayi ba. Bawai don bata buqatar hakan ta faru ba....aah
haka kawai taji aikata hakan bazaiyi ba,saita nutsa yatsunta cikin gashinta
kawai tanajin kanta kamar ana yamutsashi......umarninta kadai take da muradin
cikawa.
Kusan
saman idanunsa hasken alfijir ya fara keta duhun sararin samaniya yana kore
duhun daya mamayeta,duniya ta fara haskaka da siririn hasken nan dake juyewa
izuwa hasken rana dake wadatar duniya da halittun cikinta.
Wayarsa
ya kalla,a gida a lokuta irin wadannan ya kammala duka wasu addu'insa.....yana
shiri ne ya fita gym da yake bawa awa daya.....so amma a yau din yadda yakejin
jikinsa da sauran gajiya bazai iya komai ba,sai ya miqa hannunsa yana jawo
wayarsa da yaga tana haske sanda qarfe bakwai da rabi na safe ya cika.
Joshua
ne.....ma'aikacinsa dake kula da bangaren marketing da price na gold da Diamond
a kamfaninnikansa. Yana cikin manyan ma'aikatan da baya iya tsallakema kiransu.
Cike da mamakin kiran sassafe irin wannan ya sanya wayar a kunnensa
"Hello......" Fu'ad ya fadi da muryarsa maras
hayaniya musamman daya kasance yanzun safiya ce
"Hello sir........good morning sir......ina expecting
zuwa yanzu baka duba business side news paper da magazines ba ko?"
"Morning Joshua.......what's going on?"
"Sir......sun karya darajar gold da Diamond duka
tsakanin tsakiyar daren jiya zuwa yau da safe".
"La'ilaha illlallah" Labbansa suka motsa ya furta
a nutse idanunsa suna lumshewa. Daga yadda Joshua ke masa magana adan rude ya
tabbatar abun ba qarami bane.
"Cool down Joshua......i will be online yanzu in sha
Allah"
"Okay sir......but sir a irin wannan yanayin da sabon
kamfani ke shirin fara aiki akwai hadari sosai a ciki.....akwai barazanar
tsayawar abubuwa da yawa mo durqushewarsu......sir inaji a jikina an shirya
wannan abunne kawai".
"Calm down Joshua,ba abinda zai faru in sha
Allah.....let work together okay?".
"Okay sir....." Ya amsa da damuwa sosai a cikin
muryarsa.
Kiran ya
yanke yana sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da maida hankalinsa kan fuskar
wayar tasa. Dole ya miqe a nutse ya fara bincika inda system dinsa suke da
sauran kayan aikinsa.
Cup rabin
qaramin cup tasha taji tea din ya isheta. A nutse ta maidashi ta ajiye tana bin
cup din da kallo. Ya mata kyau sosai,amma kuma ba wannan tunanin bane a qasan
ranta,ta janye idanunta tana lumshe. Ta ina rayuwa zata fara?,yaya rayuwar zata
kasance?. Idanunta ta bude,sai suka sauka akan wayar da matar dake amsa sunan
surukarta ta bata jiya. Daga jiya zuwa yau sai takejin komai kamar ya canza.
Har a ranta da zuciyarta sam bata jin matar ko kadan.......tana jin wani
qaqqarfan abu a kanta da yafi kama da qiyayya......qiyayyar batasan ta mece
ba.....saidai koma meye baya rasa nasaba da katsalandan da suka yiwa rayuwarta
ita da d'anta. Tanason kiran momma amma batasan me zatace mata ba.....kuma
kaman a yanzun ma yayi safiya da yawa ta kirata din.
Yadda taji
zuciyarta nason karyewa taji bataso......batason ta karaya tun bata gama
fuskantar komai ba. Gidan yayi mata shuru da yawa,duk da dama can ita ba
ma'abociyar son hayaniya bace....ko a gidansu zaka samu dakinsu a rufe kirif
don rage yawan hayaniyar mutanen tsakar gidan nasu,a mafi yawan lokuta ma tafi
qaunar shurun,sai takejin wata irin kewa tana shigarta.....kewar huda.....kewar
nadra....kewar haneefa. Takan tsinci kanta a wani yanayi maras dadi idan ta
tuna dasu.....ta yaya zasuci gaba da rayuwa?. Tana da nutsuwa kadan idan ta
tuna suna tare da momma bahijja,tayi imani zata cika abinda tace din,amma duk
da haka bata shirya barinsu a wannan matakin ba.
Yunqurawa
tayi ta miqe dauke da tray din don ta maidashi inda ta daukoshi,tako ina tanaji
komai da zatayi amfani dashi a cikin gidan na wucin gadi ne kuma na aro ne a
wajenta,bata da hurumin zafafa mu'amala da komai na gidan.
A karo na
biyu ta sake duban stair case din sanda zata wuce ga qofar da zata sadata da
parlor din. Sai a sannan ta sake qare mata kallo sosai. Tamkar gine ginen
turawa haka aka tsara gidan,wani irin staircase ne me kyau da aka qawata
bangonta da wani irin woods royal frames da
shukoki masu kyan launi da fararen furanni qananu qananu. Idanunta ta
janye tana jin bata da hurumin maida hankali da wajen,saidai girma gidan yana saka mata shakka da tsoro a
ranta,tana kuma cike da shakka da tantamar ita kadai ta kwana ne wai a cikin
gidan?. Saidai basket din data gani ajiye saman table din falon bayan ta dawo a
kitchen din ya fara alamta mata ba ita daya bace ba.
Tana
shirin janye idonta ta wuce ciki taji sallama daga parlor din farko. Da dan
tsoro da mamaki ta maida idanunta kan pivot door din cikin tantamar wanda yake
sallamar. Tsahon second talatin tayi,sai taji ta wuce ciki kawai,don bata jin
akwai wani abu a cikin gidan da take da haqqin lallai saita kula da yadda zai
tafi,saidai taku uku kacal ta sakejin muryar na sake jaddada sallamar. Sallamar
tayi mata nauyin da takeji bai kamata ta wofantar da ita ta Kuma wuce ba,dole
ta dawo da baya tana dosar qofar,ta turata ta bude tana saka qafanta kan step
din idanunta cikin parlor din.
Kamilalliyar macace cikin kyakkywar shiga da lullubi,tana a
tsaye,gefanta kuma kyawawan kwanduna ne guda biyu ajiye a gabanta. Murmushin
data sakarwa sabreen shi ya sassauto zuciyarta,sannan ya zabge kokwanton dake
ciki,saita samu qwarin gwiwar ci gaba da saukowa idanunsu cikin na juna
"Ina kwana" Matar data kusan haifarta ta gaidata
kafin ita takai ga gaisheta.
"Ga waje ki zauna" Tace da ita cikin qarfin hali
ba tare data amsa gaisuwan ba. A nutse kuma cikin girmamawa ta zauna,sai itama
ta samu gefen kujerar ta zauna tana maida mata gaisuwar
"Ina kwana?"
"Barka da asuba,mun tashi lafiya?"
"Alhamdulillah......ya baqunta?" Ta fada da
murmushi da kuma kulawa a muryarta
"Alhamdulillah" Ta amsa mata har yanxu tana
tunanin wace ita.
"Anni ce ta aikoni.....tace kuyi haquri har yanzu akwai
baqi cikin gidan,shi yasa ba'a kawo breakfast da wuri ba,amma gashi nan harda
lunch don kada ayi delay na kawowan da wuri shi yasa ta hada.... Tace da fatan
hakan ba damuwa?" Sunan tadan juya cikin ranta,amma kuma farat daya
hankalinta sai yakai kan matar. Murmushi tadan saki tana mamakin damuwar da
tayi dasu haka
"Ba komai.....ayi mata godiya sosai" Ta fadi tana
jin wani abu na daban akan matar. Miqewa matar tayi
"Sunana baraka.....dadaddiyar hadimar anni ce ni,zan
koma,a huta lafiya" Kai kawai ta gyada mata,har ta fice idanunta suna
kanta. Sai ta ajiye ajiyar zuciya tana maido kallonta ga basket din gabanta.
Tadan xuba masa idanu tana nazarin matar,komai nata cikin dattako.....kuma
komai nata akwai alamun nutsuwa me yawa a tattare dashi,waishin WACECE UWA a
cikinsu?,wacce mahaifiyar ta ainihi?. Wannan tambayar kusan ita daya ce abar
data damu da ita cikin lamarin kaf,sai ta miqe a nutse kaman zata bar wajen,sai
kuma ta fasa,ta tsugunna ta dauki basket din,ta taka a hankali zuwa dining area
din da aka qawata da wani dunqulalle kuma mulmulallen dining data kasa tantance
glass ne ko kuwa dutse?,ta dora basket din kawai akai,sannna ta juya tana sauka
ta wuce zuwa dakinta.
Sai daya
daidaita komai sannan ya hada connection din duk da yakeso. Bincike ya fara yi
a kasuwannin hannun jari na gold da Diamond.......da gaske an masa wani irin
mummunar faduwa da bai taba ganin yayi hakan ba tsahon fara kasuwancinsa. Baya
ya koma ya jinginar da bayansa jikin kujera yana shafa lips dinsa da yatsansa
guda daya. Da gaske akwai faduwa da hasara me yawa data samesu,musamman a irin
wannan lokacin da kwanaki kadan suka rage kamfani ya fara aiki. Zai zamana kome
xasu fitar ko su samar asara ce a garesu,dole su saidashi a qasa da farashin da
aka tsara za'a fiddashi. Saqonnin da aka yita turo masa suka dawo masa akai,ya
lumshe idonsa ya kuma budesu yana kiran sunan Allah,sai ya sake maida hannunsa
kan system din.
Kusan duk wani
ma'aikaci dake aiki qarqashinsa na kusa dana nesa sai daya nemeshi. Ya bata
lokaci sosai yana urgent meeting dasu,wanda hakan ya daukeshi aqalla a wanni
masu dan dama. Baisan kuma ya jima din a zaune ba sai da cikinsa ya fara qara.
System din ya rufe yana furzar da iska daga bakinsa. Ya tabbata babu abinda
zasu iya sakeyi......dole su rungumi dukka hasarar data tunkarosu lokaci
guda......
Akwai
manufa.......kuma anyi ne da gayya,kuma hakan ya sake bashi tabbacin dukkanin
saqonnin da aka aike masa da gaske suke.....sun shirya shiga yaqin tare
dashi.....sun shirya jan daga shi dasu. Sai ya saki wani qaramin murmushi.
Sunyi gangancin fara tsiro irin wannan abun dashi......ya tabbatar basu gama
sanin ainihin waye muhammad a kasuwancinsa ba.......wannan abun koma waninsa
bazai sauyashi ba......bazai kuma sakashi ya tsaida kowacce harka tashi ba.
Har a
jikinsa yakejin a baqon guri yake,banda haka zuwa yanzu da tuni Ameh ya dameshi
da batun abinci. Hannunsa ya miqa ya dauki wayarsa ya kunnata daga kashetan da
yayi
"Subhanallah" Ya furta da hanzari ganin har azahar
ta sanyo jiki. Bai kira anni ba.....bai kira farouq ba,baima kira kowa ba wanda
aqalla ya dace ya yiwa kowa bangajiya koda kuwa ba shine ya gayyatosun ba,amma
aqalla sabodashi suka zo. Anni ya fara kira amma sai yaji wayar a kashe,yasan
har yanzu gidan akwai sauran baqi don haka yafi kyautata zaton uzurin daya
sakata kashe wayar kenan.
Yayi zaton
zai samu saqon farouq amma sai ba tarar ba. Ya danji ba dadi,don haka kai tsaye
ya fara kiransa.
Bugu daya
ya daga kamar dai dama wayar tana hannunsa yana jiran kiran nasa ne. A nutse ya
masa sallama,daga can background yana dan jin muryar mutane.
"Kaji muryar ango......so fresh" Farouq din ya
fada kansa tsaye.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 16
"Sai yanzu aka tashi kenan?" Farouq din ya sake
fada ba tare daya damu da abinda zaice da farko ba a lallai sai ya tsokalo shi
"Eh.....ka nemeni ne?"
"Wa?,ni?,ya za'a yi na batawa kaina lokacin
nemanka?,waya gaya maka ana kiran ango a irin wannan time din?"
"To hell with you farouq a'ahhhhh" Ya fada
sounding bored kadan kadan.
Murmushi me
kama da dariya ya saki wanda har sautinsa ya bayyana sosai.
"An maka uziri kome zaka fada you're forgiven"
Hannunsa ya dora saman sumarsa yana shafawa,ya fuskanci farouq so yake kawai ya
haukatashi
"Where's anni?"
"Na barta a gida tana preparing na walima....."
"Ya salam" Fuad ya fada yana lumshe idonsa. Sam ya
mance da batun walimar kwata kwata.
"Su haajj na yiwa rakiya airport......they're
leaving".
"My regards to them please.....idan na sake nutsuwa
zuwa anjima in sha Allah i will give them a call"
"Ance maka daga yau har wani satin an maka uzuri
fa.......ka samu nutsuwa yadda ya dace dudu" Ya rigashi katse wayar wannan
ya hana fuad gaya masa abinda yayi niyyar fada din,sai kawai ya zame wayar daga
kunnensa,qasan ransa yana fassara maganar farouq da kuma sakata a inda farouq
din ke nufi
"God forbid" Ya fada qasa qasa. Hasashen gaba days
banbarakwai yayi masa sanda ya dora tunanin a muhallin da farouq ke
nufi,tattara tunanin yayi ya azashi a mizanin shirme gaba daya,ya fara lalubar
number amna.
Sai data
kusa yankewa sannan ta daga
"Hamma" Ta fada a shagwabe.
"Hamma ka manta dani.....adda tayi taking dinka
away.....as far as yadda zata iya" Ta qarasa fadi da qaramar dariya a
muryarta da ba sosai ta bayyana ba
"You amna.....lovey dovey will never be
forgotten........hayaniya yayi yawa amna.......bansan haka ake abun ba"
"Hamma yafi haka fa.....don kaqi bada hadin kai ayi
komai" Hannunsa ya dora a goshinsa yana furzar da qaramar iska. Shikam ko
zancan bayaso,abinda yake gabansa kawai yanzun shine damuwarsa.
"Ya gidan?" Ya tambayeta.
"Full with 'yan biki dake jiran walimar anni......ina
yini hamma" Ta hade amsa tambayar tasa da gaisuwa.
"Alhamdulillah.....how about anni da abba?"
"Abba dai ya fita tun dazun.....kuma ina jin sai dare
zai dawo........anni tana daga baya da mutane"
"Okay.....bata wayar"
"Okay hamma" Ta amsa shi tana miqewa gami da
ficewa.
Bai yanke
kiran ba saita maida kunnenta,tana tafiya wajen annin tana ta bashi labarai
kala kala. Bai yanketa ba yayi shuru yana saurarenta. Yasan halin amna
sarai,bata gajiya sam sam da hira.
"Kice ameh ya kirani....."
"Okay hamma.....ga anni" Saita miqawa anni
wayar,ta samu plastic chair daya daga cikin kujerun dake wajen ta zauna tana
kallon yadda aka qawata wajen walimar da wani irin tsari me kyau,tamkar wani
hamshaqin event center.
"Barka da warhaka anni......ya hidima ya rana?"
Murmushi ta sauke,har cikin ranta farinciki yana mamayarta idan ta tuna a yau
muhammad dinta ya zama cikakken magidanci
"Barka kade me babban suna.....mun tashi lafiya zance
ko mun yammata lafiya?". Tambayar tata tadan sakashi yaji nauyi,kada itama
fa ta dauka wani abune ya boyeshi,kada ta fassara wani abu na daban akan
yarinyar ma da bai samu daman ganinta ba
"Lafiya anni alhamdulillah"
"Haka akeson ji.....na aika baraka takai muku breakfast
da lunch.......nayita so nace idan ta isa ta hadani da d'iyata mu gaisa saina
sha'afa......in tana kusa bani ita"
Rasa abinda zaice yayi,yadan diririce kadan har hakan yaso ya nun alamu
a muryarsa,yayin da annin ta dauka wani abunne na daban ya kawo hakan,kodai
baiso aji muryarta a fahimci wani abu,don haka ta katseshi
"Kaga rabu da ita.....anjima idan kun iso wajen walima
ma gaisa.....za'a fara immediately after asr prayer"
"Allah ya kaimu anni.....Allah ya qara girma da
lafiya"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ta fada tana jin dadin
yadda sam baya gajiya da mata addu'a.
Ita ta
fara katse wayar,sai shima ya sauke yana kallon fuskar wayar. Inda anni ta sani
data qyale walimar nan,duk da ita walima duk inda take albarka ce. Agogo ya
kalla har daya na rana yayi,sai ya aje wayar yana jin zuwa yanzu ya kamata ya
laluba kitchen ya samu koda tea ne ya sanyawa cikinsa. Duka wani abu daya saba
sha da safe irinsu goji berries water da turmeric tea,cinnamon tea da
sauransu,wannan ya sanya yake da wani irin cikakkiyar lafiya da kuzarin da idan
ya shiga cikin maza kuzarinsa yake fita daban,kaman yadda yake da cikakkiyar
lafiya irin ta d'a namiji,wanda yayi imanin banda busy da business daya saka a
gabansa suka fatali da komai da yakeji......tabbas da bai isa yakai har wannan
lokacin haka ba,dalilin da yasa ya janyewa amfani da wasu abubuwan irinsu
ginseng tea,sai time to time idan yana da buqatar hakan,ko ya kwana biyu bai
sha ba.
Fararen
loopers slipper ya sakawa qafafunshi,wadanda suke mahadi ne na fararen pyjamas
din jikinsa da suka fidda siga da surarsa. Yanayin fatarsa kadai ya isa ya fadi
maka irin wadata da nutsuwa da yake ciki,skin dinsa so fresh da ba lallai ta
wata macen ta samu irin wannan kyan da glowing din ba.
Sai daya
shiga toilet ya daura alwala,ya dauki qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa
sannan ya maida takalmin ya nufi qofa yana gyara hannun pyjamas dinsa daya
tattare.
A nutse ta
idar da sallara azahar tana maida idanunta wajen sujjadarta. Tana jin idanun a
jikinta sunyi mata nauyi,nauyin da bata raba dayan biyu yunwa ce da kuma bacci.
Baccin kam tana da tsananin buqatarsa,ita kanta ta sani,saboda ita kanta tasan
cewa taci bashin baccin yadda ya kamata,abincinne bata jin akwai muhallin da
zata sakashi a cikinta,saidai jikinta na sake gaya mata ya zama dole ta
nemeshi.
Dole ce ta
sanyata miqewa,a nutse ta nade abun sallar,ta gyara yafen dan madaidaicin hijab
din data dauko daga closet din nata ta daure igiyar sannan ta juya tana lalubar
qofa bayan shawarar da zuciyarta ta bata nata duba cikin kayan da aka kawo ko
zata samu abinda zata saka a cikinta.
A nutse
ya sauko daga saman yana sake jin nutsuwa da gidan da tsarin gidan. Ya dauke
idanunsa daga hallway din da yake kyautata zaton shiyyarta ne. Qofan dake
damansa ya karya zai bude sai kuma ya fasa,ya koma ya kama handle din wooden
door din ya bude yana isa ga falon.
Ko ina da
komai yana nan kamar yadda ya barshi a jiya,da alamu ba'ayi amfani da parlor
din ba kwata kwata. Zarcewa yayi parlor din farko wanda keda kitchen din,ya
sauka daga kan step din a nutse sannan ya zarce zuwa dining da hake hango
basket akai,da alama saqon da anni tace ta aiko ne.
Yana daga
tsaye ya miqa hannu a mamakance ya jawo basket din,yadda aka kawoshi haka aka
ajiyeshi,da alama ba'a ko budeshi ba ballantana a taba komai a ciki.
Waye to ya
karba saqon ya shigo dashi?. Ba kowa sai ita wannan shine amsar daya bawa
kansa,don ya sani ba wanda zaiyi gigin shigowa cikin gidan saboda sunsan doka
da kuma tsarinsa. Duk wani ma'aikaci dake aiki a qarqashinsa,daga cikin company
har zuwa cikin gida kowa yana tsayawa iya limit dinsa ne,ba wanda yake wuce
qa'idar aikinsa ko kuma limit dinsa.
Komai anni
ta zuba na duka irin abinda tasan yafiso yaci da safe ya kuma ci da rana,ya
sauke qaramar ajiyar zuciya yana sake jin qaunar matar da martabarta suna
hauhawa a zuciyarsa. Baiga wani abu da zai taba annin ya bari ba ko
wayeshi,take sai yaji ransa yadan baci,ganin kamar ta wofantar da kayan da aka
kawo din. Daidai abinda cikinsa yake buqata ya zuba,kafin ya gama duka ya bata
wajen saboda rashin sabo,ya manta when last yayi serving kanshi,duk wani motsinsa
akwai masi hidimta masa.
Tsaki
kadan yaja ganin bacin da wajen yayi,ya soma wassafa yadda zai aje masu masa
hidima cikin gidan kaman yadda ya saba,don bayajin zai bari ya takura har
haka,ya dauko komai cikin qaramin serving tray ya dawo ainihin parlor din,sai
ya azashi saman side table. Har zai zauna sai ya fasa,ya dauko remote yana
lalubar channel din dake haska rate na dollar pounds da rate na diamond da
sauran harkokin kasuwanci. Har yanzu yana cike da mamakin yadda abun ya
kasance,duk da iya bincikensa har yanzu ba wanda yasan daga ina faduwar gold
din haka rugu rugu ya samo asali.
Ya soma
sipping pomegranate juice kenan idanunshi suka sauka akan basket din. Tun
basket din jiya da farouq ya hadoshi dashi,wanda shi kansa baisan anihin meye
da meye a ciki ba. Bacin ran da yaketa qoqarin boyeshi dole a wannan karon ya
bayyana kanshi.
"What's all these nonsense?" Ya fada can qasa
labbansa suna motsawa.
Kamar jira
akeyi yayi tambayar yaji alamun motsin mutum. Fararen idanunshi ya daga still
cup din yana saitin bakinsa,baikai bakinsa ba bai kuma dire ba,ya zube manyan
idanunshi a kanta. Karon farko da ya fara mata kallon kai tsaye a
rayuwarsa,karon farko da yayi mata kallon da zai iya gane face dinta.....don
kuwa a baya zai wahala ya iya cireta cikin mata goma ko biyar idan aka zube
masa su.
Kwata
kwata bata lura da mutum ba sanda take sauka daga steps din zuwa qasa don nufar
kitchen,amma da yake cikin dabi'arta akwai sanya idanu da kula da motsin komai
da komai dake kewaye da ita,da kuma sanya hankalinta bisa yanayin kowanne abu
saita dinga ji a jikinta kamar akwai wani baqon abu da babu shi dazu a parlor
din. Juyi biyu ana uku idanunta suka sauka akan nasa........itama karon farko
kuma lokaci na farko a rayuwarta datayi masa duba nakai tsaye.....duban dake
rataye da abubuwa masu yawan da suka faru.
Wani
nannauyan abu taji yana fita daga idanunshi zuwa nata yana neman kwarjanta mata
shi da wani irin madaukakin kwarjini da bata taba siffantashi a dukka
hasashenta dashi ba,sai ta janye idanunta daka kaf sashen da yake tana jin wani
bala'e'en haushinsa yana sauka mata a hankali a hankali da wani yanayi me kama
da tsanar mutum. Shine silar komai da komai,shine kuma maja ragamar kowacce
kalar qaddara data sameta da kuma zata iya samunta a nan gaba.
Tashi
zuciyar kuwa ta cika da mamaki a yanzun da idanunsa ke sake haska mata qarancin
shekaru qarara dake tattare da ita. Wani irin qyanqyaminta da wasarta suna
nasar zuciyarsa. A wannan age din nata da duka duka idan tayi wuta bai wuce ace
tana level one ba......amma s irin shekarun har take da fikirar SATA SANE FASHI
DA MAKAMI TA YANAR GIZO.....abu mafi muni kuma shine KARUWANCI BIN MAZA.
Wannan
abu na qarshe daya tuna kadai ya sanyashi yaji zuciyarsa ta sake matsewa. Koda
aboki ne dashi yake da dabi'ar neman mata......ba aboki ba,koda abokin
kasuwancinsa ne kai muddin wannan din dabi'arka ce.....muddin kuma ta bayyana
ya sani to yana haqura da huldar kasuwanci dakai.
"Zunubinsa daban dude......haka mu'amalarku ma
daban.....shi da Allah wannan halin nasa,baka da ikon canzashi" Kadan daga
cikin abinda Farooq ke yawan gaya masa. Harara yake balla masa wani lokacin
"Bani da sha'awar karbar kudi daga hannun ma'abocin
sabon ubangijinsa,wattaqu fitnatalla tusibannal lazina zalamu minkum
kaaassah(kuji tsoron fitinar da idan tazo bata shafar iya wadanda sukayi
zalinci kadai a cikinku).idan kana neman albarka ubangiji cikin samunka....kayi
qoqarin kaucewa masu saba masa,sai taka dukiyar tayi albarka". Irin
maganganun nan sun jima suna fafatawa a kansu shida farouq.
Ji tayi
kaman jikinta na neman rasa duk wani confidence.....hakanan batason wanzuwa a
muhallin da yake fesar da iska tana shaqa,sai taji kamar wadda ya fitar ita
take zuqa,don haka ta juya a nutse da zummar komawa inda ta fito,tana ji har
cikin ranta ta haqura da duk uzurin daya fiddota.
"Ke!" Ta tsinci husky voice dinsa da bata taba
jinta kamar haka a kusa kusa ba sai yau......karon farko kenan,wannan ya hadu
da saukar tsawar tasa ya sanya gabanta wani mummunar faduwa.....kafin ta samu
tayi hanzarin daidaita nutsuwarta da tattara dukka qarfin ta.
Zuciyarta ke qarfafarta kada ta tsaya.....salon kiran da yayi mata din
zallar raini ne.......yayin da ta nashi gefen ya fita hasala.
Ya za'ayi
ya kirata yarinya qarama irin haka tace zatayi ignoring nasa?,yarinyar da yayi
imanin tsakanin musaddiq da saddiq ma babu sa'anta......koda ta girmi amna ma
kuwa yayi imanin ba zata bata sama da shekara uku ko hudu ba.
"Na rantse qafarki ta sake taku daya daga nan saina
kakkaryaki na zubar" Ya fadi a hasale,saboda abinda tayi masan bazai tuna
mutumin daya taba masa hakan ba tun sanda sunansa ya shiga duniya a matsayin
muhammad fu'ad jadda.
Batasan
me yayi mata birki ba,har ta daga qafar zata taka step na farko saita mayar ta
ajiye. Zuciyarta na mata wani irin suya a qirji. Ita yau sabreen wani d'a
namiji ke kwatsawa tsawa har haka?,saboda kawai yana tutiyar ya aureta?.
"Dawo ki zauna!" Ya sake fada a kausashe har sai
da taji kaman yana daf da ita ne.
"Ki sake na maimaita miki kuma....wallahi yau a cikin
dakin karnuka zaki yini" Ya furta muryarsa na bawa me sauraro tabbacin da
gaske yake.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 17
18
Wasu
maqalallun hawaye da bata tsammacesu ba taji suna tsatsafowa daga cikin qwayar
idanunta,tayi hanzari da gaske ta dakatar dasu cikin bawa zuciyarta umarnin
"Ba faduwa.......ba bada damar ganin lago.....i want to
win". Abinda ya saka hawayen komawa kenan,saidai har yanzu tana jin
alamunsu.
Ta koma
ko ta wuce abinta?,duk abinda zaiyi ma yayi?,ko kuwa ta zauna ya lissafa nasa
qa'idojin itama ta sanya mishi nata iyakokin?. Bata tantance wanda zata dauka
ba saiga kira ya shigo wayartata. Kallon wayar kawai sai taji tamkar wata
sabuwar barazanar ce ta shigo cikin rayuwarta,sunan matar datayi saving dai
still shi yake yawo. Abisa son ranta bata da Sha'awar sauraronta.....amma bisa
tilastawar zuciyarta sai taji ba zata iya tsallakewa kiran ba,a sanyaye ta daga
ta saka wayar a kunnenta.
"Tun dazun nake zuba idanun ganin kiranki ai.....na
dauka zaki nema taimakon abu na farko da zaki fara girkawa a gidan" Muryar
maamah kenan da kalamanta na farko data fara jerowa baya ga amsa sallamarta da
tayi. Idanunta data lumshe ya tilastawa boyayyun hawayenta saukowa,amma sai
tayi hanzarin daukesu tana sauraren muryar matar.
"Na manta na gaya miki wannan ko zasu taimaka miki
wajen cimma nasara........yana da zafin rai.....yana da kafiya,bayason raini
bayason musu.......bayason qazanta........kiyi duk yadda zakiyi ki zama ke kike
ci dashi......ki sadaukar da komai masa......ki qarar da tunaninki kan duk
hanyar da zaki maido cin abincinsa hannunki.......wannan shine kadai abinda zai
sama miki 'yanci....." Saita dakata kamar me shirin bata damar cewa wani
abu kafin ta qara
"Idan kina da tambaya ko buqatar qarin bayani qofa a
bude yake......zuwa anjima kina da baqi......saidai mutum daya ta qaru.....zan
miki bayani a kanta.....af na manta na gaya miki.......dazu huda ta tsallaka
shop din tsallaken titin gidanku fa". Mummunar faduwa gabanta yayi da
ambatar sunan huda kawai a bakin maamah... Da gaske mutanen suke......sun mata
tarko da 'yan uwanta,da gaske suke suna bibiye ne da rayuwar 'yan uwanta
mahadin numfashinta?,da gaske kowanne motsi nasu a lissafe suke dashi?. Tabi
maganar maamah ta tseratar da rayuwarsu?......a yanzu tana jin kamar shine
babban haqqin daya zame mata dole ta sauke.
Batasan
ya iso wajen ba,kawai abinda taji shine zare wayar daga kunnenta. Ba qaramin
firgita tayi ba,saita waiwaya da hanzari tana fuskantarsa sanda ya zubawa
fuskar wayar idanu lokacin da kiran yake yankewa da sunan mariya b'aro baro
akai.
Ci gaba
yayi da kallon fuskar wayar har sunan yayi disappearing yana sake maimaita full
name din nata qasan zuciyarsa. Wani abu ya taso masa.......zarginsa yana daduwa
daga kaso sittin cikin dari zuwa kasu casa'in da tara cikin d'ari.
A nutse
ya maida qwayar idanunsa kan fuskarta,haka kawai taji qafafunta sunyi laushin
da kafin ya sake cewa komai ta koma ta zauna saman kujerar dake daura da
ita,tana mamakin yadda nature da colour na idanunsa suka sauya kadan.
Wayar ya
cilla mata ta sauka daidai saman cinyarta,sai ya soke duka hannuwansa cikin
aljihun wandonsa yana dubanta kai tsaye.
"Kada ki dauka zakiyi duka irin rayuwar da kikaga
dama,kada ki dauka zakiyi kalar rayuwar da kikeso.....kada kuma mi rudu da cewa
kinzo nan gidan don ki huta......ki debi adadin kudi da dukiyar da kikeso daga
jikin muhammad jadda.....idan kin dauki duka wadannan abubuwan a
ranki......" Sai kawai wani siririn murmushi ya kubce masa,ya cije redlips
dinsa yana dage kafadunsa sama
".......kina ruwa" Ya qarasa fada yana jawo wata
ottoman chair 'yar qarama zuwa gabanta yahau kai ya zauna
"Kisa a ranki nan kin shigo gidan tarbiyya da gyaran
hali ne......gidan qare kukanka.......gidan bin daidai.......wadancan kayan
duka da aka shigo dasu kin dauka a caca aka ciyosu?,ko kuma fashin yanar gizo
da kutsewa account din al'umma akayi aka samosu da zaki bar komai cikin
jakarshi?,salon idan ya lalace baki da asaran komai?" Wasu irin zafi sosai
maganganunsa sukayi mata,irin zafin da bata taba kawowa ba. Ko mahaukaciya ce
ita ta fuskanci inda batunsa ya dosa ballantana da hankalinta fes,zafin maganar
ya tilastata daga oily eyes dinta masu sheqi dake shige da nasa ta kalleshi
dasu.
Duka girarsa
ya dage sama yana dubanta da fuskar da babu digon walwala ko sassauci a ciki
"Yes.......gidan nan dama komai da zai gilma a ciki
zallar halak ce ta samar dashi.....so that bazan dauki almubazzaranci
ba......dole ki kula da komai a daidai sanda ya dace da yanayin daya
dace.....zaki zauna a cikinsa kiyi aiki irin na kowacce matar aure......zaki
zauna a cikin gida kamar yadda musulunci ya tanada......zaki kuma zaman gyara
halinki yadda zaiyi daidai da halin mataye na gari,ta yadda wataqila a gaba
idan kin hadu da wanda kika dace da ra'ayinsa,zai dauki mace ta gari ba
makwadaiciya me qarancin duka wata siffa me kyau ba.......".
Banda
sunansu huda,da zabin maamah dake mata amsa kuwwa cikin kwanya batajin zai fadi
dukka wadannan kalmomin bata zazzage masa fiye da abinda ya gaya mata ba. Ba
zata iya tuna cin mutuncinta da akayi a duniya da yakai wannan muni ba......cin
fuska irin wannan a gaban idanunta,cikin salo na gadara da ganin isa.
A nutse ta
daga idanunta da wani irin coolness ta watsasu saman fuskarsa. Kallon kallo
suka yiwa junansu na wasu sakanni,kowa da abinda ke gudana cikin zuciyarsa game
da dan uwansa. Fuska ya sake tsukewa sosai ya dage dukka girarsa biyun
"I told you.....your attitude needs a serious
adjustment.......bazanyi tolerating any nonsense ba.....just obey all of my
rules" Yana kaiwa nan ya miqe a nutse yana ajiye mug din sannan ya sake
zuba hannunsa a aljihun wandonsa still yana kallonta.
"If you have any plans i beg you kada ki fasa......if
you collect some money or something else.....kiyi duk abinda kike ganin kin
tsara" Yayi maganar wani abu yana
taba zuciyarsa,zarginsa kuma yana sake qarfi a kanta da ganin sunan maamah
kawai cikin wayarta. Wani mahaukacin bugun zuciya ya haifar mata,ba shiri ta
sake daga kanta zuwa gareshi sanda yake barin wajen. Wannan karon kam duk
qwarewarta wajen iya boye hawayenta abin ya faskara,fara tsiyaya sukayi kafin
ta sake jin muryarsa yana fadin
"Qarfe hudu akwai walima wajen anni......bana african
time don ban sanshi bama.....i hope you get it" Ya sake fada ba tare daya
waiwayeta ba.
Kasa
tashi tayi a wajen wani irin baqinciki yana nuqurqusarta. Tsantsar tsana da
haushin maamah yana sukar zuciyarta. Bata qyale ire iren wadannan
abubuwan.......ba abinda yake sakata sarewa ko fargaba,amma ta mata mugun qulli
da dabaibayi da 'yan uwanta?,why?.....me su huda sukayi da zata sakasu a wannan
wasan?,me yasa ba zata bari suyi tsakaninsu ba a nan zata fahimci wacece
sabreen din....muhammad jadda......yana buqatar ta karanta masa karatun d'iya
mace,if gana expecting taka kowacce mace don yana da dukiya da kuma
kyau......zata so ta zama macen farko da zata banbance masa tsakanin aya da
tsakuwa,amma a yanzun hakan kuwa zai yuwu?.....she needs to be very humble don
ta kubutar da 'yan uwanta......but ba zata dauki raini wulaqanci da kuma cin
fuska daga wajensa ba,wannan shine lokaci na qarshe da zata bari ya jera mata
maganganu masu zafi irin wannan,zata saka dukkan effort dinta donta gamawa
maamah aikinta cikin sati biyu ta kauce ta barsu da rayuwarsu su qarata,idanma
gasashi zatayi ta cinye dukka damuwarsu ce.....itama nata familyn ta sani,zaman
lafiyarsu da kwanciyar hankalinsu shine first priority dinta.
A
nutse ta miqe ta ta soma kauda komai badon maganganunsa ba....sai don da gaske
bai kamata abar komai a wajen ya lalace ba. Neman abinci da samunsa abune me
matuqar wahala wanda itace shaida akan hakan. Ta killace komai sannan ta
tattara ta wuce zuwa dakinta,saidai qasan ranta cunkushe yake da wani irin
bacin rai tare da lissafe lissafe masu yawan gaske game da yadda zata tunkari
rayuwar.
"Don't be sad.....kada ki takura kanki da yawa.....just
live your life normally yadda ba zaki cutu ba" Abinda zuciyarta ta dinga
nanata mata kenan.
Akan
idanunta biyu ta buga uku tazo ta shude aka doshi hudu. Bata dako niyyar shirin
komai bare akai ga batun zuwa walima. Komai nasu baya burgeta......bata da
buqatar kuma ta cudanya dasu sam sam.
Daidai
lokacin da yake samanshi bayan dawowarsa daga sallar la'asar. Yaga kira daga
security din dake waje sun shaida masa yana da baqi gasu zasu shigo ciki. Tunda
yaji haka yasan 'yan gida ne.....inda baqin fuska ne lallai saisun nema izini
an basu kafin su barsu su shigo,sai ya qarasa shiryawa cikin shaddar daya
dauko,don already wandon yana jikinsa kafin yayi receiving call din.
Wagambari ce
a jikinsa,asalin tsadajjiyar wagambari sky blue da aka yiwa wani irin dinki na
alfarma dake nuna zallar zamani da kuma sanin darajar ado da dinki. Ba wani
mutum da zaiga sutura a jikinsa ya sake ganinta ya maimaitata,kusan sakawa daya
yakewa kaya ya gama dasu,shi yasa duk sati cikin fidda suturunsa ake.
Gaban
madubi ya tsaya yana karya hular da zai sanya,shi gaba daya a takure yake,ire
iren wadannan sabgogin bai saba dasu ba kwata kwata,wani harkar taro na
biki,idan kanason ganin karsashinsa kazo sashen maganar kasuwanci. Kayan
jikinsa kansu nauyi sukeyi masa,baisan ma me yasa a kayansa na wannan watan aka
hada masa da dinkin manyan riguna ba,amna daya tuna farouq sai ya tabbatar
shirinsa ne kawai.
Halfcover ya sakawa qafarsa dan qasar italy da akayi cinikinsa da
dollars masu yawa. Ya sanya hular saman kansa take wani irin
mutum.....lafiyayyen half cast ya fito me matuqar daukan hankali da kwantaccen
kwarjini daka iya wucewa da zuciyar kowacce d'iya mace.
Waya daya
ya dauka kawai sannan ya soma barin dakin. Yana sauka ne cikin takunsa dake
bayyanar da nutsuwarsa jin kansa da kuma kamun kansa irin na cikakken namijin
daya hada abubuwa da dama.
"Wow summa wow.....hammana" Muryar amna ta fara
sauka a kunnensa sanda yake fitowa zuwa parlor din.
Yadda tayi
maganar ya sanya murmushi subuce masa,ta kuma tuna masa da lokutan baya da yake
very free ba kaman yanzu ba. Kullum ita ke bawa kwalliyarsa mark,anni na zaune
a gefe tana musu dariya,saddiq na tsokanarta wani lokaci harsu sanyata
kuka,shike tare mata shine ke hanasu.
"Hamma ka sake zama ango sak......don Allah BB
farouq,kalli ta nan gefen" Sai datayi maganar ya lura da farouq dake zaune
kujerar qarshe riqe da wayarsa yana dannawa. Kadan ya daga kai ya kalleshi ya
maida ga wayarsa
"Yayi kyau mana amna.....amma kubarni nima soyayyata
nake qoqarin gyarawa......Allah bazan qara wata uku a qasa ba.....guy dinnan
daga jiya zuwa yau kalleshi ya sake canzawa?".
"Stop it farouq......" Fuad yayi saurin fadi yana
duban amna kafin ya maida kallonsa ga farouq din. Ya fahimci sarai abinda yake
nufi,akwai amna a wajen
"Hamma........am eager to see my aunty
wallahi.....where's she?" Ta furta alamunta na nuna da gaske sabreen
takeson gani,tana jin qaunarta sosai har cikin zuciyarta saboda hammanta.
"Jeki fito da ita" Ya fada yana yiwa amna nuni da
hanyar. Bata ko tsaya sauraren komai ba ta wuce wajen da sauri saurinta.
Qarasa
takowa yayi wajen da farouq ke zaune bayan wucewar amna din,aje wayar farouq
din yayi yana dubansa.
"Mutumina......akwai labari kenan" Ya qarashe
zancan yana kashe masa ido. Harara ya gasa masa
"Gidan jarida na bude daga jiya zuwa yau baka sani
ba?" Dariya sosai farouq ya tuntsire da ita.
"Idanma hakanne Allah an maka uzuri.....da gaske ba
wani abu sabo?,baka kawo kusanci tsakaninku ba?"
"Kaga don Allah malam dakata" Ya fada da husky
voice dinsa
"Na gama gane inda ka dosa gaba daya fa.....na gaya
maka ne abinda yasa na kawo ta cikin gidan nan kenan ko kuwa?,ko bunsuru ne ka
aje?...." Dariya sosai ta qwacewa farouq fiye da dazu,yayi qasa qasa da
muryarsa yana dubansa
"Maganar gaskiya ban yarda dakai ba.....i know you
kaima ka san da wannan......a hadaka da halal dinka gidan da ba kowa saikai da
ita.....kuma kacemin bakayi filling distance din dake tsakaninku ba.....anya
wannan kyan da naga kanayi zakacemin duka a banza yake?". Rasa me zaiyi
masa ya huce yayi,sai kawai hannunsa ya fada kan remote din dake gefansa,ya
shammaceshi ya wurga masa ya sauka a kafadarsa. Duk duniya farouq kadai ke masa
irin haka,yana sake hararasa yana zura hannunsa a aljihu ya fiddo wayaraa
Idanunta
kawai ta ware daga kashingiden da take sanda taji ana knocking na qofar.
Kashingidar da ta yita ne kawai tana tunanin abubuwa masu yawa tare da qoqarin
cudanya abubuwan dake mata kai kawo cikin kwanya. Tunani kala kala ta dinga yi
sanda taji ana knocking din.....shine ya biyota ya sake cin zarafinta ko
kuwa?.....wasu ne suka sake zuwa gidan ko ko yaya?. Daga qarshe da taga bata da
zabi dole ta motsa labbanta tana fadin
"Waye?"
"Nice adda....na shigo please?" Amna tayi tambayar
cikin zaquwa. Kiran adda din da akayi sai ya sosa mata wani miki,mikin kewar
'yan uwanta wadanda su kadai ke kiranta da wannan sunan. Ambatar sunan ya
sakata miqewa ta zauna sosai tana zuro da qafafunta qasa.
"Shigo" Ta amsa kawai kai tsaye ba tare da tasan
waye ba.
"Assalamu alaikummm" Amna ta furta duka tare da
shigowarta cikin dakin cikin murmushi tana riqe da handle din qofar idanunta
akan fuskar sabreen yayin da fuskarta ke qunshe da wadataccen murmushi
"Wa'alaikumussalam" Sabreen ta amsa mata tana mata
duban rashin sani.
"Ma sha Allah" Amna ta furta a sarari tana kasa
dauke idanunta daga kan sabreen,murmushin saman fuskarta kuma ya kasa bacewa.
Dama ta sani......ta sani tabbas hammanta ya iya zabe......tasan hammanta
lallai zai zabo matar da ba irin ta kowa ba,amma bata taba tsammanin iya
zabinsa yakai har kaman haka ba.
"I know.....kece adda sabreen dinmu ko?" Tayi
tambayar da murmushi sosai tana nunata da yatsa idanunta a kanta. Dan shuru
sabreen tayi tana kallonta ba tare data iya amsa mata ba,kwanyarta na mata
lissafin wacece wannan din?. Tana da surutu sosai da alama,amma kuma yanayinta
kadai ya gaya mata me kirki ce.
"Sunana amna hamza kibiya.....nice autarsu hamma
fu'ad". Tayi mata bayani a taqaice saboda ganin yadda take mata kallon
rashin sani. Ta fahimci sarai bayaninta......qanwarsa takeson cewa,kamar ta
basar sai kuma wata zuciyar ta tambayeta
"Meye laifinta ita?" Don bataga wani hali na daban
tattare da ita ba duk da a yanzun ta fara ganinta,amma bahaushe yace alamar
qarfi tana game qiba.
Har amnan
ta sare,sai kuma taga ta saki qaramin murmushi da yayi barazanar dauke hankalin
amnan saboda yadda ya fidda kyawun innocent face dinta
"Qaraso mana" Ta furta tana miqewa tsaye tare da
komawa saman sofa bed". Dukka energy dinta ya dawo,ta tura qofar a nutse
tana ci gaba da murmushi ta tako ciki tana samun wajen zama saman wata sofa din
ta daban
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 19
19
"Am sorry aunty.....hala nayi disturbing naki kina
hutawa" Ta sake fadi tana murmushi. Maida mata martanin murmushin
tayi,wanda har sai da amnan ta furta
"Ya salam,wanne irin kyau ne haka?". Kai ta
girgiza
"Ko kadan....."
"Barka da rana,kin yini lafiya?,ya baqunta?,anni na
miki ban gajiya,munzo mu wuce dake wajen walima......kowa yanaso ya ganki don
jiya baku samu shigowa ba saboda dare ko?" Ta jero dukka abinda ke tafe da
ita da wanda ke ranta kamar ba itace anni ta jawa kunne kada tazo ta cikata da
surutu ba. A iya bayananta kawai ta gane wacece ita.....diyar matar nan da
cikin kalamanta kawai zaka fahimci nutsuwa gami da tarin ilimi a ciki,wannan ya
sanya sabreen sake sakar mata jiki kadan,saidai ta wani bangaren tana tunanin
ta inda zata zamewa zuwa walimar,don sam bata shirya sake shiga kowanne taro
ba. To na meye ma zata yita nuna fuskarta wa danginsu,bayan bawai tazo bane don
ta zauna?.
"Amma walimar......" Sai maganar tata ta katse
saboda daga mata hannu da amna tayi sakamakon shigowar kira,tayi blushing kadan
sannan ta kalli sabreen
"Anni fa ba zama anyi suruka.....ungo nasan kirannan
naki ne". Batason katsewa amna doki da farincikin da take ciki,don haka ta
miqa hannu dole ta karbi wayar
"Idan ba zaki samu daman zuwa ba diyata kada kiji kin
takura.....kiyi zamanki,dama taro ne na sanya albarka,sai a sallami
mutanen". Ji tayi ba zata iya mata haka ba,ba zata iya watsa mata qasa a
ido ba,don haka tace a hankali
"Muna hanya in sha Allah"
"To Allah yayi muku albarka,Allah ya kawoku
lafiya"
"Ameen ameen" Ta amsa tana miqawa amna wayar
idanunta nabin amnan da kallo. Ta fahimci wani farinciki takeji sosai,duk da
batasan na meye ba,ganin amna din sai ya tuna mata da huda dinta,duk da ta
girmi huda,saidai ita kuma ta girmi amna qila sa shekara uku ma ko hudu.
Dole ta
miqe ta soma qoqarin rage yafen jikinta da dankwalin kanta don shiga wanka,ta
lullube jikinta da qaton towel ta wuce tabar amna tana bata labarin sabreen
din,abinda yaso badda bacin rai da takurar zuciyar da take ciki ta shige bayi
da boyayyen murmushi a qasan fuskarta.
Komai na
toilet din na kayan wankan ba irin nata bane,amna tunda ta karanta sunan
products din da brand dinsu tasan harka ce kawai ta girma akayi. Daga yanayin
sulbi da qamshin shower gel din kadai ta sake sallamawa,wannan ya dauketa minti
kusan ashirin sannan ta gama. Towel biyu kawai ta shigo dashi,ta daura
dayan,dayan kuwa dole ta nade kanta dashi saboda sumarta data jiqa da ruwa,ba
wanda zata yafa don suturta jikinta,don haka ta sako shower slipper din zuwa
bakin qofar toilet din ta cireshi saman water proof doormats din dake sashe na
biyu na toilet din ta murda handle din ta bude qofar.
Daidai
lokacin daya soma duba agogo ganin sun sakashi dabi'ar daba tasa ba.....dabi'ar
daya tsana ya kuma ja mata kunne a dazu da kada ta soma aikatata kwata kwata.
Tsaki yaja ya fara lalubar number wayar amna,saidai ya kirata kusan sau uku
bata daga ba,wannan ya sakashi miqewa a fusace yayi ciki yana cewa farouq
"Ina zuwa".
Takawa
kawai yakeyi cikin hallway din ba tare da yasan wanne ne dakinta a ciki ba?.
Haka ya dinga gota bedrooms din a hankali,sai daya isa na qarshe sannan yadan
tsaya cak yana kasa kunne duk yasan bazaiji motsin komai ba saboda yanayin door
din,a jikinsa kawai yaji da mutum a nan,sai ya juya yana fuskantar qofar ya
murdata da dan zafin nama.
Opposite
suke tsakanin qofar toilet din dana shigowa dakin,wannan ya sanya kai tsaye
kowanne idanunsa ya fada kan dan uwansa sanda qofofin suka bude lokaci guda.
Budewar da taja hankalin amna wadda take zaune tana jiran fitowar sabreen.
Sarqewa
idanunsu sukayi lokaci guda......fuskarta tayi fresh sosai,glowing din nan da
fatarta ta qara samu saboda gyaran data samu na musamman ya sake bayyana. Ruwan
da tayi wankan dashi ya sabbaba tarwatsewar qwayoyin ruwan saman fuskarta,sai
suma zame mata tamkar wani ado,musamman sumar gaban kanta data kwanta sosai ta
kuma fito ta qasan towel din daya kimawa kanta don ta samu ya tsotse danshin da
yake jiki. Ta sassannin dogon wuyanta duka wasu daga cikin sumar sun kwanta,sai
suka zamewa wuyan nata kamar wani ado musamman kafadunya dake a tsaye da wani
irin structure me daukan hankali da kuma tudu da zaunawar dukiyar fulaninta
sosai a qirjin.
Duka
cikin qasa da second goma idanunshi suka kai wadannan. Wanda baikai mintunan da
hankali da zuciyarka zasuyi zaton duka wannan karatun za'a iya yinsa a wadannan
taqaitattun mintunan ba. Haduwar idanunsu na farko yayi mata ba zata,don bata
taba kawo bayyanarsa cikin dakin ba,don haka ta maida qofar da wani irin sauri
ta koma baya ta tsaya zuciyarta na wani irin bugawa.
Idanunsa
da yaji sunyi wani irin laushi ya janye daga bakin qofar yana tabe baki
"Kamar gaske" Ya furta qasan zuciyarsa,zuciyar
tasa tana ayyana masa Allah ne kadai yasan adadin mazan da suka ganta a
hakan,tunanin daya sanya wani abu me ciwo ya tsaye masa a wuya. Wai wanne ma
tsautsayin ya kaishi ajiye kayan da suke tamkar na kasuwa cikin gidansa?,zai
iya killaceshi da gaske ya canza masa rayuwar da ta zame masa jini da tsoka?.
"Ba damuta bane......damuwata na koya mata lesson ko
saboda gaba......tasan ba kowanne kalar mutum kake tabawa ka kwana lafiya
ba".
Duban daya
maida kan amna sai yaga itama shi take kalla.......daure fuska yayi tamau
saboda ya karanci abinda ke fuskarta harda wani qunshe dariya
"Karku kuskura ku wuce minti shida.....if not...."
Sai ya nunata da yatsa kawai ba tare da yace komai ba ya juya ya fice yana tura
musu qofar.
"Adda......wallahi hamma ya tsani jira.....nasan kema
kin sani,hurry up adda anni ma jira take" Muryar amna data sanar da ita ya
fita. Wani wawiyar ajiyar zuciya ta saki,a hankali ta saki qofar data
qanqame,sannan tabi hannuwanta da suke rawa da kallo.
Da gaske ta
tsorata,don tunda tazo duniya ba wani muharraminta daya taba ganinta a
haka,wannan shine karon farko. Qoqari tayi ta hade hannayenta waje daya tana
matsasu da kyau,sannan ta bude qofar sosai tana fitowa.
Miqewa
taga amna tanayi
"Bari na baki guri adda ki shirya a nutse....."
"Yi zamanki.....zan shiga dressing room na shirya"
Tace da amna din,don idan ta fita ta barta fitowarta zatayi mata
wahala.....infact ma zata iya canza shawarar zuwan.
Tsaf ta
shirya cikin wata doguwar riga ta atamfa bayan ta gama bulayin neman kayanta na
gida,saidai ko ire irensu bata gani ba,sun lume sun narke cikin uban suturar
dake danqare da closet dinta. Chantilly veil ta yafa daya dace sosai da atamfar
jikin nata.
Ta fito da
wani irin kyau da kai tsaye bahaushe ke cewa qyallin goshin amarci.....saidai
itakam ba days,tsabar gyaran jikin da tasha ne da kuma yadda ado ya zame mata
jiki.
"Tubarkalla ma sha Allah......tabarakarrahman......kiyi
haquri adda inata tankaki.....i can't control my words ne wallahi".
Murmushi kadan ta yiwa amna din,zuwa yanzu sai takejin kamar ta saba da halinta
ne ma,tana da saurin sabo da shiga jikin wanda take so
"Na gode" Ta fadi tana sanyawa qafafunta wasu high
hill wanda kaman an yisu ne dama musamman saboda kayan jikinta. Kamar amna din
ta mata magana amma sai ta bari kada sabreen din taga kama ta fiya rawar kai,a haka suka jero suna
fitowa zuwa parlor din.
Yayi
relaxing sosai cikin kujerar kamar wanda bacci ke shirin dauka,saidai babu ko
guda daya.....wata lafiyayyar kasala ce ta saukar masa tun daga fitowarsa daga
cikin dakin.
"Barka da fitowa sister" Maganar farouq kenan da
taja hankalinsa,ya dauke idonsa daga email din da yake dubawa wanda duka ya
raba hankalinsa gida biyu ne,daya kan ibtila'in faduwar darajar gold da diamond
da suka wayi gari dashi......daya akan saqonninsa wanda kusan duka maganar dai
daya ce,shirye shiryen bude company da yake tunanin jibi zai wuce abuja saboda
baqinsa da yake kyautata zaton zasu fara sauka.
Farat
daya ta gane muryarsa,kaman amna shima sai take kirkinsa ya lullubeta,bawai
murmushi tayi ba,amna ta sassauta fuskarta sosai suna gaisawa.
"Ya kwanan baqunta?"
"Alhamdulillah" Ta amsa masa itama tana rufe
handbag dinta data jefa wayarta a ciki
"Ma sha Allah....Allah ya bada zaman lafiya,ya baki
ikon riqeshi" Yayi maganar yana maida dubansa ga fu'ad. Ko wajensu baya
kalla tun duban farko da yayi musu bayan fitowarsu.
Batace
komai ba sai amna da tayi murmushi me sauti
"Dude.....muje ko?" Farouq ya buqaci hakan
"Kuje kai da amna.....gamu nan fitowa" Ya bashi
amsa bai ko daga kansa ba.
"Alright" Ya amsa masa yana daukan gorar ruwan da
fu'ad din ya fito musu da ita yayi gaba amna na biye dashi.
Shuru ya
shude a falon na kusan mintuna biyu,bata ce kanzil ba kaman yadda shima baice
ta tafasa a sauke ba,kowa yana ji da tashi izzar da girman kan.
Ji tayi ta
dauki iya adadin tsaiwar da zata iya.....ba zata dauki wannan halin nashi sam
sam ba,don haka ta juya ta fara motsawa da zummar barin wajen
"Hey!....Waye ya baki izinin tafiya" Ya fada da
boldness cikin muryarsa. Abun taji ya mata wani iri.......wani baqon abu guda
daya cikin rayuwarta. Batasan namiji yayi mata tsawa ba saidai ma ya
lallasheta......batasan namiji yayi mata umarni ba.....a kullum ita ke basu
umarni.......ba'a keeping dinta ta jira mutum saidai shi yayi jiranta koda
awanni nawa tayi nufin qararwa a wajen.
*DUNIYAT LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 20
20
Tana tsara
komai a sanda takeso a kuma yadda taga dama......kuma a bita a hakan.
"Kina tunanin hatta dressing naki zakici gaba da yinsa
yadda kika saba?......idan nace komai naki zai canza ina nufin komai
din......ciki harda shigar da bata dace ba.....bata kuma yi ba,ki kalli
amna.....kin ganta da irin wannan useless mayafin?". Iska sosai ta shaqa
har cikin ranta tana jin wani zafi.....abinda yakeyi matan wasu abubuwa ne da
babu d'a namijin da ya taba yi mata shi sai shi. Sai taji haqurinta ya gaza
jurewa......don haka cikin muryarta me nuna bacin rai tace
"Kana zaton baiwa ce daka shiga kasuwa ka
siyo?......meye alaqarka da dressing dina?". Maganar tata ta sakashi gyara
zamansa sosai. Yadan jijjiga kai
"Kin shirya wasan kenan kema?.....musu?,taurin
kai.....abubuwa biyu da nafi tsana a rayuwata" Yayi maganar yana kada
yatsunsa guda biyu idanunshi akanta duk da baya iya ganin fuskarta
"Bauta.....meye marabar dambe da fada?.....kina tunanin
kudin da kika sacemin kimar kudin aurenki sunkai yawan haka?......banajin
kinkai tsada haka.....well,ba wannan ba,ki shiga ki sauke wannan banzan mayafin
ki saka sutura sosai a jikinki......karki bari na maimaita maganata......i hate
it". Cak maganan ta tsaye mata a rai,wani irin bacin rai ya taso mata.
Wannan ya sanya da sauri sauri ta fara yin gaba,don tanaji muddin taci gaba da
tsaiwa a wajen zai iya gano lagon fushinta,abinda kuma taci alwashin ba zata
taba bashi dama a kai ba.
Ci gaba da
birkita closet din tayi bangaren veils cikin bacin rai,gaba daya veils din taji
basu yi mata ba,sai kawai tahau tube kayan,ta kwabesu tas ta fara neman wasu
daban.
Turkey
dress hannunta ya fada kai,cikin shigar da tafi so kenan,sai ta fara shirya
kanta cikin turkey abaya din wadda cikin qanqanin lokaci ta rufe mata jikinta
ruf,ta kuma fiddo da kyakkyawar baby face dintannan.
Haka
kawai sai taji tafijin dadin shigar,duk da dama tun asali ita din bata iya
shigar bayyanar da tsiraici ba.....kawai dai Chantilly veil yana cikin veils
din da tafi so,kuma ko a yanzun ba zata bari ya rabata dashi ba.
Motsin
tahowarta ya sakashi daga kansa a nutse. Duba daya yayi mata ya kauda
kanshi,sai ya miqe yana ficewa tun kafin ta qaraso.
"Ya Allah......wai BB don Allah a ina hamma ya samo
adda?" Amna data kasa daurewa sanda ta hangi sabreen na takowa zuwa inda
motoci ke jiransu ta fada. Iya takunta kawai saika dauka rausaya ko kuma yanga
takeyi ta cikin hill shoes din data sakawa qafafunta masu igiya.
"BB.....wai dama hamma shima yana kallon 'yammata don
Allah?". Boye dariyarsa farouq yayi,don sarai yaga isowar fu'ad wajen amma
bai nunawa amna ba
"Me yasa kika ce haka?"
"To ai......hamma fa kaman horror yake......ina
noticing nasa duka shekarun nan,Allah saiki wuce ta gabansa amma baisan wacece
ke ba......to amma ya akayi idanunsa suka kai kan addana me mugun kyau
haka?"
"Yaushe kika zama gulmammiya amna?" Farouq daya
kece da dariya ya fada yana satar kallon fu'ad dake tsaye kawai ya kasa cewa
komai. Dariyan itama takeyi
"Allah BB......ban taba ganin mutumin daya iya zaben
mace ba irin hammana......da gaske hamma ya hadu tako ina,komai nasa ya
banbanta dana kowa" Ta fadi hankalinta kwance batasan yana a wajen ba.
Zabura ta
danyi da jin gyaran muryarsa,tsaf ta dinke bakinta tana raba idanu
"A nan za'ayi walimar ne?" Ya fada yana jifan
farouq da wani irin kallo na zaka sani ne. Dariyarsa ya yiwa control yana fadin
"No.....aike muke jira,ko ka manta kaika koromu waje
zakayi ganawar sirri da madam"
"Enough" Ya fada yana tura masa murfin motar kaman
zai bugeshi cikin nuna alamun ka soma wuce gona da iri. Hakan shi yayi masa,don
haka yaja murfin ya rufe yana gaya masa shi da amna zasu tafi a nan.
Baibi ta
kansa ba ya nufi ainihin motarsa qirar Mercedes Benz G400d baqa wul daketa
daukan idanu wanda haka ke nuna
sabuntarta da kuma kalar kulawar da take samu.
Da sauri
daya daga cikinsu ya bude masa,kai tsaye ya wuce ya zauna sosai idanunsa na
sauka a kanta. Ya tsani jira sosai,baisan me yasa take tafiya kaman ba zata
qaraso wajen ba,bayan ya tabbatar taga inda ya shiga.
_wataqila da wannan take sake samun damar yaudarar maza_
tunanin daya d'arsa masa a rai kenan,wanda ya sake sanya mishi qyamarta
ainun,har yakejin kamar ma bazai iya hada numfashi da ita cikin mota guda ba.
Ba zata
bari ba ba kuma zata sake tayi wani abu na zubewar kimarta da mutuncinta gaban
guards dinsa ba,wanda dukkaninsu haushinsu takeji. Bataga meye dalilin da zai
zube qatti irin wadannan suna kewaye dashi ba kamar tsohon barawo ko wanda yaci
kayan wani ba(a iya nata sanin na iya tsaron daya zama dole me harka irin nashi
ace ya samu),me yasa bazaiyi rayuwa normal irin ta mutane ba?,da wannan kalar
tasa rayuwar kenan itama yakeso ya tursasata ta zama haka?,tayi rayuwa irin
nashi?,bazai yiwu ba kuwa.
Daidaita
zamanta tayi sannan aka maida murfin motar aka rufe mata,sai motar ta dauki
shuru sai sassanyan qamshinsa daya danne nata,har ya zamana duk wani numfashi
da zata shaqa tare da qamshin nasa yake zuwar mata hunhunta. Tsaki ta saki a
boye yadda bazai ji ba,ta maida kanta daya window din da take zaune daura
dashi. Batasan sun fara tafiya ba sai da taga motar ta fara sulalawa tana nufar
makeken gate din gidan suna gilma shukokin da aka qawata wajen dasu.
Basuyi
nisa ba kira ya shigo masa,wanda shi ya zame masa abokin tafiya. Duka
maganganun cikin harshen turanci yake yinsu da wani irin accent dake nuna
zallar qwarewa gami da gogewa a yaren. Kusan fin rabin maganganun nasa ba wani
fahimtarsu takeyi ba,don zuciyarta tayi nisa da wani tunani na daban. Ta wani
bangaren kuma yadda yake lanqwasa harshensa ba kowanne word take ganewa ba a
matsayin karatunta na wadda ya dakata daga aji biyar biyu na babbar secondary
wato senior secondary school.
Sanda
motarsu ke qoqarin cusa kai ta cikin babbar gate din dake da wani irin girma da
kuma jan hankali,a sannan ne ya katse wayar ba kuma don ya gama ba. Ya kashe
wayar gaba daya tana kallonsa ta gefen idanu,ya zurata cikin wani dan abu daya
matsa ya fito ya saka wayar ya koma ciki. Adan qaramin zamansu na mintuna ta
karanci abubuwa daban daban tattare dashi,kusan kaman komai nasa na dabanne
kuma daban yake,saita tabe baki sanda suka isa babban parking lot na alfarma da
gidan ya mallaka.
Qasa
tayi da kanta tana jan mayafin data lullube kanta dashi sanda take hangar wasu
mata suna bullowa daga wata qofa da tafi kusa da parking lot din,kafin takai
gayin komai amna ta bayyana ta kama murfin tana budewa,abinda ya bata daman jin
maganganunsu. Muryar amna ta fara ji
"Inna uwaisha......ga addan namu.......ku fito mana da
ita a hankali" Ta qarasa fada tana qaramar dariyar dake nuna zallar
farincikinta
"Kinyi qoqari auta sannu.......kin gama naki"
Wadda aka kira da uwaisha ta fadi tana matsowa gaban motar
"Kamar gaske" Sautin muryarsa ta fita a hankali ya
furta sanda kan sabreen ke qasa tana jin wani fargaba haka kawai na haduwa da
mutanen da batasan su kuma meye nasu kalar halin ba,sunan auta da taji an
ambata sai ya sanya duka tsigar jikinta ya tashi,haneefa da tun da safe take
kokawa da tunaninta ta fado mata.....ko yaya ta wuni?.
"Zallar karamci da girmamawa da mutuntawa muke gabatar
miki" Abinda inna uwaisha ta fada kenan kamar tasan abinda sabreen ke
wassafawa qasan zuciyarta. Miqa mata hannu inna uwaishan tayi tana fadin
"Sauko a hankali nayi miki jagora zuwa ciki,ki shirya
don kowa na dokin jiranki". Bata musa ba ta sakawa inna uwaishan hannunta
"Fatabarakallahu ahsanul kaliqeeen......da iya lallen
nan ma kawai an tashi kaina yallabai". Inna uwaishan ta fada tana dariya
dariya idanunta akan muhammad fu'ad dake qoqarin ficewa a motar sannan ta maida
dubanta ga amna data dage mata gira alamun Yes.
Inna
uwaisha na daya daga cikin makusantan anni da suka daukeshi tamkar d'a,duk da
cewa tana da jika qwaya daya amma idan kaga suna raha da amna saika dauka yaya
ce da qanwarta,hakanan suma ta daukesu duka mazan gidan. Bai iya cewa komai
ba,sai dan motsawa da labbansa sukayi alamun murmushin dole kawai ya sanya
qafafunsa ya fice daga motar.
Kunnuwanta
kawai ke iya jin surutansu amma idanunta suna a rufe. Batasan ina suke nufa ba
saidai idanunta na iya kallon lullubabban luxury marbles din dake shimfide a
wasu sassan na gidan,a haka taji sun isa wani daki da a nan inna uwaisha tace
da ita
"Fell free sabreen.....ki shirya amna zata tsaya
dake,idan kun kammala zan dawo mu wuce wajen taron,kowa ke yake jira". Kai
ta gyada a hankali,cikin ranta kuma tana zancan zucin wanne shirin kuma zata
sakeyi bayan na jikinta.
Sanda
amna ta gabatar mata da komai na shirin shuru kawai tayi tana bin kayan da
kallo......shin da saninsu wanne irin aure ne akayi suke wahal da kansu haka da
kashe kudade da hidima?,ko kuwa kallo kawai sukewa abun irin duban bangon
littafi ga idanuwan da basusan meye a cikinsa ba. Wata lafiyayyar Moroccan gown
dake da wani irin ado na daukan hankali......saidai kuma duk da adonnan nata
sam bata da nauyi ko kadan. Hade take da wani irin hijab dan qarami da yafi
mata kama da na Indonesia ko Malaysia.....a ciki batasan wanne ne ba. Komai na
kayan fari ne qal da wani irin haske me daukan hankali. Ita kanta bayan ta gama
shiryawa batasan lokacin data dauka tana kallon kanta ba,sai take ganin kamar
ba ita ba.....duk da kusan komai ma yana zuwa mata ne da wani irin ba zata da
bata taba zato ko kawowa cikin rayuwarta ba.
Amna ce
ta fara shigowa wadda fiye da dazun a yanzunma ta susuce wajen yabawa sabreen
din.
"Inna Allah kwanan nan hamma zai manta da wani gold da
Diamond"
"Maza dai ya jiki" Inna uwaisha ta fada tana riqe
hannun sabreen suna nufar qofar fita.
Suna
shiga wajen tasan sun iso,duk da kusan kowa na zaune a nutse ana sauraren
jawabi daga bakin malamai.
"Muna yiwa amarya barka da shigowa". Maganar data
dauki amsa kuwa cikin hall din,ta kuma bawa maamah damar fara gyarawa tsaf don
bayyanar da kanta a wajen.
Ringing biyu
wayar tayi ya daga yana sakata a kunnensa
"Ya kamata ka qaraso wajen walimar fa.....akwai mutanen
da zaku gaisa dasu"
"Bana kusa"
"Kaman yaya?" Farouq ya tambayeshi a mamakance
"Eh.....kaman yadda kaji bana kusa,uzuri ya kamani
nadan fita"
"Why.....you know......"
"Anni zata fahimceni idanma kai baka fahimta ba.....sai
na dawo" Ya amsa masa yana katse wayar ya maidata ya ajiye. Shi a yanzun
kasuwancinsa shine abinda yafi damunsa shine kuma gaba da komai,bai takurawa
kowa ya matsawa kowa ba,don hatta da saddiq daya Kamata ace a yanxun suna tare
suna duba al'amuran da suka taso musu bai masa magana ba,bai kuma ce komai
dashi ba saboda yaga ya sanya kanshi cikin hidimar bikin sosai,ya bashi lokaci
ya qare ya dawo hayyacinsa.....tafiya ce dai dasu tsakanin jibi da gata,kuma
bazai dage masa qafa ba dole ya shirya su wuce. Girgiza kai kawai farouq din
yayi,halin fu'ad saishi,baisan ma yaushe ya fita din ba bayan sun shigo cikin
gidan tare. Ya sanshi sarai ya kuma sani,wani irin mutum ne shi da kasuwancinsa
ke gaba da komai idan ka dauke shi anni abba da su saddiq,amma koma meye yana
ji a jikinsa,yana Kuma fatan duk yadda yakai ga gujewa auren da bashi wani
rashin muhimmanci ya zame masa silar shiryuwa da saituwa kaman kowanne
magidanci.
A nutse
farouq ya ratso cikin mutane ya yiwa anni rada. Kai kawai ta gyada sanda
idanunta suke kan sabreen dake zaune waje daya bata ko qwaqwaqwaran motsi. A
iya haka tana iya hangen nutsuwa a tare da ita,sannan haka kawai takejin qaunar
yarinyar cikin ranta.
Tana iya
hangen wasu abubuwan ta cikin mayafin dake lullube saman kanta,a sanda walima
tayi nisa..... Kai kawo na mutane ya qara yawa tata zuciyar cike take da
lissafe lissafe kala kala. Lumshe idonta tayi sanda aka fara gabatar da miqa
gudunmawa ga amarya,wato kowa zaizo ya zube mata tasa gudunmawar adan wani
babban qwarya dake ajiye a gabanta maimakon yin liqi,wanda daga nan za'a fara
gabatar da lectures akan zaman aure. Numfashi ta sauke daga can cikin
hunhunta,duk cika da batsewar mutanen dake a wajen bata hangi wani nata ko
mutum daya ba. Sai takejinta bare a wajen da wani irin rashin sukuni da takura.
*DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 21
21
A nutse aka
fara zuwa daya bayan daya ana zube sabbin 'yan dubu dubun fil a miqe cikin
bundles dinsu a gabanta. Ta rasa tsakanin burgewa da rashinsa wanne takeji
cikin zuciyarta?,duk da ta hangi tarin nutsuwa da kamala a komai na taron.
Idanunta
ta sake dagawa a hankali ta cikin mayafin tana kallon bakin qofar shigowa gurin
dake facing dinta......tamkar abinda ake jira kenan saita hangi huda na
shigowa. Da farko ta dauka kaman gizo idanuwanta sukeyi mata ko kuma me kama da
ita ne,saidai shigowar nadra da haneefa ya qarasa kore mata dukka shakkun data
soma ji cikin ranta. Wannan bai saketa ba taga abinda ya kusa doka zuciyarta
saboda firgici.....maamah ce.......tana biye dasu da dukkan alamun da zasu
gwada maka tare suke......tare suka shigo,don waiwayawa haneefa tayi da alama
kiran sunanta tayi,sai taga ta riqe hannunta haneefa na mata murmushi tana
maida mata sukaci gaba da takowa wajen tare.
"A ina ta gansu?,a ina ta daukosu?,ya akayi taje ko
sukazo wajenta?,tun yaushe?,me kuma take gaya musu?" Tayi tambayar sanda
taga ta tsaidasu duka su ukun kuma kowacce ta tattara mata hankalinta.
Sanye take
cikin wata 'yar ubansun super embellished me asalin tsadar da jikinta ke bada
wani irin santsi tamkar ba atamfa ba. Tun daga yanayin shigar zaka tabbatar da
gaske ta dauki duniyarta dama rayuwarta gaba daya.....hakanan da gaske komanta
yana mata dadi yana kuma tafi mata yadda takeso. Daga bayanta hajja harira ce
data shirya kanta itama cikin applique lace ruwan sararin samaniya. Ita dinma
duba daya zakayi mata ka tabbatar da halin yazo daya kamar yadda abotar tazo
daya.
Kai
tsaye ta daga yatsa tayi musu nuni da kujerar da sabreen ke zaune a kai,sai
dukkaninsu suka maida idanuwansu kanta. Fuskokinsu suka cika da farinciki duk
da basa iya ganin fuskarta sosai,suka motsa kamar zasu taho zuwa wajenta,amma
sai taga ta sunkuya tana magana dasu. Cikin qasa da second talatin taga sun
maida hankalinsu gareta.......sun kuma juya suna binta a baya zuwa hanyar data
nufa,daidai lokacin da me gabatarwa ke bada sanarwar
"Mahaifiyar ango ta shigo......uwarsa kuma zata
marabceta" Maganar data finciko hankalin sabreen daga shingen tunanin data
afka sanda take binsu da kallo suna biye da maamah sau da qafa.....kai kace
ummeensu ce ta dawo duniya.
"Uwa?.....mahaifiya?,wacece?" Ta samu kanta da
shiga wannan rudanin tare da fatar a yau ta samu warwarewarsa,don haka ta buda
dukka idanunta tana bin kowanne kusurwa da kallo tanason samun warwarar
rudaninta.
Cikin
nutsuwa da girmamawa anni ta miqe tana dosar inda maamah ke a tsaye,fuskar
annin shimfide da fara'ar data ratsa har qasan zuciyarta. Har yanzu gangar
jikinta da ruhinta basu daina jin farinciki da alfaharin aurar da fu'ad
ba......wani abu guda daya daya zamewa maamah tamkar dafi tsakiyar tsokar
zuciyarta
"Ameenatu ce ta aurar dashi" Kalmar da inda tana
da ikon gogeta tsaf saita gogeta daga dukkan wata ma'adana ta kalamai.
"Barka da zuwa......sannunku da zuwa......"
"Uwa kuma mahaifiyar muhammad fu'ad jadda ba,ai haka ya
kamata ne gabatarwarki ta fadi" Hajja harira dake tsaye gefan hannun hagun
maamah ta furta da wata irin izza.
Kallo
daya anni tayi mata ta watsar da ita gami da bawa banza ajiyarta,idanunta suna
sauka akan fuskar 'yammatan su uku da take ganin tamkar ta taba ganin fuskar a
wani waje. Kallonsu kawai tayi suka fara gaidata daya bayan daya,ta amsa musu
tana dafa kan kowaccensu da madaukakiyar fara'a da kuma kulawa,kulawar da ta
sauka har cikin idanun sabreen wadda ruhinta gaba daya yana a wajen,saidai
babban qalubalenta bata iya jin me aka tattaunawa akai.
Tun daga
tashin anni har tsaiwarta a wajen sabreen na tuna guraren data taba ganin
fuskar matar ne. Indai da gaske itace anni......itace uwa ga fu'ad ba shakka ta
santa......amma ta yaya haka ta kasance?,ya akayi yake da uwaye biyu?,me yasa
anni data taba sani duk da alkhairi ya hadasu ba ita ta nema masa ita ba?,sai
waccar baquwar fuskar da bata taba ganinta ba kafin faruwar wannan abun kaf
tsahon rayuwarta?.
"Barkanki kade Ameenatu.......sannunki da hidima"
Maamah ta maida mata da wani irin salon murmushin da ya sanya anni tajishi har
cikin jinin jikinta.
"Ina tayaki murnar aurar da fu'ad da kika samu damar
yi......wannan babbar dama ce da zata zame miki tarihi kuma abun tunawa watan
watarana.......ina aka tanadarwa mahaifiyar fu'ad domin ta zauna ita da qannen
matarsa?" Tayi tambayar kai tsaye cikin isa......
"Ai albarkacin kaza qadangare kansha ruwan kasko
mariya....muhalli har sai kin baiwa wani" Anni ta fadi duk da rabin
hankalinta yana kan yaran abubuwa masu yawa suna yawo a ranta. Waiwaya tayi ta
yafito muhsina inna uwaisha dake shirin wucewa
"Itace mariya.......a cikata da irin karamcin nan da
aka gada,koda zata cika hall dinnan da jama'arta.....a tabbatar an gamsar da
buqatarsu,a nuna mata dattako da dattijantaka" Dukka anni tayi maganganun
da kai da bakasan komai ba zaka dauka zallar magana ce kai tsaye,saidai gasu
hajja da maamah din dukkaninsu sunsan magana ce akayi musu me harshen damo.
Juyawa abinta anni tayi tana komawa cikin jama'arta,maamah tabi bayanta da
kallo tana jin zafin jirwayen datayi musu me kama da wanka. Zafafan baqaqen
maganganun data fahimci kowaccensu,amma kuma saiga murmushi yana subucewa daga
saman fuskarta
"Kwanaki kadan suka ragewa izzarki ameenatu.....na
rantse koda pant din dake jikinki da kudin muhammadu aka siyeshi saikin zareshi
kin miqomin.......na rantse sai na sanya fu'ad ya gaya miki maganganun da
zasuyi silar ajalinki......maganganun da zasu zame miki dafin da zuciyarki zata
buga ta tarwatse pieces " Tayi dukka maganganun ita da zuciyarta tana me
cike da alwashi.
Duk da
wadannan abubuwan data samu ta kuma aiwatar zuciyarta ta kasa samun nutsuwa ko
qanqani.......sam farincikinta har yanzu rabi ne......daga sanda ta iso bakin
qofar mansion House din Alhaji hamza kibiya duka sai taji ta raina nata gidan
kwata kwata. Batajin akwai wani gida ko gini da fu'ad zaiyi mata komai kyau da
dukiyar da aka narkar ya zauna mata a rai muddin zai zamana muhallin Alhaji
hamza kibiya yafi nata......indai zai zamana matsugunnin ameenatu zai d'ara
nata.
Daina
fahimtar komai tayi......daina fuskantar duk abinda ake gudanarwa tayi,dukka
idanunta dama hankalinta suna kan 'yan uwanta,suna kan kowanne motsi da kai
kawo nasu. Hankalinta taji yana tashi,bata qaunar kowacce mu'amala ko alaqa
kome qanqantarta tsakanin maamah dasu,saidai yadda taga tana jansu a jiki,ta
wani.mugun sake musu ko ita batajin ta sake musu haka. Haneefa duk girmanta
tana saman cinyarta tana wani lallabata,irin lelen da haneefa din keso a
matsayinta na auta take kuma qishirwarsa.
Cafko
hannun amna tayi wadda ta zuge tata jakar ta fara fiddo sabbin 'yan dubu dubu
kaman ba'asan ciwo da zafinsu ba.....kamar ba wasu abu masu muhimmanci ba tana
zubewa sabreen din.
"Kiramin su nadra.....kice suzo yanzu yanzu
injini". Dubanta amna tayi duk da bata iya ganin fuskarta sosai.
"Su waye?" Ta tambayeta don bata gane ba. Ajiyar
zuciya ta sauke tana qoqarin saita kanta,sai sannan ta tuna amna din bata sansu
ba
"Sun shigo yanzu su da......." Ta dakata tanason
tuna sunan da ake kiranta dashi
"Su da maamah" Kai amna ta daga tana hangensu daga
nan inda take,kwata kwata bata qaunar abinda zai hadata da matar,bata qaunar
kallon da take binta dashi irin kallon dake fita daga idanuwanta zuwa
kanta,amma zuwa aiken sabreen ya zame mata dole
"Okay" Tace da ita
"Na gode" Sabreen ta fadi da sauri saboda jin
dadin zatayi mata abinda takeso a sanda bata da damar tashi.
Da ido take
bin amna sanda take nufarsu,duk wani taku dake qara kusancin ama dasu bugun
zuciyarta qaruwa yakeyi,ta kasa dauke idonta daga kansu daidai da second guda
har zuwa sanda ta qarasa gabansu. Taga amna ta mata magana,ita kuma ta waiwaya
tayi magana dasu kafin ta sake dubanta still ta gaya mata wani abu daya sanya
amna din juyowa ta dawo mata.
"Me suka ce?" Ta fara da tambayar amna din tun
bata gaya mata komai ba
"Zasu zo.....zasu taho tare da maamah din wai".
Idanunta ta maida ta lumshe tana girgizawa amna kai kawai. Wani irin rikitaccen
yanayi yana sauko mata,kada dai ace suna jin wani sauyi na daban akan maamah
kamar yadda takejin wajabcin bin umarninta tako ina yana ratsata?.
Tun daga
wannan sa'ar nutsuwa tayi mata qaura,ta kasa debe idanunta daga kan 'yan uwan
nata,duk wani motsi murmushi da kuma fara'ar fuskarsu ya tabbatar mata suna
jinsu ne cikin sukuni da farinciki,har zuwa lokacin da aka bada sanarwar isowar
mahaifiyar ango zuwa inda surukarta take.
Tamkar
mejin tsoron wani abu haka zuciyarta taci gaba da bugawa sanda maamah ke
kusantota tana takowa wajenta dasu nadra gaba daya. Idonta ta lumshe da sake
budesu akansu gaba dayansu tana me kyautata zaton saisun iso gareta ne kai
tsaye kafin aiwatar da komai......saidai kuma akasin haka ne ya faru. Kamar
kowa suma wajen zuba kudin suka nufa,kowacce ta dire rafas na dubu dubu sabbi
guda uku dake hannunsu huda kuma ta zuba biyar. Bin kudin tayi da kallo,suka
kuma tsaye mata a rai.
"Wai ina momma bahijja?" Tambayar da bata da
amsarta batasan kuma wanda zai gaya mata amsar ba. Ta tabbatar daga kansu har
zuwa momma ba wanda zai basu wannan kudaden son suzo su zuba a
wajen.....amsarta ta fito sanda maamah ta cire wani rafas din ta bawa nadra da
zummar ta qara a ciki.
"To kuje ku gaisa" Maamah ta basu umarni sanda ta
fara zube nata kudaden da suka ja hankalin mutane da dama.
"Waye ya kawoku?, yaushe kukazo?,ina momma?" Ta
damqe hannun nadra da tafi kusa da ita tana jera musu tambayar a gaggauce daya
bayan daya.
"Momma ta tafi yau....tun da safen mukazo,mun dawo
gidan maamah......"
"Tana da kirki adda.....kuma tace kema kina nan,zamuci
gaba da ganinki.....kayanmu ma tace basai mun taho dasu ba......kawu yace muyi
zamanmu zamufi samun kulawa".
"Baki da hankali huda?" Ta fada da sauti me qarfi
tana qoqarin janye lullubinta don ta samu damar saka idanunta cikin na huda.
"Yi a hankali......idanun jamaa suna kanki" Maamah
data sunkuya saman kanta tana maida mata lullubinta ta fada da murmushi akan
fuskarta kamar wani abun arziqi take gaya mata.
"Ku tafi mu zauna daughters" Ta fada da kulawa
sosai a muryarta da cikakkiyar fara'a.
Tana jin
takunsu sanda suke sauka a wajen,ba damuwa ko wani abu cikin muryoyinsu,tana
jin tafiyar nasu na buga zuciyarta sosai,tanaso qwalla ta fita daga idanunta
komai qanqantarta ko zataji sanyi,amma ko daya bata samu wannan damar ba.
Koda aka
kirayi anni saita aike amna da wani qaramin akwati da ba wanda yasan meye a
ciki aka ajiye cikin wani salo na siyan girma.
*DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 22
22
Kafin a
tashi tsaf ta rasa sauran nutsuwarta,wani irin tashin hankali takeji maras
misali daga kowanne lungu da sashe na zuciyarta. Ba abinda ke gilmawa ta idanu
da zuciyarta sai huda nadra da haneefa......ina momma bahijja?.....ina momma
bahijja?,.....da gaske ne sun bawa maamah yaran?,ya akayi haka ta kasance?,ya
akayi ta tafi ba tare da sunyi sallama?,ya akayi ta tafi ta barsu bata cika
mata alqawarin data dauka akan 'yan uwanta ba?......zata sakene ta kalli
rayuwarsu ta balbalce?,ko xatayi dukkan abinda ya kama tayi don ta tseratar da
rayuwar yaran?. Wadannan sune tambayoyin da ta dinga yiwa kanta har a sanda
take cikin kebantaccen qaramin parlor din da amna ta kawota bayan tashi daga
taron,tace ta zauna zasu gana da anni.
Dogayen
yatsunta da suka sha lalle kawai take murzawa kanta a qasa,zuciyarta na wani
irin zafi tare da jin qaguwar su koma gida ta lalubi maamah suyi magana ta
sosai da ita.....koda tana jin kamar ta samu ikon sarrafa zuciyarta da bin
umarninta cikin wani irin takura da takeji ana yiwa zuciyarta,.....to amma sam
bata samu lago akan abinda takeji a zuciyarta game da 'yan uwanta. Qaunarsu
darajarsu martabarsu da kuma soyayya da shaquwar data ginu tsakaninsu ba abinda
ya sauya.
"Assalamu alaikum" Muryar anni ta ratsa falon tana
murza qofar ta shigo
"Wa'alaikumussalam" Tada daga kanta kadan tana
duban qofar gami da amsa sallamar. Kallon kallo suka yiwa junansu,kowanne a
cikin su yanason tuna inda yasan fuskar dan uwansa. Sabreen ce tayi saurin
watsar da qoqarin lalubo inda tasan fuskar annin,saboda gaba daya hankalinta
ba'a nan yake ba,sai ta samu kanta kawai da zamewa daga saman kujerar tana
gaidata,wata dabi'a data manta rabon data aikatata,amma a yau ta samu kanta da
yin saboda wani kwarjini da taji matar tayi mata.
"Koma ki zauna abinki daughter" Ta fada da kulawa
amma saita kasa hakan,saita samu kanta da zama sosai tana tanqwashe qafafunta.
"Na tsaidaki ko?,ga dare yana qara yi,duk da me babban
sunan bai qaraso ba,uzuri ya taso masa daya saka dole ya fita" Kai ta
sakeyin qasa dashi ba tare da tace mata komai ba,batasan me yasa matar take
mata kwarjini haka sosai ba.
"Bari muyi magana a taqaice a gaggauce......da farko
ina miki maraba da shigowa cikinmu da kikayi,ina fatan Allah yasa ku zama
abokan arziqin junanku.....Allah ya hada hankalinku waje daya......bani bace
mahaifiyar fuad,amma idan na kira kaina uwa a gareshi nasan banyi laifi ba,ni
din uwar riqonsa ce tun daga quruciyarsa har kawo yau.....hajiya mariya wato
maamah itace mahaifiyarsa". Dole bata shirya ba maganar ta sakata daga kai
da hanzari ta dubi anni,sai kuma ta maida ta sunkuyar
"Baiyi sa'ar uwa ba.....ke kuma bakiyi sa'ar d'an riqo
ba" Abinda ta fadi kenan qasan zuciyarta tana jin kamar a tsakaninsu annin
ta fita daban. Anya ba halinsa Allah ya duba ba ya hadashi da uwa daidai da
halinsa?. Zaren tunaninta ya katse sanda anni ke magana
"Yana da kirki.....yana karamci,yana da tausayi yana da
tausasawa amma fa.......ga mutumin daya fahimceshi. Bashi da sauqi ya fiya
tsauri,bashi da tausayi ga wanda bai fahimci shi waye ba,bayason
qarya.....bayason saba alqawari,bayason yaudara baya son ha'inci......sannan
uwa uba baya daukar raini. Abu na gaba muddin zakayi wasa da addini taku ba
zata taba zuwa daya ba.....muddin ba zaka kasance karimi kamar yadda yake ba ba
zasu taba daina sabani ba,wadannan sune kadan daga halayensa.......ameenatu"
Ta kirata da sunanta na ainihi,abinda ya motsa zuciyar sabreen kenan sosai
"Ban gaya miki duka halayensa ba don na tursasaki kula
da yarona.....na gaya miki ne don na sauqaqa miki qofofin zama dashi....na gaya
miki ne don kiyi hanzarin mamaye zuciyarsa......na kuma gaya miki ne don na
rage miki wahalar fuskantarsa......naso ace na samu zama da wasu mutane mafi
kusanci dake don na tambayi naki halayyar na isar masa dasu a
shimfide.....domin cikar mafarkina shine......gidan muhammadu yafi gidan
dukkanin wani magidance zama aljannar DUNIYA......gidansa ya zame masa kaffara
akan kowanne abu daya fuskanta a rayuwarsa a baya" Anni ta qarashe maganar
har tsakiyar zuciyarta tana fatan mafarkinta ya tabbata. Miqa hannu tayi a
nutse ta kamo hannun sabreen ta sanya cikin nata
"Idan har zaki bashi dukkanin kulawa......idan har xaki
nuna masa zallar soyayya irin soyayyar da uwar kewa danta.....idan har zaki
kasance me addini tsafta da kwalliya.....xaki kula da abincin muhammadu tabbas
kin gama samunsa a tafin hannunki......yana cikin yunwar soyayya da
kulawa.....muddin ya samu isashiya da zata qosar dashi babu ko haufi kin gama
mallakar zuciyarsa dama rayuwarsa gaba daya".
Ta
saurara ta kuma fahimci duka zantukan annin,saidai cikin nata zuciyar wani
magana takeyi na daban
"Inama ace zaki fahimci waye danki sani na zahiri ba
fuska biyunsa ba......inama wata daban kike budewa sirrikansa wadda ta shirya
xama dashi ba SABREEN me zaman wucin gadi ba".
Dole ta
sanyashi kashe duka wayoyinsa tun a hanya a sanda abdussabur yake tuqashi zuwa
gidan anni.
A cikin
jikinsa da zuciyarsa yakejin wata irin galabaita da bai taba jin irinta ba
saboda zurfafa da tunanin da yayi. Yana da kyau yaci gaba da tafiya a gabar da
yake na sanya idanu akan kowanne motsi da abinda dukka yake da alaqa da maamah.
A zarginsa me girma da qarfi ya sake hawa kan yarinyar.......ya sake samun
gamsuwa da cewa akwai shirin daya shigo da ita gidan,tunda har qarfin alaqarsu
yakai girman da zata kebanceta da wata number wayar ta daban wadda shi kansa
baisan da ita ba. Wunin yau gaba daya fiye da rabin tunaninsa yau duka ya tafi
ne akan hakan.
Bazaice
maamah maqiyayarsa ce ba.....hakanan bazaice bata sonshi ba,amma ta fifita kudi
dukiya da abun duniya sama da tasu soyayyar.......kusan yayi mata fari kuma
cikakken sanin da dan adam kan iya yiwa zanen tafin hannunsa koma
fuskarsa......bazaiyi wasa da rayuwarsa ba.....hakanan bazai barwa maamah
kowacce irin dama ba.....hakanan zai saka yarinyar a wasan da zata qara
fahimtar batasan komai ba cikin duniya.....zai dafata da ruwa da kuma jinin
jikinta.
Yayi
sallama ya shiga parlor dinne a sanda anni ke miqa mata wata irin takarda me
daukan idanu dake qunshe da littatafai na addu'o'i
"Akwai tsaftatattun addu'o'in mallakar miji a
ciki,wadanda basu da wani aibu illa ko shirka a ciki,saidai suna matuqar tasiri
wajen kama miki zuciyar mijinki a gareki" Ko alamun fa'ida bataji cikin
bayanin anni ba......wannan mallkar da take fadi inda zata yiwu ta bawa maamah
ita ta mallaki dan nata kamar yadda tace,ita kuma ta sakar mata 'yan uwa tabbas
shine zatafi farinciki.
Yana zaune
yana sauraren anni tana jaddada mata
"Ki raqe addu'a da kyau.....a yanzun kece garkuwan
mijinki,garkuwar gidanki ma gaba daya"
Baki ya tabe yana siririn tsaki qasan ransa. Inda anni tasan wacece ita
tabbas da bata wahalar da kanta wajen mata wannan dogon jawabin ba,da tayi
saving energy dinta kawai saboda gaba,a sanda zata fahimci wala'alla ko
haruffan baqin dake cikin littafin ba zata iya hadawa ba ballantana ta
karanta,don shi kam daidai da karatun sallarta bashi da tabbaci akai,don ya sani
cewa Allah ya fada cikin qur'ani me girma
_haqiqa sallah tana hana alfasha da duk wani nau'in abunqi_.
Ya tabbatar da nutsatsiya kuma cikkiyar sallah takeyi bata yadda za'ayi ta kasa
rabuwa da dabi'ar karuwanci da bin maza.
Ko a motar
kamar ba wanda yasan da zaman juna. Kusan nasa tunanin ma na tafiyar dake
gabansa ne daga yanzu zuwa kowanne lokaci,yayin da nata tunanin ya.lula duniyar
yadda zata fidda 'yan uwanta daga wannan wasan da bata shirya shigarsu ciki ba.
Sanda
suka isa gidan sam bata wani jira guard sun bude mata qofa ba,gurds din da take
mutuwar jin haushinsu tun daga sanda suka hanata rawar gaban hantsi a gidansu.
A yanzu kuma a wannan gidan ta fahimci dasu ake kowanne motsi,wannan wacce irin
masifa ce kamar raqibu da atidu da buwayin sarki ya saukar maka da suka zama
lallai ka rayu dasu don su dauki dukkan ayyukanka,masu kyau ko akasin haka.
A
gaggauce ta wuce duka falukan ta zarce hallway zuwa bedroom din,burinta kawai
ta isa ga gallababbiyar wayar ta hadu da maamah.
Da zafin
nama ta birkita inda ta aje wayar kafin su fita,saidai kuma sama ko qasa ba
wayar ba dalilinta. Cak ta tsaya tana gwama numfashi,sai kawai ta bude jakar
data dawo da ita ta fidda asalin wayarta da take kiran kowa da kowa da ita.
Asalin
layin maamah din ta kira,wanda bugu biyu ta daga,saidai bata jiyo komai ba sai
muryar haneefa daga gefe da alama hira take mata ita kuma tana fadin
"Allah auta?" Idanu ta runtse,ta lura da gaske ta
shiryawa wasan...... Ta ruwan sanyi takeso ta cutar da rayukan da basuji ba
basu gani ba.
"Me kikeso?,me kike buqata?" Ta tambayeta kai
tsaye ba tare data damu ta amsa sallamar data mata ba. Wani shu'umin murmushi
ta aje,sannan ta jita tana cewa
"Haneefa jeki kwanta kema,idan na gama zanzo na daukeki
mu wuce daki tare"
"Tom" Ta amsa mata kamar yadda yawanci haka
maganarta take,abun kuma daya sake sokar zuciyar sabreen kenan.
"Mallakamin d'ana nakeso kiyi.....ni kuma zan mallaka
miki 'yan uwanki ta ruwan sanyi,dama naki ne". Tayi mata bayanin hankali
kwance. Suya sosai taji zuciyarta tanayi,tanason fadin maganganu da
dama......tanason tayi abubuwa da dama amma kaman an danne harshensa sai zallar
bacin ran dake mata zullo
"Why ni?,me yasa saini ne?" Ta fusgi kalmar daga
harshenta ta watsawa maamah ita.
"Saboda ni a wajenki kawai na hango irin zarrar da nake
buqata......a aikinki na gano abinda zaisa aikina ya cimma gaci.....uwa uba
kina da wani irin kyau da zai iya saurin rusunar da zuciya ya kuma narka
zuciyar kowanne d'a namiji". Qit kawai ta kashe wayar tana jifa da ita
gami da cusa dukka yatsunta goma cikin sumarta.
Maganganun maman sun isheta haka,a yanzu basu take da buqatar ji ba.
Kowacce tsiga ta jikinta ta miqe,taji wani irin matsuwa da fatan isowar kayan
aikin maamah din hannunta. Inama ace zai yuwu ta danneshi tayita dura.masa
abincin?,daga safe zuwa yamma ya zame mata mallakakke kaman yadda takeso ita
kuma ta samu yancin 'yan uwanta. Tabbas! Inda babu 'yan uwanta da maamah din
tayi garkuwa dasu,babu abinda zai hanata nuna mata ainihin kalarta da kuma
ainihin yadda wasan zai gudana.
*DUNIYATA LITTAFI
KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 23
23
Har wani
nauyi idanunshi ke masa saboda tsohuwar gajiya da sabuwar gajiya dake a
jikinsa,ga kuma wadda ke jiransa a gaba. Wanka ya fara yi,sai kawai ya sauya
pyjamas dinsa ba tare da yabi takan abinci ba don baijin gajiya zata barshi
yayi hakan yabi lafiyar lallausan gadon nashi dake gewaye da kyawawan pillows
daa luxury bedsheet din dake qarawa bed din zama wani na musamman me cike da
alfarma da wata nutsuwar samun lafiyayyen bacci.
Numfashi
biyu kacal ya sauke wani lallausan ringtone ya katse masa relaxing din da yayi.
Duk kiran da zai shigo wayar yasan na wani makusancinsa ne,hakanan a baya so
din ya miqa hannu ya dauko shafaffiyar wayar me wani irin kyan daukan hankali.
Sunanta da
ya gani ya sanyashi miqewa daga kwanciya zuwa kashingida zuciyarsa tana
bugawa,ya lumshe idonsa yana budewa lokaci daya,can qasan ransa yana fatan
Allah yasa ba wani jagwal dinne ya taso ba ko zai sameshi.
Cikakkiyar sallama yayi mata,ta amsa da wani irin yanayi na karsashi da
kulawa.
"Akwai baqi a qofar gida,sun gaya min securities na
gidan sun hanasu shigowa" Har ya sauke qafafunsa qasan gadon da zummar
yaje ya duba ta na'urar tsaronsa,sai ya tuna ashe ba'a gida yake ba nan wani
sabon muhalli ne,baida tabbacin an gama installing nasu,dole ya koma ya zauna
gefan gadon a nutse yace
"Baqi kuma maamah?....at these late hours?"
"Eh......ba wasu baqi bane......me aiki ce nace tazo
don ta tayata zama,da kuma yanayin gidan naku dole saida mataimaki daban".
Numfashi sosai ya zuqa yana fesarwa,kowanne taqi kuma kowanne taku da motsi na
maamah magana ce me zaman kanta.....wanzuwar aiki ne da sai ka saka hasashenka
da kyau zaka iya cimmasa.
"Amma maamah ina tunanin tafiya zamuyi.....dani da itan
gaba daya jibi idan Allah ya kaimu....so koda tazo dinma zata zauna a gidan ne
ita kadai.....nace if possible ta bari idan mun dawo....i will call you saiki
turota" Har tsakiyar kanta taji
wani abu ya tsarta mata,hakan kuma ya bayyana har cikin sautinta daya canza nan
da nan,abinda ya sake bashi wani haske.
"Har zuwa yaushe zaku dawo?".
"2to 3days ne.....just bude kamfani kawai zanyi na
dawo" Ya bata amsa bawai yana nufin dukkan maganganun daya fada haka suke
ba. Duk da bai iya qarya ba......amma a wannan muhallin ya samu fatawar qarya a
kansa a yanzu halastacciya ce.
Adadin
kwanakin da taji basu da yawa sai taji damuwarta taqaitacciya ce........ta cika
da fatan tafiyar ta sake basu kusancin da zai damqa mata dukka amanarsa a
hannunta,yadda suna dawowa komai zai fara cikin sauqi aminci da kuma nasara
"To yayi baida damuwa.....ammmm amma ba....kace su
barta ta shigo na bada saqo ta bawa d'iyata". Kai ya jinjina yana cewa
"Alright" Sai ya gintse kiran. Wadanda suke on
duty ya duba sannan kai tsaye ya kira daya daga cikinsu. Saidai kafin basu
damar bata damar shigowa sai daya basu dan qaramin aikin da tun kafin zuwaira
ta qarasa ciki suka gama aiwatarwa suka tura masa.
Bawai
bayan ta shigo cikin gidan ba......tun daga farkon layin daya amsa sunan
MUHAMMAD JADDA STREET ta gama raina kanta dama komai nata,bata sake tsinkewa ba
sai da suka iso qofar gate gate guda biyu da fuskar gidan ke dashi daban
daban......ta gama kuma narkewa gaba daya tun daga harabar gidan har zuwa falon
farko da suka zauna suna dakon sabreen.
Kowanne
motsi da yadda laila ta gaza sukuni,ta kasa danne zallar zalamarta da kuma
dimuwa da yadda gidan yake duka kan idanun zuwaira take yinsu,zuwairan da tayi
banza da ranta tamkar ma batasan tanayi ba. Mummunar qullaci ta samu zuciyarta
dayi akan hajja harira.....ko maamah bata fuskanci manufar harira na hadota da
ita ba ta gama karantar komai.....baqinciki qyashi da hassadar ta zauna ita
daya a gidan take mata......to itama ta lashi takobin zata gara nata wasan akan
laila da hajja,zata kuma murza musu kalar nata zaren.
Karo na
biyu kiran daya shigo mata yadan darsa mamaki a ranta,saidai a yanzun da 'yan
uwanta ke tare da ita,bata jin zata iya tsallakewa kowanne kira da zatayi
mata.....don tana cike da tsoro da fargabar shudewar kowanne minti a sanda suke
tare da ita.
"Ki sauka zuwa falonki kina da baqi.....saqon farko
kawai naci su baki.....kiyi qoqarin fara amfani dashi daga gobe zuwa
jibi". Bata jira cewarta ba ta katse kiran,saita sauke wayar daga kunnenta
tana binta da kallo kamar bata gane yaren da maamah tayi magana dashi ba.
𝐌𝐢𝐧𝐭𝐮𝐧𝐚
𝐭𝐚𝐥𝐚𝐭𝐢𝐧 𝐛𝐚𝐲𝐚
𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐚 𝐬𝐡𝐮𝐝𝐞
Daidai sanda
jerin motocinsa ke fita daga gidan don komawa nasu gidan,tana zaune daga gefe
zuciyarta tayi wani irin nauyi dauke da tarin kalamai da al'amura da tayo
tsarabarsu cikin gidan.
Tasan
tayi qasa d window din motar sanda amna tayo mata rakiya tana mata
bangajiya,amma batasanma bata maidashi ta rufe ba saboda yadda zuciyarta tayi
nisa a wani bigire na daban.
Daidai
lokacin da yake zaune bayan motarsa yana danna wayarsa yana qoqarin neman
location na gidan da yazo din. Nishin motocin yaja hankalinsa ya cire kansa
daga wayar yana maidawa kansu.
Motocin
muhammad fuad jadda daban suke,kaman yadda komai daya shafi jadda diamond chore
resources ya fita daban. Cikin qirjinsa
yake jin buri da fatan inama ya kasance tamkar wannan matashin me matuqar
sa'a?.....wanda ya fado duniyarsa da wani irin sa'a da yayi Imani ba kowanne
dan adam ke samun koda shigenta ba. A lokaci na quruciya......da qananun
shekaru sanda jini ke zagayawa da kyau a jikinsa......ace ya mallaki d'anyun
kudade irin wadannan?.....ya mallaki kyau da sura irin wannan?.....yayi wani
irin tambari da kuma suna,sunan daya watsu sassan duniya dama kuma ba'a batun
tambarar sunansa a qasarsa ta haihuwa.
Kamar
cikin majigin film.....kamar wulqawar walqiya cikin sararin samaniya ya hangi
wani Kyakkyawar fuskar......fuskar daya aza dukkanin burinsa a
kanta......fuskar daya sha kwana ya tashi da cikakkiyar sha'awarta tare da
tunanin yadda zai maidata ta zama tasa har abada......fuskar da daga qarshe ta
jefashi cikin bala'i masifa da barazanar faduwar kowacce daraja arziqi da
wadatarsa a yanzu da yaketa fafutukar maidawa......fuskar da a yanzun ba fuskar
da yake yunwar nema ya d'aid'aita rayuwarta irinta.
Bazai iya
cewa ga sanda ya zamo ya kuma diro daga saman motar ba sai da ya fara takawa da
zafin nama da zummar ya kamosu,ingarman motocin suka masa wani irin fit suka
barshi da kama iska ba tare ma da sunsan meye shirinsa ba.
"Damn it!!" Ya fada a kausashe yana kaiwa iska
naushi da hannunsa. Da gaske itace matar da muhammad fu'ad ya aura?,da gaske
itace amaryar da akace masa ana yiwa walima yanzu haka cikin gidan Alhaji hamza
kibiya?. Wani irin shu'umin murmushi ya subuce masa ya mamaye fushin da yake
kwance akan fuskarsa,ya koma ya daki bayan motarsa da hannunsa daya dunqule
"Good......komai yayi daidai" Ya kuma fada a fili
yana buga wani tsalle ya koma saman motar yana ci gaba da sakin murmushi,a
hankali a hankali murmushin nasa yake qaruwa kafin daga bisani kuma ya kece da
wata iriyar dariya yana sake bugun bayan motar gami da furta
"MUHSEENA" ainihin sunan da yake shine STAMP
dinshi. Da sauri ya kuma saukowa,ya bude backseat din motarsa ya finciko wata
magazine. Magazine ne da suka fidda sanarwar daurin auren da komai da komai,a
sama an rubuta da manyan baqin
_THE BILLIONAIRE'S WEDDING FATIHA_ Kusan babbban abinda suka
yita jaddadawa shine......bikin babban mutum me arziqi kaman muhammad jadda
din,yazo ba tare da wasu shagulgula da aka dade ana hasashen za'ayi ba,luxury
events da kowa ke mafarkin zaiyi a matakin arziqi irin nasa,shin meye sirrin?.
Murmushi ya kuma saki sanda ya karanta tambayar qarshe,sai yaji kaman shi ya
cancanci ya amsa tambayar.
"How i wish ina wajen da aka buga labarin nan?,tabbas
dana basu full details na wacece wadda ya aura,ta yaya zaiyi shagulgula bayan
BARAUNIYA ya aura?,TSOHUWAR KILAKI?" Ya fada a bayyane
"Ameenatu!" Ya kira sunanta na ainihi dake rubuce
jikin katin.
"You will pay it......dole zaki biya ninkin
farashinki" Ya sake fadi still a bayyane,boyayyen fushin nan dake kwance
qasan ransa yana wani tasowa yana bashi tururin bacin rai har saman fuskarsa.
A gaggauce
ya koma cikin motar tasa ya wurga magazine din,shima ya shige ya kunnata gami
da bata wuta ya finciketa yana barin layin don sam yama mance maqasudin abinda
ya kawoshi layin.
*_S A B R E E N_*
Tun bayan
sallar asuba take a zaune saman abun sallarta a qoqarinta na hana kanta komawa
baccin daya zame mata al'ada duk safiyar duniya. Bata da matsalar shirya su
haneefa breakfast da sauransu,duka wannan huda zatayi kafin su wuce,sai yau
abun ya zame mata banbarakwai.
Zuwa
qarfe bakwai idanunta duka sun daddaure mata sunyi mata wani iri,ta miqe a
hankali ta ninke abun sallar sannan ta taka tana nufar wata drawer ta zauna
gefan gadon tana jawota.
Ledar
jiya ce da zuwaira ta kawo mata,ta fiddota tana qarewa ledar kallo. Abubuwa
biyu suna karakaina cikin ranta,kokwanto da kuma qwarin gwiwa,saidai kuma
qwarin gwiwarta a wannan safiyar tamkar yana son korar kokwanton da takeji,don
haka ta riqe ledar da kyau ta fara takawa tana fita a dakin. Can qasan
zuciyarta ta birkita da tunanin me ya samu wayar momma?,me yasa ta kasa
samunta?. Daga daren jiya zuwa asubar yau ta kirayeta har batasan adadi ba,tanaso
taji daga bakinta.......tanason taji me yasa tabar su huda a hannun waccar
matar?.
Tsaiwa
tayi cikin kitchen din tana tunanin me dame zata dafa ko ta soya da komai zai
narke a ciki ba tare daya bada wata alama ba?. Aqalla ta kusa minti biyar kafin
ta wuce store din.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 24
24
Inda aka
yiwa dankali Kyakkyawar ajiya ta duba,ta debi yadda take ganin zai isa,ta bude
freezer shima ta debi nema ta rufe tana dawowa kitchen din.
Yau sai
gata kace kace cikin hidimar hada breakfast,abinda ya zame mata sai lokaci
lokaci idan huda bata da lafiya sannan ta karbeta.
Awa biyu
ta share cikin kitchen din,sanda ta gama ta gama gajiya gaba daya,amma haka ta
zaba warmer ta soma zuba komai a ciki.
Sanda ta
bude ledar da zummar fara gudanar da aikinta cikin ruwan tea da dankalin data
soya da kuma farfesun naman sai taji hannunta yana rawa. Hannuwan nata ta sanya
da zummar qulle ledar ta maida ciki amma sai sunan HUDA NADRA HANEEFA ya fado
mata......daga bisani maganganun maamah suka dawo.mata fes,sai takejin kamar
umarni ne akeyi mata na KI AIWATAR.
Kai ta
soma girgizawa,'yan uwanta sune haqqin farko da suka zame mata wajibi ta fara
kubutarwa.......ba zata wofantar da rayuwarsu ba saboda mas'alar mutumin da ko
qanqani baisan zafinta ko darajarta ba,don haka ta kunce komai......takuma
aiwatar dashi kamar yadda zuwaira ta zana mata,ta debi kayan abincin ta jerasu
saman dining.
Tsaiwa
tayi tana kallonsu,kamar ba zata bar gurin ba,sai kuma taja da baya ta fara
takawa tana sauka daga wajen.
▄A nutse yake
saukowa daga saman stairs din,sanye da wata lafiyayyar suit ta kamfanin BRIONI
da suka zama number daya wajen fidda suit na manyan mutane daga auduga da
zararruka masu daraja. Yayi wani irin kyau sassanyan kyau kaman yadda yanayinsa
yake nunawa kamar yau din bai tashi da wannan kuzarin nasa ba dake sake bada
bayanin cikakkiyar lafiyar da yake da ita. Qafafunsa sanye cikin rufaffun
takalman dake faman daukan idanu suna qara bayyanar darajar da yawan nauyin
kudaden da aka sanya aka siyesu. Hannunsa daya cikin aljihun trouser dinsa,daya
hannun kuma yana sarrafa wayarsa. Sassanyan turaren nan nasa da bai cika
hayaniya da yawa ba ina busawa a hankali yana karade ko ina. Wani irin qamshi
ne na musamman dake tashin kan mutane da dama,saidai idan ka debe farouq har
yau ba wanda zai iya gaya maka exactly sunan perfume din da yake using.
Musaddiq da saddiq sunsha zuwa su sata,amma sun kasa samunshi ako ina bare su
siya.
A yadda
yake saukowa daga shi sai wayarsa zaka rantse ba wata muhimmiyar tafiya bace a
gabansa,kamar zaije qofar gidane ya dawo. Haka tsarin tafiyarsa yake,baya
daukan komai sai documents dinsa da wasu mihimman abubuwa amma banda sutura.
Kusan duk qasa ko garin da yake da huldar kasuwanci dasu yana da permanent
gidan da ba abinda gidan ke buqata sai isowarsa.....idan ya sauka a wani gurin
daban ba gidajensa ba to yayi hakanne saboda salon bad da hankali da wasa da
hankulan abokan adawa na kasuwanci ko kuma dalili na ra'ayin qashin kanshi na
haka kawai yaso.
Duba daya
ya yiwa hallway din ya maida idanunsa ga qofar da zata sadashi da parlor
din,sai ya maida wayarsa side pocket na rigarsa sannan ya maida daya hannun
shima cikin trouser dinsa yana takawa a nutse cikin falon.
Sai
daya zagaya falon tas ya gama duba komai,ya tabbatar komai yana a muhallin daya
kamata ya zauna,sannan ya zarce falo.na biyu ya tabbatar da komai a yadda
yakeson ya zama,sannan ya zarce kitchen zuwa store ya duba komai.
Sanda
yake baro kitchen din hankalinsa yakai kan dining din dake jere da warmers,ya
zubawa gurin idanu na wasu mintuna yana qanqance ido,kafin kuma ya sauya
akalarsa yana nufar wajen zuciyarsa cike fal da mamaki.
Cak ya
tsaya kan warmers din yana sake binsu da kallo tamkar wanda ke neman sunan
wanda ya qera warmers din a jikinsu. Ya kusa mintuna biyu kafin ya zare
hannuwansa daga aljihun ya fiddosu,bakinsa da yake motsi kadan kadan zaka kalla
kasan akwai abinda yake fadi wanda duka bazai wuce addu'a ba,sannan ya miqa
hannunsa a nutse zuwa ga warmer din yana furta
"Bismillah" A fili,ya murzata ya bude. Daya bayan
daya ya bude komai,hatta da hot water dispenser din da tayi using ta adana tea
din sai daya saka cup ya zuba ya jerasu a gabansa yana qare musu wani irin
kallo na qurilla.
Ya kusa
mintuna biyar a haka,sai ya saki wani siririn murmushi yana girgiza kai,ya saka
hannunsa ya maida komai yadda yake kamar ba'a taba ba. Hannunsa ya miqa daga
gefan table din ya ciro sticky notes guda daya,yayi gajeran rubutu ya manne
mata jin warmer din ya juya da dan hanzari ba kaman dazu ba yana sauka a wajen.
"Tabbas ita din aiken maamah ce......" Abinda ya
gayawa kansa kawai kenan ya gangara yana ficewa gaba daya daga falon bayan ya
tsinke waya guda daya data rage ta telephone din dake parlor din.
Kowanne
ma'aikaci yana tsaye a matsayarsa suna jiran dakon fitowarsa. Dukka guards
dinsa suna tsaye a inda ya kamata kowa ya tsaya. A yau shigar fari kowannensu
yayi,da wani irin tsarin shiga da sutura da zata bayyana alfarmar wanda suke
aiki a qarqashinsa. Abdulgafar shugaban tawagar tsaronsa shi ya fara nufoshi a
gaggauce cike da kuzari yana tarbarsa cikin girmamawa kaman yadda suka saba shi
da mataimakinsa jordan
"Good morning sir" Ya fara gaidashi kafin
muryoyinsu ya karade wajen suna gaidashi suma
"Morning.....hope you are fine?"
"Fine sir" Suka hada baki wajen amsawa
"Good" Ya maida musu yana gyada kanshi.
"Jordan" Fuad yayi kiransa
"Sir" Ya amsa yana matsowa.
"Where's abdulbasit?"
"Am here sir" Wanda aka kira da abdulbasit ya
furta yana matsowa cikin shigar wani uniform da yasha banban da nasu jordan
"Have you finished?" Kai ya gyada a girmame
"Yes sir...."
"Okay,kada ka manta.....zan bar muku
jordan.....jordan,ba shiga ba fita har sai na dawo ko na bada umarnin hakan. Ko
waye bazai shiga ba,ko waye kuma bazai fita ba......hope i made it clear?"
"Yes sir" Jordan din ya gyada kai,don shi ya
fahimci inda aikin yasa gaba,zasu maimaita salon aikin da sukayi satittikan da
suka wuce kenan.
"Yi mana addu'a" Ya fada a taqaice yana duban
abdulra'uf wanda kusan duk sanda qaramin meeting irin haka ya kamasu shike da
alhakin hakan.
Cikin
mintuna uku aka kammala kowa ya wuce motarsu,motocin suka jeru kamar
kullum,security din dake kula da qofa ya wangale musu ita suka fice daya bayan
daya.
"Am on the way......banason jira" Abinda ya gayawa
saddiq kenan da yayi kiransa sanda suke a cikin motar,sai ya kashe wayar kawai
ya maida aljihu. Titi ya zubawa ido yana fesar da iska daga bakinsa. Baya
tunanin maamah zata saka a kasheshi saidai wani abu na daban,amma ita kuma
fa?,may be ta tsallake gona da iri,wala'alla ta wice limit da iyakokinta,amma
duka ita maamah bata gani ba?,why zata zabi mace me irin wadannan dabi'u da
halayen ta kasance a tare dashi?. Tambayar da yaji ta sake quntata zuciyarsa,abinda
kuma bayaso ya faru kenan don yau din yana buqatar freshness don gobe rana ce
me muhimmanci a wajensa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 25
25
"Nayi
zaton tare zaku tafi?" Shine abinda anni tace dashi sanda yake zaune sosai
gaban abba suna breakfast dashi. Kai ya girgiza
"Ba daman hakan anni,idan munje ma zata dinga wuni ita
daya ne saboda ba zama zanyi ba......akwai baqi da sauran shirin da zamuyi daga
yau zuwa goben in sha Allah" Kai ya jinjina
"To Allah yayi jagora.....yasa a bude a sa'a"
"Allahumma ameen" Suka kusa hada baki wajen amsawa
shi da abban.
"Amma ba za'a kai mata abokin zama ba?" . Anni ta
fada cikin salon nuna kulawa. Basarwa yayi don baison anni ta gane komai game
da lamarin
"Ba ita daya bace anni,banajin zata damu,akwai mutane a
gidan". Kai ta gyada
"To Allah ya tsare"
"Ameen ya rahman" Ya sake amsa mata.
Duka duka
mintuna arba'in suka qara suka fice a gidan shi da musaddiq zuwa airport inda
private jet dinsa ke jiran isowarsu.
A
hankali hasken ranar dake ratsowa ta tsakanin labule ya soma qarawa dakin haske
yana kuma tabbatar da bayyanar rana sosai ya wuce kai tsaye ya taddata har inda
take kwance,wanda wannan shine abinda ya sanya idanunta budewa a hankali suka
kuma sauka kai tsaye kan agogon dake manne a dakin.
Sha biyu
na rana saura minti biyar kacal shine abinda idanunta suka gani,abinda ya
sanyata ware idanunta gaba daya tana kuma miqewa da dan sauri. Bayan Hannunta
ta saka ta mutstsike idonta tana sake duban lokaci,sam batasan tayi bacci me
nauyi haka ba,don ko wanka bata samu tayi ba ta koma ta kwanta bayan ta
tabbatar ta gama duk abinda ya dace.
Miqewa
tayi tana miqa,tana jin yadda gajiya kebin duka sassan jikinta,can cikin
zuciyarta kuma tana raya lallai zuwa yanzu ya debi abincin yaci,tana sake jin
wani tabbaci da qwarin gwiwar komawarta zuwa ga rayuwarsu ita da 'yan uwanta.
Toilet ta
wuce tayi wanka,ta fito ta shirya cikin doguwar rigar atamfarJulius gold data
zauna mata daidai jikinta da wani irin dinki da bazai takuraka ba. Sai a sannan
taji cikinta yana wani yamutsawa....a lokacin ta tuna lokacin data dauka
rabonta da wani abu me suna abinci cikakke. Plate tummy dinta ta shafa,sai ta
miqe a nutse tana nufar hanyar fita daga dakin.
Tun daga
nesa idanunta nakan stairs din har tazo ta gotata tana fita falon farkon. Tadan
shaqi iskar dake kadawa tsakanin hallway stairs din da parlor din,wani qamshi
ne ke kai kawo na daban wanda bata taba jin sassanyan qamshi irinsa ba,wani
sashe daban na zuciyarta kuma tana jin kamar ta taba ji ko sanin irin qamshin.
Xarcewa
falo na biyu tayi,tunda kuma ta fito idanunta suna kan dining din. Gudun
zuciyarta ya qaru kadan,yayin da ta cika da fatan taras da komai ya tafi
daidai.
Bude
komai tayi,daga kallon farko ta fahimci ba'a taba komai ba.....daga nan din
kuma dukka gwiwoyinta na qafa da hannu sukayi wani irin sanyi,sai taji ta kasa
tsaiwa,taja kujera daya ta zauna tana girgiza dispensers din taji ko yawan
adadin tea din ya ragu?. Nan ma ba abinda ya sauya,yadda ta zubashi haka nauyin
yake,sai ta saka hannuwanta guda biyu tana dafe kanta,daidai sanda idanunta
suka sauka kan sticky notes din dake maqale a wajen iska tana dan kadata.
Hannu daya
ta saka ta ballota daga inda take liqen,ta sanya idanunta akan kwantaccen
rubutun dake a tsare kamar wanda aka tafa a inji bawai hannune yayishi ba
_mission accomplished_
iya abinda takardar ta qunsa kenan. Jujjuyata ta shiga yi tanason
fahimtar saqon dake rubuce a jiki amma ta gaza kaiwa ga nan,abu daya ne kawai
ya tsaye mata a rai da baici din ba. A niyyarta ta koma daki ta zauna ta jira
wai koda zai sauko yaci bisa rashin sanin ya dade dayin nisa cikin gajimare.
Amma qaguwa dason taga yaci din ya hanata komawar,sai tayi zaune a parlor
parlor din tana saka kunne akan kowanne motsi na gidan,amma sam motsin da take
iya ji din ba wani motsi bane na azo a gani,don hatta da securities na gidan
bawai suna kusa da ita bane bare ta jiyo motsin nasu da kyau.
Sha biyu
daya daya da rabi biyu biyu da rabi ba wani batun motsin kowa da komai cikin
gidan,zuwa lokacin ta fara sarewa da lallai bazaya sauko ba,don koda wasa bata
kawo cewa wai baya cikin gidan ba. Koda zai sauko a yadda suka lissafa mata
halinsa tayi imanin bazaici komai na daga breakfast din ba,wannan ya sanyata
cikin mutuwar jiki ta tattare kwanukan tayi kitchen dasu ta ajjiye tana tunanin
yadda zatayi da kayan abincin.
A makare
ranar tayi sallar azahar......har ta idar da sallar tunaninta ya karkata ga me
ya kamata tayi?,ta shaidawa maamah din ko ta barta?,kada sanar mata ya sanyata
ta dauka cewa gazawa ce har ta nemi yin wani motsi akan qannenta.
Wannan
tunanin ya sanyata ta share,duk kuwa da cewa wani sashe na zuciyarta a matse
yake data gaya matan,amma ta danne da wani irin qarfin hali tana saka ran zai
fito yaci na dare.
Tana
idar da sallar la'asar ta fada kitchen,ko a sannan ma tsaiwa tayi tana tunanin
wanne irin kalar abinci zatayi da zaija ra'ayinsa har haqarta ya cimma ruwa?.
Sai data kusa qure tunaninta kaf sannan ta zabi abu daya,ya wuce zuwa store
tana duba dukkanin abinda take da buqata.
Dab da
magariba ta baro gaban dining din data cika da warmers masu dauke da abinci.
Tana takawa zuwa hallway din tana satar kallon stairs din. Zuciyarta cike da
mamakin wanne irin mutum ne shi haka?,wanne irin mugun baqin hali ne dashi da
har zai debi wadannan wannin a qunshe a sama ba tare daya sauko ko anji
motsinsa ba?
"Ko yana zuwa masallacin ma oho" Ta furta a ranta
a sarari tana jan tsaki gami da tabe baki,ta tura qofar dakinta ta shiga tana
addu'a yadda a daren nan data saka hope me yawa,ta zuba komai da yawan
adadi.....Allah yasa a wannan daren komai ya ratsahi har fiye da yadda maamah
din keso don ta samu tickets din matsawa daga rayuwarsu ita da 'yan uwanta.
Cikin
toilet dinta tayi wanka,takuma shirya cikin sassaqan cotton lite material me
sauqi. Sallar magariba tayi,sai taci gaba da zama a nan. A hankali yaran suka
fado mata,sai taji tana kewarsu,tana so taji!muryarsu koda kuwa maamah din zata
kafa mata wani sharadi na daban kafin ta barta ta gansu,wannan tunanin ya
sanyata miqewa a nutse tana mamakin duka yau bata dauki wayarta bata kuma yi
amfani da ita ba.
Kai
tsaye tasan inda ta aje wayar tata,can ta nufa,ta daga wajen da zummar
dauka,saidai kuma wayar tace daukeni inda kika ajiyeni. Mamaki kadan ya
kamata,amma sai ta share tana tunanin qila ta canza mata waje ne ta kuma manta
inda ta ajjiyeta,don haka ta fara bincikawa guraren dake daura da nan ko a nan
ta ajiye din.
Guri
hudu duka bataga wayar ba ba alamarta,ganin zata gajiyar da kanta saita ajiye
wannan ta koma laluben wayarta ta asali data barta a handbag din da suka dawo
da ita jiya dake ajiye saman mudubin nata tunda ta ajiye jakar. Kaf ta lalube
jakar sannan ta zazzageta,saidai babu wayarta babu alamarta a ciki. Mamaki
yadan sanyata ja da baya,nan ma zuciyarta ta soma ayyana mata wataqila itama ya
canza mata waje ne,don haka sai ta fara jaye jayen lockers tana bincike dakin.
Wasa wasa har closet dinta ta duba babu wasu alama na akwai wayoyin. A hankali
ta dawo tana zamewa ta zauna daga qasan carpet din da aka qawata gaban sofa bed
din tana maida numfashi.
"Ya akayi haka?,me yake faruwa?,dukka wayoyinta babu ko
guda daya?" Ji tayi sam ta kasa aminta ko ta samu nutsuwa,sai kawai ta
fadada bincikenta har zuwa kitchen dining area waiko ta barsu a can,saidai babu
komai kamar dai yadda ta gani a dakin.
A parlor
din ta zame ta zauna,tana jin wani shakka da kokwanto na shigarta. Kota wacce
fuska bataga waje ko wani sarari da wani zai samu daman shigowa gida irin
wannan ba.....me wasu irin madaukakan katangu da kuma gwabza gwabzan security
irin wadannan ballantana tayi tunanin wani ya hauro ya shigo musu...... Da
sauri ta zauna sosai tana qanqance idanunta sanda wani tunani ya fado mata.
"Idan har haka ne shine kenan ya dauke
wayoyin?,yaushe?,garin yaya?,a ina kuma ya samu damar aiwatar da hakan?"
Tambayoyin dake danqare a kanta kenan data dinga juyasu.
Idanunta
ta maida tana duban sashen da stairs dinsa suke,zuciyarta na bugawa kadan
kadan,tana jin kamar ta tashi ta haura ta sameshi a can,taji meye hujjarsa na
daukar mata wayoyi,bayan hakan ba huruminta bane?.
Bata
fahimci cewa gidan ba kowa ba......ita daya ke rayuwa a cikinsa duk girmansa ba
sai da sha daya na dare ta gota a idanunta. Sai a sannan taji wani irin tsoro
ya soma mamayarta sanda zuciyarta ke bata hasashen ita daya ce qwallin qwal a
gidan. Wani irin karyewa zuciyarta tayi,tsoro yana sake shigarta sanda take
qudundune cikin duvet dinta. Bata taba kwana ita daya ba koda cikin dakinsu
ballantana a gidansu gaba daya ba.....wanne irin azzalumi ne shi da zaya fita
yabarta a gidan da yafi qarfin zaman mutum hudu ma yace ta kwana ta rayu ita
kadai?.....ba wayar da zata kira wani ballanta taji sassauci......koda ta duba
wayar girke dake parlor din da zummar ta sadata da security din da suke waje
taji ko zata samu aron waya daga hannunsu cikin rashin sa'a ta samu an yanke
sadarwarta,ba zata iya yin magana da kowa ba banda dakunan dake cikin gidan.
Kanta ta
cusa cikin pillow din tana jin yadda bugun zuciyarta ya qara tsananta sanda
karen dake wani sashe daban na gidan ya tsananta haushinsa. Bata taba tunanin
akwai halittar tsoro a qirjinta har haka ba sai yau.....ashe dukka jarumtar da
take zaton tana da ita ba jarumta bace.....ko tace ta tsaya ne kadai ta
bangaren saita maza daukan darasin rayuwa da sanin ciwon rasa wani abu da
xukata suke tsananin so da qauna.
Batasan
ya akayi ba ta samu da qyar wani takurarren bacci yayi awon gaba da ita.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 26
26
Kwana daya
kwana biyu haka awanni suka dinga juyawa da ita cikin gidan,cikin wani irin
matsanancin shuru kewa da kuma kadaici. A hankali ta dinga jin wani matsanancin
takura,ta yaya zata zauna irin haka ba waya ba gilmawar kowanne dan adam?,tv
kuwa sam taqi ta kalleta bare ta gwada kunnata. Da farko ta dauka zata iya
jurewa,amma sannu a hankali saita fahimci ashe mutum rahama ne a kusa da
kai,koda kuwa ba wata mu'amala da zata hadaka dashi. Tayi dukka juriyar da zata
iyayi sai taji haqurinta ya soma gazawa. Wani danqararren bacin rai ne yake
cinta game dashi wanda qilan inda yabar mata wayar ma a wannan karon batajin
akwai abinda zai mata shamaki daga kiransa ta zazzage masa abinda yake cikinta.
Ta yaya ita din da ta kwashi shekara aqalla biyar zuwa shida,ba wata ranar
banza da zata fito ta fadi bata fita ba.....yanzu kawai rana tsaka ta wayi gari
da mummunan kulle irin wannan?. Ko a baya batata ji a ranta akwai wani lokaci
da zayazo a sanyawa qafafunta irin wannan sasarin ba,ba lissafin aure kwata
kwata cikin kanta shi ya sanya bata kawo yiwuwar afkuwar hakan a kanta ba koda
sau daya.
Ranar
data cika kwana na hudu,tun qarfe goma na safe taji takai maqurar da ba zata
iya jurewa ba. Sha daya da rabi daidai ta kammala shirinta cikin atamfa. Ta
taka a hankali zuwa inda take da tabbacin ta ajiye kudinta data shigo dasu
cikin gidan,ta bude locker din ta zura hannunta don debosu,don ta gama tsarawa
kanta zata taka ta fita ta samu napep duk kuwa da cewa tasan area din kwata
kwata yana da wahala kaga abun hawa na haya.....to amma ta gwammace tayi
tattaki zuwa babban titinsu tayita jira cikin rana har ta samu abun hawan da
zai kaita gida. Zuciyarta da tunaninta gaba daya yana kan taje ta binciki
lafiyarsu huda.....kowanne dare dasu take kwana dasu kuma take tashi,suna cikin
aminci ko kuwa aah?......da qyar ta iya jure wadannan kwanakin suka shude ba
tare da tasan komai game dasu ba.
Ta dauka
yadda ta dokanta ta fita ne idanunta suke mata gizo sanda ta hangi babu ko
burbushin kudi a wajen,amma data bude sosai sai taga gaskiya take gani.......ba
komai a ciki kamar yadda ta gani da farko.
Mamakinta
ya ninku akan mamakinta na kwanaki hudun da suka shude........ta sulale tana
sake zama a saman stool din dake kusa da ita.
"Wai wa yake da alhakin aikata haka?" Ta sake
tambayar kanta tana jin tantama akan tabbacin zargin farko da zuciyarta ta
bata.
Duk
wani karsashi na fitar saita rasashi......yaushe ya samu damar shigar mata
daki?,dame dame ya bincika mata?,me zaiyi da wayarta?,dame dame zai bibiya
cikin wayar?. Wadannan tunanin su suka sakata a gaba,ta kasa tuna komai ko
abinda ya dace tayi,har sai da agogo ya alamta mata sha biyu dai dai na rana.
Cikin
qarfafawa kai gwiwa ta koma toilet ta sake wanke fuskarta,ta dawo ta wuce
closet ta dauki handbag da shoe da zai dace da shigarta sannan ta soma barin
dakin tana jefa atm dinta a jaka da zummar idan ta fita ta samu wani guri ta
cire kudi daga account dinta.
Wannan ce
ranar farko kuma karan farko data fito daga cikin gidan a yanayi irin wannan.
Faffadar haraba yalwatacciya me wani irin tsari me jan hankali. Kusan gurare da
yawa an qawatashi da koriyar ciyawa a maimakon tiles marbles ko concrete da
akafi yawan amfani dashi. Sai wasu irin fararen stone da aka zuba a wasu daga
cikin hanyoyin da zaka taka ka wuce zuwa haraba ta biyu. Idanunta suna iya gane
nata wasu qofofi da babu qofa a jikinsu face wani irin design da aka musu wanda
batasan ainihin inda zasu sadaka dashi ba. Sosai harabar ta qawatar da wani
irin yanayi da zakayi tsammanin ba cikin qasata nigeria kake ba.....saidai
wutar dake can qasan zuciyarta ta danne burgewar da wajen yayi mata,taci gaba
da tafiya cikin confidence zuwa qofar gate din da take da tabbacin zata sadata
da waje.
Tsaye
kawai tayi don bata fahimci ta inda zata ratsa ta wuce ba,sam qofar ba irin
qofofin data saba gani bane. Gajiya tayi da tsaiwar ta kuma gaji da kallonta da
tunanin ta inda zata fita din,don haka ta saka hannu ta soma knocking da
tunanin zasu iya jinta.
Tun tana
knocking din a hankali har ta fahimci ba kowa ke jinta ba,ta qara dada qarfinsa
saidai a banza don ba wani motsi da taji da zai bara hope din wani na kusa
zaiji ya kuma budeta,wannan ya qara hasala mata zuciya,ko a kurkuku take
bangaren muggan laifin kisa ko fashi da makami iya horon da za'ayi mata
kenan,don haka ta sake maida kai wajen buga qofar da kyau ba tare da tunanin
cewa babu me jinta ba.
A hankali
wani sashe kadan daga saman qofar ya zuge kanshi da kanshi. Fuskar jordan ta
bayyana wannan karon sanye cikin uniform din daya zama kayan sawa ga duk wani
ne aikin tsaro dake cikin gidan.
"Good afternoon maa". Ya furta da wannan
matsananciyar girmamawar da yake mata wadda ba abinda take sawa zuciyarta sai
wani irin qarin takaicinsa. Fuskar jordan fuskace da ba zata manta da ita ba ko
kadan
"Open the door" Ta fada adan fusace tana
kallonsa,tana jin kamar ta miqa hannu ta zabga masa mari. Cikin rusunawa da
girmamawa kaman yadda ya saba ya fara mata magana da hausa
"Am sorry maa......boss bai bada umarni ba,idan ba
damuwa ko zaki kirashi kuyi magana tukunna?". Idanunta ta janye kawai daga
kan jordan din bacin ranta yana ninkuwa,abinda yayi mata a wancan lokacin shi
ya maimaita mata kenan?,waishin me yake daukan kansa ne shi?,don yana da
kudi?,yana da dukiya shi yasa yake tunanin zaiyi duk abinda yaga dama?,zai taka
wanda takeso a duk sanda yaso?,zai wulaqanta mutane sannan kuma ya kwana
lafiya?. Ta ina zata nemeshi bayan babu ko waya guda daya a tare da ita?,ta ina
zasuyi magana bayan ya yanke sadarwar gidan gaba daya?,koda ma komai yana nan a
muhallinsa ta rantse ba zata kirashi ba.
"Kawu ne ya jawo miki" Amsar data dawo cikin kanta
kenan. Idan ma kira ne shine mutumin daya kamata ace ta kira,har yanzu tana ji
a jikinta kan ta inda ake hawa ta nan ake sauka,kawun shine ya bada ita ya kuma
saida mutuncinta.......don ta nata bangaren ba'a kan muhammad fu'ad bane farau
shallakewa maza masu kudi da kuma hadari......don haka don shi kadai bazai zame
mata matsala ba inda anbi karatun yadda ta saba. Har taji kamar ta sare,sai
taga idan ta bari hakan ta kasance yasha da ita,don haka ta matsa bakin gate
din
"Can you barrow me your phone?". Ta tambayeshi
tana kallonsa. Jinin jikinsa yasha,yadan kalleta yana kokwanto. Yaya zata rasa
waya tana a gida irin wannan?.
"Afwan madam.....amma me zakiyi da waya?" Idanunta
da suke mata zafi ta lumshe
"Zan kira uncle dina ne.....i lost my phone". Dan
jim yayi kadan,sai kuma ya amsa mata yana sanya hannu a aljihu ya fiddo wayar
ya miqa mata bayan ya sake bude glass din ya qara girma.
Yadda
yake bata wayar kamar tana a kurkuku ya sake matsa zuciyarta ya qara yawan
adadin bacin ran da take ciki.
Wani
sashe daban na gidan ta koma ta zauna saman wasu rukunin kujeru da aka qawata
cikin wata rumfar bamboo dake bada iska me kyau da sanyi. Da qyar ta iya hada
lambobin kawun don ba haddacewa ta taba zama tayi ba.....saidai kawai kira na
yau da gobe daya bata daman kallonsu daya bayan daya suka kuma zauna a kanta.
Bugu biyu
kawun ya daga da cikakkiyar sallamar data kusa sanyata jan tsaki
"Kamar gaske" Ta fadi a ranta tana amsa sallamar
tasa a daqile.
"Wa nake ji kamar sabreena?" Ya fadi da annashuwa
cikin muryarsa,zuciyars na bashi tabbacin lallai zama ya soma miqawa,wataqila
wani alkhairinma ta bugo tayi masa
"Nice" Ta amsashi a hankali
"Kai madalla Allah.....ma sha Allah,amma fa naji dadin
kiranki kin kyauta diyar albarka,dama inata zube kunne naji kiran
naki......"
"Eh gashi na kira......na kiraka ne kuma na gaya
maka.......wannan mutumin daka saida masa dukka 'yan cina da mutuncina ya
kamata ka kirashi ka bashi labarin haihuwata akayi bawai a baiwa aka ribatoni
ba.......ka fada masa abinda ke tsakaninka dashi daban da abinda ke tsakanina
dashi,bazan iya daukan dukka wannan izzar tasa da izgilancinsa ba......ina da
'yance kafin zuwansa zan kuma ci gaba da kasancewa me 'yanci a rayuwata.....don
har yanzu babu d'a namijin da zai dinga ruling dina yadda yaga dama ba tare da
naso haka ta kasance ba".
"Kai jama'a.....waike wacce irin yarinya ce ne me
butulci?,Allah yayi miki wannan babban gamo da katar din da miliyoyin mata ke
fatan samu amma ki zauna kina shashanci?,yo Allah na tuba idan ranka ya dade
baiyi mulki da izza ba meye zaiyi?,kudi ne dashi fa?,arziqi garai irin arziqin
da gwamnati ma wani lokaci biyayya takeyi maka.......ina gani malam rufa'i?,to
wallahi bada ni ba.....hasalima ni bamu taba waya dashi ba,dan uwansa kuwa
farouqu bazan dauki sirrin gidan ma'aurata nakai masa ba Allah bazai la'anceni
ba,in zaki nutsu kiyi biyayya ki tara abinda kika tara karki mana buqulu
to,amma wannan jan kunnen bada ni ba.....wane mutum inji mutuwa,Allah baki da
hankali sabreena" Har ya qare maganganun idanunta suna kulle saboda yadda
yake mata magan da qarfi da hayaniya,uwa uba ita bataga dalilin dogon jawabinsa
ba.
"Kawu" Ta kirashi a nutse.
"Yaushe su huda suka zama cikin kayan gado da har
za'ayi rabonsu zuwa ga wata mace da basu hada alaqar komai dasu ba?".
"Wata mace?,Allah na yarda dai da gaske akwai sauran
qarancin nunar hankali a tare dake.......kina magana akan hajiya mariyah
surukarki?,mutuniyar kirki me yawan alkhairi da son zumunci?,yo wannan kika
fadi mummunar kalma a kanta aisai Allah ya tsine miki albarka.......ni baza'a
zageta dani ba,sai anjima sabreena" Kafin ta ankara ya yanke wayar,abinda
ya sanyata a razani ta maida dubanta kan fuskar wayar tana kallonta cikin
mamaki.
A wannan
karon duk yadda taso tare kukan sai da hawaye ya sauko mata bayan ta maida
wayar wa Jordan. Sai kawai ta soma tattaki da sassarfa tana komawa ciki cikin
yankewar kowanne tsammani.
A falo na
biyu ta zube don ta gaza isa bedroom din. Wasu irin hawaye masu zafi suka fara
gangaro mata. Me yasa rayuwa zata juye mata da zazzafan yanayi irin wannan dare
daya?,yanayin da ko s mafarki bata taba tunanin zaya risketa ba?. Ya cika mugu
na gaske,ya rufe mata kowacce qofa ko hanya da zata samu sassauci......me ya
rage ita kuwa tsakaninta dashi banda itama tayi duk yadda zatayi tayi nesa
dashi?,me ya rage banda ta aiwatar da nufin maamah a kansa don ya gwada shiga
halin mulkin mallakawa d'an adam yaji idan hakan da dadi?.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 27
27
★★Madaidaiciyar haraba ce wadda yanayinta yayi kama da gine ginen turawa
ainun,irin gine ginen qasashen qetare,saidai kuma ba harabar kadai ba.....gidan
dama sauran gidajen dake wajen dama unguwar gaba daya ba zaka dauka kana cikin
abujar nigeria bane ba.
Tamkar
shi daya ne cikin gidan saboda rashin hayaniyar jama'a da kuma motsi,saidai a
yawancin lokuta yakan zabi yanayi irin wannan don bawa zuciyarsa hutu da
kwanyarsa. Bayan doguwar gwagwarmayar tabbatuwar buduwar kamfaninsa ap lagos
kwanaki uku da suka wuce,sai ya zabi tsaiwa a abujan don ya sanya ido game da
gudanarwar kamfanin koda na sati guda ne kafin ya koma bakin nasa ayyukan da
suma a yanzu suke buqatar hankalinsa.
Farin
boxer ne a jikinsa da wata cotton shirt me gajeran hannu wanda ta bayyana
ginuwar muscles na jikinsa,zubi da qirar qarfin da yake da ita.
Tataccen
natural ruwan blood orange ne a gabansa da ba'a sirka masa shi da sinadarin
komai ba kaman yadda yake dabi'arsa ce a haka. Yafison komai natural da za'a
sarrafashi da hannu,duk irin dukiyar da yake da ita amma yana sarrafa kanshi
wajen sanin abinda zaici,wannan ya sanya yake da wata irin cikakkiyar lafiya.
Wayoyin
dake gabansa ya sake maida idanunsa akai,ya sake miqa hannu ya dauki daya daga
ciki yana jujjuyata. Ba komai a ciki,baiga kuma komai ba. Dayar number maamah
dince kawai akai,ba contact ko daya,kaman yadda ba massages a ciki,duk wani
social app dake kai baya aiki ba'a budeshi ba,kamar yadda daya wayar take
itama. Ba Facebook ba insta ba tiktok,ko watsapp babu duk da yana zaton an taba
amfani dashi a kanta an rufe ne. Yanason ya zurfafa binciken sama da haka,amma
sai wani sashe na zuciyarsa ya tunasar dashi haramcin zurfafa bincike akan dan
adam......amma su ya halatta ya bincikesu har haka?,bayason maamah taci gaba da
jefa qafafunta cikin halaka.....dole uwa uwa ce.....mutum daya ce duk duniya ke
amsa wannan sunan......kamar yadda yayi imani yarinyar sai ya karanta mata
menene rayuwa kafin ya sakar mata qofofin 'yanci ta yadda ba zata sake zama
guba ga kowa ba.
Maida
wayar yayi ya ajiye,yana jin kamar zuwa yanzu ya kamata ya wuce gida hakanan ko
don hankalin anni ya kwanta. Ya fahimci kamar tana zargin bai taho da yarinyar
ba,amma da yake gwanar kawaici ce ita bata ce masa komai a kai ba. Ya sani ma
inda farouq yana nan zuwa yanzu da tuni ya tona mishi asiri,sai Allah yasa suka
shiga wata seminar kwata kwata bashi da lokacin kanshi.
Wayarsa ya
dauko ya lalubi saddiq
"Kana ina ne?" Kanshi yadan shafa cikin jin shakka
da nauyinsa
"Katamfe extension" Ya amsa masa yana addu'an kada
ya masa fada. Bayajin doguwar magana a kansa sosai,hasalima wata kasala ke
damunsa,ruwan dumi yakeso yasha ya sake kwanciya,don haka kawai ya bashi saqon
a dunqule
"Kayi magana da team su shirya flight,gobe zamu wuce
gida"
"Okay in sha Allah" Ya amsashi yana jin dadin
yadda bai matsa masa ba bare ya sanyashi baro soyayyar da yake raino a lokacin.
Wayar ya
mayar aljihun boxer din nasa,sannan ya dauke sauran kayayyakinsa da suke wajen
ya fara saukowa daga farfajiyar dake a matsakaicin tsaho,shi ba upstairs ba shi
ba qasa ba,amma lallai saiya biyo ta cikin dab da qofar parlor sannan ya shiga
parlor din ya wuce duk inda zaije.
Sam
hankalinsa ba'a wajen yake ba sanda yake saukowar,cikin wani irin mamaki qofar
parlor din ta bude sannan ta bayyana gaba dayanta cikin ba zata.
Saura
kadan ya hada jiki da ita,don ta shigo ne da wani irin zafin nama,banda shima
me zafin namar ne yaja baya da sauri da ba abinda zai hana jikkunansu haduwa
guri guda.
Cikin
second biyu ya maido hankalinsa jikinsa,suka fara yiwa juna kallon kallo.
Fareeda,d'iya ga ambassador din nigeria a qasar china. Matashiyar da
duniya ke gara mata fiye da yadda takeso,ta samu gata.....ta samu ilimi.....ta
mallaki kyau......tana da tsananin wayewar da bata barinta fayyace daidai a
addininta da ba daidai ba.......wayewar dake haska mata komai ya yiwa ranta
dadi.....komai ranta keso daidai ne,wayewar da gatan da sukayi mata jagora tare
da nuna mata kome takeso lallai zata sameshi ta kowacce hanya.
Doguwa ce
fara sannan kuma siririya,wadda ke tattalin jikinta da amfani da mayuka da kuma
supplement masu tsananin aji da tsada ba tare data bari zallar hutun da take
ciki ya zama jagoran gyaruwar komai nata ba. Zai wahala ka kalleta ka kirata da
mummuna kai tsaye......saidai bata cikin sahun kyawawan da kallo daya zai sanya
ka gamsu kyakkyawa ce,tana mataki na kyau a middle class....duk da tana kai
kanta high class a koda yaushe tana ganin ta cancanta da aje kanta a can.
Ta jima
tana jin sunan muhammad fu'ad jadda yana gilmawa kunnuwanta.....wani lokaci
daga bakin manyan friends dinta yaran gata irinta,wani lokaci kuma daga bakin
mahaifinta. Saidai ko sau daya hakan bai taba jan hankalinta ba,saboda tana da
wata izza akan namiji da saidai ya nemeta,don ta hada komai da take ganin babu
kalar d'a namijin da bata zarce masa ba......in fact tana tunanin ma ita har
yanzu cikin wannan duniyar da muke ciki babu kalar mijinta. Sau tari idan sunan
ya gilma mata kawai tana surantashi kamar sauran alhazawan masu kudin dake
hauka a kanta,masu shekaru,kai duka furfura ko kuma furfurar ta fara
ketowa,masu qiba da ajiyayyen tumbi,masu matan aure uku hudu da tarin 'ya'ya.
Bisa
rakiyar tilas data yiwa mahaifinta nigeria don zuwa bikin bude company din
JADDA SPARKLE WORLD daga nan su qarasa garinsu gaisuwar mutuwar qanin
mahaifinsa da ya kusa cimma wata uku da rasuwar amma bai samu zuwa ba. Kafaffe
kuma tsayayyen yaya ga kakansu qwaya daya daga rage shi ya zuba bala'i akan
fareeda,sam yarinyar ba wanda ta sani a cikin su kaf,saboda rabonta da garin
tun batafi shekara biyar ba a duniya,basa qaunar zuwa kwata kwata,wannan ya
sanya mahaifinta ambassador khaleed mustapha ya tilasta mata saboda rufe bakin
mutane.
A karon
farko da sanarwar bayyanar me kamfanin kan dandamalin jawabi ta ratsa
microphone din,ta daga kanta daga kan wayarta da take qoqarin posting hotunanta
a shafukanta,ta kuma saukesu akan muhammad fu'ad dake tsaye gaban abun magana
yana daidaitashi yadda zai dace da bakinsa.
Wata
lafiyayyar suit ce a jikinsa data tsone idon duk mutumin dake zaune a wajen.
Suit din da musamman aka sarrafata tun daga qasar Italy saboda rana irin
wannan. Ta sake fidda tsahonsa da murjewar jikinsa da wani irin mahaukacin
kwarjini da ya zame masa garkuwa wajen karya maqiya da abokan gabarsa.
Idanunsan nan masu wani irin kyau da bata taba ganin irinsu ba suna yawo saman
fuskokin tarin al'ummar da sukazo wajen saboda shi yayi cikakakkiyar sallamar
da duk wanda ya sanshi yasan wata abace da baya tsallakewa yinta ako ina koda
wanne irin mutane ne a gabansa,ba ruwansa da banbancin addini qabila ko kuma
yare.....ako yaushe yana yin abinda xai ci gaba da tuna masa....zai kuma ci
gaba da bayyanawa ko waye suke tare cewa SHI MUSULMI NE.
Sanda ya
fara jawabin taron da wani irin tataccen turanci da lanqwashewar harshen da
zaka rantse cikin fadar queen Elizabeth aka haifeshi sai dataji kowacce gaba ta
jikinta ta saki. Wani irin abu da bata taba ji akan kowa ba ya soma bin sassan
gudanar jini na jikinta yana aika saqo wa zuciyarta,wanda kafin ya kammala
bayanansa ya sauka gaba daya ya wuce da nutsuwarta dama zuciyarta gaba daya.
Ta
fahimci akwai ire irenta da yawa a wajen bayan tashin taron,saidai ba alamun
samun fuska ko dama daga wajen kowacce diya mace,wannan dalilin ya sanya tabi
ta hanyar mahaifinta.
Ta samu
damar gaisawa dashi,saidai abu na farko daya sanyaya mata jiki hannu data bashi
da nufin suyi hand shaking kamar yadda yake gaisawa da kowa,sai ya jefa mata
wani irin kallo ya maida hankalinsa ga wani abu na daban.
Bata
haqura ba sai data sanya mahaifinta ya nema ganawa dashi a masaukinsa dake
banana island kafin yabar lagos kenan,a nan ta fito kanta tsaye ta gaya masa
abinda ke dauke dashi,amma sai ya saki wani murmushi daya qarasa qona mata
ruwan jiki gaba daya,ya kuma bata saqon daya kusa tashin kanta a aiki.
"Am so sorry kinji....ni bana soyayya.....infact ba
time na ire iren wadannan shirmen,ina fata kema zaki maida hankalinki akan
karatunki okay?" Gaba daya shirme ya dauki abun,yadda ya tsaya ya mata
maganar ma ta tabbatar albarkacin mahaifinta taci. Still bata jin zata iya
haqura dashi,ta samu daman ganinsa a karo na biyu ba tare da yasan ita bace. A
nan ta gane ainihin wayeshi,ya fiddo mata true color dinsa,abinda ya birkitata
kenan,batayi qasa a gwiwa ba ta bashi tabbacin bata taba neman abu ta rasa
ba.....a kansa kuma ba zata fara ba,zatayi duk yadda zatayi don ganin ta
mallaki soyayyarsa ta kuma mallakeshi.....ta kuma ci masa alwashin duk inda ya
shiga tana biye dashi har sai randa ta samu abinda takeso.
Ko a
yanzun zare rafkeken sunglasses din idanunta tayi tana qoqarin sakar masa
murmushi,yayin da ransa ya motsu da zummar baci amma kuma mamaki ya mamaye
wannan gurbin.
"May i ask who's let you in?" Yayi maganar yana
qoqarin danne fushinsa. Murmushi ta kuma saki tana rolling idanunta cikin salon
jan hankali
"As your guest,i think you should welcome me
first" Ta furta tana narke murya. Baya ya sake ja kadan ganin tana qara
takowa inda yake
"What brings you here?" Wannan karon ya fada adan
tsaurare,alamun bacin ransa suna fitowa fili. Kallonsa tayi a kaikaice tana
sake yadda da maganganun da aka gaya mata a kansa. He's not a womanizer,he's
not into playing games with women......ta yaya kike tunanin zakiyi winning
kansa?" . Ta tuna da maganar da daya daga cikin qawayenta suka mata. A
lokacin ta dauki zancan nata ne a matsayin kishi,saboda samun cikakakkiyar dama
da tayi da take ganin zata kawoshi cikin rayuwarta,damar da mata da yawa suke
nema basu samu ba.
"Am here for you fu'ad.....please ka bani gurin zama
tukunna mu tattauna a nutse"
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 28
28
"Get
out of my house" Ya fadi ba alamun fara'a ko walwala a tattare dashi.
Wannan fuskar me cike da miskilanci,wadda zai wahala kaga wani abu me kama da
murmushi a kanta ta sake dinkewa tsaf
"Please mana" Ta fada da wata irin shagwaba tana
hade hannayenta waje daya
"Zaki fita ko sai na kira masu fiddamin dake?" Ya
kuma fada yana ware mata idanunsa da suke da wani irin kyau me jan hankali
wanda suka sake fusgar hankalinta.
Bai ankara
ba bai kuma taba kawo haka zata kasance ba ya tsinceta ta fada cikin faffadan
qirjinsa tana neman kai masa kyakkyawar runguma. Baiyi wata wata ba bai kuma
sake bata koda minti biyar a jikinsa ya yakiceta ya watsar gefe. Wani irin
tafasa zuciyarsa keyi,wanna shine karo na farko da wata mace ta rungumeshi irin
haka.
"Tashi ki fita thn ranki bai qarasa baci
ba,stupid!" Ya fadi a tsawace yana nuna mata qofa. Miqewa tayi tana kade
jikinta,duk da ba wani baci tayi ko datti ba saboda gurin fes yake da wata irin
tsafta da take ta'ammali da ita a komai nasa,cikin borin kunya tace
"Yakice ni daga jikinka baya nufin fidda soyayyarka
daga zuciyata......zan tafi,amma kuma zan dawo,zan kuma ci gaba da kasancewa
dakai,zan zama cikin kowanne motsi naka har sai na cimma nasara na samu abinda
nakeso". Daga wannan ta dauki jakarta tana nufar qofa da dan sauri,qasan
zuciyarta da tsoron yadda mode dinsa ya koma,amma abinda takeji a kansa ya
danne komai.
Iska me
zafi ya furzar yana shafa sumarsa da tafin hannunsa. Kwata kwata yaqi jinin
mace maras jan aji........yana matuqar son mace me aji.....mace me dan wani
tasiri kadan na girman kai,wanda girman kai a wajen mace yana alamta alamu na
kamun kai,girman kai yana cikin siffar da akeson mace dashi.....amma a
mu'amalarta da maza kamar haka. Komawa yayi saman kujera ya zauna yana fidda
numfashi me huci. Yana daya daga cikin abinda yasa ya rasa interest akan
mata,yana daya daga cikin abinda ya sanya har yanzu ya kasa gano macen da zata
sace zuciyarsa kwata kwata.......saboda yanzun mata yana hangen sun rasa
dabi'un nan guda biyu zuwa uku masu tsananin tsada fiye da diamond...... Masu
tsananin zame musu ado fiye da adon gold a jikinsu,wato KUNYA da kuma KAMUN
KAI.
Wayarsa ya
dauka ya kira abdus_samad yana qoqarin danne fushinsa,bugu daya tak ya daga
"Who gave her permission to enter?" Tambayar da
yayi kenan a taqaice.
"Am sir......" Ya fada adan daburce don jikinsa
yana bashi laifi yayi
"Did someone invite her in?" Tambayar ta qarasa
daburtashi gaba daya,ya kuma fahimci laifi yayi.
"Am sorry sir......am sorry,naga diyan
ambassador....."
"Keep quite......are you out of your sense?,don diyar
ambassador ce?,meye alaqana da ita?,dama akwai wannan tsarin na ku barmin
mutane suna shigomin guri anyhow?,meye amfaninku idan haka zata ci gaba da
kasancewa?" Ya kasa magana kawai sai haquri da yake faman jera bashi,don
tunda yake dashi irin fada irin haka bai taba hadasu dashi ba. Bai jira cewarsa
ba ya yanke wayar yana ajiye wani tsaki. Ji yayi sam zaman parlor din ya
isheshi,bama parlor din bama,abujan gaba daya,ya miqe yana wucewa bedroom
dinsa,cikin jikinsa gaba daya yana jin kamar ya yanke inda nata jikin ya
tabashi. Bacin rai sosai yakeji a qirjinsa,duk wani nau'i na sabo ya
tsaneshi,sai yau gashi ta sakashi abinda yake matuqar gudu da kaucewa. Yasha
shiga harkoki da abubuwan dake cakude da mata,amma yanayin kamewarsa da kuma
miskilancinsa yasa suke tsoronsa matuqa,ba wadda take zuwa masa da zancan
banza,tun daga secondary school university da tafiyansa service,duka Allah ya
tsareshi ya kuma tsare imaninsa,duk da
irin farkamakin da yake samu.
Yana gaban
wardrobe yana sauya kayan jikinsa yaji ana masa knocking,muryarsa can qasa da
sauran tasirin bacin rai a ciki ya tambaya
"Waye?"
"Saddiq ne hamma".
"Come in" Ya bashi dama lokacin da yake sanya
rigar jikinsa.
Yanayin
yadda yaji sadiq din ya shigo ya tilasta juyawa yana duban fuskarsa. Sai yabi
hannunsa da kallo wanda yake dauke da system
"What's wrong with you?" Ya tambayeshi yana
tsareshi da idanu. Kasa amsa masa yayi,sai daya samu waje ya zauna daga saman
carpet ya ajjiye system din sannan yace
"We got the announcement........ana zargin an samu
muggan qwayoyi cikin jewelry company dinmu". Ya qarasa fada yana buda masa
saqonnin da suka samu daga dukkan kafofin dake da alaqa dasu daya nabin daya.
Hannuwansa
kawai ya zube cikin aljihunsa yana kallon system din. Yanajin wani yanayi yana
zagayashi,hankalinsa nason tashi amma yana gayawa kansa da kansa
"All is well" A irin wannan lokutan na
tsanani,lokutan da jarabawa irin wannan ke tunkararsa rauni yakan rugo da gudu
ya mamayeshi.....a irin wannan lokacin yakanji yana da buqatar wata halittar a
gefe da zata same masa qwarin gwiwa......banda qannensa banda farouq da yawan
daukan mas'alolinsa yake ganin suna masa yawa,ya kamata ya rage masa daukan
matsalolinsa haka.....tun daga quruciya kunnuwan farouq zuciyarsa dama gangar
jikinsa suke fama da matsalolinsa.....zuwa yanzu ya kamata ace ya huta.....anni,wata
irin rumfa ce sha shirgi ita da abban gaba daya,ya kamata kunnuwansu su samu
sassaucin jin damuwoyinsu a yanzu haka da girma yazowa kowannensu.......akwai
personal mutum da yake buqata daga gefe da zai zauna a wannan matsayin.
"Hamma wannan saqonnin barazanar basa da alaqa da
faruwar wannan abun kuwa?". Kai yake jinjinawa sanda yake takawa a hankali
yana matsawa daga wajen
"Definitely......but I'll make it clear im not
Intimidated" Ya fada da wani irin qwarin gwiwa yana dora top saman rigar
t.shirt din jikinsa.
"Let's go.....ka kira William kace ya samemu a
can....."
"Amma hamma.....flight isn't ready"
"We'll take the road" Ya furta yana riga saddiq
yin gaba.
Kafin
sukai ga isa lagos ya gama shirya dukkan abinda ya kamata ace ya tsara din.
Suna dab da shiga garin har a sannan idanunshi biyu,ko daya baiji wani buqatar
bacci ko kuma ya huta ba. Yaja qaramin tsaki sanda suka dauki hanyar
kamfanonin. Ya fahimci ita kalmar SO ko a meye ta shiga wahala ce kawai da
walagigi da ruhi,wannan ya sanya banda soyayyar family dinsa bai taba saka
soyayyar komai cikin ranshi ba,sai yanzu gashi kwatsam......kamfanin ya shiga
ransa har baisan adadi ba......gashi kuma ya zama abu na farko da son nasa
keson zame masa wahala,da wannan ya qara ji a zuciyarsa lallai tabbas ya kamata
ya nisanci soyayya iyakar iyawarsa.
Duk da
sun nuna matsayinsa yafi ya taso da kansa amma ya kauda wannan. Ya karbi duk
wani bincike nasu ya dora da nashi. Da gaske an samu wani dan qaramin store
cikin kamfaninsa cike da qwayoyin da inda wani me qaramin matsayinne ba shakka
sai ya tafi dauri gidan gyaran hali,amma da yake a nigeria muke.....kuma kura
ma tasan gidan me babban sanda sai ya zamana dakatar da kamfanin kawai akayi
sai bincike ya kammala.
Bayajin
zai iya bari maqiyansa su kalli faduwarsa da wurwuri haka,wannan ya qara masa
qaimin shiga binciken da kansa gadan gadan.
Ya
fuskanci tarin abubuwa masu yawa cikin case din,wannna ya qara masa qaimi,bai
kuma yarda yayi handling case din ma kowa ba.
Duka da
bacci da cin abincinsa qalilan ne. Amintattun experts investigators din daya
aminta dasu kawai suke aiki ka'in da na'in,ba dare ba rana. Bai gayawa kowa
abinda ake ciki ba banda anni da yace ta tayashi da addu'a,akwai matsala amma
qarama ce ba wata babba ba,haka ya gayawa abba da farouq. Saidai sam hankalin
farouq ya gaza kwanciya,don yana dawowa daga seminar dinsa ya biyo bayasa a
washegari.
Yadda ya
ganshi ya tabbatar abun ba qarami bane,don ya nuna har a jikinsa don kuwa ya
dan rame kadan saboda rashin bawa abinci muhimmanci. Ya sake sallamawa da miqa
wuya kan muhamnadun yaci sunan muhammad din,namijin gaske ne da gaske......daga
yadda ya tunkari komai yake gabatar dashi da dukka qarfin gwiwarsa da
jarumtarsa kadai ya qara tabbatarwa NAMIJIN DUNIYA NE.
Yanata
qoqarin dodging komai farouq ya dubeshi.
"4weeks without me dude.......have you noticed your
appearance?.....check your reflection" Ya fada yana kama hannunsa zuwa
gaban concealed mirror din dake wajen.
Ya kalli
fuskar tasa kaman yadda farouq ya buqata,sai ya saki murmushi ya miqa hannu
yana shafa fuskarsa.
"Chill out mana dude,nayi settling komai,It's come to
an end......My evidence supports my claim....and it speaks for itself,all the
fact are on my side,na gama komai gobe zasu saki kamfanin.....abu daya ya rage
na gano shine,who's pulling the string" Hannunsa farouq ya riqo yana
girmama qarfin jarumtarsa,yana jin inama ya samu irin wannan jarumtar tasa
"We'll leave no stone unturned,we'll find him
together" Rungume kafadar farouq yayi,yana sake jin qaunarsa cikin ransa.
A gaba ya
sakashi ranar,yasa ya ajiye komai tunda bincike ya kammala. Da kansa ya zauna
ya masa gyaran fuska da sauran wasu abubuwa,yana masa suna hira yana bashi
labarin nasa progress din da aka samu bayan seminar din. Duk duniya da farouq
kadai yake irin wannan sakewar. Ranar duka tare suka qarar da ita,sai dare
sannan kowa ya wuce makwancinsa,da zummar gobe da kamfani yaci gaba da aiki
jibi tabbas dole su wuce gida,wanda sam bai fahimci meye ma'anar matsawar da
farouq din yayi bama.
Ya dauki
wayar da zummar kashewa ya tarar da tarin miscalls da kuma saqonni,guda daya ya
duba ya fahimci wacece. Fareeda ce....saqo bayan saqo kamar bata da wani sauran
aikinyi sai tura masa da saqon.
"How did she get ahold of my number?" Ya tambayi
kansa da kansa. Tunawa da yayi da mahaifinta ya sauqaqe masa wahala,yasan samun
numbersa zai zame mata wani abu kenan me sauqi. Tsaki yaja ba tare da yabi
takai ba,ya kashe wayar ya kwanta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 29
29
★Cikin
kwanakin har ruwan jikinta takeji kaman ya qare saboda tsabar wani irin kadaici
da dumbin tunani da yake cike a kanta. Sati hudu cur tana a cikin gidan......ba
motsin kowa ba gilmawar kowa,ba hira da kowa,ba waya,daga ita sai tv sai karen
gidan dake haushi nesa da muhallinta. Ada ko parlor din bata fitowa tana qunshe
a daki,daga bisani ta fahimci depression na loneliness zai iya kamata,don haka
da kadan da kadan ta fara fitowa tana zama.
Saidai
daga zaman sai bacci,sai wanka sai wata kwanciyar. Gyaran gidan kansa bai wani
dameta ba,don tana ganin ba wani muhalli bane da zata damu kanta a
kansa,hasalima a nata ganin waje ne da lokaci kawai take jira ta barshi. Abu
biyu take gyarawa,bedroom dinta sai kitchen din da ba wani abun arziqi take
dafawa ba. Tun ranar da tayi abincin safen nan rabonta da tayi wani cikakken
abinci ta sawa cikinta,iyakar yunwa idan ta ciyota ta soya qwai guda biyu...
Kota dafa indomie guda daya kota soya potatoes taci shikenan.
A
kwanakin tana jin yadda qirjinta yake riqewa amma taqi damuwa da wannan bare
takai hankalinta kai,abu daya kawai take jira ya dawo,tayi duk yadda zatayi ta
cika aikin maamah ta samu freedom. Ta sani tana da wata fitinanniyar ulcer data
kusa sanyata tabi bayan mahaifi da mahaifiyarta bayan rasuwar ummensu. Ulcer
data samo asali daga matsiyaciyar yunwar da tayi mugun horasu,takaita matakin
da take xubda aman jini. Ta jima rabon data tashi,tunda ta samu sassaucin
rayuwa suke iya ci su qoshi,amma a kwanakin nan da take bata alamu taqi maida
hankalinta sam sam.
★"Alhamdulillah" Shine abinda ya furta lokacin da ya fito daga
toilet wanda ya barshi wata guda cur kenan.
Shirya
kansa ya fara yi cikin butter milk color pyjamas yana tunanin kiran me sunan
malam da ameh gobe kowa ya dora aikinsa a inda ya tsaya. Sam har ga Allah ya
sha'afa da ita,abinda ya sameshi ya shafe abubuwa da yawa a kansa.
Gidan
duka ya masa datti a yadda yake tsantseni da tsananin tsafta,ya kammala shirin
nasa sai ya kasa saukowa saboda gajiya,ya bude freezer dinsa dake dining area
dinsa na sama yana fatan samun wani abun.
Wuta ce
24/7 da kome zaka ajjiye a fridge din
zaka sameshi fresh. Damammiyar fura ya ciro wadda ba komai cikinta daga nono
din sai furar da aka markadasu suka hade jikinsu sosai. Furar daya samu ta masa
daidai,don abace dame relaxing jiki da bada bacci me kyau da daddare saboda
sinadaran da gero ke dauke dashi. Ta masa sanyi,baya kuma shan abu me sanyi
sosai har haka,wannan ya sanya ya ajiyeta ya koma ya kunna tv don ya rage
mintunan da zaiyi jiran furar.
Kadan
kadan takejin kamar wani baqon sauti cikin gidan sanda take baro kitchen inda
ta soya qwai guda biyu,tana taraddadin ci ma saboda maiqon dake jiki amma kuma
batajin tana da wani abinciii bayan shi.
Fargaba
taji tana cikata,wani irin matsanancin tsoro ya saukar mata. Sound ne tabbas
wanda bata tantance na meye ba. To ko haurowa gidan akayi?,ko wani ne ya shigo
ciki ya boye ba tare da sanin securities din ba?. Duka ba kalar tunanin da
batayi ba,jikinta na rawa ta qarasa dakinta ta maida qofar ta rufe tana maida
numfashi. Jin still da sound din sai tsoron yaqi barinta,ta taka da hanzari
tabi duka windows din ta kulle sannan ta dawo tsakiyar dakin ta zauna tana raba
ido tare da sauraron koma meye daga inda zai bullo.
Sai data
masa daidai sannan ya kashe tv din,ya dauketa ya hada da cup da spoon ya wuce
daki.
Sake
kasa kunnenta tayi da kyau,a yanzu ba sound din,saita lumshe ido tana qoqarin
saita nutsuwar kanta. Bata taba sanin kadaici masifa bane sai yanzu,bata taba
sanin haka yake taba ruhi da rayuwar mutum ba sai yanzu. Wasu hawaye suka biyo
ta lumsassun idanunta suka gangaro kan fuskarta. Gaba daya ta koma wata raguwa
a kwanakin,zuciyarta kwata kwata ba wannan qwarin da tsaurin sai wani irin
rauni da ya sake cikata,sai kawai ta kifa kanta saman pillow din ta saki
siririn kuka,fried egg din da bata iya ci ba kenan.
★Bacci yayi
sosai wanda da qyar ya tashi sallar asuba wadda duk tsanani zai wahala ta kubce
masa. Koda ya koma yunwa ce ta tadashi,cikinsa gaba daya kamar an masa yasa.
Yadan yamutsa fuska kadan yana tunanin me zaici?. Inda ameh yana nan ya
tabbatar yanzun da yake qarfe sha biyu na rana ya gama breakfast yana jiran
umarnin hada lunch da za'a kai company ko kuma ya jirayi zuwan dafa dinner.
Brush ya
fara shiga yayi sannan ya fito,ya dauki wayarsa guda daya a ciki ya kunnata.
Kamar jira akeyi sabbin saqonni suka shiga turereniyar shigowa,baibi takai ba
ya lalubi number ameh,bai sameshi ba,yaja dan qaramin tsaki,wala'alla ya lalata
wayarsa kaman yadda ya saba,waya bata fiya dadewa a hannunsa ba zakaji ta fadi
ko kuma ta lalace,wannan dalilin ya sanya ameh din kansa baida cikakken number
boss din nasa,wanda dama kusan duk wanda ya mallaki number wayarsa ya cancanta
kuma yana da connection dashi nakai tsaye irinsu ameh din dame sunan malam.
Amna ya
kira,bugu biyu ta daga.
"Hamma......barka da dawowa"
"Barka kade amna"
"Good morning hamma......ya hanya ya gajiya?"
"Alhamdulillah......ya makaranta?,kun fara shiga
lectures?". Kai ta gyada
"Mun fara hamma......ba dadi hamma ba
supporter.......BB farouq yace na cika shirme......ya saddiq tsokanana yake
koda kuna nan......nayi missing ya musaddiq har yanzu bai dawo ba......please
hamma kace ya dawo haka?" Ta qarasa maganar a shagwabe.
"Zai dawo soon" Ya furta badon yana nufin ya
barshi ya dawo nan kusa ba. Tun tuni ya aike da musaddiq din wani aiki don ya
nisantashi da maamah,bayason zamansa a nan ya tabbatar idan yana nan watarana
maamah zataci galaba a kansa. Hakanan baison fitowa kai tsaye ya nunawa
musaddiq komai akan maamah
"Allah ya dawo dashi lafiya....."
"Ameeen amneee......ki hadani da anni idan kin
fito.....ki gayawa ameh lallai lallai yazo yau"
"In sha Allah hamma" Tana shirin tambayarsa
sabreen ya ajiye wayar.....saita bari kawai ta shigo gidan da kanta tayi mata
barka da dawowa.
Yadda taji
yunwa na kama mata cikinta da gaske ya sanyata miqewa bisa dole. Yau kam sanye
take da silk sleeping dress maroon color,riga ce iya cinya da wandonta dogo har
qasa,saidai kuma tana da dan budadden wuya kadan. Duk da ramewa data danyi
hakan bai hana rigar mata kyau ba,ta kuma zauna cif a jikinta. Jikinta ta jawo
ta sauka daga saman gadon,tasa hannu ta tattare gashin kanta waje daya a
qeyarta,ta taka a haka zuwa gaban madubi,ta jawo dan madaidaicin jewelry
organizer din dake saman madubi ta budeshi,hair clip guda daya babba ta
maqaleshi sannan ta samu vintage scarf ta daure kanta,wanda jelarsa dankwalin
ta zauka kafadar hagu da damanta. Akwai socks a qafarta,wadda sanyin ac din
gidan ya sanya dole take sakata saboda yadda marbles din yake daukan sanyi
sosai,kwata kwata batasan ya ake controlling duka Airconditoners din ba bare ta
daidaita shi,hakanan kawai take haquri. Sauqinta daya ana cikin yanayi na zafin
farkon kasancewar damuna,banda haka ta tabbatar ba qaramar illa zatayi mata ba.
A nutse ta
murda qofar,ta fara leqo da kanta tukunna tana tuna motsin da taji jiya,sai
data tabbatar shuru wajen yake ba alamun komai sannan ta fara fitowa a darare
tana sanda hannunta dauke da plate din soyayyen qwan.
Yau haka
nan ya sauko da qafafunsa bai sanya takalmi ba. Fara tas din qafarsa dake da
dogayen yatsu yake takawa a nutse yana sauka daga stairs din hankalinsa yana
kan wayar da yake amsawa ta William,yanason sake tabbatar da komai na company
din yana tafiya lafiya lau.
Sanda ta
buda qofar da zata sadata da parlor din farko ta sanya qafarta lokacin ya kusa
da stairs din qarshe,wannan ya bashi damar ganin wulgawar mutum ba tare daya
tantance waye ba.
Dan
tsam yayi da ransa sai kuma yadan qara hanzarin saukowar don yaga waye ya gilma
din,sam zuciyarsa na masa nisa da tuna tana cikin gidan.
Da wani
irin sassarfa take qoqarin fita a falon ta sada kanta da falo na biyu na gidan
ta boye kanta a kitchen. Murya takeji sosai tana sake kusanto inda take,tsoro
ya sake cikata,kenan wani ne ya kwana a gidan akayi mata kwanton bauna?,har sai
da akaji fitowarta sannan ya bayyana?. Ta shiga uku,su waye suka shigo?,abu
daya ta sani ko zasu yankata su cinye ba wanda yasan sun shigo saboda tazarar
dake tsakaninta da security din gidan.
Tana
saurin isa ga kitchen don ta buya yana sassarfar shan gaban macen daya gani.
Kusan dukansu sai abun yazo musu lokaci guda,yana dab da cimmata tunaninsa ya
dawo kansa. Ashe yabar wata cikin gida......akwai yarinyar dake rayuwa cikin
gidan,wannan tunanin ya sanyashi tsaiwa cak,tsaiwar tasa ta bata damar wucewa
kitchen din cikin matuqar sauri ta maida qofar ta kulle harda murza key.
Qofar yabi da
kallo yana zare wayar daga kunnensa. Mamaki kadan yana kamashi,anya
qwaqwalwarta lafiya qalau take kuwa?. A nutse ya xura wayar a aljuhunsa yana
dage kafadunsa cikin I don't care manner,sai kuma ya koma saman daya daga cikin
kujerun ya zauna yana canza channel,kadan kadan kuma yana kallon falon. Ba wani
tarkace bane ko wani abu a ciki,amma tsaftarsa bata masa ba. Ya saba duk inda
ya wurga idanunsa ya ganshi fes yana qyalli da daukan idanu,amma a nan din
idanunsa suna iya ganin qura a wasu guraren. Qaramin tsaki yaja can qasan
ranshi yana fadin bazai dauki qazanta ba. Minti biyar yana jira yaga ta bude
qofan amma ba alama,yunwa yakeji sosai,yana buqatar wani abu me nauyi da zai
sanyawa cikinsa. Baya wasa sam da cikinsa,mutum ne me son lafiyayyen abinci
musamman wanda ya dace da tsarinsa.
Miqewa
yayi ya taka a hankali ya isa bakin kitchen din,har a sannan tana maqale bayan
qofar tana tunanin yadda za'a yi ta kubuta daga hannun mutumin da batasan yadda
akayi ya shigo gidan ba. Knocking din daya fara yi a hankali ya sake
gigitata,ta qanqame jikinta guri daya tana runtse idanunta hankali a tashe. Sau
biyar yana bugawar ba wani motsinta,ranshi ya sake baci,sai kawai yabar wajen
yana takawa a hankali ya nufi wata qofa daban da zata sadashi da kitchen din ta
baya.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 30
30
Jin an dakata
da bugun ya sanyata sulalewa a wajen tana dafe qirjinta. Bata ankara ba hawaye
ya balle mata,dama ta yaya za'a barta a gida irin wannan ita daya idan ba dama
anyi shirin salwantar da rayuwarta bane da gangan. Tunda take a rayuwarta bata
taba sanin tsoro na ainihi irin wannan ba.
Qofar
data hanga ya sanya taji relief,ta goge fuskarta ta mmiqe a hankali cikin sanda
tana nufar qofar ko zata samu wata hanya da zata fice daga cikin gidan zuwa
bakin gate.
Tana miqa
hannunta tana riqe handle din da zummar bude qofar daidai lokacin shima ya bude
qofar da dan zafin nama,abinda ya sanyata ta biyo qofar takuma yi kyakkyawan
masauki a jikinsa.
Dif shi
da ita wuta ta dauke musu,ita gaba daya tayi mutuwar tsaye je zuciyarta na wani
mahaukacin bugu cikin saddaqarwa kan ta shiga hannun koma waye......yayin da
shi kuma ba zatar fadowarta jikinsa ya sanya komai ya tsaye masa can na wucin
gadi.
Hannunsa
ya sanya ya janyeta gefe yana hade rai da wani mugun miskilanci,ya hade girar
sama data qasa yana dubanta sanda ta samu ta dafe kitchen cabinet din don ya
taimaka wajen tsaiwa
"What's this?" Ya furta a dake yana hade rai. Can
qasan ransa yana jin haushi haushi yana saukar masa. Da biyu ta fada jikinsa ko
meye?,ko tsabar sabawa da hada jiki da wasu ne?,a yanzun an turketa kusan wata
guda ba tare da d'a namiji ba ta kasa daurewa?.
"Ya kamata ki saita kanki,nan din ba irin sauran
guraren da kika saba rayuwa bane....ki koyi controlling feelings dinki"
Abinda yace da ita kenan yana takawa zuwa gaba hadi da miqa hannunshi yana bude
drawers din sama.
Sosai ta
tattara dukka dauriyarta da nutsuwarta ta dawo da ita gangar jikinta tana ta
kokawar hadiye tsoronta. Wani irin takaici ya
kamata bayan data fuskanci shine. Ya akayi tayi gangancin gaza gane
shine ya dawo?,bacin rai ya hanata komai,sai kawai ta juya tana takawa zuwa
qofar data kulleta da hannunta ta fara bude key din da wani irin zafin nama.
Duk da a
rude take amma tasan sau biyu ta murza key din,yanzun ma sau biyun ta bude amma
kuma data tura sai qofar taqi budewa. Sake murzawa tayi daya biyu har sau uku
amma ba alamar qofar zata budu. Wasa wasa haka ta sake gwadawa amma jiya i
yau,sai taji gudun zuciyarta na qara daduwa,don burinta kawai shine ta fita a
kitchen din.
Tayi iya
duka qoqarinta amma ko gezau qofan baiyi ba,wannan ya sanya duk wani karsashi
nata ya sulale,ta zame hannunta daga jikin qofar zuciyarta fal da tunanin ta
yaya zata juya tabi ta daya qofar bayan yana kai kawo a kitchen din yana
harkokinsa?.
Duk wani
motsi nata yana ankare dashi,har yadda ta dinga qoqarin bude qofar amma taqi
koda motsi. Idanunshi jifa jifa a kanta sanda yake kai kawo tsakanin store din
yana duba abinda zai iya sarrafawa da kuma dawowarsa kitchen din ya fara
marinating kifi da zummar ya gasa shi,abinda ya manta rabonsa da yayi. Ya
kammala cikin sauqi,saboda akwai komai kawai zubawa zaiyi ya saka a oven ya
saita masa lokaci,sai ya saka din ya saita time ya koma ya jingina da kitchen
cabinet din yana harde hannunsa a qirji yana jiran time ya cika yayin da yake
sauraren voice note din da ya tarar daga William.
Da fari
baiko kalli sashenta ba koda sau daya kuwa,amma a hankali sanda hankalinsa yayi
nisa da sauraren voice din sai kunnuwansa suka sauko masa raguwar sautin
yunqurin bude qofar da taketa yi.
A nutse
ya daga idanun nan nashi dake da wani irin shape da yanayi me daukan hankali ya
saukesu a bayanta daya fidda cikakken shape dinta saboda yadda kayan suka zauna
mata cif da cif,daga kafafunta zuwa qugunta yayin da qugun zuwa cinyoyinta suka
bude sosai suka bada wani faffadan qugu da yalwatattun cinyoyi.
Vintage
scarf din dake kanta ya zame ba tare data sani ba,saidai yana maqale a
wuyanta,wannan ya sanya har clip din kanta pink color daya matse gashinta ya
rage tsahonsa da yawansa ya bayyana.
Baisan
me ya maida idanunsa saman mazaunanta ba da suka bayyana sosai saboda silk
material din dake jikinta,uwa uba kuma rigar bata qarasa rufe mata su ba.
Abinda ya fara fado masa shine hirar amna da wasu qawayenta daya taba tsinta
dake maganar maganin hips da sauran wasu hanyoyin qarawa mace hips.
"Ita dinma ba zata kubuta daga amfani dasu
ba......" Ya furta a ransa bayan da zuciyarsa ta tuna masa wacece ita?.
"Allah ne yasan maza nawa ne suka taba kai hannunsu
wajen,maza nawa ne suka taba taba wajen sukasan ya fadi da tudunsa yake"
Wani mahaukacin tsaki daya cika kitchen din yaja,wani mummunan bacin rai yana
saukar masa. Hannayensa ya saki kawai yana komawa zuwa bakin oven din yana jin
zaman kitchen din yana gundurarsa. A duk sanda ya tuna iya shekarun haihuwarta
a duniya da tayi kwata kwata na shekara ashirin da hudu cikin ta ashirin da
biyar......da kuma adadin yawan mazan da akace masa takai qasa ko kuma ta taba
mu'amala dasu,duk sai yaga ta masa baqiqirin,sai yaji wani abu ya tsaye masa a
rai idan ya kalli koda gilmawarta ne
"Idan tasan me yawan sha'awace me ya hanata ta fadi
gaskiyarta a gida ayi mata aure?" Ya sake rayawa a ransa.
Kwata
kwata baya cikin jerin mutanen dake da ra'ayin riqau akan yaransu mata na sai
sun gama karatu kafin a aurar dasu. Ya dauki izinina daga yadda yanayin
halittarshi yake......wanda hakan yana daya daga cikin abinda ya sanya ya maida
kwanyar da zata tsarta masa tunani na sha'awa a ransa cikin muguwar hidima da
sabgar da idan ba mugun qaddara ba baida time da zata dauki wannan feeling din
ta harba zuciyarsa har zuwa sassan jikinsa. Saboda kwata kwata bai shirya aure
ba,totally mata basu taba burgeshi ba.....uwa uba bai tsara tsomasu a rayuwarsa
nan kusa ba,saboda abinda yake kalla kusan dukkaninsu dukiyarka ko nasararka
suke aure.
(Kira gareku iyaye mata,a matsayinki na uwa ya kamata ki
lura da yanayin kowanne yaro da kika haifa,don dukkaninsu ke kika haifesu,don
kamanninsu daya hakan bawai yana nufin asalin halittarsu daya ba. Wani lokaci
yaro namiji zaiyita nuna sha'awar aure,amma sai a masa caaa ace ya fiya tsaurin
ido......wani lokaci yarinya na nuna wannan sai ace ta fiya rashin kunya da
tsaurin idanu,ba tare sam da duba da cewa halitta bace daga ubangiji,sai kuyi
mata mummunar fahimta,aci alwashin sai an turata jami'a,koshi yaran aci burin
zuzzurfan karatu a kansa ko kuma sai yayi kudi. Kuskure ne wannan babban,daga
namiji har mace idan aka fuskanci haka tattare dasu,idan tana da manemi
nagartacce a aurar da ita yafi alkhairi,idan namiji ne yana da halin riqe
kansa,ko kuna da wadatar riqe masa matar kafin ya qarasa zama mutum to a rufa
masa asiri ayi auren a huta. Idan ba hali ko koya musu azumin litinin da
alhamis,su lazimci karatun qur'ani,yawan tunasarwa da wa'azi,duk juyi kuma kada
a dinga barinsu suna yawan kadaicewa a daki,a kusantasu da abokai na gari,da
zarar dama ta samu kuma ayi a aurar dasu,Allah ya iya mana ya tarbiyyantar mana
ameen summa ameen).
Cikin
sa'a ya samu ya gasu,sai kawai ya sakashi duka har aluminum foil din cikin
plate,ya soma takawa yana hanyar ficewa ta daya qofar.
Har ya
kusa qofa sai ya fasa fitan,ja yayi ya tsaya sannan a hankali ya waiwayo,sai ya
ware idanunshi a kanta yanata qoqarin kaucewa kallon guraren da yake ganin bai
kamata ya kalla din ba. Cikin jikinta
taji kamar da idanunshi a kanta,tuntuni taji ya tsaya da tafiyar da yakeyi
abinda yake bata tabbacin bai fita din ba. Bata qaunar koda wanzuwarsu a waje
daya sam shi da ita. Haushinsa takeji sosai,irin haushin da ko gilmawarsa
batason gani ballantana qamshin turarensa. Cikin dakiya da jarumta ta soma
takowa da zummar gewayeshi ta fice ba tare data yarda ta kalli ko gefen da yake
tsaye ba ballantana tasan me ya tsaidashi din,tunda dai taga ya shigo ta nan
din ta tabbatar hanya ce duk da bata taba bi ta nan din ba.
Sai da tazo
daf dashi zata gotashi din,cikin ba zata ya sanya qafarshi yana blocking duk
wata hanya da zata wuce. Ta qasa ta kalli yadda yayi blocking din nata,wani abu
ya sake zuwa yayi mata tsaye a wuya,sai take jin ta dauki iya abinda zata iya
dauka daga gareshi,abun nashi kaman yanason ya qure iyakar haqurinta. Bashi da
masaniyar kakkaifar katangar qarfe da garkuwar maamah a gareta shi yasa yake
samunta a yadda ya so?,shi yasa yake samun daman juyata yadda yaga dama?,ko
yana tsammanin izzarsa da dukiyarsa da sunansa duka su suka siya masa wannan.
"Ka ban hanya zan wuce!" Ta fada adan zafafe tana
jin zuciyarta kamar zata fashe. Duka abubuwan da yayi mata basu isheshi
ba?,yanzun kuma sai ya qara da tarwatsa mata zuciya ta hanyar tsoratata?. Me
yasa dole sai ya shiga harkan rayuwarta ne?.
Hannunsa
ya goye a qirjinsa bayan ya ajiye glass dish din da hake hannunsa yana dubanta.
Kana kallon yadda Adams Apple dinsa ke sama da qasa kasan Shima nashi ran ya
fara baci. Ya sake gasgata komai a kanta,yadda kunya ke nuna qaranci a tattare
da ita. Yayi zaton zaizo ya sameta tayi laushi amma baiga alamun hakan ba.
"Excuse me?" Ta kuma fada tana kafeshi da oily
eyes dinta wanda ba kasafai ka fiya gane da qwalla a ciki ko babu ba,saboda
koda yaushe yanayinsu tamkar an diga mai ko ruwa a cikin su haka suke.
Kanta ta
maida gaba ta hade jikinta sosai da zummar rabe masa,saidai ya hanata wannan
damar,abinda ya sanyata sake tsaiwa kenan tana furzar da zazzafar iska daga
bakinta.
"Me kakeso ne?!......me kake buqata?,kome da kayi bai
isheka ba?,ka kulleni for good one month.....kayi disconnecting komai da kowa
daga gareni......yanzun kuma ka dawo kanason kasheni da tsoro?,me kake
so?" Tayi maganar zallar bacin rai yana nuna kansa a fuskarta,tana kuma
jin radadin abinda yayi matan da gaske.
"Enough.....ya isheni!" Ta sake fada tana ware
hannuwanta tare da fidda girman oily eyes dinta a kansa.
"Am not your......."
"Just stop!" Yayi maganar da muryar data ratsa har
cikin kwanyarta,ta kuma sanyata runtse idanun dole
"Am not your mate......dole kisan da wanne harshe zaki
dinga min magana!" Ya sake maimaita mata a tsawace. Ji tayi kaman kanta
bazai iya dauka ba,muryarsa tayi amsa kuwwa akunnuwanta sosai da kalar tsawar
data manta rabonta da irinta,sai kawai ta juya da zummar koma yayane ya rabeshi
ta wuce. Saidai kuma ina,yana ganin shirinta ya sanya hannu ya riqe hannunta da
zummar dawo da ita da baya.....don dole ya fara saita mata harshenta kafin
komai.
Cikin
rashin sa'a dukka maballan gaban rigar suka fara balle kansu da kansu saboda
riqon da yayi mata. Abinda ya qara yawan adadin tashin hankalinta kenan jin
iska ta fara ratsa ainihin fatarta,abinda yake tabbatar mata da cewa tabbas
qirjinta tun daga sama zuwa qasa yana bayyana a waje.
"Leave me.....ka sakeni!" Ta tattara qarfinta tana
fada cikin tsawar da batasan ta yita bama saboda gigita da tsoron fitar
tsiraicinta a gabansa,babban abun tashin hankalin da hannu daya taketa qoqarin
kamo rigar saboda daya hannun yana riqe cikin nasa.
Tsawar
tata ya sake rura wutar fushin dake zuciyarsa wadda keta qissima masa abubuwa
kala kala a kanta na irin hukuncin da zai mata. Ba'a saba masa rashin kunya
haka ba,don haka baima san me ya dace yayi mata cikin zafin nan ba,sai kawai ya
sake fincikota da qarfin da sai da taji hannunta ya amsa,batayi wata wata ba ta
fada qirjinsa gaba daya.
Bakinta yaqi mutuwa,ta tattara dukka qarfinta tana son tureshi tana
bayyana tsantsar fushinta cikin maganganunta,ransa ke qara baci,zuciya kuma
tana sake tunzurashi......yana da fushi yana da zuciya,amma ba kasafai ya fiya
son tashin hankali ba
"Shut your mouth" Ya fadi yana dubanta da
kyau,saidai kaman bata ji ba,tana magana ne ransa yana baci,ya sakeyi mata
riqon tsauri ba tare daya damu da son qwacewa takeson yi ba
"Zip it....Hold your tongue" Still fushin da take
ciki ya hanata gane me yake fada....zuwa lokacin hawayen da taketa tattalinsu
sun fara yiwa kansu gurbi saman fuskarta.
"Silence yourself......Don't annoy me!" Ya fada da
husky voice dinsa......fushin da yakeji bayason ya bari yayi hukunci a irin
wannan lokacin,don haka kawai sainya zabi riqe fuskarta cikin tafukan
hannayensa da kyau yana furzar da iska me zafi daga bakinsa a saman
fuskarta,idanunshi kan lips dinta dake magana suna rawa,sai kawai ya hade
bakunansu guri daya.
Wata
irin tsotsa yakewa lips din nata cikin salon fushi da bacin rai. Tun a karon
farko hankalinta ya fara dawowa kan abinda yakeyi saboda tsananin zafin daya
ratsa lips din nata. A lokacin ne kuma ta fara yunqurin tureshi ta raba kanta
da mummunan zugin da takeji saman lips din nata amma a banza,don ko motsawa
baiyi ba,bai kuma rabu da ita ba sai daya tabbatar taji a jikinta,lips din ya
ninka girmansa na asali......sannan yaja da baya yana dan tureta har sai data
dafe kitchen cabinet.
Qirjinsa
sama da qasa yakeyi cikin mode na fushi da kuma mix na wani feeling da yaji
yana ratsa tsakiyar fushin nasa. Gefe tayi da fuskarta saboda kuka daya taho
mata sosai tana dauke dubanta daga cikin idanunsa da suka sauya launi.
"Im not getting into it na zauna ina miki explaining ko
doraki a hanya......i have many ways to punish you" Ya fada sautinsa yana
rarrabewa kamar wanda yayi tseren gudu ya gaji,sai ya fusgi dish dinsa yana
ficewa daga kitchen din.
Duk da
tasan ya fice din amma ta gaza dago kanta,don jikinta ta tabbatar rawa yakeyi
ko ta ina. Sai data kusa minti daya sannan ta motsa da nufin fita itama
tacan,amma sai taji QIT kamar an cire maqullin jikin wannan qofar aka murda
handle din aka bude sannna aka juya ana barin wajen.
Ko daga
qamshin turarensa kawai ta gane shine ya bude,batayi wata wata ba ta qarasa
wangale qofar ta kuma taka tana fita ba tare da ta tsaya tantancewa da mutum a
falon ba ko kuma babu.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 31
_Daga abdullahi dan abbas R.A,wata kuyanga(baiwa)budurwa
tazo wajen manzon Allah S A W,ta gaya mishi cewa,babanta yayi mata auren
dole,sai manzon Allah S A W ya bata zabi(haquri da auren ko a raba)_
_____________________________
31
Idanunta a
rurrufe ta tura qofar dakin nata ta shiga,ta kuma maida key din ta rufe tana
jin kamar zai sake biyota ne. Wani azababben kuka ta saki tana jin yadda
labbanta ke wani irin zugi kamar zasu cire daga saman bakin nata. Tako ta ina
tun daga saman labban nata har zuwa fuskarta dama qirjinta ba abinda suke
fitarwa sai wannan mayataccen qamshin nasa.
Ta jima
tana kuka gami da murza lips din,tana fatan zugin da takeji ya ragu.....har
batasan iya adadin lokutan data shafe a
haka ba. Qarar agogon dakin ya sanyata maida idanunta da sukayi mata nauyi
saman agogon,lokaci yaja.....saita miqe da dan hanzari ta zauna.
Kaman yadda jikinta bai daina rawa ba haka zuciyarta da
labbanta basu daina mata zafi ba. Duka
hannuwanta ta saka ta rufe fuskarta dashi tana ci gaba da sauraren bugun
zuciyarta.
"Ba lokacin wannan bane sabreen.....ba lokacin bata
lokaci bane wannan,kina sake bawa maamah damar kasancewa da 'yan uwanki ne
kawai a kowacce daqiqa....lokacin aiki ne tuquru yanzu don qwatar kai.....ki
daina bari normal halittan namiji kamar saura yana firgitaki......wanne iri ne
baki gani ba?" Taji ana gaya mata daga can wani sashe na zuciyarta. Abinda
ya zaburar da ita kenan ta fara zame kayan baccin jikinta ta daura towel ta
wuce bandaki.
Wanka
tayi ta dawo ta shirya cikin atamfa doguwar riga,ta gyara ta matseshi cikin
hair tie masu wani irin adon stones masu garai garai a jikinsu dan madaidaita.
Bata
saka komai a fuskarta ba,amma tayi wani irin kyau duk da ramar da tayi,saidai
kuma fatarta tayi fresh saboda zama waje daya da rashin bawa rana damar qona
fatarta,uwa uba har yanzu mayataccen gyaran jikin nan yana nan baibar jikinta
ba,batasan wanne irin rantsatsen hadi bane annin ta biya kudi akayi mata.
Duk da
yunwar dake qwaqular cikinta amma sai taji sam ba zata iya zama ba,hasalima
duka tasirin yunwar ya gushe,kitchen take da muradin shiga ta shirya abincin
dare,wanda take fatan koda batayi na rana ba aqalla a samu na dare.
Da dan
hanzarinta take fitowa daga hallway din,hankalinta yayi gaba zuwa kitchen
sautin muryarta ya dakatar da ita
"Adda sabreen" Amna da shigowarta kenan ta fadi
fuskarta cike da murmushi. Suna hada idanu ta sakar mata fuska da salon nata
murmushin. Haka kawai tana tuna mata da huda duk da hudan miskila ce ba kaman
amna ba,amma sai take mata yanayi da hudan.
"Yaushe kika shigo?,afwan ban sani ba ina ciki ina
wanka" Ta fada tana neman gefan wata kujerar daban ta zauna. Da
murmushinta tace
"Adda sai an miki uzuri,matafiyi ba'a rasashi da gajiya
a jikinsa,ni har zan kunna wayata ma na duba wani assignment kafin ku samu
fitowa" Kyawawan fararen idanunta
sabreen ta fiddo waje.
"Haba dai,ya zaki zauna kiyita jira,da kin qarasa
kinmin magana ai". Bakinta ta rufe da tafin hannunta
"Kinaso hamma ya ballan qafa?,ba'a shiga shiyyar
dakinsa direct ai,BB farouq ne kawai ya isa". Tabe baki tayi a fakaice,can
qasan ranta tana fahimtar tsananin izza gareshi da shegen mulki.
Fara sako
mata zancansa da tayi yasa sabreen miqewa cikin qarfin hali da son nuna komai
lafiya
"Bari na baki ruwa kisha"
"Am full adda.....saidai na rakaki kitchen naga kaman
kitchen zaki shiga" Kafada ta daga da murmushi
"Alright.....muje"
"Yau hamma za'ayi full da abincin addana.....yadda
yakeson abinci me dadi na tabbatar adda na ba daga baya ba.....in fact ma tunda
har kikayi nasarar samun hamma na na tabbatar komai kin hada" Tayi maganar
da dariya dariyar tsokana. Bata ce mata komai ba,tadai qoqarta sauke mata
murmushi kawai.
Sanda
suka shiga kitchen din duk sai taji ta takura,ta rasa ta inda zata fara,saboda
idan maganar qwarewa ake ta fannin girki tasan bata cikin jerin wadannan
matan,infact ma ita ba gwanar shiga kitchen bace sam.....to ina ma taga
time?,tana ta abinda qannenta zasuci susha su lulluba sutura,suyi magani idan
lalura ta taso?. Tasan huda ta tsere mata sosai ta fagen iya girki,don tun tana
fita tana barinsu hudan tana musu tsumburin burin har tazo ta qware.
"Kaman ya kamata kiyi surprising hamma na ko?"
Amna ta fadi da murmushi tana duban sabreen. Kallonta kawai tayi kallon dake
nuna alaman tambaya,sai amnan ta daga kafada
"Gift dina na yau zan gaya miki best food nashi da
daddare.....but nima zaki bani tukuici ki gayamin sirrin skin dinki adda don
Allah?" Ta qarasa fada a shagwabe. Abun dariya yaso bawa sabreen saidai
batayi ba illa murmushi data saki,ta kalli fatar tata ta kalli amna,ita bataga
wani kyau da fatarta tafi ta amna ba
"Seriously adda kina burgeni at the first time dana
fara ganinki.....kawai naji jinina ya hadu da naki" Ta fadi da gasken ta
yadda a furucinta zaka fahimci da gasken take.
Kusan
tana zaune amna ta hada duka ingredients din na kalar abincin. Ta miqe tana
daura apron data gani tana bawa amna daya,sai qararrawar dake kitchen din ta
dauki tsuwwa.
Amna ce ta
duba,saita waiwayo ta kalleta
"Kira ne daga bakin gate" Tayi maganar tana miqa
mata wayar
"Ki daga" Tace da ita,ba musu ta saka a
kunne,bayan wasu sakanni ta dawo da dubanta kan sabreen
"Wai baqi ne dake.....zuwaira daga wajen hajiya mariya
maamah". Maganar taji ta bugu qirjinta don tazo mata kamar a bazata,sam ta
mance da issue dinsu,sai ta fara zare apron din tana cewa
"Kice a barsu su shigo" Yadda ta fada mata haka ta
gaya musu,ta zare apron din ta ajiyeta ta soma dosar kitchen din tana cewa
"Ina zuwa amna"
"Ba damuwa adda" Ta amsata tana matsawa kitchen
din don ci gaba da aikin.
Kasa
tsaiwa tayi daga cikin parlor din,ta taka har qofar qarshe wadda daga ita sai
balcony din da zaka sauka zuwa farfajiyar gidan. Tsaye tayi kawai riqe da
qofar,ba abinda ya hanata hango wajen sai lafiyayyen curtain din daya raba
tsakaninsu.
"Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta fara rasa
falon kafin ta bayyana Laila na biye da ita a baya da luggage dinta dake da
girma,tana takawa d'ai d'ai,tana sake ganin alatun da aka xubawa gidan,sai take
ganin wancan zuwa bataga komai bama.
"Wa'alaikumussalam" Ta amsa mata idanunsu yana
haduwa waje daya dana laila.
Wata
faduwar gaba ta saukarwa lailan lokacin da idanunta ya shiga cikin na sabreen
dake tsaye tana jiran shigowarsu
"Kambu.....who's she?" Ta samu kanta da furtawa a
qasan zuciyarta saidai kuma labbanta a sarari ma rawa sukeyi.
Yanayin
kallon da lailan ke mata sam baiyi mata ba,a nutse da wani irin jan aji ta debe
kallonta daga kan lailan tana maidawa kan zuwaira dake qoqarin gaidata
"Basai kin tsuguna ba......ta nan ga qofa nan a nan din
akwai dakuna a ciki,ku zabi duk wanda yayi muku" Ta amsata a taqaice don
ko tsaiwarsu a wajen sai taji bata qauna. Tasan da qofar ne cikin ranakun zaman
kadaicin data dinga yi cikin gidan
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 32
_Daga abdullahi dan umar R.A yace."manzan Allah S A W
ya hana auren shigaari,shi kuwa auren shigaari shine,mutum ya aurar da d'iyarsa
ga wani,bisa sharadin Shima wancan zai aura masa tasa 'yar,kuma babu biyan
sadaki a tsakaninsu(musanye kenan)_
_bukhari da muslim ne suka rawaito_
___________________________
32
Tasan qofar
ne cikin ranakun zaman kadaicin data dingayi cikin gidan da kuma Yanayin wajen kuma tasan guri ne baqi na kusa
bayan boys quaters da gidan ya mallaka na musamman da yake daga can bayan
gidan. Bata da matsala dasu,koda dakunan hallway suka zaba kuwa,don kowacce
rana a lissafe kwanakinta cikin gidan suke.
"To.....to madallah......bari mu qarasa" Xuwaira
ta fada tana wucewa gaba laila tana biye da ita. Duk wani taku daya biyu na
lailan saisun hada idanu da sabreen din wadda ke tsaye yana karantar yanayin
kowanne a cikinsu.
Dauke
dubanta tayi,sai ta koma saman kujerar falon ta zauna kawai yanayin jikinta
yana neman sauyawa.
"Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta sake ratso
falon. Idanunta ta daga a hankali tana duban zuwaira sanda take takowa falon
riqe da waya a hannunta fuskarta a sake
"Ranki ya dade.....hajiya nason ganawa dake" Tayi
maganar tana miqa mata wani qaramin akwati da sabreen din ta kasa amsa sai
binsa da kallo da tayi. Daya hannun waya daya akwati,kuma dukkaninsu idanun
zuwaira suna gaya mata ana da buqatar karbar kowanne.
Cikin
kwanyarta taji ana umartarta data karba,ba wani laka a jikinta ta karba
dukkaninsu
"Sirri yana da matuqar muhimmanci......hajiya nason
sirri matuqa" Ta tsinci muryar zuwaira tana gaya mata. Idanu ta waiwayowa
ta zubawa zuwairan,sai kawai ta dauke kanta tana nufar hanyar hallway don
komawa dakinta.
Kaman ana
jira ta shiga dakin wayar tahau kadawa,ta zubawa sunan da zuwaira tayi saving
dashi wato hajjaju. Tattaro dukka wata dauriya tata tayi,ta hadiye wani yawu me
kauri sannan ta daga kiran ta sakashi a hands free hana ajiye wayar saman
cinyoyinta.
"Ka kula da ita.....huda kuje ya baki magani kisha
kafin ki kwanta.....sannu qawata". Abinda kunnuwanta suka fara jiye mata
kenan wanda ya sanya tsigogin jikinta tashi. Ta runtse idanunta tanajin kamar
an daukk guduma an kwada mata saman kanta.
"Huda kuma?" Ta motsa labbanta tana furtawa a
wahalce. Murmushin maama ne ya soma riskarta kafin tace
"Eh,huda.....ko bazatayi lalura ba?......kowanne sakaci
da zakiyi akwai sakamakonsa kan halittar da kika fi so fiye da komai da kuma
kowa......"
"Bani huda din" Ta fada kanta tsaye da wani irin
yanayi me kaushi. Wata qaramar murmushi me kama da dariya ta saki
"Da wuri haka?,zabin cetonsu ai yana hannunki tunda na
gabatar miki da dukka kayan aiki.......bansan me yasa kika yanke sadarwar dake
tsakaninmu ba.....saidai koma meye wannan ba damuwa ta bace......kowanne
ganganci kuskure ko sakaci sakamakonsa rubutacce ne a nan......"
"Idan kikayi kuskuren cutar da ko farcen daya daga
cikinsu ne......to lallai ba shakka ba mallaka miki danki zanyi ba......zan
sadar dashi da kabarinsa ne,zan mallakaws barzahu shi a madadin ki"
Sabreen ta fada cikin tsawa da wani irin birkitaccen sauti daya ratsa
maamah,taji kuma har cikin jikinta da gaske ta fadi maganar. Ta danyi jim kadan
tana jin wata shakka tana ratsa ta,sai kuma ta saki wata dariya
"Bismillah mana......indai har kina ganin hallaka mutum
kamar muhammad jadda abune me sauqi....."
"Akwai abinda yafimin wannan sauqi?.....aikinki ya
ninka shi wahala sau dubunnan da bazasu qirgu ba.......idan naso a safiyar gobe
za'a wayi gari da sanarwar jana'izarsa hajiya maamah.......saboda haka ki
kula......akwai kadarata a hannunki......a nan kuma akwai ruhinki dama
kadararki gaba daya a tare dani" Daga wannan ta yanke wayar.
Zare
wayar daga kunnenta maamah tayi tana kallo. Wani irin mamaki da tsoro yana
kamata,wacce irin yarinya ce wanannan?,wadda bata tsoro ko shakkar duk wani abu
girman tsoron dake tattare dashi?.
Gabanta
yayi mummunar faduwa sanda ta tuna zancan idan taso za'a sanar da jana'izar
fu'ad din a gobe. Ta motsa da wani irin hanzari ta miqe sai kuma ta koma ta
zauna. Waye zata gayawa?,shi fu'ad din?,tace yakula da za'a iya kasheshi?,to
waye zai kasheshin?,ya kuma zatayi masa bayani akan yadda akayi ta sani?,ya
daina cin abinci?,wannan kuma shine burinta babba a yanzu ya karbi abinci daga
hannunta don samun cikar burinta,ta yaya zata sanya idanu akan wani abu daban
da zata shirya wanda zai sauka daga kan tsari da kuma muradinta?. Zuwaira ce ta
fado mata rai,sai taji tana samun sassaucin tsoron da kuma firgicin da take
ciki.
Hannunta
dukka biyun ta sanya ta dafe kanta.
"Huda,ya kula da ita ya bata magani tasha?,who's
she?" Abinda ta dinga maimaitawa kenan. Hudan da har yanzu take ganin tana
buqatar therapy tana buqatar counselling akan mikin da nasir yayi
mata.......yanzun kuma tana shirin sake fadawa wani abun na daban?,kanta da
zuciyarta kuwa zasu iya dauka?,ya kamata ta ciyar da d'anta ta kowacce siga
muradinta.....idan yaso in taga dama bayan ta mallakeshi ta yayyankashi ta
cinye.
Abu daya
ta kasa jurewa ya kuma gaza barin zuciyarta huda,ta yaya zata ji muryarta?.
Bata taba jin dauke wayoyin ya dameta ba irin yau,ta dinga jin kamar tayi hauka
idan ta tuna ba wata sauran hanya da zata iya samun damar magana da huda.
Sosai
tayi qoqarin ganin amna bata gane komai akan fuskarta ba. Ta kama mata aikin
sukaci gaba dayi,tana ci gaba da mata hira tana bata labarin fu'ad. Kwata kwata
bata jinta ma ballantana ta fahimci abinda amna din ke fada,a haka suka kammala
amna ta fito tabar mata kitchen din. Sosai ta zazzaga dukkan abinda ya kamata
ta sake juya abinci ya koma ainihin launinsa. Ta tsaya kaman ko yaushe ta
zubawa abincin idanu zuciyarta na wani yamutsawa,mafi rinjaye na zuciyarta tana
jin kamar wani yanayi mara dadi,wani yanayi da yafi kama da rashin jin dadi?,rashin kyautatawa?,ko aikata
abinda ba daidai ba?. Itama bata sani ba,bata taba zaton da hannunta zata iya
ciyar da kowanne dan adam abinda bai kamata yacishi ba......saidai abu daya ta
sani shine....itadin guba ce ga duk wanda yace zai kawowa innocent rayukan nan
guda uku farmaki.
Takun da
taji dake alamta mata an shigo kitchen din shine abinda yayi bala'in razanata.
Da sauri a kuma birkice ta daga kanta tana duban me shigowar. Zuwaira ce
fuskarta da murmushi ta qaraso cikin girmamawa.
"Afuwa,dama cewa nayi bari nazo naji ko akwai aikin da
za'a kama miki?" Tayi maganar tana duban warmers din da a gaban idanunta
tana labe sabreen din ta cika aikinta tsaf. Idanunta ta lumshe tana jin yadda
zuciyarta ke bugawa,sannan ta tattaro dukka qarfinta ta bude idonta akan
zuwairan
"Wannan shine kuskurenku na farko,bana buqatar ki sake
shiga wani guri a cikin gidan nan ba tare da kin tsaya kin nemi izini ba an
kuma baki" Kai ta rusunar
"Ayi haquri bazai sake faruwa ba in sha Allahu"
Bata iya amsa mata ba,sai kawai warmers din data mata nuni dasu
"Ki kaisu kan dining" Tayi maganar tana dosar
qofar fita a kitchen din,don sam bata da qwarin tsaiwa ci gaba da magana.
Tana
sanya qafafunta da zummar fita tana sako tata qafar abinda ya sanya suka kusa
karo da juna,yatsun qafarta suna caki na sabreen haka gwiwarta saita tsaya cak
bata ja baya ba bata kuma koma ba. Tsaiwa cak itama sabreen din tayi tana
danjin qafarta na dan radadin kadan saboda qafafunta akwai alamun tana ajiye
farce.
Shirun
da sabreen din taji ya sanyata daga kanta ta sauke dubanta akan laila. Tana
tsaye cak ba alamun zata kauce mata ta bata hanya. Bisa dukkan alamunta tana
jiran sabreen ne ta kauce mata,kota koma sai ita ta wuce. Cikin qasa da second
biyu sabreen din taji wani abu ya saukar mata,wani abu me kama da izza da jin
mallaka ya mamayeta. Ta lumshe idanunta sannan ta zubesu fes akan laila tana
duban tsakiyar qwayar idanunta da wani irin kallo dake qure qarfin halin mutum.
Da farko itama laila din ta zuba mata idanu,saidai a hankali wani kakkaifan abu
ke ranqwafar da nata idanun. A hankali taji ta gaza jurewa,saita dauke dubanta
daga kan sabreen din tana ja da baya,ba tare data sake dubanta ba ta rabata ta
wuce a tsanake ba tare data sake duban sashen da take a tsaye ba.
Da idanu
tabi sabreen din har ta wuce,ta maido dubanta cikin kitchen din tana jin kamar
yau karon farko ta tozarta......a karon farko taji wata 'ya mace tayi mata
kwarjini,har kuma ta juyata ba tare data furta kowacce kalma daga bakinta ba.
Hada ido sukayi da zuwaira,sai zuwairan ta tabe baki tana dauke kai. Cike take
dama da lailan,cike kuma take da yadda maamah ta dinga jaddada mata ta girmama
lailan,don gidan fu'ad a wajen lailan tamkar gidan mahaifinta yake,tammar kuma
gidan yayanta da suke uwa daya uba daya yake.
"Idan me guri yazo dai me tabarma nadeta yakeyi,nan din
dai akwai macen data amsa sunan matar gidan,komai ayishi bisa
takatsantsan". Sarai ta fahimci abinda zuwairan ke nufi,amma sai taga sam
bata da lokacinta,don abinda sabreen tayi yafi tsaye mata a rai,yadda zaiyi
handling nata. Da gaske komai na gidan yayi mata,da gaske zuwa yanzu tanaso ace
itace mamallakiyar gidan. Ta cika gidan da izzarta da mulkinta da kuma ikonta
kwatankwacin hajja,tako ina ta zama ME MULKIN gidan.
Samun amna
tayi tana shirin tafiya.
"Har me?" Ta fada cikin nuna kulawa. Murmushi ta
saki
"Driverna na aje adda tun dazun fa,daga cewa anni zanzo
na miki sannu da zuwa". Fararen idanunta da a yau take jinsu wani iri ta
kada,bata da energy din dogon magana.
Closet
dinta ta bude kawai tayita fiddo abinda take ganin ya kamata ta bawa amna. Ta
hada abubuwa cikin qaramar jaka me kyau da daukan hankali.
Ido amna ta
fiddo tana nuna tsananin murna da mamaki
"Duka adda?" Ta fada da murmushi. Abun ya burge
sabreen sosai,yadda amna din ta nuna,duk kuwa da cewa tasan tafi qarfin duka
abinda zata bata din.
Fitowar
zuwaira da laila daga kitchen din ya danja hankalin amna dake qoqarin ficewa,ta
bisu da kallo kawai kafin ta juya a hankali ta fara takawa tana fita daga
falon.
"Sai haquri ranki ya dade....laila kenan..... D'iyar
hajja harira.....hajja harira 'yar majalissar zartarwa hajiya mariya
maamah". A badini kyakkyawan masauki maganar zuwaira ta samu,hajja hariran
da sukayi tattaki har cikin gidansu suka kai qudurin aurota don su cimma
buqatarsu?,ta yaya zata manta wadannan fuskokin,ranar,dama abinda ya faru a
ranar....har maamah din tana da qarfin halin ajiye budurwa irin wannan a gidan
d'an data haifa?,wanne irin kwado ne wannan?,budurwar da babu wata alaqa tsakaninsu
face ta zallar qawancen dake tsakaninsu?,a tsarin abota da mu'amala da zata
fishshi dan adam tasu bata kan ko guda daya. Kai ta jinjina,information din ya
mata kyau da ma'ana,amma kuma batajin zata sakewa zuwaira ko ta nuna jin dadin
hakan.
"Ya kamata ki dinga tsaiwa a iyakokinki kawai"
Abinda tace da ita kenan tana takawa zuwa hallway dinta don komawa dakinta,duk
da har yanzu ba wani cikakkiyar nutsuwa ko sukunin data samu daga uban tunanin
dake addabarta,gefe guda kuma tana cike da fata da fargabar sanya abincin a
bakinsa ya zarce zuwa cikinsa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 33
_Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar
da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin
ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_
33
★"ma
sha Allah,sannunta da qoqari" Anni ta fada sanda ta gama ganin kayan da
amna ta kawo wanda sabreen ta bata.
"Tana da kirki anni......amma sai nake ganin hamma me
irin halinsa ya dauko,she's so quite,batason hayaniya da yawa,bata fiya bada
amsa ba ko magana,tafi yawan murmushi kawai". Murmushi anni ta sauke,har
zuciyarta tana sake jin yarinyar tayi mata,a duk wani lokaci da maganarta zata
tashi tana sake jin sabreen ta kwanta mata ne.
"Ai dama sai hali yazo daya ake iya zama ko?,Allah ya
qara hada hankulansu......yauwa farouq yayi nemanki kuwa sanda kika
fita......naji kaman yana maganar zaku abuja passport dinki yayi expired,za'a
sake miki wani". Idanu amna ta fiddo sannan ta qanqame anni
"Anni hala Lokacin tafiya ya kusa?". Dan tureta
kadan tayi daga jikinta
"Gashi kuwa kin gani keda tafiye tafiye basa
isarki" Dariyar jin dadi ta qyalqyale dashi.
"Amna wannan tafiyan daban yake a rayuwata Allah,ba
wani trip da yakaimin wannan dadi....whole family fa anni.....wannan karan kuma
abun zaifimin dadi saboda nima na samu partner addana,adda sabreen,na daina
maqalewa su ya saddiq suna wulaqantani,wannan karon tafiyar zai zama na
musamman" Tayi.maganar with full excitement. Da kallo kawai amna ta bita
kafin ta saki murmushi,ita kanta tasan tafiyar zata qara dadi musamman da
idanunta zasu dinga gane mata fuad dinta da iyalinsa a gefe,cikon mafarkinta
kenan
"Anni bari naje na sameshi" Ta fada tana daga
yatsunta gami da lissafa watan da tafiyar tasu zata kama
"Yes" Ta furta tana jin farinciki yana
lullubeta,saita cilla da sauri zata fita tana cewa
"Dis time har abba fa sai na karbi kudin tsaraba a
hannunshi,komai bibbiyu zan dinga siya nida addana"
"Kunfi kusa ai" Anni ta bata amsa. Dakatawa daga
fitar da anni taga amna tayi shi ya sanyata daga kai tana dubanta zuciyarta
cike da tambaya. A sanyaye taga amna din ta dawo tana zama gefanta
"Lafiyarki ke kuma?" Ta tambayeta tana nazartarta
da kyau
"Wani abu na gani anni a gidan hamma". Jin an
ambaci fu'ad din ya sanyata tattara hankalinta akanta
"Me kenan?" Ta amsawa amnan cikin zuciyarta tana
fatan ba wata matsala bace a tsakaninsu.
"Anni.....me aikin gidan maamah na gani,ita da wata
budurwa......bansan budurwar ba amma tana kama da wannan qawar maamah din
aminiyarta dinnan....."
".....hajja harira" Anni ta samu kanta da fada ba
tare data shirya ba
"Eh ita" Ajiyar zuciya anni ta fesar
"To shine me amna?" Ta furta cikin hikima. Tun
asalin tarbiyya anni irin matannan ne da basa bari yaro yana kawo musu hira ko
maganar wani guri. Qasa amna tayi da idonta
"Ba komai,kawai anni ji nayi jikina bai aminta dasu
ba,daga yanayinsu fa anni kamar a gidan zasu kwana fa,qilan ma komawa gidan
sukayi Allah anni". Ta fada tana bata rai. Da kallo tabi amnan,amna din ba
yarinya ce qanqanuwa har can can ba,kome ake ciki ko yake faruwa tabbas dole
tana gani tana kuma fahimta.
"Hammanku majibancin lamura da jama'a ne,bazai zama
abun mamaki ba idan anga sabbi ko baqin fuska a gidansa ba,kedai kici gaba da
taya dukka 'yan uwanki da addu'a". Kai kawai amna ta gyada ba tare data
samu cikakkiyar gamsuwa da bayanin anni ba,ta miqe tana fita daga dakin kamar
yadda tayi niyya da farko.
Fitar amna
dukka sai hankalinta ya dawo jikinta,sam sam taji bata gamsu da wanzuwar
zuwaira da waccar yarinyar a gidan ba. Tasan wacece maamah,tasan kuma dukkanin
wanda ya rabu da ita yaya dabi'arsa zata iya kasancewa. Indai da wata manufa ko
wani qullin daban aran maamah din,muddin tana raye ba zata taba bari haqarta ta
cimma ruwa ba. Koda ta dauke idanu akan abubuwa da yawa,koda tayi kawaici akan
abubuwa masu yawa....amma a nan ba zata bari ba,ba zata bari tabi fu'ad har
rayuwa cikin gidansa ta ruguzata ba. Saita jawo wayarta tana qoqarin danna
kiran.
*SABREEN*
Batasan
adadin sau nawa ta leqa dining din ba da zummar ganin ko ta samu nasara ya taba
kayan abincin?. Saidai a duk gewayen da zatayi bataga wani alamun taba komai ba
cikin kayan dake danqare a table din ba.
Ba iya
yaci abincin bane kawai damuwarta ba aah......tanaso tayi amfani da wannan
damar ta karbi wayarta a hannunsa,tanaso duk yadda za'a yi ta samu cikakken
bayanin yadda su hudan suka koma qarqashin kulawa da mulkin maamah. Abun yana
tsananin daure mata kai......ta yarda da momma bahijja....ta kumayi imanin haka
siddan ba zata bari haka ta faru ba,duk dadai ma batasan ainihin wacece maamah
din ba. Sam bata sako kawu rufai a ciki,shikam tasan ko ya fita sanin wacece
mariya to zai aikata fiye da hakan ma.
Zuwa sha
daya na dare haqurinta ya gaza,ta miqe da wani irin kaiwa maqurar haquri tana
yafa mayafinta saman doguwar rigar jikinta ba tare data buqaci dankwali ba ta
sanya slippers dinta tana bude qofar dakin ta fice.
Kamar
magen dake kwanton farautar kamun bera haka ta dinga tafiya a hankali tana
durfafar stair case din dake facing dinta. Duk taku daya sai bugun zuciyarta ya
qaru,amma kuma tuna huda nadra da haneefa kadai ke qara mata qwarin gwiwa.
Tana jin
a kansu zata iya komai,zata kuma fuskanta da tunkarar komai da kowa.
Cak ta
tsaya a stairs din farko tana jin kaman wanda ke kusa sosai da ita idan ya
qurawa qirjinta idanu zai iya ganin yadda zuciyarta ke bugawa ma.
"Shi waye?,mutum ne kamar kowa,mutum ne kamar ni,bashi
da wuta bashi da aljanna,bai isa kuma ya yankani ya cinye namana ba" Ta
gayawa kanta da kanta murya can qasa qasa dukka tana zaton BUGUN ZUCIYARTA zai
daidaita. Aqalla ta tsaya jiran mintuna kusan goma amma still ba abinda ya
canza,sai kawai ta runtse idanunta ta kama makarin stairs din ta fara haurawa
saman da wani irin confidence da batasan daga inda ta aro shi ba.
Idan ba
jikinta da hancinta ne ya mata qarya ba,to tabbas atmosphere da weather na
wajen daban yake dana kowanne bangare na gidan. Wani irin lullumsan yanayi da
wani irin kebantaccen qamshi da bata taba jin makamancinsa ba. Bata taba lura
da cewa shimfidadden carpet bane kan stairs din sai a yanzun da qafafunta ke
barazanar nutsewa a cikinsa. Bayan qafafunta sun nutse din kuma wani irin
sassanyan yanayi tafukan qafarta ke riska a can cikin carpet din. Duk yadda
taso jure qauyancinta amma abun yafi qarfinta,dole ta dinga bin carpet din da
kallo har zuwa sanda ta riski wata pivot door wadda gefe da gefanta duka glass
ne da bazaka iya hango ainihin parlor din ba,yayin da daga tsakiya ta kasance
ta gogagen katako da aka yima design na zamani wanda ya maidata smart door. Tun
daga zubin qofar tasan wajene na musamman kuma kebantacce,ta bangare guda kuma
taji dadin samun qofar a bude,banda haka da sai tayi tsaiwar da qofar zata gama
tantance wace kafin ta bata daman shiga parlor din.
Mutum ne shi
me wani irin jiki wanda baya qaunar zafi tun asali,saidai duk da hakan tsananin
kare lafiyarsa ya sanya bai fiya kwararawa kansa A.c ba. Duk wanda ya sanshi ya
sanshi da wannan dabi'ar na kaucewa abubuwa masu sanyi ciki kuwa harda ac din.
Zaune yake
saman wata qawatacciyar minotti sofa qwaya biyu dake bayan qwatattun Belgium
sofas din da aka yiwa yalwataccen parlor din ado masu wani irin design me
daukan hankali. Daga bayan Belgium sofas din aka yi wani muhalli na daban da
aka zuba minotti sofas guda biyu wanda suke bashi daman kashingida ko miqe
qafafunsa a duk sanda yaso.
Dogayen
qafafunsa na miqe saman sofa din,yayin da night shirt dinsa ke ajiye a
gefe,daga shi sai gajeran wandon rigar wanda iyakacinsa cinyoyinsa. Hakan ya
bayyana zallar halittar fararen cinyoyinsa dake lullube da baqa sidik din
gargasa. Madaidaiciyar Ac ke kadawa cikin dakin,wadda ba lallai yanayin sanyin
ya sanya ka fahimci itace ba saboda glass door din dake hannun hagu na falon da
yake a bude,tatacciya iska me kyau dake tasowa daga jikin tsirran da aka qawata
wajen dasu tana busowa zuwa cikin falon. Tattacciyar iskar data sanya masa
kasala da mutuwar jiki,duk karsashin aikin da yakeyi ya soma raguwa.
Turo
qofar da akayi shi ya sanyashi dauke idanunsa daga karanta saqon da William ya
tura masa ta email da suke buqatar ya duba da kyau ya karanta ya kuma sanya
hannu.
Fes yake
ganin fuskarta wadda ke tsaye daga bakin qofar,fuskar data bayyana tsakanin
lullubin mayafinta wanda yadan zame baya kadan ya bawa kwantacciyar sumar dake
gaban goshinta daman bayyana sosai. Fararen idanunta da suke da wani irin haske
ta zube a kansa wani abu na dukan zuciyarta saboda yadda ta sameshi.
Ba wani
abu da gajeran wandon jikinsa ya suturta sai qasan cibiyarsa zuwa cinyarsa,don
bai samu daman qarasawa gwiwarsa bama sam. Ginannen jikin nasa daya samu kulawa
ta kowanne fanni,motsa jiki,tsananin tsafta da kuma cima me kyau. Kwantaccen
gashin dake cike da qirjinsa shi ya zamewa faffadan qirijinsa tamkar adon baqin
abu bisa farin yanki ko farar takarda. Wani irin kwantaccen gashi daya shirya
kansa da wani irin siririn layi har zuwa cibiyarsa ya zarce har qasa.
Har
cikin jikinta taji rudewa sosai,don wani abune da tsahon rayuwarta bata taba
gani ba,hakazalika bata taba hasashen zata shigo ta sameshi a haka ba. Cikin
zafin nama ta juya da niyyar komawa inda ta fito,don batajin zata iya ci gaba
da daurewa kallon wannan halittar tasa. Da nasa salon hanzarin da kuma son
qurewa rashin kunyarta tare da qoqarin fuskantar wani abu daga gareta ya dauki
remote na qofan ya dannan close,take ta rufe kanta da wata irin gaggawa kamar
qiftawar ido. Cak ta tsaya zuciyarta na bugawa sosai,tsoro yanaso ya kamata
Amma kuma wannan dakakkiyar zuciyar ta taso mata,taji a ranta cewa idanma ta
juya ta fita ta nuna masa ta damu dashi kenan ta kuma damu da wanzuwarsa a
haka.
Nasa
idanun ya janye daga kanta yana hade ransa tsam waje daya. Duk da kallon data
masa bai wuce na second biyar ba amma ya fahimci lallai ta qarewa jikinsa
kallo.
Hannu ya
miqa gefansa ya jawo night shirt dinsa ya zura,sai ya koma ya jingina da fuskar
minotti sofa din yana ci gaba scrolling saqon yana dubawa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 34
_Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W
yace:Duk macen da waliyyai biyu suka aurar da ita ga maza mabanbanta a lokaci
guda,to ita din mallakin na farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_
34
Minti daya
biyu uku har zuwa biyar bataji motsin komai ba,wannan ya sanya tayi tsammanin
yabar falon ne,don haka ta juyo a hankali tana sake zube idanunta a wajen da
yake. Haushi takaici da bacin rai suka hadu suka lullubeta ganin aikinsa yake
hankali kwance,sai ta gyara tsaiwarta sosai tana fuskantarsa ganin ya lullube
wannan faffadan qirjin nasa,wannan ya dan rage mata kaifin abinda takeji,duk da
cewa cinyoyinsa dake a waje nason sakata a razani da tsoro.
Rasa
ta yadda zatayi calling attention dinsa tayi,sai ta danyi gyaran murya kadan
cikin qufula da fusata. Minti guda kaman baisan tana wajen ba kafin ya motsa,ya
daga kansa da idanunsa daga kan hasken system din yana zubesu a kanta da wani
irin kallo na qurilla. Karo na farko yadda ya tsareta da ido taji kaman yanaso
yayi mata nauyi,jajayen lips dinsa hasken fararen qwayar idanunsa wani abu ne
da bata taba gani wajen wani d'a namiji ba sai a kansa,akan nasa ma a yau data
masa kallo itama nakai tsaye.
"Wayoyina nazo karba saboda ina da buqatarsu.......
Akwai mutane masu muhimmanci a rayuwata da nake da buqatar na dinga magana
dasu" Ta fada tana tsuke girarta da kyau tana kuma tura dan qaramin
bakinta gaba wanda sam batasan ma tanayi ba,saboda zuciyarta cike take da
haushi. A hankali ya sauke idanunsa zuwa saman qaramin bakin nata data tattara
lips dinta duka ta turasu gaba. Wasu irin siraran lips da sai kayi tsammanin
jambaki ta shafa musu. Tsigar jikinsa ta zuba kadan saboda bayyanar daya daga
cikin abinda ke burgeshi a jikin mace yake kuma lissafin ya sameshi kenan,wato
cute lips masu nau'in light pink ko red me haske irin nasa.
"A hakar kamar cikakkiyar mace" Ya fada qasan
ransa yana jan tsakin da baisan ma ya fito sarari ba. A duk lokacin da zai
kalleta sake raina shekarunta yakeyi,hakanan a duk sanda zaya kalletan sai
mamaki ya sake cikashi game da yadda ta samu cikakkiyar shaida da certificate
din zama KARUWA. shi kam gaba daya ma baisan me yahau kan mazajen dake mu'amala
da ita ba,a bisa qa'ida da yanayin halittarsa ta masa yarinta da yawa. Yanason
macen daya tabbatar zata iya dauke lalurarsa komai girmanta,ire iren sabreen din
guda goma yana ganin yafi qarfinsu nesa ba kusa ba,baima san abinda mazajen da
ta dinga tatsewa me suke tsammanin samu haka daga gareta ba da har ta samu
tasirin gusar musu da hankali.
"Labari kike bani?.....ko tambaya kike?,ko daukan
excuse?" Yayi maganar a nutse yana dage mata dukka girarsa guda biyun
bayan ya dora qafarsa daya saman daya,ya kuma yi relaxing jikin makarin sofa
din.
Duk sai
ta ji ya muzantata,akanme zai dinga mata tambaya akan abinda ya gama fahimtar
inda ta dosa?. Tsaiwarta tadan gyara tanason hana kanta jin nauyin idanuwanta.
"Amma dai cikin zamanmu ba sharadin tabamin
waya.....wayata sirrina ne,bana tunanin akwai abinda ya shafeka a
ciki" Ido ya zuba mata kamar
bazaiyi magana ba,yanaso yaci gaba da karantar bayan karatun da yayi mata na
binciken da yayi a kanta. Ya fuskanci akwai burbishi da tasirin rashin kunya
tattare da ita. Yarinyar da ko saddiq ba sa'anta bane ballanta musaddiq ko
farouq.....amma tana da zarrar tsaiwa ta fadi mishi magana yadda takeso. Wannan
wani abune da ba wata diya mace data iya fuskantarsa dashi....kai koda dan
uwansa namiji yana matuqar shakkar hakan. Uwa uba akwai tasiri na girman kai da
rashin tsoro tare da ita,yanaso yaga ya zatayi handling wadannan attitude guda
biyun da wadannan shekarun nata?.
Kaman
zaiyi magana sai wayarsa ta dauki tsuwwa,manhajar da yakanyi amfani da ita wasu
lokuta da zata gaya masa cikakken sunan wanda ke kiransa koda bashi da number
wayarsa ta karanto masa sunan fareeda Khaleed mustapha. Kusan a tare suka kalli
wayar shi da ita,a nutse ya cire hannunsa ya kashe wayar gaba daya bayan yayi
rejecting call din,amfanin manhajar kenan ta gaya masa wanda ke kira,basai ya
saki aikinsa ya dauka ba ya zamana me kira baida wani muhimmanci har
haka,saboda mutum ne shi mai darajta lokaci.
Agogo ya
kalla sannan a nutse ya maida dubanshi kanta bayan ya sauke qafafunsa duka
qasa,abinda ya sanyata sake kame ganinta gudun kada idanun nata su gano mata
abinda yafi qarfinta,don ta lura kamar bayajin nauyin zamansa a haka.
"Kin tsallake iyakarki,kin shigomin part ba tare da
Neman izini ko sallama ba......and kin tsaya kina ban labari akan abinda bai
shafeni ba.......wai...." Ya fada yana tsuke fuskarsa sosai gami da maida
qafafunsa saman table sabanin dazu dake kan sofa
"Meye amfanin zamanki a gidan nan?.. Kina zaton na kawoki ne don na killaceki
waje daya kiji dadin rayuwa?,ki samu tsaro kiji dadin ci gaba da qwamushe
asusun mutane?,ko na kawoki ne don kizo kicinye min abinci na?,ko kin dauka na
daukoki ne don wani abu daban?,thought ma dai nasan ba zaki taba mafarkin
wannan shirmen ne wato SO ya sanya na kawoki ba....." Wani radadi takeji
yana taba zuciyarta,abu daya da zata iya yabonsa akai takuma san ya qware akai
shine baqar magana kamar tsohon mahauci,idaninta da suka fara canza launi takai
kansa,ya gyara zamanshi sosai yana hade yatsun hannunsa guri daya yana maida
dubansa kanta.
"Kina magana akan sharadi yarjejeniya da
sauransu......for now ma yakamata kisan me ya shigo dake cikin gidan
nan.......Initially don ki gane me ake kira da respect........attitude dinki su
koma irin na kowanne mutum.....secondly kuma..........ki maida min dukka kudina
da kika debe.....don ban nema kudina saboda mata irinku su mora ba......"
Wani kallo harrr ta bishi dashi,sai ya daga dukka girarsa sama
"Yes......duk wanda zayaci kudina to yana da cikakkiyar
hujjar da zata bashi daman cin in a polite way.......da naso a ranar da kika
diba a ranar zan saka a kawomin ke har nan..... " Idanu ta zubawa
Kyakkywar fuskarsa yadda yake bayani a nutse hankalinsa kwance. Ashe shi din ma
mayen kudi ne?,kallon kitse akewa rogo?. Eh tasan tabbas ta cire kudade masu
nauyi da yawan da ita kanta sai data girgiza,amma kuma bata dauka har xai sanya
qulafucinsa akan kudin daya tsere musu ba har haka.
"Baki da hanyar da zaki biya Muhammad jadda
kudinsa?......zan taimakeki tsill dai don kada kiyi prison a banza.........daga
yau ya daukeki aikin shara da gyara masa bedroom da kuma wanke masa toilet
dinsa......zan biyaki kaman yadda yake biyan kowanni ma'aikaci dame aiki a
qasansa.......but.....i will not pay you anything.......zanyi writing down
komai har ki kammala biyana" Yakai qarshen maganar gaskiyar abinda yake
fada tana fita daga cikin idanunsa. Soma tattare takardunsa yayi
"You can go" Ya furta cikin halin ko in kula.
A
lokacin tana jin kamar ta qarasa gabansa ta amayar masa da dukka abinda ke
zuciyarta,tana jin kamar ta isa gabansa ta nuna masa wace real sabreen,amma
kuma wani sashe na zuciyarta yana kwabarta tare da gaya mata any mistake idan
tayi itace a ciki.
"Ya soma cin abincinki shine abinda ya kamata ki damu
dashi bawai maganganunsa ba......if kikayi abinda zai sake sanya masa shakkan
sakewa da gidan dukka ayyukanki zasu koma baya.... Sisters dinki zasu ci gaba
da zama qarqashin hadari" Maganganun da suka fito daga qasan zuciyarta
kenan,suka kuma sanyata tsaiwa cak daga takun data fara don matsawa zuwa
gareshi.
Remote
din ya dauka ya bude mata qofar yana ci gaba da abinda yakeyi
"Hey" Taji ya sake fada sanda ta sanya qafarta
daya a waje,saita dakata ba tare data waiwayo ba
"Mind you....banason qazanta,i don't want it,ki
kiyaye". Da sassarfa da kuma hanzari ta soma sauka saga stairs din har
kamar zata fadi. Kuka ne yakeson qwace mata amma bataso yaji ko ya gani,don ta
yiwa kanta alqawari ba zata taba bari yasan lagonta ba.
Baqincikinta yadda ya fadi mata dukka maganar da ke ransa,nata zuciyar
da ruhi cike maqil da maganganu amma TARKON da take ciki yasa bazaiyuwu ta
fiddasu ba.
*_Washegari_*
Tun shida na
safe zuwaira ke kai kawo tsakanin shiyyarsu zuwa ainihin falon da kuma kitchen
din. Jin shuru ba alamun tashi sai ta fara aikin gyaran dukka falukan da kuma
kitchen din. Duk wani motsi da zataji hankalinta yana kai,tanaso ta samu
cikakken bayani akan komai yadda zata zama cikakkiyar informer na maamah.
Tanason bata duk kalar bayanan da takeso don tana son ta doke matsayin hajja
harira wajen maamah. Ta kowacce fuska da kuma yanayi tanason ta taka matsayin
da zata zama aljihun daman maamah a sanda burin maamah ya cika din. Itama tata
zuciyar da ruhin cike suke da nata kalar burin da take fatan zuwan ranar
wanzuwarsa.
Wani
irin qarfi ta sanya ta danne zuciyarta ta fito shirya masa breakfast,duk da
asara akayi daren jiya na dukka girkin da sukayi,sai tashi tayi tsakiyan dare
ta kwashesu ta zuba a inda ta saba zubawa.
Yau din
cikakkiyar shiga tayi,ta rufe jikinta sosai tunda ta fahimci ba ita kadai bace
cikin gidan. Idanunta duka sunyi nauyi saboda kuka da rashin cikakken bacci. A
hankali take ratsa falon hankalinta yana qofar kitchen din.
"Barka da fitowa ranki shi dade" Taso ta tsorata
kadan,don gaba daya ta manta da wata baba zuwaira a gidan. Ta sauke dubanta a
kanta sanda zuwaira ke qare mata kallon qwaqwaf. A jiya batayi cikakken bacci
ba sai data gama fahimtar inda kowannensu yake kwana ita dashi. A gaban
idanunta ta sauko daga samanshi a gaggauce cikin bacin rai ta fada
dakinta,abincin dataxo ta kwashe kuma baici ba,a daren itama bata kwanta ba ta
sharhantawa maamah komai.
"Ya zama dole na matsa mata lamba ta yaudaroshi ya zama
a tafin hannunta" Abinda maamah ta furta kenan,tsoron taurin kai irin nasa
yana damunta. Tasan halinsa da kafiya akan abinda baida niyya baiyi masa
ba......amma zata sake yin amfani da qarfinta a matsayinta na uwa karo na biyu.
"Barka kade" Ta amsa mata a taqaice ba tare data
sake dubanta ba tayi kitchen
"Nace ba,ba abinda za'ayi kuma?"
"Babu....kije saina nemeki" Ta amsa mata a
taqaice,don kwata kwata batason doguwar magana gaba daya. Da kallo zuwaira ta
bita har ta shige kitchen din,sai ta saki murmushi tana ji a ranta ya kamata
taci tudu biyu fa......bangaren maamah din da bangaren yarinyar.....abinda ta
kwana kenan tana tunani akai,gwara tayi amfani da damarta,ta yadda koda gaba
kome ya faru zai zame mata ribar qafa,salon maganar nan da hausawa kance idan
tayi ruwa rijiya,idan kuma batayi ba masai.
Dukka
4glass stove gas din ta kunna kowanne ta dora abu akai. Da zafi zafinta ta saka
'yar basirarta ta kammale breakfast din cikin taqaitaccen lokaci,ta gyara inda
zata gyara ta fara daukan luxury Warmers din tana jerasu saman dining.
Cikin
ginshira da wani irin tsanaki gami da nutsuwa yake saukowa daga saman stairs
din,kunnensa manne da Bluetooth yana amsa waya,lokaci guda kuma yana qoqarin
gyara tie dinsa.
Hankalinta
yayi nisa sosai cikin duniyar tunani,fargaba kuma na sake cikata kamar kullum
na kada a sake tafka asara yaqi cin komai kamar kullum,asarar da take sake
kusantata da faduwarta da samun matsala a rayuwarta.
Tun daga
nesan idanunshi suna kanta,duk da baiga fuskarta ba amma ya gane itace. Sai ya
dauke dubansa yana haurawa zuwa steps din ya wuce zuwa kitchen. Qamshinsa kadai
shi ya ankarar da ita,ta daga kanta tana bin bayansa da kallo gabanta yana wani
irin faduwa,cikin mutuwar jiki ta ajjiye spoons din hannunta taja kujera daya
tana jiran fitowarsa cike da hope.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 35
_Daga abdullahi dan abbas R.A yace,Lokacin da aliyyu R.A ya
auri nana fadima,sai manzon Allah S A W yace"ka bata wani abu(a matsayin
sadakinta),sai sayyadina Aliyyu yace "ba komai a wajena" Sai manzan
Allah S A W yace "ina sulkenka?"_
35
Coffee ya
hadawa kansa,yayi tsaye jikin kitchen cabinet yana kurba a hankali. Kwanakin
nan duka baici wani abincin arziqi ba,sai kame kame da cin abincin waje,wanda
yasan totally isn't safe musamman ga mutum sannanne irinsa da ta kowacce fuska
cikin barazana da qoqarin kawo musu hari ake ta duk wata siririyar kafa da za'a
samu dama. Iya lamarin maamah da yarinyar ya isa zama izina a gareshi,abu a
cikin gidan.... Amma kuma farautarka akeyi.
Sai
yaji gaba daya coffee din ya fice masa a kai,yana qaramin tsaki ya ajiye cup
din,ya ciri paper towel ya goge lips dinsa duk da ba baci sukayi ba ya fara
takawa a nutse yana fita a kitchen din.
Sau
daya tak ya kalleta ya dauke kansa,ya taka a nutse yana isa gabanta. Tsaiwarsa
ta sanyata daga kanta,akwai inches tsakaninsu amma tana jin kamar ba wani gap
daya rage musu. Idanunsa saman lips din nan nata da suke very smooth,ba digon
komai akai sai ainihin color dinsa. Smart key na qofarsa ya dora saman table
din,ya kuma harbasa gabanta. Ya motsa labbansa zaice wani abu wayarsa ta fara
fidda wani tattausan ring me kama da sarewa,irin ring din da zai iya haifarwa
da mutum karyewar zuciya musamman ga masu karyayyiyar zuciyar. Fareeda
Khaleed mustapha sunan wanda ke yunqurin
samun sadarwa dashi kenan aka sanar mishi. Maimaita kiran sunan me kiran wayar
ta soma yi kamar ba zata dakata ba. Saman kunnuwanta sunan ya sauka,irin sunan
da taji a wancan daren. Iska ya furzar daga bakinsa yana sauke numfashi,sannan
yana qaramin tsaki gami da ciro wayar da wani dan zafin nama yana yanke kiran
ya jefata aljihun yana sake sakin tsakin. Baki ta tabe qasa qasa tana kauda
fuskarta wani sashen,can qasan zuciyarta kuwa gulma take,tasan za'a
rina.....koda dukka jikinta kunnuwa ne ba zata taba yarda mutum kamar muhammad
jadda bashi da kowa ba.....mutum kamar muhammad jadda baida ajiyayyun 'yammata
da yake debe kewarsa dasu ba......ba zata yiwa kanta qarya ba,idan tace mummuna
ne ko bai hadu ba tasan tabbas wannan din gundumemiyar qarya ce ta zabgawa
kanta......to kuwa tasan zai wahala a rasashi da wasu halaye da sukayi kama da
wannan. A iya rayuwarta.....a iya mazan data hadu dasu harda wadanda basu
kaishi bama,masu kudi sosai matasa masu jini a jika,taga dabi'u kala daban
daban da halayen da bata ma tsammaci ganinsu ba,yaga yadda matan aurensu suke
ba komai ba a wajensu......taga irin qalubalen da shuke fuskanta a tattare
dasu....matasan cikinsu harma da masu yawaitar shekaru,wannan abun ya sake cire
mata sha'awar abubuwan nan guda biyu a ranta SOYAYYA da kuma AURE. Gadai guda
daya nan ya cimmata,saidai tana da yaqinin ba zata bari yayi galaba a kanta
ba,yayin da take bawa kanta tabbacin tafi qarfin wata soyayya taci galaba a
kanta,don idan ka dauke soyayyar qannenta bata taba tsintar kanta cikin
soyayyar komai ba,wannan shine yake sake bata yaqini tabbaci da nutsuwan ba
zata taba yin soyayya ba....saidai ita a sota
(Nace uhmmm....maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta).
Idanunsa ya maida saman fuskarta,a nutse ya fara magana kamar wanda ya hada
jini da gidan sarauta.
"You can start your work today.......but......ya kamata
ki sani,nasan komai da yake every single room......sannan nasan place dinshi,so
do your own business......kiyi iya abinda akace kiyi" Daga haka sai ya
juya a nutse don sauka a wajen,saidai kuma muryar da yaji tana gaidashi ya
sanyashi tsaiwa yana juyawa wajen.
Zuwaira ce
a durqushe a wajen,da yanayin da yake tabbatar masa ba yanzu yanzu ta shigo ba.
Sunkuyar da kanta tayi sanda ya zube mata kaifafan idanun nan nasa,yayi mata
wani irin kwarjini da bata taba ganinsa idanun kowanne mahaluki ba sai a kansa.
Wannan kwarjinin nasa ya sanya suke qauracew waje duk sanda ya shigo gaida
maamah. Sosai goshinta ya soma tsatstsafo da gumi,tana ganin kamar a iya
kallonsa kadai zai iya bankado komai ya kuma fallasashi.
"Who are you?" Yayi tambayar kai tsaye ba wani
wasa ko sassauci a muryarsa,abinda ya sanya zuwaira ta ida rudewa,ga turancin
daya jefeta dashi wanda ya saka a duhu
"Eh....na'ammmm.....eh"
"Wacece ke?" Ya maida mata tambayar da hausa.
Caraf ta kama maganar tasa
"Nice zuwaira.....zuwaira ce,me aikin da hajiya maamah
ta aiko don taya uwargida sabgogi da hidimomin gida". Ta qarashe fada tana
daddafe hannuwanta a qasa,saboda ji tayi kamar zata fadi daga tsugunnen.
Hannayensa
kawai ya zube a aljihun wandonsa yana ci gaba da kallonta,yana kuma son ganin
fuskarta sosai. Duk wani daya rabi maamah yana da nashi question mark din a
wajensa.....duk wani wanda maamah zatayi qoqarin hada connection tsakaninsa
dashi baida aminci ko nutsuwa kwata kwata dashi,don haka yake sake shawarwarin
qarawa musaddiq kwanakin zamansa a qasar da ya aikeshi ba tare da wani
qwaqwaran dalili ko kuma buqatar hakan ba.
Hannayensa
nasa ya sauke ya soma takawa yana sauka daga wajen,zuwa sannan qiris ya ragewa
zuwaira ta saki fitsari a wando.
"Kada na sake ganin gilmawarki cikin gidan nan indai
ina nan......duk ranar kuma da kikayi sake hakan ya faru.....ki fara hada
kayanki na barin gidan nan....basai nace ba"
"In sha Allahu ranka ya dade,tuba nake" Ta fada
dukka jikinta yana rawa.
Daga ita
har sabreen ba wanda yacewa da dan uwansa komai. Kusan minti biyar da fitarsa
sannan ta tattara qarfinta ta miqe tana sake hawa steps din dining da sabreen
ke zaune akai. Fuskarta qunshe da munafukin murmushin nan ta soma gaidata
"Barka da asuba ranki ya dade.....ashe har kin gama
aikin?,ba zaki jira nazo ba?,hidimar ai sai tayi miki yawa,da sai na rage miki
ai.....iyaka idan na gama abincin ki bada kalar maganin da za'a zuba a
ciki......kedin abar tausayi ce ranki ya dade,kullum addu'ata da fatana ki
kubuta daga hannun hajiya mariya lafiya" Zuwaira tayi maganar cikin
matuqar sanyin muryar.....tsantsar alhini da kuma nuna damuwa.
Tunda
zuwaira ke maganganun nan a jejjere sabreen bata daga kai ta kalleta ba sai da
tazo gabar qarshen maganar tata. Kalmar tausayi data furta a maganar nata yaja
hankalin sabreen ya kuma tsaye mata a rai. Sosai ta zubawa zuwaira idanu tana
son tantance gaskiyar abinda ta fada,saidai kuma abun mamaki haka kawai sai
taji ta kasa gamsuwa da ita.
Boyayyen
numfashi ta sauke,sannan ta tattara hankalinta a kanta tana hade ranta tsaf
"Wannan duka ba huruminki bane.....kiyi abinda ya
cancanci kiyi kawai" Sai ta miqe daga saman kujerar tana niyyar tafiya. Da
sauri zuwairan ba tare da ta ji ciwon tsaidata a wata iyaka da tayi ba tace
"To ranki ya dade abincin fa?,yauma saidai a
zubda?"
"Idan kina da buqatar ci kya iya ci ai" Ta amsa
mata da gatse tana sauka daga step din idanunta yana sauka kan laila dake
shigowa parlor din.
Sanye
take da robber gown wadda tabi kowanne shape na jikinta ta lafe mata. Fuskar
nan fes da kwalliya zaka rantse ba safiya bane ba. Ba komai a kanta sai
wani qaramin bandana da bai rufe komai a
gashin kanta ba. Wani mahaukacin tashin qamshi jikinta keyi,wanda turaren
turare ne na musamman da aka tanada saboda wani mutum na daban.
Duk da
fuska ko kuma jikinta ba wata kwalliya.....amma haka kawai ta fusgi hankalinta.
Sassanyan kyan nan nata da baya buqatar kwalliya ko wani abu makamancin haka
yana nan shimgide saman fuskarta. Haka kawai taji ta muzanta duk da kwalliyar
dake jikinta,amma duk da haka sai taji ta raina kanta. Tashin farko wasu
kalmomi na hajja suka dawo mata fes cikin kwanya suka qara mata azama da qwarin
gwiwa. Muhammad jadda kawai take da buqatar gani,don haka taci gaba da shigowa
falon tana jin izza tare da fatan ko yaya ta gwadawa sabreen wani abu da zai
sosa ranta.
Kallo daya
ta yiwa lailan ta watsar da ganinta a wajen,taci gaba da wucewa ciki ba tare
data damu da kallon qurillar da laila ke mata ba. Ita sam bata ma dauketa a
sunan damuwarta ba,damuwarta ta tsaya ne kan yadda yake neman maidata boyi
boyin qarfi da yaji. Ta share masa sassa ta hada da wankin bandakinsa dama
underwears dinsa,tana jin koda sama da qasa zasu hade ba zatayi wannan aikin
ba. Lumshe idanunta tayi tana qara jin takaici yana cikata. Bashi da masaniyar
hatta da girkin da take masa dole ce ta sanya take masa ba?,har wani qyashi da
baqinciki ke rufeta gami da kasalar bacin rai duk sanda ta tsinci kanta dumu
dumu a kitchen tana hidimar dafa masa abinci.
Dakinta
kawai ta wuce bayan ta saqale masa key dinsa jikin qofarsa,tana fatan ya dawo
ya samu sassansa da muqullansa a inda ya barsu.
Dining
din laila ta wuce kai tsaye tana wani taku kai kace itace matar gidan,ranta ya
cika maqil da kishi da hassadar sabreen din. Ko daga nesa ka hangosu sabreen
din ta fita quruciya.......amma miskilancin yarinyar da shegen girman kanta
mamaki yake bata. Bata taba mata kallo biyu ba....kai zata ma iya rantsewa sau
daya ta mata nutsasten kallon cikin idanu Randa taso blocking mata hanya. So
take ko yaya taga wutar kishinta a idanunta,to amma kullum suka hadu tana yin
kamar babu aka kawo gidan aka ajiye ba dan adam ba.
"Ma aka dafa?" Ta tambayi zuwaira Kai tsaye tana
latsa wayarta sanda zuwaira ta kusa gama kwashe warmers din.
"Sai yanzu Allah yayimin tashi,don haka saiki jira na
gama da aikin matar gidan tukunna" Zuwaira ta gaya mata gatse gatse gami
da satar idanunta ta gasa mata harara. Kullum ta tuna warning da kuma jan
kunnenta akan ta yiwa yarinyar biyayya da hajiya mariya da hajja uwar yarinyar
suka mata akan tabi yarinyar sau da qafa bama matar gidan ba.....sai taji kamar
ta zabge yarinyar da mari.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 36
_An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi
yace,manzon Allah S A W yace,idan miji ya kira matarsa zuwa shimfida taqi
zuwa,mala'iku zasuyita la'antarta har gari ya waye_
*_qarqashin wannan hadisin akwai qarin haske,idan a wannan
qin da tayi kuma ta samu ciki koda ta rasu wajen haihuwa wasu malamai suna
ganin bata samu wannan shahadar da mace me naquda ke samu ba idan ta rasu_*
36
"Ki
gaggauta da Allah.... Am starving,ko ki bani wannan da kike debewa in fara
dashi"
"Sannu akuya......" Zuwaira ta fada a ranta,amma a
fili saita ajiye mata warmer din tana cewa
"Zaki iya ci mana.....amma kafin kicin ki fara sanarwa
tsohuwarki gudun maida laifi a kaina" Ta fada dadan zafin rai. Haka kawai
sai laila tasha jinin jikinta,don haka ta miqe tana sauka daga wajen
"Fresh nakeso.....kada ki wuce minti talatin" Bata
ma iya amsa mata ba ta dauke ragowar warmer din tana wucewa kitchen din gami da
jan tsaki qasa qasa.
Tafiyar
minti arba'in da shida ta sadashi da mansion House din alhaji hamza kibiya. A
qofar tafkeken gate din dake qara nuna alfarmar dake cikin gidan motocin suka
tsaya bisa umarninsa,don yanaso ne ya gaida anni ya fito......ya kuma haida
maamah din sannan ya wuce office din. Akwai cushewar ayyuka sosai yau din bisa
schedule din da saddiq dinsa na yau da saddiq ya tura masa tun jiya da
dare,wannan ya sanyashi fita da wuri. Wani irin qarin investors suketa samu a
dukka kamfanoninsu,duk da yana yin komai bisa kula don ya tabbatar akwai
mutanen dake bibiye dashi,kuma nasararsa a wancan lokacin yayi imanin ta
tarwatsa musu dukka shirinsu..... Faduwarsu kuwa da shurunsu yayi amannar bawai
suna nufin komai ya wuce bane.
Gidane
dake cike da tsari,da kuma kusan duk wanda yake gidan bisa tsari da sanin ya
kamata yake zaune. Kowa yasan aikinsa,tun daga kan security guards da sauran
masu aiki na cikin gida dama farfajiyar gidan,hakanan bayin Allah da suke daukan nauyi dake wani sashe daban na
cikin gidan me kama da qaramin estate kowa bisa tsari da sanin ya kamata yake.
Duk girman
gidan ko.ina fes yake da wani irin tsafta da qamshi. Ya zuqi qamshin har cikin
hunhunsa sanda yake zama saman sofas na qaramin falon anni da mutanen da suke
mafi kusanci da ita ne kadai ke iya haurowa har nan. Ba abinda ke saukar masa
da nutsuwa kasala gami da tayar masa da wnai Tsunammen feelings irin qamshi.
Duk sonshi da qamshin wannan ya sanyashi haqura dashi kan bedsheets da duvet
nashi da pillow,wanda muddin ya kwanta akai da qamshi irin wannan to zai wahala
bai kwana cikin wahala ba,ko kuma ya tashi da mafarkin da zai wajabta masa
wanka kafin yakai ga sallar asuba.
Normally
yanaso kowanne kusurwa na inda zaiyi mu'amala dashi ya zama kaman haka,sai ya
lumshe idonsa kafin ya budesu sanda yaji sallamar anni.
Da dogon
hijabin nan nata har qasa ta shigo wanda ke alamta masa sallar walaha take ya
tasota. A wajenta ya koyi sallar walaha,tun yana yi yana fashi batabi jininsa
ba har takai ya saba,ko a ina yake,kome kuma yake yi sai ya katseshi
yayi,saidai idan abubuwan sunsha kansa ko sunfi qarfinsa ba yadda zaiyi.
Fuskarta
shimfide da kararramammen murmushin nan nata ta qarasa shigowa,tayi bismillaha
tana zama saman kujerar abinda ya sanyashi zamowa daga samanta yana gaidata.
"Tashi ka koma ka zauna" Tace dashi don ba kasafai
yake iya zama saman kujerar ba idan suna kai ko ita ko abbansu,harma da maamah
din kanta.
Kai ya
girgiza yana tanqwashe qafafunsa saman carpet kamar qaramin yaro
"Nan ma ya isa anni.....akwai kunun tsamiya?" Kai
tadan daga tana dubansa. Batayi tsammanin zai qara tambayar abinci ba sam sam
daga wajenta,don kuwa a yanzun magidanci sunansa,saidai kuma ta masa uzuri,don
tunda akayi auren bai taba neman komai ba,don haka tace dashi
"Akwai.....kasan dole ne kullum sai an yiwa
abbanku.....har yanzu gargajiya taqi barinku,bari nasa a kawo maka" Ta
fada da murmushi. Shima tsadajjen murmushin nan da kusan annin tafi kowa
ganinsa a duniya ya sake
"Anni akwai abubuwa masu muhimmanci me tarin yawa a
gero,inda mutane sunsan meye gero anni da kusan duka mun koma cinsa".
Murmushi ta kuma yi tana miqewa gaba daya
"Gaskiya mana naga kun qulla kyakkyawar alaqa da
fura.....nikam wannan traditional doctor din naka ya sake canzaka gaba
daya" Murmushi kawai ya saki,shi kansa ya sani kalar cimarsa ba iri daya
bace data kowa,sau tari a wani taro ko a sanda ya buqaci cin abinci da baqinsa
na Africa ko nan Nigerian,sukan cika da mamaki idan sunga kalar abincin da yake
ci.
Da kanta
annin ta shiryo komai saman tray,harda qarin lafiyayyen qosai da kuma farfesun
kan rago da yasha kayan qamshi tafarnuwa da wadatacciyar albasa. Akwai abinda
takeson ta karanta a tattare dashi a fakaice a matsayinta na uwa bawai kai
tsaye ba. Tun daga ranar da amna ta gaya mata zaunuwar zuwaira a gidan ko sau daya bata taba hutawa
da tunani ba. Ta kasa aminta hakanan ta kasa gamsuwa. Fu'ad dan maamah ne halak
malak,duniya ma ta shaida hakan,saidai tana jin bai kyautu tabar mata rayuwarsa
ba,rayuwar da aka fafata aka sha fama kafin fara daidaituwar komai a cikinta.
Allah shine ya raya muhammad fu'ad din,amma kuma itace sila,tasha fama qwarai
da gaske,faman da har batason tunawa,faman da shine ya zama silar shaquwa
tsakaninsu me yawan gaske. Har batason tuna wahalar da tasha dashi kafin cire
shi daga depression daya samu kansa a ciki.
Tana
shigowa ya miqe,bai barta ta qaraso ba ya isketa a hanya ya karba tray din ya
qaraso dashi. Sanda yake shan kunun a nutse yana kuma cin qosan tana zaune a
gabansa tana karantarsa,tana jin zuciyarta na matsewa,ta kuma damu tayi masa
maganar dake qasan ranta,duk da haka tayi jarumtar sanda ya kammala sannan a
tsanake tace dashi.
"Muhammadu...."
"Na'am anni" Ya amsa mata a nutse yana jin wata
nutsuwa da qoshi na musamman yana ratsa cikinsa.
"Nace anya yarinyar nan basai an taimaka mata da qarin
masu aiki ba?,gidan nan sai nakega ko masu aiki nawa aka zuba masa yana
buqatarsu ko don sauqaqawa matar gidan,duk da yake kai baka fiya son mu'amalar
masu aiki ba cikin sha'aninka". Murmushi kadan ya saki,baisan wanda a
duniya ya sanshi sosai ya kuma karanceshi tas sama da anni ba.
"Kiyi duk yadda ya dace anni......" Ya bata amsa
cikin girmamawar data sake sanyata ta jishi a ranta sosai.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 37
_Daga ibn juhaim bin haris RA(wannan sunan sahabin annabi ne😄),yace:Manzan
Allah S A W yace "da me wucewa ta gaban me sallah yasan abinda yake kansa
na sabo,tabbas da ya tsaya(ya jira me sallahn ya gama)tsahon gwargwadon shekara
arba'in shine yafi masa alkhairi akan ya wuce ta gabansa_
_Bukhari da muslim ne suka rawaito_
37
"Da ina
tunanin na tura mata ma'u da maigidanta malam ibrahim.......zataji dadin zama
da ma'u sosai.....ina kyautata zaton haka,malam ibrahim kuwa koda kana da
ma'aikata da sauransu zakaji dadin zama dashi in sha Allah".
"Anni ki zartar da komai da kike ganin ya
kamata......ba buqatar sai kin gayamin anni" Ya sake fada har a zuciyarsa
yana jin annin ta isa ta zartar da komai din.
Kai ta
jinjina tana dan murmushi,har qasan ranta tana jin dadin yadda ya bata girma da
kuma dama,duk da cewa tasan cewa abune me wahala ya musanta akan duk abinda
tace din. Har bakin parlor na biyu tayi masa tattaki,bakin ta fal cike da
addu'ar data zame mata dole,kowacce rana dukkaninsu su hudun basa kaucewa samun
kyakkyawar addu'arta da bata gajiya da binsu da ita.
Qafarta
daya saman daya take zaue cikin qawataccen parlor din nata da idan ka kirashi
kai taaye da aljannar duniya bakayi kuskure ba,duk da ita a nata ganin sam har
yanzu bai kai matsayin da take buri tsari da kuma mafarkin yakai ba.
Dukkan
hankalinta ta baiwa zuwaira dake zayyane mata jawaban da muhimmancinsu a
wajenta ya wuce kimar komai data mallaka a duniya. Jawabin dake da wani irin
kima tamkar ta zinare a idanunta. Duk da bayanan ba abinda suke haifar mata sai
wani irin tashin hankali. ba irin
bayanan da take buqatar taji kenan ba.....amma duk da haka suna da muhimmanci a
wajenta,don sune zasu zame mata tamkar tsani kuma fitilar da zata haska mata
matakalar da zata taka zuwa matakin gaba.
"Amma fa tana qoqarin ganin ta aiwatar da
aikinta......saidai ban hangi wata
shaquwa soyayya ko kusanci da junansu ba ko kadan"
"Wannan kuma aikinta ne......ita kuma ya kamata ace ta
fara samar da wannan dangantakar a tsakaninsu......a nan gazawar tata ta
fito.....ta kowacce hanya ya kamata ta yaudari zuciyarsa har ya aminta da ita
ya miqa mata wuya.......aikinki yana kyau zuwaira,ina buqatar magana da ita
yanzun nan kafin na yiwa tufkar hanci tun daga tushiya"
"Yanzun zan sadaki da ita uwar dakina" Zuwaira ta
fada cikin karsashi gami da jin dadin lambar yabon data samu.
Batasan
adadin sau nawa ta duba agogo ba tana zaman jira da dakon kiran zuwaira.
Qaguwar da tayi ya hanata jira zuwairan ta kirata ta maida kiran zuwa wayarta.
Ya shiga
a daidai kuwa,sanda take rusune daga bakin bedroom din sabreen tana qoqarin
fahimtar da ita amfanin kiran.
"Ina jinki kamar d'iyata ko jikata....ki daure ki
saurareta,taqi kadan zai rage ku rabu in sha Allah". Duk bata gamsu da
matar ba,duk da batajin nutsuwa da matar ko kalamanta,amma a ciki akwai abinda
takejin gaskiya ne,a ciki akwai abinda takejin da gaske ya kusa tabbata din
TAQI KADAN YA RAGE SU RABU.
Hannu ta
saka ta karbi wayar,sai ta tura qofar bedroom din ta rufe ta koma ciki. Tana
takawa cikin idanunta suna kan fuskar wayar,yau din a matuqar tunzure take,so
batason wani magana da zata sake hasala hali da kuma yanayin da take ciki.
Gaban
madubinta taja stool ta zauna,sannan ta kunna wayar ta sakata a hands free ta
dorata saman madubin,sannan kuma a hankali ta maida idanunta saman fuskarta
kamar me kallon maamah din zaune a gabanta.
"Ina jinki" Ta furta a nutse yana goye hannuwanta
a qirjinta.
"Ina fata kina cikin lafiya da kuma aminci qarqashin
kulawar d'ana?" Tayi maganar a nutse tana son kamo bakin zaren ainihin
maganarsu. Kamar ba zata amsa mata ba,sai ta daga idanunta daga kallon dogayen
yatsunta da gaba daya lallen da akayi mata na aure ya fice tas,tamkar ma ba'a
taba digawa yatsunta lalle ba,ta maida oily eyes din nata cikin madubin daya
bayyanar da fuskarta dinnan me shimfidadden kyau dake dauke yau din da wani
irin kwantaccen fushi. Zubawa fuskar tata idanu tayi kamar yau ta fara ganin kanta
da kanta,iya kallon kawai yana motsa zuciyarta gami da tuna mata a karan kanta
wacece sabreen,wani sashe na zuciyarta ya motsa yayi aikin daya jima baiyi
ba,taji wani abu ya darsu a zuciyarta wanda ta jima tana yunqurin daddago dashi
amma yana komawa
"Ki ajiye wannan a gefe.....yaya jikin huda?" Tayi
mata tambayar da take kwana da ita tana tashi ba tare da tasan waye zata yiwa
ita ya kuma basu cikikkiyar amsar da take buqata ba.
"Jikin huda?.....alhamdulillah......saidai ban da
tabbacin yadda ya kamata ya kasance". A hankali ta lumshe idonta tana son
yiwa amsar tambayar tata fashin baqi. Bugun zuciyarta yana son ninka gudunsa
saboda samun mabanbantan amsoshi daga mabanbantan lunguna da saquna na
zuciyartata wadanda basuyi daidai da fatanta dama abinda takeso taji ba.
"Mu ajiye wannan......zan dan yaba miki game da yadd
kike qoqarin ciyar dashi abinda muka baki,saidai har yanzu kin gaza cimma
manufar abinda kikeyi din......caring kulawa.....ba wata halitta da batasan
kulawa.....dole ki fara samun zuciyarsa kafin ki samu cikinsa da
jikinsa....."
".......ba wannan cikin jarjejeniyarmu.......wai
shin..kina zaton ina da buqatar zuciyarsa?,ko ina da buqatar hanyar da zata
sadar dani ga shiga zuciyarsa?". Tayi maganar kanta tsaye da wani irin
tsauri,saboda zafi da a yau zuciyarta keyi mata,tana jin kamar wani abu me kama
da gajiya da kuma fara jin takura yana mintsinin zuciyarta.
Murmushi me
sauti maamah din ta saki tana gyara zamanta
"Bana fatan ki samu zama ko shiga zuciyarsa na
dindindin,a taqaicema dai....banda yanayi irin na lalura banjin kinkai quality
din da zan baki license na shiga zuciyar mutum me tsada,namiji irin muhammadu
ba.....amma karki manta,dole ne ki sadaukar masa da komai don isa ga
burinmu.....idan nace komai ina nufin komai da komai fa,na zabeki ne saboda ina
da tsammanin zaki iya bada komai don cikar muradina.....koda kuwa jikinki
ne...."
"Ya isa!" Ta furta a tsawace saboda jin maganar
tata ta fara shallake guri,uwa uba tana neman fin qarfin kanta.
"Kibi a hankali......a yanzun duk da ban mallakeshi
ba,amma zakisha mamakin abinda zai biyo baya idan har na shaida masa matarsa
tana min shouting tana kuma dagamin murya....." Zafin radadin maganarta ta
farko bata saketa ba,don haka bata maida hankali sosai akan maganarta ta biyu
ba. Burinta shine ta furzar mata da abinda yake ranta,tana jin kamar takai
maqurar da zasu dinga wasan tamaula da ita tsakanin ita da d'anta.
"Zanci gaba da ci dashi kaman yadda iya abinda yake zayyane kenan a bisa
yarjejeniyarmu......daga hakan banajin zan qara akan komai.....faduwarki ko
nasararki ya ta'allaqa ne da yadda na samu tabbacin lafiyar qannena" Daga
haka ta katse wayar kawai tana ajeta a gefe.
Taso
tayi tariyar maganganun da sukayi da maamah din,amma a yau sai taji gaba daya
bata da buqatar tuna komai.....kawai tana jin ba zata iya ci gaba da zamowa
kamar tamaula tsakanin su ba. Wani irin confidence takeji,saita miqe tana
komawa bakin qofar da zummar ajewa zuwaira wayarta,ta dauka duk sanda ta
dawo,don ko haduwa da ita bata sonyi. Ga mamakinta a tsaye ta sameta a bakin
qofar kamar wadda aka bawa gadinta. Wani kallo ta jefeta dashi tana jin sam
matar bata mata ba
"Ba wani abu da ake buqata?" Ta fada da sauri
bayan ta karbi wayar ganin sabreen din na zummar shigewa ciki
"Babu" Ta bata amsa a taqaice tana maida qofarta
ta kulle.
Yadda
yau yarinyar ke amsa mata magana a tsaitsaye sai takejin kamar akwai abinda ta
taka,akwai abinda ya bata confidence a kanta. Ci gaba tayi da juya wayar a
hannunta tunaninta yana yin nisa gami da rarrabuwa kashi kashi. Wani tunani ya kutso mata cikin kwanyarta
"Me yasa ba zaki murza kambunki ba?,ki gwada qarfin iko
da mulkinki ba har akan fu'ad din?" Wani sashen na zuciyarta ya bata
shawara. Shuru tayi tana sauraren daya bangaren tare da juyar maganar cikin
kwanyarta. Kai ta gyada tana bawa kanta tabbacin tabbas wannan din zaiyi
aiki.....koda baiyi diki dari bisa dari ba to akwai yiwuwar samuwar galaba.
Tana
qoqarin kiransa ta shaida masa tana buqatar ganinsa sallamarsa ta mamayeta.
Tana amsa sallamar farinciki na cika
zuciyarta yadda Allah ya dubeta ya jefo mata shi,saidai a saman fuskarta ba
haka bane. Ranta yana hade,hakanan ta boye duk farincikinta don tanason ko meye
zata gaya masa ya daukeshi da muhimmanci.
Sai
daya iso gabanta ya zame yana gaidata ta hanyar tsugunawa saman qafafunta.
Bayan ya gama gaidata din shuru ya biyo baya,a nutse yace
"Ba komai da ake buqata?,ba wani matsala?" Yayi
tambayar data zame masa wajib duk sanda yazo gaidatan don qoqarin sauke haqqin
Allah da yakejin ya zama wajibi ya sauke din.
Kai ta
girgiza fuskarta a daure.
"Ba abind nake buqata.....amma matsala dai
akwaita". Daidaita tsugunnonsa yayi kafin ya zame ya zauna sosai a
gabanta. Duk sanda tayi wannan yanayin kota furta magana makamanciyar wannan
zai wahala idan ba wani aikin bane zaya zameshi. Idanunsa yadan lumshe gami da
budesu duka lokaci guda cikin qoqarin hadiye fargabarsa,yana tunkarar qalubale
komai girmansa.....gaagwarmaya komai wahala da kuma taurinta,amma har yanzu
zuciyarsa baya iya jure wadannan halayen da maamah din,dabi'unta suna kassarashi,ya
kasa sabawa,baisan me yasa ba,ko don ita dinn wata jigo ce da abubuwanta ke
tafiya ba yadda ya kamata ace sun tafi ba?.
"Wacce matsala ce?,me yake faruwa?" Ya tambayeta a
nutse.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 38
_Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; "idan
dayanku yazo masallaci,ya duba takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya
kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_
*_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin
ba najasa a jiki_*
38
"Muhammadu" Ta kirashi da ainihin sunansa,ba tare
kuma data bari ya amsa ba ta dora
"Nikam bansan a rayuwa akwai wani abu da yafi
haihuwarku da nayi muhimmanci ba"
Idanu ya zuba mata yana jin tamkar ya tashi ya fita da gudu ya tserewa
maganganunta,don yasan zai wahala ba kamar kullum bane,dora masa nauyi da
mas'uliyyar da zai gaza dauka kota masa tauri. Kai ya girgiza,ya buda baki zai
magana ta sake danneshi da kalamanta
"Bansan wanne irin rashin muhimmanci nake dashi a
rayuwarku ba da har zan zartar da hukunci cikin rayuwarka,nace kum ga alfarma
ko abinda nakeso kayimin ka gaza yi din,ace har yanzu maganganun ameenatu da
umarninta yana zama gaba da nawa?" Ta qarashe maganar tana jin dacin haka
sosai har cikin zuciyarta. Batasan wanne tozarci ma ya kamata ameenatu ta
fuskanta ba aduk sanda haqanta ya cimma ruwa,har yanzu idan tayi hasashen
abinda zata saka ta fuskanta sai taga wannan hukuncin yayi kadan.
Sam baya
qaunar ta dinga sanyo maganar anni cikin maganganu da ayyukansu,don bazai iya
tuna sanda anni ita tayi magana a kanta ba indai ba alkhairi ba.
"Muhammadu.......yanzu ni da hannuna na baka amanar
yarinyar mutane......na roqeka ka mu'amalanceta kamar kowanne miji da
mata.......ka kyautata mata ma faranta mata,ka jata a jiki amma haka ga
gagara?,ka kasa cikamin wannan alfarmar da zata bayya a irin kima da martabata
a idon yarinyar?". Qasa yayi da kansa,shi maganar ma nauyi tayi masa sosai
akai. Ta wani gefen kuma ranshi da zuciyarsa suma motsa. Yanzu har taurin kan
yarinyar da tsaurin idonta yakai ace ta kawo ma maamah qararsa?,har da maganganu
irin wadannan marasa dadin ji?. Sai data gama dukkan wani fada baice komai
ba,har sai da tayi shuru sannan yace
"Kiyi haquri,in sha Allah za'a sake yin qoqarin gyarawa
da canzawa". Ya furta a taqaice. Har cikin ranta yadda ya amsa mata haka a
sauqaqe ya faranta mata sosai
"To Allah yayi albarka" Ta fadi kalmar da bazaice
when last da yaji ta fada ba. Muryarsa a sanyaye ya amsa mata,sannan ya miqe
yana mata sallama yana fita daga falon.
Tun kafin
ya qaraso Jordan ya wangale masa qofa,da wani irin zafi ya isa ya shige motar
Jordan ya maida murfin motar ya rufe. Suit dinsa na sama ya fara ballewa yana
zareta daga jikinsa saboda wani irin zafi da yakeji tun daga zuciyarsa har
cikin fuskarsa. Iske me qarfi ya fesar daga bakinsa bayan ya zuqi wata
"Wanne abune meqarfi da girma a tsakaninsu bayan
wannan?" Ya jefawa kansa da kansa tambayar yana motsa labbansa.
"Ita ta shiga jikin maamah ko maamah ce ta shiga
jikinta?" Ya sake maimaita tambayar da ba wanda zai iya bashi amsarta.
Yanzun har matsayinta da girmanta wajen maamah yakai ya samu sanyawar albarkar
maamah din saboda dalilinta?,wanne aiki take mata haka me faranta rai bayan
abinda yake suspecting?. Tunanin daya rakashi kenan har cikin office dinsa,ya
kuma wuni yana tayashi zama,duk kuwa da uban tarin ayyukan daya samu suna
jiransa. Duba documents da sanya hannu cikin wasu takardun,wasu takardun suna
da buqatar hankalinsa da nutsuwarsa kafin yakai ga sanya hannu,da qyar ya hada
hankalinsa bayan sallar la'asar ya soma duba wasun,bayan ya yiwa kansa matsayar
matakin da zai dauka.
Komawa
tayi ta sake kwanciya bayan sallar la'asar din,tana lissafin nan da awa daya
koda rabi zata shiga kitchen saboda shi.....saboda mutumin da ba ganin girma
qima ko martaba sam sam tsakaninsu. Idanunta ta runtse,a yau tana jin wani zafi
zafi na yadda maamah ta bautar da ita. Batasan me yake tilastata lallai saita
yi sai kuma ta cika muradin maamah din ba. Tsaki taja tana bude idanun nata,sai
suka fada saman gift din da anni ta bata ranar da suka je.
Dan
murmushi ta saki qasan zuciyarta,matar ta kwanta mata a rai,tana da wani irin
calmness me taba zuciya nutsuwa da kuma wani irin kwarjini. Tashi tayi tsam ta
daukosu ta dawo ta zauna saman abun sallarta data tashi ta soma budewa tana
tuna fuskar matar da takejin kamar ta taba ganinta a wani wajen kafin yanzu.
Littafin farko ta dauka daya qunshi addu'o'i akan kowanne abu,harkokinmu
na yau da kullum. Shafin farko ta bude,sai ta dinga tuna zamanin da ummensu ke
raye,Lokacin da take tsaye a kansu kai da fata,ba batun fashin islamiyya ko
wani abu da yayi kama da wannan. A duk dare itace malamarsu,zata zauna a
tsakiyarsu saita tabbatar kowanne karatunsa ya zaunar masa akai,musamman
karatun addini da a nan tafi qarfi,na bokon tafi jiran abbansu idan ya
dawo,musamman idan ya zamana itace da girki,idan ba ita bace dole saita dauki
uzuri an bata lokaci.
Hannu
tasa ta shafi addu'ar farko da sam ta mantata cikin rayuwarta,ummensu itace ta
fara koya mata ita tana kuma iya tuna lokacin har yanzu,sai ta tashi ta koma
saman sofa ta zame kadan tana bin addu'o'in daya bayan daya tana dubawa suna
kuma sake tuno mata da kansu.
Sosai
takejin dadin karatun,don ya debe mata kewa me yawan gaske. Babu zato daga
saman kanta din,daidai wata kyakkyawar qaramin luxury stand taji qaraurawa tana
kadawa. Zubawa wajen ido tayi,wata mulmulalliyar na'ura ce da take zubi da
telephone. Tunawa tayi amna ta taba dagawa tayi kira zuwa parlor sanda
sukazo,sai a sannan ta tuna na'urar sadarwa ce da aka shiryata duka gidan da
kuma tsakanin dakunan gidan har zuwa Kutchen,wannan ya bata qwarin gwiwar saka
hannu ta daga ta sanya a kunnenta.
"Ranki ya dade......malamarki ce tazo,sabuwar malamar
da yallabai ya daukar Miki saboda karatun yamma".
"Malama kuma?" Ta tambayi kanta da kanta cikin
tsananin mamaki tana son tuna yaushe sukayi wannan maganar da shi?.
"Duk cikin salon da zai miki mugunta ya cusguna miki ne
kaman yadda ya dauki alwashi". Ido ta lumshe tana budesu sannan a nutse
tace mata
"Ki sallameta zuwaira......ko kuma ta jira wanda ya
tattagota din" Daga nan ta kife wayar tana komawa ta zauna qirjinta a
quntace.
Wannan
abun da yayi me yake nufi kenan?,ita din jahila ce?,ko batasan komai ba saishi
zai sanya a karanta mata?. Wannan tunanin ya tsaidata,sai data gama baqin ran
da bacin ran sabon salon wulaqanta mutum daya bullo dashi......hakanan ba don
taso ba ta miqe tana wucewa kitchen.
Tana
shiga zuwaira na fadowa,sai ta waiwayo tana kallonta. Cikin jikinta wani abu ya
bata,ta yaya duk wani motsinta zuwairan kamar tana biye dashi ne?
"Ranki ya dade dame za'a taimaka miki dashi?" A
nutse ta juya kawai ta fara aikin gabanta,kamar ba zata amsa mata ba sai kuma
ta tura mata lettuce da cabbage carrot da peas tace ta gyara ta yanka mata.
Zaman
kurame kawai sukeyi cikin kitchen din,zuwaira nata satar kallonta tana son ta
dan tabota da magana don ta gina alaqar sabo a tsakaninsu amma bataga wannan
fuskar ba sam
"Tashin hankali" Zuwairan ta fada qasa qasa,daga
ita har mijin haka fuskokinsu suke kamar na shanu? Ta tambayi kanta,ita dai har
yanzu bata taba ganin fara'a ko dariyar dayansu ba.
Sai da
suka kammala komai sannan ta fidda magungunan zata cakuda kaman yadda ta saba.
Ta bude murfin ta karkata gorar,sai kuma ta tsaya cak. A hankali ta daga
idanunta ta zubesu akan zuwaira data tsaida komai tana son tabbatar da zubawar.
Karon farko da cikin jikinta taji kamar nauyin idanuwan wani yana kallonta
zatayi abinda bashi ya dace ace tayi ba akan wani,duk kuwa da tasan jirgi daya
shine ya debo zuwaira da ainihin me kwangilar,amma a yau saita ji wani nauyi.
"Zaki iya bani space?" Ta jefa mata tambayar taba
dinke girarta sosai fiye da dazu.
"Au to....to ranki ya dade" Ta fada adan daburce
sannan ta juya tana fita a kitchen din. Haushi ya sanyata kwarara da yawa,idan
komai ya qare ai a huta,taga ta inda zata tuhumeta kuma,sai taja tsaki tana
jefa roban a shara sannan ta juya ta fice tana baiwa zuwaira dake falo umarnin
taje ta jerasu,sai ta wuce kai tsaye zuwa dakinta.
Itama
din a gaggauce ta shiryasu tana kallon kayan,baki ta tabe,tana jin haushin
yadda lafiyayyen abinci irin haka yake salwanta,ga nasu iyalan can cikin yunwa
da buqatar abincin da baikai wannan bama,amma akan mutum daya anata asarar
lafiyayyen abinci irin wannan. Hankalinta ta maido jikinta da sauri,saita juya
tana barin falon cikin son kiyaye dokarsa da tsoron kada ya dawo ya sameta a
wajen kamar yadda ya shardanta mata.
K'arfe Tara
da wasu mintuna motocinsa suka tsaya a farfajiyar gidan bisa halastaccen
parking da kowanne driver na kowacce mota ya qware akai. A nan harabar gidan ya
barsu ya wuce ciki shi dame sunan malam,wanda iyakarsa qofar parlor din farko
ya juya shima yana komawa cikin guard da security na gidan dake qoqarin
tabbatar da tsaro da lafiyar kowacce mota kafin masu tafiya su wuce a sake
tabbatar da tsaron gidan sannan a maidashi a rufe kaman yadda yake,shida da
fita kuma sai da izinin masu gidan.
A
hankali yake ratsa falon farko zuwa na biyu kafin ya isa stairs dinsa. A gajiye
yake don duk sanda yayi dare irin haka a company to tabbas cinkoson aiki ya
riqeshi ne.
Tun daga
nesa yana taka stairs din ya hangi maqullin maqale jikin qofar,ya isa a hankali
ya sanya hannu ya cire sannan ya tura qofar parlor din. A nan zarginsa ya
tabbata,mug din da yayi amfani dashi a daren jiya yana zaune abinsa dirshan
saman side table din,yayin da dish din da yayi amfani shima dashi yake zaune
saman dining abinsa hankali kwance.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
39
_Daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace:mazan
Allah S A W ya ambaci ranar juma'a,yana cewa "A CIKINTA KAWAI WANI
LOKACI,BA WANI BAWA MUSULMI DA ZAI RUSKETA YANA ME TSAIWA YANA SALLAH YANA
ROQON ALLAH WANI ABU FACE SAI ALLAH YA BASHI ABINDA YA ROQA DIN". sai
manzon Allah yayi nuni da hannunsa na qanqantar lokacin (ma'ana baida
tsaho,Allah yasa muna cikin wadanda zamu yita ruskarshi)_
Wani bacin rai ne karon farko ya sauko masa,ba abinda ya
dawo masa akai sai abinda ya faru a dazu. Yadda maamah ta fitittike tana
jaddada masa yadda takeso ya mu'amalanceta ko ya kula da ita,amma ko kusa ko
alama shi baiga alamun tasan darajar kalmar aure ba koda kuwa auren 'yar tsana
aka daura,ballantana shi data deba kudaden da ranta keso,karamci kuma ya sanya
suka qara mata da wasu abubuwan da shi kansa baisan me su anni suka kashe ba.
Duka sai
yaji abun bai masa ba bai kuma zauna masa akai ba,ya kamata ya qara bata
lesson. Yana takawa zuwa bedroom din nasa yana watsar da kayan hannunsa,kama
daga socks takalminsa suit briefcase dinsa da sauran tarkacen daya shigo dasu.
Wani budewa hancinsa yakeyi yana tsukewa saboda bacin rai,ya tsani raini ya
kuma fahimci halinta ne,ya tsani rashin kunya ya kuma karanci dabi'arta ne. Bai
dakata ba sai da yayi wanka,ya hadawa kansa fruit salad a gurguje yasha,sannan
ya zauna yana jawo wayar sadarwar yana kiran number dakin nata.
Ta gama
komai tuntuni,ta kuma jima da kwanciyar saidai baccin da baizo ba. Tayi mamakin
jin kiran,saita sanya hannu ta dauka tana tunanin zuwaira ce,ko meye kuma ya
faru a daren nan oho?.
Muryarsa
taji sabanin muryar zuwaira da tayi tunanin itace. Har tsakiyar kanta sautin
muryar ta sauka mata da wani irin zuzzurfan amo
"Hello" Ya fada yana qoqarin hadiye bacin ran dake
taso masa. Matsar da kan wayar tayi daga kunnenta da zummar sauke wayar,kaman
yasan abinda take shirin yi ta tsinci muryarsa cikin zafi yana magana
"Kika kuskura kika sauken waya....zakisha mamaki
na". Tsauri umarnin nasa yayi mata,saita samu kanta da gaza ajiye wayar.
Sau tari tana mamakin yadda yake cin galaba a kanta haka da sauri,umarninsa
yake saurin ratsata,wani abu guda daya da ta raina akan kowanne d'a namiji.
Bata taba zato ko tunanin akwai wani lokaci da zaizo da wani namiji zai iya
juyata ko ya canzata daga abinda yayi mata daidai cikin rayuwarta ba,sai ga
abun yana tafiya cikin rashin zato bare tsammani.....kamar a cikin duniyar
mafarkinta.
Ci gaba
tayi da riqon wayar ba tare data ce komai ba,haka daga nasa bangaren bataji ya
sake furta komai ba. Kusan minti daya wayar na a riqe a hannunta,sakannin kuma
suna ci gaba da motsawa. Kaman daga cikin wayar taji an murda qofa an kuma
budeta. Sauyin yanayin qamshin daya soma mata sallama ne ya shaida mata tabbas
an bude mata qofa,ba kuma cikin wayar bane a zahiri ne.
Tana
kwance ne rub da ciki,don haka ta waiwaya kadan don tabbatarwa da idanunta.
Muhammad jadda ne,tsaye daga baki qofar dakin yana riqe da handle din,daure da
lallausan farin towel wanda ke dauke da tambarin VERSACE baro baro a jiki. Gaba
daya towel din ya daurashi ne daga iya qugunsa,ya kuma sauka sosai zuwa
mararsa,abinda ya bata damar ganin full ginannen jikin nan dake cike da
lallausar gargasa data kwanta tayi luf luf.
Fadin
kafadunsa ya sanya bata ko iya hangen qofa,sai yau ta sake fahimtar GIANT ne na
gaske,da murjajjen jiki da kuma ginannun tsokokin damtse dana qirjin
wato(muscles).
Wani
mahaukacin faduwa gabanta yayi,a yau taga abinda bata gani ba a wancan ranar
data sameshi a parlor dinsa.....ko don yau din a tsaye yake da dukka tsahonsa
da kuma wadataccen haske a dakin nata?.
Duk yadda
take da kafiya da taurin rai sai data gaza ci gaba da kallonsa,wani irin tsoro
ya kamata wanda ya tilasta mata maida kanta ta kwantar saman pillow tana baiwa
qofar dakin baya,wato qeyarta ke kallon qofar kenan.
Gabanta
ya sake yankewa ya fadi sanda taji ya maida qofar ya rufe gami da murxa key,ta
fidda idanunta dukka biyun waje tanason yin hasahen abinda zai iya faruwa da
ita,saidai bata gama wannan ba taji an sanya hannu an birkitota gaba daya,sai
gata ta koma rigingine a maimakon rub da ciki da take a dazu.
Gaba
daya ya zame mata rumfa saman kanta,tamkar me barazanar hanata ganin komai na
dakin sai wannan mudadden jikin nasa.
Da
hanzari ta sanya tafukan hannayenta guda biyu da zummar tureshi saboda yadda
yake neman hade space din dake tsakaninsu,amma ko gezau kamar ma ba wani hannu
daya sauka a jikinsa. Bai bata second chance ba ya kama hannuwan nata ya matse
cikin hannunsa guda daya.
Qoqarin
qwatar kanta sosai ta farayi tana tureshi,amma baiko motsa ba,yana riqe da
hannuwanta gaba daya yana kuma ci gaba da zube mata idanunsan nan
"Ka sakeni......ka cikamin hannu" Ta fada sanda ta
fahimci ko kusa ko alama bata da qarfin da zata iya amsar kanta a hannunsa. Ta
cikin idanunta ya fahimci laushi tayi,hakanan qarfinta ne ya fara qarewa.
Bayajin zai qyaleta haka sai ya bata mummunar barazanar da ba zata qara kai
qararshi wani guri ba. Duk dabaya tunanin wani tsoro me yawa a tattare da itan
duba da ita din WACECE?. Ba wani sabon abu bane a wajenta cudanya da maza,duk
da maza suna suka tara kamar yadda mata suma suka tara suna.
"Inajin a matse kike a sauke miki jarabar da take
damunki ko?,wannan ya sanya ba kunya cikin idanunki kika je kina kai qara a
inda kike tunanin za'a sanyani sexual affairs dake ko?". Duf wuta ta dauke
mata,daga iya kalmar sex data shigo maganar ta tabbatar lallai babbar magana
aka baro. Yaushe takai qararsa?,kuma gurin waye?,me tace tana da buqata?,duka
wadannan tambayoyin sune suka soma mata yawo saman kai,kuma inda tana da hali
tana da buqatar amsarsu,saidai a yadda komai yake a hautsine bata jin tana da tattararriyar
nutsuwar nemansa da wadannan amsoshin.
Tana aje
wannan tunanin yana sakin hannun nata,ya miqa hannu da wani irin zafin nama
zuwa Coller din rigarta,wadda tsaurin riqon da yayi mata ya bawa bottom daya
damar tsinkewa fit. Fitarsa sai ya zamana kamar ya hada da fitar nutsuwa daga
gangar jikinta,wani tashin hankali ya rufto mata har kala biyu. Na farko yadda
yayi kusa da ita da towel din da kadan ya rage marabarsa da tsirara,don babu
abunda ya lullube illa mararsa zuwa gwiwarsa,na biyu kuma fitar maballin
rigarta sai ya tuna mata waccan ranar a kitchen. Ranar da har yau idan ta dauki
rigar data sanya a ranar sai taji qamshin wannan mayataccen turaren nasa,abinda
ya sanyata kenan tayi adabo da rigar duk kuwa yadda take sonta. Saboda duk
sanda ta sakata haka yadda abin ya faru zai yita dawowa kanta,hakanan kuma
zatayita tuna yadda ya azabtar mata da lips haushinsa yayita kai komo kenan a
ranta har sai ta raba kanta da ita.
Matse
hannunta yayi yana saukar dashi daga gaban rigar don so yake ya tsinke maballi
na biyu,kafin ta iya komai har ya samu nasarar yin hakan,ya kuma wuce zuwa
maballi na gaba,abinda ya sakata saka hannuwanta dukka biyun ta cukuikuye gaban
rigar,cikin fushi kuma taci gaba da magana
"Don't touch me.......ka daina tabani mana.... Wai mene
haka?!". Ta qarasa fadi sanda ya tattara hannuwanta da zummar turesu,cikin
rashin sa'a hannuwan nasa suka samu nasarar sauka daidai saman tudun qirjinta
wanda ke tsaye car babu bra. Sabonta ne idan zata kwanta dukka saita ciresu,don
tana jin kamar suna hanata cikakken bacci.
Daga shi
har ita ba wanda baiji kaman an yarfa masa wuta a jikinsa ba,yayin dashi ya
hada wani azababben shock daya ratsa jininsa da wani irin mahaukacin gudu ya
aike saqo qwaqwalwarsa ya kuma dawo da saqon yana rabawa zuwa sassan jikinsa
gaba daya.
Taji
komai har cikin jinin jikinta,sai taji kamar an zare mata dukka wata laka tata
da wani irin firgici da tsoro bakinta ya furta
"Please......don Allah ka bari" Kalaman nata na
qarshe ya fito da zirarowar hawaye zuwa saman kuncinta.
Duk yadda
yaso ya zarce da tsoratata gami da gigitata cikin mugunta sai yaji ya kasa,haka
ya sake mata rigar yana dauke idanunsa daga kanta ba tare daya bari sun sauka a
inda take boyewar ba tamkar sulalewar ruwan kalkashi a tafukan hannun mutum.
Zuciyarsa ta cika da wani irin mahaukacin mamaki......daga ina wannan weakness
din ya taho?,ya tambayi kansa da kansa can qasar zuciyarsa. Bai taba niyyatar
zai dauki mataki akan wani abu ba tare daya qarasa aiwatar da qudurinsa ba,bai
taba jin rauni akan duk wani abu daya sanya a gaba ba sai akan wannan dan
qaramin aikin.
Tattare
jikinta tayi waje daya tana neman hanyar sauka daga saman gadon,amma sai ya
sanya gwiwarsa ya take gefan rigar,ya waiwayo a nutse ya zube mata idanunsan
nan masu dauke da wani kakkaifan maganadisu,wanda duk yadda sukakai ga haske
sun surka launi a yau din.
"Kina zaton zan hada jiki dake ko?,over my dead
body......duk randa zan hada jiki dake ki sanya a ranki ranar mutuwarki ne
kawai yazo,don zan niqaki da kyau kaman yadda engine ke niqa tsaba ya koma
gari....." Yatsunsa ya murza saman fuskarta sannan yace
"Sharadi guda biyu ne zan baki idan kin kiyaye
shikenan.....na farko....kada ki kuskura ki sake kaiwa maamah qarata koda akan
meye kuwa....ban hanaki kaiwa anni ba idan kinga zaki iya fine.....sharadi.na
biyu duk randa na sake miki umarnin yin wani abu kika watsar kina daukan kanki
wata tsiya.....zakiga abinda zai biyo baya,sai na sanya an sako Michael yayi
dambu da namanki,ki tashi kizo ki gyaran sassa.....ki kuma samu note pad ki
rubuta day one don lissafinmu yafi tafiya daidai" Yana kaiwa nan yaja jikinsa yana sauka daga
gadon,ya kuma fara takawa hankali kwance yana fita daga dakin.
Da
sassarfa yake haurawa saman cikin tuhumar kansa da kansa. Baisan kanshi da
kasawa ko gazawa ba,ya akayi ya kasa bata mummunan punishment yadda ya kamata?.
Koda ya tsaya gaban mirror na toilet din,sai ya dinga jin haushin kansa da
kansa. Baisan wani weakness nasa ko kadan ba......amma sai ya samu kansa yana
tsoron kada fa wannan ya zama shine weakness dinsa?.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 40
_Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya
kasance yana nemawa mumunai maza da mata gafara a kowacce juma'a_
_harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga
ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA
DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA MATSANANCIN SONSA S A W_
________________________________
Moroccon cotton jallab ya saka ta maza maroon color me
gajeran hannu,wadda aka yiwa ado da gold din zarurruka masu kauri. Har hantar
cikinta sai data kada sanda taji fitowarsa zuwa falon,amma ta dake bata nuna
ba,tana duqe tana goge stand tv lokaci lokaci tana goge 'yan hawayen daketa
qoqarin lallai sai sun sake karya mata zuciya.
Kai
tsaye ya wuce saman minotti sofa dinsa yana lumshe idanunsa,wata azababbiyar
kasala nason saukar masa. Dole yana buqatar wani abu da zaiyi awakening dinsa
for some hours don yana da aiki.
"Ke..." Ya kirata idanunsa suna lumshewa kadan.
Kiran ya mata ciwo,amma kuma dole ta nuna tasan da ita yake maganar.
"Bring me some coffee" Ya furta yana dauke idonshi
a kanta ya lumshesu don kaucewa kallonta.
Ajiye
duster din hannunta tayi qirjinta na mata wata suya,ta fara takawa don isa
qofar da zata saukar da ita daga saman
"Hey.....ina zaki?" Ya furta da rashin qwarin
murya. Sai kuma ya mata nuni da nasa kitchen din da idanunsa,kai tsaye ta gane
me yake nufi,ta kuma canza akalar tafiyar tata zuwa can din.
Tayita
dube dube da tsoron kada ta tabo wani abun duba da yanayin machine da utensils
din dake kitchen din daya sake shan bamban dana qasa nesa ba kusa ba. Da qyar
ta samu ta kammala,duk da bata da guarantee din yayi ko baiyi ba,don itadai ba
damunta yayi ba,koda ya dameta ma ba irin wannan bane.....nasun irin nasun ne
wato daidai matsayinsu yaku bayi.
Saman tea
tray ta hado da cups. Ta qasan idanu cikin lumsassun idanunsa yake kallonta
sanda take nufoshi da wani irin kallon da zaka rantse da Allah bacci yakeyi.
Yana qoqarin binciken kansa me yasa yaketa tunawa da abinda ya faru?,amma ya
rasa dalili,haushin kansa sosai yakeji a yanzun,yana ganin kamar wannan hanyar
ta sanya tsoro a zuciyarta bazatayi aiki ba.....zata iya dasa masa matsalar da
zata gagari gangar jikinsa watan watarana.
Yadda
jikinta yayi laushi sosai yake karanta,yana mamakin macen data saba
mu'amalantar maza kala daban daban me ya sanyata jikinta yayi laushi don ya
mata wani qaramin riqo da bai taka kara ya karya ba?.
"Kana murzata ne ta hanyar da ba haka su suke mata
ba,da ta irin tasu hanyar ce qila ba abinda zai sanya jikinta laushi" Wani
sashe na zuciyarsa ya bashi amsa.
A gabansa
ta ajiye tana jin inama zata samu wata dama ta zuba masa wannan abun cikin tea
dinsa?,qila cikin kwanaki uku ta samu nasarar da zata cika aikinta,ta tattara
tabar wannan DUNIYAR tasu ta koma tata ainihin duniyar.
"Serve me" Ya fada da murya can qasa. Sake baci
ranta yayi,gaba daya a hankali yana son canzata ta koma 'yar aikinsa kenan
kome?. Tsugunnawa tayi a nutse ta soma zuba masan tana qoqarin danne zuciyarta
amma ta kasa jin relief. A sanda parlor din ya dauki shuru,wayarsa da tafi kusa
da ita ta soma kuka alamun shigowar kira. Kallo daya ta yiwa wayar ta dauke
kanta,yarinyar kullum ce dai wato fareeda khaleed mustapha. Qaramar tsuka
taja,ita ta sani zaa rina,mutum kamar muhammad jadda ace yana zaune lafiya bisa
kyawawan dabi'u?,ai ta qalubalanci wannan. Banda akwai wata gurbatacciyar alaqa
me zai dinga shigo da kiranta cikin wayarsa a kowanne dare?,a daidai lokaci
irin wannan da mafi yawan lokuta yake kebancewa shi kadai?.
Tana miqa
masa coffee din yana daukan wayar yana kallon screen din ransa yana baci,ya
dauke dubansa daga kan fuskar wayar da yakeji kamar ya bugata da bango saboda
yadda tsananin nacin fareeda ya soma shallake hankalinsa,ya aje dubansa akan
fuskarta dake a dinke sosai.
"Fara sha kafin ki bani" Yace da ita a taqaice.
Duban rashin fahimta tayi masa,sai ya kafeta da idanu kafin yace
"Do you think am a fool?,kina zaton zan karba nasha any
how?....." Ya qarasa maganar yana daidaita zamanshi sannan ya tura mata
teatray din
"Take a sip first" Sai data ja numfashi sosai ta
aikawa hunhunta sannan ta samu zuciyarta taci gaba da aiki yadda ya dace,me
yake nufi data fara sha?,ta tambayi kanta.
"Kada ki barwa kanki qofar zargi" Wata zuciyar ta
shawarceta. A nutse ta dauka mug din ta kurba kadan sannan ta ajiye masa,zata
motsa yace
"Hang on for a bit" Ya fadi cikin halin shariya
yana maida hankalinsa kuma kan fareeda tare da tunanin ta inda zai bullo mata.
Ambassador
yana da kima da mutunci a idanunsa,musamman daya kasance babba harda furfura a
fuskarshi,saidai fareeda tana crossing line da yawa da baya bari a crossing
masa shi.
"What's bothering you?" Ya fadi adan fusace,yayin
data narke marya Kamar qanqanuwar yarinya
"Kaineee" Labbansa duka ya cusa cikin bakinsa yana
qoqarin hadiye takaicin data bashi. Sai ya sauke idonsa akan sabreen wadda
baisan ta soma barin wajen ba sai a sannan.
"Where to?" Ya jefa mata tambayar data tabbata
yanason jin inda zata ne. Ita ba zata tsaya tana jinsa yana hirarshi da matan
banzanshi ba,ba damuwarta bane ya yanke dukan abinda yake ganin ya dace da
rayuwarsa.....amma ita kuma ba wanda zai tilastata yin abinda batayi niyya
ba......wannan din dabi'arta ne da ba canzawa. Sai data yi qaramin yaqi da
zuciyarta sannan ta iya lanqwasa harshenta ta sarrafashi tana fadin
"Dare yayi inaso na kwanta"
"Idan kin gama you can go" Ya fada cikin halin ko
in kula yana katse kiran fareeda itama gami da sanyata a DND mode sannan yaja
coffee dinsa ya soma kurba.
Sassa ne na
alfarma dake da yalwa wadatar kayan alatu dana qarau wadanda ke buqatar a
gogesu,wannan shi ya sake bata mata lokaci ya kuma dauketa har kusan sha biyu
na dare abinda ya bata mamaki samunsa sa
tayi dungurgur ya sanya system a gaba ya zuba mata idanunsa yana
sarrafata,wanda motsin takunta ya sanyashi rage mata haske sosai har baka ganin
abinda ke allon.
Baki ta
tabe ta qarasa,zuciyarta na ayyana nata waye ma yasan abinda yakeyi tsakiyar
darennan.
"You are free" Ya amsa mata ba tare daya waiwayota
ba,sai ta fara nufar qofar a ran ta tana fadin
"Shi mugun mutum ba kasafai bacci dama ya fiya damunsa
ba".
Gyaran
yayi masa sosai,don yafi qawatar dashi fiye da coffee din,don sam bai masa dadi
ba irin yadda yakeso ya kasance ba. Jallab din jikinsa ya zare ya wuce toilet
da zummar daura alwalar kwanciya bacci.
★Duk a kasalance take kowanne aiki a yau,tun daga safiya
zuwa daren da take kammala girkin daren. Sai takejin wani irin qosawa,gaba daya
ta fara gajiya da komai. Tunda take wannan shine karon farko data aboci kitchen
safe da dare da zummar dora sanwar girki.
Kamar ko
yaushe bayan ta kammala abincin,ta taka a hankali tana nufar inda ta boye
akwatin. Ta jawo ta miqa hannu ta fito dashi sannan ta bude. Kayan cikin ta
fara fitowa dasu kaman yadda ta saba,daya bayan daya kuma ta soma zubasu saman
abincin ta cakude dasu. Yau daya sai ta tsaya kawai tana kallon abincin,wani
irin rashin dadi takejin zuciyarta tana mata a yau din,a kasalance ta maida
kayan ta kuma rufe ta maidasu ma'ajiyarsu sannan ta dawo ta soma daukansu zuwa
dining don yau kwata kwata ma bata bari zuwaira ta shigo mata ba. Batason
doguwar magana,hakanan batason sanya idanu da wannan shegen binbinin kallon da
take binta dashi a kowanne daqiqa.
Dab da
zata isa dining din saita dinga ji kamar qamshinsa. Batasan ya akayi
ba.....amma tun daga waccan ranar ta haddace wannan nataccen qamshin turaren
nasa da har yanzu yake maqale jikin rigunanta guda biyu. Sosai takejin
qamshin,to amma ta raba idanunta ko ina cikin parlor din bata ga wani alamun
shigowarsa ko shigowar wani ba. Agogo ta sake kalla sanda take ajiye warmer
din,mintuna kadan ya rage ayi sallar magariba.....wannan lokacin kuwa ba lokacin
dawowarsa gida bane,don qarfi da yaji ta haddace lokacin dawowar tasa saboda
yadda ta aza dukka damuwarta akan cikar burinta na yaci abincin.
Watsar
da tunanin tayi,taci gaba da shirya komai ta kammala,ta tsaya kawai tana kallon
yadda komai yake jere saman dining din.
"Inama ace yau daya burina ya samu ya cika?" Ta
furta qasan ranta duk da tana jin wani sashe na zuciyarta kaman yana qyamatar
hakan ya faru,sai kuma ta juya tana nufar hallway din da zai sadata da dakin.
Dab da zata shige laila ta murda pivot door din tana shigowa falon tayi kwalliya sosai cikin wani silk material
da aka tsarawa dinkin daya dace da shape din jikinta sosai. Red ne colour dinsa
wannan ya sanya farar fatarta data samu gyara da pills na qara fari da allurai
na qara hips da sauransu ya sake qawata shigar tata. Kome takeyi tana da
cikakken goyon bayan hajja wadda a kullum burinta ta fita daban,ta kuma zama
daban din ta kowacce hanya cikin mata.
Idanu
suka hada,sai sabreen din ta dauke idonta kamar kullum,ta kuma taka a nutsenta
tana wuceta,tana jin bata da wani lokaci nata sam sam.
Da idanu
ta raka sabreen da wani irin kallo na qurilla,allurar kishi tana
tsikararta,tana tambayar kanta da wanne irin products haka take amfani masu
tsananin qarfi?. Tana ji ana cewa kowanne dan adam tara yake bai cika goma
ba.....to amma ita sai take ganin tamkar a halittar sabreen goma take cif cif!.
Tsaki taja
tana maida dubanta kan dining din. A yunwace ta shigo,ta samu zuwaira kuma bata
nan,tabbacin a yau kenan saita shigo da kanta neman abinda zataci.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 41
_Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace:
"anayin wanka akan abubuwa guda biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan
anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa gawa wanka)_
__________________________
Matsawa taci
gaba dayi zuwa wajen dining din,tana cike da haushin yadda a kullum ake jigilar
qawata wajen da warmers na alfarma wadanda suke bata tabbacin abinci ne
lafiyayye.....to amma kullum idan ta tuna maganar da hajja ta gaya mata akan
abincin sai ta maida qwalamarta bisa tilas. Asali ita din mutum ce da ba
kasafai ta fiya bawa irin wadannan abubuwan muhimmanci ba. Hasalima tana ganin
idan ba dominka aka shirya abu ba bazai taba tasiri a kanka ba.
A nutse
ta isa wajen,ta kuma jawo warmer din farko ta soma budeta,budewar da ya qara
adadin yunwar da takeji taji kuma bata da wata hanya illa ta toshe yunwar dake
sakadar mata hanji kamar bata taba cin komai ba.
Yau gajiya
takeji sosai a jikinta,wannan ya sanya data idar da sallah isha'i wanda duka
zama tayi a wajen bayan magariba sai data yi isha din sannan ta tashi. Wannan
Dabi'arta ce qwaya daya da har yanzu bata rabu da gangar jikinta ba,burbushin
raino da tarbiyyar ummensu,bata wasa da sallah sam koda bayan gushewar
ummen,kuma ita kanta ta hori 'yan uwanta sosai akai
(Ko hori yaranku da sallah.....tana da matuqar tasiri wajen
hana bawa sabon Allah da kuma gyara halinsa,kamar yadda Allah ya fada cikin
qur'aninsa me girma,tabbas sallah tana hana alfasha da munkari,Allah ya bamu
dacewa ameen summa ameen). Tana shirin shiga wankan saita samu kanta da
maimaita addu'o'in data karanta a littafin da anni ta bata wanda shi ya qara
sanyata jin dadin zaman. Tana nanata addu'o'in suna tuna mata da zamanin da
suke qananu......lokacin da ummee ke korasu makarantar allo ranakun weekend,ita
hadiyya da sameeha. Qaramin murmushi ya kubce mata,tadan girgiza kai tana jin
kewar lokacin quruciyar tata,tana jin inama tana da ikon dawo da wancan
lokacin,ashe ba abinda yakai zamanin quruciya dadi.
Pyjamas
ta saka baqaqe gaba daya da suka sake haska mata fatarta,sai ta dora qaramin
farin Malaysian hijab saman kanta bayan ta nannade gashinta a tsakiyar kanta
cikin ponytail holder,hakan ya sanya kan yadan tashi kadan kamar tayi acuci
maza na.
Fararen
flip flops ta zurawa fara tas din qafarta,wadda duk wani lalle ya fita a
jiki,sai tsantsar haske daga qara da gogewa kamar jini zaiyi tsartuwa.
Hankalinsa na rarrabe akan wayarsa sanda yake qarasowa cikin falon.
Daidai lokacin da laila ke saukowa daga dining din sai ya zamana mutum na farko
da idanunta suka fada a kai. Cak ta tsaya ana zare duk wani noti na
jikinta,wannan shine karon farko data taba gaba da gaba da muhammad jadda,kusan
duka a baki ko cikin magazines da news paper take ganinsa.
Duk
yadda tasha fasaltashi a zahirinsa ya wuce nan,wani irin ingarman namiji da a
iya tafiyarsa kadai ta hangi izzarsa da kuma cikar isarsa.
Kaman a
jikinsa yaji ana kallonsa,wannan dalilin ya sanya daga idanunsa yana duban
sashen da yaji jikinsa yafi rinjaye. Suna hada idanu gaba daya kwarjininsa ya
mata wani irin mamaya data gaza riqe kanta,duk wata zarra da jin kai da takeji
tana dashi a matsayinta na diya mace ya sulale yayi nasa waje. Yadda ya kafeta
da idanunsan nan masu qunshe da wani sirri sai taji komai yana kwance mata
"Barka da dare" Tayi namijin qoqarin furtawa
bakinta yana son hardewa
"Yauwa" Kawai ya amsa mata dashi.
"Nice laila....'yar gidan hajja.....hajja harira ta
maamah" Tayi bayanin a nata zaton hakan zai burgeshi ko kuma ya sake bata
matsayi na musamman a matsayinta na 'yar aminiyar mahaifiyarsa.
Fuska
yadan yamutsa kadan yana fahimtar inda ta dosa.
"Yayi kyau.....ban fadi muku banson kowa around us ba
idan ina gida?" Yayi maganar fuskarsa na wadace da wani irin daurewa kamar
baisan sunan wani abu waishi dariya ba,don dama da bacin rai ya sauko.
Kasaqe
tayi tana mamaki,tabbas zuwaira ta shaida mata,amma ko a sannan kallon banza ta
watsa mata ta wuce dakinta,don tana ganin ita ta wuce wannan dokar tayi aiki a
kanta. Tana jin kanta tamkar ita din halastacciyar 'yar gidan ce,don haka bata
ma wani tsaya amfani da dokar ba bare ta kiyayeta. Tana shigowa a duk sanda
taso tayi abinda takeso ta fita,saidai da yake dukkaninsu ba ma'abocin zaman
falon bane kowa sabgar gabansa yake shi yasa ba wanda ta taba karo dashi a
cikinsu.
"Get out of my sight......and kada ki sake bari mu
hadu" Ya fada cike da zallar umarni ba tare kuma daya kalli sashen da take
ba yaci gaba da tafiya kansa tsaye zuwa dining din.
Ajiye
wayoyinsa yayi bayan ya gama abinda yake,ya maida hankalinsa ga abincin yana
dubansa. Yau zai kawo qarshen duka wannan drama din ya ayyana hakan a
ransa,daidai sanda take fitowa daga parlor din zuwa ainihin falon da yake ciki.
Kai tsaye
dama idanunta kan dining din suka fada,don ya zame mata wani aiki na daban
kiyaye waye a wajen da kuma duba waiko ya zauna cin abincin?. Bataso yadda
tashin farko suka hada idanu ba don zaya dauka ne kawai kallonshi takeyi,take
tata izzar itama ta motsa,ta dauke kai sosai tana takawa zuwa qofar kitchen.
"Hey.....com here" Ya fada da matsakaiciyar murya.
Tanason gwada masa tsiwar amma tana tsoron abinda zai biyo baya,dole ta dawo
din fuskarta shimfide da kalar nata miskilancin.
"Serve me" Ya fada cikin basarwa yana bude
wayarsa. Cak ta tsaya,tana jin kamar kunnuwanta ne suke jiye mata ba daidai ba.
Ta zuba masa abincin fa ya buqata?,ta tambayi kanta tana neman qarin haske.
"Zuba abincin nace" Ya sake maimaita mata ba tare
daya dubeta ba. Wani irin abu taji ya tsargawa sassan jikinta. Ta dade tana
fatan zuwan wannan ranar,ta dauka duk sanda taxo din zata kasance mutum da tafi
kowa murna a duniya,amma kuma sabanin murnar mutuwar jiki taji.
Matsawa
tayi sosai gaban table din,ta ware qananun luxury table mat din ta sake
shimfidasu,sannan ya zari plate da bowl ta soma zuba komai tsaka tsakin
quantity sannan ta jera masa a gabansa.
Wayar ya
ajiye a gefansa,ya miqa hannu da kanshi ya ciro spoons guda biyu ya saka cikin
abincin sannan ya dubeta
"Oya.... Let's eat together" Ya furta yana matso
da drinks din da aka aje a wajen duk da ba abun shansa bane sam sam duk wani
drink da company ta sarrafa.
Ba shiri
ta bude idanunta a kansa,ji tayi kaman an dauko guduma an shirga mata. Cikin
qasa da minti daya tayi qoqarin daidaita nutsuwarta dukka a qoqarinta na
daidaita komai,ta girgiza kai tana fadin
"Na qoshi". Sake ware idanunshi sosai yayi a kanta
yana dubanta,abinda ya sake sanyata kenan a tsilla tsilla,tana kyautata zaton
akwai wani abu me nauyi da idanunsa ke dauke dashi,wanda muddin ya kama
zuzzurfan kallo irin wannan sai kajishi har qashinka.
"I think kin fito ne ke debi abincin right?"
Daburcewa tayi yanda ya kama abinda ya fito da ita din kansa tsaye kamar me
gani har hanji. Bata saba qarya ba koda wanne irin hukunci aka tanadar
mata,wannan ya sanya kai tsaye ta bashi amsa da eh.
"Good.....kinga wannan shi yafi kamata muci tare
ko?" Ya fada cikin sigar saukar dakai yana turo abincin gabanta. Kanta ta
sake kadawa,gaba daya yana birkitata ganin yadda yake matsantawa saita zauna
sunci abincin
"Seat down!" Ya fada da wani irin husky voice yana
buga hannunsa saman table din har abincin dake cikin plate din yana watsewa
saman table din. Batasan sanda ta zauna ba kaman yadda ya buqata tana qoqarin
kaucewa kallon fuskarsa da har hancinsa ya fara yin ja alamun tsananin bacin
rai wajen farin mutum kenan.
"Kinsan abinda zan gaya miki guda daya?" Yayi
maganar qasa qasa kamar ba shine yanzu ya buga wannan tsawar ba,bai jira ta
amsa ba ya dora da fadin
"Duk sanda kika qara yimin girki a gidan nan saikin
cinyeshi tsaf!". Gigicewa ta sakeyi da abinda yace,maganar daya fada kawai
ta sanya hasashenta ya tsaya daidai inda take zatonsa
"Be warned!" Ya furta yana ranqwafowa sosai saman
kanta har tana iya sheqar dumin numfashinsa da yake futarwa daga hancinsa. Baya
yaja ga kwashe wayoyinsa,zuciyarsa na masa wani irin zafi ya soma sauka daga
wajen yana dosar hanyar da zata sadashi da stair dinsa.
Maamah
uwarsa ce,ba yadda zaiyi da ita,amma zaiyi dukkan abinda zai iya ya toshe
kowacce qofa da zata samu nasarar budeta a kansa ko kuma waninsa muddin yana da
iko da masaniya.
Koda ya
koma saman duk yadda yaso yayi keeping kanshi busy ya manta da komai sai ya
kasa. Mahaifiyarsa......macen daya biya kudade aka daura mata igiyarsa..... A
duniya idan akwai wasu mata da sukafi kowa kusanci dakai suna sama da wadannan
ne?. Me suke nema a tare dashi?,amsar daya kasa laluba kenan. Sosai abun ya
dinga masa ciwo,shi yasa ko sau daya bai taba aminta da ita ba,ko sau daya bai
taba jin ya gamsu da ita ba......takowacce fuska tana da qatuwar lam'a da tabon
da shi shine babbar shaida......bayan tarin shaidun da ya samu har abinda be
nema bama an bashi,ta yaya zai iya kallonta a matsayin wankakkiya?,ta yaya zai
iya yafe mata?. Yanason ya zame mata lesson me girma a rayuwarta,zai kuma ganar
da ita kuskurenta na shiga rayuwarsa hakanan kai tsaye.
Daga
qarshe dai dole ya kunna karatun qur'ani daya karade ilahirin sassan nasa,yayi
kwance kawai idanunsa a lumshe sautin yana shiga kunnensa,sannu a hankali kuma
nutsuwa ta fara samuwa a jikinsa.
Ko
qwaqwaran motsi kasa yinsa tayi ballantana ta tashi daga wajen,batasan adadin
lokutan data shafe zaune a wajen ba,har sai data daga idanu taga agogo yana
gaya mata qarfe goma da rabi saura mintina biyar sannan ta iya miqewa.
Zuwa
sannan hatta da qafafunta sunyi wani irin nauyi da sanyi,saita gaza shiga
kitchen din ta zarce hallway din sannan ta fada dakinta. Rasa abinda ya kamata
ta tuna tayi,ganinta yayi kenan koko yaya?. Karon farko da taji wata irin
nadama na saukar mata. Ya akayi ta biyewa mamah din ta yarda ta ciyar dashi
gubar da batasan ranar yankewarta ba?,wacece maamah din?,me kuma take
qullawa?,me take buqata ne a rayuwarta sama da rayuwar da take ciki?.
Zafi
sosai takeji cikin ruhinta,tunda take bata taba sha'awar ciyar da wani ko
shayar d wani wani abu me illa irin wannan ba,koda sanda take shirya gyara
zaman mazan da suka zabi harka da mata kuwa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 42
_Daba abu hurairah RA yace,manzon Allah S A W yace
"mafi falalar sallah bayan sallar farilla itace sallar dare_
*_ga falala ga kaifi,biyan buqata kaman yankan wuqa😄,Allah
ya bada ikon jurewa_*
____________________________
★Qarfe tara na
safiyar alhamis ce wadda aka wayi gari da lullumi qwarai,sakamakon hadarin
farko daya fara hada jikinsa tun bayan sallar asubahi. Bai bada ruwa ba amma
kuma ya yiwa rana shamaki daga fitowa tayi rawar gaban hantsi kamar yadda ta
saba kowacce safiya saman sararin samaniya.
Yanayin sai
ya haifar da yanayi me dadi da kuma sanyaya zukatan da suke cikin wani yanayi.
A irin
wannan lokacin ne muhammad jadda mamallakin kamfanin jadda diamondchore
resources yake saukowa a hankali daga samanshi. Cikin shigar aiki,saidai kuma
yau zaka dauka juma'a ce saboda shigar kaftan yayi. Dinkin zamani daya zauna
masa sosai,ya kuma fidda sigar kyan nan nasa da kana kallonsa zaka tabbatar
tabbas halfcast ne shi din wato ruwa biyu.
Cikin parlor
din ya samu tuni ameh ya kammala shirya masa komai na breakfast dinsa. Ameh din
shi ya koma masa girki tun bayan wancan abun daya faru,yaja daya daga cikin
kujerun wajen ya zauna ameh din ya gaidashi cikin rusunawa. Amsawa yayi da
kulawa sannan ya fara serving nasa,yana yi yana dibansa da labarai,wanda kusan
dukansu labaran da suka fita ne a jaridar safiyar. Ameh din yana da karance
karance da yawan sauraran kafafen yada labarai,don haka a mafi yawan lokuta
idan bai samu damar duba news paper ba shike bashi latest na cikinsu.
A nutse ta
maida littafin amdatul ahkam da take dubawa,ta kuma d'auki zaduzzaujaini ta
sakashi a ciki don yin alama akan inda ta tsaya din. Saman side bed drawer tayi
masa kyakkyawar ajiya tana jin wata nutsuwa tana ratsata. Sati guda kacal kenan
da fara karatunsu da rumaisa'u d'iyar malam amma wani nutsuwa takeji da gamsuwa
da karatun. Rumaisa'u din da tayi tsananin mamakin ganinta a matsayin malamarta
da ya dauko mata domin daukan karatun addini a hannunta. Zuwanta kusan uku tana
rejecting tana qin fitowa......sai ana hudun ta fito da zummar yiwa malamin ko
malamar bayanin ta daina wahalar da kanta tana zuwa......ta gayawa wanda ya
aikota dalibar bata da buqatar wani karatun. Ganin rumaisa'u din sai ya
zagwanye komai daga zuciyarta,ta cika da mamakin zuwanta gidan,saidai daga baya
rumaisa'u din ta gaya mata
"Hamma muhammad tsohon dalibin malam ne"
"Gwara da kika ce tsohon" Sabreen ta furta a
ranta. Don tako ta ina bataga ta inda ya dace ko ya cancanta mugu maqetacin
mutum kamar fu'ad din ba ya hada alaqa da malam ba. Daga haka ba wani zance
daya qara shiga tsakaninsu,sai hiran duniya kawai da kuma karatun daya biyo
baya.
Da farko
kawai dai tana sauraren rumaisa'u dinne,amma karatun kwata bayayi mata wani
armashi ko burgeta. Saidai lokaci guda kuma a rana daya data arawa rumaisa'u
hankalinta sai taji karatun ya fara shiga kanta,mafari kenan data fara hada
hankalinta da zummar Tsintar abinda ta Tsinta,saidai tafi tafi sai ta fahimci
karatun yafi qarfin ka tsinta kawai. Ita kanta rumaisa'u mamaki takeyi
ainun....mamakin yadda karatun yake gudu saboda yadda suke qara karatun da
yawa. Ta sallama da gaske karatun yana gudu ne saboda wata irin sharp brain da
Allah ya bawa sabreen din,irin kwanyar da bata taba ganin irinta ba. Don duka
karatun da sukayi da yammaci,zuwa wani yammaci din sabreen din ta narkashi ya
koma cikin kwanyarta.
Tun asali
tana da bala'in son karatu,musamman na addini din,saidai wani dalilin me zuwa
ya ture wani. Ratayuwar hidimar qannenta saman wuya da kafadunta ya sanya tilas
ta haqura da komai ta tattara ta ajiye,a yanzun kuma data fara shiga cikin abun
sosai sai takejin komai kamar an yaye mata wani hijabi ne da da ya lullube
kwanya da idanunta.
Tun sanda ta
fahimci ya ajiye cook dinsa cikin gidan saita saita lokacin ta,sanda zata fito
tayi sabgarta daga shi har cook din nasa basa gidan,hakazalika kafin su dawo ta
kammala komai ta koma daki abinta.
Tayi mamakin
yau da taji yunwa da safe da wuri haka,to amma kuma idan ta tuna ba wani abun
arziqi take ci ba musamman jiya da dare bata saka wani abu me muhimmanci a
bakinta ba sai taga ba abun mamaki bane.
Indonesian
hijab down squeeze ta saka saman soft and cotton nigh gown din jikinta da bata
fidda siffarta ba,saidai tadan lafe mata a mazaunai saboda taushinta. Hijab din
ya qara qawata mata fuska,fuskar data fita sosai ta tsakiyar hijab din da wani
irin kyau kai kace itama haifaffiyar Indonesia dince. Ta qarasa gaban mirror ta
qara turare a jikinta dan kadan kamar yadda ya zame mata wajibi,sai ta tsaya
tana duban fuskartata. Wani irin glowing skin dinta yakeyi wanda ita kanta ta
rasa dalili,saidai a yawancin lokuta tana bawa kanta amsa da wataqila zaman
guri daya ne,sabanin baya da kullum muddin gari zai waye rana ta fito to zata
saka qafarta a waje ta fita.
A hankali
take tako hallway din,yau kawai tana jin nishadi cikin ranta sosai da
cikakkiyar nutsuwar da batasan dalilinta ba,kwanyarta tana bitar wasu daga
cikin karatuttukan data haddace,a haka ta rasa parlour na farko ta wuce zuwa na
biyu.
Tana
murza glass door din ta sanyo qafafunta ya daga idanunsa a hankali daga inda
yake zaune ya zubesu fes saman fuskarta,idonta ya shiga nasa,sai ta janye nata
idon a hankali,ta kuma ja da baya tana komawa da bayan a maimakon fitowa da
tayi niyyar yi. Sam bata qaunar gamuwa dashi,a kwanakin data janye kanta daga
komai da zai sanya su hadu ta kama karatunta sai take samun wata irin nutsuwa a
zuciyarta. Ta dauki kwanaki rabon daya sanyata cikin idanunsa,daga shi har
maamah sai takeji kamar Allah ne yayi mata maganin matsalarsu.
Janye nasa
idanun yayi shima bayan ta koma da baya tana kuma komawa ciki. Yadan jijjiga
kai kadan yana daukan mug din gabansa ya sanya a bakinsa. Tana gyara bedroom
dinsa kamar yadda sukayi sharadi,saidai daga wannan ko gilmawarta bai sake gani
ba tun daga ranar. Can qasan zuciyarsa tana cike da wasi wasi da kuma qiyasi
akan abubuwa da dama. Sai yake zargin shurunta dana maamah dukka kamar akwai
wani magana a qasa,don haka ya jawo wayarsa ya kira me sunan malam. Cikin qasa
da second ashirin suka gama magana,ya shaida masa ya nema farouq ya turo
amintacce kuma sirrintaccen me musu installing CCTV.
Mules din
qafarsa ya maida,sannan ya ciri napkin guda daya yana goge dan abinda ya bata
masa hannu kafin yace da ameh.
"At night.....ka dafa paw paw leaves ka ajiyemin da
duminsa.....daga yau inaso ya zama first drink dina for morning". Kai ameh
ya jinjina cikin girmamawa
"As you wish sir". Sai ya sauka a nutse amma
hankalinsa yana dan kan qofar kadan,yanason sake tabbatarwa komawa tayi ta fasa
shigowa saboda yana wajen?.
Murmushi ameh
yayi yana binsa da kallo,sosai boss dinsa yake burgeshi,yayi aiki kafin wajensa
gidajen manyan attajirai da dama,amma baiga mutum me kiyaye lafiyarsa da yasan
sirrin abinci ba irin boss din nasa ba. Yasan duk wani abu da zai gyara
lafiyarsa a matsayinsa na namiji,yasan duk wani abu da zai gyara masa lafiyar
ido da fatarsa,hakanan yasan duk wani abu da yake natural anti aging remedies
kala kala. Ire iren abubuwan da shi yake tanadarwa manyan da yayi aiki a
qarqashinsu don inganta lafiyarsu da gina garkuwar jikinsu suke qin ci ko sha
don ba dadi a baki ko basusan muhimmancinsa ba......sai gashi shi kullum ne sai
an tanadar masa da wannan abun morning and evening. Akwai hadin salad daya
dinga mamaki sanda yaga yana cinsa farkon xuwansa,musamman da yake yasan yadda
yake inganta qarfi da lafiyar d'a namiji,da yawan wasu abubuwan ma shike qaruwa
dashi a wajensa. Baya son maggi da yawa a abinci,kaman yadda sanyi zaqi da kuma
maiqo da abokansa bane sam sam
(Mata da yawa suna complain din rashin lasting din mazansu a
other room,sunsha magani sunsha maganin amma a banza,anata samun sabani da
sauran masu matsaloli,to wallahi wallahi da yawansu maggi shine yake
kashesu,inda kinsan yadda maggi yake kashe lafiyar mazajenmu da kinyi mugun
gudunsa kuwa,kiga mace ta saka farin magi a abinci,tazo ta saka wadancan cubes
din kala daban daban,ta hada drink ta laftawa miji sugar,ga uban sanyi,abinci
mai yana kwanciya,ba ruwanki da manja ma sam sam,to billahillazi kunji na rantse
muku haka zaita zame miki mace,kuma duk irin maganin da zaisha fa a
banza,muddin ana kan cin magin nan,tashi daya ba zaki iya dainawa ba,amna
gradually zaki dinga janyewa,idan goma kike sawa ki koma bakwai daga haka ki
koma hudu,tabbas indai zaki dimanci haka zaki ga canji,ki ajiye farin maggi
kwata kwata,zaqi da maiqo duka ki rage masa,hadin wancan salad din in sha Allah
zan kawo muku shi a gaba,ya gwada cin na sati biyu bayan kin janye magin kiga
ikon Allah,koda me gida yana da lafiya ma normal ne kina iya hada masa shi ya
dinga ci,amma ina maimaita muku ku raba kanku da kayan d'an d'anon nan,Allah
yasa mu dace).
Kamar
kowacce safiya muddin yana da isashen lokaci......ba baqi ba meeting na early
morning da sauransu,zuwa duba lafiyar anni da gaida maamah din yana cikin
schedule dinsa na kullum.
A
farfajiyar gidan kamar ko yaushe ya samu guard dinsa,kowa na tsaye akan
aikinsa. Bai qaraso bama amma tuni Jordan ya buda masa bugatti dinsa yana jiran
qarasowarsa.
Cikin
girmamawa da nuna kulawa suka gaidashi ya amsa yana bincikar lafiyar kowa kaman
kowacce safiya,sai daya tabbatar da kowa lafiya sannan ya miqawa saddiq da
kusan a makare yake isowa kayan hannunsa,wannan dalilin ya sanya baya samun
shiga cikin gidan duk zuwan da yakeyi.
Sun dauki
hanya sosai kiran musaddiq ya shigo masa,ya fidda wayar yana connecting nata da
Bluetooth dinsa yana amsa wayar.
"Hamma na gama komai......sai yaushe zan dawo?"
Musaddiq din ya amsa a karye da alama gida yakeson dawowar.
"Ka dawo kayi me?" Ya tambayeshi yana jin tantama
a dawowar tasa.
"Hamma nayi missing anni......nayi missing
saddiq". Iska kadan ya furzar daga bakinsa wadda ta fita da qamshin mint
leaves saboda mouth fresh dinsa kenan na dindindin
" Anni kuna waya haka saddiq.....kuma ko ita nasan bata
da damuwa me yawa a tafiyarka.... Dude ne kawai nakeji ban kyauta masa ba dana
dauke masa personal assistant......shima nasan ya
fahimceni.....oops......anyways......nan da sati biyu zamu hade a madeena in
sha Allah,it was family trip time". Har a muryarsa yaji dadi
"Hamma na Manta da lissafinma.....okay..."
"Hope komai naka ba matsala ko?,daga can zaka iya shiga
koda Jeddah ne sai ka qaraso madeena"
"Direct entry zanyi hamma.....i can't wait to see my
family".
"Alright....ka kula da kanka" Ya furta cikin
kulawa
"Na gode hamma" Ya ambata suna ajiye wayar. Wayar
ya zubawa idanu yana tuna wasu abubuwa da suka shude..... Ita rayuwa dukanta tana komawa tarihi ne
watarana......bai taba zaton a rintsin da suka fuskanta shi da musaddiq ba
akwai ranar da zatazo kamar haka komai ya wuce ba......yadda kula da musaddiq
da bashi rayuwa me kyau ya sanya hannuwansa sukayi kanta.....tunaninsa ya
dimauta,kwanyarsa ta kusa jirkicewa da daina iya tuna kome me kyau.....ambaton
sunan maamah ya zame musu kamar wata jarabawa.
Hannunsa
yasa ya shafi fuskarsa yana son ajiye tunanin a gefe.....yanzu yanzu zai iya
rasa kowacce nutsuwa tasa,ya kuma rasa duk wani courage na aiki daya fito dashi
a yau din.
"Gidan maamah zai fara tsayawa" Yace da saddiq don
ya shaidawa driver din shi kuma ya sanar da ayarin motocin. Yayi hakanne don
yasan muddin ya shiga gidan maamah a yanayin da yake ciki na tuna munanan
abubuwan data aikata baga rayuwarsu kadai ba......anni itace zata zamewa
zuciyarsa yayyafin ruwan sanyin da zai wanke duk wani baci da ransa yayi.
Kamar
kullum da qafa ya taka daga inda suka ajiye motocin zuwa cikin gidan. Malam
sa'adu ya matso da sauri yana bude masa qaramar qofar kasancewarsa shugaban
masu gadi na gidan a yanzu. Tunda aka mallakawa maamah din wannan gidan yafi
qarfin gadin malam sa'adu shi kadai,dole sai daya hada mata da security,amma
kuma kowa yana qarqashin malam sa'adun ne wanda shike da permanent chair. Har
kullum burgeshi hali da dabi'ar muhammadun takeyi,ya taka dukkan wani matsayi
da bawa zaizo ubangiji ya kaishi a rayuwa,amma bai dauki hakan a bakin komai
ba.
Gaisawa
sukayi kamar kullum,sannan ya taka yana shigewa cikin gidan da ma'aikatan dake
bakin aiki kowa yake zubewa yana gaidashi.
Daidai
sanda yake sallama a falon daidai sanda take fitowa daga kitchen din
gidan,Hannunta dauke da qatuwat warmer kamar ma rinjayarta takeyi.
Huda
ce,ta bishi da kallo tana amsa sallamar tasa cikin kallon baqunta. Yadan sake
dubanta kadan,sai yake jin kamar yasan fuskar,amma kuma sai ya kauda wannan
tunanin yana neman wajen zama,daidai sanda take gaidashi cikin ladabi daya zame
musu jiki tun tale tale
"Ina kwana?" Ko daya maida dubansa kanta sai yaga
har ranqwafawa tayi irin na ban girman nan
"Lafiya la....." Amsa gaisuwar ta katse saboda
yadd warmer din taso subuce mata daga hannunta. Cikin zafin nama ya isa ya
karba yana fadin
"Kibi a hankali......" Sai ya taka yana kaita
saman dining din ya ajiye.
"Maamah ko?" Ta tambayeshi qasa qasa kaman me
tsoron tambayar,don itadai yana mata kama da mijin adda sabreen din su. Kai ya
jinjina kadan a ransa yana mamakin ina kuma maamah ta samota?.
"Bari na kira maka ita" Ta fada da dan
saurinta,can qasan ranta yana cike da murna,yau kam taga wani daya danganci
addansu.....ko gaisuwa ta aike mata tunda yawan lokuta maamah tana cewa ta kira
basa kusa. Wayar hannunta da maamah ta bata kuwa da komai akai,hasalima suna
waya kusan kullum da momma bahijja,amma batasan me yasa number adda sabreen din
kota kira sam sam bata shiga ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
43
_Daga anas dan malik R.A yace:an rawaito daga manzon Allah S
A W,ya 'yanta matarsa SAFIYYA,kuma ya sanya 'yantata din a matsayin shine
sadakinta_
_bukhari da muslmin suka rawaito_
A step na
biyu taga maamah din tana saukowa daga saman,hannunta cikin na haneefa daketa
bata labari.
"Yammatana ya akayi?" Ta tambayi huda tana dan
sake mata murmushin nan nata da kusan sun sana dashi.
"Baqo ne kikayi" Ta fada tana dan waiwayawa inda
fu'ad ke zaune,hannunsa dauke da remote yana sauya tasha,bawai kuma don yanason
kallon bane aah....sai don kawai bayason kallon fuskar maamah din sakamakon
abubuwan daya tuna da suka motsa ranshi.
"Muje to" Ta amsata har qasan ranta tana jin dadin
yadda huda din ta kasa gane wanene. Tanason sanyata ta koma daki don kada suyi
wata magana da zata fahimci wayeshi a wajensu?,amma kuma ta rasa wanne uzurin
zata bata tunda dai abinci zataci akan dining. Uwa uba kowanne motsi nata da
maganganunta tana yinsu ne a ankare,bata bari tayi wani abu da zai sanya shakka
a ransu ko ta gaza juyasu yadda takeso.
Tunda
suka sauko din haneefa ta zubawa fu'ad ido. Tabbas shine mijin adda sabreen,ta
ganshi har sau biyu bata kuma mance ba,sannan bata sake ganinsa ba sai yau.
Saman
kujerar maamah ta zauna,haneefa ta zauna a gefanta still idanunta suna kanshi
ta kasa daukewa. Sanda ya gama gaida maamah din sai nasa idanun suka sauka akan
yarinyar. Kamanninta suka fusgi idanunshi sosai,ya sake ganin wata kamar ta
daban bayan wadda ya baro dazu tana me komawa falo bayan sun hada idanu.
Murmushi haneefa ta sakar masa sanda taga shima ya dan kafeta da ido. Ya
murmusa kadan tana shirin janye idanunsa sai yaga ta zame tana fadin
"Ina kwana mijin adda sabreen?". Kallon mamaki
yake bibta dashi,mamakin da bai gama sakinsa ba tace
"Sunana haneefa nice autan adda sabreen,'yar mitsisiyar
dakinmu". Baisan ya akayi murmushi ya ratsa miskilar fuskar nan tasa ya
bayyana ba,ashe masu son sarautar autancin suna da yawa. Yanayinta sak sai ya
tuna masa da yanayin amna.
" Ya isa haka haneefa....kije kuyi break ko ki koma
daki wajen nadra ku kalli cartoon" Maamah tayi hanzarin dakatar da
tattaunawar tasu. A nutse ya cira kansa yana duban fuskar maamah din,haka kawai
sai yaji yana da buqatar ci gaba da magana da yarinyar.
"Qyaleta muyi hira maamah....she's very smart" Ya
fada da wani irin tone a muryarsa,wasu abubuwa da wani irin gudu suka fara
bijiro masa,yayin da gumi ya fara tsargawa maamah ta cikin rigarta.
Ta
sani,tafi kowa ma samin haneefa she's very smart,fiye ma da zatonta,wannan ya
sanya tafi janta a jiki da kuma kaffa kaffa da ita.
"Indai surutun haneefa ne saika gaji dashi......ni kuma
magana nakeso nayi dakai,next time idan kazo sai kuyi hirar" Ta fada tana
dan hade rai gami da gyara zama.
Sake
dubanta yayi a karo na biyu,abubuwa biyu suka hade masa waje guda. Har yanzu
dabi'ar nan tata tarashin son yara tana nan?,banbanci qarara me kuma fadin
gaske na farko tsakaninta da anni. Indai haka ne yara uku ne cikin gidanma
kenan?,akwai daya a cikin daki?. Me ya kaita dauko yara har uku?,ita da basu
dameta ba?. Meye abun damuwa don yana hira da yarinya qarama?.
Agogonsa
ya kalla,sai ya maida dubansa ga fuskarta.
"Ba damuwa ai,yau muna da enough time sama da
kullum". Kafin ya sake cewa wani abu haneefa tace
" Zaka kaini naga adda sabreen?......don Allah hamma
kada kace aah" Ta fada tana narke murya. Maganar taja hankalin huda dake
saman dining,itama saita ajiye spoon din abincin da takeci ta maido hankalinta
kansu.
Gumin
dake tsatsatsafowa maamah din ya sake yawaita,da sauri kamar ana tankadata tace
"Aah fa haneefa......ni da kaina mukayi zan kaiku haka
ne?".
"Eh amma har yanzu baki kaimu ba maamah,shi kuma hamma
ma daga can yake ko?" Ta maida tambayar kansa. Kansa ya gyada a nutse yana
karantarta.
"Maamah ki barshi ya kaimu ko anjima ne,in yaso saimu
dawo da kanmu" Huda itama ta saka baki,don da gaske sunyi tsananin kewar
sabreen din.
Sanda ta
waiwaya da nufin yiwa huda din magana sai maganar fu'ad ta dakatar da komai.
"Jeki dauki hularki kuzo muje nasa a ajiyeku" Yayi
maganar kansa tsaye,maganar data daki tsakiyar kan maamah da wani irin ba zata.
Har ga
Allah kanshi tsaye ya fada kuma hankalinsa kwance,kawai dai a cikin zuciyarsa
ya dade da rashin aminta da kowanne motsi na maamah din. Bashi da gamsuwa akan
abubuwa da yawa sa suka shafeta,shi yasa a kusan komai idanu da zuciyarsa suna
akai.
Cikin qasa
da minti uku sai gasu kowacce da mayafinta. Dab da zasu fita daga falon ta
kirayi sunan huda da yanayin da tunda hudan tazo gidan bata taba gani cikin
muryarta ko sautinta ba. Fuskarta a dinke ba fara'ar nan da suke kwana suke
tashi da ganinta akan fuskarsu
"Kada ku wuce ko ina,daga can ko dawo gida,zanwa driver
magana zai biyo bayanku,karku wuce awa daya......." Idanu huda tadan zuba
mata,sai kuma kawai ta gyada kai mamakin sauyawar maman tana kamata. Tasha musu
alqawarin fa zata kaisu.......sai kuma daga baya tace ai wani uzuri ne ya taso
sai bayan wani lokaci,duk da ta lura akwai permanent driver a gidan da yake
zaune baya aikin komai.
Yana
zaune daga cikin motar saidai qafafunsa suna a waje ba'akai ga rufe masa murfin
ba suka fito. Yadan daga kai ya kallesu,dukkaninsu suna kama da ita saidai
qaramar ta fisu daukan kamanni sosai da ita. Mamaki kadan yana dan kamashi na
ganin banbanci muraran tsakaninsu. Dukkansu da alama suna da sauqin hali da
kuma tarbiyya sosai,don ba wanda ya gaidashi a tsaye a cikinsu saida suka
rusuna
"Ta fita zakka kenan" Ya gayawa kansa da kansa
yana sauko qafafunsa qasa ya fito waje.
"Abdulgaffar" Ya kirayi shugaban tawagar tsaron
nasa,ya matso da gaggawa yana rusunawa
"A cire mota daya a sakasu a kaisu gida" Ya bada
umarni hankalinsa yana kan kiran fareeda dake shigo masa. Kaman yadda baya
gajiya da qin dagawa hakanan itama bata gajiya da kiran nasa,yaja wani dogon
tsaki yana komawa motar,ranshi yana tsananin baci da kalar wannan kiran nata da
dukkanin numbers dinsa,kamar wadda batasan abinda ya dace ba,baisan ma ya akayi
take da dukka numbers din nasa ba.
"Soulmate" Sunan da tayi kiransa dashi kenan da
wani irin salo na kashe murya da jan ra'ayi.
"Why?.....ke bakya gajiya da kira ne?,it's so
annoying.....please don't do it again.....stop it" Ya fada da sautin bacin
rai a muryarsa.
"Haba ka fahimceni mana" Ta sake fada da hanzari
cikin tsoron kada ya katse mata wayar..... Kada ya ajiye wayar bayan ta samu
dama ya daga wayar bayan dukka wahalar da tasha
"Na fahimci me?....ke bakya ganewa cewa macace ke?,ke
ya kamata abi bawai kibi ba?.....kina mantawa mace da kamun kai aka
Santa?.....". Da sauri take girgiza kai
"Indai a kanka ne bani da wadannan qualities
din....."
"Okay....then karki sake kirana....." Yaja qaramin
tsaki yana yanke kiran hadi da jan dogon tsaki yana wurga wayar gefe.
Gaba
daya soyayya tana sake tona masa kanta a matsayin wani abu da yafi komai zama
matsala da takura a rayuwa,shi yasa bazai bari ta kunno rayuwarshi yanzu ba har
sai sanda ya shirya ya kuma kebe mata lokaci nayin nata.
Idanunshi
akan motar BMW din da aka sanyasu a ciki,sai da yaga fitarsu a gidan sannan
yayi musu umarni suka tashi motocin suna fita suma daga layin.
Sauke
labulen window din da yake bata daman ganin farfajiyar gidan tayi cikin wata
irin matsananciyar fargaba da kuma tashin hankali. Gaba daya kowacce idea tata
ta kunce,ta rasa wanne zaren tunani zata kamo?.
Wacce irin
baqar rana ce yau?,wanne tsautsayi ne qaddara ya sanyata lokacin shigowarsa ya
kubce mata har ta saki yaran haka?. Idanunta ta mayar saman agogo......sai a
sannan ta lura,yau ya sabawa lokacin shigowar tasa ne,ya shigo da wuri ba kaman
yadda ya saba ba,sai tasa hannu tana sharbe gumin fuskarta da tafin hannunta.
Da dan
hanzari ta taka da kanta tana fita farfajiyar gidan tana qwalawa mansir
kira,kiran daya sanyashi sakin duk abinda yakeyi ya qaraso babu shiri.
"Ka fito da mota,kabi bayan motar jadda diamond zuwa
gidan muhammadu......akwai yara da sukaje gaida matar gidan,suna shiga minti
goma kacal ka aika su taso ka dawomin dasu......mansir?,idan ka kuskura aka
samu akasi baka maidominsu akan kari ba to ka kuka da kanka......ban yarda ku
biya ko ina ba......ban kuma yarda ka ajesu ako ina ba" Ta fada tana zare
idanu tanaji a jikinta tamkar wani abu zai faru.
"In sha Allahu ba zaa samu ko daya daga ciki ba"
Daga haka saita juya tana komawa ciki.
Kasa
zama tayi ko a cikinma,a jikinta takejin kamar akwai wani abu da ba daidai ba
"Ki kira zuwaira kisa ta kula miki da motsinsu"
Wani sashe na zuciyarta ya bata shawara.
Bibbiyu
ta dinga hada stairs din tana haurawa samanta,cikin lokaci qanqani ta isa
dakinta,ta zauna gefan gado tana daukan wayarta dake saman drawer ta fara kiran
zuwairan.
Saidai
kash!,kiran farko aka shaida mata kwata kwata wayar a kashe take,ta sake
gwadawa cikin rashin gamsuwa da bayanin farko na na'urar......still sukace mata
yana a kashe,ta sake dai gwadawa a karo na uku,nan dinma amsar dukka daya
ce,saita ajiye wayar a gefanta tana jan wani matsiyacin tsaki
44
_Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W
yace:Duk macen da waliyyai biyu suka aurar da ita ga maza mabanbanta a lokaci
guda,to ita din mallakin na farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_
"Tur da
halinki zuwaira,Allah wadai da halinki" Ta fada tana cika tana batsewa,har
cikin ranta tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta tafi gidan da kanta. To amma kuma
idan tayi duba ga wasu abubuwa,hakan bame yiwuwa bane,dole taci gaba da zama
tana gwada kiran akai akai,yayi da idanunta ya ta'allaqa akan agogo tana
qidanye da mintunan fitarsu daga gidan.
Daga
qarshe ta sare kan samun xuwaira,to amma dole tana da buqatar kiran wani da
zame zame mata garkuwa a can gidan
"Laila" Zuciyarta ta tunasar da ita.
"Yauwa" Ta fada da madaukakin zumudi,ta soma
lalubar number wayar lailan.
Duk da
safiya ce amma ta kusan awa guda da rabi a gidan nasu. Cikin asalin dakin da
yake shine mallakinta,saman gadon sun qule ita da mahaifiyarta hajja harira
wadda ta tsareta da idanu bayan ta gama zayyane mata karonsu da fu'ad na
qarshe.
Sai da
tayi kaman ba zata daina kallon nata ba kafin taja wani tsaki tana dauke
dubanta daga kanta.
"To wai meye ma amfanin zamanki a gidan laila?,kada ki
zama albasa mana wadda batayi halin ruwa ba?,na kaiki gidan badon kin rasa
wajen zama ci sha ko sutura ko kuma gata cikin naku gidan ba.....na kaiki ne
saboda ki karanci komai.....ki haddace komai ki kuma bi kowanne taku da motsi
na kowa a gidan kafin mu fara gabatar da namu shirin koda kuwa.mariya batayi
nasara ba......nasarar mariya ko faduwarta ba damuwata bane.....hasalima inda
zata fadi hakan shine daidai a tare dani......kinsan me?" Kai laila ta girgiza
tana jin faduwar gaba da kiran sunan maamah da akayi.
"Nasarata itace ya kamata ta fara samuwa......nasarata
ita ya kamata ta fara wanzuwa kafin ta mariya........ni ya kamata na fara samun
fu'ad na mallaka miki shi......muddin mariya ta rigamu samun fu'ad to ba shakka
dukkan wata nasara da muka sanya rai a kanta zata iya zuwa mana da tsauraran
hanyoyi da matakai......shan kai nake da buqata mu yiwa mariya laila.....donme
kikaje kika kwanta kina bacci?,waye ya gaya miki nasara na zuwa ta sameka har
inda kaka?,bakisan fita ake a nemota ba?!" Tayi maganar da alamun qunan
rai a cikin muryarta,hatta kuma da lailan ta karanci haka,saidai batasan me
yasa a kwanakin nan takejin sam bata da damuwa akan wannan lissafin na hajja
ba......tamkar wannan lissafin an zare mata shi kwata kwata daga zuciyarta.
"Ban sauka ba hajja......kawai dai saina dinga jin
kamar idan mukayi hakan bamu kyautawa maamah ba,kamar idan mukabi komai a sannu
zaifi....." . Baki kawai hajja harira ta sake tana kallon laila da wani
mamaki daya taru a fuskarta,kuma koda ta zubawa lailan idanu saita karanci da
gaske take maganar. Tana shirin yin magana aka turo qofar aka shigo.
Madeena ce
dauke da serving tray data jero dukka kayan dadin da aka dafawa hajjan a
matsayin abincin safe. Tun asuba take tsaye don kawai ta faranta mata,kuma bata
da tabbacin zata yaba ko kuma tayi accepting abincin gaba daya.
"Gasu hajja an gama....." Ta fada tana rusunawa ba
tare data iya hada ido da ita ba. Wani abu me nauyi da girma ya riga ya sauka a
zuciyarta game da zancan laila,don haka bacin ran daya taso mata maimakon ta
huceshi akan laila sai ta fara ragewa akan madeena
"Wannan wanne irin iskancin banza ne?,ina ciki muna
sirri da yarinya saiki wani bankowa mutane daki?". Murya a karye cike da
ladabi tace
"Kiyi haquri,kin manta ke kikace idan na gama na kawo
miki a daki zakici"
"Naji da Allah.....koma dashi ki aje saman
table......tsnnnnn" Ta qarasa da tsaki.
"Awnnn..... Me dame kika dafa mata ne?" Laila tayi
tambayar tana maida dubanta ga madeena wadda je tiri tirin fita da tray din.
Ido kawai hajja ta zubawa laila tana mamakin yadda take nuna halin ko in kula
da magana me muhimmanci irin wannan. Dawowa madeena tayi ta durqusa ta bude
mata dukka bowls da warmers din,sai lailan ta karyar da wuya.
"Wallahi meat pie nake mugun kwadayin ci da safen
nan.......don Allah hadamin yaji naman rago cikin sosai" Ta fada kanta
tsaye da sigar umarni.
"Tom" Madeena ta amsawa lailan wadda a qalla tayi
qanwa ta hudu da ita,ta miqe ta kwanukan tana sauka.
"Idan da a rayuwa tsaiwa ake duba abinda ya
kamata......inda a rayuwa jira ake sannan ayi abinda ya dace........tabbas ke
kanki da baki juya matan yayunki kamar haka ba" Hajja tayi zancan tana
tsare laila da ido tare da qoqarin maida mata girman zancan cikin zuciyarta.
Dan
muskutawa laila tayi tadan kashingida,har yanzu a ranta ita batajin damuwar
komai,duk da kuwa bayan kowacce daqiqa sai hoton kyakkyawar fuskar nan tasa ta
gilma ta gaban idonta,abinda ke sakata sakin ajiyar zuciya lokaci lokaci gami
da sakin qaramin murmushi.
"Inaso komai sauya.....inason ki canza akalarki daga
yau.......dole gobe ki dawo ki karbi naki kayan aikin......ki kula da
zuwaira......banason tasan komai.....bana son kuma ta fuskanci komai" Ta
fada tana tsareta da ido. Saidai bata kai ga amsawa ba wayarta dake saman kanta
ta dauki tsuwwa. Tana daga kwancen ta daga kanta tana duban me kiran,saidai
ganin sunanta kadai ya sanyata wani irin zabura hadi da tashi zaune.
Hakan kuma
baiyi mata ba sai data zamo daga saman gadon ta durqusa a qasa sanda take daga
kiran hade da sallama. Dukka wadannan abubuwan da tayi su suka ja hankalin
hajjan sosai taji tanaso taji da wanne mutum me matuqar girma da daraja haka a
rayuwarta take waya?.
"Ina kwana maamah.....kin tashi lafiya?,kiyi haquri
inata zuci zucin na kiraki na gaidaki da safen nan.....amma na kasa tuna waye
zan kira". Maganar ta yiwa maamah banbarakwai,to amma bata wani kawo komai
a ranta ba,duk da laila bata taba mata magana da ladabi rusunawa da kuma kirki
irin haka ba
"Ba komai,kina gida ne zan baki wani aiki?". Rawa
jikinta ya hauyi saita miqe tana daukan mayafinta
"Bana gida maamah.....amma bani minti goma sha biyar
yanzu zan isa gidan,saiki gayamin abinda kikeso ayi miki ko mene". Mamaki
kadan ya sake kamata,to amma a yanzu garkuwa kawai take nema don haka ta amsa
mata da
"Okay......idan kika isa ki kirani"
"Ko kibar wayarma kawai on hold karki kashe yanzu yanzu
zan isa,zanyi sauri ma saboda agama komai da wuri". Wani mamakin dai still
ya kamata,amma sai tace
" Zan sake kiranki"
"To" Ta amsa mata tana sauke wayar. Jakarta ta
kaiwa sura,kamar ma ta manta da hajja dake wajen,kowanne sashe na jikinta rawa
yakeyi,ta jefa wayar a jaka ta rataya tana yafa mayafinta. Sai a sannan hajja
da mamaki ya kasheta ta kira sunanta da qarfi
"Waike da waye kike waya haka lokaci guda hankalinki ya
tashi?". Murmushi ta sakarwa hajjan sanda take saka takalminta
"Maamah ce fa?,ta tambayeni ne ina gida?,wani aiki zata
sakani kinga ya kamata na koma ai.....bai kamata ma ace na fita ban tambayeta
ba,amma zan bata haquri daga baya.....hajja na tafi,idan na gama mata da wuri
zan tambayeta,idan ta barni gobe na dawo zan dawo".
Mamaki da
ganin almarar abun ya hanata cewa komai,ta sanqame a wajen kawai baki bude tana
bin laila da kallo wadda keta sambada sauri kamar zataci da baka.
*_turqashi?,wai meke faruwa?,nace meke faruwa ne
jama'a?,shin qaiqayi ne koma kan masheqiya ko kuwa yaya?,wanda lamarin nan ya
yiwa dadi ya danna 1😂,wanda baiji dadi ba ya danna 2_*
*_gasu huda a hanyar zuwa gidan addansu,yaya zata kasance
kenan?_*
*_yanzu wasan zai fara tafiya daidai💪🏽_*
*_muje zuwa🙌🏽_*
45
_Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar
da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin
ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_
Ware
idanunta tayi sanda ta isa dining area,sai ta tsaya cak tana sake ware idanunta
da kyau tamkar wadda bata gani sosai,kwanyarta na gayawa zuciyarta kawai
yaudarar kanta takeyi,basu huda dinta bane.....ba nadra a wajen......auta
haneefa tana hannun waccar azzalumar
"Adda.." Muryoyinsu suka zame mata kamar tsani a
gareta na tashi daga wani dogon mafarki,kamar wadda aka daki bayanta,sai ta
fara nufarsu tanason ta tabasu don ta tabbatar shin su dinne?.
Allah ne
kadai ya sauko da ita daga steps din,don qafafunta hardewa kawai sukeyi har
zuwa sanda ta isa garesu. Haneefa da tafi kusa da ita ta jawo,ta miqa hannu
tana shafar fuskarta,sai kuma taja hannun huda ta riqe d kyau,sannan ta dafa
kafadar nadra.
Murmushi
suka fara yi mata,da alama sun gane abinda take nufi,kuma dariya sukeso suyi
mata,saidai yanzun ba Lokacin dariya bane.
"Ku tsaya a nan ina zuwa" Shine abinda ta fada
kenan tana juyawa ciki cikin gudu gudu sauri sauri. Ko ina a jikinta rawa
yakeyi,batasan ya akayi suka kubuto ba,tana ji a jikinta addu'ar data tsananta
a wannan Lokacin Allah ya karba mata.
Birkice
closet dinta tayi wajen neman hijab daya tamkar idanunta basa gani,da qyar
idanunta suka nuna mata wani ruwan sararin samaniya,ta sanya hannu ta fuzgoshi
ta saka,sannan ta dawo falon.
"Ku taso......ku taso mj tafi" Ta fada da wani
irin hanzarin daya sanyasu tsaiwa kawai suka zuba mata idanu,har sai data fusgi
hannun nadra da haneefa sannan huda ta biyo bayanta a mamakance.
Tana
riqe da hannuwansun take ratsa farfajiyar gidan,girmanta yasa take ganin kamar
ba zasu fita daga ciki ba maamah zata riskesu,kamar tayi nisa da yawa. Security
da sauran ma'aikata nata zubewa suna gaidata,amma ita ba wannan bane a
gabanta,don ko gane gaisuwar nata basa yi.
Kai tsaye
kuma a karon farko security suka bude mata gate ta fice. Taci gaba da jan
hannunsu da wani irin sauri da kaf rayuwarta bata tana yin tafiya da irinsa ba
"Ina zamuje adda?,ko zama baki barmu munyi ba?"
Haneefa ta tambaya adan shagwabe saboda saurin da suke zubawa din ya fara
isarta
"Zaki gani auta......karki damu" Ta ambata tana
duban hanya,daidai sanda ta hangi tahowar motar da tafi mata kama da motar da
akan kawo maamah a ciki.
Hagu da
damanta ta duba,ba wani gurin labewa. Unguwa ce da dukka gine ginenta ke bisa
tsari,layukansu shimfide da wadatacciyar kwalta,manyan gidaje da kowanne gate
yake a kulle dame gadi ko kuma kare.
Cikin
ikon Allah ta hangi gida daya da qaramar qofar dame gadi kan fito a bude,saita
jasu zuwa can ta kuma turasu ciki itama tana me shigewa.
A gabanta
motar tazo ta wuce da gudu,saita sake kamo hannun haneefa tana cewa
"Kuzo mu tafi" Zuciyarta na tsananta bugu qwarai.
Sai da
sukayi tafiya me nisa kafin su samu adaidaita sahu,kasancewar unguwar unguwace
ta masu kwalli masu hannu da shuni,zai wahala kaga abun hawa na haya a cikinta.
Koda zai shigo ma sai ainihin security da suke gadin unguwar sunyi checking sun
tabbatar da amincinsa da ingancinsa. Basa wasa ta wannan fannin saboda dukka
unguwar manyan mutane ne a cikinta.
Sai data
tabbatar me abun hawan yayi nisa da unguwar sannan ta sauke ajiyar zuciya,ta
juya a hankali tana kallonsu sai taga dukkaninsu ita suka zubawa ido,da alama
qarin bayani suke nema. Murmushi kawai ta saki,ta dora hannunta saman kansu ta
shafa tana cewa
"Zakuji komai......bari mu isa".
Kamar yadda
zama ya gagareta haka tsaiwar ma sai taji kamar tana neman gagararta. Wani
tashin hankali takeji mara misaltuwa,yaran su kadai ne hope dinta,idan har tayi
loosing yaran tabbas bata da wani sauran hope.
Yadda
take juya yarinyar tayi imanin bawai girman asiri bane.....don dama ya bata
tabbacin abun bame qarfi bane,idanma me yawan addu'a ce kwana uku zai saketa.
In kuma me qarfin kurwa ce da tsananin hasken taurari sati biyu zuwa wata daya
zai iya sakinta.
A yadda
take maida mata magana da tsananin izza da rashin tsoro,ta tabbatar komai ya
saketa,kawai tana biyeta ne saboda yaran da suke hannunta.......idan babu su ya
zata kaya mata kenan?.
Wani
tashin hankalin ya sake rufto mata data tuna da waya fa a Hannun huda. Ita ta
siya mata ita sati guda daya wuce kenan data sake jawota jikinta. Yau idan
sukayi amfani da wayar suka kira wani fa?. Abinda ya sakata rarumar tata wayar
don sake kiran zuwaira ta karbo mata wayar ko da qarfi ne,tana me manta ma
wayar zuwaira din a kashe take.
Cikin sa'a
bugu biyu ta dauka,muryarta na nuna alamun bacci. Ashar ta lailayo mata wanda
ya sanya zuwaira miqe ta zauna da duwawunta
"Dama bacci na aikeki kiyi?Kinsan aikinki kuwa?,kinsan
muhimmancin abinda na aikeki kiyi zuwaira?!" Maamah ta tambaya a tsawace
tana jin kamar ta jawo zuwaira daga cikin wayar ta zabga mata mari. Rawa jikin
zuwaira ya dauka,batason tayi asarar maamah tun yanzu alhalin bata samu tudun
dafawa ba.
"Kiyimin aikin gafara hajiya......tuba nake"
"Ki rufemin baki,ki tashi ki dubamin cikin gidanku,daga
parlor din matar gidan har bedroom dinta,akwai qannenta da sukazo,ki fara
karbamin wayar hannun babbar,minti goma kuma nace ki qara musu su taso ki
biyosu har sai kin kawominsu gidannan".
"Angama ranki ya dade" Ta fada tana miqewa da
hanzari har dankwalinta yana faduwa,duk da ranta a bace yake ainun da irin
tsawar data daka matan.
Parlor
ta duba na farko dana biyu duka ba kowa. A kitchen ta samu ma'u tana juye mata
kunun a flask gudun kada yayi sanyi jin shuru bata dawo ba.
Ido suka
hada mau ta dauke dubanta a wajen. Haka kawai jininsu baizo daya da zuwairan
ba,duk da ma'u bata nuna mata komai,saidai ita zuwairan cike take da haushin
ma'un ganin yadda sabreen din ke mu'amalantarta sama da yadda take sakar mata.
Ko ina na
gidan ta duba,tana shirin fita farfajiyar gidan ta duba can sai ga laila ta
shigo afujajan
"Ina matar gidan?" Lailan ta tambayi xuwaira.
"Ban sani ba nima" Ta bata amsa cikin jin haushi
zuciyarta tana raya mata itama aikin dubata ta bata.
Dole data
gama dube dubenta ta dawo parlor din,daidai sanda ma'u ta kammala komai tazo ta
rabesu tana ficewa abinta ba tare da tace da kowa komai ba.
Dukkansu
qoqarin kiran maamah suke don kowa ya fara shaida mata yadda ake ciki. Laila ce
ta fara samunta,cikin tsananin biyayyar data sanya zuwaira sakin baki tare da
tunanin ko wani sabon makircin shiga jikinta suka qullo ta tsaya tana dubanta
"Maamah kaman bata gidan nan fa?". Wata zazzafar
zufa ce ta karyo mata,taji kamar gudawa zata tsinke mata. To amma yaushe suka
shigo da har za'ace basa cikin gidan?.
"Kun duba ko ina da ina?" Kai laila ta girgiza
tana duban hallway din
"Banda bedrooms dinta"
"Me kuke jira?,ku dubamin har can" Ta bata umarni
a tsawace har sai da wayar hannun lailan ta kusa faduwa.
"Zan shiga na duba" Lailan ta fada tana duban
zuwaira. Wani kallo ta watsa mata tana samun daya daga cikin kujerun ta zauna
tana tabe baki.
Da
karsashinta ta soma nufar dakunan,har cikin ranta tana jin dokin shiga taga
dakunan ya suke?,tunda koda hallway din bata taba takawa ba bare akai ga shiga
ciki.
"Alhamdulillah" Ta samu kanta da furtawa lokacin
dame napep ya ajiyesu a qofar gidan. Sai a sannan hankalinta ya dawo jikinta,ta
tuna bata riqo komai a hannunta ba.
"Don Allah dan yi haquri,bari a karbo maka
kudinka,fitar ce ba'a tsanake ba" Ta fada tana dubansa. Bai wani damu ba
sam,saboda yanayinta kadai ya tabbatar masa idan bai samu qarin abinda ya
kamata a bashi ba to tabbas ba za'a rageshi da komai ba. Waiwayawa tayi ta
kalli su huda
"Ku shiga ciki ku karbomin dubu biyar wajen titi".
Huda ce tayi gaba suka bita a baya. Basu jima ba nadra ta fito da kudin ta
miqawa sabreen din,ta karba ta bashi sannan suka wuce cikin gidan a tare.
Tana
sallama aishatu ta fara gani,tana duqe tana wankin uniform dinta daga can bakin
famfon da akayi musu saboda hidima irin wannan. Tadan zubawa yarinyar idanu
farinciki yana ratsata. Ko a iya aishatu kawai idan ta kalla tana jin wani
farinciki da sassauci yana ratsata,kamar ba aishatun da aka debe tsammani da
rayuwa da ita ba,kamar ba aishatun da idan ka fita ba zakayi tsammanin zaka
dawo ka sameta a raye ba. Sai data dago don yin shanya suka hada idanu,ta
watsar da uniform din,ta rugo da gudu tana kiran sunanta
"Adda sabreeennn" Ta maqaleta da kyau,sai itama ta
tsugunna tana rungumeta cikin jikinta qwallar farinciki na sauka a idanunta.
"Aishatu......haka kika koma?......alhamdulillah"
Ta fada tana shafa sumarta me santsi.
"Adda na warke.......na samu sauqi adda" Ta fada
itama tana kwantar da kanta a kafadarta.
"Ki barta ta qaraso ciki mana aishatu" Muryar titi
ta ratso kunnuwansu tana dubansu cikin murmushi,daga nesa kuma tana kallon
yadda sabreen din tayi wani irin kyau,fatarta ta qara tsananin haske da wani
irin murjewa,sai glowing takeyi duk da tadan fada kadan qibarta ta ragu.
Tana riqe da
hannun aishatun suka shiga parlor din titi. Duka sauran yaran falon suka miqe
don basu fahimci ita ake magana ba.
Dukkaninsu
suka baibayeta suna qoqarin kiran sunanta,sai ta zame kawai ta zauna tana
rungumesu cikin jikinta gaba daya tana kiran sunansu daya bayan daya.
Ruwa da
lemon zobo da titi din ke saidawa ta dire musu tana zama gefanta. Sai a sannan
yaran duka suka tashi suna ficewa don basu sarari.
"Banyi zaton sake ganinki nan kusa ba" Titi ta
fada bayan sun gama gaisawa da gaske farinciki yana nunawa saman fuskarta,duba
da sanin babban mutumin data aura. Murmushi sabreen din tayi wanda yakai mata
har zuci,musamman data tuna daga rana irin ta yau ta nesanta maamah din da
rayuwar qannenta kenan,nesantawa ta har abada
"Me zai hana titi?,ban fara fita bane kawai" Ta
amsata tana gyara zamanta
"To ma sha Allah,ubangiji ya sanya alkhairi,ya bada
zaman lafiya ya kade fitina". Bata amsa duka wadannan addu'o'i na titi din
ba,sai tace da ita
"Alfarma nazo nema titi don girman Allah" Kallonta
titi takeyi wani yanayi yana bin fuskarta
"Haba sabreen.....haba don Allah,aike din kifi qarfin
alfarma......saidai bada umarni kawai" Murmushi ta saki tana girgiza
kai,har yanzu suna mata wani madaukakin kallo.
"Su huda na kawo miki,inaso kuma ki riqemin su zuwa
wani lokaci,don Allah titi ko nan da qofar gida bana so su leqa idan zai yiwu
bare sukai ga fita waje.......akwai gagarumar matsala da take tunkararmu gaba
daya,akwai masu bibiyar rayuwarsu,ki kulamin dasu don Allah". Sosai
maganar ta shigi titi,saita girgiza kai tana fadin
"Aiko su din ba jininki bane sabreena sai inda qarfina
ya qare......ba abinda bakiyi mana ba,banda ke da Allah ya jefo mana da yanzu
bansan a wanne bigire rayuwarmu take kai ba......zan kula miki dasu fiye da
yadda kike muradi"
"Na gode titi......kina da tsohuwar waya da bakya
amfani da ita?"
"Banga abun godiya a nan ba,hasalima kamar wajibi na na
aikata.....akwai wayata da kika canzamin sanda zamuyi tafiyar nan......bari na
dauko miki ita"
"Idan zan samu da wata wayar daban zanyi kira" Ta
fadi tana qoqarin hada numbers din momma a kanta.
Banda tana
da kaifin basira da saurin riqe abu ba yadda zata iya hada number wayar momma
din,saidai cikin ikon Allah ta hadasu tsaf ta kuma kira zuciyarta na bugawa da
fatan ta kira daidai.
Bugu uku
aka daga,muryar momma ta mamaye speaker din tana amsawa da sautin da yake kama
sak dana ummensu,sautin da har tata mutuwar ta risketa ba zata manta dashi ba.
"Mom......momma" Sabreen din ta kirata bakinta
yana rawa idanunta suna cika fal da hawaye.
"Sabreena?.......kun dawo?,yaushe kika dawo?"
"Daga ina?" Ta tambayi momma din a mamakance
qwallar idonta suna tsagaitawa.
"Tafiyar da kukayi mana ke da me gidan.......ko sanda
zan koma ai naso haduwa dake dole sai hannun surukarki nabar
qannenki.......saboda dole sai passport dinsu ya zama ready.....duk dama dai
munyi magana tana ta iya bakin qoqarin ta,kuma kusan kullum sai munyi waya da
yaran". Mamaki ya sandarar da sabreen,sai ta bude bakinta a hankali
"Momma me ya faru?,ban fahimta ba,ita ta nema ki bata
su?"
46
"Eh kusan hakanne,don naso ganinki ban samu ganin naki
ba......tafiyar tawa bata shiri bace......abbansu ne rashin lafiya ta taso
masa,dole kuma ana buqatata a kusa,a yadda na tsara zan jira passport din nasu
da komai ya kammala,amna dole na tafi saboda jinyarsa,saidai ba inda zan barsu
don ban aminta da hannun kowa ba. Randa nake wannan tunanin saiga surukarki
Allah ya jeho ta. Ita ta roqeni na bata yaran zata sanya mai gidanki yayi
magana don a kammala basu komai da wuri,tace kuma zata turosu ko ta kawominsu
da kanta,to amma lokacin da nayi tsammani ma sai gashi har ya gota. Kawai
abinda yake kwantarmin da hankali duk sanda mukayi waya da yaran alamu suna
nunamin basu da matsala ko damuwar komai". Kai kawai sabreen ke jinjinawa
tana sake girmama kaidin maamah din. Ta tabbatar ita zata kawo tsaiko a samun
fasfunansu,wataqila ma kuwa an samu ta riqe ne taqi gayawa momma din. Tanason
ta yiwa momma bayanin da zata fahimceta,amma kuma bataso ta daga mata hankali.
Tana ji a jikinta zata iya komai,kuma wannan lokacin kamar wata dama ce da
Allah ya ara mata akan maamah din
"Momma"
"Na'am sabreen"
"Komai da kike kallonsa a haka yanzu a zahiri ba'a haka
yake ba........abinda zance rayuwarsu tana cikin hadari babba........basa
hannunta yanzun suna wani hannun na daban,saidai bana son ki gayawa kowa,don
Allah mommma......koda ta kiraki kiyi kaman bakisan abinda yake faruwa
ba.......in sha Allah nan da kwanaki kadan zan turosu su biyoki". Shuru
momma din tayi tanaji a jikinta ba lafiya
"Amma sabreen me yake faruwa?".
"Ba wani mummunan abu bane momma,kada ki tashi
hankalinki.....kawai dai komai kiyishi kamar bakisan anayi ba" Kai ta jinjina bawai don hankalinta ya kwanta
ba sukayi sallama.
Tana ajiye
wayar ta sabule zobunan hannunta guda biyu na gold,ta kama hannun titi ta
zubasu tana kallon idanunta.
"Yanzu bani da contact na kowa.....inaso ki saida
wannan,ki nema mutumin da ya muku visa na fita india ya yiwa su huda duka su
ukun komai,inaso kada su wuce sati biyu a nan don Allah titi". Zobunan ta
kalla sannan ta maida dubanta ga sabreen
"In sha Allah.....zanyi duk yadda zanyi na miki abinda
kikeso". Kai ta jinjina tana jin wata nutsuwa tana saukar mata. Murya ta
daga ta kira huda,ta shigo ita daya,abinda ya sanya titi miqewa don basu guri.
"Ina wayar hannunki?" Ba musu ta dauki wayar daga
kan cinyarta ta miqawa sabreen din. Saita karbeta tana juyata a hannunta. Waya
ce me asalin tsada da kyau wanda kusan sai wane da wane. Idanunta ta maida
fuskarta tana kallonta
"Huda baki dago komai ba?,bakiji komai ba game da matar
da aka kira da sunan uwar mijina?" Tayi mata tambayar kai tsaye tanason
samun wani abu daya danganci maamah. Shuru hudan tayi,tana qoqarin recalling
komai,tun daga ranar farkonsu cikin gidan kawo yau.
Siririyar ajiyar zuciya ta sauke,a hankali ta maida dubanta ga sabreen
"Inajin kawai batamin ba.....duk kirkin da take gwadana
mana sai nakeji jini na da nata kaman bai hadu ba.......sannan yadda take mana
kirki kaman ba haka dabi'arta take ga masu aiki qarqashinta ba" Hudan ta
fadi abinda da gaske haka takeji a zuciyarta take kuma hasashe.
Wani
siririn murmushi sabreen ta saki tana saukar da kanta qasa gami da juya wayar
hannunta. Anzo daidai gabar da tafiso.....anzo daidai wajen da zata gwadawa
maamah shege......anzo daidai gurin da zatayi wasa da hankali da kuma tunaninta
kamar yadda mage kanyi da qadangare ko bera a duk sa'ilin da yayi gigi ko
kakambar shiga hannunta.
Daukewa
murmushin fuskarta yayi lokaci guda,ta maida kallonta kan hudan
"Ina fata ba wani abu na cutarwa data taba
muku......idan kuma akwaishi ko da da mugun kallo ne ina saurarenki". Kai
ta girgiza tana kallon addar tata,tanason kuma fahimtar dalilin da yasa taketa
mata tambayoyi haka
"Babu kwata kwata adda......saidai kawai nidai
hankalina ya kasa nutsuwa da ita...
Musamman da ya zamana kusan ko yaushe tana mana alqwarin zata kawomu
wajenki sai kuma ta gaza cikawa.....har sai da mijinki yazo.....shi yace ta
barmu muje". Jinjina kai take tana duban huda dake bayani,fuad ne
kenan.......me yasa yace suzo din?,shima akwai yiwuwar yana da nashi boyayyen
manufar?.
"Kinsan garkuwa tayi daku?,kidnapping a fakaice?"
Tambayar ta zowa huda a bazata,ta zaro idanunta waje tana dafe hannunta saman
qirjinta.
"Kidnapping fa adda?" Kai ya gyada mata gami da
lumshe idanunta,sai kuma tace
"You are free in sha Allah.....zaku bi momma mali
soon......abu daya nakeson na gaya miki ko bayan kun tafi......be smart as much
as you can.......ki dinga amfani da kwanyarki da basirarki.....ki kula da nadra
da Haneefa,ki zame musu garkuwa kamar yadda na zame muku.....sannan......ki
zama mara saurin yarda da mutune,walau maza ko mata,a family yake ko a wajen
family......saurin yarda tushen kowacce rushewa ce" Ta qarasa maganar tana
nunata da yatsa.
Iska ta
zuqa sosai sanda take cikin napep din sannan ta furzar da ita waje,tana jinta
kamar mutumin daya dauki dutsen dala da gauron dutse yau Allah ya 'yan tashi ya
samu saukeshi daga saman kansa. Sakayau take jinta,wani farinciki yana ratsata
gami da iskar abun hawa wadda ta manta rabon data ratsata. Ta ware idanu sosai
tana kallon titi.....Don yaushe rabonta data fito?,ko fitarta ta qarshe cikin
rufaffar mota ne qarqashin kulawar jami'an tsaro.
"Sabreena Ahmad AKA MUHSEENA" Sunan da taji an
ambata kenan saitin kunnenta. Ko daga bacci ta tashi tasan waye?......wannan
wata shaidace kuma stamp ne daya kasance nasa shi kadai. Mashkur....ta gayawa
kanta da kanta,don haka ta tattara dukka nutsuwarta da qarfin halinta ta maida
sashen da sautin ya fito.
Shi
dinne,zaune a seat din driver,ya dafe dukka hannuwansa saman steering din motar
yana jifanta da wani zazzafan kallo. Duk da yadda haushinta da wutar son daukar
fansa ke ruruwa a ruhinsa.......amma hakan bai hana shaidan harbawa zuciyarsa
wutar matsananciyar sha'awarta ba. A yadda yake hangen wani lafiyayyen kyau a
tattare da skin dinta......wani irin kyau da abaya fatarta bata sameshi ba,sai
yakejin burinsa ya ninku zuwa gida biyu,YA DAUKI FANSA sannan kuma YA KASHE
QISHIRWAR SHA'AWARTA A RANSA. Dadaddiyar qishirwar data maidashi sakarai kuma
shashasha a kanta duk da tarin tsananin wayonsa.
"Damn it!" Ya furta da qarfi yana dukan steering
din motar tasa gami da cije lips dinsa gami da kashe mata idanu guda daya.
Salin alin ta dauke dubanta daga kansa,tana jin wani matsanancin faduwar gaba
yana saukar mata. Faduwar gaban da bata taba ji ba a kansa ko akan wani d'a
namiji ba idan ka dauke fu'ad din
"To ko wannan shine haqqin aure da kowacce mace kejin
nauyinsa a kanta?" Ta tambayi kanta da kanta tana jinjina girman abun.
Kafin ya sake cewa komai traffic light ya sakesu,motarsu ta riga tasa yin gaba.
Cikin mamaki sai ta samu kanta da addu'ar kada ubangiji ya bashi ikon ganinsu
har ya biyosu yaga gidan da take,duk da ta sani......gidan su zai wahala ya
zama wani boyayyen gida da zai wahalar da za'a iya ganoshi.
*MUHAMMAD FU'AD*
Basuyi
nisa can can ba ya tuna yabar file dinsa a gida,wanda file ne dake da
muhimmanci ya dubashi a yau ya tura da bayanan cikinsa ga company din da suka
nema sanya hannun jarinsu a kamfanin. Ba kasafai ya fiya son yin alqawari ba
tare daya cikashi ba,idan har hakan ta kasance ta tabbas baida yadda zaiyi
ne,don haka ya sanya su saddiq sukayi gaba,shi kuma suka juya da wasu motocin
suna dawowa gidan.
Wuri wuri
zuwaira tayi ta shiga raba idanu sanda taji dirin shigowar motocin nasa harabar
gidan. Raba idanu ta shiga yi sannan ta furta kalmar
"Na shiga uku!" Bayan ta tuna gargadin da yayi
mata a ranar daya fara ganinta. Yadda tasan halinsa ta kuma haddaceshi bata
haddace fuskarsa haka ba,ta tabbatar yazo ya sameta a sassan kamar yadda ya
gargadeta shan ruwanta a gidan ya qare. Wani abu guda daya da bata qaunar ya
faru......zaman gidan yafi mata zaman ko ina......zaman gidan cike kuma yake da
'yanci,ba kyara ba tsangwama,hakanan ba nauyayen aikace aikace a
cikinsa,sabanin gidan maamah din da yake cike da tsarabe tsarabe kala kala.
Wuf tayi
ta miqe tana dosar qofar da zata sadata da sassansu kamar zata ci da baka,cikin
ranta cike fal da Allah ya qarawa laila tare da fatan ubangiji ya hadata dashi
yaci zarafinta har fiye da tunaninta taga yadda abun zai kaya.
Da
nutsuwar nan tasa ya shigo cikin falon,idanunsa suna kan inda ta tsaya a dazun
sannan ta waiwaya tana komawa ciki. Ya janye lumsassun idanunsa yana wucewa
parlor na biyu,daga nan ya doshi qofar da zata sadashi da hallway da kuma
stairs dinsa.
Saurin ja
yayi da baya kaman yadda itama taja da baya da sauri. Ya zuba mata idanu yayin
da ita kuma kwarjininsa yaso bugar da ita. Bata shirya ba amma sai gata tana
rusunawa gami da gaidashi
"Barka da safiya hamma.....ya aiki?"
"Kece laila?" Ya tambayeta yana dinke girarsa tsaf
saboda yadda yaga abun ya masa wani iri. Ta yaya zata ratsa privacy dinsu ta
shigo har nan wajen?,wani irin rashin hankali ne da ita matar gidan zata bari
haka ya faru?. Shi din wani irin mutum ne me tsananin son privacy,kamar yadda
yake da iyakoki akan komai daya shafi rayuwarsa.....kuma kowanne mutum da nashi
iyakar.
Murmushi ta
saki tana wani karyar da wuya gami da rolling idanunta a kansa
"Eh hamma.....nice.....baka gane ni ba?,nazo ne
duba.....ammm.....ammm sabreen,maamah nason magana da ita da gaggawa,so kuma
unfortunately sai na duba ko ina na gidan amma babu ita.....infact ma ta
fita.....".
Banbarakwai yaji maganar kamar da wani yare daban take magana. Ta
fita?,zuwa ina kenan?,sannan da izinin waye ta fita?. Ajiye duka maganganun
yayi gefe guda yana dubanta
"What I have told you tun ranar farko?.....so ki hada
kayanki kibar gidan nan" Yayi maganar da murya me kaushi dake cike da
zallar umarni.
Hukuncin
ya daketa so sai hakanan ya mata tsanani,iya ganinsa data sakeyi yanzu ya sake
tada tsimin soyayyarsa a zuciyarta,saita dubeshi a rikice
"Amma hamma....maamah ce....."
"Arguing won't help the situation" Ya fada da wani
irin yanayi maras hargagi saidai kuma me ban tsoro ne a idanuwanta. Sum sum da
wani irin sagaggiyar gwiwa tsoro da bacin rai ta miqe tana fita daga wajen. Ya
bita da wani irin matsiyacin kallo,sannan yaja tsaki kamar zai tsinke
harshensa.
Har ya taka
stair case din sai kuma ya dakata. Ta fita bata gidan?,maganar ta dawo masa fes
cikin kansa. Juyawa yayi don tabbatar da abinda lailan ta fada,ya fara bincike
gidan guri guri.
Kaf ya
gama duba ko ina a gidan,ya kuma tabbatar bata nan din. Wani wutar fushi yaji
tana ruruwa cikin ransa,yana so yaje ya saukewa duka Securities na gidan,amna
kuma wata zuciyar na gaya masa MARTABAR AURE koda sunanta MATARKA KADAI A FATAR
BAKI.
Samun
kansa yayi da bin lafiyar daya daga cikin kujerun parlor din farko,yayi
relaxing kawai a ciki yana jin yadda jijiyoyin kansa suke harbawa,ba abinda
zuciya bata raya masa ba,ina ta tafi?,wajen su waye taje?.
"Da igiyar aure na?" Ya tambayi kansa da kansa
yana jin yadda zuciyarsa yadda take tafasa. Bai taba tunanin akwai wata diya
mace da zai bari tayi masa wasa da igiyoyin aurensa da ya biya sadakin daya
nemo da guminsa ya bayar ba,kai koda sadakarta aka bashi muddin da sunan
muhammadu fu'ad jikan jadda aka daura bazai taba bari wani abu ya gilmawa
mutuncin igiyarsa ba......idan shi ya warwareta tofa wannan daya.
Ba kasafai
ake barin napep shiga unguwar ba,wannan ya sanyata dole ta sauka daga baya ta
sallameshi,sannan ta fara takawa cikin nutsatsen takunta zuwa street din nasu.
Duk gidan
dake da security a wajen suna ganinta sai taga suna miqo gaisuwa da wani irin
respect,abun sai ya shiga bata mamaki ita kanta. Wai har girma da matsayinsa
yakai wannan?,sannu sannu sai taga alamun mamaki bisa fuskar duk wanda ya ganta
tana takowa da qafafunta.
A hankali
taji alamun tafiyar tayar mota daga bayanta. Bata waiwaya ba,don tun can dama
ita bame damuwa da abinda bai shafeta bane
47
_Daga abdullahi dan abbas R.A yace,Lokacin da aliyyu R.A ya
auri nana fadima,sai manzon Allah S A W yace"ka bata wani abu(a matsayin
sadakinta),sai sayyadina Aliyyu yace "ba komai a wajena" Sai manzan
Allah S A W yace "ina sulkenka?"_
"Ameenatu" Taji muryar nan dai ta dazu tayi
kiranta. Sai da taja numfashi sosai tana son danne bugun da zuciyarta keyi
sannan ta waiwaya inda ya daidaita motarsa saitinta,yana zaune kusa da window
yana murxa steering hankali kwance fuskarsa shimfide da wani shu'umin murmushi.
"Na rantse wannan karon ba zaki sha ba......na miki
wannan alqawarin muddin na haifu cikin uwata da ubana......lallai saina maida
sha'awata a kanki......sai kuma na bankadawa duniya wacece ke bayan na maido
kudadena cikin dukiyata......ki rubuta ki ajiye" Daga haka yayi saluting
nata,sannan ya taka motar da gudu yana wuceta.
Bata fasa
takawa tana nufar gida ba,kamar yadda bata fasa bin bayan motarsa da kallo ba
har ya qurewa street din nasu. Wata mahaukaciyar fargaba tana ratsa
zuciyarta,sunan mashkur tare da cikakken sanin wayeshi yana gewa tunaninta,a
haka ta isa qofar gidan,ta kuma yi tsaye tana duban dogayen katangun gidan
kamar me karantar ilimin zanen gidaje.
Tana
wassafa yadda zai iya tsallake wadannan dogayen katangun mansion House
din......tana qiyasta ta yaya zai iya wuce wadannan securities din da samudawan
dake tsaron kowacce kusurwa ta gidan?. Tsaron gidan kadai ya dan sanyawa
zuciyarta nutsuwa.....saidai kuma bai kore fargaba ko kuma ya mantar da ita
wanene ASALIN MASHKUR BA.
Gangar
hankalinta bata dawo jikinta ba sai data sanya qafafunta cikin gidan,idanuwanta
kuma sukayi mata arba luxury cars dinsa dinnan dake ajiye a parking lot na
gidan.
Sai
yanzu ta tuna bata nema izinin kowa ba sanda zata fita,don sam ta manta hakan
yana cikin wata doka dake kan kowacce macen aure.....baya ga haka.....a lokacin
ba abinda take iya tunawa illa hanyoyin da zata nesanta rayuwarsu da maamah
din.
Da
confidence din ba lallai su hadu ba har ta wuce daki.....ba lallai ma yasan
bata a cikin gidan ba ta tura glass door din parlor din tana sanya qafafunta.
Da bude
qofar da haduwar idanuwansu lokaci guda ya faru. Iya kallon data gani cikin
rusunannun idanuwansa sun bata wata fargaba da bata taba jinta akan kowa da
komai ba.
Dakiya
ta aro ta azawa ranta,tana jin a ranta a yanzu daidai take da kowa a
cikinsu.....ko shi ko mamarsa. Tana jin lokaci bijirewa dukka wani sharuda nasu
yazo,tana jin abinda ya rage mata biyu ne......ta samu tabbacin fitarsu zuwa
mali a sannan takejin zaman wannan qallagaggen gidan dama me gidan gaba daya ya
qare mata.
Cikin
dakiya da basarwa taci gaba da takowa kaman bataga kowa zaune a parlor din.
Tsaf ya gama karanta da kuma fahimtar abinda take shirin aikatawa. Ba za'a
fishi sanin miskilanci take taken miskili da kowacce dabi'a tasa ba,sai ya
dauke kai kaman bai damu da takunta ba,zuciyarsa na sake matsewa,ransa kuma
yana qara baci har zuwa sanda ta raba tsakiyar falon.
Ba zato
ba tsammani ta tsinceshi a gabanta. Tsaiwarsa yayi mugun dab da ita,hucin fitar
numfashinsa da wani irin dumi da yake bayyanar da bacin rai da zuciyarsa ke
ciki yana sauka saman goshinta. Motsawa tayi da nufin ja baya don bata tazara a
tsakaninsu qirjinta na wani irin bugawa,saidai da tsananin zafin naman nan nasa
ya cafki hannunta yana matsawa da kyau
"Daga ina kike?!,ina kika fita?,gurin waye kika
je?" Ya tambaya a jere cikin tsawar data ratsa dodon kunnenta har sai data
runtse idanunta.
Tattara
dukka qarfinta tayi ta sabule hannunta daga nasa,wanda ta samu sauqin hakanne
saboda banguls din hannunta ya riqe saita zame ta barshi dasu,saidai ko taku
biyu batayi ba ya rufo mata baya,sai ya zamana tana tafiya da baya da baya,shi
kuma yana maida qafarsa kowanne gurbi data cira qafartata.
Kowanne
taku guda daya sai qwayar idanunta sun gauraya da nashi. Abinda take gani cikin
idonsa batasan wanne iri bane......wani yanayi ne da bazata iya fasaltashi ba.
Yana sake kunsatota yana sake maimaita mata tambayoyin da suke sake
razanata,bata ankara ba taji ta bugi bango,tabbacin kowanne space ya qare mata
kenan,sai tayi cak sanda ya iso dab da ita,cikken motsi idan tayi yana iya sata
ta kasance cikin jikinsa.
"Gurin wa kika je?,me kuma kikaje yi nace!"
"Ban sani ba" Ta fada da rawar murya tana qoqarin
daidata mode dinta. Ko kusa ko alama bata tanadi amsar da zata bashi ba.....shi
kuma ya matsa mata da tambaya.....tambayar da ba abinda take mata sai qara
fusatata......GURIN WA KIKA JE?,ME KIKAYI?,idan ya fada din sai taji kamar ha
debo garwashin wuta ya watsawa sassan jikinta ne. Ba abinda yake tuna mata sai
mummunar kalmar yawan mutane musamman na cikin gidansu suke jifanta da
ita.....kalmar da koda ta nuna ta shanyeta tana iya hana idanunta bacci da wani
matsanancin fushi da bacin rai.....shima irinta yakeso ya ara ya yafa yayi aiki
da ita a kanta?,batajin kunnuwanta zasu iya jurar ci gaba da jin ana jifanta da
kalmar da bata da masaniyar komai a kanta.
Hannuwansa ya dunqule waje guda yanason hana kansa marinta da zuciyarsa
keda muradin yi. Bayaso yakai hannunsa jikinta......baya so ta zama mace ta
farko daya fara mari duk kuwa da yanajin ta cancanci haka.
"Karki bari nayita maimaita maganata......ina kika fita
ba tare da izinina ba?....wajen wa kika je?!!!!" Yayi zancan da wani irin
qaraji daya sanyata curewa waje guda,kowanne sashe na jikinta ya dauki rawa
"Banje wajen kowa ba.....ni ba wajen wanda naje"
"....You're going to regret messing with me,for the
last time....ina kikaje?" Ya sake tambayar yana sanya hannuwansa duka
biyun dake a dunqule ya daki bangon da take maqale a jiki ta saitin kunnuwanta.
Abinda ya sake gigitata kenan ta saka hannuwanta duka biyun tana toshe
kunnuwanta gami da rruntse idanunta. Zuwa sannan kowacce jarumta dake jikinta
tabi ruwa.....ba abinda ya rage mata sai rauni daya narke zuwa kuka.
Cikin
qasa da second biyu ta tsinci hannuwan nata jikin nata hannun dake toshe da
kunnenta yana saukesu,da wani irin taushi da sanyin murya taji yana fadin
"Is okay......wanne irin matsoraciya ce ke?.enough,stop
crying please" Bata qara tuna komai ba ta tsinci kanta saman faffadan
qirjinsa,ya sanya hannunsa daya ya lullube bayanta,daya hannun kuma yana shafa
gadon bayan nata da irin salon da uwa kanyi don lallashin jaririnta.
Wani
sassanyan qamshi dake ratsowa daga qirjinsa da kuma kowanne sashe na jikinsa ya
cika hancinta da wani irin sanyi daya soma qoqarin daidaita yanayinta. Saidai
hakan ya gaza samuwa,don qarasa rudata yayi,daga yadda kunnuwanta ke iya jin
yadda zuciyarsa take bugawa kadai ya tabbatar mata fusatarsa ta gaske
ce......amma me ya sanyashi sauya yanayi haka cikin qanqanin lokaci tamkar
wahainiya?. To kodai yana da boyayyun aljanu da suke sauyashi haka da sauri?.
Bata gama
wannan tunanin ba muryar ma'u ta zame mata amsa
"Ina neman afuwa ranka ya dade.....ayimin afuwa"
Ta furta da tsananin kunya tana sadda kanta qasa. Bata taba tunanin zatazo ta
samesu haka dab da juna ba,kwata kwata ma batayi tunanin suna nan ba,tasan me
gidan dai ya fita......dawowar da tayi kuma tazo dubawa amna ko ta dawo?,don
sun hadu ta daya qofar sai kawai ta shiga sassanta da taji sabreen din bata
nan.
Kai kawai
ya gyada yana ci gaba da shafa bayanta kadan kadan
"Hajiya amna ce tace nazo na duba kota dawo......"
"......ta dawo.....amma batajin dadi,kice ta
qaraso" Da sauri ma'u ta amsa ta juya tana ficewa a gaggauce.
Kaman yana
jira ne ma'u din ta fita ya saka hannunsa ya tureta daga jikinsa. Banda yana
kusa da bangon daya bata kariya ba abinda zai hanata zubewa qasa. Da wani
fusataccen kallo yake dubanta.
"Kada ki dauka na yarda ne da abinda kika
gayamin......muddin na bincika na samu wani abu na daban saina miki mafi munin
hukuncin da baki taba tunani ba......hakanan duk ranar da kika qara gangancin
fita koda qofar gidan nan ne ba tare da izinina ba......saikinyi dana sanin
sani na........nan din gida ne da aka gina da tsaftatacciyar dukiya ta
halas.....ba bariki bane ba ba kuma hotel ko gidan karuwai ba" Daga haka
ya juya yana daukan file dinsa dake ajiye saman daya daga cikin kujerun falon yana
ficewa da sassarfa.
Wani irin
kuka ne yakeson qwace mata amma tana hana kanta,don idan har kunnuwanta sun
jiye mata daidai amna na gidan,kuma zata iya iskota koda wanne lokaci,dole ta
tattaro dukka wani bacin rai tana hadiyeshi,saidai kuma abinda takeji yafi
qarfin abinda zuciyarta zata iya dauka,sai bacin ranta ya zabi fita ta hanyar
fitar hawaye daga idanunta zuwa saman fuskarta,ta lallaba tana neman kujera
daya ta zauna a kai tana dafe da kanta.
"Oh god........ damn it....." Abinda ya dinga
maimaitawa kenan cikin mota yana saka yatsunsa cikin sumar kansa.
Ya manta
yaushe ne lokaci na qarshe daya fusata irin haka.....yaushe rabon da yaji
zallar bacin rai irin wannan dake ratsa kowanne sassa na jikinsa. Ya alaqanta
hakan da tozarta igiyar aure da yake shirin faruwa. Sai ya samu kansa da
blaming kansa,me yasa zai daga hankalinsa har haka?,ai duk wanda ya siya rariya
yasan zata zubda ruwa. Ransa yaji yana qara baci,sai ya yiwa driver magana ya
qara speed na motor din.
48
_An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi
yace,manzon Allah S A W yace,idan miji ya kira matarsa zuwa shimfida taqi
zuwa,mala'iku zasuyita la'antarta har gari ya waye_
*_qarqashin wannan hadisin akwai qarin haske,idan a wannan
qin da tayi kuma ta samu ciki koda ta rasu wajen haihuwa wasu malamai suna
ganin bata samu wannan shahadar da mace me naquda ke samu ba idan ta rasu_*
*MAAMAH*
Tunda ta
cewa zuwaira taje ta duba mata su taci gaba da kiran wayarta ba qaqqautawa don
ta matsu taji feedback,saidai kuma shuru ba'a picking wayar. Saita koma kiran
wayar laila ita dinma duka sammakal. Kamar ta dora hannuwanta akai tayita rusa
ihu haka taji,ta tsinewa zuwaira da laila a ranta batasan adadi ba
"Dukkaninku baku da amfani" Ta fada da fushi,sai
taji kamar ba zata iya zama ba....wannan karon zata tafi gidan fuad da kanta ne
ta dubo meke faruwa ba tare da damuwa da komai ba.
Tana taka
qafarta kiran zuwaira ya shigo,tayi qoqarin hadiye fushinta tana fatar samun
feedback me dadi,saidai amsar da zuwaira ta bata ya kusa sanyata zubewa qasa
warwas
"Bata gidan ita kanta.....kuma akan idanuna ta dawo ita
kadai". Iya haka kadai ya bawa maamah amsar abinda taketa zulumin ya faru.
Ta kwashesu,ta tseratar dasu,amma dai bata sare ba,tana da sauran hope,don haka
kai tsaye ta fara kiran number huda.
Kiran
duniya computer ta gaya mata ta kuma jaddada mata wannan layin a kashe yake. Ta
laluba wayarta kaf ta rasa number wayar bokanta tana me mancewa da cewa mutumin
baya riqe waya,yo mutumin dake rayuwar tsakiyar dajin Allah ina gaya service ma
bare waya ta dameshi?,mutumin da yake kewaye da aljanu,suke kai masa saqo kuma
ku amso masa ko daga ina ne?,me zaiyi da waya?.
Hajja
harira ce ta fado mata,ba bata lokaci ta danna number dinta tahau kira.
*Hajja harira*
Tun fitar
laila bata iya tashi daga wajen ba,idan tace ta qulla tunani sama da dubu da
kwancesu tsaf a wajen ba zatayi musu ba. Duk wani tunaninta idan yaje ya dawo a
waje daya yake cakewa,tun tana neman qaryata abinda take zargi har zuciyarta ta
gama yin ittifaqin amsar dai itace
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ta furta da
wani matsanancin tashin hankali. Tayi imani muddin abinda take zargi ne ya
tabbata.....to lallai laila zata qare rayuwarta kaf wajen bautar maamah......
Asiri ne da bashi da makari sai mutuwa.....yaci uban bita zaizai,yafi uban tace
saidai kafin tace. Ita mariya zata yiwa haka?,wannan shine sakamakon alkhairin
da ita tayi mata?.
Kamar
tasan itace a gaban tunaninta saiga kiranta ya shigo. Kamar kada ta daga amma
kuma wani tunani daya darsu a ranta ya sanyata gyaran murya ta daidaita
muryarta sannan ta daga din.
"Al'amura kamar suna shirin kwabewa hajja.....ina
tsoron kada zancan mutumin nan ya fara tabbata......ki taimakeni hajja".
Maamah ta fada da tsananin damuwa,damuwar data saka hajja taji wani bangaren na
tata damuwar da tashin hankalin suna samun sassauci.....ko banza ba ita kadai
ke cikin damuwa ba......ba kuma ita kadai zata ci gaba da zama a cikinta
ba,taci alwashin dukka yadda zatayi zata yi don maamah taci gaba da tabbata
cikin damuwar ta,waye ya gaya mata yaro yana wasa da kan maciji koda kuwa ya
rasa abun wasa?.
Yanayinta ta daidaita don yayi dai dai da yadda maamah zataso taji,tana
mamakin zallar rainin hankali irin nata. Bayan mummunar sakayyar da tayi
mata,kuma wai ta nemeta da tata matsalar tamkar ma batasan me ya faru ba?.
"Me yake faruwa?"
"Garkuwata ta subucemin......daga yanzu zuwa kowanne
lokaci zan iya fuskantar barazana daga wajen abun hari na,kowanne hope nawa
kuma ya subuce hajja.....meye abunyi?" Ta qarasa maganar da sigar tambaya
cike da damuwa. Iska hajja ta furzar tana dan bubbuga tafin qafarta kadan
kadan,a nutse tace da ita.
"Bani lokaci mariya nayi tunani......mintuna kadan nake
buqata". Jikinta a sanyaye ta amsa mata suna katse wayar su dukka biyun.
Wayarta
take dan bugawa cikin tafin hannunta cikin salo na tunani. Mariya shegen kai
ce,tana da nata matsanancin wayon da kai da kake rayuwa da ita kayi kadan ka
fahimci komai idan ba ita taso ba.......saidai kuma a wannan yanayin da ake
ciki mariya tana tafin hannunta ne. Bata isa tayi wani motsi cikakke ba ba tare
da ita ba,itace ginshiqin.....itace kuma madogarar. To shin batasan abinda tayi
mata bane?,batasan me ya faru ba?,ko tsananin iya bariki ce kawai?.
"Inaso na samu tabbaci" Ta furta tana daukar
wayarta data aje tun daxun ta sake lalubar number maamah din.
Bugu daya
tak ta daga,ta sanya wayar a kunnenta tana kiran sunan hajja.
"Duk abinda zaka daukoshi ko ka matso dashi don biyan
buqatarka......kuma ya gaza yin wannan aikin sai nakega bashi da wani
amfani,kau dashi kawai zaifi.....me zai hana ta gusa daga rayuwar fuad tun
kafin matsalolin da boka ya baki a dunqule su fara bayyana har sufi qarfin
shawowarki?....ga laila nan?,umarni na da naki sune zasu zama abun binta,a
azata a bigiren da wannan ke kai,nayi Imani da laila......tabbas ba zata sabawa
tsarinmu ba......sirrinmu kuma a lullube".
Nauyi
maamah taji maganar tayi mata,sannan sam bataji maganar ta kama hankalinta ba.
Har cikin jininta da zuciyarta takejin laila bata mata ba,kwata kwata bata dace
da wannan aikin ba,bata dace ma ta zama matarsa ba koda na minti guda ne kuwa.
Tasan wacce hajja farin sani,tana tunanin ita ko yaronta zasu kubuta daga
ayyukanta ne?,sai ta girgiza kai a fili tana jin abun bai kama hankalinta ba.
To amma dole sai tabi ta takatsantsan kafin ta fahimtar da hajja din,tafi kowa
sanin hajjan akan laila bata dagawa kowa da komai qafa.
"Aah fa hajja harira,laila ni dake duka 'yarmu
ce......ba zamj jefata cikin wannan risk din da wahalar ba......qyale bare
dai,wanda idan ya sabawa tsarinmu kowanne mataki zai iya fadawa
kansa........kamar yadda itama wannan din MUMMUNAN SAKAMAKO na rantse miki da
Allah zai yita bibiyarta......ba zan qyaleta ba,sai na banbance mata tsakanin
aya da tsakuwa!" .
Turqashi!.....hajja ta fada qasan ranta,kai tsaye a bayyana ko a
kaikaice maamah bata qaunar laila ta kafa tarihin zama matar muhammad me
jadda.....wannan shine amsar tambayarta kai tsaye idan aka cire kauce kauce.
"Ke yanzun wanne shiri ne na gaba kike ganin ya kamata
muyi?" Ta mata tambayar tana relaxing kanta don samun bakin zaren daga
inda zata dasa nata aikin.
"Ki bari tukunna na samu nutsuwa daga wannan,abubuwa su
hau kan saiti,zaki ganewa idanuwanki ba tare da nace dake komai ba". Ta
fadi mata kaman yadda ta saba. Tana da boye duk wani shiri nata,zai wahala tana
kan shiri ka sani,ko a baya wannan ne ya zama SILA da sanadin da LAILA ta shiga
DUNIYAR lissafinta,qila data tsaya neman fashin baqi wajen boka kamar yadda
hajja taso suji......ba shakka da qila yanzun haka laila bata fada wannan BAQAR
MASIFAR ba....dukka hajja ke wannan tunanin cikin ranta tana jin wani bacin rai
yana taso mata.
Hajjan ta
bude baki zatace wani abu sautin kukan laila ya mamayi kunnuwanta daga cikin
wayar. Wani abu ya daketa,tayi shuru tana sauraren tambayar da maamah keyi mata
kafin kiran ya yanke.
"Tashin hankali!" Ta fada a sarari tana miqewa
tsaye,ji take kamar ta wuce kai tsaye gidan maamah amma wata zuciyar na jan
kunnenta
"Sai kinyi kamar baki sani ba......sai kinyi kamar baki
fahimci komai ba,saikin maida komai ba komai ba". Wadannan maganganun suka
sanyata rusuna ta koma ta zauna wuta naci gaba da balbala a zuciyarta. Daidai
sannan nafessa ta shigo da mopper da broomstick tare da sallama a sanyaye cikin
girmamawa.
"Ubanme kika shigo kiyimin?". Kai ta sunkunyar
"Kiyi haquri,haidar ne ya tashi da zazzabin haqori yau
shi yasa ban shigo sharar da wuri ba". Duk da jikanta ne bata tsaya ta
nuna kulawa ko alhinin komai ba,hasalima bata fahimci gaya mata take baida
lafiya ba yaron,sai ta daka mata tsawa tana fadin
" Sharar da bakiyita dazu ba sai yanzu ko?,baqar
munafuka,fita ki bani waje". Tashi sosai hankalim nafeesa yayi,take
idanunta suka tara ruwan hawaye,tana tsoron me zata gayawa d'anta a kanta idan
ya dawo,tanason aurenta batason ta kashe mata shi,wannan ya sanya ta sulale
tana tsugunnawa ta soma mata magiya tana bata haquri
"Ki tashi bani waje kafin na rufeki da duka,sharar ce
nace banaso ko ana dole?" A nan ta fahimci bawai iya rashin sharar bane
kawai da ba'ayi ba ya sanyata haka,akwai wani abu na daban da ya bata mata
rai,wannan ya bata sassauci sai ta miqe tana sake bata haquri ta bude qofar ta
fita gami da rufe mata. A qasan ranta tana tafe tana addu'ar
"Ubangiji ka qara mata damuwa fiye da damuwoyin data
sanyawa zukatanmu.......ya rabbi ka shagaltar da ita da damuwarta ta yadda zata
zame mana mu kuma hutun da bamu taba samunsa cikin gidajen mazajenmu ba".
49
_Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; "idan
dayanku yazo masallaci,ya duba takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya
kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_
*_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin
ba najasa ko dauda a jiki_*
49
Ta furta har
tsakiyar ranta tana jin ciwon bautar da suke ciki,wadda basusan ranar fitarsu a
ciki din ba,sunfi kyautata zaton wataqila sai ranar da surukar tasu ta kwanta
dama.
Ajiye
wayar maamah tayi a gefanta tana duban laila da hawaye ya yiwa fuskarta shabe
shabe
"Lafiya laila?,me yake faruwa?" Ta maimaita
tambayar tana riqe hannunta
"Hamma fu'ad ne maamah......ya koreni". Fuska ta
ya mutse tana duban lailan,tashin hankalin da take ciki a yanzun bata jin yakai
korar laila daga gidan fu'ad,duk kuwa da cewa hakan da yayi taji ya tabata ya
kuma qara bacin ran da takeji a ranta. Ya nuna bata isa ba kenan kamar yadda ta
saba.....amma yanzun ba shine abinda ya kamata ta damu dashi ba.....tanason
tasan ina yaran?.......ina suka shige?,meye manufar yarinyar?,meye takunta na
gaba?.
"Kina da buqatar ki koma gidan?" Maamah tayi mata
tambayar kai tsaye,don son tabbatar da maganar da sukayi da hajja a yanzun.
Shuru lailan tayi,tana jin tamkar kowanne tsari na zuciyarta da kuma tunani na
qwaqwalwarta ya birkice,tsare tsarenta......burikanta dama duk wani abu dake
gabanta sai takejin yana sauya muhalli. Tanason fu'ad sosai......tana kuma jin
soyayyarsa.......amma sai takejin zama da maamah yafi mata zama da fu'ad
dadi......hakanan ko me maamah ta furta shine umarninta,to tabbas zata iya aikatashi
komai tsanani da tsaurinsa.
"Inason hamma fu'ad sosai,inaso na aureshi.......kuma
hajja tayimin alqawarin sai na aureshi....." Maganar sai ta zowa maamah
banbarakwai,tayi mata saukar ba zata,ta xubawa laila idanu tana mamakin
furucinta tare da tantamar lafiyar qwaqwalwar laila din.
"Tayi miki alqawari?,yaushe kenan laila?" Maamah
data tattara dukka hankalinta akan lailan ta fada cikin tsananin mutuwa da kuma
sanyin jiki.
"Tun sanda ake shirin auren hamma fu'ad.....ta kaini
gidan na zauna don na karanceshi tsaf,sannan ta bani ayyukan da zan bashi yaci
saboda jawo da hankalinsa kaina da kuma siyan soyayyata......wanda daga qarshe
takeson ya dawo hannunta gaba daya".
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Maamah ta
fada tana jin saman kujerar yayi mata tudu da yawa,ba zata iya zama a kai ba
duk da laushinta,sai ta sulale ta zauna sosai a qasa. Ta sake zubawa laila
idanu sosai maganar na ratsata,amma kuma tana cike da tantama da tunanin
cikakkiyar lafiyar kwanyar laila.
"Tabbas laila ta fara shaye shaye" Shine abinda
maamah ke ayyanawa a ranta. Ba yadda za'ayi hankalin laila
daidai......lafiyarta kuma qalau ta dauki babban sirri da labarin cikakkiyar
cin amana irin wannan ta gaya mata.
"Don Allah kada kiyi fushi dani.....kome kike buqata
zan miki maamah" Laila ta fada alamu na bayyana kuka nason qwace mata.
Al'amarin ya sake jefa maamah a madaukakin mamaki
"Me kikeso in sake baki labari?" Laila da gabanta
keta faduwa cikin matsanancin tsoron kada ta batawa maamah ta fada tana
durqusawa a gabanta.
Mamaki ya
sake kashe maamah,ta sake saka idanu ko zataga wani abu na tabin hankali ko
hauka tattare da laila,saidai ko kadan bataga wannan ba illa tsantsar biyayya
da faranta rai da takeso ta yiwa maamah din.
"Ki nutsu mariya.....ki nutsu,makashinka
tabarmarka......makashinka yana tare da kai" Wata zuciyar ta ankarar da
ita,wannan ya sanya ta aje mamakinta da tunaninta meke faruwa?,ta maida
hankalinta ga laila
"Tashi ki zauna sosai muyi magana" Cikin hanzari
ta miqe ta koma inda saitin inda maamah ke nuna mata ta zauna.
"Me yasa kika yanke hukuncin gayamin sirrinku ke da
mamarki?" Ta tambayeta da matsanancin mamaki.
"Saboda ya zamemin dole na inyi miki biyayya.....inajin
cewa ke din kamar uwargijiyata ce.....ni kuma baiwarki,inajin kamar dama can an
halicceni ne don na miki biyayya,inajin komai zai iya samu na muddin ban miki
biyayya ba......burina na mutu ina miki biyayya.....burina na mutu ina bauta
miki". Ta qarashe maganar da zallar gaskiya da kuma yanayin da yake nuna
cewa da gaske take furta maganar dake cikin ranta din. Kowacce tsiga ta jikin
maamah sai data zuba,wannan shine kwatankwacin abinda take buri,take fata take
kuma mafarkin taji ta kuma gani daga wajen fu'ad......ya akayi haka ta kasance
akan laila.
"Laila......akwai abinda aka dafawa fu'ad a gidansa
baici ba ke kika ci?" Ta jefa mata tambayar da zallar kokwanto a ranta.
Kai tsaye
ta gyada mata kai tana dubanta
"Eh.....kwana hudu da suka wuce,naci abincin dare a
dining dinsu"
"Shikenan!" Maamah ta furta tana runtse
idonta,tayi tsam da ranta bata iya cewa komai ba. Tsahon wasu sakanni tana
nazari a zuciyarta,kafin kuma a hankali taji kowanne tashin hankali yana
sulalewa daga zuciyartata. Idanunta ta ware akan lailan
"Meye shirinku a kaina.....meye shirinku akan
fu'ad?" Tambayar data yiwa laila kenan tana da yaqinin da tabbacin zata
gaya mata komai tiryan tiryan.
Shuru
maamah tayi tana biye da laila din har ta gama kwashe mata bayanin komai. Ba
bayanin yadda lailan ta zayyane mata komai bane yafi daga mata hankali ba,qulli
da tuggun da hajja ta shirya qarqashin nata shirin shine abu mafi tsoratarwa da
razanarwa a wajenta.
Don baje
sirrinsu tasan zata samu information akan dukkanin abinda ya shafi hajja sama
da abinda laila ta gaya mata ma a yanzu.....muddin wannan hadadden tanadin data
yiwa fu'ad ne ya isa cikin laila.....to ko kashi lailan zatayi kuma take da
buqatar ta shaida mata kafin ta yishi.....lallai ko bayan gida zai kashe laila
ba zatayi ba sai da yarjewar maamah.
Take
dukkanin wani alhini da fargabar cin abincin da laila tayi ya fice daga zuciyar
maamah. Baqincikinta daya asarar data jawo mata,gagarumin shirinta daya
baci,wanda ta kashewa maquden kudade masu yawan gaske don ta samu fu'ad a
hannunta,yanxu samun laila me zai tsinana mata?,banda kaya da zata zame mata?.
Idan
akwai riba guda da zata samu itace......ribar nunawa hajja kuskurenta na
ha'intar qauna da aminci da tayi
"Lallai zan mulki laila ko don na nunawa hajja itadin
qanqanuwar maciyar amana ce.....zan mulki laila a gaban idanunta.....zan kuma
bautar da ita yadda take bautar da d'iyoyin mutane cikin gidanta".
Duk da
takaici tashin hankali da baqinciki daya cika mata zuciya amma saita dubi laila
da dan murmushi
"Zaki zauna dani?" Da sauri ta daga kanta tana jin
kamar an mata rahama ne
"Zan zauna.....zan zauna dake maamah.....hakan yafimin
komai dadi a duniya"
"Da kyau" Ta fada a hankali,dan daga murya tayi
sannan ta kira daya daga cikin masu aikinta na gidan tace
"A bata daki" Ta bisu da kallo sai data tabbatar
sun fice a falon sannan ta maida hankalinta cikin jikinta,
Iska me
zafi ta furzar tana lula kanta cikin duniyar tufka da warwara......babu babban
target dinta a yanzu haka idan ba sabreen ba. Bata gidan ta fita.....shine
abinda ta yita nanatawa tana shafa lips dinta da yatsantsa. Da sauri kaman
wadda aka tsikara ta jawo wayarta,ta tafi kai tsaye izuwa ma'ajiyar lambobi ta
zarce can qasa.
A jere
numbers din nasu suke,saidai kuma tayita kai kawo akan waye zata kira a
cikinsu?,waye yafi zafin aiki?. Cak idanunta ya tsaya akan wata number da aka
rubuta sunan HANZARI bata tsaya jinkiri ba ta danna kan number ta tura gaba
izuwa kira.
Bugu daya
tak aka daga,da wata iriyar birktacciyar murya ake fadin
"Allah yabar mana ke uwar dakina maganin kuka na".
Wannan kirarin nasa yana fasa mata kai ainun,kuma ko a yanzun shi kadai ya bata
tarin qwarin gwiwa
"Nayi missing target hanzari.......ka shirya ko da
kowanne lokaci zaka iya jin kirana......idan kiran kuma ya tabbata......babban
aiki nake da buqatar ayimin wanda daga shi bani da sauran haufi ko
matsala"
"An gama uwar dakina" Ya fada da qatuwar
muryarsa,bata jira komai ba ta kashe kiran,ta kuma maida akalar kiran nata zuwa
ga number huda.
Abu daya
dai ake sake gaya mata,layin a kashe yake,saita saita lokutan da zataci gaba da
kira daga nan har zuwa awa ashirin da hudu,ta aje wayar ta kuma shiga tunanin
meye abunyi na gaba?.
*MASHKUR*
A hankali
ya sake gilmawa da motar ta gaban gidan,ba kuma wai don yana da wani abunyi ba
ko kuma lalura ke sanyashi wannan zirga zirgar da yakeyi ba......aah,yana yine
saboda nazartar gidan da kuma dukka wani kai kawo na jama'ar gidan dama
ma'aikatan dake aiki cikin gidan daga dare har rana. Wadanda suke shifting da
kuma wadanda zamansu kenan.
Yayi
gaba,amma sai yaci gaba da kallon gidan ta rearview mirror yana kada kansa a
hankali. Babba duk inda yake babba ne,gidan na daya daga cikin dream house
dinsa daya jima yana tunanin idan har ya samu yadda yakeso a shekaru goma masu
zuwa zaya mallaki irinsa. Hannunsa ya sanya ya daki steering din motar yana jin
wani zafi cikin ransa. Yarinyar tasha dashi da yawa a rayuwa,banda wani abu
daya rinjayi zuciyarsa tabbas plan A dinsa a yanzu shine zai zama plan B,plan B
kuma shine a plan A,to amma duka wannan bazaiyi aiki ba......yana ganin gwara
ya fara diban ganimar tukunna,idan yaso ko meye zai faru daga baya me sauqi ne.
"Ina fata ka gama kallon komai?" Yayi magana da
mutumin dake zaune a back seat wanda zai wahala ka iya fahimtar da mutum a
gurin.
Kai ya
jinjina yana motsa system din dake saman cinyarsa
"Na gani......aiki ne me bala'in hatsari da dukkaninmu
zamu jefa rayuwarmu cikin hatsari........amma kuma,ranar biyan buqata rai ba'a
bakin komai yake ba.......let's try it......idan mukayi winning...." Sai
ya saki murmushi yana rufe system din
"Zamu kasance mutane mafi sa'ar zuwa duniya" Ya
qarasa maganar yana dukan bayan kujerar dake a gabansa. Iya nasarar da yayi
musu hasashe ta saka mashkur qyaqyacewa da dariya
"Inaso naji dandanonta.....inaso naji ya
take.....bansan adadin mafarkin da nayi a kanta,ban taba sanya kwadayina akan
wata 'ya mace ba tunda na fara sanin 'ya'ya mata....wannan macen ta zullemin
bansan ya take ba sai a kanta,dole ta fahimci wannan kuskuren data
aikata!" Ya fada da qwarin gwiwa qwarai da gaske,yana jin ya zaqu da komai
ya tabbata.
"Bazan iya dogon jira ba Mike.......ka shirya komai
tsakanin kwanakin nan biyu" Daga hakan sai kawai ya qarawa motar wuta
sosai suna gaggawar ficewa daga layin.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
50
_Daga ibn juhaim bin haris RA(wannan sunan sahabin annabi ne😄),yace:Manzan
Allah S A W yace "da me wucewa ta gaban me sallah yasan abinda yake kansa
na sabo,tabbas da ya tsaya(ya jira me sallahn ya gama)tsahon gwargwadon shekara
arba'in shine yafi masa alkhairi akan ya wuce ta gabansa_
_Bukhari da muslim ne suka rawaito_
50
★Daure da
babban towel ta fito daga wanka,qaramin tana tsane doguwar sassalka sumarta
dake a jiqe sharkaf da ruwa,alamu dake bada tabbacin wankesa tayi. Idanunta a
lullumshe tana jin kalan nauyin da yayi mata saboda kukan da tasha a jiya. Duk
da nauyin da zuciyarta tayi mata amma ta wani fannin sai take jinta sawai kamar
wani nannauyan dutse dake danne da ita ne ya sauka. Tun daga jiyan data
tabbatar ta miqasu hannun da bata haufi akan zasu cutu ko wani abu maras kyau
zai samu riskarsu.
Tana daga
gaban madubin,kadan kadan tana hangen yadda iska take kada labulayen dakin,wata
sassanyar iska me dadi kadan kadan tana ratsowa cikin dakin. Lumshe ido ta
sakeyi sanda ta gama gyara gashinta ta matseshi cikin ponytail holder bayan ta
lanqwasa jelarsa me tsaho sosai,fuskarta ta fito sosai,sai ta sake lumshe
manyan idanunta da suka rusuna sosai. Zuciyarta ciwo takeyi idan ta tuna da
tuhumar da yayi mata jiyan,tana jin wani zafi cikin qirjinta duk sanda kalmar
"Wajen wa kika je?" Ta dawo mata a kunnenta
"Me kikayi?" Tana sake sakata jin zuciyarta na
matsew a qirjinta.
Vibration
din da taji daga gefanta shi ya ware zaren tunanin dake qulluwa cikin kanta.
Maida dubanta tayi wajen,wayar huda data karba ce wadda ta sakawa charge tun da
asuba,bayan wayar ta cika kuma sai ta kunna kanta da kanta kamar yadda tsarin
wayar yake.
Sunan
MAAMAH data gani ya isheta bayanin wacece,wani matsiyacin tsaki taja tana janye
idanunta daga kan wayar,sannan ta juya tana wucewa closet dinta don neman kayan
da zata saka.
Idan ta
tuna abinda d'anta da ita sukayi mata,sai taji kanta ya cika da shawarwarin
hanyoyin da zata dauki mummunar fansa a kansu kafin ta tattare tabar rayuwarsu.
Duk da cewa nashi me sauqi ne,don baiyi yunqurin taba mata kowa nata ba,saidai
ya taba mata zuciyarta da munanan kalmomin da koda tayi nesa da rayuwarsa bata
jin zata iya mancesu.
Har zuwa
yanzu da take wannan tunanin ta rasa wanne kalar abu ya kamata ta yiwa maamah?.
Abu daya tayi ittifaqi akai shine......tabbas zata banbance mata tsakanin aya
da tsakuwa......zata kuma shayar da ita mafi girman mamaki.
Tabbas
inda tana da ra'ayin d'anta......lallai da zata mallakeshi a gaban idanunta
ne,mallakar da babu boka babu malam.......mallaka ta ruwan sanyin da sai ta
gwammace bata sanyata a shirmen shirinta ba.
Har ta
ciro kayan ta dawo ta shirya cikin Palazzo da
blouse data kasance cif cif jikinta don bata buqatar kaya masu nauyi
kiran bai daina shigowa ba,ta kammala ta feshe jikinta da turare . Scarf ta
sanyawa kanta sannan ta taka a hankali tana isa inda wayar take sanda take dab
da tsinkewa.
Stool taja
ta zauna bayan ta daga kiran ta sakashi a handfree ta kuma ajiye saman mirror
table din tana tattara hankalinta akai.
"Dawa nake magana?" Abinda ya fara fita kenan daga
bakin maamah da wani yanayi na zaquwa da son jin wayar a hannun wa take?.
Idonta ta lumshe sannan ta bude
"Gaggawar ta meye?,kina tunanin wayar huda zata kasance
a hannun wani qato ne?,ko a hannun wata sabanin halastacciyar 'yar uwarta data
shirya sadaukar da tata rayuwar saboda tasu?". Maganar ta kama zuciyar
maamah sosai,ta kuma saukar mata da matsananciyar fargabar data bata tabbacin
KOMAI YA QARE saidai a sake sabon zubi da lale.
"Naga alamar hakan......kin kuma yi qoqarin sadaukar da
rayuwarki ma 'yan uwanki.....ni shaida ce,amma inaso kisan wani abu
guda.......kina wasa da baqin kumurcin maciji ne daya shirya dukka dafinsa da
xummar harbi ga duk wanda yabi ta hanyarsa" Wani dan murmushi ta sakarwa
maamah din tana murza hannuwanta,har yanzu tana jin bata gama dawowa ainihin
sabreen dinta ta asali ba......amma kuma da alama komai yana bisa hanyar
saituwa
"Shi wannan macijin.....idan har yayi sake halittar
data fishi sanin kogon da yake kwana yake kuma tunqaho dashi.......tabbas akwai
yiwuwar a cimmasa har inda yake......a kuma sanyashi ya yanke wannan kan dake
dauke da dafin da kansa da kansa ba tare da yasan hakan ta faru ba....."
"Ke dakata qaramar alhaki!" Maamah ta furta bayan
dukkan haqurinta ya gaza da yadda yarinyar dake qarqashin igiyar auren d'anta
ke iya maida mata magana me zafi haka kanta tsaye......ba shayi ba
fargaba,yarinyar da a haife dukka cikin 'ya'yanta ba sa'anta.
"Shshshsh....." Sabreen ta fada tana dora yatsanta
akan lips tamkar maamah na zaune a gabanta.
"Meye na saurin fusata haka?.....ina cewa abun baiyi
zafi har haka ba?" Ta furta da alamun murmushi cikin muryarta.
"Yaro man kaza......yaro baisan wuta ba sai ya
taka..."
"Your royal highness......har yanzu bansan meye dalilin
wadannan zafafan kiraye kirayen ba da safennan". Iya maqura a rainin
hankali maamah tana jin sabreen tayi mata shi,ta dinga qoqarin tausa kanta da
daidaita kanta kada yarinyar ta tunzurata furta abinda batayi niyya ba.
"Yaro yaro ne.......sabreena......kina da masaniyar
cewa nice na tsugunna na haifi fuad?" Dan murmusawa tayi kadan sannan tace
"Haka naji labari!"
"Amma kina da yaqinin ni na daukoki ko kawoki cikin
gidan na maidaki sunan matarsa?.......idan naso qasa da awa biyu rak! Zaki rasa
wannan damar?" . Qaramar dariya ta saki ma maamah din,ta gyara zamanta
sosai tana kallon kanta a madubi. A yau hirar nishadi take bata a maimakon
razani da take samu a kwanakin baya da suka shude.
"Kina zaton kina da wani makami da zaki iya fiddani
daga gidan yaron naki?........kiyi haquri da abinda zance......amma ko shaidan
a yanzu bai isa ya fiddani daga gidan yaron naki da kike tutiya ba........bana
son danki ko kadan bazan kuma taba sonshi ba......amma yadda kika sakoni cikin
rayuwarku......kika maidani matarsa da qarfin qwanji dana kudi.......to haka
fitata daga gidansa da rayuwarku zata kasande bisa zabin kaina a kuma duk sanda
nayi niyya......so kibi a hankali,bawai sonshi nake ba.....infact ma baiyimin
ba.......amma bazan fita daga rayuwarku ba har sai sanda nayi niyya"
"Qarya kike....baki isa ba!"
"Dama bance na isa ba......amma zan gwada saiki tayani
tabbatarwa...."
"Kina kirawa kanki ruwa!,zaki iya rasa rayuwarki ta
dalilin haka fa!"
"Bari na fara raba naki d'an da rayuwarsa tukunna ki
fara ganin kalar wannan baqin cikin kafin ki aiwatar a kaina......zan shayar
dashi ruwan guba a ruwan shayinsa na yanzu a maimakon tsubbace
tsubbacenki....." Tana kaiwa nan ta
kashe kiran tana ma kashe wayar gaba daya.
Murmushi
ta dinga yiwa kanta a madubi,hirar ta sanya mata nishadi sosai,ko ba komai ta
dasa mata tsoro da fargici tabbas na mintunan data ambata.
Da gasken
haka shine ya faru. Wani irin gumi ya fara tsatstsafowa maamah da wani irin
kalar tashin hankali. Zuwa yanzu bata da tabbas akan yarinyar.......tana ji a
jikinta zata iya aikata komai da tace din. Kasa zama tayi,jikinta yana rawa ta
soma lalubar layin fu'ad tanason gargadarsa akan ya kaucewa komai da zai fito a
yanzu daga hannun yarinyar.
Kira
kusan goma tayi masa a jere saidai ba wanda ya daga,abinda ya sake tsananta
tashin hankalinta kenan,ta dinga duban agogo tana qirga mitunan da yarinyar ta
kwasa mata.
Daidai
lokacin ma shi ya jima a office. Ayyukane da yawa a gabansa da suka hade masa
saboda jiya bai samu yin komai ba a office din yayi baqi da suka tsaidashi har
zuwa dare.
Daga
jiyan zuwa yau komai zaiyi yana yinsa ne cikin wani irin fushi da zafin ran da
hatta saddiq ya fahimci akwai abinda ke damunsa,kuma tabbas ranshi a bace yake.
Ture file
din gabansa yayi yana jan wani mugun tsaki. A duk sanda ya tuna ko abun ya fado
masa a rai sai yaji wani mugun bacin rai yana lullubeshi. Tashi yayi daga kan
ainihin kujerarsa yana takawa a nutse,yasa hannunsa yana sassauta tie din dake
wuyansa cikin wani irin yanayi da yakejin kamar numfashin da yake shaqa yana
masa kadan.
"Why i cares so much?" Ya motsa labbansa yana
furtawa da wani irin zafi. Ba kasafai yake sanya kulawarsa ko damuwarsa akan
komai ba sai abinda yake da muhimmanci a rayuwarsa. Ya tabbatar a karan kansa
she's nothing to him amma me yasa abun yake masa zafi
"Igiyar aurena" Abinda yake da tabbacin shine
dalilin tsaiwar abun a ransa. Sai daya sassauta tie din hade da belt din
suspenders din jikinsa,sannan ya jsa ga dispenser dinsa ya tsiyayi ruwan sanyi
ya rage sanyinsa ta hanyar zuba ruwan zafi kadan akai,sannan ya koma saman
recliner chair din dake gefe wadda aka ajeta don gajeran hutu irin wannan ya
zauna akai.
Kadan ya
samu sassauci sanda yasha ruwan,ya dire cup din idanunsa suna sauka kan wayarsa
dake haske. Da farko ya share yana tsammanin fareeda ce data zama kaman wata
mahaukaciya. Kusan kullum cikin canza layin da zata kirashi dashi gudun kada
yaqi dauka. Layinsa nada wani tsari na hana baqin numbers shigo masa amma nata
kiran ya tsallake wannan shingen bai kuma san dalili ba. Sabanin mamakinsa sai
yaga maamah.
Baya iya
qin daga wayarta komai runtsi,duk da daga ita har anni zai wahala su kirashi a
irin wannan lokacin,sai ya jawo wayar ya daga yana sanyata a kunnensa.
"Kana ina?" Abinda ta fara tambaya kenan tana
qoqarin daidaita muryarta
"Ina office.....wani abu ya faru?" Ya tambayeta a
mamakance
"Daga yau wannan yarinyar......." Sai kuma ta
dakata saboda wani qaqqarfan gargadi da aka watso mata daga can qasan
zuciyarta. Dan jim tayi shima sai yaci gaba da sauraronta baice komai ba
"Shikenan,ka kula dai da kyau" Ta yanke tunaninsu
su duka biyun da fadin haka.
Wani haushi
ya cikata bayan ta aje wayar,ita yarinyar zatayi wa wasa da tunani irin
wannan?,tabbas idan har ta bari yarinyar ta qara kwanaki uku a
gidanma.......bata amsa sunan mariya ba.
*_to masu karatu......me maamah zatayi da zai saka auren
sabreen qarewa cikin kwanaki uku?.....wanne qwarin gwiwa ko tabbaci sabreen ke
dashi wanda yasa taci alwashi ko shaidan bai isa ya kashe mata aure
ba?.....muje zuwa jama'a,WANNAN ALQALAMIN NA HUGUMA ZAZZAFA NE_*
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
51
_Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya
kasance yana nemawa mumunai maza da mata gafara a kowacce juma'a_
_harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga
ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA
DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA MATSANANCIN SONSA S A W_
Sai data fara lalubar number da take da muradin yin magana
da ita sannan zuciyarta taci gaba da kwabar data fara mata.
"Da kinason gayawa fu'ad me?,ya saki yarinyar?,kada ya
amince da ita?,kada yaci abun hannunta?,bayan ke kika aura masa ita?,ke kika
bashi tabbaci akan ingancinta da kuma cancantar aurensa da ita?,bayan ko sati
biyu ba'ayi ba ke dindai ke kika kafa masa sharadin ya bata kulawarsa?,ya
sota?,ya jata a jikinsa?,kinason dabawa kanki wuqa?,kinason sanya wani zargin
saman zargin dake kansa naki?".
Wannan
tunanin ya sakata sakin ajiyar zuciyar tana kiran number da tazo kai,a gefe
guda tana mamakin abinda ya hana hajja nemanta ko zuwa gurinta ko tuntubarta
akan matsalar da ta shaida mata jiya,TABBACIN DUKKAMIN MAGANGANUN LAILA BA
QARYA KO SHAKKA AKAI KENAN. Sai taja qwafa tana gyada kai
"Duk wanda yaci tuwo dani miya yasha" Ta furta a
bayyane,daidai sanda taji an murda qofar dakin an shigo laila ta bayyana.
Da kallo
tabi lailan har zuwa sanda ta qaraso gabanta. Ta durqusa saman gwiwoyinta wani
abu da bata taba yiwa maamah shi ba duk da matsayinta na qawar mahaifiyarta
shekara da shekaru.
"Ina kwana maamah" Ta furta cikin tsantsar ladabi
har bata iya hada idanunta da nata.
Kai ta
daga ta kalleta,dukka wani bayanin plan nasu da lailan tayi mata jiya sai ya
shiga dawo mata kanta tar tamkar a lokacin take labarta mata. Wani bacin rai da
radadin da wanda akaci amana keji ya taso mata,sai ta maida kanta ga waya kawai
tana tura masa saqo. Sai data tabbatar saqon ya shiga sannan ta kalli
laila,wadda kafin lokacin duk wani kalar tashin hankali laila ta shigeshi. Tana
jin kamar ta dora hannunta aka ta yita zunduma ihu,iya yadda maamah taqi amsa
mata gaisuwa ya sanyata cikin firgicin kodai wani laifi tayi mata?. A yanzu a
rayuwa bata jin akwai wani abu da zai daga mata hankali sama da taga fushin
maamah.....ko kuma tayi wani abu da zai saba umarninta.
"Lafiya qalau....." Amsa matan kawai da tayi ya
sanyata sakin wata sassanyar ajiyar zuciya,tana godewa Allah da ba wani abu
tayi daya bata mata rai ba.
"Na shiga dakinki naga basu shareba.....na gyara
miki,saiki duba idan akwai abinda baiyi ba ki gayan a sake gyara mikin". A
nutse take qarewa laila kallo,ji take a ranta inama ace fu'ad ne haka a gabanta
yake wannan bayanin bawai laila ba?,inama ace aikinta ya fada daidai?,i yanzu
da batasan wanne irin farinciki take ciki ba.....lallai da zata kasance wata
halitta mafi farinciki a fadin duniya,ta qarasa wannan tunanin tana runtse
idanunta gami da budesu.
"Basai na duba ba,saidai anjima kafin na kwanta ki
sake"
"To ba matsala.....waida so nake naje wajen
hajja.....jiya muna magana bamu gama ba kika kirani" Kai ta girgiza,duk da
tanason sake samun information,don tayi imanin duk abinda zasu tattauna tamkar
a gabanta za'a yishi,to amma kuma tana buqatar ta kammala da aikin sabreen
tukunna......tabbas komai da zai biyo baya me sauqi ne.
"Ki kirata ki gaya mata nace ba yau ba,zan duba gobe na
gani idan ya dace kije goben" Ta fada kanta tsaye tana ci gaba da riqon
wayarta cikin jiran tsammanin shigowar kiran hanzari nan da kowanne lokaci.
Sanda
laila ke gayawa hajja saqon maamah kai tsaye murmushi ta saki bayan sun gama
wayar tana jinjina kai
"Mariya!.....Mariya,zan miki babban karatun da
gogewarsa sai a cikin kabarinki,a sanda qasusuwan mowacce halitta ta jikinki ta
gauraye da qasa,kin bani qofofi masu yawan gaske ba tare da kin sani ba.....zan
shiga ta kowacce qofa......na fita ta kowacce qofa.....na shiga kuma cikin
rigarki na dimauta duniyarki......sannan na hana muradinki da mafarkinki su
zama gaskiya" Abinda ta fada kenan tana qurawa wayarta idanu dake aje tana
ta burarin nemon taimakon a daga kiran daya shigo.
Tun safen
har azahar zuwa la'asar da tayi dukka cikin dakon shigowar kiransa take. Sai
bayan la'asar din liqis cikin ba zata daya daga cikin masu aikinta suka shaida
mata tana da baqo me suna hanzari.
"Ki rakoshi can cikin setting room,kada a barshi a
waje" Ta fada cikin doki da zumudi,ta miqe tana daukan dankwalinta ta
maida kanta,har ranta tana jin mafita tana tunkaro ta.
Fitowarta
ya sanya hanzari sauke qafafunsa da suke dore daya saman daya. Sanye cikin
baqar shiga,wandon jeans da shirt dukka baqaqe,sai baqar hular Ascot cap daya jawota tadan rufe fuskarsa
kadan.
"Barka da fitowa" Yayi maganar yana miqa mata
nannadaddun takardun dake hannunsa,sai ta fasa zama ta sanya hannu ta karba
sannan ta zauna dasu ta soma budewa tana cewa
"Aiki dakai akwai jan kudi.....amma kuma akwai hanzari
kamar yadda sunanka yake" Ta fadi a nutse tana bin list na sunayen da
kallo da kuma hotunan.
Sai data
gama qare musu kallo tas sannan ta kaudasu daga fuskarta tana kallonsa
"Kin gansu hajjaju?" Ya rigata fada,sai ta gyada
kai ranta yana yin fari.
"Kayi qoqari sosai hanzari.....amma waye kake ganin ya
dace mu dauka?" Ta fadi maganar tana sake kallon list din. Matsowa gaba
yayi kadan ya miqa mata hannunsa yana cewa
"Kawo nan ki gani" Ba musu ta miqa masa,ya aza
takardar saman teburin dake tsakaninsu yana binsu da yatsa daya bayan
daya,kafin daga bisani hannunsa ya tsaya daidai fuskar mashkur,sai ya daga kai
yana kallonta.
Duk da
baiyi magana ba bai kuma ce komai ba amma maamah ta fuskanci abinda yasa gaba
da abinda yake nufi. Sai ta zuba masa idanu tana sauraron qarin bayaninsa.
"Wannan shine mashkur......dan tsuntsu me wayo
kenan..." Yayi maganar yana sake xuba yatsunsa saman fuskar mashkur. Sake
jan hoton gabanta tayi,tunda ya aje din dama kusan fuskarsa tafi jan
hankalinta. Yana da kyau daidai misali,wanda zaiyi daidai da plan dinsu,ta
jinjina kai tana duban hanzari
"Yayi......a tsara komai.....amma karka
manta,secretly" Ta fada tana nuna hanzari da yatsa.
"An gama" Ya furta yana murmushi.
*FAREEDA*
Ci gaba tayi
da duba bayanan,murmushi yana sake wanzuwa saman fuskarta. Murmushin da takejin
yana gauraya da farinciki da take da yaqinin zai zame mata tabbatacce ta hanyar
samarwa da zuciya da ruhi abinda sukesu ta sassauqar hanya.
Sake bude
shafin qarshe na takardun tayi,take hotonta ya mamaye screen din tab din nata
gaba daya,shafin qarshen daya zama shine na qarshe data bude cikin dukka
bayanan data samu. Ta barshi a qarshe ne saboda dukka sauran shafukan na dauke
da full details da bayanan da suka faranta mata rai sosai,sukayi kuma daidai da
muradinta.
Hoton
sabreen din daya cika allon tab din ta zubawa idanu. Wani abu yana tsarga mata
tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafukan qafafunta. Wani mahaukacin wutar kishi
ke ruruwa cikin zuciyarta. Ta kusa kwashe sakanni talatin a haka,kafin ta dafe
dukka hannuwanta saman kujerar da take kai tayi zullo zuwa gaba har a sannan ta
gaza dauke idanun nata. Labbanta suka motsa kadan rana son kiran ainihin sunan
nata,saidai ya tsaya ne can qasan maqoshinta ba tare da sautin harafin ya fita
ba. Adan hanzarce ta maida hannunta saman tab din tana komawa shafin da yake da
alaqa da komai daya shafi sabreen din,ta sake karantawa sosai kamar me shirin
haddace komai daya shafeta
"How comes?" Ta tambayi kanta tana yamutse fuska
lokacin da takai qarshen bayanan
"Karuwa?......How did he get married to her?" Ta
sake tambayar kanta da kanta
"She's karuwa officially fa?" Ta kuma nanatawa
cikin zallar mamaki. Ba wata amsa data samu daga kowanne sashe na
kwanyarta,saita dage kafadunta duka biyun sama tana sakin murmushi,lallai komai
zai tafi da alama daidai
"Fu'ad isn't your type madam.....its over between you
too" Tayi maganar tana nuna hoton sabreen da dan yatsa,saidai ba abinda ya
canza zuciyarta daga mahaukacin kishinta da takeji.
Ta kowacce
fuska,ta kowanne bangare sabreen din ta yaga mata indai ana batun kyau ne da
sassanyan zubi da ta tabbatar yana daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin
fu'ad din,banda hakan.....yadda ta samu full details dinsa zai wahala ya nuna
interest akan karuwa har ya aureta.
"It's my turn......my time to shine has come" Ta
fada da qwarin gwiwa,ta miqe tana nufar closet dinta ta sauke luxury luggage
dinta guda daya ta fara selecting kaya tana shiryawa a ciki ba tare da jiran
kowa cikin masu aikinta ba.
Cikin
qasa da mituna sha biyar ta gama packing komai da komai nata,sannan ta dawo ta
dauki wayarta ta kira number abbanta.
"Hello dad....." Ta fada a shagwabe. Ita din 'yar
gaban goshinsa ce da dukka yaransa babu wanda ya kamo matsayinta a zuciyarsa. A
kullum tana maida kanta tamkar 'yar shekara goma a gabansa,haka shima yake biye
mata,saidai hatsabibancinta da girman izzarta ta dara tashi shi da yake da
muqamin ambassador din gaba daya.
"Dad.....ayimin booking flight please......gobe nakeso
if possible,it's an urgent dad..." Ta furta a shagwabe kamar yarinyar dake
tsakanin shekara shida zuwa bakwai
"Thank you dad" Ta fada da murnarta jin ya bata
tabbacin zaisa a mata booking private jet.
Da murmushi
sosai a fuskarta ta soma turawa zababbun qawayenta da za'ayi tafiyar tare dasu
request. Cikin qasa da minti goma ta gama komai,sai ta sauke wayar ta matsa
gaban dan wani madaidaicin table dake dauke da tukunyar shi sha ta fara qoqarin
hadata. Tanajin a yanayin da take ciki na farinciki ita daya zata tayata
sarrafa murnarta,
Kyakkyawar zuqa tayi mata tana bulbular da iskar daga dukka qofofin
hanci da bakinta,ta lumshe idonta fuskar sabreen na mata shawagi tsakanin
tunaninta da qwayar idanunta
"Blast it!" Ta fada da qunan zuciya tana kaiwa
iska naushi,tana jin kaman tayi using acid ta dauke wannan kyan da ya hanawa
zuciyarta sukuni.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
52
_Daga dariq dan shihab RA,manzon Allah S A W yace
"juma'a haqqi ce kuma wajibi akan kowanne musulmi yayita cikin jam'i,sai
akan mutum hudu kawai(ta sauka),MACE,BAWA,YARO DA MARA LAFIYA"_
_Abu dawud ne ya rawaito_
★Shuru ne
ya biyo baya duk da wayar tana riqe a kunnenta. Dukka bayanan zuwaira ta gama
saurara wadanda suka gama bata tabbacin lallai da gaske yaran sunyi nisan da ba
wanda zaice ga inda suke......uwa uba kuma yarinyar tana ci gaba da harkokin
gabanta hankali kwance kamar ba wani qalubale a gabanta.
"Ni kaina yanzu komai na taba ko nace zanyi mata
dakatar dani takeyi,waccar munafukar me aikin da ameena ta kawo mata yanzu da
ita takeyi,munafuka me shegen iyayi da bariki,idan kikaga yadda takeyi mata
zaki rantse da Allah sabreena ce babba ba ita ba". Wani tattauran yawu
maamah ta hadiye,tsananin bacin rai yana sake cikata
"Ki saurara,ki sanya dukka kunnuwanki da hankalinki
dama idanunki kan gidan......kada kice komai,kuma kada kiyi komai,akwai
gagarumin al'amari da zai faru cikin gidan.....abu daya nakeso kiyimin,ki
kasance me bibiyar diddiqi bayan faruwar lamarin" Abinda maamah ta gaya
mata kenam ta kuma yanke kiran. Bin wayar tayi da kallo......har a sannan
tanaji a ranta muddin tabar sabreen din taci galabar ci gaba da rayuwa tana
shan inuwa da arziqin danta lalallai ba shakka bata cika mariya. Shekaru da
gwagwarmar rayuwa da gogayya da tayi da kalar mata daban daban bai amfaneta da
komai ba.....shekarun data kwashe ma a duniya basuyi mata amfanin komai ba,dole
ta fiddota daga gidan......wannan shine zai bata damar yin walagigi da
rayuwarta da kuma d'aid'aita rayuwarta kamar yadda ta d'ai d'aita mata burinta.
Qarfe daya
da rabi na rana driver din hajja ya faka motarsu qarqashin muhallin da aka
tanada saboda ajiyar motoci. Koda ya tsaida motar ya kuma kasheta amma hakan
bai sanya hajja fitowa daga cikin motar ba. Da idanu take bin kowanne sashe na
ginin gidan da kallo tamkar yanzu ta fara ganinsa. Saidai sam a badini ba
wannan bane damuwarta ba......ba kuma shi take kallo ba.
Tana
nazarin yadda ALKHAIRI ya juye izuwa SHARRI,ta gama tura mota tsaf tana shirin
buleta da balbalin hayaqi maras dadin shaqa?,hayaqi mafi cutarwa cikin qofofin
hanci da kwanyarta?..
Wata
gauruwar ajiyar zuciya ta sauke,sannan ta balle murfin motar yau da kanta tana
fitowa,sabanin a baya da sai driver ya fito da kansa ya bude mata sannan ta
fito. Gyara yafen mayafinta tayi,kanta tsaye kuma take takawa zuwa hanyar da
zata sadar da ita da ainihin cikin gidan.
Duk taku
daya idan tayi la'anar maamah take cikin ranta,tana ji a jiki ta jefeta a wata
kalar musiba da batasan ranar fitarsu ba. Zuciyarta tana mata wani qunci da ita
kanta batasan iya adadinsa ba......amma wani sashen na zuciyartata yana sake
jaddada mata
"Fushi ba naki bane.....nasara bata masu gaggawa ko
saurin fushi bace!" Wannan shine abinda yaketa mata burki take hadiyewa da
qyar. A jiya da qyar bacci barawo ya dauketa,cikin fargaba da tsoron fitar
dukkanin sirrinsu daga bakin laila..... Yanayin aikin bokansu dabanne,a aikin
da aka tanadarwa fu'ad harda na rariyar baki,wanda baida wani sirri na kansa
sai abinda maamah ta buqaci ya sirranta,muddin maganin yayi tasiri a jikin
laila kamar yadda aka tsara.....hakan yana nufin duk wani sirri nata yanzu a
tafin hannun mariya yake?.
Wannan
tunanin ya hana mata cikakken bacci da safe,ta dinga qididdiga da lissafin
wucewar sa'o'i don ta samu ta fito zuwa gidan mariyan. Tanaso taga yanayin
fuskarta,abinda zai nuna shine zai zame mata amsa na abinda take zato da zargi.
Duk da cewa na tsuburi ya mata alqawarin ba abinda laila zata iya gayawa
maamah.....to amma tasan aikin bokansu daban yake dana kowanne boka.
Sau daya
tak! Yake maka aiki.....idan har yayi maka na biyu to tabbas ka taki sa'a,uwa
uba yawan yawan ayyukansa basu da makari.....shi yasa ta jima tana murza zaren
rayuwarta ta kowanne fanni.....a yanzu kuma bata fatan wata matsala tazo mata
ta wannan fuskar.
Idanunta
akan parlor din maamah.....falon da kullum maamah din ke kusheshi da ganin
tsadar kayan adon ciki bai kama qafar na gidan alhaji hamza ba.....Parlor din
da ita kuma hajja harira kullum kwanan duniya ta daga kai ta kalleshi sai
kishin zamowarsa mallakar mariya ya baibaye zuciyarta da wata irin hassada me
tsananin qarfi. Iya bariki da qwarewa wajen boyewa koma waye yanayin da kake
ciki ya sanya maamah din bata taba fahimtar komai ba.
Takun da
taji ana fitowa daga kitchen ya sanyata waiwayawa cikin tsammanin daya daga
cikin masu aikin gidanne wadanda su zasu yiwa maamah maganar ta iso tana son
ganawa da ita. Amma kuma sabanin hakan,laila ta gani a gaba,dauke da kwando
cike da warmers kala kala,saman rigar jikinta kuma apron ce a daure.
"Laila?!" Ta kira sunanta cikin qaraji da wani
kalar madaukakin mamaki tana takawa da hanzari don isa gabanta.
"Sannu da zuwa hajja" Lailan ta furta fuskarta
shimfide da murmushi dake nuna ba wani abu da takejin ba daidai bane
"Bari na ajewa maamah abincinta nazo mu gaisa" Ta
furta tana wucewa dining din. A nutse ta shirya komai.....kamar ba lailanta
diyar gata ba,lailan da idan taci abinci ko kwanon da taci abincin batasan ta
janyeshi ba......lailan da saidai tana mimmiqe saman sofa ko gado ta zabi
abinda take da sha'awar ci.....wannan lailan itace yau a kitchen da rigar 'yan
aiki?.
Sanda
ta kammala shiryawar saita dago tana murmushi,suka hada idanu da hajjan tace
"Ina wuni?,na kira miki maamah din?,Allah yasa bata
kwanta bacci ba don tace ko waye yazo kada a tasheta"
"Gani nan laila baccin baizo ba....kun gama ne?"
Maamah dake saukowa daga stairs din ta fada.
Tare suka
daga kai suna dubanta,sanye take da applique lace purple color da ya dan ciza
kadan,dinkin doguwar riga da aka qawatata da wani irin dinki me daukan hankali.
Shigar tabi jikinta....wadda ke bayyanar da zallar izzarta da isarta.
"Kun gama laila?" Kai ta shiga gyadawa kaman mara
hankali da sauri
"Mun gama maamah ko akwai wani abun?". Ta fada a
rusune. Murmushi maamah ta saki tana dafa kafadarta
"Amma dai yau kin koyi yadda ake dambun gargajiya da
kuma liver salad ko?". Murmushi ta saki kaman wata shashasha
"Sosai ma maamah.....ai kin taimaken na gode
sosai". Ta fada tana rusunawa a wajen.
"Shikenan,yanzun zaki iya yin wanka,idan kin gama kiyi
zamanki a daki kada ka fito yanzu"
"To maamah" Ta amsa mata a ladabce tana juyawa ba
tare data dubi ko bangaren da hajja take tsaye ba. Idanu suka hada da
hajjan,wata tayi wata irin mutuwar tsaye. Gefe guda kuma taci gaba daya tamkar
qwaqwalwarta ta daina aiki ne gaba daya. Wani qaramin shu'umin murmushi maamah
ta saki,ta juya da hanzari bangare da laila ke tafiya
"Au.....nikam nace kin gaida mamanki kuwa?" Kai ta
girgiza tana fadin
"Bakice ba ai". Fuska kadan maamah ta bata
"Haba ke kuwa auta.....yarinyar kirki,zo ku gaisa
mana....wataqila sanda zata tafi ai baki fito ba". Dawowa tayi ta rusuna
har qasa tana gaida hajjan abinda bai taba faruwa ba kenan tsahon rayuwarta. Da
fari idanuwa kawai hajjan ta saki tana kallon lailan,har sai da taji lailan ta
maimaita gaisuwar sannan ta duqa tana dagota daga tsugunnon da tayi
"Ki dauko mayafinki kizo mu tafi gida" Ta fada
muryarta na rawa amma tana qoqarin danne rauninta don bata fatan maamah din ta
gani.
Kai ta
girgiza tana duban maamah wadda tayi kaman batasan abinda ke faruwa ba,tana
laluben wajen zama hankalinta akan fuskar wayarta
"Nafison nan hajja.....ni ki barni a nan" Ta fada
tana zamewa daga jikin maamah din ta wuce abinta hankalinta kwance zuwa hanyar
dakin da aka bata.
"Bismillah.......zauna mana surukata" Maamah ta
fada fuskarta a sake. Kalmar suruka din da maamah ta fadi shine ya sanya hajja
jin wani abu tamkar wutar lantarki ta fusgeta. Cikin qasa da minti guda gumi ya
fara tsatsatsafo mata ta kowacce kafar gashi ta jikinta.
"Atika!" Maamah ta qwalawa me aikinta kira,wanda
cikin qasa da minti daya ta bayyana,sanin da sukayi mata batason ta kiraka ka
samu jinkirin zuwa.
"Dauki remote ki kunnawa surukata A.c,karki saka da
yawa kada kuma ta saukar mata da zazzabi"
"To hajiya" Atika ta fada da rawar jiki tana me
aiwatar da abinda maamah ta umarceta.
Zagayawa kawai kalmar takeyi cikin kunnuwan hajja.....indai har kalmar
surukuta zata fita daga bakin maamah a wannan yanayin,lallai ne ba abinda bata
sani ba kenan.
"Ki maida hankalinki jikinki hajja......har mariya ce
zata firgitaki har haka?". Wani sashe na zuciyarta ya bata qwarin gwiwa
har ta samu qarfin halin tattara 'yar nutsuwar jikinta tana neman wajen zama
gami da fuskantar maamah.
"Mariya......zuwa nayi na duba lafiyar laila.....ya
kuka tashi?". Murmushin nan dai ta kuma saki,sannan ta ajiye wayarta a
gefe tana bada hankalinta gaba daya a kan hajja
"Laila tana lafiya......kuma zata ci gaba da kasancewa
lafiya sumul a hannuna......kinsan na iya riqon 'ya'yan jama'a" Ta fada
hankalinta kwance.
Murmushin
qarfin hali hajja ta saki,sannan ta jinjina kai
"Ai na sani mariya......mun tashi lafiya?"
"Lafiyarmu sumul qalau hajja....." Daga nan ta
fada nazarin da wacce kalma zata tunkareta. Idanunta ta daga tana duban maamah.
"Muna magana jiya sai kuma Kira ya yanke....."
"Eh wannan case din na gama solving nasa,saura fitar
result"
"Zancanmu fa kan laila da fu'ad?" Hajja ta jefa
mata tambayar kai tsaye,duk kuwa da cewa ita kanta me bawa wani amsa
ce.....saidai tanaso takai mariya inda take buqatar aje.
Buda
baki maamah tayi da nufin cewa wani abu......amma sallamar jarma daya daga
cikin masu gadin gidan yayi sallama daga can bakin qofar falon.
"Malam jarma ya akayi?" Maamah ta buqata sani
sanda yake duqewa a wajen
"Baqi gareki hajiya......ban sani ba zasu iya qarasowa
ko a maidasu?". Fuskarta da dan mamaki take dubansa
"Baqi kuma?,daga ina?"
"Diyar ambassador Khaled mustapha ce,haka tace a gaya
miki". Wani madaukakin mamaki ya cika maamah din,ba ita kadai ba,hatta da
hajja sunan yaja hankalinta qwarai da gaske.
Miqewa
maamah din tayi tsaye tana dubansa
"Maza ayi mata izini ta shigo......na tabbatar koma
meye ya kawota nan,silar haihuwar ALKHAIRI ne fu'ad" Ta furta tana jin
wani irin alfahari da haihuwarsa fiye da kowanne lokaci. Uwa uba tana yine da
biyu,don ta tabbatar gaba daya hankalin hajja yana kan abinda yake faruwa.
Sanye
take da wani matsiyacin yadi da aka narkar da kudade masu nauyi kafin siyansa
da yagalgalashi,aka kuma yi masa dinkin fitted gown data zauna a jikin
laila......kai kace a jikinta aka dinkashi.
Yadda
dinkin ya zauna mata a jikinta.....hatta da dagawar numfashi daga cikinta da
qirjinta kana ganin gudanarsa. Ba mayafi a jikinta,sai dankwalin material din
da aka mata wani dauri dashi saika rantse hula ce ta kafata. Wasu nau'ikan dan
kunne manya ne a kunnenta,wanda suke tafe da.manyan banguls da suka dace sak
kalar material din jikinta kamar a company daya aka qerasu. Highhill ta sanya
masu tsananin tsini sarqafe da igiyoyi,kaman yadda qwayar idanunta ke saye da
tafkeken glass daya kusa cinye rabin fuskarta. Labbanta kwance reras da lip
gloss,iya wannan kadai zai gaya maka tafiya akayi irin ta masu abun,ba wahalar
hanya tunda sararin samaniya ne yayi aikin.
Yadda take
taku daya bayan daya tana takowa ciki,idanunta kan kowanne sashe na parlor din
tana yaba alatun da aka zuba.....haka bakinta ke bada satin qas qas na chewing
gum din da take taunawa cikin bakinta.
Tana daga
tsakiya,gefe da gefanta kuma fitattu kuma manyan qawayenta ne,lubna da
jalilah,daga bayanta kuma masu aikinta ne data taho dasu suma guda biyun.
Fuskar
fareeda ba boyayyar fuska bace musamman idan kaidin ma'abocin kallon news ko
dabdala a social media ne. Kusan duk wani motsi na mahaifinta ko na siyasarsa
zaka ganta a ciki zaka kuma tsinceta a ciki dumu dumu.
Lafiyayyen murmushi ya kubcewa maamah,ta taka a hankali tana marabtarsu.
Doso sun da maamah tayi shi ya sanya laila cire glass din fuskarta dukka a
qoqarin ta na nunawa girmamawa ga maamah din.
Cikin qasa
da minti biyar suka yiwa kansu mazauni a parlor din,sannan kuma gabansu ya cika
da nau'in kayan ciye ciye daban daban na alfarma.
"Nasan zakiyi mamakin zuwana wajenki maamah?" Ta
fada tana qoqarin karyar da muryarta.
Kai maamah
ta jinjina,tako ta ina tanajin wani girma yana hawa kanta
53
_Daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace:mazan
Allah S A W ya ambaci ranar juma'a,yana cewa "A CIKINTA KAWAI WANI
LOKACI,BA WANI BAWA MUSULMI DA ZAI RUSKETA YANA ME TSAIWA YANA SALLAH YANA
ROQON ALLAH WANI ABU FACE SAI ALLAH YA BASHI ABINDA YA ROQA DIN". sai
manzon Allah yayi nuni da hannunsa na qanqantar lokacin (ma'ana baida
tsaho,Allah yasa muna cikin wadanda zamu yita ruskarshi)_
"Eh
to.....zai iya kasancewa abun mamakin ta wani fuskar,ta wata fuskar kuma ba
abun mamaki bane,musamman idan kikayi duba da irin kalar zuri'ar da Allah ya
bani" Tayi maganar da nufin jifa ga ma'anoni guda biyu tana gyara zamanta.
Kai laila
ta jinjina tana tsare maamah da ido,tun kafin tazo ta hadu da ita tasan wacece
ita,don haka ko sau daya bataji d'ar ba na samun nasara ta hannunta ba.
"Ko zamu iya kebewa muyi magana?" Laila ta fada
tana duban maamah.
"Me zai hana?,bismillah" Maamah ta fada tana
miqewa,sannan ta fara takawa,sai kuma ta tsaya tana duban hajja,wadda keta
kokawa da zuciyarta akan tayi abinda ya kamata
"Yi haquri hajja.....zamu gana,yanzu zamu fito" Ta
fadi mata tana sakin wani murmushi dake dauke da ma'anoni da dama. Sabon mariya
ne......jifan maqiyi da murmushi ko kuma abokin adawa,wannan shine kusan makami
na farko da take fara yaqar zuciyar abokin burminta,yayi tsammanin ita din
wawiya ce.....itadin ba wani abu da zata iya,saidai kuma daga qarshe reshe ne
yake juyewa da mujiya,sai taje maka da wani irin kalar farmakin da zaya kaika
qasa koda baka shirya hakan ba. Bata da cikin mutanen da mariyan zata iya
farmaka ta haka har kuma ta samu galaba,saboda sanayya ce ta kar da kar,ba wani
abu ko hali nata da zata layance mata dashi.
Dan
madaidaicin parlor din shima sai daya ja hankalin laila,duk da ba wani baqon
abu a ciki wanda bata sani ba.....amma yanayin tsarin da yadda aka zuba komai
luxury ya bala'in shiga ranta. Wannan karon maamah ta fahimci haka,saita jefeta
da murmushi sanda take zama tace
"Hala kema ya burgeki?,aikin muhammaduna
kenan.....komai nasa me tsari ne". Lumshe idanu laila tayi tana sake ji
yana kuma shiga ranta,jini da jijiya harma da b'argonta qaunarsa tana sake
ratsata
"Inama zaki lamuncemin na zama matarsa.......bisa
farashin dala dubu d'ari" Ta furta qasa qasa tana kallon maamah.
Zubawa
laila idanu tayi sosai tana jin sautin muryarta yana zagaya dakin,duk kuwa da
cewa ta kammala taqaitaccen bayanin nata dake qunshe da saqo me tsananin
nauyi.....ci gaba tayi da kallon laila tana son tantance Gaskiyar abinda ta
fada ko kuma akasin hakan.....magana ake ta kusan million dari da hamsin ko da
sittin fa......kawai don tanason fu'ad?,kawai don tanason ta aureshi?.
Wane sashe
na zuciyarta da kwanyarta da yake da kaso mafi girma wajen tsara mata komai ya
harba,wannan ya sanya duk wani abu data shirya ambatawa ya wargaje,take ta
sauya yanayin fuskarta daga me yalwar fara'a zuwa tsukakkiya
"Wane irin magana ne wannan?,ance miki neman kai nakeyi
da yaro na?" Tayi maganar a dake cikin qoqarin nuna bacin rai,da kuma
tankwabar da tayin gwaggwabar garabasa da ribar da zata iya samu.
Ga
mamakinta murmushi laila ta saki,hankalinta kuma a kwance ta koma tayi relaxing
jikin kujerar tana duban maamah,sannan a nutse ta daga qafarta ta dora daya
saman daya tana ci gaba da dubanta.
"Karki wahalar da kanki.....kada kuma ki wahalar da
shari'a,kada kiyi kaman bakison kudi hajjiya......idan sun miki kadan kawai
kice na qara miki,sai na qara mikin a wuce gurin.....fu'ad kawai nakeso,kudi ba
matsalata bace sam sam". Sake tsare laila tayi da ido a karo na biyu tana
karantar gaskiyar abinda take fada har zuciyarta. Qwaqwalwarta ta lula zuwa
duniyar tunani duk da bata barta tayi nisan zango ba.
Akan me
zata bari tayi asarar kudin da take gani a gabanta yanxu haka?,bayan tana da
damar mallakarsu?. Tabbas akawai manufar turo laila da ubangiji yayi cikisu a
daidai wannan lokacin da take neman dukka hanyar da zata cisge sabreen daga
gidan fu'ad.....babu ko shakka laila itace macen daya dace ta maye mata
gurbinta.
Duka ma
a ture ta batun kudaden da zata mallaka......babban abun alfahari ne a yadda
ubangiji ya yiwa yaronta kudi yabi sahun manyan masu kudin africa ma gaba
daya......ace kuma yau shine yake auren diyar mutum kaman ambassador khaleed
mustapha,wanda a muqamai dai na duniya tana jin ba wanda bai riqe ba,saidai
kuma a lahira idan ana riqewa.
Lallai ne
ita mariya sunanta yana dab da sake fantsama cikin bakunan al'umma.....qawaye
dangi da 'yan uwa,tana dab da sake taka wani matsayi na zama cikin manyan matan
da fu'ad har yanzu yaqi sakar mata jelar macijin tayi wasa da ita da
kyau,....wannan shine mafarin da tauraruwarta ta gaza yin haske kaman yadda
takeso. Sunanta takeso ya zama cikin jerin sahun sunayen mata masu aji da
sukafi kowanne mata a africa da duniya ma wasa da kudi.....cikin jerin sunayen
iyayen attajiran 'ya'ya da kowanne taro ake kwadayi da rububin
gayyatarsu,saboda sun zama bangon sugar ko na zuma,masu yayyafin kudi in
dollars not in naira......don tana jin zuwa yanzu a arxiqinsa ita kanta tafi
qarfin yin kyauta da naira.
"Ki rubuta dukka adadin da kikeso" Ta tsinci
muryar laila tana fadi,saita sauke idanunta akan abun rubutun da laila ta aje a
tsakaninsu tana rutsata da idanu. Maida dubanta tayi kan fuskar laila,duk da
alamu sun nuna tasan wani abu a kanta......amma ba zatayi saurin bada kai bori
yahau ba haka da wuri gudun raini.
"Ba ta wannan nake ba.....kawai ina duba cewa
mahaifinki babban mutum ne da yakai kowacce uwa taso hada jini dashi.....ko don
saboda shi zan shige miki gaba har ki samu fu'ad.......amma samun muhammad ba
abu bane me sauqi......da gareshi akwai wasu tsauraran matakai,kamar yadda nima
daga wajena akwai wani mixani da nakeso duk matar da zai aura lallai saita
cikemin su cif da cif......yanzu haka rashin cike wancan mizanin daga matarsa
ta yanzu ya sanya take fuskantar barazanar gutsirewar aurenta daga yanxu zuwa
kowanne lokaci"
"Daga yanzu zuwa kowanne lokaci?,ashe ma baki da
guarantee......ashe baki da tabbas?" Laila ta fada da narkakkun idanunta
dake nuna yadda suke da kyakkyawar alaqa da kayan maye
"Ai kawai kiban wannan kwangilar.......nan da jibi ko
gata.....kwanaki uku idan sunyi yawa zata zama tarihi a rayuwarsa......shiga
cikin mutane xai gagareta......bama ita kadsi ba,haka dukka wani dake da nasaba
ko alaqa da ita" Tayi maganar da cikakken qwarin gwiwar daya sanya maamah
tsayawa ta xubawa laila ido.
Daga jin
alwashin dake fita daga bakin laila kadai ya isa ya gaya maka ita dinma wata
akwai wani magana ta daban a kanta......itadin ma a shirye take
"Dole kema nayi takatsantsan dake.....aminta dake haka
lokaci guda babban kuskure ne......amma dole na fara miki da karin maganar nan
da hausawa ke fadin DUK WANDA YA RIGAKA KWANA DOLE YA RIGAKA TASHI.
Murmushi
ta sake mata tana dubanta,ta sake yalwata fara'ar dake saman fuskarta tana
kallonta.
"Wannan ba wani abu bane da zai zama matsala......na
baki wuqa da nama.....idan akwai wani information da kike buqata dukka a shirye
nake na baki shi". Kai laila ta jinjina tana sakin murmushi
" Zan iya gaya miki har fiye da abinda kika
sani......ina da labarin abinda na tabbatar ke baki sanshi ba". Ta qarashe
maganar tana bude handbag dinta qirar kamfanin Hermes ta zaro cheque.
Rubutu
tayi samansa hankali kwance tayi kuma sign dinta,sannan ta miqawa maamah. Kudi
ne a rubuce kamar yadda ta furta zata bayar da farko,maamah din bata gama
wannan tunanin ba muryarta ta sake fargar da ita
"Wannan din somin tabi ne.....muddin kikayi nasarar
zama surukata,zaki mallaki wata power ta fada a ji a manyan gurare da dama ta
hannun mahaifina".
Komai
ganinsa maaamah ta dinga yi kaman cikin mafarki,duk da ta tattara dukka
mamakinta ta hadiye don ba buqatar laila ta karanci komai.
"Zamu iya ganawa dashi a yau?" Laila ta tambaya
maamah tana jin kwadayin ganinsa a daren yau.
"Baki da matsala da wannan"
"Zamu wuce masauki yanzu haka don mu huta sosai,bayan
magrib sai na dawo,hakan yayi?"
"Yayi" Maamah ta fada tana daga zaune har
yanzu,don mamakin da taketa boyewa yaqi barin zuciyarta. A gabanta Laila ta
miqe tana fita daga parlor din,maamah kuma ta rakata da idanu.
Tana fita
daman jira takeyi,ta miqa hannu ta jawo cheque din tana dubawa
"Da gaske adadin ta rubuta,akwai genuine din signature
nata da komai?" Sake jujjuyashi tayi a hannunta,sai kuma wani murmushi ya
qwace mata.
"Lallai ni mariye me sa'a ce,ko rashin samun fu'ad a
hannu akan lokaci na yarda lokaci kawai ne baiyi ba" Ta gayawa kanta da
kanta tana gyara zamanta sosai tana jin kamar kanta zai fashe saboda wata izza
da take saukar mata har tsakiyar ruhinta. Ta zubawa guri daya idanu murmushi na
fita daga fuskarta lokaci bayan lokaci. Yau da wacce irin sa'a ta tashi?,wacce
addu'a tayi yau?,babu....shine amsar data bawa kanta da kanta,don ko basmala
cikakkiya bata jin tayi tun daga safe kawo yanzu.
A dan fusace
ta juyo jin an murda qofar ana shigowa,saboda ita din bata sakarwa kowa da kowa
shigo mata guri kai tsaye ba....ko waye kai saika nema izini ta kuma baka.
Idanu
suka zubawa juna ita da hajja,saita janye cheque dinta tana lanqwasheshi ta
daga pillow din kujerar gefanta ta saka a qasansa. Idanun hajja yana kai,abun
kuma ya sake haifar mata da wani matsanancin bacin rai. Iya wannan abun da
mariya takeyi kawai ya isa gaya mata komai daya faru ya faru ne bisa son ranta
da kuma zabinta. Tunda suke da mariyan ba rufa rufa irin wannan
tsakaninsu......tayi baqi ta kasa ganawa dasu a gabanta?,taga takarda duk da batasan
ta mece ba amma mariyan ta jata ta boye?.
"Kinga surukarki ko?,diyar ambassador khaleed
mustapha" . Maamah ta sake maimaita abinda tasan already hajjan ta jishi.
"Musaddiq ne kenan shima????". Kai da maamah kr
girgizawa ya hana hajja qarasawa.
" Fu'ad dai,d'ana fu'ad ". Da wani mahaukacin
mamaki hajja ke bin maamah dake doka murmushi da kallo
"Kinga Kalar surukan da ake fatan samu......wadanda
za'a ciccibi juna....ba wadanda suke hangen turmusheka kai da mafarkinka
ba.....maciya amana masu fatan kayi gyangadi su kafta maka sara.......zan shiga
ciki in huta,ina da baqi anjima......idan kin gama ki rufe gurin.....karki damu
kanki da lamarin laila......dama haka rayuwa take.....ka riqe dan wasu kaima a
riqe naka,duniyar juyawa take haka da sauri........su madeena sun isheki
zama.....ni kuma laila kadai ta isheni" Tana qarasa maganarta ta fara
takawa zata fice
54
_Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace:
"anayin wanka akan abubuwa guda biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan
anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa gawa wanka)_
"Mariya!" Hajja da zuwa lokacin ta kasa riqe kanta
ta kirata a hautsine
"Koda wasa......koda tsautsayi kada kiyi tunanin cutar
da laila......karki manta dukka sirrikanki a nan suke" Tayi maganar tana
nuna mata tafin hannunta.
Murmushi
ta kuma sakar mata sannan ta juyo sosai tana amsata.
"Wadannan sirrikan da kike da ganin sun isa abun
tunqaho.....nabar miki su halak malak kiyi yadda kikeso dasu.....laila kuwa a
yanzu mallakina ce,baki da hurumi a kanta,idan kuma kina ganin zaki iya to
bismilla,ga fili ga me doki,kinsan dakin dana sanya aka sauketa ai" Ta
furta tana nuna mata hanya,sannan ta juya hankalinta kwance tana fita daga
dakin.
★k'arfe biyar
da rabi yammacin ranar jerin luxury cars dinsa sukayi matsugunni a babban
sashen ajiyar motoci na mansion House din nasa. Wani baqon abu daya kwana biyu
baiyi ba,wato dawowa gida a lokaci irin wannan. Dawowarsa da wuri shine qarfe
takwas zuwa tara na dare,wanda ita kanta matar gidan batasan lokutan dawowarsa
ba.
Kaman ko
yaushe daga farfajiyar gidan ya tsaida kowa ya kuma sallami kowa,wanda kusan
quarters ne guda daga can wani sashe daban na gidan da yawancinsu suke da nasu
apartment din,ba lallai ma ka fahimci da wasu dake rayuwa cikin gidan bayan
ainihin masu gidan saboda nisan tazarar dake a tsakaninsu.
A hankali
yake takawa zuwa ciki suna magana da farouq qasa qasa.
"Na fita daga company,kuma ina tunanin sai gobe zan sak
shiga......wani irin headache ne yake matsamin tun jiya......but daga dazun
zuwa yanzu kaman ya qaru"
"Dude.....kana over work fa?,Allow your self
downtime......kana da aure amma a suna kawai......kasan benefit na aure kuwa da
ba zasu qirgu ba?....Emotional support and mental health duka zaka samesu if ka
bawa matarka damar shiga rayuwarka"....
" Hey.....zaka fara ko?,waye ya gaya maka kowacce mace
ake bawa dama ta shiga rayuwarka?,wasu matan poison ne fiye da yadda kake
kimantawa,they are wicked" Ya fadi yana hadiye wani yawu lokacin da
madaurin tunaninsa ya warware yana koma masa can shekarun baya.....sanda maamah
ta zama silar rasa lafiyar mahaifinsu duk da kasancewarsa mutum ke kazar
kazar,ta kuma zama silar barinsa sararin da suke kai yanxu suke rayuwa akai
wato DUNIYA. Daidai sanda ta sauka daga saman high chair din data zauna a akai
cikin kitchen din suna taba hira da ma'u,wadda take hada qullin wainar shinkafa
zata soya musu
"Bari na dauko na dawo" Tace da ma'u din tana
gyara yafen qaramin Chantilly veil din data lullube sassalkan gashinta. Furucin
nasa ya sanyata tsaiwa cak sanda muryarsa ta kaiwa kunnuwanta saqon da yake
isarwa farouq,sai taja da baya tayi tsaye jikin qofar yana jiran wucewarsa don
ta wuce itama zuwa dakin.
"Let's try not to judge people and instead understand
their perspectives".
"Am not judging fa......dude ba zaka gane bane,na iso
gida.....i need to rest.....call you later"
"Okay byee" Farouq ya fada yana sauke wayar iska ya furzar daga bakinsa yana duban file
din dake gabansa cikin katafaren kamfanin sarrafa kayan abincinsu dake sharada
industrial area. Yanaji a ransa zai sake rage kwanakin tafiyar nan tasu ko
wataqila hakan zai kawo kasuncin da yake fata tsakaninsa da ita. Yasha
attempting saka amna cikin abun,yasan zatayi aiki sosai.....saidai kuma amna
din quruciya tayi mata yawa,baisan ya zata dauki abun ba,uwa uba yana buqatar
yayi komai cikin sirri.
Shurun da
taji cikin parlor din ya sanyata tunanin ya wuce,ta sauke siririyar ajiyar
zuciya,kunnuwanta na maimaita mata da meye da meye ya fada akan mata?. Siririn
tsaki ta saki zuciyarta na siffantashi da jerantashi cikin sahun mazan da sam
bausan mutuncin diya mace ba....suke mata kallon kuma wata halitta da bata da
wata daraja kwata kwata.
Siririn
tsakin daya sanyashi daga kansa a hankali daga rufe bottle na ruwan da ya tsaya
ya bude yasha saboda yadda maqoshinsa ya bushe,yana ji kamar bazai iya qarasawa
saman ba.
Guri daya
idanunsu suka hadu,ya kafeta da qwayar idanunsa da sukayi wani laushi tubus
saboda yadda ciwon kan ke sara masa lungu da saqo na cikin kansa. A hankali ta
zare nata idanun daga kanshi,sannan ta koma da baya zuwa kitchen din ba tare
data qara koda second uku a wajen ba.
Kansa
shima ya dauke yana ajiye robar,sannan ya soma takawa a nutse yana wucewa ciki
kafin ya haura zuwa saman. Tun daga wancan ranar bai qara ganin gilmawarta ba
cikin gidan,wasu lokutan ma sai yaje gaida anni ta tambayeshi iyali take fado
masa a rai. Wani irin mummuna fito na fito yayi da kansa akan damuwa da abinda
tayi masa a ranar din,yana ganin bai cancanci ya sanya damuwarta a ransa har
haka ba.....sai ya sake qarawa kansa wani busy din akan wanda yake ciki,yana
saka ran wannan ya zama silar mancewarsa da komai,wanda yawan ayyukan da suka
zarta qa'ida din daya azawa kansa yake kyautata zaton shine silar wannan ciwon
kan da ya fara fama dashi.
A gajiye da
wani irin bacin rai da baisan meye dalilin faruwarsa ba daga shigowarsa gidan
ya dinga zare suit din jikinsa yana zubarwa,duk da cewa ba al'adarsa bace
hakan.
Bathroom
ya wuce kai tsaye,ya hada ruwa me dumi da zai dace da yanayin sassanyar iskar
dake kadawa,wanda asalinta hadarine daya hado,bai saukar da ruwan ba,amma ya
canza kala zuwa ruwan toka,ya kuma bada iska me sanyin dadi dake busawa da
qamshin qasa,yanayin da yake bada tabbacin anyi ruwa a wani gurin kusa da kano.
Mintuna
kusan arbain ya fito daure da towel,gargasar jikinsa dama sumar kansa duka sun
jiqe da ruwa. Faffadan qirjinsa dake lullube da gargasa ya fara gogewa da towel
din yana isa gaban madubi,daidai sanda yaga wayarsa na haske. Kaman ya share
saboda bayason doguwar magana,amma koda ya duba yaga maamah ce sai ya zamana
bashi da wani zabi daya wuce ya daga kiran.
Sai daya
zauna saman bean bag chair din dake ajiye a gefe sannna ya daga hade da
sallama.
"Barka da yamma" Ya dora da fada yana lumshe
idanunsa saboda yadda kansa yake sarawa.
"Barka kadai......kana office ne?,inason ganinka idan
kun tashi,akwai muhimmiyar magana da zamuyi da kai,sannan akwai baqi da sukeson
ganinka" Ta fada kanta tsaye. Yatsun hannunsa da baya riqe da wayar ya
cusa cikin sumarsa,yanajin yadda ta jero buqatunta kai tsaye ba tare da neman
jin uzuri ba.....ya ya wuni?,akwai damuwa?,yana da lafiya ko babu?. Baisan sai
yaushe wannan dabi'ar tata na damuwarta itace kadai damuwa zata sauya
ba.....baisan sai yaushe zata damu da damuwar wani ba ta aje tata damuwar da
son kan a gefe ba.
"Bana company na dawo gida....."
"Okay,to ya za'a yi kenan?,don duk yadda za'ayi inason
ganinka lallai lallai a yau din,ko meye kakeyi ka katseshi kazo ka sameni"
Ta sake fadi da dukka sautin da zai gaya masa da gaske take.
Jaririyar
ajiyar zuciya ya sauke yana cire yatsunsa daga sumar tasa
"Ciwon kai nake maamah.......amma zansha magani na
kwanta zuwa anjima zan shigo" Ya fada da raunanniyar murya,yana jin har
qasan ransa ya rasa wani part me girma a rayuwarsa,yanajin ya rasa wani abu me
matuqar muhimmanci a rayuwarsa. Duk da yana da anni,yana da farouq,yana da
saddiq da musaddiq,amma lokuta da dama yana jin kamar shi kadai ne.....yanajin
kamar shi kadai yake rayuwa a duniyar,wani irin maraici da kadaici yana
mamayarsa.
"Allah ya kaimu,kada kayi dare da yawa Allah ya
sawwaqe" Ta hade maganar duka lokaci guda.
Ya jima
idanunsa saman wayar yana kallonta,zuciyarsa na tuna masa abubuwa da dama ciki
harda abbansu. Tun asali shike damuwa kuma shike kasa bacci idan dayansu baida
lafiya,koda ciwon baikai ya kawo ba. Tun da can ita din bame damuwa da
lamuransu bace,tafi damuwa da duk hanyar da zata maida taro ta koma sisi.
Sai daya
bushe tas bai sani ba kafin ya miqe yana isa ga walk-in closet dinsa,boxer
kawai ya zura bayan ya mulke jikinsa da cream dinsa,ya kuma shafe jikinsa da
turarukansa,sai ya koma gefen gado ya zauna bayan ya balli wasu tabs na saukar
da ciwon kai ya sha,ya dauki remote guda uku,daya ya zuge duka labulayen dakin
dashi,daya ya kashe hasken duka fitilun dakin banda ta gefen gadon,dayan kuma
ya saisaita sanyin ac din yadda zai daidai da yanayin da yake ciki.
Cikin
duvet ya shiga ya duqunqune yana lumshe idanunsa gami da sauke nannauyan
numfashi,ya lumshe idanunsa yana son fatattakar kowanne tunani da lissafe
lissafe ko zai samu brain dinsa tadan huce.
Ana kiraye
kirayen sallar magariba ya farka daga gajeran baccin daya daukeshi,yaji dadi
sosai a jikinsa,sai ya wuce toilet yayi tsarki ya daura alwala. Masallaci ya
wuce kai tsaye,akayi magariba da ishai duka dashi,sannan ya dawo ya shirya
cikin tattausar exclusive Morocco ta maza me zuwa hade da wandonta. Kalar royal
blue ce,sai akayi mata ado da gold zare daga wuyanta hannu aljihu qasan wandon
da tsagar gefe da gefe na rigar. Wata zagayyar hula ya dora saman kansa ruwan
gold din,wanda yawanci yankin larabawa su sukafi ta'ammali da ita,take farin
bafullatanin nan muhammadu jikan jadda ya fito da wani irin kyau da zai wahala
ka kalleshi sau daya ka kauda idanu
(Niko nace uhmmmm,kaman kuwa yasan zance akazo yi gurinsa😂).
Clogs
ya sanya gold color,ya feshe jikinsa da mayen turarensan nan dake saurin kama
zuciya.
Key ya
laluba a ma'ajiyarsu ya dauki spare key din daya daga cikin motocinsa. Yau din
da kansa yake sha'awar yin driving,abinda ya jima rabonsa da yayi. Yanason ya
shaqi fresh air dinnan shi kadai ba tare da wani a gefensa ba wai da sunan yana
kare lafiyarsa ba.
Ta
kammale komai a daki kaman yadda ta saba duk dare,wanda idan ta shiga kuma ita
da fitowa koda hallway ne sai kuma da safe. Tun wancan ranar ta sake jin ta
tsani dukka wani abu da zai sake hadasu ko ya hada alaqarta dashi. Idan ta tuna
tambayarsa din kuma takanji wani mugun haushinsa na sake mamayarta,tana jin a
sannan me yasa bata amsa masa da eh wajen wani naje ba?.
Sai
data zauna tsaf sannan ta duba night stand fridge dinta babu ruwa ko qwaya daya
a ciki. Baida girma fridge din,don haka kadan kadan take saka ruwan saboda
gorar zata cika waje. Miqewa tayi tana yamutsa fuska,ta dauki Indonesian hijab
dinta navy blue ta zura wanda ya haskata matuqa,ya kuma fidda lallausar sumar
dake kwance gaban goshinta. Harta miqe ta dauki wayar huda da zuwa yanzun tayi
nisa da amfani da ita,tayi playing drama din da take kalla daga inda take,a
haka ta fita rabin hankalinta yana kan wayar.
Wannan
dalilin ya sanya bataji saukowarsa ba daga stairs din saboda lallausan clogs
din dake qafarsa baya bada sauti ko kadan,duk kuwa da cewa da dan sassarfa yake
saukowar yana gaggawar isa ga mota,so yake yaje ya dawo da wuri akwai ayyukan
da bai samu daman yi ba dazu,yanaso ko cikin daki ya ragesu.
Stairs
din ya danyi kwana kadan wanda sai kazo rabi sannan zaka hangi wanda ke fitowa
daga farkon hallway din,kaman shima......sai daya zo rabi sannan ya ganta.
Idanunsa suka sauka saman fuskarta data fita fes cikin tsakiyar hijabin kalar
luxury Morocco din jikinsa. Hasken dake fitowa daga cikin wayar ya haske
fararen idanunta dake sheqi kamar an diga mai. Bai fasa saukowa ba kaman yadda
taci gaba da takawa idanunta kafe akan wayar,har sai da cikin jikinta taji
kamar ta iso qofar da zata sadata da parlor din.
Daga kan da
zatayi ta tsinceta dab dashi sanda yake stair din qarshe. Sai ta juya a hankali
da zummar yi masa yadda ta saba wato komawa don ta kubcewa hada numfashi dashi.
55
_Daga abu hurairah RA yace,manzan Allah S A W yace: "ku
kashe baqaqe guda biyu koda kuna cikin sallah; MACIJI DA KUNAMA_
Taku biyu kacal tayi ya cimmata,ya kuma sanya hannunsa ya
dawo da ita baya,sai gata tsaye cak a gabansa kaman ba inda ta matsa. Idanunta
tsakiyar nasa idanun da suka qaa girma kadan saboda ciwon kan dazu,yayin da
hucin numfashinsa ya dinga fita cakude da qamshin turaren jikinsa yana kaiwa ga
hancinsa.
"Wanne kalan dodo ne ko abun tsoro a jikina da kike
gani?" Ya jefa mata tambayar a zafafe yana ware mata idanunsa. Ja baya
tayi niyyar yi da sauri saboda yadda ta dan tsorata kadan da yadda idanun nasa
suka qara girma,ga wani shimfidadden kwarjini dake fita daga cikinsu ya daki
zuciyarta lokaci guda ya kuma ninka gudu da bugun zuciyartata.
Hannunsa
qwaya daya ya sanya yasake dawo da ita gabansa yana sake bude mata girman
dukkanin idanunsa.
"Ki nunan abinda ke baki tsoro a jikina nace!" Ya
fada da dan tsawar takaicin abinda takeyi masan. Shi tun farko mutum me dan kai
tsaye,koda laifi kayi masa yafison ka fuskanceshi kai tsaye.....haka koda
matsala kake dashi yafiso ka tunkareshi kai tsaye ku warwareta.
So take
ta maida masa me zafi ko zata fanshe abinda ya gaya mata ranar nan,amma sai ta
lalubi kwanyarta da bakinta tsaf ta rasa komai kamar an mata sata.
Ringing din
wayarsa ne ya sanyashi maida dubansa ga wayar. Kusan a tare idanunsu suka kai
kai,kuma daga shi din har ita sunga sunan da yake rubuce a kai FAREEDA KHALED MUSTPHA.
Maida
dubanta tayi ga fuskarsa ba tare da tasan dalilin hakan ba,sai kawai ta zabi ta
zille ta tsakanin qofar ragon da yayi mata,saidai kuma tana motsawa kamar
hankalinsa yana maqale ne a jikinta ya daga kai ya watsa mata idanunsa bayan ya
maida wayar aljihu ya sakeyin kicin kicin da fuska.
"Daga yau duk ranar da kika qara ganina kika koma kaman
kinga dodo saina biki har cikin dakin na zaneki tas ciki da baya". Maganar
tayi mata banbarakwai,kamar wata nadra ko haneefa?,wannan mamakin ya bayyanata
tsakiyar qwayar idanunta da baisan me yasa yake yawan sanya nasa idanun a
cikinsu ba duk sanda magana irin haka ta hadasu.
"Kina mamaki ne?,ko kina ganin kin wuce duka?,ki gwada
koda gobe ne ki gani.....and,daga yau kada ki sake ganina baki gaidani
ba......tunda ko banza ana ci dake ai ko?,koda ban baki abinda wadancan suke
bakin ba" Ya qarashe maganar yana sakar mata hanya.
Cikin
qasa da second uku ruwan hawaye ya tararwa idanunta,ya za'ayi ya qara mata ciwo
akan wancan ciwon,tana jin lallai yau ta barshi ya tafi haka yaci bulus din da
ba'a taba cinta a kanta ba
"Ka daina burga kaman kana da abun bayarwar.......ni
bana buqatar ragowar su fareeda tunda akwai masu fresh......." Cak maganar
ta tsaye mata a maqoshi sanda yayi wani irin waiwayowa daidai sanda yake dab da
zarcewa falon. Batasan ta juya ba har ta soma tafiya zuwa dakinta ba sai da
taji tana taka lallausan carpet din dake shimfide daga tsakiyar wajen.
Dif wuta ta
dauke masa,zuciyarsa ta shiga raya masa nau'ikan hukunci mafi tsauri daya dace
yayi mata. Saidai kiran wayarsa ya sake katse masa duk wani hanzari,ya duba
kiran a fusace yana tunanin fareeda ce,amma ganin maamah ya sanyashi tattare
duk wani bala'i daya taso masa ya hadiyeshi,sannan ya daga wayar yace da
ita a taqaice
"On my way"
"To ka hanzarta" Maamah ta fadi tana jin dadin
yana hanya bawai yaqi amsa kiran nata bane.
Kai ya
jijjiga yana takawa a hankali yana ficewa,saidai a ransa yaci alwashin dole ya
ajiye mata abun tunawar da bazai sake fadin magana ta maida masa ba. Duka duka
shekarunta nawa amma sanadin aure raini yana neman shiga tsakani?". Ya
fada qasan ranshi sanda yake tayar da motar.
Da wani
irin speed yake jan motar,wanda dama sabonshi ne gudu a mota,ba tun yau ba ba
kowa ke iya shiga mota ba indai shine zai tuqa. Idonsa ya lumshe yana tuna
abinda tace masan,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa.....zai wahala
cikakkiyar budurwa me kunya ta iya fadin hakan.....ita kuwa bata cikin kowanne
sahu,dom haka idan ta fadi sama da haka ma fuad kada kayi mamaki.....kowa yasai
rariya yasan zata zubda ruwa.
Har ya isa
gidan maamah wannan kalmar ta kasa fita a ranshi
"Ragowar su farida....kamar ma kana da abun
bayarwar" Har cikin ransa ya gamsu ta rainashi,sai ya samu Kansa da kallon
Kansa a side mirror,yana tuna dararen da yake kashewa a tsaye ba tare daya isa
ya kwanta ba bare ya samu cikakken bacci saboda tsananin yadda ya kame
kanshi. Da wannan bacin ran,da kuma
tunanin hukunci mafi tsananin daya kamata ya dauka ya isa parlor din maamah.
Mamaki na
gasken gaske ya cikashi lokacin da yayi sallama ya tsinci fareeda cikin masu
amsa masa sallamar tasa. Tana zaune hankali kwance saman sofa din parlor din.
Sanye take da riga da wandon Palazzo daya bude sosai daga qasa. Rigar me
gajeran hanny ta lafe a jikinta ta kamar yadda Palazzo din ya fidda shape din
hips din ta zuwa qugunta. Bandana ce
kawai saman kanta,hannunta riqe da wayarta.
Kallo daya
tak ya mata ya dauke kansa kai kace bai taba sanin wata halitta a duniya me ire
iren kama da ita ba. Qasan maqoshinsa kuwa kawai kaiwa da kawowa maqogoronsa
yakeyi,adams apple dinsa yana motsi daga sama zuwa qasa,ya taka a nutse kuma
kai tsaye ya wuce gaban maamah din a ladabce.
Tunda yayi
sallamar ya shigo taji gaba daya an tsinke duk wata jijiya daka iya baiwa dan
adam kuzari daga jikinta. Tunda take haukan son fuad bata taba tunanin
haduwarsa da kyansa ya zarta yadda ta gagganshi bama sai yanzu data ganshi
cikin shigar mutanen Morocco,wanda nan Nigeria zaka ga suna kama da tufafin da
sarakuna ke sanyawa musamman idan suna ganawa da baqi cikin gida. Numfashinta
cak yaso tsayawa,muhammad fuad ya wuce yadda take hangensa a nesa,a take taji
tabbas zata iya sadaukar da komai data mallaka don ta samu fuad din a matsayin
mijin aure
(Anya....fuad din fa me tsada ne......amma muje zuwa,tunda
kin kama maamah wataqila kina da rabo).
Kusan
duka gaisuwar da sukayi shida maamah da gajeriyar gabatarwar da maamah tayi
masa bata ji ba
"Baquwar taka ce muhammadu.......ina me umartarka ka
saurareta ka kuma fahimceta.....duk wanda yayo tattaki qafa da qafa ya taho
gareka saboda yana sonka ba qaramin masoyi bane,idan Allah yaso kuma matarka
ce" Ta fadi maganan qarshe tana yunqurawa ta miqe.
Daga kai
yayi yana duban maamah sanda take jifan fareeda da murmushi,da salo kuma na
bada goyon baya take cewa
"Gashinan fareeda,bari na shiga na fito kafin ku
gama"
_idan Allah yaso kuma matarka ce_ yaji amsa kuwwar maganarta
ta qarshe tana nanata kanta cikin kunnuwansa. Maganar sai taso ta masa kama da
maganar data masa daidai sanda ta tilastashi auren waccar yarinyar.......me
yake shirin faruwa?.ya tambayi kansa.
"It will never happened" Ya fada yana qaryata
komai da zuciyarsa ke qiyasta masa zai iya faruwa.
"Hi......ka ganni har gida?,yanzu ka yarda garin masoyi
baya nisa ko?" Ta fada tana sakar masa murmushi,murmushin nata dake daidai
da diban garwashin wuta ta watsa masa.
Wannan bai
dameta ba,yanayin fuskarsa duka bata sakashi a mizanin damuwa ba.......zai gata
ta zame tana saukowa qasa. Ta qaraso dab dashi tayi Zaman raquma tana dubansa
"Please Muhammed kada kayi rejecting dina.....na maka
alqawarin zame maka duk kalar matar da kakeso kake buri" Ta furta da
tsananin narkewa.
"Stop it please......ke me yasa baki nemawa kanki
martaba mutunci da kima?". Ya fada bayan ya daga mata hannu ya dakatar da
ita daga maganan farko launin idanunsa sun fara sauyawa saboda bacin rai.
A rikice
ta girgiza kai ganin yana juye mata zuw wannan fuad din me wahalar
samu.....wannan fu'ad din me tsananin tsauri
"Mutunci martaba da kima duka susha zamansu muddin zan
samu muhammad fuad". Shuru ya ratsa qarshen maganarta,ya xuba mata ido
yana sansano alamu alamun hauka tattare da ita,sai ya matsar da fuskarsa kusa
da tata kadan,da wani sauti can qasa wanda tsanantar bacin rai da kuma sarawar
da kansa yayi ya dawo da ciwonsa sabo fil ya tilas masa maganar a haka yace
"Gashi shi kuma muhammad fu'ad din saida wadannan
abubuwan ake samunsa......." Daga haka ya miqe tsam da zafin nama,sai gata
ta miqe tare dashi cikin tsoro da fargabar kada yaqi tsayawa ya saurareta duk
da kuwa ta dangana da mahaifiyarsa.
"Umarni nake baki......ki tattara kayanki kibar gidan
nan,kada na dawo jibi na sameki,don gobe ma tayimin kadan,bazan iya shaqar iska
a wajen da kika dade a cikinsa ba". Yana kaiwa qarshe ya juya da zafin
nama me gauraye da fushi ya soma fita.
Ta dauka
zata jure saita kasa,ta bishi a baya da gudu gudu tana kiran sunanss,saidai ko
ta kanta baibi ba,ya bude motarsa ya shige ya kunna ya tasheta da wani irin
qarfi ya fusgeta yana fita a gidan,don ko sanda ta qaraso sawayen motar kawai
ta samu,saita zube a wajen tana qwala kiran sunansa,abinda kunnuwan maamah suka
jiye mata kenan,ta fara saukowa da sassarfa daga sama.
Baisan
yadda yakai kanshi gida ba saboda tashin hankali da tsananin ciwon kan daya
saukar masa,shidai yaji daya daga cikin security nasa na cewa yabar motar daga
nan zai qarasa shigo da ita ya gyara parking din.
"Sai yaushe maamah zata canza?,sai yaushe zata zama
cikakkiyar uwa?,sai yaushe zata zabi girma da mutunci sama da kudi?,sai
yaushe?,sai yaushe?".
Kusan
wannan shine abinda ya sanyashi kwana ya kuma tashi da ciwon kan daya hanashi
fita,ya kuma kashe dukka wayoyinsa don baya qaunar ya nemi wani ko shi a
nemeshi.
*_WASHEGARI__*
*_BAQIN DARE_*
*_MUHAMMAD JADDA RESIDENT_*
*10:45 NA DARE*
Tunda ta
fara kallon film din hankalinta bai kwanta ba sai yau da taga qarshensa. Duk da
cewa ya bata mata lokaci sosai,don sai a yanzun sha daya saura na dare ta
kammala......amma kuma ya haifar mata da wani irin nishadi a zuciyarta,nishadin
da duk idan ta tuna yadda rayuwar stars din ta kasance a ciki sai taji ta saki
dan murmushi kadan. Sam ita din ba ma'abociyar kallo bace......wannan shine
film na farko data fara kara full kuma wai korean series.
Idanunta ta lumshe tana shaqar iskar dake kadawa sosai take kuma yiwa
kanta hanya ta windows din dakin da yawanci yakan barshi a bude saboda samun
fresh air da tafi iskar ac artificial air dadi a wajenta.
Gabanta yadan buga kadan,tayi kuma hanzarin bude idanunta sanda taji
kaman motsin taba window din. Ta tsaya cak daga qoqarin fidda rigar jikinta da
takeyi,tsahon mintuna biyar bata sake jin komai ba,saita matsa gaban windows
din dukansu,ta bisu daya bayan daya ta zugesu,ta kuma sanya musu lock.
"Sabreena kin zama matsoraciya" Ta tsokani kanta
da kanta,ta kuma sakarwa kanta da kanta din murmushi. Ita kanta batasan yaushe
ta koma hakan ba,saidai girman gidan koda rana ce ta take tsoro yake bata,duk
da tassn cike yake da security musamman idan ma'u ta gama kai kawonta ita da
ameh kowa ya wuce gefansa.
Towel ta
daura babba,har zata wuce toilet din taji kaman yau garin da iska,don haka ta
miqa hannu ta dauki hijab din da tayi salla dashi ta zura a jikinta ta wuce
bandakin.
Tana wankan
amma kadan kadan takejin gabanta yana faduwa wanda ita kanta batasan dalili ba.
Yau din sai ta samu kanta da rage tsahon lokacin da takan dauka a
bandakin,cikin qasa da mintuna goma ta kammala,tayi brush ta busar da
kanta,sannan ta daura towel din ta maida hijabinta ta fara takowa tana fitowa.
Sanda ta
dora hannunta akan handle din gabanta ya sake yankewa ya fadi.
"Hasbiyallahu wa ni'imal wakeel" Ta furta a
hankali kaman yadda yanzu yadan fara zama a jikinta,don cikin jadawalin
karatunsu da rumaisa akwai azkar sosai da addu'o'i masu yawan gaske.
Jiki a
sanyaye ta murda handle din ta jawo qofar ta bude sannan ta fito,kai tsaye ta
soma nufar madubi. Abun mamakin yadda takejin baqon qamshi cikin dakin,tadan
tsaya kadan tana buda hancinta still qamshin takeji,sai kuma tunanin iskar dake
ratsowa ta cikin rufaffun windows din qilan ke debo qamshin daga waje zuwa
dakin,don haka hankalinta kwance ta qarasa gaban mirror din tana duba fuskarta
da jiya taqi wani qurji qwaya daya ya fito mata.
Wutace
tsaf ta dauke mata kafin wata mahaukaciyar faduwar gaba ta rufto mata,tun daga
saman kanta har zuwa yatsun qafafunta da ganin fuskar dake tsaye a bayanta.
Dagawa
qirjinta ya shiga yi daga sama zuwa qasa cikin wata irin razana da takejin
kamar tana shirin dimaucewa ne......sake matsota yakeyi idanunsa cikin
nata,kaman yadda fuskarsa ke shimfide da shu'umin murmushin nan data saba gani
a fuskarsa a shekarun baya.
"Mmmm........." Ta dinga yunqurin fadin
sunansa,amma sai taji kaman an sanya gum an manne labbanta na sama da qasa guri
guda.
*_TOFA!_*
*_WAYE WANNAN?_*
*_NACE WAYE WANNAN?_*
*_MUHAMMAD FU'AD NE DA KANSA?_*
*_KO KUMA WANI MUTUMIN NE NA DABAN?_*
*_TURQASHI_*
*_Allah yasa muna cikin masu rabon ganin ranar litinin
lafiya_*
*_karku yadda karki yarda aci gaba da sukuwa da zamiya cikin
labarin nan ba tare dake ba_*
*DA SAURAN KALLO!!!*
Tofa nayi qarqaf😂😂
Allah ya bani ikon baku na ranar monday🙏🏽🙏🏽🙏🏽😂
56
_Daga ummu habiba uwar muminai Allah ya qara yarda a gareta
tace,naji manzon Allah S A W yana cewa "duk wanda ya sallaci raka'a sha biyu daga rana zuwa dare(bayan sallar
farillai guda biyar),Allah zai gina masa gida dasu a aljanna_
_muslmin ne ya rawaito_
_raka'o'in nan sha biyu sune,biyu kafin asuba,hudu kafin
azahar da biyu bayan azahar,biyu bayan magariba,biyu bayan isha'i saiki qara da
wuturi_
_Sannan akwai hidisi me zaman kansa abdullahi bin umar ya
rawaito,manzan Allah S A W yace ALLAH KA YIWA BAYAN DAKE SALLAH RAKA'A HUDU
KAFIN SALLAR LA'ASAR RAHAMA_
*_IBADA DUK IBADA CE,AMMA MAFI SOYUWAR AIKI A WAJEN ALLAH
DUK QANQANTARSA SHINE WANDA ZAKA DAWWAMA KANA YI,SAIKA DAUKI WANDA KASAN ZAKA
IYA DOREWA_*
Tana kallonsa ta cikin madubin yana ci gaba da kusanto inda
take,saidai gaba daya ta kasa motsa koda yatsanta ne ballantana tayi tunanin
abu na gaba daya kamata ace ta aiwatar.
Shu'umin
murmushinsa da kallon da yake dubanta dashi duka ba wanda ya fasa,yaci gaba da
kusantota kowacce gaba ta jikinsa tana jin wani shauqi tare da dokanta ta sadar
da kanshi gareta. Irin yadda ya fitinu da ita ba abu bane me sauqin fassarawa
ba......sai kuma gashi a bagas zaice ko a banza wata hanya ta samun isa gareta
ta riskeshi cikin sauqi,wanda zai iya kiran hakan da qatotuwar sa'a cikin
rayuwarsa.
"Mashkur!" Ta fusgi sunan da hanzari ta kirashi a
tsawace bayan ta maimaita la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen
har batasan adadi ba.
Tsaiwar da
yayi ita ta bata damar waiwayowa da wani irin hanzari kamar wadda aka fusga.
Idanu ta zuba masa kaman yadda shima idanun ya zuba mata yake kallonta da dukka
iyakacin kallonsa.
"Me ya kawoka gidan mutane?......har dakin matar
aure?" Ta fadi da wata irin birkitacciyar murya data cika da razani da
tsoro.
Wata irin
dariya ya qyaqyace da ita,harda komawa ya fada saman gadon nata,sannan ya tashi
ya miqe yana fuskantarta. Ya bude baki zaiyi magana a hankali sautin saukar
ruwan saman farko ya baqunci kunnensu,shatin ruwan ya fara sauka ta glass din
windown dakin sai ya saki murmushi yana dawo da dubansa kanta.
"Kin gani ko?,.....ko Allah ma yana sona......ko Allah
ma yasan kin cuceni....kuma ko Allah yasan kedin azzaluma ce,wannan zubar ruwan
shi zai sake toshe kunnen duk wani da kike tunanin zai ceceki ko zai kawo miki
dauki,duk da kuwa wannan ginin gidan naku dama kaman anyishi ne domin ni,yana
riqe sirrin kowanne motsi yadda ya kamata". Ya fada yana kallon yanayin
roofing na dakin yana sakin murmushi.
"Nayi mamaki wai da kike tambayata abinda ya
kawoni,bayan akwai basussuka na da yawa a kanki?".
"Mashkur ka haukacene?,kasan gidan waye ka shigo?,gidan
matar aure har tsakiyar dakin aurenta..... " Fara takowa yayi yana sake
nufota yana dariya
"Ina cikin gidan muhammad fu'ad jadda,the owner of
jadda diamondchore resources.......sannan ke din sabreena ce,mata a
wajensa.....bayanin yayi daidai?" Ya jefa mata tambayar yana dage mata
dukka girarsa biyun bayan ya tsaya daga takowar da yakeyi.
"Ko kina buqatar wani qarin bayanin?......kinaso ne na
gaya miki da license dina na shigo gidan nan?,da license daga hannun wata mace
mafi kusanci da me gidan?". Daukan tunaninta yayi ya luluqa wajen lalubar
ma'anar abinda yake fada,da license daga hannun wata mace mafi kusa da me
gidan?,wace kenan?.
Kaman
yasan abinda take tunani a kai yace
"No dear......kada ki wahal da kanki wajen tunanin
wace..... Ki bari na gama kashe qishirwata sosai sannan mu zauna mu
tattauna..... I need you.....na azabtu da yadda asara biyu ta fadamin......babu
ke ba kudina......come please" Ya furta yana kawo mata cafka.
Batasan
tana da tsananin zafin nama har haka ba sai data kufce masa ya kama iska.
Sukabi hannunsa da kallo dukka su biyun shi da ita. Shi dariya ya saki yana
jijjiga kai
"Kada ki dauka kedin me sa'a ce ko da yaushe.......idan
a wancan karon kin kubcemin...... Na rantse wannan karon baki isa ki kubuta
ba,koda kuwa a gaban mijinki ne a yau sai na kashe qishirwar dake raina"
Ya furta yana daga rigarsa,take ta hangi hancin bindiga daga aljihun trouser
dinsa. Kaman an debo bulo an jibga mata haka taji wani matsanancin tashin
hankali ya keto mata,bata gama sauke abinda ya taso mata ba ta ganshi ya taso
mata yayo kanta gadan gadan. Wani irin qarfi ne yazo mata,ta tattara hijabin jikinta
da batakai ga cireshi ba da kyau ta haura sofa bed din dake gabanta ta wuce
tsakiyar gadon
"Ka fita min a gida....
Ka fita tun ban tada security din gidan nan ba" Ta fada tana duban
sashen da wayar girke take a dakin wadda zata baka daman kiran kowanne sashe na
gidan. Ta shiga shock sosai sanda ta lura ya gutsire wayar gaba daya ya fasa
kan,duka yaushe yayi hakan da ko alama bataji ba.
Dariya ya
saki yana cewa
"Kinga abinda ya samu telephone din ko?....." Bata bari ya qarasa ba ta tattara dukkanin
qarfinta ta kwarara ihu tana fadin
"Wani ya taimakeni" Abinda ta dinga maimaitawa
kenan har sai da taji maqoshinta yana wani suya da radadi. Dakatawa tayi hawaye
suna cika idanunta,tana duban mashkur dake qyaqyata dariya.
"Zan iya qara miki lokaci kici gaba da ihu......kiyita
ihu har iya yadda kikeso".
"Fuad!. ....fuad!!!!" Ta sake qwalawa kiran
sunansa. Karo na farko da ta fara ambatar sunan nasa kenan.
"Yana can yana bacci" Ya fada yana juyi kaman zai
taka rawa
"Na sakashi bacci,kuma bazai tashi yanzu ba,sai na gama
hutawa da matarsa" Ya sake maimaitawa cikin yanayin nishadin da kana
kallonsa zakayi imani yakai masa har qasan zuciyarsa nishadin da yake ciki.
"Mashkur,........ka saurara haka,ya kamata kasan
kuskure kake tafkawa ba qarami ba.......ketawa matar aure haddi mashkur?!"
Ta furta a tsawace. Dariyar nishadi ya saki yana kallonta,ya kama button din
rigarsa ta saman ya fara ballewa yana zareta ya yar.
"Kada kiyi kaman bakisan komai ba.......kina tunanin
yaune na farko dana fara kwanciya da matan aure?,na kwanta dasu har bansan
adadi ba......kawai ke dince ta daban,kin kasa fita a raina......bazan miki
qarya ba,koda na dandana yadda kike banajin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare
da ke ba......shawara daya kawai zan baki,kada kiyimin gaddama.......ki bani
kawai salin alin don na tabbatar kinsan komai,ba wani abu baqo a wajenki"
Sasai
kalamansa sukayi mata nauyi a qirji,ta tabbatar inda za'a tsaga jikinta ba za'a
taras da jini ko digo ba saboda tsananin tsoro da fargici. Ranta yakai maqurar
baci sanda taga yana yunqurin haurowa gadon
"Har ka mutu mashkur ba zaka taba samun komai daga
gareni ba.... Ko gawata tafi qarfinka
mashkur bare gangar jikina a sanda numfashi yake busawa".
"Well.....tunda kin zabi muje ta haka dake!" Da
furucin da haurowarsa saman gadon duka lokaci guda suka faru. Wani tsalle tayi
da zummar barin gadon,saidai kuma ya samu nasarar take qasan hijabinta da
qafarsa ganin zata kufce masa,abinda ya sanyata data dira din bata sauka a
daidai ba,hannunta ya daki side bed ya bada wani irin qum.
Qara ta
saki cikin tsananin azaba......azabar da bata hanata ci gaba da qoqarin qwatar
kanta ba,cikin sa'a santsin bedsheets din dana hijabinta suka sanyashi ya zame
zaman lallausar katifar,saita miqe itama,amma ta kuma zamewa take fuskarta ta
bugi gefan bedside din still.
Bata damu
da radadin daya sake ratsata ba.....sake miqewa tayi tana harin qofa,abinda ya
lura dashi kenan shima ya miqe da azama,tana isa qofar shima yana qarasawa
sanda take kici kicin bude key din,ta finciketa ya watsar ya saka key ya kulle
qofar. A zafafe yabar bakin qofar yana nufar qofar toilet yana cewa.
"Yau zaki gane waye mashkur.....tunda baki zabi komai
ya kasance ta hanyar maslaha ba"
Key din jikin qofar toilet din shima ya murza ya kulle,tana kallonsa
sanda take qoqarin sake tashi saboda buguwar da tayi a hannu da fuska,yadan
bude window din waje ya watsa Keys din sannan ya sake waiwayota.
"Kaji tsoron Allah mashkur......kada ka keta haddin
aure.......da auren wani a kaina.......ba bazawara ko budurwa bace!"
"Allah yasa tattabara ce ke" Ya fada cikin rashin
damuwa yana durfafota da sassarfa kaman me wasan motsa jiki.
Cafka ya
sake kawo.mata ta sake samun nasarar gocewa abinda ya sake qona masa rai,sai
kawai ya zabi ya galabaitar da ita.....don duka alamu sun nuna masa cewa gwana
ce wajen iya zilliya,kada ta bata masa time ta kuma bata masa plan,don haka
yakai mata naushi.
Ya sameta
ta kafadarta ne yayin da nashi hannun ya wuce ya daki bango,abinda ya sanya
wata azaba me tsanani ratsa kwanyarsa.
"Ouch!" Ya fada cikin tsananin jin zafi,yayin da
zuciyarsa ta sake tunzura
"Ni xaki sanya naji rauni?". Yana kaiwa nan ya
shammaceta yakai mata qafa ya kwasheta,take ta fadi ta bugu da qasa.
"Wayyo Allah na" Ta fada cikin tsananin radadi
tana riqe qugunta gami da runtse idanunta. Wannan shine abinda ya bashi daman
isowa gareta,ya kama bayan kanta inda ta tattare gashinta tayi gammo dashi ya
riqe gam. Wata azaba ta ziyarci tsakiyar kanta zuwa qwaqwalwarta,ba shiri ta
sake qwalla qarar da zuwa yanzu ta yanke tsammani akwai me cetonta.
Yana riqe
da kan nata ya turata har saman dressing table dinta,baiyi wata wata ba ya buga
goshinta samanshi,take goshin nata ya fashe,saidai kuma tana dagowa ta dago da
bedside lamp da akayi ado da ita saman mirror din ta kwatsa mata ita tsakiyar
kanta,abinda ya sanyashi sakinta ba shiri yana dafe da wajen.
Duk da
wajen bai shafe ba amma take yayi wani malulu azaba ta shiga ratsashi tako ina.
Ya kalleta
sanda jini ya fara diga jikin sky blue din hijabinta yana jin wani fushi mara
misali yana saukar masa. Bai taba tunanin zaiyi minti biyar ba daga sanda ya
shigo dakin ba tare daya samu galaba a kanta ba,sai gashi yanzu wankin hula
yana neman kaishi dare...
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 57
57
_Daga abu hurairah RA yace,manzon Allah S A W yace
"mafi falalar sallah bayan sallar farilla itace sallar dare_
*_ga falala ga kaifi,biyan buqata kaman yankan wuqa😄,Allah
ya bada ikon jurewa_*
Ga mamakinta sai taga ya samu waje ya zauna yana mulmula
wajen. Tsahon mintuna tana tsaye tana kallonsa tana dafe da inda jinin keci
gaba da diga bata da abun tareshi. Ko na minti guda taqi yarda ta dauke
kallonsa a kanta gudun kada ya mamayeta bata shirya ba. Hannun nasa ya sauke,ya
fidda kwalin wiwi,ya zari guda biyu ya kunna musu ashana sannan ya sanya duka
biyun a bakinsa ya soma zuqa cikin gwanancewa. Yadda ya tsara zaiyi da ita sai
yaji me yasa bai taho da kayan mayensa ba?,ko banza yafi samun kalan nishadin
da yakeso?,ya yanke ya fara zama yasha wiwi dinne don yadan huce kadan ta yadda
zaifijin gardin abun.
Tunda ya
kunna wiwi din hankalinta yayi mummunan tashi. Ta san tabbas zata shiga wani
mummunan yanayi ne da idan batayi wasa ba xai galabaitar da ita. Asthma
dinta,ba kalar hayaqin dake saurin tayar da ita irin hayaqin wiwi taba da
shisha. Matsawa baya ta dinga yi tana duban yadda hayaqin ya fara gauraye
dakin,yana canxa yanayinsa daga ainihin qamshi xuwa gurbataccen warinta maras
dadin shaqa.
Dukka hijabin
ta cukuikuyeshi tana rufe hancinta dashi,a hankali tana jin yanayinta yana son
ya fara sauyawa.
"Zaki fahimci abinda ake nufi yau da asalin fyade"
Kamar mugun dawa haka ya miqe zumbur ya kuma nufota,ta juya itama da nata
hanzarin da nufin barin gurin,saidai tuni ya miqa hannu ya danqo hijabinta ya
dawo da ita gabansa tana fuskantarsa. Yadda take qoqarin toshe hancinta a nasa
tunanin ya karanci batason warin wiwin ne,don haka ya zuqeta sosai ya kuma soma
fesa mata ita saman fuskarta. Kauda kanta tayi sosai tana dauke numfashin da
zuwa sannan tana jin kamar ya fara daina isarta
"Ba wannan hijabin ba?" Ya fada yan yamutsa
hijabin cikin hannunsa,abinda ya sanya ta takurewa gaba daya guri guda tana
qoqarin neman hanyar da zata samu iska me kyau gudun gushewar hankalinta,wanda
wannan na daya daga cikin damar da zai samu cikakkiya kan ya aikata komai
hankalinsa kwance.
Wata
wawiyar zuqa ya yiwa wiwi din ya sake fesa mata kan fuska,sannan ta birkitota
gaba daya yana kici kicin fincike hijabin daga jikin ta.
Dole ta
daga fuskarta,duk da yamutsewar hazon dakin dole ta bude kafofin shan iskarta
ta fara masa magana a rarrabe
"Kada ka ketamin haddi na,kada ka lalatamin
mutuncina" Tayi.maganar sanda ya samu nasarar salube kan hijabin daga
kanta. Bayyanar sassalkar sumarta ya sanyashi sake gigicewa,bai taba tunanin ta
mallaki suma har haka ba.
"Wow" Ya fada yana qoqarin samun wuyan hijabin don
itace hanya mafi sauqi da zata bashi damar tsarge hijabin cikin sauqi daga
jikinta. Ta fahimci abinda yake shirin yi,saita tattara dukka dan qarfinta ta
cukuikuyeshi da kyau tana kiran sunansa cikin qaraji gami da fadin
"Kada ka aikata!.....ka qyaleni mashkurrrr!!!!".
A hankali ya
bude idanunsa wadanda basu sauka akan komai ba sai agogon dake gefan gadon
nashi. Idanu ya zuba mishi kafin ya miqa hannu a hankali yana jawoshi yana duba
time da weather na gari. A nan yaga alamun saukar ruwan sama,sai ya maidashi
sannan a hankali ya furta addu'a yayin saukar ruwan sama
'ALLAHUMMA SAYYIBAN NAFI'AN'.
A nutse ya
tashi daga kwanciyar,ya motsa kadan yana sauke qafafunsa daga qasan gadon wanda
suka sauka daidai bedroom slippers dinsa yana jin yadda gaba daya ciwon kan da
yakeji din ya sauka. A yanzun tsabar ta'ammali da home remedies ya sanya ba
kasafai ya fiya afawa kansa qwayoyin bature ba yayin zazzabi da ciwon kai ba.
Miqewa
yayi ya fara takawa zuwa qofa yana mamakin yawan baccin da yayi,yadan shafi
cikinsa yana jin yadda yunwa ta fara yamutsa hanjinsa,don haka ya yanke
shawarar ya sauka qasa kawai yaci abinci,yadan duba ayyukansa koda na awa biyu
ne kafin ya sake kwanciya.
A parlor
ya tsaya ya duba wayarsa,ya samu tarin miscal amma ciki na farouq yafi yawa,ya
samu saqonsa da yake masa mita akan bai bada komai na tafiyarsu ba bayan saura
sati guda. Qasan zuciyarsa kawai yayi murmushi yana sauka daga duba saqonnin.
Har ya aje wayar wani tunani ya fado masa,sai ya tsaya ya zubawa qofa idanu.
Yana
tuna tahowarta ne jiya daga bedroom dinta zuwa qofan falo. Tabbas idan idanunsa
ba qarya sukayi masa ba kallo yaga tanayi.
"A ina ta samu waya?,waye ya bata waya?" Ya yiwa
kansa tambayar a bayyane yana zurfafa nazarin ta inda zata samu waya tana cikin
gida.
Kaman
yadda ya sanya doka ya sani ba wanda ke shiga gidan,sai amna da tazo baifi sau
biyu ba. Amna kuwa yayi imanin ba zata taba bata waya ba musamman idan ta gaya
mata shi ya karbe. Duk abinda yayi ko ya aikata amna tasan yana da dalili,ta
fita saninsa,so ba zata karya dokarsa ba.
Kai ya
jinjina yana tuna fitar da tayi ba tare da sani ko izininsa ba rannan,tabbas
wayar tana da alaqa da wannan fitar duk da ya bincika babu wani abu da yayi
kama da gurin wani taje.....amma how and when ta samu waya?.
Tambayar data masa susa kenan a qirji. Yanaji kaman ya kamata ya maida
hankali a saka CCTV din. Company din yazo har sau biyu shi yace su bari ya zama
free ya kirasu,yana jin kamar gamsuwa daya fara bawa kansa don tana karatun
addini sosai a yanzu ta hannun jikar malam.....kaman bai kamata ya bata amanna
har haka ba.
Da wannan
tunanin ya bude smart door dinsa,ya kuma fara sauka zuwa qasa.
Abinda
ya soma bashi mamaki shine jin gaurayar wani qamshi qamshi me kama da wari wari
da gauraye stairs din. Koda ya kawo qarshenta sai yaji warin yana dada qarfi,ya
tsaya cak yana buda hancinsa sosai,a nan yaji daga inda warin yafi qarfi.
Mamaki
ya kamashi sosai,yana da wani irin experience na iya hasashen abu da gano
sauyawar motsi ko yanayi kaman wanda ya karanci aikin binciken tsaro na sirri.
Fara takawa yayi zuwa cikin hallway din a hankali,yana sake shiga ciki xarginsa
kuma na sake qarfafa saboda daduwar warin da sai a sannan ya fahimci warin wiwi
ne.
"Wiwi?" Ta maimaita sunanta can qasan maqoshinsa
sanda ya iso bakin qofar dakin.
Tsaiwar
da yayi duka baifi ta minti guda ba,amma sai yaji jikinsa bai aminta da dakin
ba,baya buqatar yayi knocking don ba qa'idar bincike bace akan abinda kakeson
ganin gaskiyarsa quru quru,juyawa yayi da sassarfa yana tuna inda yaga an
tanada a dakin nasa saboda ajiye kowanne key na kowacce qofa ta gidan a
matsayinsa na mamallakin Master bedroom.
Dubawa
daya ya hango master key,sai ya daukoshi yana juyawa gami da saukowa kai tsaye
yana nufar hallway din.
Ta riqe ya
riqr,yaja taja,har daga baya ya fahimci kamar hayaqin wiwin din kawai ke iya
bugar da ita. Hakan ya sakashi tsugunnawa ya dauki guntuwar data rage,ya jata
da kyau ya fesa mata a fuska. Numfashin ta ne ya soma yankewa,ta jawoshi da
wani irin hanzari tana tuna komai zai iya faruwa idan ta sake ta rasa
numfashinta. Ci gaba yayi da bulbula mata tana ci gaba da riqe numfashin nata
da taimakon hasbunallahu wa ni'imal wakil da take ambata cikin maqogoronta.
Dariyar
mugunta ya saki,sai kuma yace
"Are you asthmatic?" Bai jira komai ba ya danna
mata wiwi din a baki,abinda ya birkitata kenan ya sanyata hautsinewar da
batasan sanda ta daki al'aurarsa da gwiwar qafarta ba,tsananin zafi ya sakashi
sakinta gami da hankadata....dukka jikinta ya gama saki,numfashinta kuma yayi
qaura daga gangar jikinta,wannan ya sanyata tafiya luuuuu bakin qofar
dakin,wanda haka dama ya saita da nufin fuskarta ta daki qofa ta kuma suma
kafin ya gama daidaita radadin daya ziyarceshi.
Saidai
kuma tana isa bakin qofar sai yayi daidai da sanda ya murza handle ya
bude,abubuwa biyu duka dakeshi,warin wiwi da fadowarta qirjinsa da guntun wiwin
a bakinta,sulalewarta a jikinsa ya sanyata ta gangara ta fadi ta gefen
bakinta,ta qarasa zubewa a jikinsa unconscious.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 58
58
_Daga ibn abbas RA,manzan Allah S A W yace"duk wanda
yaji kiran sallah baije yayi sallar ba(ya zauna ya yita a gida).to bashi da
sallah,saidai idan wani uzuri ya hanashi fita(kamar yanayin firgici na rashin
tsaro ko tsoro)_
Dukkanin hannayensa ya sanya tallabota jikinsa yana bin
guntun wiwin din daya fadi da kallo. Maido dubansa ya sakeyi fuskarta cikin
wani irin yanayi dashi kansa baisan yadda zai fassarashi ba,sannan ya sake daga
kansa yana bin mashkur dake tsaye da wani birkitaccen kallo. Na wucin gadi tsaf
tunaninsa ya tsaya kafin qwaqwalwarsa ta dawo da aiki,yayi hanzarin maida
dubansa fuskarta da take bayyanar da gushewar numfashi a tattare da ita.
Tattarota
yayi sosai sannan ya dagata cak yana jin wani abu yana zagayaw a gangar
jikinsa. Waye wannan cikin dakinta?,waye wannan da yanayin da ya tabbatar masa
ba mutumin kirki ko aziqi ne ba.....me ya kawo qaton gardi cikin tsakiyar
dakinta daya kaure da mummunan warin wiwi. Duka yana da buqatar wadannan
amsoshin,to amma kuma hankalinsa ya rabu gida biyu yana jin kamar ya fara cetar
numfashinta da ya dauke shine abu mafi muhimmanci na farko a tare dashi.
"Ina zakaje da ita?" Muryar mashkur dake a shaqe
ta sauka a kunnuwansa sanda ya fara dosar qofar dakin da ita. Wani mahaukacin
mamaki ya kasheshi daya sanyashi waiwayowa ya zubewa mashkur idanunsa. A karon
farko kaifin birkitattun idanun fu'ad din suka ratsa nasa jijiyoyin idanun suka
kuma aike saqo ga sassan jikinsa,saidai kuma a yadda yakejin zuciyar tasa a
tsike......ba muhammad jadda ba...koma waye zai iya fito na fito dashi indai
akan cikar muradinsa ne.
"Shawara zan baka ka ajiyeta ka rufe mana qofa......don
ba suma ba......ko mutuwa tayi tabbas sai na biya buqatata a kanta.......ita ta
kira wannan ruwan.......ita ta kira fitina a sanda fitinar take bacci".
Wani dummmm fu'ad yaji kunnuwansa sun masa na wani lokaci,take wani irin gumi
ke dumi ya soma fesowa ta kowacce kafar gashi ta jikinsa. Idanunsa suka soma
sauya launi tamkar an diga jan zabibi a cikinsu.
Murna da
mamaki suka cakude suka saukarwa mashkur sanda yaga ya sake turo qofar dakin
yana dawowa. Saidai shakku sun cikashi a sanda yake tuna waye muhammad
fu'ad?......wanne risk ya tsallake kafin ya zama abinda ya zama yanzu?,kafin ma
ya mallaki asalin abinda ya zama shine silar arxiqinsa a yanxu?.
Kyakkyawar ajiya yayi mata saman sofa din,da wani irin zafi ya miqe yana
nufar inda mashkur yake tsaye yana danne da inda ta doka masa bedside lamp da
har yanzu wajen yake masa matuqar zugi.
Tun daga
yadda idanunsa suka jirkice da kuma yadda jikinsa yake wani irin shaking
hankalin mashkur ya fara dawowa jikinsa.
"Dakata!......kada ka qaraso nan wajen!" Mashkur
ya fara da qarfi shima yana qoqarin ciro bindigar dake maqale a qugunsa.
"Waye kai?!" Fu'ad ya watsawa mashkur tambaya da
sautin tsawar data sanya dukka dakin ya dauki amsa kuwa ba tare daya damu da
bindigar dake riqe a hannun mashkur din ba.
"Sanin koni wanene bazai maka amfani ba......abu daya
zan baka shawara kaman dai dazu,ka juya ka fita salin alin ka barni da
ita". Kalmar tasa ta qarshe ta sake zamantowa tamkar digar ruwan dalma
saman sabuwar fatar jariri. Ya daga qafarsa ya soma takawa da wani irin fushi
zuwa inda mashkur ke tsaye idanunsa na sake ninka rinewarsu,kai kace bai
fahimci da gaske bindiga bace a hannun mashkur ba.
"Waye kai!!!" Ya sake maimaitawa kaman zai tsaga
dakin da muryarsa yana jin wani bala'i daga saman zuciyarsa. Takowar tasa da
yadda yake durfafarsa ba wani sauran tsoro......yana tunkararsa ne kai tsaye
kaman bindigar wasan yara ce riqe a hannunsa bata gaske ba shine yake saka
dulmiya mashkur a matsanancin mamaki......mamakin da yake qarasa dauke ragowar
duk wata nutsuwa dake jikinsa yana kuma dagula masa lissafi da Kalar jarumtar
da yake hange tattare dashi.
"Ina sake gaya maka,kaman yadda ta jawoni
rayuwarta......yau ko zaka mutu sai na kwanta da matark......." Bai samu
daman qarasawa ba saboda saukr kwalbar turare saman daidai bakinsa,ta kuma
fashe a take,abinda ya bata daman yankan wani sashe na fuskarsa.......ya kuma
sanya jini soma diga.
Saukar
kwalbar a fuskarsa ya sanya bindigar subucewa daga hannunsa. Jinin daya soma
diga a fuskarsa baija hankalinsa ba fiye da faduwar bindigar daga hannunsa.
Yayi imani bashi da garkuwar data wuce masa bindigar,kuma muddin ta subuce masa
to tabbas dukkan wata dama ta subuce masa,tuna wannan ya sanyashi durqusawa ya
saka hannu yana laluben inda ta tsalle ta fadi.
Daga can
gefan gadon ya hangota,da azama da kuma sassarfa ya zura hannunsa da zummar
daukota,saidai kuma ya makara,don yana dora hannunsa akai qafar fu'ad na sauka
saman hannun nasa.
Da dukkan
qarfinsa ya take masa hannun,wani irin zafi da radadi suka ziyarceshi yana jin
kamar dukka yatsunsa biyar sun karye. Daya hannun nasa mashkur ya sanya da
nufin ture qafar fu'ad din,amma ta nan ma ya rigashi ta hanyar sanya daga qafar
tasa ya daki tsintsiyar hannun fu'ad din,bai kuma bari radadin ya gama ratsashi
ba ya sake take daya hannun da dole ta sakashi ya zare hannun daga saman
bindigar. Da qafa fu'ad ya daki bindigar ta qarasa shigewa can qarqashin
gadon,abinda ya daga hankalin mashkur kenan
"Komai zai iya kwabemin......dole na samu abinda nazo
nema koda guda daya ne cikin biyu...." Bai qarasa qulla mafitar data dace
dashi ba wani kyakkyawan naushi ya saukar masa a tsakiyar kansa.
Azaba ce
ta ratsashi tun daga tsakiyar qwaqwalwarsa har zuwa tafin qafarsa,bai murmure
ba wani lafiyayyen naushin ya sauka a kumatunsa. Qarfin naushin ya sakashi yin
baya,yayu taga taga zai fadi ya dire da qafarsa. Cikin abinda bai gaza second
daya ba yaji wani abu me yauqi da gishiri ya cika masa baki,dole ya hadiye ko
ya zubar wanda zubarwar yakejin zaifi masa,sai ya furzar din yana jin yadda
kansa ya sake qullewa da azabar data zarce har cikin bakinsa. Furzar da jinin
saman marbles din ya bada sauti,saiga haqoransa nan jere reras guda hudu da
haskensu ya bayyana cikin jajur din jinin.
Idanu
warwaje yake duban fu'ad,ya tabbatar ya masa illa ta farko kenan da har ya mutu
da ita xai tafi lahira?,zuciya ta ciyosa,ta yaya yana namiji shima haka ya
tsaya ya masa irin wannan barnar,wannan tunanin ya sanya koda yakai masa naushi
na uku ya kauce ya naushi iska,sannan kuma hannunsa ya zarce zuwa ga glass din
madubi dake daura da wajen,take ya tarwatse zuwa piece's,ya kuma samu lallausar
fatar hannunsa ya yanki inda yakeso. Cikin qasa da second daya shima jini ya
soma diga da mugun gudu a a tafin hannunsa da bayan hannun nasa,wannan shine
abinda ya baiwa.mashkur qwarin gwiwa,ya kuma Tunxura fu'ad ya sake kai masa
wani naushin ba tare daya damu da jinin da yake zubarwa ba. Ya sake samunsa
still a wuyansa,zuwa sannan qaramin fitsari ya qwace ma mashkur saboda azabar
da yaji ta sauka akan kowacce jijiya tashi. Yanke hukuncin maida martani
yayi,cikin nasa fushin yakai masa nasa naushin yans cewa
"Bari na nuna maka iya tawa bajintar" Saidai baiko
qaraso inda yake ba ya yiwa hannun nasa wani mummunan bugun da sai da yaji
qarar qaramin qashin dake riqe da tsintsiyar hannun nasa.
Wani ihu
ya kwarara don azaba,ihun da lallai inda qaramin gida ne wala'alla har jama'ar
dake farkon layinsu sai sunji......sautin ihun nasa ya samu ratsawa tsawa ta
kowacce kafa dake dakin,ta kuma isa ga kunnen daya daga cikin securities na
gidan dake on duty a daren,yaketa kuma kai kawo domin tabbatar da tsaron gidan
da amincin masu gidan.
Tsayawa yayi sosai yana son tantance daga inda qarar ya fito,a lokacin
fu'ad ya sake isa inda yake ya kuma daki gwiwarsa da qafa,abinda ya sanyashi
zubewa saman gwiwoyin nasa shima yana sakin ihu karo na biyu saboda yadda yaji
qoqon gwiwarsa kaman ya fice fit daga jikinsa.
"Zan saka kayi nadama,zakayi dana sanin abinda
kakemin......wallahi sai na d'an d'ani xumarta kamar yadda kuma kuka d'an
d'ana......saina huce fushina a kanta,sai nayi mata fata fata......" Wani
mulmulallen abu me kama da wuta yazo ya daki zuciyarsa,har baisan sanda ya sake
saka hannu yakai masa dukan daya sanya haqoransa na gaba wannan karon suka
baqunci waje ba yana wani irin huci kamar tsohon kumurci.
A
gigice ya sake fidda idanunsa yana kallon haqoransa guda biyar zube a gabansa
cikin jini,a qiyasi ya rasa haqora aqalla goma sha biyar,sha biyar suka rage
masa a baki......sai ya saki wata kururuwar data tabbatarwa security din daga
cikin gidanne.
Wayarsa
ya zaro ya fara kiran number gaggawa ta cikin gidan,saidai kiran daga parlor
hallway xuwa sassansa ya tsaya,bai kawo dakin sabreen ba saboda datse layin da
mashkur yayi. Cikin gunji duk da yadda jini yake ambaliya a bakinsa amma bai
fasa duban fu'ad dake jawo wata cable me kauri ba yace
"Saina lalata rayuwarka......sain......" Maganan
ta katse saboda wani naushin daya sake xuba masa a tsakiyar kai,take wuta ta dauke masa,sashen
maganarsa kuma ya dakata na wucin gadi,sannan ya tafi yifff ya fada akan
jininsa jikinsa yana saki,komai baya aiki illa numfashinsa dake fita a wahalce.
Da qafa
ya dakeshi ya juyashi,ya tsugunna yana sanya cable din daga hannunsa zuwa
qafafunsa,sai daya tabbatar ya daureshi sosai sannan ya fara jansa kaman mushe
ko kayan wanki yana bude dakin ya fiddoshi.
Sai daya
kawo parlor na biyu sannan ya zubeshi a tsakiya. Jijiyar kansa na wani mugun
gudu da harbawa ya qarasa gaban telephone ya fara kiran sashen tsaro na gidan.
"Yes sir......" Security din dake tsaye yana jiran
kota kwana ya fada sanda kiran fu'ad ya riskeshi.
"Ku bincika min cikin gidan nan da kewayensa.......ina
kyautata zaton akwai wani mutumin daban.....na baku minti goma kacal" Yadda yaji muryar boss din nasu a yau sai
yaji wani tsoro da razani ya kamashi,bai taba magana dasu da irin wannan sautin
dake cike da fushi da tsawa ba. Maida wayar yayi sannan ya matsa cikin hikima
ya qyasawa abokin aikinsa.
A zuciye
ya wurgar da kan wayar,sannan ya juyo yana takowa zuwa inda ya ajiye mashkur.
Zagayashi
yayi har kusan sau uku,zuciyarsa na masa wani irin tsalle a qirji,ba abinda
zuciyarsa ke gaya masa illa ya dauko bindigar ya fasa tsakiyar kansa da ita.
Numfashi yaja sosai,sai ya juya yana komawa ciki bayan tunawa da yayi da
ita,sa'annan muddin yaci gaba da zama a gaban mashkur zai harbeshi dinne abinda
yaketa qoqarin hana kansa aiwatarwa.
A bude
qofar dakin yake,wannan ya bashi damar shiga kansa tsaye. Dakin da zuwa sannan
gaba daya komai na cikinsa ya hargitse,banda fasasssun glass da kwalaben
fitilar data kwatsawa mashkur ba komai a qasan,sai wargatsatstsun kayan dake
saman dressing table dinta da suka tarwatse a qasa.
Inda take
kwace ya maida idanunsa,har yanzu tana kwance inda ya barta din,idanunsa kafe a
kanta ya qarasa gabanta. Sauka idanunsa yayi a saitin bakinta,pink lips dinta
da suka sauya launi kadan suka kuma bushe qamas,hoton yadda wiwin ta zauna akan
lips dinta ya dawo masa,wani mulmulallen abu ya tokare masa wuya,da sauri ya
ture hoton daga kwanyarsa,ya tsugunna a gabanta yana tunanin me zaiyi mata?,me
ya kamata ya fara yi?.
Sake maida
dubansa yayi ga fuskarta wadda har dogon dokin wuyanta ya bayyana,hakanan wani
sashe na kafadunta saboda saukar hijabin da ya fara samun nasarar yagawa. Sauka
dubansa ya qarayi xuwa saitin qirjinta,inda a daidai nan hijabin ya nuna
muguwat cukuikuyewar da zata gaya maka an riqe wajen ne da mugun riqo. Qirjinsa
yaji ya wani doka,yawun bakinsa kuma yaji ya dauke qaf kaman ba'a taba halittar
yawu cikin bakinsa ba. Abinda bai taba ji ba tsahon rayuwarsa yau karon farko
ya jishi......wata mummunar faduwa gaba,sannan take yaji hannuwansa da
qafafunsa sun fara rawa sakamakon tunanin daya bijiro masa. Sake xubawa wajen
ido yayi,yayin da zuciya ta fara masa imagination na hannuwan mashkur a
wajen,wani abu me qarfi ya daki zuciyarsa har sai da ya fusgo numfashinsa da
kyau,dai dai sanda yaji itama ta ja numfashin da matsanancin qarfi har sai da
qirjinta ya daga.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 59
59
Da wani irin yanayi numfashin nata ya soma fita,abinda ya
sanyashi karon farko tunaninsa yazo masa cewa asthmatic ce. Miqewa yayi yana
ranqwafawa saman kanta da nufin dagota ya canza mata makwanci duk da abinda
yakeji,yana dagata din towel din jikinta yana zamewa ya kuma fadi saman
qafafunsa.
"La haula wala quwwata illa billah" Ya furta a
sarari da wani irin bugawa da zuciyarsa tayi yana jin sautin har cikin
kunnuwansa. Wani jiri da dan qaramin duhu yaji yana mamayarsa har sai daya
lumshe idanunsa yana jan numfashi da kyau,ya tattaro dukka ragowar qarfinsa ya
hada waje daya sannan ya soma takawa da ita ya ajiyeta saman gadon.
Zamewa
hijabinta ya qarayi,santala santalan fararen cinyoyinta suka fito,ya dauke
idonsa da sauri yana jin yadda bugun zuciyarsa ya dake qaruwa,sai ya sanya
hannu yana jan hijab din yana jin zuciyarsa na qara quntata waje daya kaman an
daureta a tsakanin qirjinsa
"Why?" Ya fada da mabayyanin sauti yana jin
idanunsa na masa wani yaji yaji. Ta yaya wani zai samu hanyan shigo masa
gida?,garin yaya hakan zata faru?. Kai ya girgiza,hankalinsa bazai dauki wannan
ba.......kanshi da tunaninsa ba zasu iya karba ba. Taimakon gaggawa ya soma
bata kaman yadda sukewa anni idan irin haka ta taso. Sam ya kasa hada bakinsa
da nata saboda warin wiwin da yake tashi daga ciki,wanda yana daya daga cikin
abubuwan mayen da ya yiwa muguwar tsana.
Laluba
aljihunsa yayi,sai a sannan ya tuna da wayarsa,ya cirota a nutse yana budewa
gami da nemo number saddiq. Saddiq dinne kadai yasan bai fiya bacci da wuri
ba,shima kaman shi yake,yanayin aikinsu ya sanya sukan iya raba dare a gida
suna rage ayyuka. Bugu daya tak kuwa ya daga,muryarsa can qasa yace
"Barka da dare hamma..." Bai amsa gaisuwar tasa ba
yace masa.
"Ka nemomin Dr rubayya......please ku kawota gida yanzu
if possible"
"Subhanallah...waye baida lafiya hamma?". Rasa
amsar ma da zai bawa saddiq din yayi,sai kawai yace masa
"Ba wani abu bane can.....just kayi sauri ku
qaraso".
Sauke
wayar saddiq yayi yana duban farouq dake zaune a gefansa,wanda tunda ya daga
wayar yaji da waye suke waya ya maida hankalinsa wajen duk da idanunsa suna kan
system dinsa yau din yana sashen su
saddiq dinne,don shima aiki gareshi sosai,sun samu sabon iri da sukeson su fara
gwadawa manoma da manyan manoma da 'yan kasuwa,yanaso yayi settling na komai
kafin ya kwanta,charger dinsa na system dinsa tayi masa tutsu,dole ya shigo ya
karbi ta saddiq din ya jona gudun kada tayi shutting down.
"Lafiya yace maka ba?" Farouq ya fada kansa tsaye yana duban saddiq.
Daga masa kai saddiq din yayi,sai farouq din ya soma tattare ayyukan nasa waje
daya ya killace yana cewa
"Ka kirata kace zamu biyo mu dauketa......fu'ad bazai
taba gaya maka worsening na komai ba indai shine". Ya furta yana saving
ayyukan da sauri cikin aikin nasa,wannan ya sanya saddiq shima ya soma qoqarin
kiran nata.
Sai daya
ajiye wayar saman bedsheets dinnan sannan ya lura da hannunsa da har yanzu yake
tsatsafar jini. Radadin dake cikin zuciyarsa ya danne wanda yake ji a
hannunsa,shi yasa sam bayajin komai a hannun nasa. Idanunsa ya sake mayarwa
kanta,sai kawai ya samu kansa da miqewa yana daukan wayarsa,ya daidaita iskar
dakin saboda gumi daya gani saman goshinta ya qara hasken qwan dakin sannan ya
fara takawa cikin takatsatsan gudun kada ya taka wani abu ya soma fita a dakin
yana komawa parlor.
Tun bai
qarasa ba ya hangesu sun cika hannunsu da wani baqin kakkauran matashi wanda ke
sanye da baqaqen kaya full dress,tun daga hula riga zuwa wandon jikinsa. Iya
riqon da sukayi masa kadai zai gaya maka yadda ya matsu a hannunsu.
Ci gaba
yayi da takowa yana karantarsa,duk wani alamu dake nuna tashin hankali da
rudani sun tabbata a fuska da jikinsa.
"Sakeshi" Fu'ad ya fadi yana jin hatta da security
din gidan suma a yau bazasu tsira a hannunsa ba. Gaban mashkur ya qarasa ya
zauna saman kujerar falon
"Ku zaunarmin dashi a nan" Ya fada yana musu nuni
da gefan mashkur din. Wani mugun duka sukayi masa wanda ya sanyashi zubewa ba
shiri yana fasa qara.
"Ku jirani a waje" Fu'ad din ya fadi yana qoqarin
hana jinin dake diga a hannunsa bata sofa din da yake kai.
Kallon
fu'ad kawai matashin yakeyi,yana jin yadda kashi da fitsari gaba daya suke
neman kufce masa,saidai kuma yasan babban kuskure na gaba da zaiyi shine ya
saki fitsari ko kashi a wannan kyakkyawan falon. Zai iya cewa a tarihin
rayuwarsa kaf.....a tarihin manya manyan laifukan daya aikata a rayuwarsa bai
taba cin karo da mutumin da yayi masa kwarjini irin muhammad jadda ba. Yana
zube a gabansa yana jira yaji koda wata kalma daya daga bakinsa amma ko qwayar
idanunsa bai daga ya kalleshi ba bare ya sanya ran wata tambaya zata biyo
baya,ta goge jinin hannunsa kawai yake da lallausar tissue din daya ciro a
tissue box din dake gefansa.
Bawai yayi
hakan bane saboda ciwon yana da muhimmanci a rayuwarsa ba.....a'ah......yayi
shuru ne saboda a yanzu babban muradinsa shine yayi mummunan lahani a garesu da
babu me iya gane fuskokinsu,duk kuwa da cewa ko a yanzun fuskar mashkur ta haye
tayi kumburin da dukka wata halittar fuskar ta sauya daga asalin yadda
take,abinda yake sake sanya tsoro me yawa kenan ga zuciyar hanzari.
"Don Allah me gida....
Kayimin rai,ka tausayamin me gida......don girman Allah". Kalaman
hanzari kenan wanda ya gaza jiran yaji abinda fu'ad din zai fada. Cillar da
tissue din yayi,sannan ya daga idanunsa da har yau launinsu bai koma daidai ba
ya aza akan hanzari
"Waye ya gayyato ka?,duka ku biyun kuma waye ya aiko
ku?' Tambayoyi guda biyun da a wajen hanzari suke masa kamanceceniya da
tambayar kabari ga kafiri a ranar daren farko
"Shine!.....shine wallahi" Hanzari ya fada yana
nuna mashkur dake yashe a qasa har yanzu bakinsa na fidda jini.
A yadda
mashkur din yake yayita qoqarin murgina kai ya kalli koda idanun hanzari ne
amma ya kasa ballantana ya fadi wata kalma da zata zama kariyar kai a gareshi.
Kiran sunan mashkur da hanzari yayi shine abu mafi sauqi.....mafita mafi sauqi
a gareshi akan ya ayyana ko ya ambaci daga inda ainihin kwangilar aikin ta
fito,wanda fadin daidai yake da fadawar mutanen da suka jibanceshi da yawa
cikin masifa da bala'in da baisan ranar fitarsu ba......gwara ya danganta
kanshi da mashkur.....kusan yasan waye.....kuma koda yafi haka hatsari yazan
bazai zartashi a hatsari da hatsabibanci
ba.......koda ya zartashi yasan bazaikai mutanen da suka qirqirar da aikin ba.
"Kana da masaniyar cewa maqabarta ka kawo
kanka?......nan da kake zaune Motuare ce?!" Ya furta da sautin da hatta da
mashkur sai da yaji kaman an buga masa guduma still saman ka bayan masifar
azabar da yake ciki.
Firfito
da idanu hanzari yayi.......yayi gwagwarmayar rayuwa da yawa......ayyukan
rashin imani bila'adadin......ya shiga komar Jami'an tsaro masu yawan
gaske......da wannan kadai yana iya gane mutum da muhallin da ake magana ta
gaske kai. Salati ya debo wanda ya manta rabon da ya ambaceshi a bakinsa,sallah
kanta ba'a maganarta sam bars aje ga gurbin xama ayi wani xakiri ko tasbihi.
"Zip your mouth!" Fu'ad ya furta da fushi
"Ko burbushinku ba zaa samu ba.......daga yau ba zaku
sake gigin tsallaka gonar wani ba"
"Innalillahi wa inna alaihi....." Ya jiyo muryar
daga can gefe tana fada cikin maqyarqyata saboda tsananin tsoron data shiga.
Duk tsawarsa guda daya sai taji kamar ana finco mata hantarta tare da qoqarin
bintiko zuciyarta daga muhallin da take a dashe.
Waiwayawa
yayi yana mamakin wanda ya rage a falon bayan ya bada umarnin kowa ya fice.
Zuwaira ce tsaye yana rawar dari kamar wadda ruwan da yayi saura har yanzu yake
sauka kadan kadan a kanta ya qare.
Sulalewa
tayi a wajen tana jin wata razana tana saukar mata,idanunsa sun mata wani kaifi
da bata da juriyar daukarsu. Yadda yake magana ga duk wanda yake falon zai
tabbatar abinda yake fadin zai aikata ne. Ba wasa ko digo cikin kalamansa.
Itakam a yanzun ina ta shirya mutuwa?,a irin wannan qadamin da take lissafin
sake inganta rayuwarta da jin dadin da yake hange daga wasu?,itama ta samu ta
dandala ta baza nata ikon da isar kafin zuwan randa zata bar numfashi?,shine
tun a yanzu a gabanta wannan manya manyan alkaba'in yake faruwa?.
Idanu
ya zuba mata da kyau yana qoqarin karantarta,saidai kuma kafin yayi nisa an
murza pivot door din daga can wajen falon an shigo.
Farouq ne a
gaba,Dr rubayya a tsakiya sai saddiq daga bayanta .
Shigowarsun kawai cikin falon....hada idanunsa da farouq sai yaji kaman
an janye wani kaso na bala'i da masifar da yakeji tana kunnuwa cikin zuciyarsa.
Wani irin tashin hankalin da baisan dame zai fasaltashi ba.
Dr
rubayya na qoqarin gaidashi.....saidai shi hanyar hallway din kawai yake nuna
mata da yatsa ba tare da yace komai ba,sai itama bata sake magana ba kasancewar
halinsa ba baqonta bane,ta wuce da kayan aikinta kai tsaye zuwa hanyar.
"Ka leqa ka kiramin saddam......suzo.su biyu" Yace
da saddiq da rinannun idanunsa da suka sanya saddiq shan jinin jikinsa bayan
mutane biyun da ya gani zube a wajen. Shima baice komai ba ya juya yana fita
daga falon.
A nutse
farouq ya isa gabanshi,ba tare da yace komai ba duk da idanunsa na nuna kaduwa
da abinda yake gani ya kama hannunsa yadan juya sannan ya saki
"Dude.......wai meke faruwa?" Ya qarasa maganar
yana saka idanunsa cikin na fu'ad din.
Janye
nasa idon faud din yayi daga na Farooq yana hadiye wani abu me tauri daga qasan
zuciyarsa. To shi ta yaya ma zai fara bada wannan mummunan labarin?,yace
meye?,yace masa wiwi ya kamasu suna sha har ya bugu asthma dinta ya tashi?,ko
yace masa ta gayyato maza cikin gidan sun bugu sukaso gwada mata qarfi?,ko kuma
yace sharri akayi mata?,barayi zai kirasu ko 'yan fashi?,zaice sun hauro masa
gida ne?,gida ma irin nasa?,gidan da ba wani abu daya isa ya shiga ko ya fita
cikinsa saida cikakken tsaro da kulawar security......waye hankalinsa zai
dauka?,waye zai yadda da wannan labarin?.
"Ka kwashesu ka sakaminsu a cage din dogs
dincan....." Ya fada yana miqewa sanda hanzari ke qoqarin riqo rigarsa a
gigice
"Kayi mana rai oga.....ka hukuntamu duk yadda kaso,amma
kada ka hadamu da karnukan can.....wallahi ko kafin safiya sun gama cinye
namanmu oga...." Yayi magana fitsarin da yaketa son riqeshi yana kubce
masa. Tun shigowarsu gidan yanayin karnukan ya tabbatar masa sunsha banban da
dukka karnuka daya sani. Basu bi ta gefensu ba.....amma wani abun mamaki yadda
suketa haushi ya ninku,yana ganin sanda me kula dasu ya dubasu,ya kuma yiwa
security na gidan magana suna sake bincike sassannin gidan amma basu ga komai ba
saboda sun shigo ne ta hanya mafi sirri da samun tabbaci,kuma sun samu mafakar
da binciken me bincike bazai taba kaiwa nan ba.
"What are you waiting for?!!!" Fu'ad da dama
dukkaninsu suma a cike yake dasu ya fada a tsawace,ba shiri suka
durfafesu,hanzari yayi wuf ya kama qafarsa yana sake roqonsa.
Wani
wawan duka yakai masa da qafar daya sanya hanzari zubewa warwas,basu saurara
masa ba suka sungumeshi suka hada da mashkur da tsabar razana ya kasa
magana,sai yakejin kamar qiyama ce zata tashi. Yasan illar karnukan,don sanda
yake sharafinsa ya ajesu a gidansa sun kusa guda biyar,hakanan baisan adadin
mutanen da ya sanya suka yagalgala ba.
"Karku sakasu a cikin cage din.....ku ajiyesu dakin
kusa dashi" Ya basu umarni sanda suke kicin kicin fita dashi.
"Okay sir" Suka amsa masa sanin wayeye farouq
wajen boss din nasu. Shi daya ne duk duniya yake tada hukuncin da fu'ad yayi
kuma ta zauna ba tare da haufi ko kankare ba,shi yasa suka karba umarnin nasa
kaman yadda ya basu.
Yadda yaga
komai yasan ba lafiya ba.......yadda kuma yaga yanayin hannunsa da gidan ya
tabbatar akwai gagarumin wani abu daya faru.....uwa uba wani kwantaccen fushi d
yake gani a fuskar Fu'ad ya sanar masa akwai matsala ko a yadda ya fita a
fusace.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 60
60
Tun bai
qarasa inda yake hangen security na gidan daya tara ba yakejin muryarsa dauke
da fushi me nauyi. Fada yake da duka zuciyarsa da jikinsa ma,sam kaman ya manta
dare ne a yanzun......daren ma kuma irin daren da akayi ruwan sama ya dauke
wanda ke ninka kowanne dare a shuru da daukewar sawu.
"Your services are no longer required......you were
fired!"
"Ya salam" Farouq ya fadi,abinda yaketa sauri ya
dakatar dashi kenan. Fushinsa na yau yanata bashi mamaki,sau tari shike daukan
abu da sauqi......yawancin lokuta shike jan qafa da jan lokaci akan abubuwa
irin wadannan......yana bin komai da lura a kuma tsare,har sai ya tabbatar
dashi a inda ya dace.
Kasa cewa
komai yayi,don su kansu ma'aikatan da security din dake on duty a daren kowa
cikin matuqar tashin hankali yake. Yadda suke roqonsa da mabanbantan harsunansu
dukka sai suka bawa farouq din tausayi. Kowanne a cikinsu idan ka dubi fuskarsa
ya kadu da hukuncin ba zata na me gidan nasu.
"Calm down.....ya isa" Farouq ya isa gabansu yana
fadi bayan komawar fu'ad din ciki. Hankulansu kuwa suka bashi cikin mutuwar
jiki hankali a tashe.
"Ku kwantar da hankalinku.....kowa ya koma bakin
aikinsa kafin wayewar gari......but,ku sake tsaurara kula kafin muga abinda
hali zaiyi.
Duk da
bawai tabbaci ya basu na cewa ya dawo dasu bakin aiki ba amma hakan ya faranta
musu. Sun sani babu wani guri da zasu samu walwalar rayuwa da 'yanci da albashi
me tsananin azabar tsoka kaman gidan jadda.....salary yake musu na kece
raini......irin salary din da sunyi imani ko a villa suke aiki babu me biyansu
irinsa. Uwa uba ga ihsani da alkhairi da suke samu kowanne lokaci,wanda ya
kusan kamo abinda ake biyansu albashin aikinsu. Da yawansu suna jin idan ba
gidan Muhammad jadda ba babu a inda zasu iya aiki,shi yasa suke riqe da aikinsu
fiye da yadda ma yake tsammanin zasuyi.
A
parlor ya sameshi a tsaye kaman wanda zama ya gagareshi. Baice masa komai ba ya
taka inda yake tsayen ya riqe hannunsa sannan ya wuce dashi,suka ratsa hallway
din suka saura samansa.
Saman
monotti sofa ya zaunar dashi,ya taka da kansa zuwa shiyyar da aka tanada don
ajjiye first aid box,don kusan yasan komai na gidan tunda shine ma tsara yadda
zai kasance din.
A
gabansa ya zauna,ya bude box din ya ciro cotton wool da spirit ya tsiyaya ya
fara goge masa ciwon. Sai a yanzu yake danjin radadin da hannun ke masa amma
kadan kadan,saidai har yanzu abinda yakeji a zuciyarsa ya dara wanda ke a
hannunsa.
"Ko meye da sauqi ake daukarsa......da irin wannan
temper din da kake ji a ranka komai fa bazai warware ba" Farouq ya fada
yana qarasa goge masan,har yanzu kuma yana mamakin abinda ya birkita nutsatsen
mutum irin fu'ad din. Duk da ya sani,ba abu bane me sauqi a keta alfarmar
gidanka a shigo maka ba......to amma kuma yadda yasan fu'ad zai iya cewa tun
wani zamani can daya shude rabon da yaga wannan attitude din a tattare dashi.
Wayar tafi
da gidanka din dake falon,wadda ke ajiye kusa da console mirror din parlor din
ce ta dauki tsuwwa. Saddiq dake zaune daga gefe dukka jikinsa a mace ne ya
dauka
"Daga hallway bedroom ne"
"Ka daga ko Dr rubayya ce" Farouq ya fadi sanda
yake tattare ragowa ragowan audugan da yayi amfani dashi. Maganan second goma
sukayi kwata kwata,ya sauke wayar yana duban farouq
"Dr ce ke magana.....tace ta kammala......amma wai
tanason ganin hamma".
"Ka gaya mata tayi abinda ya dace kawai basai nazo
ba" Ya fada yana jin ciwon kan daya tashi da jin dadin ya sauka yana son
dawowa. Kai farouq ya girgiza yana dubansa,muryarsa a qasa qasa yadda saddiq
bazaijishi ba yace
"Dole kaje tunda tace kaje din.....dole saika gwadawa
duniya halinka?" Idanunsa da har yanzu basu koma fararensu ba ya watsawa
farouq,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya tsuke bakinsa. Kamar bazai tashi ba
kafin ya miqe yana kiran sunan Allah,wanda motsawar bakinsa ne kadai zaisa gane
hakan.
A hankali
yake sauka zuwa qasan,saidai duk sanda ya kusanci dakin sai abun daya faru
mintunan baya yayita dawo masa. Bama irin idan ya tuna ba komai a
jikinta......daga ita sai towel sai hijab,sai yaji tamkar iskar da yake shaqa
tayi masa kadan. Su biyu a daki tana daga ita sai shi.....su biyu a dakin da
babu cikakkiyar sutura a jikinta......gaban hijabinta yasha cukuikuiya?.....duk
sanda ya kawo nan sai ya lumshe idonsa saboda ji yake kaman an dauka adda an
kafta masa sara a tsakiyar kansa.
Handle
din ya murza ya tura ya shiga da sallama saman labbansa. Ma'u dake gyara dakin
ta dago daga kwashe sharar data gama,ta rusuna tana gaidashi duk da dare
ne,sannan ta kwashe dustpan da vacuum cleaner din tayi waje dasu.
Haka kawai
ya samu kansa da bayason kallon fuskarta,don ba abinda yake tuna masa sai a
yanayin data fado jikinsa.
"Numfashinta ya koma normal,kuma yanzun haka bacci take
me kyau.....ko da wanne lokaci ma zata farka abinta........amma please
sir......koda asthma dinta baiyi tsanani ba at least ya kamata ace an ajjiye
mata in healer.....and ya kamata ta dinga kula da gujewa ta'ammali da abubuwa
masu hayaqi da yawa". Kai kawai ya
jinjina ma Dr rubayya
"Allah ya qara afuwa yasa kaffara.......idan kuma ana
buqatar wani abun.....am ready in sha Allah,koda yaushe kuka kirani am
available for your needs".
"Thank you" Ya fada can qasa da kalar miskilancin
nan nasa da ba wani baqon abu bane a wajenta.
Already
kafin ta fita ya kira saddiq ya gaya masa gata nan su maidata gida,yana kuma
sauke wayar kiran farouq ya shigo masa
"Mu duka mun wuce gida,but.....na kira wasu daga cikin
guards dinka an qara akan na cikin gidan......in sha Allah kome zaiyi
daidai......but please please.....karka dauki doka a hannunka akan mutanen
nan". Farouq ya fada cikin narke murya. Ya dade da sanin halinsa,muddin
ranshi yakai qololuwar baci irin wannan bai iya hukunci ba.
"Kaji?" Farouq ya sake maimaitawa jin yayi shuru
baice komai ba.
"Alright" Ya fadi a hankali kamar wanda maqoronsa
ke masa ciwo yana gintse kiran.
Iska ya
sake furzarwa daga bakinsa,daga jikinsa har zuciyarsa babu wani abu dake masa
dadi,sai ciwo kawai.....wani irin ciwo me radadi a gangar jiki da zuciyar.
Karon
farko ya maida dubansa saman fuskarta,wanda daidai nan idanunsa suka hangar
masa wayar dake gefan pillow dinta. Wani abu ya tsarga masa har yatsun
qafarsa,sai ya miqa hannu ya dauko wayar.
Tabbas
itace wayar daya gani a hannunta shekaran jiya.....wayar da baisan yadda akayi
taxo gidan ba ta kuma zama mallakinta har take amfani da ita.
Jujjuya
wayar yayi sosai yana qare mata kallo,sai ya latsa malatsin gefe haske ya
kawo,ya sanya dan yatsa ya shafi fuskarta take ta bude.
Bangaren kira ya shiga ya soma dubawa,kirane da numbers barkatai wanda
kusan dukansu babu suna. Ci gaba yayi da dubawa har zuwa kan date din shekaran
jiya wanda wata number data qare da 01 itace number qarshe da aka amsa kira da
ita.
Kai ya
jinjina a hankali yana komawa bangaren saqonnin karta kwana wato sms. Dunqule
hannunsa yayi da kyau yana ci gaba da duba saqonnin da suka shigo da
mabanbantan numbers suma,wanda dukkaninsu suna dauke ne da nau'ikan kalaman
soyayya iri iri,saidai kowanne saqo ba wata amsa guda daya da ta maida masa.
Kasa ci
gaba yayi da dubawa saboda yadda dukka jikinsa ya dauki tsuma,sai ya kashe
wayar ya jefata aljihunsa sannan ya miqe yana dubanta da wani zafin zuciya.
Takawa ya soma yi a hankali,har cikin jiki da zuciyarsa yana jin bazai iya zama
da ita na daren gaba daya ba a daki daya,sai daya hau saman sannan ya kira
sashen ma'u yace taje ta kula da ita,baima aje wayar daidai ba ya dora kansa a
hankali saman sofa din yana fidda numfashi kansa kaman zai fado.
Tunani ne
iri daban daban suke barazanar tarwatsa masa kai,ya rasa da wanne zaiji?,da
wanne zai fara?,meye daidai cikin hasashensa meye ba daidai ba?,ganin yana
neman rasa nutsuwarsa cikin qasa da minti talatin,sai ya miqe a gaggauce ya
jawo earpiece ya toshe kunnuwansa da karatun qur'ani,abinda ya sanya duk abinda
yakeji ya soma sauka a hankali,nutsuwarsa ta soma daidaita,nauyin da yakeji a
qirjinsa da zuciyarsa suka soma raguwa,sannu a hankali ya maida idanunsa ya
lumshe wani bacci yana yin awon gaba dashi a cikin falon.
*_TO ASUBA TA GARI......SAIDAI KUMA KO DAME SAFIYAR RANAR
ZATA WAYE MUSU DASHI?_*
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 61
61
Tun daga
sanda ta farka bata samu wata nutsuwa ko kwanciyar hankali ba sai bayan data
tabbatar ba wani abu a jikinta da mshkur din ya samu kaiwa gareshi
"Allah na gode maka.....Allah na gode maka" Ta
dinga maimaitawa cikin bandaki hawaye na layi bisa kuncinta.
Wanka ta
sakeyi dab da asuba da ruwa me dumi sosai,koda ta fito ma'u ta ajiye mata wasu
kayan da zata saka. Har zata fita ta bata waje ta canza kayan tace ta
zauna,tana jin ma'u kamar jininta,tana jin gamsuwa da dabi'un ma'un. Mutum ce
me kamun kai sosai,kawaici gami da kauda kai daga kan komai da bai shafeta ba
ko kuma ba'a sanya da ita ba,wannan yana daya daga cikin dabi'un da suka sake
sanyawa hankalinta ya kwanta da ma'un.
Ko data
shirya hijabi da abun sallah ta buqata,ma'un ta bata ta koma ta zauna. Ta
shimfida ta tada sallar. Isha'in da bata samu yi ba a dazu ta bayar,sannan ta
dora da shafa'i ta kuma zarce da nafilfilun da ita kanta batasan adadin guda
nawa tayi ba. Sam sam bata jin koda digon bacci a idanunta,samun kanta tayi da
tsananta addu'o'i masu yawan gaske cikin sallarta. Idanunta sun zubda hawaye
masu yawan da adazu bata zubda su ba,jikinta yayi wani mugun sanyi zuwa bayan
wani lokaci,qafafunta sunsha tsaiwar da zama kawai take da buqata,saita zauna
din tana irga tashihi da yatsun hannunta.
Tuna abinda
ya faru da ita dazun kawai razani yake haifar mata,yayin da kwanyarta tayi
nisan zango wajen tunanin waye yake da alhakin zamewa mashkur jagoran daya
risketa har cikin dakinta.
Tayita
qoqarin tuna abinda ya faru bayan zubewarta amma ta kasa tuna komi......abinda
kawai take iya tunawa sanda ya shigo dakin da fadawa jikinsa da tayi tana neman
tallafi cikin kubcewar numfashi.
Kiran farko
dana biyu duka akan kunnenta akayi shi,bayan sauran masallatai sun tada tasu
sallar sai itama ta miqe ta bada nata faralin.
Ci gaba
tayi da zama still a wajen......tana tsammanin wai ko zataji bacci amma babu
shi ba alamarsa. Wani firgici takeji har tsakiyar zuciyarta wanda bada taimakon
hailala da takeyi zuwa yazu batajin zata iya zaman dakin ma gaba daya.
Sanda gari
yayi haske ta kalli ma'u dake gefe a zaune,qaunar ma'un da darajarta yana
qaruwa cikin idanunta. Sam tana lura da ita batayi bacci ma itama
"Kije ki huta ma'u.....baki samu bacci ba kema"
Sabreen ta fada muryarta a karye da wani irin sanyi da bata taba yi ba. Dan
murmushi ta saka tana gyara zamanta
"Ba wani damuwa.....bai kamata ai na barki ke kadai
ba......saidai ko idan kina buqatar cin wani abu?" Kai sabreen ta girgiza
mata
"Bana buqatar komai.....kije kidan rage baccin ma'u ki
kintsa......kya dawo daga baya,bana buqatar komai". Kai ta jinjina sannan
ta miqe tana mata sallama ta fice.
Qarasa
shafa addu'o'inta tayi ta miqe tana son jin qara watsa wani ruwan dumin ko
jikinta zai qara yi mata dadi. Wannan karon saita taka zuwa bakin qofa ta murza
lock dake jikin qofar kamar me tsoron maimaituwar abinda ya faru daren jiya ya
sake faruwa,sannan ta juya a hankali tana wucewa toilet din.
Tare dasu
Jordan da farouq ya kawo suka wuce sallar asuba,wadda duk da qarancin baccinsa
hakan bai hanashi samun sallar asuba ba. Tun daga fitarsu zuwa dawowarsu su
kansu sun fahimci sam yau ba'a mode dinsa yake ba. Idan kai baqo ne a rayuwarsa
ba lallai ka fahimci lokutan walwalarsa dana bacin ransa ba......kawai zai zame
maka kaman daya ne saboda rashin fara'a da bai da ita......amma gasu da suke
tare dashi tsahon shekaru,suna iya fahimtar walwalarsa da akasinta dukka
qarqashin dabi'arsa me kamanceceniya da juna.
"Mu qarasa ciki jordan" Yace da jordan din bayan
sun shigo ainihin farfajiyar gidan. Ba musu ya takewa uban gidan nasa baya suna
takawa zuwa dakin da ya bada umarni a ajjiye masa su.
Duk da
kusan dabi'ar gidan shuru ce,amma a yau tana jin gidan ya sake zama shuru gaba
daya. Hakan yake don tun daga gate din farko na gidan zakaji gidan yayi wani
mugun shurun da ko tarin wani babu. Zaka rantse da Allah mutuwa akayi cikin
gidan saboda yadda kowa ya sake shiga nutsuwarsa. A mugun kasalance da wani
irin rashin kuzari ta shirya cikin atamfa dinkin plain zani da riga,wanda babu
wani ado da akayi mata ko guda daya face qwarewa da gwanancewar dinki daga
telan nasu.
Dare daya
amma gaba daya ta fada,tayi wani rama da ta bayyana har a qasusuwan
wuyanta,fuskarta tayi fayau,inda ya fashe a jiya sai yanxu ya fito sosai ta
ganshi. Tsaga ce 'yar siririya bame yawa ba,fuskarta tayi wani fayau kaman
wadda tayi zazzabin dare. Koda ta kalli fuskarta gaba daya sai taji zuciyarta
ta karye,ta koma da baya a hankali tana sake tuna yadda mashkur ya fado mata
daki.
Duk wanda
wani bala'i ya sameshi kalleshi kawai......ashe fiye da haka matan da ibtila'in
fyade ya fadawa suke ji?. Raurau idanunta sukayi,can qasan ranta sai ta samu
kanta da godewa Allah da ya bata ikon tsame mata da yawa da suka fuskanci
ibtila'i irin wannan zuwa sauyin rayuwa daya kawo musu sassauci da rangwame.
Qasa
tayi da kanta,daidai lokacin da taji ana mata knocking. A nata zaton ma'u
ce......wannan ya sanyata kanta tsaye ta nufi qofar ta kuma bude tana bada
hanya,saidai a maimakon ma'u anni ta gani,gefanta kuma amna ce tsaye tana riqe
da purse din annin.
Wani irin
nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,tayi qasa da kanta tana basu
hanya.
"Ai jikinma yayi kyau.....basai mun shigo har uwar daki
ba,mu koma falo mu gaisa a can" Anni ta fada cikin dattakon nata tana
juyawa da nuna alamu na surukuta
"Da kun qaraso din dai anni" Sabreen ta fada adan
kunyace da nufin tsaida annin
"A'ah qaraso nan din sabreen.....ki fito a hankali
karki gaggawa" Anni ta fadi tana qara yin gaba,amna da abun yaketa burgeta
takeson tayi tsokana nata binsu da dariya.
Dukka
hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana qare musu kallo cikin quntataccen
qaramin store din ajiyar kayan aikin sola dana engine din gidan idan ya samu
matsala. Daga daren jiya zuwa yau idan
ka kalli fuskokinsu sai kace basu bane,kada ma mashkur daya kwana a daure yaji
labari.
A duk
sanda ya kalli mashkur din shi kadai yasan abinda yakeji......har yanzu
maganganunsa sunqi daina amsa kuwwa a kuwwa a kunnensa.......har yanzu ya gaza
daina tuna sunyi gamayya a daki guda qarqashin abun shaye shaye guda.
Taku biyu
yayi y is gaban qofar yana duban mashkur din
"Waye ya aikoka?,ko kaine ka aiko kanka da kanka
makasarka?" Kai ya mirgina alamun eh.....koda meye zai faru bayajin zai
iya buda baki ya fallasa wannan sirrin.......sirrin da idan har ya bari ya fita
to tabbas shima ya gama jin dadin rayuwarsa har gaba da abada koda yayi escape.
Abu ne bisa sharadi da yarjejeniyar da aka qullata bisa masaniya da kuma abinda
zai faru a qarshe.
Sosai fu'ad
ya zuba masa idanu yana karantarsa,yanayinsa ya tabbatar masa bai shirya fadin
gaskiya ba duk da baqar wahalar da ta nuna kanta a tattare dashi. Bayajin zai
iya wahalar da kansa tsaiwa yana batawa kansa lokacin tambayarsu,yana da
wadanda zasu tafi masa dasu har su gane kuskuren da suka tafka na shiga gonar
da ba nasu ba. Hannu kawai ya daga ya yiwa Jordan alama,Jordan din ya jinjina
kai sannan ya juya yana fita hanyar waje da sassarfa irin ta majiyin
qarfi,cikin qasa da minti biyar sai gashi sun shigo da wani.
Kakkauran mutum ne,me qiba da
madaidaicin tsaho,yana da baqar fata data haska sosai cikin color din uniform
din 'yan sandan dake jikinsa. Maqale da jikin rigar rubutun sunansa ne
S.nuhu,wanda iya rank dinsa zai nuna maka cewa shine commissioner of police na
jahar gaba daya.
Salute na
juna sukayi shi da fu'ad din,sannan yace
"Yallabai yace idan da damuwa ayi gaba dasu" Kai
fu'ad ya jinjina yana baro jikin qofar yana takowa a hankali gami da dubansa
"A wuce dasu a ajjiyemin su,har sai zuwa sanda na
buqacesu". Kai s nuhu ya gyada cikin girmamawa,daga yanda fu'ad yayi
maganar ya gama fahimtar komai. Suna girmamashi kaman yadda yake girmamasu,tun
daga can copral har zuwa matakin qarshe na samansu,wannan ya sanya basuyi qasa
a gwiwa ba suka bashi kyautar jami'an tsaro cikin mutanensu,mutum ne me qoqarin
kiyayewa da mutunta doka. Yana da qarfin mulki dana dukiyar da zai iya komai da
yaga dama musamman a yanayi irin na qasarnan da zaka iya komai ba komai bane,amma
baya yin hakan,komai din yana qoqarin ganin ya azashi akan mizanin daya dace.
"Don girman Allah ka taimakeni.....kayimin
sutura.....yallabai ni na fadi gaskiya,na fadi gaskiyata......iyakar gaskiyata
kenan". Hanzari ya fada yana hade Hannayensa waje guda yana kallon fu'ad
da tuni ya soma wucewa xuwa cikin gida.
Ko muryarsu
bayason ji bare yakai ga kallon fuskokinsu,don haka baiko waiwayo ba bare ya
saurareshi. CP s.nuhu ya daka masa tsawa
"Miqe muje......ku daukeshi ku samin a mota,mutanen
banza kawai......banda ma me jadda din kuka samu waye kamanshi da zaku keta
masa haddin gida ku shiga ku wayi gari haka da sauran lafiyarku?,ba a nan zamu
gane gaskiyar taka ba......muje don ubanka" Cp ya fada shi kansa abun yana
masa takaici.
Sam baisan
da zuwan annin gidan da safen ba,don haka kanshi tsaye ya shiga falon
hankalinsa yana ga samanshi. So yake ya isa ya kulle kansa don baya buqatar
ganin kowa kaman yadda bai buqatar hayaniya ko dogon magana sam sam. Saidai
yana sanya qafarsa a falon yaji muryar annin sanda take fadin.
"Allah ya qara lafiya......yasa kaffara,saiki dinga
kula da jikinki da kyau,Allah ya inganta". Murna ta kama amna,duk yadda
taso cinye maganar amma sai data fito
" Anni......wai.....wai hamma shima ya kusa zama
daddy?".
"Ungo nan" Anni ta fada tana watsa mata yatsunta
biyar,saita saka hannu ta qunshe bakinta tana dariya.
Shikam
daga shi har sabreen dake zaune daga gefe maganar tazo musu a wani irin ba
zata.
"Allah ya inganta?....zama daddy?,wata qaryar ta gilla
musu kenan?" Ya fada qasan ranshi yana yamutsa fuska gami da watsa mata
wani irin kallo duk kuwa da cewa yana nesa kadan dasu,sannan dukkansu ba wanda
yasan ma ya shigo parlor din. Kai ya jinjina wani abu yana tsaye masa a wuya
"To yaushe tayi cikin?" Yaji tambayar ta taso daga
ransa,take yaji kansa ya qara masa wani nauyi saboda wani tunani da yazo ransa.
Dukka
juriyarsa da yakejin kamar tana sulalewa ya tattaro yana sake maimaita
sallamarsa,suka daga kai dukansu suna amsawa banda sabreen da tayi qasa da nata
idanun tana jin sam sam bata sha'awar dubanshi.
Gefan anni ya
zauna kaman yadda ya saba a gida,duk sanda zai iso gabanta gefan ta nan ne
wurin zamanshi. Tuni amna ta kama kanta tana gaidashi cikin tsoro,don tasan zai
wahala baiji abinda ta fada ba.
"Ina kwana?" Sabreen ta samu kanta da fadi duk da
bata dubeshi ba,haka kawai takejin wani irin nauyin anni.
"Lafiya qalau.....ya jikin?" Ya furta a dake yana
dan duban fuskarta kadan wajen daya lura a jiya ya fashe,baiga komai ba don ta
rufe wajen da dan kwali,sai ya dauke dubansa daga kanta zuciyarsa tana masa
zafi.
Ba abinda ya
hanga saman fuskartata sai guntuwar wiwin daya gani jiya a bakinta,zuciyarsa ta
sake matsewa,baya jin zai samu wani nutsuwa a zuciyarsa muddin bai samu
cikakken bayani abinda yake faruwa ba ko kuma ya farun.
Hankalinsa
ya maida kan annin ya soma gaidata cikin nutsuwa da girmamawa. Yaji dadin yadda
farouq bai daga mata hankali ba ya gaya mata abinda ya faru a gidan ba jiya da
daddare,yadai gaya mata kawai sabreen dinne bata da lafiya
"Allah ya qara lafiya.....sai ka kula da ita
sosai.....inajin idan zai yiwu ma nabar amna a gidan,don a yanayin mace irin
haka zaman kadaici qara miki ciwo kawai yakeyi". Dan satan kallon anni
yayi,ya fuskanci tunda ta zauna a wajen kawai kallon me ciki take yiwa sabreen
din,inda anni tasan cakwakiyar da yake ciki zama zatayi tayita masa kuka.
Kwata
kwata a birkice yake kan lamarin,kusan komai nema yake ya dagule masa,yana jin
kamar kwanyarsa ta daina aiki yadda ya kamata. Ya lumshe idanunsa yana jin
ciwon yadda mahaifiyarsa ta xama silar qulluwar alaqa tsakaninsa da yarinyar da
kullum munanan boyayyun halayenta sake bayyana sukeyi.
"Ashsha......da kinyi zamanki ai,ina ke ina hidima damu
ke da ba cikakkiyar lafiya gareki ba?" Anni ta fadi sanda Sabreen din ta
fito daga kitchen ta ajiye mata tray dake dauke da spicy black tea soyayyen
qwai da kuma farfesun kan rago wanda ta yi tun shekaran jiya waccan amma ta
kasa ci,kasancewar ita din cin abinci ba damunta yayi ba. Zataci din amma
gutsul gutsul kamar na dan qaramin yaro,shi yasa ko yaya ita ko ma'u suka girka
abu sai yayi musu yawa.
Sallamar
da akayi daga bakin qofa ya maida hankalinsu can.
"Sannunku dai.....gafaranku" Zuwairan ke fadi tana
rarraba idanu. Zuciyarta cike fal da fargaban kada shigowarta ya zama silar
barinta aiki.....amma kuma tana jin relief na wani fannin idan ta tuna tana da
assurance na bazaice komai ba muddin annin tazo gaidawa.
Zubewa
ta gaidashi,amsawa daya yayi mata,ganin hakan sai ta tattara hankalinta ta
maida kan annin tana zuba gaisuwa.
"Ya mukaji da wannan abu?" Zuwairan ta fada duk da
a tsorace take.
"Ke!" Fuad ya fadi da kakkaurar muryarsan nan dake
saurin isar da saqo gun wanda aka kira saboda zurfin muryar da wani irin kaifi
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 62
62
"Eh......na'am" Ta fadi adan zabure
"Kin taba samun matsalan qwaqwalwa?" Ya tambayeta
kai tsaye da wani kallo da yaso rikita duk lissafinta. Kai ta fara girgizawa
"Ranka ya dade.....aah"
"Good" Ya jinjina kai
"Bacen a gun" Ya fada a taqaice wanda yana kaiwa
qarshe tana miqewa da hanzari gami da cewa
"Tuba nake.....tuba nake". Daga shi anni har amna
binta sukayi da kallo,a mamakance anni ta maido dubanta kansa bayan ta fice
"Allah me mutane.....ina ka samo wannan
Muhammadu?"
"Maamah ce....." Ya fadi a taqaice yana jin wani
abu game da matar tare da bin hanyar da ta wuce da kallo kaman tana wajen har a
lokacin. Tun bai qarasa ba ta fahimci inda zancan ya dosa,kai kawai ta gyada
tana fadin
"Allah ya rufa asiri......mu zamu wuce.....diyata"
Anni ta fadi tana murmushi. Qasa sabreen ta sakeyi da kanta tana dan qaramin
murmushi. Karon farko idanunsa suka soma kaiwa kanta,karon farko kuma yaga wani
abu me.kama da murmushi akan fuskarta......hakanan lokaci na farko da yaga wani
alamu na wata aba wai ita KUNYA a tare da ita. Tsaki yaja qasan ranshi,bayajin
wannan abun da takeyi har qasan ranta take yinsa,yadda ta wani sunkuyar da
kanta,abinda bai taba gani ba a tare da ita sai yau.
"Allah ya qara sauqi kinji.....ki kula da jikinki da
kyau" Anni ta fadi tana jin yaqinin kamar abinda dai take hasashen ne yake
tare da sabreen. Har cikin zuciyarta takejin yarinyar,tana kuma jin kamar ta
taba ganinta a wani wajen kafin yanxu,amma kuma ta gaza tunawa.
"Ameen anni.....na gode" Siririyar muryarta da yau
kadai tayi wani irin laushi ta fito tana furta hakan har yanzu kanta a qasa.
Dukkaninsu suka takawa anni xuwa inda lafiyayyar BMW dinta take jiranta
da masu tsaro lafiyarta mutum biyu
"Zamu tafi tare da amna din.....amma anjima da dare in
sha Allah zata dawo,sai kinfi jin dadin xaman......nasan halin
Muhammadu....indai kin ganshi gida zaune to saidai annual leave dinshi yazo ko
kuma baida lafiya da gasken gaske". Haka kawai ta samu kanta da kallonshi
ta gefen idonta. Duk da ba dogon zama sukayi ba,gajeran zama ne maras dadi da
ma'ana,zaman da baida wani alqibla ko kadan,amma ta karanci dabi'u masu yawa
tattare dashi. Aiki kaman baisan ciwon kansa ba,kamar kuma yafi kowa sanin
muhimmancin lokaci,bata taba ganinsa ba system ko takardu ba.....sannan zaman
kadaici baya damunsa sam sam.
Suna a
tsaye motar ta soma motsawa tana fita ta tafkeken gate din gidan. Idanunta akan
bayan motar,tana jin kaman ta hanasu tafiya ita da amna din,dan wanzuwarsu na
qananun mintuna kadai sai taji kaman an rage mata wani nauyi da takeji a
zuciyarta. Lallai maraici babbar masifa ce,ciwo ne wanda bashi da magani har
xuwa randa naka ajalin xai ruskeka,wanda ya rasa uwa shi daya yasan irin asarar
daya tafka da ba zata fadu ba.
Sai da
motar ta gama ficewa tas sannan ta tuna a inda take a tsaye,da kuma wajen waye
take?. Ba tare data juya ta kalli inda yake a tsayen ba ta juya a hankali tana
komawa ciki.
Da kallo
ya bita ranshi yana sake masa susa......idanunsa suka sauka kan hips dinta da
suka bayyana sosai saboda mayafin dake saman kanta bame girma bane,take
zuciyarsa ta wullo masa hoton hijabinta na jiya da yasha cukuikuiya,wani
zazzafan abu me tauri ya taso masa da ya sanya ya gaza riqe kansa,sai kawai
yabi bayanta yana jin ya zama dole lallai lallai yasan kome.
Tana dab
da isa qofar da zata sadata da parlor dinsu na farko ya cimmata. Bata zaceshi
ba ta tsinceshi a gabanta. Kallon kallo suka yiwa junansu,wani irin kallo na
tsakiyar idanu,tsakanin shi da ita kowa zuciyarsa na dauke da wani irin nauyi
da baisan yadda zai rageshi ba.
Ta dauka
zata iya jurewa ci gaba da kallon tsakiyar idanun nasa amma sai taji ta sare
nan da nan,ta janyesu bugun zuciyarta na daduwa wanda batasan meye sila ba.
Qasa tayi da kanta,so samu ta rabeshi ta wuce saboda fushi take gani cikin
idanunsa,ita kuma yanzu qirjinta bazai iya daukan fada masifa ko tashin hankali
ba hakanan. Kai kawo kawai adams apple dinsa keyi alamun akwai abinda yaketa
qoqarin hadiyewa,jiyan ce kawai ke dawo masa,yana tuna sanda ya dagata towel
din jikinta daya xame warwas a qasa,daga ita sai hijabi. Sai daya tabbatar yayi
babban aikin rage fushinsa da abinda yakeji sannan ya soma magana,cikin bacin
rai amma kuma yanata kokawar kalmasa harshensa,don bayani yake buqatar ji,duk
da cewa ta kowacce fuska.....duk kuma inda ya juya.....kowacce hujja idan ya
daga,ya tattaro ta nan data can ba abinda take sake nuna masa sai ainihin
WACECE ITA.
"Wancan lokacin.......na taba ganinsa cikin hotel a
abuja yana cigiyar karuwarshi da suka kama daki,ta kwashe masa kudade masu yawa
kwatankwacin yadda ya faru da kamfanin JADDA DIAMOND CHORES RESOURCES,sanda
naga fuskan wayar ba kowa bace a ciki sai KE!......Wanene shi?,ya akayi ya
shigomin cikin gidana?,cikin dakin da aka gina da tsaftatacciyar dukiya ta
halak?".
Wani irin
duka tambayar tasa tayi mata,wadda tazo mata hade da labarin da batasan ya faru
ba......eh ta taba binsa abuja.....kuma aikin mashkur kusan shine aiki na
qarshe da tayi har yau kuma bata sake sha'awar maimaita wani abu makamancinsa
ba.......amma yaushe ya fiddo hotonta ya nunata a matsayin karuwa yana
cigiyarta?. KARUWA kalma mafi muni da tafi tsana taji ta gilma a
kunnuwanta......duk yadda takai tsakaninka da ita muddin xaka kira wannan sunan
a gaban fuskarta......to takan iya manta ya kuke da ita?.
"Am asking you......" Ya fada yana jin ya soma
hasala ganin shurun da tayi kamar ba da ita yake magana ba.
"Ban sani ba......." Ta bashi amsa muryarta tana
so ta fara rawa. Me zata gaya masa wanda zai sanya ya fahimceta?.
"Baki sani ba kaman yaya?,ya shigo har dakin ba tare an
fasa kowanne gini na gidan nan ba......ya shigo dakinki ba tare da kinyi
yunqurin kiran koda security daya na gidan nan ba......ya shigo dakinki daidai
lokacin kwanciyar baccinki?,a sanda kike daure da towel kadai da hijabi?"
Ya qarasa maganar yana qarasawa dab da ita,yana kuma kaiwa qarshe a tsawace har
sai data lumshe idanunta ta kuma gaza budesu.
Tsawa......tsawa,bata son tsawa,bata qaunarta,tsawar ma daga wajen d'a
namiji.....wanda tuni ta karanci sun jima da raina ajawalin mata. Wani abu data
jima da shawa kanta alwashi,raini.....wulaqanci.....izgili da toxarci na da
namiji,ita ko 'yan uwanta ba wanda zata lamunta ya daukesu.
"Ban sani ba nima" Ta sake maimaita masa don da
gasken batasan yadda akayi mashkur ya shigo ba.
"Harda wayar daya baki kenan itama ita ta kawo
kanta?!.....nace ita ta kawo kanta?!!!" Ya fadi da qarfi kaman yana shirin
fasa mata kunnuwa.
"Stop it!.....wanne kakeso na amsa maka?,wacce tuhuma
kakeso na baka amsarta?!" Itama ta maida masa muryarta na rawa,oily eyes
dinta suna qara walainiya cikin hasken ranar daya fara dagawa.
"Ni kikewa shouting?" Ya tambayeta da tsananin
mamaki,saidai kuma qarar wayarsa ta janye magana ta gaba da yaso fadi. Bai fiya
daga waya a cikin irin wannan yanayin da yake cikin tsananin fushi ba......amma
yana expecting kira me muhimmanci daga gurin wani dan kasuwa mazaunin qasar
ivory Coast,dole ya ciro wayar.
Shi da ita
dukansu akan sunan FAREEDA KHALEED MUSTAPHA ya sauka,ita ta fara janye idanunta
tana jin wata wani fushinta yana ninkuwa.
Ya sanyata
a gaba da tarin tambayoyinsa amma shi a daidai lokacin karuwarshi ko
yarinyarsa.....batasan da wanne suna zata kirata ba ita ke kiransa?.
Ta nashi
bangaren banda muhimmancin da wayar ke dashi a wajensa tabbas ba abinda zai
hanashi tarwatsata ita kanta wayar a wajen bama fareeda kawai ba.
"Sorry sir" Yaji an fada da sauri,abinda yakai
hankalinsu kenan wajen. Me sunan malam ne,da sassarfa yake barin wajen saboda
kunyar yadda ya samesu a tsaye dab da juna,baisan kuma zai samesu a hakan ba da
bai biyo ta wajen ba.
"Zo nan" Ya kirashi a nutse yana duban hannunsa
dake dauke da newspaper daya saba ajiye masa duk safiya daga kamfanin jaridu
daban daban.
Sunkuyawa
tayi ta zame ta gefansa tana takawa don barin wajen,haka kawai taji bama zata
iya zama ta fuskanceshi ba sam. Kwata kwata bata yarda dashi ba
Shima.....wacece faridan?,meye alaqarsu da koda yaushe layinsa cikin karbar
kiranta yake?. Yana jin wucewarta amma bai waiwaya ba don hankalinsa yana kan
me sunan malam.
"Good morning sir" Ya sake gaidashi cikin
girmamawa yana rusunawa ba tare daya miqa masa newspaper din ba kaman yadda ya
saba,duk da yawancin lokuta ma yana samunsu ne a daura da dining suna jiran
fitowarsa,idan ga kammala dubawa kuma zai kwashesu sai kuma fitowar gobe.
"Morning.....how you doing?"
"Fine sir" Still ya kuma amsa masa amma ba alamun
zai miqa masa su. Abun yadan bawa fuad mamaki,yana shirin miqa masa hannunsa
don ya bashi kira ya kuma shigo masa.
Kai tsaye
aka gaya masa farouq ne don haka ya daga ba wani bata lokaci
"Good morning dude" Farouq ya furta kaman yadda ya
saba masa,saidai kuma daga can qasan muryarsa kaman yana iya tsinto wani abun
"Morning......mun tashi lafiya?"
"Fine.....ya jikin naka?,ka fita ne ko ka sauko daga
stairs?" Duka farouq din ya cure tambayoyin ya masa,abinda yaja hankalin
fu'ad kenan.
"Ban fita ba......na sauko qasa na rako anni yanxun xan
koma ciki".
"Good.....but do me a favor mana" Ya fada yana
fatan idanunsa basuga abinda ya gani ba.
"Ehnnnnn" Fu'ad ya fada yana jin zaquwa na jin
abinda zai fito a bakinsa.
"Kayi skipping duba newspapers na yau mana......instead
of that ka bani aron time din muyi magana" Yadda farouq yayi maganan kawai
ya sanyashi yasha jinin jikinsa,sai kawai ya miqawa me sunan malam hannunsa
yana masa nuni da newspapers din da yake rqe dasu yana kafeshi da idanun nan
nasa da kwarjini ke cike dasu kullum ba tare da ya sauke wayar a kunnensa ba.
"Kowanne lokaci na yini na zan iya baka farouq,not the
only news time" Ya bashi amsa sanda me sunan malam ya miqo masa newspapers
din da hannu biyu cikin mutuwar jiki,ya kuma janye daga wajen da sassarfa don
bazai iya tsaiwa yana dubansa a sanda yake kallon labarin dake buge a jaridar
ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 63
63
"Wannan abun kawai nake buqata please" Farouq ya maimaita
sanda ya shiga motarsa dake farfajiyar gidan. So yake yaja maganan da tsaho
sannan ya cimmasa kafin ya duba abinda ke faruwan saidai sanda yake bashi amsa
na qarshe yana bashi amsar ne sanda idanunsa suka sauka akan tittle na labarin
da yaci shafin farko gaba dayansa na jaridun guda biyu.
*_TSINTAR DAMI A KALA_*
_BABBAR JARABAWA......SHIN KUSAN WACECE ASALIN MATAR
MATASHIN MILLIONAIRE DINNAN MAMALLAKIN KAMFANINNIKAN DAKE SARRAFA GWALA
GWALAI?_
"Farouq.....you have my time,amma kafin
sannan......" Maganar ta yanke masa sanda makeken hotonta ya biyo bayan
title din ita da mashkur.
Hoto ne
da aka daukeshi gaban wani hotel da sunan kawai ya iya kalla ba tare daya
tantance wanne bane.......sanda ya bude mata murfin motar ita kuma tana qoqarin
fitowa a motar yana riqe da handbag dinta.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Ya fada yana jin
dukka gabbansa suna daukan dumi kafin daga baya kuma suyi wani irin sanyi kaman
ba'a jikinsa suke ba.
_mrs muhammad fu'ad jadda sabreen ahmad_.
Baya jin
idanunsa zasu iya ci gaba da kallon abinda ke gabansa,sai kawai ya hade
newspapers din waje daya ya curesu a hannunsa yana takawa zuwa cikin gidan ba
tare daya tsaya tuna cewa magana suke da farouq ba,kuma yabar farouq din akan
line na waya.
Shuuuu din
da farouq yakeji ya sanyashi qarfafa zarginsa akwai abinda ya faru,sai kawai ya
aje wayar ba tare daya kasheta ba,ya tada motar da wani irin hanzari wanda
yanayin gaggawar da security na gidan suka ga yanayi ya sakasu dage masa qofa
ya fice tun bai qaraso ba.
Bazaice
ga wani abu da ya faru daga sanda yakai kansa samansa ba banda azababben ciwon
kai da yake masa kutufo kota ina. Ba abinda bakinsa ke furtawa sai
Astgafirullah yana me kyautata zaton akwai wani abu daya aikatawa ubangiji
wanda ba daidai ba shi yasa ya jarabceshi da wadannan abubuwan. Dukka komai
akan yarinya daya?.......yarinyar da koda ta zame masa zabi a nasa qashin kan
hakan ba lallai ya tabbataba banda miqewa da kafewar maamah akan lamarin?.
Da qyar
ya iya amsa sallamar farouq sanda ya bude smart door din ya qaraso cikin parlor
din idanunsa akan fu'ad. A yadda yaga idanunsa sun jirkita ya tabbatar labarin
ya gama ruskarsa.
Da idanu
yabi farouq din,har zuwa sanda ya qaraso,ya tsugunna ya debi duqunqunannun
jaridun ya bude ya kuma rufesu a take.
"Da gayya aka buga wannan news din......."
"To menene qaryar da sukayi a ciki?.....ban karanta
sauran labarinta a qasa da suka saka ba.......amma wanne ne qarya farouq?"
Maida dubansa yayi kan fu'ad da yake dubansa kai tsaye. A zahiri jijiyoyin
kansa ke tashi sosai har sun nuna ta farar fatarsa,wanda abadini yake nuna
ciwon kai yakeyi sosai,irin ciwon kan da ya dinga addaba masa sanda yake fama
da matsalar depression dinsa,wanda ya tabbatar ya jima rabonsa dashi.....
Sakin baki
yayi yana kallon fu'ad din daya fara magana cikin sanyi saidai akwai zafi me
yawa a kalamansa.
"Stop dude.....ina gaya maka.....don't judge book by
his cover.........ka daina judging mutane haka"
"Judging nasu nake ma?,bayan ina da full details na
evidence akan duk maganan da nakeyi farouq akan yarinyar?" Yayi maganan da
sanyin dai,amma lafuzzansa na nuna zallar zafin da yakeji.
"Evidence kadai bazasu tabbatar da hakan ba.......kayi
managing personal boundaries tsakaninku kaman na kowanne miji da mata,akwai
buqatar wani sensitive......"
"Haba mana!" Fu'ad da yakeji zuciyarsa na matsewa
kaman zata fashe ya tsaida farouq yana zama sosai yana jin jiri daga inda yake
zaunen.
"Kada bakinka yakai nan wajen.......bakasan wacece ita
bane farouq?,bakasan sunan da kowa yake kiranta dashi ba?,baka gani jikin
newspapers ba?"
"Na gani.....na kuma sani......kuma ka rigani sanin
haka kace zaka daukota ka gyarata......ya akayi ka kasa fu'ad?" Ya jefa
masa tambayar yana riqe habarsa. Kansa ya jijjiga sosai yana duban farouq
"Ban kasa ba......bazan kuma kasa ba......abu daya
kemin burki.....duk sanda na kalleta sai naji tayi qanqanta da yawa nayi mata
kalar azabobin dana tanadar mata......tayi mitsitsiya na sanyata a prison din
dana shirya mata......amma duk sanda ta aikata wani abu kota bullo da wani
abun........sai naga nine naketa kuskuren kallon tayi qanqanta......a abinda
zuciyata ke rayamin wannan karon......duk hukuncin da yazo na dauka a kanta a
tunanina na qarshe dashi zanyi amfani......"
"Banda divorcee......"
"Harda shi idan ta kama" Ya fada confidently.
Ido Farooq
ya zuba masa kawai,ga mamakin fu'ad sai yaga ya saki wani irin murmushi yana
girgiza kai. Shima duban farouq din yake kafin yaji murmushinsa ya bata masa
rai. Bayajin a yanayin da yake ciki ya kamata wani abu me kama da murmushi ya
fita a fuskan farouq,don haka ya miqe tsam yana dosar bedroom dinsa. Da hanzari
farouq ya miqe yana kiransa
"Wait dude.....wait" Don ya tabbatar wannan
bedroom din nasa me smart door idan ya shiga ya rufe baka isa ka bude ba muddin
bai sakaka cikin wadanda zasu iya budeta ba. Bai saurareshi ba ya shige dakin
abinsa,da qarfi ya rufe qofar yabar farouq a nan a tsaye. A yanzun da baya
ganinsa sai murmushinsa ya ninka na dazu,bayan minti uku yayi qoqarin daidaita
kansa,ya matsa yana daukan telephone na falo din ya kira cikin dakin nasa.
Yayita
kira yana jiyota tana ringing,kaman bazai daga ba kafin ya daga daga baya,ya
sakata a kunne ba tare da yace komai ba.
"Am really sorry dude.....na hango wani abu ne daban da
yake durfafoka da matuqar qarfi fiye da qarfin guguwa......amma it seems like
baka ganshi ba baka kuma fahimceshi ba......anyways kayi aiki da hankalinka da
intelligent dinnan dana sanka dashi.......am always free,and then it's time to
act for koma waye behind all these issues......na tabbatar akwai wani abu
boyayye......think wisely......am always by your side.....take a rest,but
please kasha magani".
Sanyaya
ranshi sosai maganganun farouq sukayi,yayi shuru kawai yana saurarenshi bai iya
ce masa komai ba......shi kansa baisan me yasa a bangaren nan kaman
qwalqwalwarsa bata iya aiki daidai ba?. Yana jin kamar ya gaji......yana
buqatar hutu da gaske na jiki dana kwanya
"Am tired farouq......I'm feeling burnt,i need some
time to unwind and focus on my well-being......kayi magana da saddiq.....i want
him to schedule my annual leave cikin kwana uku".
"Kowa ma lokacin hutunsa yazo......International
gateway to Maldives" Ya furta yana motsa labbansa gami da jefa hannunsa
sama yana kwatanta yadda jirgi yake cillawa sama yayin daya cirata daga qasa.
"Zan kawo nesa zuwa kusa......zan dawo da mafarki zuwa
gaskiya......komai zai warware.....zan kuma baka mamakin yadda zan juya maka
rayuwarka dare daya" Farouq ya fada yana dariya kaman mummunan abu irin
wannan bai faru ba.
Kawai wani
nishadi yakeji qasan ransa idan yayi imagination na yadda komai zai kasance,sai
yaji kawai ya qagu shi Kansa lokacin yayi,sai ya juya ya tattare key da wayarsa
yana maidawa aljihu ya soma sauka yana barin gidan,ko saddiq dinma bazai nema
ba.....shi zai shirya komai,sai komai din ya kammala sannan kowa yaji ya gani.
*_tom......me karatu?,wanne plan kake tunanin farouq yana
dashi akan fu'ad?,muje zuwa_*
Yana driving a
mota amma tunani fal kanshi. Tunda yake bai taba hangen wani abu daya jigata
fu'ad komai tsananinsa ba kaman wannan......anya ba burbushin wannan halittar
daya tsirowa zuciyarsa kuwa?, wadda kusan itace jigo na kowanne tsanani da
wahala da zuciya kan iya shiga akan wani dan adam?.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 64
64
Bayason
irin fushin da yakeji cikin ruhinsa da jikinsa gaba daya......yana buqatar yayi
cooling down ko yaya ne,a lokacin ayar nan da taxo cikin alqur'ani me girma ta
fado masa
"Ku saurara.......da ambaton Allah kadai zukata ke
samun nutsuwa"
"Sadaqallahul azeem" Ya fadi yana miqewa hadi da
fara jin sassauci daga tuna ayar kawai.
Toilet
dinsa ya shiga,ya daura alwala me kyau,sannan ya dawo cikin dakin yana kunna
chandelier din dake kafe tsakiyar dakin,wadda ke hade da Bluetooth da kuma
fanka me bada sassanyan iskar data banbanta data sauran fankoki. Remote ya
dauka ya kashe hasken don baya buqatarsa,ya kuma kunna speaker din dake jiki
yana daidaitata da wayarss,take muryar fasihin malamin nan limamin ka'aba wato
sheik abdurrahman assudais ta karade dakin cikin sauti mafi tsarki na karatun
alqur'ani.
Relaxing
yayi sosai soman sofa din dake dakin yana jin wani sukuni ya soma ratsahi,kaf a
cikin malamai idan akwai wani sauti da yafi so yafi qauna bazai wuce sautin
sheik abdurrahman assudais ba,wannan dalilin yaja ra'ayinsa qira'arsa gaba daya
ta juye zuwa ta sudais din sak.....da wannan qira'ar yayi sauka,kuma har yau
itace a bakinsa.
Idanunsa a
lumshe yana ci gaba da bin sautin,bazaice yana jin yunwa ba ko kadan,zamansa a
haka duk duniya yafi komai yi masa dadi,a haka ya shafe kusan awanni biyu har
zuwa sanda wayarsa tayi haske,kira kuma ya shigo wayar tasa.
Hannu ya
sanya ya jawo yana dubawa,ganin me kiran ya sakashi daukan remote din dake
gefansa,ya kashe volume din gaba daya sannan ya daga wayar yana sakata a hands
free.
"Good afternoon sir......yanzu haka dukka shugabannin
gidan jaridan suna hannunmu". Zamanshi sosai ya gyara cikin kujerar yana
harde qafafunsa waje daya
"Well-done,good job khaleed,akaiminsu housing estate na
darmanawa.......by 4 zan fito in sha Allah"
"Yes sir" Ya fada cikin tsananin nuna ladabi,bai
sake jiran komai daga wajensa ba ya kashe wayar yana ajeta gefe. Bai sake
batawa kansa rai da tunani ba ya dauki remote din da xummar qara volume
din,cikin ransa yana jin bazai sake barin komai ya bata ranshi har haka
ba......ko meye ya faru da ita ita ta jawo......amma fa bazai taba lamunta a
taba masa igiyar aure ba,ko kuma sunansa ya fito a ciki ba ko na ahalinsa.
Wani kiran
ne ya sake shigowa dole ya aje remote din. Asp ne yake kiran,shima bai jinkiri
ba ya daga.
"Sir........mun sama musu gurin ajiya na
musamman......kuma zamu tuhumesu da kyau har sai sun fadi gaskiyar wanda ya
aikosu".
"Na gode......but inaso ku barmin wannan a
hannuna......ku ajiyesun irin ajiyar data dace dasu har xuwa sanda zasu furta
wanda ya basu hanya da daman shigowar"
"Okay boss...."
"Thank you" Ya sake fadi labbansa suna motsawa.
Wannan
bacin ran da yaketa son hadiyewa still dai ya sake taso masa,ya sanya hannunsa
ya shafi kansa. Zai iya cewa tun daga guards dinsa zuwa securities dinsa
amintattu ne,bashi da ko kwanto da ko shakka akan koda mutum daya daga ciki,duk
da dan adam tara yake bai cika goma ba......kuma wasu daga cikin 'yan adam din
masu iya canzawa ne a duk sanda sukaso a karan kansu,walau dalili na son zuciya
ko makamancin hakan......amma su kam yayi imanin yadda yake mu'amalantarsu
daban yake da sauran yadda masu gida ke mu'amala da yaran gidansu.
Kyautatawarsa a garesu ta daban ce kaman yadda qaunarsu a gareshi ta daban ce.
To amma a yanzun yadda yakejin zuciyarsa komai ma yana iya faruwa......sannan a
yadda yasan ya gidansa yake,abune me wahala a iya keta tsaron gidan a shigo
haka siddan ba tare da idon sani ko mataimaki sannanne ba.
Volume dinsa
ya qaro yana fatan sake samun nutsuwa da daidaituwar zuciyar da zata bashi
qwarin gwiwar fita zuwa yammacin. Bai tashi ba sai da akayi sallar azahar,ya
daura alwala ya fito don halartar jam'in sallah kaman yadda ya saba muddin yana
kusa da masallaci.
Dukkanin
ma'aikatan kowa rabe rabe ya dinga yi daga ganin fitowarsa. Zukatansu a razane
yake abinda ya sanya gidan ya sake daukan shuru gaba daya kamar ba wata halitta
a gidan me rai da tayi saura.
Bai dawo
cikin gidan ba sai la'asar,don ganinsa yau free haka da rana ya sanya masu
buqata suka dinga shigowa masallacin. Bai hanasu ba ya zauna ya dinga sauraren
kokensu daya bayan daya. Ba wanda ya bari ya tashi a wajen ba tare da gaggwaban
abun alkhairi ba,jordan na tare dashi shi ya tashi sauraronsu,sukayi la'asar ya
miqe ya wuce gida qirjinsa cike da nauyi. Sai yake sake ganin yadda ubangiji ke
tsara rayuwa yadda yaso.......matsalar wani bata wani ba......a yadda unguwar
take baiyi zaton masu qaramin qarfi dake neman taimako na shawagi a cikinta ba.
Ya dubi kansa sanda yake wucewa ta babban glass door din da zaka taras a gate
din farko na gidan. Ubangiji ya azurtashi da dukiya me yawan gaske......lafiya
da wadata......saidai ya samu naqasu ta bangaren uwa da mace ta gari,wanda
wadannan abubuwa biyun sune jigo a rayuwar kowanne dan adam. Ga wasu can su
kuma nasu burin shine INAMA MUNE ME JADDA?,ba tare da sunsan ainihin waye me
jaddan ba?,me yake fuskanta?,wacce rayuwa take going through......(wannan ya
zamana izina a garemu gaba daya,kafin kayi burin inama kaine wane?,kayi tunanin
mene rayuwarsa ta badini?,kayi tunanin wadanne qayoyi ya tattaka da tsinika
kafin yakai ga isowa nan inda yake?,ko yaushe idan kaga wani mutum da rayuwarsa
ke burgeka,ma roqa Allah ta hanya daban bata hanyar Allah yasa na zama kaman
wane ba.....bayan fuskar wane dinnan kawai kake gani bakasan cikinsa ya yake
ba,Allah ka kyautata rayuwarmu,ka bamu tsira duniya da lahira)"
Da tarin
tunane tunane yake ratsowa falon daya xama wani irin shuru. Gaba daya kallon
gidan yake wani iri,har a gangar jikinsa yakejin ya gaji da xaman cikinsa. Wuf
ya hangi gilmawarta daga kitchen kaman zata kifa tana nufar qofarsu. Har yaci
gaba da tafiya wani abu ya sauko cikin tunaninsa
"Ke!" Yayi kiranta da wani amon sauti da a take ya
tara zazzafar gudawa cikin tumbinta
"Na'am......na'am ranka ya dade" Zuwaira ta fada
wadda ke rungume da wani abu da baisan meye ba. Hannuwansa ya zube cikin
aljihun wandonsa yana qare mata kallo,zuciyarsa tana raya masa wani abu game da
ita. Wani abu me kama da xargi tuhuma da kuma rashin aminci a kanta yaji yana
tsarga masa. Irin kallon jadda din ba kowanne mutum ke iya jurarsa ba,sai mutum
me babbar kurwa,me babbar kurwar ma wanda ya cika da gaskiya da kuma amana,ba
wani ha'inci cikin lamarinsa,wannan ya sanya zuwaira ta dinga jin kamar yana
karance duk wani sirri dake tattare a qirjinta zuwa cikinta,tamkar ya sanya
microscope yana tantance adadin qulla qulla da harqallar data taba shiryawa
tsahon rayuwarta,wannan ya qarawa adadin zuciyarta gudu,ya kuma hanata ci gaba
da daidaituwa akan qafafunta,saita sulale ta duqa saman qafafunta
"Allah ya taimaka.....tuba nake,bansan kana cikin gidan
ba ai......da ba'a fito ba,wannana bun daya faru ranka ya dade shine ya hanani
nutsuwa.......hajiya naketa son dubawa aga yanayin da take ciki....."
"Ke" Ya sake kiranta yana dage dukka girarsa sama
guda biyun.
"Na'am yallabai na'am......."
"Ki tarkata komai naki kibar gidannan cikin qasa da
minti goma....."
"To an gama ranka ya dade,aisai a komawa hajiya maamah
baya goya marayu" Ta furta tana jin
wani sassauci da rangwame a ruhinta. A abinda takeji yanzun sallamarta shine
babban gatan da yayi mata,duk sanda taji muryarsa sai kowacce kafa ta jikinta
ta jiqe da gumi. Sai a yanxu take ganin cewa da gaske xaman gidan jadda yafi
qarfinta,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa. A baya tana tunanin duk randa yace
taje ya sallameta zataji tashin hankali maras iyaka......amma a yau sai takejin
kamar 'yanci ne daga bata zuwa zamowa halastaccen d'a.
"Kinsan me?" Ya fada yana sake dubanta,saita
dakata tana saurarensa.
"Bazan dubi tsufanki ko digon furfura koda qwaya daya
dake tsakiyar kanki ba......muddin naxo na sameki kin koma gifan gidan
maamah........ki tabbatar daga ranar kin tashi daga aiki......kiyi nesa da ita
da komai da kowa daya danganceta.....and hakan bawai xai sakaki kin tsira
ba,duk mutumin da yake gidan nan daga kwana uku baya zuwa jiya da abin ya faru
baxai tsira ba a waje na......wanda kawai zai tsira shine MAI GASKIYA ".
Duburbucewa tayi har akwatin kayan asirin maamah na shirin tarwatsewa daga
hannunta. Gab gab gab haka hannuwanta da qafafunta suka dinga haduwa waje
daya,wannan wanne irin kalar tashin hankali ne?,wanne irin yaro ne wannan maras
imani.... Lallai dole mallakarsa ta yiwa mariya wahala,zuwaira ta furta hakan a
ranta sanda take ta qoqarin kai kanta ga sassansu don ta samu ta sulale kaman
yadda ya shawarceta. Ayadda ta sanshi tana ganin ko cinye namanka yace zaiyi
zai iya......musamman shi daya mallaki masu gidan ranar da babu me tuhumarsa ko
bin ba'asin abinda yayin.
Gaba daya
wunin yau duka hankalinta yana kan wayoyinta,bama ita ba.....hatta da fareeda
kowanne motsi nata yake kan social media's tana hasashen watsuwar abun a
kowacce kafan sada zumunta. Sanda taga ankai azahar shuru sai duk wata nutsuwa
ta soma barin gangar jikinta,hankalinta ya gaza kwanciya kwata kwata,ta kuma
shirya kai tsaye ta kira driver ya dauketa zuwa gidan maamah.
A sannan
ita dinma duban wayar take tayi.......tanaso ta samu wani haske ko yaya
yake.......tunda ta zauna take saqa yadda komai zai kasance.......take qiyasta
irin tozarcin da zata yiwa sabreen. Lallai sai ta sanyata ta fahimci wutsiyar
raqumi tayi nesa da qasa.......ita kanta batasan adadin yawan tozarci da
qasqancin da zata sanyata ta fuskanta ba.
Mamakinta ya tsananta ainun da rashin samun kai,sai taji ta kasa
jira,kai tsaye ta daga waya don kiran fareeda,amma sai fareedan ta hutashe da
ita saboda turo qofan setting room din da tayi ta shigo tana taunar chewing gum
kaman yadda ya zame mata al'ada,duk kuwa da cewa yau din bata cikin wannan mode
din,amma cin chewing gum din ya zame mata dabi'a.
"Ke nake shirin kira yanzun.......banga tasirin aikinki
ko wani motsi na daban ba" Maamah din ta furta kanta tsaye tana duban
idanun fareeda. Idanu tadan xubawa maamah din,mamakin dabi'arta tana dan
kamata. Kanta tsaye take magana akan duk wani abu daya shafi buqatarta,ba
ruwanta da wata matsalarka ko fuskantar yanayin da kake ciki.
Kanta ta
dauke tana qarasowa ciki,sannan ta yiwa kanta mazauni saman hannun sofa din
tana harde hannuwanta a qirjinta
"Wannan shine aiki mafi kashe kudi da nayi......sannan
shine aiki mafi jinkirin samun nasara" Tayi maganar tana duban maamah din.
"Masu aiki sun kammala.......naki aikin da nawa duka ba
wanda ya kawo result me kyau........abu daya ya rage shine,ki kira d'anki ki
tuntubi sakamako daga gareshi". Gyara zamanta maamah tayi tana duban
fareeda,ta soma fahimtar wasu halayenta da inda dabi'unta suka sanya gaba,bata
gayawa fareeda tayi failing a nata agenda din ba.....ya akayi amma ta sani?.
"Na yarda har abada yaro yaro ne.......kina tunanin
samun galaba akan duk wani lamari daya shafi fu'ad abune me sauqi?,inda kuwa
hakanne da bakizo gabana ba......da babu ke cikin babin qaddararmu sam
sam" Maamah ta fadi tana duban fareeda.
"Duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi
bazai hango ba..........a naki lisssafin kiran fu'ad kai tsaye na jefeshi da
salon tambayoyinki abune me sauqi da zai sanya mu wanye lafiya?" Ta qarasa
maganar tana duban fareeda data zubawa maamah nata idanun.
"Kina iya kiransa ta wata siga daban ki kuma zaqulo
bayanan da kikeso......amma zai zama
babban kuskuren rayuwarki ki biyo masa ta waccan hanyar taki....."
"Amma bisa alqawari da yarjejeniya.......xaki zama
tsanina na mallakar fu'ad haka ne?"
"Har yanxu ina kan wannan bakan.......amma fidda
sabreen daga gidansa aikinki ne......zai iya zama nawa aikin,amma kuma salon
aikin nan da yake zamowa ba waji bi". Sun jima suna kallon kallo
tsakaninsu,kowanne da kalar saqar dake cikin zuciyarsa game da dan uwansa,kafin
fareeda ta fiddo wayar da musamman saboda kiran fuad din ta tanadeta. Da
kowacce waya da kuma kowanne layi ta kirashi ba zata sameshi ba saida wannan
wayar kadai.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 65
65
_Manzon Allah S A W bai taba aibata abinci ba,idan ya
burgeshi sai yaci,idan kuma baiyi masa ba sai ya qyaleshi(ba tare daya
aibatashi ba)_
Tsaf ya
shirya cikin trouser dark blue na yadin vicuna,yayin da sanya black shirt data
fidda ainihin kan sassalkar fatar nan tasa me tsananin haske,wadda ta cakuda da
hutu da jin dadin dake bayyana kansa cikin kowanne hali yake. Kyakkyawar
qasumbar fuskarsa da bata da cika irin ta cukus ta sake qawata fuskarsa da
sanya masa kwarjini,tana da santsi kwatankwacin sumar dake lullube saman kansa.
Baqa ce sidik kaman gashin girarsa dana idanunsa,hakanan kaman sauran gargasar
dake lullube da sassan jikinsa. Agogo fata ya daura a tsintsiyar hannunsa me
tsananin tsada daya dace da shigarsa dama tsadar kayan jikinsa,yabi ko ina na
jikinsa ya feshe da lallausan turaren nan nasa me taushin qamshi.
Tsananin
dauriya kawai ta sanyawa ruhinta,tun bayan dawowar amna da batakai magarib ba
kaman yadda anni tace taketa qoqarin shimfida walwala akan fuskarta,duk da cewa
abun ba haka yake ba daga qasan zuciyartata. Amna din ta dabance,tana da
barkwanci da sakin jiki ga duk wanda ta yarda dashi,wannan ya sanya cikin qasa
da awa guda taji nauyin dake qirjinta yana raguwa,lokaci lokaci labarun amnan
suna sake dauke hankalinta daga yanayin da take ji.
Ita ta
tilastata da yammacin kan su fito daga daki zuwa kitchen
"Wainan fulawa nake sha'awa.......yakumbo ce take
mana,ta tafi ganin gida tun wancan satin,muje na gwada ko zan iya please
adda" Ba zata iya qin tankwabar da
tayinta ba,haka ta maqala hijab saman doguwar rigarta ta bita kitchen din,wanda
a qarshe sabreen dince ta hada Mata wainar ta soya mata ta kuma tara mata a
warmers. Ta cika da mamakin yadda akayi amnan ta iya girki kala kala amma bata
iya wainar fulawa ba. Qwarewar amnan a girki yana bata sha'awa,harma takanji
tana sha'awa itama iya kalolin abinciccika.
Suna a
saman dining tana kallon yadda amnan ke santin wainar fulawan,time to time tana
murmushi kawai. Ta sake yarda da gaske rayuwa mataki mataki ce,kowanne da kuma
kalar muhalli da hurbin data ajeshi.
Duk da
fiye da rabin hankalinta bashi a wajen,amma hakan ba hanata jin saukowarsa ba a
jikinta. Qamshin turarensa ne ya fara isa ga hancinta,kafin daga bisani qamshin
ya fara mamaye parlor din.
Cikin dabara
ta dauke duban ta daga wajen da yake takowa,tanason nuna sam sam ma bata ganshi
ba. Duk sanda fuskarsa zai bayyana a gareta,ba abinda yake tuna mata sai
tambayoyinsan nan data tsana,tambayoyin dake matuqar qona masa rai ba kadan ba.
"Hamma......barka da yamma" Amna ta furta da
murmushi saman fuskarta sanda ta waiwaya ta ganshi,sai ta aje wayar hannunta
tana bashi hankalinta gaba daya
"Barks lovey dovey" Yayi maganar da wani
kwantaccen sauti daya sanya sabreen taji tsigar jikinta ya zuba,take kuma ta
daga kanta a hankali kaman me tsoron ganin wani abun tsoro,duk yadda taso ta
yiwa idanunta shamaki amma sai da suka fada kan fuskarsa,ta kuma ci karo da
wani yanayi dake shimfide saman fuskarsa din. Shi ba murmushi ba sannan kuma
ba'a daure fuskar take ba......saidai yana yin ya nuna ya zama very calm ba
kaman yadda take ganinsa kwanakin da duka wadannan abubuwan suka faru ba.
Zamewa amna
tayi tana sake gaidashi bayan gaisuwar daxu,ya amsa yana motsawa alamun xai
wuce. Wayarsa dake riqe a hannunsa ta fara bada wani sassanyan sautin sarewa
maras hayaniya da yawa,kafin daga bisani sunan FAREEDA KHALED MUSTAPHA ya fita
tarwai ta cikin speaker din. Duk yadda taso watsar da sunan daga cikin
kunnuwanta amma hakan ya gagara. Sunane data jima tana jinsa akai akai,har kuma
ya soma zama a kwanyartata. Maida hankalinta tayi ga amna amma saita gaza ci
gaba da hakan,batasan yadda akayi idanunta suka dauketa zuwa fuskarsa ba. Wayar
ya daga zuwa fuskarshi yana duban me kiran,sosai ya zubawa numbers din nata
idanu,manhajar daya dora kan wayar tasa ke harbawa daga gefan hagu na wayar
tana nuna masa abinda fareeda din ke aiki dashi wanda ke fasa duk wani shinge
da zai saka number dinta,duk sanda ta jira kiran ya samu damar isowar gareshi
kai tsaye. Dan qaramin murmushi ya subuce masa wanda iyakacinsa labbansa,saidai
a nata idanun qaruwar murmushin ta gani. Idanunta taja ta lumshe daga kallon
dark pink lips dinsa. Batasan me yasa gabanta yayi wata wawiyar faduwa ba,sai
kawai taji bata da sha'awar ci gaba da zama a wajen. Tsam ta miqe sanda amna ke
ce masa
"A dawo lafiya hamma...." Ta fara saukowa daga
steps din,a cikin jikinta taji amna din na satar kallonta,wani nauyi ta sakar
mata da bisa dole ta motsa labbanta tana fadin
"Adawo lafiya" Sosai yaji kalmomin sun zama baqi a
kunnensa,har ya motsa kaman zai waiwaya sai kuma baiyi hakan ba ya amsa
"Allah yasa" Yana takawa gami da ficewa da takun
nan nasa da ta dade da haddaceshi. Wani irin taku yakeyi tamkar namijin
toro,zakayi tunanin wani saraki ne,ko kuma yana qawata takun nasa daidai da
yadda zaija hankalin masu kallonshi.
Ficewarsa
daga falon ya bata wani qaramin sukuni,sai ta fasa komawa dakin ta sauka saman
sofas din dake falon ta zauna tana maida numfashi. Idanunta ta maida hanyar
daya wuce din
"Fareeda KHALED MUSTAPHA" Sunan ya dawo mata radam
a kunne,murmushinsa kuma ya sake giftawa ta idanunta,ta sake lumshe idonta ta
kuma budesu lokaci daya
"Waya sani ma ko ita ta kirashi?,wa yasan inda
zasuje?" Ta furta can qasan zuciyarta tana tuna irin tuhumomin da take
gani a kanta cikin idanunsa.
"Waye yasan abinda shi yake aikatawa ma?" Ta sake
samun kanta da fada qasan zuciyarta. Ko daya ba zata taba aminta da cewa shi
din a tsare yake ba......taga matasa masu tarin yawa da ni'ima da baiwar
dukiyar da yake da ita yasu bata taka rabinsa bama......amma qazantar dake
cikinsu sai Allah. Kamar dai shi......a haka kamilallen mutum....amma badininsu
wata irin danqararriyar qazantace maras dadin gani ko tabawa.
"Adda......." Taji muryar amna daga gefanta.
Fararen idanunta ta daga tana duban amna gami da katse tunanin dake kai kawo a
ranta
"Amna" Ta amsa mata murya qasa qasa tana nazartar
fuskarta. Fuska ta narke sosai tana zagayowa gabanta ta zauna.
"Nace wani abu adda bazai zama shishshigi ba?"
Tayi maganar da alamun son ta furta abinda ke bakinta. Qaramin murmushi ta
sakar mata don ta bata nutsuwa da gamsuwa akan duk maganar da zatayi
"Fadi amna mana"
Sai data gyara zamanta tana maida mata murmushin sannan tace
"Yaaa saddiq yana bani labarin hamma......duk da na
fisu sanin hamma ta wasu abubuwan.......amma ya saddiq kuma zai iya fina saboda
shi din PA dinsa ne.....duk inda zai saka qafa a gida ko a office suna
tare.......kinsan waye hamma kuwa?,ya yake?" Tayi tambayar da murmushin
daya kusa zama dariya akan fuskarta.
Numfashi
taja a boye tana jin sunansa kawai da amna ta kira yana qara yawaita bugun
zuciyarta,inda zata iya zata dakatar da amna daga yi mata duk wata hira data
shafeshi......kwanaki kaddan suka rage masa cikin rayuwarta.......tana jiran
kawai ranar da zata samu tabbacin su huda sun isa mali lafiya hannun momma
bahijja.......a wannan lokacin komai zai tarwatse.
"Saikin fada amna" Ta fadi bawai don ranta yana so
ba,sake gyara zama sosai tayi ta riqo hannun sabreen
"He's a loving and caring partner.he wants a deeply
romantic connection with his wife" Ta fada murya can qasa,kaman tana
tunanin yana kusa dasu kuma tana tsoron kada ya jiyota. Dukka idanunta sabreen
ta fiddo waje tana kallon amna,yadda amna din tayi maganar da wani confidence
da qwarin gwiwa ya bawa sabreen mamaki.....can qasan zuciyarta kuma sai taji
kaman tanason taja hira kadan da amna din. Abu daya dai tayi amanna fuskar fuad
ta gida daban......fuskarta ta gidansa daban.....kamar yadda fuskarsa ta mu'amalarsa
ta waje daban,banda haka mutum kaman fuad dinne zata siffanta haka?.
"Kina da ja ko adda?......" Ta tambayi sabreen kai
tsaye,tana jin tanason tayi hira da ita.......tanaso ta fadi mata abinda ta
fuskanta ko ita ta fahimci ba daidai ba
"I swear adda........He envisions a future where he and
his wife grow old together,hand in hand......ko a gabana wannan yasha
fadinsa......musamman idan suna hira na sako da sako shi da BB
farouq.......hamma na yana son soyayya,ya kuma cancanceta......hammana yana son
kulawa......that's why yakeji dani,komai na hammana daban yake a
wajena.....tausayin hamma nakeji coz....He suffered a lot in his life
He had a rough past" Ta fada dukka a jere tana riqe da
hannun sabreen kaman hakan shine zai saka ta fahimta abinda takeji a zuciyarta
na tausayin hamman nata. Baki da idanu kawai sabreen ta sake tana kallon
amna,tana sake gasgatawa da imanin cewa eh lallai da gaske wannan mugun yana da
muhalli me girma da fadi a rayuwarta......amma wanne irin hardness ne haka ya
fuskanta?,mutumin da ya rayu tsakanin iyaye biyu 'yan uwa hudu?,mutumin dake
cikin daula da dukiya?.
"Believe me adda......please,ki qara akan kulawan da
kike bawa hamma,He's passionate about building a strong loving relationship
with his wife.......na dade da sanin duk wadda ta samu hamma fuad.....She's the
luckiest woman alive and she's incredible fortunate" Murmushi ta samu
kanta da subucewa dashi,saita miqa hannu ta riqe amna din sosai bawai don
maganganu da yabo a kansa sun burgeta ba,aah......sai don ita din mutum ce me
girmama 'yan uwantaka,saboda tasan girman soyayya da qaunar dake tsakanin 'yan
uwa me girma ce......itace babbar shaida ta farko akan hakan akan kanta ma.
"Duka wannan yabon amna......anya baki fiya son kanki
da yawa ba kuwa da wannan birkitaccen hamman naki?" . Murmushi amnan ta
saki itama,har qasan ranta taji dadin yadda sabreen ta karba maganganunta,amma
har ga Allah tana son matar hammanta ta zama dream wife nashi kaman yadda
dukkaninsu suka fahimta
"Ki budewa hammana zuciyarki da kyau.....zaki sha
mamaki adda.......inajin tukuicin zuwa dubai zakimin duk sati.....nayita zuwa
ina ganin burj" Murmushi ta sakeyi kawai batace komai ba......abinda ya
bawa amna daman sake cewa
"Adda.......na baki kadan daga tarihin hammana dana
samu tun kafin a haifeni.....wannan ne kadai zai zame miki jagora wajen sake
fahimtar waye.....ya kuma.baki qwarin gwiwan tallafarsa" Zame hannuwanta
tayi daga cikin na amna tana girgiza kai
"Zaki bani.....amma ba yanzu ba amna.....kinga bana jin
dadi sosai" Itama tayi maganar tana narkewa amna kaman yadda amnan keyi.
Murmushi ta saki tana tuna warning nata da anni tayi akan ta kula da ita,kuma
kada ta matsa mata da yawa,don haka sai tace
"Mu barshi pending......har sai kin samu lafiya"
Kai ta gyada tana lumshe ido kadan
"Na gode" Har qasan zuciyarta tana jin dadin yadda
amna ta fahimceta ta qyaleta. Sam bata son jin komai daya shafeshi,saboda tasan
zasu fadi kirkinsa ne kawai bawai don haka yake ba,zasu fadi kirkinsa ne don
haka yake nuna musu a fuska da mu'amalarsa da su,amma a waje kuwa.....babban
azzalumi ne a wajenta mugu kuma.
Maida
dubanta tayi kan maamah
"Ban taba kiran wani d'a namiji da adadi me yawa ba
irin wannan sai d'anki......na masa kiran qarshe......inaso naga naki
qoqarin" Abinda fareeda ta fada kenan ranta yana motsuwa hadi da qara baci
akan lamarin. Bata taba daukan plan dinta bazaiyi wani aiki ba,kudade ta kashe
masu nauyi don a buga ninkin adadin news paper din da aka saba bugawa a kowacce
rana......sannan a fiddata tituna a kuma rabata kyauta ga kowa basai kowa ya
siya news paper ba a ranar.
Guri daya
maamah ta zubawa idanu tana murza tafin hannunta,tana ji a jikinta lokaci yayi
da zata koma wajen boka ta zube masa komai.......ta gaya masa buqatarta ta
gaba,ta zube masa ruwan kudin da ko bai shirya ba dole yayi aikin nan......daga
can wani loko na zuciyarta tana fargaba.......tana fargabar kalamansa na can
watannin baya......kalamansa na qarshe a haduwarsu ta qarshe dashi.
_taurarinta nada tsananin haske da wahalar cusa kai a
cikinsu.......tabata abune da zai iya zuwa da nasara da kuma
akasinta.........KINYI KUSKUREN ZABINTA......amma itace mahadin masarrafin
b'arin nasa tauraron..........taurarinta sune abokan tafiyar nasa
taurarin.........kusan komai nasu suna kamanceceniya da juna.......ITACE TA
DACE DA CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMU GUSHEWAR AKASIN DA NAKE HANGOWA_
Gumi ne
taji yana tsatsatsafo mata......a take sai taji ai kaman ta fara shiga matsalar
daya ambata mata. Sai yanzu kwanyarta ta fara aikin da a wancan lokacin bata
yishi ba wato na fahimtar ma'anonin maganganunsa. Kenan aikin banza
takeyi?,kenan ba wadda zata iya cika mata burinta akan faud sai sabreen din da
take kokawar fitarwa a gidan?,wannan wanne AKASI NE da boka ke magana a kai
wanda yace muddin ya gushe ita zata iya cika mata burinta......wanne akasi ne?.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 66
66
_ko kisan manzan Allah S A W da kansa ya kasance yana neman
tsari daga sharrin abinda ya aikata da wanda bai aikata ba? Yakan
ce"Allahumma inni a'uzu bika min sharri ma amiltu wamin sharri ma lam
a'amal"_
_shi daya kasance Allah ya gafarta masa duk wani abu da
zaiyi da wanda ma yayi,ina gake?_
Dukka jikinta
sai ya dauki wani irin dumi,tamkar ma ta manta da fareeda dake zaune
gefanta,wani yalwataccen tashin hankali ya duro mata......cikin qasa da minti
guda taji tana tsananin buqatar ganinsa.
"Ke nake sauraro" Muryar fareeda ta yanke mata
tunaninta. Idanu ta zubawa fareedan na wasu daqiqu kafin ta kammala tunani a
kanta dukka cikin sakanni,murmushi ta sakar mata.
"Mu da kikaga muna cimma nasara a rayuwarmu......ba da
gaggawa muke tafi da komai ba......kibarmin komai a hannuna......indai kinga
baki samu fu'ad ba.....to tabbas bani na haifeshi ba". Maganar ta faranta
ran fareeda duk da ta xuba mata kokwanto me yawan gaske. Amma itama ta yarda da
kanta......tasan kuma nata kalar takun,don haka ta miqe da nata murmushin tana
ajiye mata bundle na dollars.
"Ki qara da wannan......amma buqatata yazo ya ganni
koda na minti talatinne kacal" Ta furta tana zuge zip din Jakarta,a qasan
ranta kuma tana samun tabbacin da gaske ne fu'ad baya sakar mata zallar ruwan
kudi.......abu na farko daya fara jefa mata shakka a zuciyarta akan matar.
Matashin
billionaire irin muhammad jadda......wanda tsananin yawan dukiya da arziqin
daya mallaka a gefe guda quruciya da kyau su suka saka mata kwadayin
mallakarsa......kudaden data bata din ya kamata ace a kullum a arziqinsa basufi
kudin siyan wasu qananun abubuwa ba....amma ya zamana ita ke fara'a da
samunsu?. A arziqin mahaifinta idan aka kasa arziqin fu'ad hamsin qwaya daya
ne.....amma ace ita karan kanta tana da qarfin halin yin kyauta irin wannan?.
TABBAS AKWAI MAGANA.....MAGANGANU MA,ta furta a sarari qasa qasa.
Kudin
kawai take juyawa a hannunta farinciki yana kamata. Ta samu kudin da zata
tunkari aikinta,duk da tana baqincikin yadda kudin xasu salwanta,amma kuma idan
ta tuna da ribanya ribarsu da zatayi sai taji koda ta salwantar da finsu ma ba
komai bane. Saidai tana buqatar magana da yarinyar.......maganar da zata sake
bata haske akan mataki na gaba da zata tabbatarwa boka shi take da buqata. Wa
zara kira?zuwaira.....
Kira
daya biyu uku hudu har goma wayar zuwaira a kashe take. Tayi tsaki har batasan
adadinsu ba,da waye zatayi magana ya hadata da yarinyar?. Tsam ta miqe data
tuna daxun maganarsu ta qarshe zuwaira ta gaya mata yarinyar taje gidan ita da
mamarta,saidai batasan ko tana can ko sun dawo ba. Ta qwalawa badawiyya kira
"Ki tafi gidan hamza ki karbomin number wannan
yarinyar"
"To hajiya" Ta amsa mata a ladabce sannan ta juya
tana ficewa ba tare data tsaya jiran komai ba.
Hannunsa ya
sanya saman labbansa kawai yana sauraren bayanin manager na gidan jarida na
qarshe da yakeyi,wanda banbancinsa dana sauran qalilanne
"Amma wallahi wallahi ranka ya dade kaman yadda 'yan
uwana suka fada ne......wallahi bansan sadda aka buga labarin ba......ni dinma
kamarsu gayyata na samu na taron 'yan jarida unexpected.......amma sanda na iso
na samu jaridar ta fara fita hannun dealers na dakatar da saidata......waye
zaiyi wasa da mutum kamar kai?,wanne gangancinne zai debi mutum......ko baya ga
haka kana da mutunci da martabar da bai kamata mu bari a bata sunanka dana
iyalinka ta wannan hanyar ba" Mutumin da aqalla ya kusa shekara sittin a
duniya ya fada cikin matsanancin takaicin yadda duk karamci irin na jadda
jaridarsa ta shiga sahun wadanda suka ci masa mutunci....duk da Allah ya
taqaita an daqile fitar jaridar.
Iska me
zafi ya furzar daga bakinsa yana sauke qafafunsa qasa,kanshi yana sake daukan
zafi da lamarin.
"Inason list na dukka mutanen dake da aiki a ranar a
dakin buga labarai.......da full details na kowa" Ya fadi a ransa yana jin
zaiyi aikin daya jima baiyi ba.
"Sir.......ai mun kammala wannan.....muna jira ne kawai
ka gama ji daga bakinsu......dukkanin dealers din mun karbi copy na newspapers
din daga hannunsu,yanzu haka ba wanda keda sample nata.....Allah yasa munyi
abun da sauri basukai ga rarrabawa qananun 'yan kasuwa ba,mun samu dukkanin
jerin mutane hamsin da uku dake da aiki ranar a gidajen jaridu ukun......saidai
mun rasa mutane uku a ciki,mutum daya daga gidan kowacce jarida......abinda ya
qarfafa zarginmu akan suke da hannu.......na tura ma'aikata don binciken inda
suke,kuma ina saka ran koda wanne lokaci zasu bani information,amma sauran mun
tabbatar basu da masaniya akan komai" Wani abune daya tsaya masa tun jiya
ya dinga sulalewa yana narke masa,ya gyada kai yana jin sassaucin dunqulallen
abun daya tare masa wuya. Kafin yayi magana aka nemi izinin shigowa dakin.
Ma'aikacin ya duba ya kuma bada izinin shigowa.
Salute
nasa sukayi mutum biyun da suka shigo,suka kuma miqa masa wani takardu.
"Auwal sadi.....nura mahadi......labaran
isyaku.....gaba dayansu mun samu tabbacin sun fita daga qasar nan kusan awanni
biyu da suka shude,saidai kowannensu mun samu tabbacin qasar daya
sauka.....auwal ya sauka a uk.......nura South Korea......shi kuma labaran ya
sauka a china".
"South korea.....UK.....china" Fu'ad ya furta
sunayen a fili yana irgawa da yatsunsa,sai ya fesar da iska a bakinsa yana
maida dubansa kan CP.
"Well done sir......i really appreciate your
effort,thank you for your hard work.......a sallamesu inason muyi magana
privately"
"Okay sir" Ya amsa masa cikin girmamawa.
Cikin qasa
da mintuna ya sallami kowa,ya kuma riski fu'ad din cikin motarsa qirar Mercedes
sprinter. Duk yadda yaso mazewa da ganin alatun dake cikin motar tamkar kana
cikin wani hamshaqin parlor din bawai mota ba amma ya gaza,sai daya daga kanshi
ya kalli saman roofing din da yafi kama da lafiyayyen roofing din dakin sanda
fu'ad ke qara hasken cikin motar daga galaxy blue stars zuwa brighter light.
"Ina expecting tafiya nan da kwanaki uku......inason
kayi gaba da kula da komai har zuwa sanda zan dawo......saidai banason binciken
ya dakata......zanyi qoqarin ganin an kawosu daga dukka qasashen da suka
tsallaka din don su fadi wanda ya basu contract din......wadancan mutum biyun
kuma,ko tambayarsu bana fata kuyi.....ajiya na baku......irin ajiyar nan ta
ma'anan ajiya" Yakai qarshen maganar yana tura cheque na kudi daya rubuta
masa masu yawan gaske. Kai ya girgiza
"Nop sir.....bazan amshi komai ba,aikina ne nakeyi kuma
dole mutum irinka a masa aikin daya dace saboda alfanunsa ga al'umma".
Wani abu dake gefansa ya dannan wata qaramar ma'ajiya ta fito,ya jefa cheque
din yana cewa
"Ba bribing naka nakeyi ba.......wannan din kyauta ne
na baka,na jima da sanin wanene kai......inda baka cancanata ba ko qwandalata
ba zata shiga hannunka ba.....kana daya daga cikin mutane masu aiki tuquru da
qoqarin kamanta gaskiya duk da yadda qasarmu ta lalace.....so you deserve
it,xan baka koda bakamin aikin komai ba"
"Thank you sir.....thank you so much" S.nuhu ya
fada yana jin dadin gwaggwabar kyautar da me jadda din ya bashi.
Tunda wuri
taqi zaman parlor din don batason ma ya dawo shi ya gansu ko ita ta ganshi,ta
zame tayi zamanta a daki dole amna ma ta biyo ta can.
Tana
saman sofa din dake gefe daya a dakin,amna na zaune saman tattausan carpet din
tana assignment. Idanunta kan takardun tana jin sha'awar amna din,tana jin
inama ace itace ta samu dama irinta amna?,inama ace ta samu daman zuzzurfan
karatu kaman amna?,wadda gata ya sanya tace bazatayi karatu wata qasar ba
tsabar samun dama.
Maida
bangon littafin tayi tana duban sabreen cikin murmushi
"Done......sai yanzu hankalina ya kwanta...lecturer
dinnan mugu ne adda.....any mistake game over" Murmushi ta tayata dashi,ta
jawo jakarta tana qoqarin maida litattafan
"Adda......kin taba jin labarin labarin uwar data
watsar da yaranta tun suna qananu ba tare data damu da waye zai kula dasu
ba?,waye zai zama gatansu?" Takai qarshen maganar tana zuba idonta akan
fuskar sabreen. Maganar sai tayi ma sabreen wani iri,a hankali ta girgiza kanta
"Aah amna"
"Kin taba jin labari,bayan wasu shekaru ta dawo
garesu,amma kinsan me yasanya ta dawo garesu?" Kai sabreen ta sake
girgizawa
"Kudi......arziqi da rufin asirin da suka samu tazo
ci,ba yadda suka rayu bane damuwarta......ba lafiyarsu ko akasinta ba".
Idanu sabreen ta zubawa amna tana jin labarin ya kasa kama hankalinta,tsahon
wasu mintina ba wanda yace da kowa komai,har sai da sabreen ta fara magana
"Wanne irin cukurkudadden labari ne wannan amna?,a ina
kika jiyoshi." Qaramar dariya amna ta saki tana janye jakarta gefe
"Labarin mijinki kenan.....hamma na....." Bata
qarasa ba shigowar saqo wayarta ya katse sauran maganar dake bakinta. Wani irin
shuru sabreen tayi lokacin da hankalin amna yayi kan wayarta
"Maamah?,mariya?....." Abinda kawai sabreen ke iya juyawa cikin
ranta kenan
"Bai rayu da ita ba?......batasan komai nasu
ba?......batasan wahalarsu ba?,dukiyarsu tasa ta dawo??,dukiya???" Tarin
tambayoyin da suka jujjuyawa cikin kwanyarta kenan. Maganganun amna gaba daya
sai suka kasance mata kamar ta jefeta da wata cukurkudaddiyar sarqa,ta kasa
hada daya da daya ya bata biyu.
"Unbleavable!......oh my god!" Amna ta furta da
wani irin qaraji,abinda ya yanke zaren tunanin sabreen kenan,ko kafin ta farga
har amna ta fado jikinta ta cukuikuyeta
"From nigeria to Maldives........wedding bells
adda.......wedding bells" Ta fada tana dariyar dake cakude da farinciki
zalla a muryarta. Qoqarin dagata sabreen
takeyi cikin murmushi da mamakin abinda ya sanyata tsananin farinciki irin haka
"Zaki karyani auta" Ta fada a dan shagwabe tana
riqe amna din. Da sauri ta dagata tana fadin
"Am sorry adda.....wani irin mamaki uncle BB ya
bani......yayi surprising dina irin wanda ya jima baimin ba......adda hutunmu
na wannan shekarar zai fara daga Maldives......kinsan mafarkaina akan wajen
kuwa?,kowanne year idan anzo zaben wanne qasa za'a je idan na kawo sai BB da
saddiq sun kushemin.......yaa musaddiq kawai ke goyon baya na" Ta qarasa
maganar muryarta a narke,da alama tana jin haushin yadda abun yake kasancewa.
Dan murmushi sabreen ta saki,don ita inda take maganar ma batasan ina bane
ballantana tasan muhimmancin da yake dashi ba da za'a dokanta aje.
"Your dream have come true"
"Really adda.......adda wannan shine tafiyan da
zatafimin kowacce dadi da alama......ina da sister like you nima wannan
karan.......ha saddiq ya daina yimin gori idan za'a fita......i don't know
yadda zan miki bayanin Maldives......but gani ya kori ji" Dan qaramin
murmushi ta aje mata kawai don ita bataga wani abun doki ba a nan.
"Labari na biyu adda.....muna da biki,borno zatayi
kira......bikin BB farouq date din yayi daidai da dawowarmu da sati biyu
kacal".
"Ma sha Allah.....Allah ya sanya alkhairi"
"Wannan qarshen shekaran bame sauqi bace
adda......can't wait......bari na bawa besty labari" Ta fadi tana laluben
number wayar aminiyarta guda daya da take da ita.
"Adda......anya ba honeymoon BB farouq ya hada muku
keda hamma ba?" Amna ta dakata daga qoqarin kiran besty din nata da take
tana duban sabreen. Bata jira ma sabreen ta bata amsa ba ta saki dan qaramin
ihu tana tsalle gefe
"It makes sense👌.....that's my big bro
farouq" Amna ta fada tana dariya nishadi kaman zai kasheta. Baki kawai
sabreen ta kama tana kallon amna
"Amna......nace miki binku zanyi?". Tana dariya ta
bata amsa
" It's for the whole family adda........kowa ma yana
tafiya hutu a wannan lokacin,indai kai under jadda family kake......hatta
ma'aikatan dake aiki cikin gida lokacin hutunsu ne.....kawai dai,nayi mamakin
rage date din da aka saba tafiyan" Ta fada tana duba wayarta.
Rasa
abinda sabreen zata fada tayi,maganan gaskiya ita sam bata shirya zuwa ko ina
dasu ba,don bata jin tana cikin family dinsu,hasalima tazara take son bayarwa
tsakaninsu.
Duk sanda
amna ke waya da qawarta ita tayi nisa wajen juya maganganun amnan. Wani irin
mamaki ke tsarga mata,wai dama haka matar take tun usul?,ta yaya zata samu
gaskiyan abinda amna ta gaya mata?,tun tale tale gurbataccen hali gareta?,indai
haka ne mene yaran sukayi me muni da zata cutar dasu?. Kwanyarta ta sake
harbawa,da qarfi da yaji ta soma qoqarin hada daya da biyu ko zata bata daidai
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
67
_Manzan Allah S A W yace "idan dayanku zaiyi fada/zai
daki dan uwansa,to ya guji fuska/kada ya mari fuskarsa_
🧏🏽 _sai a kiyaye,mari ko dukan fuska
haramunne a musulunci_
"Biri yayi kama da mutum,tsananin qaunarta da duniya da
kuma dukiya,shine silar qoqarin mallakar d'anta ta qarfi da yaji?,wannan shine
daliinta?". Numfashi ta fitar me nauyi tana saka hannuwanta saman fuskarta
" Adda......maamah keson magana dake" Amna da
sunan maamah din ya fito ta true call din ya gaya mata wace ta fada kai
tsaye,duk da bata da tabbacin da sabreen takeson magana.
Hannu
kawai ta bawa amna,tana maida wayar kunnenta.
"Har yanzu kina kan bakanki?,kinci gaba da lamuntar
jefa rayuwarki cikin hatsari maimakon tseratar da rayuwar taki?,a naki
tsammanin kin tsira kin tseratar da yan uwanki?"
"Idan kura tana maganin zawo ta yiwa kanta mana?".
Dif maamah tayi,batayi gaggawar amsa mata ba,don maganar ta jefeta da wani
qudundunanniyar ma'ana.
"Kece kike sake tafka kuskure akan kuskure......kuma
kwanaki dukka wani sirrinki yana qarewa.......komai yana dab da bakaduwa tamkar
yadda iska ke diban lallausan gari tana watsashi cikin mutane........ashe ba
kaina kika fara nuna rashin sanin darajar halittar D'A ba......ashe baiwa ce
sanin darajar haihuwa a zuciyar iyaye......d'anki bashi da muhalli ko daya a
zuciyata ko rayuwata,.....kaman yadda banda sha'awar zaman aure
dashi......saidai fita a gidansa da rayuwarsa duka sai sanda naga dama... Kinsan yaushe nake nufi?" Bummm zuciyar
maamah ta buga tun bataji qarshen zancen ba
"Zan fita ne a sanda na gama karanta masa ainihin WACCE
KALAR UWA yake da ita......ba don ina sonsa ba......sai don alkhairi guda daya
tak da yayimin........ya karbo 'yan uwana daga hannunki ya
kawominsu......abinda yayi silar takawarsu tudun muntsira......ya sanyasu
hayewa duk wasu qananun qullinki.....zan saka masa da iya wannan,don bashi da
wata nagarta ko guda daya da zata sanya sabreen sha'awar kasancewa
dashi......ki riqe wannan......ki rubuta ki ajiye......sabreen ce zata zame
miki silar BANKADA!" Tana kaiwa nan
saita kashe wayar ta azata saman cinyarta tana ci gaba da lullube fuskarta
"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" Ta
dinga maimaitawa,tsanar uwa da danta duka suna turereniya cikin zuciyarta.
Ko da
amna ta dawo abinci kawai taci ta fara list na abubuwan da zasu buqata lokacin
tafiyar da abinda zasuje dashi. Ba wani abu data tofawa amna sai idanu da take
binta dashi. Ba qaramin jarumta tayi ba da take iya binta da murmushi ba,gaba
daya ganin abun take a wani abu maras yuwuwa,ita ba ahalinsu bace,bata kuma
tunanin zata zama ahalin nasu.....hasalima gaba daya lissafinta yafi karkata ga
qarawarta gaba kafin sukai ga dawowa daga yawon qasashe hudun da suka tsara
zasuyi,kowacce qasa zaman sati guda zasuyi,ciki kuwa harda umra data zame musu
dole duk lokaci irin wannan.
Dukka
maganganun sabreen sukayi mata tsaye a rai,a daren ranar duk inda ta juya
furucinta ne ke mata kai kawo a rai.
Tanaso jin
rauni game da yarinyar yana sauko mata,amma wannan dakakkiyar zuciyar da
shedaninta dake gefe suna gaya mata
_karamar halitta irin ta mace......yarinya qarama me qananun
shekaru bai kamata taga rauninki ba.....bai kamata ace itace taci galaba
samanki ba_. Abu daya ta kasa samun aminci akan yarinyar shine
'Yiwuwar aikata komai". Ko ba'a fada ba ta
sani......sabreen zata iya aikata komai,tana da taurin zuciya da qwarin zuciya
dama zarrar da zata iya yin komai.....wannan zarrar tata ita taja hankalinta ta
zabota zuwa ga aikin da bata taba kawo komai zai warware da wata irin faduwa da
rashin nasara haka ba.
Tunda ta
idar da sallar asuba bata koma bacci ba. Ta jira har sanda gari yasha,sannan
tayi wanka,ta shirya kaman kullum da qasaitattar shigar nan tata dake qara mata
jin izza da jin takai inda ya kamata ace takai din,saidai bata qarasa gabar da
take da muradin qarasawa ba.
Wayarta ta
fitar ta kira driver dinta,ya tabbatar mata yanzu haka yana cikin mota yana
jiranta,kai tsaye ta dauki jakarta tana yafa mayafinta ta fice.
Dab da
zata bar falon taji laila na kiranta
"Maamah" Tsaiwa tayi tana jan tsaki,don bata
shirya komai ya dakatar da ita ba. Qarasowa lailan tayi,ta kuma zube a gaban
maamah din. Sam tun daga waccan ranar bata iya tsaiwa gaban maamah.....magana
ce ko gaisuwa zubewa takeyi a gabanta tamkar bawa da uban gidansa.
"Ina fatan ba wani abu nayi miki ba maamah?" Ta
tambaya da tsananin tsoron kada ranta ya baci
"Naga zaki fita baki tasoni ko kisa an gayamin ba"
. Wani qaramin tsaki maamah din ta saki,wannan abun ya fara isarta,ba wani
motsi da zatayi sai yarinyar ta buwayeta. Irin wannan abun da akan fu'ad ya
fada tabbas zata iya cewa tafi kowanne mutum sa'ar zuwa duniya. Ko yaya taga
fuskarta ta canza takanyi kaman zata fashe da kuka,komai kuma har abinda bai
dace ta sani ba game da lailan lailan saita gaya mata
"Unguwa zanje,kafin na dawo ki gyara falo din,ki hada
da bedroom din,duk abinda kika gani ki ajiyeminshi inda kika ganshi,kada kibar
kowa ya hauramin sama,akwai underwears dina dana cire ki wankesu ki shanya a
backyard ki jira su bushe ki dawo min dasu ciki"
"In sha Allah an gama,Allah ya dawo dake lafiya"
"Amin" Ta amsa tana yin gaba. Sau tari idan taso
bautar da laila sama da haka sai wata zuciyar ta gaya mata lailan kome tayi
bisa jagorancin mahaifiyarta ne,wannan ya sanya take sassauta mata akan abubuwa
da dama.
Tafiyar
awa daya da rabi cif suka fara gangarawa mummunan jejin,sai da suka sake kashe
wata awar sannan suka isa. Daga nesa ta sanya driver din ya sauketa,sannan ta
tattare zanin tsadaddar atamfar jikinta ta fara tsallake qayoyi da busassun
tsirrai tana wucewa ciki.
Gurine da
zaiyi wahala kaje ka taras d wani duk da tarin al'ummar dake zuwa wajen a kulli
yaumin neman duniya,tamkar sun manta da wata rana da zaa shimfidesu babu wannan
ruhin daya zama masarrafi na motsinsu da kai kawonsu izuwa gurare daban daban.
Ba wata
kafa a jikinta da bata fitar da gumi sanda take zaune a gabansa tana jiran
bayanansa na qarshe. Da qyar ta samu ya ganta.....don sharadinsa ne baya aiki
biyu akan matsala guda daya.
"ZANGON NASARAKI guda daya ya rage miki......BANKADA
zata sameki.....tonon asirinki zai fara daga yanzu zuwa kowanne
lokaci.....zangon nasararki zai iya narkewa ya dulmiya sanadin hakan!!!"
Ya furta da wata irin murya maras dadin amo.
Dukkanin
'ya'yan hanjinta taji sun tattara sun cure guri daya,idanunta suka qara girma
saboda wani sabon kalar tashin hankali da bata taba jin makamancinsa ba
"Kanaso kacemin itace zatayi nasara a kaina?!!!"
"Me muka gaya miki wancan karon?!!!!......" Wasu
muryoyi da tafi tsammanin sun kusa guda goma sukayi amsa kuwa a wajen kafin
bokan ya karba
"KINYI GANGANCIN ZABOTA......SAIDAI TAURARONSA DA NATA
TAURARIN KADAI SUKA DACE......ITACE KADAI MAHADIN AIKINKI........zabi biyu
gareki.....ko ki kasheta duk wani burinki ya dulmiya ya koma mafarki......ko ki
barta ta rayu kina kallonta kuma naki burin shima yana raye amma babu wata dama
ko hanyar cikashi.....zan miki wani aiki guda daya......amma daga kansa!....ina
me gargadinki kada ki kuskura ki sake dawomin akan matsalar data
shafesu.......aiki yayi kyau ko akasin haka......".
"Na gode da wannan dama daka bani.....na tare dakai su
dafa maka" Ta fada jikinta yana rawa da jin qarin dama guda daya,abinda a
tarihinsa bai taba ba maimaicen aiki.
"Zaayiwa na tare dani da ma'aikata yanka......zasusha
jini wadatacce da zasuyi aikin jinkirtawar tonuwar asirinki........yayin da
zangon nasararki ya kama......nan da kwanaki goma sha hudu zuwa ashirin da
daya......kiyi duk abinda zakiyi wajen ganin muradinki ya cika......ke zaki
yiwa kanki wannan aikin.....mun miki alfarmar samun jinkiri kadai.....amma ki
sani tabbas RANAR HASARA DA RANAR TABEWA TANA NAN ZUWA.......DOLE KI FUSKANCETA
DA DUKKANIN ZUNUBANKI.........KIYI NESA NESA DA MATSANTAWA TAURARINTA........BA
NASARA TA KUSA KO TA NESA......NATA ZANGON NASARAR YANA DAB DA FADOWA
HANNUNTA".
Duka
bayanansa bai wani dameta ba......zangon nasararta da damarta guda daya daya
tabbatar mata ita tafi komai yi mata dadi. Kudade masu kaurin da suka haura
million hudu ta zube masa,sannan ta fita da baya da takalmanta a hannu ranta
fes,tana gayawa kanta dogon zangon tunani ya zame mata dole don samun
kyakkyawar mafita.
Tabbas ta
kowacce fuska tana da buqatar barin sabreen gidan koda itace murfin
nasararta.......gwara tasan yadda zatayi ta maye fareeda da ita a madadin cikar
burinta.
★Hadith yana daya daga cikin karatuttukan da suke mata dadi
qwarai. Sau tari idan suna karatunsa da rumaisa yafi kowanne littafi daukan
musu lokaci.
Ko a
yanzun da take zaune tana bita amna na zaune a gefanta,sunata hira da anni
wanda rabinta kusan na tafiyarsu ce jibi,lokaci lokaci kuma da tsare tsaren
abinda zaa gudanar da bikin farouq.
"Anni....gata karatu take,ki mata magana don
Allah" Ta fada a narke. Duk da sabreen batasan akan me amna ke magana
ba,amma sai data daga kanta da sauri. Tana balain jin kwarjinin matar da ganin
kimarta,daidai nan amnan ta miqo mata wayar tana danne dariyarta hadi da hade
hannun alamun am sorry. Da idanu ta nuna mata zan kamaki sannna ta karbi wayar
tana sakawa a kunne
"Barka da dare d'iyata.....ina fatan dai bata miki
shirme?"
"Barka da dare anni....." Ta fada tana murmushi
"Ya jikin naki?...ina fata dai kinji sauqi?"
"Alhmdlh na warware....anni na gode"
"Ba godiya ai tsakanin uwa da d'iyarta......nace
ba,nasan halin yarona sarai,duk sanda tafiya irin haka ta kama saidai a tayashi
shirya kayanshi shi kansa,nace idan akwai wani abu da kuke buqata na tafiyar
kiyi magana....karki daukeni suruka ameenatu ni mamarki ce,ki rubuta sai a
kawo,idan kuma ta amnan zakiyi to saiku fita tare goben,saiki masa
magana" Kunya ta sake
kamata,bangare daya kuma tana jin wani iri. Ta aza an soke zancan tafiya da ita
ne kwata kwata,don tun randa akayi maganar da amnan tace BB farouq yace ta bada
details dinta da sauransu bata sakejin komai akai ba.
"In sha Allah anni......Allah ya saka da alkhairi ya
qara girma"
"Ameen ameen,a baya magaji ne yake hada masa necessary
abubuwan da zai tafiyar dasu.....ina fata yanzun zaki maye gurbin hakan?"
"In sha Allah" Ta amsawa annin tana jin wani qaton nauyi ta aza mata
akai,daga nan ta miqawa amna wayar ta maida kanta kan karatun.
Amma kuma sai
karatun ya gagareta,saboda batasan yadda zata cika maganar anni ba. Batason
haduwa dashi kwata kwata,hakanan idan batayi yadda annin tace ba zai zama kaman
rainuwa,kuma amna da akayi a gabanta ba zataji dadi ba.
Dabara ce
ta fado mata,ta rufe littafin tana duban amna data gama wayar.
"Kina da number magaji din?"
"Eh ina da" Amna ta amsa mata
"Faka faka kiramin shi" Ta furta tana gyara daurin
dankwalinta. Sosai abun ya yiwa amna dadi,ta kira magajin ta hadata dashi.
"So nake nasan da meye da meye ake hadama boss idan
zaiyi tafiya?". Tayi maganar tana miqawa amna hannu alamun ta bata takarda
da abun rubutu.
A
ladabce ya dinga zayyano mata tana rubutawa,har ta gama tsaf tayi masa godiya
ta yanke kiran,ta miqawa amna bironta ita kuma ta miqe da takardar a
hannunta,amna ta bita da kallo tana murmushi. Tasan abinda take shirin
yi,zataje ta hada masa jaka tana tunanin baya nan kafin ya dawo,saidai tun
daxun taga shigowarsa,kawai bata gaya mata bane tunda ta lura ba hawa saman
take ba,itadai adduarta daya Allah yasa adda sabreen din bata cikin sahun
shashashun matan nan da basu iya baiwa miji kulawa,duk da itadai a hakanta a
halittarta bataga alamun hakan ba.
Duk da
tana da yaqinin baya nan,amma duk taku daya sai bugun zuciyarta ya qaru,kaman
yadda numfashinta ke fita da nauyi.
Bude smart
door dinsa bame wahala bane a wajenta,saboda tuntuni ya sanyata cikin sahun
masu shiga kai tsaye.
Ko ina
fes kaman yadda ta saba,yana fita da safe take shiga,tasan lokacin fitarsa,zai
kuma wahala ya wuce wannan time din be fita ba,zata shiga ta kintsa komai. Duk
da baya barin komai sai dan goge goge da qananun datti,bai taba barin
underwears dinsa ba koda kuwa singlet nashi bata taba gani ba,abinda ma ya
sanya mata qaramar nutsuwa kenan.
Bedroom
dinsa ta wuce,tayi kuma amfani da details din da magaji ya bata ta dinga fiddo
da komai,sai data hada shi tsaf sannan ta rufe briefcase da luggage din ta
ajiyesu a gurbin da ta tabbatar zai wahala ya kasa ganinsa.
Yadda
batayi zaton ganinsa ba haka shima baiyi wannan zaton ba. Batasan ya shigo
saman ba kwata kwata. Ta zare idanunta daga cikin nasa idanun da yau take ganin
kamar sun rusuna sunyi kuma laushi,can qasan ranta tana mamakin yadda ya
balbalawa kansa A.c tayi qau a falon,abinda iya saninta dashi ba sabonshi bace.
Idan kaga ya kunnata ma to tabbas ranan ana zafi,ko kuma bai samu irin fresh
air din da yakeso ba.
Kanta ta
dauke sosai ta fara takawa zata wuceshi,yau daya sai taji tana jin shakkar
giftashi,koda kuma bata kalleshi ba tana jin kaman idanunsa a kanta suke.
Allah ne
kadai ya sauko da ita,don bibbiyu bibbiyu take hada stairs din tana
saukowa,tana jin kamar zai biyota yayi jan masifar daya saba,tana kawowa bakin
bedroom dinta ta saki numfashi tana danne qirjinta.
Sai
data bacewa ganinsa ya dauke kansa daga wajen yana maida hankalinsa kan wayar
huda dake hannunsa wadda yakewa kallon wayarta. Tun ranar yake sake zurfafa
bincike cikin wayar......amma kullum abinda zai gani a ciki taba masa rai
yakeyi. Tarin massages na nuna zallar soyayya da kewa,zuciyarsa ba irin abinda
bata raya masa yayi ba amma yana danneta d wani irin qarfi dashi kansa baisan
yana da ita ba. Abu daya ke taka masa burki,cases din da zaiyi tafiya ya
bari,amma ya tabbatar zuwa sanda zai dawo komai yayi settling......a lokacin
zata kwashi kashinta a hannu,zaikaita ainihin kurkukun da itace asalin wadda ya
tanadar mata.
Qarar
wayarsa ya janye hankalinsa daga wancan tunanin,ya dauka yana dubawa don kusan
duka saqon da zai shigo masa me amfani ne.
_ko a kusa ko a nesa duk inda zaka ina tare da kai,toshe
kirana bawai yana nufin toshe soyayyarka daga zuciyata bane........ferree dinka
ce_ ta saka sign na kiss da love daga qasa
Matse
wayar yayi a hannunsa,yanajin bai taba jin tsanar wani abu a duniya ba irin
yarinyar......tabbas tace zataci gaba da bibiyarsa nan da sati daya zai nema
mahaifinta yayi magana dashi. Y janye diyarsa ya siya mata girman da ita ta
gaza siyawa kanta.
★A daren washegari zai shigo mata amna tayi kawai da wata
irin luggage da itadai idan tace ta taba ganin akwatin daya mata kyau irin
wannan tayi qarya. Komai da matafiyi zai buqata an kammala mata shi an damqa
mata a hannu. Wayar amna ta karba tayi kiran titi bayan ta zuba numbers din
titin data rubuta ta aje saboda gudun bacewa. Har yanzu tana mamakin yadda
wayar huda ta sake bacewa a dakin,saidai zuciyarta tanata qarfafa mata zargin
shine ya sake daukewa.......don tun randa wancan incident din ya faru bata sake
ganinta ba.
Magana
sosai sukayi da titi din dasu huda,ta kira momma bahijja ma ta mata
sallama,hankalinta ya kwanta sosai data samu yaqinin cewa kwana uku da
tafiyarsu suma zasu isa mali,kunya tadan kamata sanda momma din ke tsokanarta
honeymoon zasuje?
"Saura satittika kadan ya rage nima na biyo bayansu
zuwa tushen mahaifiyata momma" Ta furta a ranta.
Sosai
taji zuciyarta sakayau,hankalinta ya sake kwanciya,amma saita dinga jinta cikin
wani kadaici,tana jin kamar ita daya tayi saura a Nigeria,saidai kuma tana jin
sassauci idan ta tuna itadinma kwanaki
kadan zata iskesu su sake shimfida sabuwar rayuwa me inganci tare.
_hmmmm,nace ko dama zata bada daman hakan?_
*_MALDIVES........_*
*KOMAI NISAN JIFA*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
68
*_Na muku post saboda jiran kwana biyu da kukayi,don Allah
banason complain,dole zaa zo inda kuketa zakwadin🧏🏽🤦🏽♀️🙄_
_Allah don isar mulkinka,don buwayarka,don girman soyayyar
da take tsakaninka da muhammadurrasulillahi,dukkaninmu bayinka ne,amma akwai
bayinka dake zaluntarmu suna fitar mana da pages,Allah kafi kowa sanin yadda
muke wahala,mun killace haqqinmu bamu tilastawa kowa ba akan yazo inda
yake,amma suna biyomu suna zaluntarmu YA ARHAMAR RAHIMEEN KAFI KOWA SANIN BAMU
ZALUNCESU BA....YA ALLAH KO WACECE IDAN BATA DAINA BA ALLAH MUN GATA NAN,MUN
KAWO QARARTA KOTUNKA ME ADALCI,YA ALLAH....YADDA TAKE TARWATSA MANA KASUWANCI
UBANGIJIN SAMMAI DA QASSAI KA TARWATSA NATA KASUWANCIN,ASARAR DA TAKE JA MANA
ALLAH KA NINNINKA MATA WANNAN ASARAR AKAN NATA KASUWANCIN DON ISAR MUHAMMADUR
RASULILLAHI A FADARKA AMEEN_
*_REPUBLIC OF MALDIVES_*
*MALÉ*
*Velana international airport malé_*
Misalin qarfe
hudu agogon Maldives wanda yayi daidai da qarfe takwas na dare agogon Nigeria
private jet din mallakin Muhammad fu'ad jadda wanda ke dauke da sunan JADDA
WINGS ya sauka a babban filin tashi da saukan jiragen sama na velana
international airport dake babban birnin Maldives wato malé.
Daidai
sanda jirgin ya kammala tsaiwa gaba daya sabreen ta sauke numfashi a hankali
tana lumshe idanunta gami da budesu kusan lokaci daya.
Wani abune
da take ganinsa tamkar cikin mafarkanta,gata cikin qasar da koda sunanta sai
lokuta d'aid'aiku ta taba jinta ballantana mafarkinta yakai ga zuwa qasar.
Tun daga
kano zuwa lagos da suka sauka na wasu mintuna,kafin daga bisani jirginsu ya
taso zuwa Maldives tasan tabbas duniya cike take da yalwa da fadi. Abu guda
daya daya dinga bata sha'awa.....wanda ita kanta batasan abun na burgeta ba,sai
data samu kanta tana fatan
"Allah yasa nan gaba kadan rayuwarmu ta kasance kaman
haka....ni huda nadra haneefa". Bawai kalan arziqin jadda family bane
abinda yaja hankalinta da gasken gaske ba....a'ah.....kalar qaunar
juna.....bawa juna kulawa da kuma soyayyan juna da take gani a idanunsu irin na
zallar 'yan uwantaka.
A
tsakaninsu zata iya cewa ta zama 'yar kallo kome daukan rahoto,duk kuwa da cewa
sunata qoqarin jefota cikin hirarrakinsu da kowacce magana data shafesu. Sau
tari saidai ta murmusa kawai,tana karance da halayen kusan kowa a cikinsu.
Farouq
nada tsananin kirki......yana da nuna kulawa da soyayya da 'yan uwansa,yana da
wasa da dariya da 'yan uwansa.....amma mugun muskili ne kuma hutsu idan baiga
dama ba.
Saddiq yana
da zuciya,yana da saurin fushi amma kuma yana da saurin saukowa,yana da kula da
damuwa qwarai da gaske da al'amarin 'yan uwansa.
Musaddiq dataji sunata waya dashi kafin tashin jirginsu,wanda a yanzu
haka shi yayi landing ma a Maldives din,bazatace ga hali ko dabi'arsa ba,illa
abu guda daya data lura. Shima me yawan nuna kulawa ga 'yan uwansa ne da damuwa
dasu.
Sai oga
boss muhammad fu'ad jadda.........shi kadai halinsa yasha banban ta kowacce
fuska da 'yan uwansa......ta fuska daya sukayi musharakar halaye,wato ta fannin
qauna ga 'yan uwansa......wata irin qauna da a fuska ba zaka ganta ba,hakanan a
fili ba zakaga wani alamun damuwa ko kulawa da lamarin kowa bama tattare
dashi,saidai kuma yana ankare da motsin kowa da kai kawonsu. Wani irin bahagon
miskili da koda magana zaiyi saika rantse ya lissafe take,bayason lafuzansa
kuma su qare,kaman tattalinsu yake,baya magana ya maimaita maka,kaman yadda bai
fiya nuna damuwa ko zafafawa akan al'amura ba. Zaka dauka bai damu da komai
ba,baya kuma kula da komai,saidai kaifin lurarsa akan komai tasha banban data
kowa. Yana da wani irin fahimtar komai da kowanne motsi dake kewaye dashi,yana
da kaifin lissafi,dogon tsinkaye da nazari kafin yayi magana. Ba'a kan komai
kakeji yayi magana ba,ba kowanne abu bane zai kalla yace wani abu ba koda yana
sane da wannan abun.
Dukkaninsu
sunyi tarayya akan abu guda wato son anni......kowa a cikinsu wani unique love
yake nunawa annin da qauna me tsananin yawa......takan shiga lissafi me zurfi
idan maamah ta fado ranta,amma kuma idan ta tara da 'yan maganganun da amna ta
fara yi mata,sai taga lallai komai yana da nasaba da wannan.
Ko yanzun ma
da jirgin ya tsaya,saddiq nata fiddo musu luggage dinsu daga overhead
compartment jordan na sauka dasu,shi kam sai a sannan ya rufe system dinsa da
batasan abinda yakeyi ba a ciki tunda jirgi ya daga.
Tun zamansu
daga lagos har kawo yanzu tana gabanshi. Tana jin farouq daya gaji da yadda ya
bata hankalinsa yace
"Yallabai hutu fa zamu tafi,tun yanzu ka fara bata
tsarin hutun?,ya kamata komai a ajjiyeshi a side ko?". Kai ya
girgiza,kaman bazaiyi magana ba,sai daga baya ya daga idanunsa ya zubewa farouq
dinsu
"Ba zaka gane ba.......koda na tafi hutu bazai yiwu har
ta internet na tafi offline ba" Baki farouq ya tabe yana jinjina kansa,can
qasan zuciyarsa shi yasan me yake tsarawa.
Jordan ne
ya qarasa ya tattare masa dukka tarkacensa,yayin da shi kuma ya miqe yana zube
hannuwansa cikin aljihun 3pices suit din jikinsa yana takawa gaban anni.
Duqawa
gabanta yayi kadan yana gyara mata zaman takalmanta da take qoqarin sakawa.
"Ina fatan zaman jirgi bai saka ciwon qafarki ya tashi
ba?" Murmushi ta saki,tana fatan yadda yake da tsananin kulawa a kanta
taga yana yin sama da haka akan matarsa.
"Alhmdlh......last checkup din da mukaje ai sun bada
dokoki,kuma na kiyaye alhmdlh......je ka duba matarka" Ta fadi tana miqewa
hadi da ambaton bismillah.
A kunnen
sabreen anni ta furta hakan,numfashinta yadan tsaya na wucin gadi,ta danyo
rolling idanunta tana miqewa. Batason kowanne abu da zai hadata dashi
ballantana ya gasa mata magana. Maganan daya gaya mata kafin tasowarsu daga
lagos kadai ya isheta basai ya qara mata da wani ba.
Cikin
ma'aikatan airport dinne,wani a cikinsu yaketa haba haba dasu ita da amna.
Itakam bata kawo komai cikin ranta ba,don bata ma sake masa ba,amna ce kawai ke
dan amsa tambayoyinsa,har zuwa sanda zasu wuce sai yace
"You look so familiar madam....." Ya fada yana
dubanta da murmushi. A dan mamakance ta waiwaya tana dubansa,kafin kuma tace
komai ya sake fadin.
"A abuja......hotel din....."
"Stop mr man!" Dakakkiyar muryar fu'ad ta dakatar
da mutumin cikin kaduwar hanji. Sam baiga isowarsa wajen ba,mutumin tun dazu
yake masa kwarjini.
Duqar da
kansa yayi da sauri cikin rawar jiki yana cewa
"Sorry sir". Bai ko kulashi ba ya kalli amna,da
idanu yayi mata sign na ta wuce,sai tayi qasa da kanta tana yin gaba. Ganin
amna ta wuce itama saita taka zata bita,bai hanata ba,yabi bayanta shima,saidai
ya gasa mata maganar da sai da qwalla ta diga ta samu sassauci
"Shi abun qwarai da mummuna tabo gareshi......mu'amala
da tarin mazaje ba shine mutuntaka ba ta d'iya mace.... Mutuncinta namiji daya
da zai amsa sunan mijinta,bariki bata da riba kota rana daya ce kuwa......duk
wanda zai hada zuri'a da macen bariki saiya shirya......ba qaramin cutarwa bace
ga 'ya'yan da zasu haifa idan aka ture nashi matsalan na qashin kansa".
"Macen bariki......mu'amala da tarin mazaje"
Wadannan kalmomin su sukafi komai tsaye mata a rai.
Wanne irin
mummunan kallo yakeyi mata ne wai har haka?,wanne mummunan fassara yake mata
ne?. Tana ji ta soma gajiya,ta fara kaiwa iyaka,daga yanzu zuwa kowanne lokaci
zata iya fashe masa.......ba zata iya ci gaba da dauka ko jurar irin wadannan
tuhume tuhumen da maganganunsa da basu da tushe ba,tana jin zuciyarta da
idanunta na mata wani irin suya,bata samu sassauci ba sai bayan da jirginsu ya
doshi Maldives......hirarrakin family din da uwa me goya marayu wato anni ita
ta sama mata relief a zuciyarta,saidai tana jin ta wani irin sake tsanarsa,ta
kuma sake tsanar hada komai dashi.
Gabanta
ya tako,abinda ya sanya amna gocewa da sauri tunda ita ke first seat da zummar
yin gaba
"Karki fita......ki jirata" Ya fadi da husky voice
dinnan nasa data sake dakewa,tun daga tashinsu daga lagos din bayan wancan abun
daya faru zuwa yanzu tana ankare da hamman nata. Sai dacin rai kawai yakeyi
wanda shi kansa baisan yana yi ba,jifa jita take satar kallonsa,har a sannan
kuma ta tabo sabreen
"Adda........wai dama haka hamma yake da kishi?,daga
cewa you look familiar?.....haka hamma yake sonki?" Ta fada tana murmushi
kaman abun yana burgeta. Sau daya tak ta kalli fuskarsa sanda yake fama da
system dinsa,saita maida idanunta ga window din jirgin tana duban yadda suke
dai da daidai da gajimare. Abun yana burgeta,tunda shine karon farko data fara
keta hazo......saidai can qasan ranta yana cunkushe da halayensa.
"Ba kishi bane.....izza ce wulaqanci da kuma
izgili.....har yanzu banga wani kyakkyawan halayensa guda daya ba......koma dai
meye saura kwanaki kadan suka rage na barshi shi da halinsa dama tarin dukiyar
dake sanyashi dagawa izgili da girman kan ma" Tayi dukka maganar a
ranta,amma a fili murmushi kawai ta yiwa amna. Amnan bata damu ba taci gaba da
dauko mata gulmarsa kadan kadan,tunda ta saba da halinta na wannan fannin. Ba
komai sabreen din ke bude baki ta bada amsa ba a maganganu da dama.
To a
yanzun da yake tsaye a gabanta bata dubeshi,sam bata qaunar hada idanu dashi.
"Ko meye zakiyi a yanzu ki dinga tunawa akwai igiyata a
kanki......bazan kuma lamunci kowanne abu da zai zama tozarci ga igiyata
ba......zan iya daukan kowanne mataki mara dadi muddin kikayi wani abu daya
sabawa shari'a......ki kula,ki kula da kyau". Kasa jurewa tayi,haka siddan
daga saukarsu a qasar,kowa ya sauka da walwala itama ta samu ta fara tattalin
tata zai watsa mata ita. Fararen idanunta ta daga ta watsa masa wani.kallo
tsakiyar idanu. Wani haske suka fitar sosai saboda fushin dake cikinsu,wani salon
kallo da baiyi kama da harara ba,shi kuma ba kallon banza ba. Ta motsa siraran
lips dinta zata ce wani abu,sau kuma taga hakan baida ma wani fa'ida......bata
da sauran lokacin batawa,don haka ta soma qoqarin rab'eshi ta fice.
Sosai
taji an damqi hannunta da wani tsatsauran riqo,ta waiwayo da hanzari tana
dubansa,ya damqeta ne ba tare da ya ko waiwayo ya kalleta ba,qeyarsa kawai take
iya gani,da hannu daya ya jawota ya dawo da ita gabansa,ya sanyata a tsakanin
idanunsa yana mata wani irin kallo da taji ya tsaye mata a sassan jikinta,ya
kuma soma sauke rashin kunyar da taji tana taso mata
"Duk sanda kika sake gangancin wuceni ina magana.....na
rantse da Allah sai na gwada miki ina da banbancin da lusaran mazan barikinki
marasa daraja......dole ki amsa min kowacce magana kaman yadda nakeso.....don
banajin muryarki tafi tawa tsada ko daraja.....ko banza adadin mazan da sukaji
muryarki baikai adadin matan da sukaji tawa ba......kinjini?!" Ya furta da
dan tsauri idanunsa na kallon wani gurin daban sabanin cikin idanunta
"Eh naji" Ta amsa a sanyaye kanta yana kallon
qasa. Shigowar farouq ta gani daga bayansu,wanda ta tabbatar shi bai gani
ba,sai ya sakar mata hannun yana juyawa gami da takawa a hankali yana ficewa a
jirgin.
Hawayen da
take riqewa ne suka yiwa kansu da kansu hanya. Ta sanya tissue tana daukesu
"Ya isa......ya isa" Take gayawa kanta da kanta.
Tana cin alwashi a ranta ko ya bata takardarta.....ko bai bata ba,sauna sauka a
nigeria zaman aurensu ya qare......ko ya sallameta ko bai sallameta ba wannan
duka damuwarsa ce,alwashi ta ciwa kanta.....wannan karon babu abinda zai
dakatar da ita......ba kuma wanda zai hanata.
A hankali
ta fara takawa itama tana nufar qofa da shimfidadden matakalar da aka jinginewa
jirgin. A nutse take sauka tana qoqarin daidaita mode dinta gudun saka damuwa a
zukatan amna da anni.
Three
pieces turkish gown ne a jikinta,wadda take hade da strips skirt da kuma blouse
data zauna daidai jikinta,tayi kuma took in da ita kaman yadda tsarin kayan
yake,sannan ta kawo doguwar gown din kayan me budadden gaba data sauka har qasa
ta kuma bude sosai daga qasan. Qafafunta high hill ne masu madauri da suka dace
da kalan rigan. Sosai kayan suka karbeta,baka ganin komai sai fuskarta,zaka
rantse da Allah bata hada nasaba ta kusa ko ta nesa da nigeria ba.
"Wallahi anni adda sabreen kyau takeyimin......komai
nata me kyau ne.....duk kayan data saka sai naga kaman don ita aka yisu"
Ta fadi maganan tana matsawa kunnen anni,saidai fuad dake tsaye daura dasu yaji
abinda ta fada din.
Haka
kawai ya samu kansa da daga kan nasa,suka kuma yi masa jagora a kanta duk da
yadda yake qoqarin hana hakan faruwa. A kasalance take tafiya saboda bacin
rai,sai hakan ya sake zama kaman cikar adon tafiyartata. Idanunta suna lumshewa
kadan gami da bude kansu duk a qoqarinta na hana zuciyarta karyewa,ta kuma hana
idanunta zubda ruwan hawayen da takeji suna tattara kansu. Amna dake mata
murmushi ta maidawa martanin murmushinta,abinda ya sanya pink lips dinta
motsawa kadan.
"Ya salam" Ya fada can qasan ransa saboda tsigar
jikinsa da yaji ta zuba yarrrr.....tun daga tafin qafarsa har zuwa tsakiyar
kansa. Wanccan ranar ya tuna.......ranar daya sanya lips dinsa saman
nata......shi.kadai yasan me yaji,shi kadai yasan yadda ya iya qwace kansa daga
yanayin daya shiga......yayi imani a ranar inda ace shi din manemin mata
ne,baisan adadin mata nawa zai nema ba a ranar.....inda shi mashayi ne,baisan
adadin kwalba nawa zaisha ba......inda ace shi din asharari ne bayajin cikin
kwana uku ma wata macen zata sauke masa abinda yaji a jikinsa a wannan lokacin.
Bayajin zai iya ci gaba da tsaiwa a wajen bare ta fahimta ko farouq ya gano
canzawarsa,don haka sai ya juya kawai yana takawa a nutse yana matsawa daga
wajen gami da sake kame kansa da kyau gudun zubewar kima.
Dukkaninsu motar da tazo tararsu ta dauke,mota ce me seat kusan hudu
bayan wajen hutawa daga can baya. Shi da farouq suna seat guda,sabreen anni da
amna suna set na qarshe.
"A ina ka samar mana gida?" Fuad dake gyara agogon
hannunsa ya tambayi farouq. Takardun hannunsa ya fara budewa daya bayan daya
kafin yace yana tsaida idanunsa akan wata takarda guda daya.
"RANGALI ISLAND RESORT......garden villa na masa mana
gida.....baiyi tsada cancan ba,duk da Maldivian Rufiyaa mukayi cinikin,ahmad ne
ya siya gidan ta hannun wani,da nayi converting kudin da naira sai naga basuyi
yawa ba" . Kai kawai ya jinjina,farouq akwai iya aiki,musamman idan akazo
batu na tafiya tourism.
"Ina fatan yalwatacce ne,kasan mun sake qaruwa this
time?". Idanu ya zuba masa,kaman yace masa waye ya qarun da sukayi yawan
da zaa nema bangajejen gida?,amma sai yaga kulashi ma bata time da plan ne,don
haka ya bishi da
" Yes" Kawai farouq yace masa yana boye dariyan
dake qasan ransa.
Idanunta
akan hanya sanda suke wuce lafiyayyun hanyoyin da suka sha banbam dana qasarmu
nigeria. Ko daga iya nan ta tsaya ta tabbatar wata duniya ta daban ta shigo. Ta
shigo wata duniya da tayi nisa qwarai da tata DUNIYAr data rayu cikinta. Qarfi
da yaji takeson komawa 'yar qauye,ta sauke nannauyan ajiyar zuciya sanda
motarsu ke shiga wani street me dauke da lafiyayyar hanya da wadatar tsirrai.
daga gefe da gefan hanyoyin tana iya hangen ruwa can nesa dasu,wani irin ruwa
dake bada blue colour,bata sani ba.....color dinshine haka ko kuma 'yar tazarar
dake tsakaninsu take nuna mata haka.
Daidai
qofan wani madaidaicin kyakkyawan gida motar ta fara slow kafin ta samu wajen
tsaiwa. Su suka fara fita suka jira fitowar anni,sannan ita da amna suka biyo
bayanta.
Tare
suka jera da farouq har qofan gidan su kuma suna biye dasu,jordan da drivern
motar suna biye dasu da luggage dinsu.
Dab da zasu
isa qofan gidan qofar ta bude da kanta. Farin matashi ne ya bayyana wanda duka
duka shekarunsa ba zasu haura talatin da takwas ba,daga gefansa musaddiq ne da
suka jero tare,wanda kamanninsa da fuad ta wasu bangarori da yawa suke bayyana
kansu. Yana sanye da jeans da shirt yayin da musaddiq jikinsa ke sanye da
jallabiyya saqar marocco,kansa kuma akwai qaramar hular da mukafi mata laqabi
da tashi ka fiya naci haka ma mutumin dake gefan musaddiq din. Akwai haske
sosai saman fuskar tashi dake bayyana musulunci tattare dashi.
Da
sassarfa musaddiq din yake qarasowa garesu,idanunshi duka suna kan anni,yana
isowa gaban nata baiyi duba da wani girmansa ba,ya bude dukka hannayensa ya
rungume annin yana fadin
"I missed you so much anni......sai naji kaman ba
zakuzo ba.....kwana biyu kawai amma sai naji tayi nisa" Murmushin dake
shimfide kan fuskarta kadai ya isa ya gaya maka farincikin dake ranta na
ganinsa da tayi,zallar qauna irin wadda ba kasafai ake samunta wajen wani ba
idan ka dauke uwa.
"Kayi nisan kiwo yaro na......ka tayani roqon hammanku
kada ya sake daukemin kai har haka" Ranqwafowa yayi wajen fuskar
annin,yana yin qasa qasa da muryarsa don kada fu'ad yaji
"Na rantse anni nima bazan sake yarda ba.....ki jawa
danki kunne"
"Kai kai......hamman?,ai kuwa kaman a kunnensa"
Amna data zuro musu kai ta fada tana raba idanu. Duban amna yayi yana dan
yamutsa fuska
"Bama haka dake auta......kinsan ni dake duk muna
together" Ya furta yana daga mata yatsunsa biyu cikin salon son samun
goyon bayanta. Fuska ta shagwabe tana cewa
"Zan iya haqura nayi shuru idan tsarabata tafi ta kowa
yawa" Tayi maganar tana kashe ido daya sannan ta dora
"Idan kuma ba haka ba.....ga addana a gefe,ita zan
gayawa ta shaida masa abinda kace da mijinta" Ta qarasa maganar tana nuna
sabreen da yatsa.
Sai a sannan
ta lura da sabreen din dake gefansu. Ya dora idonshi a kanta yana dan kafeta da
kallo na wasu sakanni. Sosai yaji yasan fuskartata,ba yau ne ranar farko daya
fara ganin fuskar ba. Cikin qasa da second biyar ya tuna inda ya santa. Tabbas
bazai taba iya mantawa da fuskar ba.....fuskar data dinga fada saboda lafiyar
anninsu.......fuskar data zama silar ceto rayuwar anninsu,to amma kuma sai yaji
kaman bai kamata farat daya haka a matsayinsa na baquwar fuska a gareta yayi
gaggawar tuhumarta inda ya santa ba.....ballanta ma ita din da take matsayin
yaaya a wajensa.
"Tuba naki adda.....ayimin aikin gafara.....da gaske
hamma baida dadi shi yasa takeson hadoni dashi" Ya fada yana hade
hannayensa duka biyu waje daya.
Batasan ya
akayi murmushi ya qwace mata ba,murmushin daya afku saman idanun fu'ad dake dan
nesa kadan dasu yana karbar takardu hannun ahmad tare da sake karbar wasu
bayanai,don tuni farouq ya wuce cikin gidan yana sake duba yanayinsa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
69
Wani abu ya
hadiye da baisan meye shi ba,wato ita duk inda taga maza sakin jikinta
takeyi?,a ina tasan musaddiq da daga haduwar farko xata sake masa fuska da
murmushi har haka?. Idanu ya xuba mata yana kallon yadda take duban musaddiq
kai tsaye.
"Anyi maka.....amna ma na tabbatar tsokanarka take,don
kullum cikin kewarka take,nasha labarinka a wajenta sosai". Ta fada har
zuciyarta tana mamakin family din. Kowa na gidan kenan me kirki ne,shi kadai ne
maras kirki,maras fara'a,marason jama'a?. Ta tambayi kanta sanda idanunta ya
sauka a kanshi. Cikin sa'a idanunsu suka sarqafe guri guda,kusan tare kowa ya
dauke dubansa daga kan dan uwansa,sai ya miqa hannu yana karbar takardar hannun
ahmad. Da yaren dhivehi asalin harshen mutanen qasar ahmad din yake masa
godiyan da batasan ta mece ba. Ga mamakinta sai taji ya maida masa shima da
yaren sannan ya
ya soma takawa shima yana wucewa ciki da qasaitaccen takun
nan nasa. Tana jin muryar musaddiq yana fadin
"Godiya nakeyi" Tare da maida kansa ga anni.
"Zan kamaki,saikin gayamin dalilin da yasa kina kewata
amma baki taba fadimin ko sau daya ba".
"Diyata zo mu wuce ciki,wadannan idan kika biye musu
zaki wuni a tsaye ne kam" Anni ta furta tana saka hannunta ta kamo hannun
sabreen suka fara wucewa cikin gidan. Duk kunyar anni sai ta kamata,tayi qasa
da kanta tana biye da ita. Batasan wani abu a duniya da takejin nauyinsa haka
ba kaman annin,tana da wani kima a idanunta na musamman.
"Yanzu nake
shirin leqawa na kiraki ki shigo ciki......wancan shirmammiyar tunda ta hadu da
dan uwanta kuma ai shi kenan.....may be daga nan ma yawo zasu wuce iyayen
zumudi".
" Saddiq....." Fu'ad dake zaune hannun kujera yana
duba takardun daya karba yayi kiran Sadiq dake qoqarin daukan ruwa a fridge.
Samun kanta tayi da lumshe idonta,batasan me yasa muryarsa take mata nauyi da
yawa ba,ba ita ya kira ba,amma sautin kiran yakai mata har tsakiyar qirjinta.
Muryarsa tana da wani irin amo me ratsa mutum koda ba dakai yake magana ba.
"Na'am" Sadiq yabar abinda yakeyi ya waiwaya yana
dubansa,bai daga kai ya kalleshi ba yace
"Fita ka gayawa musaddiq kada suje ko ina"
"Okay" Ya fada yana ajiye ruwan gami da kama
hanyar fita. Numfashi kawai ta aje tana tabe baki,kowa a sake yake amma
bandashi,ya iya bada umarni,daga wannan sai wancan,kuma yana iya gama magana
dakai kaf ba tare da ya kalli fuskarka ba,ta rasa wanne irin mulki ne haka a
cikin jininsa?. Idan kuma muguntarsa ya motsa,ta lura kowa ma da idanu yake
hukuntashi,ko don yasan akwai wani abu me nauyi a cikin kallonsa oho?,saita
dauke kai gefe tana tabe baki,idanunta kuwa suka sauka kan wani glass door wanda
daga nan kana iya hangen wani ruwa nesa kadan dasu dake lullube da farin yashi
kaman ta miqa hannu ta kamo.
"Gidan ya miki anni?" Ya fada yana sauke takardar
daga fuskarsa bayan ya gama jan ajin nasa.
"Tubarkallah ma sha Allah" Anni ta fada cikin
walwalar data bayyana har saman fuskarta tana kallon kowanne sashe na gidan
"Allah ya qara rufa muku asiri duniya da
lahira.....Allah ya ninka albarka cikin rayuwarku"
"Allahumma ameen" Suka fada shi da farouq a kusan
tare.
"Anni ta shiga ta huta.....akwai awa kusan daya da rabi
kafin sallar magarib.....inajin yau ba wanda zai fita sai gobe idan Allah ya
kaimu" Ya fada yana duba agogon hannunsa sannan ya sauke.
Cikin aljihun
trouser dinsa farouq ya sanya hannu ya ciro key,ya kuma nufi wani daki cikin
dakunan dake parlor din,ya bude dakin ya tura qofan yana duban amna
"Ja luggage dinki dana anni kikai muku ciki" Yace
da ita daidai sanda take shigowa, Amsa masa tayi to tana yin yadda yace din,ya
waiwaya yana kallon musaddiq da musaddiq
"Bude dakin can musaddiq ku sakawa addanmu nata
kayan" Ya fadi yana miqawa musaddiq din key din,sannan ya kalli Sadiq
"Saka mana namu a dakin musaddiq sai muyi
squatting......addanmu ki shiga ki huta" Ya fada cikin murmushi da
girmamawa fal muryarshi,qasan ransa kuma wasai da yadda plan dinsa ya tafi
daidai.
Harde
hannayensa yayi kawai a qirji yana qarewa farouq kallo,wato abinda ya tsara ma
ran shi zaiyi kenan?,shi yasa koda ya buqaci picture ko video na gidan ya hana
mishi gani.
Yasan
sarai shi fu'ad din yake kalla,ya kuma shiryama koma meye zaice ko zaiyi,don
haka ya basar yaqi kallonsa kaman baisan ma yana a wajen ba. Fridge kawai ya
bude yana duba meye da meye a ciki yana kuma masa lissafin me dame ya kamata su
ajiye na kwanakinsu a qasar. Wani haushi ya cikashi,ya cika yayi fam da rainin
hankalin da farouq din ya shirya masa. To amma a yadda yaga farouq din ya
tabbatar ya shiryawa duk wani rigimarsa ne,so dole ya fara bin komai a
hankali,tunda basu kadai bane,akwai anni,bazaiso kuma anni taji ko taga komai
ba.
"Wanne irin gida ne wannan farouq?" Ya fada calmly
yana qoqarin danne takaicinsa. Sai daya ajiye gorar hannunsa sannan ya waiwayo
yana dubansa
"Me fa?" Yayi tambayar kansa tsaye. Sai daya
lumshe idonsa ya bude lokaci guda yana jin takaicin rainin wayon farouq da idan
ya motsa tsaf xai iya cewa ma bai sanka ba.
"3bedroom?,why not a siya me 4bedrooms farouq?"
"Akwai baquwar halitta ne a cikinmu da bata samu waje
ba?". Kai fu'ad ya girgiza yanason gajarce maganar,don ciki yakeso ya
shiga yayi bacci ko na awa daya ne
"Babu.....amma dakunan sunyi kadan.....kafi kowa sanin
bana iya hada daki da kowa ba ko tun ba yau ba?"
"To dawa na hadaka.....kajimin mutum zaimin
sharri" Rainin hankalin farouq yakai masa ko ina,yana dab da bashi naushi
idan baiyi wasa ba,sai ya ware hannunsa daga qirji yana dubansa
"Ka canza plan dinnan,ta koma dakinsu anni tayi
squatting tare dasu,saddiq su kwana da musaddiq.....kai kuma muje mu kwana
tare". Baya yaja da sauri yana zare ido kaman yaga abun tsoro.
"Mu kwana da kai?,alfanun uban me zanyi maka fu'ad?,me
zakaji da kwana da namiji gardi dan uwanka bayan ga halalinka a
gefe?" Maganar ta fara girmar
kunnuwan fu'ad,tun ba yau ba yasan farouq idan baiso ba tantirin kansa
ne,baisan sanda hannunsa yakai kan cup din da saddiq yasha ruwa ba ya jefeshi
dashi,Allah yasa yana da zafin nama ya cafe
"Na rantse da Allah xan ruguza maka kai......kai wanne
irin dan iska ne?,maganan da nake maka daban yadda zaka juyan zance daban?,ta
yaya zan kwana da wata alhalin muna muhalli daya da anni?". Dariya tana
cin farouq amma ya maze
"To ba dole nace haka ba?,ga mace me namiji zai
maka?,nima bazan kwana da gardi ba,ka cire riga wannan qattin muscles din naka
suyita bawa mutum tsoro.....in fact ma ni na fara rehearsal na yadda zan fara
kwanciya daga ni sai fannah ta....anni kuma da kake magana akwai wanda zai
kaita son ganinku tare....ko turmusheta kayi a gabanta ai saidai tabar muku
gurin da gudu.....banson gulma banson k......" Bai qarasa ba yaji saukar
abu a qeyarsa,agogon hannunsa ya kwance ya sake jifansa dashi don ya rasa dame
zai jefeshi wannan karon.
Dafe
wajen yayi ya waiwayo yana dubansa fuska a hade
"Amma dai kasan wannan zallar cin zali ne ko?,ni nakar
xomon?,kaje ka yiwa anni bayanin abinda yasa zaka aikota kwana da ita daki daya
mana da kanka".
"Ya isheka farouq" Ya fada yana nunashi da
yatsa,alamun ya fara qureshi.
"Oho" Ya fada yana sungumar ruwansa yayi dakinsu
baiko sake waiwayoshi ba.
Shuru ne ya
ratsa falon bayan wucewar farouq din,sai motsinsu kadan kadan da yake jiyowa
daga dakunansu. Maganar gaskiya farouq ya cuceshi,inda kuma yasan da wannan da
tuni ya sanya an canza musu gida da yafi haka yawan dakuna kafin su qaraso.
Miqewa yayi abisa dole yana soma dosar dakin,abu daya ya sani shi bayason
takura,yana son bajewa sosai ya sake a duk inda ya zabi rayuwa,so wanzuwarta
cikin dakin kuwa bazai bari ya zama silar hanashi sakewa ba.
*Maamah*
Sake juya
tickets din hannunta tayi guda biyu tana sake qare masa kallo. Mamaki da wani
irin dunqulallen baqinciki yana yayyanka zuciyarta. Ta rasa wanne hamshaqinne
ya juya tafiyar daga farkonta ta koma qarshe?. Maldevis shine waje na farko da
zasu je a qa'ida kaman yadda ta samu tabbacin dukka iyalin gidan alhj hamza
kibiya can suka wuce.....saudiyya kuma shine waje na qarshe da zasu ziyarta
daga nan kuma sai gida Nigeria,amma wanne hamshaqinne ya karkatar da tata
akalar tafiya daga saudiyya kafin ta sauka maldevis sannan su rankaya su wuce
turkey tare?.
"Hajiya ameena.....tabbas wannan aikin ameena ne"
Ta fadi tana jin wutar qiyayyar matar tana sake ninkuwa a ranta. Zazzafar iska
ta furzar tana fitar da idanunta waje irin na zallar takaici da kuma tunani.
Ita kuwa ta yaya zata dagawa ameena qafa?,ta yaya zata bar ameena taci gaba da
shaqar iska cikin aminci?,ba ragi tsakaninta da ameena har abada......yadda
bata barta ta samu cikakken iko da mulki da 'ya'yanta ba.....tabbas haka zata
zama silar tarwatsa nata ahalin gaba daya,duk wanda ya gaya mata cuta ba shakka
ita mutuwa zata gwada masa,sai kawai taja wayarta tana laluben fareeda,tana jin
wannan karon a gaban idanun ameenatun zata gwada mata nata izzar da qarfin
mulkin kasancewar uwar data dauki cikin fu'ad tayi naqudarsa ta kuma
haifeshi.......a gaban idanun kowa zata gwadawa sabreen ta isa da
danta......zata nuna mata kuma tana da ikon sanya yaronta ya auri mata d'ai
d'ai har guda uku rigis bayan ita.
Shuru
fareeda tayi tana sauraren bayanan maamah,saidai kuma zuciyarta cike fal da
bacin rai da baqin kishin sabreen. Wata zazzafar iska ta furzar tana ajiye
bututun shisha dinta ta gyara zamanta
"Maldives ai gida ne......ina da sauran visa din qasar
da ban gama cinyeta ba,muddin na samu ticket jibi warhaka ina can......ko ba
ticket zan sanya daddy yamin hiring private jet......kya sameni a can"
Daga haka ta yanke wayar tana latsa wayarta ba bata lokaci tana neman number
wayar daddy din nata.
Tafasa
kawai zuciyarta takeyi,wannan karon da zafi zafinta zata shiga,zata budewa
sabreen aiki sosai kaman yadda zata budewa fu'ad,tana jin komai mai sauqi
ne......amma zata bari ta tabbatar da samun private jet ko ticket to Maldives.
Bugu daya
rak ya daga,ba kasafai ta fiya masa sallama ba,kusan sallamarta kiran sunansa
ne
"Daddyyyy.....maldevis" Ta fada da wata irin
shagwaba kamar yarinyar da aka Haifa jiya jiya
"Mamana......maldevis a daren nan?"
"Daddy gobe......ina da sauran visa na da kamin last
two months.......ticket kawai daddy nakeso......please daddy,it's an urgent
need daddy". Murmushi ya saki yana juya kai kafin yace
"Wani irin emergency issue ne haka ya taso
mamana.....nifa mamana yanzun duk hankalina yana kan aure,kiyi aure haka
mamana.....ki zabi duk kalar mijin da kk so zan tsaya miki" Maganar sai taji kaman tazo akan gaba,ta saki
dariya tana cewa
"Nayi maka alqawari daddy.....indai na samu wucewa
Maldives gobe ko jibi,ina dawowa zan gabatar maka da mijin da zan aura"
"Really mama na?!" Ya tambaya da excitement cikin
muryarsa
"Yes dad.....na taba maka qarya ne?" Ta sake fada
cikin narke murya
"No mamana......bani minti goma.....i will get back to
you"
"Thank youuuuuuu" Ta fada da sautin dariya tana
sauke wayar.
Lips nata
ta cinje tana duban wayar gami da saqa abubuwa iri daban daban akan fu'ad. Zuwa
sannan ta gama karance halayensa na girman kai da izza,yana da tsananin taurin
kan data tabbatar ita din kanta shaida ce,taso koda bata aureshi ba ya bata
hadin kai su mori quruciyarsu tare,amma martanin da yayi mata ya mata ciwon
data jima tana riritashi a zuciyarta.
"Tabbas saina biyo masa ta bayan gida,idan baiyi wasa
ba sunansa ne zai fito a next newspapers da magazine ba na waccan karuwar matar
tasa ba......tunda shine garkuwarta.......shi din ya kamata na taba
qarfinsa" Ta fada da murmushin mugunta tana murza yatsunta bayan ta
tabbatar da hukuncin daya fado ranta shine abinda ya kamata ta zartar.
Qarar
wayarta ya dawo da hankalinta,ta daga da sauri ganin me kiran. Wani ihun murna
ta saki sosai tana jin dadi
"I love you daddy......thank you so so much......bansan
ma ya zan gode maka ba" Ta fada duk a rude saboda jin dadin samun ticket
na tafiya Maldives jibi. Tana Lagos don haka ba ita babu bin jirgi zuwa Lagos
din,kawai kanta tsaye jibi zata bi qatar Airways zuwa can
"Ki kawomin miji kawai bayan kin dawo"
"Baka da matsala dad....." Ta fada tana yanke
kiran.
Tun a daren
ta gama komai,ta gama hada komai ta kuma tanadi komai gudun samun matsala goben
kada ta tashi da uzurin da zata tashi ba'a daidai ba har ya jawo ta hada
kayanta ba daidai ba.
*_hmmmmmm,uhmmmmmmmmm_*
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 70
70
Sam sam bata
fahimci daki daya farouq ya hadesu ba sai da ya murda handle din ya shigo cikin
sallama. Daidai lokacin da taketa qoqarin kauda luggage din zuwa kyakkyawan
gurin ajiyar kaya dake a dakin bayan ta ware scarfs din kanta ta daure sumarta
dashi.
Kallon
juna sukayi,sai kowa yayi qoqarin dauke idonsa daga kan dan uwansa. Haka kawai
ta samu gabanta da faduwa,tunaninta kuma ya koma baya na yadda aka kasafta
dakunan
"Tashin hankali!.....shine part na na?" Ta fadawa
kanta da kanta. Sam sam bata taba hango yiwuwar wanzuwarsu a daki daya
ba......ita da mutumin da basa ga maciji sam sam,ta yaya zata iya hada numfashi
dashi qarqashin rufin daki guda daya?,lallai inda tasan da yiwuwar faruwar
hakan wannan kadai a wajenta ya isa dalilin da zai hanata yin tafiyar ma gaba
daya.
Sakin
abinda takeyi tayi ta kuma ware veil dinta ta lullube kanta dashi dukka tana
satar kallonsa. Baiko nuna yasan da tsaiwarta a wajen ba,hasalima yanata
daddaga labulayen dakin yana laluba sauran gurare irinsu socket na dakin,switch
da sauran gurare saboda tsaro,gudun samun wata boyayyar camera da basusan da
ita ba.
Baisan ta
fice ba sai da yaji alamun jan qofar,ya bi qofar da kallo kafin daga bisani ya
dauke dubansa daga wajen yana ci gaba da abinda yakeyi.
Wannan
dukka ba take taken raini bane ba?,amma ba wanda ya jawo masa illa farouq,kuma
tabbas zaija kunnensa,bazai yiwu cikin qasashe biyu da xasu sake zuwa a gaba ya
qara hada musu guri ba,duk da kusan duka qasashen ba inda baida gida mallakin
kansa uku ko hudu,da kansa zai zabi gidan da yakeso saboda gudun faruwar hakan.
Sai daya
tabbatar da lafiyar dakin sannan ya soma rage kayan jikinsa,don bazai iya bacci
haka ba,ko wankan ma bayajin zaiyishi sai idan ya tashi,duk da farouq nason
rage masa jin dadinsa.....don da gaske hutu yazoyi,yazo.ya huta inda ba zaa
sashi magana bs ko ciwon kai.
Turus tayi
sanda ta fito parlor din,wayam ba kowa sai dan motsinsu daga dakunansu. Bin
duka qofofin dakunan dake kulle tayi da kallo,saita rasa meye abunyi.
Da kunya
dai ta jewa dakinsu anni wanda ta tabbatar a yanzun suma hutawa sukeyi,idan ma
taje tace mata me?. Ba zata zauna daki daya da d'anta ba wanda mijinta ne a
qa'ida duk duniya kuma haka suke kallonsu?,wanda sukasan sahihin zamansu
mutanene daidaiku.......hatta da amna bata sanya ran ta gama fahimtar komai da
komai. Rasa madafa tayi,dole a qarshe kwanyarta ta gaya mata bata da sauran
wani abunyi illa ta koma dakin ta rungumi haquri na yau,zuwa gobe saita nemawa
kanta dalili da mafitar da zata sanya a raba dakin.
Daidai
sanda ya isa bakin qofa da zummar kashe switch na qwan ita kuma ta murza qofar
ta shigo. Baikai ga kashewa ba,don haka tsaf ta ganshi.
Murdadde
kuma qaqqarfan muhammad fu'ad jadda,ma'abocin daga qarfe da dukka surar jikinsa
ta koma ta qarfafan maza,saidai surar batayi muni ba,ta dace da zatinsa ta kuma
shekarunsa.
Babu
komai a jikinsa sai gajeran wando iyakar cinyoyinsa,gaba daya faffadan qirjinsa
dake lullube da ni'imtaccen tattausan gashi ya tare kusan rabin qofar
dashi,abinda ya sanyata saura kadan ta fada qirjin nasa,abinda kuma ya saka
tsoro ya kusan sanyata shidewa,ta daburce duka cikin qanqanin lokaci,saita juya
da hanzari da zummar ficewa a dakin don ba zata juri ganinsa haka ba.
Sosai ya
raina sanya hannu qwaya daya ya jawota zuwa gabansa,yanzun hakan ma yayi
mata,ya kuma ajeta a gefe,ya saka hannu ya murza key din qofar ya rufe dakin,ya
cilla key din saman gado sannan ya juya yana kashe switch din. Dakin yayi
duhu,saidai duhun bazai hanaka ganin komai dake dakin ba amma bada fitacciyar
suffarsa ba. Takawa yakeyi hankalinsa kwance zuwa gadon kaman ba'a tube yake ba
"Sannu a hankali wataran zan baki mamaki tunda na
hanaki wannan rainin hankalin da kikemin kaman dodo......sai kace a kaina kika
taba ganin namiji a t......" Sai kuma bai qarasa ba yaja tsaki sanda yake
dora kansa saman pillow hadi da lumshe idanunsa ya sauke numfashi.
Komai ta
kasa cewa saboda tsoro daya cakude da takaici. Ta zuba ma fuskarsa idanu duk da
bata iya ganinta sosai tana jin bacin rai yana taso mata. Ta tsani koda kalma
daya ta hadasu shi yasa take kauce masa,don kowacce magana zai gaya mata bame
dadi bace a zuciyarta da kunnuwanta.
Don kanta
ta samu waje ta nade tana curewa guri daya bayan ta gaji da tsaiwa,don tuni
yaja duvet ya rufe jikinsa dukka gaba daya har saman kansa.
Tsakiyar
baccinsa ya dinga ganinta tana nufoshi cikin swimsuit sanda yake zaune daga
gaban swimming pool din yana kallonta. Kanta tsaye ta yiwa kanta mazauni saman
cinyarsa,yayin da albarkatun qirjinta yake tokare masa fuska da wani irin salo
na tsokana,baisan ya akayi ba ya samu kansa da goga fuskarsa a jikinsu,abinda
ya tashi kowacce tsiga ta jikinsa kenan,kowacce kafar jikinsa ta soma fidda
zufa,ya kuma jawota ya qanqameta da kyau yana cusa fuskarsa tsakiyarsu kaman me
neman taimako.
Wani
birkitaccen salo takeyi masa,wanda ya taimaka wajen fitarsa a hayyacinsa,ya
kuma juyeta saman sun lounger din da yake kai,take al'amura suka fara kankama
tsakaninsa da ita.
Karar
fadawar wani abu ruwan dake gabansu shi ya farkar dashi har a zahiri. Idanunsa
ya runtse da qarfi yana jin wani abu yana yawo a sassan jikinsa. Yana jin
tamkar a yanzun idanu biyu komai yake faruwa,wani irin zazzafan yanayi da ya
jima bai tsinci kanshi a ciki ba saboda yadda yake yawaita yin takatsantsan.
"Why?,why?" Ya tambayi kansa da kansa muryarsa can
cikin maqogoronsa. Me yasa zata biyo shi har baccinsa?,ba zata qyaleshi ya huta
ba kenan?. Ko a baya da yake fuskantar irin mafarke mafarken nan......babu guda
daya daya taba ganin ainihin fuskar ko gangar jiki,wannan shine na farko da
komanta ya bayyanar masa a zahiri.
Fitowarta
daga toilet shi ya sanya ya ware rinannun idanunsa a kanta. Duk da bata iya
ganinsa sosai amma taga alamun ya farka daga baccin. Dama ya kamata ace ya
farka din,tunda agogo ya nuna mata lokacin magariba yayi,amma kuma batasan
yadda zata tayar dashi ba,to ya samawa kansa lafiya daya farka din. Dakin ya
mata duhu saboda yadda duhu ya soma mamaye garin,saita laluba har ta dace da
makunnin ta kunna qwan dakin,take haske ya gauraye ko ina tarwai. Idanunsa ya
lumshe yana cusa shi cikin pillow
"Oh shit" Ya fada qasa qasa. Qoqarin tashi yake
kafin hakan takai ga faruwa sai gashi ta rigashi kunna hasken dakin. Ta yaya
zai iya tashi ya miqe ya wuce zuwa bandaki a yanayin da yake ciki?,tambayar
dashi kansa baisan amsarta ba.
A nata
bangaren ta gama gajiya da zaman dakin,burinta kawai ya budeta ta fita,bataga
wani alfanun zamansu suna musayar numfashi ba idan ba tsabar muguntar nashi
bane ya motsa. Ta duba luggage dinta ma sam bata ga hijab ba,sai mayafai ta
hada kusan uku dasu zatayi sallar. Ba ita ta hada kayan ba,zata iya cewa
batasan ma meye a ciki ba,anni ce ta musu siyayyar duk da uban lodin kayan da
suke da wanda ita kanta batasan adadi ba,amna kuma ta shirya mata tace basai ta
buda ba ta saka mata komai,ta kuma biye matan bata duba ba.
Bashi da
wani sauran abinda ya rage illa dole ya tashi din,don haka ya tattara uban
duvet din ya nadeshi a jikinsa ya sauka yana wucewa toilet din a gurguje. Ta
danyi mamakin shigarsa toilet fa duvet,amma sai kuma sai ta kauda abun daga
ranta ta shimfida abun sallah tana jiran lokaci ya qarasa cika.
Ya jima
a toilet din yana qoqarin ganin yanayinsa ya daidaita,yasha azaba qwarai har ya
dinga tunanin anya yau zai tsallake kuwa?. Kowanne jijiya ta jikinsa aikawa
take da saqo,sai bayan kusan minti talatin ya samu yanayinsa ya dawo
daidai,amma abinda yakeji a jikinsa bai sauya ba tunda jikin bai samu abinda
yakeso ba. Dukka jikinsa ya wani mutu qwarai da wata irin kasala data sakar
masa da nauyin jiki,haka yayi wanka ya daura alwala ya fito. Sauqinta daya data
samu tana sallah sanda ya fito din,don da alama a yanzun ma gaba gadi ya fito
abinsa,ya buda kayansa ya shirya cikin Moroccan jallabiyya black me adon golden
din zare,ya saka qaramae gold din hula ya feshe jikinsa da turare sannan ya
dauki key ya bude qofan ya fice don zuwa su hada jam'i dasu saddiq kaman yadda
suka saba duk sanda sukayi tafiya a qasashen daba masallaci a kusa da
masaukinsu.
Fitarsa
sai taji kaman ta samu 'yanci ne,ta kammala sallarta ta fada wanka. Koda ta
fito lokacin isha'i yayi,tasan qwarai tana da nauyin wanka,amma na yau ya haura
na kullum saboda ba qaramar wahala tasha wajen gane yadda zatayi amfani da
kayan bandakin ba.
Da
karsashinta ta isa ga luggage dinta,saidai kaf ta cajeshi babu wata suturar
arziqi da zata iya sakata ta fita,sai uban lingerie data zuba mata kaman
karuwar dake neman customer.
Takaici ya
sanyata komawa ta zauna ta rafka tagumi,kusan mintina ashirin ta kashe a haka
kafin ta jawo akwatin ta sake birkiceshi ko zata dace. Baqinciki ya sanyata
daga lingerie din daya bayan daya tana qare musu kallo. Kaya ne na rashin
kunyar da ita kanta kunyar wasu a ciki takeji idan ta daga
"Amna kin kwafsamin.....kin kasheni......shi yasa
kikace kada na duba kayan" Ta fada a fili daidai sanda ta daga wata
lingerie din da aka yiwa wani yanka na wulaqanci,aka fidda gidan mama daga qasa
kuma aka mata wata huda.
Shigowarsa da sallamarsa duka lokacin guda ne,ta saki rigar da sauri ya
bita da kallo,ta miqa hannu da gaggawa ta tattareta ita da sauran tana zubawa a
akwatin sannan ta miqe.
Tanason
masa maganan ya turo mata amna amma batason halinsan nan,ya kammala abinda
yakeyi ya doshi hanyar fita
"Idan kin gama abinda kikeyi din ki fito za'ayi
dinner"
"Don Allah ka turomin amna" Ta katsi numfashi tana
fadi da sauri har sai daya waiwayo ya kalleta,karon farko da magana ta nutsuwa
da respect harma da begging a ciki ya taba hadasu,sai baice komai ba ya fice
abinsa.
Harara ta
ballawa qofan tana jin baiken kanta,me yasa ma ta roqeshi?,gashinan ya yarfata
a banza,dama me hali ai baya fasa halinsa,ta tsugunna tana hade kayan cikin
takaici. Saidai ko gamawa batayi ba amna tayi sallama,ta tsaya daga qofa tana
leqowa a darare.
"Ki shigo malama" Ta furta tana jifanta da harara.
"Shigowa makwancin hamma din kai tsaye haka hadari
ne" Ta fada tana shigowa kaman yadda ta buqata. Tana mamakin irin tsoronsa
da sukeyi da yadda suke kiyayarsa qwarai.
"Yau fada zamuyi dake har anni saita shigo
sasanci"
"Me nayi adda?" Ta tambaya tana waro idanunta gami
da dafe qirjinta
"Kayan da kika zubamin dama kenan amna?" Ta
tambayeta tana dan kama kunnenta. Dafe kunnen tayi dariya tana kamata,duk da
riqon babu zafi amma tace
"Wayyo kunnen autar anni......aradu anni ce tace duka
na zuba miki su,ni kuma da naji tace haka saina kwashe wadancan......bansan mix
ya kamata ayi ba" . Kunya ta saukarwa sabreen,sai kawai ta saki kunnen
amna din
"Saikije ki daukomin hijab dinki,kayan fice ficen ma
duk na fasa sakasu tunda baki sakamin kayan zaman gida na arziqi ba,da hijab
zanta zama"
"Kaina bisa wuya na" Ta furta tana dariya gami da
ficewa. Gudun jira sai kawai ta shirya kanta cikin riga da wandon,rigar ta
sauko mata har saman mazaunanta,wandon kuma cif jikinta,don ya fidda sigar
santala santalan cinyoyinta da faffadan qugunta.
Murda
qofan ya sanyata juyowa da sauri tana zaton amna ce ta dawo,saidai a maimakon
amna din sai taga hammanta. Fuad ne tsaye fuskarsa babu walwala,kai tsaye ya
soma kallonta tun daga qasan qafafunta,idanunsa kuma suka cake akan
qirjinta,abinda ya sanya yaji wani yarrr tsigar jikinsa ta zuba. Fes abinda
yaji da dumi da qamshin da wajen kiyi ya dawo masa fes a qwalqwalrsa,sosai jini
ya harba ko ina a jikinsa,yayi gaggawar damqe numfashinsa gami da hana faruwar
abinda yake shirin faruwar dashi.
Kallon
qurillar da a yau yayi mata karon farko a tarayyarsu ya ratsa kowanne jini dake
gudu a sassan jikinta. Idan tace zata juya masa baya nan ma tasan bata tsira
ba,komai na jikinta ita kañta tayi imanin a bayyane yake.
"Karki fara gangancin fitowa a haka......ki nema kinomo
ko hijab ki saka a jikinki". Sai ya saki qofar yana juyawa yana jin
numfashinsa kaman zai tsaya da aiki.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 71
71
Tun kafin
ya qaraso idanun farouq yana kanshi,fata ne fal zuciyarsa na daidaituwar
al'amura,yasan sarai halin fu'ad......yana da kafiya da taurin kai akan
abubuwan da bai fuskancesu ba,amma da zarar ya fuskanta din yafi kowa bawa abun
muhimmanci.
Ba jiya ko
yau suke tare da fu'ad ba,tsohuwar alaqa ce da aka kafata tun basu mallaki
hankalin kawunansu ba,mutuwar jiki a wajen fu'ad na fassara abu guda ne tattare
dashi,rashin lafiya ta jiki irin ta kowa,da kuma motsawar feeling irin na
kowanne lafiyayyen namiji.
"Baka da lafiya ne dude?" Farouq ya fada qasa qasa
sanda fu'ad ke zama a dining din kusa da farouq din. Qoqarin murjewa yayi yana
cewa
"Am fine......bacci nayi bai kuma isheni yadda ya
kamata ba"
"I see..." Kawai ya furta da salon dashi kansa
yasan farouq din bai aminta ba.
Tare suka
jero da amna din suna fitowa,sai ya zare idonsa daga kan wayarsa yana duban
sashenta. Baiyi tsammanin zata saka hijab din kamar yadda ya umarta ba,saboda
yasam taurin kanta da kafiyarta,sai yaji wani sanyi na ratsashi ganin karon
farko tayi abinda yace da ita.
Gaida anni ta
sakeyi tana rusunawa,sannan suma suka gaidata harda farouq da yake da sauqin
kai.
Amna ce ta
soma servings nasu daga girkin cook din da sukayo hiring anan qasar wato
hidaya. Musulma ce data qware wajen sarrafa abinciccikan qasashe da dama. Yawa
yawan wadanda takewa aiki masu hannu da shuni ne don ta qware matuqa wajen iya
sarrafa tukunya. Da kudi sosai ake daukanta tayi maka iya adadin watanni ko
kwanakin da kakeso,amma a wajen mutane irinsu fu'ad din wannan din ba wani aiki
bane babba.
"Sabreen" Anni ta fada tana dubanta
"Na'am anni"
"Tashi ki serving mijinki" Wani nauyi taji ta aza
mata,amma hakanan ta miqe ta dauki plate ta soma xuba mishin. Tana xubawa tana
kallonsa wai ko zaice ya isa haka,amma abun takaici dukka hankalinsa yana kan
wayarsa
"Qila ma chart yakeyi da fareeda" Wata zuciyar ta
raya mata. Wato fareedan ce mutum.....ita tana tsaye saboda shi amma.baida
lokacinta?.
Duka anni na
ankare da komai,abinda ya sake tabbatar mata da tunaninta
"It's family time muhammadu....a aje wayar nan haka
ko?". Kansa ya daga ya dubi anni yana gyada kai yana sakin qaramin
murmushi. Karon farko data gayawa kanta da gaske yana da kyau kaman yadda
takeji daga bakin mutane. Bata taba ganin wani abu me kama da murmushi akan
fuskarsa ba sai a yau,zancan amna ya sake tabbata na ba wanda yake samun fu'ad
din a asalin fu'ad dinsa sai anni.
"Is okay" Yace sanda yake maida hankalinsa kan
abincin data zuba masan.
Abinci
sukeci cikin qauna da fahimtar juna,saidai ita din ta koma tamkar bare a
cikinsu,hasalima ta kasa sakewa sam,sai juya spoon takeyi.
Sai kunnuwa
data sanya sanda suke lissafin ina da ina zaa fara fita a goben. Amna keta
lissafin abinda zasu kashe
"Adda nawa zaa saka miki a account" Amna ta
tambayi sabreen,murmushi kadan tayi ta girgiza kai
"Ko sisi amna.....me zan siya?"
"Tsaraba mana adda.... Akwai traditional market nasu
fa,zakiga abubuwa da yawa da zasu burgeki.....kinji anni wai batason
komai......adda komai sai tace bataso?".
"Musaddiq ka saka mata wani abu itama... Mijinta ya qara mata,idan kuma bata da dolla
account saina ara mata nawa guda daya". Anni ta fada tana
murmushi,kunyarta tana dada burgeta sosai. Tsam ya miqe abinsa yana dauke
wayoyinsa.
"Zan kwanta anni"
"Mu tashi lafiya,muma kusan kwanciya kowa zaiyi ai dare
ya fara" A nan ya barsu ya gangara
ya wuce dakinsa,don bayajin sakewa har yanzu a jikinsa.
71
Tun kafin
ya qaraso idanun farouq yana kanshi,fata ne fal zuciyarsa na daidaituwar
al'amura,yasan sarai halin fu'ad......yana da kafiya da taurin kai akan
abubuwan da bai fuskancesu ba,amma da zarar ya fuskanta din yafi kowa bawa abun
muhimmanci.
Ba jiya ko
yau suke tare da fu'ad ba,tsohuwar alaqa ce da aka kafata tun basu mallaki
hankalin kawunansu ba,mutuwar jiki a wajen fu'ad na fassara abu guda ne tattare
dashi,rashin lafiya ta jiki irin ta kowa,da kuma motsawar feeling irin na
kowanne lafiyayyen namiji.
"Baka da lafiya ne dude?" Farouq ya fada qasa qasa
sanda fu'ad ke zama a dining din kusa da farouq din. Qoqarin murjewa yayi yana
cewa
"Am fine......bacci nayi bai kuma isheni yadda ya
kamata ba"
"I see..." Kawai ya furta da salon dashi kansa
yasan farouq din bai aminta ba.
Tare suka
jero da amna din suna fitowa,sai ya zare idonsa daga kan wayarsa yana duban
sashenta. Baiyi tsammanin zata saka hijab din kamar yadda ya umarta ba,saboda
yasam taurin kanta da kafiyarta,sai yaji wani sanyi na ratsashi ganin karon
farko tayi abinda yace da ita.
Gaida anni ta
sakeyi tana rusunawa,sannan suma suka gaidata harda farouq da yake da sauqin
kai.
Amna ce ta
soma servings nasu daga girkin cook din da sukayo hiring anan qasar wato
hidaya. Musulma ce data qware wajen sarrafa abinciccikan qasashe da dama. Yawa
yawan wadanda takewa aiki masu hannu da shuni ne don ta qware matuqa wajen iya
sarrafa tukunya. Da kudi sosai ake daukanta tayi maka iya adadin watanni ko
kwanakin da kakeso,amma a wajen mutane irinsu fu'ad din wannan din ba wani aiki
bane babba.
"Sabreen" Anni ta fada tana dubanta
"Na'am anni"
"Tashi ki serving mijinki" Wani nauyi taji ta aza
mata,amma hakanan ta miqe ta dauki plate ta soma xuba mishin. Tana xubawa tana
kallonsa wai ko zaice ya isa haka,amma abun takaici dukka hankalinsa yana kan
wayarsa
"Qila ma chart yakeyi da fareeda" Wata zuciyar ta
raya mata. Wato fareedan ce mutum.....ita tana tsaye saboda shi amma.baida
lokacinta?.
Duka anni na
ankare da komai,abinda ya sake tabbatar mata da tunaninta
"It's family time muhammadu....a aje wayar nan haka
ko?". Kansa ya daga ya dubi anni yana gyada kai yana sakin qaramin
murmushi. Karon farko data gayawa kanta da gaske yana da kyau kaman yadda
takeji daga bakin mutane. Bata taba ganin wani abu me kama da murmushi akan
fuskarsa ba sai a yau,zancan amna ya sake tabbata na ba wanda yake samun fu'ad
din a asalin fu'ad dinsa sai anni.
"Is okay" Yace sanda yake maida hankalinsa kan
abincin data zuba masan.
Abinci
sukeci cikin qauna da fahimtar juna,saidai ita din ta koma tamkar bare a
cikinsu,hasalima ta kasa sakewa sam,sai juya spoon takeyi.
Sai kunnuwa
data sanya sanda suke lissafin ina da ina zaa fara fita a goben. Amna keta
lissafin abinda zasu kashe
"Adda nawa zaa saka miki a account" Amna ta
tambayi sabreen,murmushi kadan tayi ta girgiza kai
"Ko sisi amna.....me zan siya?"
"Tsaraba mana adda.... Akwai traditional market nasu
fa,zakiga abubuwa da yawa da zasu burgeki.....kinji anni wai batason
komai......adda komai sai tace bataso?".
"Musaddiq ka saka mata wani abu itama... Mijinta ya qara mata,idan kuma bata da dolla
account saina ara mata nawa guda daya". Anni ta fada tana
murmushi,kunyarta tana dada burgeta sosai. Tsam ya miqe abinsa yana dauke
wayoyinsa.
"Zan kwanta anni"
"Mu tashi lafiya,muma kusan kwanciya kowa zaiyi ai dare
ya fara" A nan ya barsu ya gangara
ya wuce dakinsa,don bayajin sakewa har yanzu a jikinsa.
Wani
mummunan horo kawai yakeji farouq yayi masa na hadashi kwana daki daya da ita.
Gaba dayansa sai yake jinsa kaman a birkice yake,tun yana qaryata wanzuwarta
daki daya dashi ne ya sanya yanayinsa komawa hakan,har yayi amanna cewa
hakanne. A dare daya tak ya kasa samin isashen bacci har zuwa wayewar
gari,wayewar garin da ya tashi da ninkin rashin kuzari da karsashi a tattare
dashi,fiye ma da yadda ya kwana jiya.
Kowanne
motsi farouq yana ankare dashi,dariya qasan ranshi kaman zata kasheshi.
"Duk dacin ranka.....duk miskilancinka halittar mace
tafi qarfinka ko kai waye......qaton tuzuru dakai sai taurin kai da kafiyan da
ba inda zasu kaika?,dama can sarari ka samu,nisan tazarar dake tsakaninku ya
sanya kake ganin kamar baka da wata buqata ko sha'awa irin ta d'a
namiji.....wallahi qarya kake fu'ad......a wannan fannin ni kaina na sallama
maka.....zan gani idan tusa zata hura huta......daga yau zuwa gobe kawai na
baka,if kaci gaba da taurin kai.....nasan matakin da zan dauka a kanka"
Farouq yayi dukka wannan gulmar cikin zuciyarsa yana duban fu'ad dake zaune
yana kurbar maca and ginseng tea. Kaman baiso yake daga cup din zuwa
bakinsa,shi kansa,ranshi a jagule,baiso irin wannan yanayin ya tasammasa a irin
wannan lokacin ba sam,saidai koma meye zaya faru bayajin zai yarda koda da wasa
ya hada jikinsa da ita. Jikin da akullum ya kalla sai yayita lissafin adadin
maza nawa ne suka rabeshi?,adadin maza nawa ne suka tabashi?,dame dame sukayi
da ita?. Yana da bala'in qyanqyami na fitar hankali,wannan qyanqyamin ya sanya
bayajin shikam ko mata biyu zai iya aura,gwara ya tattara mutuntakarsa a
muhalli daya. Uwa uba wani irin kishi ne dashi,ba kuma wai yanzu ba,tun tale
tale zai iya cewa da kishin ya tashi,dashi aka halicceshi. Baisan maruka nawa
yasha daga hannun maamah ba sanda take kawo maza gidan abokan kasuwancinta da
suke siyan shaddodin da ta soma business dinsu ba,baisan adadin yawan dukan da
yasha a kansu ba......saboda muddin zaka sanya qafarka a gidansu,to shi kuwa
zai kafe ya cake a qofa ya hanaka qarasawa ciki.
"Babanmu baya so......ya hana maza shigar masa gida,ka
koma ka aiko qanwarka ko yayarka" Wadannan sune lafuzzansa a yayin da
fuskarsa kan cika da wani irin fushi da zafin zuciya. Kusan baki suke
sakewa,kusan duka duka shekarunsa a sannan ba zasu wuce goma sha daya ba,amma
zuciyar manya gareshi,zuciyar data kubuta daga dukkanin tsoro saboda kare
martaba da haqqin mahaifinsa. Wani lokacin idan ta jawoshi ta daka ta
daka,abbansa dake daki kwance yana jiyya shi zaita kiransa,shi zai
lallasheshi,yakan ce
"Komai na duniya me wucewa ne me babban suna.....komai
kuma haquri ne yake zama silar cin nasararsa......ka daina bari ana tabamin
lafiyarka me tsadar nan kaji?" Sau tari duk kalan dukan da zata masan ba
kasafai ya fiya kuka ba,duk da cewa duka ne ba kadan ba,wani lokaci harda
abinda bai kamata ayi dukan ba. Idanunsa saidai suyi jajir,yayita hadiyar yawu
da wani irin tsauri
"Abba......gidanka ne fa,ta yaya kana kwance zasu dinga
tsallakowa suna shigo maka?" Murmushi yakan yi,duk da yakan tsinci ciwo
cikin murmushin nasa
"Watarana sai labari me babban suna". Ire iren
wadannan hirarrakin da abbansa har yau ya kasa sabawa da tunasu,har yau ya kasa
jin Normal ne a rayuwarsa,har yau kansa baya iya jure tunasu,duk sanda sukazo
masa sai yaji kaman kansa zai tarwatse,sai ya sakejin wani abu yana sanya nisa
me tarin yawa tsakaninsa da maamah din,yakan ji kaman bazai iya qara idanu ya
kalleta ko ya mutuntata ba......amma ta wani fannin.........uwa data cancanci a
kirata mahaifiya irin ameenatu anni......itace ke riqo da hannunsu a ko
yaushe,ta kuma qarfafesu da yi mata biyayya. Rana daya daya fahimci ta fara
sana'ar dalilin aure,adadin maza da matan dake kai kawo a gidan suka dadu,a
ranar ya yiwa wani mummunan rotsen da da qyara aka kashe maganar a police
station. Ranar nisan kwana ne kadai ya kawoshi yau da ake magana,don ta sakashi
a daki ne ta masa wani irin duka da sai da ya daina numfashi,tun abban nasu
dake daga kwance ba daman tashi ya ceceshi yana kiran sunanta gami da qoqarin
dakatar da ita,har yawun bakinsa ya dauke tsaf,yayi shuru ya zubawa sarautar
Allah ido,yana jin sautin dukan da maganganunta,amma baya iya jin koda tarin
muhammad. Yasan halinsa.....sha wuya ne dake iya shanye zafi da tsananin
duka,yasan kowanne irin nau'in azaba take masa bazaiyi magana ba.
"Me shegen baqin hali irin na ubansa.......baka isa ka
hanani neman kudi ba wallahi,yadda talauci ke neman kai ubanka ramin qabarinsa
tun lokacinsa baiyi ba......ni bazan zauna talaucin yayi ajalina ba". Qarshe dai musaddiq ya aika ya dinga zuba
masa ruwa kafin ya farfado.
Ta dauka
zai rusuna daga ranar,amma sai taga kaman ma bashi ta daka ba,sai ya canza
sabon salon kora da hali wajen yayyanka musu takalmi,karta mota da sace tayoyin
motar ko na babur.......still marasa haquri a cikinsu police station
suka.kaishi da qyar ta karboshi,zuciyarsa kuma na a tsaye bai rusuna ba,dolen
dole ta tattara ta canza sana'a,waccan din saidai tayi a wani wajen daban amma
ba cikin gidansu ba.
Ajiye
roban maca root din dana ginseng farouq yayi yana kallonsa.
"Amma yallabai......wadannan abubuwan biyu kaman suna
enhancing libido fa.....and..... ". Wani kallo fu'ad ya watsa masa da
idanunshi da sukayi laushi qwarai,ya miqa hannu yana fusge container din ya
ajiye a gabansa
"Baka lura kuma yana boosting energy ba?" Ya fada
cikin jin haushi. Dariya sosai ya qunshe farouq din yana gyada kai kaman
qadangare
"Yes.....yes na gani,kaman kai kenan da kayi loosing
energy dinka ko?.....wannan bazai boosta maka komai ba dude.......you need
a......."
"Zip it" Ya katseshi da kakkausan kallon nan nasa.
Shikam farouq bai gama maganansa ba,baiga abinda zai sanya a hanashi fadin
abinda yai niyya ba,sai ya janye baya yana daga kafadu.
"Duk wani abu da zai maidaka namijin gaske you're
Comsumpting......but ka kasa kunna engine din kadan......" Bai qarasa ba
ya cire spoon din cikin mug din ya jefeshi dashi,abinda ya sanyashi kasa qarasa
maganan......amma kuma ya kece da dariya,wanda shigowar anni parlor din ya
dakatar dashi daga dariyar.
"Farouqu.....zoka miqawa muhammadu ya dubamin wannan
address din.........wata qawata ce muna magana dazu ashe sun shigo suma".
Karbar address din yayi ya kalla,bai gane gurin ba don haka ya miqawa fu'ad.
"Few kilometers ne tsakaninmu,zaki je ne anni?" Ya
tambaya yana dubanta.
"Eh amma sai wajen gobe nake tunani.....tunda yau kaman
naji amna tana fadan inda zasuje,ba zaa bar gidan ba kowa ba duk da ba wani abu
bane". Kai ya jinjina ya ajiye takardar,sannan ya daga mug dinsa yana
shanye ginseng tea dinsa abinsa,ba tare da ya maida kai ga kallon da farouq
yaketa binsa dashi ba.
Dukkaninsu farouq ya xuba a mota suka fice. Sosai suka zaga
garin,guraren da sukaje sun kusa biyar,amma duk da haka amna bata gaji ba,fadi
takeyi
"Ya farouq.....don Allah mu zaga Maldives gaba daya
kafin mu tafi,tunda island ne baida girma can can". Dariya musaddiq ya
bushe dashi yana kallonta
"Kinsan yawan guraren da suke dashi kuwa amnee......a
qalla fa gurare dari da tamanin amnee,yaushe zamu iya zagayeshi?"
"But......amma please BB,gobe ma ka fita damu,inason
naci rihaakuru fish paste.......kifin Maldives please ya musaddiq" Ta fada
tana narke murya.
"Ki bani cin hanci mana saina roqar mana shi,harda
traditional market dinsu.......rannan naga suna saida abubuwan gargajiya
sosai.......i assured zakiji dadin gurin" Maganan musaddiq ta sake gigita
amnee,ta dinga roqar farouq,har sai data saka sabreen a ciki.
"Please BB farouq......a taimaki autan anni mana"
Sabreen din ta fada da sassanyar muryarta dake da wani irin nutsuwa. Murmushi
farouq ya saki,tana da kima a idanunsa da martaba me yawa,yana ganin mutuncinta
sosai saboda yanayin nutsuwarta da kamun kanta.
"An gama tunda.matar.oga ta saka baki" Dariya ya
basu dukkaninsu har ita sabreen din sai data murmusa kadan. Har yau ya kasa
yarda ko sau daya da binciken fu'ad a kanta......baisan meye dalili ba,duk da
ya sani shi din mutum ne mara gaggawa akan kowa da komai......amma gaba daya
halayensa sun canza a kanta,bazaice kuma ga wani dalili babba guda daya ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 72
72
Kusan dare ya soma nisa sanda suka isa gida,basu kuma lura
da hakan ba sai da suka shiga parlor din gidan suka sameshi zaune saman qananun
sofas din dake a falon. Yau idanunsa suna saye cikin farin glass wanda hasken
allon system din gabansa ya sake fidda hasken kwalbar glass din. Kallo daya
farouq ya masa yasan ta baci,ba kasafai ya fiya amfani da glass din ba sai idan
idanunsa suna masa wani iri,don yana zuqe hasken kowanne abun amfani kafin ya
samu shiga kai tsaye cikin idanun nasa.
Gaba
dayansu kowa sum sum ya soma shigewa cikin falon yana dosar qofar dakinsa.
Mamaki ya cikata ganin har suka tako veranda din farko na gidan sunata karadi
abinsu kuma cike da karsashi......amma da ganin wanzuwarsa kowa ya kama kansa.
"Sai da safe" Ta tsinci muryar farouq da shima ya
kama kansa zuwa dakinsu,abinda ya sanya jikinta yin laqwas itama ta qara
hanzari zuwa nasu dakin ganin kowa ya fashe daga parlor din.
A gaggauce
ta shige toilet da duka kayan wankanta,tayi wankanta ta kuma shirya a can,tana
fitowa kuwa ta nade saman sofa din data kwana jiya akai tana curewa waje daya
cikin comforter din data dauke. Bawai sanyi takeji ba ko wani abu,kawai tanason
takurawa kanta ne tayi bacci kafin ya shigo.
Bata jima
da kwanciya ba kuwa taji shigowarsa,ya ajiye komai a muhallinsa ya taka zuwa
toilet. Da alwalarsa ya dawo dakin,kamar jiya ya shimfida abun sallah ya fara
sallolin da batasan sanda ya gamasu ba,don gajiyar da tayi yau din ya dinga
sassauke duk qashin jikinta gajiya tana fita.
★W A S H E G A
R I★
K'arfe
hudu na yammaci dukkaninsu suna tsaye gaban motar suna qoqarin shiga,saidai
gurin ya kaure da hayaniya wanda kusan qananun fada ne da musu tsakanin saddiq
da amna wanda dukkaninsu bakinsu baya iya shuru.
Tuni
Jordan yayi zaune mazaunin driver yana jira su kammala shiga
"Anni tayi warning na kaiwa dare......i think wancan
hamman naku yakai qararku an fitar masa da mata har dare.....oya guys.....hurry
up muje mu dawo" Ya fada yana dan buga seat din motar,abinda ya sanya
musaddiq soma shiga yana cewa amna.
"Yau zai gane qaramin talaka ne....... Don't argue with
him.......shigo auta" Musaddiq ya shiga maganan don ya kawo qarshen fadan.
Juyawa
amnan tayi ta miqawa sabreen wani baqin kati da yafi kama da atm
"Matar oga.....yau ina jakanki.......ga wannan anni
tace na baki,naki kudin tsarabar ne da boss ya saka miki kiyi siyayya".
Bin card din tayi da kallo,ita bata taba ganin card ma irinsa ba,to amma kuma
ita me zatayi da kudinsa?. Ko fitarsu jiya ma ba wani abu ta siya ba,amma duk
da haka saida farouq ya cikata da siyayyar da ko budewa ma batayi ba. Hannu
tasa ta karba card din kawai,ta daga qafanta tana niyyar shiga motar sautin
musaddiq ya sauka a kunnenta
"Wow........kallemin guy dincan" Ya fada yana tabo
sadiq
"Tashin sense" Saddiq ya furta yana kallon fu'ad
dake tahowa. Cikin wani irin taku me dan sassarfa,sanye yake da wasu lafiyayyun
suspenders da suka sake bayyana ainihin zallar quruciyarsa,suka kuma sake
kwashe shekarunsa suka boyesu tas......saika rantse da Allah shi din sa'ansu
saddiq ne.
Saman
kansa homburg hat ce data fidda kyakkyawar fuskarsa da wani irin kwarjini da
kwantacenn kyau da zai iya gaya maka lallai shi din ruwa biyu ne da ake kira da
halfcast. Sosai kayan suka zauna masa a jikinsa,rigan na dan bayyana muscles
din da jikinsa ke dashi,wannan kadai zai gaya maka qaqqarfa kuma ginannen jikin
da yake dashi.
"Gayennan yana wuta.....anya ba zamu koma ciki mu canza
dressing ba......kada maldivians dinnan su dauka age mate dinmu ne fa"
Musaddiq ya fada sounding seriously. Dariya sosai amna ta fashe dashi tana dora
kanta kafadar saddiq
"An gaya muku ya fu'ad wai sa'anku ne?,ku sallama kawai
ku huta......idan kanajin babban kifi to shine.......kunga maza kun raina kanku
ko?" Dungureta saddiq yayi yana janye jikinsa
"Zakiyi dariya da kyau ai......abinda ya kamata ki fara
tambaya ko ki damu dashi shine dalilin da yasa ya fito.....ku koma ciki ba zaku
je ba,ko ya fito ne mu fita tare kinga yau shikenan......ba sauran sakewa"
Tsit dukkansu sukayi,saboda sunsan halinsa zai aikata da gaske. Kowa ya dauke
wuta a cikinsu suna fargabar hukuncinsa,har zuwa sanda ya qaraso.
Da ido
kawai ya yiwa Jordan inkiya ya fito daga mazaunin driver din,ya zagayo kujerar
me zaman banza ta kusa da driver ya shiga yana cewa farouq
"Shiga mu tafi". Da kallo farouq ya bishi,har ya
shiga ya zauna,ya daga idanunsa masu cike da kwarjini ya kalleshi yana daga
waje
"Ko ba zaka tafi bane ka tsaya kana kallona?" Kai
kawai farouq ya kada yana tunanin abinda ya sauya ma fu'ad ra'ayi ya aminta da
karan kansa zai bisu.
Yau fitar
dadinta sai taji baikai na jiya ba tun akan hanya,duk hirarsu suna kiyayewa da
hayaniya ko abinda zasu fadi. Hira suke da farouq a gaban mota duk da batajin
me suke fada,a haka suka isa guri na farko.
Sunyi
yawo sosai cikin kasuwannin da suke da kayan gargajiya na al'adun qasar
Maldives.....sunyi siyayya kaman ba gobe,duk da bata taba komai daga card din
da amna ta bata ba,hasalima a cikin mota ta barshi cikin handbag dinta da bata
fito da ita ba.
Gurare
da yawa idan sunje zamansa yake cikin mota,dama shi din bai damu da shiga
gurare irin wadannan ba. Koda sunyi tafiya guraren da yakanje gurare ne da suke
da alaqa da kasuwancinsa,ko tarihi na kasuwanci ko kuma zai amfani
kasuwancinsa,shi yasa yau din suka cika sosai da mamakin ganin yabi bayansu,duk
da dukkaninsu kowa ya ta'allaqa hakan da sabreen ce sila.
Guri na
qarshe da suka je,suna fitowa ya miqa hannu ya karba key na motar daga hannun
jordan
"Zaka iya komawa gida" Yace dashi kai tsaye.
Takawa yayi a hankali ya isa gaban motar,hannunsa daya zube a aljihun
wandonsa,yasa hannu ya bude motar ya shige seat din driver.
Junansu
suka kalla tsakanin saddiq da musaddiq da amna,mamaki ya cika kowa ganin yau
hamma da kansa zaiyi driving?,wani abu da suka jima basu ga yayi ba
"Zaku shigo mu tafi ko na wuce abuna?" Ya leqo
kansa yana magana dasu da miskilar fuskar nan tasa. Har rige rigen shiga suka
dinga yi kowa mamaki kwance qasan zuciyarsa.
Kaman
yadda kusan komai nasa ya banbamta dana kowa haka tuqinsa,driving yakeyi cikin
wata irin qwarewa da nutsuwa,gudu baiyi yawa ba......haka babu laqai laqai.
"Ina muka nufa ne sir?" Farouq daya kula ya sauya
hanya ya tambayeshi yana kallon fuskarsa dake a dinke tsaf. Shi kwata kwata ma
guraren da sukaje kaman basu bashi walwala ba ko kadan.
"Siyar daku zanyi na qara jari" Ya amsa masa a
taqaice yana sake maida dubansa sosai ga titin. Dariya sosai farouq ya saki
yana relaxing jikin kujerar motar
"Hakan yayi ai......dadin abun bamu kadai ka debo ba
ai" Yayi maganar yana turo p_cap dinsa gaba. Sarai ya gane me yake
nufi,shi kuwa bazai kulashi ba,saboda neman wajen da zai dan sake samun relief
kawai yakeyi.
Sannu a
hankali suka shiga Vaadhoo island sunan
dake rubuce baro baro a allon sanarwa. Ihu amna keson saki na murna amma sanin
wanda ke driving bayason magana me tsauri ko hayaniya ya sanyata danne bakinta
ta dole tana duban saddiq dake zaune opposite dinta. Gira ya daga mata alamun
tambaya,saita nuna masa map na inda suke ta qaramin screen din dake maqale a
gefansu.
"Vaadhoo.......glowing island!......sea of stars"
Ta fada da wani irin farinciki daya lullbeta don sai a sannan ta lura da sun
qaraso glowing island din.
"Addana.......mijinki is very incredible
wollah.......kinyi dace......kin dace....he's very calm,ya iya surprise,komai
nashi unique ne" Ta fada farinciki yana kamata,farincikin yau zata ga inda
ruwa yake haske......yashi da qasar gurin itama ke haske tamkar an watsa
taurari,wannan yana gaya musu qila ya musu booking na kwana a wannan sabuwar
duniya,ko kuma zasu kai dare a wajen suka yadda komai yake gudana.
Murmushi
kawai tabi amna dashi......babu wani abun burgewa tattare da yayan
nata......itace dai bata sani ba. Amma kuma sai itama ta samu kanta da fara
sallamawa al'amarin sanda suka isa adhaaran prestige,ma'aikatan wajen kuma suka
iso suna maraba dasu,da alama sunsan da zuwansu wajen.
Da idanu
kawai take bin gurin,da gasken gaske ta zama 'yar qauye tuburan. Gidaje ko
dakuna zatace saman ruwa da wani irin tsari me jan hankali. Bata da sauran
abunyi illa bayansu da tabi kaman yadda taga sunbi daya daga cikin ma'aikatan
saman wani shimfidadden abu daya zama hanya kuma abu daya da zai hanaka tafiya
saman ruwan.
Kai tsaye
zata iya kiransa hotel ko gidan saukan baqi. Suka miqawa kowannensu wani dan
card da komai da komai,sai amna ta daga kai ta kalleta bayan ta gama dubawa.
"Ga inda zamu zauna can.....zamuci abincin dare a
nan.......zami fita sea of stars muyi kallo harmu shiga idan da yiwuwar
haka.....komai mukeso zamuje mu karba......amma adda naso kwana
zamuyi......inama hamma yace mu kwana?" Amna ta fada tana duban sabreen da
hankalinta yake kan ruwan dake gaban door glass din. Shimfidadden ruwa ne iya
ganinka wanda yake bada kalan sky blue,abun akwai mamaki yadda mutane keta
harkokinsu Kai tsaye suna kai kawo kaman cikin gidajensu suke.
"Muje dakinmu adda" Amna ta fada da doki tana yin
gaba,bayan ta fidda wayarta ta fara daukan hotuna da videos.
Bata yiwa
kanta da kanta qoro ba,idanu ta bude sosai tana kallo,yanayin iska da tsarin
wajen ya banbanta da duk wani guri data taba zuwa.
Gaba
daya hankalinta a tashe yake,kaman yadda tunaninta yake a jagule waje daya. Iya
zunzurutun dollars din data kashe don tsara komai,tun daga zuwanta Maldives da
zamanta a wajen ba wani abu bane na damuwa muddin buqata zata biya. Bahaushe
yace ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba. Ya zuwa yanzu da take
zaune gaban glass door din tunani ne fal zuciyarta,tana jin kamar tayi wauta da
take zaune tana lissafin zai wahala fu'ad din ya tsallake wannan island din ba
tare daya shigoshi ba.
Tayi zurfi
cikin tunanin daya cika mata kwanyarta taji sn daneta daga baya gami da
maqaleta da kyau.
"You didn't missed your target......you hit it!"
Wanda ke maqale a bayanta ta fada da murya me qarfi.
A zabure
ta cire hannuwanta daga wuyanta gami da waiwayowa gareta,tana jin abun kaman
mafarki,idanunta dukka a waje take dubanta
"Ki gayan gaskiya.....bazan iya jurewa ba idan
kikacemin qarya kike"
"Wallahi wallahi me jadda ya shigo......but shi da
familynshi ne duka,but kaman dakuna daban daban ne"
"Thank god.......ki miqawa wannan Chinese boy din
wannan abun.......banason kuskure......after 30minutes zan shiga dakin,ya saka
cameran daidai yadda zai nuna komai.......ya tabbatar yayi diluting tablet din
a ruwa da lemonsa".
"Done!......breaking news zaya fita zuwa ga
Nigeria" Ta fada tana barkewa da dariya,yayin da fareeda ta tayata da
qaramar dariya mata sauti. Juyawa tayi ta fita,sai ita kuma ta soma zame kayan
jikinta da gagggawa tana wucewa wata siririn hanya da zai kaita toilet.
Cikin qasa
da minti goma ta fito,ta kuma tsaya a side din dressing ta soma balle wasu
turaruka tana shafe lungu da saqo na jikinta,ta ware gashin kanta da kyau ta
jiqashi da sassanyan qamshin turare,sannan ta bude wani jaka ta zazzage kayan
ciki tana dagasu kafin ta fara shirya kanta a cikinsu.
Wasu
gantalallun riga da wando ne,very skinny,ba iya jeans din ba,har rigar data
sanya. Ba wani sirri boyayye ko bayyananne da Allah ya wadatata dashi da bai
fito ba walau qashi ko tsoka,me tudu ko me kwari.
"Wow......wow" Taji an fada daga bayanta. Kadan ta
juya tana kallonta don batasan ta shigo ba. Hannu ta watsa mata tana tambayarta
alamun yayi?
"Perfect.......kome kamun kan mutum ya ganki sai ya
fada......ga kuma wadancan abubuwan na aikinsu yadda ya dace.......zance zaisha
banban nan da nan......fatan nasara" Ta fada tana daga mata babban yatsa.
Wani shu'umin murmushi ta saki tana takawa gaban madubin,ta sake juyawa sosai a
gabansa tana qarewa kanta kallo. Ita kanta ta yaba da kanta ballantana wata
halittar d'a namiji?.
"Yadda bai sassautawa zuciyata ba bazan sassauta masa
ba.......sai na tabbatar na zama cikakkiyar matarsa da shaidu na halas sannan
zan barshi ya shaqi numfashi me kyau" Ta qarasa maganar tana daukan
chewing gum ta jefa a bakinta tana duban qawartata
"Sai na dawo?" Ido ta lumshe sannna ta budesu a
kanta.
"Inajin inama ace nice yau zan samu nasarar kasancewa
da namiji irin muhammad jadda......koda bai aureni ba babbar nasara ce wannan a
wajena......best wishes" Wani kallo fareeda ta watsa mata
"To mayya........wata miyar ai sai a maqota,babban goro
sai magogin qarfe kuma" Dariya ta sheqe da ita
"Na sani qawata" Itama saita tayata tana ficewa
zuciyarta fes yau din.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 73
73
Karo na uku ya sake daukan cup din yana kurban tataccen
ruwan strawberry din da shine abu na farko daya soma zaba akai masa. Ya maida
cup din ya ajiye yana zare belt din suspenders dinsa. Sosai gurin ya masa kyau
ya kuma qawatar dashi,banda annin da suka baro a gida ita daya ba shakka ba
abinda xai sakashi qin yanke hukuncin kwana a wajen,amma ko iya hakan ma nan da
eleven yasan ya samu refreshment din da yakeso ai.
Mamaki
ya cikashi jin an murda qofar an kuma shigo,ya waiwaya yana tunanin saddiq ne
ko musaddiq,saidai kuma fuskar daya gani tasha banban da fuskokinsu gaba daya.
Da kanta
ta fito don karbawa amna grilled fish dinta don girmamawa ga yarinyar yadda
take kimantata da ganin girmanta,amnan tana da wani irin kirki da sauqin kan da
yake bawa sabreen mamaki,don haka tace
"Zauna addanki ne zata amso kifin nan da kiketa
kwadayi".
A gurin
ta samu musaddiq shima zai karba nasa order din,wani tsari ne dasu akan grilled
fish......zaka je wajen da kanka,zasu nuna maka inda kifayen ki ninqayarsu
cikin ruwa ba tare da sanin kwanakinsu qayyadaddu bane,zaka nuna irin kifin da
kakeso take a ciroshi a gasa maka a baka ka wuce. Kusan tare suka zaba aka kuma
musu irin gashin da sukeso,musaddiq din ya miqa mata daya plate din hannunsa
"Addanmu......taimaka ki miqawa hamma wannan
please.....kunfi kusa da dakinsa....Allah yasa banyi laifi ba" Murmushi
kawai tayi ta karba,tana mamakin yadda suke bata girma haka,bayan duk cikinsu
idan ka dauke amna bata girmi kowa ba. Ason ranta tace ya taimaka mata ya
qarasa masa dashi,to amma tana jin nauyin kasa masa alfarmar ko don yadda suke
daukanta.
A nutse
take takawa tana duba dakin da take tunanin kamar ya shiga ciki.
"Na gaya maka.....kana ganin kaman d wasa
nake?......zanci gaba da kasancewa a kowanne taku naka......zan kasance cikin
kowanne fitar numfashi da daqiqa naka.......makahon so nake maka.......i can't
imagining yadda xan iya ci gaba da rayuwa babu kai". Tayi maganar tana
karantar qwayar idanunsa. Tanaso ne komai ya kankama a jikinsa kafin takai ga
cikar burinta.......tanason kowanne hankali yayi nesa da tunaninsa kafin ta
aiwatar da komai.
Wani
qaqqarfan yanayi dake taso masa ya sanya ya kasa cewa komai. Kokawa kawai
yakeyi da abinda yakeji din,yanason tabbatarwa da ba wannan qaqqarfan abun bane
ke qoqarin motsawa?. Yana tsaka da wannan kokawar da duk wani control dake aiki
a jikinsa ya tsinci fadowarta jikinsa,ta sanya dukka hannayenta ta masa wata
irin bahaguwar runguma kaman zata shige cikinsa tana fadin.
Sake
kallon number dakin tayi da kyau,ta sake samun tabbacin shine,saita murza
handle din tana murmushin hattararta da yadda ta iya gane dakin,ta tura qofan
tana sanya qafafunta ciki.
"I need you......i need you please jadda......kada ka
juyawa zuciyar dake sonka baya.....ka bari na sauke maka abinda
kakeji.......kaima kana cikin irin yana yina......na gani a qwayar
idanunka" Kalaman da ta fara maraba dasu kenan kafin qwayoyin idanunta su
sauka a kansu.
Idan
idanunta ba qarya sukayi mata ba fareeda khaleed mustapha ce cikin mummunar
shiga.......dukka su biyun suna a tsaye,yayin data samu kyakkyawan maxauni a
qirjinsa saboda tsahonsa daya shanye nata.
"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu
minazzalimeen" Ta fusga daga qasan zuciyarta zuwa labbanta,saidai sautin
baikai ga fita a sarari ba ta samu ta janye qafafunta ta koma da baya.
Dukka
jikinta bari yakeyi,abinda ya sanya plates din guda biyu duka suka kife ruf a
qasa.
"Sorry madam" Wata murya ta tsarga saman
kanta,kafin ta dago ma har ya tsuguna yana kwashe duka plates din. Baya taja
kawai ta tsaya tana qoqarin maida numfashinta daidai,don bata da wani qarfi na
kwashe barnar da tayi sam.
"Relax Sabreen relax mana.....fareeda dince baki sani
ba?,ko fareeda dince bakisan yana bibiya ba?,sau nawa kikaga kiranta a wayarshi
da luluqin dare?,me kudi ne fa?,yana da kudin da zai iya gayyatar ko wacce mace
ta debe masa kewa......that's why aure baya a gabansa......karki yaudari kanki
sama da haka ma zaki iya gani...."
"And then waye shi a gurinki da zaki rude har
haka?" Wannan gigitacciyar tambayar ta fado mata,abinda ya sanyata gayyato
duk wata nutsuwa dake kowacce kafa ta jikinta ta azawa ranta tana duban
matashin daya miqe yana dubanta da plates din a hannunsa. Cikin harshen turanci
ya fara mata magana
"Sannu ko?,muje su canza miki wani kifin" Duk da
ba'a hayyacinta take ba amma koda ta dubeshi da kyau sai taji a jikinta mutumim
africa ne,duk kuwa da cewa shi din ba baqi bane.
Duk wani
zaren tunaninta ya gama kwancewa,don haka bata da wani zabi illa binsa ta
karbowa Sabreen wani kifin,saboda bata da abinda zatace mata idan ta koma dakin
haka.
Tana biye
dashi yana qoqarin janta da hira da mata tambayoyin da bama iya amsa masa
takeyi ba saboda yadda zuciyarta ke tsananin gudu.
Hannunsa
daya ya sanya ya yakice fareedan gefe zuciyarsa tana wani irin mahaukacin bugu.
Fushi da feelings gaba daya sun hadu suna neman sauya tsarin bugun zuciya dana
numfashinsa.
"Wacce irin dabba ce ke?,a hankalinki kike kuwa?"
Ya fada da wata irin tsawa data kusa tarwatsa duk wani plan nata......amma data
tuna wannan shine plan dinta na qarshe saita miqe da hanzari tana cewa
"Bazan taba iya qyaleka ba,sonka mahadin bugun
numfashina ne....ka soni please.....koda na iya yaun....." Bata samu damar
qarasawa ba saboda wani bahagon mari daya dauketa dashi yana huci,sai gata qasa
warwas ta zube bayan ta tuntsura ta dawo ta zauna.
Huci yake
fitarwa sosai yana jin yadda jikinsa ke sake rikicewa
"Daga yau ya zama na farko kuma na qarshe da kika sake
shiga hanyata ta kowacce fuska.....if not.....zan batar dake ne a
banza......idiot kawai mara amfani!" Yana kaiwa nan ya miqa hannunsa ya
dauki key din motarsa da wayar dake ajiye tare dashi guri daya,bai kuma tsaya
sauraron kukan data saki tana kiran sunansa ba ya sanya kai ya fice.
Yana ji
a jikinsa ba daidai yake ba,hakanan baya jin zai qara koda minti guda cikin
island din ba.......kaman yadda bazai iya tsaiwa nemansu farouq ba,haka ya nufi
hanyar barin wajen wani irin fushi yana lasar zuciyarsa.
Kaman
cikin gizo idanunsa suka sauka a kanta. Tana tsaye suna facing juna ita dashi.
Ya miqa mata kifin da aka nadeshi cikin aluminum foil yana sakar mata murmushi.
Bata da wani zabi da ya wuce maida masa martani duk da irin abinda takeji qasan
ranta.
"Thank you" Ta fadi tana juyawa. Taku uku kacal
tayi ta tsinceshi a gabanta babu zato ba tsammani. Wani irin zazzafan kallo
take tsinta cikin idanunsa.....wani kakkaifan kallo da kaifinsa ya zarce na
takobi.....kallon da tsananin bacin rai yake da matuqar tasiri a cikinsa.
Kallo ne
daya tabata har cikin b'argonta ya aika saqo sassan jikinta,saidai girma da
nauyin abinda ta gani qasa da minti biyar cikin dakinsa ya dakushe kowacce
razana tata. Nata fushin ne yake tasowa wanda a dazu tsananin razana da tayi ya
cakude da firgici ta rasa ainihin abinda takeji sai yanzu. Yatsansa ya daga
yana nuna fuskarta,sai kuma ya sanya hannusa ya damqi nata hannun ba tare daya
damu da plate din dake hannunta ba,ya finciketa da wata irin sauri daya qure
yanayin adadin tafiyarta ta kasa daidaita tafiyarta da tasa,sai hadawa da tayi
da sassarfa.
Qoqari
taketa yi ta qwace hannunta amma ko cikakken motsi ta kasa yi a hannunsa,kaman
yadda bai saketa ba haka bai waiwayeta ba,har sai daya dangana da motar. Seat
din gaba ya bude ya kuma sanyata a ciki ya rufe,sannan ya zagaya seat din
driver ya shiga,ya tayar da motar d wani dan irin zafin nama,yayu reverse ya
fusgeta da wani irin gudu na tashin hankali.
Dimaucewa tayi gaba daya har sai data sanya tafukan hannayenta ta rufe
dukka kunnuwanta. Ta kasa kallon titi ko sau daya saboda yadda jikinta yake
gaya mata irin gudun da yakeyi da ita.
Tsahon
tafiyar mintina ashirin da sukayi bakajin komai sai qarar iska dake son kutse
ta cikin window din motar. Birkin da yaja da wani irin qarfi shi ya kusa sakata
tintsurowa daga nata seat din.
Murfin ya
bude ya fita.....ta dauka a nan abun zai tsaya amma sai taga yana zagayowa inda
take zaune. Sake bude motar yayi,ya kuma cafko hannunta kamar dazu ya fito da
ita,ba tare daya tsaya kulle motar ba yaci gaba da janta har zuwa cikin gidan.
Suka ratsa veranda suka wuce parlor suka tuqe zuwa ga bedroom dinsu. Sai da
sukakai tsakiyar dakin yaja burki yana sakinta da qarfi,ta turje taja ta tsaya
tana haki idanunta a kansa.
Haki
yake yana nunata da yatsa,yana son yayi magana amma yadda zuciyarsa ke bugawa a
jejjere cikin son wuce qa'idarsa ya sanya ya gaza fadin komai. Kaman daga sama
ya fusgo kalaman
"Da kowanne namiji ma tsayawa kikeyi?,kowanne namiji ma
fuska kike bashi?,wacce iri ce ke!,nace wacce iri ce ke?". Wani kalan
tashin hankali taji yana sauke mata saman kai,ta runtse idanunta ta kuma budesu
lokaci guda fushinta na qara hauhawa.....wanne irin dan rainin hankali ne shi
haka?,ta gaji!,takai maqura!
"Daga rana irin ta yau ba zaki sake fita daga nan ba
har sai randa zamu bar qasar nan.......zakita zama a dakin nan naga ta yadda
zakiga wani d'a namijin,waishin kowa ma burgeki yakeyi?,kowa ma son kudinsa
kike?"
"Eh......kaman yadda kowacce mace take
burgeka!.....kaman yadda kake shirya plan ka kama masauki kawai don ka hadu da
wata!.......idan kaga namiji yana burgeni to tabbas shi din ba ragowar wasu
bane.......ba sauran wata 'ya mace bane......isashen namiji ne da yake da abun
bayarwar ba muna maza b......." Tun daga tsakiyar kanta jijiyar dake aike
da saqo ta harbawa kwanyarta saqon KINYI KUSKURE!. Da wani irin hautsinannen
yanayi ya waiwayo yana fuskantarta bayan kalamanta sun masa shamaki daga fitar
daya fara niyyar yi
"Me kika ce?......ragowar wasu?......mema kika ce
rannan?,bani da abun baki ko?......kina tunanin zan hada jikina dake ne?.
Araharki tayi yawa da ko da wasa ban sha'awar kasancewa tare dake,saidai a yau
har cikin raina nakeji ya kamata na karbi sadakina......har kuma cikin raina
nakeji ya kamata na banbance miki tsakanin ragowar wasu da wadanda suke da abun
bayarwa dama wanda basu dashi.....tare da hakan ina me baqinciki da zaki zama
mace ta farko da zata karbi budurcin muhammad fuad" Maganarsa taxo qarshe daidai
da sanda shima ya kaita qarshe,ya kuma hadeta da bangon daya zama guri na
qarshe da zata sanya qafafunta.
Hannu daya
ya saka ya soma tsinke button din gaban rigarta na sama,yayi wani irin tsalle
yana fita daga gaban rigar tata ya fadi saman marble din dakin. Kafin tayi wani
yunqurin ya sanya hannu ya tsinke na biyu,na uku ya biyo bayansa a jejjere da
wani irin sauri idanunshi na kafe tsakiyar nata.
Caraf ta
kama yatsunsa tana riqewa da wani irin kalar tashin hankali,ganin button daya
ya rage farar vest din dake manne a fatar jikinta ta bayyana.
"Kada ke ketamin haddina......kada ka tab......"
Kalmar keta haddin data fada ta zafafeshi da kyau,sai yaji kaman ta gama raina
masa wayo. Shi daya biya sadaki shi ake kirawa keta haddi?,cikin qasa sa second
biyu ya raba rigar da jikinta ya kuma tsinke hannuwan vest din jikinta ya
zameta zuwa saman cikinta.
A firgice
ta nemi dunqulewa waje daya,saidai ya rigata ta hanyar lalubar tafukan
hannayenta ya sanya nasa a ciki ya kuma kafesu da bango,har a lokacin cikin
idanunta kawai yake kalla,yanason magana amma kowacce kalma ta gagara fita a
bakinsa,yanason ya koya mata darasi fiye da yadda take tsammani,yanaso ya kashe
bakin nan gaba daya,ta yadda koda da wasa akace mata ta yiwa wani me suna
muhammad rashin kunya ba zata fara ba. Tsoron da yake gani a yanzu cikin
idanunta ko kadan bai sanya a ransa na gaske bane,yafi kallon hakan da zallar
rainin hankai kawai dason kad'ar da hankalinsa.
Hannayen
nata ya saki da sauri ya riao qugunta d wani irin zazzafan riqo,ya kawo
fuskarta saitin tasa kafin yaja da baya yana sanya fuskarsa cikin wuyanta yana
sauke mata wani irn numfashi me dumi daya gigitata lokaci guda.
Ba ita daya
ta gigice ba.....duk wani kwantaccen tsumi dake jikinsa sai daya motsa,ya kamo
numfashinsa da qyar sanda ya cusa fuskarsa tsakanin breast dinta. Wani
lallausan qamshi dake fita tsakaninsu yaqarasa wargaza lisaafinsa,ya kuma tayar
da aikin qwayoyin da yasha ba tare da saninsa ba. Hannunsa ya sanya ya fara
murza fatar jikinta,daga kafadarta zuwa yatsun hannunta sannna ya zurasu cikin
nasa ya damqesu waje daya.
Qafafunsa yaji ba zasu iya daukansa ba,baya so kuma ya rasa qarfinsa ko
daya ko yaji wani softness akan hukuncin da zai mata. Yanason ya bata babban
darasin da bazata iya gogeshi ba,yanason ya goge duk wani raini da take
masa.....sassaucin da yake gwada mata yanason ta fahimci adalci ne irin nasa da
ganin damarsa......daga qarshe yanason ya banbance mata karatun maza suna suka
tara.
Rabata
yayi da qasa yana jefata saman gadon. Tayi juyi da zummar kifewa ta sauka a
gadon da muryarta da take wani irin shaking
"Banaso......nace maka bana so.....ni ba 'yar iska
bace" Wani malalacin murmushi ya qwace masa tamkar wanda ya bugu sosai da
kayan maye,wanj gefen na zuciyarsa kuma na masa ciwo da kalmarta. Auren nasa ne
iskanci?,bayan duk wani yawo data gama yi lungu da saqo?,shi zata rainawa
hankali ta nuna batasan komai ba banda ma lallai ta rainashi?,ai ya zama dole
ya goge wannan rainin daga rana irin ta yau.
"Zaki gane waye dan iskan gaske tsakanina dake" Ya
fada yana tarota,yayin da rub da cikin ya zame masa kaman wata sassauqar hanya
ta rabata da bra dinta,ya kuma birkitota idanunsa suna sauka akan qirjinta.
Kaman an
jona masa wuta haka yaji,a lokacin da take sanya duka tafukan hannayenta tana
rufe qirjin nata kuka yana qwace mata. Baqinciki yadda ya tsiraitata yana
kamata,bata tsira da komai ba sai fatar jikinta,siraran tafukan hannayen nata
basu wani rufe abun arziqi a jikinta ba,sai ta fara yunqurin jawo duvet,abinda
ya bashi daman kauda hannayen nata ya kuma maye gurbinsu da faffadan qirjinsa.
_na gaji,tun safe nake qoqarin hada muku pages dinnan don na
burgeku🥹,muje zuwa a gobe in sha Allah_
_wallahi wallahi duk wadda ta fitarmin da pages dinnan bazan
iya yafe mata ba,yadda zata daukeshi ta fiddashi ubangiji ya qwace abunda tasha
wahala a kansa daga hannunta🥲🥲🥲🥲_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 74
74
Nauyinsa
gaba daya ya aza mata,abinda ya sanya numfashinta yin nauyi,yayin da nasa
numfashin ya soma qoqarin yin qaura daga gangar jikinsa. Shi daya yasan kalar
abinda yaji sanda farar jikinsa ta manne da tudun qirjinta. Karon farko a
rayuwarsa da ya taba jin wani abu makamancin wannan.....karon farko da wani abu
me kama da wannan ya taba gilmawa rayuwarsa. Baisan yadda zai iya controlling
feelings dinsa ba a irin yadda wani magnet yake jansa ba.
Hannunsa
dukka biyun ya sanya ya riqe kanta cikin tafukan hannayensa yana kallon
fuskarta. Idanunsa ya sauka akan pink lips dinta da suka sake zama pink sosai.
Magana takeyi da alama amma kunnuwansa basa tantance abinda take fada. Motsasun
da takeyi sai suka zame masa kaman wata tsokanarsa takeyi......shauqinsu ya
kamashi sosai saboda irin nau'in siraran lips din da yake muradi ne......amma
kuma sai wani abu yazo ya tsaye masa a wuya sanda zuciyarsa ta darsa masa
"Ko mutum nawa ne suka dora bakinsu akai?" Yana
kaiwa qarshen maganar ya dora lips din nata saman nashi,ya kuma lalubo na qasa
ya riqeshi gam tsakanin harshensa. Kaman ya samu lollipop haka ya dinga
sarrafashi,cike da wani irin zafin zuciya da yakejin yana watsuwa saman
qirjinsa. Tun kwanyarsa na darsa mana adadin mazan da suka kai jikinsu da
bakinsu wajen da duk hannu da bakinsa zaikai har ya birkice gaba daya.
Zuciyarsa tayi wani irin rauni......rauni na baqinciki,bangare daya kuma wani
irin zazzafan shauqi na azalzalar zuciyarsa. Komai kwanyarsa sai ya
cakude......haduwar abubuwa guda biyu a gangar jikinsa duka lokaci guda,sai ya
dinga ji kaman zai zaunce......kaman gangar jikinsa da qwaqwalwarsa ba zasu iya
daukan komai ba.
"Ka rabu dani......bace banaso......bana so......ka
sakeni......ba 'yar iska bace ni" Maganganunta na qarshe kenan da yaji ta
furtasu labbanta suna rawa kaman yadda kowanne sashe na jikinta yake
rawa,idanunta sun fito sosai sun qara girma kaman yadda wani irin hawaye me
dumi ya cikasu fal har ya gaza adanasu suka fara zirarowa. Labbanta qirjinta
dama wasu sasassa na jikinta dukka radadi suke mata. Komai yana mata da wani
irin zafi da zata iya kiransa na mugunta kai tsaye. Wani mahaukacin tsoronsa
tuni ya gauraye jikinta da zuciyarta. Tsoron abinda ta fuskanci yana da niyyar
yi.....wani abu guda daya wanda ko a irin mafarkan da mutane keyi ita bata taba
mafarkin faruwarsa a kanta ba.
"Why?" Ya tambaya da tasa muryar dake rawa kaman
wanda kejin sanyi. Ya ware mata idanunsa da farinciki ya koma kaman an diga
manja. Labbansa da suka sake zama red sosai shima dukkansu rawa suke,da alama
akwai abinda yake da niyyar fada me nauyi daga zuciyarsa amma sunwa lips dinsa
girman da lafazin ya kasa fita.
"Why?!.....me yasa baki jirani ba?" Ya sake fada
wannan karon a gigice sannan kuma a tsawace,kaman mawunyacin zaki. Tsawar tasa
ta qara gigitata,ta rasa me ya kamata tayi sai kawai ta saki kuka.
"You're just 25yrs old.....me yasa baki jira rana irin
na yau ba?,waye da waye ya taba tabaki?.......na rantse sai nayi
ajalinsu......saina kashesu!" Ya fada da wata birkitacciyar murya da zata
tabbatar maka tabbas ba'a hayyacinsa
yake ba......hakanan kuma fushine danqare a zuciyarsa.
"Me yasa suka shigamin gona ta?,me yasa kika basu
dama?,me yasa?......Bari naji meye sukaji?,bazan qyalesu ba!" Ya fada a
zafafe cikin fitar hayyaci yana zamewa kadan daga jikinta tare da rage daidaita
tsahon nasu da yayi. Hannunsa ya aza saman cikinta ya kuma fara saukar dashi
zuwa qasan mararta. Wani numfashi taja me tsaho har wani rami dake qashin
wuyanta yana lobawa ciki. Duk yadda hannayenta ke rawa batasan da sauran
ragowar qarfinta ba sai da taji hannunsa a wajen da ba wata halitta data taba
bari takai wajen ba,ta yiwa hannunsa mummunan riqo da muryarta dake rarrabewa.
"Kk.....kak....karka....yimin haka......kayi haquri
please,don Allah".
"Ina da abun bakin ai?,baki sani ba?" Ya tambayeta
yana dage dukka girarsa akan fuskarta rinannun idanunsa na qara girma.
"Nas......na"
"Shshsshshh" Ya fada tana dora dogon yatsansa akan
lips dinsa yana ci gaba da duban tsakiyar idonta.
"Don't tell me kin sani......zakifi ganewa idan kika
gani a aikace...." Ya fada lokaci guda yana ture hannunta.
"Don All........" Ta sake yunqurin masa
magiya.....wannan karon kuka take da gaske,saidai baima barta ta qarasa ba ya
maida gurbin maganar tata da cewa
"Karkimin magiya ko ki hadani da Allah.......nima dan
iskanne......ya kamata nabi sahun sauran ko?......but definitely saikin
bambance tsakanina dasu......." Ya fada yana ture hannun nata da gasken
gaske wannan karon,ya kuma maqaleshi a inda bata da damar motsawa.
Tana
jin sanda iska ta qara yawaita a gurin,alamun dake nuna hijabin dake wajen ya
yaye. Ta runtse idonta da qarfi tana jin zuciyarta tana tsintstsinkewa gaba
daya,wani abune da bata taba imagining ba kaf rayuwarta
"Ban taba bawa kowa kaina ba.....ban taba bari ko
yatsana an riqe ba.....na rantse maka......ka yarda dani" Ta fadi tana fata da yaqinin ya qyaleta,wanda
ko a iya hala ya barta ta tabbata ya gama da ita......ya kalli jikinta yadda
ranshi keso ta cikin hasken fararen qwayayen dakin,wadanda suka yiwa dakin
qawanya tarwai kaman rana. Wai inji bahaushe yace ko a jikinsa wai an mintsini
kakkausa,sam baima fahimci bayaninta ba.....don a sannan ba wannan bane a gabansa.........yanaso
ne ya huce duk wani haushinsa a kanta......koda tayi mu'amala da maza
million......yanason dasa mata stamp dinsa......wanda zata mutu tana tunawa
MUHAMMAD JADDA daban yake da sauran maza,sau daya tak a rayuwarsa yakeson ya
aje mata wannan tarihin da zai kasa goguwa a ranta,daga rana irin ta yau
bayajin xai iya sake bin hanyar da mazan da basu da adadi suka bi.
Randa tace
masa baida abun bayarwa......ragowarsu fareeda,tsananin kai zuciya nesa kawai
yayi.......a daren yaso yayi mata yadda ba zata sake marmarin bin wani d'a
namiji ba.....amma a yau yana jin zai tattara mata duka hukuncin da ko maza
dari ta taba bi tabbas sai gabbanta sun gaya mata.
Maidata yayi
jikinsa gaba daya,ya manneta cikin jikinsa da wani irin tsatstsauran riqo kaman
zai ballata. Hatta da bakinta sai daya kasheshi tas ta hanyar sakayashi cikin
nasa bakin dake fidda qamshin mint leaves,yadda numfashinsa ke fita da dumi sosai yake ratsa qofofin hancinta yana
aikewa qwalqwalwarta wani irin saqo me rikita lissafi,matsanancin tsoro ya
shigeta na yadda a yau komai nashi da nata suke gauraya waje daya......yawun
bakunansu.......numfashinsu,dumin fatarsu dama laushinta,qamshin jikkunansu na
lausasan turarukansu dama komai da komai. Cikin tsakiyar wannan
firgicin......tana tsaka da tunanin mafita ta tsinci baqon abu yana wanzuwa a
jikinta.......baqon abu mafi gigitarwa da debe hankalin diya mace musamman a
sanda bata tsammaceshi ba.
Wani irin
azaba ta ziyarci kwanyarta irin wadda bata taba ji ba,duk da bakinta toshe yake
da nashi amma hakan bai hana wani irin gunji fita daga hancinta da bakinta
ba,ba wata kalma data samu daman fita.....amma gunjinta abune da idan kana dab
da dakin kana iya tsinkayen motsin fitarsa.
Yadda
yake samarwa kansa gurbi a hanyar da wani yanayi da yayi masa kama da sabon
muhalli sai abun ya gigitashi da wani irin mamaki. Zato yake daga gareshi
ne......baiyi yadda ya dace ba,don ko a mafarkan da ya sha yi bai taba darsawa
a ranshi zai samu wani abu me kama da sunan budurci watk virginity a tattare da
ita ba,don haka ya sake mata dukka qarfinsa ya kuma soma samawa kansa hanya da
dukka kuzarinsa zuciya na gaya masa ya fanshe duk wata kebewarta da wani d'a
namiji karon farko kuma na qarshe kaman yadda ya tsara hakan ya kasance.
Sake
gigicewa tayi da kalar azabar da takeji
"Ban taba yi ba......ka qyaleni!" Abinda takeson
ta fada kenan amma bai bata daman haka ba. Ci gaba yayi da abinda ya saka a
gabansa,yana jin wani irin yanayi da bai taba tsintar kansa a ciki ba yana
mamayarsa. Yana sake kutsawa yana sake shiga mamakin abinda yaketa taraswa
din,wani irin abu yakeji saman kansa me kama da hauka......kowanne hanya da
kunnuwansa zasu isar masa da wani sauti har yakai ga kwanyarsa don ta tantance
abinda ya dace yayi da wanda bai dace ba.....limit din daya kamata ya tsaya da
wanda zai wuce dukka sun toshe,wata duniya daban ya zarce wadda baya ganin
komai kuma bayajin komai.......daga shi sai abinda ya sanya a gaba kawai.
Komai ya
qarasa kwance masa sanda ya tabbatar ya gama bude kowacce hanya ya kuma kai
qarshe,ya fara aiwatar da komai da wani irin tsumammen kuzari da bai taba
tunanin ya jima haka a ajikinsa ba. A lokacin ne shima komai ya qarasa kwance
masa,bakinta da yake rufe dashi ya gagara ci gaba da riqonsa ya sulale yana
cusa fuskarsa tsakanin wuyanta da qirjinta.
"Hammm.......hammmmmmmmmaaaaaa" Ta samu kanta da
fadi da wata lanqwasashiyar murya tana jin kaman mala'ikan mutuwa ne yake
saukar mata.
"Yaaaaafffff......fffuuuuu......hammmmm" Ta sake
hado kalmomin da zummar tsaidashi ko bashi haquri tana ji a ranta wataqila taci
nasara ya saurareta,wataqila ya sassauta mata azabar da yake gana mata komai
girman laifinta a gurinsa,wataqila ya.mata wannan alfarmar karon farko data
taba neman alfarma irin wannan a wajensa.......saidai kuma inaaaa........wani
azaba daya ratsa tsakiyarta sai dukka kalaman suka subuce mata,numfashinta kuma
ya qwace mata.....duhu ya ziyarci idanuwanta da kwanyarta.
Yaji ya
kuma ga kaman haruffan sunansa akan labbanta,saidai baisan ainihin abinda bakin
nata ya fadi ba. Duk da ya fahimci inda komai ya dosa yana kuma ta qoqarin
controlling kansa amma ya kasa.......ya kasa yiwa kansa waigi.......ya gaza
tsaida kansa ko saisaita kansa koda na minti daya,bayajin kuma akwai wani abu
dake da qarfin daidait nutsuwarsa a daidai irin wannan lokacin. Wani irin sabon
kuzari yakeji a jikinsa da bai taba jin irinsa ba.....wani sabon qarfi yakeji
tattare dashi,yana jin kaman akwai inda yakeso ya isa,akwai inda yakeso yakai
dole dole......kaman idan bai isa wajen ba zai iya mutuwa.......kaman idan bai
qarasa muhallin ba akwai wani abu maras kyau da zai iya faruwa dashi,yana jin
wani abu can kusa da ransa dama zuciyarsa gaba daya,yana jin yadda yake shawagi
cikin wani sarari da baisan iyakar fadinsa ba.
Wulgawar
wani second cikin tunani da lokacinsa da wani irin gigitaccen yanayi shi ya
dawo da hankalinsa jikinsa. Wani irin numfashi me dauke da wani irin sauti
kamar numfashinsa yana shirin barin gangar jikinsa ya sauke......saukar
numfashin da tafi kamanceceniya da gurnanin zaki,kowacce gaba a jikinsa ta saki
ya aza mata dukka qarfinsa wani zazzafan gumi naci gaba da keto masa ta kowanne
kafan gashi dake jikinsa. Qin sakinta yayi ko ya raba jikinsa da ita.......yana
jin kamar idan ya matsa koda kuwa Inches biyu daga gareta zata bace
masa......yana jin ko yaya ya motsa kadan zata iya subuce masa,yana jin kamar
motsinsa yana iya sanyashi ya rasata. Wata qaqqarfar runguma yayi mata cikin
ni'imtaccen ingarman qirjinsa. Jiqaqqen gumin dake tsakanin sumarta goshinta da
wuyanta gaba daya ya dinga gangarowa yana cakuduwa da nasa,scents na turaren
jikinsu ya sake zama wani irin me sanyi tsananin jikkunansu. Wani irin
ni'imtaccen qamshi yakeji yana tashi daga jikinta.......qamshin daya zamewa
hancinsa na daban,irin qamshin da zai iya rantsewa bai taba jin abu me dadi a
hanci irinsa ba......all over her body ko ina idan zai iya tunawa wani irin
qamshi me laushi yake fitarwa.
"Dama haka matan suke?" Ya tambayi kansa yana
qiyasta adadin shekarun daya dauka yana zaluntar kansa ta hanyar haramtawa
kansa wannan nutsuwar da wannan ni'imtacciyar rayuwar.
Tunaninsa
kaf ya dawo da baya da baya har zuwa sanda ya fara maidata mallakinsa.....har
zuwa sanda ya fara keta gonar tasa.
"She's a virgin?" Labbansa suka motsa ya furta a
fili saidai can qasan maqoshinsa,tamkar dai yana tsoron fada,tamkar dai yana
tsoro kada kowa yaji. Yanajin yadda maqogoransa gaba daya ya soye kaman ba wani
sauran yawu daya rage a jikinsa.
Wani
qaqqarfan abu yaji yana mamayarsa bayan wani irin nauyi da yaji tamkar ya sauka
tsakanin qirjinsa zuwa mararsa. Yana jinsa yayi wani irin sakayau tamkar ma
idan ya miqe iska zata iya dibansa ta watsar. Wata irin nutsuwa da bai taba cin
karo da irinta ba ke ratsashi,kaman sabuwar iska sabuwar rayuwa da kuma sabon
ruhi aka bashi. Yana jin wani yanayi na daban na musamman na mamaye ilahirin
bargo da jininsa. Idonsa ya runtse da qarfi yana fadin
"How did it turn out like this?,what's the story behind
this??" Ya sake maimaitawa kaman me tsoron kowa da komai,kaman bayaso kowa
yaji fitar sautin daga bakinsa. Kwanyarsa na cakudewa da kalolin tunanuka iri
daban daban,negative da positive dukka lokaci guda.
Dif!.
Kowanne lantarki dake kansa ya dauke ya daina aiki na wasu sakanni kafin kuma a
hankali engine din karbo saqo da aikewa ya soma motsawa yana dawowa saitinsa.
Fuskarta da yanayin reaction dinta kukanta dukka hade da magiyarta lokacin da
yake yunqurin kaiwa bangon da yake muradi.......yadda labbanta suka dinga
motsawa.....yadda oily eyes dinnan da bai taba lura da tsananin haskensu da
sheqinsu ba irin yau suke jujjuyawa cike da tsoro firgici da razanin
kasancewarsu abu guda
"Wannan shine tsoron da akan gani idanun kowacce d'iya
mace a darenta na farko......ranarta ta farko da zata fara sanin d'a
namiji?" Ya tambayi kansa sannan ya amsawa kansa da cewa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 75
75
"Yes...yes" Zamewa yayi daga gareta yana rage mata
nauyin daya aza mata. Tafukan hannayensa gaba daya ya sanya yana qoqarin dago
fuskarta da sumar kanta ta zame labule a tsakaninsu,fiye da rabin hankalinsa
yana kan dukiyar fulaninta da suke wani irin fusgar hankalinsa suke sanyashi
jin kaman ya qare rayuwarsa a tsakaninsu ba tare da ya motsa ko ina ba. Hannu
ya sanya ya yaye sumar data rufe fuskartata jikinsa gaba daya yana rawa ya kasa
samun daidaito. Tari Tarin abubuwa keta kutse cikin tunaninsa suna fara masa
tilawa.....tun daga randa furucin farko ya fara hadasu da ita,yanata qoqarin
tuna abinda ya soma gaya mata.......yanata qoqarin tuna da wanne harshe yare ko
lafazi zaiyi amfani ya fahimtar da ita HAQURI bisa Tarin kalamansa marasa dadi
da ma'ana wadanda baisan adadin yawansu ba.
Da wata
irin martaba kima da darajarta da sukayi masa fadowar bazata cikin tsokar
zuciyarsa,suka cakuda da kowanne digon jini dake yawo cikin jikinsa yakai
fuskarsa saman tata ya hadesu guri guda,hancinsa ya saitu da kyakkyawan
hancinta me tudu da tsaho.
"Am.....soo.....amsor....." Yayita qoqarin
maimaitawa yana jin wani matsanancin ciwon kai daya saukar masa lokaci daya. Sai ya zame kansa ya saukar
dashi a kafadarta yana cusa fuskarsa cikin wuyanta. Yana ji ne kaman ya zama
wani irin ragon mutum kuma rarrauna......yana jin kaman kuka yakeso yayi ko zai
sake rage nauyin dake cikin zuciyarsa.
"Ya akayi na zama haka?,how?" Ya tambayi
kansa,kafin kuma a hankali ya dora labbansa saman kunnenta cikin salo na rada.
"Can you hear me.....am sorry......i didn't mean
to......to" Sai ya kasa qarasawa saboda bugun numfashinsa daya tsaya cak
lokacin daya fahimci babu fitar numfashi sam a hancinta. Fuskarsa ya sake kaiwa
daidai hancinta,da gaske ba fitar numfashi sam sam a tattare da ita,wani abu da
yazo masa a tsananin ba zata ya sanyashi gigicewar da har baisan sanda ya kira
sunanta ba
"Sabreeeennn" Ya furta yana tashi sosai hannayensa
dafe da gadon,saidai kuma danshin da yaji cikin tafin hannunsa ya sanyashi kai
idanunsa wajen ba shiri.
"Jini?" Ya furta yana sake fidda idanunsa waje,ya
fadi kalmar ne kamar me tambayar kansa da kansa,kamar kuma me bawa kansa da
kansa tabbaci.
Da sauri
ya saka hannu yana jawo comforter din da rabin jikinta yake a rufe rabi kuma
take kai,take ya saketa don bazai iya kallon yadda lafiyayyen jan jini ke
kwance a jikin farin comforter din ba,jikinsa ya dauki rawa gaba daya......kai
kace ba shine mamallakin kamfanin diamond da gold dinnan ba.....kai kace ba
shine Muhammad jadda dake razana zukatan maza ba......kai kace ba shine dan
gwagwarmayar nan ba.....hustler na gaske wanda baisan tsoro bs bare maganan ja
da baya....yakan iya sanya qafarsa kan kowanne bigire ko mataki da ake fargaba
saka qafa saboda hatsarinsa....yana fafata da koma waye komai hatsarin dake
tattare dashi......yau sai gashi labbansa na sama dana qasa suna haduwa ya gaza
koda ambatar sunanta.
"Me ka aikata haka fuad?,me ka aikata mata?" Ya
fadawa kansa da kansa da qarfi yana sanya tafukan hannayensa dukka biyun yana
kama kansa da kyau.
Sauka
yayi daga gadon da gaggawa yana nufan fridge din dake killace a daya daga cikin
corner din parlor din ya bude. Sassanyan ruwa ya fiddo,ya dawo saman gadon yana
tattarota cikin duvet din da shi kansa yayi bala'in staining sosai ya azata
saman cinyarsa. A cikin tafin hannunsa ya zuba ruwan ya soma shafa mata daga
fuska zuwa wuyanta. Sau uku kenan yana yin hakan.....amma ba wani motsi da
tayi.
"Oh my god!...." Ya fada yana wurgar da gorar
ruwan ta fadi qasa ta fata tsiyaya. Fuskarsa ya kafa saman nata fuskan,ya riqe
hancinta ya kuma bude bakinta ya soma bata iska ta ciki.
Mintuna
kadan yaji taja wani irin numfashi da ya tsarga mata har tsakiyar cikinta kafin
ta fiddoshi,dagawar qirjinta ya alamta masa dawowar numfashinta,sai ya miqe
yana duban fuskarta da tayi wani irin jawur idanunta da suke a rufe suka nuna
dagawarsu.
"Sabrrrrrr" Ya taqaita sunan nata saboda fitar
hawaye daga rufaffun idanunta suka kuma gangaro ta gefan kunnenta.
"I was wrong to do that......How can i make it
right?" Ya fada yana jin hankalinsa
na sake tashi. Bay qaunar kuka sam sam sam,musamman kuka na diya mace. Daya
daga cikin abinda ya dinga daga masa hankali lokacin quruciya kukan
musaddiq......kukan musaddiq a duk dare sanda maamah ta tafi ta barsu.....kukan
abbansa sai ya zama abu mafi tsanani da azaba daya taba gani.....wadannan
abubuwan suka sanya ya tsani kuka ainun.....duk da yana da tsananin dakiyar nuna
bai dameshin ba.
Hannunsa ya
dora saman goshinta don cire mata gashin daya sake lullube mata goshin,yana jin
kowacce kalma ya debo saita qwace daga bakinsa.......yanajin duk duniya ba wata
kalma harshe yare ko lafazi da zaiyi daidai da kunnuwanta idan ya
fadesu......shi a karan kansa yakejin kamar ba'a qirqiri wata kalma ta ban
haquri da ta dace ko zata dace da girman laifinsa ba. Da sauri ya janye
hannunsa yana jin yadda fatar jikinta ke fidda wani irin huci kaman yadda jikinsa
ke fitarwa
"Ya salam.......ya salam......am sorry,i hurt you
sabrrr......Am sorry.....i hurt you,I'll do everything possible to make you
feel better" Ya fada yana neman yadda zai gyara mata zamanta a jikinsa.
Jinginarta a jikinsa jinta take kaman wani nau'in azaba na daban,batasan yadda
wata rai zata fahimci yadda takeji ba.....tana jin kamar zata sake suma ne,don
numfashinta sam baya kaiwa hunhunta yadda ya kamata. Tanaso ta gaya masa ya
janye jikinsa daga nata amma ba wannan bakin,sai kawai kukanta ya qaru akan
nada,abinda ya sake hargitsashi kenan.
A
zahirin gaskiya baisan yadda zaiyi mata ba don baisan yadda akeyi ba,hasalima
shi bai taba zama yayi tunanin zuwan rana irin wanna ba a nan gaba a rayuwarsa
bare ya nemi ilimin yadda akeyi ba.
Jikinsa ya
zame yana jin yadda zazzabi ke dafa qasusuwansa......amma tashin hankalin jinin
da yake gani daga jikinsa ya dame wannan. Wayarsa ya dauka,sai ya samu kansa da
rasa wanda zai kira.....wazai kira?,wa zai gayawa?,yace masa me?.
"Farouq" Kawai shine sunan daya fado masa. Bai
damu ba da yadda farouq din zai kalli abun.....abinda kawai ya dameshi yadda
zai ceci ranta daga ta'addancin daya tabbatar yayi mata. Idan ya daga kai ya
kalli inda jinin ke kwance sai yaji ya aikata baqin fasadi ne kawai yau a daren
nan,qaramin kisan kai kawai yakeji ya aikata.
"Hello......zamu kwana ne....wajen nan fa yayimin,ina
tunanin dawowa nida fannah....."
"Am at home" Kawai ya fada da wani irin sound da
yaja hankalin farouq din. Aje yanayinsa yayi gefe da wasan dake cikin muryarsa
ya bawa fuad hankalinsa
"Is something wrong?" Ya fada da tsananin kulawa a
muryarsa. Sai daya runtse idanunsa sannan ya budesu yana maidasu inda take
kwance sannan yace
"Yes farouq......a rude nake.....please help.....i
don't know what to do"
"You are not alone......am here to help,take your time
and tell me what's happening?" Farouq ya sake fadi cikin yanayin kwantar
da murya.
"We had our first night farouq......i caused her
serious injury" Ya fada da tsananin nauyin abinda yake fita daga bakin
nasa,saidai kuma ya zama dole yayi hakan,don gani yake kaman tana dab da komawa
sumanta.
Wutace ta
daukewa farouq din. Shima maganan ya masa dan nauyi kadan,duk da ya jima da
sanin duk wadda zatayi irin wannan karon da fuad din abun bazai zama da sauqi
ba. Don ya bashi relief sai yace.
"Relax....ina zuwa". Yana sauke wayar daga
kunnensa. Murmushi kadan ga qwace masa duk da qasan ransa tausayin adda sabreen
ne fal. Yasan za'a fuskanci hakan daga fuad din,duk da tsananin wayewarsa da
sanin lunguna da saqo na qasan duniya.....gogewarsa da mmu'amalarsa da kalar
mutane daban daban jinsi daban daban......amma yau saboda tsananin kamewarsa da
zame kansa daga dukkan wani batu ko sabga data shafi wannan fannin ya rasa
yadda zai taimakawa matarsa. A ransa yaji tabbas ciwon ba qarami bane tunda
yaji damuwa sosai a muryarsa.
Ya jima
yana kallon number wayar anni ta qasar yana kwatanta yadda zai kirata ya gaya
mata. Wannan din wani training ne nata data musu. Ko.meye nasu idan ya samesu
komai nauyinsa bata yarda wani ya fara jibantar matsalarsu ba kafin ita bare a nan din baisan waye zai kira ba,dole
ya koma ya shiga sms ya tura mata saqo kaman haka.
_"Muhammad yana dakinsa......he needs your
assistance"_ yana tura mata ya aje wayar,don bayason ta kira neman qarin
bayani don wabillahi baisan ya zai mata shi ba.
Tsaiwa
cak yayi kuma wani abu yana dawo.masa da baya.
"Ya akayi first night yazu musu da hakan if ba virgin
bace?" Ya raya maganar a ransa,sai kuma yayi saurin kawar da ita don shi
ya jima da qaryata duk wani hasashe na fuad tun ba yau ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 76
76
Sanda saqon
ya iski anni dawowarta gidan kenan,tazo ta samu gidan ba kowa basu dawo ba.
Daki ta wuce ta sauya kaya ta dauki wayar tana fitowa parlor da zummar kiransu
taji me ya kaisu yin dare bayan tayi warning dinsu kan hakan kafin su tafi?.
Jiya sam bataga sukuni ko walwala saman fuskar fuad ba,kuma tana ankare
dashi,yadda ya kasa ya tsare a falon,bai koma daki ba sai bayan dawowarsu.
Tasan yana da zurfin ciki sosai,ba kasafai ka fiya sani ko gane abinda yake
damunsa ba,amma ita din uwace,koda wanne yare sukayi magana su dukkaninsu tana
iya fahimtarsu.
Shigowar
saqon ya dakatar da ita daga qoqarin kiran nasu da takeyi
"Wani sabon sakarcin ne kuma haka?" Ta fada tana
zama saman kujera da gorar ruwan dake hannunta ganin me saqon farouq ne.
Sau biyu
tana maimaita saqon,tasan tunda ya fada da gaske fuad na cikin gidan,duk da
bataji alamun akwai kowa ba a ciki,amma sai kuma saqon yaja hankalinta. Cikin
fargabar kada wani mummunan abu ne ya faru dashi ta ajiye gorar ruwan tana
maida hijab din jikinta,ta miqe idanunta kan qofar dakin,ta taka a hankali ta
isa qofar.
Knocking
ta fara yi,knocking din farko ya sauka kunnuwan fuad dake tsugunne gaban gadon
yana monitoring numfashinta,gani yakeyi ko yaya ya matsa zai iya sauke idanunsa
a kanta ya tarar ba numfashi tattare da ita.
"Waye?" Yayi namijin qoqarin tambaya
"Anninku ce" Ta fada a nutse. Idonsa ya lumshe ya
kuma bude duka lokaci daya yana furta
"Rabbi yassir wala'ta'asir.....ya salam sallim"
Yana jin kaf rayuwanshi idan ka debe rayuwar da maamah ta jefasu y taba shiga
tashin hankali irin na yau ba. Baisan ta yaya zai bari anni ta shigo ta gansu a
haka ba duk da zuwa yanzun ya saka Moroccan jallabiyya a jikinsa tun sanda ya
kira farouq. Ita dince sam jikinta yaqi tabuwa masa,da yakai hannu kusa da ita
sai maga ruwan hawayen dake idanunta yana qaruwa,ba bakin magana sam sam a tare
da ita,amma duban data masa guda biyu tal ya karanto wani irin fushi da kyara a
tattare da ita.
"Ki taimaka please.....ki bari ko riga na saka
miki" Wani fusataccem fushi ne ya
sauko mata,ya saka mata riga bayan ya gama ketata ya kuma keta haddi da duk
wani mutunci nata da take taqama dashi,ta kuma killaceshi tsahon lokaci?.
Yadda ta
maida idanunta ta kulle ba tare data ko motsa ba ya tabbatar masa bata buqatar
ganinsa ne gaba daya,ga anni na tsaye a qofa dole bazai yiwu ya barta tanata
jira ba,haka ya doshi qofar can qasan ransa yana fadin
"Me yasa kayi haka farouq?" Yana qiyasta da wanne
idanu zai daga ya kalli anni?.
Fuskarsa kawai ta kalla da yadda ya bude qofar cikin rashin karsashi
tasha jinin jikinta.
"Kana lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi
da ido. A yau dai ko karen hauka ne ya cijeshi baya jin zai iya kallon idanun
anni bare ya mata bayani. Ratsewa yayi
gefe da alamun bata hanya. Itama batace komai ba,ta maida dubanta ne daga cikin
dakin tana hango iya abinda zata iya gani din wanda carpet ne da dressing
mirror kawai take iya gani,sai ta maida dubanta kan fuskarsa da a yau yakejin
idanun anni tako ina a kansa da wani irin nauyi. Batace komai ba itama ta
ratseshi ta soma takawa cikin dakin,wanda taku biyu kacal tayi shi kuma ya fice
yana laluben inda zaije ya aje kayan kunyanshi nesa da annin,saidai a taku na
hudu idanunta suka sauka akan Sabreen,jinin dake jajur yayi staining jikin
duvet da comforter din ya marabceta,cikin qasa da second uku ta fahimci me ya
faru.
"Subhanallah" Ta fadi tsigar jikinta yana tashi.
Tasan ko meye ya faru a wajen artabu akasha ba kadan ba,ko tayi taurin kai yaje
mata da dukka qarfinsa,qarfin da sam sam tsakanin nata da nashi baizo daya ba.
"Muhammadu......maida qofar nan ka rufe" Annin ta
fada da madaukakin sauti sanda yake dab da bakin qofar parlor din. Cak ya
dakata da abinda yakeyi din,ya maida qofar ya kulle kaman yadda anni ta
buqata,ya dawo kuma a hankali cikin parlor din yana laluben wajen zama. Gangar
jiki duka da zuciya sai yakejin kaman ba tasa ba,zafin zazzabi yana ci gaba da
lullubeshi yana raunana jikinsa,saidai yadda kunyar anni ta rufeshi tafi masa
nauyi akan zazzabin.
A
mamakance take isa gaban gadon
"Ikon Allah" Tafada qasan ranta,wato ita dake
lissafin ganin result ta hanyar dauka
jika,ashe karatunma sai yanzu aka farashi?.
Sautin
muryar anni cikin dakin sai tayi fatan inama qasa zata tsage ta wuce
ciki?,yanzun yana da tsaurin idanun kiran ummansa taga barnar da yayi?,wanne
irin terere ne wannna yaja musu?,anni fa.....anni,ya manta surukarta ce?,ya
manta akwai kunya me girma tsakaninsu?.
"Subhanallah......ya salam" Anni ta.maimaita
wannan karon a sarari saboda jinin data gani muraran daya wuce wanda ta hanga
daba bakin qofa. Dukka jikinta yayi sanyi sosai,ta tabbata babban barna
muhammad din yayi.
"Sannu......tashi a hankali ki qarasa bandaki"
Anni ta fada tana kamata da tsananin takatsantsan ta yadda zafin ciwukan
jikinta ba zasu dameta da yawa ba.
Wata
siririyar qara sabreen din ta saki,qafafunta kuma suka lanqwashe tilas ta koma
ta kwanta duk da anni riqe take da ita. Hawaye ne ke fita ta gefen
fuskarta,tsananin tausayinta ya kama anni. Bata taba kawowa muhammad xai gwada
rashin haquri irin haka ba,dole yarinyar tana buqatar motsawa ta gyara jikinta
kafin ma a samu bakin zaren gane iya adadin barnar data afku.
Yana
daga falon amma.yana iya hangensu saboda a bude anni tabar qofar,uwa uba yana
zaune saitin wajen,saidai yayi kaman bashi a wajen.
"Muhammadu" Anni ta kirashi kai tsaye,ya amsa yana
tasowa. Idanunshi a kanta yana sauraren bayanin anni.
"Akwai ruwa me dumi a toilet.......ka kaita ta gyara
jikinta tukunna.....ina zuwa" Anni ta fada tana nufar qofa don itama zuwa
yanzun kunyar ke neman kayar da ita.
Hakan
yayi masa,yabi bayan annin ya maida qofar ya murza key,sannna ya tako zuwa ciki
yana nade hannun rigarsa. Sai yanxu kwanyarsa ta fara dawowa aiki,bazai kuma
saurareta ba zaiyi kaman yadda anni tace,zaiyi yadda ya dace,dom haka yana
qarasawa gabanta ya sanya hannu ya dauketa cak kaman jaririya haihuwar yau,ya
lullubeta cikin qirjinsa yana wuce toilet din da ita.
Yana jin
yadda ta damqe hannuwansa da kyau,da alama haushin dake cikin zuciyarta ne
takejin kamar riqon tsaurinta a garesa zai sassauta abinda labbanta da bakinta
ba zasu iya fada a yanzu ba.
Sake
yaye mata dukka suturar jikinta yayi,ta sake runtse ido abun yana mata zafi.
Cikin wasu mintuna jikinta ya zama bayyananne a wajensa?,yana qare mata kallo
haka kanshi tsaye da kaifafan idanunsa da takejinsu a kanta?.
"Bazan kalleki ba indai har bakison hakan.....zan kulle
idanuna har saikin bani izinin na budesu" Haushi da takaici suka
lullubeta,harara takeson jefa masa zazzafa amma bataji idanunta suna a daidai
din da zai ga harara tata yadda ya kamata. Banda ya raina mata wayo yana tsare
yana qare mata kallo da wani irin yanayi dake qara kashe masa gangar
jiki.....amma kuma yana gaya mata zai kulle idanunsa?, daga baya kenan wai anyi
sadaka da karuwa ta furta a ranta.
Sake
dagata yayi cak ba kuma bata lokaci ya sakata cikin bathtub din da anni ta hada
ruwa me dumi qwarai. Wahalalliyar qara ta saki da muryarta dake nuna duka
qarfinta ya qare.
"Ka sakeni....ka cireni a ciki" Ta fada hawaye na
layi bibbiyu akan fuskarta. Wani irin narkewa zuciyarsa tayi da tsananin
tausayinta da bai taba jin irinsa akan kowacce diya mace ba idan ka cire anni
da amna. Saidai ko kafin ma yayi mata yadda tace ta sake masa wani zazzafan
cizo a hannunsa dake dafe da tub din.
"Ouch!" Ya fada yana runtse idanunsa saboda
tsananin cizon data sakar masa. Ware manyan idanunsa dinnan yayi a kanta bayan
ya budesu,idanun da bataji komai tsahon xamani zata iya mance memory din daya
aje mata a yau. Labbansa ya motsa yana jin zafin zazzabin har cikin idanunsa,to
amma yanayin daya sakata a ciki yafi komai da yakeji ciwo. Ya sani ya shigeta
ne da duk wani qarfinsa,yana tsammanin samunta budaddiyar hanya ga
kowa......sai abun yazo masa a wata irin bazata a sanda bazai iya controlling
din kansa ba kuma
"I'm truly sorry for the pain I've caused" Ya fada
da wani irin calmness cikin muryarsa,sai ya sanya hannu yana cirota daga
bathtub din,yana jin bazai juri barinta tana jin abinda takeji din
ba......baisan girman pain din ba bare ya kwatantashi,saidai koma meye ya
tabbatar radadinsa ya wuce wasa.
Bedside
drawer ta isa tsigar jikinta na sake tashi gana girgiza kai da jinjina barnar
data tabbatar ba qarama yayi ba,wayarta ta dauka ta duba last call dinta.
Qawarta da suka rabu dazu hajja saudat ta kira.
"Kuna da wata gynecologist ne mace da zata iya home
service kuwa?" Anni ta tambayeta kai tsaye.
"Eh akwai.....'yar qasar syria ce.....tana da kirki
sosai fadwa haleem".
"Na gode.....kimin magana da ita please,ki bata address
na gidana.....if possible tunda bamu da nisa kada ta wuce one hour"
"In sha Allah kusa muke ai"
"Na gode" Anni ta fada tana katse kiran. Farouq ta
koma kira,saidai kira har biyu bai daga ba,sai ana ukun sannan ya daga yana
sosa kai.
"Ku kwana a can,ku biyasu kudin kwana daya.....but
kakaimin amna gidan saudat acan nakeso ita din ta kwana"
"Okay.....in sha Allah" Farouq ya amsa shima yana
jin dadin hakanma da tace,don shi kansa a yanzu ji yake ya zama surukinta,ina
ga fuad din. Yadai tabbatar ba zasu qarke lafiya ba idan ya dawo hayyacinsa,to
amma wa suke dashi sama da anni?,itace qawarsu abokiyarsu kuma.
_uhmmmm....tofa,sabreen naga kin dauki zafi da yawa😄😄.....amma
dai muje zuwa_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 77
77
Da wani irin
yanayi yake wanke mata kowanne sashe na jikinta da ruwan shower gel din. Wani
kuka take saki kawai tana ji har a ranta ya gama da ita,bata da wani sauran
qarfi da zata dakatar dashi ko guda daya,cizo kam ta masa shi har batasan adadi
ba,amma ko a fuska baya nuna mata yaji zafinsa bare akai ga dakatawa da abinda
yakeyi,tamkar ma ba jikinsa take ciza ba,idan ta saka bakinta ma tsaiwa yakeyi
har sai ta cire don kanta. Shi kadai yasan me yake sake ji cikin jikinsa,ji
yakeyi kaman baiyi komai bama,wani sabon feeling ke taso masa saboda santsin
shower gel din dake sassan hannuwansa wanda da tafin hannu kawai yake dauraye
mata jikin ba tare daya nema loofah ba. Kafin ya gama wanketa launin idanunshi
sun sake canzawa sosai,numfashinsa yana masa nauyi tsakanin qirjinsa da
hunhunsa,inda zai samu....inda zai yuwu yana buqatar sake kasancewa tare da ita
ko yaya ne.....koda na mintuna kadanne,amma shi kansa yasan yadda take a yanzu
dole tana buqatar medical care. Bai taba jin ya zama addicted to wani abu ba
irin wannan abun,cikin qasa da wasu awanni qalilan yana jin kamar an halicci
abunne sabodashi shi kadai.
Hannunsa
ya sanya ya riqo qugunta bayan ya fiddota daga bathtub din. Idanunta yake kalla
sosai wadanda suka rine saboda azabar kuka. Taqi kallonsa ta kuma sanya duka
hannuwanta biyu tana turashi baya,amma ko motsi baiyi ba bare tasa ran zai
matsa. Yadda takejin dumin fitar numfashinsa a rarrabe yana sake dasa mata
matsanancin tsoronsa,shigen wannan yanayin taji daga gareshi dazu,a yanzun idan
yace zai maimaita abinda yayi dazun ta tabbatar saidai ta taqaitawa kanta
wahala kawai tayi sallama da duniya......ita kadai tasan abinda takeji,ita
kadai tasan radadin da takeji yana ratsata a duk wani motsi da zatayi.
"Sabrrrrr....." Ya fada da sautin dake kama da
rad'a,wani irin narkakken sauti dake da amo na can qasan maqoshi,idanunsa cike
fal da wata irin mahaukaciyar soyayya da baiyi zaton cikin zuciyar tasa akwai
wani space daya ragewa wata halitta ba.
Kanta ta
dauke gefe,maganganu takeson gasa masa amma tana jin idan ta tsaya ta maida
masa koda kalma daya ma yana da wannan darajar ashe?.
"Sabreeennn" Wannan karon ya kira sunanta full da
wani irin sassanyan kuma kwantaccen sauti. Idonta ta lumshe tana mamakin jin
sunan yau radam saman bakinsa,kiran sunansa a bakinsa daban yake da yadda kowa
ke kiranta,kaman yadda komai nashi yake daban haka furucin sunanta a
bakinsa.....amma kuma zuciyarta saita ture hakan,haushinsa ya taso ya maye
gurbin wannan.
"I know.....nayi abubuwa masu yawa......na bata miki
rai da yawa......na gaya miki maganganu masu yawa......i hurt you.....i really
hurt you even...." Sai ya kasa qarasawa saboda yadda zuciyarsa take rauni.
"Na bata miki da yawa.....na sani,but dukan abinda nayi
shine akan hujja da evidence da binciken da nayi wanda yazo da negative reviews......sabrrrr" Ya sake
kiranta a karo na uku yana sake zube qwayoyin idanunsa dake cike da shauqi a
kanta,yana jin kamar ya dauketa ya bude qirjinsa ya boyeta,yana jin kamar ya
hadiyeta ya huta da abinda yakeji qasan zuciyarsa.
Ganin da
gaske ba zata kalleshi ba sai ya sanya hannu qasan habarta yana juyo da
fuskarta. A zafafe ta qwace tana hadiye kukan daya taso mata,ba abinda take
muradi a yanzun irin ya sake mata qugunta tayi nesa dashi,ya gama kalle komai
da komai nata.....wannan laifin nasa batasan yadda zata gogeshi ba.
Sake kamo
fuskar yayi ta qwace,sai kawo ya jawota cikin jikinsa ya mata wata kyakkyawar
runguma. A karo na biyu fatar jikinsu ta sake haduwa guri daya,wani qaton
numfashi ya qwace mata,kaman yadda qaramin yaron da yasha kuka kan saki ajiyar
zuciya sanda ya samu kyakkyawar runguma da lallashi daga wajen mamansa.
"My heartfelt apologies" Ya sake fada da wani
sassanyan sauti me tada tsigar jiki yana miqa hannu ya sake musu ruwa saman
kansu shi da ita. Saukar ruwan ya sake tayar masa da abinda yakeji ninkin na
dazu,abinda ya qarasa gigitashi kenan,ya dagata yana hadeta da bangon toilet
din,ya fara abubuwan da yasan zai samu sauqi da sassaucin abinda yakeji.
Wani irin
tsoro ne ya sake kamata,takaici da baqincikin yadda yake sarrafa jikinta yadda
yaga dama,sai ta sake sakin kuka me sauti tana sake tureshi dakai masa duka da
siraran tafin hannunsa. Ba abinda yaji saiji da yayi ma kaman tana sake
zugashi,sautin kukanta kawai yake iya ji daya sake zame masa kaman zuga
zugi,don sai ya dinga jin kaman kukan wani abu daban takeyi bana baqinciki
ba,deep inside yasan na baqinciki ne,but bazai iya qyaleta ba ko yaya......yana
buqatar samun sassauci koda baiyi me gaba daya ba,yanajin zuciyarsa da
rayuwarsa tana sake mannuwa da ita,yana jin kamar duk wani fitar numfashinsa ya
ta'allaqa da ita ne.
Sai daya
tabbatar ya samu nutsuwar da yake da buqata sannan ya jata jikinsa yana fitar d
wani zazzafan numfashi,ya gama kashe mata jiki da tsoro itama,dole ta jingina
da jikin nasa tana jin yadda zukatansu ke wani irin gudu,musamman shi da bugun
zuciyarsa ke shiga cikin kunnenta sosai saboda kan nata dake kwance a qirjinsa.
Duk da
ruwan dake zuba saman kansu yana kwaranyewa a sassan jikinsu gaba daya amma
hakan bai hanashi tantance dumin hawayenta saman fatar jikinsa ba. Ya gaza bude
idanunsa,sau hannunsa guda daya yake shafar sassalkan gashinta daya watsu har
gadon bayanta,ya kuma manne sosai saboda ruwan dake zuba
"Am sorry......I'm genuinely sorry,My apologies from
the bottom of my heart" Ya fada yana kissing goshinta softly.
Ture
fuskarsa tayi tana sake qayyade adadin rashin imaninsa......tadai san saboda
itace kawai ya gwada mata wannan rashin tausayin,banda haka ta tabbatar inda
duka mata haka sukeji ba abinda zai sanya su zauna ko suci gaba da yin aure.
"Leave me" Ta fada tana qoqarin tashi daga
jikinsa. Hannunsa ya sanya ya damqota sosai yana cewa
"I can't......ko mutuwa bata isa ya rabani dake ba
sabrrrrrr.....zan yita baki haquri har ranar da numfashina ya fita daga gangar
jikina......zanta baki haquri ko sau dubu a rana kikeso.....karki wahalar damu
gaba daya ta hanyar cewa na barki ko na nisanceki.....don wallahi wallahi
wallahi bazan iya ba......i can't do it" Ya qarasa fada yana sake matseta
jikin bango sosai sannan ya fara tsarkake jikinsa idanunsa a kanta.
So yake
qarfi da yaji sai ya cire kowacce kunya daga idanunta,tsaiwarsa haka a gabanta
tana jin shine abu mafi girma firgici da razani da suka taba gani. Cikin
mintuna kadan ya gama ya kashe shower din,ya jawo babban towel ya wareshi. Ta
dauka zai rufa ne ko ita ya bata daman rufawa.....maimakon haka sai ya jawota
jikinsa ya bude towel din ya nadesu su biyun a ciki.
Shi da
ita ba wanda numfashinsa baiso yin qaura ba saboda yadda jikinsu ya sake
gauraya dana juna
"Shshshsh" Ya fada yana qoqarin daidaita
numfashinsa,don bayason tace komai,hannunsa ya sanya a gadon bayanta ya matseta
cikin jikinsa gami da rabata da qasa kaman yadda zaka rungumi yaro a haka suka
fita a toilet din.
Batasan
da gangan yayi ba?,oho.....amma gaba daya suka zube a gadon yana fadawa
samanta. Ya aje mata nauyinsa sosai har sai da numfashinta ya fara nauyi
"Oh....sorry" Ya furta yana dagata gami da bar
mata towel din a tare da ita. Rintse ido tayi tana qin dubansa,bai damu ba ya
jawo boxer dinsa dake yashe a gefe tun dazun ya saka,ya sanya hannu ya sauketa
zuwa sofa bed ya fara tattare comforter da bedsheets din harma da pillow case
din,don bayason anni ta sake dawowa idanunta su gani. Toilet ya koma ya shiga
sheqa musu ruwa,jikinsa yayi wani irin sanyi ganin yadda ruwan ke wanko jinin.
Da gaske ya shigeta ne da tabbaci da yaqinin ta riga ta saba......ya kuma samu
qofar a kulle gam....dole taji ciwo koma wanne iri akace masa taji. A yadda
yakejin cikakkiyar lafiya a jikinsa ya sani,koda bazawara ce yaje mata da irin
yanayin jiya lallai saita yabawa aya zaqinta ballantana ita din da take sabon
hannu.
Luggage
dinta ya bude,ya fidda mata kaya bayan ya saka wata sassauqar riga a jikinsa
over sized shirt da wandonta. Fara ce qal data dace da black trouser dinsa.
Sama sama yake jinsa shima,saidai abinda ke gabansa ya shafe komai.
Da rinannun
idanunta ta dubeshi sanda ya aje mata kayan,tana so ne ya matsa ya bata waje ta
shirya amma bataga alamun xai matsa din ba,hasalima tsaye yake a kanta ya zube
duka hannayensa a aljihun wandonsa kaman zai lasheta,ya zube mata nauyayan
idanunsan nan yana jin kamar ya buda qirjinsa ya fiddo mata mahaukaciyar
soyayyar data sakar masa.
"Ka fita zan shirya" Ta fada a taqaice ba tare
data kalleshi ba,hannayensa ya fidda daga aljihunsa ya juya a hankali ya fita.
Duk yadda
taso ta miqe sosai don ta shirya amma hakan ya gagareta,ba zata iya tsaiwa
normal kaman kowa ba,abinda ya sanya hawaye yaci gaba da zuba a idanunta,saita
dinga jin data sani ta barshi ya taimaka mata,amma kuma batason komai da zai
dinga hadata dashi. Da qyar ta lallaba ta saka underwears dinta ta maida
rigar,sannan ta lallaba hannun damanta ta kwanta tana ci gaba da fitar da ruwan
hawaye.
A nutse
anni ta murda qofar tana shigowa da sallama,wata kunya ta taso ta
lullubeta,saita rufe idanunta tamkar me bacci,tana fata annin taji kaman baccin
takeyi ta juya ta barta.
"Sannu....." Anni ta fada a hankali da alama ta
fahimci ba baccin takeyi ba.
"Zaki iya tashi?,doctor zata shigo ta dubaki". Kai
kawai ta gyadawa anni ba tare data iya furta komai ba,ta motsa a hankali tana
tunanin yadda zata tashi din. Matsawa annin tayi ta kamata a nutse tana cewa
"Yi a hankali" Tausayinta yana kama annin. Yanayin
yanayine bame dadi ba,iya yau kawai ta fahimci yaron nata yadda jikinsa ke
agine hakama komai nasa
"Allah ya baki ikon jurewa" Annin ta fada cikin
ranta. Sai a yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake kaucewa abubuwa da
dama,azumin litinin da alhamis akai akai,harma wani lokaci yakanyi azumin
annabi dawud,yau yayi gobe ya huta. Wani lokaci takance
"Ka dinga hutawa mana me babban suna......ga azumi ga
aiki,shi kansa aikin busy din da kake sakawa kanka pressure din tana
yawa". Sau tari murmushi kawai yakeyi ko ya kafa mata hujja da
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 78
78
"Ba
isashen time na tsayawa cin abincin,wani lokaci azumin yafi,idanma banyi ba
coffee ne sai ruwa sai fura ko yoghurt ". A yau ta fahimci ainihin
dalilinsa,saita dinga furta
" Alhamdulillah" Qasan zuciyarta. Da gaske Allah
ya tsare mata yaranta gabansu da bayansu kaman yadda take yawaita addua a dukka
salllolinta na nafila ko na farilla. Tayi imanin inda wani ne ya samu
cikakkiyar dama irinta fu'ad din,tarin dukiya kyau ilimi da suna da yayi a
duniya ba irin haramtattun ayyukan da bazai aikata ba,ta sani akwai dubban mata
dake a shirye su bada kansu ga irin wadannan mutanen,koda ba zasu samu komai ba
a wajensu daukaka ce ace yau suna tare dasu.
Sai data
zaunar da sabreen yadda zataji dadin zaman sannan ta juya a hankali tana fita
parlor din.
Minti daya
ta dawo tare da baquwar fuskar. Dr fadwa siririya fara tas,duba daya zaka
fahimci shekarunta duka duka ba zasu haura arba'in ba zuwa da biyu. Anni tana
gaba dauke da tea tray,Dr fadwa na biye da ita.
Qasa
sabreen tayi da qwayar idanunta,ba zata iya kallonsu ba dukka su biyun,har Dr
fadwa dake matsayin baquwa a idanunta. Ajiye tea tray din anni tayi tana duban
Dr fadwa. Kai Dr fadwa ta gyadawa anni,sai annin ta maida dubanta ga sabreen
"Ga likita na.....zata dubaki in sha Allah,ki saki
jikinki.....itama 'yar gida ce" Kai ta dagawa anni a hankali,tana jin
takun anni da fitarta a dakin,ta kuma ja qofar ta rufe musu.
Dubanta Dr
fadwa take tana kuma karantarta. Ko ba'a gaya mata ba ta fahimci ita din bame
saurin sakewa da mutane bace,ta miqa hannu a nutse ta kama hannunta ta sanya a
nata,abinda ya sanya sabreen daga kanta ta kalleta da risunannun idanunta. Da
sassauqan turanci take tambayarta da sakakkiyar murya.
"Kinci abinci?" Kai ta girgiza mata a hankali. Ba
zata iya tuna wani abincin kirki da taci ba,tun na dazun kafin su fita,ko acan
wajen cin kifi ma bata saki jiki taci komai ba,kasancewar ita ba ma'abociyar
cin abinci cikin jama'a bane. Kai tsaye Dr fadwa ta jawo tea tray din zuwa
saman cinyarta tana matsawa dab da sabreen
"Ki saki jiki kici abinci......sai na dubaki,kada ki
damu da yawa......hakan yana faruwa ga 'ya'ya mata da yawa,musamman da yake
yadda kowacce mace halittanta daban,haka kowanne namiji shima nashi halittan
daban......fashewar budurcin mace yana iya kawo fitar jini.....amma komai zai
zama daidai kinji?" Kai ta daga a hankali,ta kuma miqa hannu tana karbar
mug din da anni ta hada mata tea me dumi sosai da kauri.
Ita kanta
tasan ba komai a cikinta,ballantana kuma da abun ya faru sai taji kamar anyi
mata yasa,kamar an kwashe 'ya'yan hanjinta gaba daya,kamar iska tana turata
zuwa gaba.
Kadan
kadan take shan tea din,dr fadwa bata matsa wajen kallonta ko yi mata wata
tambaya ba ta daban,ta bata time sosai tana duba wayarta har taga ta ajiye.
Wayar ta bari ta daga kai tana kallonta,batasha da yawa ba amma saita qyaleta
don tasan lallai yanayin bame dadi bane.
Kauda
tray din tayi ta matso kusa da ita tana dubanta
"Sunana fadwa kefa?"
"Ameenatu" Ta furta idanunta suna dan lumshewa
"Sabreen sunan inkiya?" Kai ta gyada,saita fidda
takarda fara ta rubuta sunan akai.
"Eheennn......ina ne yake miki ciwo yanzu?" Shuru
tayi don tamabayar tayi mata nauyi da yawa,uwa uba ma gurare da yawa ciwon suke
mata,tun daga lips dinta......qirjinta....hatta da tafukan hannunta da suka sha
murxa zafi zafi takeji suna mata.
"Ki sake sosai kiyimin bayani,shi yasa madam ta fita ta
bamu guri......zai iya zama ciwo me zafi nan gaba idan baki bayani ba".
Hannu tasa ta nuna mata wajen ba tare data iya kallon idanun fadwa ba.
"Alright......zan duba wajen idan ba damuwa?" Ta
fadi da nufin neman izini. Dif tayi abun yana mata wani iri,shikenan ita kuma
jikinta ya zama wani budadden guri?
"Kiyi haquri....saboda lafiyarki,bazai dauki lokaci
ba" Ta fada da sigar lallashi. Kai ta gyada mata a sanyaye.
"Kin shirya?" Dr fadwa ta fada tana kallonta sanda
ta kwanta kamar yadda ta kwatanta mata. Kai ta gyada mata tana rufe idonta
saboda kunya.
A
hankali ta fara dubata cikin qwarewa da nutsuwa yadda ba zata fama mata ba.
"Oh my god.......subhanallah" Abinda ta fada kenan
tana maida mata doguwar rigarta.
"Kin masa gardama ko musu?" Dr fadwa ta fada tana
kallon fuskar sabreen din da tuntuni ta canza kala zuwa red. Tambayar sai ta
zama kaman ta bata license din sabon kuka,ita me zata ce mata?,batasan ma me
tayi ba.....musu ko taurin kan batasan wanne ne tayi a ciki ba,batasan wanne ne
ya faru ba.
"Irinsu sir.......ba kasafai za'ayi musu musu a irin
wannan lokacin a wanye lafiya qalau ba.....next time kada ki qara musu ko
gardama,mijinki yana da duk wani personality da kowacce 'ya mace zatayi
alfaharin samunsa a matsayin miji,.....kulawa da tattali yake buqata,ko don
gaba kada ki sake matse jikinki da hana masa kanki haka". Sanda take fadin
next time din ji take kaman ta ture Dr fadwa,itakam wacce irin sauna ce da zata
yarda taci gaba da zama da mutum irinsa?,wanda bisan ciwo ko darajar dan adam
ba?,balle ma har hakan taci gaba da faruwa wai a gaba?.
Daidai nan
anni ta tura qofar ta shigo,da murmushi take tambayar Dr fadwa
"Kin gama?" Kai ta girgiza tana dan murmushi itama
"Aah fa......madam yaronki aiki ya baro.....bleeding
din data dinga yi ta samu tier ne.....so dole sai an mata stitches..."
Idanu kadan anni ta fiddo,har jikinta tana jin wani iri. Lallai Allah kadai
yasan azabar da tasha tunda har an kai ga batun dinki.
"Gurin yayi ciwo sosai gaskiya.....harda bruises banda
tier din,dole a dinki wajen,inda first degree tier ne da sauqi....so amma
yanzun ma idan kina ganin a bari......"
"No.....a dinke Dr" Anni tayi saurin dakatar da Dr
fadwa din. A yadda taga yanayin fu'ad din da idanunshi ba yadda zata bari a bar
sabreen din a bude,tun sanda momma ta gaya mata marainiya ce takejin kamar kula
da sabreen din wani haqqi ne daya rataya a wuyanta.
"Kiyi haquri a dinke sabreen kinji?,wannan gurin shine
mutuncin duk wata d'iya mace a wajen mijinta.....akwai zafi amma zai wuce kaman
bai faru ba,wannan shi ake kira da cikakken mutunci mijinki ya zamana shi ya
karbi wannan abun ba wasu shashashai a waje ba.....nayi alfahari da
hakan......na kuma yi alfahari dake kaman yadda nasan yake a wajen
mijinki" Anni ta fada a tausashe hannunta saman kan sabreen da kunya ta
hanata koda motsawa bare ta bude idanunta.
Sake fita
anni tayi ta basu waje don sabreen din ta sake sosai. Dr fadwa kuma ta shirya
komai,ta kuma yi mata allurar da sai data zubda qwalla kafin a gama,batasan
azaban yana gaba ba sai da aka fara dinkin.
Neman
sakayya wajen Alla data dinga yi har batasan sau adadin nawa ta fadi ba,saidai
duka cikin ranta takeyi,bakinta baya iya furta komai sai ruwan hawaye dake fita
Dr fadwa na mata sannu.
Kasa
zama yayi a falon,sai kawai ya tura qofar dakinsu saddiq ya shige. Kwance yayi
kawai saman gadonsu,ya kasa tuna komai sai hankalinsa dake can dakin inda ya
barosu,yaji shigar dr fadwa da anni da fitowar annin duka,baisan me yake faruwa
ba don haka ya kasa samun nutsuwa. Gefe guda wani irin sarqaqiya ya shiga.
"KARUWA" Sunanta ma farko kenan daya fara zuwa
kunnensa,yaci gaba kuma da zuwa masa daga bakunan mabanbantan mutane. Kenan dukka wadannan bincike da shaidun duka
shaidan zur ne?,duka shaidan qarya ne?. Idan har hakan ya kasance kuma ganin da
yayi mata a hotel fa?,mashkur dake hannunsu a yanzu haka yana nemanta afujajan
da sunan wadda ta kwashe masa komai nasa?,ganinta da yayi fa tare da mika'il?,a
cikin kamfaninsa tana fitowa daga toilet dinsa?,binciken daya tabbatar kuma ita
ta kwashe kudaden asusun kamfaninsa fa?,wannan kuma mene?. Ta yaya zai
fahimta?,ta yaya zai gane?,waye zai warware masa?.
"Ka nutsu fu'ad.......diban kudi yasha banban da bada
mutunci.....don tana kwashe kudaden maza.....don kana ganinsu tare hakan ba
yana nufin tana basu kanya bane,kowanne matsayinsa daban,cakudasu waje daya
kuma shine zai sanya ka kasa banbance inda komai ya dosa" Wani sashe can
qarqashin lungun zuciyarsa ya gaya masa.
Sau uku yana
leqa parlor din ko zaiga ko yaji motsin anni ko wani abu da zai bashi haske
amma baiji ba. Kunyarsa da kawaicinsa duka suka qare,sai kawai ya buda qofar
dakin ya fito kai tsaye yana tunkarar dakin.
Itace ta
farko da idanunsa suka fada kanta bayan bude qofar da yayi. Ta wani sake fadawa
farat daya saboda masifar dinkin. Ko baka santa ba tsakanin a wannin nan idan
ka kalli fuskarta zakasan tayi kalar kukan da bata taba irinsa ba.
Idanunsa ya
maida kan Dr fadwa,likitan da sai da tazo ya tuna ya taba saninta a Egypt,ta
taba dubashi da yayi wani zazzabi,hankalinta kuma da nutsuwarta shine abinda ya
sanya ya bata daman bashi magani.
"Welcome sir" Ta fada cikin girmamawa. Kai ya
gyada yaja kujera yana zama hankalinshi a kanta. Daga kallon da yayi mata ta
fahimci qarin bayani yake nema. Dama kuma dole akwai buqatar masa qarin bayanin
don ta fahimci kaman yana cikin mazan nan marasa haquri akan abinda ya shafi
janibin auratayya.
"Mun kammala,anyi mata stitches.....but please sir,tana
buqatar hutu na koda 3to 4 weeks kafin a sake tabata,saboda a bawa dinkin daman
warkewa yadda ya kamata". Ido ya lumshe sannan ya bude yana jinjina kai.
"Mun gode....ta yaya zaa biyaki?".
"Madam ta biya sir.....Allah ya qara lafiya" Kai
ya jinjina yana girmama qaunarsu da anni. Tsantsar kulawa da qauna irin wadda
akasan uwa kadai take da wannan zuciyar. Komai idan ya kama qoqari takeyi tayi
musu shi ba tare data jira yin kowa ko cewar kowa ba.
Tatttare
kayanta tayi ta fice taja musu qofar.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 79
79
A hankali ya dauke dubansa daga kan qofar zuwa inda take
zaune. Idanunsa ya zuba mata yana jin akwai wani boyayyen abu ciki rayuwarta,wadanne irin masharrantan mutane ne
tattare da ita haka?,wadanda ba zasu iya fadin alkhairi a kanta ba?,wadanda ba
zasu iya suturta aibunta ba a sanda akazo bincike a kanta ba?. Idan bai manta
ba,ya samu tabbacin cikin wadanda suka bada shaida a kanta harda matar
babanta,sanda yake jaddadawa abdul haleem bayason fake bincike,baya son kuma
gurbataccen shaidu.
"Wacece a cikinsu?" Ya tambayi kansa da kansa yana
takawa gabanta,tausayi da wata irin mahaukaciyar qauna tata tana hudashi. A
yanzun yana jin a shirye yake da duk wani mutum da zai taba rayuwarta,a shirye
yake ya bada dukkan abinda ya mallaka a kanta.....in fact a yadda ta zame masa
mahadin numfashi a yanxun......ba dukiyarsa kadai ba.....hatta da rayuwarsa a
shirye yake ya bata ita. Yana jin ya shirya kame duk wani wanda ya bada shaidar
banza a kanta,ya shirya tuhumarsu ko su waye....komai yawansu.....komai kuma
kusancin dake tsakaninsu da ita.
A
jikinta takejin wanzuwarsa a wajen,wannan ya sanya ta sake zabar ci gaba da
rufe idanunta,har ya iso gefanta,ya zame kan gwiwoyinsa yana aza qarfinsa akai.
Hannusa ya miqa ya kamo tattausan tafin hannunta,ta motsa da sauri ta nufin
zamewa amma ya rigata,ya kamo hannun nata da daya hannun ya saka tsakiyar
hannayensa yana duban rufaffen idonta. Dukka kalamansa sun gama qwace
masa,komai ya auno sai yaji bai hau mizanin bada haquri ba....amma hakanan zaici
gaba da gwadawa don ya shirya karbar ko meye daga gareta hannu bibbiyu.
" Can you feel any pain or discomfort?" Ya
tambayeta kaman zai maida idanunshi cikin fuskarta. Shuru ne ya zame masa
amsa,bata ko motsa ba ballantana ta nuna tasan da ita yake. Sake matsa hannunta yayi kadan a tausashe,ya motsa
labbansa yace
"Sabrrrrr" Nan ma shuru ba wani motsi ko amsa.
Jawo hannun nata yayi kadan,ya kuma matso dashi ya dora tafin hannun nata saman
qirjinsa saitin zuciyarsa.
Tabbas har
cikin jininta taji bugun zuciyarsa.....kaman yadda dumin cikin hannunsa da
wanda taji cikin qirjinsa ya tabbatar mata da zazzafan zazzabin da yakeyi,amma
ko daya sai taji bataji tausayinsa ba.
"Im filled with regret for what i did,am truly
sorry......please kice wani abu man" Ya fadi cikin zaquwar ji daga
gareta,amma still ba wani canji. Shurunta sai yaji yana kasheshi har cikin
tsokar zuciyarsa,shirunta sai yaji yana masa wani irin ciwo......baya fatan ta
zama me hukunci da shuru wanda kusan halinsa kenan,ya kuma san ciwon hakan.
"Sabrrrr......I'll do everything to prevent it on the
future nayi alqaw....." Future din daya fada shi ya sanyata janye hannunta
sa wani irin sauri,saidai kuma kash zafin namansa ya qure nata,kafin ta samu
daman boye hannun ya sake kamoshi yana jin wani nisa da takeson haifarwa
tsakaninsu. Cikin yanayi na karaya ya sake aza tafin hannun nata saman
kuncinta,ya kuma dora kansa akai kaman wanda ya samu pillow
"My heart was beaten past sabrrrrr........zata iya
bugawa wallahi......please sabr say something mana......"
"Ka qyaleniiiiii....." Ta fada cikin daga murya
tare da wani irin sautin kuka wanda yayi daidai da shigowar anni. Tsaiwa tayi
cak tana dubansa,kaman zata koma sai kuma ta tuna da zancan Dr fadwa,don haka
ta qaraso cikin,amma ta dauke kai kaman bataga abinda ya faru ba. Idanunsa ya
aza kan annin,sai ya janye jikinsa daga wajen yana komawa inda dr fadwa ta
tashi wajen data ajiye documents din da tayi rubutu a ciki.
"Daughter" Ta kira sabreen a hankali wadda ke
qoqarin boye hawayenta da mode na fuskarta.
"Naam" Ta amsa tana murmushi
"Akwai ciwo ko ya ragu?,idan akwai tace tayi
prescribing wasu magunguna,ta tura ta pharmacy dinsu zaa karbo ko a kawo
miki".
" Akwai ragowa" Ta fadi tana jin yadda gurin ya
daddaure mata
"Zai daina in sha Allah" Maida kallonta tayi
kansa.
"Ka hada mata kayanta da duk zata buqata......zatayi
matsa zuwa dakina,zan kula da ita zuwa sanda ciwon zai warke" Anni ta fada
adan dake. Da mamaki ya kalli annin yana jin rashin dadi yana saukar masa,abun
sam bai masa ba,yana ganin kamar shi yafi cancanta a bari yayi jinyarta,yayin
da sabreen taji kamar an mata rahama,wani sanyi ya fara sauka saman
zuciyarta.....zata matsa daga kusa dashi......zata bada rata me yawan gaske
kuwa tsakaninsu,tana jin sai taso ma zata bari idanunsa ya hadu da nata,tabbas
da wannan damar zatayi amfani tayi nesa dashi,nisan da zai fara tun daga yanzu
har kuma abada
_uhmmm.....sabreen,anya me jadda zai bari kuwa?,to dai zami
gani_
Kaman
yadda ani ta buqata haka ya hada mata kayan,yana kallo anni ta kamata a hankali
har suka fice a dakin. Ba jimawa ta dawo ta dauki luggage din nata ta sake
fita,sai ya koma ya fada saman Kujera kaman wanda baida laka a jikinsa. Dakin
yake bi da kallo,sai yake ganin dakin ya masa wani mugun fili kaman an dauke
wani abu da yaci gurbi me yawa a dakin.
Hannunsa ya
kutsa cikin sumar kansa yana fidda numfashin daya qara zama me zafi saboda
zazzabin jikinsa. Wannan zaman bazai masa ba,yana jin kaman bazai iya kwana a
dakin shi daya ba,kaman ya masa girma,abinda bai taba ji ba kenan tunda yake
kwana a daki shi daya ba sai yau.
Wayarsa
ta dake gefe ce ta dauki ringing,kaman bazai daga ba amma ya daure ya miqa
hannu,anni ce,a sanyaye ya daga yana fatan ba wani abun bane da zai sake sanya
nisa tsakaninsa da sabreen din ba
"Ka nema magani kasha kaima jikinka akwai
zazzabi". Da qyar ya motsa labbansa yana fadin
"To" Ta katse wayar ya sauke shima yana jinjinawa
da kulawa tare da damuwa da lamarinsu irin na anni.
Hannu
ya dafa zai miqe ya aza hannunsa kan takardar da Dr fadwa ta rubuta,ya dauketa
zummar sauya mata waje,idanunsa suka sauka kan sunanta.
"Ameenatu Ahmad" Ya furta sunan a fili
"Is her real name ameenatu?" Ya tambayi kansa a
mamakance. Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi,wani abune da bai taba sani ba sai
yau
"Ya rahman" Ya furta a karye. Duk wata me suna
ameena darajarta daban yake a ranta,kima da mutuncinta ya zarta na sauran mata
a wajensa duka dalilin anni. Koda list aka kawo masa idanunsa ya sauka kan
sunan ameena yana fara tsinceta daban kafin kowa.
"Ameenatu" Ya maimaita sunan can qasan maqoshinsa
yana jin wani abu me matuqar qarfi yana kwaranya tare da jinin jikinsa zuwa
zuciyarsa da kowanne sashe na jikinsa. Qarfin abun yana jin kamar yafi qarfinsa
da gasken gaske bare ya tareshi.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 80
80
A daddafe ya
nemi magani yasha,har cikin ransa yake ji tabbas Allah yana sonshi,ubangiji na
qaunarsa......bai debe komai da kowa daga hannunsa ba......Allah ya dubeshi,ya
killace masa ita da wani irin tsaro da bai taba tunanin wanzuwarsa a tattare da
ita ba. Duk da ciwon kansa sai ya samu kansa da tashi ya wuce toilet,qarfe daya
saura na dare,ya daura alwala ya dawo ya shimfida abun salla ya kabbara salla.
Raka'a biyu rak yayi amma sun kasance masu tsaho sosai,kuka sosai yakeyi cikin
sujjadarsa cikin godewa Allah da kuma yaba karamci irin nasa. Ya sake imani da
karamcin ubangiji me girma da fadi ne,ya masa wani irin ba zata mara misali da
bai taba kawota ba.
Duk kusan
inda ya juya fadi dakin yake sakeyi masa,wani irin emptiness yakeji cikin dakin
qirjinsa dama zuciyarsa.....wata irin kewa da bai taba jin irinta akan kowacce
halitta ba sai a kanta,duk shudewar daqiqa daya tana dawo masa ne da yammacin
zaice ko darensu na daxu. Ya zuqi numfashi ya fesar yana jin kaman daren yayi
masa nisan da gari bazai waye ba ballantana ya sake ganinta. Bayajin baya ga
anni akwai wanda zai masa hakan......bazai lamunci wani ya rabasu koda kuwa na
qiftawan ido ne.
"Me yasa ban dauketa ba kafin anni takai ga yanke
wannan hukuncin?" Ya tambayi kansa yana jin ciwon nisan data masa.
Hannunsa yakai kan qirjinsa daidai inda faffadan qirjin nasa ya manne da nata a
dazu.
"Beautiful" Ya furta yana shafa labbansa bayan ya
tuna kyan gurin ga qayatarwarsa. A cike suke kuma a tsaye da wani irin shape me
jan hankali,ba wata alama data nuna hannu ya taba kawa wajen koda na kwanaki
qalilan ne. Wani numfashin ya sake fitarwa........ Yaji yana buqatar sanin duk
wani me mummunar shaida a kanta.....yanason sake tusa bincikensa.......yaji
yana shaawar bin kowanne diddigi na rayuwarta....koda bata gaya masa da kanta
ba dole zaiyi wannan aikin. Bayason kunnuwansa da zuciyarsa su dinga tuna masa
maganganun daya gaya mata
"Kyakkyawar Kalma sadaka ce" Ya tuna wani sahihin
hadisin ma'aiki akan furta kalma me kyau ga dan uwanka musulmi. Baisan me yasa
yake kasa controlling anger dinsa a kanta ba,baisan me yasa yake tsananin jin
zafin komai daya shafeta ba.....sai a yanzu daya soma tuhumar kansa da fadawa
soyayya a sanda baisan ita bace saboda mummunar shaidar da ya yiwa soyayyar.
Yaga mata kala kala da suka kawo kansu gareshi.....mata iri iri dake da wata
irin qazamtacciyar rayuwa,amma bai taba jin zafin rayuwar da suke ciki ba
saboda ya bawa kansa amsa da baya da issue dasu,bugu da qari ma su suka jefa
kansu suka zabi wannan rayuwar.
Daga daren
zuwa wayewar gari ya zame masa wani zamani daban me zaman kansa......kamar ba
tazarar awanni bane kawai a tsakaninsu. Yayi sallar asuba cikin daki ne karon
farko da zai iya tuna sanda hakan ya faru,ya kuma ci gaba da zama a wajen yana
hailala istigfari,salatin annabi kaman yadda ya saba,sannan ya zarce da karanta
wasu shafuka cikin qur'ani. Sanda ya rufe mas hafin qur'anin daga kan tab dinsa
da yayi karatun dashi gari ya soma haske. A irin wannan lokacin yakan fita gym
ne,amma a yanzu baya da wannan kuzarin da zai iya fita ko ina,fatansa kawai
gari ya qarasa haske yaji motsin su annin ya samu chance na ganinta.
Kansa
ya aje gefan gadon yana lumshe idanunsa,hannunsa saman kayanta da tun daren
daya zaresu ya watsar bai iya kwashesu ba. Yamutsasu yakeyi cikin tafin
hannunsa a hankali wani sabon feeling na sake shigarsa. Kowacce safiya sassanya
irin wannan yakanyi fama da irin wannan yanayin tun asali can dama......a
yanzun sai abun ya zama double,ya jawo vest din da bra din duka ya cusa a
hancinsa yana shaqar sassanyan qamshin nan daya dasa masa tarihi cikin rayuwarsa.
(Tsokaci:- Mostly maza suna samun feeling sosai daidai
wannan time din,saiki kula da buqatar mijinki,ko yaro gareki namiji koda qarami
wanda bai balaga ba daga lokacin zuwa wayewar gari ki lura da kyau,indai
tsiraicinsa yana dagawa a irin wannan lokacin to tabbas lafiyayye ne,idan kuma
kikaga akasin hakan to sai a fara nema masa magani).
Ba abind
qamshin ke sake masa sai qara tada zaune tsaye,kaman ya shide kayan cikin
hancinsa haka yakeji,ya tattarasu ya mannesu a qirjinsa yana qoqarin baiwa
kansa haquri.
Baisan
sanda wani irin bacci yayi awon gaba dashi ba,wanda ya cika da mafarkanta kala
kala,ko wanne waje suna tare cikin shauqattancen yanayi me tafiyar da
hankali,da wani irin yanayi mai tafiyar da hankali.
Koda ya farka
yanayin daya samu kansa a ciki ya sabbaba masa sake wani wankan ibadan,sannan
yayi gama garin wanka ya fito daure da towel yana duban a gogo. Baisan wanne
aiki yayi haka ba da har yunwa ke zaqalqalar cikinsa,saidai duk da yunwar da
yakeji ganinta yana jin yafi masa cin abincin muhimmanci.
A nutse ya
shirya cikin wasu pajama masu dogon hannu butter colors da aka yiwa adon gold
color din zare da mix din baqi dan kadan daga gaban rigar da tambarin kamfanin
Louise Vuitton. Fuskarsa tayi fresh sosai da wani irin sassanyan yanayi a
kanta. Yadda ya gyara sumarshi ya sake zama very calm guy,idanun nan dake da
wani irin sirri sun rissuna sosai,ya feshe jikinsa da sassanyan turarukansa
yana sake maida dubansa ga agogo.
Karfe sha
biyu harda wasu mintuna akai agogon qasar Maldives. Yayi mamakin tsahon lokacin
da yaci yana baccin,sai ya maida turaren ya zura flip flops masu taushi da suka
dace da adon gaban rigar. Idan ka kalleshi zaka dauka wani guri zai fita
ne,haka yake,yana da wani irin tsari da koda cikin gida yayi wanka zaka ganshi
neat very well dressed.
A nutse
ya murza qofan dakin yana fita parlor din,ba kowa a ciki bama motsin kowa,sai
ya taka zuwa saitin dakin anni yana duban dakinsu farouq dake alamta masa har
yanzu basu dawo ba.
A nutse
yayi knocking,yayi tsai yana irga adadin gudun zuciyarsa tare da raya abubuwa
da yawa da zasu iya faruwa cikin dakin.
"Shigo mana" Anni dake fitowa daga toilet ta fada.
Koda bataji
muryarsa ba ta tabbatar shine yake knocking qofar,abinda ya sanyata gyara
zamanta sosai saman wani tattausan carpet dan madadaici da anni ta shimfida
mata ta zauna a kai.
Boubou
gown ne a jikinta mai taushi ta asalin 'yar qasar Egypt wadda tafe da
mayafinta. Milk color ne da adon lime green a jiki daya sake qawata yadin
rigar. Gashinta na tattare waje guda ta kuma daureshi da sassauqan dauri da
bazai dameta ba. Fuskarta tayi wani irin fayau ta kuma qara haske da
glowing,duk da kana ganinta zakasan cewa ba komai saman fatarta tata,ko man
arziqi bata shafa ba. Kwana da annin zata iya kiransa wani abu dake cike da
baiwa da kulawa,tayi wani bacci da bata taba tunanin zata yishi ba saboda
dinkin dake a jikinta. Ta dauka radadin ciwin shi zai fara tagayyarata,ya kuma
hana mata baccinta,sai gashi ta samu wani irin bacci hankali kwance cikin
kulawar annin da ko yaya ta motsa itama sai ta motsa,idanunta da hankalinta duka
yana a kanta.
Umdatul ahkam
ne saman cinyarta take duba karatun baya da sukayi da rumasa'u. Annin ta lura
bata da waya ko wani abu da zai debe mata kewa,a lokacin Umdatul ahkam din yana
hannun annin,taga sabreen din tana yawan kallon littafin,don haka ta tambayeta.
"Ko zaki karanta?" Kai ta dagawa annin a
kunyace,tun jiya ta gaza cire kunyar nan da annin tace mata ta cireta,ita ba
suruka take a wajenta ba,ita din uwa ce amma ta kasa. Hatta da bubu din jikinta
yanzu haka ta annin ce
"Ki amfani da wadannan,saikinfi sakewa yadda dinkin
za'a samu ya warke da wuri" Anni tace da ita.
Itace
abu na farko da idanunsa suka fara sauka akai. Ya janye dubansa daga kan
fuskarta zuwa ga littafin hannunta,haka kawai yaji wani sanyi yana ratsa
zuciyarsa,ya motsa labbansa yana yin sallama cike da fatan zata daga kanta ta
kalleshi koda ba zata amsa ba,amma maimakon hakan sai anni ta amsa mata tana
turr hijabinta data cire kafin shigarta bandakin ta zauna gefan gadon tana nuna
masa stool din dressing mirror din gami da karantar yadda dukka hankalinsa yake
a kanta tamkar zai wuce gabanta kai tsaye. Ta godewa Alla daya bata basirar
dauketa daga dakin.... A matsayinta na babba abinda take gani cikin idanunsa
muddin ta barshi da ita tasan dinki koda guda nawa za'ayi mata warkewarsa saita
Allah.
Zama yayi
saman stool din yana qoqarin maida mode dinsa daidai da yadda ya saba yiwa
annin,duk da wata irin kunya dake rugowa da gudu tana dabaibayeshi,ya kasa
kallon tsakiyar idanunta yadda ya saba.
"Barka da safiya anni.....ina kwana?" Ya furta
yana rusunawa duk da a zaune yake.
"Barka kade......an tashi lpy?" Sassalkar sumarsa
ha shafa da tafin hannunsa yana satar kallon sabreen ta qasan hannun nasa.
Wannan tambayar ta anni sai yakejin kamar gatse yake masa amma ya amsa da
"Lafiya alhamdulillah......yame jikin?" Ya hada
kunyars waje daya yana nufin kaita qasa da kuma son janyo hankalin sabreen da
ko motsawa batayi ba ballantana ta nuna tasan yana wajen.
"Alhamdulillah" Anni ta amsa masa a taqaice,don
ita kanta tuna abun kawai yana sakata cikin wata irin kunya.
Idanu anni
ta maida kanta,zuwa yanzu ko ita yarinya ce ta gama fahimtar wanne irin zama
sukeyi,saidai tambaya daya data kasa samun amsarta.....ta yaya ta zama zabinsa
bayan baya so?.
"Sabreen" Anni ta kirata,kiran daya sanya ta daga
kai zuwa ga annin ba tare data kalli sashensa ba. Wani iri yaji.....shi yake da
muradin ta fara kalla,shi takeso ta dinga fara kalla kowacce safiya idan yana
da ikon hakan.
"Mijinki ya shigo". Lumshe idonsa yayi yana jin
dadin kalmar da yadda ani ta fadeta da wani irin taukidi
"Kul.....ba kyau a wajen mace taqi gaida
miji......Allah bazaiyi farinciki da hakan ba" Anni ta fada tana jin wani
abu yana taba ranta a kansu duka su biyun
"Ya Allah ka taqaita musu jarrabawarsu......kada ka
sanya soyayya ta zama wata sabuwar jarrabawa a garesu".
"In sha Allah anni" Ta fada tana dan jin nauyin
abinda tayin,bawai a kansa ba.....a'ah akan anni ne. Tsam annin ta miqe tana
cewa.
"Bari na duba matar can ko ta dora abincin rana?".
Saita nufi qofa a hankali tana ficewa daga dakin harda jan qofar.
Wani dadi ya
dinga ratsashi da anni ta basu wannan space din,sai kawai ya harde hannayensa
duka biyun saman qirjinsa yana qare mata kallo.
Wani irin
kallo ne da yasha banban d kowanne irin kallo,wani irin kallo dake cike da
shauqi da matsananciyar soyayyar da yakeji kaman tafi qarfin wannan faffadan
qirjin nasa dama tsokar zuciyar dake lullube a ciki. Wani kalan so da yafi
qarfin a hada sunan son shauqi dama qauna duka a dunqule waje guda,baima san
sunan da zai bata ba. Yana ganin yadda ta maida dubanta kan hadith din tana
buda shafin gaba,alamun ta gama da shafin baya kenan. Boyayyen murmushi ya saki
wanda ya tabbatar ba zata gani ba,tayi masa wani irin mugun kyau tamkar furen
fulawa. Lips dinta ya kalla da kyau,ta sake tsuke dan qaramin bakinnan nata
waje daya,da gani kai basai an gaya maka ba akwai fushi kwance cikin zuciyar
'yammatan nasa.
"Zansha tsiwa.....zansha rashin kunya,amma duka ina
maraba dasu,akwai kebantacce kuma killataccen gurin da aka tanada saboda
su" Ya gayawa kansa da kansa yana jin shauqinsa yana qaruwa a iya kallonta
kawai kafin yaji kallon ya daina gamsar dashi,duminta kawai yake da muradin
ji,duk da zuciyarsa tana gargadarsa da cewa kuskure ne aikata hakan,musamman a
mode din da take ciki,uwa uba kuma cikin dakin anni?. Saidai kuma magnet din
dake jansa yafi qarfinsa,bazai iya controlling kansa ba. Tsam ya miqe ya sauka
daga saman stool din,ya zube hannayensa a aljihun wandonsa,ya motsa labbansa a
nutse.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 81
_An tambayi nana Aisha R.A,menene dabi'un manzan Allah S A
W,sai tace: dabi'unsa alqur'ani ne(ma'ana yadda qur'ani ke koyarwa da fadin
kalolin kyawawan dabi'u dukka haka halayen fiyayyen halitta S A W yake)_
81
"Sabrrrrr" Ya kirata da sautin nan dake ratsa kunnuwanta ya
aike da wani saqo me sauri zuwa kwanyarta. Ko motsawa batayi ba bare ya kula da
taji kiran ko bata ji ba,sai ya sauya shawara shima,ya cire hannunsa daga
aljihun wandonsa ya fara takawa inda take zaune.
Sarai
taji takowarsa,amma sai takejin bata da wani sauran abinda zataji tsoro tattare
dashi. Batasan gaibu ta gayawa kanta ba sai da taji hucin numfashinsa dab da
fuskarta,kafin ta daga kai ya sanya hannu ya zare littafin ya sanyashi a
gefanta,ya kuma maida gurbinsa da kansa. Yayi kwanciyar rigingine ne,fuskarsa
na kallon sama tana kuma kallon fuskarta,ya hade hannayensa a qirji kaman me
sallah,ya tsurawa qirjinta ido daya fuskanci zuciyarta ce take bugawa shi yasa
ya fara dagawa sama da qasa kadan kadan.
Boyayyen
murmushi ya saki.....tana da raunanniyar zuciya me cike da tsoro,saidai,kuma
fushinta taurin kanta da kafiyarta kaman suna so su rinjayeta.
A
tsorace take ainun da yadda ya kankane mata cinta,bata so kuma tayi masa magana
sam sam,tana jin bai cancanci kalaman bakinta ba. Haduwar jikinsa da nata sai
ya tuna mata da wanzuwar fareeda data gani yammacin jiya cikin jikinsa,abinda
ya hadu da fushinta ya sake zafafan zuciyarta kenan ta tattara lausasan tafukan
hannayenta zata ture kansa daga cinyarta. Hannuwansa ya saka ya riqesu yana
kallon tsakanin haskensu da taushinsu da tun a idanu ma suka nuna hakan.
"Kin cewa anni zaki dinga gaisheni....kuma tamkar
alqawari ne,bayan ta fita kuma kin karya alqawarin da ko minti uku bai cika
ba.....na taso da kaina don nazo na gaidaki sai kuma ki koreni?,kinyimin adalci
kenan?". Idanunta ta zuba masa a zafafe kalmar adalcin daya fada tana bata
haushi. Shikam har yayi maganan adalci idan akazo batu a kansa?.
Batajin
zata bari yaji koda kalma guda a bakinta,don haka ta gwammace hadiye
takaicinta,ta maida kanta gefe bata furta komai ba tana qoqarin zame kansa daga
cinyarta. Ganin haka sai ya juya da zafin nama ya koma rub da ciki,still kanshi
yana kan cinyarta. A wannan karon ma sai ya qaro da sanya hannayensa ya zagayo
bayanta dasu ya mata zobe kanan ya sakata a Tsakanin hannayensa.
"Good morning my sweetest women..........ina fatan kin
tashi lafiya?" Ta fada yana sauke wani irin ajiyar zuciya gami da lumshe
Idanunsa yana mamakin yadda take saka zuciyarsa bugawa haka.
Duk da
baya dubanta haka ta zubewa qeyarsa me kwantacciyar suma idanu,tana jin gaba
daya ya zame mata qarfen qafa. Duk wani motsi da zatayi don qwatar kanta sake
qanqameta yakeyi sosai,hatta da tafukan hannayenta ya mannesu cikin nasa,ya
saki ajiyar zuciya sannan yace
"Ina fatan kowanne ciwo da kika ji ya zame miki silar
samun rahamar ubangijinki.......na gode......na gode.....na gode sau babu adadi
da killacemin kanki da kikayi......na gode da kika qaryatamin zancan mutane a
kanki.....kika kuma bani tabbacin da bandashia baya" Kaman susa bisa
ciwonta haka maganganunsa suka zame mata,ta qwace hannun nata da qarfin zuciya
irin nata tana ture kansa,amma sai ya sake rungume hips dinta sosai kaman zai
maida kansa cikinta.
"Duk yadda zakiyi qoqarin korata daga rayuwarki wannan
din mafarki ne......bazan iya ba......bazan iya barinki ba koda na second guda
ne,indai zan iya rayuwa babu ruhi ko numfashi......tabbas zan iya rayuwa babu
ke.....ke din ruhina ce.....numfashi na ce.....kuma jinin jikina,a cikinsu
wanne ne idan babu rayuwa zata tabbata da cikakkiyar ma'anarta?"
"Ya isa......ka dagani" Ta fada adan tsaurare
saboda wani irin nishi da sauti da yake sakar mata daya sanya ta fara daina
gane komai,wata irin tafiyar tsutsa yakewa tafukan hannayenta da take jinta har
cikin qasusuwa da bargonta.
"Ka daga ni ko na maka ihu na kira
anni......." Murmushi ya sakar mata
hankalinsa kwance ba tare daya motsa ko ya fasa abinda yakeyi ba
"Ki taimakeni ki kiramin ita......wataqila zata tayani
gaya miki irin matsayin da me jadda ya baki.....ita din uwace dake fuskantar
kowanne yare da 'ya'yanta zasuyi magana dashi". Da gaske yake mata,bataga
wani alama ko kadan a tattare dashi na razani ko tsoro ba,saima sake gyara
zamansa da yakeyi saman cinyoyinta kamar ya samu wata DUNIYARSA a wajen.
"Zan sake maimaita miki.....zanta baki haquri.....zanta
baki damar horani har zuwa sanda zaki huce........amma karkiyi zaton akwai wani
kalar bore da zakiyi da zai sanya na haqura dake.....kece rayuwata.....banajin
bugun numfashi na yana fita da sunan kowacce mace a duniya sai ke" Ya
qarasa fadin maganan yana sake qanqameta.
"Wayyo dinki na" Ta fada da qarfi,abinda ya
sanyashi miqewa a gigice a kuma razane yana riqeta da kyau.
Ya bude
baki zaice wani abu ta sanya duka hannuwanta ta tunkudeshi sai gashi ya tafi da
baya ya fadi. Ba wani abu da taji na zafi ko ya samu dinkin nata,tayi hakanne
dama kawai don ya saketa.
Baiyi wani
qoqarin tashi ba saima sake bajewa da yayi yana sakar mata murmushi
"Next time ba zaki nasara ba" Daidai nan anni ta
turo qofar a gaggauce saboda sautinta kaman da taji. Shigowar anni ya sakashi
miqewa da sauri,yana dan kade jikinsa a kunyace. Yadda anni ta zuba masa idanu
yasan tuhumarsa takeyi ba tare data jefa masa kalmar tambaya akan tuhumar tasa
ba. Ta janye Idanunta ta mayar kan sabreen
"Lafiya?" Tambayar ta yiwa sabreen nauyi,batasan
me zatace mata ba,sai tayi qasa da kanta ta kasa amsa mata.
"Zaka iya tafiya abinka,amma kasan ba'a takurawa mara
lafiya right?" Tuni ya Fahimci me anni ke nufi,sai kawai ya gyara hannun
rigarsa yana fadin
"Afwan" Ya juya yana fita a hankali bayan ya saci
kallon sabreen din data kasa cikakken motsi.
Gabanta
anni ta qaraso a hankali,taja stool din daya tashi akai ta zauna tana dubanta.
"Sabreen" Ta kirata a tausashe. Da qyar ta motsa
labbanta tana amsawa sa
"Na'am" Tana lanqwasa yatsunta,ta tabbatar idanun
anni sunkai kan littafin da fu'ad ya aje a gefanta,wanda duk wanda ya kalla
zaice ita ta aje din don yafi kusa da ita.
"Ki lallaba jikinki ki warke yadda ya kamata,kada ki
yarda kiyi sakacin da dadin bakinsa zai sanya ki bashi dama ya lalata abinda ke
jikinki.....dukkaninsu 'ya'yana ne....kuma nasan halin kowa......shi namiji da
kike gani dukkaninsu halinsu daya,abu kadanne ya banbanta wannan da
wancan" Anni tayi maganar kanta tsaye.
Tsoro da
kunya suka cakudu suka sanya hawaye taruwa idanunta,kunyar kada anni ta dauka
wani abun suka aikatawa,ko ta bashi daman yin wani abu da ita. Muryarta yana
raurau,idañunta cike da hawaye ta daga kai tana duban gefan annin.
"Wallahi Allah anni ni ban......"
"Shshssh.....bance kiyi rantsuwa ba sabreen,kome meye
ya faru babu haramci a ciki,mijinki ne halal din juna kuke......amma nasan
halin maza sarai.....akan wannan wajen komai ma zasu iyayi.....kusan a nan aka
sanya hankalinsu,a nan ne kuma ke kike da power din iya sarrafasu yadda
kikeso.... Dole ki bashi kulawa ta musamman,don ke nan ne naki mulkin
yake......a yanayin da kike ciki dinnan kuma ba wani abu bane don ya miki dadin
baki ya karba,tsaf kika bashin amshewa zaiyi.....amma sabuwar wahala kuma
takice". Gaba daya kunya ta sakata saka hannunta ta rufe fuskarta tana
sakin kuka,ya cuceta ya sakata jin nauyin anni,ya sanya anni tana tunanin wani
abu a kanta
"Wallahi Allah anni......ni ba komai da......"
"Kul....ni ban tambaya ba,namiki bayanin da zai
amfaneki ne,nace kuma ki kula,bance ki fadamin sirrinku ba,maza oya......goge
hawayen" Anni ta fada tana tashi zuwa gaban dressing table,ta kuma jawo
wata locker dake jiki ta ciro wasu kwalaye guda biyu ta dawo wajen sabreen din
wanda ta sanya gefan mayafinta tana share hawayen daya zubo mata. Ba zata sake
yarda ko fuskarta ya gani ba bare yasa anni ta zargeta,idan shi baida kunya ita
akwai kunya a jininta.
"Daga gobe wannan sabun dashi zaki dinga amfani wajen
tsarki,idan kikayi sati daya akwai saqon da zai iso zan baki ki amfani dasu,zan
miki bayani suma idan sun iso".
" Na gode" Ta fada tana jin kunya tana dawainiya
da ita,amma sai ta lura ita anni ko a jikinta,tamkar yadda uwa zatayi magana da
'yartane wadda shaquwa da fahimtar juna yayi nisa a tsakaninsu.
Kyakkyawar
farfajiyar gidan ya fita yana tasbihi qasan ransa,ranshi fes da wani irin
farinciki da yaji yana samun mazauni a zuciyarsa. Tabbas ya sake yarda...kudi
ko wadata ko wani jin dadi na rayuwa bata taba cika saida macen aure.....cikar
kamalar namiji itace aure ya yarda da wannan. A tsakanin jiya da yau,duk da
birkitaccen yanayin da komai yazo masa sai yake jinsa a wani cikakken mutum me
cikar kamala da mutuntaka,duk wani nauyi dake kowanne gaba na jikinsa kaman an
sanya ruwa an wanke masa. Kwanyarsa a yanzu a cike yake da tunanin yadda zai
gina kyakkyawar rayuwar auratayya ne kawai,gidan dake cike da soyayya da kuma
qaunar juna.....irin qaunar da zata maida gidansu tamkar dausayin aljanna ta
duniya. Bai damu ko kadan da dukka wadannan boren nata ba,yayi imani na wani
dan lokaci qanqani ne,kuma zata yishi ta gama......komai zai daidaita. Yayi
alqawarin dimautata da zazzaqar soyayyar da zata mance kanta gaba daya,ko
tanaso ko bataso,ko ta yarda ko kada ta yarda......zai nuna mata qarfin qwajin
zuciya da nasa salon na sace zuciyar d'iya mace,a banza ma yake aikata hakan ba
tare da yasan yaushe hakan yake faruwa ba?,ballantansa wannan me license?.
Zamanshi
kenan cab ya tsaya a qofar gidan nasu.ba wani me maida hankali bane shi kan
abubuwan da basu shafeshi ba,don haka ya maida kansa ga wayarsa yana duba sunan
da yayi saving number CP s.nuhu. a yanzun yana jin wani qaimi da wani irin
priority a kansa na tunkarar dukka badaqalar daya baro a Nigeria. Indai har ya
sameta a cikakkiyar mace budurwa wadda mutuncinta bai samu koda rawa ba balle
tasgaro to tabbas dukka mutanen can akwai daga inda suka bullo,akwai kuma
mabanbantan dalilai da suka shigo da ita rayuwarta. Me suke buqata?,wanne
dalilai ke garesu?.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 82
_Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin
ayyuka da kuma tarin lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar
dashi,ga tarin mutane da baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman
haqqinsu ne a kansu a wajen Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya
zalunci wannan,ana biyansu da haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai
cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa sun qare za'a koma ana diban zunubin
mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana lafta masa,daga qarshe sai ya tashi
baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi umarni wa mala'iku su jefashi a
wuta( Allah ka tsaremu🙏🏽)_
_bukhair da muslim_
82
Tun yana
daga cikin motar idanunsa suka sauka akan fuskar fu'ad din. Wani irin murmushi
da ya fito tun daga qasar zuciyarsa ya wanzu a fuskarsa. Tabbas aure rahama ne
kaman yadda mata suke rahama ga rayuwar wanda ya dace dasu. Daga inda yake yana
iya hangen wani annuri na musamman na fita daga miskilar fuskar nan da ba'a
lamunce mata murmushi ba a kowanne lokaci sai lokaci lokaci idan shi da kansa
kuma yaso hakan,amma a yau yana ganin wani sakewa akan fuskar daya tabbatar
koshi me fuskar ba lalllai yasan da ita ba.
"That's my bro muhammad fu'ad jadda" Ya fada qasan
ransa yana taya fu'ad murna gami da kama murfin motar ya fito. Ci gaba yayi da
kallonsa ba tare dashi ya sani ba,idan har za'a tambayeshi mutum na farko dake
bashi mamaki a duniyarsa fuad dinne.......mutum na farko da rayuwarsa tamkar
madubi ce a wajensa.....mutum na farko da tausayinsa bai taba raguwa a ransa ba
fuad dinne. Yana da sauqi kayi masa mummunar fassara idan bakasan halinsa
ba,bakasan wanene shi ba,amma kuma kuna wuce wannan level din dashi zaka
fahimci mutane irinsa a duniya qalilanne.
"Ka kama kanka farouq.....banda tsokana da yawa,kafi
kowa sanin wayeshi" Ya gayawa kansa da kansa saboda yadda yakejin wata
dariya nason fara taso masa tun bai qarasa wajen da fu'ad din yake ba
"Ka wuceshi kawai kaman baka ganshi ba indai kasan ba
zaka iya riqe dariyarka ba" Wani sashen na zuciyarsa ya bashi shawara don
da gaske dariyar nan bayajin zata riqu. Yafi yarda da shawarar zuciyarsa ta
biyu,don haka ya zaro wayarsa yahau kiran fannah ba tare daya shirya ba,a
sannan harsu amna sun wuce cikin gidan.
Baisan
adadin sau nawa murmushi ya kubcewa fuskarsa ba. Duk da waya ce a hannunsa amma
ba abinda yake gilmawa idanunsa sai ita din. A wannin da suka shude masa sunyi
masa wani irin tasiri da har ya mutu ba zasu taba goge masa ba. Wasu irin
mintuna na musamman da suka fara cikin fushi suka kuma qare da wani abu me
matuqar ban mamaki da bai taba kawoshi ba a ransa.
Bai
lura da saqon ba don haka cikin sauqi hannunsa ya danna saqon ba tare da ya
shirya ba
*_Kada ka taba tunanin zaka subucemin.....kada ka taba
tunanin zaka kubcemin........a shirye nake nayi komai don na mallakeka.....ciki
kuwa harda taba alaqar dake tsakaninka da KARUWAR da kake kira matar aure a
gareka,fareeda khaleed mustapha_
Wani irin
kallo yakewa saqon yana sake karantashi daga farkonsa zuwa qarshensa,
"Karuwa?" Ya maimaita sunan da wani irin yanayi da
yakejin kaman ana yankar naman zuciyarsa.
"Fareeda?" Ya sake maimaita nata sunan yana jin
wani irin fushi yana taso masa. Fareeda da ire irenta baya jin zai dagawa
waninsu qafa da kalmar KARUWA ta fita a bakinsa muddin suna nufin kalmar ne
akan SABREEN. Zaiyi shari'a da kowa a kanta......zai kuma tsaya mata akan duk
wanda ya jefeta da wannan kalmar. Har ya fara laluben number fareeda din kai
tsaye Muryarshi kawai yaji ya daga kai yana kallonsa. Farouq ne,shi kuwa da
gasken gaske wai bai ganshi ba,ya daga hanci sama yana amsa wayar kanshi a sama
yana duban qofar gidan.
Ganinsa
kawai sai yaji fushinsa ya soma sassauta,dan uwa kuma abokin kuka tun daha
quruciyarsa har kwanan gobe bai fasa ba. Tsaf ya gama karantar farouq din,sanin
da yayi masa sani ne ba na yau ko na jiya ba,ya gama karantar abinda ya
shirya,don haka har ya gotashi ya sanya hannu ya fincikoshi baya gami da zaunar
dashi a gefansa.
"Zauna kayi dariyarka yadda kakeso" Ya fada yana
shan mur gami da dage girarsa dukka biyun sama tare da qoqarin danne abinda ya
taso masa game da saqon fareeda. Maganar fu'ad din sai ta zama kaman tsokana ga
farouq din,take kuwa kowacce dariya dake cinsa ta fashe,ya soma
qyaqyatata,harda sauka daga kan concrete chair din ya zame yayi Zaman dirshan
cikin grass carpet din yana dariyarsa abunsa.
"Kayi me isarka,don wallahi muka shiga ciki kayimin a
gaban yaran nan saina faffasa maka baki" Ya sake fada yana hade ranshi
"Aah...me yayi zafi?,bani na kar zomon bafa,wallahi ko
ratayar ma ba'a bani ba" Ya fadi yana qoqarin danne dariyarsa. Wani kallo
ya watsawa farouq din yanata qoqarin maintaining girmansa.
"Farouq?"
"Allah ya taimakeka" Farouq ya fada yana daga masa
hannu da shigen gaisuwar sarakai
"Kada ka batamin mode dina" Ya fada yana ware masa
idanunsa duka a kansa.
"Ango ai baka laifi koka kashe dan masu
gida......girmanka ne,Allah ya taimakeka tuba nake....." Naushi ya kawo
masa Allah ya rufa masa asiri ya kauce ya samu iska,farouq din ya sake komawa
da baya yana sassauta dariyar tasa,don magana yakeso suyi me muhimmanci.
★ *FAREEDA*
Da qyar ta
tattara kanta tana laluben hanyar fita daga dakin. Tunda take a rayuwarta bata
taba jin ta muzanta irin na wannan ranar ba,don ko data koma daki kasa hada
idanu tayi da lubna qawarta.
"Ke da zaki bude wuta kuyi spending night din gaba daya
kya dawo haka da wuri?" Ta tsareta da tambaya sanda ta hautsina kayanta
tana laluben inda take ajiye kayan mayenta ko zata samu wani abu da zai dauke
mata baqincikin da takeji. Bata samu komai ba,abinda ya sake hautsinata
kenan,ta kama gashin kanta ya damqe da qarfi sannan ta sake tana dakawa lubna
tsawa
"Get out of my sight.....idiot" Tabe baki lubna
tayi tana matsawa gefe. Ta sani indai muhammad jadda ne ta qwallafa rai a kansa
yanzun ma ta fara wahala da sonshi,bata taba jin wadda a tarihi ta taba samun
koda alamu alamun nasara ba a kansa. Da qyar ta iya hada abinda ya bugar da ita
ta zube tana bacci ruhinta cike da cin alwashin cikin mutuncin maamah idan ta
farka,tare da shaida mata ta dawo mata da kudadenta da dukka taci muddin ba
zata iya mallaka mata d'anta ba. Ta dauka duniya ba wadda take da iko dashi
sama da ita....ta kuma dauka mallaka mata shi shine abu mafi sauqi da zata
iyayi mata.
*MAAMAH*
Tun saukarta
a qasar ba zata ce ga wata cikikakkiyar ibada data iya samu ta aiwatar ba,dukka
hankalinta da tunaninta yana a kansu. Me dame yake kashewa ameenatu?,me dame
sabreen ki shiryawa a kanshi?,ta bayyana masa sirrinta ne kaman yadda taci
alwashi ko.kuwa?. Babban a binda yafi damunta da tsaya mata a rai batun
fareeda,gashi har yau din ba taji komai daga gareta ba,bata kirata ba ita kuma
bata da number wayarta bare ta fara nemanta.
Abu daya ta sani shine.......tabbas.....kofa zatayi yawo tsirarara.....koda
malami ko babu.....koda boka ko babu saita nunawa SABREEN DA AMEENATU girman
isarta akan danta. Idan har bata sanya fu'ad ya auri fareeda ba ba shakka ita
din ba diyas halas bace.
Bayan
sallar la'asar kawai saita kasa sukuni,tsakanin jiya da yau kawai saita dinga
jin kaman wani abu zai faru ko ya faru,wannan ya sanya ta lalubi number wayarsa
ta soma kiransa cikin jin isar mallakinta ne shi ya kamata ya zamanto sai yadda
tace ko ta lamunce sannan ayi.
Qarar wayar
fu'ad din ta sanya hankalinsa ya koma kan wayar daga kan farouq da ya fahimci
iya shege kawai yakeson samun dam yayi masa......baisan yadda zuciyarsa ta
tumbatsa da wani irin yanayi akan yarinyar ba?. Komai bai dameshi ba irin yadda
zai maidata mallakinsa fiye da yadda ya maidata a yanzun......yanaso ita kanta
a jikinta ta sallama cewa ita din mallakarsa ce har abada,sai ya kalli farouq
ya daga masa yatsa alamun zai amsa wayar. Kai ya jinjina masa,saidai kafin
yakai ga dagawar wayar ta yanke. Qoqarin lalubota yakeyi ya kira sai tex ya
fado masa
_"Duk wanda kayi gangancin kamawa ko hukuntawa cikin
mutanenmu dake hannunka.......ba shakka labarin matarka zai zama labari na
farko da zai zama fitaccen labari kowacce safiya saman jaridun qasar mu da
qasashen dake huldar kasuwanci dakai,suke kuma ganin kima da daraja a tare da
kai_
Wani irin
fusgar hankalinsa saqon yayi,saidai kuma kafin ya sarrafa kwanyarsa ya fahimci
komai kiran maamah ya danne saqon,dole ya kauda abinda ke taso masa ya daga
kiran yana sawa a kunnensa,bakinsa dauke da addu'ar
"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa'anta
taj'alal hazna iza shi'ita sahla". cike da fatan ba wani abu bane na daban
zata baro dashi ba bayan abubuwan dake dabaibaye dashi ba.
*_Da sauran masu bibiye da rayuwarsa kenan_*
*_Ya zafafa da gaske wajen yin campaign na samun soyayyar
ta,xaiyi nasara ko kuma zata zille masa?_*
*_shin fareeda zatayi nasara ta hannun maamah kuwa?,kaman
yadda tayi nasarar sanyashi auren sabreen a wancan lokacin?_*
*_munata gangarowa da MAFARIN warwarar kowanne qulli da
tonuwar binnannun asirai_*
*_sai ince muje zuwa dai_*
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 83
_An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane
ukun da baxasu shiga aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_
_"WANDA YAKE ZINA TUN YANA YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_
_2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_
_Bukhari da muslim_
83
Cikin
cikikakkiyar nutsuwarsa yayi sallama,zuciyarsa bata fasa neman dauki da ambaton
sunan Allah ba.
"Wa'alaikumussalam" Ta amsa masa a dake,tanaso ya
fahimci cewa lallai shi din me laifi ne a wajenta.....wannan fahimtar tata da
zaiyi ya zama sila kuma jagora zuwa ga wanzuwa da amsar babban burinta a yanxu
na auren fareeda.
A nutse ya
fara gaidata,ta amsa masa a dake kaman dazun. Shuru ya ratsa na wasu sakanni
kafin tace.
"Baku hadu da fareeda bane?" Mamaki kadan ya
kamashi,mamakin yadda akayi maamah din tasan da zuwan fareeda Maldives.
"Mun hadu" Ya amsa mata kai tsaye,kasancewar mutum
ne shi da wahala ko tsanani basa sakashi yayi qarya.
"Amma me ya hanaka zama me masaukinta?......tunda kana
da tabbacin ba don kowa tazo ba sai don kai". Mamaki ya sake kamashi,ya
lumshe idanunsa yana jin takaicinsa yana sake daduwa. Gaba daya maamah din
kowacce rana sake jirkita takeyi tamkar wahainiya,wasu abubuwan nata da takeyi
sai ya dinga ganin tamkar ba cikin hayyacinta take ba. Maamah ke magana,uwar
data kawoshi duniya,inda wani ne ya masa magana makamanciyar wannan yana da
amsoshi masu yawa da zai bata.
"Bansan da zuwanta.....batayi shawara dani ba kafin ta
taho.....and a yanzun ina da iyali maamah,bani da wata alaqa da ita ta kusa ko
ta nesa,banda dangantaka da ita" Ya
amsa mata da kwantacciyar murya duk da tarin quna da bacin ran da yake ji na
cin zuciyarsa.
Idanunta ta
qanqance cikin jin tashin hankali yana ratsata a hankali a hankali. Meye yake
shurin faruwa?,meye yake faruwa da har yau din fuad da bakinsa ke ambaton INA
DA IYALI?. Yaushe ne ta samu wannan matsayin a wajensa?,wata kalma da bata taba
jin ta fito daga bakinsa ba?.
Tarin
masifa da wani irin tsanar sabreen tana ratsata,batasan wanne kalar abu ya
kamata ta yiwa yarinyar ba......a yanzun a dukka illar da aka mata a rayuwa
bayan ameenatu sabreen din itace ta biyu,koda ta raba sabreen da fu'ad bata jin
taci riba idan tabar yarinyar haka siddan taci gaba da rayuwarta,tana jin ya
kamata ta ajewa rayuwarta wani babban tabo ko miki da zai sanya koda a gaba
zata zamewa wasu izina a kanta. To amma babban qalubale da barazanarta a yanzu
shine TA WACCE HANYA ZATA RABASU?. Haka kawai take jin matsanancin faduwar gaba
da fargaba idan ta tuna kalaman sabreen akan auren fu'ad,bawai ta fara son
fu'ad bane matsalarta,idan hakan zata kasance ma zai zame mata daidai,tsoron
shine shi fu'ad din......yana da wata irin zuciya da bata iya soyayya ba kaman
yadda bata iya qiyayya ba......yana da wata irin zuciya me riqe abinda takeso
da gasken gaske..... Wata irin zuciya da idan tana so tana so.....idan bataso
bataso,zuciyar da zata iya sadaukarwa da abinda takeso komai data mallaka.....ta
zamewa abinda take qauna kariya daga dukkan wata iska ko kuma guguwa.
"Wanne iyalin kake magana akai fu'ad?,iyalin da nice
silar wanzuwarsu a rayuwarka?.....ko kuma iyalin da babu wata kima ko martaba a
tattare dasu?.....ko kuma ni da aka tsinceni daga ayarin tafiya aka wofantar
dani saboda kun nunawa duniya bani da wata daraja a wajenku?,ni din ba kowa
bace a wajenku?". Wani ciwon kai dukka maganganunta sukaso tasar masa
lokaci daya,ya sanya tafin hannunsa ya dafe goshinsa yana murzashi a hankali
tare da lalubo me ya kamata yace mata?,gefe guda kalmar IYALIN DA BASU DA WATA KIMA
KO MARTABA tana masa zillo cikin kwanya.
"AKWAI WANI ABU A LULLUBE" yaji wani saqo na
zuciyarsa yana gaya masa. Idan har maamah ta aura masa sabreen ne saboda ta
yarda da tarbiyyarta kaman yadda tace da farko......me ya kawo wannan maganar a
kanta a yanzu?. Bayajin akwai wani abu qwaya daya da zai iya tunawa wanda ya
taba hadasu koda cikakkiyar magana bare yayi tunanin akwai abinda ta taba yi
mata.
"Fareeda ta taso qafa da qafa.......ta sameni har
muhallina......ta girmamani matarka ta tabamin haka?,fareeda tabar qasarta ta
biyoka har inda kake,bata da kowa batasan kowa ba saboda tana sonka.......me
matarka ta taba yi me kama da wannan?". Kanshi yaji ya sake qullewa......a
yau din duka me ya kawo maganganu akan sabreen?,me yahau kan maamah duka akan
sabreen din?.
"Ina me baka umarni a matsayina na uwar data
haifeka.......nan da kwanaki goma zan bar qasar nan......ba wani jirgi da
zanbi,ba wanda zaizo ya daukeni....kai da kanka nakeso kazo ka daukeni ka kuma
kawoni Maldives......ka kuma soke barinku qasar ka daidaitashi da nawa barin
har sai na kammala uzurina sannan mu tafi......daga qarshe ina me baka umarni
kaje kaga fareeda......ka kuma marabceta kaman yadda kowanne baqo yake marabtar
baqonsa......wannan umarni na ne indai nice na haifeka" Daga haka ta yanke
kiran ba tare data jira cewarsa ba.
Shima wayar
ya sauke daga kunnensa yana kallonta,kafin ya sakata a tafin hannunsa yana dan
dokata kadan kadan. Kallonsa farouq yayi kafin ya aje dubansa ga wayar
hannunsa. Ya fahimci wadda tayi kiran ya kuma ji wani abun da take cewa saboda
magana take da qarfi da kuma fushi.
A abinda
yake lisssfawa zaiwa fareeda kowanne ya debo sai yaga yayi masa kadan. A
hankali maganganun maamah din sai yaji kamar suna tafiya da farincikinsa suna
son rushe duk wata walwala daya samu.
Idanunsa ya
bude kan farouq yana hadiye kowanne bacin rai da maamah ta sanya masa da
rudanin saqon daya shigo wayarsa a dazun.
"Ina jinka......kaman magana kakeso muyi ko?" Yace
da farouq. Idanu yadan zubawa fu'ad din,sai yaji tausayinsa yana kamashi.
Kowacce ni'ima da baiwa ta rayuwa Allah yayi masa......amma ya rasa UWA TA
GARI. Ya sake yarda tabbas rayuwa jarabawa ce,hakanan kowanne dan adam akwai
inda tashi jarabawar take,ba wanda yake samun jin dadin duniya dari bisa dari.
Murmushi
farouq ya sakar masa,sai yaji bazai iya kowacce magana dashi a irin wannan
yanayin ba,don haka ya sauya akalar zancan yana yin murya qasa qasa
"Wai yaya akayi wannan gingimarin ta iya hawa saman
keke?,karaya nawa keken ya samu?,duk da ni shaida ne akan yadda keken ya kusa
komawa akwala sabod......" Naushi yakai masa cikin sa'a ya daki iska. Ya
fahimci lallai da gaske farouq so yake ya maidashi birin wasanshi. Gefe farouq
ya koma yana dariya,can qasan ransa yana jin dadin hararar da fu'ad yake watsa
masa,yasan tabbas ko bai nasarar gusar da baqincikinsa ba zai rage masa wani
abu.
"Wallahi ka iya bakinka akan iyali na......kada ka
yarda mu saka qafar wando daya dakai" Yayi maganar yana nunashi da
yatsansa.
Ido farouq
ya zaro yana daga hannuwansa sama
"Ya salam.....kace me?,iyalinka?,unbelievable.....wazai
tayani jin wannan kalmar.......sabreen won the battle" Qaramin dutse ya
dauka zai jefeshi ya kwasa da sassarfa ya wuce cikin gida yana cewa
"Wallahi ta haukatashi......ya zama madoki" Tilas
dariya ta subuce saman labbansa. Sai da farouq ya bacewa ganinsa sannan ya
maida hankalinsa kan wayarsa. Kai tsaye ya kira jordan sukayi magana ta wasu
mintuna sannan ya kashe,ya kalli agogonsa yana lissafin awannin da suka rage su
kaishi gurin target dinsa.
★K'arfe
takwas na dare agogon Maldives ya gama shiryawa cikin wasu lafiyayyun trouser
da t.shirt. ta fidda sigarsa sosai da wani sassanyan kyau ke tsayawa a zuciyar
dukkanin 'ya macen data Kalleshi. Wani irin mutum ne da zai wahala ka kalleshi
ka kauda kai,koda baka furta komai a kanshi ba amma zai tsaye maka a zuciyarka
da idanuwanka. Jikinsa yabi ya feshe da turarukansa,sannan ya sanya sau ciki a
qafarsa,ya dauki wayarsa da maqulli ya nufi qofar fita daga dakin.
Dukkaninsu
suna dining area suna cin dinner. Kusan tunda suka iso garin tare suke cin
abincin safe dana dare,na rana ne kowa da tsarin cin abincinsa bai yuwu suci
lokaci guda. Ire iren wadannan abubuwan sune suke qarawa iyalan anni hadin kai
qaunar juna shaquwa tare da fahimtar juna.
A kanta
idanunsa suka fara sauka,wani irin abu ya tsarga masa tun daga kwanyarsa har
zuwa tafin qafarsa. Tun jiya bai sake sanyata a idanunsa ba,suna dakin annin
ita da amna. Bazaice ga abinda sukeyi ba,amma lokaci lokaci yana jin muryar
amnan da motsinsu,ita kanta amnan bata sake fitowa ba. Ita da amna suna seat
din kusa da juna,kaman magana suke qasa qasa,baka iya ji saboda musaddiq da
saddiq da suka cika gurin da musunsu da bai gane ma akan meye suke musun ba.
Kaman
wadda aka umarta,nata fararen idanun da a kwanakin yaga kaman sun qara girma ta
daga ta watsa masa cikin rashin sanin shi dinne ya is wajen. Qwayoyin idanunsu
suka gauraye da wani irin mabanbantan feeling. Da sauri ta janye qwayar idonta
yayin da nata kallon a gareshi ya zame masa kamar wani irin dafi daya sabbabba
mutuwar dukkan wasu gabbai a jikinsa. Tsigar jikinsa ta zuba sanda ta soma
motsa wadannan siraran lips din nata tana tauna Chip's din dake gabanta. Bazai
taba manta abinda yaji daga kowanne sashe na jikinsa ba a ranar farko daya soma
tsotsar tausasan lips dinta ba......wani mahaukacin saqo da suka aike masa da
baisan inda zai iya adana yawansu a kwanyarsa ba. Yanzun da take juyasu tana
tauna sai ya zamana tamkar tsokanarsa takeyi haka yakeji tana aika saqo kowanne
sassa na jikinsa.
Fitowarsa
ya sassauta tashin muryar saddiq da musaddiq din,kowa ya maida hankalinsa
jikinsa,kasancewar sunsanshi mutum ne da baison ire iren musunnan nasa. Yakance
"Shashanci ne wannan,kuna da abubuwan yi da yawa a
gabanku cikin rayuwarku,shi ya kamata ku fuskata" Sau tari musaddiq
yakanyi dariya idan bai wajen
"Shifa hamma ya dauka kowa irinsa ne.....ba baki nayi
mana ba,amma ba zamu iya achieving abinda yayi achieving ba.....we are doing
the best,amma ba zamuyi kaman nasa ba". Kujerar dake opposite dintata ya
zauna,sam table din baida fadi sosai,wannan yana iya sawa idan ka zura jiki da
yawa gwiwarka ta iya taba ta abokin zamanka.
Zamansa a
wajen sai taji kaman gaba daya ya cika wajen.....kwarjininsa da qamshin
sassanyan turarensa gaba daya ya gauraye wajen. Nauyin idanuwansa takeji har
tsakiyar kanta,abinda bata taba ji ba a kansa tsahon tarayyarsu.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 84
_Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha
da munkari_
_Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa
iyaye,zuwan gidan boka shirka kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya
tuntubi sahihancin sallarsa_
84
"Barka da
fitowa hamma" Amna ta fada wadda sun hadu yau kusan sau uku sun riga da
sun gaisa already.
"Lovey dovey.....barka da dare" Ya fada cikin wani
irin aji kaman me qididdige adadin kalamansa na ranar. Murmurshi amna ta saki qasa qasa.
"Hamma.....kada ka saka adda sabreen taji kishi
fa.....sunan nan for now ya kamata ace nata ne". Daga shi har ita nauyi
maganan ya musu musamman da anni ke a wajen,wadda tayi burus kaman bataji ba
tana qarasa shan black tea dinta. Amnan ya kalla sannan a dabarance ya saci
kallon sabreen din. Bayajin akwai wani suna daya cancanci ya kirata
dashi......har yanzun duk sunan daya bata sai yaji tafi gaban wannan sunan.
Daidai lokacin tana jefawa amna harara da fararen qwayar idanunta ne,wani irin
kyau yaga ta sakeyi masa,tsigar jikinsa yaji ta zuba sosai har sai daya lumshe
idonsa.
"Ka maida hankalinka fa.....aiki zaka fita kayi"
Wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa ganin tana neman dagula dukkanin
lissafinsa.
"Yi serving hammanku takwarata" Anni data kammala
shan tea din ta yiwa sabreen magana. Hakan ya masifar yi masa dadi,sai ya ajiye
mug din daya dauko da farko yayi relaxing bayansa jikin kujera yana jin jikinsa
yana sake mutuwa gaba daya....wani irin feeling yana taso masa yana sake kashe
masa duk wani kuzari nasa.
Sai data
ji gabanta ya fadi da anni ta fadi haka,amma dole ta ajiye fork din hannunta ta
miqe,fork din yabi da kallo,gaba daya ya gama karantarta,bata qaunar abinci ko
kusa ko alama....bayajin zai iya bari taci gaba da hakan,dole ta dinga cin
abinci me inganci tana qoshi,bayajin indai zata dinga zama ba abincin kirki
zata iya dauke lalurarsa yadda yakeso. Shi kansa wani lokaci yana tsoron
kansa,tun a lokacin da yake shi kadai ma.....shi da kansa yasan yana da buqatar
mace me juriya kafin ya samu abinda yakeso. Faruwar abunnan kuma ya tabbatar
masa sa zarginsa,bai taba kawowa ma zata iya dauke buqatarsa.....duk da abinda
ya farun yasan akwai aikin gaggawa da kuma rashin sabo a tattare da ita,amma
yasan cewa lallai akwai aiki a gabansa,dole sai ya horar da ita yadda zata dace
da muradi da tsarinsa.
Kwata
kwata ya mance ya samu farouq a wajen,ya shagala wajen qare mata kallo ta qasan
idanunsa. Zaka dauka sam ba ita yake kallo ba,amma kowanne motsi da zatayi
idanunshi suna kanta sanda take zuba masa abincin. A cikin qaramin hijab
take,amma shi ba hijab yake gani ba,wannan kyakkyawar surar tata yake
gani,kyakkyawar surar da yakejin koda zata shekara a yana ganinta zallarta
bazai gaji ba......kyakkyawar surar data kusa qwace kowanne tunani tasa,ta kusa
sanyashi manta waye muhammad jadda gaba daya. Wani sashe na zuciyarsa dake
danqare da mahaukacin kishinta ya soma masa zafi,gani yakeyi musaddiq saddiq da
farouq dake zaune a wajen suma suna iya ganin abinda yake gani.....yana jin
kamar duka suma qare mata kallo sukeyi.
"Gyara kintsi yallabai.....anni fa na wajen nan kada a
tafka abun kunya" Cikin kunnuwansa ya tsinci muryar farouq yana fada.
Cikin dakiya ya gyara zamansa yana basarwa,abinda ya kusan sawa farouq ya fashe
da dariya.
"Shi yasa ake cewa bawa yaji tsoron Allahnsa koda
yaushe" Farouq ya kuma fada sama sama. Tunu fuad ya gama karantar abinda
yake fada,so amma yanzun baida energy din kulashi. Hannu yasa don karbar mug
din da take miqo masa,cikin dabara ya hade da zara zara yatunta da suka ja
hankalinsa sosai,ya kuma motsa hannun nasa yana lullube bayan hannunta da tafin
hannunsa.
"Thank you" Ya fada da wani irin sauti can qasan
maqoshinsa yana karbar mug din.
Kaman an
yarfa mata ruwan sanyi haka taji sanda dumin tafin hannunsa yake ratsa kowacce
jijiya ta jikinta,ta koma ta zauna tana jin cikin ta duka ya gama cushewa ta
qoshi da chips din,sai ta koma juya cokalin kawai.
Tana jin
hirarrakinsu amma ita din ta gaza cewa komai,kaman yadda shima ta fahimci jifa
jifa yake cewa wani abu. Kanta da idanunta cikin plate din,ta gagara daga
idanunta saboda yadda takejin kowanne motsi nata ita yake kallo,ranta ya dinga
baci kadan kadan,wannan wanne irin kallon wuce qa'ida ne?. Ta aje kallo a
muhallin mazan bariki,wanda yawancinsu suna amfani da wannan hanyar idan sunso
dilmiyar dake su afakaki komarsu.....wannan dalilin ya sanya da wurwuri take
qarawa namijin da ya fiya kallon wuta. Amma wannan karon nasa kallon sai taji
ya banbanta da nasu,don nashi kashe mata jiki yakeyi,ya kuma aza mata wani
kwarjininsa sosai da har yake hanata sakewa.
Tsoro
sosai taji sanda taji ana lalubar tafin hannunta ta qasan kujerar. Ta fidda
idanu waje tanason fahimtar waye,saidai ya bata haske ta hanyar cewa.
"Miqo min tissue paper dincan please" Da wani
narkakkiyar murya. Kallonsa tayi ya kashe mata ido daya,ta janye dubanta da
sauri tana tura masa tissue din,ya dauka ya aje gefe yana ci gaba da cin
abincinsa tabbacin ba amfani zaiyi da ita ba kenan.
Tana ji
tana kuma gani yaci gaba da murxa tafin hannun nata ta qasan table
din,lallausan tafin hannunsa yana saukar mata da wata irin kasala da kuma
tsoro,bai bata dama ba ballantana ta miqe ta nesanta kanta dashi,ba kuma zata
iya nunawa kowa abinda yake faruwa ba.
"Amman adda.....you look familiar,tun randa kuka iso
Maldives naji kaman na taba ganin face dinki......kin taba zuwa asibitin
SAMHG?" Musaddiq ya shigo da maganar cikin hirarsu. Duban musaddiq tayi
tana qoqarin daidaita yanayinta kada wani ya fahimci akwai abinda ke faruwa
under the table.
"Eh......kaman sau daya ba......na taba kai
wata....." Zancanta kuma sai ya katse,ta maida dubanta kan fuskar anni.
Duk tsahon watannin da kwanakin sai yanzu fuskar ta dawo mata fes cikin kanta.
Matar nan data fadi wajen sallah asma dinta taso tashi.
"Exactly anni itace..." Ya fada yana sakin
murmushi sosai gami da ture abincin gabansa.
"Anni ya akayi kika samota?.....wannan data dinga mana
masifa saboda mun barki ba kowa a wajenki.....wannan dinnan dataqi bayyana
kanta bare ki gode mata,bayan ta dawo miki da jakanki ba'a dauki komai a ciki
ba". Maganganun musaddiq suma sanyashi daga kai daga abincin da yakeci
yana maidawa kan fuskarta gami da matse yatsunta softly cikin nasa,yanason yaji
qarin bayani,yanason samun tabbacin da gaske ita ta taba cetar anninsu?. Anni da mamakin duniya ya isheta ta ware
hannunta tana sakin qaramar dariyar farinciki
"Ban sani ba musaddiq......hammanku zaka
tambaya.....duk da shima nasan bai sani ba,tunda bai santa ba" Ta qarashe maganar tana kamo hannun sabreen
ta riqe cikin nata
"Yau kuwa zan miki godiyar da nayita so nayi miki ban
samu dama ba.......sai gashi cikin hikimar ubangiji wadda ta ceci raina ta zama
mata ga yaro na......dame zan saka miki sabreen?". Numfashi taja sosai
kaman numfashinta zai qwace mata saboda yadda ta qasan table din fuad din ke
mata wani irin salo tsakiyar tafukan hannayenta. Ta kasa fadin komai,sai muryar
anni data sake ratsowa.
"Komai zan miki ban saka miki ba takwara.....lallai
kinyimin abinda bazan iya saka miki dashi ba.....wallet dina babu ko sisi da
aka taba a ciki,kaman yadda wayata ta dawo lafiya lau.....ubangiji ya jiqan
magabatanki ya kyautata makwancinsu.....na gode na gode sosai". Murmushin
jin nauyin annin ta saki tana yin qasa da kanta.
"Ba komai anni......idan har kana da hali dole ka
taimaki wanda yake buqatar taimakon nan,da jikinka koda kudinka". Kai take
jinjinawa tare da sake qaunar sabreen din,qasan ranta kuma tana tsara wanne abu
zata mallakawa sabreen madadin kirkinta gareta?. Hirar yadda abun ya faru a
ranar aka fara maidawa,kadan kadan yana kallon fuskarta yana cin abincin,kallon
dake qara bashi qwarin gwiwar cin abincin. Duk wani hirar abun da sukeyi sai
yakejin kamar suna qara mata gurbi ne da muhalli cikin rayuwarsa.
"Ashe ta mallaki wannan dabi'ar me kyau?" Ya
tambayi kansa yana tuna kiran wayar anni daya dinga yi a wancan lokacin.
"Dama can me tsiwa ce.....dama can bata da tsoro"
Ya fada qasan ransa yana tuna yadda ta daga wayanshi har sukaso yin fada.
Tana
kallonsa ya gama laqai laqai dinsa,abincin da zaici cikin minti ashirin sai
daya jashi talatin da biyar,kafin ya gama duk ta jiqe da gumi,tayi saurin
miqewa tana cewa
"Bari nayi fitsari" Sanda ta samu ya cire hannunsa
a nata.
"Karki yadda da tsarin yin nesa dani......bazan lamunta
ba" Ya fada mata qasa qasa sanda take giftashi. Numfashi kawai ta dinga
saukarwa cikin bandakin tana jin bacin ransa,haka kurum zai fara zame mata
takura ya hanata sakewa?.
Wucewarta
yasa yaji cin abincinsa ya qare,ya dan ture plate din yana miqewa.
"Anni zanje Vaadhoo......but bazan jima ba".
Maganansa ya daki kunnenta sanda ta murda qofar dakin anni zata shige. Bata
fasa shiga din ba,duk da tayi kaman ta tsaya ta kuma waiwaya ta kalleshi.
" Vadhoo kuma?,wajen wa?" Ta tambayi kanta tana
zama gefan gadonsu zuciyarta na tuna mata abinda ya faru na qarshe a wajen a
waccan ranar.......ranar data bashi dama ya bude wata qofa da ba tashi
ba....qofar da bata tanadawa kowa ita ba. Kusan minti uku tayi zaune a
wajen,bata shiga bandakin ba bata kuma san me take tunawa ba. Wani mugun tsaki
taja,hankalinta yana dawowa jikinta
"Ko ina ma zaije menene naki a ciki?" Ta tambayi
kanta da kanta sannna ta miqe da confidence tana shiga bandakin don rage
fitsarin da taji mararta ta tara.
Sanda
Jordan ke bude masa murfin motar yaji amna na kiransa. Sai daya shiga ya zauna
yabar qafafunsa a waje sannan ya jira isowarta.
"Ga card dinka hamma" Ta fada tana miqa masa black
card din. Hannu yasa ya karba yana juyawa. Yana jira yaga nawa aka cira?,amma
har yau baiga an dauki ko sisi ba.
"Amneee.....kun gama amfani dashi ne?". Kai ta
mirgina tana dubansa a shagwabe kaman yadda ta saba musu.
"Hamma.....adda na kam daban take,taqi karba ma bare ta
cire komai,duk inda akaje ko za'a siya abu sai tace bata buqatan komai.....haka
adda take wai?,bata da buri sam sam?". Idanusa yadan lumshe yana kuma
budesu lokaci guda,wani abu yana saukar masa a zuciyarsa. Yasha aje abubuwa
masu daraja da amfani a dakinsa amma koda ta gyara masa inda ya aje komai haka
yake zuwa ya sameshi. Baisan adadin dollars da pounds din da yake ajiyewa ba
amma ko qwaya daya bai taba dubawa yaga ta zara ba. Kai yake jinjinawa,yanason
karantar wacece ita?,yanason ya santa sani na zahiri.....a dazun yaji anni na
yiwa iyayenta addu'a marainiya ce da gaske?.
Wani guri
ya danna ya zira card din,yana jin a jikinsa bazai iya tafiya bai ganta kusa
dashi ba,bazai iya tafiya baiji dumin jikinta ba,qilan idan ya tafi a haka
bazai iya aikata komai ba,don haka yace
"Jeki ki kiramin ita......but kiyi sauri ana
jirana"
"To" Amna ta fada tana juyawa ciki.
Tana
fitowa daga toilet din amna na shigowa.
"Matar hamma hamma yana kiranki.....yace kiyi sauri zai
fita ne" Ta fada da dan dariya alamun tsokana kenan a muryarta. Ta bude
bakinta da zummar aika masa ba zata samu daman zuwa ba saita hangi anni na
shigowa daga baya,wannan ya sanya taja bakinta ta rufe.
Batasan
me zata cewa amna ba,zataje ko bazata je ba......amma yadda anni tayi magana ya
tabbatar mata annin tayi supporting taje din.
"Idan kin dawo takwara ga ragowan magungunanki
nan" Ta aje wata 'yar jaka a hannunta ta juya tana bar musu dakin. Sai
dataga fitar anni ta gasawa amna harara.
"Tsakaninki da Allah shi ya aikoki?,banason wasa
amna?" Ido ta zaro waje tana duban sabreen gami da son boye dariyarta.
"Am serious Allah adda......ba ruwana shikeson ganin
matarsa" Ta fadi tana watsa hannaye. Harararta ta sakeyi ta taka tana
neman hijabinta daidai nan anni ta sake shigowa.
"Kuyi da jiki kuzo inason ganinku" Maganan ya gaya
mata da ita anni take,sai kawai ta zunduma hijabinta tayi gaba tana qunquni
cikin zuciyarta. Itakam ta shirya barinsa cikin kwanaki kadan,....don meye
zaita kusanta kanshi da ita?,waima ba zaluntarta da cutarta yakeso yayi
ba?,kuma duka yayi?,meye sauran abinda yake nema kuma?.
A hankali
ta dinga takawa har ta isa dab da bakin qofar motar inda yake zaune. Tunda ta
fara takowar idanunshi yana zube a kanta ta side mirror. Ya lumshe idanu ya
bude yafi sau goma,yana jin tana tayar masa da makamansa,wani irin taku gareta
da bai taba lura dashi ba sai yanzu......takun qasaita takeyi kamar na bijimin
dawisu.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 85
85
"Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen" Ya motsa labbansa yana
fada yana kallon yadda sassan jikinta ke juya kansu sanda take takawar. Da
hannunsa ya dafe kansa yana jin kishi yana cin zuciyarsa,ta fita da abaya me
madauri......ta fita da Chantilly......ta fita da qaramin mayafi duka dai kenan
kowa ya taba ganin jikinta?.
"Dole na killace kayana" Ya fadawa kansa da kansa
cikin qwarin gwiwa.
Kaman
bashi yake neman susucewa ba sanda take takowar ba ta cikin madubi,data iso
gabansa sai ya zubawa fuskar nan tasa wannan izzar tasa data sanshi da ita. Ya
dubeta a kaikaice.
"Haka ake zuwa kiran miji,ka yima mutum tsaye
aka?" Ya fada a dake girarsa a tsuke. Duba daya ta masa ya mata kwarjini
ta dauke kai,ta soma mita qasan ranta saidai batasan labbanta suna motsawa ba
"Waye yace ka kirani ina zamana?,sai kayi rayuwarka
nayi tawa ai,kada wanda ya damu wani"
"Shigo ki gayamin abinda kike cewa" Yayi maganar
duka da jawota cikin motar lokaci guda,sai gata kwance a qirjinsa ya dafeta
sosai cikin jikinsa,yasa daya hannun nasa yana rufe murfin motar,sannan ya taba
wani abu take glass din motar duka suka zama tentac fitilun motar suka koma
blue me haske da fari. Sun samu cikakken tsaro da hijabi ta yadda bame iya
ganinsu.
Qoqarin tashi
takeyi a jikinsa amma ya hana mata wannan damar,ya mata wata kyakkyawar runguma
data sanya numfashinsa ya soma sauya.
Maimakon
ya barta ta tashinma sai ya kamo fuskarta ya riqeta dab da tashi yana kallon
qwayar idanunta,hannunsa daya sauka a qirjinta zuwa wuyanta yana jin yadda
zuciyarta ke bugu tak tak tak.
"Ms kike fada dazun?,speak louder" Yayi maganar
hucin numfashinsa daya gauraya da qamshin mint na bakinsa tare da sassanyan
turarensa suna neman lahantata da tsoronsa da kuma wani kwarjini. Mutsu mutsu ta fara yi cikin tsoron sauyawar
da taga launin idanunsa sun fara yi tace
"Nifa bance komai ba" Shuru ya mata bai amsa mata,sai qarewa
kyakkyawar fuskarta kallo da yakeyi,kwantacciyar gashin gira dana ido,pink lips
dinta da suka dan dago saboda yadda ya riqe fuskarta. Ajiyar zuciya ta kubce
masa,ya fahimci kaman akwai tsorosa a lamarinta abinda bai fara ganinsa ba sai
bayan faruwar abun,duk da Dr fadwa ta gaya masa zai iya experiencing hakan a na
gaba dama.....so dole next time yabi komai a sannu.
Hannu ya
sanya ya fara zame hijb din jikinta yana hade rai.
"Ba cewa nayi fa kizo muje gidan wa'azi ba......wannan
abun haramunne ki sanyamin shi....na kiraki ne na koya miki yadda ake gaida
miji fa". Sosai ta tattamke hijab din tana jin hankalinta yana tashi. Kai
ta fara girgiza masa,tasan muddin ya fidda mata hijabin ya sake gamawa da ita.
"Karkiyi gardama......bana so" Ya fada mata da
idanunsa da suka qarasa jirkicewa yana girgiza mata kansa gami da kallonta kai
tsaye ta cikin nata qwayoyin idanun. Bata yarda ba ta fara qoqarin saita
hanashi cirewa,bata Ankara ba ta jita luuu ta zame ta kwanta,sai daga bisani ta
Fahimci kwantar da kujerar yayi ta koma kaman wani qaramin gado.
Daga
qasa ya sanya duka qarfinsa ya tattare hijabin a zafafe,abinda ya sanya ta gefe
da gefe jilbab din ya soma yageqwa dinkin yana farkewa,bai saurara mata ba sai
daya tsargeshi ta bangare daya ya koma kaman mayafi,kafin sannan hawaye ya gama
jiqa mata fuska. Qarasa tattareshi yayi ya zareshi daga jikinta,take skirt
dinta da iyakarshi qaurinta ya bayyana,vest din jikinta data dameta ita fito
wadda zallarta ta saka babu ko brazier a jikinta. Saman na shanunta idanunsa ya
tsaya,ya zuba musu idanu yana kallon yadda suka cika rigar. Wani irin shauqi ke
fusgarsa zuwa garesu,don haka ya miqa hannayensa da zummar kaiwa garesu ya cire
rigan data masa shamaki dasu. Tunawa tayi last time da haka ya fara,don haka ta
hada dukkanin qarfinta ta riqe masa hannu.
"Don't fight it" Ya furta low and husky voice
dinsa,idanunsa a tsaye car cikin nata kaman yana tabbatar mata da gaskiyar
abinda ya fada mata dinne Idanunsa full with mixture emotions.
Kai ta
sake girgiza masa,ba zata iya barinsa yaci gaba da rabar jikinta har haka
ba.....in fact ma bataga dalili ba,ta sake daga hannunta da nufin
tureshi,saidai ga mamakinta tsam ya riqe hannayen nata,ya jawo wani abu kaman
belt a jikin motar ya maqale hannayen a jiki. Bazai iya handling hannayen duka
biyu lokaci guda a yadda yake jinsa ba......haka bazai iya kuma jurar yadda
zata hanashi rawar gaban hantsi ba. Idanu ta fiddo duka waje tana dubansa gami
da duban hannayen nata,daidaita tsahonsu yayi,ya sanya hannuwansa ya tallafo
fuskarta,yasa hannunsa yana matsar da gashinta daya barbazu a fuskarta zuwa
gefe.
"Am sorry if i misbehaved you......nutsuwa zaki bani
dan kadan.......bazan wuce iyaka ba.....nima ina buqatar lafiyarki......inaso
ki warke da wuri" Yayi maganar qirjinsa na dagawa da wani matsanancin
bugun zuciya. Kafin tace komai ya hade bakinsu guri daya,ya kuma fara yamutsata
da kalan wani abu da bata sanin meye shi ba,batasan kuma akwai kalar abun a
duniya ba. Kuka sosai ta saki na yadda yake yamutsata son ranshi,gashi kuma
bata da ikon qwatar kanta,tana ji tana gani ya isa ga inda yaketa fusgar hankalin
nasa. Fuskarsa ya boye a tsakaninsu kafin ya soma sauke mata wani zazzafan huci
daya dinga sauka kai tsaye cikin fatarta yana ratsa sassan jikinta. Ko daya kukanta bai dakatar dashi ba,har sai
da yaji ana knocking motar da dan qarfi. Zame jikinsa yayi gefe yana jan tsaki
me qarfi,abinda ya bata damar komawa rub da ciki ko zata samun sutura da jikin
kujerar motar. Da qyar ya iya bude idanunsa,jikinsa ya gama sakewa gaba daya ya
azashi kan qaramin allon computer din dake maqale a wajen. Farouq ne tsaye hankalinsa
kusan duka akan wayarsa,yana kallonsa ya sake saka yatsunsa yayi knocking,sai
kawai ya dunqule hannunsa ya daki kujerar da yake kai,kafin yaja jikinsa yana
miqewa.
Hannunsa
yasa ya birkitota a tausashe,ta saka hannuwanta tana kare jikinta....saidai
batasan sanda ta saki hannayen nata ta damqo hannunsa dake shirin yaye skirt
dinta duka zuwa cikinta ba,wanda dama tuni ya tattare ya bayyana santala
santalan cinyoyinta.
Birkitattun idanunsa ya zuba mata,kai take girgiza masa da guntun
hawayenta. Bayani yakeson mata amma ya kasa,koda ya bude bakinsa ba kalmar data
iya fita,har sai da yaja gyaran murya sannna ya samu maqogaronsa ya washe.
"Inason na gani ne ko dinkin ya warke......ba wani abu
zanyi miki ba" Ya fada a tausashe. Kuka ta kuma saki tana jin wani
rikitaccen yanayi yana mamayarta,duk yadda yayi mata bai isheshi ba har sai ya
bankada sirrinta?.
Wani
knocking da farouq din ya qara saki shi ya ratsa har kwanyarsa ya kuma dakatar
dashi,ya kalli farouq din ta camera din yaji kaman yakai masa naushi ta ciki. A
hankali ya saki skirt din,ya kuma zame hannunsa daga nata ya miqa hannu yana
dagota,sannan ya taimaka mata ta maida kayanta gaba daya. Yana daga zaune a
wajen ya dannan lock ya bude mata,ta sauri ta soma sauka ta fice tana kauda
kanta ba tare data yarda sun hada ido da farouq ba.
Sai daya
tabbatar ta fita ya sanyo kai ciki. Idanunsa yakai kan kujerar data koma
qaramin gado,sai ya maida dubansa kan fuad dake zaune dafe da kansa da dukka
hannayensa duka biyu farouq din zaiyi magana ya saka hannu ya bude daya side
din motar ya fice da sauri,sai ya bishi da kallo sannna daga bisani ya sheqe da
dariya,ya saka hannu ya dauke masa agogonsa da da alama baisan ya fice a
hannunsa ba.
"Allah yasa ta haukataka" Farouq ya fada yana
mimmiqewa abinsa saman kujerar abun yana masa dadi. Ba yaro bane shi,yana
kallon wajen yasan da magana.
Kai tsaye
ya wuce cikin gidan,Allah ya taimakeshi bai samu kowa a parlor ba,sai ya zarce
zuwa dakinsa yana sauke numfashi cikin
tsananin kasala. Tun a motar ya tabbatar wanka ya kamashi,ya fidda kayan
jikinsa gaba daya ya wuce toilet ya sakarwa kansa ruwa me dumi. Gilmawarta
kawai idanunsa suke ganin cikin toilet din,kowannw motsi nata......fitar hawaye
cikin kyawawan idanunta da bai taba lura da wani irin tsaga da zubi da Allah ya
basu ba sai yau......tausasan lips da tafukan hannayenta.....wani irin cikakken
hips da bai taba ganin irinsu ba duk da cewa kallon mata ba dabi'arsa bace
daman.
Sai da
yaji nutsuwa tazo masa sannan yayi wankan ya fito,ya sake shirya kansa cikin
wasu qananun kayan ya kuma ficewa.
Koda ya
koma motar baiko kalli farouq ba,ya rufe murfin ya bawa Jordan umarnin ya tayar
su tafi.
Bata iya
komawa cikin gidan ba,saita zagaya ta baya can tana tattara nutsuwarta. Ta kusa
mintuna talatin kafin ta samo kanta,ta sake gyara hijab dinta sannan ta wuce
cikin gidan gabanta yana faduwa,tana fatan Allah yasa kada anni ta gane komai.
Kaman
wata mara gaskiya haka ta tura qofar dakin tana saka kanta. Duban farko anni
tayi mata ta tabbatar kuka tayi,sai ta dauke kanta kawai tana tattare kayanta
ta fita ta basu dakin. Fitar annin yadan bata nutsuwa kadan,ta taka a hankali
ta zauna saman sofa inda amna ke zaune tana buga game.
Bata
cewa amnan komai ba don batasan me zata fada ba,gani take yarinyar itama ta
karanci komai,kawai saita zame ta kwanta ta maida idanunta ta kulle. Ga
mamakinta sai komai ya dinga dawo mata,zuciyarta ta dinga wani irin bugu sanda
ta motsa taji jikinta yana fidda sassanyan qamshin nan nasa.
"Qamshin turaren hamma adda sabreen.....ko ya sammiki
ne ki sanmin nima?" Amna data tsaida game dinta ta fada tana duban
sabreen. Gabanta ya fadi,tadan ware idanunta kadan tana duban amna,saita rasa
ma abinda zata ce mata,don haka ta juya kwanciyarta tana bawa amna baya sannan
ta amsa mata da
"Bacci nakeji amna please". Qaramin murmushi ya
subucewa amnan
"Ni na sani.....hamma na bazai qyaleki ba.....hamma na
ba gama garin maza bane,saikinso hamma kamar ba gobe.....sai kinso hamma sama
da komai da kike dashi" Amma a fili sai tace
"Ayi bacci me dadi tare da mafarkin hamma na" Tana
jinta amma bata ce komai ba,tsoro takeyi kada ta fadi abinda zai sanya a gane
komai tattare da ita.
Har suka
soma daukan hanya ba wanda yace da kowa komai,sai daga bisani fuad din ya gyara
zamansa yana tambayar farouq ba tare daya kalleshi ba
"Ina zaka ne ka shigo mana mota?" Yayi maganan a
dake,wanda duka farouq yasan yayi ne don borin kunya kada ya sake masa magana
kan abinda ya shigo ya tarar.
"Kai ina zaka?"
"Vaadhoo"
Ya amsa masa kai tsaye.
"Me zakayi ne a Vaadhoo?" Farouq ya tambayeshi
yana duban.
"Gurin fareeda.....but don't ask too much" Ya amsa
masa a gajarce. Bai iya qarya ba.....shi yasa ya masa kandagarki. Motsawa kadan
farouq yayi,yaga fareeda a ranar kafin su baro vaadhoo din,kuma jikinsa haka
kawai ya bashi akwai abinda ya faru. Ba kasafai ya fiya son barin fuad idan
yana fushi ya dauki.mataki akan mutum ba,shi yasa fitowar da yayi ya zargi wani
abu ya kasa zama ya biyoshi,ya Tabbatar indai wani abu ne ya hadashi da
fareedan bazai barta tasha da kyau ba koda waye ubanta,to amma sai yakama bakinsa,baiso
yace wani abun farouq din ya sauya shima.
_uhmmmm.....fareeda?.....ga maza nan gareki....malam farouqu
ko muhammad jadda zai barka ka shiga har inda zaije din?,bari mu gani_
_maza maganin maza....da d'aya da d'aya komai zai fallasa_
_ina muku barka da litinin da cikakken yaqinin mun dawo sai
munga abinda ya turewa buzu nadi,na gode_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 86
86
Idanu sosai
farouq ya zuba masa,kaman zaiyi magana sai ya fasa ya maida kansa kan wayarsa
sukaci gaba da chart da fanna. Abu daya ya sani shine,bazai bar fuad ya qarasa
wajen fareeda shi kadai haka kai tsaye ba,don yasan halinsa sarai.....bai iya
daukan abubuwa serous ba.
Jifa jifa
suke maganganu da suka shafi kasuwanci,wanda saisun samu dama irin haka
sukeyi,duk da kusan shirun fu'ad yafi yawa. Har yanzu tsigar jikinsa zubawa
takeyi idan ya tuna abinda idanunsa suka gani tattare da ita karo biyu
kenan,har yanzu yana jin kowanne sassa nata cikin hannunsa da jikinsa kaman
suna tare.
"Anya zan iya barinta for 2months kuwa?" Ya
tambayi kansa cikin shakka da kokwanto.
Ba jimawa
suka isa Vaadhoo suka kuma wuce glowing beach. Wayarsa ya ciro a nutse,ya
rubuta gajeran saqo ya turawa mutum biyu sannan ya maida wayar aljihunsa yana
gyara zamanshi. Yasan manufar farouq.....yasan meya sanya ya biyoshi,shi kuma
baya fatan abinda zai rageshi ko ya hanashi cin uban fareeda la'ada waje.
Zarginta yake dari bisa dari akan wasu abubuwa da dama,yana da tabbacin zaiji
abubuwa da dama daga bakinta akam sabreen. Ya shirya kare mutuncinta da
martabarta,ya shirya tsaya mata a duk inda ake buqatar wanda zai tsaya
maka......ya kuma shirya nunawa duniya ita din matarsa ce kuma iyalinsa ce dake
da kima mutunci da martaba kaman kowacce mace.
A
hankali motar ta dinga ratsa farin yashin da bame yawa ba,kasancewar sasannin
tsibirin ruwa yafi yawa,ba kasafai kake doguwar tafiya bisa mota ba saidai boat
boat.
Kyakkyawan
parking jordan yayi,fu'ad ya sanya hannunsa ya bude motar yana sanya qafafunsa
waje. Budewa farouq yayi shima ya fita,ya zagayo gefan fu'ad din sannan suka
fara takawa zuwa muhallin da aka tanada saboda zaman shan iska. Da idanu ya
yiwa jordan alama,sai yaja baya ya barsu su biyun har suka isa saman kujerun.
Suna zama wasu Maldivians guda uku suka qaraso. Cikin harshen dhivehi daya
kasance yaren qasar,biyu daga cikinsu suka zauna dayan ya juya zuwa sashen da
aka tanadi abubuwan sha saboda baqi. Ba jimawa ya dawo ya zube musu halal
drinks da ruwa da gasashen kifin da aka wadata da vegetables da da lemon.
Agogon hannunsa fu'ad ya kalla,yaja baya yana miqewa.
"Ina zuwa" Ya fada yana basarwa,hankalin farouq
yakai kanshi,amma maganan da daya daga cikinsu ya masa cikin harshen turanci ya
dauki hankalinsa,ganin fu'ad din gaba kadan ya matsa yana waya bawai gurin ya
bari ba gaba daya sai ya maida hankalinsa kan mutumin,saboda ya masa magana
akan abinda ya shafeshi ne wato harkar noma da Samar da iri da taki na zamani.
Sannu sannu ya bashi hankalinsa sosai saboda hirar tayi masa,da wannan fu'ad ya
samu ya zille abunsa ba tare da farouq ya ankara ba.
Yana
takawa zuwa dakin shida Jordan ranshi na sake baci. Ya tabbatar a ranar akwai
abinda yasha......akwai abinda ta bashi. Yaya akayi ma tasan dakin daya
sauka?,har ta samu access da dakin cikin sauqi?,bayan wajen ya sani wajene me
tsaro da matuqar sirri.
A lokacin
tana zaine d'ai d'ai saman gadon tana busa shisharta. A kwanakin shisha kawai
take bugawa cikinta ta hada da syrup. Tuni ta kori lubna daga dakin,saboda tana
jin bata buqatar kowa a kusa da ita. Tana buqatar abinda zatayi refreshing
damuwarta kafin tasan abinyi next. Bata taba tunanin zata hadu da asara da
faduwa ba irin wannan,ta dauka komai zai tafi daidai,musamman data san cewa ba
qaramin dosage ta sanya a zuba masa ba. Sai gashi cikin mintuna qalilan komai
ya wargaje,tsananin taurin kansa da kafiyarsa ya hana komai yayi tasiri.
Tun bai
murda qofan ba qamshin flavors din ya soma masa maraba,ya yatsine fuska rai
bace yana isa qofan. Duk da wajen mutane da yawa flavour na shisha qamshi yake
musu.....amma tsananin yadda ya tsani shaye shaye ya sanya shi a wajensa baida
maraba da warin wiwi. Daga ranar kuma da bincike ya tabbatar da zuqa daya na
shisha daidai yake da ka shanye sigari kara dara biyu ya sake mata muguwar
tsana,inda Allah ya rufa musu asiri kaf dinsu Allah ya duba addu'ar anni a
kansu,babu me shan komai koda shishan da wasu suke mata kallon ba abar shaye
shaye bace.
Kallon
farko da suka yiwa juna ita dashi,ita din saita dauka cikin gizanniya take
ganinsa bawai me jadda bane real ain. Ta ajiye tiyo din shishan tana miqewa
zumbur farinciki yana ratsata,wata mayaudariyar zuciya daga can cikin qirjinta
tana gaya mata
"Ya rasa me kashe masa wutan sha'awarsa.....har yanzu
abun na ruruwa a jikinsa shi yasa ya dawo miki......ya tabbatar ke zaki iya
masa wannan aikin" Da wannan
yaudararrun kalaman ta soma tafiya da sassarfa tana nufarsa fuskarta da
shimfidaddiyar fara'a. Saidai kuma dab da zata isa gareshi ya qare yatsunsa
biyar ya sauke mata wasu lafiyayyun maruka guda biyu qwarara hagu da
dama,marukan da suka sanya kowanne connection na jikinta tsayawa na wucin gadi
kafin komai ya dawo mata aiki.
Sai a
sannan sashen dake gaya mata gaskiyar komai ya fara aiki,ta lura da wani
lafiyayyen bala'i dake kwance saman kyakkyawar fuskar da a yau ta juye kaman ta
mayunwaci kuma fusataccen zaki.
Nuni
kawai ya mata da hannu na wajen zama,ta kalli gurin sannan ta maida dubanta
kanshi zuciyarta na mata wani irin zafi. A yau ita fareeda Khalid mustapha wani
d'a namiji ya sanya hannunsa saman fuska.....isashiyar macen da mata da dama
suke buri gami da fatan hawa matsayinta?......macen da batasan adadin mazan da
tayi rejecting ba da suke fatan mallaka mata komai nasu don ta kasance tare
dasu?.
"Ni ka mara?" Tayi tambayar da yanayin dake nuna
tsananin zafin da marin ya mata,bawai ga iya fuskarta kawai ba.....har cikin
zuciyarta da ruhinta.
"Kina buqatar qari ne?" Ya tambayeta yana dage
dukka girarsa guda biyu,hannayensa xube a aljihun wandonsa don ya tabbatar idan
ba hakan yayi ba zai iya rufeta da mahaukacin duka. Shi kuma bai shirya aza
hannunsa saman qazamin jikinta ba.....don bayajin ta samu wannan darajar. Marin
da yayi mata dinma ya gaza shanyewa azo gabar ne,yana kuma son bata alamun cewa
gagarumin bala'i ne ta daukowa kanta da bata da qarfin ikon tarewa kanta shi.
Taku ukun da yayi yana jifanta da wani qasqantaccen kallo ya sake rage tazarar
dake tsakaninsu sosai,wannan ya qara yawan kwarjininsa cikin idanunta,ya kuma
sake qara mata tsoronsa. Abinda tafiso a rayuwarta shine ya kusantota,amma a
yanzun da ya kusantota din sai take jin kamar wani baqin kumurcin maciji ne
yake nufota.
Da hannu
ya sake nuna mata seat yana zube mata idanun nan nasa dake da wani ajiyayyen
kwarjini na musamman,wannan karon ba musu ta koma da baya ta zauna,saidai har
qasan ranta tana rubuta abinda yayi matan a matsayin yaci bashi.
Gabanta ya
iso yaja kujera dab da ita ya zauna,har tana jin fesowar qamshin sassanyan
turaren nasa. Bata taba tunanun kwarjininsa yakai haka ba sai a yanzu daya sake
kafeta da idanunsa da suka qara girma,ya zuba mata idanu kaman bazai daina
kallonta ba. Ba abinda yake gani tattare da ita sai wata mummunar mace maras
aji da kuma fasali idan ya dauko hoton fuskar sabreen dinsa ya kwatantata da
tata. Wata ballagazar mace da babu wani abun burgewa qwaya daya tattare da ita.
"Tambayoyi ne zan miki su da bansan qwaya nawa
bane,amsarsu kawai nake da buqata.......samun amsoshinsu sune
kubutarki.......ki manta ubanki waye da farko.....sannan kema ki manta wacece
ke......kiyi tunanin makomarki da abinda zai iya faruwa dake.......ki manta kin
bawa mariya ahmad kudade don ta mallaka miki Muhammad fu'ad....." Ya fadi
maganar yana jin wani d'aci yana tasowa daga qasan zuciyarsa,yana jin zuciyarsa
kuma ta matse waje daya. Da wani irin zafin nama ta bude idanunta a kansa tana
mamakin ta yaya yasan da wannan deal din?.
Sai daya
hadiye abinda ya taso masan sannan yaci gaba da magana.
"Baki da wani ko wani abu da zai iya mallaka miki
wannan muhammadun har abada" Ya sake fadi yana nuna qirjinsa da yatsarsa.
"Koda babu ameenatu sabreen a gefe na......ballanta
tana cikin DUNIYATA tana cikin rayuwata....na tsere miki tserewa ta har
abada.....bama keba,duk wasu mata ire irenki......WAYE YA BAKI DAMAN KIRAN
MATATA DA KARUWA?.....WAYE YA BAKI WANNAN LASISIN?" ya mata tambayar farko
da ita tafi tsaye masa a wuya fiye da kowanne abu.
Wata irin
wutar kishi ta taso mata,ta kuma yaudareta da cewa ya zauna ne yaci fuskarta
kawai......ta yaya tana cikin jerin masoyansa zai zauna yana mata tambaya akan
wata mace da batajin ta fita komai?.
"Au bakasan karuwa kowa yake kiranta ba?,bakasan karuwa
ka aura ba dama?". Ta fada tana danne tsoron dake taso.mata,saboda yadda
zuciyarta ke qarfafa mata gwiwar idan yaga tsoro a idanunta to tabbas ta karya
lagon kanta da kanta.
Labbansa na
qasa ya cije yana kausa kansa daga fuskarta,kalamanta suna qonashi da wani irin
zafi.
"Jordan" Akwai yace yana dunqule hannunsa waje
daya,saboda bayason yakai hannunsa kan qazamin jikinta.
Taku daya
jordan ya qaraso bayanta,wanda kwata kwata bata kawo komai a kiran nasa da yayi
ba,ba zato ba tsammani taji an take yatsun qafarta an kuma murjesu da kyau har
sai data fasa wata qara tana jin azaba tana ratsata,qarar yatsun kuma suka
baqunci kunnenta da qas....qas.....qas...daya bayan daya,tabbacin qasusuwansu
ne suke rarrabuwa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
EID MUBARAK TO YOU ALL
ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEN SUMMA AMEEN
SHUKRAN JAMEE'AN🙌🏽🙌🏽🙌🏽🥰🥰🥰
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 87
87
"Ka dagani......ka sakeni!qafata.....qafata" Ta
fada a mugun rude kuka da fitsari dukka yana qwace mata lokaci guda,sake take
dayar yayi sosai yadda itama yasan zataji a jikinta ba alamun tausayi sam a
tare da jordan din. Sai daya kalli fu'ad sannan ya bada damar ya matsa baya,ya
dauke qafarsa yana cewa.
"Kiyi magana dashi da manners.....kiyi magana dashi in
a polite way......idan ba haka ba kafin bincike ya kammala duka sai na kusa
dake sun kasa ganeki". Ko jordan bai fadi haka ba ta fahimci abinda ke
shirin faruwa kenan.
" Shut up!" Fu'ad ya daka mata tsawa yana kallon
yadda ta sauya launi tun karon farko.
"Wannan shine ya baki qwarin gwiwar buga sunana dana
matata a jarida?.....bakisan ta fiki daraja ba?,ta fiki mutunci......ta fiki
duk wani abu da mace ke jin tana taqama dashi ba......su wadanda suka baki
shawarar aikata hakan basu gaya miki waye muhammad jadda ba?!" Ya jefeta
da tambaya yana jin wani tururin bacin rai yana taso masa.
Tayi
matuqar rudewa,ta kuma girgixa qwarai da gaske. An gaya mata....ma'aikatan ma
sun gaya mata,da qyar ta samu suka yadda zasuyi aikin. Sun jaddada mata waye
jadda din,amma a sannan idanunta basa ji basa gani,burinta kawai ta bata mata
suna......ta tona mata asirin da shi kansa baisan dashi ba,ta saka masa shakka
da kokwanto me yawa a kanta.
"Su waye kika aika cikin gidana har dakin
matata!?" Ya sake mata wata tsawar da sai da taji 'yar qwarya qwaryar
gudawa ta hadu a cikin ta ta cure lokaci guda,glass doors din dakin kaman zasu
tsage saboda yadda suka amsa.
Tashin
hankali......kada dai ace ta taka sahun barawo?,da yaushe kuma aka shiga gidan
nasa?......wata shigar akayi bayan wadda mahaifiyarsa tasa ayi?.
Da sauri
ta fara girgiza kai tana dubansa da sabbin hawaye,don gaba daya yatsunta bata
jinsu a gangar jikinta.
"Ban sani ba wallahi.....bani
bace.....saidai.....saidai....." B'am bakinta ya bame ya kuma kasa kama
sunan maamah kaman yadda take da marmarin shaida masa ita ce. Tanason gaya masa
mahaifiyarsa ce,ga sunan a bakinta amma ta kasa furtashi waje,ta dinga kokawa
da harshenta amma kaman wadda gabbai ko rassan maganarta suka samu matsala.
"Saidai me?" Ya tambayeta yana tsareta da idanu
yanason samun ragowar tabbacin da yakeson samu.
"Na gidan jaridan......nice" Maimakon wancan
bayanin ta sake bashi yaqini akan wancan tana sunkuyar da kanta,baqinciki da
bacin rai yana cika zuciyarta. Me ya sameta ta kasa gaya masa sirrin da baisan
dashi ba?,idan ita yasa an mata irin wannan mummunan dukan ita kuma da take
uwarsa tana son taga ya zaiyi da ita.
Idanu ya
zuba mata,yana ji a jikinsa akwai saura......akwai abinda yayi saura.....akwai
abinda jikinsa yake bashi game da ita wanda ya rage bata fada ba.
Saman
qafafunta ya maida kallonsa bayan yaja kujerarsa nesa da ita. Ta sauqaqawa
kanta wahala......don ba qaramin bugu yaso Jordan yayi mata ba da qattin
qwanjinsa. Yaso ya rage mata adadin yawan haqoran dake a bakinta ko zasu zame
mata tunasarwar shigarta hurumin muhammad fuad anan gaba,ya kuma zamewa 'yan
baya izina. Qafar ta tasa tayi suntum cikin qaramin lokaci,alamun mummunan
targade ko karaya sun samu wajen zama. Banda ita din mace ce baya jin iya
wannan dukan ya wadatar dashi,amma duba jinsinta yakeyi.....idan yace zai
zazzage dukka muguntarsa a kanta ba zata wanye lafiya ba. Ya maida kallonsa ga
fuskarta da har ta suntume,kamatunta sun tasa sun soma hayewa saboda munin
marin daya sauke mata,idanunta har sun fara yin ciki
"Zan baki dama ta qarshe da zaki fice daga
rayuwata.....ki kuma sanyawa ranki baki taba sanin wata me suna sabreen
ba.....fu'ad kuwa ki saka a ranki a saqe saqen mafarki kika taba
saninsa.......saidai kafin sannan......na baki wata guda kacal kije kiyi jinyar
qafafunki da fuskarki,zan sake waiwayarki......ba kuma waiwaye na arziqi ba.
Sa'arki daya labaran ba inda suka fita.....yau da newspapers dinnan sun
fita...." Sai ya kada kai daga hagu zuwa dama
"Ko buzunki ba za'a samu ba ina me tabbatar miki da
wannan" Ya qarasa fada yana nunata da yatsa.
"Kije kiyi jinya kafin amsa tuhuma ta gaba......ruwanki
ki gayawa babanki......ruwanki ki rufe bakinki wannan matsalarki ce......amma
inaso ki rubuta ki ajiye.....idan ma kina da plan na guduwa wani guri da kike
tunanin zaki samu tsaro to ki sani.......lahira ce kawai zaki tafi ki kubuta
daga tuhumar muhammad jadda" Daga haka ya miqe tsam yana takawa yana barin
dakin.
Har yakai
qofa sai ya dakata,ya juyo ya watsa mata wani kallo sannan yace.
"Daga yau.....na yanke duk wata alaqa tsakaninki da
maamah......idan kuma baki yarda ba ko kina doubting akai......ki sake koda
kiran layin wayarta ne.....koda sau daya ne" Ya furta yana daga doguwar
yatsarshi dan manuni,sannna ya sanya qafa ya fice abinsa.
Tunda tazo
duniya ba'a taba gwada mata azaba irin wannan ba......tunda uwarta ta haifeta
bata taba ganin qasqancin d'a namiji ba irin na jadda. Inda wanine yau yayi
mata wannan abun ta tabbatar bazaisha ba a hannun daddynta dama ita kanta. To
amma.muhammad jadda fa?,ta sani farin sani cewa wutsiyar raqumi tayi nesa da
qasa. Alfarmarsa ta wuce duk yadda ake tunani,duk arziqi da alfarmar ubanta da
take taqama dasu bai wuce yaron jadda ba. Ta sake tsinkewa da lamarinsa sanda
daddynta da kansa yake bata labarin yadda fu'ad din ya soke masa wata kwangilar
millions of naira,wanda gwamnatin tarayya taso bashi amma jaddan ya fahimci cin
hanci da rashin kyan aikin yayi yawa. Ya fusata a sannan baisan waye jaddan
ba,ya kuma bazama da zummar a nemo masa wayeshi a hada musu zama....saidai
randa ya soma yi masa ganin farko ya kuma zauna dashi da qyar ya qwaci
kujerarsa ta ambassador. Har qasa yakai yana hurwa da neman ya rufa masa
asiri,ya barshi ne bisa sharadin komai zai dinga tafiya bisa adalci da amana,ya
kuma tsaya da iya muqami da dukiyar da Allah ya bashi. Tun daga ranar suka yiwa
juna farin sani,labarin da daddyn nata kuma ya bata ya sanya mata tsananin son
mallakar fu'ad din. Tanason namiji me qarfin izza da mulki gami da iko
takowacce fuska,a duk inda ya tsaya yayi magana za'a dakata a saurareshi,a duk
inda yayi umarni dole za'a bi.....to amma sai gashi dare daya komi ya watse
komi ya wargaje mata daga hannunta.
"Zan iya barinsa kuwa?" Ta tambayi kanta sanda
wata zuciyar ta fara mata saqa da mugun zare.....zuciyar ta fara ayyana mata
daukan BAQAR FANSA da kowanne irin hukunci daya kamata ta zartar kawai a kansa.
_uhmmmm,nidai nace wanda baiji bari ba yaji hoho_
Ido farouq
ya zuba masa sanda yake dawowa wajen. Sai a sannna hankalinsa ya kawo abinda
fu'ad din yayi masa. Cikin dakewa da kuma basarwa yace yana zama.
"Sarkin noma.....na dawo" Sarai yasan magana ya
gaya masa,amma ganin ma ya zaro wayarsa ya soma lalubar wata number sai kawai
ya qyaleshi da duk abinda zaice dashi,illa dai yace masa.
"Ina fatan baka rabata da numfashinta ba"
"Ta samu wannan tsiran saboda batayi musu ko gardama
ba" Yana kaiwa nan ya saka wayar a kunnensa yana magana da daya bangren.
Ya kusa
mintuna talatin yana amsa wayar kafin daga qarshe ya rufe da
"Aikinka na kyau CP.....good job,akwai
zuwaira......akwai harira ko something hajja......yes......yes" Daga haka
sukayi sallama.
Zazzafar
numfashi ya sauke yana aje wayara a gabansa gami da watsa idanunsa saman
glowing beach din da ruwansa ya fara komawa sea of stars,hakanan yashin dake
kwance a wajen ya soma glowing sosai kaman an warwatsa taurari a qasan wajen.
"Wai wanne irin kame kake ne dude?.....har mutum nawa
zaka saka a kulle maka?". Idanunsa da suka masa nauyi saboda tunanin daya
cika zuciyarsa ya janye ya maida kan farouq,ya kafeshi da idanu sosai saboda
tunaninsa ba'a wajen yake ba. Gaba daya tunaninsa ya ta'allaqa a kanta,yana jin
a yadda yanayin wajen ya masa kyau da dadi kamata yayi ace tana tare dashi
yanzu haka a gefansa,ya shaqi daddadan qamshin jikinta.....lallausar fatar nan
tata me wani irin dumi me bawa zuciya da gangar jiki nutsuwa.
"Duk wanda ya taba kiranta da karuwa......duk wanda ya
taba yi mata sharri ko qazafin zina ko neman maza......bazan qyale kowa ba
farouq". Kallonshi sosai farouq yakeyi yana kallon yadda idanunsa suka
jirkice da wani irin giyar soyayya me qarfin gaske. Ya karanci wani muguwar
kwankwada fu'ad ya yiwa giyar soyayyar sabreen din,ta kuma bugar dashi fiye da
yadda ya kamata.
"To amma ai sai ka hada da kanka da kanka a kullewar
ko?" Ya fada yana dage masa girarsa duka biyun sama. Kallon days jefeshi
dashi ya tabbatar masa b'arna fu'ad zai masa,ya sanshi yasan abinda zai iya
aikatawa,don haka yaja kujerarsa baya da sauri yana dariya. Qwafa yaja yana
gyada kai,baisan abinda yakeji ba tabbas farouq da bai qara masa ciwo akan ciwo
ba.
Barinsa
yayi yaci dariyarsa me isarsa kafin ya kira sunansa.
"Yes sir" Ya amsa masa har yanzun lamarin fu'ad da
gaske yana bashi dariya. Yana sassauta masa ne kadai saboda yasan bashi da wani
gurin samun sassaucin sai wajensa.
Sai daya
ware idanunsa a kansa sosai sannan ya tashi ya zauna yana dubansa.
"Me yasa soyayya take haka ne?" Yayi tambayar
sounding serious......saidai kuma abun ya bawa farouq dariya amma ya danneta.
"Me tayi maka kuma?" Ya tambayeshi yana matse
dariyarsa da kyau. Kasa magana yayi don baisan ma yadda zai kwatanta masa
ba,sai kawai ya dora hannunsa akan qirjinsa da yakeji zuciyarsa na azalzalarsa
akanta. Ya dauki wasu sakanni kafin ya iya buda bakinsa a hankali da wani irin
calmness.
"Bansan adadin Lokacin da na dauka ina sonta
ba......amma inaji a jikina ba sai bayan abun nan ya faru ba na fara
sonta.....kaman wani dadadden so ne daya saba dashi.....na taso dashi,aka kuma
haifeni dashi". Sosai maganganunsa ke ratsa farouq......da gaske ne fu'ad
din yana sawun mutanen da suke iya boye so ba ko su daukeshi da sauqi ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 88
88
"Kayi
qoqarin koya mata yadda zata soka........ta fahimceka.......tasan ainihin waye
kai da kuma rayuwarka,daga nan komai zaizo da sauqi......zan baka kowanne kalan
goyon baya da kakeso.....nayi maka alqawari......amma nima kayimin uzuri daya
alfarma daya" Ya fada yana kama hannun fu'ad din.
"Fadi muji dude" Ya fada yana sake jin qaunar
farouq da kimarsa tana ratsashi.
"Duk sanda naga taka kalar haukan soyayyar ka yiwa
Allah karka hanani inyi dariya......i swear wallahi kai babanmu ne ta
nan.....nayi imani da gaske irinku masu shuru shurun nan kunfi kowa zurmawa da
iya rikita mata". Danawa bayan hannun farouq dake cikin nasa duka yayi
yana zame hannunsa sannna ya miqe.
"Ka lallabani farouq......kasan Allah zan daga
aurenka?".
"Iyeeee.....eh ai kayi haka mana,tunda kai ka samu
kanka ka zazzage lalurarka ta shekara da shekaru...."
"Idan bata haukatani ba farouq kai zaka haukatani"
Kawai yace dashi yana yin gaba abinsa. Da sauri farouq din ya tashi yabi
bayansa,don yasan tsaf zai iya tafiya ya barshi a wajen. Tuni suka gaya masa an
biya kudin komai da komai tun kafin suzo ma,harda qarin wasu kudin spare da
yayi ragowa idan suna buqatar qarin wani abun.
★Karo na kusan
barkatai ya qara daga fuskar wayarsa ya kalla yana hadiye wani abu me tauri a
maqoshinsa. Kwanaki kusan takwas kenan rabon daya sanyata a Idaninshi,tun ranar
da sukeja Vaadhoo Island shi da farouq bata sake bari yaga face dinta ba.
Da farko
yayi tunanin zai jure,kwana daya biyu uku hudu ana biyar din yaji bazai iya
ba,yakai bango kaman numfashinsa na shirin masa qaura. Ba ganin face dinta ba
kuma jin muryarta?. Koda ya shiga dakin da nufin gaida anni tanajin alamunsa
take shigewa duvet ta kwanta abinta. Ya fuskanci kaman tana garkuwa ne da anni
wadda ba lallai ta fahimci abinda yake faruwa. Yana jin nauyin anni yana jin
kunyarta,amma ta fara kaishi bangon da yakejin yana dab da ajiye kunyar a gefe.
Wayar
amna ya soma kira yana sanyata ta bata wayar. A kunnensa yakejin sanda amna
take bata wayar amma saita karba ta kife taci gaba da sabgarta. Idan ya kira
amna ta wayar anni tana bashi tabbacin wayar na hannunta,sai mintuna suyita
tafiya babu ko motsinta bare tarinta. Da yaga haka saiya koma kiran annin yasa
a bata,still dai haka take masa,kwanaki uku kenan yau tana masa haka,adadin
kwanakin da lissafinsa yake gaya masa jibi ne yarjejeniyarsu da anni na zuwa
daukota daga macca.
Bazai iya
jure wannan ba......da kansa ya sanya order din wayoyi har guda biyu aka kawo
mata,Falcon supernova iPhone 6 pink diamond edition irin wayar dake hannunshi
kenan. Sai iphone 4s elite gold. Dukkaninsu wayoyi ne masu tsananin tsada da ba
kowa yasan da zamansu ba,saboda ba kowa keda qarfin tattalin arziqin mallakarsu
ba. An qera jikinsu ne da diamond da kuma gold masu tsananin daraja.
Yana jin
cewa idan ya bata wayar ya zamana tana da tata mallakin kanta dole idan ya kira
ta daga din.
Har ya
gama shirin kwanciya tun goma na dare amma kewar nan da yakeji ta hanashi
kwanciyar,ya tashi ya sanya pyjamas dinsa light blue da suka amsheshi sosai ya
sanya flipp flops dinsa ya kwashi wayoyin ya wuce dakin anni.
Tana zaune
abinta qasan carpet dauke da littafin hadisinta da yafi mata dadi akan komai a
yanzun. Tayi kyau kaman wata 'yar baby cikin milk color din Indonesian hijab me
haske sosai daya fidda fuskarta.
Tunda taji
sallamarsa wani abu ya tsarga mata,ya shammaceta sosai,yau ko qamshin turaren
nan nasa da takeji bata jishi ba.
"Barka da dare anni...." Ya fada cikin girmamawa
yana zama saman sofa din dake opposite dinta,kansa tsaye yau duka idanunsa suna
kanta. Ji yakeyi kaman yayi shekara takwas ne bai ganta ba bawai kwana takwas
ba. A yau din har anni ta ankar da hakan,tadan dauke kai kaman bata gani ba
cikin jin nauyi tace.
"Barka kade me babban suna.....mun yini lpy?"
"Alhamdulillah" Ya amsa mata yana maida dubansa ga
amna data tsugunna tana gaidashi.
"Lovey dovey.....barka da dare"
"Barka kadai hamma". Sak tayi,bata da niyyar
magana kowacce iri ta hadasu,amma gaisuwar anni data amna ta daureta,dole ta
gyara zamanta daidai sannan tace
"Barka da dare,ina yini?" Kowanne gaba ta jikinsa
sai data amsa sautinta,bai taba sanin yayi masifar kewar muryarta kawai bama
sai yanzu,amma duk da haka ya dake yana hade fuska.
"Bazan amsa ba.......sau nawa ina kira a wayar amna
nace ta baki?.....sau nawa ina kiran wayar anni a baki saiki ajemin
waya.....saboda kin rainani?". Dukka duf dakin yayi,nauyi ya kama anni da
kunya......yayin da sabreen din wata masifaffiyar kunya nauyin anni da fargabar
kada ya ballo magana gaban annin ya kamashi. Amna kanta sak tayi,saita miqe
kawai ta fara lalubar hanyar fita kada ayi fadan soyayya a gabanta,duk abinta
itama wani lokaci tana kunyar annin.
"Anni" Ya kira annin kai tsaye yana maida dubansa
sashenta.
"Muhammadu" Ta fada cikin jin nauyi itama.
"Ta rainani anni.....a qasana take amma tana iya aje
waya idan na kirata".
"Baki kyauta ba takwara....bakisan aljannar mace tana
qarqashin qafar mijinta ba?.....kada ki sake kinji ko?". Qasa tayi da
kanta zuciyarta na karyewa tare da tarin haushinsa. Tun ranar da taga fareeda
kwance a jikinsa ta tsani ganinsa ta kuma tsani ganin fareedan itama. Dama can
sun shirya abunsu ne shi yasa da suka gama yawace yawacensu ya kori Jordan ya
kaisu can saboda suna da agenda din haduwa......sannan daga qarshe saboda
zalunci yazo yayi mata mummunan fyade irin wannan......ya karbi abinda sam ba nasa
bane.
"In sha Allah anni......kayi haquri". Ta fada a
sanyaye ba tare data kalleshi ba. Wani abu ya hadiye a wuyansa,shi ba haka yaso
abun ya tsaya ba,ba haka yakeso ba.....sam bai gamsu ba. Yana tsaka da wannan
tunanin yaga ta ajiye littafin ta miqe tana cewa
" Zan dauko ruwa kitchen " Tayi maganar ba tare da
yasan dawa take ba.....izinin wa take nema?,saidai kawai ya tsinci anni tana
cewa.
"To ba laifi" Sai ta taka a sannu ta fice. Yadan
bita da kallo kafin ya dauke kanshi,shi ya sani ba wani ruwa da zata sha,kawai
ta aikata hakanne don kada ta zauna inda yake.
Kwata kwata
zaman dakin sai ya yaji ya gundureshi. Ya miqawa amna kwalayen wayar wadda
shigowarta kenan yana cewa.
"Ki ajiye mata idan ta shigo ta zaba" Sannan ya
miqe yana cewa anni.
"Jibi zanje na taho da maamah daga saudiyya.....kwana
biyu kawai zan dawo in sha Allah"
"Ma sha Allah,hakan yana da kyau,Allah yayi
albarka,banda banbancin fitowar visa ma ai da tuni.muna nan a tare,Allah ya
kaika lafiya" Amsawa yayi da ameen yana fita a dakin gami dayi mata sai da
safe.
Guri
kawai ta samu tayi zamanta cikin kitchen din,zaman nan din ya fiye mata zama a
dakin,qarfin halinsa kawai take gani,ga mari ga tsinka jaka?,ko kunyar annin
bayaji kansa tsaye yake kai mata qararta?.
Sam sam
yaji ya gagara wucewa dakinsa kaman yadda yayi niyyar yi,duk da yau din ransa
yadan baci da ita. Sauya akalarsa yayi zuwa kitchen din,yanason ya tabbatar
tana can din ko kuwa?,me ma takeyi?.
Idanunsa
ya zube a kanta,tana gaban sink ta kunna famfo kawai ta tara hannuwanta kaman
me lissafin adadin digon ruwan daya fado hannunta.
A hankali
yake takawa don bayason ta jishi,ya samu nasarar isa dab da ita kuwa kafin
mayataccen turarensa ya shaida mata isowarsa. Ta motsa da hanzari da nufin
waiwayowa,saidai kuma ya rigata da hanzari da kuma zafin nama yayi mata
kyakkyawan masauki cikin qirjinsa. Ta baya ya rungumeta tsam,zuqar farko da ya
yiwa jikinta daddadan turarenta ya ratsa qofofin hancinsa ya kuma tayar masa da
duk wani ajiyayyen tsumi dake jikinsa. Numfashinta ya kusa daukewa saboda
yanayin jikinsa da taji ya fara canzawa,maimakon ya barta ta zame yadda take ta
qoqarin yi sai ma ya sake manneta da jikinsa yana zura fuskarsa tsakanin
wuyanta,ya kuma tura daya hannun nasa ta saman rigarta yana qoqarin kaiwa ga
wancan wajen.
Hannunsa
take qoqarin riqewa....bai hanata ba amma kuma ya soma zare duk wani qarfi da
take dashi saboda dumin numfashinsa da yake sakarwa sasannin wuyanta zuwa cikin
kunnenta,take kowanne sashe na jikinta ya dauki rawa harda muryarta.
"Ka bari don Allah" Ta fada cikin rawar murya,sai
ya dakata cak yana hautsinota ta dawo suna fuskantar juna. Da rinannun idanunsa
da suka fara canza kala yace mata
"Ke kinsan girman Allahn ne?" Yafada yana dage
mata girarsa duka biyun. Samun kanta tayi da kasa kallonshi,saita kauda
fuskarta gefe. Hannu yasa ya dawo da fuskartata daidai saitin tasa yana
dubanta.
"Uhnnn.....nace kinsan girmansa?.....kinsan aure
dukansa sunansa aure a wajen Allah?,kina matar aure amma baki iya kula da
mijinki ba?.....baki iya komai bafa.....idan nace komai ina nufin komai irin na
mata....matan ma matan aure........kinaso na mutu ne sabreen?" Mamakinsa
ya kamata,ya gama rungume rungumensa sannan yanzu ya mata wata magana ta
daban?.
"Bakya kishina ne?"
"Sonka nake da zanyi kishinka?" Ta fada a tsiwace
tana murguda bakinta.
Idanunsa
ya lumshe ya kuma budesu kusan lokaci guda,siririn murmushi ya kubce masa yana
kallon baby face dinta da danjaririn bakinta data murguda masa. Ba abu me dadi
ta gaya masa ba,don maganar ta sokeshi a tsakiyar zuicyarsa,saidai kuma ta masa
wani mugun kyau,kuma yaji ta bakinta ko ba yawa a wannan fannin.
Sake
jawota yayi ya matseta da kyau kaman zai rabata gida biyu,ya sanya yatsarsa
guda daya ya fara zagaye labbanta sai tayi sauri zata turasu ciki,ya shammaceta
ya hada mata da yatsan nasa,dole ta saki labban nata,abinda ya bashi daman riqo
fuskarta da kyau ya kuma hade labban nasu waje daya.
Wani irin
sarrafasu yakeyi a tausashe da nuna zallar qauna,abinda bata zata ba daga
gareshi. Ta dauka anytime kiss abune me zafi ga labba,cikin minti biyu taji
kowacce gaba a jikinta tana saki,kafin kwanyarta ta ankarar da ita suna kitchen
sakamakon qarar qofar kitchen din. Tureshi tayi da sauri,ta saka bayan hannunta
tana goge labban nata. Da fushi a muryarta tace.
"Banason wannan abun.....wannan ai qazanta ce"
Tayi maganar ne da harara,harara data fidda farare sol din idanunta. Kamar dafi
haka yaji ta zuba masa jikinsa dukka ya amsa,ya shammaceta ya jawota ya sake
matseta yana same hade bakunansu,ya tattara miyau din bakinsa duka ya dure
mata. Bai barta ba sai daya tabbatar ta hadiye sannan ya sake boyeta a qirjinsa
sanda ta saki siririn kuka.
"Am so sorry.....inason mu sake zama abu daya ne bayan
wanda muka sake zama din.....amma tunda na miki ba daidai ba.....biyani yawu
na" Ya fada yana qoqarin sake kai bakinsa cikin nata. Ta gama fuskantar
wayo ne kawai yake son ya mata,don haka ta fara qoqarin hanashi amma bai bata
dama ba,haka ya dinga zuqe duk wani yawu dake bakinta sai da numfashinsa ya
fara fita daban daban daga qirjinsa sannan ya sake ta yana maida numfashi.
"Duk abinda na miki idan bakiso zaki fara biyana daga
yau......ki karbi wayarki a hannun amna" Yana kaiwa nan ya juya yana barin
kitchen din saboda jin yana neman loosing control dinsa. Ya riga yayi
alqawarima ransa indai ba takura yayi maqurar iyaka da zai iya shiga halaka
ba.....bazai sake karbar komai ta qarfi ba....zaiyi iya yinsa ya amintar da
ita.
Idanunshi a
rufe suke,sam bai kula da farouq dake zaune a parlor din ba sai da yaji
muryarsa yana cewa
"Ranka ya dade sir" Yana dunqule hannunsa irin na
girmamawa. Kallo daya ya masa ya fahimci zai wahala bai shiga kitchen da zummar
dauko wani abun ba idanunsa sunyi masa gamo,don haka baima tsaya biye ta tasa
ba ya wuce daki abinsa yana jin dariyar farouq din. Saidai qasan ransa yasha
alwashin tasu ce shi da farouq din,yaga alaman bazai taba barinsa ya sake
ba.....baya jin zasu qare zamansu a Maldives a wannan gidan....musamman da
maamah ke dab da isowa,yana jin gidan tabbas ya musu kadan ,don haka ba wanda ya
sani bayan ya sakarwa kanshi ruwa ya fito,ya yiwa Jordan maganar duba musu wani
apartment din a siya zuwa nan da jibi yalwatacce sosai da yafi wannan.
Sulalewa
tayi a nan tana dafe da kanta,da qyar ta iya saita kanta ta miqe tana gyara
yamutsatsen hijabinta da tuni ya saukeshi daga kanta. Can qasan ranta tana
mamaki,wanne irin tsafta ne dashi haka?,duk sanda yayi kusa da ita irin haka
qamshin mint leaves ne ke fita a bakinsa,wanda da alama ya kama bakin nasa
sosai,wanne irin freshener na baka yake amfani dashi haka?. Tsaki taja qasan
ranta tana ture wannan tunanin daga ranta,ta matsa gaban sink ta ringa watsawa
fuskarta ruwa don kada ta koma anni ko amna wani ya gane wani abu,sai data
tabbatar taji daidai sannan ta dauki gorar ruwa daya ta fita a kitchen din.
Farouq din yasan tabbas zata fito,bayaso kuma taji kunya ko nauyinsa,don haka
sai ya wuce dakinsu bayan shigewar fu'ad,wannan ya bata daman shigewa dakinsu
salin alin.
Qin yarda
tayi ta hada ido da kowa kota zauna,sai tayi shigewarta duvet kawai tana
qundundunewa waje daya. Amna tana toilet,batasan kuma ta shigowa ba sai data
fito. Cikin hanzari ta qaraso dakin tana cewa.
"Albishirinki adda?" Daga can qasan maqoshinta ta amsa da
"Goro". Tana bin amna da kallo wadda ta dosota da
kwalayen waya guda biyu ta zauna gefanta.
Duka biyun
ta zaresu daga kwalinsu,bakinta ya kasa rufuwa.
"Ya Allah kaban miji irin hammana.....you're luckiest
woman adda....." Idanu sabreen tadan fidda
"Bakwa kunyar anni amna?,yanzun da tana dakin haka zaki
ce?" Dariya ta qyalqyale dashi.
"Ki zabi daya.....idan nice ma duka zance
inaso......falcon supernova.....the most expensive phone in the world.....it's
worth more than 77mil in naira......irinta hamma na ke using,ita kuma wannan
itace ta biyun ta a tsada" Amna ta fada tana juya duka wayoyin tana duban
sabreen.
Adadin
kudaden kawai sai da suka sanya kanta yayi tsawa,million saba'in da bakwai?,ina
zata kai irin wannan wayar?,wacece ita?,waye ubanta a Nigeria?,idam shi ya riqe
matsayinsa yakai ne.....arziqinsa yakai....amma kuma ita fa?,ita da take dorin
dosano?,kwanaki nawa ya rage mata ra barshi ma kwata kwata?.
Numfashi taja
ta lumshe idanunta tana kullesu,ba zata iya gayawa amna kai tsaye bata so
ba.....ba zata kuma karba ba,don haka tace.
"Ki ajiyesu,zan duba gobe"
"Done.....amma please ki dauki irinta hammana please
adda"
"Naji" Tace da amna don kawai ta bata wuri ta
shaqata.
_nikuwa nace ya kamata sabreen ki karbi wayar nan don ki
gigita surukarki hajiya maamah da ita,kin bata tabbacin mallakar fu'ad da
taketa fafutuka taki ce kenan_😂😂😂
Tana sane
ta narke tun daga daren ranar har wani daren,tayi qaryar zazzabi don kada anni
tace taje suyi sallama da fu'ad da zai tashi zuwa macca kai tsaye gobe da safe.
Ta samu nasara kuwa.....don har ya shigo ya musu sallama tana kwance tana
baccin qarya.....duk da cikin jikinta tana jin idanunsa a kanta suna yawo,ya
juya ya fice su anni suna taka masa.
_Turqashi......maamah bisa hanya_
_komai fa yana shirin faruwa me karatu_
_idan nace komai.ina nufin komai ma😂_
_pages din gobe masu zafi ne,kada ka yarda su wuceka_
_Ya zata kaya tsakanin maamah da sabreen ga anni a
tsakiyarsu?_
_yaya zata kaya sanda maamah ta fahimci zazzafar soyayyar
sabreen a idanun susutaccen d'anta?_
_shin zata iya dauka?,ko zata cika qudurinta na rabasu?_
_Shikenan fareeda ta haqura?,ko zata sake wani motsin?_
_waye da waye ne suka shiga hannu?_
_ita kanta fareedan ta sha ko kuwa?_
_akwai ragowar zafafan al'amura fa masu karatu,muje zuwa ga
gangarar labarin_🧏🏽
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 89
89
Iska me zafi
ya furzar daga bakinsa yana dan dafe goshinsa,duk wani energy nasa yaji yana
tafiya,ta yaya zai iya tafiya wani qasar ba tare da sunyi sallama da ita ba?.
Ya sani ya kuma fahimci tana sane duk tayi hakan,wayarma daya batan baiga
alamun ko guda daya a hannunta ba. Iska ya sake furzarwa yana jin tsoron kada
dai furucinta na rannan ya zama gaske da tace bata sonshi. Sai ya zura hannunsa
a aljihunsa ya fito da wayarsa ya fara kiran number amna.
Ita da
anni ce kawai a dakin,annin ita ta karbi wayar saita miqa mata tana cewa.
"Hammanku ne......basu tafi ba kenan" Ba zata iya
musu da annin ba bata kuma fita ba bayan ta bata wayar bare ta aje wayar yadda
ta saba masa. Ta latsa ta sanyata a kunnenta,ta motsa labbanta a hankali tana
amsa yin sallama.
Har
tsakiyar zuciyarsa yaji saukar sautin sallamartata. Yayi jarumtar daidaita
yanayinsa don bayaso ta fahimci komai,don yana son komai zai gaya mata ta
daukeshi da muhimmanci.
"Ina kika shiga?" Ya mata tambayar a gajarce data
rasa amsar da zata bashi. Shuru tayi tana kame kamen abinda zata gaya masa,bata
samu ba har ya sake cewa.
"Kinsan tafiya zanyi yau really?" Can qasan
zuciyarta tayi qaramin tsuka tana cewa
"To mene ruwana da tafiyarka?,ka wuce mana ta can ma
karka dawo Maldives,amma a fili sai ta zabi jan bakinta tayi shuru.
"Alright......yayi kyau....ina wayar dana bawa amna ta
baki?,baki dinne bata yi ba?". Ya sake tambaya da wani irin shan qamshi da
bata taba ji ya mata ba,hakan sai ya mata kwarjini gami da taba zuciyarta.
"Ta bani" Ta amsa masa a hankali kaman wadda
batason tayi magana. Amsan ta bashi haushi kadan,don shi daya yasan yadda ya
matsu da jin muryarta amma taja wayar ta ajiye.
"Bakiga daman amfani dashi ba kenan?.....well....bazan
miki komai ba a yanzun.....amma kika sake har na dawo na samu wayar a yadda na
baki ita.....sai nayi punishing naki ta hanyar da bame iya karbanki......and
idan ma kin bude kin fara using da ita....if kika ce zakimin abinda kikemin a
wayar anni da amna bawai kin tsira bane.....take care of your
self......byee" Ya fada yana sauke wayar. Sai a sannan yaji zuciyarsa ta
koma daidai,duk da ba irin wannan sallamar yaso suyi ba,amma at least ya samu
nutsuwa kadan. Bayaso ya fiya zafafa mata da yawa....don baida tabbaci ko
yaqinin zuciyarta ta karbeshi,saidai ko meye yana da yaqinin bazai qyelata haka
ba,sai yayi mata dashe da kuma ginin da bazai kankaru ba.
Wayar tabi
da kallo kafin ta ajiyeta a gefanta. Sau tari idan yana wani abun sai zuciyarta
ta dinga gaya mata plan ne kawai da siyasa irin ta 'yan kasuwa,kamar kawai
yanaso yaci gaba da mata wayo yana amfana da jikinta ne. Har yanzu ta gaza
gasgata kanta wai mutum kamar muhammad fu'ad da mutunci ko arziqi ba shine
silar gamuwarsu ba ace dare daya don kawai ya amshi budurcinta ya koma haka ba.
Kulawa qauna soyayya da wani irin mayataccen yanayi da bata taba ji ko gani ba.
A duk mazan da sukayi alaqa dasu a baya bata taba ganin wani abu na musamman
kebantacce tattare dasu irin wannan ba. Da gaske wannan shine son?,da gaske
wannan din ake kira da soyayya ko kuwa yaudara ce zallarta?.
_to masu karatu ku bata amsa_
★ *_Makka/Jeddah_*
Tafiyar awa
biyar zuwa shida ta kaisu garin jedda,a nan ya tsaya yayi wanka ya saka hirami
ya dauki niyyar umararsa. Daga nan kuma lafiyayyen train ya daukesu kai tsaye
zuwa makka.....motar da aka tanadar masa ta qarasa dashi masauki cikin hotels
mafi tsada dake dab da harami.
Fairmont
makkah clock Royal tower nan ya zaba,ko maamah dinma yasa an maidata can,hotel
ne dake da kusanci sosai da haram,kai tsaye daga dakinka kana iya hango ka'aba.
Baida gurin sauka duk zuwan da zaiyi sai nan din,saboda samun kusanci da Allah
da samun daman yin addu'o'insa sosai koda cikin dare ya farka. Sau tari yakan
jima gaban window din dakinsa yana qarewa dakin Allah kallo,cike da shauqi da
tsoron azabarsa da kuma fatan samun rahamarsa,yana jin inama yayi zamansa a nan
ya qare rayuwarsa.
Nutsuwarsa
da samun salamar ruhinsa daban yake jinsu a ransa duk lokacin daya shigo
wajen,yana jin kansa sosai kusa da Allah,don haka koda ya iso wucewa yayi kai
tsaye yayi dawafi da sa'ayi yayi sallarsa raka'a biyu ya sauke umararsa. Bai
nema ganin maamah ba sai daya sauke faralin umran da bayajin zata isheshi. Zuwa
yanzu baisan sau adadin nawa yayita ba.....bayajin kuma zai daina yin nata
muddin da numfashi a jikinsa da kuma damar zuwan.
Dakinsa
ya koma royal suit ya sallami abdulbasit da abdul gaffar da abdus sabur wanda
su ya sanya suzo su zauna tare dashi. Hiraminsa ya cire ya nema wasu kayan ya
sanya yana duba lokaci. Akwai gajiya sosai tattare dashi,yana buqatar ya hutawa
kwanyarsa sosai don ya samu space din yadda zai iya tunkarar ko meye maamah
zata zo masa dashi. Labulen dakinsa ya daga,idanunsa suka sauka akan dakin
Allah,wajen tarwai yake da cikakken haske kamar kullum,da tarin bayin Allah
masu neman duniya dama lahirar gaba daya. Bayason wani babban abu ya faru
tsakaninsa da maamah a irin wannan wajen,dole yana buqatar neman taimakon
Allah.
Nannuyar
ajiyar zuciya ya sauke sanda fuskarta ta dawo masa tarwai cikin idanunsa.
Idanunsa akan ka'aba din,ya sanya hannunsa saman qirjinsa ya dafe yana jin
yadda qirjin nasa ya cika da soyayyarta,a hankali ya furta.
"Ya raheem......kada ka bawa mahaifiyata galaba a kaina
muddin da sabonka da kuma son zuciya tazo". Sai ya dakata yana jan
numfashinsa sosai.
"Ya ubangiji.....kaine mahaliccin zukata.... Kaine ke
iya jujjuyasu a duk sanda kakeso,ya rabb,kafin kowa sanin menene abinda ke
zuciyata na ainihi a kanta,ban aikata mata komai ba don na zalunceta ko na
cuceta ba,ban aikata mata komai saboda qiyayya ko abisa sanina ba....ya
rahman....ka sanya mata matsananciyar soyayyata a zuciyarta,ka sanya ta soni
irin son da nagartacciyar uwa kewa d'anta......irin son da bashi da
misali.....irin soyayyar da na jima ina fata da burin samu daga wajen macen
aurena.....ya ubangiji,na gode maka abisa kowacce ni'ima da kayi a
gareni.....na yadda cewa mahaifiyata itace jarrabawar rayuwata......na rasa
soyayyarta soyayya ta ainihin da aka santa daga zuciyar uwa zuwa
'ya'yanta.....ya Allah yadda kayimin madadi da anni.....na roqeka kayimin
madadi da ameenatu sabreen.....ka maidata sanyin idaniyata......Allah ka
azurtani da salihan yara ta tsatsonta.....ka sanya albarka cikin kowacce
tarayya da zanyi da ita....Allah ka wankemin idanuna da samun qarin 'yan uwa
nagartattu bayan su musaddiq,wato yaran da ameenatu zata haifamin" Ya
qarasa addu'ar labbansa suna sanyi,zuciyarsa tana jin wani irin sassauci da
sauqi,a take kuma sai kewarta ta cikashi. Baisan me ya sanya dukkanin burinsa a
yanzu ya fara karkatawa kan samun 'ya'ya ba......abune daya jima a ranshi,amma
halin maamah da yadda ta watsar da rayuwarsu ya kashe wannan burin. Yana ganin
duk macen da zai dauko ma haka zata kasance akan 'ya'yansa kaman yadda maamah
tayi musu ta kuma yiwa abbansu.
Sakin
labulen yayi a hankali,yana ji a jikinsa tamkar dukkanin addu'o'insa sun
amsu,sai ya koma ya zauna bakin gadonsa yana daukan wayarsa.
Maamah din
yaso kira don ya shaida mata ya iso,amma cikin rashin sa'a sai ya kasa samunta.
Hakan ya masa dadi,don ko ba komai zai samu ya matse gajiyar daya debo,don haka
ya aje mata tex kawai,sai ya tsinci kansa da neman layin wayar sabreen din.
Bai taba
zaton zai samu wayar a bude ba,bai dauka zataji warning dinsa ba,amma ga
mamakinsa dab da zata tsinke aka daga. Lumshe idanunsa yayi yana jin qarin wani
sassaucin da rangwamen yana sauka a zuciyarsa,ya koma da baya ya kwanta akan
gadon bayansa bayan ya sanya pillow qasan kansa.
Shuru kawai
tayi tana sauraren iskar dake fita ta wayar.
"Baki iya sallama ba?.....me yasa kullum kike maida
kanki yarinya sosai?" Ya tambayeta a tausashe yana jin ba dadi baqin
halayenta. Ta maida kanta wata sokuwa a gabansa,ba dogon magana sam.....musu ko
tsiwarma sai taga dama takeyi masa su.
"Assalamu alaikum" Ta samu kanta da masa sallamar.
Qasan ranta a tsorace take da maganansa kadan kadan. Tanaso su rabu ba tare
daya sake taba jikinta ko ya kasance da ita ba......amma ta duba ta dubo ba
wani hanya daya rage illa ta bishi ta yadda ya bullo mata,ba tare daya ankara
ba zai wayi gari babu ita.
Wani
sauti na daban yakeji yana shiga kunnensa tamkar yau ya fara jin amsuwar
sallama.
"Amincin Allah kema ya tabbata a gareki
DUNIYATA.......gani kusa da dakin Allah.....me kike buqatar na roqa
miki?". Ya fada da wani kwantacce kuma sassanyan sauti da shauqi da kewa
suka cikashi.
Har cikin
jikinta taji maganarsa ta mata dadi,tana da tarin buqatun da zata roqa a wajen
Allah idan har qaddarar zuwa wajen ta tabbata a kanta. A yanzu dukka ta qosa
subar Maldives,tana jin nauyin tambayar amna wanne guri zasu je next.....amma a
nata zabin a ture dukka kowacce qasa a barta a tsakanin saudiyya zuwa madeena.
Tana tsaka da wannan lissafinne taji muryarsa yana cewa.
"Na roqo ubangiji yasa ki soni....irin matsanancin son
da ba zaki iya rayuwa ba tare dani ba.......na roqi Allah ya sanya ki zama
madawwamiyar ni'ima a gareni......na roqeshi kada ya baki ikon barina koda kina
da nufin aikata hakan.......ya mallakamin rayuwarki gaba daya daga farkonta har
qarshenta.......sannan na roqeshi ya bani 'ya'ya masu yawa ta jikinki.....duk
shekara so samu ki haifemin tagwaye ko uku uku......"
"Please mana" Batasan sanda ta tsaidashi da fadin
wadannan kalmomin ba. Tunda ya fara jero mata abinda ya roqa din zuciyarta ke
wani irin bugu,ta sani gurin da yake wajene da babu wasa a cikinsa.....wajene
da komai ka roqa amsashshe ne a wajen Allah......tana tsoron kada addu'arsa ta
cita.....kada ta kamata,idan hakan ya kasance ina zata saka burin rayuwa tare
da 'yan uwanta bisa kyakkyawar rayuwa?.
Dan qaramin
murmushi ya subuce masa yana jiyo alamun tsoro cikin sautinta.
"Tsoron me kike haka?,akwai cutarwa cikin
addu'ata?" Ya tambayeta yana ji a ransa inama hirar zatayi tsaho
tsakaninsu.
Kai ta
girgiza kaman yana gabanta,da gaske tsoro yana sake cikata.
"Wannan son kai ne.....zallar son kaine a cikin
addu'arka,ka roqi Allah wani abun daban ba wannan ba" Tayi.maganar da dan
hasala a muryarta tana ganin kaman da gayya yayi hakan. Boyayyen murmushi da
bai bari taji sautinsa ba ya subuce masa.
"Me ruwanki da abinda zan roqa Allah yayimin?"
"Ina da ruwa dashi.....saboda a kaina ka roqi
ubangiji...."
"Ke kuma kina tsoron hakan ya tabbata?.....to idan akan
wata daban na roqa fa?" Shuru ya ratsa kunnensu na wasu sakanni kafin yaji
tace
"Wannan kuma ruwanka bana sabreen ba" Ta samu
kanta da fada,sannan ta gimtse wayar tana kasheta gaba daya.
Yaji saukar
layin nata,sai ya zame wayar daga kunnensa murmushi yaqi barin fuskarsa. Me
yasa tun asali baiyi dabarar bata waya ba kaman haka ya kuma kafa mata sharuda
ba,haka hira da masoyi take da dadi dama?. To amma wani hanzari ba gudu
ba.....me yasa tayi shuru sanda yayi mata tambaya ta qarshe kafin tace
ruwansa?.
Maido
fuskar wayar yayi saitinsa,ya rubuta mata gajeran saqo ya tura mata,ya koma ya
kwanta rigingine wayar ba rungume a qirjinsa. Wani murmushi ke fita saman
fuskarsa kadan kadan,zuciyarsa cike da fatan saisaita kansa akan
yarinyar.....don da haka ne kawai zai saitata a hanyar da yakeso ta tabbata a
kai.
Shidai
baisan ya akayi bacci yayi awon gaba dashi ba,saidai ya cika mafarkansa
duka,cikin kowanne gani da zai mata cikin qauna soyayya da kuma kulawa. Harda
wanda ya gansu kewaye da yara qananu masu kama dashi sosai. Wannan mafarkin shi
ya haska asubarsa,ya shiga bandaki ya daura alwala cike da wani kwantaccen
farinciki qasan ransa.
Cikin
jallabiyya 'yar Indonesia fara qal ya shirya ta maza,ya shafe jikinsa da
lallausan turarensa ya saka hular tashi ka fiya naci saman kansa fara qal
itama,ya dauki tasbaharsa counter data kasance farar itama.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 90
90
Wayarsa ya
zura a aljihunsa bayan ya duba number dakin maamah. Kai tsaye can ya nufa yana
tafiya da cikakkiyar nutsuwa a tare dashi,bakinsa dauke da ambaton Allah.
Yanaso ya samu sahun gaba gaba,wannan ya sanya yake tashi da wuri koda
yaushe,ya kuma isa masallacin da wuri.
Kallon
kallo suka yiwa juna shi da maamah din,alamu sun nuna tashinta kenan a bacci.
Bata ce masa komai ba ta saki qofar ta juya zuwa ciki ya bita a baya. Guri ya
samu ya zauna yana duban dakin dake cike da kaya wanda ya tabbatar tsaraba ce.
Yaushe ma taxo?,yaushe ta samu daman yin ibada sosai har ta fada yin wata
tsaraba?. Duk abinda zata siya din ba abinda bata dashi a gida,amma fadan hakan
kaman laifi ne a wajensa.
Bandaki ta
shiga ta daura alwala sannan ta fito,tana sauya hijabin jikinta ya soma gaidata
kaman yadda ya saba cikin bata haqqinta na uwa daidai misali na girmamawa.
"Ka shigo tun jiya.....sai yanzu aka baka daman zuwa
inda nake?". Idonsa ya kawar,shi yasan ko.meye zai faru tsakaninsa da
maamah din bame sauqi bane,saidai ko meye ya gayawa Allah yana kuma da yaqinin
komai zaizo masa cikin sauqi.
"Nayi qoqarin kiranki ban sameki ba,na aje miki saqo na
dauka zaki amsa,banyi zaton a irin lokacin zan sameki a daki ba shi yasa na
koma na huta,sai bacci ya daukeni" Ya fada a taqaice. Qwafa kawai taja
tana qare masa kallo a fakaice. Ita kadai tasan me takeji a ranta,ita kadai
kuma tasan me ta shirya zata aiwatar.....tana ji a ranta idan har bata sanya
fu'ad ya auri fareeda ba lallai ta cika lusara asararra,wala'alla fareeda din
itace wannan hasken nasarar guda daya da boka ya mata albishir dashi.
Har ya gama
shiryawa suka fice tare bata sake cewa komai ba,dama ba wani sabo ko shaquwa
tsakaninsu ballanta hira me kama da irin wannan ta biyo baya.
Zata iya
cewa bata taba samun sallar asuba irin haka ba kaman yau,basu bar masallacin ba
sai da gari yayi haske,suka hadu gaban hotel din nasu ya dauketa yin breakfast
duk da akwai bada breakfast a tsarin hotel din nasu.
Ba wani
abu ya karba ba illa coffee,itakam abubuwa da yawa yasa aka ajiye mata,yana
sipping coffee din nasa amma hankalinta yana kanshi. Inama ace wannan kulawar
ita daya a duniya yake bawa irinta?,inama yadda suka zauna a haka haka yake
zama da ita koda yaushe yana kula da duk wani motsinta......yana jira yaji
umarninta ko haninta?.
"Muhammadu" Ta krashi bayan ta gama tauna yadda
zata fuskanceshi. Burinta a yanzu bai Gaza ganin fitar sabreen cak daga
rayuwarsa ba. Da idanu kawai ya amsa mata ta hanyar kallonta.
"Wacce irin mace kake aura mara hankali da tunani kuma
mara kirki Muhammadu?". Gaba daya sai maganar tazo masa a bazata,ya kasa
kuma fahimtar abinda maamah keson cewa.
"Banda yarinyar nan bata da kirki bata da mutunci
batasan girman uwar mijinta ba.....bata taba kirana ta gaidani ba?,bata taba
tambayar lafiyata ba.....bata ma taba nemana ba wai sunan tana auren d'ana?,ni
kuwa wallahi ba'a haifi diyar da tana auren dana kuma zata min riqon sakainar
kashi ba" Ta fada cikin fada sosai tana dan dukan table din da suke kai
kadan.
Zame
hannunsa yayi daga jikin mug din yana zubawa maamah din idanu. Zaren
tunanukansa suna qulluwa waje guda cike da wani irin mamaki. A nan dimma akwai
wani qullin?, ya tambayi kansa da kansa. A abinda yake kallo akwai cikakkiyar
fahimtar juna tsakanin maamah da sabreen wanda shi ya zama silar daukota zuwa
rayuwarsa,a yanzun me ya bata wannan alaqar da jikinsa ya jima yana gaya masa
gurbatacciya ce?,to kodai zai samu wani hint din a nan ne?.
Tabbas
inda a watannin baya da suka shude maamah ta fadi haka akan sabreen bazai
dameshi ba.....in fact ma zai dauka ta fara gane wacece menene kuma
halinta,amma kuma a yanzun sai yaji kalaman kaman sunyi tsauri da yawa. Ya
shirya tare mata fada ko batanci kowanne iri ne kuma koda waye,don haka ya
gyara zamansa yana fadin.
"Maamah.....inajin kinfi kowa sanin wacce iri ce
sabreen.....tunda daga hannunki ta fito,kuma na tabbatar ba zakimin zaben tumun
dare ba.....amma maganan waya bata da waya,duka wayoyinta suma hannuna".
Har tsakiyar kanta taji wani abu ya tsarga mata,wato ita yarinyar zata gwadawa
bariki ta bashi wayoyinta?,a tunaninta yin hakan shine zai sanya ta tsallake
tarkunanta?. Ta jima tana zaton salwantar da wayoyin tayi,wannan yayi saving
nata bata taba gwada Kiran layukan ba,inda ta kira din kenan yana iya zargar komai
ko ya binciko komai?.
"Sannan kiyi haquri zan mata fada zata gyara" Ya
sake fada yana kallon reaction na maamah din. Yadda ta daga kai da sauri tana
dubansa ya sake bashi wani qarin percentage na zarginsa a kanta. Yaushe alaqa
tayi nisa tsakaninsu da yake kareta?,yaushe ma duka duka ta kirashi ta masa jan
kunnen ya kula da ita?,bariki ce ko nata kalar tsubbun ta shayar dashi kaman
yadda jikinta keta bata zata aikata haka?.
"Ai karma ta gyara....ni d'ana bazai auri mace daya ba
ballantana ta samu daman juyashi da zaton nata ne ita kadai,don haka ka
shirya........na zabar maka fareeda mazaunin matarka ta biyu......muna komawa
da sati biyu kacal zaayi komai a gama.....don banajin tafiyarka da sabreen
zatayi nisan zango,akwai canje canjen dabi'u da halaye da nake ji a tattare da
ita" Sosai yake kallonta,ba kuma don komai ba sai don maganganunta masu
kama da almara. Auren fareeda wannan yasan wani abune da bashi da maraba da
tatsuniyar gizo da qoqi,uwa uba ma fareedan dukkaninta ba damuwarsa bace,don
tana under control nashi,kowanne motsi nata yana sane dashi.....abinda kawai
yaja hankalinsa shine zancan sabreen. Wanne sauyin halaye take ji game da
ita?,meye dalilinta dukka na damuwa da al'amuranta?. Wanne laifi mutumin da
baka jinsa ko ganinka yayi maka da zata dinga zarginsa da aza masa laifi
kacokam haka?.
"Kar kayi kuskuren cewa zakamin gardama akan auren
fareeda,nasani sarai shurunka yana nufin abubuwa da dama.....muna dab da
muhallin amsa addu'a,zanje gaba ga Allah na roqeshi ya fiddamin haqqin
haihuwarka da nayi" Idanunsa ya
lumshe maganganunta suna sukarshi. Baisan me yasa ako da yaushe barazanarta iri
guda bace a kansu,yadda ta damu da neman haqqin Allah a kansu bata damu da nema
musu albarka haka ba?.
"Relax.....cool down.....badai fareeda bane
matsalar?" Kai ta jijjiga
"Itace"
"Done" Ya fada da wata ma'anar ta daban. Shi kadai
yasan me ya sake shiryawa me kuma zaiyi. Binta da kallo yake kawai sanda taci
gaba da cin abincinta,yana hangen tarin sassauci data samu can boye cikin
fuskarta da karbar zancan fareeda da yayi. Wani irin quna zuciyarsa keyi
musamnan idan ya tuna duk wannan abun da takeyi fa siyanta fareeda kenan tayi.
TO TA YAYA TA HADU DA SABREEN?,MENENE SILAR HADASU AURE DA ITA?,MEYE MANUFAR?.
Wasu tambayoyi da suke masa susa a qirji,ya tabbatar tunda take muradin hadashi
da fareeda bisa wats manufar.....tabbas haduwarsa da sabreen ma akwai
manufa,saidai ita sabreen yasan bata da kudin da zata siya maamah.....to meye
SILA?. Ba wadda ta fado a ransa a sannan sai hajja,a take kaman an cillota
cikin tunaninsa,saboda muhimmancin abun a take ya ciro wayarsa ya tafa qaramin
massage ya tura yana cewa.
_ina buqatar kowanne motsi na rayuwarta ya zama abun bi
kafin na qaraso,bata buqatar kamu,amma ina buqatar ayi mata daurin talala_ sai
daya tabbatar da shigar saqon sannan ya maida wayar aljihunsa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 91
91
Sosai maamah tayi amfani da wannan damar ta dinga karbar
kudade daga hannunsa tana tsaraba. Baice komai ba don ba wannan muhallin
bane,bai kuma hanata siyan abinda duka take so ba.
★ *_makka to Maldives_*
Kwanaki
shida sukayi a maimakon kwana biyu ko ukun da ya tsara zasuyi. Kusan ita ta
dinga jan kwanakin duka a nufinta na tafi da tsarinta yadda takeso. Abu daya ne
kawai yake dan bata mamaki,yadda take kasa samun wayar fareeda kwata kwata,ta
gwada dukka layukanta amma ta gaza samunta,mamakinta yana sake daduwa idan ta
irga kwanakin taga ko sau daya bataga gilmawar kiran fareedan ba.
Sun sauka
Maldives dab da sanda rana ke shirin faduwa,wannan ya sake haska tsibirin
ma'abocin ruwa da wani irin yanayi me daukan hankali.
Baki
kawai maamah ke tabewa,a zahirin gaskiya ba zata ce island din baiyi mata
ba,saboda guri ne da yafi kama da aljannar duniya,amma baqinciki da bacin rai
suna cikata idan ta tuna cewa ahalin alhaji hamza suka zabi wajen. Ranta ya
sake baci sosai cikin wani irin baqinciki da fushi sanda taji tsadar da rayuwa
cikin tsibirin yake dashi,da kuma yawan adadin kudaden da ake kashewa kowanne
kwana daya cikin resorts da sauran guraren dake kewaye da wajen.
"Nikam banga abun burgewa a nan waje ba.....guri duk
ruwa,koda yake ba lafinka bane.....kai ka zama dan amshin shata ne kawai sai
abinda aka tsara maka,kuma tsabar zallar mugunta ne saboda basusan zafin
dukiyar ba,ba tasu bace......dolla million nawa ka kashe musu?" Ta maida
tambayarta ga fu'ad dake zaune a gefanta cikin motar da Jordan yazo daukarsu.
Boyayyar
ajiyar zuciya ya sauke yana rufe idonsa gami da budesu,tunda yake bai taba jin
kwanaki masu wahalar wadannan ba,wadansu irin kwanaki ne da sam babu armashi a
cikinsu. Ya sanya ran samun nutsuwa daga wajen sabreen tun ranar farko data
daga wayarsa,saidai kuma bai sake samunta a waya ba har yau da suke dawowa
qasar.
"Farouq ne ya dauki nauyin komai" Ya bata amsar da
azahiri haka take,gida ne kawai zai iya cewa nashi sai jet din da suka taho a
ciki. Idanu ta dauke tana tabe bakinta.
"Haka dama zaka ce,saboda kana qoqarin basu kariya,ina
jiye maka ranar nadamar damqa ragamar rayuwarka a hannun mutanen da basusan
ciwon haihuwarka ba.....gefe daya ga matar da nake kyautata zaton zuwa yanzu
sun hada baki da ita don su sake cimma manufofinsu" Gaba daya maganganunta baya qaunar jinsu,baya
iya daukan kowanne mummunan kalami a kan ahalin alhaji hamza kibiya din. Sun
masa komai a rayuwa,idan yace komai yana nufin komai din,don wataqila idan bacin
su da yanzun baisan rayuwarsa a wanne matsayi take ciki ba.
Duk
maganganunta yayi shuru yana jinsu,qananun mitoci ne da basu da tushe
ballantana makama. Banda zata fassara abun da wani yanayi na daban tabbas da
gida daban zai kamata tayi zamanta ita kadai,saidai hakan yasan ba mafita
bace,ba abinda zai sake jawowa sai wani damuwan na daban.
Tun anesa
ya hangi musaddiq da saddiq zaune daga gaban gidan. Sanye suke da kaya iri daya
black jeans da white din t.shirt. Tsaf zakayi tunanin twins ne saboda yadda
komai nasu ya kusan zama iri daya.
Sosai
maamah ta qanqance idanu tana dubansu,wani irin abu yana tsarga mata
"Turqashi" Ta furta qasa qasa. Da alama ameenatu
tana ci gaba da mamayar komai daya kasance mallakinta. A sanda hankalinta yayi
nisa,ta dogara kuma da sabreen hakan sai ya zamana kaman ta bawa ameenatu wata
qofa ko dama naci gaba da baza mallakarta tsakanin yaranta. Ba zata iya tuna
watanta nawa bataga musaddiq ba,jininta.....tsatsonta,ya gaya mata fu'ad dinne
ya aikeshi wani aiki dubai da Qatar,amma yanzun gashi tare da ameenatu,gashi
manne da ahalin alhaji hamza kibiya.
Tsaiwar
motan yaja hankalinsu su duka,motar ba baquwarsu bace don haka dukkaninsu suka
miqe zuwa gaban motar.
"Barka da zuwa maamah" Musaddiq ya fada yana
niyyar karbar jakar hannunta. Kasa jurewa tayi ta jefeshi da harara duk data
sakar masa jakar.
"Uwarka ta taso daga wani gurin amma ka gaza zuwa
airport tarbarta kana nan manne da uwar wasu?". Maganar ta masa ba dadi
har hakan ya bayyana saman fuskarsa. Yadan basar yana amsar jakar sannan yace.
"Hamma ne.....bai bada assurance na yau din zaku taso
ba".
" Barka da zuwa maamah ina yini?" Saddiq ya fada
yana dan matsowa kusa da musaddiq. Waiwayowa tayi,ta aje masa wani kallo tun
daga sama zuwa qasa kafin ta amsa masa sheqeqe tana bin bayan fuad zuwa cikin
gidan. Koda riga ta gani a jikinsu baqincinta takeyi,gani takeyi kudin fuad ne
ya siya musu wannan riga takalmi da kuma daular da suke ciki ma gaba daya. Tana
ganin sunyi amfani da nasibin danta ne kawai suna morarsa bayan sun rabata
dashi.
Tunda ta
idar da sallar la'asar take manne da earpiece a kunnenta tana sauraron karatun
littafin umdatul ahkam. Sanye take da Indonesian set skirt ne da hijab dinsu
madaidaici sai rigar da iyakarta qugunta. Dark green ne da suka haska fatarta
sosai,ta tattare gashinta ta daureshi tsakiyar kanta bayan amna ta gama
jagwalgwala matashi da sunan zata mata kitso. Ta kasa kitson saboda
santsinsa,don haka ta bisu da hair clips ta tattare mata shi,ita kuma ta daureshi
da ribbons don tace ba zata saka mata hair ppin ba. Kayane masu taushi da
sakewa a jiki,duka anni ce ta saya mata su kusan kala shida.
A kwana
biyar din sauqi ya samu sosai,ita kanta a jikinta takejin ta warke da taimakon
wasu irin herbs 'yan Indonesia da anni ta bata.
A kwana
biyar din ta wani murje,hankalinta kwance bata ganin wulgawarsa bare fargaba ta
dameta. Hatta anni ta karanci yadda hankalinta ya sake kwanciya,ta daiyi
murmushi kawai saboda tasan tsakanin miji da mata sai Allah,bare wadannan data
fahimci yanzu ne yake fafutukar gina gwamnatinsa.
Batasan
me za'ayi ba a gidan,don duka hankalinta yana kan karatunta,itadai ta shiga
kitchen tana taya amna da anni girki. Annin ta fara fita ta barsu a ciki,amna
ta fidda Warmers din tana shiryawa,ita kuma ta tsaya tana gyaran kitchen din.
Idanunta d'ai d'ai cikin parlor din tana kallon wata sabuwar duniyar.
Fuad ya dauke idonsa a kanta yana sallama don sanar da anni da amna dake dining
suna magana shigowarsu.
"Wa'alaikumussalam......marhaba da matafiya" Anni
ta fada da murmushi saman fuskarta tana saukowa daga dining area din tana
nufosu.
Tun bata
qaraso ba maamah ta fara qare mata kallo,tayi kyau cikin super embellished me
asalin tsadar. Kwanciyar hankali nutsuwarta da riqonta da ibada sun sanya wani
irin kwarjini akan fuskarta gami da fidda ainihin quruciyarta,kai bakace itace
uwa ga saddiq da farouq ba.
Tako ta ina
sai take ganin annin ta fita samun duniya ne,wannan shine sirrin wannan kyan da
take gani tattare da ita. Dom ta sutura tana sanya sama da suturar dake jikin
annin a yanzu.
"Barkanku da zuwa.....saddiq ku dauki luggage dinta
zuwa daki......me babban suna ya akayi baka bada exact time din da zaku sauka
ba?" Anni ta fada tana dauke kai daga irin duban da maamah ke mata
"Na sha'afa ne anni.....amma gamu mun iso
alhamdulillah" Yayi maganar yana shafa sumar kansa,gaba daya hankalinsa
yana wajen amna yana tunanin ganin sabreen tare da ita.
"Alhamdulillah.....haka akeso ai.....bismillah Mariya
mana kunata tsaye?" Anni ta fada tana jifan maamah da murmushi. Idanu
maamah ta janye a kanta,tana jin wani abu yana tokare mata wuya. Yau ita akewa
tayin zama a gidan d'anta?.
"Da baki gaggawa ba ameenatu,zama kam nina
cancanceshi" Ta fada tana son maida maganar cikin yanayi na wasa wasa.
Sosai maganar ta samu muhalli a zuciyar anni,ita kuma ta sani bawai da wasa
mariya ke maganar ba,saidai koma meye ta shiryama zama da mariya din albarkacin
muhammad fu'ad din.
"Zo mana amna" Anni ta fada tana kiran amna dake
zaune kawai. Haka kawai takejin batason rabar matar......bata son yanayin
kallon da take binta dashi. Qarasowa tayi inda annin take,ta sani sarai anni na
iyayi mata fada don haka ta rusuna tana gida maamah data fidda mayafinta ta aje
gefe da bawa kowa na wajen tabbacin tazo gurin data isa ne. Kaman yadda ta saba
amsa musu gaisuwa haka ta amsawa amna.
"A gabatar mata da ruwa....sun sha hanya ita da
hammanki".
"Karki kawomin zallar ruwa,lemo nake buqata da wani
abun tabawar bawai dangin ruwa kadai ba" Daga amnan har anni ba wanda ya
nuna yaji abinda tace,illa anni ta dubi amna
"Ki duba fridge kiyi warming pizza da samosa ki hado
dashi". Kai amna ta gyada a sanyaye tana nufar kitchen din. Har yanzu ta
kasa aminta da gamsuwa matar wai itace mahaifiya ga hammansu.
Gefe anni ta
samu ta zauna tana gayawa kanta da kanta. Maamah ta cancanci kawaicinta kawai
saboda fu'ad din. Sam sabreen bataji shigowar amna ba sai data gama hada kayan
zata fita sannan ta riqota tana cire earpiece din kunnenta.
"Ki cewa anni an kammala,sai meye za'a dora
mata?". Kai kawai ta gyada mata ta fice,tanason ce mata hamman ya dawo
amma kuma yanayin sanyin jikin data tsinci kanta a ciki ya hana mata.
Sake daga
kansa yayi cikin matuqar zaquwa yana sanya ran ganin fitowarta a kitchen din
tare da amna. Saidai a yanzun ma amnan kawai ya gani ta fito. Iska ya zuqa
sosai yana fesarwa
"Me take buqata dashi ne?,hauka take so ya fara gwada
mata tuburan?" Ya tambayi kansa yana jin zuciyarsa tana quntata waje daya.
Sheqeqe
maamah tabi tray din da amna ta shiryo,ta tabe baki wanda muraran duk wanda ya
kalleta zai gani. Baya amna taja tana gayawa anni saqon sabreen,abinda yasa
ruwan da maamah ta kurba yayi mata cak a maqogaro.
Juya zancen
takeyi tsakanin rai da zuciyarta. Me haka yake nufi?,kyakkyawar alaqa tsakanin
sabreen din kena da ameenatu?,yarinyar ke niyyar zame mata qadangaren bakin
tulu ko.kuma ameenatun?,waye ainihin matsalarta a cikin su biyun?.
Ta
bangaren fu'ad din sai ya dinga ji ransa yana sake baci....dole ya sake
tabbatar mata ita mallakinsa ce,dole ya sake tuna mata muhammad fu'ad mijinta
ne.....mijin da bazai juri qaurace masa ba.....mijin da bazai juri bada umarni
tasa qafa ta take ba saboda raini.
"Kice ruwan zafi kawai zata dafa......ta fito ga baqi
sunzo tazo su gaisa". Anni ta fada tana duban amna. Baisan ya miqe tsaye
ba,shidai yaji yana gayaw anni
"Bari na samo warm water.....nasha sanyi a haram da
yawa" Yayi maganar yana jin wani magnet yana jansa zuwa kitchen din,ba
tare da ya tuna waye da waye a wajen ba.
Ajiye
cup din hannunta maamah tayi tana binsa da kallo sanda yake takawa hankali
kwance zuwa kitchen din. Tuni amna ta wuce dakinsu don ba zatayi gangancin
komawa kitchen din ba tunda can hammansu ya nufa.
Wani
mamaki yake kashe maamah tana daga zaunen. Ita din ba yarinya bace haihuwar
jiya ko yau,ta sani sarai ita yabi....sabreena yabi bako shakka. Daga yanayin
fu'ad din kawai tasan akwai abinda ke jansa zuwa can din,wani dakiya da shariya
ta gani tattare dashi wanda bata taba ganin irinsa ba. Yadda yake tafiya zuwa
kitchen din hankalinsa kwance kaman ba wani idon kunya a wajen?.
Sanda
tayi nisa da binsa da kallo a lokacin anni itama tayi nisa da qare mata kallo da kuma fahimtar
rudewarta da kuma canzawar yanayinta lokaci guda.
"Ya rabb......kasa addu'ar dana bata tsahon dare ina
yinta ce ka amsa.....ubangiji ka sanya wannan mummunan qullin ka juyar dashi
zuwa kyakkyawa". Anni ta sake jaddada addu'arta can qasan zuciyarta wani
murmushin nishadi yana subuce mata.
"Tabbas kina dab da ganin yadda ubangiji ke jujjuya
al'amura......kina kuma dab da samun ciwon hauka muddin akan Sabreen da fu'ad
ne" Anni ta sake fada qasan ranta.
Ba jiya
yau ko shekaran jiya ba take karantar duk wani motsi na fu'ad ba.....me babban
suna ya canza gaba daya.....ya shiga wata gawurtacciyar koma ta soyayya wadda
tayi imani shi kansa baisan girman abinda ya fada a cikinsa ba......karantar
irin wannan yanayin kuma sai uwa ko gawutaccen masoyi.
"Zan shige daki na shirya.....naga magarib tana dab da
isowa.....ga masaukinki can,a huta lafiya" Muryar anni ta dawo da ita daga
rudanin data shiga. Bata sake cewa maamah din komai ba,saidai ta barta da
kallon murmushin dake kwance akan fuskarta. Ita ba zata bari fu'ad ya fito ya
sameta ba ballanta yaji kunya ko ya raga daga soyayyar da yayi niyyar nunawa
matarsa ba.....ta barwa maamah ta fara kallon sample kafin anihin abun ya
bayyana a idanunta gaba daya.
Idanunta
ciki ciki tabi anni da kallo har ta isa dakinta.
"Ta ina kuma ameenatun ta sake bullomin?" Ta yiwa
kanta tambayar zuciyarta cike da kokwanton murmushin data gani saman fuskarta.
_turqashi😂😂,anya maamah nan din gidan
zamanki ne kuwa?_
_maji ma gani dai_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 92
92
A hankali ya
tura qofar kitchen din sannan ya maidata ya rufe a nutse bayan ya karanci
earpiece ne a kunnenta,sai ya maida bayansa jikin qofar kitchen din,ya goye
hannayensa a qirji yana qare mata kallo.
Ta fidda
hijabij jikinta ta saqaleshi a hanger na kitchen din don tafi jin dadin yin
aikin,bata da damuwa kan musaddiq ko saddiq,dukkaninsu idan zasu shiga wani
guri cikin gidan saisun tsaya daga waje sunyi sallama. Sassalkan gashinta da
amna ta kame mata su da hair clips masu kaloli da shapes daban daban jelarsa ta
baje sosai a bayanta. Baqi sidik ne yanata shining saboda ko da can ita din
bame wasa bace da gyaran jikinta ma gaba daya. Idanunsa ya lumshe yana bin
sauran sassan jikinta da kallo,qugunta ya bude sosai ta cikin skirt din dake
jikinta,shape dinta ya fita sosai da duk wani sura na kyau da Allah ya bata.
"Ya salam" Ya furta qasan ransa saboda wani irin
magnet dake fusgarsa zuwa gareta. Wani sashe na zuciyarsa ya raya masa inda
wani tsakanin musaddiq da saddiq ne ya shigo a haka zai ganta?. Raba jikinsa
yayi da qofar ya fara takawa a nutse yana dosarta.
Dukan
hankalinta yayi nisa wajen killace plates din data wanke. Kwata kwata bata
kawowa ranta wai dawowarsa ba ballantana shigowarsa kitchen din ba. Ta gama
jerawa tayi taku biyu baya don matsawa daga wajen,santsin man daya diga a qasan
tiles din ya kwasheta,tayi baya zata fadi a matuqar tsorace. Hannayensa ya
sanya duka biyun ya tarota,take ta samu masauki a faffadan qirijinsa.
Gam ta
sanya hannu tana riqeshi ba tare data fahimci a jikin wanda take ba,tunaninta
duka ta samu wani abunne ta kama.
Fadowarta
jikinsa ya bashi daman qarewa kyakkyawar fuskarta kallo. Karon farko da wannan
tsiwatacciyar fuskar ta fito a matsayin matsoraciyar fuska. Sauke idanunsa yayi
saman qirjinta dake sama da qasa alamun tsoro muraran da kuma yawan adadin
bugun da zuciyarta ta qara. Cikin qasa da second ashirin hankalinta ya fara
dawowa jikinta bayan ta tabbatar batasha qasa ba,ta zuqi numfashi sosai wanda
hakan ya taimaka mata wajen isar lallausan qamshinsa qofofin hancinta ya kuma
isar da saqon waye me turaren cikin kwanyarta.
Idanunta
ta ware da sauri,take suka fada saman fuskarsa dake dab da tata,sukayi wani
zuzzurfan musayar numfashi daya hautsina masa tunani karon farko. Kyakkyawar
fuskar nan tasa dake shimfide da wani irin kyau da ba kowacce fuskar d'a namiji
ke da baiwar irinsa ba.....wani irin kyau me cakude da kwarjini musamman cikin
narkakkun idanunsa da kallon cikinsu yasha banban da idanun kowacce d'a namiji
data taba kalla.
Cikin
sauri ta tura qirjinsa baya tana zamewa daga jikinsa,saidai ya gwada mata
halittar sam ba daya bane ta hanyar miqa hannunsa ya damqota. Wata kyakkyawar
runguma yayi mata ta baya gana matseta cikin jikinsa,ya aza fuskarsa saman
kafadarta,sannan ya motsa labbansa da wani irin nannauyan numfashi.
"Am back.....am home.......but......" Ya fada yana
dagata gami da juyo da ita gaba daya tana fuskantarsa sosai. Raina kanta tayi
sosai ganin yadda ta koma 'yar qarama a gabansa,ya kuma ritsata da wannan
kallon nasa yana duban duka qwayoyin idanunta kafin ya jefa mata tambayarsa.
"You break my rules hajjaju.....don't blame me indai na
tashi hukuntaki" Yayi maganar cikin nuna mata da gaske yake yana miqa
hannunsa zai shafi gefan fuskarta. Baya taja da sauri,abinda ya sanya ya tsaya
ya zuba mata ido. Da gaske take batason koda yatsarta ya taba.....ko yaya ya
kusanta kanshi da ita saitayi wani abu da zai nuna bataso.
"Ya kamata kabar kitchen din nan kafin wani ya shigo ya
ganka" Ta fadi masa tana qoqarin maida hijabinta. Taku uku ya isa
gabanta,ya sanya hannu ya fusge hijabin yana kuma jawo kujera dab da ita ya
zauna ranshi a hade yana fadin.
"Wace irin mace ce ke?.....bakiyi kewata ba?" Yayi
tambayar da gasken gaske tun daga qasan zuciyarsa,yana fatan ko sau daya yaji
tace tayi kewarsa.
Wani
kallo ta watsa masa sannan ta janye idanunta,ta taka tana kashe gas din sannan
ta soma tafiya a nutse zuwa bakin qofa. Iya hakan ya bashi tabbacin ficewa
zatayi,ba kuma zaka kulashi ba kenan. A zafafe ya miqe yana wurgi da hijabin
nata,ya sake shan gabanta yana mata wani duba nakai tsaye. Ko ba'a gaya mata ba
zuwa yanzu tana saurin gane abinda ya taba zuciyarsa. Sauyawar yanayinsa wani
abu ne da yake saurin razanata.
Soma hade
tazarar dake tsakanin su yayi yana duban idanunta sosai.
"Na tsani nuna halin ko in kula......na tsani wannan
attitude din.....Please behave.....or I'll have to take disciplinary
action" Yayi maganar har zuciyarsa yana nufin abinda ya fada din soft lips
dinta masu kalan red dake motsawa kadan kadan alamun tsiwa na cinta suna fusgar
hankalinsa. Yasha imagination na sanda zata mallaka masa su ba gardama ba tare
daya qwata da qarfi ba......bama iya su kadai bama.....dukkaninta yakewa wannan
fatan da kuma burin. Lallausan tafin hannunta ya matsa yana sauraren Jin muryarta.
Muryar data zame masa abokiyar hirarsa a mafarki tun waccan ranar data amsa
wayarsa a garin makka.
Idanunta ta
jjanye daga kanshi,har yanzu batajin zata iya kulashi din......duk sanda ta
kalli fuskarsa fareeda take gani kwance cikin qirjinsa.....duk sanda ta
kalleshi munanan maganganunsa a kanta take tunawa.....muguntarsa da musguna
mata da mugayen maganganu,don haka ta taka zuwa side din hagunsa da nufin
rabeshi ta fice.
Cak ya
dagata ya azata saman kitchen cabinet din ba tare da tunanin tayi kusa da qofa
ba,ko kuma jama'ar dake gidan ba. Hannayensa ya sanya ya zagaye bayanta dasu,ya
hana mata kowacce dama da zata raba jikinta da nasa,ya kuma yi kane kane a
fuskarta ya hanata matsawa ko kadan,da wannan daman ya samu ya riqe lips dinta
da suke tsone masa idanu ya fara aike mata da wani irin tattausan kiss. Ba
wannan zafin ba kuma wannan hanzarin,wani irin sarrafata yakeyi da wani irin
sanyi da salo daya soma zare mata duk wani kuzari da takeji da kuma zafin da
takeji a kansa.
Duk wani
tunani nata ya tsaya cak tun daga sanda ya wuce cikin kitchen din. Wani abune
da yazo mata a bazata wanda bata taba tunanin zai faru ba. Yau fu'ad ne a
gabanta ya tsallake yabi mace kitchen da zummar zai samo ruwan dumi?.
Cup din
hannunta ta ajiye tunaninta yana komawa baya,ta saita dukkan idanunta da
hankalinta akan qofar kitchen din tana lissafin mintuna nawa zaiyi kafin ya
fito. Falon yayi shuru saboda wucewar kowa sai ita daya data rage,ta dauke
kanta tana duban agogon hannunta bayan shudewar mintuna biyar din data tabbatar
ko dafa ruwan za'ayi wadannan mintunan sun wadatar. Kujerar da take kai din sai
takejin kamar ta mata nisa da bakin qofar. Miqewa tayi tsam tana canza kujera mafi kusa da bakin kitchen din
tana sauke wani zazzafan huci,tanata qoqarin hana zuciyarta ci gaba da hasashen
abubuwa daban daban da zuciyarta ke saqa mata.
"Da gaske yarinyar nan 'yar bariki ce.....da gaske
bariki takeson gwadamin?.....wai uban me yakeyi a kitchen din?,da gayya ta
tsareshi kenan don ta gwada mata iyakarta?" Wadannan tunane tunane su
sukaci gaba da kai kawo tsakanin zuciya da kwanyar maamah. Sake matsawa tayi
kujera ta gaba tana sake zurfafa jinta da kuma idanunta akan qofar kitchen
din,amma bata iya jiyo komai,abinda ya sake assasa baqincikinta. Wai wanne
tsautsayi ne ya hanata tsaiwa a nigeria tasa ayiwa fu'ad da sabreen din mummunan
farraqu?,irin farraqun da ko me irin sunanta zai tsani ballantana ita da kanta.
Maida
idanunta tayi ga agogo tana duba adadin lokutan da aka shafe. To badai dafa
ruwan dumi ba....ko dan mutum za'a dafa a wannan gabar yaci ace ya dahu wani irin tsalle zuciyar ta keyi,wani sashe
na zuciyar na bata shawarar shiga kitchen din da kanta taga qaryar rashin
kunya. Sau uku tana miqewa sai ta koma ta zauna cikin shakka da kokwanto.
Batasan ya zataji ba idan taje ta tadda daidai da abinda tunaninta yake bata.
Qaqqarfan motsin da taji daga kitchen din ya qarasa tunzura zuciyarta,ta miqe
da wani irin gaggawa ta durfafi kitchen din.
Baya
fahimtar komai sai sabreen din dake gabansa......kowanne sashe na jikinsa
karbar saqo yakeyi iyaka,baisan wanne irin kebantaccen shauqi yakeji haka a
kanta ba. A yadda yakejin kansa a lokacin yana jin kamar duniyar ma tayi musu
kadan shi da ita. Ya sake zurfafa harshensa cikin bakinta yana sake zare mata
duk wani kuzari nata. Qwace masa numfashinsa ya dinga yi yana kamoshi da qyar,a
daidai wannan lokacin maamah ta qaraso bakin qofar kitchen din cikin zaton zata
samesu tsakiya ko qarshen kitchen din.
Tamkar an
juya kwanyarta daga sama zuwa qasa haka taji. Wani irin shock jikinta ya dauka
na tsakanin mamaki da kuma tsoro,jikinta da qafafunta gaba daya suka dauki
kyarma,saita juya da matsanancin sauri tana jin juwa na shirin kayar da ita.
Tana juyawa yana zare bakinsa a nata,baiganta duka ba,amma yaga wani sashe na
rigarta. Zazzafan numfashi ya furzar yana cure hannun sabreen dukka cikin kasa
hadi da kifi fuskarsa a bayan hannuwan nasu yana qoqarin daidaita numfashinsa.
"Maamah" Ya fada can qasan ranshi,kwata kwata ya
manta ya barta a parlor,amma yayi tsammanin yadda anni ta wuce daki itama dakin
ta nufa. Daga fuskarsa yayi data sauya launi yana zubesu saman tata fuskar.
Fuskarta ta kawar tana qoqarin dauke hawayen dake shirin zubo mata. Ya
gansu,don haka ya sanya hannu da nufin dawo da fuskarta saitin nasa,saidai ta
rigashi ta hanyar ture hannuwan nasa. A wahalce a kuma kasalance yace.
"Na jima ina baki wannan shawarar......zanci gaba kuma
da maimaita miki ita....kada kice zaki gwada raba kanki dani......zaki wahalar
da rayukanmu ne kawai......don fu'ad bai shirya rabuwa da duk macen data sanshi
a d'a namiji ba......fu'ad bai shirya rabuwa da sabrrrr ba" Yana kaiwa nan
ya zame hannuwansa daga nata,yaja baya still idanunshi a kanta yana tunanin
maamah na parlor din har yanzu ko tabar wajen.
Har
takai qofar dakinta ta fasa shiga,ta samu kujera ta zube tana qoqarin qwato
koda abu guda ne cikin tarin abubuwan da suke karakaina a kanta.
Da
gaske bariki ne zalla za'a gwada mata?......ta samu nasarar mallakarsa
ne?,yaushe ta ingizashi zuwa soyayyarta?,tayi imani a banza fu'ad bazaiso mace
irinta ba......matar da karuwanci da bariki suka zama shaida kuma tambarinta na
farko koda mutuwa tayi?.
Hannuwansa ya miqa mata bayan ya gama daidaita mode dinsa. Bata ko
kalleshi ba bare yasa ran zata bashi hannun nata.
"Musunki da gardamarki zasu iya tunzurani na aikata
abinda banyi niyya ba.....karki manta kawaici kawai nakeyi miki.....karki yadda
kawaicina ya qare......kika bari hakan ta faru.....to tabbas ki rubuta ki
ajjiye zan daukeki na kaiki wata duniya da ba wanda ya isa ya ganki sai
muhammad fu'ad shi kadai". Fararen idanunta da suka sake glowing saboda
siririn hawayen da yake a ciki ta watsa masa,kai tsaye ya saka hannu yana dafe
qirjinsa hadi da lumshe idanunsa kafin ya sauke hannun nasa ya saka hannu ya
kamo lallausan tafin hannunta yana sauko da ita.
"Kinci bashi da yawa na rashin kula da abubuwan da suka
ratayi a kanki nawa......duk wani abu nawa daya kamata ace kinyi bakiyi ba ki
rubuta ki ajiye ya shiga sahun bashi". Kasa musanta masa tayi sanda yake
riqe da hannunta suna fita a kitchen din.
Hannun
kujera ta koma ta zauna tana hade hannayenta a qirji zuciyarta tana mata wani
irin zafi. Bata jin zata iya daukan wannan abun sam ba zata jura ba.....tana da
shakka idan har zata iya barin sabreen a gefen danta har xuwa lokacin data
tanadar mata.
Sanda ta
daga idanun nata don sake duban kitchen din sai tayi kyakkyawan gani,yana riqe
da hannunta gam da taketa qoqarin zamewa.
"Kina qarawa kanki laifi akan laifi......please ki
hutar da kanki" Ya fada yana lumshe idonsa gami da jin yadda riqe hannunta
kadai ke sakarwa jikinsa wadansu kaifafan makamai.
"Muhammadu" Ta kirashi da wani kaifi da yake nuna
zallar bala'i da bacin rai da zuciyarta ke ciki,musamman data lura bai ankara
da wanzuwarta a wajen ba.
_ayimin afuwa a karbi wannan ba yawa,mu hadu gobe in sha
Allah_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 93
93
Kiran data masan yaja hankalinsu shida sabreen din,idanunsu
suka hadu karon farko ita da sabreen suka sakarwa juna wani kallon kallo kafin
sabreen din ta janye idanunta salin alin tana kuma sulale hannuwanta daga cikin
nasa. Ta kowanne fanni jikinta ya bata al'amura da dama akan matar daga kallon
farko kawai,ta danne zuciyarta tadan ciji labbanta na qasa ta taka a hankali
tana qarasawa gabanta.
Abinda
bata taba kawowa zai faru ba,sabreen din ta zame a gabanta tana fadin.
"Barka da yamma". Ruwan mamaki ya gama kasheta,ta
dauke idanunta daga kanta tana maidawa kan fuad din. Sam idonsa bai kansu,kamar
ma bashi a wajen.
"Turqashi.....ni zaki saka cikin kokwanto?" Ta
ayyana a ranta. Cikin kwanakinsu dashi a saudiyya ta dinga jeranta masa huduba
da qorafin rashin kirkin matarsa da fatan samun wata kafa da zata sake
nesantata daga rayuwarsa.......a yanzun kuma sai ga yarinyar da take complain a
kanta zube a gabanta tana kwasan gaisuwa.
"Ta yaro kyau take bata qarko......idan kinsan wata
bakisan wata ba yarinya".
"Lafiya qalau......sai yau kika iya tunawa da
wanzuwata?" Tayi maganar tanason tabbatar da maganarta ta farko a zuciyar
fu'ad da ya fara wucewa zuwa dakinsu.
"Aah fa.....wannan d'iyar tamu sai kin mata
uzuri.......tunda mukazo Maldives ba lafiya.....yanzun haka jinya take"
Muryar anni ta ratsa plan din maamah din ta kuma wargazashi,sannan ta saukar
mata wani irin gigitaccen yanayi daya hautsina kwanyar maman.
"Bata da lafiya?,me kuma ya sameta?" Tayi subul da
bakan jefa tambayar dake yawo tsakanin zuciya da harshenta.
"Tashi daga tsugonan nan karki wahala da
yawa.......jeki watsa ruwa ki huta,Allah yayi albarka" Anni ya fadi tana
taya sabreen ta miqe. Ko waiwayen maamah
din sabreen bata sake yi ba......zubewarta a gabanta yana da nasaba da
musaddiq.......mutum ne cikakke d'aya da d'aya,wanda ke tsananin ganin kimarta
da kuma mutuncinta......idan har zata iya wuce mahaifiyarsa saboda wani abu
daban da tsakaninsu ne kawai.....to tabbas bata mutunta mutuntawar da yake mata
ba. Ya girmeta amma baya iya gaidata a tsaye ba tare daya duqa mata ba.....dame
zata biyashi.
Yadda
maamah tabi sabreen da kallo zuciyarta na wani irin duka ya sanya anni sakin
gyaran murya. Dawo da dubanta tayi kan annin ita kuma ta basar tana cewa
"Dazun kina tambayar me ya sameta.....lalurarmu ca ta
mata......matar aure ai ba'a rabata da qananun lalurori" Anni ta fada tana
ajjiye diffuser din da dama ita ta fito da ita ba tare data sake kallon fuskan
maamah ba.
Wani dummm
taji kunnuwanta har qwaqwalwarta sunayi. Maganan anni maimakon bata haske sai
duhu ma data sake sanyata a ciki. Lalura ta mata ciki ko bari?,wanne anni ke
nufi a ciki?. Tsaye tayi a wajen kamar sakarya,kafin wani lokaci falon ya sake
zama sai ita daya a ciki.
A daren
tayi nadamar da batasan adadinta ba na tsananta bincike har kunnuwanta sukaji
mata maganar da ta gaza samun amsarta. Magana me harshe damo mafi rudani data taba ji. Idan tace a
daren tayi bacci to tabbas me karatu ma yasan tayi qarya,ta qulla ta kuma
kwance har batasan adadin sau nawa ba. Tayi rantsuwa ta kuma lashi takobin
muddin ciki ne da yarinyar......muddin tayi kuskuren samun juna biyu da
muhammadun lallai saita sakata cikin nadama da dana sanin da babu ranar
fitarta. Daga qarshe ta yanke shawarar sanya idanu a dukka motsinsu don tasan
wanne mizani zata dora mataki na gaba
★Jiyan tunda wuri ta gama shirinta ta kwanta abinta,don haka
daga maamah har d'an nata babu wanda yaga gilmawarta sam. Cikin rashin sani
maamah din ta tsareshi wajenta da hirarrakinta marasa armashi,a nata tunanin
Daki daya suke kwana,duk da tana kokwanton hakan a ranta,amma zargin cikin da
takeson tabbatarwa ya kasa bata nutsuwa ko tabbacin taren suke ko ba tare ba.
Duk da
akwai cook dinsu ta musamman dake zuwa musu girki tun a wancan gidan,amma sai
ta kasa kwanciya bayan gari ya fara haske. Daga amna har anni da bacci ya dauke
saman abun sallah tana tsaka da karatun qur'ani basusan da fitar ba.
Haka kawai
takejin bai kamata ace ita da amna duka suna kwance ba har sai sun jira cook
tazo. Ta san ba wani qwarewa tayi da kalolin girke girke irin nasu na masu
hannu da shuni ba,amma ko yaya tana da rawar da zata taka,tana kuma da
gudunmawar da zata bayar,zata kuma iya dafawa aci ba qorafi ko mummunan rashin
dadi.
Shuru
parlor din nasu,kowacce qofar daki kuma a rufe,haka ta ratsa a nutse har ta isa
kitchen din. Bata da tabbacin ya tashi,amma still sai taqi fidda hijabin
nata,don ma qarami ne bazai hanata kowanne aiki ba,ta fara duba freezer da
ma'ajiyar abincin tana tunanin me dame zata fara aiwatarwa kafin matar ta iso?.
Tunda ta
idar da sallah tana saman abun sallar,bawai kuma zikiri ko karatun qur'ani
takeyi ba.....aah babu ko guda daya. Ta zauna ne kawai tana gadin lokaci,ta
zauna ke kawai tana sanya kunne da idanu akan kowanne motsi da zata iya jiyowa
daga parlor din.
Tunda yayi
sallar asuba shi dinma bai koma ba,wani irin bacci ne mara dadi kwata kwata ya
daukeshi. Zuwa lokacin yana jin kamar haqurinsa yana dab da qarewa,cikin sati
hudu anci sati uku.....baisan wanne haqurin zaici gaba dayi ba sama da wannan.
A jiyan sanda ya baro wajen maamah yayi zaton daya koma dakinsa zai samu anni
ta turo ta,ya fuskanci anni ma kaman tana bayanta ne,banda haka yaci ace an
duba lamarinsa an bashi matarsa. Farouq kadai yasan zai iya masa wannan
aikin,saidai kuma shaqiyancin farouq din kawai yasan ya isheshi kafin ya samu
yayi masa abinda yakeso din.
Kayan
jikinsa ya canza zuwa kayan motsa jiki da suka fitar da murdaddiyar surar nan
tasa da ginannen jikinsa. Kwana biyun da bai motsa jiki ba sai yake jin jikinsa
kaman yana masa ciwo,ya sanya rufaffun takalma a qafarsa ya kashe wayoyinsa ya
ajiye ya fito.
Already
ya samu gym nan kusa dasu,ba wani nisa ne tsakaninsu ba,don a qasa ya qarasa da
sassarfa. Awa guda kacal ya gama ya kammala ya fito,suka jero shida jordan suna
magaganu jifa jifa akan abinda ya shafesu.
A nutse ya
buda qofar parlor din yana takawa a hankali,idanunshi still akan qofar dakin
anni. Idanun nasa ya janye yana lumshesu,yana jin inama zaya samu daman da zai
qarasa gareta. Wata kewarta ke ratsashi....kewarta ba kuma iya kewar fuskarta
kawai ba......dumin jikinta.....qamshinta.....da tausasan labbanta.....harda
tsiwar nan tata da wani lokaci take maidata qanqanuwar yarinya ba tare data san
da hakan ba.
Har zai
wuce dakinsa yaji yana buqatar ruwa,tunda baishan ruwa yawanci bayan kammala
motsa jiki sai bugun zuciyarsa ya daidaita.
A nutse
yake takawa xuwa kitchen din,cikin jikinsa da zuciyarsa sai ya dinga jin kaman
akwai wani abu me muhimmanci a wajen,kaman yana qara kusanci da wani bangare na
musamman daya tsage daga zuciyarsa.
Idanu ya
zuba mata sosai sanda yake hangota,kaman shigen jiya saidai yau tana maqale da
farin mayafi,tana tsaye gaban tarin Irish potatoes din da take barewa a nutse
da peeler. Idanunshi ya lumshe yana kuma budesu duka lokaci guda,yana jin wani
abu yana taso masa. Tun daga waccan ranar.....tun daga kuma wancan lokacin
zuciyarsa bata sake samun nutsuwa ba,yana jinsa kaman bashi bane,yana jin kamar
an sauyashi ne da wani mutum na daban ba muhammad jadda ba. Ta hana zuciyarsa
hutawa tun daga wancan lokacin,ta kuma hana masa damar sanin WACECE ITA?. A
jikinsa yake jin akwai wani daban tattare da ita.....akwai wani boyayyen labari
a bayan wannan matsiwaciyar fuskar.
Kaman jiya
dai,yau kam baisan me ya dauke hankalinta har haka ba,gwara jiyan akwai
earpiece a kunnenta,wanda sai bayan ya zare yaji abinda take saurara din.
Takawa yakeyi a hankali har ya isa bayanta.
"Salam alaikum" Ya fada yana harde hannunsa a
qirji qamshin turarenta me wani irin sanyi yana buso masa. Wani irin faduwa
gabanta yayi,ta tsorata ainun da jin muryarsa dab da ita,amma sai ta dake taqi
waiwayowa,ta motsa labbanta muryarta can qasa ta amsa
"Wa'alaikumussalam" Ba tare data waiwayo ba tana
ci gaba da bare dankalin. Shuru ya ratsa tsakaninsu,ya fahimci ba zata juyo
bane don haka ya taka yana zagayawa ta gabanta a nutse ya tsaya a gaban
nata,tazarar inches kadan tsakaninsu.
Hannu ya
miqa kawai ya zare peeler din daga hannnunta,ya kuma miqa daya hannun ya zare
irish din da take barewa. Fararen idanunta ta daga da zummar masa tsiwar
tata,saidai cikin sa'a caraf suka shige tsakiyar nasa idanun. Da sauri ta kauda
qwayar idanunta gefe,duk wani rashin kunya data tanadi yi masa ya soma zurarewa
gefe.
"Duk karatun da kukeyi har yanzu baki koyi gaida miji
ba?" Ya tambayeta calmly da wani irin sassanyan sauti. Gaza dubansa tayi
saboda yadda kwarjininsa yake neman cika kitchen din gaba daya. Wadannan
muscles din nasa ba qaramin tsoratata suke ba,har bata qaunar ya sanya qananun
kaya. Ita daya tasan me takeji idan ta gansu,ita daya tasan irin qwarin da suke
dashi,saita zabi matsawa daga wajen ko zata samu daman shaqar iska me kyau
wadda bata gauraya da dumin numfashinsa ba da kuma na turarensa daya qara sanyi
saboda cakuduwa sa gumin jikinsa da yayi.
Da qafa
kawai ya tokareta,sannan ya daga nashi fararen idanun ya watsa mata,tayi zaton
zai janyesu daga kanta don haka bata janye nata ba,idanunta suka sauka a
hankali saman redlips dinsa masu tudu da wani irin shape,quarter million din
dake zagaye da habarsa zuwa zaman labban nasa ya sake zamewa labban nashi wani
ado na daban. Haka kawai tsigar jikinta taji ta tashi,abinda bata taba ji ba
tsahon ganinta da duk wani d'a namiji. Qoqarin janye idanunta tayi,da qyar ta
samu nasarar yin hakan kowanne sashe na jikinta taji yana daukan sanyi,rudewa
taji tana shirin yi kaman barawon daya shiga tuhuma a hannun hukuma.
Wani
siririn murmushi daga can qasan zuciyarsa ya qwace masa
"Dama bakisan ni naga dama nake qyaleki ba
yarinya" Ya fada can qasan ransa,amma a sarari sai ya juya gefansa saman
cabinet din,ya ajiye peeler din da Irish din,ya sanya hannuwansa ya zagayesu ta
mazaunanta yana jawota jikinsa da dan zafi zafi,abinda ya bata daman zubewa a
qirjinsa kafin ta daga kai tana neman qwacewa.
"Stop ita DUNIYATA" Ya fada softly idanunsa a
kulle yana yadda fatar singalilin hannun ta ke gogar nashi tana tayar masa da
tsigar jiki.
"When.....sai yaushe zaki fahimci cewa KECE
DUNIYATA?" Ya qarasa maganar yana ware idanunshi gaba daya akan fuskarta.
Wannan karon kasa jure kallonsa tayi,saita runtse idonta tana hade rai sosai.
"Banaso kana tabamin jiki.....bana so"
"Am addicted to you.......tabaki shine favourite thing
a rayuwata gaba daya" Ya maida mata amsa kai tsaye yana me bata tabbaci ya
kuma sake matso da ita sosai yana mannata da jikinsa.
Gigicewa
tayi sanda taji ta saki ajiyar zuciya tare da tashi ajiyar zuciyar,kunya da
wani irin takaici ya lullubeta,abinda taji haduwar jikinsu ya saukar mata ba
zata iya shanyeshi ba idan bata bawa zuciyarta daman numfasawa ba......to amma
kuma ta dauka a boye ta saki nata ajiyar zuciyar. Fitar sautin ajiyar zuciyar
tata ya sakashi ware dukkanin idanunsa a kanta yana dubanta,duba ne na qurilla
da son gane meye ya taba wannan zuciyar?.
A gaggauce
gama shiryawa tsaf cikin Holland vlisco me asalin tsadar,an xuba mata dinkin
manyan mata na buba,ta kuma cika wuyanta da hannunta da kayan ado na gold.
Macace me son izza da alfahari,wadda idan tazo guri so samu kowa ya dusashe a
gurin sai iya tauraruwarta kadai. Ta tsaya gaban madubi ta tabbatar komai yayi
a shigarta sannan ta juya ta dauki wayarta tana nufin fita a dakin. So take ta
kasa ta tsare......so take komai zai dinga wakana cikin gidan ya dinga
kasancewa saman idonta,bataso tsakanin sabreen ko fu'ad wani yayi wani motsi da
zai zarta ganinta da idanunta,wannan karon salon da zata bullo musu dashi na
dabanne,har sai ta samu tabbatuwar nasara a gareta. Tanaso da iya dressing
dinta kawai ameentu ta fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,ameenatu ta
sake tabbatarwa da kanta cewa ita din fa itace mahaifiya ga muhammad
jadda.......ba wata mace a duniya ta biyunta.
Cikin takun
isa take fita parlor din tana qarewa ko ina na parlor din kallo. Siyan gida a
qasashen waje musamman gidaje irin wadannan ba abu bane da za'ayi maganan
qananun kudade ba. Abinda ta lura dashi wasa wasa ameenatu ta maida mata yaro
saniyar tatsa kenan,taja wata irin qwafa tana samun sofa guda daya ta hakimce a
kanta.
Daga
inda take ta sanya remote ta kunna tv,tayi sa'a tashar farko ta kamota a inda
suke gabatar da abincij breakfast na yaren mutanen qasar china.
Minti
uku kacal taji tunaninta ya koma ga kitchen din gidan,tanaso ta tantance dame
dame ya jibge musu suke ci?,wanne irin gadara kuma ake gwadawa a wajen?,don
haka ta miqe tsam tana maida flats shoe dinta tana nufar kitchen din.
Yau kam
sai data shigo sosai sannan idanunta ya sauka a kansu. Mugun gigicewa tayi fiye
da jiyan,saboda yanayin data gansu a yau din yafi na jiyan munin gani.
"Na shiga uku ni mariya!" Ta fada muryarta na rawa
tana yunqurin juyawa,wanda saurin da take ta matsa a wajen santsin gurin ya
debeta ta kusa zamewa,cikin taimakon Allah ta kama murfin freezer ta riqe tana
tsaiwa saman qafafunta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 94
94
Daga
shi har sabreen din sai a lokacin suka dawo hayyacinsu. Ita ta fara zamewa ta
tsakiya tana raba jikinta da nashi haushi yana cikata. Yana son lalla qarfi da
yaji sai ya koya mata dabi'ar da ba tata ba......lallai lallai sai ya sanyata
tana yin abinda ba halinta ba.......batasan me zata masa da zai sanyashi
nesanta kansa da ita ba. Batason yadda yake warning nata kan bata isa ta raba
kanta dashi.......a nata wajen ba wani abu me sauqi a wajenta sama da wannan
din......zaman Maldives ya bashi wannan damar,isarsu Nigeria kuma zata yanke
kowacce alaqa da yake tunanin ya qulla da ita.
Juyawa
tayi tana fita a kitchen din ba tare data sake kallonsu ba. Qirjinta ne kawai
yake bugawa da wani irin bacin rai da kuma rudanin abinda ta gani din.
"Wanne irin asiri tayi masa?,wanne irin asiri ne
wannan?,maqale mata?" Ta dinga jerawa kanta tambayar da bata batasan
amsarta ba. Yadda zuciyarta ke matsewa da bacin rai sai takejin idan tayi shuru
tsaf zuciyarta zata iya bugawa......don haka ta soma sakin ruwan sababi.
"Wanne wacce irin masifa ce?,gida sai kace gidan
arna?,to wallahi ni bazan lamunci wannan ruwan tantirancin da barikin ba
ehe....dole kowa ya gyara zamanshi,ni ba shashashar uwa bace ko banzar
suruka,kome mutum yazo dashi ina daidai dashi ne".
"Oops" Abinda fu'ad ya fada kenan yana dafe
goshinsa da tafin hannunsa,zuwa yanzu yanajin anya zai iya rayuwa da mutane
kuwa muddin yana tare da sabreen din?,anya gidan nan duk da haka bai musu kadan
ba?,wannan zaman zai yuwu kuwa?. Duba daya sabreen tayi masa ta zare idanunta
tana lalubar hanyar fita daga kitchen din ranta a bace.
Jiya
tayi zargin giftawar mutum dama a kitchen din,koda suka fita sukaga sai ita
kadaice a falom zuciyarta ta dinga raya mata ita ta shigo......amma ba kasafai
ta fiya son dorawa dan adam zargi ba,don haka ta cire abun a ranta,qarshe ma ta
gayawa kanta.
"Idanma itace ita ta jiyo......zaiyi mata dadi idan
idanunta suka gani ta kuma tayata rabata da maqalallen d'anta. Dab da zata fice
a kitchen din yayi caraf ya kamo hannunta yana sake janta jikinsa. Dubansa tayi
idanunta na bayyanar da bacin da ranta yayi
"Bayan maamah din ko akwai wanda kakeso ya sake shigowa
ya ganmu ne?" Ta masa tambayar da salon gatse kanta tsaye tana duban
qwayar idanunsa duk da tsaurin da kallon yake mata.
"Yes" Ya bata amsa shima kai tsaye yana kallonta
"Saura anni.....anni ce akwai ta rage bata gani
ba.....ita nakeso ta gani.....don ta hakanne kawai zata fahimci ina tsananin
buqatar matata". Har tsakiyar kwanyarta taji yadda ya fidda sautin
maganar,wani abu me kama da jin kunya da nauyinsa ya danso kamata,saidai tana
ganin ya kamata ta fito masa a mutum don ya sasssuta yadda yake yawan hada
jikinsa da nata. Da alama da gaske yake
fadi....da gaske yakeson annin ta gani,tunda daga nan inda suke tsayen tana iya
jin muryar annin na tambayar maamah
"Lafiya mariya?" Batajira jin amsar da zata bata
ba ta soma kokawar qwatar kanta.
"Annin ma?" Ta fada tana ware idanunta cikin
kallon me kama da harara harara. Yadda ta yiwa idanun nata kusan kasheshi yaso
yi,hannunsa ya miqa a hankali ya nufi gashin idanunta da suka sake zara zara
saboda buda idanunta da tayin,abinda yadan saukar mata da tsoro ta rufe idonta
da sauri. Kusan dariya abun ya bata,ya zuba mata idanu yana ganin yadda
zuciyarta ke bugu sosai tun daga wuyanta zuwa qirjinta dake lullube da hijabi.
"Bakisan harsashin da kika sake jefamin ba da wadannan
idanun naki ba......a karo na gaba tsiwar nan zan cire gaba dayanta na maida
gurbinta da zazzafar soyayya....." Ambatar soyayyar ya sakata bude
idanunta a kanshi,tanason nuna masa tawayenta koda ta hanyar murguda baki ne
amma tana kokwanton kada ta jawa kanta,sai kawai ta zabi zame jikinta daga nasa
gudun kada annin ta samu isowar kitchen din. Still sake riqe hannunta yayi,ga
mamakinta hankalinsa kwance yake janta zuwa falon kaman wani dan jagora. Daga can
qarqashin zuciyarsa kuma wani kokwanto da mamaki ne fal ransa. Me yake tunzura
maamah din a duk sanda ta gansu haka a tare?,bayan tafi kowa sanin igiyar aure
ce ya hadasu?,me yasa yake ganin fushi kwance a fuskarta game da sabreen bayan
a nashi tunanin zatafi kowa murna da farincikin kasancewar hakan?. Idan bar ba
mantuwa yayi ba.....duka duka ba'a yi watanni biyu ba data masa kyakkyawan
warning akan bawa yarinyar kulawa.....meye ya canza wannan?,wannan kadai yana
sake bashi signal na AKWAI WANI ABU.
Dukka
juriyarta da dakiyarta ta tattara sanda suka iso parlor din,kanta tsaye ba tare
da tabi ya banbamin maamah ba ta wuce zuwa dakin anni. Ko wani bai gaya mata ba
tasan maamah din ta bita da kallo ne,kallon da ita daya tasan ma'anarsa. Tana
qasan shower tana jin yadda ruwan kebin sassan jikinta amma mayataccen qamshin
nan nasa bai matsa ko nan da can ba,duk inda ya aza hannunsa a jikinta sai ta
tuna idan takai hannunta,ta kammala wankanta tsaf ba tare da tasan yadda suka
qare a parlor ba don ba damuwarta bane. Ta jona dryer nan cikin toilet din da
busar da kanta,sai abun ya fado mata a rai.
Hala kishi
maamah take da ita?,hala maamah tana tsoron kada ta karbe mata yaro?,qila
maamah tana zaton mallakarta ce ita sabreen ke niyyar qwacewa?. Siririn tsaki
ta saki a ranta tana fadin
"Inda tabi a hankali ma wannan rayuwar tasu batamin
ba......dab nake da bar mata d'anta" Tayi zancan cikin ranta saidai
idanunta na kallon fuskarta ta madubin dake gabanta. Dif sai kuma tunaninta ya
tsaya cak tana sake maimaita furucinta na qarshe.
"Idan shi zaki iya barinsa.....zaki iya barin anni da
amna?" Tambayar data tsaida duk wani tunaninta kenan,sai ta samu kanta da
neman tabbacin zata iya ko ba zata iya ba?.
"Su nadra huda haneefa sunfi muhimmanci cikin
rayuwata" Ta gayawa kanta a gaggauce tana kunna dryer din da hanzari tana
son binne wannan tunanin daga ranta.
Idan banda
rudin zuciya ma duka duka yaushe ta sansu?,yaushe ta fara rayuwa dasu da har
zata shiga shakkar iya barinsu?.
A
nutse ya shirya cikin riga da skirt na sakakkun English wears. Basu kamata ba
amma sun mata wani irin dan banzan kyau,musamman sata daure gashinta data
gyarashi da kyau tsakiyar kanta. Wani qaramin hijabin ta samu ta sake dorawa
saman kanta,saidai wannan din da kadan ya rufe saman qirjinta.
Tana
jin amna na mata tsiya
"Wannan kwalliyar adda bazan iya cankan nawa hamma zai
siyeta ba......kullum sai na dinga jin inama nice ke adda....inama nike da
kyanki?" Harararta tayi
"Zageni da kyau amna.....har kina iya cewa wai na fiki
kyau?".
" Da gaske nake adda....ke kam ba zaki gani ba tunda a
jikinki yake"
"Bazan gani ba dai saboda kin fadi abinda bashi
bane.....matsamin kada lokacin walaha ya kubcemin" Ta fadi tana sanya
dogon hijabinta,da wannan suka rabu amna ta shiga wanka ita kuma ta tayar da
sallar.
Tana
shafa addu'o'inta anni ta shigo tana dubanta.
"An gama breakfast.....lokacin cin yayi....ki fara yin
gaba kafin amna ta gama nata laqai laqai din" . Kanta ta daga ta dubi
anni,tanason gaya mata ba zata fita ba..batason sake fita kwata kwata bare taga
matar,maganganunta na dazun sun mata zafi data dangantasu da kafirai,amma kome
zatayi tana duba musaddiq ne. Bataso taci gaba da kusantar inda take har hakan
ya jawo musu matsala,amma sai taga kaman bai dace ta gayawa anni ba zata fita
ba.
Abun
sallar ta nade,ta rage hijabin saman sannan ta sanya tattausan bedroom slipper
din tana fita a dakin.
Kowa yana
saman dining din a zaune kan tashi kujerar,wanda ya rage kawai ita anni sai
amna. Cook din na tsaye tana serving kowa da kalar abincin da yafi sha'awa.
Hankalinsa yana ga farouq wanda ke gwada masa wani sabon app da suka qirqira
don manoma. Musaddiq da saddiq na nasu hiran saidai qasa qasa,sai ya zamana
maamah din ce kadai zaune tana qarewa abincin alatun kallo tare da jin bacin
ran kudin da aka narka tun daga hiring me girkin zuwa kudin kayan abincin.
Maamah
dince mutum ta farko data fara ganinta,kallo daya tak da sabreen tayi mata ta
fahimci abinda ke kawo a ranta. Batason irin wannan kallon haka......saidai ta
bawa kanta tabbacin indai wannan dabi'ar na tare da matar zai wahala su rabu
lafiya. Ba komai zata iya dauka daga gareta ba,abinda ta dauka a baya ma ya
wadatar.....yanzun tana jinta 'ya me cikakken 'yanci ne da bata qarqashin
juyawar kowa.
Cikin
jikinsa yaji alamun wanzuwarta a wajen,ya daga kansa a natse yana duban sassan
da take tahowa. Fuskarta tayi masa kyau kaman ba dazu ya ganta ba,tafiyarta me
cakude da nutsuwar nan tana tsananin burgeshi,tun a wani lokaci can baya ba
tare da yasan da hakan ba.
Kasa
dauke idanunsa yayi daga kanta,yana fatan ta dubeshi da fararen qwayar idanun
nan nasa. Ta gefe yaji an taboshi,sarai yasan farouq ne don babu me masa haka
saishi
"Ina fata ba idanunka ne a kanta ba?" Ya soma
tambayar farouq din ba tare daya dauke idonsa a kanta ba ko g waiwayo ya
dubeshi ba. Can qasan zuciyarsa dariya ta taso masa ya danne,shi bama ta
dalilin tabashin yake ba,abinda ya dameshi kawai kada ya kalle masa mata?. Ya
manta saman table din akwai mamansa?,sam kaman baisan da wanzuwarta ba?,ita
yake qoqarin ankarar dashi,don tun fitowar sabreen din maamah din ta fahimci
mayataccen kallon da fuad din yake binta dashi,abinda ya sake tunzurata,ta dinga
kokawa da zuciyarta da kuma fuskarta akan ta shanye amma ta gagara yin hakan.
"Ni bazan kalli haram ba.....don soon halal dina na
tafe......amma dai ka gyara idanunka akwai iyaye a wajen" Shaf har kuma ga
Allah ya mance da maamah din a wajen,furucin farouq din ya ankarar dashi,sai
kawai ya zare idonsa akan sabreen din yana dojewa kallon maamah,don shine hanya
daya da zai kaucewa tuhumarta ko bacin nasa ran.
"Ta yaya zamu rayu a wajen nan?" Ya tambayi kansa
da kansa yana jin idanun maamah a kansa saidai yaqi yarda ya kalleta ko sau
daya,sai ya jawo tab din gabansa yana ci gaba da duba taswirar da suke magana
akai kafin fitowarta shi da farouq.
"Matsa kusa da mijinki kiyi serving nashi".
Furucin anni kenan daya sauka a kunnensa bayan fitowarta daga daki tayi joining
nasu a dining table din.
Sosai
maganar ta anni tayi masa dadi,ya murmusa can qasan ransa yana addu'ar a daren
yau ta bashi matarsa. Yana jin yakai taki maqura tako ina,muddin kuma akaci
gaba da tafiya a haka baisan me zai faru ba.
Satar
kallonsa tayi kaman yadda maamah ta saci nasu kallon. Har ta buda baki zatayi
magana sai wata zuciyar ta tunasar da ita,wawa shike saurin fasa abinda ke
cikinsa,sai taci gaba da juya abincin tana noticing kowa.
Ganin
baiko kalli sassan da take ba bayan annin tayi magana sai ya bata qwarin gwiwar
miqewa,ta matsar da kujerar dake kusa dashi a hankali ta yiwa kanta wajen
tsaiwa.
Cikin
takatsantsan take zuba masa komai,don ya tattara komai ya ajiye ne ya zuba mata
idanu yana bata order zuba kaza,rage kaza,kaza kadan zaki zuba. Wannan yaso
daburtata,don sau biyu yana kai hannu yana riqe serving spoon din da take zuba
abincin dashi da zummar kada ta zuba masa mayonnaise da man farfesun naman kan
ragon daya dan taso a sama. Ita daya sai kuma maamah suka fahimci yana sane
yake hakan,don duk riqewar sai ya hada da hannunta cikin nasa.
Da qyar
ta samu ta kammala zuba masa din,sannan ta aje komai a gabansa. Dubawa take
tana neman plate din da zata zuba nata abincin,duk da tasan zai wahala ta iya
cin abin arziqi,don ya sanyata a gaba da idanunsa da suke sake zama marasa
kunya marasa jin nauyin jama'a. Tun asali ta tsani yawan kallo,to amma shi din
ta fahimci ya qware sosai wajen wannan dabi'ar,abinda yafi bata mamaki
shine......kana iya wuceshi baisan waye kai ba.....kana iya gama sabgoginka a
kusa dashi baima tantance me kakeyi ba......amma ita me yasa yake sha'awar
sanya mata idanunsa?.
"Zauna muyi squatting.......wannan abincin ina zan
kaishi?" Ta tsinci muryarsa katsam yana fadi gami da gyara mata kujerar
dake kusa dashi.
Yadda wuta
ta dauke mata haka wuta ta daukewa maamah,kaman kuma hadin baki wajen duka sai
ya dauki shuru,sake tura kujerar yayi kusa da ita,bata da wani option sai
janyota da tayi ta koma a sanyaye ta zauna a kai. Tayi zaton shikenan,zai tsaya
iya haka ne,a'ah......sai daya sake janyo tashi kujerar ta zama kusa da ita
sosai har gwiwoyinsu suna gogar na juna.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 95
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
*_Kina da buqatar fara kasuwanci amma baki da jari?_*
*_ko kina da jama'a amma baki da jarin fara kasuwanci?_*
*_kin cika wayarki da contact na qawaye da abokai amma bakya
qaruwa dasu?_*
*_MAZA ZO KIYI JOINING HUGUMA CLOSET_*
*_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun
suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_*
*lace*
*kowanne nau'in shaddodi*
*yadika na maza da mata*
*mayafai*
*lafaya*
*takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da
qanana*
*sarqoqi da agoguna*
*under wears*
*abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza*
*_SIYAN DAYA NE NA AMFANIN GIDA KO KUMA REPOSTING ZAKI DINGA
YI KINA DORA RIBARKI?_*
*_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?_*
*Sassauqan farashi me ban mamaki*
*_Qawata adonku da samar muku da latest kaya shine
muradinmu_*
_______________________________
95
Ya jima
yana tsara yadda bata abinci zai zamo qarqashin kulawarsa. Yana ankare da yadda
take walagigi da cin abinci,wani abu sam da bai dameta ba,a iya zamanta a
gidansa ya lura da haka,kusan duk sati sai ya leqa store din gidan don ya duba
koda akwai wani abu daya qare ba kuma zata iya magana ba a qaro mata,duk sanda
ta shiga yana samun kitchen din danqare da kayan masarufi alamun dai ba wani
amfani akeyi dasu ba.
Tsahon
wahala da rayuwar da yayi zamanin quruciya me cike da rashin gata da wahala
yasa yasan illar da yunwa ke dashi,wannan ya sanya sam baya wasa da lamarin
ciyarwa,koda kuwa ga mutanen da ba'a qarqashinsa suke ba.
Sau da
dama idan ya kalleta yakan ji a ransa zatafi haka murjewa da cika muddin ta
maida kai ga abinci,bayason ta zama raguwa ko ta kasa jurewa lalurarsa,shi yasa
yake ganin shi yafi cancanta da kanshi ya tsaya a kanta ta wannan bangaren.
A
hankali taji saukar sassanyan tafin qafarsa saman qafarta. Wani abu taji ya
tsarga mata har cikin kwanyarta. Ta daga idanunta a hankali ta zubesu cikin
nasa,kusancin dake tsakaninsu yayi tsananin kusa da har ya sanya ta hangi wani
abu cikin qwayar idanunsa.
"Be serious mana....kisa hannu kici abinci ko na baki
da kaina" Ya fada da sound din da babu meji sai ita. Idanun ta kawar don
ya gama kashe mata jiki,ta dubi zara zaran yatunsa daya sanya cikin abincin
masu farare qal din nails da lunula a qasan farcen daya qarama faratansa kyau.
Batayi ko
lomar farko ba amna ta fito cikin skirt itama da riga English wears,sakakku
kaman na Sabreen din,hannunta dauke da wayar sabreen da sam ta manta ma da
babinta.
"Adda.....na saka miki ita tayi full charge.....nikam
ko iya yau ne a bani aronta" Ta fada tana murmushi gami da miqa hannu ta
aje mata ita saman table din a gabanta.
Bata gama
aje numfashin data shaqa ba idanunta suka sauka akan wayar,
"super nova....diamond edition" Sunan wayar kai
tsaye yazo kanta daga kallon farko da tayi mata tana sake kallonta da kyau don
tabbatarwa da kanta batayi dimuwa ko kuskure ba.
"Tashin hankali......kambun bala'i" Ta samu kanta
tana fadi can qasan ranta a tsananin gigice. Wayar million sabain da kusan
bakwai a hannun karuwar 'yar barikin?,ita kuwa tana me?,yarinyar data dauko ta
zame mata tsani na samun ire iren wadannan damarmaki sai a wayi gari tana
budewa kanta da kanta nata damarmarkin?,wanne irin bacci tayi haka ita
mariya?,wanne irin asararren bacci tayi?,yarinyar da a iya duniyanci da qwarewa
duka baifi ta lomaceta ba?,me yasa take neman zame mata qadangaren bakin tulu?.
Ba zato ba
tsammani naman data zuba a bakinta romonsa ya subuce mata ya wuce mata mashaqar
iska,take tari ya sarqeta me matuqar qarfi ta shiga yinsa ba qaqqautawa.
Musaddiq
da yafi kusa da ita shi ya bata ruwan data samu tasha tarin ya lafa,sannu kawai
suke mata,sai taji gaba daya iskar wajen ta mata kadan ba zata iya zaman wajen
ba,don haka tsam ta miqe tana sauka a wajen hannunta saman qirjinta anni na
mata sannu cikin kulawa.
"Ku debi abincin ku bita dashi" Anni ta fada. A
gareta sai taji kaman chance anni ta bata na matsawa daga wajen,don haka ta
motsa da nufin miqewa amma ya maidata ya zaunar da hanyar danne mata qafa.
Idanunta ta daga ta kalleshi,sai ya dage mata dukka girarsa biyun yana tsare
gida.
Dole taja
bakinta tayi shuru gudun tashin tashina gaban anni
"Amna diba kikai mata" Fuad din ya bawa amna
umarni kai tsaye,tana kallo amna ta shirya abincin musaddiq ya dauka mata wasu
suka gangara zuwa dakin annin.
Koda ta
shiga dakinma still numfashinta tana jin kaman baya isarta,sai ta kunna a.c ta
dauki remote din ac din tana qure number qarshe,kafin ta qarasa gaban gado tana
wurgi da dan kwalinta. Me yasa duk wani kafi da ta sanya aka mata baya aiki a
kanta?. Ta tambayi kanta da kanta. Duk mutumin da zata daukeshi aiki cikin
tafiyarta.....duk mutumin da zai ratso da kansa tsakiyar harqallarta sai ta
tabbatar ta mallaki bakinsa da tunaninsa.....to amma ita me yasa ta kasa samuwa
cikin tafin hannunta?.
"KINYI KUSKUREN ZABOTA......AKWAI NADAMA ME
YAWA......TAURARINTA BASA TABUWA" Duka maganganun bokan suka dawo mata
kamar sannan yake furta mata su.
Juyawa
tayi tana neman zama daidai nan musaddiq dake gaba ya shigo amna na biye dashi.
"Anni ce tace a kawo miki daki,idan kin huta sai
kici" Cewar musaddiq.
"Saboda ga mayunwaciya?.....shi zaki a jejinsa har sai
an masa tayin abinci?,aisaidai abinda ya farauto yaci ya bawa sauran namun daji
su qarasa abinda ya rage din" Ta fada tana makawa amna harara. Amna din
bata ko daga kai ta kalleta ba,tadai qarasa ta ajiye tray din kusa da inda
musaddiq ya ajiye nasa ta juya tana ficewa,sai shima ya soma bin bayanta ba
tare da kowa yace komai ba.
"Kai musaddiqu zo nan" Ta kirashi a fusace ganin
yabi sahun amna. Qofar ya saka zai dawo ciki ta watsa masa harara
"Rufen qofata shashasha mara kishin uwarsa,kaima ka
soma hawa turbar dan uwanka ko?,an zagi uwarku shine zungui zungui zakabi
bayanta?" Ta fada a matuqar hasale,a yau tana jin shi kansa musaddiq din
ya zama silar faruwar wasu abubuwan. Yau inda ace ya bata goyon baya da
nasarorin da zata samu zuwa yanzu sun haura haka.
Baice
komai ba ya rufe qofar ya dawo ya zauna yana dubanta.
"Uban waye ya siyawa waccar karyar 'yan barikin waya me
tsada har haka?" Ta fara jifansa da
tambayar da tafi damunta. Fuska yadan yamutsa kadan yana maimaita
sunan,hankalinsa ma gaza cafko ainihin wa take nufi.
"Kai maida hankalinka.....sabreena nake nufi" Cak
tunaninsa ya dakata na wucin gadi cike da mamaki. Dama addan take kira da
wannan mummunan sunan?.
"Hamma ne....amma ai ta cancanci abinda yafi waya ma
maamah,tunda ita din matarsa ce,kuma yana da halin siya mata,uwa uba ma kuma
tana da hankali da nutsuwa,ta cancanci fin haka ma"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.....kasan me kake
cewa musaddiq?" Maamah ta fada cikin tsananin tashin hankali,idan har
abinda kunnuwanta suke jiye mata lallai shima ya shiga tarkonta......sai taji
gaba daya hankalinta yana qoqarin kubce mata. Amma da yake bariki iyawa ce,sai
tayi qoqarin maida hankalinta gangar jikinta sannan ta zauna a gefansa.
"Amma meye amfaninka a gurinsa musaddiq?,dan uwanka
yana irin wannan almubazzaranci da dukiya amma kana ganinsa?,ba zaka saitashi
ba?,ba zaka hanashi ba?,ba zaka sanarmin ba don in daidaita al'amuransa
ba?,wayar million saba'in wa matarsa uwarsa bata da ta ko million
talatin?". Shuru kawai yayi maganganun maamah suna masa banbarakwai. Kai
tsaye zai iya cewa ta jahilci rayuwarsu da gasken gaske,kuma kome zai gaya mata
ba fahimtarsu zatayi ba,don haka ya zuba mata idanu kawai yana dubanta har takai
qarshen maganarta. Da kanta ta sallameshi ta koma tana zama cikin matuqar
firgici da bacin rai,zuwa yanzu tana kyautata zaton BOKAnta tabbas ya
gaza.....yaqin nan da bakinta zata yishi,da dukka wata power irin ta uwa da
Allah ya bata.
Wuni guda
gaba daya bata bawa kwanyarta wani sukuni ba ko kadan,gaba daya tunaninta ta
tattarashi akan yadda zata yanke wanzuwar sabreen cikin rayuwar d'anta. Zuwa
sannan jikinta yana bata ci gaba da wanzuwar sabreen din bazai haifar mata da
d'a me ido ba. A dukka shawarwarinta zuciyarta tafi rinjayarta ta bangare
guda......ta raba auren ko da tsiya koda tsiya tsiya......da qarfi da yaji koda
kowa hakan bai masa ba.....zata gwada qarfin qwanjinta da kuma adadin girma
izza da nata ikon na uwa.
Wannan
saqar data gama yi ita ta sanya ta fita cin abincin daren ranar da wani irin
izza da cikakkiyar qwarin gwiwar samun mafita.
Ta
samesu duka saman dining din,ta bisu da kallo daya bayan daya tana jin ciwon
yadda annin ta samu daman hade kansu duka,yaran da suke nata da wadanda suke ba
nata ba. Ta saki qaramin shu'umin murmushi qasan ranta tana bawa kanta tabbacin
komai dab yake da qarewa.....muddin ta samu nasarar yage KASKA wato sabreen
daga jikinta,sauran zata qarasashi ne da dukka qarfinta.
Kujera taja
ta zauna tana shaqar iska d'ai d'ai,ta sake ware idanunta tana nan sashen da
fu'ad yake saidai bata ganshi ba,ta buda baki zatayi tambaya ya shigo parlor
din da nutsatsen takunsa.
Sanye yake
da suspender da Fedora hat datayi matuqar masa kyau,tamkar wani baturen
England,kunnensa maqale da earpiece amma dukka hankalinsa yana kan sabreen dake
zaune gefe idanunta akan amna da wunin yau duka take more wayar sabreen din.
Wani abu ya sosa masa zuciya,baisan wanne irin taurin kai gareta ba......koda
wasa bai taba tunanin zata sanya qafa ta shure maganarsa ba,saidai nan kusa
yayi imanin zai ladabatar da ita don duka cikin halinta shine hali guda daya da
bazai iya jurarsa ba.
Kaman
dai dazun anni ta sanyata tayi serving nashi,ta miqe a hankali daga gefansa
tana qoqarin zuba mishi soyayyar shinkafar. Hannu ya sanya ya jawo cucumber a
gefansa ya tura gabanta yana fadin
"Slice it" Ya fada da wani irin shanqamshi daya
dan bata mamaki. Hannu ta saka ta jawota,ta dora saman plate ta soma yankawa.
Sosai zuciyarta tayi zurfi a tunani,abinda ya janye hankalinta kenan har wuqar
da take yanka cocumber din ta taba hannunta.
"Wayyo Allah na" Ta fada tana yarfar da hannu tana
jin zafi da radadin wuqar yana shigarta.
"Yankewa kikayi adda?" Amna ta fada da sauri tana
matsowa,abinda yaja hankalinsa kenan zuwa gareta daga kan wayar da yake
latsawa.
"Ya salam" Ya fadi yana jin tsigar jikinsa na
tashi da jinin dake biyo hannunta,har baisan sanda wayar hannunsa ta sulale ba
maamah tabi wayar da kallo.
Tuni ya
miqe ya kama yatsan da jinin ke fita yana kallo,har cikin jikinsa yakejin kamar
shi ya yanke din.
"Me yasa bakiyi a hankali ba?" Ya fada yana zube
mata fararen idanunsa. Kanta ta kawar gefe tana jin kallon nasa ya aza mata
nauyi da yawa,uwa uba ga maamah a wajen da batason komai ya sake hadasu.
"Musaddiq......duba dakin anni ka samo mana abun wanke
ciwo" Ya fadi yana janyeta daga tsakanin dining din zuwa kujerun falon ya
samu waje ya zaunar da ita yanayin tsaye a kanta.
Da qyar
maamah ta iya lalubar numfashinta,ya zama dole a yau ta datse wannan
igiyar......ya zama dole ta bata ta kuma tarwatsa koma meye yarinyar ta
qulla.....kowanne irin shu'umin malami ta samu ita mariya saita nuna musu qarya
suke duka ita dashi din.
"Idan ya gama qaramar haukar......ka gaya masa ni
uwarsa mariya ina kiransa zuwa dakina" Ta bawa musaddiq saqon don tana jin
kota gefansu ba zata iya rabawa ba bare ta tsaya tayi magana da dayansu shi ko
sabreen din. Kai tsaye hanyar dakinta ta nufa tana harhada hanya.....a yau koda
sakin sabreen shine abu na qarshe da zata aiwatar a rayuwarta saita tabbatar ya
afku kafin ranta ya fice daga gangar jikinta.
*_dan dan dan dan dan dan.........masu
karatu.....uhmmmmm......bakina da goro.....zamu gani kuma......shin xai tabbata
ko kuwa?,sai nace ku tara dani ranar litinin in sha Allah,na gode_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 96
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
*_Kina da buqatar fara kasuwanci amma baki da jari?_*
*_ko kina da jama'a amma baki da jarin fara kasuwanci?_*
*_kin cika wayarki da contact na qawaye da abokai amma bakya
qaruwa dasu?_*
*_MAZA ZO KIYI JOINING HUGUMA CLOSET_*
*_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun
suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_*
*lace*
*kowanne nau'in shaddodi*
*yadika na maza da mata*
*mayafai*
*lafaya*
*takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da
qanana*
*sarqoqi da agoguna*
*under wears*
*abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza*
*_SIYAN DAYA NE NA AMFANIN GIDA KO KUMA REPOSTING ZAKI DINGA
YI KINA DORA RIBARKI?_*
*_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?_*
*Sassauqan farashi me ban mamaki*
*_Qawata adonku da samar muku da latest kaya shine
muradinmu_*
____________________________
96
_An tambayi nana Aisha R.A,menene dabi'un manzan Allah S A
W,sai tace: dabi'unsa alqur'ani ne(ma'ana yadda qur'ani ke koyarwa da fadin
kalolin kyawawan dabi'u dukka haka halayen fiyayyen halitta S A W yake)_
A nutse ya zaunar da ita saman kujerun yana riqe da yatsar
tata tamkar wadda taji wani gagarumin ciwo. Sosai idanusa suka bayyana tsananin
damuwa,ya tsugunna a gabanta a hankali idanunsa na saman fuskarta. Bata yarda
ta kalleshi ba,tana ji kusancin dake tsakaninsu kaman yana sake yin yawa,tana
ankare da yadda maamah tabar wajen cikin wani irin yanayi da yafi kama da
zallar fushi da kuma fusata,a haka musaddiq din ya dawo ya aje masa qaramin
akwatin yana komawa da baya don barin wajen kaman yadda sauran suka bari da
d'aya da d'aya. Dukkaninsu wata kalar soyayya suke gani a shimfide saman
fuskarsa,kaman yadda idanunsa basu boye komai ba.
Murmushi ya subucewa farouq din yana jin fu'ad yana sake tafiya
dashi,duk da komai yasan yana yinsa ne ba cikin hayyacinsa ba saboda bugar
dashi da giyar soyayya tayi.......ya sanya P_cap dinsa yana daukar key din
motarsu ya saka a aljihunsa don fita dama ke garesu da daren ya soma sauka ta
bayan kujerun yana barin parlor din,don shi kansa bazai iya zama yaga ya wannan
love game din zai wakana ba. Wani sashe na zuciyarsa kuma cike taf da mamakin
mode din maamah......fushin dake tattare da ita da saqon data barwa musaddiq.
Ya jima yana wani tunani akan matar......ya dade yana wani hasashe a
kanta,saidai a sanin da ya yiwa fu'ad ba zasu kasa hasaso abu guda ba.
Zama yayi
sosai gaban nata yana fida spirit ya tsiyaya cikin wani dan abu na silver,ya
tsoma a auduga sannan ya dago yana kallonta. Still taqi bashi daman kallonta.
Wani irin yanayi takeji yana bibiyar zuciyarta kaman zai narkar da ita. Yau ita
sabreen yankewarta a hannu ya zama damuwar wani?,wani baqon lamari ne a wajenta
da batasan ya zata fassarashi ba.
"Kin shirya?" Ya tambayeta da wani irin sauti,kasa
ce masa komai tayi sai ya dora audugar saman yatsan nata.
"Wash" Ta fada tana qoqarin janye yatsanta gami da
runtse idonta.
Hanata
daman hakan yayi,sai ya zubawa fuskarta idanu yana ganin yau d'aya wannan
tsiwar ta tafi sai alamun rauni da radadi.
"Am sorry" Ya fada can qasan maqoshinsa da wani
kalan sauti daban ba irin na dazu ba,abun daya tilasta mata bude idonta ta
zubesu cikin nasa. Abinda yakeso dama kenan,sosai yayi qoqarin riqe qwayar
idanunta cikin nasa,ya matso da yatsar saitin bakinsa yana busa mata a
hankali,abinda ya hadu da sanyin spirit din dana bakinsa ya bada wani abu daya
sanya tsigar jikinta zubawa,tanaso ta janye hannun ya hanata,hakanan dole tabar
masa hannun tana jin yadda jikinta duka ya mutu.
"Ya daina zafin?" Ya tambayana yana dorawa kansa
alhakin yankewartata. Kai ta gyada masa a hankali,burinta kawai ya gama yabar
mata hannunta ya matsa daga kusa da ita din.
Tsaf
ya gyara,saida jinin ya tsaya da fita sannan ya kammale komai,ya qwalawa amna
kira ta qaraso.
"Ki dauke kayan.....ki kula da ita zanje na dawo,zamu
taho tare da anni" Kai ta gyada tana tsugunna tana hade kadan gami da yiwa
sabreen sannu. Kai kawai ta daga,ita bataga wani ciwo da taji wanda yakai
girman sannun da take mata ba.
Hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana kallonta,har sai da amna ta
gaya hada komai suka wuce dakin annin.
Ajiyar
zuciya ta subuce masa,yana saqa abubuwa da yawa a kanta,sai sannan ya duba inda
yabar farouq a zaune,baya nan,yasan kuma ya fita qilan yana jiransa cikin
mota,don haka sai ya fara takawa a nutse yana barin parlor din ba tare da
musaddiq daya basu space ya isar da saqon maamah ba.
A mota ya
samu farouq yayi d'ai d'ai suna shan hira da fanna dinsa. Kusan duka hirarsu
yanzu tafi rinjaye ne akan shirye shiryen bikinsu. Baice masa komai ba ya miqa
masa hannu ya karbi key din motar ya shiga ya tayar da kansa suka fara fita
daga gidan gaba daya.
Basuyi
nisa sosai ba farouq ya kammala wayarsa,ya ajiyeta gefe yana cewa.
"Sai yanzu hankalinka ya dawo kenan?" Ya fada yana
kanne ido daya da sigar tsokana. Waiwayawa yayi ya balla masa harara sannan ya
dauke kansa,kaman bazai tanka ba sai daga baya yace.
"Ina baka shawara kaqi ji ko?.....ina gaya maka ka
dauke idanunka daga kan lamarina ni da iyali na amma kaqi ji ko?". Sosai
dariya ta zowa farouq,ya kuma soma yin abarsa yana cewa.
"Allahu akhbar......dadin abun ma muma mun kusa aje
iyalin nan muji abunda akeji......muji ya giyar soyayyar nan take bugar da
mutum" Qaramun murmushi ya saki daya sake fidda kyan fuskarsa yana duban
hanya.
"Kota tashi bugar dakai farouq ba zaka ji abinda nakeji
a kan sabrrr ba.....nata son daban yake a zuciyata......ban taba jin soyayyar
abu a raina har haka ba.....bansan daga ina wannan qaqqarfar alaqar ke sake
gina kanta ba duk wayewar gari zuwa faduwar rana" Yakai qarshen maganar
yana furzar da numfashi a bakinsa.
Ido farouq
ya zuba masa.......tabbas zuwa yanzu ya tabbatar da gaske MAHAUKACIN SO fu'ad
din yakewa sabreen,irin soyayyar da bai zaci zata kamashi ba har ibada.
Miskilancinsa da komai nasa na dabanne.......amma zuwa yanzu soyayya tana
sauyashi zuwa wani mutum na daban,idan ya zauna yana masa magana akan yadda
yakejin sabreen din cikin ranshi abun yana bashi mamaki sosai......yana jin
kaman ba me babban sunansa ba,wanda komai da kowa basu dameshi ba idan ka cire
su da anni.
"Inaji a raina da zuciyata......akwai wani abu cikin
rayuwarta......akwai boyayyen abu.......i need to know farouq".
"Kabi a sannu........da sannu zakasan komai din".
Kai ya gyada masa.
"Na sani......but am eager to know about everything
about her......inaji kaman akwai sauran mutane daya kamata na hukunta bayan
wadanda suke hannuna yanzu" Yayi maganar yana jin kalmar karuwa da
kowannensu ya taba fada a kanta tana masa zafi har can qasan ransa.
"But naji maamah tana nemanka ma...." Farouq ya
fadi yana tsoron kada fu'ad din yaji amma yaqi zuwa.
"Maamah kuma.......ba wanda ya fadamin" Ya furta
haka kawai yaji gabansa yana faduwa. Ba kasafai kiranta ke zama alkhairi
ba.....kai zaima iya generalizing cewa kiranta ba wani alkhairi ko abu me
muhimmanci da d'a zai iya tsinta a cikinsa.
"Musaddiq ta fadiwa.....bansan me yasa bai gaya maka
ba"
"Yabar parlor din ne......anyway koma meye zamu koma
gidan.....saina qarasa" Ya fadi zuciyarta tana son lalubo dalilin kiran
amma ya gaza.
Kai kawo
ta dinga yi cikin dakin nata tana tattare kowanne tashin hankali da take ganin
zata sauke masa har zuwa sanda zata tursasashi guntule igiyar jarababben auren
data hada. Bata taba dana sanin aikata wani abu ba irin hada aurensa da
sabreen......tabbas yarinyar tana neman zame mata qadangaren bakin
tulu......itace cikakken ma'anar karin maganar nan da ake cewa DAN HAKKIN DAKA
RAINA SHIKE TSONE MAKA IDANU. Inda qannenta suna hannunta kawo yanzu tayi imani
da yaqinin da batasan ma wanne hukunci zata sakasu su karba ba a madadin 'yar
uwarsu ba.
Minti daya
zuwa goma sha biyar ta lissafa amma bataji shigowarsa ba,wannan ya sakata
daukan wayarta ta kira musaddiq.
Ba'a daga
ba amma taji an turo qofar dakin nata an shigo. Koda ta waiwaya musaddiq
dinne,ajiye wayar tayi tana dubansa.
"Ina yayan naka?".
"Na shiga daki kafin ya kammala,ina fitowa na tarar sun
fita shi da BB farouq". Wani irin kallo ta watsa masa cikin fushi tana
qanqance idanu.
"Kasan me kayi musaddiq?!,kasan muhimmancin wannan
kiran kuwa?....har yakai na baka saqo ka kasa zama ka jirayeshi ka isar
masa?,kana hauka ne musaddiq!" Ta fada da wani yanayi daya bashi mamaki me
kama da zata kai masa duka. A mamakance ya shanye mamakin yana yin qasa da
kansa kafin yasake dubanta.
"Kiyi haquri,idan ya dawo saina sanar masa,ko ina
sukaje nasan ba nisa sukayi ba".
" Baka da hankali.....bani da wannan lokacin,bani da
Lokacin bata lokaci......wuce ka kiramin sabreen" Ta sake fada cikin daga
murya tana nuna masa qofa.
Mamaki ya
sake kamashi ganin yadda ta birkice,yaga dai koma meye duk inda sukaje a gidan
zasu dawo su kwana.....amma duka me ya kawo wannan yanayin mara dadi?. Yankewa
kansa wahalar tunanin yayi ya juya a salube yana fita a dakin.
Tana
zaune daga gefan gadon tana duba hotunan da amna tace ta dauka a wayarta sanda
saqon ya isketa. Ta daga kai tana duban musaddiq a mamakance.
"Taje inji maamah" Ta sake maimaita saqon tana
zubewa musaddiq dubanta. Tana juya dalilin kiranne da kuma abinda zai iya biyo
baya a kiran. Bawai tana tsoron zuwa bane.....babu shakkarta ko dis cikin
ranta.....bata wani tsoro ko shayin fuskantarta......kawai tana duba girman
musaddiq ne da tabbas zata ce masa yaje yace mata bata zuwa.
"Gani nan zuwa" Ta amsa masa tana aje wayar a
gefanta sannan ta miqe tana zura qaramin Malaysian hijab dinta ta taka a
hankali tana dosar qofar fita a dakin. Zuciyarta fal saqe saqe,cikin jikinta
takejin koma meye ya sanya ta kira BA ALKHAIRI BANE.....koma meye kuma ta
shirya fuskantarta.
Tana
tsaye ta zubawa qofar idanu tana dakon shigowarta,tana jin kaman tayi nawar
isowar.....a haka ta murza qofar ta shigo kai tsaye ba tare data maida qofar ta
kulle ba. Kallon kallo suka yiwa junansu me wani irin zurfi kafin maamah ta
soma magana.
"Bakisan adadin kuskure da wasan da kikayi da rayuwarki
ba sabreen......bakisan gona da adadin iyakokin da kika sanya qafa kika tattaka
ba......amma koma meye a yau zan yanke wannan alaqar da kike taqama
dashi......yau dinnan.....kuma a nan wajen zan tabbatar miki da tsinkewar
igiyoyin aurenki". Manyan idanunta ta maida ta lumshesu a nutse sannan ta
budesu.
"In har don wannan ne ni banga dalilin kirana da kikayi
ba......wani abune da ke daya ya shafa maamah.....don Allah saboda daraja da
mutuncin musaddiq da nake gani na roqeki kibarni na huta..... Allow me to
rest.......tsakanina dake ba kare bin damo. Contract ne nace bazanyi ba dama ba
tun yau ba,yana da wahalar gaske na yiwa rayuwata hukunci ayi challenge dina a
sakani warwareshi......na bar miki contact dinki......na karbi rayuwar qannena
kuma akwai abinda yayi saura?" Ta qarasa maganar tana zube mata idanunta
wadanda suka fara tunasar da maamah wace ainihin sabreeen din......ta fara
juyewa kuma zuwa tsohuwar sabreeen da ake dab da jana'izar halayenta.
Wani
irin mamaki maganganunta suka bawa maamah din,ranta ya sake dugunzuma.
"Kina tunanin kinci bulus?,rayuwar yarona zaki gwadawa
bariki?,a gaban idanuna zaki gwada aiki a kansa?"
"Wanne yaron naki?" Ta fada cikin calmness.
"Indai wannan ruhin dakike burin mallaka ne kike
tunanin nayi wani abu a kai to ki hutar da kanki......banason wata hayaniya
akan hakan don bani da sauran buqatarsa a rayuwata".
"Yanzu kuwa zan tsinke duk wasu igiyoyi da suke
tsakaninku" Ta fada a zafafe tana sungumar wayarta. Tana jin ya mata tsaho
ta jirayi dawowarsa......ya mata tsaho har sai sanda ya dawo gidan ta gwada
mata koda magani ko babu akwai sauran power na uwa da zata iya sakashi ya mata
dukkan abinda tayi niyya.
Mamakin
maamah din ya sake cika sabreeen din. Tanaso ta gogewa matar haddar kanta
tsaf.......tanaso ta gwada mata wani abu kansa amma inda akaci sa'a har yanzun
da take tsaye bata jin jituwar halayensu shi da ita.....tabbas don a tsukin
kafin ta hada karonta tabar rayuwarsu saita aje mata zazzafan darasi.
Mummunan faduwa gabansa yayi sanda kiran ya shigo wayarsa,abinda zai iya
cewa ya manta rabon da ya jishi.
"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis......aslih li
sha'ani kullahu fala takilni ila nafsi darfata ainin" Ya motsa bakinsa a
nutse ya karantata kafin ya daga wayar ya hadata da earpiece din da ya jawo ya
saka a kunnensa,don ba kasafai yake magana da ita a hands free ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 97
97
_An rawaito daga
manzan Allah S A W yana cewa"babu wanda zai shiga aljanna alhali akwai
qwayar zarra na haqqin dan'uwansa a kansa_
_Bukhari da muslim_
"Muhammadu kana jina?" Tayi lafazin da wani irin kaushi.
"Ina jinki maamah"
"Indai ni uwarka ce dana haifeka.....na shayar dakai
nono na har ka zama mutum.....ina umartarka a duk inda kake ka dawo gida yanzu
yanzu......a sanda kake shigowar kuwa ina buqatar shaidar sakin matarka
sabreeen......ma'ana ka datse dukka igiyoyin aurenka dake wuyanta.....muddin
baka dawo ka aikata hakan ba daga yau ka dauka sunanka tsina......". Da
wani azama ya latse kiran don bazai iya saurara ba. Sauti mafi muni da zai iya
cewa kunnuwansa sun sake saurara kenan bayan tsahon shekaru.....sauti na biyi
da ya kusa sanyashi kaman zai zare bayan sautin ALLAH YAYI MASA RASUWA ME
BABBAN SUNA.....KUYI HAQURI...a ranar da ake gaya masa rasuwar mahaifinsa.
Subuce
masa steering motar yayi abinda ya ankarar da farouq kenan,ya sanya hannu da
wani irin zafin nama ya kamoshi yana furta.
"Subhanallah" Da wani irin qarfi. Karbar steering
yayi yana qoqarin maida hankalinsa jikinsa amma sai yaji hakan ya
gagareshi,wannan ya sakashi gangarawa gefan titi ya tsaida motar yana fita daga
ciki.
Numfashi
yake ja sosai zuwa hunhunsa yana jin iskar da yake shaqa ta masa kadan,ko
tambaya daya ya kasa amsawa farouq dake gefansa,sai daga baya ya fusgi kalmar
"Mu koma gida farouq.....now" Bai musa ba ya bude
masa murfin motar,ya taka da wani irin yanayi yana shiga,shima ya shiga
mazaunin driver ya kunna motar yana juya kanta zuwa hanyar da suka baro.
Ga
mamakinta sanda ta sauke wayar a fusace saita samu idanun sabreeen a kanta da
wani irin nutsuwa tana dubanta.
"In don wannan abunne.....ai da basai kin tasoni
ba,zaki iya aiwatarwa koda bana wajen" Ta fada tana zama saman stool din
dakin tana kallonta.
"Sabreeen tana zaman zamanta aka gayyatota kan abinda
bai cikin tsarinta......sabreeen tace bataso.....ba zatayi ba akayi amfani da
rayuka uku masu matuqar muhimmanci fiye da nata ruhin aka sakata yin abinda
bata taba yiwa wani ba......ta yaya a yanzun saboda ita din ba kowan kowa bace
za'a cisgeta daga inda aka dasata?" Kai ta girgiza.
"Yadda aka gayyatoni ba shiri......bazan fita a sanda
ban shirya ba,saboda gaba a guji taba rayuka irin na ameenatu din.....da kin
kwantar da hankalinki ma zan fita.....amma fa a sanda nayi niyya,a sanda koshi
wanda kika hada alaqarmu dashi din bai shirya ba......amma tunda kin zabi na
fita a sanda kikeso kaman yadda kika shigo dani a sanda kikeso......inajin ya
kamata shi wanda akayi komai dominshi yasan yadda aka qulla abun aka kuma
warwareshi.....don nagaya yanamin wani gani gani yana kuma kallona a matsayin
makwadaiciyar dukiyarsa......bayan kuma ata nan gefansa akwai uwarmu gaba
daya" Tayi maganar fuskarta da
murmushi kaman me fadin wasu kalmomi masu dadi. Abinda kenan yake sake qule
maamah......yadda qaramar alhakin ke zama tana yaba mata zance duk yadda taga
dama. Iya wannan kadai ya isheta hujjar qwace suna da license na zama
surukarta. Suruka take nema irin wadda zata juyata kaman d'iyar data
haifa,wadda zata bita kaman yadda raqumi yake biyar akalarsa ba saba hanya.
"Kina tunanin ke dinnan qaramar alhaki kina da wani
hujja dalilo ko qwarin gwiwar fadan magana akaina d'ana ya yarda?".
"Aah" Ta fada idonta akan wayarta tana dannawa
wadda ke sake tsokane idanun maamah.
"Ni bance dole ya yarda ba....amma dai qila wannan zai
taimaka" Ta qarasa maganar tana kunna wani sauti wanda sai data waiwayo
dashi maamah ta fahimci video ne.
Tayi
matuqar kaduwa,ta kuma yi mummunar razana da yadda ta gansu tarwai ita da Hajj
harira......rana ta farko da suka fara takawa gidansu dakinsu suna gabatar mata
da contract din aurenta da fu'ad. Komai ya fita kaman yanzu ake dauka,da sautin
muryarsu da komai.
Boyayyen
murmushi ta saki ganin yadda abun ya daki.maamah da wani.irin razanannen
yanayi. Boyayyar CCTV camera din data saka a parlor din kenan ba tare da sanin
kowa ba. Zama da JIB ya qareta abubuwa da yawa,tun sanda tayi noticing canzawar
huda awancan lokacin da Naseer yaso bata ta,ta yanke ta sakata,wanda ita ta
taimaka mata taga duk wani motsi na huda.....ya kuma sake qarfafa mata zargin
da shi yayi sila ta gano komai.
"Wannan kawai zan nuna masa don yasan cewa bani na kawo
kaina rayuwarsa.......ba sonshi nake ba.......ban taba kuma sonsa
ba.....banajin kuma zan soshi din.......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki
yayi......" Maganarta ta tsaya a nan sanda lallausan qamshinsa ya marabci
hancinta.....kaman giftawar walqiya kuma sai gashi a wanze cikin dakin a wani
birkitaccen yanayi.
Wani irin
kallo da yake saukar mata shi ya sanyata zare idanunta daga kanshi. Wani irin
birkitaccen kallo yake mata zuciyarsa na wani mahaukacin bugawa da kalamanta na
qarshe da kunnuwansa sukayi katarin ji
"Ba sonshi nake ba......ban taba kuma sonsa ba,bana jin
kuma zan soshi din......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki
yayi......". Inda tasan girma da nauyin da kalaman sukayiwa qirjinsa
tabbas ba zata fadesu ba.
Janye nasa
idanun shima yayi daga kanta da suke sake sauya launi saboda bacin ran da
yakeji cikin ransa. Yayin da idanun maamah suke zube a kansa ita
kuma.....zuciyarta na quna tare da jaddada mata baqar mallaka sabreen din tayi
masa da yake kasa sukuni a duk sanda take waje......yake kasa aza idanunsa akan
kowacce halitta idan ba ita ba.
Da
confidence dinsa ya shiga cikin dakin,yana jin cewa idanma tazo ta gayawa
maamah ne bata sonshi don ta sanya su rabu.....ba shakka ta dauko aikin da
bazata iya qareshi ba.....a yanxu a kuma yadda yake jinta a kusa da kowacce
jijiya ta jikinsa.....ko mutuwa bayajin xaya lamuncewa ta rabashi da ita.
"Gani" Ya fada yana dosana gefan sofa din dakin.
Idanu
maamah ta zuba masa tana jin wani irin abu yana birkitata. Ga qoshi ga kwanan
yunwa,gashi a gabanta cikin qasa da mintunan data nema ya isketa......gashi a
gabanta cikin neman umarninta ya kuma cikashi.....rijiya ta bada ruwa guga ya
hana. Ko sau daya koda a cikin mafarkanta na zahiri da na badini.......bata
taba tunanin sabreen din nada kaifin basirar ajiye kowacce hujja data shafi
rayuwarta ba.....tunanin hana faruwar hakan ya sanyata bata waya ta musamman da
zasu dinga communicating......wadda bata nadar komai....komai din kuma idan ya
nadu ma zai goge kanshi da kanshi ne automatically.
"Tashi kaje kawai.......zan sake nemanka a lokacin da
ya dace" Ta fada tana zubewa sabreen wani kallo dake nuna zallar gargadi
da yiwuwar afkuwar komai a karonsu na gaba.
Sam sam
sai yaji hankalinsa ya gaza kama maganar maamah din.......kamar ba ita bace ta
kirashi ga waya mintuna kadan da suka shude ba cikin wani irin zazzafan
yanayi?,to meye ya sauyata da sauri haka?.
Waiwayawa
yayi kai tsaye yana duban sabreen,saidai idanunta kaf baya kansu yana kan wayar
hannunta. Sake maido dubansa yayi ga maamah,har yanzu shi take
kallo......saidai kuma da alama kalaman bakinta na sallamarsa ba sune a qasan
zuciyarta ba.
"Kaje nace" Ta sake maimaita masa tana fargabar
kada yaci gaba da zama ta kunna video din a gabansa. Kaman bazai miqe ba sai
kuma ya miqe din,ya sake duban sabreen da still tayi kaman bata wajen kaman
kuma ba kowa cikin dakin. Maganganunta suka dinga tsikarar zuciyarsa da wani
irin ciwo. Girman qin da take masa har yakai ta zauna ta fayyacewa duniya?,ta
fayyacewa kowa?,shi kam idan bai dasawa sabreen jarababben sonshi ba rako maza
yayi duniya kenan,da wannan zafin da fushin ya fice a dakin.
Miqewa
tayi sanda ta tabbatar ya fita,tadan kalli maamah din kadan,kaman zatayi magana
sai kuma ta shanyeta tana tuna cewa ba sa'arta bace.
"Karki saki jiki kiyi farinciki da tsammanin kin kubuta
ko kinci nasara akan mariya.....a'ah....wasa farin girki wannan,hausawa sukace
somin tabi ne wannan hatsin gara a buta". Dan waiwayowa tayi,sai ta sake
mata murmushi kawai tana sanya qafarta waje.
Bawai
kaman jiran fitowarta yake ba......dama jiran fitowartata yake......ba zato ba
tsammani taji ya cafke hannunta,bai kuma tsaya sauraren komai ba ya soma tafiya
da ita zuwa bakin qofa.
"Ina zaka kaini?.....ina zamuje?.....ka sakarmin
hannuna......wannan bai kamata ba,ni ba inda zanje......ka sakeni......wai ina
zamuje?" Ta sake tambayarsa da qarfi wanda ko sau daya bai waiwayo ya
kalleta ba sai daya tabbatar ya sanyata cikin motar ya kwashe qafafunta ya
maida ciki ya rufe ya kuma zagayo ya zauna gefanta.
Wani irin
zama da ya bata daman jin irin hucin dake fita daga can cikin zuciyarsa har
saman fuskarsa. Ya tsareta da kallo da idanunsa da sukayi kaman kwanciyar jini
daga qasansu saboda zallar bacin rai.....farar fatar fuskarsa itama ta canza
launi zuwa reddish kaman wanda aka dinga yamutsa fuskar da maruka.
"Zan kaiki na killace......a muhallin da ba wanda ya
isa ya ganki......zan kaiki inda zamu rayu daga ni sai ke.....zan kaiki inda ba
zaki sake ganin kowa ba sai muhammad fu'ad.....zan kaiki wajen da soyayyar
fu'ad ce kadai 'yancinki da zaki samu" Yayi maganar yana sauke don rage
radadin da zuciyarsa ke masa. Kafin tace wani abu ta fahimci motar tasu ta fara
motsawa tana fita daga gidan.
Hankalinta ya dan tashi,saboda sanin halinsa da tayi,to amma sai tabi
shawarar zuciyarta ta hanyar dakewa kaman abinda ya fada din bazai tabbata ba
ko bai dameta ba.
Tana iya
jin wata irin birkitacciyar ajiyar zuciya da yake saukewa,har tsakiyar
kwanyarta takejin fitar ajiyar zuciyar wanda ba zata ce ga dalili ba. Ya maida
bayansa yayi relaxing sosai jikin kujerar yana sauke numfashi kaman wanda yaci
kuka. A hankali taji ya laluba tafin hannunta ya sanya nashi. Mannewa sukayi
guri guda abinda ya sanya tsigar jikinta tashi,tana iya jin yadda dumin tafin
hannunsa yake bin kowacce jijiya ta jikinta dake aika saqo,tayi yunqurin zame
hannun amma ya hanata,saima ya sanya hannunsa guda daya ya tayar da motar,cikin
qwarewa yake sarrafa steering din da hannu daya suna ficewa daga gidan.
Batace masa
komai ba.....amma jikinta ya soma sanyi da ganin hanyar da suka dauka. Basu
taba bin hanyar ba duk a fice ficensu.
Wani irin
guri ne da zata iya cewa tsahon rayuwarta bata taba ganin gurin makamancinsa
ba.....wani tsuburi na musamman dake kewaye da ruwa wanda kafin su qarasa dab
da wajen ya ajiye motarsa,tun bai fito ba ma'aikatan gurin suka qaraso.
Idanunta ta daga tana duban sunan dake maqale a signboard CONRAD RANGALI ISLAND
RESORT. Sanda take dawo da idanunta ya kammala kashe motar ya zare belt din
jikinsa,tattausan tafin hannunsa ya miqa mata yana tsareta da fararen
idanunsa,a hankali ta kalli hannun sannan ta kalli fararen qwayar idanunsa da
suka fara komawa daidai a lokacin.
Yayi wani
irin laushi gaba dayansa,tun daga qwayar idanunsa zuwa gangar jikinsa zaka
karanci hakan.
"Banaso.....karkimin musu.....na gaji.....na gaji da
jin musu,taurin kai,saba maganata.....i beg you koda na awanni kadanne kawai
kibi umarnina,koda na iya yau ne" Ya fada da wani sauti me matuqar laushi.
Haka kawai taji wani abu me kama da tausayi yanason saukar mata.......duk wani
izza da qasaita nashi duka ya zuge tsakanin tafiyarsu zuwa yanzu. Gefe guda
halaye da dabi'un matar da take kiran kanta a matsayin mahaifiyarsa yana dawo
mata. Wanne irin barazana wannan uwa keyi da rayuwar d'anta?, ta tambayi kanta.
Tunawa take da rayuwar da tayi a gidansu,tsakanin kawunta da kishiyoyin
mahaifiyarta,dabi'unsu da mu'amalarsu a kanta gaba daya wasu iri ne da basu da
dadin ji ballantana gani.....ta fuskanci rashin nutsuwa da barazana me tarin
yawa......yau inaga ace mahaifiya da kanta keyi maka haka?.
Tana
tsaka da wannan tunanin ta tsinceshi saman kanta,har ya zagayo ya bude mata
qofar side dinta,bai gaji ba ya sake saka hannunsa ya kama tafin hannunta yana
tayata fita a motar.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 98
98
_Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin
ayyuka da kuma tarin lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar
dashi,ga tarin mutane da baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman
haqqinsu ne a kansu a wajen Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya
zalunci wannan,ana biyansu da haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai
cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa sun qare za'a koma ana diban zunubin
mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana lafta masa,daga qarshe sai ya tashi
baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi umarni wa mala'iku su jefashi a
wuta( Allah ka tsaremu🙏🏽)_
_bukhair da muslim_
Sosai ya riqeta yana zagayo da hannunsa zuwa qugunta,sai ta kasa janyewa
kaman yadda ta saba saboda idanun mutane,zagaye da ma'aikatan suka taka har
zuwa inda wani boat ke ajiye. Kadan kadan zuciyarta ke bugawa saboda
shimfidadden ruwan dake zagaye da wajen fari qal da yake bada wani color me
kama da sky blue.
"Ina zamuje saman ruwa kuma?" Ta tambayi kanta
tana jin tsoro yana shigarta. Tunda take a rayuwarta wanna shine karo na farko
da zata taba shiga jirgin ruwa,duk da wannan din wani irin jirgi ne da zai nuna
maka tsadar da yake dashi,tsarinsa daban yake da sauran jiragen da take
gani,yana da wata fargajiya da kujerun zama masu daukan hankali.
Bata
fahimci maganar da suke ba don cikin harshen Dhivehi suke magana yaren 'yan
qasar. Can qasan ranta tana mamakin yadda ya iya harshen haka,a zamanta dashi
taji yana yaruka kala kala da batasan yadda ya iyasu ba. Hannunta ya sanya
cikin nasa suka fara yin gaba don shiga boats din,saita tsaya ba tare data
motsa qafarta ba tana matse yatsunsa cikin nata ba tare da tasan tayi hakan ba.
Zuciyarta ke bugawa kadan kadan cikin tsoron shiga boats din,ta yaya zasuyi
tafiya saman ruwa?,ruwan ma shimfidadde irin wannan?.
Kallo
daya yayi mata ya karanci tsoron da yake idanunta,yayi qasa qasa da muryarsa
duk da bajinsu za'ayi ba yace
"You're safe.......idan kina tare dani you are
safe......ki shirya zamu koma rayuwa cikin ruwa,har sai sanda kika koyi
soyayyar muhammad jadda.....i can't lose you" Yana kaiwa nan ya sake
sanyata a jikinsa sosai yana takawa da ita saman katakon da zai qarasa dasu
cikin jirgin.
Dole
qanwar naqi tsoron ya ladabtar da ita tayi zaune cikin jikinsa,har zuwa sanda
suka qarasa shiga,sai a sannan taga irin qawatar da aka yiwa boats din
sosai,banda saman ruwan suke da bazata yarda cikinsa suke ba. Bai barta ba sai
daya zaunar da ita saman qawatattun kujerun dake a wajen,ya samu wadda ke
fuskantar tata ya zauna yana goye hannayensa a qirjinsa idanunshi a kanta. Har
yanzun idan ka masa zuzzurfan kallo zaka karanci ranshi yana bace ne,yana kawai
qoqarin dannewa ne. Tana jin nauyin idanunsa a kanta sosai,inda zai mata
alfarma da ya rage nauyinsu a kanta. Ma'aikacin jirgin ne ya qaraso yana miqa
masa wasu qananun blanket guda biyu masu taushi,ya sanya hannu ya karba ya
ajiye a gabansa daidai sanda jirgin ya fara motsawa yana harbawa cikin ruwan.
Ido ta
runtse tana curewa waje daya,'ya'yan hanjinta suna kaduwa tana jin kaman zata
nutse ne a ruwan,sanda jirgin ya tashi sosai ya fara keta ruwan da gudu sai
taji kaman kanta zai juye,wannan ya sanyata bude qafafunta ta cusa kanta a ciki
zuciyarta na wani irin bugu.
Batasan sanda ya iso gabanta ba,ta daiji lausasan hannayensa saman tafin
qafarta. Ta dago idanunta a hankali tana kallonsa,sai ya miqe ya ware blanket
din yana lulluba mata,sannan ya koma ya tsugunna a gabanta yana lalubar tafin
hannunta. Bata hanashi ba,don tana buqatar wani a kusa da ita,yadda ruwan keyi
takejin kaman zasu fada ne,sai ta maida idanunta ta kulle gam.
Tana
jin yadda yake murza tafin hannun nata daga gefe,tamkar me dauke da wani sihiri
a nasa a hannun......a hankali sai taji bugun zuciyarta yana daidaita,tsoronta
yana raguwa sosai.
Tafiyar mintuna idanunta suka fara hangen wani gini tsakiyar
ruwan,mamaki ya cikata har sai data ware idanunta sosai tana duban ginin.
Qawataccen gini ne da yake a tsakiyar ruwan,tako ina ruwa ne ba wani qasa a
wajen ko wani tsandauri kusa da wajen bare tace ga yadda akayi dabara aka dora
ginin.
"The Muraka hotel" Ta fadi sunan data gani an
rubuta manya manya sama.
"Hotel?" Ta maimaita sunan qasan ranta,wanne irin
hotel ne haka tsakiyar ruwa?,ta sake tambayar kanta a mamakance. Kada dai yace
mata nan zasu zauna?,cikin ruwan kaman wasu 'ya'yan aljanu?.
A sanyaye
ta aza idanunta a kan fuskarsa sanda jirgin ke tsaiwa daidai wata hanya me kama
da gada da ta tabbatar ta nan ne zasu qarasa ainihin ginin hotel din. Girarsa
duka biyun ya dage mata da wannan miskilar fuskar nashi,sannan ya miqe a nutse
yana zare hannunsa daga nata,ya miqa hannun ya cire mata blanket din sannan ya
sake kamata ta miqe tsaye suna fita a boat din yana magana da ma'aikatan.
Wata
qaramar mota ce me qafa uku me budadden sama ta tsaya a gabansu,ya kama mata
hannu tana taka cikin motar sannan shima yabi bayanta,a hankali driver din ya
gaidashi ya amsa masa da yarensu sannan ya tashi motar suka fara ratsa gadar.
Tashin
hankali.....ta fada a ranta tana ware idanu tana kallon rayuwa a cikin ruwa.
Tun basu qarasa ba ta dinga ganin mutane jifa jifa tsakanin hanyar zuwa hotel
din suna al'amuransu hankali kwance. Ita kallon ruwanma kawai dake gefe da
gefen gadan ta qasansu daga mata hankali yake,a tsorace take har batasan sanda
ta cure a kafadunsa ba.
Boyayyen
murmushi ya saki batare daya kalleta ba bare ta gane hakan. Yana buqatar wannan
tsoronne dama a tattare da ita,samuwar tsoron shine zai sake kusantata
dashi......samuwar tsoron shine zai tattaro masa dukka rayuwarta a hannunsa,a
inda ba anni ba amna.....ba farouq ba musaddiq ba kuma saddiq ballantana tayi
tunanin zata janye jikinta dashi,zata rayu dashi shi kadai......daga shi sai
ita a duniyar da ba wanda ya sansu,a duniyar da bazata iya guduwa ko ina ba.
Gajeriyar
tafiya ce ta kaisu bakin qofar shiga hotel din. Luxury iya luxury da ko bakasan
abinda duniya ke ciki ba idanunka zasu gaya maka. Wani irin gini na alfarma da
zata iya cewa bata tsammaci samunsa a haka ba.
Wayarta
dake hannunta tadan kada,ta bude tafin hannunta tana kallon fuskar wayar.
"Welcome to the muraka,the first world's under water
villa" Idanunta ta janye daga kan wayar tana maidawa fuskarsa,sai ta kasa
cewa komai illa tsoro da take sake jin yana mamayarta.
Binsa
kawai takeyi har zuwa reception,inda suka karbi komai ya kuma sake riqe
hannunta suna takawa a hankali zuwa dakinsu.
Ta kasa
tsaida idanunta guri daya,mamakinta yanata qaruwa yadda take taka wajen tamkar
a gida. Tana taka tsandauri alhalin tasan tsakiyar ruwa suke tsundum,ta sake
riqe yatsunsa da kyau ko tsoron da takeji zai ragu.
Sanda yake
bude qofan living room din dake dauke da bedroom dinsa da toilet harda kitchen
mutuwar tsaye tayi. Glass doors ne tako ina da zai baka daman ganin kowacce
fuska ta shimfidadden ruwan da suke kai. Luxury suite ne dake da bedroom biyu
living room biyu duk da daya take gani a yanzun. Baice mata komai ba yana riqe
da hannunta har suka shiga bedroom din.
Zare
hannunsa yayi daga nata,yaja baya yana zube hannunsa a aljihun wandonsa yana
dubanta.
"Ga first bedroom.....muje kiga dayan,saiki zabi wanne
zaki zauna a ciki" Yayi maganar idanunsa suna lumshewa yana jin wani abu
ya soma fusgarsa a kanta. Fararen idanunta ta aza masa,ita sam batasan ma yadda
zata kwana cikin wannan ruwan ba,hannunsa ya miqa ya sake riqo yatsunta yana
fita a dakin.
Daga
wani sashen daban suka iske stairs da sukayi qasa,ya ware yatsunsa yana zurasu
cikin nata ya jawota jikinsa sosai sannan suka fara takawa zuwa qasan.
Idanunta ta fidda sosai zuciyarta na harbawa da mugun gudu ganin suna
nutsewa qasan ruwa. Tsoronta ya sake ninkuwa tana kallon yadda sukeyin qasa ta
bangon glass da ginin yake dashi. Jikinta duka ya dauki rawa ganin yadda
halittun ruwa ke linqaya a cikinsa suna wucewa abinsu hankali kwance ta bangon
glass din.
"Hamm......" Ta motsa bakinta don kiran sunansa
amma saita kasa. Ya jita sarai,kuma yana jin tasirin tsoro sosai a muryarta da
jikinta duk da bai waiwaya ya kalleta ba. Idonsa ya lumshe yana son sake jin
sunan HAMMA a bakinta wanda sau daya tak
ya taba ji ta ambata a wancan ranar. Ba inda zai kawota ya boyeta yadda yake
so......ya dora mata karatun da yakeso irin nan din. A nan ne kawai yake da
tabbacin cire wannan tsiwar tata gaba daya ba tare da yayita cusa kansa zuwa
gareta ba. Yaji dadin samun information din tana da tsoro wasu lokutan,wannan
ya sake bashi qwarin gwiwar ci gaba da zama a Maldives ko don saboda ita.
"Nidai.....wannan gurin" Ta sake fada muryarta na
sake tsinkewa saboda hango wani babban kifi yana matsowa kusa da glass din.
"Wayyo Allah na" Ta fada da qarfi tana
ruqunqumeshi cikin jikinta da wani irin tsatsauran riqo daya sakashi sakin wata
qatuwar ajiyar zuciya. Wani irin riqo ta masa da ya tabbatar inda a hayyacinta
take ba zata masa shi ba,ya ware idonsa yana duban abinda ya tsoratata. Wasu
irin kifaye ne guda biyu masu girma da suka matso dab dasu kaman masu
sansanasu,sai suka juya abinsu suna wucewa gami da kada jelarsu. Qaramin
murmushi ya subuce masa,inda wannan ne a the Muraka ya fara bata tsoro to
tabbas wata babban dama ce a wajensa,zasu kuma qulla kyakkyawar abota da tsoro
din.
Duk da sun
tafi amma bai tadata a jikinsa ba,don yadda ta maqale shi din shi yayi masa,sai
yaji wani sashe na nauyi da bacin ran da yakeji yana kwaranyewa.
"Is okay.....sun wuce fa,ba abinda zasuyi miki.....
You're safe na gaya miki" Ya fada cikin sauti na rada dab da
kunnuwanta,abinda ya sanya tsigar jikinta tayi wani irin yarfawa kenan.
Fuskarta
ta daga a narke tana dubansa,duban da yayi kusanci da yawa a tsakaninsu har
suna musayar numfashin juna,tadan taka zata ja da baya ya riqo bayanta ta
hanyar tarota da tafin hannunsa yana sakar mata wani irin abu cikin idanun
nasa.
"Stay close to me" Ya fada can qasan maqoshinsa
yana qoqarin danne feeling da yakeji yana taso masa a kanta. Yana gayawa kansa
ba yanzu ba......ba yau ba.
Bata taba
jin kasala irin na yanzu ba,saita sauke dubanta daga kansa saidai fuskarta da
yanayinta gaba daya ya fidda wani quruciya tata sosai,har ya fara contemplating
akan ainihin shekarunta.
"Tsoro nakeji......ka maidani wajen anni" Ta fada
da wata shagwababbiyar murya da batasan ta yita ba.
Wani
qawataccen murmushi ya saki,ya saketa yaja hannunta zuwa wata lafiyyar sofa
dake wani corner na dakin zai zaunar da ita,saidai suna zuwa dab da wajen wasu
gungun kifaye suna iso zasu wuce. A zabure ta taka tana sake fadawa jikinsa ta
riqeshi da kyau,muryarta da zuciyarta suna karyewa.
"Ka gani ko?" Ta fada kaman zata saki kuka. A
wannan karon duk yadda yake danne dariyarsa sai da ta fito da wani irin
nutsatsen sauti. Riqet yayi da kyau yana qarasawa da ita gefan gadon ya zaunar
da ita,ya koma gabanta ya tsugunna a nutse saman qafafunsa. Kanta ta daga
sama,still ruwa ne sosai a saman nasu da wasu halittun ruwan suna rayuwa abinsu
hankalinsu kwance,fuskarta a kwabe a kuma narke ta kalkeshi,saita nuna gurin da
yatsa tana tabe baki kaman qaramin yaro zai saki kuka.
Gaba daya
yanayinta yaji ya tashi kansa.....dukka quruciyarta da tsoronta sun gama
bayyana,abinda bai taba gani ba tattare da ita,hakan ya bashi wani irin
farinciki da sai daya sanya fuskarsa cikin tafin hannunta yana boye dariyarsa.
Baisan haka muraka zai bashi farinciki ba......tabbas da ya jima da kawosu
gurin,wannan tsoron yakeson gani cikin idanunta.
Daidaita
mode dinsa yayi yana kallonta.
"Meet my gaze" Ya furta da natsatsiyar muryarsa
yana cire wasa a yanayinsa. Kaman yadda ya buqata haka ta tattara hankalinta
dama idanunta cikin nasa. Bata taba zaton zata iya dogon kallo cikin qwayar
idanunsa ba sai yau. Batasan me ya riqeta ba har ta iya kallonsa na tsahon
wannan lokacin,saidai tsakanin mintunan taga abubuwa masu yawa cikin idanun
nasa......taga kuma abubuwa masu yawa. Wani irin kyawawan idanu da yau ta fara
karantar hakan,tsahon wasu mintuna suna yiwa juna kallon qurilla wanda
dukkaninsu da yanayin daya haifarwa da kowa,hannunta ya sake riqewa sosai yana
murza a nutse
"You're under my watch....I'll shield you.....i promise
to keep you safe.....take my word for it" Ya fada yana bata tabbaci.
"Yaushe zamu koma gida?" Ta fada cikin sanyi da
wannan tsoron dake gilmawa cikin idanunta. Dan qaramin murmushi ya sake mata
wanda ya sanyata qifta idanunta sau biyu akan fuskarsa.
"Is in your hand......." Idanunta ta fidda waje
tana waresu a kanshi
"Ni kuma?" Ta tambaya cikin rashin wayo. Kafadarsa
ya dage mata
"Yes......" Ya fadi tare da ajiyar zuciya,muryarsa
ta sake zama low sosai,yayi qasa d qwayar idanunsa yana kallonta.
"I crave love and affection in my life,i need someone
to talk to,someone who cares......ina da anni ina dasu musaddiq,amma inajin
still akwai wani ruhi da nake da buqata daban bayansu cikin rayuwata......Can
you fill that role?" Ya jefa mata tambayar yana sake tsareta da kallo.
Karon
farko da takejin wani abu daban a kanshi. Yana dasu anni amma yana kewar wani
abu.....me yasa dukka zancansa babu maamah a ciki?,me yasa duka wannan qaunar
da shaquwa da take gani tsakaninsu da maamah bata ganinsa tsakaninsu dasu?.
"Don't stress yourself" Ya fada yana miqewa gami
da zame hannunta cikin nasa.
"Which apartment you prepare?,up or down?" Ya
tambayeta yana goye hannunsa a qirji yana son ci gaba da ganin drama dinnan
tata.
Idanunta
ta dan ware a narke tana dubansa kaman ruwan hawaye na kwanciya🥹,tana
tunanin wanne gurinne zaifi mata,ta zauna a qasan ruwa da kifi ya hallakata?,ko
ta zauna a saman shima still ruwan dake kadawa yayita kawo mata farmaki?. Qasa
cikin ruwa take tsundum da take ganin kaman glasses din da suka zama katangun
dakin kaman zasu tsage ruwan ya shigo.....shi kuma saman nisan ruwan da suke
ciki kawai ya isheta firgici.
"Is alright......ki zauna a qasan,zan koma saman"
Ya fada yana fara takawa. Ai batasan sanda ta hantsilo ta biyoshi a baya ba,ja yayi ya tsaya yana danne
dariyarsa.
"Eheennn" Ya fada yana dubanta da salon tambaya.
Kasan masa magana tayi,sai qasa da tayi da kanta tana murza yatsunta,haka kawai
yau takejin nauyinsa,ita magana ta Allah daga saman har qasan ba inda zata
yarda ta zauna ita daya,gani take kaman zata rasa rayuwarta ne. To amma ta yaya
zata gaya masa hakan?,fada masa hakan ma ai daidai yake da ce masa su rayu daki
daya,idan kuwa zasu zauna daki daya kenan yana nufin suyi sharing komai?.
"We can room mate?" Ya tambayeta a tausashe yana
lalubar qwayar idanunta. Tambayan ta mata tsauri,a zahirin gaskiya a yanzun ba
wata mafitan da tafi wannan,don dai ita ba zata bari ta zauna ita kadai
ba......amma kuma tana juya yadda hakan zai kasance.
"Let's room together" Ya fada yana wucewa zuwa
matakalun da zasu maidashi sama. Wannan karon sai da yayi da gasken gaske
sannan ya hana dariyarsa fitowa,don duk inda ya aje qafarsa nan take
jefawa,bata yarda ma ya koma saman ya barta a dakin can qasan ruwan ba. Tana
tsaye ya dauki wani luggage me kyau da batasan sanda aka kawoshi ba da wani
kwali na daban.
"Ranar farko zai zama a dakin sama.....rana na biyu
underwater nakeso nayi bacci......hakan yayi?" Ya fada yana daga gira daya
gami d qarewa tsoronta kallo a fakaice. Kai kawai ta gyada don nata da wani
sauran zabi,tsoron da takeji ma ya isheta.
"Okay.....stay here.....zan duba wani abu zan dawo
yanzu" Ya fada yana bata tabbaci da idanunsa. Kai ta daga masa,tana kallo
ya bude qofan ya ratsa living room ya fice.
A sanyaye
ta sauke idanunta ga ruwan da take kallo gashi gata,wai a haka cikin daki kake
kaman ka sanya hannu ka kamoshi. Kujerar da aka aje gaban qofar glass din ta
matsa ta zauna tana sake ganin kusancinta da ruwan.
"Subhana man kalaqal kalqa wa'ahsahum adad" Ta
fada a ranta tana sake jin girman zatin Allah yana kamata. Ba shakka da yawanmu
'yan adam bamusan waye Allah ba,kawai muna fadinsa ne a bakunanmu ba tare da
halasto girmansa a zukatanmu ba. Iya halittar ruwan ya ishi bayinsa sake
sallamawa lamarinsa. Ta sauke numfashi tana maida kallonta cikin dakin,idanunta
ya sauka kan littafin dake ajiye saman dan qaramin table din dake gabanta.
Hannu ta miqa ta dauka,ta fara budewa,cikakken bayani ne akan gurin,taswirar
dakin da suka kama inda toilet da restaurant da komai yake.
Idanunta ya
tsaya cak kan farashin wajen,adadin kudin da zaka biya duk kwana daya
tal,dollar dubu hamsin kimanin million saba'in da wani abu.
Idanu ta
fidda waje mamaki yana kasheta,zuciyarta ta kasa gasgata farashin,ko a
mafarkinta bata taba tunanin akwai me kudin da zai iya wannan ba daga
qasarmu,amma sai take ganin kaman yayi yawa kudaden.....kaman yayi
almubazzaranci,sai wani sashe na zuciyarta ke tuna mata hirar da amna ke yawan
mata na hamma din. Tabbas ya isa ne yakai.....kudinsa kuma ya zarta yadda take
kallonsa,mutumin dake sarrafa diamond da gold ya fitar qasashen
qetare......gold ko diamond din kamfaninsa kaman abinci yake a wajensu saboda
farinjininsa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 99
99
_Daga abdullahi dan
mas'ud R A yace:manzan Allah S A W yace "BAZAI SHIGA ALJANNA BA,DUK WANDA
AKWAI KWATANKWACIN KWAYAR ZARRA(MAFI QANQANTAR ABU) NA GIRMAN KAI A ZUCIYARSA_
_muslim ya rawaito_
Ajiyar
zuciya ta sauke tana rufe littafin,yayin da a can qasan zuciyarta taji ta raina
matsayinta,wacece ita da har zama zai hadasu da mutum me daraja irin muhammad
jadda din?,mutumin da iya yau kawai tasan ya tserewa matakin rayuwa da
ita.......ya mata nisa fau fau......ya kuma tsere mata irin da mugun nisan
tazarar nan..
"Amma me yasa duk da wannan tarin matsayin nasa da zai
iya auren kowanne nau'in mace a duniya.....duk da wannan dukiyar......kyau da
ilimi dake gareshi ya nacewa rayuwarsa sai ni?,me yasa ya kasa rabuwa dani yaje
yayi rayuwarsa?" Tambayoyin da suka zo kanta kenan. Ta kalli wayarta dake
ajiye gefe,ada tana mamakin yawan kudin wayar,sai gashi a nan din kowacce rana
zasu kashe kimanin kudin wayar a kwanan gurin kawai,banda personal cook da taga
suna dashi da komai da komai da za'a zo kullum a maka personally.
"Allah me iko" Ta fada bayan data kunna wayarta ta
tadda WiFi da cikakken network na wayar,ta maida dubanta kan ruwan,kaman ba'a
kan ruwa suke ba?.
Daidai
nan ya tura qofan ya sake shigowa,tadan zabura kadan saboda da gaske a tsorace
take. Murmushi ya saki dan siriri daya qara masa wani kwarjini da kyau.
"I'll safeguard you....indai kina tare da Jadda kisa a
ranki baki da sauran tsoro ko damuwa" Ya fada a tausashe sanda yake
qarasowa dakin da wani kyakkyawan tray a hannunsa ya ajiye saman table din
gabanta. Haka kawai taji kalamansa suna samun matsugunni a zuciyarta,su huda
suka fado mata......indai har hakan ya tabbata hakan na nufin qannenta zasu iya
rayuwa da ita?,qannenta zasu samu kowanne kalan rayuwa da take mafarki?"
Ta tambayi kanta idanunta zube kan price na wajen ba tare da tasan nan din ta
bude ba. To amma meye tabbacin da take dashi a kansa?,kada fa ta rudi
kanta........yanzun nan ta sake fahimtar wanne irin tarin dukiya da girman
matsayi da yake dashi.......tasan cewa kwata kwata babu hadi
tsakaninsu......zaren ba kalar yadin bane......bata da wani assurance.
Baya
kadan yaja a hankali,ya sauke gwiwoyinsa qasa yana tsugunnawa a gabanta,hannu
ya sanya yana janye littafin yana sauke idanunsa a wajen,saita bishi da kallo
haka kawai tanajin kaman yayi almubazzaranci......kaman ya kamata tace wani
abu,kaman ya dace ta masa gyara.
"Wannan.......gurin nan kaman yayi tsada da
yawa......muna da wajen da zamu kwana fa?". A nutse ya daga idanun nasa
yana ajesu a fuskarta,wani abu me kama da murmushi shimfide saman
fuskartasa,har tsakiyar zuciyarsa yana jin dadin kusanta kanshi da ita,koda
kuwa na qananun sakanni ne sai yaji yana samun nutsuwa.
"Duk tsadarshi baikai ki tsada ba.......You're
priceless,no cost is to high......I'd spend my last dime on you,you're worth
every penny" Ya qarasa fadi yana duban idanunta......yanajin inama zata
bashi dama ya shige jikinta.....ya dora kansa saman kafadarta?,ya sauke ajiyar
zuciyar da zata kawo masa sassauci da irin yanayin da yakeji a zuciya da gangar
jikinsa". Karon farko da itama ta zuba masa idanu......tanaso ta tabbatar
da gaskiyar abinda ya fada ko kuma akasinta......tanaso ta tabbatar har
zuciyarsa abinda ya fara ko wani sabon salon yaudarar ne?. Kasa jurar kallonsa
tayi kama kullum,ta dauke kanta ta maida still saman ruwan,tana ganin yadda
duhun dare ya cakudu da hasken fitilun da aka wadata duka resort din dashi,jifa
jifa halittun kifaye nau'i daban daban suna kai kawo. Lissafin kudin take cikin
ranta,inda zai rabawa marayu irinta wanne dadi zasuji,saita kasa shuru still,ta
buda bakinta a hankali ba tare data kalleshi ba.
"Inda zaka kaishi qasata.......akwai tarin marayu da
marasa qarfi da zasu shiga cikin walwala da farinciki sanadin haka.....zasuyita
sanya maka albarka.....mutane masu yawan gaske da suke kwana cikin yunwa da
ciwo......suke kwana cikin halin babu.....'yammata da yawa sun rasa mutuncinsu
sanadin talauci,iyaye da yawa sun rasa 'ya'yansu saboda abinda zasu sanya a
bakinsu" Takai qarshen maganar wani abu yana taba ranta,wani abu yana taso
mata yana tuna mata abinda ya wuce a baya.
Sosai.....sosai da sosai maqurar gaske yaji tayi wani bala'in
burgeshi......irin burgewar da ya jima baiji wani dan adam ya masa ita ba. A
bangaren taimako idan ana maganarsa.....baisan adadin mutanen da suka dogara da
rayuwarsa ba......baisan adadin mutanen da suke qarqashin kulawarsa ko kulawar
wasu nashi ba,ba'a iya Nigeria kadai ba......bai bari tallafinsa ya tsaya a
qasata ba kawai,ya leqa maqwaftan qasashe sosai,saidai kusan komai zaiyi baya
bari a fadi sunansa ko a saka sunansa,wani kaso mafi girma na dukiyarsa ya ware
ya kuma sadaukarwa al'umma........to amma kuma hirar tasu,yana buqatar tayi
tsaho,yana buqatar wannan kusancin a tattare da ita......yana kuma cirar wasu
abubuwa daga sautin muryarta da yanayin yadda take maganar daga qasan
zuciyarta.....kamar akwai wani abu daya shafeta cikin maganganunta.
A nutse ya
miqe yana zama kujerar dake facing nata,yana zube idonsa a kanta tare da
qoqarin lalubo qwayar idanunta.
"Exactly......kin kawo point me girma......me zai hana
ki karbi aikin a hannuna?.....a matsayin personal assistant nawa a wannan
bangaren?" Maganar tasa taja hankalinta sosai har sai data waiwayo ta
dubeshi da raunanan idanunta. Wannan din yana daya daga cikin cikar burin
rayuwarta,ta zama sila na shigar da farinciki zukatan wasu,ta zama sanadin
yayewar damuwar wasu....amma tana ganin kaman zatayi shishshigi ne ta shiga
rayuwar da sam ba tata bace.
Ya
fahimci akwai kokwanto sosai cikin kallon da take binsa dashi,sai ya sakar mata
murmushi yana dunqule hannunsa guri guda,saboda kallon da take masan kaman tana
sakar masa wasu harsasai ne cikin jikinsa.
"Da gaske......ina buqatar irin hakan.....irinki cikin
rayuwata.....amma wannan karon ni zan biyaki.....bake zaki biyani ba" Ya
qarasa fada yana kallon qwayar idanunta. Murmushi dan siriri ya qwace mata,ta
kawar da kanta gefe tana kaucewa ganinsa. Wani irin kyau fuskarta ta sake
masa,murmushinta ya tsaya masa a zuciya,ya kasa dauke idonsa a kanta,iya adadin
murmushin da ya taba gani akan fuskarta qididdigagge ne,ashe haka murmushi yake
mata kyau?.
Yasan me ta
tuna,don haka shima boyayyen murmushi ya saki,ya ciri wata farar takarda da
abun rubutu da suka samu a gurin ya tura gabanta.
"Zan shiga wanka......kafin na fito ki rubuta adadin
salary din da kikeso,daga kan million goma har million dari". Waiwayowa
tayi a nutse,ta dafe takardar tana dubansa.
"Ba komai ne akeyinsa saboda kudi ba......kaman yadda
ba komai bane kudi ke iya siyansa ba......wasu ladaddakin sunfi duniya da
abinda ke cikinta muhimmanci a rayuwar d'an adam" Ta qarasa furucin yana
duban labbanta da suke motsawa da wani irin yanayi dake matuqar daukan
hankalinsa. Kai ya jinjina yana miqewa gami da matsawa a nutse yana zare socks
din qafarsa.
"Na sani....saidai ko Allah daya haliccemu ya sanya
ladan kowanne aiki.....kaman yadda idan nayi aiki haqqina ne ka biyani....haka
idan akamin haqqi ne akan kowa na biyashi" Ya qarasa fada sanda yake zare
rigar jikinsa.
Kanta ta
dauke da sauri daga kansa zuciyarta na harbawa,batason kallon wannan ginannen
jikin shi wai baisan hakan bane?.
Murmushi
kadan ya saki,ya karanci me take daukewa kan sarai,sai ya fara takawa zuwa inda
ta maida kan nata,ya saka hannu yana zuge duka curtain din da suka zama hijabi
ga idanuwa,suka lullube gilasan suka hana mata kallon ruwan dake gabanta din.
Maida idonta tayi ta lumshe,da alama dai taci alwashin ba zata kalleshi din ba.
Kai ya jinjina,shi kadai yasan me yake saqawa a zuciyarsa......da sannu zai
saita komai kan tsarin da yakeso,a nutse yabi kowanne curtain ya zugeshi,sannan
ya dauki bath set dinsa ya soma dosan toilet.
Kadan ta
bude idanunta taga yana tafiya bandakin,tasan kuma indai ya shiga ita daya zai
bari sai ruwan nan dake kada hankalinta. Zumbur ta miqe da gudu gudu ta rufa
masa baya,sai ya tsaya ya waiwayo yana kallonta sanda ya sanya qafarsa a qofar
toilet din.
Yadda ya
zuba mata idanu ya sanyata yin qasa da kanta,tasan yana neman ba'asin biyoshin
da tayin,tana wasa da farcenta tace.
"Tsoro nakeji" A shagwabe har batasan sanda sautin
tattausar muryarta ya koma haka ba. Wani numfashi ya zuqa me zurfi yana
dubanta,yana bala'in son shagwaba fiye da yadda kowa zai fahimta.......saidai
ba wanda yasan da wannan dabi'ar tasa saishi kadai,don ya sanya a ransa ba
shagwabar da zata burgeshi saita matarsa. Yana cikin jinsin mazan da shagwaba
ke tafiya dasu,yasa hannunsa yana shafan qirjinsa dake cike da gargasa muryarsa
a maqoshi yace.
"Ba wani abu fa.....kina cikin aminci,na miki alqawari
daga yanzu har qarshen numfashinmu.....ba iya nan kawai ba.....a dukka fadin
rayuwarki ba wani abu daya isa ya sake cutar dake muddin fu'ad yana raye".
Idanu ta ware tana kallon qasan curtain din,ruwan yadan kada alamun wucewar
kifi. Tanason kallonsa ta tabbatar masa da tsoronta amma kuma batason kallon
muscles dinnan nasa.
"Still tsoron dai?" Ya tambayeta yana dage mata
gira,saita daga masa kanta.
"Okay.....yanzu to ya zamuyi?" Ya tambayeta yana
zube mata idanunsa. Satar kallonsa tayi kadan sannan ta dauke kanta,itama bata
sani ba......batasan ya zasuyi ba,kawai dai abinda ta sani ba zata yarda ta
zauna ita kadai ba. Kaman yasan abinda take saqawa yace mata.
"Zaki shigo ciki ki jirani na gama wankan?" Ya
mata tayi yana da tabbacin ba zatayi accepting ba. Waro idanu tayi tana
kallonsa kai tsaye tana mantawa da batason ganin qirar jikinsa ma.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 100
100
_Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha
da munkari_
_Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa
iyaye,zuwan gidan boka shirka kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya
tuntubi sahihancin sallarsa_
"Ki
zauna to ki jirani......bazan iya kwanciya banyi wanka ba.....if not ki shigo
sai muyi wankan tare" Ya fada yana matsa mata hanya. Ai da sauri sauri
taja baya,ya saki murmushi ya matsa kusa da stool ya dauko mata ya ajiye mata
qofan toilet din
"Oya.....zauna a nan". A sanyaye ta zauna din
kaman me gadinsa,yayin da shi kuma ya wuce ciki. Sai daya shiga ya kunna shower
sannan dariyarsa ta subuce....
Bai taba kawowa a ransa muraaka zai kawo masa wannan
kusancin da yaketa fata tsakanin shi da ita ba sai yanzu......tabbas inda yasan
da hakan da tuni ya jima da daukota wannan duniyar.
Idanu ta
yita rarrabawa,tana sanyawa a ranta muddin taji wani abun da baiyi mata ba zata
afka bandakin ne,komai ta fanjama fanjam,saidai har ya gama din ba taji komai
ba. Daure da towel ya fito a tsukakken qugunsa,ya fito mata sak kaman wani dan
wasan dambe na duniya. Kanta ta dauke ta miqe tana basarwa gami da barin wajen
zata koma saman sofa.
"Kiyi wanka ki sake kaya kizo muje muci abinci"
Ita da yayi zancan abinci ma saita rasa cikin wannan rayuwar ruwan ina za'a
samu wani abincin kirki.
Bata musa
masa ba don itama ya zame mata al'ada yin wankan kafin ta kwanta,saita dinga
dube duben wanne sponge xatayi amfani dashi?,in fact ma tafiya ce ta dole dole
ko kayan da zata sauya bata taho dasu ba.
Miqa mata
bath set dinsa yayi yana kafeta da ido,salin alin ta karba don wannan kallon
nasa bata qaunarsa,wani iri yake sata tana ji gaba daya.
A tsorace
ta kammala wankan,duk minti guda sai taji kaman kifayen zasu shigo su
sameta,data gama ma hakanan ta maida kayan data cire ta fito dasu.
Sanda
take shigowa ya kammala shirinsa tsaf,cikin polo shirt fara qal me ratsin
black,sai black trouser shima daya zauna a jikinsa sosai yana nuna zallar
hasken fatarsa. Duk yadda taso ta qaryata kanta sanda zuciyarta ke fadin yayi
kyau amma ta kasa haka,wani irin kyau kayan sukayi masa kaman saboda shi aka
qerasu.
Kallo
daya ya mata ya dauke kansa,ya dauki wayarsa yana cewa.
"Ga kaya nan ki canza.....ki sameni a sitting
room" Yana fadin haka yayi gaba. Taku biyu tayi da zummar biyoshi ya
dakata yana waiwayowa. Wata siririyar dariya ta qwace masa.
"Dama matsoraciya ce ke har haka?,bazan tafi na barki
ba.....zan baki space ne ki shirya,in kuma kinaso zan zauna na tayaki
shiryawar.....nima zanzo hakan" Fuska ta bata tana dakatawa daga binsa
din. Kai ta girgiza yana sauke murmushi ya juya yana barin dakin.
Jikinta
ta qanqame waje daya kafin daga bisani ta nufi luggage din daya nuna mata,ta
kwantar da ita ta zugeta tana duba kayan ciki.
"Turqashi" Ta fada bayan ta ajiye rigar qarshe
data daga a kayan. Kusan an sake maimaita abinda amna ta mata,kaf kayan bataga
wata riga da zata suturce mata jiki ba,wasu irin kaya ne masu kama da qannen
dasu gwara babu su,sai kawai ta zauna a qasa tana saka kayan a gaba gami da
buga tagumi da hannu daya.
Lokaci yake dubawa,sai yaga ya wuce qa'idar lokacin wanka da
shiryawarta,wanda tuni ya fara riqewa a kansa,aje wayarsa yayi ya miqe yana
komawa dakin.
Kanta ta
dago suka hada ido,sai ya maida dubansa ga akwatin,tayashi tayi itama,ta kalli
akwatin ta kuma kalleshi,idanunta kadai sun gaya masa abinda take nufi,ya saki
qofan ya qaraso ciki.
A
gaban akwatin ya tsugunna ya fara daga kayan shima,tun baiyi nisa ba ya cire
wata gown yana ajeta gefe. Da ido tabi rigar,saboda ta dagata taga yadda
take,kusan gaba daya bayan rigar a kwakwashe yake sai zararruka da ake zargawa
ta bayan rigar a daure. Ta gaban kuma ajiyayyen breast cup ne da koda me
zubabbun qirji ta tabbatar sai sun tashesu tsaye ballantana irin nata.
Da
idanu yayi mata nuni kan ta dauka ta sanya,tsoro ya bayyana qarara a
fuskarta,tadan ware idanu kadan tana jifansa da alamar tambaya. Idanu ya lumshe
mata gami da kada kai,ya tsugunna ya dauki rigar sannan ya soma takawa a nutse
yana rage tazarar dake a tsakaninsu. Dab da zai isa ta fahimceshi,saita yunqura
da zummar janyewa amma ya fita zafin nama don tuni yayi ram da hannunta cikin
nasa.
"Kowanne musu da taurin kai akwai cost dinsa a wajen
nan" Ya rada mata a kunne sanda yake rungumeta cikin jikinsa yana lalubar zip din rigar
tata.
Kai ta
soma kada masa,don indai zai rabata ne da wannan rigar tamkar ya rabata da
komai ne,saboda ba komai din a jikinta,don bata iya maimaicen pant da brazier
ba don haka ta zura rigan kawai ba tare data sanyasu ba,da nufin ta nema wasu
idan ta fito.
"Ka bari......zan saka Allah" Ta fada a tsorace
muryarta tana rawa.
"Is too late" Ya furta can qasan maqoshinsa yana
shaqar daddadan qamshinta duk kuwa da cewa wanka tayi. Bai bata damar fadin
kalma ta biyu ba ta zuge rigar tsaf da jan zip qwaya daya tak.
"Don't move.......saka miki kawai zanyi muje muci
abinci......musu ne banaso.....kinqi ki gane kuma.....leave me mana na gama
miki a nutse mu wuce?,idan da rigima kuka kikeso to na iyata kwando
kwando" Ya sanya labbansa saman kunnenta ya karanta mata. Idanunta a
runtse tsigar jikinta na zubawa,daga yadda yayi maganar tabbas da gaske
yake......wata zuciyar ya shawarceta tayi haquri na sakanni ya saka matan kaman
yadda yace.....dole ya barta idan ya saka mata din ai. Wani abu ta hadiye a
maqogoronta cikin matuqar tsoro tana kulle idanunta,tana jin wani iri na yadda
zai sake samun damar kallon surarta da taba jikinta a karo na biyu bayan
alqawari da tayiwa kanta makamancin hakan bazai sake faruwa ba......tana jin
sanda iska ta hura fatar jikinta,tana jin sanda yadan rabata da jikinsa ya
salube rigar ta sulale qasa. Dukka jikinta ya dauki rawa da bari ganinta cikin
yanayin da ko mahaifiyarta bata taba ganinta ba.......duk da ba haske bane
tarwai a dakin amma ba abinda zai hanaka ganin mutum sosai da sosai,tsoronta ya
ninku,ta dinga jin kaman qasa ta tsage ta hadiyeta a ciki.
Da qyar
ya kamo numfashinsa dakeson kubce masa saboda sauka da idanunsa sukayi a wajen.
Ya miqa hannunsa yana me burin isa gurin,sai kuma ya tsaya cak yana janyesu a
hankali,wata qatuwar ajiyar zuciya ta kubce masa kaman yaron da aka yiwa dukan
tsiya yaci kuka ya qoshi,da wani irin zafin nama ya juyata fuskarta ta daina
facing dinsa,saidai can dinma ba sauqi,hips dinta ke tsokane masa idanu,sai
kawai ya rabata da jikinsa waiko hakan zai sanya ya rage ganin abubuwan da yake
gani din.
Baisan
shima nasa hannuwan rawa sukeyi ba sai bayan ya zura mata rigar ya dagata daga
jikinsa yana zazzarga mata igiyoyin dake riqe da bayan rigar. Sosai hannuwansa
suka kama rawa,daure igiyoyin suka gagareshi. Ya runtse idanunsa da matuqar
qarfi yana fatan daidaituwar mode dinsa,saidai ko daya bude ba abinda ya canza
saima numfashinsa daya fara fuzga kaman me ciwon asthma.
Hannuwansa ya dora saman kafadunta gaba daya ya juyo da ita da wani irin
hanzari,yadda red din gown din ta sake haskata sai yaso.tafiya da ragowar
numfashinsa da yake kokawa dashi. Gaba daya labbansa rawa suke kaman me rawar
sanyi ya soma lalubo kalmominsa......
"DUNIYA TA.... please,kiyimin alfarma na sake kasancewa
dake karo na biyu......please na roqeki karkice zaki hanani" Firgicin data
shiga ya kusa fin nasa,take itama jikinta ya kama rawa,ta zare idanunta duka a
kansa tana jin kaman zasu zazzago tsabar tsoro. Ta motsa labbanta zatayi masa
magana a tsorace amma ya rigata
"Am so sorry.....naso na barki har sai sanda kika fara
sona.....naso na barki har sai sanda kika gamsu da kanki kikayi accepting
muhammad fu'ad......but.....kece DUNIYATA bani da wani gurin zuwa sai wajenki
din dai" Sake rudata kalamansa sukeyi,batasan yadda zata masa bayani
bama,neman gurin tsira kawai takeyi,saita saka hannunta tana neman zame
hannuwansa daga kafadarta. Sarai ta fahimci a rude yake kaman yadda take a
rude,idanma tace zata tsaya masa bayani bazai fahimta ba. Damqe kafadun nata
yayi idanunsa suna sake juyewa hadi da canza launi.
"Please mana.....na miki alqawari wannan
karon......I'll be gentle with you.....i will never harm you again" Ya
fada yana jin kaman ana qara izashi zuwa gareta.....kaman yana qara loosing
tunaninsa gaba daya. Sake buda baki tayi still bata sare ba,duk da tsoron dake
sake dabaibayeta da nufin masa bayani ko kadanne,amma sai.ya kama hannuwanta
duka ya sanya tsakiyar tafin hannunsa kaman me begging dinta
"Please....please.......na yadda da kowacce kalan
tuhuma zakiyimin......na yadda da kowanne zarginki a kaina......kome kikace
nayi ina neman gafara akai......kinqi bani dama tun a baya nayi bayanin
kaina......I'm pleading with you.......grant me this favor" Ya qarasa
maganar yana zubewa a gabanta......
Ji yake
ya shirya rasa komai.....ya shirya kuma sadaukar mata da komai,yayi qasa da
kansa yana jiran cewarta jikinsa naci gaba da rawa.
Wani abu
ya tsarga mata jin digar wani abu me dumi saman tafin qafafunta,wata irin
faduwar gaba ta ziyarceta saboda abinda zuciyarta ta raya mata.
"Muhammad fu'ad jadda ne kuka a gabanta?,muhammad fu'ad
fa?,wanda gidan jaridu da mujallu kowacce fitowar rana zuwa faduwarta suke
rububin buga labari akan kamfaninsa......suke rububin fidda labari akan kalan
jarumtarsa tun kan ya balaga har zuwa girmansa......jaddan da qasashen duniya
keyi dashi?,jaddan da maganarsa manyan kamfanonin qasashen qetare dake sarrafa
diamond sukeji?,yau shine under her feet?.
Daidai
inda zaren tunaninta ya tsaya kenan,sai dauko mata sunkutarta da fu'ad din yayi
zuwa lafiyayyar shimfidar da muraaka suit suka zubeta musamman saboda masoya
masu yawon watan zuma wato honeymoon irinsu fu'ad din.
"Am sorry DUNIYATA.....am sorry my world" Shine
abinda ke fita daga bakinsa cikin wani irin
gigitaccen yanayi. Tsoro ne fal qirjinta da zuciyarta,tuni ta fara sakin
nata kukan tana hango kanta gaban Dr fadwa ana sake dinketa. Tana sake
rewinding azabar da tasha wancan ranar.....ta kasa mantawa da yanayin daren da
kuma lokaci. Hatta da wucewar kowacce daqiqa a lissafe take a wajenta....abune
da ya kasa barin kanta da mafarkanta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 101
101
_An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane
ukun da baxasu shiga aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_
_"WANDA YAKE ZINA TUN YANA YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_
_2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_
_Bukhari da muslim_
"Kar ka
cutar dani" Ta fada a galabaice tana jin yanayinta yana canzawa.
"Bazan iya cutar dake ba.......sonki ne yayimin
yawa.....ki taimakamin na koyi controlling nasa" Ya fada ba tare daya
saurara mata ba.
"In ka cutar dani ko ka zalunceni......"
"Ki daga hannu ki roqi Allah ya hukunta miki ni.....ki
roqi Allah yayi miki sakayya......ya jarabceni da wani son da yafi wannan yawa
da fadi" Ya fadi yana tallafo kanta gami da sanya jirkitattun qwayar
idanunsa cikin nata dake cike fal da hawaye......dukka hannayensa suna rawa
kaman wanda aka tsamo daga ruwan sanyi. Idanunsa kawai firgitata suke,ta saka
hannu zata riqeshi saidai ko kadan bayason sakejin wata magiya tata,don haka ya
rufe bakinta ruf da nasa.
A hankali
ya shiga aike mata wasu irin zafafan saqonni.......wasu irin abubuwa da tun
tana turewa har suka fara kama mata kwanya.....suka jefa ta a duniyar
tunani.....suka dauki duk wani tsoro nata da fargabarta sukayi cilli dasu can
bayan gadon.....suka gusar da duk wani hankalinta tunaninta taurin kanta tsiwa
dama tsoronta. A hankali saiga me jadda yana komawa fagen,fagen da bai taba
zaton zai sake ziyarta ba karo na biyu cikin rayuwarsa.......yayi musu ragama
da jagora zuwa wata sabuwar duniyar da shi da ita basusan akwaita daban
bace.....tasha banban da duniyarsu ta wancan karon nasu.
★Tun yana dakon
jiran fu'ad har ya soma lalubarsa cikin gidan,don dakinsu ya shiga zaman
jiransa. Ko ina ya duba bai ganshi ba,bai wani zurafafa tunani ba ya dauki wata
motar ya fita ya zauna da baqin nasu,suka kammala meeting din ya sallamesu,ya
kuma hada duka documents din a take ya aika masa ta email. Kaman yadda suka
tsara daga wajen sai ya wuce dauko anni data tafi wani herbal center a
traditional market dinsu. Suna mota take tambayarsa fu'ad din
"Mun fito tare so uzuri ya maidamu,sai nace bari nazo
na daukeki" Daga haka suka rufr chapter din suka dauko wata har suka isa
gida.
Komai anni
ta gama har tayi shirin kanwaciya amma bataga sabreen ba. Tana saman abun
sallah tana shafa addu'ar shafai da wutirinta tace da amna.
"Ina ameenatu ta shiga ne?" Kai ta girgiza,itama
tun dazu take nazari
"Ban sani ba wallahi anni,maamah dai tayi kiranta,tunda
ta fita kuma bata dawo ba". Shuru anni tayi haka kawai taji gabanta yana
faduwa.
" Maamah ce ta kirata?,tunda ta fita kuma bata dawo
ba?" Ta sake maimaita statement din tana duban idanun amna. Kai ta gyada
mata.
"Turqashi" Anni ta fada tana miqewa hankalinta
yana tashi,zuciya ta fara fasalta mata abubuwa kala daban daban da zasu iya
faruwa.
"Indai wani abune ya faru kaman yadda zuciyata ke
gayamin......indai wani abu mariya ta aikata na cutarwa ga
ameenatu.......tabbas saita gane bata da wayo......a wannan karon saina nuna
mata ainihin kalata" Anni tayi maganar a zuciyarta tana zare hijabin
jikinta,ta dauki dankwali ta daura tana duban amna
"Ki zauna ina zuwa" Abinda kawai tace da ita kenan
ta murda qofar tana ficewa.
_tofa.....😂😂😂,me anni zatayi?,masu
karatu ku tarota,ku gaya mata ba ruwan maamah a nan......dan annin ne yayi
kidnapping takwararta da kansa_🏃🏽♀️🏃🏽♀️🏃🏽♀️🏃🏽♀️😆😂😂
Daidai
lokacin da maamah ke dakinta,abun duniya yana sake ta'azzarar mata da wani irin
zafi qunci da tashin hankali. Kaf tunaninta ya karkata akan yadda zata raba
sabreen da wannan copy din video din da yake hannunta.....rabata dashi din
shine tamkar mabudin iya wurgar da ita daga rayuwarsu cikin qasqanci da
tozarcin data tanadar mata.
Ta duba
agogo ta duba agogo har sau babu adadi......ta duba agogo duk bayan kowanne
wucewar daqiqa.....cikin saka ran fuad zai dawo ya lallasheta......fu'ad zai
dawo yaji meye damuwarta kaman kowanne d'a yakewa iyayensa,saidai tun tana
dubawa tana kuma lissafawa har ta bacewa lissafin.
Kowacce
alama da shaida ta nuna mata bazai dawo ba.....ya fita abinsa ne,bashi kuma da
niyyar bata wannan lallashi da kulawar da take yunwarsa. Ranta yakai qarshen
baci,da gaske dai bai dauketa uwa ba mahaifiya.....kunnuwanta na tuna mata wata
hira da taji musaddiq da saddiq nayi,suna gulmar fu'ad din. Ya fita aiki ranar
sai gashi ya dawo da Rana,suka dinga dariya suna gulmarsa,wai da zai fita ne
yaga ran anni kaman a bace....da yaje office ya kasa sukuni,dawowar da yayi
yazo zagayata ne ya tabbatar ta warware,ba kuma wani a cikinsu bane ya bata
mata rai ba.
Tuna wannan
kawai ya sake hura wutar zuciyarta,sai kuma ta tsinci knocking da fushi yasa ta
kasa tambayar waye,ta miqe kawai ta bude qofar a fusace.
Anni ta
gani a tsaye tana duban ta,wani irin kallon kallo dake dauke da ma'anoni da
yawa a zukatan kowannensu.
"Zuwa nayi duba sabreen.....ta shiga dakinki kuma har
yanzu bata dawo ba?,ina kika kaita?". Me neman kuka ne wanda aka jefa da
kashin awaki,wanda yake jiran kadan ya fashe,saita fito daga dakin gaba daya
tana duban anni tana huci.
"Dama dab nake da zuwa wajenki na tambayeki wanne irin
baqin sihiri kika yiwa 'ya'yana?,wacce irin shirka kika ta'ammali da ita
ameena?,da yake bani da haqqinki sai gashi kin kawo kanki da kanki kina tambaya
akan abinda ni yafi cancanta na tambayeshi". Mamakin maamah din ya
kasheta,ta zuba mata idanu sosai tana ganin yadda take haqilo kaman zata fidda
maqogoronta.
"Mariya......tambaya daya ce nayi ina kika kai
sabreen?,don bata dawo dakinta ba". Wani banzan kallo ta watsawa anni tana
dubanta.
" Au.....bacewar karuwa dama abun mamaki ne?,har akwai
mamaki don an wayi gari an tarar karuwa ta gudu daga dakinta?"
"Subhanallah" Anni ta fada tana ware idanunta akan
maamah mamaki yana ratsata. Surukarta?,matar d'anta take kira karuwa saboda
wani son zuciya nata?.
"Ameena.....ina me baki shawarar warware duk wani qulli
da kikasan kin yiwa yarana tun daga zamanin quruciya zuwa yanzu.....idan kuma
kinqi wallahi wallahi ni mariya bazan qyale ba......na dauki cikin yaran wata
tara na haifesu.....naci kashinsu da fitsarinsu amma rana daya azomin da bariki
da salon mallaka?,ubanme kike basu wanda ni bazan iya basu ba?,uban me kike
musu?". Sosai zagin ya sosa zuciyar anni,sai ta koma ta zauna tana qare
mata kallo hannayenta harde a qirjinta.
Duk wasu
sarari da filaye na yiwa maamah kara zuwa yanzu sun fara cika,bata kuma da
saura wanda zata bude mata taci gaba da
zuba jujinta. Kai tsaye kuma hankalinta kwance ta kirata
"Mariya......abinda na basu baki dashi.......kin kuma
rasashi har abada......yadda kika kasa rungumarsu kiji qansu a sanda suke da
rauni......to kema kin rasa wannan cikakken tausasawar sai wadda zasuyi miki
donsu fita haqqinki da haqqin addininsu......shima wannan din xasuyi miki shine
saboda sun mori iyayen goyo da sukasan hagunsu da damansu.....daidansu daba
daidai ba......banda haka ke dasu dama dukkan abinda suka mallaka sai gani sai
hange daga nesa. Inda ce hankalinki a daidai yake......inda ace hankalinki
cikin jikinki yake.....ba cikin dimuwa kike ta neman duniya idanu rufe ita da
abinda yake cikin ta ba......da baki buqatar bayani kan me yasa kika rasa kike
kuma rasa kowacce dama,take kuma kufce miki.......bari na gaya miki wani
abu.....ni ameenatu na tsere miki.....ni ameenatu ba zaki taba kamoni a zukatan
naki 'ya'yan ba bare nawa 'ya'yan.....sauran dukkanin abinda zaki zata ko ki
tuhuma wannan ke kika sani.....kuma keda zuciyarki......zuciyar bawa
birninsa,abu daya zance miki shine......kada ki yarda kada kuma ki kuskura wani
abu ya samu sabreen,idan kikayi wannan gangancin to tabbas zan saka a binneki a
cikin qasar Maldives me tarin farin rairayi" Ta qarashe maganar tana nuna
maamah da yatsa,sannan ta miqe tsaye sosai.
"Daga yau gobe zuwa jibi naga dawowar diyata cikin
gidan nan.....ko da fu'ad ne yace zaiyi ganganci da rayuwarta shi dake aurenta
saina hukuntashi.....ballantana ke da nake kyautata zaton kwangilarta kika
dauko". Anni na kaiwa nan ta juya tana barin wajen,tanata qoqarin
controlling fushinta kada maamah din ta ganshi.
"Aikin banza kenan qafafa da mallakin wani.....ke me ya
hanaki haifar kamarsa?,kinga sai kiji dadin yin mulkin mallakar da kyau ba tare
da kowa yaga wallenki ko ya qalubalanceki ba" Tayi maganar da nufin fusata
zuciyar anni.
Da wani
lafiyayyen murmushi ta waiwayo tana kallonta.
"Banda abinki tunda kin haifomin ai kin hutasshe
dani......don yadda nake hutawa ko asalin wadda ta kotseshi bata rabauta da
wannan ba....idan kinajin tsuntsu daga sama gasashe to fu'ad ne a hannun
ameenatu" Ta qarashe maganar tana bude mata tafukan hannayenta sannan ta
juya taci gaba da tafiya abinta.
Kamar
hauka zai kamata haka taji maganganun anni saman kanta. Kasa shuru tayi ta soma
zuba ruwan masifa da zagi.
"Ameenatu.....nafi qarfinki....nafi qarfinki
wallahi,bakisan wacece mariya ba....kibar ganin zamani ya cimmata......to ki
giwa ta fadi tafi qarfin wawa,tafi qarfin kiyashi ya jata.....zan nuna miki
asalin wasan indai na haifu cikin uwata da ubana".
Bataji
komai cikin abinda take fada ba,don already ta wuce daki ta kuma maida qofar ta
kulle.
"Bari yazo shima zai sameni.....bazan sake kwana gida
daya da wannan annamimiyar makirar ba.....dole yazo ya zaba,koni ko ita"
Ta fada kaman zararriya tana jawo luggage dinta tana watsa kayanta ciki,sai
kuma ta tsaya cak.
"Ina yarinyar ta shiga?" Ta tambayi kanta gargadin
anni da fuskar daba wasa tana dawo mata,saita saki kayan hannunta ta koma gefen
gadon ta zauna.
Wani gumi
ne ya tsargo mata tana jin hankalinta ya fara kadawa. Anni tana da power din da
bata da ita.....tabbas ne wannan,don idan akace ana buqatar ganin fuskar maman
muhammad jadda ta anni ce za'a fara nunowa.....daukakar fu'ad ta sanyashi alaqa
da manyan mutane da hankali baya zato,da yawansu kuma suna alaqa da anni a
matsayin itace mahaifiyarsa......KENAN UMARNI DAYA ZATAYI A KANTA AYI MATA
YADDA TAKESO?.
Tambayar
data sanya 'ya'yan hanjinta curewa waje daya kenan,saita jawo wayarta da sauri
tana nemam number fu'ad.
Kiran
duniya wayarsa a kashe,ta kira tun tana irgawa harta bacewa lissafi,sai ta aje
wayar kawai gefe tana tunanin meye abunyi?.
_😂😂😂,maganin dan banza karen
maguzawa ko inji hausawa.....shin a wannan lokacin hajiya maamah xata shiga
hannu ko kuwa?_
_meye hasashenku?_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 102
102
Tsaye take gaban
qawataccen madubin bandakin me tsananin haske da hasken rana daya soma mamaye
sararin samaniya ta bullo ta wasu sassan glasses na bandakin ya kutso ciki.
Daure
take da bathrobe me tsananin taushi,fara qal data zauna a jikinta bisa taimakon
igiyoyin dake maqale a jikinta,saman kanta daure da towel data nade gashinta me
tsaho da santsi,wanda ruwan da ya jiqashi ya sanyashi kwanciya ta gaban
goshinta dama wasu sassa na wuyanta. Brush ne riqe a hannunta.....amma sai ta
kasa matsa toothpaste a jiki,saita buge da kallon fuskarta ta jikin madubi data
fito tarwai kaman ka saka hannu ka ciro.
Daren
jiya ke faman mata yawo cikin kwanya......tanata tuna shudewar kowacce daqiqa a
tsakaninta dashi. Iya yawan abun kunyar data tafka bazai barta hada idanu dashi
ba,ba zata iya ba sam koda daidai da minti daya.
Duk yadda
take tunanin abun zaizo kaman na farko sai komai yazo mata da ba zata,saida
komai ya kammala sannan ta tsinciki kanta tsakanin hannuwansa,bata da wani zabi
illa fashe masa da kukan kunya. Ya sani sarai......yasan abinda takema
kukan,amma sai yayi kaman bai fahimta,ya lalace sosai wajen
rarrashinta......daga qarshe ya juye mata tashi kalar shagwabar data sake
tsumata,ta sanyata tayi luf ba shiri tana jin kunya da nauyinsa suna kamata.
Zare
brush din daga hannunta da taji anyi ya sanyata firgita
"Good morning sleepy head" Ya fada yana tsaye daga
gefanta ya kashe mata idanu yana qoqarin saka mata toothpaste din.
"Morning" Ta fada tana sadda kanta qasa tana jin
wani irin nauyinsa da bata taba ji ba. Tunda taji ya tashi ita taqi koda
motsawa,har yayi wanka ya fito yayi sallah yadan fita a dakin,fitar nasa tayi
amfani dashi tayi wuf ta shiga wankan da xummar ta shirya kafin ya fito tayi
sallah ta sake boyewa cikin duvet.
"Feel free......brush kawai zanyi na fita" Ya fada
yana matsowa bayanta. Dab da ita ya tsaya,har jikinsa yana gugar nata,fuskarsa
ta fito bayan tata ta cikin madubin,ya zube idanunsa fes da suka qara wani irin
haske saman tata fuskar ta cikin madubin. Wani irin murmushi ne kwance a
fuskarsa.....wata irin shimfidaddiyar walwala da makamanciyarta bata taba
wanzuwa saman fuskar tasa ba da annuri suke fita daga fuskar tasa. Qwayar
idanunta yaketa laluba yana son ya kalla amma ta hana mishi kallo,ta zura brush
din kawai a bakinta tana wankewa tana kuma jin yadda yake sake shigewa jikinta
da sunan brush zaiyi.
Ta gefe
da gefen cikinta ya zura hannuwansa ya zari brush dun,ya saka toothpaste duk a
hakan yana sake shige mata,ya tura brush din bakinsa ya soma wankewa shima a
hankali yana sake maida idonsa ga fuskarta data futo sosai ta madubin. Wani
kallo yake mata ko qiftawa baya yi,yana fatan tayi kuskure ko sau daya ta daga
kai ta kalleshi,yana son karantarta ta cikin idanunta sosai,ya sake matsawa
sosai jikinta yana sansana kanta dake fidda wani irin sassanyan qamshi.
Ta gama
nata brush din amma tanata juyashi a hannunta,ta rasa yadda zata gaya
masa.....ta kasa daga kai ta kalleshi ma bare ta samu qwarin gwiwar gaya masa.
Ya karanci hakan,murmushi ya qwace masa.
"Wannan kunyar daga ina?" Ya tambayi kansa da
kansa daga can qasan zuciyarsa.
Yana sane
yaci gaba da cinye musu lokaci,yanason tayi magana amma kuma ta gaza,har zuwa
sanda taji ta soma tuqewa,saita ajiye brush din,ta kuma juyo da hanzari tana
fadin.
"Ni na gama" Qurjinsa ta fada kai tsaye,don babu
wani space da zai bata daman wucewa. Kan qirjinsa idanunta suka
fada,ni'imtaccen gargasar qirjin tayi maraba,ta daga idonta a hankali tana
kallon tazarar nisan tsahon dake tsakaninsu. Ya fita tsaho sosai,duk da cewa
ita din ba gajeriya bace,idanunta suka sauka kan Adam's apple dinsa daya fito
sosai ta maqogoronsa kaman zai fado.
Wani abu
guda daya tal da yake burgeta ga halittan namiji kenan......batasan meyasa yake
burgeta ba,amma dai tasan yana bata mamaki,ta jima kuma tanason taji abun ya
yake,tauri ne dashi?,yana musu zafi ko kuwa?,ba tare da tunanin komai ba ta
miqa yatsanta a hankali zuwa wajen ta tabashi.
Cikin
kowanne jini dake harbawa a jikinsa yaji saukar yatsan nata,ya hadiye wani abu
daya sanya Adam's apple din motsi yayi qasa ya sake dawowa saman. Kasa jurewa
abinda yakeji din yayi,sai ya fincikota sosai zuwa jikinsa ya matseta a
qirjinsa da kyau yana dora fuskarsa saman wuyanta.
"Wannan tsokana ne ai......yanzun kuma inda zan ritsaki
kona nema fansa saiki isheni da kukan banza......har a kiramin anni ma da momma
ko?". Kunya ce ta kamata me tsanani,akan jiya yake tsokanarta ta
sani......sannan ita kanta batasan ma'anar abinda tayin ba yanzun,taji tana
sha'awar tabawa ne kawai.
"Nifa wannan gaisuwar baiyimin ba......ina buqatar
zuzzurfan alaqa tsakanin da iyalina......inason ki zama
qawata.....aminiyata......mamana.....yayata.....qanwata....oh" Sai kuma ya
tsaya yana dagota daga jikinsa gami da dan dukan goshinsa.
"Ashe fa ance sai anyi shawarar za'a soni ko aah
ko?" Ya fada yana ware mata idanunsa. Kauda kanta tayi gefe daya zuciyarta
na bugawa,wani murmushi yana son kubce mata amma tana hana hakan,bata ankara ba
taji ya dagata cak ya azata gefan sink din bandakin,hakan ya bawa santala
santalan cinyoyinta daman bayyana don bathrobe din ta dage kadan.
"Kinsan me?" Ya fada yana tsayawa tsakanin
cinyoyinta,hucin numfashinsa dana daddadan turarensa yana sauka a fuskarta.
"Karki wahalar da kanki DUNIYATA kice saikin koyawa
kanki sona......" Daga kai tayi ta kalleshi abinda yakeson gani kenan dama
tun dazu,saidai ita din tayi hakanne saboda mamakin maganarsa. Girarsa ya dage
mata dukka biyun yana jin dadin ganin qwayar idanunta. Oily eyes daya jima yana
kokwanto shin akwaisu?,sai gasu a jikin abinda yake mallakinsa gaba daya.
"Yes.....iya soyayyar da nake miki ma ta ishemu mu rayu
ni dake.....bake kadai bama.....har babies din da zamu haifa nan gaba" Ya
fada yana dora hannunsa saman plate tummy dinta,abinda ya sanyata jan wani irin
numfashi saboda tafin hannunsa guda daya daya dora saman budaddun cinyoyinta.
"DUNIYATA....Kinsan yara nawa nakeso ki haifamin?"
Kasa amsa masa tayi,tafi buqatar ya matsa baya kadan kada ya dagula mata
lissafi,abinda ta fahimta kaman yana son sake mata wayo ne kawai yake saka
kusanta kanshi da ita.
"Karka zaqe da yawa.....har yanzu ban gama yanke
hukunci ba" Ta fada cikin tsanani dakiya. Dariya yakeso yayi sosai amma ya
dake,ya fahimci qarfin hali irin nata da zallar qi fadi dake dawainiya da ita.
"Don't worry.....kedai ki tayani ji ma kawai ya wadatar
dani" Yana kaiwa nan ya sunkuceta gaba daya tamkar ya dauki 'yar jaririya
yana takowa zuwa bedroom din.
"Ka saukeni" Ta fada a narke,saboda ta lura gaba
daya ya raina dagata,ya maidata kamar wata 'yar bebin roba.
"Ta yaya zakiyi nauyi kina wasa da abinci?,indai
kinason mu shirya saikin koyi cin abinci irin na muhammad fu'ad" Yakai
qarshen maganar yana direta saman sofa bed,sannan ya fara takawa a hankali zuwa
saman dressing table yana kwaso kayan shafanshi data tabbatar yafi qarfin
talaka irinta.
Gabanta ya
zubesu gaba daya sannan shima yabisu ya zauna a gabanta yana tankwashe qafa
tamkar bawa da uban gidansa. Ya soma bude cream cream din da wasu irin abubuwa
da batace ga sunansu ba ya fara tatsawa a hannunsa sannan ya kamo hannunta yana
juye mata su a ciki.
"Zaki iya haifamin yara dozen biyu?" Yayi maganar
murya a sanyaye da wani zuzzurfan sauti yana riqe da hannunta da yake maida
cream din daga hannunsa zuwa nata.
Idanu tadan
wara tana dubansa da kyau.
"Please am serious.....ko through IVF ne.....a dinga
saka miki biyar biyar.....nayi alqawari ba zaki sha wahala ba.....zan biya ko
nawa ne a ciresu cikin aminci.....zan kashe miki ko nawa ne DUNIYATA.....nayi
alqawari" Mamaki sake kasheta yayi ganin yadda yake maganan da dukka
gaskiyarsa,hakan ya bayyana itama a idanunta,sai ya saki wani murmushi yanayin
fuskarsa yana canzawa.
"Kina mamaki ko?" Ya tambayeta yana sakar mata
hannu don ta samu daman shafa man daya tatso mata.
"Naso mu da yawa abbanmu ya haifa.....nayi wannan burin
saboda gidan masu yara da yawa yana burgeni,saidai kuma mu biyu aka
haifa.....inaso na tarawa abbana zuria me yawan gaske.....zuri'ar da zasu
dawwama suna masa addu'a da sadaqa jariya.....bani da sha'awa ko burin auren
mata biyu.....dake kadai nakeso na rayu DUNIYATA shi yasa nakeso ke din daya ki
zama uwar dukka yarana" Ya qarasa fada yana dubanta.
"Baga fareeda ba?" Tayi zancan da wani yanayi da
ya sanya murmushi kubce masa,yadan dafa goshinsa yana cewa.
"Maganan fareedan bai wuce ba?..... apologize din da
nayi jiya baiyi ba?.....okay am ready to repeat it" Ya fada yana jinjina
yadda abun yafi tsaya mata a rai fiye da komai. Kafadunta duka biyun ta daga
tana kauda kai
"Ina ruwana nikam.....am temporary......"
"Temporary?" Ya katseta cikin maimaitawa yana
dubanta da kyau ba tare da ya barta ta qarasa fada ba,sai ya ajiye boyayyen
numfashi
"You're my world.....kece DUNIYATA sabrrrrr....na
rantse da Allah.....banda ubangijin daya haliccemu ba wanda ya isa ya qwaceki a
hannuna.....ke kanki baki isa ki raba kanki dani ba.......ko mutuwa ina kai
qararta wajen Allah.....muddin tana da nufin rabani dake ubangiji ya hukuntamin
ita". Sosai maganarsa ta ratsata,taci gaba da shafa wa hannayenta man
cikin wani irin kasala ba tare data dago idanunta ta kalleshi ba.
"Ya kamata muje kiyi break" Ya fada yana katse
shirun hadi da miqewa. Batasan me ya matsa yayi ba sai daya miqo mata rigar
saman cinyarta.
Rigar jiya
ce dai da bata saka ba,saita daga ido tana masa kallon Why?. Kafada ya daga
yana watsa hannuwansa.
"Zan iya saka miki if ba zaki iya sawa ba" Kai ta
girgiza masa da sauri,don ta tuna jiyan,daga saka rigar labari yasha banban.
"To ka fita sai na shirya" Ta fada a shagwabe
still
"Inje ina?,bayan ko na fita dinma saina dawo na taimaka
miki na daure miki rigar kin manta?" Ya fada hannuwansa na goye a qirjinsa
yana qare mata kallo,don hatta cikin bathrobe din ba qaramin kyau tayi masa ba.
"Na rufe idona.....inkin gama sakawa ki gayamin"
Ya fada yana juya mata baya gami da maida kallonsa qofa yana ganin gilmawar
ruwa ta tsakanin labulayen da basu gama rufuwa ba.
A gurguje ta
saka rigar,tanayi tana waiwaye wai kada ya juyo ya ganta bata sani ba. Dariya
yakeyi abinsa can qasan ransa,don yana ganinta tarwai ta wani glass dake
gabansa ba tare da ta sani ba.
"Zan iya juyowa?" Ya tambaya yana danne dariyarsa.
"Eh" Ta fada tana turo baki gaba,abinda yayi
matuqar burgeshi har yaji kaman ya kama lips din ya shanye.
A nutse ya
dinga bin igiyoyin yana daure mata,kowacce daya saiya tambaya
"Tayi haka?" Kai take daga masa mafi yawa,ta koma
kaman kurman qarfi da yaki,ta tabbatar kaf halittun bayanta ya gama qare musu
kallo,tana jin yadda yake sakin ajiyar zuciya time to time. Yadda maroon din
rigar ta zauna daga bayanta kadai ya qawatar dashi gami da tafiya da
hankalinsa. Ya dora yatsunsa a hankali saman fatar wuyanta,inda wajen ya danyi
jajaja. Hannunta ta dora saman nasa tana dan danne wajen,guri kusan uku duka
haka sukayi,yasan kuma shine sila,zare hannun nasa yayi yana juyo da ita tana
fuskantarsa.
Idanunsa
ya lumshe yana kuma budesu duka samanta.
"You look so gorgeous" Ya motsa labbansa yana
furtawa da wani irin sassanyan yanayi yana duban qirjinta da yayi redness shima
guri uku. Yatsantsa yakai wajen yadan taba sannan yace
"Does it hurt?" Fuska ta kwabe masa cike da
shagwaba kaman zata sake masa kuka,sai ya yarfar da hannunsa yana fadin.
"Ayyah.....sorry,bari na fanshi wannan ciwon" Ya
fada yana ja da baya fuskarsa da murmushi. Luggage dinsa ya kwantar ya bude,ya
ciro wani dan mitsitsin box ya tako gabanta.
"Qaramim gift ne....for you duniyata" Ya fada yana
ciro wani siririn agogo dake zuba qyalli. Koda bakasan meye ba kasan abune me
matuqar daraja,kallo daya zakayi masa kasan abune me tsadar gaske,bashi da
girma ko fadi amma yana daukan ido sosai. Matsowa yayi kusa da ita sosai,ya
miqa mata hannunsa yana kallonta da ido. Ta fahimci me yake nufi amma saita
noqe,bai wani tsaya jiranta ba yasa hannunsa ya kamo hannun nata sannan ya fara
saka mata agogon.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 103
103
"Ya
subhanallah" Ya fada yana juya hannun cikin tafin hannunsa. Ya mata wani
irin kyau kaman saboda ita aka qirqireshi,ya zuba idon hannu yana jujjuyashi
kafin a hankali yace.
"Our latest wrist watch...2025,kin masa kyau
duniyata.....nayi accepting wannan design din saboda ke,koda baiyi daidai da
ra'ayin dealers dinmu ba,i love it for the sake of you" Ya qarasa maganar
a tausashe yana kai hannunsa yayi kissing hannun nata,still idanunsa a
kanshi,ya zura hannunsa a aljihunsa ya fiddo wayarsa ya laluba wata number ya
kira. Bugu daya aka dauka,da hausa taji yana magana.
"Mun siya design dinnan......sannan madam ta ninka
price din da wasu dollars din akai ainihin price din". Ya fada a nutse da
alama yana magana da wasu ne
" Alright " Taji ya sake fadi yana katse
kiran,yana maida wayar aljihunsa tana dubansa idanunta a warwaje,sai daya daga
kai sannan suka hada ido,fuska ta narke
"Wacce madam din?" Ta tambaya da siririyar
muryarta dinnan,miskilin murmushi ya sake mata
"Akwai wata bayan ke?" Saita sake fidda idanun
"Ban da kudin siya fa....thought dai bansan nawa
bane"
"Amma kina da muhammad jadda ko?" Ya furta yana ja
baya kadan idanunsa a kanta. Yana jin dadin kallonta sosai,sai yakejin duk wata
tsohuwar kewa ta rayuwarshi tana sulalewa,yana jinsa wani sabon mutum na daban.
Duban hannun
nata tayi,haka kawai taji kaman ya saka mata wani abu me daraja da yawa,sai
takejin hannun ya mata nauyi.
"Na gode.....na gode sosai" Ta samu kanta da
furtawa a sanyaye. Wani tsadajjen qaramin murmushi ya saki yana girgiza kansa.
"No.....no need duniyata.......ba irin wannan godiyar
nakeso ba.....the only one i want........" Sai bai qarasa ba ya mata nuni
da shimfidadden gadon. Da sauri ta juya masa bayanta tana kasa hada ido
dashi,ta fahimci yana bawa abunnan muhimmanci tamkar baisan kayan kunya bane?.
A nutse
taji ana yafa mata abu ta baya,ta daga kanta sai taga wata baqar sassalkar
abaya ce,manal alhammadi shine tambarin da yake maqale a hannun rigar,ta fidda
idanunta tana jin wani abu yana girmamarta,ta taba jin company din,wanda dukka
abayas da yake fitarwa luxury ne masu tsada da aji sosai,ta sansu ne saboda ita
din masoyiyar abayar ce.
"Ba wani kunya tsakanin muhammad fu'ad da
duniyarsa......ba kunya tsakanin muhammad fu'ad da matarsa......abinda kawai
yake buqata......madawwamiyar soyayya da zata mamaye rayuwarsa.....ta bashi
wani farinciki da nutsuwa daya rasa a rayuwarsa.....duk da cewa ina zaqewa da
yawa.......amma wannan abun nake bara" Ya rigata fada kafin ita ta fada.
Boyayyen murmushi ya subuce mata,wato daga jiya zuwa yau ya fara haddace irin
kalmominta kenan da take yawan maimaita masa?.
Juyo da
ita yayi yana zura mata hannayen rigar ya furta
"Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen.....komai saikin
masa kyau?" Yayi maganar yana dage girarsa.
"Komai saina masa kyau?.....ko komai sai yamin
kyau?" Ta tambayeshi tana mamakin yadda yake juya maganar daga qarshe ta
koma farko.
"Kece kike musu kyau basu keyi miki ba.....don dama
kedin me kyau ce.....you're not ordinary duniyata" Yayi maganar sanda ya
dago daga tsugunnan balle mata button din da yayi har qasa. Mayafin ya warware
yayi mata lafiyayyen rolling tana tsaye tana kallon ikon Allah,ya kama hannunta
zuwa gaban mirror yayi tsaye a bayanta.
"Duk wani abu me daraja rufeshi akeyi a
killaceshi" Ya furta a nutse yana duban kyakkyawar fuskarta ta cikin
madubin,yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa saboda ita,kishinta yana sake
ratsashi da kyau,yana sake jin tabbas......lallai ba wanda zaisha ba kuma wanda
zaici bulus daga cikin mutanen dake hannunsa a yanxu.......tun daga kansu
mashkur har zuwa kan zuwaira da bibo.
"Ga aro nan na baki.....idan munci abinci mun dawo zaki
bani kayata" Ya fadi wannan karon yana dan sanya seriousness saman
fuskarsa. Dan dubansa tayi kadan,sai ya gyada mata kai alamun tabbatarwa.
Yanaso ne yayita kallonta,yanason wucewar kowacce daqiqa tayishi bisa
idanunsa,yanaso yaci gaba da kallon baiwa da ni'imar da Allah yayi masa,yanaso
su kasance a haka shi da ita......da zaiyiwu su qare rayuwarsu cikin irin
wannan yanayin na dagashi sai ita.
Yana
maqale da hannunta suke sauka zuwa bangaren cin abinci,private ne wanda ya
dauko musu cook dinne musamman saboda iya su biyun. Sun samu dining room din
cike da cima kala kala,abincin Africa da wasu na Nigeria. Macace da batace ga
daga qasar da take ba,ta tarbesu cikin haba haba sannan ta fara serving nasu
cikin kulawa,lokaci lokaci tana magana da fu'ad da hankalinsa ke waya cikin
yaren Dhivehi,har ta kammala ta juya ta fita tana basu guri.
Juya
spoon din take kawai a plate din tana hadiye wani abu a qirjinta. Batasan meye
ba amma ya tsaye mata a wuya. Bai ankara ba,sai daya gama uzurinsa da waya
sannan. A mamakance yake dubanta.
"Start mana madam....banason wasa da abinci fa?".
"Itama fareedan ce?" Ta tambayeshi da wani salo
daya sanyashi karantar zallar kishin dake kwance a idanunta,saidai kuma a
sarari qwalla ce kwance saman oily eyes dinsa,sai suka qara wani sheqi.
Dariya
yakeson mata saboda wani irin farinciki yaji yana lullubeshi,tun daga saman
zuciyarsa yana sauka ta kowanne sashe na gangar jikinsa. Har ya fara winning
haka da wuri? Ya tambayi kansa yana taya kanshi murna,amma a bayyane sai ya
lanqwasa fuskarsa alamun tausayi.
"Me kuma nayi?". Muryarta na rawa kadan tace.
"Kunata magana da yaren da banaji.....tanata maka hira
kana amsawa?". Wannan karon kam kasa boyuwa dariyarsa tayi,abinda ya
tunzurata kenan.
" Karki wuce gona da iri sabreen,karki rudu ki fada
soyayyar abinda ba yafi qarfin ajinki.....abinda yafi qarfinki,abinda baki da
tabbas a kansa.....shin kin Manta maamah tana nan?". Tambayar data
tarwatsa duk wani qwarin gwiwa da take qoqarin tattarawa kanta,taji kuma komai
ya tsaya mata cak.
Dab da
ita ya dawo ya zauna,ya kama hannayenta ya saka cikin nasa yana matsawa a
hankali.
"Kin taba ganin mutum ya canza DUNIYARSA?" ya mata
tambayar kai tsaye,qasa tayi da kanta don sai takejin tana son jefa rayuwarta
cikin hadari ne kawai,muddin ta sakewa zuciyarta ta fada sonshi to ba shakka ta
fada babban tarko......babban tarkon da zai bawa maamah daman walagigi da
rayuwarta yadda taga dama.
"Amsar itace aah......ke duniyata ce,babu daman na
sauyaki ko na hadaki da wata ko wani abun......ni muhammad jadda naki ne ke
kadai,don ke kadai aka halicceni.....ki rubuta wannan ki ajiye"
_to zamu gani,anya hajiya maamah zata qyale kuwa???_
*ANNI*
Tun a jam'in
sallar asuba da sukazo yi taga bata ga fu'ad ba.....still da tace farouq ya
turo mata shi komin dare baizo ba,har suka gama waya da abba Alhaji hamza
kibiya dake tashi umrar ta kwanta amma ba fu'ad din ba dalilinsa.
Sanda
suka kammala sallar sai tayi zaune kawai tana lazimi,tunaninta yana
rarrabuwa,bataga fu'ad ba......bataga sabreen ba,duka ina suka shiga?. Ta wata
fuskar sai takejin relief na rashin ganinsu su duka biyun,don zuciyarta na
qissima mata wani abu,ta wani bangaren kuma bataso ta sake jikinta akan
hakan,saboda tasan wace mariya din.
Takwas
saura farouq ya shigo gaidata. Yana daga zaune gabanta ya dan dubi amna dake
kwance tana shirin komawa bacci
"Ta duba qur'aninta kuwa?". Kai anni ta daga masa
" Ta duba" Sai ya jinjina kai. Wani sabo ne da
raino data musu dukkansu,dole kowacce safiya....komai uzurinka ko meye kakeyi
ka fara duba qur'ani kafin komai.
"Kiramin fu'ad.....ka gwadamin dukka layukansa"
Anni ta fadi tana gyara zamanta.
"Na gwada wani tun jiya a kashe,amma bari na gwada
sauran" Farouq ya fada hankalinsa kwance,don shi kam ya gama hasashen inda
aka haihu a ragaya ma. Baya tunanin ko maamah ta yiwa fu'ad farin sanin da shi
yayi masa.
Daya
bayan daya yabi layukansa yana kira amma kowanne gaya masa ake a kashe yake,sai
ya daga ido kawai yana duban anni da fuskarta ta shiga damuwa.
"To ina ya shiga?,ina kuma sabreen?". Dariyarsa ya
danne yana dan saka alhini a saman tasa fuskar shima
"Karki damu anni in sha Allah jikina yana bani suna
tare,bari na tura masa email da SMS duka" Ya fada yana fara rubuta
saqonnin ya kuma aike masan kaman yadda yace,duk da yasan zai wahala ya gani a
kwanakin nan,lallai indai ya samu nasarar dauke sabreen ne tofa sai baaba ta
gani.
*MAAMAH*
Idan tace
hankalinta a kwance yake daga daren zuwa safiyar tayi qarya. Ta kirashi ta
kirashi har batasan adadin sau nawa ba. Tabbas ta sani,a yanxu duk duniya idan
ameenatu tace itace mahaifiya ga fu'ad,kuma tana tuhumarta batan sabreen ba
wanda ya isa ya hana a daureta,ba wanda zai fiddata idan ba fu'ad din ba,da
sauran mutuncinta,bataso wasan ya qare a haka,saidai hakan ya sake ninka
qiyayyar anni sosai a ranta. Ita daya taketa shawa kanta alwashin saita yiwa
ameenatu abu mafi munin da ba zata tabawa mantawa da ita ba,idan don tayi
wannan ne don ta nuna mata iyakarta ne ganin suna qasar da ba tasu ba.....to
tabbas ita kuma zata bar mata wani babban tabo a rayuwarta da ba zata taba
mantawa dashi ba.
Musaddiq
ta kira ta sanyashi nema mata fu'ad din,saidai shima kiran duniya wayar sunqi
tafiya.
"Maamah wayoyinsa a kulle suke" Maganan data sake
sakata a taraddadi da tunane tunane iri iri.
"Kada fa ya zamana ameenatu ta salwantar mata da yaro
ne takeson tayi garkuwa da ita akan batun haka da wuri?" Wannan shine
tunanin daketa mata kai kawo.
"Ya kamata ki xama cikin shiri.....ki xama a
ankare.....karki nuna mata tsoronki,ki tabbatar mata da.naki zargin kema"
Abinda zuciyarta take nanata mata kenan,wanda shine kuma ya bata qwarin gwiwa.
Cikin
kwanakin sai ya zamana wani irin zama ake a gidan,kallo kallo kawai akeyi
tsakanin maamah da anni din. Duk da maamah tana cikin d'ari d'ari da tunanin
inda fu'ad da sabreen dinma suke......amma ta azawa ranta wani dakiya. Ta
fannin annin kowanne taku na maamah din saman idanunta yake,ba komai take
dubawa ba sai idanun yaransu da suke rayuwa guri daya,zai zame musu wani abu na
daban kuma na tashin hankali idan suka ga wani sabani muraran a tsakaninsu,banda
hakan a shirye anni yake akan maamah wannan karon.....duk da tana danjin relief
idan farouq na bata tabbacin fu'ad da sabreen din suna lafiya.
Farouq din
ya fahimci abinda ke faruwa,saidai bai nuna musu komai ba,yayi ma kaman bai
sani ba,saidai time to time shima yana neman fu'ad din ta waya,amma dif kakeji
ko sau daya bai taba katarin samunsa ba.....a haka sannu a sannu sai gashi an
kwashe sati guda cif ba wanda yaji motsinsu ko yasan inda suke.
Zuwa
sannan hankalin anni ya tashi sosai,kusan kullum sai tasa farouq ya kira mata
shi,mafi qaranci sau biyu a rana,saboda kwanakin barinsu Maldives kusan za'a ce
yayi,kwana uku ko hudu suka rage musi,gashi babu shi ba sabreen din.
Tun tana
yiwa maamah din kara har abun yaci tura,ranar daya rage kwanaki uku subar
qasar,da wani yammaci suna parlor. Amna ke mata kalba saman dogon gashinta da
tafi masa kalba akan kitso,maamah tana daga gefe zaune tana kallo cikin tv. Ta
tsiri wannan zamanne kawai don ta nunawa anni ba abinda zai tsoratata,hakanan
itama me cikakken iko ce,duk da cikin rashin cikakkiyar nutsuwa itama take. Ba
sabreen ce ma damuwarta ba danta shine damuwarta,idan tana da damuwa akan
sabreen din bazai wuce na yadda take gudun kada anni ta fake da wannan ta
tozartata a idon duniya ba.
Farouq ne
ya shigo da sallama,kaman yadda suke koyi da tarbiyyar anni da umarninta,ya
yiwa maamah barka da gida,ta amsa masa a d'age kaman yadda ta saba. Mugun
haushinsa takeji.....tana ganinsa a asalin tantirin munafuki tun daga
quruciyarsa kawo yanzu,kai tsaye zata iya cewa shine kanwa uwar gami da yaja
mata yaro cikin gidansu ya hadashi da mayun iyayensa da suka kasa sakar mata
kurwar d'a,suka hanata taci arziqin d'anta yadda ya dace. Ko a yanzun gani take
cutar fu'ad kawai yakeyi yana amfana da arziqinsa,yana tatsarsa ne shima.....ba
wani tare da suka samo arziqin,ba kuma wai iya harkar noma da kayan abinci yake
wannan fantamawar ba,dukiyar gold da diamond din d'anta ce.
"Farouq......kwanaki uku suka rage mana mubar
Maldives.....ka samomin 'ya'yana?" Tayi maganar cikin salon son isar da
saqo ga maamah.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 104
104
Kalmar
'ya'yana din kuwa ta daki zuciyar maamah da wani matsanancin kishi. Wato har
fu'ad dinma ya tashi daga sunan dan riqo ya koma danta?.
"Aah anni....inata dai qoqari" Ya amsa mata yana
fahimtar inda saqonta yasa gaba. Kai ta jijjjiga
"Zan sabawa fu'ad kuwa muddin qafafunsa yasa ya tafi
bai sanarwa iyayensa ba.....idan kuma wani keda hannu kan hakan....na rantse da
Allah ko waye bazan barshi ba.....tashi kaje,tsakanin yau da gobe nakeso ka
lalubomin shi" Kai kawai kada mata yana tashi,maimakon ya koma daki sai ya
juya yana sake ficewa a gidan.
Yau din
Jordan ya nema kai tsaye,shima ya gaya masa tun randa suka fita tare bai sake
ganinsa ba. Ci gaba yayi da bibiyarsa ta waya amma a banza,sai ya koma ya
lalubi system dinsa da yakan ajiye schedule nasa da komai. Yasan password nasa
da komai don haka kai tsaye ya bude ya shiga. Zallar aminci ne da yarda da kuma
dawwamammiyar qauna,shima iya abinda yaje nema ya shiga ya duba kawai ya fito.
Bai samu bayanin komai ba,hasalima bai ajiye inda zashi ba banda ranar da
sukayi zasu fita din satin baya daya wuce ranar daya bace kenan.
Awa daya
ya bawa ransa zai sake kiransa,idan bai sameshi ba kuwa aikin safa da marwa ya
sameshi cikin tsibirin Maldives,wala'alla sai yayi hayar boat ko skis ya gewaye
tsibirin Maldives ya nemowa anni 'ya'yanta.
"Oops.....wannan soyayya taku nima ta jefani kwale
kwale.....where are you?.....anni ke kika jawo,da kin damqa masa matarsa salin
alin dani kaina ban tsinciki kaina a halin da nake ciki ba" Ya fada yana
furzar da iska daga bakinsa gami da yin relaxing jikin kujera yana lumshe ido.
Murmushi ne kuma ya qwace masa saboda hango fuskar maamah da yayi,tayi wani
laushi da yaushi ba tare data fahimci hakan ba
"Wato anni kema kinsan takan tsiya?" Ya fada qasan
ransa yana komawa ya kwanta sosai saman sofa din.
★Gaba daya ya
wani narke saman sofa din bayan ya miqe qafafunsa saman table din gabansa daya
dora system dinsa. Tun dazun ya kunna system din amma ya gaza saka mata
password ya budeta. Sai yau yakejin ya kamata ko farouq yasan inda yake,don
yayi imanin ko kowa bai nemesa ba anni zata nemesa,zata kuma damu da rashin
ganinsu.
Gilmawarta kadai a gabansa yana debe hankali daga gangar jikinsa,a
kwanakin nan shi kansa yasan mahaukacin so yake mata wanda baisan adadinsa ba.
Idan ya kebe yana salla,yana yawan tuhumar kansa wanne irin so yake mata
wannana?,abu daya ke sanya masa relief addu'o'in daya debe tsahon rayuwarsa
yana yi akan.
"Ya Allah,idan ka tashi dasamin soyayyar wata 'ya
mace.....ka jarabceni da soyayyar da zan iya.....ka dasamin soyayyar macen data
dace dani ta dace da rayuwar 'ya'yana,macen da zata soni itama sama da yadda
nakeson kaina....macen da ni karan kaina takeso ba abinda na mallaka
ba.....macen da zata fifitani sama da kowa da komai....tsaftatacciyar
mace.....kamila aaqila....aabida,ya Allah,kada ka jarabceni yadda ka jarrabi
mahaifina......ubangiji ka azurtani nida dan uwana da matayen da zasu rufe
ciwukan da suke cikin zukatanmu kaman yadda kayi mana baiwa da samun
anni". Idan ya tuna wannan addu'ar sai yaji son da yakewa sabreen din ba
komai bane.....yayi imanin Allah bazai wofantar da addu'ar da aka dauki tsahon
lokaci ana qwanqwasa qofarsa saboda ita ba.
Duk wasu
kaya nata tunda sukazo wajen tayi bankwana dasu,daga kayan safiya zuwa na dare
duka tana shigarta ne a bisa zabinsa. Tun tana dojewa har ta fara ragewa,don
idanma tace zata musa shi zai tubeta ya kuma sanya matan. Yayi amfani sosai da
damarsa......yayi amfani da tsoronta da gurin ya mata wani irin sabo da kwana a
jikinsa,ya sanya wata shaquwa me qarfi a zuciyarta da wannan. Ranar farko da
hakan ta fara kasancewa.....
Tayi wani irin bacci da idan zata iya tunawa irin baccin
qarshe da tayi saman cinyar ummenta ranar da asthma dinta ya tashi. But bacci
cikin jikinsa yana da wasu qa'idoji da ta kasa kiyayesu har yanzu. Wani sabon
abune kwanciya hakanan ba tare data rabawa jikinta komai ba....shi kuma kullum
sai ya maimaita mata bayan ya maidata yadda yake
"That's my rules". Daga qarshe wayo yake
mats,wayon da yake sanyawa washegari ta tashi da matsananciyar kunyarsa da bata
iya hada idanu dashi.
Duk
yadda taso ta gano yadda yake iya cimmata ya firgitata ya fiddata daga saitinta
ta kaucewa wannan abun amma ta gagara......wani lokaci har jira takeyi yayi
wani motsi don tayi masa tawaye.....to amma da an iso gurin sai ya sanyata ta
manta wacece a ina kuma take?,sai bayan qura ta lafa ta isheshi da kukan banza
da qorafi. Wani lokaci ya biye mata ya lalace wajen rarrashi.....wani lokaci
kuma yaja hancinta
"Har yanzu baki fara koyan maida martani ba......am
dreaming about it,saikin gama kwashe alkhairan kuma ayitamin kukan
abunga...." Gulma tason yakeson cewa,fadi ne kawai bazaiyi ba.
"Sabrrrr" Ya kirata jikinsa yana sake macewa. Wani
irin Palazzo ne a jikinta da wata 'yar top data zauna mata sosai a jikinta,ta
kuma bayyana masa albarkatun qirjinta yadda yakeso. Kanta yasha hair pins wanda
shi ya zauna ya shiryata,ya kuma gyara mata kan yadda yakeson gani.
Yasha
wahala sosai wajen nesanta kanshi da mata,ya kame kansa,ya runtse ganinsa ya
kuma kiyaye al'aurarsa.....wannan ya sanya yaci alwashin ko meye dake burgeshi
game da mace sai yayi qara'insa a jikin matarsa......sai ya kalla yadda ranshi
keso. Yana ankare da ita a takure taka,yasan zaayi hakan,don shima ko sau daya
bai bari idanunsa sun huta da kallonta ba.
Duk sanda
yaga dari darinta akan sakin jiki ga d'a namijin da ya kasance mijinta sai yaji
wani qunan rai da bacin rai ga wadanda suka dinga sadakar mutuncinta,suka kuma
dangantata da sunan KARUWA.
"Zo kiji" Ya fada a galabaice yana miqa mata
hannunsa sanda tazo gilmashi. Baima bata lokacin tunani ba ya sanya hannunsa ya
jawota saman cinyarsa yadda ya saba mata. Sam bata masa nauyi wajen dauka ko
jawowa,kaman wata leda yake daukanta.
Matseta
yayi a jikinsa yana rungumeta sosai,ya kuma dauko system din ya aza saman
cinyarta yana saka password dinsa.
"Massages nakeson dubawa amma gaba daya kin hanani
sukuni.....sai rarrabamin hankali kike,gwara ki zauna mu duba tare,wataqila
nafi samun nutsuwar dubawar"
"Me nayi kuma?" Ta tambaya a shagwabe. Hancinta
yaja yana kashe mata idanu
"Aah hajiyata....komai mafa kinyi.....satar da kikayi a
gangar jikin muhammad fu'ad.....zuciyarsa dinnan ta tafi kenan,bana jin zata
dawo masa har abada" Ya fada yana sakinta gami da fara buda saqon farko
wanda ya sakashi sakin murmushi ganin saqonnin farouq a jejjere a jejjere. Na
qarshen ya fara budawa wanda bai wuce mintuna talatin da turowa ba.
_"You're rocking the boat,you're fanning the
flames.......dude.....ka shiga hankalinka ka dawo gida.....yaqi zai barke
tsakanin ummominka.....am serious dude"_ shine saqon qarshe daya gani
mintuna talatin baya. Dan murmushi ya saki yana tabe baki,yasan abinda farouq
zai masa qarya.....ya kuma san wanda bazai masa qarya ba,wannan statement din
nashi yasan real ne ba wasa yake masa ba,sai ya danna replies ya soma bashi
amsa
_"Step back BB.....leave them.....nasan anni ba zata
biye abun yayi worst ba.....ina nan ina neman hadin kan DUNIYATA.....zamu hadu
a airport ranar Tuesday to makka in sha Allah"_ yana tura masa ya koma
duba ragowar saqonni masu muhimmanci yana ragewa,saidai kusan bayan kowanne
minti daya sai ya tura kansa cikin rigar ta. Tureshi tayi har sau biyu,ana ukun
yayi warning nata
"Idan kika sake ban yafe ba" Idanunta dukka ta
fidda idanunta waje tana dubansa a mamakance,rai ya hada
"Yes....aikin karanta walau alattanur ko wajen
rumaisa?" Qasa tayi da kanta tana tunawa da hadisin,ya kuma aza mata wata
irin kunyarsa sosai. Yadda yaga tayi ya masa dadi.......da gaske karatun yana
kama zuciyarta har haka,tsaf fa zai iya komawa wajen malam ci gaba da daukan
karatuttukan da zasu sanyashi sake sanyata ta sake zama sassanya.....buqatar
maje haji sallah. Yadda tayin ya bashi daman dauke hannuwansa daga can system
din ya maida inda yafi muradi da wani tattausan yanayi yana sake shigewa
jikinta.
"So kike na zama dan is......" Batasan ta saka
tafin hannunta saman bakinsa ba.....batasan sadda hakan ta kasance ba sai data
tsinciki narkakkun idanunsa cikin nata,hakan sai ya zama kaman wani lasisi ta
bashi kenan daya sakashi yunqurawa dauke da ita,daidai sanda saqon farouq da
mamakin fu'ad din ya kasheshi ya shigo system din,ta baya ya saka qafa ya
tureta ba tare daya damu da idan ta fadi zata iya fashewa ba
"Just leave me have this moment,don't dampen the
mood" Yayi maganan kaman wanda yasha giya ya maku,saidai duk da hakan abun
mamakin shine,sanda ya mata masauki saman tattausan gadon da harshensa dake
hardewa yace da ita.
"Let me relish this moment,and then I'll tell you more
about fu'ad. Ya kamata kisan waye fu'ad......am ready to make you DUNIYATA da gasken gaske.......inason kisan komai nawa
da gaske......".
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 105
105
_Barkanmu da dawowa,fatan munyi sallah lpy,ubangiji ya
maimaita mana cikin lafiya aminci da kwanciyar hankali_
Batasan me
yake tsarga mata ba duk sanda ya kirata ta DUNIYATA ba,wani irin feeling takeji
yana motsa zuciyarta,wanda tun tana qaryatawa har ta soma yarda tana jin wani
abu a ran nata duk sanda ya ambaci sunan. Yafi mata dadi ya kirata DUNIYATA
akan ya kirata my world.
Susutacciya ya maidata yadda ta fahimci ya soma maidata a wadannan
kwanakin,lallai so yake sai ya matso komai a kansa dake cikin zuciyarta. Ta
sani tabbas muddin zaici gaba da wannan salon......muddin zaici gaba da tafiyar
da ita da wannan tsumammen yanayin to ba shakka zata gaza boye duk wani abu
dake zuciyartata kuwa.......yana kuma dab da maidata mahaukaciya da gasken
gaske,zata rasa duk wannan dauriyar tata da basarwa da takeyi.
D'aya
bayan daya ya dinga zare hair pins din da dama shi ya zauna ya jera mata su,duk
daya idan ya zare yana ware gashinta me tsaho baqi da santsi,wanda zuwa yanzun
hair mist dinsu shi da ita ya zama guda daya,kaman yadda mayataccen mouth fresh
dinsu ya zama products daya. Kusan komai nata cikin kwanakinnan ya canza mata
zuwa kalar wanda yakeso,qamshinta,creams lip gloss da komai ma......komai kuma
me tsada ne fiye da tunaninta,ranar data duba kudin perfume din daya sauya mata
zaune kawai tayi tana binsa da kallo ba tare da yasan ma me ake ba. Su huda na
wata duniyar duk da tayi imanin suna cikin kulawa......amma ita tana nan tana
rayuwar da take ganin tafi qarfin matsayinta?.
Sai daya
zare mata duk pins din,sannan ya kutsa yatsunsa cikin sumarta yana barbazata
yadda yakeso,ta fahimci tana daya daga cikin abubuwan da suke matuqar burgeshi
ga diya mace. Kaman yasan abinda yake saqawa muryarsa me kama data mashaya ta
sauka a kunnenta
"I love it duniyata......kina da komai da nakeso.....
Please ki sake bani dama na gina miki wasu dabi'u.......na dade ina kame kaina
daga kallon Haram da kuma zina.......i only want my pure halal.......please ki
qarasa mallakamin kanki da rayuwarki gaba daya I want the best from you,i want
the best relationship with you" Ya qarashe maganar yana mata wata
kyakkyawar runguma kafin ya fara maidata birkitacciya yana cireta daga ainihin
tunani nutsuwa da saitinta. Batasan wanne abu daban yake buqata daga gareta ba.....batasan
wanne best yake nema ba bayan duka fitar da ita daga tsarinta da yakeyi. Yana
sakata jin wani irin nauyi da kunya da bata taba tsintar kanta a ciki ba.
Ko yanxun
da qura ta lafa tana gaban madubi yana tsaye a bayanta yana bata dan kunnenta
tana maidawa daya bayan daya,ya kafeta da idanu murmushi na fita daga kan
fuskarsa qasa qasa. Idan yana kallon fuskarta a irin wannan yanayin sai komai
ya dinga dawo masa. Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa kaman zai fashe don
tsananin cika da qaunarta da sukayi,yadda yakeji a duk sanda suka kasance da
juna.....yasha imagination abun idan tana participating itama,yana kwadayin
yaga wannan lokacin.
Taku uku
ya qara ya hade tazarar dake tsakaninsu,ya dora fuskarsa saman kafadarta yana
dubansu a tare shi da ita ta fuskar madubin.
"Idan Allah ya bamu 'ya'ya......wanne irin kyau xasuyi
my world?". Wani kunya ya saukar mata,tayi qasa da kanta qaramin murmushi
yana subuce mata. Shima murmushin ya saki,a duk sanda kunya haka ta bayyana
saman fuskarta tana mata wani irin kebantaccen kyau na musamman.
"DUNIYATA.......Why aren't you responding?" Idanu
ta daga alamun tambaya ba tare data yarda ta kalli tsakiyar idonsa ba. Ya
fahimci haka,sai yasa yatsunsa yayi gefe da gashinta yana cusa bakinsa ta
kunnenta abinda ya sanya tsigar jikinta tashi.
"On bed dear......" Ta fahimci inda ya dosa,don
haka bata bari ya qarasa bama ta soma neman inda zata boye fuskarta. Ire iren
rashin kunyarsa suna sakata jin wani irin nauyi ba kadan ba.
"Ko sai randa aka yanke shawarar ana sona ko ba'a
sona?" Ya sassauta muryarsa yana fadi qasa qasa gami da riqe hannayenta da
kyau qaramin murmushi yana subuce masa.
"I hope wannan ranan zata zo soon.......na matsu,ko
akwai wani abu da ake buqatar nayi da za'a gayan I LOVE YOU MUHAMMAD FU'AD
JADDA?....." Ya tambayeta da gasken gaske,har qasan zuciyarsa yana
sha'awan jin ta fadi hakan. Kai ta girgiza tana basarwa,neman tserewa takeyi ya
kuma fuskanceta,don haka ya sunkuceta kawai yana nufan stairs din da sukayi
dakin qasa.
Idanu ta
fitar waje,har ha Allah tsoron dakin qasan nan takeyi,yatsa ya saka ya lakuce
mata hanci yana girgiza kai.
"Relax.....you're safe my world.....bazan taba yin wasa
da DUNIYATA ba fa". Kasa ce masa komai tayi sai idanu data lumshe tana
shaqar daddadan qamshinsa daya cika mata hanci,ta kwantar da kanta a qirjinsa
tana jin bugun zuciyarsa. Batasan me yasa ko yaushe bugun zuciyarsa daban yake
ba,wani bugu ne me sauri sauri wanda tasan qa'idan bugun baikai haka sauri ba.
Idanunta saman dakin duke kallo,yadda ruwa yake gudu saman kansu tare da kifaye
kala kala ba tare da ko damshin ruwa ko qwaya daya ya tabasu ba,ta dauke idanu
tana tasbihi ga ubangijinta.
Saman
lafiyayyen gadon dakin ya ajiyeta,ya dawo gabanta ya tsugunna yana zagaye
hannuwansa da qugunta.
"Muhammad fuad jadda.......d'an alhj Muhammad
ne,haifaffen bafulatanin mambila......,ta gefan mahaifiya kuma...." Sai ya
danyi shuru yana hadiyar numfashi.
"Mariya da akafi sani da maamah itace
mahaifiyata.....bafulatanar mayo belwa ganye local government" Hannuwanta
ya riqe a tausashe cikin nasa zuciyarsa na karyewa.
"Lokaci na farko da zan bude bakina na fasawa wani dan
adam daban rayuwata.....waye ni?....me naji me na
fuskanta?.....sabrrrrrr.....abbana......abbana yana cikin jerin sahun mutumin
da nafiso nafi qauna kaf cikin rayuwata.......saidai mun rasashi a sanda mukafi
qaunarsa......mun rasashi a sanda mukafi buqatarsa......mun rasashi saboda
wa'adinsa ya cika.....amma da taimakon maamah". Kai ta daga tana
dubansa,tana ji yana tayar mata da wani mikin ciwo dake zuciyarta.
Kai ya
gyada mata idanunsa suna sauya launi.
"Ta shayar dashi guba......ta dura masa miyagun
maganganu da suka qarasa illata gangar jikinsa da zuciyarsa,suka Haifa masa da
ciwon zuciya......kalmomin bakin maamah su suka jefa abba na a matsanancin
ciwo......ciwon da haquri ya gadar dashi dashi,ya kuma ci gaba da tara masa
guba na maganganun da suka zama silar fashewar zuciyarsa daga qarshe. Tun a
gaban idanunsa muje ganin qasqanci da wulaqanci,ba wanda yake samun tausasawa
ko kulawa daga gareta,daga shi mijinta harmu 'ya'yanta......bazan boye miki
komai ba......bamusan dadin uwa ba,bamusan wani abu da ake kira dadi tsakanin
mahaifiya da 'ya'yanta ba,mun rayu tamkar irin rayuwar da bawa zaiyi a hannun
ubangidansa,walwala 'yanci da farinciki dukka yayi mana qaura,mun rayu tamkar
agololi kuma 'ya'yan riqo......abbanmu kuma ya zama tamkar wani yaro gida bame
gida ba......ba abinda tafi bawa mutunci da kima sama da KUDI sama da tayi KUDI
sama da abbanmu dole ya zama me KUDI ya nemo KUDIn da zatayi kalar rayuwar da
takeso,yayi lafiya ko kada yayi......ya rayu ko kada ya rayu,muyi lafiya
tarbiyya ilimi mu tsaftatu mu qoshi duk basa cikin lissafinta,abinda ya dameta
shine KUDI.....sabrrrrr..... Mun rayu cikin qasqantacciyar rayuwar da al'umma
suka gaza janmu a jiki a garin da bamu da kowa,kowa yana ganin tunda wadda tayi
silar zuwanmu duniya ta gaza tallafawa da tausayawa rayuwarmu,lallai mudin
akwai wani abun aibu ne a tattare damu. Taji a rant ba zata iya rayuwa damu
ba,ba zata iya zama damu bs,ta watsar damu da abba dake buqatarta saboda
matsanancin ciwon zuciya dake sake kwantar dashi....duk inda abba bai qwallafa
rai a soyayyarta ba,tayi nesa dashi shi yafi alkhairi,kunnuwansa xasu daina
kwana su wayi gari da jin munanan kalmominta a kansa wanda hakan shizai bashi
lafiya da wuri.....saidai kuma sonta ya zame masa jarrabin rayuwa,ya kasa
haqura da nesanta kanta damu da tayi,ya sake zame masa silar hauhawar ciwonsa.
Nayi kwasar kashi......nayi aikin bola da hannuwana duk don na kula da musaddiq
da abbana......nayi sharar kasuwa nayi ta kwata har bansan iyakarsu ba kawai
don na samo abinda xan kula da abbana da musaddiq.......munci abincin bola
saboda gudun yunwa kada ta halakamu.......na kwana da GAWAr abbana.......na
kwana da gawar mahaifiyar abbana JADDA saman cinyata dukkansu ba tare da nasan
mutuwa sukayi ba ko bacci?,naci gaba da gadin gawarsu ba tare da nasan ya akewa
gawa ba?,a shekarun da duka duka baifi a koreka daga bakin gawa ba idan kana da
gata don kada kaga abinda shekarunka basukai ba. Jadda tazo mana da wani irin
gata da muka dinga tunanin wahalarmj ta yanke......ta saida duk komai nata don
tazo ta kula damu......ta bamu wani jin dadi wanda ko maamah da tayi silar
zuwanmu duniyata tsahon shekarun da mukayi tare da ita bata taba bamu irinsa
ba. Saidai sanda muke tsaka d wannan tunanin ashe ragowar kwanakinta na rayuwa
yazo qararwa tare damu ajalinta yazo mata a kusa.....ta sake kwanciya ta barmu
a wani irin yanayi. Daga sannan muka sake gane meye ma'anar rayuwa?,muna ta
tunanin maamah zataji labarin komai......zataji tausayinmu ta dawo garemu amma inaaa......wanda
yayi nisa bayajin kira........wata kalma da maqocinmu ya fada a kanta sanda ya
dawo daga kudu yace mana ya ganta a can.......taqi barin raina da
zuciyata.......har yanzu da ita nake kallonta.......bansan ranar da zata bar
zuciyata ba.........maamah dinnan dai da daga qarshe naji duk duniya ba wani
abu da nake qyamatar ya kusanci inda muke......itace silar mutuwar abba......ke
daya kikasan wannan a duniya......na kamata har sau uku tana ciyar dashi da
abubuwan da likita ya hanashi ci saboda suna tunzira ciwonsa.......suna kuma
iya sanyawa komai ya faru dashi ciki harda rasa rayuwanshi......a dukk ukun nan
dana kamata tayi alqawarin ba zata qara ba.....mantawa takeyi ne......na
fahimci abinda ya sanyata take aikata haka ta hirarta da qawarta da har yanxun
nake tunanin kamar matar nan harira da suke tare ne......so take ta kashe
auren,so take abbanmu ya saketa shi kuma yaqi......tace tana buqatar tayi
arziqo,tana buqatar freedom amma yaqi sallamarta....wannan shine
dalilinta......shine kuma silar tunzurar ciwonsa har ya kaishi ga
kushewarsa......ba ita ta kasheshi ba kenan sabrrrrr?" Yayi mata tambayar
da wani irin yanayi daya tsorata sabreen qwarai da gaske.......yanayin da yake
tabbatar mata wani abu ne guda daya da yake masa ciwo har yau har gobe a
zuciyarsa......salon tambayar data tabbatar ya jima yana so ya yiwa wani dan
adam ita......amma rashin jin kowa a matsayin na kusa da zuciyarsa sosai ya
sanya ya gaza furtawa kowa,yadda yayi tambayar kaman hankalinsa na neman
gushewa daga jikinsa sai ta kama kafadarsa da kyau tana riqewa kuka yana shirin
qwace mata......tana jin ashe suna da yawa irinsu wadanda suka rayu cikin
wulaqantacciyar rayuwa?......amma dashi dake da sauran uwa a raye........dasu
da ba ko daya ga dangi masu tsananin jifa da zumunci waye yafi rashin sa'a.
"Sabrrrr" Ya rigata sakeyin magana duk da tana
buqatar magana dashi.
"Idan kika gwada yimin abinda maamah ta yiwa
abbana......nima mutuwa zanyi kaman abba.......saboda na fahimci zuciyata irin
tashi ce......bamu iya soyayyar qarya ba,bamu iya soyayya da wasa ba,bamu iya
yiwa masoyi qaramin riqo ba.......a halittarmu yake.......wannan ya sanya na
tsani soyayya na kuma tsani kowacce 'ya Mace......anni ce mace qwaya daya data
fara samun qauna irin ta uwa daga gareni bayan faruwar komai......amma hatta da
amna bata samu komai daga gareni ba sai sanda naga tana shirin mutuwa ta barmu........bazan
jure ba sabrrrrr idan kikace zaki gujeni......bazan iya dauka ba idan kika ce
zaki barni sabrrrrr,da gaske nake nima mutuwa zanyi" Ya qarasa fada
muryarsa da dukkanin jikinsa suna wani irin rawa,tabbacin ya tabo mikin da
baida kamarsa a rayuwarsa.
Gaba daya
sai ta rude,ta rasa yadda zatayi dashi,ga wani irin ciwo daya tayar mata wanda
baida magani illa itama tabar hawayen idanunta su sauka ko xata rage abinda
takeji tsakanin qirjinta zuwa zuciyarta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 106
106
"Kasan
wace sabreen din da kake muradin ta tabbata a matsayin taka?". Ta fada
muryarta na yayyankewa. Wani kyakkyawan riqo yayi mata yana sakata cikin
jikinsa.
"Na sani......na sani,iya abinda kuma na sani a kanta
ya isheni yanxu haka......abinda ya ragemin ME YASA WANNAN TSAYAYYAR SABREEN
DIN sauri bada kai ta yarda da wannan muhammad jadda din?,shima bana fatan
kiban labari,da kaina zan lalubo......duk wanda keda hannu wajen maida sunanki
wancan mummunan sunan baxai shaba.....sai na hukuntashi" Ya fada jikinsa
na daukar rawa gaba daya.
Luf
sukayi a jikin junansu,kowa yana qoqarin controlling yanayinsa,sannu a hankali
yanayinsu ya fara daidaita,saidai kuma a hankali taji jikinsa yana daukan wani
irin dumi......kafin kace meye wannan zazzafan zazzabi ya rufeshi me tsananin
zafin da har cikin fatarta da tsokarta takejin zafinsa.
Rudewa
tayi sosai,ta fara qoqarin zamewa daga jikinsa tana fadin.
"Zafin yayi yawa......yayi yawa ka bari a samo
magani".
"Banaso ki kira mana kowa a gida.......inason kwanakin
nan biyu da suka rage nayisu dake.......banason kowa ya shigo
tsakani" Ya fadi dumin numfashinsa
yana saukar mata saman goshinta. Kai ta girgixa hankalinta yana tashi.
"Jikinka yayi zafi da yawa...akwai buqatar temperature
din yayi qasa". Sake sanyata yayi a jikinsa ya lullubeta da kyau
"It's not......haka fever na yake......zai sauka"
Ya fada yana lumshe idanunsa duk kuwa da cewa yau zazzabin na daban yake
jinsa,don har kusan cikin qasusuwansa yakeji kaman ana karyasu,saidai
kwanciyarta a jikinsa yafi masa komai a yanzu haka.
★Shi kadai ya
dinga dariya sanda saqon fu'ad ya tarar dashi. Hannu yasa yana shafa kwantaccen
sajensa yana duban saqon yana sake karantawa. Wato ko yaya kusanci yakai
tsakaninka da iyaye akwai sanda soyayya da matar aure ke diban nasu kason idan
kusanci yakai kusanci. Bai taba tunanin akwai sanda fu'ad zai nemi kebewa shi
daya ya barsu tsahon kwanaki ba tare da ya buqaci kowa yasan inda yake ba....ko
ya rabi kowa ba. A nutse ya maida masa amsa sannan ya juya akalar motar yana
komawa gida don bawa anni saqon d'anta. Fitarsa dama kenan daga gidan yana
tsammanin zai iya samunsa a wani gurin,amma yanayin amsarsa kawai ya tabbatar
masa ba zai ganshi ba koda ya shiga neman nasa.
Suna dab
da kammala kalbar da amna kewa annin ya shiga parlor din,yadda ya barsu a daxun
haka ya samesu,kowa zaune yana sabgar gabanshi.
"Anni.......sai kisa haquri,ba zaki samu ganin yaronki
ba sai Thursday a airport,haka yacemin" Ya fada yana daga kafadunsa.
Maganan farouq taja hankalin maamah duk da bata waiwaya sashensu ba bata kuma
nuna taji abinda suke tattaunawa ba,ta riqe waya kawai a hannunta kaman tana
daddannawa amma maganganunsu take saurara.
Qaramin
murmushi anni ta saki,iya bada saqon da yayi a gaban maamah dinma ya wadatar
mata,tabbas zai isar mata da wani muhimmin saqo,duk da ta san farouq din ya
fadi ne kawai ba tare da wani nufi ko wata manufa ba,ya fada ne kanshi tsaye.
"Indai suna lafiya alhamdulillah,lafiyarsu tafimin
komai" Sosai maganar ta soki maamah,ta tattaro wani yawu me tauri ta
hadiye da qyar tana qoqarin daidaita numfashinta.
"Na rantse da Allah yadda kika dasa baqinciki cikin
rayuwata.....saina dasa miki fiye dashi a taki rayuwar......indai har ban
aikata haka ba lallai ba shakka ni mariya 'yar zina nake" Ta fada cikin
zuciyarta wata wutar daukan fansa tana ruruwa cikin zuciyarta. A yanzun inda
za'a bata bindiga.....aka ce ta kashe maqiyinta qwaya daya da tafi tsana a
duniya.....to xata nemo harsasai guda biyu ne,ta kashe Alhaji hamza da
ameenatu.....harsashinta na ukun kuwa muddin ya samu to sabreen ce ta gaba. Tayi
imanin bariki ce zallah......zallar barikice ta sanyata janye mata yaro,wannan
dukka plans din yarinyar ne,ita ta shirya ta tsara ta kuma gabatar,amma indai
da numfashi a gangar jikinta saita gaya fahimtar da ita tazarar shekaru a
rayuwa ba qarya bace,dukkan wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi.
Har tana
niyyar miqewa ta wuce dakinta,don ba abinda take gani a parlor din face abinda
zai daga mata hankali yakuma sake tunzura mata zuciya,sai ga musaddiq ya shigo.
Ta dauka itace mutum na farko da zai fara gani,tayi zaton itace ta farko da zai
fara zarcewa wajenta,saidai gaba daya hankalinsa yana kansu anni.
"Lalala....waye ya saki kitso?" Musaddiq ya fada
yana fito da idanunsa waje ba tare daya lura anni takewa kitson ba. Kwabe fuska
kuwa tayi tana nuna anni da bata ganinta da comb din hannunta.
"Nice nan dan gidanku" Anni ta fada tana hade
rai,saidai kuma qasan hade ran nata murmushi ne boyayye a kwance da zaka iya
karantarsa.
"Ai banga ke bace" Ya fada yana shafa kansa yana
saukar da ganinsa qasa gami da qoqarin boye damuwarsa.
"Maza ka qarasa sakaltata.....tunda shi wancan yayi
gudun hijira......nidai wallahi karku sakani cikin masu yiwa mijin da zata aura
bayanin sangartacciyar da zai aura ahto" Farouq ya fada yana miqewa gami
da jifan musaddiq da harara.
"Basai kun wahalar da kanku ba BB.......mijin yafi kowa
fahimtar wacece ita.... Lafiya qalau ba wanda zaiji bari ya gani" Musaddiq
ya fada kansa tsaye yana aje dubansa kan fuskar amna. Maganan yadan tabata,sai
ya hade mata da jin nauyi,bakinta yayi murus tayi qasa da idanunta tana tsaga
kalban anni din. Ganin haka sai shima ya juya xai fita,sai a sannan subutar
bakin da yayi ya dawo masa.
"Kan uban buhun babbakun bala'i" Maamah ta fada
tana jin numfashinta kamar zai tsinke daga hunhunta yayi qaura yabar gangar
jikinta. Ba ita kadai ba,kusan duk wanda yake wajen ya dauki haske,saidai nasu
kyawawan zukatan cika sukayi da farinciki duk da basu nuna hakan kai tsaye ba.
"Kai musaddiqu!" Maamah ta fusgi sunansa da wani
irin sauti sanda yake bin bayan farouq xasu fice a falon. Farouq din bai dakata
ba ya fice abinsa,sai musaddiq daya tsaya sannan ya dawo da baya.
"Ban ganki ba kina falon ashe.....barka da yamma".
"Don uban banka ta yaya dama zaka ganni?,ai ba zaka
taba ganina ba daman tunda idaniyarku ta jima a kulle,amma aidaka shigo kaga
qannen uwarka da yayyen uwarka rututu ko?". Maganan ta masa nauyi
qwarai,bayaso kuma taci gaba a haka,don yasan inda qarshen maganar xata tsaya.
"Ba'a canzawa tuwo dai suna wallahi.....komai tsahon
xamani da shudewarsa dole abar masa sunansa.....dole kuma abar masa siffa da
kamarsa........kasan me yasa na tsaidaka?" Ta tafi Kai tsaye ga abinda
yake tsunkulin zuciyarta.
"Inaso na gaya maka ka shaidawa dan uwannaka........ban
haifi yaron da xai yiwa kansa zabin matar aure ba,yadda na kawoku duniya ba
tare da shawarinku ba......haka zan zabawa kowanne days a cikinku kalar macen
da tayimin.....ba kuma uban daya isa ya hanani tunda ba adopting naku nayo
ba,haka ba tsintoku nayi ba.......mutum ya sabamin kuma daidai nake dana tsine
masa albarka sai me?,da can ma aina rayu babu shi......tashi ka bani waje
shashasha wand baisan gurin dake masa ciwo ba". Tsam ya miqe kamar yadda ta
buqata,zuciyarsa na masa wani irin bugu kaman zata balle qirjinsa ta fito,a
haka ya lalubi hanya ya fice yana fatan samun wadayacciyar iska da tafi ta
parlor din yawa.
Ko sanda
zata gama da farouq tuni anni ta jima da wucewa dakinsu ita da amna,suna shiga
anni ta maida qofar ta rufe,idanunta zube saman fuskar amna da yanayi na tuhuma
take kallonta.
"Amna!,kalleni da kyau!!" Anni ta fada adan
tsawace tana budewa amna dukka girman idanunta,abinda bai taba faruwa ba
tsakaninsu.
"Akwai wata alaqa ta daban bayan ta yaya da qanwarsa
tsakaninki da musaddiq?" A dan tsorace amna ta daga kai ta kalli anni,wani
irin tsoron annin ya mamayeta abinda bata taba ji ba a kanta tunda ta haifeta.
Koda cikin tsoro take muddin anni na gefenta tana samun aminci,amma yau annin
ce abar tsoron da kanta.
"Tambayarki nakeyi kinyi tsaye kina qaremin kallo"
Anni ta fada bayan ta lura da yadda zuciyar amna kr bugawa. Ba zuciyar amna
kawai ba,itama tata zuciyar bugawa takeyi......tana bugawa bawai don tsoron
mariya ko tsoron abinda zata iyayi bane.....aah,tana bugawa ne saboda tsoron
fitina. Bata qaunar wata fitinar sam a shekarunta da suka fara turawa,ko a
yanzunma a haka addu'a take Ubangiji ya ganar da mariya......yasa ta fahimci
rayuwa a zahirin yadda take.
"Bab......babbu anni"
"Kin tabbatar?" Ta sake tsareta da tambayar tana
dage girarta duka sama. Kai ta gyada mata a sanyaye,ba kuma don wai tana da
tabbacin ba.
"Idanma baki da tabbacin inaso ki samoshi a duk inda
yake,gina alaqa mukeso ayi bawai a sake rusata da sabuwar matsala ba" Tana
kaiwa nan ta wuce cikin dakin tabar amna da tarin nazarce nazarce cikin
kwanyarta,tsoro da fargaba suna cikata,tana jin kamar wani farinciki yana dab
da barin rayuwarta.
★Tsakanin jiya da
yau gaba daya zazzabinnasa kusan cikin jikinta yayishi,jinyar tasa da komai
nasa ya nadeta ya hanata aiwatar da komai,sallah kawai ke tashinsu. Duk wani
motsi nasa idan ta kalleshi labarinsa ke mata yawo,duk da tanajin akwai ragowar
side da bai gama cika ba,tana tsananin buqatar jin yadda anni ta iya riqon
kafaffen mutum irin fuad ta maidashi cikakken mutum haka ta ruwan sanyi,tanata
jera labaran nasu......tanason banbance shi da ita waye yafi wani fuskantar
qalubale?.
Ta wani
fannin gaba daya ya aza mata nauyinsa,ya narke mata ya zama wani shagwababbe
shagwababbe za'ace?. Wannan narkewar tasa kuma ta fahimci yana sake amfani da
ita ne yana budewa kansa wasu rufaffun qofofi dake cikin lungunan zuciyarta.
Yanayin kallonsa me sanyata tana jin kamar zata narke ne......ko yaya ya riqe
mata hannu sai taji kaman ta mallaki farincikin duniya ne dana lahira,kwana
cikin jikinsa ya zame mata wani abu na musamman ga gangar jikinta dama
zuciyarta,ta yadda komai nauyin baccinta.....muddin ya saketa ko ya matsa daga
jikinta sai nata barcin yayi qaura. Ta fahimci wani abu tattare dashi,yana da
tsananin ibadar da duk riqon da zazzabin yayi masa hakan baya hanashi tashi
sallar dare,hakanan ko meye yakeyi idan time na sallah ya shiga xai ajiye yaje
yayi,koda itace cikin jikinsa duk yadd yake mararin jinsa tare da ita to zai
ajeta gefe sai ya bada farillan nan ya hada da nafilar kafin ko bayan kowacce
sallah.
A hankali
sai taji wani quruciyar data rasa sanadin hawan girma kanta tana dawo mata. Ita
dinma saita sake zama wata sakaltacciya,zuciyarta ta koma baya can sanda take
da gatan ummienta da abbanta.
A
safiyar ranar alhamis dinne ya bude dukka wayoyinsu shi da ita,duk da shi din
taga kaman kwana biyu yana buda wani dan qaramin abu shi ba tab ba shi ba
system ba yana fita outside deck yana zama yayi wayoyin da batasan da waye
yakeyi ba.
Ita ta
fara shiga tayi wankanta a sannan yana salatud dhuha kafin ya kammala. Tasan
muddin ya kammala zaice saisun shiga sunyi wankan nan tare,abinda ta kasa
sabawa har yanzu,saidai idan Allah ya bashi sa'a yayi mata kutse,takanji kamar
ta koma cikin cikinta saboda kunya.
Tana
gaban mirror tana shiryawa yana addu'o'insa,baice mata komai ba harta gama
shirinta cikin Turkish dressing. Budadden wando me kama da Palazzo da rigarsa
data sauko har gwiwa me dogon hannu.
Ta masa
wani irin kyau da ya sanya ya dinga jin tsigar jikinsa na tashi,to amma ba
daman yin komai saboda awa biyu kadai ya rage Lokacin tashinsu. Banda private
jet nema da warhaka suna airport din.
Yana
fara cire kayansa ta nufi qofa zata gudu setting room,taku uku ya cimmata ya
maida qofan ya rufe ya sanya lock,sannan ya koma a nutse yana qarasa fidda
kayan jikinsa. Gefe daya tayi da kanta zuciyarta na bugawa,har yau har kwanan
gobe ta kasa sabawa da wannan kalar abun nashi. Yana ganinta baice komai ba,ya
kammala ya daure qugunsa da towel,bata ankara ba ba kuma zato kawai taji yayi
sama da ita ya fara takawa yana dosar bandaki.
Wutsil
wutsil ta fara da qafafunta tana bashi excuse.
"Na gama shiryawa fa..... Please ka saukeni,zan
jiraka Allah bazan fita ba" Bai kalleta bama sai daya shiga toilet din.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 107
107
"Nasha
gaya miki ai......duk sanda kikayi rushing to bathroom kikayi taking shower
baki jirani ba......sunan wannan wankan FAKE.....Bakisan sunna bane miji da
mata suyi wanka a tare suna kamfata a mazubi guda daya?......bakisan hadis
dinnan ba?" Ya fadi bayan ya zumbulata a bathtub ya dafe hannayensa duka
gaban bathtub din yana zube mata narkakkun idanunsa.
Gefe
tayi da kanta da idanunta da suka cika da qwallar yadda ya sanyata ta jiqe gaba
daya,a tsaiwar da yayi a gabanta tana tsoron towel dinsa ya kwance batasan ya
zatayi ba.
"Mu gama wankan na nuna miki number na Hadith din da
raweeh din" Yana kaiwa nan sai gashi tsundum cikin bathtub din.
"Zakiga takan tsiya" Ya fada qasan ranshi. Shigewa
jikinta yayi sosai shigewa bata wasa ba. Wasu irin abubuwa ya fara mata bayan
ya samu nasarar cire mata komai data shigo toilet din dashi. Fahimtar inda ya
dosa ya sanyata fara doje masa tana barin ya bari.....lokaci zai qure
fa?,saidai cikin qasa da mintuna biyar ya yaudare bakinta da duk wani kuzari
nasa da salon yaudarar nan tashi,tayi luf tana sauke numfashi gami da amsar
saqonninsa da kyau,duk kuwa da yadda zuciyarta ke warning nata.
Shurun da
taji ya kusa sanyata bude idanunta,Allah ya taimaketa batakai gayin hakan ba
zuciyarta ta gaya mata ke ya tsaya yake kallo. Haka dinne,ya zuba mata idanu
yana karantar yadda dafin da ya zuba mata yake bibiyar duk wani jininta da
bugun numfashinta,amma qi fadi irin nata da tsananin jan girma da ajinta ya
hanata zubda makamanta ta fito masa a mutum.....saidai ya shirya maganinta
shima wannan karon,duk da ya samu dukkan wata shaida data tabbatar masa ya bude
wata babbar qofa a zuciyarta da rayuwarta gaba daya,qofar daya tabbatar ba wani
mahaluki daya taba zuwa koda kusa da ita......yayi nasarar bude zuciyarta gaba
daya da wata irin nasara da bai taba kawowa a ransa ba. Saidai ya lura yadda
take da wani irin aji na daban.......haka soyayyarta take ta daban.....
Ya samu aji
yadda yakeso da kamun kai har fiye da yadda yake hasashen za'a samu wajen wata
diya mace,komai nata me ajinne.
"Lokaci yana qurewa......quick" Ya fada yana zare
jikinsa daga ita gami da barinta a yanayin data zurma dukka jikinta da
zuciyarta.
Kasa
motsawa tayi ko kadan,tayi shuru tana jin wani abu yana mata yawo kowanne sashe
na jikinta. Karon farko da taji wani abu me kama da haushi ya tsaya mata a
wuya,da haushi sanda kake expecting wani abu daga gurin wani kuma ya zamana
baka samu komai in return ba.
Kasa
motsawa tayi,yana wankansa hankali kwance yana satar kallonta,yadda tayi relax
cikin ruwan ya masa dadi. Nan kusa yasan zai samu dukkan abinda yake buri da
muradi,ya kammala wankansa tsaf ya daura towel ya nufi qofa yana cewa.
"Hurry up".
Da qyar ta
bude idanunta,idanunta suna cika da hawaye,haka kawai taji zuciyarta tana
karyewa,sai ta dinga jin zafin abun a zuciyarta. Dolenta ko tanaso ko bataso
tasan wanka ya kamata,don bata da tabbacin bai kamata din ba.
Can qasan
ranta taji wani abu me kama da haushinsa yana kamata,don haka koda ta fito ta
samu ya gama shiryawa. Wani irin sassanyan kyau yayi cikin 3pieces suit saqar
kamfanin Hugo Boss dan qasar Germany,rufaffen takalmin qafarsa na kamfanin
berluti ya sake fitar da kimar shigarsa,ya kuma qara fidda ainihin darajar
dukiya da Allah yayi masa.
Kallo
guda dayan data masa kowanne sashe na zuciya da gangar jikinta ya aminta da
tsananin kyan da yayi,ya kuma soma qoqarin hura wutar daya kunna mata a
toilet,sai tayi ta mata don ba'ace ta maza ba,ta danne komai daga ranta ta soma
takowa cikin dakin tana yin kaman bata san da zamanshi ba.
Comb din
da take taje kanshi dashi ya ajiye yan lumshe idanunsa,shan qamshinta yayi masa
dari bisa dari,sai ya sake fidda mata wani kima daban a idanunsa.
Takowa
kadan yayi ya tsaya daga bayanta,yana qare mata kallo,shauqinta yana
fusgarsa,saidai duk da hakan yayi qoqarin controlling kansa yana boye
hannayensa cikin trouser dinsa. So yake ya manna mata taji irin yadda yakeji a
kanta ko yaya ne.
"Sabrrrrrr" Ya kirata da wani irin tone daya kusa
tarwatsa duk wani dauriya nata. Yi tayi kaman bata jishi ba,ya leqa fuskarta ta
gefe sanda take qoqarin goge ruwan sumarta. Wani dadi ne ya kusa sumar
dashi,duk da qoqarin boye masa ruwan sumar nata da takeyi amma tuni shi ya gama
fahimtar inda karatun ya sanya gaba. Lallai tarkonsa yayi kamu......tarkonsa ya
kama kurciya. Yanason tabbatarwa da gaske fushi tayi don ya barta saman
hanya?,don haka ya qara taku biyu gaba zuwa inda take yana kuma sake ambatar sunanta.
"Sabrrrr" Idanunta ta sake lumshewa gami da
budesu,saidai har yanxun dai bata motsa ba bare ta amsa masa.
"My world" Ya sake kiranta yana qara rage tazarar
dake tsananin su har yanxun yana leqen fuskarta.
"Duniyata" Ya fada da wani coolness daidai sanda
ya isa bayanta ya kama qugunta ya riqe yana mannata da jikinsa.
Duk wata
tsiga ta jikinta sai daya tasheta da iya haka kawai,to amma duk da taji haka
hakan baxai sanyata saurin bada kanta ba,don haka ta hada qarfinta duka tana
qoqarin turashi gami da cewa.
"I need to get dressed"
"No....you don't" Ya amsa mata yana juyo da ita
gaba daya suna facing din juna,sannan ya juyata zuwa yana hadata da bango gami
da ajiye mata wani zazzafan kiss.
Ta fahimci
so yake kawai ya birkitata ya sake tafiyanshi kaman daxu,itakam wani irin sanyi
takeji yana ratsa mata qasusuwanta da kyau kaman ana hura mata ac.
"Am cold" Ta fada tana sasssuta muryarta saboda
yadda yake qara kashe mata jiki.
"I'll keep you warm" Ya bata amsa muryarsa can
qasan maqoshinsa,a zafafe ya soma aje mata kisses masu dimauta nutsuwa.
Kamo
hankalinta tayi da qyar tana kauda fuskarta,jikinta nema yake ya fara
shaking,matakin da tasan indai takai ba zata iya qwatar kanta ba.
"Am not wearing anything under this towel" Da
bugaggun idanunsa ya saki murmushi yana dafe bangon da dukka hannayensa
"I know" Ya fadi yana daga girarsa sama. Sosai
taja numfashin daya aike mata da sassanyan turaren nan nasa dake kasheta,yadda
ya sakata a tsakiyar yana baza mata qamshinsa da dumin numfashinsa tana jin
kaman zata sume ne.
"Please" Ta fada da raunanniyar murya. Batason
yaga faduwarta ko lagonta gaba daya,amma ta karanci kamar ya shiryawa hakanne.
"Don't fight it" Ya fada yana qoqarin maida
bakinsa cikin nata.
"Am in towel fa...." Ta fadi tana qarasa narke
masa gaba daya.
"I don't care" Ya fada kaman me rada yana jin
yadda shima ya fara kunnuwa,ya sanya hannunsa yana mayar mata da gashin kanta
daya rufe fuskarta baya gami da saka idanunsa sosai cikin nata kaman bazai
daina kallonta ba,wani irin sassanyan kallo yake mata kaman zai hadiyeta,abinda
ya sanya taji qafafunta kaman zasu watsar da ita.
"Yau zamu fita a muraaka......still Muhammad fuad anata
tunanin hukuncin da za'a yanke a kansa?". Kasa bashi amsa tayi,daidai nan
wayoyinsu suka dauki tsuwwa lokaci guda kaman hadin baki.
" Farouq ne,wallahi nasan farouq ne" Ya fada a
wani jigace. Sosai dariya ta taso mata,amma bata da qarfin yinta,saidai wani
mamaki ya kamata da taga daya daga cikin masu kiran farouq dinne.
Kiran
farouq din ita ya ceceta,sai yaja baya ya zauna yana daga wayar,ita kuma ta
kwashi kayanta ta koma toilet din.
Sanda
ta fito ya gama hada komai,ya bita da kallo kafin ya daga yatsansa yana
karkadawa. Luggage dinta ya sauke,ya birkitata da kyau ya ciro wata oversize
abaya,ya hado da wani Malaysian hijab ya miqa mata.
Bata musa
ba ta karba,zata koma ciki ta sauya ya bake ko ina gami da mata nuni kan ta
shirya a nan. Bata tsaya jan dogon magana ba,tunda ta fahimci makara suke gab
dayi,ta shirya tsaf ya kama igiyan rigar dana hijab din duka ya daure mata
sannan yaja baya yana kallonta.
"Ya salam.....How can i disguise you?" Yayi Maga
nan da gaske yana jin da zai yiwu ya hana kowanne ido kallonta kome wahala zai
iya bin tsarin.
"Oho nima ban sani ba" Ta fada tana tura baki gaba
don da gaske tana jin haushin abinda ya matan,duk da tana qoqarin nuna bata
damu ba.
Dariyarsa
ya danne yasa hannu ya jawota baya yana basarwa.
"Karmu fita ki canza......if not.... I'll be open about
my feelings for you....i won't feel ashamed of anyone...." Idanunta ta
fidda warwaje,a yadda ta shaida rufewar idanunsa akan duk abinda zuciyarsa ta
karkata akai,tasan zai iya aikata komai da komai,tana kuma tsoro da nauyin
hakan. Hancinta yadan matse yana gane tsoronta.
"Don hana hakan faruwa......Handle me
delicately....fine"
"Ya salam" Ta fada tana jin fargabarsa yana
kamata. Hannu ya miqa ya riqe hannunta yana fadin
"Ki barshi,Jordan zai kula da komai da muk....."
Bai qarasa fada ba dumin hannunta ya ratsa sassan jikinsa,sai ya dakata da
maganar yana kai hannunsa goshinta da sauri.
"Ya salam......fever?,when?" Ya fada a rude.
Idonta ta kada kadan,ita ta dauka ma zafin jikin bai fito ba,iya ita kadai
takejinsa a qashinta.
"Bai dade ba......i will be fine" Kai ya girgixa
yana yana azawa kansa laifin,yana ganin kaman maidata ruwa da yayi da sanyata
zubawa kanta ruwa shi ya jawo hakan.
"No.....mu tsaya ki samu relief,zansa farouq yayi
magana da......" Hannunta ta dora da sauri saman nasa hannun.
"I'll manage". Dan jim yayi yana kokwanto kafin
yace.
"Really?" Kai ta gyada masa duk da yadda taji
kanta yana sara mata. Bataso ace duk jama'ar dake can suna jiransa jiran ya
tashi a banza saboda ita kadai,hakan sam baiyi tsari ba,sannan ita kanta bata
qarfafashi yayi abinda ya dace ba.
Yadda
yake riqe da ita kaman zaiyi mata tafiyar da qafafunta ya sanya mata Tsananin
jin kunya,saidai gurin ta sake fahimtar na masoya ne,kowa sabgar gabansa
yakeyi,a haka suka iso private boat din da iya ita dashi kawai zai fitar zuwa
Conrad island su ruski motarsu su wuce airport,don ko Jordan wani boat din
daban ya biyo ba nasu ba.
*MAAMAH*
Kaman wadda
bata da aikinyi haka ta dinga bin diddigin shudewar kowanne awa da minti na
zamansu a gurin da delay din fu'ad na qarasowa gurin. Ba shakka banda idanunsu
ameenatu a wajen ba abinda zai hanata komawa gefe tayi kuka koda na minti
ashirinne,wataqila ta samu sassaucin abinda takeji cikin zuciyarta.
Yau ita
mariya ta wayi gari karyar farautarta ta farauto abinda take da muradi ta
sakashi a gaba tana wasa dashi yadda taga dama?. Yau ita mariya ita ke zaune
tana jiran dakon isowar yaronta?,wata macen bariki ta riqeshi tsahon wasu
kwanaki?,a yau da take jiran qarasowarsa kuma sai time din da taga daman
ganinsa kowa zai ganshi?,ita kuwa idan batayi taba rayuwar mutanen nan biyu ba
ai tayi asarar zuwanta duniya.
Guda
gudan baqinciki haka ta dinga hadiyarsa tana korawa da yawun bakinta,tana sake
tsarawa da shirya yadda zata gigita rayuwarsu duka su biyun idan sun sauka
Nigeria. Tana jin kamar idan ta jira su koma ya mata nisa,don haka ta koma gefe
ta zaro wayarta tana duba wata number tana jin gwara ta shirya komai tun
yanzu,ta yadda komai din zai fara da wuruwuri. Sauran ma'aikatanta dake hannun
yanzu haka dukansu bata da wata damuwa a kansu,tasan akwai babban aiki a kansu
daba wanda ya isa ya furta sunanta da sunan toxarci ko tona asiri.
Tana
qoqarin kira wani kiran ya shigo. Matsanancin mamaki ya kamata ganin sunan
fareeda yana yawo saman screen din,bata tsaya jinkiri ba ta daga wayar tana
kiran sunanta.
"Na'am....ya kike?" Tayi namijin qoqarin tausar
kanta ta karya harshenta ta tambayeta.
"Ina kika shiga fareeda?,bayan kinsan babban aiki muka
tunkara?" Sake hadiye wata guduma da taxo kan harshenta tayi,tasani cewa
banda tana tausar kanta ta samu isa ga dalilin kiran da tuni ta jima da
daddannawa mariya zagi.
"Kowanne aiki ma yazo qarshe......kowacce magana anzo
qarshenta......kowanne al'amari dadinsa da wuyarsa sun qare..... Kedai kawai
turamin date din da zaku iso Nigeria,da airport da zaku sauka,kano ko Lagos ko
abuja". Daga kai tayi tana duban musaddiq dake nesa kadan da ita.
"Musaddiq" Ta kirashi tana sauke wayar,waiwayowa
yayi sannan ya fara takawa a hankali har
ya iso gabanta,a tsume ta danna kan number ta miqa masa wayar.
"Kayi confirming na date din komawarmu da airport din
da zamu sauka ka rubutamin a nan ka tura". Wayar ya karba yana
kalla,number ba suna,hakan yadan saka shakka cikin ransa,amma ta wani sashen
kuma daya tuna kalmar UWA UWA CE sai ya rubuta kaman yadda tace din,ya tura
bayan ya gama kalle numbers din tsaf sannan ya miqa mata yana barin wajen.
Details
din daya rubuta take kalla
"Me fareeda zatayi dashi?" Taji tambayar ta tsargo
mata. Cak ta tsaya tana son laluba amsar amma kuma saita kasa. Wani sashe na
zuciyarta sai taji yadan shiga fargaba kadan,sai kuma daya sashen ya taso ya
danneshi yana gaya mata.
"Fareeda masoyiya ce....wataqila akwai mafitar data
samo mana,zatayi abinda ni na kasa yi wataqila"
(Ni kuwa nace ummm inji me ciwon haqori......ba girin girin
ba tayi mai dai,maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta).
Aje
wannan tunanin tayi tana tureshi gefe,ta kashe wayar tana ajeta da zummar ci
gaba da lissafin sai yaushe zata bar fu'ad din ya qaraso?,sai kuma idanunta
sukayi mata kyakkyawan gani.
A nutse
suke takowa da wani irin qyallin da idan ka kirashi na amarci bakayi laifi ko
kuskurr ba. Kanta yana aje saman kafadarsa wanda tayi hakanne bisa dole saboda
jiri jiri data fara ji. Da farko taqi ganin zasu shiga jama'a ne,amma daga baya
dole ta kwanta din saboda indai batayi hakan ba tana iya faduwa ko ya dagata ya
dauketa in ya tabbatar hakan zata faru. Tsakiyar qirjinta kuma wani abune ya
dunqule mata,tana jin kaman amai ne yake taruwar mata,saidai bata gasgata hakan
ba ganin lafiya qalau take ai,bataci wani abu daya bata mata ciki ba bare tace.
"Na shiga uku......la haula wala quwwata" Maamah
ta fada tana jin yanayinta yana hautsinewa gaba daya.......
"Anya.....anya.....anya?" Ta dinga maimaitawa
cikin zuciyarta tana tsoron furta abinda ke cikin zuciyarta.
"KINYI KUSKUREN ZABOTA" Maganar bokan ta sake
maimaita kanta cikin kwanyarta.
"Bazai faru ba.....saidai ita tayi danasani" Ta
fada tana furxar da iske me qarfi daga hunhunta zuwa bakinta.
_uhmmmmmmmmm_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 108
108
Idanunta ta
dan lumshe kana ta budesu,tana iya hangen maamah dake farko,farouq daga gefanta kadan yanata amsa
waya,anni daga can gaba ita amna. Musaddiq da saddiq ne bata hango ba,ko kuma
yadda amai din yaketa faman mata kai kawo tsakanin cikinta da maqogorone ya
hanata ganinsu oho
"Amai nakeji" Ta fada qasa qasa kanta a
kafadarsa,don ta tabbatar zai iya kufce mata tsaf kafin sukai wajensu. Hannunsa
yasa ya riqe hannayenta sosai,kafin ya sake riqe tafin hannunta da kyau yana
cewa
"Ga can hanyar washroom,zaki iya qarasawa?" Ya
tambaya a tausashe. Kai ta jinjina masa
"Oya.....be fast" Ya fada yana mata riqon da
zataji dadin tafiyan da kyau,duk da ba haka ranshi yaso ba,yaso ace ta bari ya
rage mata wahalar tafiyar kawai.
Murmurshi farouq ya saki,daga inda yake yana kallonsu,duk kuma da
bayajin abinda suke fadi amma yadda yake kaffa kaffa da ita ya tabbatar masa
dude dinsa ya qarasa zarewa......hauka tuburan na soyayya yasan ya
sameshi,baisan kuma ya za'a qare da lamarin kula da gold da diamond ba,lokaci
yayi na daukan sabbin ma'aikata kenan amintattu na kusa kusa dasu.
Ta
bangaren maamah kuwa ta shaqa iya shaqa,wannan karon kasa riqe ashar dinta tayi
sai data furtata,ta furzar da iska tana dan dukan gefanta. Ta yadda duk macen
data taba bariki.masifa ce,abune a jininsu da komai dadewa sai an saida hali. A
nata tunanin sabreen tana sane tayi hakan,tunda ta ganta,tayi ne kawai don kada
su hadu da fu'ad din kai tsaye,tayi ne kawai don ta nesantata dashi,daga qarshe
kuma tayi ne kawai don ta gwada mata tata iyakar.
"Zakiga taki iyakar a sanda kika qare a gidan tabbabbu
mahaukata" Ta fadi a fusace tana qoqarin danne abinda takeji. Tanajin
kaman ta saka hannu aka ta fasa ihu,tana
jin kaman yanzu yanzu ta bude ido taga babu sabreen an shafe babinta daga
tarihin rayuwarsu.....akwai lokaci abinda zuciyarta keta nanata mata kenan. Ta
yarda da hakan,to amma shi lokacin yaushe xaixo?,amsar tambayar da bata santa
ba kenan.
A nutse
ya koma baya yana qare mata kallo bayan ta gama aman tana wanke kyakkyawar
fuskarta da take wani fresh da ita. Ta kammala ta gyara hijab dinta sannan ta
juyo,saidai ba zato ba tsammani ta sameshi tsaye yana qare mata kallo kamar yau
ya fara ganinta.
Qaramar
harara ta watsa masa da fararen idanunta,sai ya daga hannayensa sama alamun
surrender sannan ya hade tafukan hannayensa alamun ban haquri kafin ya sauke
yace.
"Kinci wani abune da yake baki reaction?" Ya
tambaya da yanayi na seriousness. Dan shuru tayi tanason tunawa,saidai kuma iya
saninta ba wani abu da taci din. Kai ta girgixa masa tana tsane hannunta da
towel din daya miqo mata. Taku biyu yayi ya matso gabanta,ya cire hannunsa a
hankali yana taba fuskarta kafin ya xare ya xurashi ta qasan hijabinta yana
tattaba dogon wuyanta. Abinda ya dauke mata numfashinta kenan na wucin gadi,don
bayan jin temperature na jikinta sai daya hada da tsokanota har sai da taja baya
tana ture hannuwansa. Jirin da taji yasa ta tsaiwa tadan dafe kanta,kaman
walqiya yakai gareta tana riqota jikinsa.
"Idan bazai yiwu ba mu wuce Seychelles......ki qara
hutawa a can saimu samesu......xatafi burgeki akan Maldives" Ya qarasa
maganan cikin kulawa. Fararen idanunta ta sake watsa masa. A abinda take gani
cikin idanunsa ba hutawa zai barta tayi ba,saidai ya qara mata lalura ne kawai.
Batasan inane Seychelles ba.......iya Maldives ma ya suka qare ya kaita qasan
ruwa?,ita kuma Seychelles ai qila cikin cikin kada(crocodile)xasuyi rayuwa. Ta
fahimci a son ranshi kowa ya mutu a barsu su rayu su kadai.
"Muna sake makara" Ta fadi a shagwabe kaman xata
narke. Abunda yayi masifar qayatar dashi,har sai da yaja baya yana gwada yadda
tayin. Dariya taso qwace mata amma tayi hanzarin kauda kanta,sai kawai ta dauki
wayarta ta soma takawa zata tafi ta barshi.
"Ganganci ma kenan" Ya fada yana zaburowa ya
daidaita tafiyarshi da tata.
Wannan
karon farouq suka fara taraswa,suns hada ido da farouq din dai ya wani
basar,yana dauko wannan tsohon dabi'an nasa na miskilanci wa mutane ya azawa
fuskarsa.
"To waye ya damu dakai?" Farouq ya fada yana
jifansa da harara,ya maida kallonsa ga sabreen da kunya ta fara mata qawanya.
Tanaso ta zame hannunta ne daga nashi amma yaqi bata damar hakan
"Madam barka da zuwa......inajin xamu iya wucewa ayi
miki screening,minti arbain ya rage lokacin tashin yayi dama" Farouq ya
fada a girmame.
"Izinin wa ka nema da xaka kama yiwa mutane magana da
mata?,if kana da wani important issue da kakeso lallai kayi magana da ita a kai
ba gani ba?,dani zaka fara magana na nema maka izini ai ko?" Fu'ad ya fada
sounding seriously. Dariya ta kama farouq sosai,yaja da baya ya kama kabbara
kafin yace
"Dole ne kam,dole ne na nema izini ai.....don ko bugeni
kayi na fadi ai ba'a shari'a da wanda ba cikin hayyacinsa yake ba......madam
kiyi haquri kinji......wannan zama dashi sai me haquri".
" Na rantse harda Allah farouq kana qarawa kanka da
kanka kwanakin bikinka ne" Fu'ad ya fada da gaske gaske,abinda ya sanya
farouq ya fara shiga taitayinsa kenan. Yasan halinsa,idan har yace abu yasan ta
yadda zai maida abunnan yadda yace din,shi kuwa wannan ruwan madarar soyayyar
da yaga ana aiwatarwa shi a haramta masa wanzuwar tasa ai anyoshi......gwara
yaje ya dandana shima kam.
"Nif bance komai ba.....daga welcoming naku?.....madam
ki qarasa ciki"
"Ba ruwanka......banason kana min magana da mata
fa,kana takurata,banaso kana sata magana.....she's sick".
"Sick?" Farouq ya tambaya,daidai sannan taji
xamanta tsakanin drama din farouq da fu'ad ba nata bane,ta sabule hannunta ta
qarfi ta soma yin gaba tana barinsu.
"Dude......ba sake lahani kayi mata ba ko?,wallahi
wannan karon anni ba zata barka ba". Harara ya wurga masa
"Wai sa'anka ne ni farouq?"
"Inafa.....mutumin da yaje inda ni banje ba?" Murmushi ya saki,yasan da gaske farouq ya
damu dashi da lamarinsu ne gaba daya,kowacce tambaya yana yinta ne don tabbatar
da lafiyar kowannensu.
"Juts a fever" Ya maida masa a taqaice idanunsa
suna kan sabreen data iss gaban maamah ta tsugunna tana gaidata.
"Allah yasa qwallonka ne ya fada a raga......zanso naga
first born na gold runner" Sosai maganar taja hankalin fu'ad,sai ya kasa
cewa farouq komai yadai bishi da kallo. Zuciyarsa bugawa takeyi so fast amma
yanason dakatar da ita. Bayason maganan farouq ta masa tasiri,ya tasirantu da
cewa shine kuma bashidin bane.
Sautin
dariyar maamah a sanda take tsugunne gabanta tana gaidata shi yaja
hankalinta,ta daga kanta a hankali ta kalleta. Qaqqarfan murmushi takeyi da
gaske wanda yafi kama da dariya
"Kin gama naki......ni kuma zanyi nawa" Abinda
tace da ita kenan kawai tana maida kanta ga wayarta.
"Tashi kije yarinya" Hakanan ta samu qwarin gwiwar
aje mata murmushi itama sannan ta yunqura ta miqe tana fadin
"Hasbunallahu wani'imal wakeel,ni'imal maula wa
ni'imannasir". Da kallo maamah ta bita sanda take takawa tana barin wajen.
Ta aje mata shakka sosai cikin ranta,ta sani itadin kuma shaida ce,ba kasafai
murmushin yarinyar yake xama alkhairi ba,so amma koma meye wannan karon ta
shirya kawar da ita me gaba daya idan ta kama ayi hakan.
Amna ce ta
rugo da sassarfarta ta kawo mata runguma,abinda ya kusa sabbaba faduwarsu gaba
daya,Allah ya kawoshi ya sanya hannu ya tareta ta fada hannunsa.
"Ki kula" Ya fada adan dake sannan ya maida
dubansa ga amna.
"Be soft with her amna" Kai ta gyada a sanyaye
kunya tana kamata. Kwanaki ne kadai tayi bata ga adda sabreen din ba,amma sai
taga ta canza mata gaba daya. Wani ajiyayyen kyau na musamman,qamshinta da
komai nata ya zama wani na daban
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 109
109
a nutse
amna ta riqe mata yatsu,duk da yadda ta fahimci fu'ad din kaman yafi so tabar
masa kayansa,to amma itama sabreen ita ta naniqewa,saboda bataso yayi wani abu
daban da zai sanyata jin kunya gaban anni. Tayi imani kuma dukka hankali da
idanun maamah yana a kansu,nunawa ne kawai ba zatayi ba. Abu guda daya daya
tsaye mata a rai,ya gaza barin kwanyarta ta huta duk da yadda takejin jikinta
shine dariyar maamah din. Ta gama karantar kowanne taku da motsi na
matar......ta kuma sake sallamawa al'amarinta daga labarin fu'ad din. Ta
tabbatar ba wata halitta da bazata iya cutarwa ba tunda har ta iya cutar da
mijinta da kuma d'anta. Directly or indirectly tana farautar rayuwar 'ya'yanta
ne ba tare da tasan hakan ba. A ranta taji dole ta qara takatsantsan da ita
fiye da baya,sai taji kaman a baya ma kulawa da kiyayewa al'amuranta da takeyi
kaman tayi sakaci,tabbas inda tasan wacece ita har haka......inda tasan wacece
ita irin sanin da tayi mata a yanzu lallai ba shakka zata kiyaye komai nata
fiye da yadda tayi a baya.
"Hannunki dumi adda.....kaman akwai zazzabi a
jikinki" Amna ta fada cikin kulawa dab da zasu qarasa kusa da anni. Kai ta
girgizawa amna din tana sanya murmushi saman fuskarta
"Ba wani me yawa bane......zai sauka in sha Allah,karki
gayawa anni ki daga hankalinta" Dan jim tayi kaman ba zata amsa ba,don
bataga dalilin da mutum baida lafiya ba kuma sannan yace kada a fadi.
Hannu
anni ta miqa mata sanda take shirin durqusawa ta gaidata.
"Dawo nan ki zauna" Ta fada qasan ranta wasai da
farinciki. Iya yadda taga fu'ad din ya koma a 'yan kwanakin da baya kusa dasu
kadai ya bata tabbacin lallai komai yana tafiya daidai,ba fu'ad kawai
ba.....hatta sabreen din ta canza mata gaba daya. Fatarta wani glowing kawai
takeyi,hakanan idanunta sun qara haske da kuma girma.
Tsananin
kunyar anni takeji kaman zata nutse......ko kusa ko alama yadda takejin nauyin
anni yana kamata batajin koda kusa da haka akan maamah,bata ce kuma ga dalili
ba.
"Sai kuma ka buge da sacemin diya ko?" Anni ta
fada tana duban fu'ad daya gaidata. Karon farko shima kunyar anni ta
kamashi,tattausan murmushin nan nasa da anni ta jima bata gani ba ya subuce
masa,yasa hannunsa ya shafi baqa sidik din sumarsa da kudin da take lasa yayi
jarin mutane da yawa.
Matsawa
amna kadan tayi kusa da anni tana rada mata sabreen din zazzabi takeyi. A nutse
amna ta dubi fu'ad
"Me ya samu ameenatu?" Fararen idanunsa ya sauke
kan fuskar sabreen din sannan ya dubi anni.
"Dan zazzabi ne dazu da zamu fito ya sauko
mata......nace ma muje ta karba magana but ta dage wai zatayi managing"
Kai anni tadan kada kadan.
"Manage da ciwo?......to Allah ya sawwaqe,idan muka
sauka dubai bai tsaya ba sai taga likita,ba kyau zama da ciwo ai"
"Ameen" Ya amsa yana satar kallon sabreen din.
Jinsu kawai takeyi,amma wani sabon amanne suketa kokawa dashi.
"Bani ruwa amna" Ta fada a hankali tana tunanin
idan tasha ruwan zai fada mata. Motsin bakinta kadai ya kalla ya fahimci me
tace,ya matso a hankali bayan ya karbi gorar ruwan hannun jordan dake nesa
kadan dasu,ya bude mata ya tako inda take yana tsugunnawa saman qafafunsa yakai
robar bakinta.
Tsam
maamah ta dauke idanunta tana kullesu gaba daya,qirjinta na sake bugawa sosai
tana jin kaman haki yanason kamata. Zazzabi?.....wanne irin zazzabi bayan ba'a
Nigeria ake ba ballantana ace malaria ce?,wannan tsugonnan bata ruwan......ko
ita da take uwarsa ba zata iya tuna ranar daya tsugunna haka gabanta yana bata
ruwa ba......lallai dole ta batar da yarinyar nan bat daga duniya.
Kai ta
girgiza masa alamun xata iya sannan ta karba da kanta. Kurba uku tayi taji
kaman ya isheta,sai ta miqa masa robar.
"Is okay?" Ya fada yana motsa labbansa a nutse
idanunshi a kanta kaman me tsoron kada ta bace masa. Kai ta gyada a kunyace
tana saka kanta cikin mayafinta,bataso batason wannan kallon,halakata yakeyi
gaba daya.
"Kai Muhammadu" Maamah data gaza jurewa ta qwala
masa kira,tana jin ya kamata ko yaya tayi wani abu da zata shiga lamarin ciwon
don samun report da zai bata daman aiwatar da duk abinda ya dace da gaggawa.
Tsam ya
miqe yana amsa mata,sannan ya fara takawa gabanta sanda farouq ya iso yana gaya
musu lokacin tashinsu yayi.
"Sakamin takalma na......bazan iya durquso ba" Ta
fadi tana qoqarin saisaita fushinta. Baice komai ba ya tsugunna gabanta yana
tura mata takalman,ta fara saka qafafunta a ciki qirjinta a quntace.
"Ita matar taka me ya sameta da ni bani da mutuncin
sanin komai saidai naji daga bakin bare?". Daidai sanda ta gama zura
takalman sai ya zare hannuwansa yana shirin miqewa.
" Zazzabi ne kawai......shima din dazu ne yazo bawai a
kwance take ba".
"Zazzabi?,tana iya cin abinci?" Kai ya gyada mata a nutse don baisan me zaice
mata ba,ita sabreen idan ya sakata sahun masu cin abinci ma ya zalunci
sakamakon da zai gayawa.me bincike.
"Akwai tashin zuciya?" Ta sake tambaya cikin bin
qwaqwafi da son tabbatar da zarginta. Kai ta girgiza mata alamun a'ah.
"Ciwon mara ko ciwon ciki fa?" Ta sake tambaya
tana kafeshi da idanunta. Kansa ya mayar gefe kafin ya dawo da dubansa kanta.
"Ban sani ba maamah.... Duka duka zazzabin na awa daya
ne".
" Eh dama da irin sakacinnan naku sai ciki ya shiga ya
fice abinsa ma baku sani ba......banason ganganci da rayuwa shi yasa nake
tambaya,dama wani aikin ai sai uwa ita data damu da rayuwar 'ya'yanta damuwa ta
haqiqa.......tana yin amai ne?" Tambayarta ta qarshe da yaji yakai
bango,hannuwansa suna zube a aljihun wandonsa sai kawai ya zubewa maamah
kallonsa. Karon farko kenan tun bayan shudewar shekaru ashirin kusan da hudu
rabon daya kalleta tsakiyar qwayar ido irin haka. Komai daya danganceta yaji
yana dawo masa.......gaba daya tambayoyin nan nata basu zama komai ba face suna
sake bude masa wani abu da yake zargi a kanta.
Duk yadda
ake maganar kwarjininsa bata taba yarda da gaske yana da wani irin kebantaccen
kwarjini ba sai yau. Idanunsa sukayi mata wani irin nauyi,sai taji tana
daburcewa.
"To Allah ya kawo sauqi,sai a bincika ai aji meye,ko
tsohuwar malaria ce" Ta fada tana miqewa tsaye,wanda hakan bai sakashi
dauke kallonsa ba a kanta,har sai da yaji muryar farouq
"Dude....." Waiwayawa yayi yana dubansa,sai ya
nuna masa agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa,wannan shine ya ceci maamah
daga irin kallon nasa ya juya yana nufar farouq din.
"Wai......ka jini da yaro?,haka yakewa
mutane?......muje zuwa,na rantse har da Allah muddin abinda nake zargi ya
tabbata ga yarinyar nan bazan taba aminta na hada jini da ita ba......muddin
wani me rai ne a jikinta ni mariyatu bazan bari ya taka duniya ba" Ta fadi
tana cike da fatan ya zamana ma ba abinda take tunani bane.
Amna
najin takunsa a bayansu ta zame hannunta daga na sabreen din ta qara sauri zuwa
gaba ta cimma anni abinta suka jera tare. Matsowa yayi yana daidaita tafiyarta
da tashi,ba zato y dauki hannunsa ya aza saman kafadarta yana jawota zuwa
jikinsa.
"Kinga yadda kike tafiya kuwa?,you need my
support......dont reject it" Ya qarasa fada yana furzar da iska.
"Inajin body temperature dinki kaman yana hawa......you
need medical care........banaso komai ya tabaki duniyata" Ya fadi yana
waiwayawa ya dora mata qwayoyin idanunsa. Nauyin nan dai taji,sai tadan basar
tana dauke kanta gefe
"Zafin kaman na dazu ne,bai wani qaru ba" Ta fadi
saboda batason yace zaa kaita asibiti. Idan tayi ciwo a Maldives ba zata damu
ba......amma ciwo tsakanin makka da madina bata son hakan ta kasance,saboda
qashene da take da burin xuwa a rayuwarta kafin ta koma ga
mahaliccinta.....qasa ce da ta tara tarin shigifar addu'o'i take kuma kuma son
tayi bajakolinsu a nan.....ba zataso wani abu ya kawo.mata tsaiko ba. Tana da
tarin buqatun da batasan adadinsu ba,batasan kuma kwanaki nawa zata shafe kafin
ta gama jerosu ba.
Ba idanun
wanda sukayi masa nauyi,a haka suka jera suna taka steps na jirgin har suka isa
ciki. Suna shiga din matuqin jirgin yayi salute nashi sannna ya bashi hannu
sukayi musabaha ya buqaci magana dashi,wannan ya sanya ta zame jikinta suka
jera da amna suna wucewa ciki don samun seat din zama.
Tuni
maamah ta yiwa kanta mazauni a executive suit,a nata zaton shine guri na qarshe
da yafi kowanne tsari,batasan sam da VIP suit ba,wanda wada dama mazauni ne na
fu'ad din shi kadai,saidai idan yaso wani ya shigo ya zauna.
A
Aminitiy anni tayi zamanta,zaman jirgi ba baqonta bane,amna ma a nan ta zauna
sai sabreen ta zauna kusa da ita suna taba hira abinsu,saidai komai ya tsaye
mata a wuya,hatta ruwan da tasha.
Yana
takowa ta tsakaninsu xai wuce VIP suit zazzafan aman ya taso mata,ta saka hannu
da nufin tareshi ta miqe da saurin don wucewa lavatory.......saidai inaaa,wani
karo da tayi da fu'ad din take aman ya qarasa fitowa ta kuma soma kwararashi
tun daga qirjinsa saman lafiyayyar suit dinsa har saman qafafunsa. Ba wannan
bane damuwarsa.......yadda take kakarin amai duk jikinta yana kyarma shi yafi
daga hankalinta,ya bita da sauri a rude yana fadin.
"Subhanallah......ya salam......sannu.....am
sorry" Kaman zai sake mata kuka. Yadda ya kanainaye abarsa su anni sai
baya suka tsaya suns jera mata sannu tana ci gaba da yunquri kaman zata fidda
kayan cikinta.
Kafin ta
gama kanta ya fara sarawa da wani irin ciwo,zazzabi jikinta kuma ya sake
ninkuwa akan nada.
Shi ya
karbi ruwan daga hannun daya daga cikin crew din ya bata tasha saboda yadda
take haki,ya saka hannu ya dagata suka wuce lavatory.
Da idanu
take binsa kawai sanda yake qoqarin gyara mata jikinta ba tare da ya damu da
qazantar data zuba masa a nasa jikin ba. Idanunta ta lumshe a hankali a kansa
sanyi yana ratsa gabbanta. Ta dauka zaiyi mata fada,ko zai nuna fushi saman
fuskarsa,ko yayita hargagi idan ta kama ya tureta ma,amma sai taga sabanin
hakan. Gaba daya ya bata attention dinsa,tanaji anni na cewa amna ta biyosu ko
xata tayashi da wani abun yace "no need.....zauna kawai".
Wani
irin abu taji yana ratsata a kanshi,ta zuba masa ido sosai sanda yake goge mata
saman qafafunta da takalminta daya dan baci,saita miqa hannu ta zaro napkins
dake ajiye a lavatory din ta tsugunna a gabansa tana daidaita tsahonsu. A nutse
ya dago suka hada idanu,fararen zagayyun idanuwansa sun qara haske wanda suke
sauya launi nan da nan da wani abun ya taba zuciyarsa,sai ta langabe sannan a
nutse ya dora napkin din saman qirjinsa tana cewa.
"Am sorry" Ta furta a hankali. Labbanta yabi da
kallo yana jin suna qara burgeshi,murmushi ya subuce masa wanda ya sake qara
fidda kyansa,hannuwansa duka ya saka ya daga kafadunta suka miqe tsaye,idanunta
yake kalla
"Sorry for what?" Shima ya tambayeta muryarsa can
qasan maqoshi. Idonta ta janye tana nuna qirjinsa da yatsarta,sai shima ya
maida dubansa wajen. Murmushi ya kuma saki,ya kamata yana jinginata da jikin
mirror din gurin,sannan yaja da baya ya soma balle button din suit din
farkon,ya xareta ya ajiyeta a gefe,ya sake balle button din ta biyun itama ya
ajiyeta a gefe,sai ga shirt din cikin ta ukun ta fito fes ba abinda ya tabata.
Idonsa ya sake dagowa ya kalleta sannna ya daga mata kafadunsa gami da watsa
hannuwa alamun ba abinda ya sameshi. Murmushi ta saki itama abinda ya kusa
narkar dashi kenan,fararen jerarrun haqoranta sun fito reras tamkar adon
lu'ulu'u,har qasan ranta taji dadi da dayar rigar bata baci ba,ya sunkuya a
nutse ya zare takalman qafarsa sai socks kawai daya rage,sai ya miqa hannu ya
kama hannuwanta,a hankali yace
"Kinga abinda nake gudu ko?,zazzabin nan ya dawo
sosai".
" Ba matsala......zai"
"Da matsala mana......bakisan yanzun nan sai na rasa
nutsuwata ba saboda wannan zazzabin?" Ya tambayeta da dukka idanuwansa a
kanta suna kuma karanta gaskiyar abinda yake fadi daga qasan zuciyarsa ne. Wani
abu na daban takeji,wai yau ita ake damuwa da ciwonta?,matar da saidai ta damu
da ciwon wasu amma nata ciwon dai damuwar qannenta ne kurum?.
A nutse ya
riqe mata hannu suna takowa har xuwa bakin wani dan box,yasa hannu ya danna ya
budeshi,saiga loafers masu kyau ya ciro ya saka a qafarsa sannan ya kalleta
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 110
110
"Zan iya
daukarki mu qarasa?" Kai ta girgiza masa da sauri,sai ya dauke kai bai
sake cewa komai ba.
Qafafunta
takejin kamar ba zasu iya daukarta ba sanda daya daga cikin crew din ke gyaran
wajen aman haka taja jiki tana komawa gurin ta. Xarginta yana sake qarfi da
kowanne motsi na yarinyar,amma jikinta da zuciyarta sunqi aminta da cewa coki
zai iya kasancewa a jikinta. Ita ta kawo yarinyar rayuwarsa kuma har yanxu bata
manta da fafatawar da akayi dashi kafin ya karbeta ba......to mene haka yayi
sautin sauya masa ra'ayi game da yarinyar idan ba sihiri bane?. Wannan abun
yafi qarfin bariki......ta samu kalar kulawa da damuwar da ko amernatun bata
sameta ba. Har yanzunda take zaune idanunta suna iya gane mata yadda hankalinsa
yayi mugun tashi da aman da takeyi din,baya jin kunyar kowa dake tsaye a
wajen,kamarma ya manta da wanxuwar kowa a wajen saishi da ita kawai....dole ta
lalubo musabbabin ciwon nan da dukka iyawarta,musaddiq ne kawai kuma zatabi ta
kanshi ta samu information din da takeso hankali kwance.
Tayita zuba
idanu ta gansu ta inda su anni ko maamah suke amma sai tsintar kanta tayi a VIP
suit. Ta yita maimaita sunan bayan ganin wajen,wajen yaci sunansa dari bisa
dari,zama rantse da Allah ba cikin jirgi kake ba,don ko windows sai ka danne
wani abu sannan zai yaye maka su. Akwai mini bed da sofas masu tsananin kyau da
taushi a gurin,tamkar kana cikin wani qawataccen madaidaicin parlor maras
tarkace da hayaniya,harda office area da aka yiwa gurin daya ajiye tarkacen
kayan aikinsa kamansu system dinsa da wasu documents nashi.
Gadon
yaso tayi kwanciyarta amma taqi,sai ya ajiyeta saman recliner,ya jawo foot
setter din dake qasanta ya dora mata qafanta akai sannan ya lullubeta da wani
sky blue din blanket sannan ya juya a hankali yana fita a wajen ta wata qaramar
qofa.
Numfashi
taja sosai tana saukewa,tana yawo da qwayar idanunta cikin wajen. Wani
nutsatsen guri ne da yaci sunan VIP suit din,daga ita saishi a wajen,guri ne da
idan kana nan bazakasan meye yake faruwa cikin jirgin bama. Tabbas duniya girma
gareta kuma fadi gareta,sannan ta sake yarda ta sallama kuma rayuwa
mataki!mataki ce. Daga shigarta family din jadda taga abubuwa masu yawan gaske
da idan a baya akace mata akwaisu a duniya hankalinta bazai dauka ba,da gaske
ne kudi ba wasa bane.....arziqi kuma ba qarya bane......kudi nada wani irin
power......suna mallakawa mutum girma da fadin ikon da baisan iyakarsu ba. Wani
lokacin idan ta kalleshi sai ta dinga jin yafi qarfinta nesa ba kusa ba......ya
kuma tserewa ajinta.....wani lokacin saita dinga jin kokwanto da shakkar sake
masa dukka gaba daya.....kada a gaba ya samu dukkan komai ya kuma zame ya barta
tunda tabbas ita ba ajinsa bace,saidai kuma wucewar kowacce daqiqa da second
yana sake bata dukkan wani dalili na soyayyar gaskiya a aikace ba wai a baki
ba. Maida idonta tayi ta rufe tanajin yadda zazzabin ke ratsa qasusuwanta,gefe
guda kuma tana jin irin tababar da akeyi tsakanin bangarorin zuciyarta dukka
akan MUHAMMAD FU'AD JADDA.
Motsinsa
taji kafin taji sautin nutsatstsiyar muryar nan tasa da sautari takan mata
gizo.
"I'd appreciate it if everyone could stay where they
are,am looking for some peace and quite,i need some time to myself.......madam
bata da lafiya" Yayi maganar cikin dakiya da miskilancin nan nasa.
"Okay sir" Crew din data kawo masa abubuwan daya
buqata ta fadi tana juyawa bayan ta ajjiye masa. Idanunsa ya daga ya mayar kan
farouq daya tsayar daga qofa ba tare da ya barshi ya qaraso ba.
"Karkace komai.....wannan saqok ba da crew dinka kawai
kake ba.....ni akewa jirwaye da kaman wanka.....aini kaina yanzu nasan kafi
qarfina.......system zaka bani zan rage wani aiki kafin mu qarasa
dubai......acan zamuyi layover". Hannu ya miqa cikin shariya ya jawota ya
miqa masa yana kafeshi da idanu,dole dariya ta qwacewa farouq ya amsa yana
komawa.
"Wallahi duk kaci bashi saina rama"
"Can maka" Ya fada yana takowa ciki,sai tayi
saurin lumshe idanunta don kada ya kamata tana qare masa kallo. Rigar ta zauna
masa sosai ta fidda muscle dinsa dake boye a rigar,hakanan ta sake haskashi
qwarai,dram dinsa da farouq sai data sakata murmusawa duk da yadda takejin
zazzabin na rarakarta. Shikam yayi sa'a daya samu amini kaman farouq a sanda
yake cikin yanayi na tsanani......ita ta rasa kaman farouq din,ta kuma rasa
abbanta da ummienta,su huda kadai suka rage mata,take taji wata kewarsu tana
kamata.
Tayi
nisa a tunaninta ta jishi cikin jikinta.
"Oya.....get up" Ya fada yana dan dagota. Mug din
hannunsa ta kalla,ita yanzu ba zata iya sawa cikinta komai ba,saita langabe
masa tana girgixa kai.
"Bazan iya sha ba"
"Even a little?" Ya tambayeta tana dage mata
girarsa dake da cikakken eyebrows,kai ta daga masa a hankali tace.
"Zansha idan na huta.....I'm feeling
nauseated" Hannunsa yasa a tausashe
ya shafi gefan fuskarta,sannan ya jawo wani qaramin ottoman sofa ya zauna a
kai.
Haka kawai
ya sakata a gaba,yana kurbar tea din yana qare mata kallo kaman wanda ya samu
mirror,blanket dinta taja zata rufe fuskarta ya saka hannu daya ya riqeshi gam.
"Ki barni mana na kalla......wannan face din kawai nake
kalla naji nutsuwa ta saukarmin" Ya fada a karye kaman wani maraya,har sai
da taji tausayinsa ya tsarga mata.
Hakan bai
isheshi ba,koda ya kammaka sai tsintarsa tayi cikin blanket din,ya haye
recliner din abinsa yana cusa kansa a cikin blanket din
"Wannan ta miki fadi,bari na cike miki space din daya
rage" Ya fada yana shigewa abinsa ya kamota cikin jikinsa sosai.
"Kai....ya salam......your temperature is too
high" Ya fada yana matseta a jikinsa sosai. Ita kanta ta sani,qaruwa kawai
zazzabin yake,sai kawai tayi luf a jikinsa shi kuma yayi mata masauki me kyau.
Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kowanne yana sauraren bugun zuciyar dan
uwansa,suna jin sanda jirgin ya soma motsawa,bayan wasu mintuna kuma ya cira
yana lulawa sararin samaniya dasu.
★a awannin da
sukayi suna tafiya cikin sararin samaniya duka bacci tayi sosai,duk da irin
zazzabin dake a jikinta bai kuma sauka ba. Tafiyar awanni biyar suka sauka a
dubai Abu Dhabi.
Movenpick hotel and apartments nan farouq ya kama musu,5star hotel ne
dake da tsada saboda kusancinsa da burj alkhalifa. Ya zabar musu shi saboda
yafi kusa da American hospital.
Kafin su
qarasa ma tuni yayi booking Dr din da zata dubata,don ya tabbatar fu'ad bazai
yarda mo giyar wake yasha namiji ya taba sabreen ba.
Cikin
mintuna kadan ya kammala dubata,akwai test da taso ayi amma fu'ad din yace suna
kan hanya,awanni kadan zasu wuce madina,a can za'ayi mata general checkup gaba
daya,ta bata kawai taimakon da zazzabin zai sauka.
Ruwa ta saka
mata wanda zai suake zafin zazzabin,ya kuma bata qwarin jiki,wannan ya sabbaba
ba mata wani sabon baccin bayan wanda tayi.
Kwata
kwata hankalinta yaqi kwanciya kaman yadda bataso fu'ad din yace abar test din
ba,zataso taji mene ne?,wanne irin lalura ce wannan tun daga wata uwa duniya
har nan gurin?.
"Wanne irin abune da zai sanya ka hana a gwadata aga
abinda yake damunta?,idan akayi maya treatment da ka fa?" Maamah data kasa
hadiye abinda yake cin ranta ta fada tana duban fu'ad.
Duba daya
anni tayi mata ta maida dubanta ga plate din abincinta da yake dukkaninsu suna
kan dining table. Maganin shege karen maguzawa,ta fahimci duk wata alqibla ta
maamah.......tana kuma karance da dukmotsina,wannan dalilin shi ya sanya duk
sujjadarta idan ta aza goshinta a qasa saita yiwa Allah magiyar ya sanya rabo
ne a jikin sabreen din,wala'alla wannan ya zamewa mariya ishara a rayuwarta.
"Ni banason wannan tangal tangal din da rayuwa,karo na
gaba dole a gwadata asan me yake damunta,ayita zauje da ciwo ba'asan wanne iri
bane?".
"Na alkhairi ne" Shine abinda anni taso
fadi,saidai kuma ta duba cewa da d'anta take magana.....bari ta barta da pain
din rashin sanin taqameme din ciwon sabreen din,sai hasashe sai zargi da zato
da zai hana zuciyarta nutsuwa guri guda.
Shurun da
akayi mata ya sake qonata sosai,taso tayita jan maganan ne amma ba wanda ya
tayata a cikinsu,dole ta qunshe maganarta,daga qarshe ma abincjn qin ciyuwa
mata yayi,saita koma daki ta kasa zama.
"Ko na sakashi ya kawomin ita da xummar zan kula da ita
zuwa safiya?,ta nan wataqila na fahimci komai?" Ta shawarci kanta da
kanta,saidai ita kanta tasan wannan shawarar bame bullewa bace,don bataga ta
inda zai aminta ya bata sabreen ba,mutumin da bai jima da dawo da ita cikinsu
ba.
Wayarta ta
dauka ta djnga laluben da wanda zata zanta,sam sam bataso rabuwarsu da hajja a
irin wannnan lokacin ba bayan muradanta basu kammala cika ba. Number bokanta ta
shiga hasashen inama akwaita?,inama yana riqe waya?,saidai nan ma ba wani
mafita dole Takoma ta zauna tana tunanin zai wahala ta zauna a makka ko!madina
harsu gama kwanakinsu,tanajin zata saka ya sanya a maidata gida ne,idan yaso su
sa taho daga baya,kafin su iso djn kuma ta gama nata shirin......sai fashewar
bomb din💥.
★★ _WASHEGARI_
*_GAMO DA KATAR_*
_Prince muhammad bin abdul'azeez airport (madina)_
A tausashe
yake riqr da tafin hannunta sanda suke saukowa daga cikin jirgin har suka
kammala saukowar. Batasan kallonta yake ba sai daya matsa hannunta,tadan daga
kanta ta dubi idanunsa. Haka kawai takejin wani farinciki yana shigarta duk da
rashin dadin da jikinta da takeji.......farincikin sauka a birnin
madina......birnin da ba birni
kamarsa,wanda yake qunshe da baiwawwaki masu tarin ni'imomi da falala.
Saukarta
a garin kadai ya tuna mata labarin madeena da ummensu tasha basu.
"Gari ne dake da wani irin nutsuwa a cikinsa,kana sauka
zakasan yasha banban da duk wani guri da kuka taba zuwa a duniya".
Ta sake
samun tabbaci yanzu haka,ta kuma sake gamsuwa da hakan dari bisa dari.
" Zuciyata tanata rayamin baby zaki haifomin
sabrrrrr......ki daure ki cikamin wannan mafarkin nawa......ni kuma zan fansar
miki da ko mene na mallaka a rayuwata" Ya qarasa maganar yana kallon
gabansa sanda suke dab da isa arrival hall. Idonta ta zare a kansa,ta jima
bataga wani mutum me jarabar son yara ba irinsa,batasan me zata ce masa ba,don
haka ta zabi yin shuru.
"Zaki bani baby my world?" Ya sake tambaya yana
dan matsa hannunta kadan na tare daya kalleta ba. Shuru ta sake yi sai shima
bai qara tambaya ba har suka qarasa gurin.
Hannu
taga yadan daga,saita maida dubanta ta gurin. Saddiq ya hango,sanye da baqar
jallabiyya ta maza da baqin hiram. Quruciyarsa da kyansan nan da suka gada daga
gurin anni ya sake fita sosai.
Kaman
giftawar walqiya,kaman kuma cikin majigi idanunta ya subuce zuwa gefansa. Farar
matashiya ce,sanye da baqar abaya itama,hannunta dauke da welcome board dake
dauke da sunan ADDA SABREEN AHMAD. Ta kasa ganin fuskar matashiyar don ta kare
fuskartata da board din. Jinin jikinta taji ya harba da gaske da wani irin
gudu,saita soma leqawa ta hagu da dama tanason ta tabbatar abinda take zargi ne
ko kuwa kawai hasashe ne irin na zuciya?.
Ta leqa
ta sake leqawa amma bataga fuskar ba,sai kawai ta maida dubanta ga fu'ad don ta
tambayeshi yana ganin abinda take gani kuwa?. Gani tayi hankalinsa baya
wajen,don haka ta sake maida dubanta gurin,saidai kuma a yanzu alluna uku take
gani maimakon daya,kuma kowanne dauke da sunanta,hakanan kowanne me riqe dashi
ba'a iya ganin fuskarta.
Cak ta
tsaya tana qare musu kallo,tana jin bugun zuciyarta yana qaruwa. Bataso ya
zamanto gizo idanunta suke mata,ta laluba kuma ya zamana ba abinda take muradi
ba,bataso ta saka rai akan abinda daga qarshe zai zamanto ba haka yake ba,ta
daga yatsunta tana sake irga allon daya bayan daya,a hankali ta samu bakinta da
furta.
"Huda.....nadra.....haneefa" Murmushi me sauti ya
subuce masa ganin yadda ta fadi sunansu a jere a yadda suke. Sautin murmushinsa
ya tabbatar mata yana ankare da komai,ya latsa wayarsa ya aike saqo a gaggauce
ga saddiq wani irin ruhin soyayya da 'yan uwantaka yana ratsashi. Yaso musaddiq
tamkar haka a duniya......a sanda ya tabbatar bashi da wani gata daya rage masa
saishi daya......ashe akwai wata halitta daban a gefe dake tsananin kulawa da
rayuka har guda uku a matsayinta na diya mace?.
Daya
bayan daya suka sauke board din,su dinne.....huda nadra da haneefa......sune
amma fuskokinsu sun canza daga su hudan data sani watannin baya sun koma wasu
mutane na daban da kamanninsu ke nuna zallar jin dadi nutsuwa da kwanciyar
hankali.
Jikinta
duka ya dauki rawa,fuskarta ta gauraya da kalolin emotions har guda biyu,dariya
da kuma kuka,ta soma qoqarin kwasa da gudu don ta cimmasu,tana ganin kamar
tafiya tayi kadan ta kaita garesu. Caraf yayi ya riqe hannunta.
"Bi a hankali......mrs muhammad jadda......bani da
tabbacin babu baby ne a jikin ki,still baki da cikakken lafiya......muje na
rakaki.....su dinne,zaki cimmasu cikin salama da nutsuwa".
" Kai....kain...." Bakinta yana rawa tanason
tambaya da samun tabbaci.
"Shshssh..... Muje" Ya fada yana mata nuni da
lumsassun idanunsa.
_Allah sarki....dan uwa rabin jiki_🥹
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 111
111
Tun kafin ta
qarasa garesu hawaye sun gama wanke mata fuskarta,taqi dauke idanunta daga
kansu koda na second guda,tana ganin kamar idan tayi hakan zasu bace mata kafin
ta sake bude idanun nata.
Suma basu
iya jira ta qaraso garesu ba,da wani irin sauri suka tunkarota kowa yana
qoqarin fara isa wajenta. Gudun nan daya hanata batasan ta yishi ba sai da ta
jita cikin jikinsu,dukkaninsu su ukun qoqari take a lokaci guda ta samu damar
rungume kowa. Bata fahimci kuka sukeyi ba sai da suka zube duka a jikinta suka
sulale qasa duka har ita din. Sheshsheqa sosai sukeyi kowanne da sunanta a
bakinsa. Wani irin sautin kuka ne me taba zukata,kukan dake cike da kewa da
qaunar juna irin wadda asalin soyayyar 'yan uwantaka take bayarwa. Ko fu'ad a
wannan karon baya yaja ya tsaya yana rungume da hannayensa,kallonsu kawai
yakeyi baiyi yunqurin yi ko cewa komai ba,saboda yasan wanne irin ciwo ne
zukata sukeji a irin wannan lokacin.
Ta rasa
sunan wa zata fara ambata?,sai kuma ta saka hannu ta fara dago haneefa auta.
Fuskar
autan ta sake cika sosai,duk wani kamanninta da ita sun sake bayyana,tayi wani
irin haske wanda da alama shine asalin color din fatarta.
"Auta......auta kece?" Ta fada wani kukan
farinciki yana sake tsinke mata. Kai haneefa ta gyada tana dariya da maqalallun
hawaye akan fuskarta.
"Nice adda......adda kin qara girma.....adda kin zama
balarabiya" Haneefa ta fadi tana shafa hannun sabreen dake riqe da nata
hannun. Qaramin dariya daya taho da hawaye ta saki tana maida kallonta ga huda.
Hudanta ta
sake zama budurwa sosai,abun abun mamaki kaman wadanda aka saka famfo ake
hurasu. Kamarsu itama ya sake fita,duk da baikai kamannin dake fuskar haneefa
ba.
"Adda......ban zaci zamu sake ganinki da wuri ba"
"Nima haka adda......" Muryar nadra ta sanyata
waiwayawa. Itama nadra din kaman sauran,saidai nata kamannin da ummenta ne suka
fito sak kaman an tsaga kara,abinda ya raunata zuciyar sabreen sosai ta miqawa
nadra hannu. Ba musu ta dora nata hannun akan na sabreen din suna duban juna.
"Nadra?....ya akayi kukayi irin wannan girman?,me kuke
ci?"
"Komai me kyau adda.....komai mai dadi hamma ya tanadar
mana,komai da zamuyi amfani dashi muci ko musha yasha banban dana dubban mutane
adda"
"Hamma?" Ta tambaya a mamakance,sai huda ta gyada
mata kai tana duban fu'ad dake nesa kadan dasu. Kanta ta daga ta waiwaya zuwa
inda yake tsayen,zuwa sannan tare da saddiq suke tsaye,batasan maganar da
sukeyi ba amma taga yana miqawa saddiq din wani card.
"Hammanki adda" Haneefa ta bata tabbaci. Maganan
data sanyata dauke dubanta daga kanshi zuwa kansu. Kai huda ta gyada mata still
tana qara tabbatar mata.
"Ya Allahu ya salamu.....when......and how?" Ta
tambayi kanta. Duka yaushe yayi hakan?,duka yaushe yasan da yaran?,yaushe yasan
inda suke?,yaushe ya shirya komai?. Ko yawan using da wannan na'urar da yake
sanda suna muraaka suit yana da alaqa da shirinsa akan haka?,take taji amsar
tambayar tazo mata.
Wani
kakkaifan abu a kansa taji ya huda zuciyarta,ta lumshe idanunta tana jin yadda
yake kwarara cikin kowanne sashe na zuciyarta dama gangar jikinta.
"Muhammad fu'ad jadda" Sunansa kadai ya dinga amsa
kuwa cikin kunnuwanta.
"Amma kun saba alqawari.....kun karya yarjejeniya
sister" Muryar nan tasa dake cike da tarin nutsuwa ta ratsa rufaffun
idanunta,sanda ta budesu sautin murmushin huda ya sauka a kunnenta.
"Wallahi hamma itace.....adda ne ta fara sakamu
kuka" Ta amsa masa tana miqewa gami da riqe dariyarta. Idanunta ta bude
fes saita samu tattausan tafin hannunsa gaban fuskarta yana miqo mata shi.
"Next time sai naci tararku idan kuka sake sanyamin
mata kuka......get up my world" Ya fada yana duqawa kadan yasa hannuwansa
yana daga kafadarta.
Wani
sanyi taji yana ratsa sannan jikinta,ta ware idonta a kansa sanda yake miqar da
ita tsaye. Fuskarsa fresh kuma normal kaman baiyi wani abu ba,ta laluba
labbanta zuciyarta dama kwanyarta gaba daya,tanason zaqulo kalaman da suka dace
tace dashi wani abu amma ta rasa.
Gyara
mata veil dinta yakeyi yana sake rufe mata jikinta gami da jan hannun
abayarnata
"Wannan kallon.......bakison zuciyata ta huta
hala?" Ya tambayeta yana balle mata button guda daya daya zame na
abayarta. Idanunta sunyi raurau sosai sun cika da hawaye,ko sau daya so take ya
kalleta......koda na second daya ne wataqila zaifi fahimtar girma da martabar
abinda yayi mata,don ta tabbatar kalaman baki sunyi qanqanta su isar da abinda
takeson isarwar,saidai yaqi ya kalletan har sai daya gama sannan ya zube mata
fararen idanunsa. Wani abune da yake yawan bata mamaki,a iya mazan data taba
kallon idanunsu ba zata iya tuna mutum daya da idanunshi suke da haske haka
ba......koda kwatankwacin nasa kuwa.
"Akwai wani abun?" Ya sake tambayarta yana
kallonta. Labbanta ta motsa amma sai ya saka yatsunsa biyu ya b'ame mata su.
"No need......bana son godiyarki ko kadan......it's my
duty......aikina ne na baki duk wani abu da zai baki farinciki......haqqina ne
samar miki da duk wani abu da zai baki nutsuwar zuciya data gangar
jiki......aikina ne.....dole na ne na matso miki da dukka farincikinki kusa
dake.....har yanzu jikinki da dumi,mu qarasa" Ya fadi yana riqe hannunta
cikin nasa sannan ya kira haneefa ya saka mata ita a gefenta,ya kira huda ya
sakata a daya gefen,yaja nadra baya sukabisu a baya yana mata magana qasa qasa
wadda sabreen batasan me yake tambayarta ba.
Tuni ta
kame a owners corner,tanason ta sake tabbatar da duk wani motsi da xai gayawa
kowa ita din isashiya ce. A bude tasa abar mata qofofin lafiyayyar motar,tana
shaqar iska d'ai d'ai tana ratsata,tana jin qofofin abubuwan daya kamata ta
aiwatar kaman suna bude mata.
Tana jin
tsaiwar anni a daura da ita,ita da amna da musaddiq da take jira su samu xama
sosai tayi masa iyakoki da lamuran annin. Batason duk wani abu da zai ci gaba
da sanya kusanci tsakaninsa da yarinyar can me kama da uwarta,zata iya kowanne
kalar hauka xata kuma iya cinye komai ta daure har ta gama da matsalar amma
banda alaqa tsakaninsa da amna din,don yanzun haka sautin dariyarsa da yarinyar
tana jinsa har tsakiyar kanta.
"Musaddiq" Ta kirayeshi tana leqo fuskarta daga
motar. Sam yana mancewa da wani warning na maamah din,kiranta ya dawo dashi
cikin hayyacinsa,ya amsa mata a nutse sannan ya dubi anni. Da ido ta masa
alaman yaje ya amsa kiran mamarshi
"Ina zuwa" Ya fadi qasa qasa yana takawa zuwa inda
take.
Kallo take
qare masa tun daga sama har qasa,ta kowanne fanni abun babu sauqi ne wai?,wai
me yasa sabbin matsaloli suke sake kunno mata kai?.
"Anya ka samu isashen ilimin sanin darajar uwa
kuwa?.....a ina ka taba ganin mutum yabar wajibinsa ya dauki mustahabbi?"
Kasa cewa komai yayi,bayason ya fadi wani abu da zata tunzura taci gaba da
zazzago maganganun da ya tabbatar anni tana ji,don muryarta a bude take magana
ko wanda ke nesa zai iya jin sautinta,kasancewar garin gari ne maras hayaniya
sam sam,albarkacin wanda yake kwance cikinta.
"To tunda nayi maka a daki bakaji ba......bari nayi
maka a gaban kowa da kowa......ni mariya ahmad.......indai nice nayi cikinka
watanni tara na haifeka.....na haramta maka zuri'ar hamza kibiya da ameenatu
haramci na har abada.....idan ka sake nuna wani abu makamancin haka kuma ban
yafe maka ba".
Idanu
fu'ad dake qarasowa wajen ya runtse maganar tana hudashi,duk wani motsi nata
qara bashi yaqini yake a kanta,tana sake haska mishi kanta da kanta tana fadada
zargin da xai iya cewa qiris ya kusa zama tabbaci.
".......kaji na gay......" Ta dora da maganar da
takeyi saidai kuma kasa qarasawa tayi sakamakon qwarewa da tayi da yawun
bakinta.
Bawai tayi
qwarewar Allah da annabi bane.....ba kuma ta qware bane haka siddan,abinda
idanunta suka hasko mata shi ya janyo mata qwarewar ya kuma zarce mata da wani
matsanancin tari daya sanya idanunta firfitowa waje.
Fu'ad
yana takewa sabreen da qannenta baya kaman wani dan aikinsu......mutumin da shi
kansa garada ne masu yawa suke gadinsa....... Saukar idanunta akansu huda ya
qarasa dauke duk wata wuta ta jikinta na wasu sakanni. Ta ina yaran suka
bullo?,daga wacce shiyya ko jaha?,ko duk cikin zallar iya barikinne na
yarinyar?. To waima da kudin ubanwa sukazo madeena?,waye ya dauki nauyinsu?.
Indai amsar dukanta FU'AD ne to lallai ta zaunar dashi ta karanta masa komai
kenan a kanta?. Indai haka ne ai la shakka zataga wani sauyi ko alamu saman
fuskarsa,to amma bataga komai ba.....wai ya abun yake?.
Tarin
tulin tambayoyin da suka hana tarin lafawa da wuri,har sai da taji maqogoronta
ya fara zafi,ta karbi ruwan da musaddiq yake bata ta kurba still idanunta akan
yaran. A yadda suka rabu dasu rabuwar qarshe......bata nuna musu duk wani plan
nata ba,tayi qoqarim basu gata da kulawa,a yanzun tana zaton zasu iso gurinta
cikin fara'a da girmamawa ne kaman yadda yake a baya,saidai yanzun ga tarin
mamakinta sun gaidata ne a tare......irin gaisuwar da zaka yiwa baquwar fuskar
da baka taba ganinta ba. Bata iya amsa musu ba saboda mamakin da ya ciyota,ta
bisu da idanu sanda suke motsawa gaba wajen anni suna gaidata.
"Ma sha Allah......aah 'yammata,lafiya alhmdlh,da alama
kun rigamu sauke taku umrar.....nasan halin saddiqu da kyau,bazai bari ku zauna
ba dama.......ga photocopy din takwara ameenatu......ma sha Allah,Allah ya yiwa
rayuwa albarka" Dukka muryoyin anni suka dinga dukan kunnenta sanda suke
haraman barin wajen bayan rarraba motar da kowa zai hau.
Madeena
kusan ta zame masa muhalli,don haka yana da gidaje nasa na qashin kansa kyawawa
har guda biyu. Ba wani gari a duniya da yake jin nutsuwar da ko jaririn dake
cikin mahaifiyarsa baikaishi samunta ba irin madeena,ta biyunta makka,to amma
yanzun saboda yana buqatar sabreen din ta huta sosai,sai yasa aka kama musu
amenities a intercontinental Darr alhijra,saboda yafi kusa da masjid annabawi.
Duk
yadda yaso ya kasance a motarsu sabreen din amma sai ya dage mata qafa,don
wataqila akwai maganganu da suka shafesu da zasuyi a tsakaninsu daya kasance
sirrinsu ne,don haka ya tura saddiq motar maamah su tafi tare,amna da anni,shi
kuma ya karbi key da kansa ya kira musaddiq
"Shiga muje" Ya fada yana shiga mazaunin driver ya
tayar da motar suna fita a nutse. Bayajin xai iya barin wadannan sakannin su
wuce maganan dake ransa yana cizonsa,shi yasa da zafi zafi ya nemi kebewa da
musaddiq din.
Shuru ya
ratsa tsakaninsu har zuwa sanda suka dauki hanyar intercontinental,muryar
hamman nasa ta masa saukar ba zata.
"Musaddiq"
"Na'am hamma" Ya amsa a sanyaye har yanzu muryar
maamah tana bugun tunaninsa.
"Kanason amna?" Tambayar da bai bata tsammani ba
ta fita daga bakin hamman nasa. Har wani firgicewa yaji yayi,yaji kaman baiji
abinda fu'ad ya fada daidai ba.
"Nn...na'am hamma?"
"Nace kana son amna?" Ya sake tambayarsa idanunsa
nakan titi yana sauraren amsarsa.
"Hamma.....amma hamma"
"Ba sunana na tambayeka ko nace ka maimaita
ba......kanason amna?,eh ko a'ah?,banason wani sharhi"
"Ina sonta hamma" Ya amsa masa yana yin qasa da
kansa a sanyaye. Kai kawai fu'ad ya jijjiga,bai kuma sake cewa dashi komai
ba,yayin da yabar musaddiq din da saqe saqe a ransa masu yawa,ya matsu yaji
hamman nasa ya sake cewa wani abu amma bai sake fadi ba,kuma tunda har mintuna
sukayi nisa yasan ba lallai ya furta komai din,don haka yayi qarfin hali ya
motsa.
"Hamma.....maamah ta fadi cewa bataso ta kuma
r......." Wani kallo ya waiwaya ya watso masa duk da tuqi yakeyi sannan ya
maida dubansa ga titi.
"Kayi magana akan abinda kowa yakeso da wanda bayaso
amma banda maamah......bana buqatar komai nata ciki harda ra'ayinta da meye
bataso da wanda takeso......abinda na sani kawai shine na sauke haqqinta na ci
sha sutura muhalli da lafiyarta......sai biyayya akan abubuwan da basu sabawa
mahalicci da kuma addini na ba.....baya ga wadannan komai a kanmu nata ba dole
bane". Yadda hammansa yayi magana ya sanyayar masa da jiki,ya sani gaskiya
ya fada....kuma koshi yana yaba masa yadda yake qoqarin bata girmanta.
Sun
rigasu isa intercontinental din,don sanda fu'ad ke parking a parking lot na
gurin ga motocinsu nan ajjiye,ya tsaida motar yace da musaddiq.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 112
112
"Ka
shiga ciki ina zuwa......ka fada mata zan shigo yanzu.....but idan naga tana
kuka zan nesantata da kowa har sai ta daina". Har zuciyarsa abun ya
qawatar da musaddiq,ya amsa masa a girmame yana bude motar sannan ya fice.
Da kallo
fu'ad ya bishi har ya bacewa ganinsa,iska me zafi ya furzar daga bakinsa,ya
sake yarda har yanzun shine garkuwar musaddiq,zai kuma ci gaba da zame masa
garkuwa har sai ya tabbatar da cikar kamalar farincikinsa.
Hannu ya
dora saman center console na motar ya dauki wayarsa,ya gyara zaman kujerarsa
sosai yayi relaxing sannan ya soma lalubar number wayar abbansu wato alhj hamza
kibiya.
Bisa
jagorancin saddiq suka wuce amenity din,sannan ya nunawa kowa dakinsa. Amna dai
da anni,nashi dakin shida musaddiq.....dakinsu huda suma su uku,sai dakin boss
din nasu da duniyarshi......farouq ne ya zama shi kadai daban. Sabreen murmushi
ta saki sanda suke bude dakinsu huda da sukace tazo taga wani abu,tana jin
farouq yana balbalin masifa.
"Shi tuzuru dama abun rainawa ne......shi yasa aka
wareni kaman wani barawo......duk wanda yayimin abu saina rama.....Allah ya
kaimu lokaci,sati ukun ai kamar yau ne".
Idanu
sabreen ta firfitar waje tana kallon matar dake zaune saman abun
sallah.....momma bahijja ce cikin kamilalliyar shiga. Idonta ta murxa tana jin
mafarki takeyi da gaske
"Qaraso sabreena.....mommmanki ce". Da gudu ta
qarasa jikinta ta zube tana sakin wani irin hautsinannen kuka
"Momma duk kun gama birkitani.....kun gama bani
mamaki,momma dama zakuzo?".
"Ko niyya babu me ita,duka aikin mijinki ne".
Kalmar ta sauka sosai a zuciyarta,ta ruqunqume momma sosai tana hangen kamilar
fuskar nan tasa. Wanne irin mutum ne shi me abun mamaki haka?,wanne irin mutum
ne shi wanda ya iya nemowa abokin rayuwarsa maqurar farinciki?.
"Zazzabi kike haka sabreena?" Momma ta fada tana
dagata a jikinta.
"Shine momma.....zai sauka,don Allah kada ki bari
hamman nan yaji,tsaf zai sakani kwanciya asibiti"
"Kinsha magani?" Ta tambayeta cikin kulawa,kai ta
gyada mata,duk da tasan ba wani magani da tasha tun a dubai,ta maida kanta ta
kwantar saman qafafunta tana cewa.
"Ya akayi komai ya faru momma?,bani labari?" Ta
furta tana riqr hannun haneefa da kyau cikin nata.
Doguwar
waya ce da sai da suka shafe aqalla awa biyu ba kadan suna tattaunawa da alhaj
hamza din,daga qarshe abban yayi shuru kafin ya sake magana.
"Na fahimceka muhammadu.......kuma na gamsu da
bayananka da hujjojinka........amma me zai hana ka jira na qaraso nan din ko ku
ku dawo gida?". Kai ya girgiza
" Kayi haquri abba.....bawai inason inyita musu dakai
bane.... Amma karka manta annabi ya fada mana,ba'a jinkirta aikin alkhairi
gaggauta yinsa ake"
"Na sani muhammadu
banaso ka kirawa kanka matsala ne gaka kai daya" Murmushi ya sake
saki yana yin gefe da kansa.
"Abba...ka manta muhammadu nake?....ka manta wannan me
babban sunan?" Qaramin murmushi ya qwacewa Alhaji hamzan
"Ban manta ba kam.....jarumin gold daga qasar yarbawa
da inyamurai" Wannan karon shi kansa fu'ad saida murmushinsa ya fadada
"Ka samu alhaj muhyidden,yana alranuna unguwar da
gidanka yake......Allah yasa haka shi yafi alkhairi......amma kabi komai a
hankali,idan akazo batun iyaye bin komai ake a sannu"
"In sha Allah abba.....na gode" Ya amsa masa yana
jin wani farinciki yana ratsashi sukayi sallama.
Zaune
kawai abban yayi da waya a hannunsa. Wanne irin yaro ne wannan Allah ya baiwa
mariya amma har yanxu batasan baiwar da Allah yayi mata ba?,tabbas ahmadu ya
dace da kalar yaron da yake zamewa mutum sadaqatul jariya bayan
ranshi.....Allah ya gama masa komai......baisan wanne irin qauna yaron yake
gwada musu ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana tashi
"Ubangiji yasa albarka albarkacin wajen......yasa kuma
silar zuwan komai qarshe kenan a tsakaninsu".
Kansa
tsaye ya wuce nashi dakin,so samu ace tana tare dashi a wannan lokacin.....to
amma kuma yasan yanzu dole ne ya mata uzuri ya daga mata qafa,ya kuma bata dama
sosai na ganawa da 'yan uwanta,don haka sai kawai ya rage kayan jikinsa ya
shiga wanka. Tsaf ya shirya cikin jallabiyya,sai gashi ya juye sak balaraben
madina. Wayarsa ya dauka ya kira saddiq bai sameshi ba,don haka ya kira
musaddiq. Bugu daya ya dauka cikin
girmamawa.
"Ka fadiwa saddiq ya shirya nan da thirty minutes mu
wuce masjid.....banason wannan ragoncin naku"
"In sha Allah hamma......amma maamah tacemin idan ka
shigo ka shiga tana son magana da kai". Agogo ya kalla,indai zai bata
minti ashirin sauran lokacin zai ishesu tafiya,ya amsa masa da okay yana katse
wayar.
Ya sani
babu wani lokaci da kiranta ya zama na alkhairi,babu wani lokaci da kiranta ya
zama me dadi,shi yasa ya yanke koma meye gwara yaje yanzu ya jishi ya tattara
damuwarsa ya tafi masallacin ma'aiki da ita ya juyeta a can. Kafin ya fita ya
duba number da abba ya tura masa,yayi kiran alhj muhyidden ya nema inda zasu
hadu.
A girmame
yace zai sameshi a masaukinsa,hakan ya yuwa fu'ad nauyi,don babba ubane a
wajensa,don haka duk wanda ya jibanceshi yana masa kallon uba shima.
"Ka zabar mana guri,zan iskeka in sha Allah ko a ina
ne". Nutsuwar fu'ad da hankalinsa ba wani baqon abu bane a wajensa,don
haka cikin masallacin yace su hadu bayan sallah isha'i,ya duba lokaci sai ya
yanke daga sallar la'asar din yayi zamansa har isha'i acan yayi jiransa,don
yana da tarin addu'o'i daman da zaiyi.
"In sha Allah zan zauna ta babus salam". Ya fadawa
alhj muhyidden.
A nutse ya
dauki casbaharsa,ya sake feshi jikinsa da lallausan turarensa sannan ya saka
wasu loafers masu taushi marasa nauyi ya fice a dakin.
Ita daya
cikin dakin tunani kaman zai fasa kwanyarta,tana zaune daga gefan gadon,madarar
almara'i ce a gabanta tana tsiyaya da kadan da kadan tana sha,don batajin
abinci xai wuce ta cikinta. Kwata kwata jinta take kaman akan qaya,lissafin
kwanakin da zasuyi a qasar takejin sun mata yawa sun mata kuma nisan da kamar
ba zata iya jira ba.
Ganin
yaran ya sake gigita tunaninta,tun sanda ta samu ta sabule yaran daga hannunta
dama tana tare dasu?,ko wani gurin ta kaisu?,ya akayi suka kasance a nan
gurin?.
Tunaninta
ya katse sanda akayi knocking qofar dakin,idanunta ta daga ta kalli qofar,tasan
ba kowa bane sai fu'ad din,murya a cunkushe tace
"Shigo" Qofar ya murda ya tura ya shigo,don bayan
fitar musaddiq tace yabar masa qofar a bude.
Kallo
daya yayi mata yasan dai kaman kullum ne,kaman yadda aka saba wani abu da ya
shafi buqatar qashin kanta ya sanya ta kirashi,saman dressing mirror ya
qaraso,ya dosana kadan ya zauna samansa yana dubanta.
"Gani" Ya fada a nutse yana shirya jin komai da
zai fita a bakinta.
"Muhammadu......wai nikam duniya na haifawa kai
ne?,wanne irin wauta da hauka kakewa rayuwarka?,sam ba ruwanka da tattala
rayuwarka?,ba ruwanka da sanin ya kamata?,ka zama baitul mali ka maida kanka
bayin wasu?". Dukka maganganunta tana yinsu ne cikin fada zafi da kuma
daga murya. A nutse ya lumshe idanunsa sannan ya budesu.
"Yanzun me akayi?,me ya faru?" Ya tambayeta a
nutse yana qare mata kallo. Bayason ranshi ya baci ko kadan,yanayin abubuwan
maamah suna neman fara ta'azzara,shi daya yasan me ya adana a zuciyarsa daya
shafeta,sirrika masu nauyi da tsanani wanda ita kanta batasan da hakan ba.
Ido itama
ta zuba masa,saidai nauyin nasa idanun yafi nata,dole ta janye idanun nata.
Tanajin zallar rainin hankali da wayo a al'amarinsa......tanajin wani irin ciwo
da yadda ya gagara zuwa hannunta tamkar ba ita ta haifeshi ba.
"Tuni na dade da sanin ni din marainiyar wayonka
ne........wadannan yaran daka debo meye alaqarka dasu da har ka fara barnatar
da dukiyarka a kansu?" Ta tambayeshi a zafafe. Idonsa ya dauke yana
qoqarin jawo sabuwar iska zuwa hunhunsa,al'amarin maamah yana daure masa kai
maqura......tana yin abubuwa da zummar ba wanda yasan kalarta ta badini a nata
hangen?.
"Maamah......nayi tunanin kece me bawa wani labarin
alaqar dake tsakanina dasu ko?,a wajenki na fara sanin dacewar kulawa da qannen
matarka,na dauka idan nayi hakan nima wani abune me kyau nayi?" Yadda ya
amsa matan ya mata wata bulala data ratsata matuqa,shuru ya gifta tsakaninsu na
wani lokaci,wani sashe na zuciyarta yana gargadarta
"Ki kula da dukka amsar da zaki bashi.....akwai.magana
cikin maganganunsa". Abinda wani sashen yake nanata mata kenan.
" Muhammadu.....ka saurara da kyau ka jini,qannen
matarka ko wani abu makamancin haka ba damuwata bane......ba ruwana da alaqarka
dasu,bana buqatar wata hidima tsakaninka dasu,wannan maganar da gaske nake gaya
maka ita,tunda kai ka zama abinda ka zama,bazan sanya ido mata su sakamin yaro
a tsakiya sai yadda sukaga damar yi dashi ba......bazan lamunta ba,tun wuri ka
saki dui wata hidima tasu,banaso na sake ji ko na sake gani muddin kana neman
albarka daga wajena". Wata qaramar dariya ta taso masa amma.ya kwantar da
ita ta hanyar lumshe idanunsa,ya jinjina kanshi da kyau mamaki yana sake
cikashi.
"Kana jina?" Ta fada da mugun zafin da takeji a
ranta.
"Maamah.....cikin arziqin da Allah yayimin......ina iya
daukan dawainiyarsu data danginsuma gaba daya ba tare da komai dana mallaka ya
samu matsala ba......dukka mutumin da ka kawoshi nan wajen yayi ibada kana da
lada na musamman,duk aikin alkhairin da kayi asalinsa kana da lada daidai da
wanda yayi aikin ba tare da an tauye ladan kowa ba.......maamah......tabbas
inda albarkar uwa ita ke sawa yaro ya rayu.....ba shakka da tuni mun jima da
amsa sunan GAWA,so inaga ba matsala bane ka zama silar sanya farinciki a
rayuwar wani......dukiyarmu da kason wasune dole a ciki da ubangiji ya sanyata
cikin tamu.....ya zama dole ka raba ka bawa kowa don fita haqqinsu da ubangiji
ya dora maka.....ina fatan ba wani magana a ciki daya bata miki" Ya qarasa
fada yana miqewa.
Mutuwar
zaune tayi kalamansa suna bata mamaki me tsanani,kasa ce masa komai tayi har ya
fara takawa zuwa qofa.
"Muna kusa da masjid nabawi,dukka sallolinku zaku iya
qarasawa kuyi a ciki.....ni na wuce sai zuwa dare" Ya qarasa fadi yana
ficewa cike da fatan kada ta sake cewa komai din bare ya tsaidashi.
A
bakin elevator ya samu su musaddiq,sai kawai suka wuce zuwa masallacin. Suna
tattaki a qafa yana sauraren hirarrakinsu,yayin da nashi Hankalin yayi nisa
zuwa wani guri na daban.
★Sau uku tana
juyawa tana qare musu kallo cikin daren,idanunta duka suna tsakanin huda nadra
da haneefa da kuma momma bahijja dake kwance saman nata gadon.
Tashi tayi
ta zauna sosai,zazzabi takeji yana sake qaruwar mata,ko amai din sai data
sakeyi dazu amma bata bari kowa a cikinsu ya gani ba,saboda wannan farincikin
da wannan walwalar take so taci gaba da gani saman fuskarsu,batason ganin komai
da zai bata wannan yanayin.
Hadewa
jikinta tayi waje daya tana jin sanyi,yayin da can qasan ranta ya cika da
ambatonsa. Tana ji ya gama yi mata komai na rayuwa.......tanaji ya gama
mallakar komai nata.....gangar jiki da kuma zuciya,tana jin ya sayi wani babban
gurbi a rayuwarta da rufe babinsa ba abu bane me yuwuwa. A yanzun daya qarasa
cika mata burinta.....
Sun gaya
mata abubuwa masu yawa da ya yiwa rayuwar su wanda bata taba kawowa mafarkinta
hakan zai kasance ba. Wani irin gini da ya yiwa rayuwarsu har ya zarta nata
mafarkin a kansu.....ko yanzu ta fadi ta mutu ta godewa Allah......tana da
dukkan tabbas da yaqini akan rayuwarsu.
Haka
kawai takejin kaman yayi tsaho ace ta jirayi gobe kafin tayi masa
godiya.....sai takeji ya cancanci ta abokanceshi a wannan daren. Tafi kowa
sanin yadda waje yake masa qunci idan ta matsa......tafi kowa sanin yadda yake
qulafucinta da son kasancewarsu tare. Tun saukarsu bai nemeta ba ko a
waya,tasan kara kawai yayi mata bawai don hakan yakeso ya kasance ba.
Zazzabinta da komai da takeji ta hadiye,ta shiga bandaki ta sake
wanka,ta dawo cikin dabara tana tunanin inda zataga luggage dinta. Ba luggage
amma akwai wani bag daban data shigo dashi,kusan duka sabbin kaya ne a
ciki,saita samu kanta da neman rigar da tasan zata dace da yanayin. Tsaf ta
gyara sumarta cikin hair mist dinta,ta kuma tajeta ta saketa a gadon bayanta.
Yadda farar tattausar rigar maras tsaho ta zauna mata a jikinta ita kanta ya
burgeta,komai ya fito das das a jikinta da wani irin salo me daukan
hankali,saita nema dogon hijabin daya rufe mata jikinta ruf ta aza saman
rigar,ta dauki wayarta ta taka a hankali tana fita a dakin.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 113
113
Waiwaye ta
dinga yi don ta tabbatar da kowa bai ganta ba,ta qarasa qofar dakin a nutse
tana fatan samunta a bude. Taci sa'a kuwa,don tana murdata ta bude din,sai ta
tura ta shige a hankali. Abinda bata sani ba tayi shuka idanun makwarwa,daidai
sanda maamah ke fitowa daga dakinta da zummar sauka floor din qasa ta rage
zaman kadaici koda cikin reception ne.
Dif wuta
ta dauke mata,wata qaqqarfar guduma ta saukar mata. Lalubawa tayi ta nema
kujerun da suke ajewa jifa jifa ta cikin hallways din ta zauna ganin duhu yana
nemam giftawa idanunta tana maida numfashi,maganar da sukayi da ita ta qarshe
ta dawo mata.
"BANA SONSHI....BAZAN KUMA TABA SONSHI BA.....BANMA
SHIRYA ZAMA DASHI BA.....AKWAI LOKACIN DA XAN TAFI.....AMMA ZAN TAFI NE KAWAI
SANDA NI NA TSARA NA TAFIN,BAWAI SANDA KE KIKA SHIRYA FARUWAR HAKAN BA".
kai ta jijjiga tana sake dilmiyewa cikin mamaki. Wato ita yarinyar take rainawa
hankali kenan?,ita takewa wasa da hankali?,wai ya akayi kaman ita mariya
yarinya 'yar cikinta wadda inda fuad mace ne yaci ace jikarta ce amma take
wasan kura da hankalinta haka?. Dukan kujerar tayi ta miqe tana komawa cikin
dakin,zata kasa ta tsare taga iya awannin da zata dauka kafin ta fito a dakin.
Matsakaicin haske ne a dakin,da alama ya kashe kowanne qwai banda side
lamp din dake gefen Kujerar data hangoshi kwance samanta.
Yana
kwance sosai ya miqe dukka wannan tsahon nasa,hasken fitilar ya haske fuskarsa
sosai. Qur'ani ne a bude kife a qirjinsa,da alama yana tsaka da karantawa bacci
ya daukeshi. Baqar sumar nan dake habarsa da qasan hancinsa girarsa da zara
zaran eyelashes dinsa sun sake qawata fuskarsa da wani irin annuri. Ita kanta
saita samu kanta da qare masa kallo,har zuwa sanda ta isa gabansa cikin sanda.
A hankali
ta tsugunna a gabansa tana sake matsawa dab dashi,qamshinsa ya taso ya daki
hancinta,abinda ya sakata lumshe idanunta ba tare data shirya ba saboda dadi da
nutsuwa da qamshin ya saukar mata.
Cikin
takatsantsan ta miqa hannunta tana zare alqur'anin da yake rungume dashi,ta
daga tana duba wacce surar yake.
Alama ce
saman ayar muhammadur rasulullah bisa dukkan alamu nan yake karantawa,ta motsa
bakinta a hankali ta furta.
"Sallalahu alaihi wa sallam" Ta sanya bakinta kan
ayar a nutse tayi kissing nata sannan ta rufe qur'anin ta adanashi.
Sake
dawowa tayi ta tsugunna saitin fuskarsa tana qare masa kallo. Karon farko data
karanci ainihin sassanyan kyau da Allah ya masa baiwa dashi. Ba banza ba yake
da wani irin kwarjini da ba kowa ke iya saka idanunsa kan fuskarsa zuwa cikin
idanunsa haka kai tsaye ba,labbansa sukayi mata kyau sosai,ta miqa hannu tana
taba dogayen eyelashes dinsa sannan ta sauko zuwa labbansa masu kalan red tadan
taba. Motsawar da taga yayi sai ta janye hannunta da sauri zuciyarta tana
bugawa,dan gyara kwanciyarsa yayi kadan zuwa hannun damansa,abinda ya bashi
daman fuskantarta sosai itama ya bata daman ganin fuskarsa sosai.
Hannunta
ta sake miqawa ta kama yatsunsa,a hankali ta motsa labbanta.
"Ka dage sai da ka farauci wannan sabuwar
zuciyar......ka dage da qarfin zuciya dana damtse sai daka fanshi wannan ruhin
da baisan soyayyar kowa ba saita 'yan uwansa......ka nuna sadaukantaka da
jarumta har sai daka yaudari zuciyar marainiya ameenatu......wallahi na
sallama......sabreen ta sallama maka,ta mallaka maka......ta kuma miqa
wuya.........na baka dukkanin soyayyata dari bisa dari......ka cinye
yaqin.....kayi nasara......na karbi faduwar ta wannan bangaren muddin wannan
shine faduwar......ka mamaye DUNIYATA ka sabuntata da irin DUNIYAR kowanne
mutum.....nima kaine DUNIYA TA" ta qarasa fada tana kallon zara zaran
yatsunsa masu farare qal din farce kaman baya taba komai dasu.
Motsin da
ya dan sakeyi ya sanya gabanta faduwa
"Idan yana jin duk abinda kika fada fa?" Wata
zuciyar ta gaya Mata,saita fidda idanunta dukka waje tana miqewa da hanzari a
ranta tana cewa.
"Da na gama jin kunya".
"Ina zaki tafi kibar zuciyar da kika gama
lugiguitawa?" Muryarsa ta daki kunnenta me dauke da alamun bacci yatsunta
na cikin wanda yaci nasarar cafkesu sanda take juyawa zata fice.
Zare
idanunta dukka tayi gabanta na harbawa,kada dai ace yana jinta?.
"Zan iya cewa kunnuwana sun manta dajin wata kalma me
dadi a rayuwarsu irin na yau......karki tafi ki barni cikin wayen wadannan
kalaman" Yayi maganar yana saukowa daga kujerar sannan ya sakar mata
hannum yana takowa bayanta.
Kane kane
yayi a bayanta yana rungumota ta baya ta hanyar aza hannuwansa saman ruwan
cikin ta. Ya cusa hancinsa ta wuyanta yana zuqo daddadan qamshinta daya soma
aike saqo sassan jikinsa da wani irin hanzari
(Karki raina turare,kada ki rabu da turare amatsayinki na
matar aure,duk yadda zan gaya miki rawa da muhimmancinsa a wajen matar aure ba
zaki gane ba......amma hatta da sha'awa turare yana tayar da ita,musamman irin
masu sanyi da laushin qamshin nan,amma ki lura,akwai inda za'ace ki kama kalar
qamshi guda da mijinki xai ganeki dashi,tom wani.namijin ba haka yake ba,wani
yafison kullum da kalar da zaiji a jikinki,bayason kala dayar nan,saiki fahimci
mijinki wanne iri ne).
"Sabrrrrr" Ya kirata a rikice yana jin wannam
feeling din da yakeji a kanta yana taso masa.
"Hamma" Ta amsa masa itama idanunta a lumshe tana
jin yadda saukar hannunsa a jikinta yake haifar mata da wani irin yanayi me
wahalar fassara.
Magana
yakeson sakeyi mata amma ya kasa,sai kawai ya fara tattara hijabin zai rabata
dashi. Hannunsa ta riqe sannan a hankali taja baya,ta tattare hijabin da kanta
ta zameshi daga jikinta ta wurgar dashi gefe daya.
"Ya subhanallah" Ya furta bakinsa yana rawa. Zai
iya cewa bai taba ganin sanda tayi masa kyau irin yau ba,tayi ado sosai da
gashinta irin yadda yakeso ya gani. Kowacce boyayyar sura ta jikinta ta bayyana
yadda yake da muradin ya gani,kafin ya qara kowanne motsi ta qara sanda bashi
mamaki ta hanyar balle hannuwan rigarta suka zame ta saka hannunta da kanta ta
zare rigar zuwa qasa sannan ta fara takowa har inda yake ta iskeshi.
Wani irin
mahaukacin tarba yayi mata cikin tsananin yunwarta,yana jin kamar yau ne rana
ta farko daya fara sanyata cikin idanunsa,martanin data soma maida masa ya
sanya yaji bashi da wata jarumta sam,yana gudun suci gaba da tsaiwa tsaf zasu
iya zubewa,sai ya sauqaqa musu ya dauke abarsa ya qarasa da ita inda sukafi
wayo.
Kirif ya
rufe musu fuskokinsu da mayalwacin
gashinta dake fesar da qamshin hair mist dinta. Gaba daya ya shiga wani rudani
da bai taba shiga irinsa ba tsahon kasancewarsu tare. Komai yayi mata saita
maida masa martani,duk inda ya nufa kafin ya qarasa tayi masa jagora,sai yaji
kaman ya kurma ihu ko xai samu sassaucin dimuwar dame yawo cikin kwanyarsa.
Yanaso
ya gaya mata ta sassauta saboda kada ta jashi yayi mata babban aiki,don yana
iya jin dumin dake jikinta,amma inaaa ta qarasa dimauta kowanne tunani nasa,ba
abinda bakinsa ke iyayi banda furta sunanta a jejjere da bada zazzafan kiss da
karbar martani daga gareta.
"Ki soni sabbrrrrr......na rantse da Allah ni kadai
nasan me nakeji a kanki......ki soni,zan miki komai....zan zame miki
komai.....zan mallaka miki komai". Fuskarsa ta riqe sosai cikin hannuwanta
tana dubansa,gaba daya kamanninsa sun sauya ya birkice sosai.
"Muhammad" Ta kirashi
"Fu'ad" Ta maimaita
"Muhammad jadda......ameenatu ta yarda ta
soka......ameenatu ta yarda ta mallaka maka kanta da rayuwar ta,ameenatu ta
zama taka har gaban abada....dakai da ameenatu yanxu duka abu daya ne.......ka
gayawa kowa wannan cikin alfahari taqama isa da samun tabbaci"
Ya riga
ya sallama,gaba daya ta gama susuta qwaqwalwarshi......yasan a yau kam duk
wanda yayi kusa da yawa da dakinsa zai iya jin motsin da xai saka zargi a
ransa,baisan me yake yi ba kaman yadda ya manta wayeshi. A lokaci ji ya dinga
yi inama akwai wata duniyar ta daban da zai iya maidasu shi da ita?,duniyar da
babu kowa saisu kadai?,wannan albishir daya samu daga bakinta......daga gari me
tsarki yafi komai masa dadi da zame masa tarihi cikin rayuwarsa.
Wani
irin dare suka raya,daren data sakar masa dukka ragamarta,ta cika masa
mafarkinsa ta hanyar bashi kowacce gudunmawa da cikakken hadin kai,saiga
muhammad fu'ad din yana mata kuka sosai kaman qaramin yaro. Kukan daya sake
susutata itama,banda abune da ubangiji ya sanyashi ya zama sirri tsakanin
ma'aurata......tabbas duniya data cika da mamaki idan akaga matashin zaki
gwarzo irin muhammad jadda yau a gaban mace yana mata kuka har haka.
Ita kanta
a rikice take,ta kuma aikatu sosai a hannunsa duk da controlling din kansa daya
dinga qoqarin yi,kafin wani lokaci zazzafan zazzabi ya sake rafketa bayan amai
data yi a jere har sau uku.
Abinda ya
daga hankalinsa kenan,ya tsaftacesu shi da ita,ya kuma shiryata cikin abayarta
me sulbi shima ya sanya jallabiiyyarsa,ya duba asibiti mafi kusa ya kirasu
donsu dauketa aje a duba masa ita,don bayajin zai iya jure wannan zazzabin yaci
gaba da taba masa ita.
Cikin
mintuna qalilan motar al_ansar hospital ta iso suka wuce da ita. Baiko samu
tsaiwa gaya musu ba,don kiran sallar farko kawai akayi,sai ya rubuta saqo kawai
ya turawa Farooq.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 114
114
Ko na
second daya bai barta ta matsa daga jikinsa ba,tana kwance cikin jikinsa da
wani irin yanayi. Cikin kowanne numfashi da zai sauke ko zai fitar jinsa takeyi
da wani irin maqalallen yanayi a cikin zuciyarta,duk bayan minti kadan sai ya
tambayeta
"Ina ne kuma yake miki ciwo?,menene yake damunki?,me
kikeso?" Ido kawai take lumshewa,don ita kadai tasan me takeji cikin
qasusuwanta,saidai tana qoqarin nuna masa all is well saboda ta fahimci a
gigice yake,amma duk da haka bataga nutsuwa a tattare dashi ba,kaman me gani
har hanji,ya fahimci duk wani motsinta.
Yanayin
zazzabin ya sanya suka fara bata taimakon gaggawa a daki na musamman,kafin daga
bisani su fara gudanar mata da test har kusan kala biyar suka tafi kan zasu
dawo da result din.
Sanda
tayi farkawa na biyu bayan tayi sallar asuba gari ya waye sosai,kusan goma
saura na safe. Shine mutum na farko data fara gani,fuskarsa ta fito fes yana
zaune daga gaban gadonta yana jan tasbaharsa,lokaci lokaci yana duba saqonni a
wayarsa.
"Sabahal khair muffin" Cikin ba zata muryarta ta
sauka a kunnensa. A nutse ya daga kansa ya sauke mata idanunsa. Itama shi take
take kallo da fararen idanunta murmushi na fita daga fuskarta.
"Muffin?......thanks ny world" Ya fadi sunan data
bashin yana masa wani mugun dadi.
"Sabahannur......khaifa asbahti?" Ya fada da
tataccen larabcin da kana ji zakasan yasan qa'idar kowanne harafi a cikinsa
yana nutsa tafin hannunsa cikin nata.
"Asbahatu bikhair walhamdulillah" Ta maida masa da
murmushin nan nata data tsinceshi saman fuskarta.
Kansa ya
langabe gefe guda kaman wani qaramin yaro,fuskarsa a narke yace mata.
"I'm scared that am going to loose you,i know it's
stupid,but i just can't stop thinking about it" Murmushi ta saki tana
danjin nauyinsa kadan
"Ka wahalar dani ne kawai......you won't lose me,am not
going anywhere in sha Allah". Riqe hannunta yayi sosai cikin nasa.
"That's my wish in sha Allah,you're the most important
thing in my life" Sosai maganganunsa suke sake samun mazauni a
zuciyarta,maganar amna data taba fada mata ta dawo mata fes akai.
"You're the luckiest woman da kika samu hamma na"
A yanzun take sake tabbatar da maganganun amnan,duk da a baya ta qaryata hakan.
"Have your breakfast and then brush your teeth"
Idanu tadan bude kadan tana kallonshi kafin ta sauke dubanta kan jerin kayan
breakfast din daya jawo gabanta saman dan wani gado.
"Ehnnnn" Ya fada yana dage mata girarsa,ya fahimci
akwai abinda takeson fadi.
"Brush din xai zama first ko?" Kai ya girgiza
"No.....Brushing teeth after breakfast helps remove
food particles and maintain oral hygiene" Shuru tayi murmushi na qwace
mata,ba a banza ba takejin su musaddiq na gulmarsa. Komai nasa yasha banban
dana kowa,tsare tsarensa ba irin na mutane bane.
A jikinsa
ya ajiyeta,ya dinga qoqarin bata breakfast din amma ta kasa cin komai a ciki.
Iya black tea kawai ta dinga kurba,tana sha yana kallon fuskarta yana qarfafa
mata gwiwa,a haka tasha rabi da qyar. Saidai tana kammalawa ya dawo duka,ta
wankesu tsaf da aman shi da ita.
Hankalinsa tashe ya danna wani guri,qasa da second sha biyar wata nurse
ta iso. Zata karbi gyaran wajen ya dakatar da ita da harshen turanci.
"Barmin zan gyara,aman nan da takeyi ne banaso,inaso
shima ya tsaya ko ya tafi,ya kamata abinci ya tsaya a cikinta hakanan".
"Likita yana dab da shigowa da dukka result na gwajin
da akyi mata,sai a sannan zaa san abinda ya kamata ayi mata,amma yanzun xan
sake saka mata ruwa don kada jikinta yayi rauni da yawa".
Yana
tsaye a gefe ranshi a jagule ta gama mata komai sannan ta fice,koda ya matso
sai ya samu har bacci yayi awon gaba da ita. Ajiyar zuciya ya sauke,yana jin
kamar ya dawo da ciwon jikinsa,agogo ya kalla.....yau din juma'a ce,yanason
samun sahun gaba gaba a masallacin ma'aiki,duk da zuwa yanzun ma yasan ya
makara,baya ga haka akwai wani al'amari me muhimmanci da zai aiwatar a can
din,wanda bayajin akwai abinda zai sanyashi jinkirtawa ko dakatawa a wannan
ranar ta juma'a. Rana ce mafi dacewa daya aiwatar da al'amarin. Idan yace zai
koma gida ya shirya ma ya bata lokaci,don haka ya daga waya kawai ya kira
farouq.
"Ka turo saddiq ko musaddiq......ina buqatan Friday
attire please".
" Ina kusa da hospital dinma......but bari na koma na
duba maka kayan...."
"Thanks dude"
"Don't mention it....ya jikin nata?" Dubansa ya
mayar kanta sannan yace
"Alhmdlh....she's sleeping,inaso naje mosque ne na dawo
kafin ta farka"
"Zaa kula maka da ita dude....kada ka damu,dukansu na
barsu suna shiryawa zasu taho nan"
"Alright" Ya fada a taqaice yana ajiye wayar.
Ba jimawa
farouq ya qaraso,dauke da wata leda me kauri. A nan parlor din dakin ya
zauna,shi kuma ya wuce ciki inda gadon sabreen din yake.
Cikin
qanqanin lokaci ya shirya,Moroccan jallabiyya ce fara tas me asalin tsada me
adon gold din zare,sai zagayayyar hular nan irin ta larabawa wadda set ce tare
sukazo da hular da loafers din dake ciki iri daya. Wani irin sassanyan kyau ya
aje,saika dauka balaraben Morocco dinne,ya matsa inda take kwance tana baccinta
kaman ba abinda ke damunta,ya sunkuya yayi kissing dinta sannan ya fara takowa
yana fitowa.
Tun bai
qaraso parlor din ba yaji muryar farouq dana likitan,yana tsaye sanye da farar
lab coat dinsa suna hira sama sama da farouq din. Fuskarsa sake ya miqawa fuad
hannu cikin sanin darajar dan adam da iya aiki,shima ya bashi suka gaisa,sannan
ya fara bude takardun hannunsa.
"After conducting the necessary tests,I'm pleased to
inform you that your wife is pregnant...." Likitan ya fada da murmushi a
fuskarsa.
Karon
farko da yaji ya koma kaman dan koyo a fannin turanci,kaman ma baya gane komai.
Ya zubawa likitan idanu yana buqatar qarin bayani,muryar farouq ta dawo dashi
hayyacinsa.
"Alhamdulillah......ya rabb
lakalhamd.....alhamdulillah......muna godiya sosai likita" Farouq daya
kasa zama ya fada yana kama hannun likitan da kyau ya riqe cikin nasa.
"Allah ya inganta......ya bata lafiya me dorewa.....ina
tayaku murna" Abinda likitan ya fada kenan yana murmushi,sannan ya miqawa
farouq takardan gwajin yana masa bayani.
"Idan ta tashi a bacci za'a qarasa bata duk wani
treatment daya kamata"
"Mun gode" Farouq ya sake maimaitawa yana karbar
takardan likitan ya juya ya fice.
Ganin gaba
daya fuad din ya zama wani statue ya sanya farouq kai masa duka
"Dude......kayi nasara.....ka jefa qwallonka a raga
daidai" Sai a sannan ya tattaro kalaman bakinsa da qyar
"Am going to be a father?" Ya tambayi farouq cikin
neman bayani gamsashe.
"Yes dude.....bakai kadai ba,harda ni,anni zata zama
grandma for the first time......zamuyi yaro ko yarinya dukanmu......" Bai
jira farouq ya kammala ba yayi masa wata wawiyar runguma hawaye suna kubce
masa.
"Ya rabba.....antal kareemul lazi ya yaraddu
sa'eelan,la'ilaha llla antar rahmanir raheem......shukran ya
Allah,shukran" Sai muryarsa ta karye,ya dora fuskarsa saman kafadar farouq
kuka nason qwace masa.
"Bansan wannan jarumin muhammadun da saurin kuka
ba.....duk da na lura sabreen ta maidashi baby da gaske" Farouq ya fada
shima zuciyarsa tana raunana amma yana qoqarin bawa kansa qwarin gwiwa. Kansa y
a daga yana riqe farouq da kyau,yanata qoqarin masa magana amma ya kasa,sai
kawai ya jijjigashi yana kada kai sannan ya taka da sassarfa yana komawa dakin.
Baccinta
take kaman yadda ya fita ya barta,ya sake sumbatarta a goshi da labbanta,a
hankali ya furta
"Kece duniyata.....na gode,na gode" Sai ya rufe
mata qofar yana komawa parlor din da sauri.
"Zanje nayi sallah masallaci......zan kuma aiwatar da
wani abu,idan zakaje mu hadu a hanya" Ya fada yana saka hannu ya kwashe
takardun ya zubasu a aljihunsa sannan ya fita da sassarfa bayan ya sanar musu
su aika me kula da ita zaije juma'a ya dawo.
Ba inda
yakejin ya kamata yaje ya juye farincikinsa da godiyarsa ga Allah irin cikin
rauda.....ya godewa Allah daya samu wannan labarin a irin wannan wajen,banda
haka ya tabbatar sai yayi qaramin hauka saboda farincikin yayi masa girman da
zuciya ba zata iya daukarsa ba ita kadai.
*_BAYAN AWA DAYA DA RABI_*
*_B A Z A T A_*
Anni,amna,musaddiq,saddiq dukkaninsu suna zaune a parlor din dakin
asibitin bayan sun shiga sun dubata tana bacci sun fito.
Huda
haneefa nadra da kuma momma bahijja sune kadai daga cikin dakin,suna taba tasu
hirar kadan kadan wadda ke cike da farincki da qaunar juna.
Maamah
dake zaune kallon kowa takeyi kawai daya bayan daya,yanayin yadda taga sabreen
a yanzu ya soma sauke mata duk wani qwarin gwiwa da takejin tana dashi akan ba
ciki bane a marar sabreen din. A shigarsu ta dazu ta gama qare mata kallo da
kyau,ba abinda idanunta suka hango mata kuma banda dashewa irin ta me yaron
ciki.
Iya
wannan abun kawai data gani ya sanya gumi ya fara yanko mata,duk da yadda
zuciyarta keta qarfafata tana mata romon bakan cewa ba ciki bane.
A yau
din batajin zata matsa daga asibitin nan ba tare da an gwada yarinyar nan ba
anga uban abinda yake damunta ba.
Sake
jan qaramin tsaki tayi jan qasa qasa tana gyara zamanta. Gaba daya zaman wajen
takeji ya gundireta,daidai lokacin fu'ad ya turo qofar dakin da sallama a
bakinsa ya shigo.
Sannu da
zuwa dukkaninsu suka fara masa banda maamah dake jifansa da wani irin kallo.
Saddiq musaddiq da amna dukka suka gaidashi da tambayar me jiki,ya amsa musu
cikin kulawa kafin ya qarasa gabansu anni yana gaidasu.
Da qyar
maamah ta amsa,ta bishi da kallo sanda yake miqewa zai wuce ciki
"Zo nan muhammadu" Ta kirashi,sai ya dawo ya samu
waje yana zama kujerar dake fuskantarta.
"Wannan ciwon da yaqici yaqi cinyewa ina ganin ya
kamata a auna yarinyar nan asan me yake damunta,kada mutane suna zamansu lafiya
taje tana yawo da ciwo tana yada ma mutane tunda gata ga yadda take a
baya". Sosai maganar maamah ta sokeshi,ya kuma fahimci inda ta sanya
gaba,anni kuwa sai da tayi da gaske ta iya controlling kanta.
Idonsa
ya lumshe kana ya budesu ya gyara zamansa.
"Ba wani ciwo da ameenatu take dauke dashi a
jikinta......tunda nine mutum na farko dana fara karbar mutuncinta na 'ya
mace......ciwonta na yanzun kuma nine silarsa.....ga bayanin nan a rubuce"
Ya fada yana zaro takardar,sai kuma ya dakata yana dubansu.
"Naji dadin ganinku a tare gaba daya" Ya fadi yana
sake zura hannunsa a aljihun rigarsa.
Dollars
dubu biyu ya fiddo sabbi kar a miqe,ya miqawa maamah takardar ya kuma miqawa
anni kudin.
"Abba......alhaji hamza kibiya ta hannuna ya karbawa
musaddiq mahmud jadda auren amna......bisa sadakin dala biyu biyu lakadan ba
ajalan ba......ta hannun wakilinsa abokinsa alhaji muhyidden kibiya da tarin
shaidu cikin masallacin annabi muhammad SAW,bisa yarjewar waliyyansu ni
muhammad fu'ad jadda da kuma abba wato alhaji hamza kibiya"......
TURQASHI!......FU'AD.....NACE ME JADDA?,WANNE IRIN MATCH KA
TARO HAKA?,KO TAKARDAR DA MAAMAH TA WARWARE BAKA BARI TA GAMA DUBAWA BA?.
TO NIDAI JAMAA WANNAN FADAN YAFI QARFINA
NAYI NAN😂😂🏃🏽♀️🏃🏽♀️🏃🏽♀️🏃🏽♀️🏃🏽♀️
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 115
_____________________________
_kin dade kina cizon yatsa kan yadda ake kacalcala suturun
yaranki da dinkuna marasa ma'ana?_
_HUGUMA na miki albishir da wajen zazzafan dinki na MS
KIDDIES WEARS,irin dinkunan yaran da kike gani a Instagram TikTok suna burgeki
kuma bakisan inda zakikai ayi miki ba ko kina tsoron tsada_
_Zafafan dinki na gayu da ado kiga yaranki sun fita dagwas
dagwas_
_ready
_MS KIDDIES na nan kano gwammaja_
*TRUSTED AND TRUSTED mun gwada mun gani*
_Maza tuntubeta a nan_
+234 708 865 2858
Ko Instagram account dinta
https://www.instagram.com/ms_kiddies_wers_by_nafs?igsh=MTljZWQwM2FsaXlxaA==
______________________________
115
Dukkanin wani
da yake numfashi a wajen saida jinin jikinsa ya daskare na wucin gadi,qwaqwale
da yawa suka dakata da aiki na wasu mintuna,yayin da idanuwa sukayi warwaje a
kansa. Kowa dubansa yake d wani irin madaukakin mamaki da tarin ba
zata,dukkaninsu kowa kwanyarsa ta kasa fahimta ko sarrafa maganarsa.
"Mem.....me kake cewa fu'ad?" Anni mutum qwaya
daya da tayi qarfin halin sake tambayarsa tana jin yadda jinin jikinta uske
tsinkewa. A nutse ya dubi annin nashi,yana da qwarin gwiwa da zato me yawa a
kanta,don haka kansa tsaye yace.
"Na aurar da amna ga musaddiq cikin masjid nabawi bisa
shaidu da wakilai da sadaki dala dubu biyu" Sai a sannan kwanyar wasu daga
ciki ta harba ta kuma dawo da aiki,ciki harda amna.
Wani
tsananin tsoro taji yana shigarta,ta shige jikin anni tana buya a bayanta gami
da cukuikuyeta,idanunta kuma suna sauka kan fuskar maamah. Wannan fuskar da
take bata wani tsoro haka kawai,fuskar da batason kallonta saboda duk wani
yanayi da alamu na rashin wanzuwar alkhairi tattare da ita tana ganinsu......a
yau mamallakiyar wannan fuskar itace a mazaunin surukarta?.
Shi
kuwa musaddiq kama hannun saddiq yayi ya riqe da kyau yana qoqarin tuna
maganganunsa da hamman masa mintuna ashirin baya da suka wuce kafin ya shigo
cikin asibitin. Abubuwa biyu ke masa kai kawo suna gwarabkiya cikin
zuciyarsa,farinciki da kuma fargaba da wani sofane na tsoro dan kadan. Kalaman
bakin maamah wani irin daci da dafi ne dasu wanda ya kasa sabawa da jinsu,baya
qaunar komai ya hadashi da ita alkhairi ko sharri,dadi ko akasinsa.
Idanu
kawai anni ta zuba ma fu'ad tana jin tsigar jikinta na tashi. Wanne irin tashin
hankali ne haka fu'ad din ya rakito mata tana zaman zamanta tana lallaba
tsufanta?. Wacce masifar ce ke shirin wanzuwa?,meye kuma zai afku gaba ga
amnanta?.
"Allah ya sanya alkhairi......yasa anyi a sa'a"
Lafuzzan suka fita daga bakin maamah da tayi qoqarin ware idanunta daga
qanqancesu da tayi.
Ba wanda
kalamanta basu bawa mamaki ba.......kaman yadda suka janyo hankalinsu ga
fuskarta wadda ta maida idanunta kan takardar hannunta tana qoqarin hana
zuciyarta tsananin bugun da takeyi,tare da fatan gumin dake yanko mata ya tsane
jikin atamfar jikinta ba tare da kowa ya gani ba.
Abu guda
daya data sani shine......tabbas fu'ad ya siyawa amna tikitin salwantar
rayuwarta......don bataga ta inda zata bari itakam da ranta da lafiyarta ta
hada jini da alhj hamza kibiya ba..... Idan fu'ad baiyi wasa ba a wannan
karon,zata rufe idanunta tayi hukuncinta kan me uwa da wabi......zata mance da
alaqar dake a tsakaninsu tunda har ya iya mancewa da matsayinta a wajensa.
Saddiq musaddiq harma da amna sai lafazin maamah din ya sanya suka fara
jin abinda ke ransu yana sassauta,wanda sam ba haka bane a qirjin anni da
fu'ad. Wani duba sukaci gaba dayi mata,kowannensu yana son karanto ainihin
ma'anar maganarta.
Sun
riga da sun sani.........banza bata kai zomo kasuwa......hakanan kowa ya tuba
don wuya to tabbas babu lada.......ba haka kawai maamah zata bada amsa ga
lamari me girma irin wannan ba......ba haka siddan zata miqa wuya ga al'amarin
daya fado bagtatan irin wanna ba.....TABBAS AKWAI WATA A QASA.
Lokacin
da idanunta suka kai kan conclusions na gwajin sabreen din sai ta fara qanqance
idanunta a hankali,ji tayi kaman debi yaji an watsa mata cikin idanunta kafin a
hankali taji kaifin ganinta kaman yana raguwa.
"Ciki?,sati uku?" Tambayar data samu daman motsa
labbanta ta yiwa kanta da kanta kenan.
Iskar
dakin taji tana mata wahalar shaqa,kamar babu isashiyar oxygen dake wulgawa ta
wajen,takai hannunta wuyanta tana janye mayafin data yafa waiko yana cikin
abinda ya jawo mata qarancin iska,still sai taji ba abinda ya canza.
Da gaske
iska ke neman mata kadan,wannan ya sanya ta soma jan iska da qarfin gaske tana
aikawa hunhunta don ta samu taci gaba da numfashi,yayin da ilahirin jikinta ya
soma rawa kadan kadan.
Musaddiq ne ya fara ankara da hakan,don fu'ad tuni ya soma takawa xuwa
dakin da sabreen take don kaucewa kallon tuhumar da anni ke jifansa dashi.
Baida matsala da duk wani tuhuma na maamah ko kuma kalar kowanne qalubale daga
gareta,damuwarsa daya yadda annin dama zata karbi abun,ko ita dinma ya shirya
mata,don bayajin akwai wani abu guda daya daya dace yayi sama da wannan din.
"Lafiya?.....kaman numfashinta baya kaiwa" Anni
data iso gurin ta fada tana duban hannunta wanda takardar gwajin da fu'ad ya
bata ta sulale ta fadi a qasa.
Yanayin
sautin anni ya sanyashi dawowa da baya,yadan daga qafa yana qarasowa wajen,sai
yayi saurin matsawa wayar dake ajiye a dakin don neman daukin likita ko nurses
ya soma kira.
Minti
guda kacal sai ga mutum biyu tare da likita sun qaraso,saman wheelchair aka
dorata sannan suka turata xuwa dakin da yake daura da wannan.
Dukkaninsu
suna farfajiyar dakin daga waje,suna jira suji bayanin da likitan zai fito
dashi. Duk bayan sakanni sai anni ta daga idanu ta dubi fu'ad,gaba daya ya gama
warware mata zaren tunaninta. Wannan wani abune nashi na daban,tsahon zamanka
dashi zaku iya qareshi ba tare da ka iya fadin gundarim halayensa ba gaba
daya,yakan zo da abubuwan da hankali da tunani basu kawosu ba,yana da bada
mamaki irin hakan,saidai bata taba kawowa zai iya aikata qunar baqin wake irin
wannan ba.
shima
kansa ya sani,duk wani kallo da anni take masa yana cure ne da mamakinsa,saidai
ya sakawa kansa wannan dakiyar da juriyar da wani irin basarwa,don haka ko sau
daya yaqi kallon anni,saidai yasan shi take kallo ta gefan idanunsa.
Basu
wani jima ba suka fito,suka qaraso gaban fu'ad din.
"Ba wani abu bane me tsanani,kawai ta shiga shocked
sosai daya sanya jininta hawa lokaci guda......irin wannan case din yana iya
jawo mutuwar barin jiki ko bugawar zuciya idan yazo da akasi.....zuwa yanzu dai
ita Allah ya tsallakar da ita,saidai kuma jininta yahau sosai,an mata allura ya
kuma sauka alhmdlh,nan da awa daya ma zata iya tafiyarta gida.......amma fa sai
tana kiyaye saka bacin rai da damuwa a ranta".
"Na gode Dr" Fu'ad ya fadi yana bawa Dr hannu
sukayi musabaha ya wuce.
Musaddiq
ya kalla sai ya taka zuwa cikin dakin saddiq ma ya bishi. Idonsa yaketa qoqarin
kawarwa daga annin don kada su hada ido ya soma takawa zai shiga ya duba maamah
din amma sai sautin annin ya katseshi.
"Ka kyauta" Ta fada kai tsaye,abinda ya sakashi
dakatawa daga tafiyar da yakeyi kenan. Shuru ya ratsa na wasu mintuna,sai kuma
ya dawo da baya a nutse ya tsaya gaban annin.
Hannuwanta
ya riqe yana zaunar da ita daidai sanda take fadin.
"Kaga irin abinda ka jawo ko?" Zame takalmin
qafarsa yayi ya zauna sosai a gabanta ba tare daya damu cewa marbles bane a
wajen.
"Ban jawo komai ba anni.....kuma komai bai faru ba,ko
ba wannan maganar irin wannan ranar irin wannan lokacin yana dab da faruwa da
maamah....... Tunda muka tashi bamu san wani abu farinciki ba sai a
sanadinku.......musaddiq ya rasa abubuwa masu yawa tun yana yaro......yanzun
kuma a sanadinta sai a haramta masa abinda yake buri yake muradi yake kuma
so?,bayan a baya ya rasa abinda yake buri da muradin kuma duka ya haqura?"
Tambayar tasa tadan taba annin,saidai duk da haka sai takejin kaman bai kyauta
ba abinda ya yiwa maamah,ko ba komai ita ta haifi musaddiq din ta kawoshi
duniya.
Ta bude
baki zata sake magana yayi caraf ya riqe hannunta sosai,abinda bai taba yi ba.
Idanunta ta daga tana duban nasa idanun,wadannan alamun bacin rai mai tsanani
din sun bayyana sosai cikin idanunsa,alamun ranshi ya motsu sosai.
"Kina tunanin ga musaddiq......zan bari amna ta auri
wani a waje koda baice yana so ba?,wanin da bamu da tabbas a kanshi?,wanin da
ban isa na hukuntashi ba idan ya cutatar da ita duk yadda muke sonta
kuwa?.........Karki sake cewa komai anni don Allah na roqeki,bakinki kada ya
sake furta komai a kansu idan ba fatan alkhairi ba......indai har yanzu kin
yarda kina kuma ji a ranki ni da musaddiq 'ya'yanki ne.....amna qanwata ce
halak malak kamar yadda musaddiq yake....to karki sake cewa komai sai fatan
alkhairi.....ko meye zai faru.....ko menene zai taso anni na roqeki ki saka
idanu.....nike da alhakin hakan kuma nine zan dauka". Gaba daya ya gama
kashe mata jiki,ya kuma kashe duk wata kalma da yake da yunqurin fadi. Fu'ad
din wani mutum ne na daban,ajiyar Allah ne,yana da kaifi wajen komai nasa,kaman
yadda nutsuwa da dattako ta mamaye dabi'arsa gaba daya.
"Kai da abba kuka hada baki ko fu'ad?" Anni tayi
tambayar a sanyaye. Wani dariya ya tasowa fu'ad,yayi qasa da kansa yana
murmusawa kafin ya daga kansa ya sake maidawa ga annin.
"Ba ruruwan abbanmu.....kada ki sashi a ciki anni,aikin
Muhammadu ne,ni kadai na kitsa abuna.....saboda asara ce babba ace ba wata
dangantaka da alaqa ta dindindin tsakaninmu da ku anni.....kun gama yi mana
komai a rayuwa....kun bamu ruhi me tsafta.....ruhi bana rai ba.....ruhi na
dabi'a addini tarbiyya da ilimi da kowanne dan adam yake da buqatarsa........ba
wata sakayya da zamu iya yi muku sama da wannan" Shuru sukayi
dukkaninsu,jinjina kai kawai anni takeyi. Duk duniya ba wanda zai kaita son
hada jini da musaddiq......to amma ita fitina ba abar so bace.
"Amma anni......me kike tsoro ne duk da tarin jarumtar
da kike da ita?" Ya fada cikin salon tsokana don yadan bata wani nutsuwar
zuciya.
Harara ta
jefa masa tana dan murmushi kadan kafin ta amsa masa
"Kafi kowa sanin ameenatu ba raguwa bace.....ameenatu
ba matsoraciya bace.....fitina ce kawai ameenatu bataso,ita din me son nutsuwa
da kwanciyar hankali ce".
"Na shaida hakan" Ya fada yana murmushi sannan ya
sakar mata hannunta.
Miqewa
tayi tana cewa
"Muje na dubata.....saika samu kadan zauna da ita,ka
kwantar mata da hankali ka fahimtar da ita har ta samu nutsuwa". Murmushi
kawai ya saki yana zube hannayensa a aljuhun rigarsa. Anni tana wasu abubuwan
kamar batasan halin maamah din ba,kamar ita din baquwa ce a dabi'unta.
A zaune
suka sameta saman gadon,har sun zare ruwa da alluran da suka saka mata. Ga
oxygen din da suka cire mata a gefe. Dakin shuru,banda qarar ac bakajin
komai,musaddiq da saddiq na zaune saman kujera suna zaman kurame su da ita.
Kallo daya
tayi musu shida annin ta dauke kanta daga sashensu,don ci gaba da kallon nasu
bazai iya Haifa musu da me ido ba,hasali ma jarumtar da take jin zatayi tsaf
zata iya kwaranyewa tayi nata wajen.
Shigowarsu ya sanya musaddiq da saddiq ficewa,don dama shikam musaddiq
zaman ya gundureshi,hanya kawai yake nema.
"Ya jikin?,Allah ya sawwaqe ya qara afuwa" Ido
maamah kawai ta runtse,batason jin sautin muryar anni sam sam. A halin da
takeso ta ganta kenan,ta kuma ganta,saidai tana bawa kanta da kanta tabbacin
wannan shine gani na qarshe da zatayi mata a haka,next time lallai zai zamana
annin ce kwance saman gadon asibiti kamar haka......wannan alwashin saita
cikashi koda numfashinta zai qare.
Juyawa
anni tayi ya fita tana basu waje,ya matso gabanta kadan yana mata sannu da
jiki. Idanu kawai ta zuba masa na wasu sakanni,sannan a hankali ta bude
bakinta.
"Ci gaba da qirqirar sabbin kurakurai suma kuskure
ne.......yayin gyaran kuskuren kuma komai yana iya faruwa da kowa ma......kasa
a maidani gida.....jibi nakeso na koma nigeria" Iya abinda ta fada kenan
tana yunqurin sauka daga saman gadon. Baice mata komai ba ya bita da
kallo,saidai kowacce kalma data fita a bakinta ya rubutata tsaf ya ajiyeta,ya
juya ya taka a hankali yana fita a dakin don cika umarninta.
Tsaye
sukayi a farfajiyar asibitin sanda motar da jordan ke tuqawa da maamah din a
ciki tana barin cikin asibitin. Musaddiq ya motsa don komawa ciki bayan bacewa
ganinsu da motar tayi.
Caraf
fu'ad ya damqo hannunsa,musaddiq ya waiwayo da sauri yana duban idanun fu'ad
din. Ko sau daya bai kalleshi ba,yaci gaba da riqe hannunsa yana takawa dashi a
hankali har zuwa gaban motarsa,yana isa abdulgafar ya bude masa ya tura
musaddiq ciki sannan shima ya shige abdulgafar ya rufesu.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 116
______________________________
_kin dade kina cizon yatsa kan yadda ake kacalcala suturun
yaranki da dinkuna marasa ma'ana?_
_HUGUMA na miki albishir da wajen zazzafan dinki na MS
KIDDIES WEARS,irin dinkunan yaran da kike gani a Instagram TikTok suna burgeki
kuma bakisan inda zakikai ayi miki ba ko kina tsoron tsada_
_Zafafan dinki na gayu da ado kiga yaranki sun fita dagwas
dagwas_
_ready
_MS KIDDIES na nan kano gwammaja_
*TRUSTED AND TRUSTED mun gwada mun gani*
_Maza tuntubeta a nan_
+234 708 865 2858
Ko Instagram account dinta
https://www.instagram.com/ms_kiddies_wers_by_nafs?igsh=MTljZWQwM2FsaXlxaA==
____________________________
116
Wadannan
tsumammun idanun nasa da ya saba hukuntashi dasu tun yana qanqaninsa ya zuba
masa. Wani irin kallon qurilla me dauke da tarin ma'anoni da suka sanya jikin
musaddiq yin sanyi tun kafin fu'ad yace komai.
"Wanne irin tsoro nake gani cikin idanunka
musaddiq?" Fu'ad ya jefa masa tambayar yana nuna qwayoyin idnunsa da
yatsunsa. Tambayar tadan daburtashi,har ya rasa me zaice masa.
"Ashe kai maqaryacin masoyi ne?......bakason soyayya
batason ragwantaka ba?,bakasan mata basason ragon namiji ba?,bakasan soyayyarka
bata cika soyayya ba sai ka amince zaka iya fuskantar dukkan wani qalubale da
hatsari akan masoyiyarka ba?,bakasan soyayya bata amsa sunanta ba sai ta samu
sadaukarwa tsananin kulawa da jure duk wani tsanani ba?........you're very
stupid musaddiq muddin baka xama tsayayyen namiji ba akan amna......na aura
maka amna don ubanka saboda ka kula mana da ita.......ban tsaya a matsayin
waliyyinka ba saboda amna ta samu wani uban bayan abba.....ni waliyyin amna ne
da bazan lamunci duk wani rashin kulawa daga gareka ba a kanta......ka riqe
musu yarinya da kyau.......ka xama jarumi a kanta koda kai rago
ne.......wallahi wallahi bazan daga maka qafa ba idan har naga ko naji wani abu
mara kyau dangane da ita a kanka ba......yiwa auren amna riqon wasa ko ka bari
tsoronka ya jagoranci igiyar aurenta dake hannunka.....to kasa a ranka baka
taba sanin wani me sunan muhammad jadda ba".
Gaba
daya jikin musaddiq yayi laushi tubus......yana tsananin qaunar amna,irin
qaunar da bai taba yiwa kowa irinta ba,to amma kuma tsoron fitinar maamah yana
neman dakushe masa komai,duk da yaji cikin ransa ruwa da iska.....ko zaa saka
kanshi gabas a yanka bazai iya rabuwa da auren amna ba.
Qofa yasa
aka bude masa ya nuna masa hanya,musaddiq ya kalli fu'ad din sai ya sauka salin
alin daga motar,yasan ba lallai a yanzu ya wani bawa ban haqurinsa muhimmanci
ba.
Abu
guda daya tak daya tuna yaji ya kwaranye masa duk wani bacin ransa.....cikinsa
dake kwance cikin mararta wanda ita kanta batasan dashi ba,murmushi ya subuce
masa ya sauka a hankali daga cikin motar yana komawa asibitin.
A
hankali ya tura qofar falon yana shiga,idanunsa suka fada kan anni. Tana tsaye
da takarda a hannunta tana dubawa,shigowar tasa ya sakata daga kai ta kalleshi.
Wani
kwantaccen farinciki me ban mamaki ya gani saman fuskarta wanda bai taba ganin
irinsa ba. Ya zare idonsa yana duban takardar sosai. Takardar dazu ce da maamah
ta saki,take ya fahimci dalilin wannan murmushin,kawai sai ya shafa sumar
kansa,karon farko yaji kunyar annin ta saukar masa,ya taka da dan hanxari yana
wucewa cikin dakin.
Sosai
murmushi ya subuce mata,ta saki sassanyan ajiyar zuciya tana jin zuciyarta na
wankewa daga dukkan wata fargaba da bacin rai.
"Ubangiji ka rabasu lafiya,ka yiwa abinda aka samu
albarka" Ta furta a sarari tana ninke takardar.
Wani sanyi
ne yaji yana ratsa zuciyarsa sanda yayi ido hudu da ita. Tana zaune tsakiyarsu
huda......haneefa tana gefanta a zaune hannunta cikin nata. Hira sukeyi irin
hirar da kana kallon fuskarsu zakasan qauna da soyayya gami da shaquwa irinta
'yan uwantaka ta huda su. Murmushi ne kawai ke fita a fuskarta,wani irin
murmushi da yake sake qawata fuskarta da wani irin lallausan kyau me daukan
hankali.
Jingina
jikinsa kawai yayi da jikin qofar,ya langabar da kansa yana qare mata kallo.
Kallo yake mata irin kallon da mutum yakewa DUNIYARSA a sanda tayi masa
dadi.....irin kallon da mutum yakewa ruhinsa a sanda yake tsananin buqatarsa da
kuma sonshi. Duniyarsa rayuwarsa dama nutsuwarsa gaba daya yake gani tattare da
ita.
Daren
jiya yake tunawa,wani irin dare me tsayawa a tsakiyar zuciyar masoyi,ta shayar
dashi wani zazzaqan abu da bai taba hasashe ko mafarkin akwai irinsa ba sai a
lokacin.
Cikin
jikinta ta dinga jin kamar akwai wani ido na musamman dake kallonta. A hankali
tayi slow da hirar tana watsa idanunta cikin dakin,sannu a hankali ta hango
fuskarsa a tsakiyar qofar yana qare mata kallo. Murmushi ya sakar mata wanda ya
qara mata nauyinsa,sai ta danyi qasa da kanta,shi kuma ya tura qofar gaba daya
yana shigowa.
Tsam
momma ta miqe tana fadin
"Qaraso mana......dama masallaci nakeso mu wuce ai,ita
ta riqemu wai lallai zamu barta ita kadai,tunda gaka kazo alhamdulillah"
Momma ta fada cikin yanayi na surukuta tana maida takalmanta.
A nutse
ya qarasa gaban gadon ya bawa haneefa dake zamowa tana sauka daga saman gadon
hannu fuskarsa qunshe da murmushi yayi bump din hannunta data miqa masa yana
kuma amsa gaisuwar huda da basu hadu da ita dazu ba
"Muna da meeting anjima" Ya fada yana dubansu,sai
suka sanya dariya suna bin bayan momma bayan sun amsa masa da
"Yes hamma". Shi da ita duka da kallo suka bisu
har suka fice,shine ya fara dawo da dubansa kanta kafin itama a hankali ta
maida duban nata kanshi.
"Karki ma fara cewa zaki tambayeni akan mene" Ya
rigata fadi,sai murmushi ya qwace mata tayi qasa da kanta.
Idonsa ya
lumshe a kanta sannan ya taka a nutse ya jawo kujera zuwa gaban gadonta. A
hankali ya zauna yana sake matsowa kusa da ita har gwiwoyonsu na gogar na
juna,ya saka lausasan tafukan hannayensa a nutse ya kamo nata cikin nasa yana
murzawa a nutse.
"Ameenatu" Ya kirata a tausashe murya a karye
kaman wanda baison kowa yaji sirrinsu. Kiran da yayi mata har cikin tsokar
naman jikinta,ya kuma aike mata da saqo ta cikin jinin dake gudu a jijiyoyin
jikinta. Labbanta ta motsa kadan tana amsa masa da
"Na'am" Sai ya lumshe idonsa labban nata suna
daukan hankalinsa.
"Ina dauke da wani albishir ameenatu,yayi girma da
nauyi sosai a qirjina" Ya qarasa fada yana zame hannunsa daga cikin
nata,sannan ya maida kansa ya kwantar saman cinyoyinta kamar wani qaramin yaro.
A hankali
ta daga hannunta ta dora saman sumarsa tana nutsa yatsunta a ciki,laushin sumar
da santsinta suka ratsa yatsun nata,sai suka sauke ajiyar zuciya lokaci guda
shi da ita kowa yana jin soyayyar dan uwansa tana keta jininsa.
"Ameenatu wannan zuciyar da wannan gangar jikin duka
naki ne.....kulawarki take buqata kici gaba da bata muddin kinaso ta rayu yadda
ya dace" Ya fada yana jin yadda bugun zuciyarsa ke daduwa daga yadda take
yamutsa sumar kansa kawai.
"Zaka samu sabreen fiye da yadda kake fata.....zaka
samu dukkan wani cikar burikanka a tattare da ita.....harma abinda tunani bai
taba baka ba". Maganarta ta tsumashi sosai,ta kuma sakashi daga kanshi
daga cinyarta. Idanu ya zuba mata sosai yana kallon qwayar idanunta,sai itama
ta samu kanta da mannewa kallon nasa,kafin ya miqe a hankali tsaye a gabanta.
Hannuwansa ya miqa mata,sai itama ta aza nata ciki ya tashe tsaye sannan
ya buda qirjinsa ya sanyata a ciki ya maida hannuwansa ya lullubeta da kyau.
Ajiyar
zuciya ce ta subuce masa,ya kwantar da kansa saman kafadarta.
"Sabrrrrr........kinsan kin bani wata kyauta da ba wani
dan adam daya taba bani makamanciyarta?" Ya soma da jefa mata tambayar
data kasa gane ma'anarta. Shurunta ya fahimtar dashi cewa ya sanyata a duhu,don
haka ya zare jikinsa a hankali sannan ya juyata ya rungumeta ta baya yana sake
nutsata sosai cikin jikinsa. A tausashe ya dora duka tafin hannunsa saman
mararta,ya dora habarsa saman kafadarta yana saka tausasan labbansa saitin
kunnenta.
"Sabrrrrr......you're pregnant......ciki ne dake,cikin
muhammad jadda......zaki zama uwar 'ya'yana ameenatu". Wani irin abu ne ya
tsarga mata tun daga tsakiyar kwanyarta har tafin qafarta,bugun zuciyarta ya
qaru sosai. Samun kanta tayi da saka nata tafin hannun saman nasa dake mararta
tun dazun,ta kasa fadin komai,don duk kalmar data kamo sai taji ta qwace
mata,tana ci gaba da sauraren saukar numfashinsa cikin kunnenta.
"Are you happy sabrrrrr?" Ya tambayeta a raunane
yana fatan ya sameta cikin irin yanayin da yake jin kansa shima.
Kai ta
gyada a sanyaye,tanajin wani irin yanayi yana ratsata,mamakin yau itace wai
dauke da ciki?,itama zata zama UWA?,zata haifi d'a ko 'ya a cikinta?,abun kamar
cikin mafarki.
"Alhmdlh" Ya fadi yana sauke mata tattausan kiss a
wuyanta,a hankali kumya ja dawo da ita tana facing dinsa sai ya rungumeta tsam
a jikinsa.
Shuru ya
ratsa tsakaninsu na sakanni,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa ta cikin
kunnuwanta dame kwance a qirjinsa,sosai kaman akwai wani abu dake taba zaman
lafiyarta,kusan minti biyu sannan ya sauke sassauqar ajiyar zuciya a sanyaye
sannan ya dagata daga jikin nasa yana kallon fuskarta. Qwayar idanunta ya
laluba ya saka nashi a ciki,da wani irin coolness ya sake kiran sunanta.
"Kinji yadda zuciyata take bugawa ko?" Ya jefa
mata tambayar yana lalubar tafin hannunta ya matse gam cikin nasa. Kasa amsa
masa tayi da baki sai kai data gyada mass,saboda cikin idanunsa abubuwa ne masu
yawa ta gani suna yawo.
"Sabrrrr.....na gode da kika karbi ajiyata da sauri
haka......inajina kaman ni kadai nake rayuwa cikin duniya......ashe rashin
haduwa da tawa DUNIYAR shine sila......sabrrrr......bansan dame zan saka miki
ba......bansan kuma da meye zan gode miki ba....kome na kalla sai naga kamar
yayi kadan,alfarma daya kawai nakeso ki yiwa rayuwata.
Kallonsa
da kalamansa gaba daya qara kashe mata jiki sukeyi,mamakin irin tsananin son da
yakewa yara ne yake sake kamata,ta motsa labbanta a hankali
"Tame?"
"Kiyimin alqawari zaki rayu dani....kiyimin alqawari ba
zaki taba rabuwa dani ba.....kiyimin alqawari zaki zauna dani,da dadi ko
babu.....cikin wadata ko talauci.....sabrrrr kiyimin alqawari ba zaki taba
tafiya ki barni da yara ba.....zaki zauna dani dasu a duk yadda nake ko suke,mu
rainesu tare.......kiyimin wannan alqawarin sabrrrr cikin wannan garin me
tsarki". Idan ba qarya idanunta sukayi mata ba hawaye ne kwance cikin
idanun muhammad jadda din......taja numfashi sosai har kaman kayan cikinta zasu
hade waje daya. Ita daya ce mutum na farko a duniya data taba ganin wadannan
tsadaddun hawayen da suke zuba SILAR QAUNA daga idanun me jadda......tana fata
ta zama mutum.na qarshe da zata gansu,kuma ta zama sila na goge hawayen daga
idanunsa gogewa ta har abada.
Abu daya
ta lura dashi har yanzu yana da tsoro game da halin mata......har yanzu wannan
ciwon da maamah ta dasawa rayuwarsu yana masa zugi da radadi.....har yanzu yana
jin kaman abinda ya faru da abbansu zai faru dadshi,a yanzu haka a shirye take
ta goge masa dukkanin wannan fargabar da shakkun,don haka ta zame hannuwanta
daga nashi,ta sulale tana duqawa saman gwiwoyinta,sai ya gaza tsaiwa ya silale
shima ya bita.
Hannuwansa ta riqe da kyau tana kallonsa cikin tsakiyar idanunsa.
"Allah ya zama shaida.....annabin Allah ya zama
shaida,ni ameenatu sabreen na shirya rayuwa dakai da dukka abinda zamu
haifa......na sadaukar maka da dukka rayuwata sadaukarwa ta har abada......dadi
ko wuya sunyi kadan su raba tsakaninmu.....zan zauna dakai tamkar dominka kadai
aka halicceni,bazan barka ba muddin bakai ka buqaci hakan......". Ai bai
iya barinta ta qarasa fada ba ya hade bakinsu guri guda.
Sai
daya tabbatar ya kwashe ragowar maganar tass daga bakinta sannan ya zare
bakinsa daga nata yana kallonta da birkitattun idanunsa.
"Ta yaya zan iya rayuwa ba'a duniyata ba?.......ta yaya
dan adam zai rayu babu duniyarsa?,indai babu ta yadda hakan zata kasance....to
ki sanya a ranki ni Muhammad jadda don ke kadai MAAMAH ta haifeni".
Batasan sanda ta zube saman kafadarsa ba tana jin wani irin alfahari yana
ratsata,tana jin tabbaci da yaqini suna ratsata.....ashe akwai sauran maza irin
muhammad jadda din?.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 117
117
Guri kawai ta
samu ta zauna cikin dakin daya kasance ita daya ce qwallin qwal a ciki. Duk
yadda taso ta cinye ta kuma jure ta kasa,bata ankara ba kawai taji ta fashe da
kuka.
Ta yaya
haka zata kasance?,bata tsira da komai ba sai hawan jini?. Wanne irin kafaffen
yaro ta haifa?.....aure tsakanin musaddiq da amna?,wacce irin asara ke
bibiyarta har haka?,da gaske kamam yadda boka ya gaya mata taurarin nasararta
ke bacewa?,taurarin nasararta ke dakushewa?,ina dukka kaifin hankalinta da
zallar iya takunta suka tafi?(ta mance cewa shi Allah gwanin hikima ne,yana iya
yiwa bawa talala,yayi shekaru aru aru yana zalinci,a nasa hangen da tunanin
nasara ce,sai Allah ya barshi da wayonsa da tunaninsa,ya turo.masa nasara a
gabansa,plan dinsa yayita tafiya daidai,kwatsam idan yaso kamashi zai da
damqeshi a tsakiyar wannan plan din da shirin nasa da yake tunanin sune mafita
a gareshi,sai ya zurma yayita bundum bundum. Idan yana da rabo sai ya gane
zunubansa da kuma kusakurensa yayi gaggawar tuba....idan baida rabo
kuwa,zaiyita ganin INA DA SAURAN DAMA,INA DA SAURAN LOKACI yana tsaka da wannan
lissafin sai ubangiji yayi ram dashi,dauri gaba dauri baya,me kwanceshi kuma
sai ubangijin daya qulle abinsa. Duk runtsi.....duk tsanani,duk yadda za'a je a
dawo karka yadda ka cuci kowa,daka cuci kowa gwara kowa din ya cuceka. Duk
juyin da za'ayi ka tabbatar zuciyarka wankakkiya ce......kana bacci amma sai
ubangiji ya zama jinka ya zama ganinka,ya zama me jagorantar
al'amuranka,ubangiji ka barmu a naka duniya da lahira,karka bari duniya da
abinda yake cikinta ya rufe mana ido don girman zatinka,karka bamu damar cutar
kowa don isarka🙏🏽🙏🏽🙏🏽).
Abune a
rayuwarta data manta rabon data yishi wato kuka,shekaru masu yawa da suka shude
mata,amma sai gashi yau tana zubda hawaye sanadin anni amna da sabreen.
"Lallai dole fansa ta biyo baya.....lallai dole ku biya
bashi da fansar zubar wadannan hawaye......dole sadaukarwa ta biyo
baya.....wala'alla akwai rayuka da zasu salwanta......rayukan da shudewarsu
shine silar wanzuwa da samun nutsuwar zuciyata" Ta fadi a fili tana kallon
idanunta da suka tasa saboda kukan data share mintuna tana yi.
A
gaggauce ta sake goge fuskarta ta,sannan ta koma wajen luggage dinta ta soma
ninke kayan ciki tana zuba wadanda suke gefen gado da kuma cikin toilet din
dakin. Tanajin ta qagauta gari ya waye,tana jinta.kaman saman qaya,a jikinta da
ruhinta takejin bata da wani sauran zama a garin,bata da sauran abinda ya rage
mata da zata zauna tayi cikin qasar(subhanallah).
★Sau tari wata
soyayyar tana zamewa madubi kuma abar sha'awa ga wanda ke gefe yana kallo. Wani
memories din na wasu masoyan kan samu wajen zama na din din din cikin kwanya ya
kasa gushewa saboda girman tsumammiyar soyayya zallar kulawa da qauna me gusar
da hankali saboda tsananin kusanci da kulawa tsakanin masoya.
Fu'ad da
sabreen......soyayyarsu ta zamewa wasu tamkar makaranta.....ko kuma allon da
zaka kalla ka karance ilimin dake shimfide a kanshi.
Wucewar
maamah Nigeria ya samar da nutsuwa me tarin yawa ga wasu zukata,wadanda sam
basusan gaibun dake tattare da tafiyartata ta barsu ba. Wani lullubabben gaibu
me cike da duhun sirrikan da ita kadai ta barwa zuciyarta shi.
Samun
sararinta da gushewar wanzuwarta a family din ya bada damar baje kolin soyayya
masu dauke da nau'ika kala kala. Sabreen da fu'ad,suna rayuwa da nunawa juna
soyyaya da kulawa tamkar sun manta da akwai wasu halittun dake gewaye dasu suna
tasu rayuwar.
Sau tari
idan fu'ad yayi wani abun saidai kowa ya runtse idanunsa,don ba wanda yake gani
sai sabreen da cikinsa dake manne a jikinta. Gaba daya kaman ya mance da kowa
sai ita sai hidimarta,wani lokacin hankali yafi zuwa jikinta akanshi,don takan
tuna da anni a wajen ta rage wani abun.
Duk da
abun ya zowa anni a sabo,amma saita zama suruka me yawan bada uzuri da dauke
kai. Bata shiga tarayyarsu ko kadan,saita dinga nesa nesa dasu gudun ji masu
kunya duka ita dasu.
Wannan
soyayyar sai ya hura wuta biyu......tsohon tsumin soyayya ya balle tsakanin
musaddiq da amnansa,duk da cewa daga nesa nesa ake komai don anni bata bari
abun ya zurfafa da yawa. Su dinma duk yadda sukaso su boye dole ita soyayya
bayyana kanta takeyi koda an boyeta. Sannu a hankali sai wata wutar munafukar
soyayyar ta soma kunnuwa kuma daban tsakanin saddiq da huda. Duk wani nuqu nuqu
da sukeyi hakan bai hana sabreen karantar komai ba,ranar sun dawo daga
masallaci take tseguntawa fu'ad hancinta ya lakace mata.
"Kin iya sa ido duniyata.......banda nidin ina da
qarfin kurwa banjin zan qwace filin soyayyar da akewa su huda.......Allah ya
taimakeni nayi hasashen tsaf zaki iya guduwa ki barni.......nayi miki yankan
baya na kawo miki su.....to me ya rage?". A mamakance ta zare idanu dariya
tana qwace mata,sai ta boye kanta cikin qirjinsa tana qoqarin musanta maganar.
Saidai
kuma a zahirin gaskiya cike take da mamaki,wanne irin mutum ne fu'ad din me
tsananin kula har haka?,ta yarda dari bisa dari baya wasa da duk abinda yakeso.
Duk
wadannan abubuwan da yake faruwa bai hanasu ibada ba tuquru........zamansu
tsakanin makka da madeena yafi yiwa fu'ad dadi sama da kowa,tunda ko banza yace
za'a qiri halittar danshi ko 'yarshi a guri me tsarki da tsarkakken ruwan
zamzam wanda shine komin sabreen. Komai da zamzam takeyi,shine ruwanta nayin
komai,iya falalar ruwan zam zam kawai ya sanya yake qara jin nutsuwa da zamansu
a nan.
Tuni ya
mata register da komai na zuwa awo da haihuwa,don yace indai yana da rai da
lafiya to tabbas a garin madeena yakeso a haifa masa yaransa,ya tsara komai ba
tare daya gayawa kowa bama.
*_K'ADDARA KO GANGANCI?_*
_KALLON KALLO_
Sau uku tana
rolling sassalkar luxury Egyptian abaya din tana warewa. Kawai sai tayi zaune
gaban madubin tana ware hannuwanta gami da binsu da kallo.
Batasan
me yasa ba......batasan kuma me yake faruwa ba,shagwabata da yayi da yi mata
hidimar komai ne sila ko kuma cikin jikinta ya sanya ta zama raguwa?.
A karo
na hudu ta sake gwadawa sai veil din ya sabule salin alin daga hannunta. Ido ta
zubawa fuskarta,sai taji hawaye kawai ya kubce mata.
Murmushi
ya saki yana qarasa sanya link din hannun kuftan jikinsa,ya soma takowa a
hankali zuwa bayanta. Tun daxun da taketa drama ita da dankwalin yana
kallonta,yasan qarshen maganar dama ta sanya kuka tunda ta zama rigimammiya ta
gaske.
Kafadunta
ya kama ya tasheta tsaye,suka hada ido sai yayi qoqarin danne dariyarsa,saidai
tuni ta riga ta gani.
Daga
hawaye sai ta sakar masa kuka me qaramin sauti.
"Subhanallah......me kuma nayi?" Ya fada yana dora
damuwa saman fuskarsa duk da da gasken dariya yakeson yayi.
"Ya isa....am sorry if I offend you" Ya fada yana
sakata a qirjinsa. Shaqa daya ta yiwa turarensa nutsuwa ta fara saukar mata,sai
ya bata lokaci sai daya tabbatar ta nutsu sannan ya dagata yana duban fuskarta.
"To mene ne?,.....uhmmm.....tell me" Tabe baki
tayi,ta miqa hannu taja kumatunsa.
"Ba mayafinne yaqi dauruwa ba,sannan kuma kai kazo
kanamin dariya saboda ina ramewa kai kuma kina qiba". Wannan karon kecewa
yayi da dariya sosai harda riqe ciki. B wani bane ya jawo masa wannan jagwal
din ba sai amna,haka kawai ta sashi gaba vanilla ice cream takeson sha,suka
yiwa anni wayo suka fice wadda ta jima da hanata shan kayan zaqi da sanyi. Koda
sukaje kasa sha tayi.ma gaba daya sai ya fita a ranta,shi kuma duk da bai
dameshi ba amma sai yaji ya masa dadi,yasa aka kawo masa ya soma sha,ashe tana
ankare,ke amna kika ce
"Hamma madeena ta karbeka Allah,ka karbe jikin adda ka
hada da naka,kanata kumatu" Ta fada tana dariya.
"Lovey dovey.....kin manta ni yayan mijinki ne
kenan?" Ya fadi hakanne don shine abu daya yanzu da yake kashe bakin
amna,ya kuma fadi hakanne don ya fuskanci sabreen din har ta kumburo fashewa
kawai take jira tayi. Ashe abun dashi ta kwana sai yanzu ake fashe masa shi.
Sulalewa
yayi ya durqusa gabanta,ya zagaye hannunsa a bayanta yana dora fuskarsa saman
mararta.
"Kazo mu bawa mama haquri....mun hanata qiba mun hanata
cin kayan dadi....mun tuba....zamu gyara halinmu" Ya qarasa maganar yana
hade hannuwansa guri daya.
Da ido ya
bita ganin daga kuka ta koma buga murmushi,ya girgiza kai kawai a ransa yana
gulma,wato me ciki sai a barta kawai.....abun kuka ko bacin rai baya mata
kadan,cikin dabara ya jata ya sauya mata yalwataccen mayafin rolling din ya
daura mata da kanshi,don bayason wani sashe na jikinta ko kadan ya fita wani ya
gani.
Yana
gama mata ana knocking qofar,yasan waye farouq ne,qiri da muzu ya zama
fusataccen qarfi da yaji,yace fu'ad ya jawo masa raini,ya hada tuxurantaka da
aure da qannensa,in fact ma qanin bayansa ya rigashi amsa sunan me aure,wannan
ta saka dole qasa daya data rage musu akayi cancelled trip din sai bayan wani
lokaci,aka aikewa da iyayen fanna date na bikin sati biyu masu zuwa wato sati
biyu da komawarsu nigeria kenan.
Hannunta
cikin nashi yadda suka saba suka fito a dakin,ta zame hannun nata a dabarance
ta qarasa gaban anni ta gaidata,ta gaida momma wadanda zasu sauka duka a
nigeria,da yammaci kuma jirgi zai wuce dasu mali saboda washegari huda zatayi
ton prints na jarabawar kammala secondary school.
Haka suka
wuce airport cikin motocin da a nan qasar yake barinsu sai kuma zuwa na gaba.
Anata zuba
soyayyar munafunci tsakanin amna da musaddiq,huda da saddiq daketa babbasarwa
kaman ba komai tsakaninsu,angon gobe farouq kuwa anata sallama da fanna ta waya
shima ya bude wuta sosai don shirye shirye sun gama kammaluwa,ranar kawai suke
jira.
Ita
kuwa kanta yana kwance kawai saman kafadarsa. Tun bata saba ba har ya riga ya
saba mata,wata kasala take fama da ita,bata iya cikakken zama ba'a jikinsa.
Tunda
jirginsu ya tashi take jin gabanta yana faduwa lokaci lokaci,tadan rufe
idanunta kadan tana jan sunan Allah,ko shima sabuwar faduwar gaban tana cikin
laulayin ta yiwa kanta da kanta tambaya.
Idonta ta
rufe tana fatan bacci yayi awon gaba da ita wai ko zata samu sassaucin abinda
takeji,tana iya jin sanda ya sanya blanket ya lullubeta,sannan ya sake rufeta
da faffadan qirjinsa yana rufeta tsam cikin jikinsa,ajiyar zuciya me sanyi ta
subuce masa ya dora habarsa saman kanta a tausashe.
Cikin
zuciyarta take roqon Allah......kada ya bata ikon butulcewa wannan bawa ko juya
masa baya.......ita kanta wani lokaci irin yadda yayi nisa a soyayyarta tana
jin kamar tata zuciyar zata narke a kansa. Tsakanin ita dashi batasan waye yafi
wani yin nisa ba,waye yafi wani yin zurfi bs,fatanta kawai shine kada su zama
masu butulcewa juna a tsakaninsu.
Tafiyar awanni biyu jirginsu ya sauka a filin sauka da tashin jiragen
sama na malam aminu kano dake kano. Sai takejin farinciki yana ratsata duk da
ta baro wani guri mai muhimmancin gaske a rayuwar duk wani musulmi.
Abu
guda daya da yaci gaba da farautarta shine faduwar gaban dake qara tsanantar
mata,duk sai take jinta a rikice har zuwa sanda suka qaraso inda jerin gwanon
motocin jadda diamond suke jiran qarasowarsu.
Kusan
dukkanin guards dinsa sun zo tararsa cike da girmamawa da kuma kewarsa da
sukayi na tsahon lokaci.
Sabule
hannunsa yayi daga cikin nata,abinda ya sanyata daga kai ta kalleshi kenan.
Murmushi
ya sakar mata me taushi yana dubanta.
"Zaku fara yin gaba saboda ki samu zama dasu huda kuyi
sallama......zan qaraso yanzun......nasan a gajiye kike amma ma'u ta tanadar
miki komai.....kada kice zaki jirani,kiyi wanka kici abinci kiyi bacci
sosai......yau akwai biyan bashi" Ya furta maganan qarshen qasa qasa yadda
ba wanda zaiji musu sirrinsu.
Duk da
yadda gabanta ke tsananta faduwa,duk da yadda takejin kaman zaini wani wawan
nisa da ita......irin nisan da takejin tazararshi tayi yawa amma saida murmushi
ya subuce mata. A tausashe yayi kissing goshinta yana dubanta. Raunin da yake
ganin cikin idanunta shi kansa baisan na meye ba,ya saka hannu da kansa ya bude
mata qofar motar dasu huda ke jiranta,ta shiga,ya tsugunna ya tattare mata
abayarta data fito waje ya maida ciki.
"Kada ka dade" Ta samu kanta da fadi masa a karye
sanda yake shirin rufe mata qofar
"In sha Allah" Ya bata amsa yana jin dadin kulawa
da damuwa dashi din data nuna,ya rufe qofar a tausashe sannan yaja baya ya kira
abdulgafar sukayi magana,ya kira abdulbasit shima sannan ya sallamesu suka
tashi motocin da zasu kaisu gida,ya rage sauran wadanda zaiyi amfani dasu ne
kawai.
Ta cikin
side mirror din motar tasu ta zuba masa idanu,suna sakeyin gaba yana nisa da
madubin har ya bacewa ganinta,saita lumshe idonta tana sauke nannauyar ajiyar
zuciya.
Tana jin
karadin su huda sanda suke fita daga airport din amma ta gaza saka baki a
hirarsu,kawai tana sauraren yadda zuciyarta take bugawa ne.......har zuwa sanda
qarar harbin bindiga har sau biyu ya sauka a kunnenta.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,hasbiyallahu
la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ta fada
da wata irin zabura tana ware idanunta gami da miqewa ta zauna sosai faduwar
gabanta yana ninkuwa.
Salatin
da taja shi ya sanya kowa a motar ya dauke wuta,momma dake seat din gaba ta
waiwayo da hanzari tana kallon fuskar sabreen din. Huda ce tayi qarfin halin
fara tambaya
"Lafiya adda?".
" Qarar harbin bindiga huda......bakuji ba?" Ta
tambayesu a rude tana raba idanunta akan fuskarsu.
"Nidai banji ba" Huda ta fada tana girgixa kai
"Naji....harbi ne,amma kamar nesa da nan" Momma ta
fadi tana dubansu daga inda take
"Nima naji momma" Nadra itama ta fada tana
dubansu. Kan hanya hankalinta yakai,sai taga kaman driver din nasu ya qara
gudun motar fiye da yadda suka fara tafiyar,hankalinta taji yana neman dagawa
sosai,sai ta kalli su momma din tanajin kaman haki yanason kamata saboda
tsananin bugawar da zuciyarta takeyi.
*_Tabdijan.......meke shirin faruwa ne?,me kuke hasashe?,me
karatu mu hadu gobe idan me duka ya kaimu_*
*_akwai yaqi kenan_*
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 118
118
"Momma ba'a nesa harbin nan yake ba......koda a nesa dinne bawai
ness can damu ba......mun baro su hamma a ciki momma.....bamusan me yake faruwa
ba.....driver!" Ta ambata da qarfi kaman numfashinta yana son qwace mata.
"Yes madam" Ya fada da dan qarfi shima yadda zata
iya jiyoshi.
"Mu koma mu duba boss......qarar harbi nakeji".
" Am sorry maaa.......nima naji,kuma umarni ne na boss
din shi ya horemu,duk sanda mukaji abu irin wannan kada mu sake mu koma da
baya......kuma ko a tsarin tsaro ma hakan ganganci ne.....kiyi haquri mu qarasa
gida.....we are safe in sha Allah". Yana kaiwa qarshen maganarsa qarar
wani harbin a jejjere har guda biyu ya sauka a kunnensu. Qarasa gigicewa tayi
gaba daya,jikinta da muryarta gaba daya suka dauki rawa.
"Ta cikin airport dinnan ne momma.....idan safe nake
hamma fu'ad fa?" Ta jefawa momma tambayar cikin rauni hawaye na gangaro
mata.
Girgixa
kai momma tayi wadda ke qoqarin boye nata tashin hankalin.
"Bazaiyiwu a koma ba kaman yadda kika ce.....hasalima
baki da tabbacin a inda suke abun yake faruwa ko wani shiyyar ne na
daban.....koda a inda suke ne ma shima bazaiso ace koma meye ya hada dake
ba....." Momma take fadi cikin son lallashinta. Sam hankalinta ba'a
jikinta yake ba,bata ma kama maganar momma ba saita jawo jakarta jikinta dukka
yana rawa ta fiddo wayarta tana cewa.
"Gabana yanata faduwa ne momma,tabbacin akwai wani abu
da ba daidai ba" Tayi maganar tana zaro wayarta da zummar kiran number
fu'ad din.
Abun
takacin abinda kuma ya sanya a karan farko tayi Allah wadai da halinta shine.
Ba number wata number da tayi kama da tasa cikin contact dinta,sai a sannan ta
tuna,waccan tafiyar da yayi ya kirata sau daya,batayi saving number nasa
bama,kuma koda ta duba call log babu number a wajen.
Kuka ne
ya qwace mata ganin yadda suke qara nisa da airport din ba tare da tasan halin
da yake ciki ba.....don gaba daya jikinta yana gaya mata akwai gagarumar
matsala.
"Ni ku saukeni......xan koma na dubashi,zan tabbatar da
lafiyarsa saimu taho tare dashi" Ta
fada muryarta na rawa.
"Kiyi haquri madam......aikina bazai cika ba saina
kaiki gida lafiya.....aikata hakan zai zama zunubi mafi girma a wajen boss,har
gwara na kaiku gida na miki alqawarin dawowa na duba miki lafiyanshi".
Abdul rauf ya bata amsa shima yana jin damuwa sosai da fargabar kada wani abu
me muni ya faru da ogansu.
Sam bata
gane abinda momma ke fadi mata ma,ta rarumo wayar ta soma lalubar number anni
ko amna. Number amna ta fara gani saita kira kawai tana fatan ta samu su daga
don su suna motar gabansu. Bugu daya aka daga,anni ce ba amna ba,kai tsaye ta
fara magana.
"Anni harbi akeyi cikin airport anni.....kice musu mu
juya mu koma,munbar hamma a can,dukkanmu mun taho saura shi kadai". Asalin
damuwa anni tana ciki,amma ta danne don kada ta kashe mata qwarin gwiwa.
"Kiyi haquri sabreena......in sha Allah yana lafiya,don
bamusan me yake faruwa ba,da mutane da yawa a ciki bamusan akan meye harbin ya
kasance ba....."
"Anni jikina yana bani wani abu.....anni don Allah ku
barni na koma"
"Ameenatu" Anni ta kirata da asalin sunanta.
"Na'am anni".
" Kita karanta lahaula walaquwwata illa
billah.......bari mu qarasa gida saimu laluba abinda ya faru kinji?". Ba
yadda zata iya ci gaba da musu da annin,don haka tace mata to kawai tana sauke
wayar daga kunnenta ba tare data kashe ba.
Hannu
momma ta miqa ta dauki wayar suka fara magana da anni.
"Ta shiga damuwa,don Allah bahijja ki bata baki,kinga
ba ita daya bace,a irin wannan yanayin bata buqatar tashin hankali".
" In sha Allah anni" Daga haka ta ajiye wayar ta kamo hannun
sabreen din.
Duk wani
kalar bada baki da bada haquri momma ta yiwa sabreen din,saidai kawai tana jin
momma dinne bawai don ta gamsu da dukka abinda suke fada ba,tana ji a jikinta
akwai wani abu maras kyau daya taba hammanta,a cikin zuciyarta da ruhinta
takejin hakan.
Yadda anni
taji muryarta ya sanya tayi ma abdur ra'uf magana dukansu suka wuce zuwa
mansion House din alhaji hamza kibiya.
A babban
parking lot na gidan motocin dukka suka tsaya. Abdulgafar ya qaraso ya bude
mata side dinta,su huda da momma suka fita ta daya side din.
Da qyar
ta miqe bayan ta zuro qafafunta waje,jikinta idanunta dama zuciyarta gaba daya
takejin sun mata wani irin nauyi. Duba daya zakayi mata ka fahimci hankalinta
baya jikinta,daga airport din zuwa gidan kuwa idanunta sun fara tasawa saboda
kukan data matsawa kanta dashi. A hankali da wani irin sanyi ta zube idanunta
akansu anni wadda ke tsaye ita da musaddiq da saddiq,dukkansu su biyun waya
sukeyi,amna kuma da alama tanata qoqarin samun wata number ne amma kiran yaqi
shiga.
"Anni na kasa samun wayarsa,a kashe take" Muryar
amna kenan data sakata jin wani jiri yana niyyar kayar da ita. Baya ta koma
kawai ta jingina da motar data fito a cikinta,tana jin momma sama sama tana
riqe hannunta.
"Na samu Jordan" Muryar saddiq kenan daya fada da
wani irin kuzari,abinda ya sanya anni da su amna duka dawowa gabansa suka
tsaya.
Dif sukayi
suna jiran joradan ya daga,amma harta qaraci ringing dinta ta katse bai daga
ba. Idanu sabreen ta mayar ta lumshe,tana jin yadda bayan wucewar kowanne
daqiqa zuciyarta ke ninka gudu kaman zata tsaga qirjinta ta fito,tana jin wata
sallamawa tana ratsata,tana jin cewa da gaske wani abu ya taba mata
hammanta......da gaske wani abu ya faru dashi cikin airport din,sai qafafunta
suka fara rauni tana jin suna fara gazawa wajen dauke nauyinta.
A
kunnenta kira na uku ya yanke ba tare da jordan ya daga ba.
"Wallahi shine.....Allah wani abun ya faru
dashi.....naji a jikina fa" Ta fadi da qarfin muryar da har na nesa saida
suka jiyota,wanda kafin su huda sukai ga riqeta ta sulale a wajen tana sakin
wani tsumammen kuka tana jin mararta na riqewa gam.
Da wani
irin sukunannen gudu anni ta qaraso,suka dagata ita da momma Hankalin annin
yana tsananin tashi.
"Karkiyi mana haka sabreen......ba abinda ya faru dashi
mana.....ga jordan nan an samu wayarsa dagawa ne baiyi ba". Idanunta fal
da kuka wadanda zuwa yanzu sun canza launi zuwa red ta kalli anni.
" Indai da gaske lafiya qalau ne ya daga wayar yayi
bayani mana?,ya daga wayar yace ba abinda ya faru mana anni?,me ya hana wayar
hamma shiga bayan sanda muka fito a jirgi ma ya amsa kira?". Rudata kawai
tambayayoyin sabreen sukayi gami da sage mata gwiwa,saita rasa amsar bata. Duk
da haka ta rungumota jikinta tana cewa.
"Amma kamar fatan alkhairi ya kamata kiyi ko sabreen da
hasashen alkhairi?"
"Na kasa anni.....zuciyata ce taketa gayamin akwai
abinda ya faru dashi,ba laifi na bane......DANGANTAKAR ZUCIYA ce tsakanina
dashi.....ko meye ya sameshi zuciyata zata gayamin saboda alaqar dake
tsakaninmu" . Sosai anni ta lura kaman hankalinta yana neman gushewa
ne,don haka ta sake riqeta da kyau tana cewa.
"Shikenan,mu shiga ciki,zan tabbatar miki lafiya qalau
yake.....zan kiramiki shi kuyi magana". Tamkar raguwar ciwo ko zugi daga
kasu daya cikin dari shine kawai d'an abinda furucin anni ya yiwa sabreen cikin
zuciyarta. Anni da momma suka riqeta da kyau kowa cike da fargaba duba da
abinda yake jikinta tattali yake buqata kaman yadda tun a madina likita ya gaya
musu suka wuce da ita zuwa ainihin babban falon gidan.
Baya kadan
anni ta dawo tayi magana da saddiq kan yayi duk yadda zaiyi ya samo ainihin
abinda ya faru sannan ta kira musaddiq suka wuce akan yazo ya zauna yayita
kiran fu'ad har sai an sameshi ya daga suyi magana ko hankalinta zai kwanta.
Kaman
yadda hawaye yaqi tsaiwa a idanunta haka ma kuka yaqi dakatawa. Ruwa me sanyi
sanyi anni ta saka aka kawo Mata,ta tsiyaya mata ta miqa mata tana fadin.
"Karbi kisha tukunna ko zuciyarki zatayi sanyi"
Kai ta girgiza kawai fuskarta shabe shabe da hawaye,abinda yake taba zukatan su
huda kenan har sai da anni ta sanya ma'u ta janyesu zuwa wani falon na daban.
"Ko nasha anni bazai iya wucewa ta wuyana ba.....inaso
nasan halin da yake ciki ne kawai". A sanyaye musaddiq daya gaji da kira
ana ce masa a kashe take ya dubeta,sai kawai ya ajiye wayar ya miqe tsam.yana
duban anni
"Ina zuwa" Ya fada yana fita da sassarfa daga
dakin. Kiransa anni takeyi saboda jikinta ya bata abinda zai aikata daga
yanayin tashin nasa,amma baiko waiwayo ba bare ya dakata.
"Innalillahi wa inna ilahi raji'un" Anni ta fada
tana sadda kanta qasa. Awa guda kenan amma ko daga security dinsa da guards
dinsa ba wanda ya samu labarin abinda ya faru. Sun koma airport din amma tun
daga tafiya me nisa ma an hana shiga gurin bare su binciki abinda ya
faru.....ina yake?,wanne hali yake ciki?. Duk da sun bayyana kansu a mazaunin
masu tsaron lafiyarsa amma an dakatar dasu an kuma basu haquri ance su jira,ko
meye ake ciki daga baya zasuji.
Zamewa tayi
sosai a nan inda tayi sallah tana kukan zuci,tana jin kamar zata hadiye
zuciyarta. Batasan ta inda zata fara rayuwa ba idan wani abun ya samu
Muhammad........batasan ta yadda zata iya karbar wannnan qaddarar ba.
Me yasa
rayuwa zatayi mata haka ne?,me yasa rayuwa zata zo mata da irin wannan yanayin
ne?,me yasa rayuwa take wasan kura da ita?,take nesantata da wadanda ta sanya
rai da fata me tsanani a kansu?,take nesantata da duk mutumin da zai jibanci
lamarinta?,duk mutumin data dora rayuwarta da burinta a kansa?.
A nan
tayi la'asar ba tare data ko motsa ba,anni tasa aka shigo mata da abinci amma
ko sha'awa baya bata ballantana tayi tunanin ci.
Xuwa qarfe
biyar ta koma tamkar ruwa saman abun sallar,zuciyarta na sake yayyankewa da
tsananin tsoro da tashin hankali.
Biyar da
mintuna anni ta sake shigowa. Duba daya zaka mata itama kasan hankalinta ba'a
kwance yake ba. Musaddiq da saddiq da baisan fitarsa ba har yanzu bai dawo
ba,hakanan tasa wayar still tana kashe shima tunda ya fita yabar gidan.
A sanyaye
ta qaraso gabanta tana qoqarin tattaro dukka dauriyarta waje daya,ta zauna a
qasa daidai saitin qafarta tana kallonta.
"Tashi ameenatu" Anni ta fadi cikin jarumta. Kaman
ba zata iya tashi ba ta daddafa ta tashi. Amanta uku ba wanda ya sani,abinda ta
dauka tayi adabo dashi tunda ta samu kulawa a madeena sai gashi tashin hankali
ya sanya ya dawo. A cikin aman nan guda uku ba kalar azabar da 'yan hanjinta
basu gani ba,don babu komai a cikin nata.
"Kinyi imani da Allah da ranar lahira?" Kai
sabreen ta gyada mata hawaye na fara taruwan mata.
"Kinyi imani da Allah shine me rayawa shine me
kashewa?,shike bada kariyarsa akan kowanne abun halitta?". Kai ta sake
gyada mata hawayen data riqe suna sauko mata.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 119
119
" To
inaso ki yarda da Allah ki kama ambatonsa....kibar masa kuma
lamarinsa.....karki dauki haqqin abinda ke kwance a mararki ta hanyar hana
kanki abinci.....don cin abincinki ko rashin cin ba abinda zai canza saima
cutar da yaronki,ki samu wani abu ko ba yawa ki sakawa cikin naki". Hawaye
sosai take tana kada kai.
"Ba hanya anni.....bana jin abinci xai samu hanyar wuce
kwata kwata".
"To ai akwai abu me ruwa ruwa a ciki,ki duba ko yaya
kisha" Ta fada tana buda kwanukan gabanta.
Lafiyayyen kunun gyada ne da yasha madara yayi fari sol,da kanta anni ta
zuba mata a mug ta saka sugar dan daidai sannan ta miqa mata.
Karba
kawai tayi tana wassafa yadda zata sanya a bakinta,kai.anni ta jinjina mata
cikin son bata qwarin gwiwa,wannan ya sakata kai mug din bakinta.
Kurba uku
kawai tayi ta dire,annin bata matsanta mata ba ta dauka kawai ta rufe ta bata
ruwa. Kurba daya shikam ta ajjiye,saboda batajin zai zauna a cikin ta. Bakinta
ya saba da zartsin zartsi na taste din zam zam. Annin ta fahimci haka,don haka
ta qwalawa ma'u kira tace ta duba store ta ciro zam zam babban roba. Ba jimawa
ta dawo dashi,annin ta bude ta tsiyaya ta bata.
Wannan
karon anci sa'a,tas ta shanyeshi ta ajiye cup din,hakan ya yiwa anni dadi,saita
matsa ta dauki counter tasbaha ta maqala mata a yatsunta
"Hasbunnallahu wa ni'imal wakil,wallahu galibun ala
amrih sau ba adadi" Kai ta gyada a hankali tana jin hankalinta yana
karkata ga addu'a maimakon kuka da bala'in tashin hankalin da takeji.
Sai da
anni taga ta kama sannan ta miqe a hankali ta nufi qofar ta fita tana rufe mata
da nufin dawo dasu huda ciki su tayata zama.
Fitar
anni da second talatin kadai wato rabin minti taji kamam muryar musaddiq cikin
kunnuwanta. Sakin counter din tayi ta miqe qirjinta na wani irin mahaukacin
bugu,cikin sanda kaman barawon daya shirya gagarumar sata ta nufi qofar,ta
kamata ta bude a hankali,sai muryar musaddiq din ta fito tas.
"Muje ka gayan me ya faru,koma meye banaso sabreen
taji" Taji anni tana fada.
Sakin
qofar tayi a hankali ta fara takawa tana biye da bayan annin,duk da cewa akwai
ginin hallway daya rabasu basa iya ganinta amma ita tana iya jinsu
sosai,cikinta hautsinawa yakeyi sosai,tana cike da tashin hankali da fargabar
abinda zataji daga bakin musaddiq din.
Hannun
musaddiq kawai anni ta kama kai tsaye ta ajeshi saman kujerun da suke
matsakaicin falon,tashin hankali da rudani sunaso suyi galaba a kanta amma tana
cinyewa.
"Gayamim musaddiq......ina fu'ad.....ina me babbban
suna?" Shuru ya danyi,yana juya yadda zai bata incomplete
information,saidai shirunsa zaifi zame mata damuwa sama da amsarsa
"Sun harbeshi" Ya fada a hankali kaman bakinsa
bayason fada.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Anni ta shiga
maimaitawa. Wani irin bugu maganar ta yiwa sabreen,abu na farko daya fara zuwa
kanta shine SUN KASHESHI.
Nutsuwarta da hankalinta ne gaba daya suka fara gushewa,sannu sannu
saita fara daina jin abinda musaddiq yaci gaba da fada.....duhu ya fara gilmawa
idanuwanta,ta suma sulalewa a wajen ta zube saman rug din.
"Harbin farko ya kauce basu sameshi ba,ya hangi
maharbin sai yayi nufin binsa shine ya sameshi a harbi na biyu dana
uku......suna tare da yaa farouq,tare ma suka yunqura suka bishin,amma yanxun
ba'a ga ya farouq ba,ba'asan ina yayi ba.....shi kansa hamman da jordan dinma
ba'asan ina akayi dasu ko yaya akayi dasu ba" Ya qarasa fadawa anni
maganar zuciyarsa tana girgiza.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Taci gaba da
maimaitawa tana jin zuciyarta na wani irin jijjiga kaman zata ballo daga
qirjinta ya fado.
"Musaddiq ina abbanku?" Ta tambaya saboda tana jin
duk wata jarumta tata da dabararta ta qare,tana buqatar tallafin abban a kusa.
Kaman yasan
shi take nema sai gashi ya sako kai,kai tsaye ta miqe ta nufeshi,bata kuma
tsaya bata lokaci ba ta fada qirjinsa hawaye yana sauka daga idanunta,wani abu
da bata taba yi ba gaban yaran tsahon shekarun.
"Ya isa ameenatu.....kiyi haquri.....duk inda suke da
halin da suke ciki za'a samosu in sha Allah,karki daga hankalinki da yawa,idan
hakan ya faru ita kuma sabreen muyi yaya da ita kenan?". Kiran sunan
sabreen din ya ankarar da ita,ta janye jikinta daga abban gabanta yana faduwa.
Sai sannan ta tuna tayita maimaita innalillahi da qarfi a dazun,wanda zai
wahala baikai cikin dakin da sabreen din take ba.
"Bari na dubota abba" Ta fada tana juyawa da
sassarfa tana nufar ciki.
Tuntuben da
tayi da ita shi ya sakata taja baya da sauri,kasa jurewa abinda idanunta suke
gani tayi,sai kawai ta saki qara tana kiran sunan abba a gigice.
Shima ya
kadu da jin qararta,wani abu da bai taba ji ameenatu tayi ba komai girman
jarrabawa,don haka da sauri yayo hanyar dakin musaddiq yana biye dashi.
"Maza jeka kira mommanta.....kada ka bari yaran su
biyoku" Abba yace da musaddiq saboda a yadda anni ta gigice yasan ba zata
iya riqe sabreen ba.
Ba shiri
momma data tayar da sallar la'asar din da bata samu daman yi ba sai sannan ta
sallame tabi bayan musaddiq. A gigice ta duqa gaban sabreen tana dagata,saidai
ba wani alamun numfashi a tattare da ita.
"Nutsuwa zakuyi ku taimaketa ta hanyar daukota mu wuce
asibiti da ita" Abba yayi qoqarin dawo musu da tunaninsu jikinsu.
Kaman gawa
haka suka dagata,suka wuce kuma kai tsaye bakin farfajiyar shigowa gidan,don
tuni musaddiq ya sanya an matso da mota gaban ginin.
Makeken
private hospital dinnan da babu kamarsa kaf Nigeria suka nufa da ita wato Noor
hospital. Idan ka shiga zakayi tsammanin kana qasashen qetare ne bawai a
Nigeria ba kuma gida kanon dabo.
Asibiti ne
da yake mallakin Muhammed fu'ad jadda.....amma a sirrance mallakar ta
kasance,ba kowa bane yasan da hakan. Duk wani kalar kayan aikin da bamu dashi
sai a qasashen qetare ya kawosu ya zuba don hana masu kudinmu fita neman magani
waje. Donsu din kawai dama yayi asibitin,don babu wani me qaramin qarfi da
zaiyi gigin kai kanshi nan. Saidai kuma kusan duka kudaden da ake samu ta
asibitin ana tafi dashi ne ta hanyar hidimar al'umma,don baya ci ko karban ko
sisi a ciki,saboda baida buqatarsu.
Dr hajar
da Dr mubeena ne suka karbeta,don ba wani likita namiji da yayi kuskuren zuwa
inda take,duk da dama kusan haka tsarin asibitin yake,mata likitoci mata ke
karbarsu,maza kuma likitoci maza.
Cikin
qwarewa suka shiga bata taimako don maido numfashinta kan saiti gudun rasa
abinda take dauke dashi,sun samu nasara saidai sun mata allurar bacci saboda ta
sake samun nutsuwa sosai,don ta shiga shocked ba kadan ba. Sunyi duk wasu gwaje
gwaje daya kamata,harda su scanning da basu tsaya anyi a madeena ba,saidai
abinda scan din yaketa nuna musu ya sanyasu a mamaki.
Hankalinta kwance take cikin dakinta tana ninke lace din data siya jiya
naira dubu dari tara da tamanin,ta kuma budeshi don ta tabbatar shi dinne.
Zuciya cike da saqe saqe da taraddadin cikar mission dinta da tafiyarsa
daidai?,ko kuma akasin hakan wato FADUWA wanda ko sunanta bata qaunar taji.
Har yanzu
zuciyarta tana mata susa idan ta tuna fattatakar da bokan yayi mata,sam yama qi
saurarenta,wanda ita bataga dalilinsa naqin sauraron nata ba bayan tana cika
masa aljihu da kudi. Ta dora kyakkyawan zato akan hajja....duk da tasan mutum
ne shi da ba'a sakashi ba'a kuma hanashi......amma tana da zato me girma akan
hajja din,wannan ya sauya akalar tunaninta na taci gaba da riqon laila.
Zuwa yanzun
lailan ya fara zame mata kaya,don ba wani abu da zata iya aiwatarwa na qashin
kanta saita tambayi maamah din. Daidai da cin abinci wannan sai data
fatattaketa,tace kada ta qara tambayarta don zataci abinci,taci ko kada taci
wannan ya rage nata.
Ko yanzun
da akayi mata knocking sai data ja tsaki,tasan bazai wuce laila din ba,don
cikin masu aikinta ba wanda ya isa ya qaraso nan wajen sai idan ita ta nemi
ganinka.
"Waye?". Ta tambaya cikin 'yar qaramar fusata.
" Laila ce".lailan ta fada jiki da muryarta dukka
suna rawa. Har ta bude baki zata koreta,sai kuma taji kaman akwai raunana a
muryarta don haka tace
"Meye kuma?,kinsan banason damu ko?".
"Kiyi haquri.....wani abu ne ya faru nazo nuna
miki,nima yanzu naga an sakashi a page din jaridar breakers".
"Shigo" Ta bata dama kai tsaye tanason jin me tazo
dashi.
Sanda ta
shigo jikinta yana rawa ta miqa mata wayar hannunta. Hannu ta sanya ta karba
cikin yamutsa fuska sai kuma ta waro idanunta dukka waje.
"AN KAIWA SHARARREN MATASHIN ATTAJIRIN NAN FARMAKI A
FILIN TASHI DA SAUKAR JIRAGEN SAMA HARI WATO MUHAMMAD FU'AD JADDA.....HARMA ANA
KYAUTATA ZATON BACEWARSA.....YANZU HAKA BA'ASAN INDA YAKE BA". Sake qarewa
rubutun kallo tayi da kyau,ta maimaita rubutun ta sake maimaitawa sai kuma
murmushi ya subuce mata duk da zulumin daya cika wani sashe na zuciyarta.
"Lokacin tarwatsewarki ameenatu yayi.......tabbas
wannan itace dama ta ta farko a kanki kafin na isa ga dama ta biyu na qarasa
murqusheki.....na kuma jefa rayuwarki data ahalinki cikin halin ni 'yasu"
Tayi maganar a sararin tana jin dadin samun wata gwagwgwabar dama da ta sameta
ta sassauqar hanya.
Idanunta
ta zube akan laila dake kallonta kawai.
"Kina da hanyar da zaki hadamin 'yan press?,ina da
buqatar gabatar da taron 'yan jarida.......ya kamata na fara gwadawa ameenatu
nawa salon da kuma ainihin kalata"
Kai laila ta girgiza.
"Bansan yadda zamu kirasu ba.....amma ina da qawa da
take aiki gidan radio.....zan shaida mata sai suzo din".
"Hakan yayi.....gobe da sassafe nake buqatar su hallara
a harabar gidan nan,bayan gida radio dinsu ina buqatar ta qara da gayyatar wasu
kafafen yad'a labaran dama na jaridun......zan biyata akan wannan aikin
gayyatar" Maamah tayi maganar tana lalubar number musaddiq,can qasan ranta
baqincikin yadda musaddiq ya kasa kiranta a matsayinta na mahaifiyarsu ya
shaida mata abinda ya farun sai a rariya ta gani.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 120
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
120
Dab da
zata tsinke ya daga,kafin yakai ga gaidata ta amshe
"Duk tsiya tuwo dai sunansa tuwo.....kuma.basai kayi
hakan ba zaka tabbatar min ni ba komin komai bace a wajenku.....abu ya samu dan
uwanka musaddiq saidai naji labari a wani wajen?,yanzun kuna ina?". Tafin
hannunsa ya sanya ya riqe goshinsa saboda yadda kansa yake sarawa......ta dage
ita kuma still saita qara masa wani ciwon.
"Muna asibiti" Ya amsa mata a taqaice.
"An ganshi ne?" Ta tambaya yana fargabar
bayyanarsa kafin ta qullawa ameenatu jakar tsabar data shirya qulla mata.
"Adda sabreen ce....."
"Tayi bari?" Ta qarasa masa da abinda zuciyarta ke
fatan ya kasance. Sai daya janye wayar a kunnensa yana dubanta kafin ya maida
cike da mamaki.
"Wanne asibiti ne?" Ta tambayeshi tana kauda
waccan tambayar ganin bai bata amsa ba.
"Noor hospital"
Iya abinda dama takeson ji kenan,tana kuma da buqatar zuwa idan barinne
sabreen din tayi ta karbi barin da hannunta ta taho dashi nan ta bawa
karnukansu su cinye su shanyen jinin,ta kuma aikawa sabreen din video din ta
yadda zai zame mata wani mummunan ciwon.
Sharp
sharp ta shirya,ta kuma kira driver ya fidda mota suka wuce noor hospital kai
tsaye.
Masifa
ta dinga yiwa driver din,tana ganin kaman baya sauri.....kamar ba zai isa akan
lokaci ba. Cikin qasa da minti arba'in sai gashi cikin noor hospital saboda
uban gudun data sanyashi ya dinga zubawa.
"Scanning din da mukayi mata ya kasa bamu ainihin abinda mukeson
gani.....saidai mun samu nasarar ganin two embryos,hakan yana alamta akwai d'a
biyu cikin mararta.....iya abinda muka gani kenan,mararta akwai nauyi da aiki
fiye da marar me dauke da yaro guda daya....so that dole ta dinga kiyaye wasu
abubuwan.....bacin ranta.....aiki me wahala da nauyi da duk abinda zai sanya
mata stress.......babies din suna lafiya......amma idan ba'a basu kulawar data
dace ba.....komai zai iya faruwa" Bayanin likitan kenan da dukkaninsa ya
sauka a kunnen maamah data shigo dakin da qarfinta,saidai ta samu annin da dr
mubeena tana mata bayani a parlor din dakin da sabreen din take.
"Za'a kiyaye in sha Allah Dr...." Anni ta fada
jikinta yana sanyaya,tana sake girmama hukuncin ubangiji da girman qudurarsa da
zatinsa.
"Allah kaine Allah,baka da abokin tarayya
Allah.....yadda ka samar da wadannan halittu naka a mahaifar mahaifiyarsu cikin
wani salo da hikima irin naka.....Allah ka fidda mahaifinsu ka kiyayeshi daga
dukkan hadari" Anni tayi adduar da take har zuciyarta ba tare da tasan da
wanzuwar maamah a wajen ba.
Duk da
taso tazo ta samu gudan jinin yaron a leda amma saita samu akasin haka.....daga
tunanin yaro daya ya koma biyu....bugu da qari ma kuma ana bata tabbacin
raunanniyar lafiyar da suke da ita.....to amma har yanzu tana da sauran abinda
ya rage wanda zata girgixa duniyar anni.....a yanzu zata gudanar da plan
A......plan B din kuma ta ajewa kwanakin da suke zuwa a gaba.
"Zaki gama munafuncinki tsaf.....da duk wata munafukar
addu'arki ki gayamin inda kika kaimin d'ana.....ni dama nasan za'azo
wajen.....ko ba dade ko bajima dole sai kinyi yunqurin salwantarmin da yaro
saboda ki handame abinda ya mallaka......to wallahi baki isa ba......ni mariya
nice uwar FU'AD,bazan kuma qyaleki ba idan yarona ya salwanta". Cak anni
ta dakata daga buda qofar ainihin dakin da sabreen ke ciki,waiwayowa tayi a
nutse cike da mamaki tana duban maamah din
"Mariya?,kinsan abinda bakinki yake fada kuwa?".
Wani kallo maamah ta watsawa anni,cike da alfahari da samun tabbaci akan
qudurinta.
"Na sani mana ameena.....kina tunanin ba'a hayyacina
nake ba?.....UWAR RIQON MUHAMMAD JADDA TAYI KIDNAPPING DINSA SABODA NEMAN KUDIN
FANSA......A HALIN YANZU BA WANDA YASAN INDA TA BOYESHI....ya kikaga taken
wannan labarin a gidajen rediyoyin Nigeria africa dama duniya gaba daya?"
Har tsakiyar kanta anni taji wani abu ya tsarga mata
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
"Dama ki riqe abarki zuwa gobe.....don kuwa goben
warhaka bana tunanin kina cikin masu cikakken 'yanci kamar haka". Ta
qarasa fada tana takawa hankali kwance tana wucewa dakin da sabreen din take.
Duk wata
jijiya ta kanta ta gama tashi saman goshinta,ba abinda qirjinta yakeyi sai
bugawa da wani irin matsanancin fushi. Kowacce kalma data fita daga bakin
maamah a kunnen sabreen ta sauka wadda ke zaune ta jingina da fuskar gadon tana
kokawa da kanta ta samu tasha tea din ko babu yawa.
Zubawa
maamah ido tayi sanda take shigowa dakin,qasan ranta cike da damuwar yadda ta
samu sabreen din zaune sosai.....ba wani alamu na fitar hayyaci ko jigata a
tattare da ita.
Kallon
kallo sukewa junansu,yayin da kallon da sabreen ke ajiye mata ya kasance wani
qazamtacce kuma wulaqantaccen kallo da bata taba ganin irinsa ba a kanta. Hakan
bai sage mata gwiwa ba,taci gaba da takowa har ta qaraso dab da gadonta sannan
ta janye dubanta daga kanta ta maidashi kan ledar ruwan da aka gama qara mata.
"Inda zan baki shawara ki dauka......da zaifimiki kyau
salin alin ki kwanta a zare miki cikin nan cikin girma da mutunci......"
".......idan ba haka ba zaki sanya a kwantar dani a
kasheni sannan ki qwaqule abinda yake marata?" Lafuzzan suka fita da wani
irin fushi da yaja hankalin maamah din zuwa gareta.
Wani
zazzafan kallo take sauke mata tana kuma ajiye mug din hannunta.
"Eh ina nufin abinda na fada din......kina zaton don
kin aikata hakan zai bani mamaki?" Ta jefa mata tambayar tana dage dukka
girarta sama,sai kuma ta girgiza kanta.
"Ko kadan bazanyi mamaki ba......matar data zabi
duniyarta akan lahirarta?,.....matar data zabi salwantar yaranta ta tsira da
qazantar duniya wato kudi!......ke nake zargi......ke nake zargi da harbin
FU'AD!......ke nake zargi da batarmin da MIJINA UBAN 'YA'YANA......" Ta
qarasa maganar tana dora hannunta saman mararta,wasu zafafan hawaye suna
taruwar mata.
Sosai
maganar ta zowa maamah a bazata,amma bata dauketa da wani muhimmanci me yawa ba
tunda tana ganin sabreen din bata da wani power hujja ko damar da zata iya
aiwatar da komai a kanta.
Girarta ta
dage duka tana yiwa sabreen duban mamaki,wani qaramin murmushin rainin wayo
yana fita akan fuskarta
"Ko?......sannu tattabara uwar aure.... Sannu me
miji,to idan nidince fa?,sai yaya?". Idanu sabreen ta zuba mata kafin wani
kwantaccen murmushi ya sauka saman fuskarta,abinda ya soma sanyawa maamah
dawowa hayyacinta. Ba jiya ko yau ba,ta sani murmushin sabreen din bashi da
dadi
"Kina daukan abun da sauqi ne har haka ko?.....haihuwar
muhammad da kikayi hakan bazai qareki da komai ba a sanda kike qoqarin rabani
dashi......haihuwarsa bazai qareki da komai ba a sanda kike qoqarin tabamin
shi....lafiyarsa hankalinsa ko dukiyarsa........ko waye yayi gigin tabamin
DUNIYATA sai inda qarfina ya qare........ciki kuwa harda ke......ke
mahaifiyarsa wadda tayi rainonsa na shekara sha hudu kawai......fu'ad DUNIYATA
ne.....duniyar da ko mutuwa nayi za'a binne ni a tsakiyarta".
Wani
gigitaccen yanayi maamah ta shiga,idanunta bibbiyu duka a warwaje take kallon
sabreen din. Kalaman yarinyar na yau sun girmi hankalinta,saidai duk da haka
zuciyarta tana tuna mata ita din MARIYA CE FA.....giwa kuma kota fadi tafi
qarfin wawa.
"Kinyi kuskuren fara son abinda nice silar zuwansa
duniya......"
"Amma ina me farincikin bake kika halicceshi ba
ko?" Ta maida mata idanunta tsaye a kanta.
"Ba wani doguwar sa'insa bane tsakanina dake kodon
albarkacin wannan dake kwance a marata...." Ta fada tana nuna cikinta da
yatsa.
"Sassauqan umarni ne na ki fiddomin mijina ko ina ya
shiga.......awa ashirin da hudu kacal kike dashi.....sannan......taron 'yan
jarida karki fasa.......hakan shi zai sauqaqewa muhammad sanin asalin launin
kalar mahaifiyarsa" Ta qarashe maganar tana daga mata wayar hannunta.
"Maimakon zazzafan labarin uwar riqo me kidnapping dan
riqonta.....wataqila sai labarin ya canza akala zuwa labarin BAQAR UWA" Ta
qarasa fada da wani mugun confidence daya nuna har cikin idanunta.
Wani
gigitaccen kallo maamah ke yiwa sabreen din,wannan wacce irin BAQAR JARABA ta
hadu da ita?,sam sam ta mance da batun video da yake cikin wayar,lallai kuwa da
ta nemi hanyar da zata salwantar dashi,saidai a yanzun ba salwantar da video
din kawai take nema ba......tana neman sassauqar hanyar da zata shafe babin
sabreen......ta kuma shafe labarin rayuwarta gaba daya daga duniya.
Ko sau
daya itama bata daga qafa daga kallon maamah din ba,a wannan karon tanajin
takai maqura.......itama takai qarshe,kuma ko meye zai faru saidai ya faru. Ko
kadan bata yi mata kallon bil'adama cikakkiya a yanzun. Tanajin ta shirya
tunkarar kowanne yaqi,ta shirya tunkarar kowanne qalubale akan muhammad fu'ad
dinta......tana jin ta shirya ta sadaukar da komai a kansa koda hakan yana
nufin salwantar numfashinta.
Tsaiwar
maamah a wajen yayi mata,don tana jin akwai sauran maganganu daya kamata ta
gaya mata,idanunta suna lumshewa da wani irin bacin rai,mararta tana murda mata
da wani irin ciwo ta kalli maamah
"Ina kyautata zaton har yanzu bakisan asalin wace
sabreen ba......amma lokaci ya kusanto da zata shaida miki ainihin
kalarta.......har yanzu baki tunzura sabreen ta nuna miki wace ita ba......to
amma yanzu anzo wannan gabar.....duk inda za'a juya duk inda zakiyi ki tsaya
tsakaninki da ita,huda nadra haneefa anni farouq musaddiq da saddiq.......uban
gayya DUNIYATA fu'ad......wadannan din ahalina ne.....jinina ne,iyaye kawunnai
kuma kakannin abinda yake yake cikina ne,uwa uba me gayya DUNIYATA jadda.......taba
daya daga cikinsu?" Saita girgiza kanta tana sake tsareta da idanu.
"Bazai taba zame miki abu me sauqi ba.....jeki gwada
idan zaki iya.....zabi ya rage naki.....nima wayewar garin goben nake
jira.....ki tara 'yan jarida.....idan kinso kiqi nemomin mijina kiga yadda
DUNIYARKI zata tarwatse a karo daya" Takai qarshen maganar rashin tsoronta
qarara yana bayyana.
"Idan kin fita ki rufen qofan" Sabreen da amai ke
tasowa ta fadi tana zamowa a nutse daga saman gadon ta doshi bandaki da 'yar
sassarfa gudun kada ta zube aman a wajen.
Dif tayi
tana sauraren sautin yunqurin aman da takeyi daga bandaki.....wasu irin taurari
suna zagaya kwanyarta tun daga gaba zuwa baya
"Wacce irin lalacewa ce ta sameki MARIYA?" Ta
tuhumi kanta da kanta tana jin wani zazzafan gumi yana karyo mata.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 121
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
121
Daga nan
inda take tana iya jin kakarin aman sabreen da take kwarashi da wani irin
wahala da kuma galabaita. Aman tana yinsa ne da dukka zuciyarta da wani irin
karyewa da sarewa,wani irin rauni ne yake cikata a duk sanda ta tuna
"Ba fu'ad a
gefanta.....qarfinta.....rayuwarta......kuma duniyarta gaba daya,hasalima ba
wanda yasan yana ina......yana raye ko ya mutu,me gobensu zata haifar musu su
duka?".
A maimakon
tausayi dake sauka zuciyar kowacce 'ya mace a sanda taga 'yar uwarta mace cikin
hali na ciwon laulayi saboda sanin ciwonsa da tsananin da yake dashi......a
bangaren maamah fitar aman sabreen sai takejin kamar wani sauti ne na barazana
a gareta......kamar wani sauti ne dake gaya mata dukkan komai naki ya kusa zuwa
qarshe.....asirinki zai tarwatse muddin haduwa da tabbatuwar alaqa yaci gaba da
wanzuwa tsakanin sabreen da fu'ad.
"Ya zanyi na cire cikinnan?,ya zanyi na rabata
dashi?" Abinda zuciyarta ta dinga gaya mata kenan da wani irin qunci da
tsananin takura.
Yunqurin
aman shi ya sanya anni qarasowa cikin dakin da wani irin mutuwar jiki da
sarewa,zallar mamaki da kuma tsananin tsoron hali da kuma dabi'ar maamah din.
Da baya da baya
ta dinga tafiya har takai bakin qofar dakin,idanun maaman akan anni,haka idanun
anni din itama akan maamah,saita juya tana fuskantar qofa ta murdata ta fice.
Asalin
gigicewa takeji gaba daya har cikin kwanyarta,me yasa duk wani motsi da zatayi
sai yarinyar ta zame mata cikas?.....me yasa take zamewa rayuwarta da duk wani
motsinta matsala ne?,yaya akayi ta gayyato matsala cikin rayuwarta?. Idan ta
duba ta sasanni da dama sai taga takunta na baya yafi kyau......takunta na baya
yafi fita akan wanda take fafatawa bayan shigowar sabreen rayuwarta. Batasan me
ya dauki hankalinta ba tun a wancan lokacin da har tabar yarinyar da video din
bata salwantar dashi ba,ko a sannan tana ganin bata da wani power.....ba kuma
abinda zata iyayi?,ko wannan shine sila?.
Cikin
tausasawa da tausayawa anni ke riqe da ita,tun tana iya fitar da dan abinda ta
samu kurba har ya zamana ba komai cikin aman sai yawu kawai,abinda ya qara
adadin galabaitarta kenan,don tanata yunqurin aman kuma babu wani sauran abinda
yayi saura a cikinta. Wani hawaye na taru idanun anni sanda take kwance ana
qara mata ruwa gudun kada galabaitar ya taba lafiyar yaran da suke
cikinta,tausayin sabreen din yana ratsa anni sosai. Ta sani ba abu bane me sauqi
wajen mace ta shiga irin wannan yanayin.....ko ita a baya data taba rasa
abba,bawai rashi na mutuwa ba,aah saidai rashi na rabuwar aure na dan
lokaci,ita kadai tasan me taji,ita kadai tasan ya taji.....ita kadai tasan
abinda ta fuskanta,to ballantana wannan,wani yanayi ne da babu tabbas ko
sahihancin zance akanshi.....wani yanayi ne da ba wanda yake da tsayayyen abun
fada akai. Gefe daya lalurar ciki.....ga qananun shekaru,ga kuma uwa uba me
kankat wato MARAICI.
Ta wani
bangaren kuma abinda ke daga mata hankali shine.....irin maganganun da taji ana
musaya tsakanin maamah da sabreen,wanne irin makami yarinyar ke dashi har haka
da ya girgiza mariya farat daya?.
Batasan
adadin lokutan data share a zaune gaban sabreen ba,tana riqe da carbinta wanda
har yatsunta sun fara zafi saboda riqonsa. Dare yayi nisa sosai,ita kadai ce
kawai,don ta hana kowa zama tare da sabreen din sai ita,gani takeyi babu wanda
zai iya kula da ita irin yadda takeso,gani takeyi dole ita kadai ce zata iya
bata wannan kulawar.
Yadda
taga rana haka taga dare,sau daya tak sabreen ta farka tsahon daren zuwa
safiya,ta bada tea dan kadan,bacci ya sake kwasheta ta koma.
Sai anni
take ganin baccin yafi zama alkhairi akan ta zauna idanun ta biyu tana kuka,ko
don saboda lafiyar yaran da take dauke dasu.
*_WASHEGARI_*
K'arfe tara na
safe a nan ta yiwa alhj hamza kibiya.....musaddiq da saddiq da sauran guards na
fu'ad wadanda suke gida da wadanda suke kan hanya sanda abun ya faru. Iya su
uku suka shigo,don ko amna ya hanata zuwa asibitin gudun kada su hadu suyita
yiwa mutane kuka.
A sannan
anni na gaban gadon sabreen din,tana ta neman yadda zata sanyata taci wani abun
komai qanqantarsa.
Karon
farko da magana me zurfi ta hada alhaji hamza da sabreen. Shi ya tsaya kan
saita saka wani abu a cikinta. Tana kuka hawaye daya bayan daya haka ta dinga
karbar tea din daga hannun momma bahijja wadda ta shigo daya baya.
Sai data
soma yunqurin dawo dashi sannan ta barta,ta wuce da mug din ta daurayeshi
sannan ta dawo dashi ta ajiye.
Shuru ya
ratsa dakin na wani lokaci,kowa ka kalli fuskarsa cikin nazari da kuma alhini
yake. Alhj hamza ne ya fara magana.
"Toh.....bamu da abinda zamu cewa ubangijinmu sai
godiya.....kafin ya jarabcemu da wannan ya mana tarin baiwa da ni'imomin da ba
zasu irgu ba....cikar iko da adalcinsa ne ya jarrabi bawa akan dukkan abinda
yaga dama a sanda yaso.....to mu ba zamu butulce masa ba,alhamdulillah da duk
yadda yayi damu......mun tattauna da masu ruwa da tsaki cikin sha'anin tsaro na
qasar nan dama maqwaftanta,kuma suna bamu tabbacin lalubo inda suke ko wani abu
daya shafesu cikin qasa da awanni ashirin da hudu in sha Allah......su kansu
guard da suke aiki qarqashinsa dukkaninsu basuyi bacci ba,ba wanda ya zauna ko
ya kwanta,aiki suke akan batun ba qaqqautawa....kuma ana samun haske sosai,su
kansu na yadda da qwarewarsu in sha Allahu komai zaizo cikin sauqi" Ya
qarasa maganar yana basu tabbaci a maganarsa dama fuskarsa.
"Ubangiji ya amince....Allah ya bayyana gaskiya a duk
inda take" Momma ta fada cikin sanyi jiki da tashin hankali. Sunan sabreen
ya kira,ta amsa masa ba tare data iya dubansa ba,don kuwa ita kadai tasan
abinda takeji.
Nasiha
sosai yayi mata me ratsa jiki da hankali akan imani da qaddara da daukarta.
"Zan dauka abba in sha Allah.....zan dauka" Ta
fadi kawai tana sauke idanunta saman tafin hannunta daya wani qara dashewa yayi
haske kaman ba cikakken jini a jikinta.
Da daya da
daya suka fara juyawa suna fita.
"Saddiq" Ta kirashi abinda ya dawo da hankalin
anni kanta don wNi abune da bata taba yi ba. Shima a mamakance ya juyo yana
kallonta,sai ta sanya hannu ta yafitoshi.
Dawowa
yayi a nutse,y jawo kujerar da momma ta tashi akai ya ajiye daura da ita.
"Gani adda" Ya fada yana mata duban mamaki.
"Akwai labari da nakeso na fitar kashi uku......kashi
daya gidan tv radio dana jaridu......kashi biyun da yayi saura tv radio ne
kawai zaiyiwu su haskashi" Ta fada tana dubansa.
Magananta
taja hankalin anni,ta kuma tuna mata da duk tattaunawarsu da maamah ta jiya.
Sakin kayansu da take kwashewa tayi wanda za'a koma dasu gida,ta tako a hankali
har inda suke.
Duban
saddiq anni tayi fuskarta ba walwala
"Tashi kaje parlor.....idan na gama hada kayan zan
kiraka" Fuskarsa da mamaki da kuma
wani zumudi nason jin qarashen maganarsa da sabreen ya miqe,saidai babu yadda
zaiyi anni ta katsi hanzarinsa.
Inda ya
tashi ta koma ta zauna tana duban sabreen.
"Wanne labari zaki fitar sabreen?"
"Yadda akayi uwa ta zama me dillancin yaronta don kawai
ta mallakeshi......yadda wata uwa ta zama azzaluma wadda batasan ciwon 'ya'yan
cikinta bama bare na wasu....yadda wata uwa ke burin murqushe 'ya'yanta ta gaji
abinda suka bari......yadda akayi sabreena ta zama matar muhammad jadda ta
hannun mahaifiyarsa" Sabreen ta fadi muryarta nason karyewa amma tana bawa
kanta da kanta qwarin gwiwa,tana jin babu wani abu da zai hanata aiwatar da
wannan abun,daga nan zuwa dare muddin bataji komai dangane da muhammad dinta
ba. Koda sabreen bata fayyacewa anni komai ba.....annin da kanta ta gama
fahimta.....wani tsohon zargi da shakkunta kan maamah lokacin aurensa shine
yakeso ya tabbata bayan wani lokaci.
"Akwai kuskure cikin aikata haka sabreen......kinsan
wanne kuskure?" Anni ta tambayi sabreen tana son qwato hankalinta da
nutsuwarta,domin kuwa ta hangi abubuwa masu tarin yawa cikin idanun sabreen din
masu kaifin gaske suna kai kawo.
"Mariya bata da asara.....domin kuwa tata rayuwar tazo
qarshe idan aka dangantata da taku......mariya bata da wata asara me yawa,kece
kike da jini a jika.....kace kike tara zuri'a yanzu.....domme zaki yiwa kanki
wannan barnar?" Anni ta fada tana kallon idanun sabreen tanason taga iya
dadin yadda maganar ta shigeta. Kai sabreen ta mirgina gefe....kamar anni ba
zata fahimci nata shimfidadden takun ba.....wannan abun wani taku ne kuma tarko
ne me kyau idan anyi amfani dashi ta hanyar daya dace......tarko ne da zata
kama kowacce kurwa ta maamah din.
"Kinsan wace mariya ta gaske?,kinsan yadda me babban
suna suka rayu?" Haka kawai taji tanason ta sakeji daga bakin anni,ta
tabbatar koda shi ya gaya mata.....koda shi ya labarta mata bazai gaya mata
yadda anni zata sanar mata ba,don haka ta kadawa anni kai a hankali tana
dubanta.
A nutse anni
ta warewa sabreen komai.....rayuwar fu'ad tun kafin tafiyar mariya da kuma
tafiyartata,yadda ta samesu da irin wahala da tasha kafin ta maidashi kalar
mutumin da yake a yau,duk wani qalubale da kuma gwagwarmayar rayuwa tasa.
Hannu
kawai sabreen ta saka ta lullube fuskarta da tafin hannuwan nata,sai takejin a
wancan ranar a Maldives tamkar bai gaya mata komai nasa bama.....kaman ba wani
abu daya gaya mata daya shafi rayuwarsa. Ta yaya zata iya controlling hawayenta
a fuskarta?,ta yaya zara iya.hana kanta zubar hawaye?,wacce irin asararriyar
uwa suka samu?,wacce irin uwace wannan wadda da ita gwara babu?. Lallai ba
shakka zatayi komai.....har fiye da abinda take hasashe a baya ma zatayi.
Amma da
irin wannan abun nata har anni ke duban ta qyaleta?,me yasa anni ba zata
fahimci cewa ita sabreen dama mutuncinta bararre ne a idanun mutane da
yawa?......me yasa anni ba zata Fahimci zata iya saudar da komai wa fu'ad
ba?,don don mutuncin nata da iyakarsa idanun fu'ad dasu anni?,duk da yafi
qarfin D'A tunda wata yarda ce da sassanyan aminci ta samu a muhallin da yafi
kowanne daraja.
"Ban gaya miki don kiyita kuka ba.....ban gaya miki don
kiyita damuwa da sanya bacin rai ba.....na gaya miki ne saboda ki
sani........ba kowanne mutum kake qarar da energy dinka a kansa ba". Kai
sabreen ta jinjina tana sauke hannuwanta.
"Taso nayi tarayya da ita wajen raya zunibinta
anni......ta kawoni da qarfi da yaji da'irar da ban shirya shigota
ba.....saidai a yanzun ina kallon juyewar al'amarin daga sharri zuwa
alkhairi...." A nutse itama ta gayawa anni yadda duka komai ya kasance
tsakanin ta da maamah a wancan lokacin. Tayi shuru anni tana jin komai yana
kwaranye mata,lallai duk inda xa'a qaunaci juna saboda Allah dole a dinga ji a
jiki a duk lokacin da wani abu zai kasance da dayan biyun. Ashe ba'a banza ba
ta dinga jin wani baqin abubuwa dangane da auren?,ba'a banza ba ta dinga jin
rashin gamsuwa da komai?.
Al'amarin maamah sai taji yana sake girma a zuciyarta. Mamakinta tana
jin kaman zai fasa ko ya kashe zuciyarta gaba daya.
*_WANI DARE!_*
Ranar ta
kasance musu wani dare da dukkaninsu suka kwana suna juyayi da mutuwar mamaki
kan halayyar mariya da komai nata.....daren ya zame musu wani dare da sabreen
ta kwanta tana jin zata dan dagawa maamah qafa saboda anni data buqaci wurga
lamarinta a kwandon shara abita da ruwan addu'a,saidai kuma wannan daren ya
zama daren da yayi silar da sabreen ta soma sakin UPDATE akan maamah......wanda
batayi tunanin akwai wani abu da zai dakatar da ita ba ko waye ko meye shi!.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 122
122
Har qarfe
sha daya na dare anni tana zaune gaban sabreen,lokacinne kuma Dr mubeena ta
gama daura mata wani ruwan daya zama shine abincinta yanzu saboda ba wani abu
da yake iya shiga cikinta ya zauna,koda ya shiga dimma sai ya fito. Rubuce
rubuce Dr mubeena ta kammala yi cikin file din sannan ta rufe,ta ajiye a gefe
tana sanya idanunta kan sabreen dake kwance da shirin yin baccin da ta tabbatar
qaryarsa ya shammaceta......saidai tasan zaizo ne kadai ta hanyar sinadaran da
suka zubawa ruwan dake shiga jikinta,wannan ne kadai yake bata daman yin baccin
daya kasance ba natural na qashin kanta ba.
Tausayi
sabreen din take bawa Dr mubeena,tako wacce fuska ta kalleta tausayi take bata.
Hannu ta miqa ta dauki abun gwajin BP din data gama gwada mata ta riqe a
hannunta,tadan sakar mata murmushi wanda sabreen qarfin hali kawai tayi ta
maida mata.
"Kiyi bacci sosai Mrs jadda......fi amanillah.....in
sha Allah boss yana cikin aminci,Allah baya bari bayinsa na gari su wulaqanta
kosu tozarta ko su wofanta" DR mubeena ta fada cikin kwantar mata da
hankali. Murmushi ta tattaro da qyar ta samu ta maida mata martani,Dr mubeena
ta kalli anni dake zaune gaban gadon kaman ko wanne dare tana riqe da
tasbaharta.
"Yau ba checking din dare,BP dinta ya kusa dawowa
daidai da yadda nake buqata,kuyi baccinku,idan Allah ya kaimu qarfe shida ko
biyar da rabi zan shigo". Ta fada cikin girmamawa itama tana jin alhini
har cikin qasusuwanta na rashin labarin komai akan fu'ad din. Murmushi kadan
anni tayi tana sauke qafafunta daga saman kujerar,yau momma ta dage lallai a
bawa anni 'yar tayin kwana ko huda ko ma'u. Ta karbi ma'u saboda ta matsanta
dole gobe su wuce mali huda taje tayi ton print dinta duk da a goben zasu rufe.
"Sannunku da qoqari kuma,Allah yayi muku albarka"
"Ameen,Allah ya qara lafiya saida safe" Tayi musu
sallama tana fita daga dakin.
Idanunta
a lumshe suke kawai,ita kadai tasan me yake yawo tsakanin qirjinta da
zuciyarta,a duk sanda kwanyarta zata harba da lafazin.
"Sun harbeshi.....ba'asan inda suke ba!" Sai taji
kaman zata mutu......sai taji kaman ba wata tazara tsakaninta da tashin
alqiyamarta. Takanji faruwar komai kamar a mafarki.....daddadan farinciki da
wata iriyar tsaftatacciyar kulawa tana shirin rikida zuwa tashin hankali da
firgici.....wannan kusancin tashin farko ya juye ya koma kewa da tsananin
buqatar makusanci izuwa zuciyarta.
Duk
dare kafin alluranta su dauketa zuwa duniyar bacci.....duniyar dasu Dr mubeena
suka matsanta mata zuwanta badon son ranta ba.....sai rayuwarsu tsakanin
Maldives da madeena tayita dawo mata tamkar a faifan CD,takanji inda ana maida
hannun agogo baya tabbas data maida.......tabbas data hanasu dawowa nigeri da
tana da masaniyar ibtila'in da zai fada musu kenan.
Tun tana
iya jin muryar anni da ma'u sama sama har ta daina ji,ganinta da ruhinta suka
koma zuwa ga wanda ya yisu nadan wucin gadi.
Shuru
da anni taji ma'u tayi shi ya bata tabbacin bacci yayi awon gaba da ita,saita
gyara zamanta saman kujerar tana ci gaba da jan tasbaharta,tunanuka kala daban
daban suna hana idanunta tafiya duniyar barawo wato bacci da itadinma duk dare
satarta yakeyi,bata kuma fiya dogon zango ba yake sakinta,takan farka da
mafarki ki razani duk dare,saidai ko sau daya bata taba farkawa ba ba tare da
ambaton hasbunallanu wani'imal wakeel a bakinta ba.
Batasan baccin yayi awan gaba da ita ba,har tasbhar hannunta ta sulale
ta fadi da hasbunallanu wani'imal wakeel data kasance ta qarshe a harshenta.
Dukkanin daukacin asibitin harda dakin ya dauki shuru,dare ya fara
nutsawa awanni suna gudu......a irin lokacin da bayinsa nagartattu ke neman
kusanci dashi saman darduma,ashararan mutane kuma suma ke nasu aikin saboda
neman duniya da abinda yake cikinta.
Daya
daga cikinsu ta samu nasarar kunnowa dakin,ta murda handle din a hankali cikin
sanda. Sanye da suturarta ta dazu,suturar qarshe data shigo dakin dasu babu
abinda ya canza,daidai da takalminta da kuma dan qaramin hijabin kanta,saidai a
yanzu akwai baqin face mask saman fuskarta koma bayan dazu.
Kai
tsaye ta wuce parlor din ta kuma tunkari dakin da sabreen ke kwance,ta saka
hannu ta bude qofar dakin tana shiga. Daga bakin qofa ta tsaya,ta qarewa kowa
kallo,ta kuma tabbatar dukkansu sunyi nisa a baccinsu. Ajiyar zuciya ta saki
hakan yana bata nutsuwa da kuma qwarin gwiwar aiwatar da abinda ya shigo da
ita,taci gaba da matsawa zuwa gadon da sabreen ke a kwance.
Daidai
inda ruwan dake saqale a hannunta ta isa,ta tsaya ta zuba masa idanu. Bisa
qa'ida ruwan yake diga kaman yadda ya dace,aiki biyu zatayi a ciki,ta
gaurayashi da sinadarin dake aljihun rigarta,ta kuma qara gudun ruwan dake
shiga sassan jikinta,wannan shi zai saurin hautsina tsarin jikinta,ya kuma
taimakawa sinadarin wajen yin aiki a jikinta da gaggawa.
To amma
ta wani bangaren tafison ta fara tabbatar da inda wayar take......wayar itace
babban burinta na farko,wanda iya ita kawai idan ta mallaka kaman yadda akayi
mata alqawari ya isheta kudin aikinta koda ba'a qara mata komai ba.
Ta
tsakanin annin da sabreen ta wuce tana miqa hannunta locker gefen
gadon,durqusawa tayi ta soma binciketa a hankali. Sai data hautsine komai bata
ganta ba,wannan ya qara gudun jinin jikinta energy dinta ya qaru fiye da yadda
ya kamata ya kasance. Tana bala'in son wayar,don itace cikar burinta. Miqewa
tsam tayi ta sake wucewa ta tsakaninsu,hannunta gefe da gefen sabreen din ta
soma lalubawa ko a nan ta ajiyeta.
Kaman
wadda aka tasa ta dinga jin wani sauyin yanayi tattare da ita tamkar wadda aka
canzawa muhalli daga wanda take ciki,jin hannu ta gefan kafadarta ya sanyata
murmurewa daga yanayin bacci zuwa rayuwar zahiri. Baqon turaren da takeji a
hancinta ya sanyata budewa idanunta qanqanuwar qofa da zata iya ganin wanda
waye haka keda kusanci sosai a kusa da ita?.
Dr
mubeena kamar take gani,amma kuma qamshin da yanayin nutsuwar sam ba ita
bace......saidai a idanu a kallon dake a fusge tabbas Dr mubeena ce.
Tabo
wayar da hannunta yayi ya sakata sakin ajiyar zuciya,ta saka hannu ta jawota ta
jefata aljihun lab coat din jikinta,sannan ta fiddo hannun da syringe da wani
irin ruwa a wata mitsitsiyar roba.
Tas ta
soma zuqe ruwan a syringe din,wanda tana dab da kammalawa anni ta motsa bakinta
dauke da HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL Tana shafa fuskarta da tafin hannunta.
Fitar
hasbunallahu din ya daki qirjinta,ya kuma sabbaba mata faduwar allurar dama
robar ruwan,abinda ya sake sakawa sabreen matuqar ankara da ita,ta sunkuya da
sauri ta dauki syringe din qirjinta yana dokawa.
Idanu
anni ta zuba mata a mamakance,duk da ta juya mata baya bata iya ganin fuskarta.
Mamakin yadda suka canza tsari ne na Shigowar likita dakin mara lafiya haka kai
tsaye?.
Kaman Dr
mubeena take gani......amma kuma abun da mamaki,Dr mubeena da ta musu sallama
sai bayan sallar asuba?,me ya dawo da ita?,kuma ta shigo dakin ba tare da sanin
kowa ba?.
"Dr akwai allurar data rage ne?" Kai ta gyada mata
kawai tana qoqarin qarasa zuqe ruwan a syringe din a gaggauce don ta qarasa
cika aikinta.
Hakan
bata samu ba kuwa,don hannu sabreen takai mata cikin shammata ta daki
hannunta,da syringe din da ruwan sukayi gefe suka watse,abinda ya darsa wani
abu da gaggawa a zuciyar anni,ta miqe sa wani irin zafin nama ta damqo
kafadarta tana juyo da ita.
Kallon
kallo suka yiwa junansu,tana shirin kubcewa anni,annin ta saka hannu ta yage
face mask din fuskarta ta.
Baquwar
fuska ce da bata santa ba.....kaman yadda ya bayyana fuskar bata Dr mubeena
bace.
"Wacece ke?!" Tambayar da anni ta mata cikin
madaukakim sautin tsawa daya qarasa farkar da ma'u ta miqe ta zauna sosai ta
yunqura ta tashi.
Kai
matar ta girgiza,ta juya da gaggawa tana nufar qofa,saidai tuni ma'u ta rigata
isa qofar ta danneta ta kulle ta zare key din.
Raba
dubanta take kan fuskar anni tana zaro ido waje,hankalinta ya soma tashi tana
tunanin girman hadarin da zata shiga muddin ta bari taje hannu.
"Kiban hanya na fita ko kuma na illataku!" Ta fada
da wata gurbatacciyar hausa da zata baka tabbacin wani yaren ce daban ba
cikakkiyar bahaushiya ba.
Daga
annin har matar ba wanda ya zaci haka,saukar kakkauran plastic plate din da
sukaci abinc dashi dazu ma'u ta sauke mata a tsakiyar kai,sai gata ta zube qasa
warwas zubewar data sanya wayar sabreen silalowa daga aljihunta.
A
hankali sabreen data sauko daga gadon ta dauki wayar tana juyata,iya daukar
wayar kawai ta bata kowacce irin amsa da take buqata koda matar batace komai
ba.
Matsawa
anni tayi da hanzari tana kiran security emergency line cikin qasa da minti
daya sai gasu sun bayyana a dakin.
Kiran
security din ya tayar da kusan duk wani security alert na asibitin,kasancewar
dakin babban daki ne,yana cikin VIP rooms da asibitin yake dasu.
Cikin
qanqanin lokaci qofar dakin ya cika da security da wadanda ihun security alert
din ya tashesu. Kusan kowa yasan wacece a dakin a cikinsu,suna da masaniyar
mahaifiyar wace a dakin,don haka fitar security alert daga dakin ya zamana
kaman tashin hankali a wajen kowa.
Sanda
chief of security service na asibitin ya shigo dakin yana neman ba'asin abinda
ya faru ya girgiza. Cikin matuqar tsoro da kuma kaduwa ya shiga bawa anni
haquri.
"Am sorry maaa.....muna dukkan iyawarmu wajen bawa
madam tsaro,bamusan ya haka ta faru ba.....amma ni da kaina banyi minti talatin
da shiga office ba bayan ba gama zagaye na tabbatar kowa yana kan aikinsa,hatta
shige da fice na asibitin nan tun bayan faruwan abun muka sake saka ido
akai....amma zamu duba in sha Allah,zamu kuma binciketa har sai mun tabbatar
daga ina take?,meye kuma ya shigo da ita dakin......muna masu bada
haquri". Kai kawai anni ke jinjinawa tana duban matar wadda tuni ta jiqe
da fitsari,ainihin mummunar suffarta dukka ta fito saboda yadda tayi wurjanjan
da kuka da tsananin tashin hankali. Haquri kawai take bayarwa hannuwanta a sama
kaman me addu'a. A haka suka jata suka fice da ita,sabreen ta koma gefan
gadonta ta zauna kawai rungume da hannayenta kanta yana cakudewa.
Dr
mubeena ta qaraso inda allurar da robar suka fadi ta sanya hand gloves ta
daukesu,har yanxu ita kanta a tsorace take jikinta kuma rawa yake. Mamaki ne
yake qara kasheta na yadda akayi amfani da kamanninta da komai nata aka shigo
dakin za'a cutar da iyalin jadda.
"Zanje dashi lab mu gwada muga meye ma taso zuba mata
cikin drip din". Dr mubeena ta fada tana duban securities din guda biyu da
suka rage a dakin. Juyawa tayi ta kalli anni da sabreen.
"Ku kwantar da hankalinku,babu abinda zai faru in sha
Allah,zasu dan xauna kadan daku kafin daga waje kafin security dinku na gida su
iso....don anyi alerting nasu abinda yake faruwa".
"Sannu Dr" Kawai anni ta iya fadi Dr mubeena ta
juya ta fice da sauri Dr kamal da yake on duty yabi bayanta abun shima yana
girgizashi. Case ne da makamancinsa bai taba faruwa cikin asibitin ba,sai gashi
yau yana shirin faruwa akan matar mutum mafi girma da kima cikin idanunsu banda
Allah ya kiyaye.
Ajiyar
zuciya me nauyi sabreen ta sauke tana dora hannunta saman cikinta a hankali.
Wat qqqarfar soyayyar abinda take dauke dashi ya ratsa mata zuciya irin wadda
bata taba ji ba,wato tako ta ina farautar rayuwarsu akeyi?,so ake a salwantar
dasu gaba daya?,kowa rayuwarsu ta tsone masa idanu ta kowacce fuska?.
"Nayi alqawarin baku kulawa da dukkanin qarfina da kuma
iyawata.....nayi alqawarin kula daku har zuwa sanda zaku taka doron
qasa......da ran mahaifinku ko babu.....da kulawarsa ko babu......zamu zame
masa madubi kuma ababen alfahari in sha Allah" Tayi maganar ita daya tana
sakejin kaman wata sabuwar alaqa na qulluwa tsakaninta da abinda ke cikinta da
batasan meyeshi ba.
Batasan
hawaye takeyi ba saida muryar anni ta ratsata.
"Ki rage damuwa da gaske sabreen ko don diyoyin cikin
ki.....karki cutar dasu....Allah shike riqe da kowanne bawa yake bashi
kariya....musamman idan ka sallama masa ka kuma miqa masa al'amarinka".
Tayi maganar a tausashe tana goge mata damshin fuskarta.
Ba wanda
ya iy komawa bacci,abinda ya sanyata yanke shawarar yin alwala,ta daura alwalar
ma'u ta shimfida mata abun sallah. Ta jima tana kaiwa Allah kokenta wanda tayi
Imani shine sarki guda daya da baya maida hannun bawansa ba tare da ya amsa
addu'arsa ba. Sanda ta idar tana zaune kanta a qasa,tana jin tattaunawar guards
din fuad daga parlor din dakin. Kusan kowannensu zuciyarsa a kusa take,muryar
abdulgafar ce ta qarshe.
"Daga yau koda wasa ba wanda zai sake gigin zuwa kusa
da inda take ma......daga gobe zuwa jibi ko da numfashinmu da jinin jikinmu zai
qare sai mun lalubo duk inda oga yake,a cikin qasar nan ko africa ko a wacce
nahiya ta duniya ma".
Numfashi
ta sauke a hankali,ta jawo wayarta tana lalubo number musaddiq. Dole ta fara
taba mata nutsuwa kaman yadda tayi musu,dole ta taba kwanciyar hankalinta ko
yaya ne,saboda itama tasan kifi na ganinka me jar koma.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 123
123
Cikin qasa da
awa daya ta gama turawa saddiq komai da komai da take buqata,sannan ta sauka
tana lalubo rubutaccen qur'ani dake kan wayarta.
Ko yaya ne
tanaso ta karanta ko zata samu sassaucin zugi da radadin da zuciyarta take
mata,don ta dade da fahimtar babu wani abu dake bawa jiki da zuciya nutsuwa
irin karatun alqur'anin.
★Zuwa sanda
gari ya qarasa haske abba ya iso,already su musaddiq dama tun cikin daren suka
qaraso,saidai da safen musaddiq yadan fita sannan ya dawo.
Dr
mubeena ta shigo da sakamakon gwajin,a sannan sabreen din tana zaune ana gyara
mata cannula dinta data goce. Idanunta a runtse tana jin radadin yadda ake
luguiguta qarfen allurar cikin Jikinta.
"Guba tayi attempting zuba mata.....wadda take bin jiki
a hankali ta lalata kowanne organ na jikin dan adam......alhmdlh da ubangiji
bai bata nasara ba......inda hakan ya faru to fa da saidai addu'a
kawai....poison ne da bashi da magani a nan qasar ko makari kwata kwata".
Kai kawai sabreen ke gyadawa tana sake girmama rashin imani da rashin tausayi
irin na wanda ya dauki nauyin abun. Zuciyarta tayi wani mugun karyewa fu'ad
jadda yana fado mata. Allah ne kadai yasan a wanne yanayi yake a yanzu?,a wanne
irin hali yake?.
Da sassarfa
take saukowa daga saman nata kaman zata hada matakala bibbiyu. Duk sanda taga
kiransa tasan tabbas lamari ya baci,ba kasafai take sanyashi ayyuka ba.....ba
kuma kowanne lokaci bane take bashi aiki na sai aikin daya kasance babba.
Yana
tsaye tsakiyar falon,hannunsa goye a bayansa yayin da idanunsa ke lullube da
baqin gilashi.
"Me ya faru?,ya ake ciki?". Baqin hannunsa ya saka
yana cire glass din nasa,bakinsa da yake baqiqqirin ya motsa.
"Aiki ya baci,kuma komai na iya faruwa saboda ta fado
hannu a sanda kowa yake abun zargi ne". Hannuwa bibbiyu ta sanya yana dafe
qirjinta dake wani irin buga mata,duka idanunta a warwaje tana jin tashin
hankali yana zagayata.
Wannan
shine aiki na qarshe da take sanya ran samun nasara a kanshi,aiki na qarshe da
take da kyakkyawan fata da hasashen indai ya tafi daidai ta gama da matsala
daya cikin matsalolin rayuwarta guda uku,aikin data kwana jiya batayi bacci ba
tana jiran jin kyakkyawan sakamako a kansa.
"Waye ka bawa aikin?,ina fatan sunana bazai fito
ba?" Ta tambayeshi zufa tana yanko mata tana jin kan an mata wanka da
ruwan zafi. Kai ya girgiza yana dubanta.
"Ko sunan wanda na bawa aikin bazai fita ba bare
sunanki bare nawa,don da kika bada aikin na bawa wani shima ya bawa wani shima
wancan wani ya bawa sannan aka bawa yarinyar......nasan yarinyar amma ban bata
aiki kai tsaye ba saboda gudun qwacewar rana irin wannan......amma.abinda yafi
bani mamaki,itadin expert ce,bata taba missing target ba tunda ta fara aiwatar
da irin wadannan ayyukan sai yau ta silarki" Yayi maganar abun yana
tsananin bashi mamaki na yadda ta fadi warwas a qaramin aiki irin wannan.
Ajiyar
zuciya ta sauke,ita komai ba damuwarta bane......kama yarinyar ko
tsallakewarta,nata damuwar shine samun tabbacin nata kubutar da kuma tsiran.
Kujera ta
samu ta zauna tana juya tambayarsa. Me yasa rashin nasarar yarinyar da
faduwarta bai tashi afka mata ba sai da aiki yazo kansu?. Tambayar data kasa
samun amsarta kenan,saidai kawai ta sakawa ranta akwai wani boyayyen abu na
daban da sabreen din ke amfani dashi.
"Labari na gaba" Ya fada yana fiddo jaridar dake
hannunsa. Kamfanin jaridar yafi kowanne kamfani fidda adadin jaridu siyar dasu
da cinikinsu,saboda yafi kowanne gidan jarida fidda labarai latest masu daukan
hankali,labarai na gaske da suke daukan hankali tsakanin kwanaki da makonni.
Hannu ta
saka ta karba tana dan mita,saboda a yanzun ba abinda tafi buqata irin ya barta
ta zauna tayi nazarin hasarar data sake fada mata. Kudade masu ciwo ta biya don
wanzuwar aikin,sai data siyar da bangles dinta na gold sannan ta biyashi kudin
aikin.
Wareta
tayi tana mita a ranta,saidai bata samu sukunin sauke mitar ba tafkeken hoton
farko daya mamaye jaridar ya dauki hankalinta.
Hoto ne da
alamu suke nuna daga cikin video aka ciroshi,fuskar hajja sosai ya fita,yayin
da ita dake gefen hajjan kwata kwata fuskarta bata fita ba bata kuma nuna ba.
Bata sani
ba.......ta gurin bugun jaridar aka samu akasi tayi damage?ko kuma ana sane aka
lalata gurin?.
Kayan
dake jikinta a jikin hoton tabi da kallo,sune dai......sune dai wadannan kayan
data sanyasu a ranar da zasuje gidansu sabreen zuwa na farko......gabanta yayi
wani mahaukacin faduwa sanda wani abu ya darsu a ranta.
"Na shiga uku?!,me zan gani wannan?" Ta tambayi
kanta da kanta hannuwanta suka dauki rawa,da wani irin sauri ta maida dubanta
saman manyan rubutun da suke saman newspaper din da aka yisu in bold style
yadda zai dauki hankalin harda na nesa.
_CIKIN WADANDA AKE ZARGI KENAN DA SACE SHARARREN ATTAJIRIN
KASUWAR GOLD DA DIAMOND KENAN MUHAMMAD JADDA_
Dukka
hannunta suka dauki rawa,wata kidima ta saukar mata,ta dubeshi gumi yana sake
tsatstsafo mata,yau itace buge cikin calendar da sunan wadda ake tuhuma da
satar d'anta?,ba wanda zai aikata wannan sai yarinyar.....don kuwa ita daya
take videos din ta tabbatar. Kamar wadda kuka zai qwacewa cikin rawar murya da
qwacewa dukkan wani hanzari daga gareta tace.
"Yaushe aka buga wannan labarin?,har ina kuma labarin
yakai?". Gyara tsaiwarsa yayi da fuskarsa da bata nuna wanzuwar imani a
zuciyarsa ko kadan yace.
"Tun da sassafe....nima a teburin me shayi naga wani
yana karantawa,sai naga kaman nasan fuskar,koda na duba sai naga fuskar hajja
harira ce.....wannan ta kusa da ita dince dai ba'a gane fuskartata". Wata
gauruwa ajiyar zuciya ta sake,tabbas zai wahala a gane fuskartata,amma ga wanda
yayi mata farin sani hakan bazai bashi wahala ba sam.
Qarar
wayarta ya sanyata zabura tana dubanta,don sam bata tsammanin kiran wayar kowa
a irin wannan lokacin. Hannu ta sanya ta dauka tana duba me kiran,hajja harira
ce,tayi kaman ba zata daga kiran ba amma sai taji tana buqatar sanin waye.
Karata
tayi a kunnenta,tana shirin yin sallama sai sallamar tata ta maqale. Muryar
hajja harira ce wadda ta fara da sauke mata zazzafan ashar.
"Ni zaki wulaqanta a duniya?,ni xaki toxarta
mariya?,meye ban miki ba a rayuwa?,saboda kin asircemin yarinya na miki
shuru?,an gaya miki shuruna yana nufin tsoro ne?,bakisan ja da baya ga rago ba
tsoro bane shirin fada ne?,ni xaki buga a jarida akan abinda bani da
masaniya?,ke bakisan kuskure bane tarar fada da wanda yasan sirrinka
ba?,ganganci ne tarar rigima da wanda yasan waye kai ba?......to kin tara kin
samu....mu zuba,dani dake shege ka fasa,hoto na gaba idan kika tashi tsirara
zaki sakani......hukuma kuma ina nan ina dakon isowarta gidana,qarqari idan sun
kamani su kulleni......idan kuma ya tabbata bani ke da hannu ba dole su
sakeni". Daga haka hajja harira ta katse kiran.
Wani tashin
hankalin na daban maamah taji yana sauko mata,har numfashinta taji kaman
yanason riqewa. Sam ba wani motsi data sakeyi akan hajja harira saboda
dalilai.guda biyu. Dalilim farko ita daya ce mutum guda daya data mallaki
sirrikanta ciki da bai,birnannun sirrikan da babu wanda ya sansu,babu wanda
yasan da zamansu sai ita din tak!. Dalili na biyu laila dake hannunta,tasan
wannan kadai ya isa ya zame mata daukan fansa game da cin amanar da hajja taso
tayi mata,to amma ko a yanzu ikirari da kurarin da hajja tayi mata bazaiyiwu ta
barta ba,don haka ta share gumin fuskarta ta soma tura mata gajeran saqo.
_"kiyi komai harira,bazan hanaki ba,amma kada ki manta
a hannu kike,laila tana gaidaki da kyau da kyau,tace kuma na gaya miki ki
kula,ki kuma kula da kanki"_
Kamar jira
shigar saqon yakeyi wani kiran ya sake shigo mata. Baquwar number ce da haka
kawai ta sanya gabanta faduwa,ta dinga bin number da kallo tana raba daya biyu.
Special number ce,simple da bata cika tarkacen lambobi da yawa ba,ta jima tana
kallonta kafin daga bisani dab da xata tsinke ta daga.
Karo na
farko da muryarta kawai ta saukar mata da wani mummunan faduwar gaba da bata
taba jin irinsa ba.
"Ina fatan saqona ya riskeki zuwa yanzu?,idan ma bai
iskeki ba to na tabbatar yana dab da iskeki......somin tabi ne kenan wannan
din.....iname sake aike miki da gargadi.....ki nemo min mijina kuma uban
'ya'yana a duk inda kika kaishi.....ba sassauci ba daga qafa.....idan nar yakai
awa saba'in da hudu.......abinda zai faru na gaba yafi qarfin
wannan......yanzun ba irin wancan lokacin bane.....lokacin da zaki zubdasu ki
watsar dasu a duk inda kikaga dama,yanzun rayuwarsu gewaye take da
masoyansu......rayuwarsu gewaye take da rayukan dake buqatar su,suke da
muhimmanci a wajensu.....suke muradi da mararin ci gaba da wanzuwa tare dasu,da
dadi ko ba dadi.....da dukiya ko babu,da lafiya ko babu,saboda su din
akeso.......zallar su din ba abinda ke tattare dasu na ni'ima ba".
Har sai
da maamah taji numfashinta ya sarqe guri daya da zafafan maganganun data soka
mata,to amma zuwa yanzun ko taqi ko taso tana ji a jikinta itace a hannu,duk da
tana ji nadan lokaci ne hakan zata kasance,sai maganan harira da suka gama
yanzu ta dawo mata.
_"Kuskure ne tarar fada da wanda yasan
sirrinka.....yasan waye kai ciki da bai"_ tabbas a dazun kawai.harira ta
bata wani darasi daua kamata ace kanta ya kawo mata,amma ko banza a yanzun ma
ta zamu wani ajiyayyen darasi da zai zame mata makamin yaqi tsakanin ita
hariran da sabreen.
"Sabreena......ki saurareni kiji.....kuskure kikeso ki
aikata wanda zaki dana sani daga baya.....ta yaya zan zama silar batan yaro na
kamar a film ko a rubutaccen wasan kwaikwayo?" Wani numfashi sabreen ta
sauke sannan tace.
"Komai da kika taba aikatawa a kansu a baya din ai
hankali bazai dauka ba......hakanan idan ka saurari labaran ba abinda zai hana
kace cikin litattsfan labarai ne ba cikin rayuwarmu ta zahiri ba....."
"Ba maganar baya akr ba......maganar yanzu akeyi
sabreen" Maamah ta fada karon farko tana sassauta muryarta gudun ballewar
sabreen din.
"Da da da yanzun duka daya ne......ba wani abu da zai
canzaki......ko a yanzun akwai wani abu da kikeson cimmawa shi ya sanyaki
tsaiwa kina bayanin nan,bawai don kinga ya dace kiyi ba,ba kjma wai don kin
damu da batan dama faruwar komai ba......kawai abjnda nake buqata daga gareki
shine......ki sakarmin mijina.....ki fice a rayuwata.....kije kiyi taki rayuwar
duk yadda kk so kika kuma tsara"
"Bani da masaniyar komai sabreen,karki manta
mana.....nifa uwa ce"
"Ni kuma me shirin zama uwar,uwarma kuwa ta gaske ba
MUNA UWA BA,uwar data shirya tsaf don bawa rayuwar yaranta kariya.....wadanda
zasu zo dama wadanda basu taho ba.....kariya daga dukkan wani kalar farmaki
daga miyagu da mafarautan mutane,irin kariyar da sunanta zai tumbatsa da
tambarin SADAUKARWA.....sadaukarwa mafi girma kuwa cikin rayuwar 'ya'ya akan
iyayensu.....irin sadaukarwar dake sanya kowanne yaro cikin alfahari da
kasancewar iyayensa su suka haifeshi". Wani irin nannauyan abu kalamanta
suka sauke mata......ta kuma isar mata da saqonni masu yawan gaske
da.maganganunta masu harshen damo.
"Ki huta lafiya" Magananta ta qarshe kenan da ita
tana yanke kiran.
Mayar da
dubanta tayi kan huda dake zaune a gabanta. Tun dazu da abba yazo asibitin yace
bai gamsu suci gaba da zama ba,Dr mubeena ta sallameta bisa alqawarin zata
dinga zuwa ganinta kullum don samun cikakken kulawa fiye da asibitinma.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 124
124
"Zaku
wuce kaman yadda ani ta buqata.....komai bazai fasa faruwa ba huda....komai
kuma bazai sauya ba sai abinda qaddararmu ta tanadar mana". Hawaye sosai
huda keyi,duk da yadda take qoqarin riqe kanta daga aikata hakan a gaban
sabreen.
"Zamu tafi adda da ciwo da firgici.....zamu tafi ba
tare da taqamaimen masaniya akan ina hamma yake ba......yadda ya kula da
lamarinmu muma ba zamuyi qasa a gwiwa ba wajen addu'ar bayyanarsa........da
kuma tonuwar asirin duk wanda keda hannu wajen kitsa komai da zai illata
rayuwar kamilin mutum me taimako irin hamma fu'ad".
Ba
qaramin jarumta sabreen din ta nuna ba a sanda suke sallama dasu nadra din da
yammacin ranar,sai takejin kaman zata sake tabbatuwa cikin kadaici,ta dinga jin
kamar ita daya ta rage a duniyar zata ci gaba kuma da rayuwa ne ita kadai.
*11:30 pm*
A hankali
ta farka daga wani nannauyan bacci daya saceta saman abun sallah bayan ta
kammala sallar nafilfilu da dukka addu'o'inta,ta kuma cika da sallar nan me
matuqar fa'ida da kuma alfanu wato sallar wuturi.
Hijabin
da dardumar dukka suna jikinta,alqur'aninta yana ajiye a gefe yayin da tasbahar
hannunta ta sulale ta fadi a qasa ba tare data sani ba. Ta qarasa bude idanunta
da fadin
"Alhamdulillahi ala kulli hal" Cikin kowanne
lokaci idan ta bude ido tsammani takeyi zata ga komai ya wuce tamkar cikin
duhun mafarki ne da hasken rayuwa da idanu biyu ya ratsata,saidai duk sanda
zata farka din tana samun komai a inda ta barshi,komai yana nan yadda yake.
Fitsari ne
ya cika mata mararta,ta sanya hannu ta zare hijabin jikinta idanunta yana sauka
saman tray din dake table din gefanta. Komai an shiryashi akai,tasan kuma
wannan aikin ma'u ne bisa umarnin anni.
Hatta da
dakin suna dawowa annin ta saka aka shiryashi yadda ya dace saboda jin dadinta.
Qafarta
tadan riqe saboda yanayin zaman da tayi a wajen na wani lokaci,ta miqe a
hankali tana nufar toilet. Ba jimawa ta fito daure da sabuwar alwala,tun daga
sanda ta fahimci muhimmancinta ta daina zama babu ita,musamman ita din da tasan
akwai mutum irin maamah dake gefe tana farautar rayuwarsu ta kowanne fanni.
(Koda baka da masaniyar takun saqa tsakaninka da wani wanda kake kyautata zaton
yana 'yan biye biyen shirkarsa,ka tabbatar baka zama ba tare da alwala ba,koba
komai ita din haske ce a gareka,ga kuma kariya da zata baka daga dukkan sharrin
me sharri).
Wani
sauqi sassauci da kuma rangwame take ji duk sanda ta tuna ta sakarwa maamah
wani tsoro da firgici,don tana zaune ta shiga shafukan sada zumunta,kai tsaye
ta dinga cin karo da labarin yanata trending,ga 'yan qarawa miya maggi da
gishiri sunata qawata topic din da kalar qarairayinsu. Har ta gama shawagin ta
sauka labarinne ta kowanne handle na bloggers da gidan jaridu mujallu harma da
celebrities.
Har zata
koma ta zauna taji qishirwa sosai ya kamata. Koda ta duba tray din ba zam zam
ma'u ta saka mata ba,ruwan gora ne,tana kyautata zaton kuma batasan ba kowanne
ruwa take iya sha din ba sai zam zam shi yasa,don haka sai kawai ta maida hijab
dinta ta zura flipp flops dinta ta nufi qofar.
Sanda take
takawa zuwa parlor din sai ta dinga jin wata kakkaurar murya tana magana,kaman
tasan muryar,kafin ta qarasa tunaninta kuwa tuni ta fusgo mata cewa muryar
abdulgaffar ce.
Sunan
fu'ad da taji an ambata ya sanya gabanta wani mummunar faduwa,qafafunta suka
fara slow suka gaza ci gaba da tafiya da ita,sai kuma suka tsaidata cak
qirjinta kaman zai fito waje.
"Mun samu nasarar gano inda yake.......farouq da pilot
dinsa sun fitar dashi daga qasar.......suna taipei capital na taiwan,asibitin
taipei wellness hospital and resort,mun samu magana da farouq,saidai na lokaci
kadanne ya datse kiran,alamu sun nuna bayason kowa yaji.....kuma haka mukayi
dashi,ya bani information dinne nima na through waya ba,yace idan zaiyiwu kada
kowa ya sani sai abba" Muryar anni rawa takeyi sosai,yayin da sabreen taji
wani murdewa da mararta tayi,tanaso taji ya fu'ad yake......tanaso taji halin
da yake ciki,muddin ta bayyana ba zasu fadi komai a gabanta ba ta
sani.....muddin sukaji motsinta kuma nan ma ba qarasa maganar zasuyi ba bare
tasan me ake ciki,don haka salin alin ta sulale tayi zaman dirshan a nan tana
dafe hannuwanta jikin wata kujera qwaya daya da aka ajiye a wajen.
"Me ya samesu abdulgaffar.....kada kace zaka boyemin
komai" Shuru abdulgaffar yayi yana sadda kansa qasa,har sai da abba ya
qagu shima yace
"Zauna ameena.....kaima zauna abdulgaffar....."
Dukkansu suka zauna sannan abban yace.
"Dani da ameena bana jin muna cikin mutanen da zaka
boye mana komai,shi kansa farouq din nasan bazai taba lissafamu a ciki ba,koda
zaice kada a fada din zai fada ne saboda matarsa......tana cikin lalurar da ba
komai dama ya kamata a gaya mata ba".
"Ba gatan da zakuyimin abba sama daku gayamin halin da
hamma yake ciki" Sabreen da jikinta ya soma daukan wani yanayi ta fada
cikin zuciyarta,tana jin kamar ta jawo abdulgaffar ya gaya mata komai da
gaggawa.
"Haka ne,sun hari boss ne,a sannan yana tsaye suna
magana da jordan,ya kauce basu sameshi ba,yana daga kai kuma ya hangi wanda
yayo harbin,baice da kowa komai ba ya soma dosar inda yake hangoshin,daga can
sama ne wani guri da ba kasafai aka fiya amfani da wajen bama,ganin ya hangoshi
kuma ya nufeshi sai ya sake yin harbin a jere har sau biyu don kada ya samu isa
gareshi,to amma kuma baiyi nasara ba,don harbin daya ne ya sameshi a
damtsansa,dayan ya sake wuceshi,harbin bai hanashi qoqarin cimma mutumin ba,ganin
yana dososhi da gaske kuma dab yake da riskarsa,jordan da farouq na biye dashi
a baya sai ya fara hade kayansa zai gudu. Har yayi taku biyu ana ukun ya
damqeshi yanason cire hular fuskar daya saka ya rufe idonsa,juyowar da zaiyi
kawai sai ya shaqa masa wani abu a handkerchief din hannunsa yana qoqarin
zamewa ya gudu,saidai kafin abinda ya shaqa masan ya kama jininsa su jordan sun
qaraso,qarasowar tasu kuma yayi daidai da zubewarsa a wajen,basusan waye da
waye a wajen yake tare dasu ba,basusan kuma waye ya aikoshi ba,wannan ya sanya
kawai suka yanke shawarar komawa dashi su fitar dashi daga qasar,shi kuma
mutumin sun sakashi hannun hukuma,He's unconscious har yanzu,wannan dalilin ya
hana oga farouq bayyana ko bayyana komai".
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Shine kawai
abinda anni ke maimaitawa. Komai jinsa sabreen tayi kaman tana saman gajimare
ko iska yake faruwa,ta dinga kokawa da numfashinta tanason kamoshi ta kuma kama
ayoyin Allah da zasu taimaketa,saidai ta gaza hakan har sai da sautin muryar
anni ya bayyana.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!" Tabi bayan
ta anni tana maimaitawa,saidai tata da wata madaukakiyar murya ce data fusgo
sautinta da qyar daga maqoshinta,sautin kuma ya iske anni dake zaune tana
maimaitata. Cak anni ta dakata tanaso taji sautin daga inda yake fitowa,jin
daga inda sautin yake ya sakata waiwayawa tana duban fuskar abba wanda shima
ita din yake kalla.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!!" Kalmar
data sake maimaitawa da wani irin gunjin kuka shiya ankarar da anni daga inda
sautin yake fitowa.
Da wani
gudu anni ta miqe tana nufar wajen hankalinta yana tashi,bai kamata sabreen
taji wannan mummunan labarin ba,bai kamata ba,labarin da aketa boyonshi ta yaya
ta jishi?".
A zaune
ta sameta tanata maimaitawa,wasu irin hawaye sun wanke fuskarta,jikinta kawai
rawa yakeyi,durqusawa tayi a gabanta tana kamata yayin da Alhaji hamza ke tsaye
a kansu shima yana tayata maimaitawa.
"Me kika fito yi sabreen?,me yasa kika fito?" Anni
ta maimaita a gigice tana riqeta cikin tsananin tsoron abinda zai iya faruwa da
ita. Numfashinta yana wani iri,ta tabbatar kuma tana da asthma ne irin
nata,tana tsoron kada ta sarqeta cikin wannan daren.
Zuciyarta taketa qoqarin bawa dakiya da juriya.......tanata qoqarin
maido wannan qwarin gwiwar juriya da jarumtartata,tanason dawo da old version
of sabreen dinta. A yanzu bata da wani buri daya wuce ta bude idonta taga fu'ad
din,ko a yaya yake......ko a wanne irin yanayi yake sai yafi mata nutsuwa akan
zamanta a nan.
"Ruwa zan sha anni" Ta fada muryarta tana
rarrabuwa.
Da kansa
Alhaji hamza ya koma ya dauko mata ruwan,ya miqawa anni ta bude ta bata sannan
yace.
"Maidata daki ameena,muje na bude miki qofa".
Riqeta anni tayi har yanzu suna maimaita hasbunallahu wani'imal wakeel tare.
Saman
gadonta ta ajiyeta tana jingina mata pillow
"Anni" Ta kira sunanta kai tsaye tana jin wani
jarumta yana shigarta. Kai kawai anni ta tada ta kalleta,don bazata iya tuna
yaushe ta kira sunanta haka ba.
"Kunason nutsuwata da kwanciyar hankalina?" Ta
tambayi anni still tana dubanta. Alhaji hamza dake tsaye daga bakin qofa anni
ta kalla,sai ya gyada mata kai,tasan umarni yayi mata sai ta dawo da dubanta
kan sabreen.
"Sosai sabreena.....sosai". Idanunta da takeji
hatta su sun mata nauyi a jikinta ta lumshe sannan ta bude.
"Abu daya nakeso anni da zai bani wannan
nutsuwar......abu guda daya take nake da buqata....." Ta fada tana daga
yatsanta daya,idanunta nayin wani iri kaman wadda tasha abun maye ta
maku.......
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 125
125
"Mene
sabreen?" Anni ta sake tambaya tana zama gefanta,tana jin kamar an salube
qashinta daga cikin tsokokin jikinta,tana fata ba abinda bazai yuwu bane
sabreen xatayi magana akai.
"Anni ku kaini wajensa" Ta fada a taqaice hawaye
suna cika fararen idanunta da tuni kalolinsu na fari da baqi ya jima da sauyawa
daga idanunta.
Da hanzari
anni ta kalleta,kai ta dan girgiza mata.
"Kiyi haquri ameenatu......ta yaya kina cikin irin
wannan yanayin zaki tafi ki ganshi a yanayin da yake ciki?,ba abinda yafi
buqata illa kiyi masa addu'a ki kuma kula da abinda yake cikinki......bazai
taba iya mantawa ba muddin kika kasa riqe abinda yake cikinki kika kasa rainan
masa su....."
"Bazan iya rainonsu ba anni muddin babu shi a kusa
dani.......zan fara lissafin yankewar numfashi daga gangar jikina daga yanzu
zuwa fitarsa na qarshe" Ta qarasa maganar hawayen da take tarewa suka
gangaro saman kuncinta.
Wani abu
ya ratsa anni da Alhaji hamza tun daga saman kansu zuwa tafin qarfinsu. Tsahon
rayuwarsu zasu iya cewa basu taba ganin zazzafar soyayya irin wannan
ba.....soyayya da qauna me wani irin zafi da radadi,soyayya da qauna ta gasken
gaske......soyayya ta a mutu da kowanne motsi da yanayi na abokin soyayya ya
tsayema dan uwansa a rai.
Rasa bakin
magana anni tayi,ta daga kanta tana duban Alhaji hamza da shima ya gama
sallamawa. Kai kawai ya jinjinawa anni sannan ya dubi sabreen.
"Indai don wannan ne ki kwanta kiyi baccinki sosai,daga
gobe zuwa jibi in sha Allah zan siya mana tickets na fita taiwan......zakije ki
ganshi....amma sai kinyimin alqawarin daga yanzu harmu tafi ba zaki sake damuwa
ba......kuma zaki sakeyimin alqawarin idan munje ba zaki daga hankalinki
ba.....ko a yaya kika sameshi zaki sawa zuciyarki nutsuwa da kwanciyar rai har
ya samu lafiya kamar yadda muke kyautata zaton hakan". Kai ta shiga
jijjigawa a jejjere.
"Nayi maka alqawari abba.....nayi maka in sha
Allah". Kai ya gyada shima,wani irin tausayinta yana kamashi,ya yiwa anni
alama da hannu sannan ya juya yana fita.
Saida
anni ta tabbatar ta kwanta ta kuma nutsu,sannna ta saka mata karatun qur'ani
qasa qasa kusa da ita,ta kira mata ma'u suka kwanta tare sannan ta fice.
Tana jin
fitar annin,saita runtse idonta tana jin wani rauni yana saukar mata,kuka
takeso tayi wanda batasan iyakarsa ba,amma kuma sautin qur'anin da yake shiga
kunnenta ya bata wata irin cikakkiyar nutsuwa,a hankali ta sake maida idanunta
ta rufe,saita dinga jin kaman wani tabbaci take samu daga zuciyarta na samun
nasara da sauqi a dukka al'amuranta,ta sake imani da wannan ayar da take cewa.
(Ku saurara,da ambaton Allah kadai zukata suke samun
nutsuwa).
A dan
gaggauce anni ta qarasa dakin Alhaji hamza,ta dubeshi,waya yakeyi yana daga
tsaye a daren,batasan koda waye yake wayar ba duk da dare ya soma nisa,sai ta
zauna tana jiransa ya kammala. Ba jimawa ya kammala din,ya dubeta yana aje
wayar
"Na saka su dubamin tickets ne xuwa taiwan.....na gobe
ko na jibi,ina zaton kuma sai jibi ma za'a samu".
"Amma abba.....kana ganin ya kamata mu dauketa mu kaita
ta dinga ganinsa cikin engine da tashin hankali?kasan tabbas sai muhammadu yafi
son rayuwar yaran nan da nashi rayuwar?,kasan sai yafi qaunar ta kula da kanta
da lafiyarta akan tashi?." Dan murmushi ne ya subucewa abban,sai ya zauna
gabanta yana dubanta.
"Ameenatu.....zuciya da ruhin soyayyarsu ba gama gari
bace irin ta kowa.....karatun da na yiwa soyayyarsu shine.....suna sake qaunar
juna da tsananin son kasancewa da junansu a sanda jarrabawa ko musiba ta samu
daya daga cikin su,sunfi qaunar duk tsanani su kusanci juna akan suyi nesa da
juna......sabreena ba zata taba samun nutsuwa ba.....ba zamu taba samun yadda
mukeson gani ba muddin bamu sadata da barin ruhinta ba.....xakisha mamaki idan
kikaga tafi nutsuwa a can fiye da anan din duk da unconscious yake?" Ya
qarasa maganar da tambaya yana duban idanun anni. Shuru annin tayi tana juya
maganar abban. Ta jima bataga soyayya me zafi jini da hanta da zuciya harma da
b'argo irin tasu ba.
Kanta ta
gyada a hankali bayan ta gama nazarin,ta kuma yarda da maganganun abban dari
bisa dari don itama taga hakan.
"Allah yayi mana jagora,ya taqaita dukkan wahala da
sharrin masu sharri"
"Allahumma ameen" Ya amsa mata yana miqewa.
_TAIWAN_
_TAIPEI_
*_Taiwan Taoyouan international airport_*
Yammaci ne
sosai sanda suka sauka a taiwan,misalim qarfe hudu na yammaci,wanda yayi daidai
da qarfe sha daya agogon nigeria.
Da yake
tafiya ce bata shiri ba,cikin motocin da gwamnati ke ajiyewa saboda baqi da
wadanda ke buqatan hayar da zaiyi driving da kansa,ya gama adadin kwanakin ka
maida inda ka karbo ita suka karba.
Abdulgaffar
ke driving din,yana yi yana duba map da address din da ya samu da zai sadashi
kai tsaye da asibitin.
Duk yadda
garin yakai ga kyau tsaruwa da daukan hankali ba wannan bane a gabanta,bama
kasafai take iya fahimtar inda suke wucewar wa,burinta kawai.shine su isa
asibitin,burinta kadai shine ta ganta a gabanshi,burinta ta ganshi a gabanta ta
daina jin cewa yayi mata wannan nisan da kowacce rana zuciyarta da gangar
jikinta suke jiye mata.
Tafiyar
mintuna arba'in suka fada ainihin titin asibitin,ba wani wanda yake iya cewa da
danuwansa komai. Saddiq musaddiq abba da anni......ballantana sabreen da take
ganin kaman laqai laqai kawai abdulgaffar yakeyi bawai tuqi ba,kaman tafiyar
kunkuru yakeyi,kamar ma bayason ya sadasu da asibitin.
Mintina
sha biyar map ya nuna musu suna daidai asibitin,suna shiga titin shine gini na
farko daga hannun dama.
Idonta ta
daga a hankali tana kallon tsararre kuma ajiyayyen ginin asibitin,wanda ko ba'a
gaya maka ba kasan cewa gurine me cike da tsari da tsananin kulawa,guri ne kuma
da lafiya ke tsaye da qafafunta.
Karo na
farko data soma yarda da gaske ko a qasashen waje akwai rayuwar masu hannu da
shuni akwai ta tsaka tsaki akwai ta talaka. Tun kafin sukai ga shiga asibitin
checking nasu da akeyi kadai ya isa ya tabbatar maka akwai tsaro sosai cikin
asibitin. Checking da ya sanya ta dinga jin kaman wani salo ne na hanata isa
garesa.....kafin yafi tsaye mata a rai sama da zaman da sukayi cikin jirgin
kafin isowarsu taiwan.
A muhallin
da aka tanada saboda ajiyar motoci abdulgaffar ya tsaida motar sannan ya
kasheta. Ta daga idanunta tana jira taji wani a cikinsu ya bude motar da zummar
fita amma bataga kowa ya motsa ba. A nutse Alhaji hamza kibiya ya fiddo wayarsa
sannan yayi kira,kiran da duka duka bai wuce minti daya ba
"Muns parking lot" Abinda ya fada kenan ya yanke
kiran yana dubansu.
"Muje ko.....ga Jordan nan zuwa". Kiran sunan
Jordan kadai ya sanya jikinta ya fara rawa,a kasalance ta sanya qafafunta waje
tana ambatar sunan Allah bayan musaddiq ya bude mata murfin motar,sai taji
jikinta kamar yayi nauyi ta dafa murfin tana fitowa.
Komawa
gefenta anni tayi tana saka hannuwanta cikin nata,ta daga kai suka hada ido da
anni.
"Karki manta alqawarinmu,kada ki sabashi......be strong
please ameenatu......na sani ke din jaruma ce" Kai ta gyadawa anni,bawai
don a yau tana jin wannan jarumtar ba,ta dade da sani da kuma fahimtar indai
akan fu'ad dinne bata da wani sauran jarumta daya rage,ita din raguwa ce ta
qarshen qarshe.
A hankali
suka fara takawa suna dosar main entrance na asibitin,wanda basuyi taku goma
cikakke ba saiga Jordan din,sukayi kacibus dashi a hallway din yana fitowa daga
elevator.
Kallo
kawai sabreen take qarewa Jordan,abinda bata taba yi ba,saidai koda bata taba
qare masa kallo ba amma ta sani yana da qiba da kuma tsaho gami da murdewar
jiki,amma a yanzun abinda idanunta suke iya gane mata shine zubewar da yayi. Ya
rame sosai duk da har yanzu wannan kuzarin yana tattare dashi,abinda ya sanya
dukka gwiwoyinta yin bala'e'en sanyi tana jin tabbas ko meye ya faru da
hammanta ba qaramin abu bane,abun har ya taba jordan har haka?.
"Welcome madam" Ya fadi mata yana tsaye daga
gefanta cikin tsananin girmamawa tausasawa da kuma kulawa. Bata iya amsa masa
ba,sai idanunta data zare daga kansa gudun kada taje ta rasa ragowar qwarin
gwiwar data rage mata.
Musaddiq
da abba da jordan su suka fara wucewa saman,kafin su kuma su kuma da saddiq su
kira wani elevator din suka shiga suka bi bayansu.
Farouq ne
mutum na farko data fara hangowa yana fitowa daga wani balcony na daban bayan
doguwar hanyar da kebantattun amenities suke. Faduwar gabanta ya sake tsananta
saboda ganin irin zubewar da jordan yayi akan fuskar farouq. Ta kasa dauke
idanunta a kanshi,kaman yadda ta lura shima din ita yake kallo. Suna takawa
zuwa inda yake shima yana matsowa garesu,har suka riski juna a hanya.
"Adda......haka kika koma?" Farouq ya fadi a
raunane yana jin wani irin tausayinta yana ratsashi. Karo na farko da yaji
yarda dari bisa dari yau yayi ido da ido da salon soyayyar da yakeji a ransa a
baya cewa babu irinta a duniyar zahiri......saidai a duniyar litattafai da kuma
fina finai.
Kanta ta
dauke tana qoqarin hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya.....tambayarsa kulawa
ce ta kawota.....amma da zaiyi mata wani abu da yafi wannan tambayar faranta
mata rai. Ya sauketa da labarin halin da hamma fu'ad yake ciki.....ya gaya mata
yanayinsa shi zaifi komai mata dadi.
"Kaima bakaga yadda ka koma ba BB?" Ta qarashe
tambayar tana kallon fuskarsa kai tsaye muryarta tana rawa,tana fatan ganin
wani mode da zai bata haske akan yanayin da fu'ad din yake ciki.
Wani
busashen murmushi yayi yana kada kansa,sannan ya maida dubansa gasu anni.
"Sannu da zuwa abba.....anni sannu da zuwa".
"Muje farouq ciki....muje dakin" Anni data kasa
haquri ta fada tana yin gaba sabreen kuwa ta sanya qafafunta ta rufa mata baya
kai tsaye xuwa dakin da sukaga farouq din ya fito.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 126
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
126
Daga balcony
din ma'aikatan lafiyar wajen suka tsaidasu,kowanne aka bashi riga da hula ya
sanya,sannan suka musanya takalman qafarsu zuwa wasu ajiyayyun tsaftatattun
fararen Crocs da suke wajen.
Lafiyayyen
parlor ne wanda aka tsarashi cikin wani irin yanayi da zai bawa me jinya dama
wanda ake jinyar yanayi me kyau,bisa wadatacciyar iska da haske,irin iskar dake
fitowa daga tsirran da aka wadata bayan dakunan dasu,wanda kana iya hangen
komai tarwai ta gilasan da dakunan ke dashi daga gaba.
Sam
parlor din baiyi kama da asibiti ba,an saka sofas set guda,tv plasma freezer da
side tables da babba guda daya,curtains da komai na parlor din fari ne qal
tamkar hannu baya tabawa saboda tsananin kula da tsafta,hakanan qamshi ne me
kwantar da hankali kawai yake fita.
"Akwai likita a ciki a tare dashi,bibbiyu bibbiyu nake
ganin ya kamata a shiga......" Farouq ya fada yana rarraba idanunshi
tsananin fuskokinsu.
Sulalewa
tayi ta zauna saman sofa din,koda farouq yace ta fara shiga batajin zata iya
hakan,gwara a cikinsu wasu su fara shiga din,yanayin fuskar kowannensu shine
zai bata qwarin gwiwar shiga ko akasin hakan.
Kaman
anni zatayi magana sai kuma ta fasa,ita da abban sukayi gaba farouq yana musu
jagora suka buda qofar suka shige.
Zaman
jiran fitowarsu annin ba wani abu bane me sauqi a wajenta,sai ta jita tamkar
tana zaman jiran isowar layin mutuwa kanta,kanta a qasa ta saka hannuwanta
dukka biyun ta dafe kanta tana jin yadda zuciyarta ke harbawa kaman zata fado
qasa. Wani motsi takeji mararta tanayi,baqon abune da bata taba jinsa ba sai a
ranar kamar ana d'allinta da yatsa.
"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa
huwa rabbul arshil azeem" Ta dinga maimaitawa labbanta kadai ke motsawa.
Da yatsunta ta dinga irga kowanne wucewae second,tanajin kaman suna wucewa da
kowanne dama na rayuwarta,tana jin kamar suna wucewa ne da farincikin rayuwarta
gaba daya.
Sai da
su abba suka kwashe mintuna kusan goma harda doriya kafin taji fitowarsu. Duk
yadda taso daga kai ta kalli reaction na fuskarsu ta gaza yin hakan,ta kasa
koda motsawa,tana jin tsoron abinda zata daga ta gani tattare dasu. Saidai
takum tafiyarsu su biyun bata tsinci komai a ciki ba,karsashi ko akasin
hakan,wanda hakan ya sake sanyata a taraddadi me yawa da kokwanto.
"Ni zan shiga" Ta fada da wani irin fusgar kalma
cikin ba zata a sanda saddiq da musaddiq ke takawa zuwa qofar dakin.
Miqewa
tayi ta zauna sosai tana dubansu sanda suka dakata daga shigar da juyyayyun
idanunta,tana jin kamar kafin su shiga su fito zata iya rasa numfashinta da
rayuwarta gaba daya,koma meye gwara ta shiga ta gani ta kuma fuskanceshi
da.dukkan iyawarta,da wannan qudurin ta taho,ba kuma zata iya canzashi ba.
Da baya
suka dawo,ba wanda ya musanta mata ko yace wani abu,saita miqe a hankali tana
jin kamar qafafunta ba zasu dauketa ba ta doshi dakin.
Ta kusa
sakkani talatin riqe da handle din ta kasa murzawa,har sai da muryar farouq
dake bayanta ta dawo da ita daidai
"Are you okay?" Ya tambayeta yana leqen fuskarta.
Kai ta gyada masa.
"Ko na bude miki?" Ya sake tambaya cikin kulawa
saita girgixa kanta ta kuma tattara gaba daya qarfin daya rage mata ta murda
qofar tana shiga.
Jijiyoyin jikinta ne taji tamkar suna tsinkewa,numfashinta kamar an
musanya mata da wani abun daban me tauri bawai lallausan iskar da kowanne me
rai yake shaqa ba. Ta dinga ganin idanunta kaman gizo suke mata,ba ainihin
abinda zata gani bane take gani......gani take zolayarta kawai idanun nata
sukeyi saboda abinda take kwana ta tashi da fatarsa kenan.....abinda take kwana
ta tashi tana mafarki da burin ya kasance kenan.
Yana
zaune saman gadon da aka tallafo bayansa aka dago kan gadon sosai yadda zaiji
dadin zama. Jikinsa sanye da rigar asibitin ruwan sararin samaniya me haske
sosai. Lallausan blanket ne lullube da qafafunsa zuwa qugunsa.
Fararen
idanunsa tarr bisa fuskarta,idanun da suka dan rusuna kamar wanda bacci yake
cike a idanun nasa. Kallon kallo ya wanzu a tsakaninsu,zukatan kowannensu yana
bugawa da sauri da wani irin doki da zumudin ganin daya bangaren zuciyar tasa.
Wasu
irin abubuwa ya dinga sakar mata suna ratsa sassan jikinta......wani irin
shauqi mahaukaciyar soyayya da zazzafar qauna ke kurdawa ta kowanne lungu na
zuciyarta. Kewarsa me matuqar qarfi ta taso ta lullube zuciyarta ta sakata jin
wani rauni na mamayarta,take idanunta suka cika da hawayen da bata da ikon
tsaidasu.
Hannunsa
daya ya miqa mata yana ware mata su alamun marabtarta yakeyi,cikin wani irin
zaquwa da dokin isowarta gareshi,batayi wata wata ba ta soma takawa da sassarfa
zuwa inda yake tana jin kaman lokacin isarta inda yake ma ya mata
yawa.....inama zaiyiwu ta zama walqiya cikin qiftawar idanu ta samu isa
gareshi.
Jikinsa
ta fada gaba daya kuka yana qwace mata,tsam ya riqeta cikin jikin nasa yana
mata kyakkyawan masauki zuciyarsa na tsananta bugu cike da wani bahagon
so,idanunsa suka dinga lumshewa da kansu,dumin jikinta yana ratsa qashinsa
bargo harda jinin dake harbawa kowanne sashe na jikinta. Hannunsa daya ya sanya
ya riqo fuskarta,idanunta yake son kallo,qwayoyin idanun nan nata da yayi
matuqar kewa yakeson gani.
Bata
hanashi ba,ta daga oily eyes dinta masu sheqi da suka jiqe da hawaye tana
kallonsa. Nutsewa idanunsu sukayi cikin na juna,wani irin feeling ke ratsa
kowannensu wanda yafi qarfin baki ya bayyanashi. Wani deep connection ya qullu
a tsakaninsu,magana ce tsakanin zuciya da zuciya kawai wadda tafi qarfin baki
ya bayyanata. Idan ya motsa labbansa sai yaji sun masa nauyi.....sai yaji kaman
sunyi kadan su isar da saqon da zuciyarsa keson fadi
"Sabrrrr" Ya samu ya fusgi kalman da qyar
zuciyarsa naci gaba da bugawa. Itama kaman zai bace mata takeji daga qiftawa
qwaya daya tak da zata yiwa idanunta,don haka ta motsa labbanta ba tare da
amsar NA'AM din da takeson furtawa ta fita a bakinta ba.
"Love is in the eyes.....eyes don't
lie.....sabrrrr.....kalli idona.....me kika gani?" Ya motsa labbansa ya
fada da wata irin narkakkiyar murya irin wadda soyayya ta yiwa lahani.
Inda yasan
yadda qwayoyin idanunsa suke narka mata bargo da bai buqaci ta kallesu har haka
ba....saidai kuma kallon nasu wani abune na musamman cikin ruhi da zuciyarta.
Ci gaba tayi da kallon idanun nasa.....taga abubuwa masu tarin yawa.....taga
abubuwa masu yawan da sai da taji kaman zata zauce,duka ita daya?,duk ita daya
muhammad fu'ad kewa wannan zazzafan son?.
Hannu ya
kama ya riqe kumatunta yana aza shimfidadden murmushi kan fuskarsa.
"You're a thousand miles away.......but no one else is
closer to my heart than you are" Ya qarasa fada yana kama fuskarta sosai
gami da hade goshinsu guri daya.
Musayar
numfashi suka fara yi a tsakaninsu,kowanne yana shaqar numfashin da dan uwansa
ya fesar,hakan na sake qara musu wani qaqqarfan alaqa tsakaninsu data tsananta
bugun zuciyarsu duka su biyun.
"Zan iya mutuwa.......Allah zan iya mutuwa idan ka sake
matsawa daga gareni irin wannan matsawar da kayi.......zaka iya rasani......ka
rasa kuma babies dinmu gaba daya" Ta qarashe maganar tana sakar masa kukan
da ya koma zuwa na shagwaba kuma a wannan lokacin.
"Nayi alqawari DUNIYATA.....nayi alqawari bazan qara
ba,i promise" Fuskarta ta qwace ta cusata cikin qirjinsa tana shaqar
wannan tattausan qamshin nasa da tayi matuqar kewa kamar zata zauce.
"I pray to god that you will stay permanently in my
life".
"I pray too my world" Ya fada yana kissing
tsakiyar kanta. Qanqameshi tayi da kyau don sake bawa kanta tabbacin reality ne
bawai mafarki ba. Kalmar "wash Allah na" Daya fada ita ta sakata
saurin sakinsa tana kallon fuskarta.
Idanunan
dai nashi ya zuba mata murmushi na fita a fuskarsa,sai ta tabe baki kaman zata
saki kuka. Da sauri ya mata nuni da hannunsa,ta waiwaya a hankali zuwa sashen
da yake nuna mata din.
Miqewa
tayi ta zauna da sauri saidai ya hanata hakan,ya jawota jikinsa ya maidata
sosai yadda zaici gaba da jin qamshinta da duminta.
"A nan suka harbeka?" Ta tambayeshi a sanyaye da
wani irin emotion na bacin rai saman fuskarta. Girarsa kawai ya dage mata yana
dubanta har yanzu fuskarsa da murmushi duk da yadda yadan fada kadan.
"Allah ya isar mana....Allah ya saka mana"
"Very soon duniyata......mu ajiye wannan maganar
yanzun......i need you duniyata.....kaman dazu naji kince babies instead of
baby right?" Ya tambaya yana tsareta da idanunsa. Tsam tayi tana
dubansa,sai kuma ta saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta
dasu.
"Yes......twins n....." Bata qarasa fada ba taji
yana lalube rigarta,saidai jikin ba qwari kwata kwata da alama don haka ya
ajiye hannun nasa yana maida numfashi. Koda ta kalleshi kwantaccen hawaye ta
gani saman idanunsa,batasan me yasa akan duk abinda ya shafeta ba shi rago ne
na gasken gaske.
"Please sabrrrr......ki dagamin rigar na gani,haka
Allah ke sona?" Yadda yayi maganar da gaske abun ya taba ranshi,ba zata
iya hanashi ba,don haka ba musu ta miqe ta yaye abayan jikinta,tayi qasa da
under wear dinta take farar fatar cikinta ta fito. Jawo qugunta yayi sosai,a
hankali ya aza labbansa saman mararta.
Har
tsakiyar kwanyarta taji wani yaarrrrr,wani abu ya tsarga mata ya saukar mata da
wani irin yanayi a sassan jikinta. Lips dinsa nakan marartata ya daga idanunsa
ya kalli yanayin fuskarta,kunya ta sakata runtse idanunta sai ya aje mata
tattausan kiss sannan ya janye bakinsa
ba tare daya saki rigar ba. Batasan me ya karanta ba,amma ya kusa mintina biyu
bakinsa yana motsi kafin ya matsa kusa ya tofa mata abinda ya karanta din,ya
sake kai hannunsa ya aza akai ya sake karanta wasu addu'o'in sannan ya sake
mata rigar.
Still
hankalinta yana kan hannunsa,tayi taku biyu zuwa wajen ya sake jawota jikinsa
"I really missed you......kiban koda 10minutes naji
duminki......ban taba zaton zan sake rayuwa ba......dazu na tashi daga suman da
nayi duniyata" Yayi maganar yana aza kansa saman kafadarta,yana jin ya
samu wani peace daya dauke masa duk wani abu da yakeji a jikinsa da zuciyarsa.
Idanunta
sukayi rau rau da hawaye
"Ko waye wannan bazan taba yafe masa ba.....ko
wayeshi" Ta fada muryarta tana rawa. Ya buda baki zaiyi magana muryar
farouq ta ratso dakin,yadan bude qofar kadan amma fuskarsa da idanunsa sun basu
baya.
"Su musaddiq kuwa zasu samu yin dubiyar nan?,ko kuma su
koma kawai sa dawo?". Sassanyan numfashi ya aje kafin ya motsa labbansa.
"Bansan me yasa baka da imani ba farouq....aidai ka
tausayamin ko?.....na yafe dubiyar,kaima ka bisu kuje ku huta......thanks so
much dude". Baki kawai farouq ya sake,ya dauka fu'ad din zai tuna dasu
anni a wajen ya sakaya zancansa?.
" Dama shi dan adam butulu ne ai,na maka welcome to the
world ai ko?,alright.....but kasan hannunka yadda yake......yana buqatan a kula
dashi.....still itama me jinyar taka ba'a dade da sallamarta daga asibiti
ba.....banajin she can take good care of you".
"I can BB.....i can wallahi" Sabreen ta samu kanta
da fadin haka ba tare da wani kunya ko d'arr ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 127
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
127
"Pay no
attention to him,brush him off" Fu'ad ya fadi yana lalubenta,abinda ya
dameshi kawai shine yaga abinda ya sameta don yaji farouq yace bata da cikakken
lafiya.
Fes farouq
yaji abinda dukkaninsu suka fada,ya jijjiga kai yana mamaki
"Fu'ad......farouq ne fa?,lafiyanka nake magana kana
gwaleni?". Hannun sabreen ya kama ba tare daya waiwaya sashen da farouq ke
tsaye ba,a yanzun baya buqatar kusanci da kowa idan ba ita ba.....idanma akace
wani zaya zauna dashi a dakin ai yana ganin an gama zaluntarsa. Yasan tsiyar
farouq tsaf zaice shine zai zauna dashi saboda mugunta,yadda ta gayawa farouq
kai tsaye zata iya kulawa dashi ya matuqar burgeshi,don haka ya qara
encouraging nata.
"Take what he says with a grain of salt,dont let him
get to you" Ya fadi yana sake juya hannuwanta yana dubawa.
Salin alin
farouq yaja qofan yana wucewa,saidai a ransa ya ayyana dashi fu'ad din yaci
tuwo,zaisan kuma miya yasha
"What's wrong with you my world?" Ya tambayeta
yana tallafo fuskarta,yaga alamun bata fahimta ba sai ya canza salon tambayar.
"Farouq.....yace baki da lafiya.....da gaske ne?"
Murmushi ta sakar masa,ta miqa hannunta a nutse tana kama habarsa me cike da
kwantaccen gashi.
"Kana tunanin zan iya lafiyayyar rayuwa sanda ake
shaidamin muffin dina yayi batan dabo cikin DUNIYARSA?" Tambayar ta sanya murmushi kubce masa
shima,ya girgiza kai yana kallon zara zaran eyelashes dinta.
"Wannan ciwon nayi.....amma daga yau na warke in sha
Allah". Knocking na qofar da akayi shi ya katse musu wannan daddadan
tattaunawar,ya kalleta yana dan hade rai da alamun gajiya da rashin jin dadi a
fuskarsa.
"Inda zai yiwu.....zan sanya a sauyamin dakin da babu
wanda ya sanshi bare a dameni" Idanu ta waro waje tana miqewa a nutse.
"Da BB yace na hure maka kunne....kuma daka cika me
butulci".
"Kibar ganin farouq haka duniyata....zai iyayin abinda
yafi nawa"
"Qarya kakemin......kunyarka tafi tawa yin
qaranci" Muryar farouq din ta ratsa dakin sanda sabreen ta bude
musu,itadai sai tayi baya tana boye fuskarta. Da idanu kawai ya bita yana sake
ganin ta canza masa,ko takan tsiyar da farouq keyi masa da raddin da yake maida
masa baibi bama sam sam.
Likitansa
ne ya shigo a bayan farouq din,sai fu'ad ya kimtsa yanayin fuskarsa ta hanyar
rage fara'arsa yana duban sabreen.
"Ki shiga toilet ki gyara lullubin kanki
sosai.....banaso ko gashi daya ya fito" Ya qarasa fada yana maida dubansa
ga likitan wanda dauke idanunsa kenan daga kan sabreen din.
Fuska a
hade fu'ad din ya kalli farouq sanda likitan ke buda qirjinsa yana auna gudun
zuciyarsa.
"Ka gaya masa,He should look down when she's
around,matar aure ce".
"Tashin hankali" Farouq ya fadi,yasan ba qaramin
daru za'a sha ba.....kowa ma sai ya shiga uku muddin duniyarsa tazo......wannan
ya sanya yaso ya boye har sai ya fara samun lafiya da kuma sauran dalilai na
tsaro da sukeso su gama binciken duk wanda keda hannu a cikin attack din ba
tare da kowa ya ankare ba. Yasan da biyu ya fadi ragowan maganan da turancin
englishi,dole yasan likitan zai fahimci wani abu.
Sanda ta
dawo daga toilet din gyaran mayafin kujera farouq yaja mata yace
"Zauna a nan" Ya fada yana ajiyeta kusa dashi.
Likitan yaci gaba da duk wani dube dubensa,ya kammala yayi rubuce rubuce ya
ajiye file din ya fita farouq ya bishi.
Idanunta
still akan hannun,har yanxu tana jin ciwon kaman cikin jikinta,yanzu kenan ida
harbin ya subuce ya sameshi a inda ba'aso yanzun da wani zancan daban kenan
akeyi?.
"Subhanallah" Ta samu kanta da furtawa tana dauke
idanunta sai caraf suka fada cikin nasa. Abinda bata sani ba kallonta yakeyi da
duk wani motsi nata. Ya miqa mata hannu yana daga kwance rigingine. Kafadarta
ta noqe tana dubansa a shagwabe.
"Kasan wadanne irin wahalallun kwanaki na dinga yi
cikin duniya kuwa?" Idanunta suna tara hawaye har batason tuna wannan
kwanakin.
"Inda nine inajin da tuni fargaba ya
kasheni.......kinsan adadin son da nake miki kuwa?" Kallonsa take har bata
qiftawa,tanason gwada ma'aunin sonsa a zuciyarta da yadda yake iqirarin nashi
yafi nata.
"Kina tantama ko?" Ya tambayeta da murmushi,kafin
wani ya sake cewa komai a cikinsu an sake shigowa.
Anni ce da
musaddiq saddiq abba da farouq gaba daya,kunya ta lullubeta,tayi qasa da kanta
tana niyyar tashi a wajen anni tace
"Yi zamanki" Suka koma saman ragowar sofas din
dake dakin suka zauna. Duk budurinnan gogan idanunsa yana kanta bai iya dauke
idanunsa ba sam sam.
Sabuwar
gaisuwa da jaje suka sake yiwa juna,dakin yayi shuru sanda farouq yake bada
labarin yadda abun ya kasance.
"Kaman gawa mukazo dashi abba......dazu da safe ya
farka......amma ko jiya da daddare bayan an gama wasu test likitan ya sake
jaddada mana abinda suka shaqa masan guba ce me qarfi....kuma idan ya wuce yau
bai farka ba ICU zasu maidashi.....cikin hukuncin Allah sai gashi ya farka da
yake yaji a jikinsa duniyarsa tana hanyar zuwa gareshi". Kunya sosai ta
sake kama sabreen,tayi qas da kanta tana jan mayafinta. Abba da annin duka
dariya kawai sukayi,saddiq ya bude abincin da sukayi takeaway da complete set
da plate da spoons ya soma zubawa kowa ma'u tana tayashi.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 128
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
___________________________
128
ma'u tana
tayashi. Parlor abba ya fita don amsa waya,sai sukaci gaba da tattaunawa a
tsakaninsu.
Zukata
sunyi sanyi sun kuma samu nutsuwa daidai gwargwado,sauran abinda ke cikinsu
bashi da yawa,godiya kawai sukema Allah daya tsallakar dasu daga fuskantar
wannan bala'in.
Idanunsa
yake saukewa a kansu,kowa cikin walwala yake da farincikin samun
kubutarsa.....kowa kuma a cikinsu soyayya da qauna ce irin ta fil'azal
tsakaninsu,amma abu guda dake taba zuciyarsa shine sam ba MAAMAH ba dalilinta.
Maman daya kamata itace a gaba kafin kowa?,maman daya dace a bisa mizani na
hankali dacewa da kamata ace itace damuwarta ta dara ta kowa.....ta d'ara ta
babarsa anni.....ta d'ara ta 'yan uwansa,ta kuma d'ara ta matarsa......saidai
sabanin hakan maamah din itace halittar da tafi kowacce halitta rashin damuwa
da yanayin nasa,sai ya maida idonsa ya rufe yana jin wannan zafin har tsakiyar
zuciyarsa.
Saddiq ya
gama da kowa farouq ya dubi musaddi
"Zubawa dude ka bashi ko kadanne ko zai karba".
Harara fu'ad ya zubawa farouq,yaso ace su anni basu wajen da ya bashi amsa
daidai dashi. Idanunsa ya juya a hankali inda sabreen ke zaune tana juya zoben
dake yatsanta,don ita ba kowanne abinci take iya ci ba.
"Ke ba zakici abincin ba?" Ya fadi da wata murya
can qasa yana mata kallon qurilla. Sau daya ta dago kai ta kalleshi ta mayar
qasa tana ci gaba da juya zoben hannun nata.
"Na qoshi". Motsawa yayi kadan yana son gyara
zamanshi.
"Zubo kizo nan" Ya sake fada ba tare daya dubi
inda anni take ba.
"Yauwa....gwara ka tilastata taci,ko ba yawa aizai
zauna,ta yaya kina da lalura amma cin abinci ya zama yaqi ameenatu?".
Idanunsa ya sake maidawa kanta,sunan ameenatu yana masa dadi sosai,idan ya
kalli fuskarta yakuma ambaci sunan sai yaji tayi bala'in dacewa da
sunan,musamman idan ya tuna tarihin asalin me sunan.
A kunyace
ta miqe,ta zuba komai dan kadan kadan sannan ta dawo.
"Zauna a nan" Ya nuna mata gefansa. Dan satar
kallon anni tayi kafin ta zauna din tana bada tazara kadan tsakaninsu sannan ta
ajiye plate din a tsakiyarsu.
Spoon ta
zura masa a ciki ta kalleshi,sai ya langabe kai yana bata fuska.
"Bazan iya ci ba.....aikinsan bani da lafiya ko?"
Sai kuma yayi qasa qasa da muryarsa yana satar kallon farouq.
"Idan kuma so kike farouq yayi mana dariya ya yadda da
gaske ba zaki iya bani kulawa ba to".
"Anni muffin.....anni a gurin"
"Kada ki damu,ita hirartama take dasu saddiq,ita kanta
zatafison taga kina kula dani......oya bani abinci" Ya fada yana lumshe
idanu saboda yadda yakejin wani yanayi yana ratsashi.
A
d'arare ta debo abincin ta taho dashi bakinsa,sai ya kauda kai yana kallonta.
"Eat first" Ya fadi yana tsareta da ido. Fuska ta
bata,batasan ta shagwabe masa ba tace
"Hamma.....bazan iya ci ba".
"Zaki iya.....zakici in sha Allah,kada kiji tsoro"
Ya bata tabbaci yana kallonta. Da kadan da kadan ta dinga miqa cokalin bakinta
har ta juye abincin,ta soma taunawa tana rolling idanunta cikin tsoron kada
amai ya biyo baya,sai taji zuciyarta ko cikinta basu wani hautsine ko juya ba
yadda suka saba ta hadiyeshi tsaf.
"Good girl.....am next" Ya fada yana gyaran
zamanshi. Debowa tayi ta miqa masa,ya bude baki ya amshe kaman qaramin yaro.
"Hmmmm........dadin abincin daya fito daga hannunki
daban yake......ban taba jin abincin da yayi dadin wannan ba......Allah ya
qarawa hannuwanki da rayuwarki albarka". Ya fada yana lumshe ido a kanta.
"Ameen" Ta amsa tana sadda kai tana satar kallon
dakin. Wayam ta gani,ba wanda ta samu a dakin duka sun fice ba tare da tasan
sanda suka fice ba,saita dawo da dubanta kan fuskarsa idanunta a warwaje.
Dariya me qaramin sauti ya saki
"Sun gudu......they can't wait to see" Fuska ta
tabe ta kyabe baki kaman zata saki kuka
"Kaga irinta ko?"
"Wayyo Allah hannuna" Ya fada shima yana karyar
dakai gami da riqe hannun da daya hannun. Tuni ta watsar da komai tayi wajen
tana riqe masa a rude.
"Sannu.....da zafi ko?,fama maka nayi?,yi haquri.....ko
a kira Doctor" Yadda ta fadi doctor din sai labbanta suka masa wani mugun
kyau. Lallausan kiss ya saukar mata saman lips din yana dariyar yadda ya cita
wasan,ya samu hanya mafi sauqi na sake kusantar da kanshi da ita.
Sai kusan
dare can sosai sannan su anni sukayi niyyar wucewa masaukinsu. Ya tsareta da
ido ganin tana hada jakarta da tarkacenta,a ransa yakejin muddin tace zata wuce
tabi su anni saidai su tafi tare,don kuwa bazai zauna ba shima tana wani gurin
yana wani muhallin na daban.
Kamar anni
tasan abinda yake tsarawa,ta ciro wani babban envelope ta aje mata a gefanta.
"Ga magungunanki nan.....kada ki kwanta baki sha
ba.....mun wuce gida mu,sai gobe idan Allah ya kaimu.....saiki kula
dashi....muhammad Allah ya qara afuwa,sai da safe". Har baisan sanda
murmushi ya kubce masa ba,yasa hannunsa me lafiya ya shafi kansa.
"Ameen anni,na gode sosai,Allah ya qara girma" Ita
kanta annin tasan godiyar da biyu ake mata ita,batace komai ba dai ta
shanye,har sunkai qofa ta waiwayo.
"Ki kula da kanki da kyau,kada ki manta da abinda
likita ya fada" Ta qarasa maganar tana sauke dubanta kan fuskar fu'ad. Ko
batayi maganan kai tsaye ba ya fahimci shi anni ke ajiyewa saqon,saboda haka
suna fita ya jawota jikinsa yana cewa.
"Ni za'a yiwa gulma?,wai anaso ana kaiwa
kasuwa......kinsa anni ta tsareni da warning,wannan maganar da biyu aka
yita,kuma dani ake nasan......ita anni ta jikokinta kawai take bata ta
d'anta" Ya fadi yana sansana kunnenta,abinda ya sanya tsigar jikinta
xubawa,ta yunqura da niyyar gocewa a jikinsa,sai ya fake kaman yadda ya saba.
"Wayyo hannuna" Dawowa tayi da sauri ta zauna tana
masa sannu.
"Muga hannun.....idan yana ciwo a kira likita
mana" Ido daya ya kashe mata yana
kallonta.
"Kece likitan ai.....jeki kulle qofan da key ki dawo na
nuna miki abinda zakimin ya rage zugin da nakeji" Ya fada yana karya wuya
kaman da gaske zugin yake. Da zuciya daya taje ta rufe din ta dawo,saidai kafin
ta ankara ya jawota jikinsa ya matseta da kyau,kota ciwon ma bayayi.
"Kada ka fama ciwonka fa.....hannunka muffin"
Taketa fada cikin damuwa,bata kula sam da yanayinsa ba sai daya riqe fuskarta
da hannunsa daya,sannan ta maida dubanta fuskarsa. Gaba daya idanunsa sun canza
launi zuwa kalan ja,kaman yadda numfashinsa yake fita a wani hautsine,take ta
fahimci inda lamarin ya dosa.
"Sabrrrrr" Yadda sautin ya fita saida tsigar
jikinta ya tashi,ta runtse idanunta tana jin ya saukar mata da wani azababben
yanayi a dukka sassan jikinta. Sunan da muddin ya kirata dashi tabbas akwai
wani abu me girma akanta cikin zuciyarsa kenan. Idanunta da sukayi laushi ta
zuba masa tana kallonsa itama,tana jin wani abu yana tasiri sosai a jikinta da
ruhinta
"I can't hear you,you have too many clothes on" Ya
fada muryarsa can qasan maqoshi. Idanunta ta maida ta lumshe,ta gani rigima ce
fal idanunsa,ta yaya kuma zai nema rigima irin haka a irin wannan yanayin da
suke ciki?.
"Please ki rage wannan kayan.....hutawa nakeso
nayi". Maganan ya sake mata nauyi,ta bude idanunta a kansa.
"Hamma......asibiti muke fa?" Ta fada a narke da
wata irin shagwaba data sake kunnashi.
"Shshshsh" Ya fada yana dora yatsansa akan lips
dinsa,idanunsa suna sake narkewa. Sake zuba masa ido tayi har sai daya karya
lagonta,a hankali ta motsa labbanta.
"Me kakeso?" Tafin hannunta ya kama sosai ya saka
cikin nasa yana murzawa,laushin tafin hannuwansu ya ratsa juna da wani irin
dumi da jikkunansu sukayi.
"A lot things duniyata...i missed you badly.....but
ukunnan....long hug....deep looks....slow kisses,i want you in the worst
way...." Can qasa yayi da muryarsa cikin salo na rad'a
"Your taste....scent,and feel of your skin next to
mine,Duniyata......our bodies could be skin on skin.....i want it all
tonight,karki hanani yin komai.....if not" Sai ya girgiza mata kai yana
kada mata yatsansa.
Gaba daya
kalamansa sun gama tsumata,sun gama tafiya da tunaninta da nutsuwarta,sai ta
zame hannayenta a hankali daga nasa,ta fara tafiya da baya da baya kafin ta
juya tana fadawa toilet.
Tsaiwa
tayi na wasu sakanni tana maida numfashi......tana sake ji da gaske fu'ad
DUNIYARTA NE.
"Nothing is hotter than a romantic man" Ta furta
tana sakin murmushi ita daya gami da rungume hannayenta a qirji tana jin
duniyar tana shawagi da ita.
Cikin
nutsuwa ta fidda kayan jikinta ta shige jacuzzi ta sakarwa kanta ruwa me dumi
bayan tayi brush,koda ta gama cikin tattausan babban towel ta lullube jikinta
ta yafa wani saman kanta.
Dole ta fita
a haka saboda kayanta suna dakin,ta soma takawa a hankali tana ficewa.
Zaune ta
sameshi saman zagayyar sofa din da aka aje don hutun majinyaci. Kwarjini ya
mata da yawa,don ba komai a jikinsa sai boxer. Faffadan qirjinsa me cike da
gargasa da dukka muscles dinsa a bayyane suke,saita danji nauyi ya
kamata,qafafunta suka dan fara rawa. Ya gani,ya kuma lura,saboda tunda ta fito
idonsa yana kanta,ta masa wani irin kyau,kyan da bai taba lura dashi ba sai
yau.
"Sabrrrr" Ya kirata a hankali sanda take kici
kicin neman kayan da zata saka. Waiwayowa tayi a kunyace ta dubeshi,yantsansa
ya kada mata yana lumshe idonsa.
"We don't need any night wear.....skin to skin
contact....it's where words fade and our souls speak" Ya qarasa maganar
yana shafa qirjinsa saitin zuciyarsa idanunsa suna sake rusuna..
Ba musu ta
watsar da kayan,ta jawo hijab ta zura tana jan under wear dinta sama. A hankali
ta tako inda yake,qamshinta yana kado masa har saman fuskarsa tun kafin takai
ga qarasowa. Idanunta taketa kaudawa gefe,batason su hada ido.
"Ka shirya na taimaka maka ka kwanta?". Shuru ya
gifta na wasu daqiqu,har tayi tsammanin amsawa ne bazaiyi ba,saidai sanda ta
daga kanta sai taga iya ya zubawa ido yake kallo idanunsa a kanta kaman zai
cinye namanta.
"Am ready my world.....but kafin sannan ki kashe duka
wutar dakin.....ki ragemin AC dinnan,ki ajemin ruwa saman drawer
dincan......sai kizo ki taimakamin din" Ya fadi yana canza ma'anar maganar
daga qarshe. Duka ga ganoshi amma tayi biris,tayi dukka abinda yace din sannan
ta tako gabansa a hankali tana miqa masa hannunta. Ido ya zuba mata,shi kadai
yasan kalar soyayyarta sake dawainiya dashi......ya yadda da gaske so zai iya
zama ajalin mutum.......yana kyautatawa Allah zato.....yadda ya yiwa soyayya
mummunar qi da mummunar fassara da kuma mummunan zato......baya saka ran
sabreen zata zama cikin jerin jarrabawarsa a rayuwa. Sai daya gama qare mata
kallo sanna ya dora hannunsa saman nata a hankali,ta hada qarfinta tana jin zai
iya dogara da ita ya miqe,amma inaaaa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa..gaba
daya ta rikito jikinsa wanda yafi kyautata zaton da gayya yayi mata haka.
"Subhanallah" Ya furta da raunanniyar muryarsa
yana boye dariyarsa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 129
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
129
Tashi tayi
tana zumbura baki alamun fushi
"You do it knowingly" Sosai ya sake boye
dariyarsa,bayaso ya bata rawarsa da tsalle da wuri,sai ya daga hannunsa irin na
surrender.
"It won't repeat itself"
"You're not kidding right?" Kai ya gyada mata
kawai dondai yasan wannan alqawarin bazai dauku ba.
Sake bashi
hannun tayi,ya miqe din saidai ya maqale a jikinta yana narke mata.
"Hamma?" Ta kirashi a shagwabe.
"Sabreen" Shima ya kirata da salon data
kirashi,abinda ya sanya ta saki dariya kenan ba tare data shirya ba.
A hankali
ya haura gadon,ta saka masa pillow daidai da yadda taga yafi kwanciya ya maida
bayansa ya kwanta a hankali,tana niyyar janyewa ba zato ba tsammani ya jawota
gaba daya cikin jikinsa tamkar baya tuna akwai ciwo a hannunsa,take ta samu
kyakkyawan masauki a jikinsa.
"Karkimin musu....karkice komai.....wannan shine
cikakken ma'anan jinyan da nakeso kiyimin......that's why nace banason jinyan
kowa sai naki,am craving you so bad....you're my place" Ya qarasa fada
sanda yake zame Undearwear din da ya rage a jikinta,sannan ya sabule hijabin
jikinta ya maye gurbinsu da jikinsa.
Bata
hanashi ba,saboda tasan zai wahala a yadda hannunsa yake ya iya wani abu me
dogon zango,ta barshi yayi birgimarsa yayi rigimarsa yadda yakeso,skin to skin
connection ya sameshi har fiye da yadda yake buri,saidai dukkaninsu ya jefasu
wani irin yanayi da ya sanya da qyar suka iya bacci,kowa na qoqarin kai
zuciyarsa nesa.
★Wani zazzafan
mari ya saukewa fuskarta,yana dubanta da wani mahaukacin fushi da bata taba
gani kan fuskarsa ba
"How dare you zaki hari mutum kaman muhammad
jadda?,have you lost your mind?" Ya qarashe maganar jijiyoyin kansa suna
tashi,yana jin kaman zaiyi qaramin hauka.
Da zallar
mamaki ta dora hannunta saman fuskarta tana duban mahaifin nata,karo na farko
daya taba dora yatsunsa biyar saman fuskarta kenan da sunan mari bada sunan
soyayya da lallabawa ba,wani abu da bai taba shiga tarihin rayuwarta ba sai
yau.....yau ita mahaifinta ya daka saboda fu'ad?.
"Abba?.....maman naka ka daka saboda wani?" Ta
tambayeshi tana nuna qirjinta da yatsanta cikin jinta cikin zallar tozarci dumu
dumu
"Wani?,wani fa kika ce?,shi wannan din da kike kira
wani kinsan wayeshi?,nace kinsan wayeshi?,kinsan rufin asirin da ya
yiwa.mahaifinki?,kinsan cewa banda shi da baki isa ki tsaya a inda kike tsaye
ba a yanzu?,kinsan waye boss na mahaifinki?,to MUHAMMAD FU'AD JADDA NE!".
Shock taji sosai irin wanda bata taba ji ba,ta cire hannunta daga kan fuskarta
tana dubansa idanunta dukka a warwaje.
"Kinsan tsakanina da talauci a yanzu takun taqi kadanne
zan afka cikinsa!......kinsan anyi freezing duk wani account nawa....anyi
banning all my properties?,duba nan...." Ya fada a hargitse yana cilla
mata wata takarda.
"Takardar sanya hannu ne na dukkanin wanda keda ruwa da
tsaki na saukeni daga muqamina.....duk a silarki fareeda!!!,ki gayamin meye ya
rage mana yanzu?!" Ya tambayeta a tsawace yana watsa mata jajayen
idanunsa.
Wani irin
tashin hankali taji yana sauko mata,kalar tashin hankalin da bata taba jin
makamancinsa ba,ta koma da baya ta zauna tana jin ta fara gani.bibbiyu.
Anyi
banning duka properties na abbanta,harda motarta suturunta,gidansu da suke
taqama da alfahari dashi.....anyi freezing accounts dinsa yana nufin harda nata
daukacin accounts din......an sallameshi daga muqaminsa yana nufin daga yanzu
an cire mata tittle na diyar AMBASSADOR KHALED MUSTAPHA?".
"This is insane.....unbelievable" Ta fada tana
girgiza kai da qarfi don kwanyarta ba zata iya daukan wadannan abubuwan duka
lokaci guda ba.
"Ba zaki gane insane bane sai lokacin da arrest warrant
ya iso cikin gidannan da zummar kamaki a mazaunin masheqiya.....don
tabbas!.....ina me Tabbatar miki jadda baya shurun banza......all these yayi ne
tauna tsakuwa kawai don aya taji tsoro.....ina me Tabbatar miki bazai raga miki
ba......kinyi yunqurin yin kisan kai......kuma bazan goya miki baya ko na hana
a hukuntaki ba". Kowanne halitta na cikinta sai data kada tsananin tsoro
"Dad......na dauka ko meye na dauko kai me tsayamin
ne?,abba yau da kanka kake wannan
maganar?". Wani banzan kallo ya watsa mata,ya matso gabanta yana
dubanta sosai.
" Ki taba kowa....ki tsokano kowa amma banda muhammad
jadda.....mayunwacin zaki ne......damisar da tafi qarfin
wasa......fareeda!!!!!.....wai mema kika sha?,still kina shaye shayenki da
alama har yanzu ko?,magana ake miki na talauci yana bakin qofa yana qwanqwasa
mana qofa fa!" Ya sake fada a gigice kuka na dab da qwace masa.
"I can't take it......bazan iya jura ba......rasaki da
hukuncin duk da jadda zai dauka a kanki yafimin sauqi akan rasa dukiyata".
Sai ya jawo wayarsa yana lalubar number muhammad jadda yana fatan samunsa ya
nemawa kansa gafara da sassauci.
Zata iya
cewa kaf tsahon rayuwarta bata taba jin wani abu daya gigita hankalinta irin
wannan maganar ba,duban dad din nata takeyi ta koma kaman gunki,kowanne sashe
na zuciyarta ya cika da tsoro da nadama da tashin hankali,ta yaya zata tunkari
wannan babbar musibar dake tunkarota?.
★Tare sukayi
sallan asuba shi da ita,ta lafe a jikinsa suna azkar tare ita dashi,a haka a
haka har bacci ya saceta ba tare data sani ba.
Bakwai da
rabi ta bude idanunta a hankali,qamshin jikinsa ya tunasar da ita a jikin wanda
take. Murmushi ya qwace mata,ta furta
"Alhamdulillah" Tana tuna daren jiya,yadda ya
baibayeta da wata zazzafa kuma tsumammiyar soyayya......tana kuma tuna yadda
dare daya ubangiji ya tsamesu daga taskun da akaso jefasu,amma har yanzu ta
gaza ajiye tunanin Who's the one behind the scenes?.
Bataso ta
zama mace me yawan sanya ido tambaya ko bin qwaqwafi akan kowanne lamura,wannan
ya sanya bata tambayeshi akan hakan ba,ta sani koma meye ba wannan ba
kadai,akan komai da komai ma idan ta cancanci taji zai gaya mata.
A hankali
a hankali ta dinga zame jikinta daga nashi. Daren jiyan tasan baiyi wani bacci
me yawa ba,ta dade tana jinsa yana mutsu mutsu kafin baccin ya daukeshi.
Tas ta
samu nasarar zare jikinta daga nashi,ta kuma maida gurbinta da pillow,saita
waiwaya tana kallon fuskarsa kawai. Wata fuska dake dauke da tarin nutsuwa da
kamala.....wata fuska dake da wani irin sassanyan kyau da zata iya rantsuwa
bata taba ganin irinsa ba.....wata fuska da Allah yayi mata baiwar kwarjini da
haiba. Samun kanta tayi da addu'ar Allah yasa yaranta suyi
kamanninsa.....zatafi son haka akan su dauko nata kamannin.
A hankali
ta dora hannunta saman mararta da yau takejin kaman an ajiye mata dutse a
ciki,ta motsa labbanta tana karanto addu'o'in tsari sannan ta sauka a hankali
daga kan gadon.
Dakin
ta kintsa duk da dauda ko tarkace,still ma akwai masu aikin da zasu shigo suyi
maka duk abinda kake da buqata. Ruwan zafi ta kunna a dispenser incase ko zaya
buqaci wani abu,duk da shima akwai kitchen da zaka kira direct a kawo maka
komai da kake buqata. Wanka takeso tayi,amma saita zauna ta tura list na
breakfast din da suke buqata zuwa kitchen sannan ta dawo ta shiga wanka.
Tunic
blouse ta saka da straight leg trousers,sannan ta saka madaidaicin Malaysian
hijab da ya qawata fuskarta da wani irin calmness.
Luggage
dinsu ta gyara ta maida cikin cabinet,a hankali ta waiwayo sai idanunta suka
sauka cikin nasa. Mamaki ya kamata,tun yaushe ya farka amma baiko motsa ba bare
ya nuna mata?,wataqila a gabansa ta saka bra ta saka kayanta ta taje gashinta
duka.
"Kinyi kyau" Ya furta yana motsa labbansa a
hankali,wanda banda tabi motsin bakin nasa ba lallai ta gane me yace ba.
Kunya ta
sakata kau da kanta ta soma takawa zuwa wajen sofa ta rusuna tana fadin.
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya my super girl?" Ya fada cikin
kulawa yana jin kwadayin jin dumin jikinta da kuma qamshinta gaba daya,tsumin
daya tayar musu jiya yana qoqarin kunna kanshi a yanzu.
"Alhmdlh...jikinka fa?" Ido ya lumshe mata sannan
ya bude
"Am fine and good....tunda gani ga duniyata"
Murmushi ta sake sakar masa. Shi duka hakan bai masa ba,ya fahimci idan ya
barta kuma a banza wannan kyan saidai ya ganshi a ido,don haka yace mata.
"Zaki taimakeni ki daga ni?".
" Why not?" Ta fada da tattausar muryarta tana isa
gareshi. Gadon ta haura,kaman jiya ta bashi hannunta saiya noqe kafada yana
kallon idonta.
"Ki hada hannu biyu.....baki da wani qwari.....ina
tsoro kada ki Fadi nayi laifi ace da fuska biyu nayi hakan" Yadda yayin ya
bata dariya,saidai ta karkada kanta.
"Zan iya"
"Really?" Ya tambaya yana daga girarsa,saita
jinjina masa kai alamun bashi tabbaci.
Kai tsaye
ya miqa mata hannunsa guda daya,ta cafe a nata,saidai kuma tashin farko tayi
kyakkyawan masauki a qirjinsa.
"I love you" Ya fadi da sauri cikin wani karyayyen
amo cikin tsakiyar kunnenta.
Murmushin
dole ya qwace mata,ta yadda da gaske da ake cewa duk wanda ya rigaka kwana dole
ya rigaka tashi,ta kuma sallama fu'ad daga jiyan har yau wayau ne kawai yayi
mata,don haka bata da sauran inkari itama ta motsa pink lips dinta da suka
fusgi hankalinsa tace
"I.....love you.....more" A rarrabe da wani sound
daya sanya ya gaza jurewa yakaiwa lips dinta kiss. Janye fuskarta tayi tana
cewa.
"Asibiti ne fa hamma.....yanzu ida....." Bata
qarasa ba aka murda qofar,abinda ya sanyata hantsalawa gefe tana neman maboya.
Maida qofar akayi da hanzari aka rufe,muryar farouq ta bayyana.
"Na shiga uku....wallahi daga yau bazan sake zuwa
asibitin nan ba". Maganar tayi tsananin bawa sabreen dariya,ta cusa kanta
a kafadar fu'ad tana boye dariyarta.
"Rabu da tuzurun banza......waya aikeshi?...sa'idon
farouq yafi qarfinsa"
"Hamma baka kyauta ba gaskiya".
"I'm only selfish when it comes to you.....zakiyimin
wanka?" Ya fada a narke a kuma shagwabe. Ido ta zaro waje,tanason duban
idanunsa tana tsoron kada ya narkata da kallon nan nasa.
"Please" Kai ta girgiza.
"Why?" Ya sake jefa mata tambayar a tausashi. boye fuskarta ta sakeyi cikin pillow.
"I can't.....bazan iya kallonka ba". Wani murmushi
yayi mara sauti yana fidda idonsa shima
"Am all yours babe....alright,hadamin komai i will do
it by myself" Hakan taji yafi mata,saita tashi da sauri ya wuce toilet din
don ya gama shiryawa da wuri kada subar su farouq a parlor suna jira,ya bita da
kallo yana jin kamar zuciyarsa ce a waje take tafiya da qafafunta.
Har cikin
toilet din ta rakashi sannan ta fito tana ja masa qofar. Tana tunanin yadda
zata fita su gaisa da farouq da wanne ido zata kalleshi taji an bude qofar
toilet din.
Ido ya
zuba mata ba tare da yace komai ba,har sai daya gama tsumata da kallonsa yadda
yakeso sannan ya motsa labbansa.
"Towel madam" Janye kallonta tayi zuciyarta na
qara gudu,tanajin kaman akwai towels a bandakin,amma bata da energy din masa
bayani,don haka ta taka a hankali hannun sofa ta dauko masa wani.
Miqa masan
da zatayi ya hado harda hannun nata ya jawota cikin toilet din ya maida qofar
ya kulle.
Sabon
wanka ya sakata ta sake bayan ya gama jagwalgwalata. Tabbas banda ciwon
hannunsa ta Tabbatar barna za'ayi a asibitin ba jinya ba. Ya aza mata wani
nauyi da ta sakejin ta gaza dubansa harta kammala shiryawa ta canza wasu kayan
zuwa riga da wando saqar india. Rigar ta kawo gwiwa haka wandon budadde ne
sosai,yalwataccen mayafin kayan ta ware tana rolling dashi,sai ya tako a
hankali ya tsaya a bayanta.
Hannunsa
guda dayan ya dora saman qugunta,ya daidaita tsahonshi da nata hana dora
fuskarsa a kafadarta.
"Ki bani lokacinki.....ko zana rayu a duniya.....ki
bani tabbacin zamana dake kinji masoyiya....nidai nidai nida nake son ki nafi
kowa jinki a zuciya" Murmushi ya
qwace mata,ta rufe idanunta tana miqa hannunta ta shafi kwantaccen gashin
fuskarsa. Muryarsa ta mata wani mugun dadi,asalin sound din yana tasowa daga
parlor dinne yana ratsowa ta cikin dakin,tsakaninsu musaddiq batasan waye
yakejin waqar ba,shi kuma yabi waqar da tattausar muryarsa da tafi ta mawaqin
dadi.
"Am starving" Ya fada yana sansanar wuyanta.
Muryarta da mugun sanyi tace
"Muje parlor na baka" Kai ya girgiza da sauri yana
dauko wayarsa dake saman table din ya soma budeta.
"Farouq ya fusata.....idan kikaji yana jin waqoqi
definitely ya fusata......yana kewan fannah dinsa" Ya fada yana dan jin
wani sashe na zuciyarsa yana tausayin farouq din,don ya yarda da gaske soyayya
mahaukaciyar abace....kewar masoyi kuma wani abune daka iya kassara mutum komai
jarumtarsa.
Murmushi me
sauti ya kubcewa sabreen,batace komai ba don fu'ad da farouq sunfi kusa.
Ya cika da
mamakin ganin tarin uban miscalls din ambassador khaleed mustapha,ba kiran bane
ya bashi mamaki,saboda yana expecting hakan dama,yawan adadin kiran da ya masa
na fitar hayyaci shine abun mamakin. Qaramin tsaki yaja yana share dukkanin
kiran,ya lalubi number saddiq.
"Shigo dasu ciki" Kawai yace yana kashe wayar.
Cikin second uku ya turo ya shigo dakin da wani kyakkyawan basket. A girmame ya
gaida sabreen ya gaida fu'ad yayi masa sannu da jiki,sannan ya ajiye basket din
ya juya ya fice.
Mayafin
data rola ya saka hannu ya cire pin din sannan y wareshi tas yana dubanta.
"Let me behold this beauty....i want to take a look at
this loneliness....i wannan see this " Ya qarasa fada yana shafar sumarta
zuwa gefen fuskarta. Zamewa tayi tana murmushi,ta qarasa gaban basket din ta
tsugunna a nutse ta fara zuba komai yadda ya dace,har zuwa sannan kunnuwansu na
sauraron waqoqon soyayyar da farouq ya ware volume abinsa yanaji. Fes waqar ke
fita da baituka na zallar soyayya,su duka kunnuwansu suna jinsu,har ta gama ta
tako a nutse tana juyawa a hankali da wani irin nutsatsen taku dake bayyana
surarta da zubin halitta me kyau da Allah ya azurtata dashi.
Sosai ta
ajiye plate din a gabansa,ta zauna kaman yadda taga yayi ta tanqwashe
qafafunta. Hannu ya saka ya cire spoons din,ya gyara hannun rigarsa yana fadin.
"Oya bismillah" Idanunshi zube a kanta. Zobanta ta
canzawa yatsa sannan ta saka hannun nata kaman yadda ya buqata.
Wani irin
shuru ne ya ratsa tsakaninsu,sai kallon kallo da yaren zukata da suke fitarwa
ta cikin idanunsu,irin yaren daya gagara zuciya ta furta.
Zuwa
lokacin waqar abdul hassan ta meerah ta soma tashi. Komai sunaji kaman a nan
aka kunnata.
Kowanne
baiti dake fita daga bakin mawaqin sai yakejin kaman ya wakilceshi
ne.....tamkar furucin da rarraunanniyar zuciyarsa ta gaza bawa bakinsa daman
furtawa ne yake fiddasu daga zuciyar tasa. Ita dinma waqar ratsata take,ta daga
fararen idanunta tana kallonsa. Ya dakata kwata kwata da cin abincin,ita yake
kallo. Karon farko data yarda da cewa,da gaske ne idan soyayya tayi qarfi
masoyi yana iya qoshi daga jin yunwa daya ganin masoyinsa kawai(kin taba fuskantar
hakan?....musamman irin yunwar da batayi worst ba....da gaske ne hakan yana
faruwa).
Qarar
wayarsa ta katsesu dukkaninsu shida ita,ya sauke nannauyan numfashi yana saka
qwayar idonsa kan wayar.
Ambassador
ne,sam bashi da niyyar sauraronsa a lokaci na kusa har haka.....saidai kuma
yana jin baida lokacin da zai bashi da zaiyita damunsa har hakan,wannan ya
sanya ya daga kiran ba tare daya dauki wayar ba ya sakata a hands free yana
maida idanunsa akanta don bai gaji da kallon kayarsa ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 130
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
130
"Ex
ambassador khaleed mustapha" Kalma ta farko da fu'ad ya fara fada bayan ya
daga wayar.
"Ranka ya dade sir......tuba muke.....tuba muke,ayimana
afuwa,ayi mana rai" Ambassador khaleed ya fada cikin matuqar qanqantar da
kai da kalmasa harshe.
"Wani abu ya faru kenan" Fu'ad ya fada cikin halin
ko in kula,abinda ya sake daga hankalin ambassador kenan. Yafi kowa sanin illar
wannan shariyar tasa,har gwara ya fito maka a mutum,yayi maka duk yadda
yakeso,yayi maka kalar hukuncin da yaga dama.
"Ranka ya dade sir.....ina me baka afuwa......ina me
baka haquri......don Allah.....don Allah a dubeni,ayimin rangwame". Gyara
zamansa yayi tare da yiwa sabreen inkiyar ta matso taci abincin. Kai ta langabe
masa,sai ya matsa da kansa ya soma diban abincin ya miqa mata yana tambayar
ambassador.
"Hala bakasan abinda yarinyarka take aitawa ba.....bama
a kaina kadai ba,har kan mutanen da take taqamar matsayinka da matakin da kake
kai sun tsaya mata sun kuma siya mata ticket na cin mutunci da qasqanci ga
kowa?". Ya masa tambayar sanda sabreen ta saka hannu ta karbe spoon din ta
maidashi bakinsa,ya bude bakin ta saka masa abincin sannan ya mata sign na
itace next da zataci.
Shuru
ambassador yayi,yana juya irin amsar da zai bawa muhammad jadda. Yasan wayeshi
farin sani ma tass kuwa.......yi masa qarya tamkar tafka wani babban kuskuren
ne,hakanan gaya masa gaskiya kuma bazai taba zama mafita ba.
"Ko ka sani ko baka sani ba wannan kai zaka bawa kanka
amsa......".
"Am really sorry sir......ayimin afuwa.......na yarda
da kowanne hukunci ya kamata kayi mata koka dauka a kanta,na aminta da hakan
ranka ya dade sir". Fareeda dake durqushe waje daya ta daga kanta da
sauri,a mamakance tana duban mahaifinta. Shi da kansa yake sallamawa me jadda
ita?,shi da kansa yake miqata izuwa gareshi kan yayi duk kalar hukuncin da yaga
dama?.
Ci gaba
yayi da cin abincinsa yana kuma morewa kallon duniyarsa. Kaman bazaice komai
ba....kaman bazai amsa ko ya sake magana ba......har ambassador ya fara sarewa
gami da fidda rai kafin yace.
"Zabin dawowar dukiyarka qwaya daya ne
tak........tsaffin kudaden qasar nan da ka danqaresu a France.......zamuyi
yarjejeniyar dawo dasu gida kuma qasata Nigeria don amfanin al'ummar
qasar". Wani razani ya sake kama ambassador,wanne irin mutum ne fu'ad
din?,kamar wani maye me gani har hanji?,kudade ne masu ciwo nauyi da yawa da
yayi imanin koda iya su kadai iyalinsa suka tsira sun rabauta,amma har ya akayi
ya ankara dasu?.
"Ina fata kana saurarena?" Fu'ad ya tambayeshi
yana cirar tissue yana goge bakinsa don abincin ya isheshi haka.
Sai daya
goge gumin fuskarsa da habar rigarsa sannan yace.
"Ina jinka......na fahimta"
"Good......secondly diyarka......rashin kyautata
tarbiyyarta wannan matsalarka ce.....damuwarka ce.....haduwarka da Allah kadai
ya isheka barazana.......tayi attempting kasheni......inaso ta gaggauta fita da
kanta media television da magazines ta tabbatarwa duniya da tayi yunqurin
aikata hakan,tayi apologize nawa......tayi na matata.....ta tabbatarwa da
duniya cikakken mutunci da darajar da iyalina ke dashi.......wannan muqulli ne
kawai na budewar daskararru da kuma qwatattun dukiyoyinka......hukuncin yunqurin
kisan kai kuma ita da hukuma.....sunsan matakin da yafi kamata su yanke a
kanta".
Ba fareeda
kadai ba.....hatta da sabreen hukuncin ya mata nauyi,tayi zaton iya hakan da
zatayi ya wanke duk sauran laifukanta...
"Amma sir.......na dauka duka hakan zai wakilci kowanne
laif......"
"Khaleed!" Fu'ad ya kirashi a tsawace cikin fushin
da har sabreen dake zaune a wajen sai data daga kai tana kallonsa,tana kallon
yadda kamanninsa ke sauyawa alamun bacin rai ya fara tasiri a zuciyarsa.
"Magana ake ta kisan kai bisa ganganci da
niyya......magana ake ta bata mutunci da daukan hayar gidajen jaridu suyi
batanci ga iyalina......kasan nawa ta kashe don kawai a buga sunan matata ta
sunna da sunan KARUWA?,waye yake bata kudin?,a ina take samosu?,a gaban waye
take dukka kalan rayuwar da taga dama?......wannan hukuncina ne ba wai shawara
bace ko alfarma.....kana da right na cewa ba zatayi ba gaba daya......wannan ya
rage naku.....dont contact me again indai akan wannan issue dinne.....i finalized
the matter"
"Please sir......please....."
"Khaleed,Not my problem to solve......Could you please
stop calling me?". Shuru ambassador yayi,ya tabbatar ba wani abu da zai
sanya fu'ad canza wannan hukuncin nasa,abinda ya bawa fu'ad daman yanke kiran
yana jan wani dogon tsaki kaman zai tsinke harshensa.
A tausashe ta karbe wayar,ta sakata a DND mode
ta ajeta gefe. Kamo lallausan tafin hannunsa tayi ta saka cikin nata tana
lalubar qwayar idanunsa,cikin nasara ta samosu,saita kafeshi da idanunta tana
kallonsa tana kuma murza tafin hannun nasa.
Cikin minti
biyar ya sauke wata nannauyan ajiyan zuciya,abinda ke tabbatar mata ya samu
relief na bacin ransa. Hannunta ta dora saman cikinta tana nake fuska a
shagwabe.
"Suna tsorata sosai idan abbee dinsu yana cikin irin
wannan fushin......sunce na bashi haquri,na gaya masa komai me wucewa ne,komai
watarana zai zama sai labari". Murmushi ya subuce masa yana lumshe
idanunsa,ya saka hannunsa ya dagota,ya dorata saman cinyarsa,tura hannunsa yayi
saman cikinta a nutse ya aza tafin hannunsa akai.
"Dukiya jarrabawa ce me zaman kanta....kaman yadda
talauci take shima jarrabawa ne,duk wanda Allah ya jarrabi bawa dashi akwai
nasa kalan qalubalen.....ki fadi musu daddynsu yana nan yana fighting akan
yadda zasu rayu cikin aminci ba tare da sauran qaya ba akan hanyarsu.....i love
them more than i love myself....."
"I hope I'm still your number one?" Ta fadi a
narke tana kyabe baki. Dole ta sanya wani murmushi me sauti ya subuce masa,ya
kama kumatunta yadan riqe yana girgizawa.
"You're filled with jealousy......madam.....ke din
DUNIYATA ce fa gaba daya". Murmushi tayi yana boye fuskarta a kafadarsa.
" Kiraminsu Musaddiq" Ya fada yana komawa normal
mode dinsa. Zamewa tayi a jikinsa a hankali ta miqe,ta taka tana fita zuwa
parlor din.
Dukkansu suna
zaune,kowa kusan wayace a hannunsa yana dannawa. Farooq kuma ya koma amsa waya.
Rusunawa sukayi suka gaidata cikin girmamawa,ta amsa musu da danjin kunya da
nauyi sannan tace musu.
"Hamma yana kiranku" Miqewa sukayi suna wucewa
ciki,banda farouq daya daga musu hannu alamun yana zuwa. So samu su shiga ciki
duka ta zauna ita a nan,don wala'alla wata magana zasuyi data shafesu,to amma
farouq yana nan,ita kuma yanzu kunyarsa takeji,dole ta juya ta koma dakin.
Yana
zaune still saman kujerar,ya miqe qafafunsa hannunsa da cup din ruwa yana sha.
Gaidashi sukayi shima cikin girmamawa kaman yadda suka saba,ya jiye glass cup
din yana amsa musu.
"Anni bata shigo ba?" Ya tambaya yana dubansu.
"Eh sai zuwa anjima kadan,abba ne yadan tashi da ciwon
kai".
"Subhanallah,amma ba wanda ya gayamin a cikinku?"
Ya fada cikin dan nuna bacin rai. Idanu kawai suka hada kowa ya sadda
kansa,kota yaya zasu gaya masa bayan ko ganinsa basu samu yi ba.
waya ya
dauka ya kira abban,suka gaisa yaji jikin bawai tsanani ko yawa yayi ba,yace
suyi xamansu yau su huta,tunda komai yana tafiya lafiya alhamdulillah,sannan
sukayi sallama ya aje wayar yana dubansu.
"A cikinku akwai wanda yayi magana da wani cikin abokai
ko 'yan uwa sanda zamu baro madeena mu sauka a nigeria?". Daga kai sukayi
suna dubansa,don tambayar tashi ta musu wani iri. Kai ya jinjina musu.
" Eh ina nufin ko a hira ba wanda ya bawa wani full
details na ranan dawowarmu da inda zamu sauka?"
"Full details?" Musaddiq ya tambaya yana kallon
hamman nasa. Kai fu'ad ya jinjina yana maida hankalinsa a kansa.
"Eh" Fu'ad ya jaddada masa.
"Akwai hamma" Musaddiq ya fada abinda ya faru a
wancan ranar yana dawo masa. Ido fu'ad ya lumshe sannan ya budesu.
"Waye?" Ya tambayeshi kai tsaye.
"Maamah ta bani wani number na tura mata details
din.....ban kawo komai a raina ba hamma......ban kuma yi tunanin akwai wata
matsala da hakan zai haifar mana ba"
Ido sosai ya zubawa musaddiq din,yana jin kanshi ya masa nauyi da
ambatar sunan maamah a lamarin. Tsoro ya kama sha da fargabar kada sunanta ya
fito cikin jerin sahun sunayen mutanen da suke da hannu a faruwar al'amarin fa.
"Me yasa zakayi haka musaddiq?......me yasa baka kiyaye
wasu abubuwa?,kana tunanin ni dakai saddiq farouq amna dama duk wanda yake
under jadda family ordinary human ne?" . Shuru yayi jikinsa yana yin
sanyi. Tun sanda abun ya faru wannan abun yake a ranshi,jiki da zuciyarsa duka
suna gaya masa akwai alaqa tsakanin abun da kuma wancan address din daya
bada,wannan ya sanyashi tilastawa kansa zama tuno digits din daya turawa
address din,ya kuma sake zaunar dasu tsaf cikin kansa.
"Baka riqe name din dake jikin contact din ba....koda
bincike ne ta yaya kake tunanin za'a iya yinsa?" Fu'ad dake kallonsa da
takaici ya fada.
"Na riqe digits din...." Shuru ya danyi yana ci
gaba da kallonsa
"Really?"
Kai ya jinjina masa,sai ya waiwaya ga saddiq.
"Ya baka digits din ka turawa saleem.....kace masa
injini" Ya fada yana maida bayansa jikin kujera yayi relaxing.
Wani irin
bacin rai ne yake ratsashi,maamah itace silar faruwar wannan abun?,to hadin
baki sukayi da fareeda kenan wajen kasheshi ko goyon baya ta bata?,hakan yana
da alaqa da hallarar kowa a asibitin da nuna zallar damuwarsa a kansa amma
banda ita?. Kanshi ya samu da girgizawa,yana jin cewa sam maamah din ba zata
aikata haka ba.
"Amma ta taimaka wajen kauda abbanku daga duniya?"
Tambayar da tazo daga qasan zuciyarsa kenan,ta kuma sake taso masa da wani irin
bacin rai.
★A hautsine take
duban mahaifin nata bayan ya gama gaya mata hanyar mabudin arziqinsa da yake
hannunta,bisa tsari da kuma dokar da fu'ad ya bayar.
"Yanaso yayi humiliating dina ne abba......ta yaya zan
fita gaban 'yan jarida na tonawa kaina da kaina asiri?....hakan kuma ba yana
nufin na wanke kaina da kaina bane?,tamkar kenan na bawa shari'a daman yankemin
hukunci da daukan mataki a kaina ta sassauqar hanya?" Ta fada tana jin
cewa aikata hakan wani abune da bazai yuwu ba.
"Kina tunanin kina da wani sauran amfani a wajena ne
fareeda muddin dukiyar dana kwashe shekara da shekaru zata salwanta ta
sanadinki?......ruwanki kimin hanyar dawowar arziqina nasan hanyar xa zaki samu
Sasaaucin hukunci.....ruwanki kiqi ni kuma da hannuna zan miqawa hukuma
ke......daga rana irin ta wannan lokaci kuma ki tabbatar na cireki daga jerin
'ya'yana.....sunan.Khaled mustapha kuma ya saraya daga wuyanki.....na haramta
miki amfani dashi haramtawa na har abada".
"Bazanyi abinda yace ba daddy.....hakanan kaima dukiyar
ka zai dawo hannunka" Ta fada tana rarumar wayarta.
Number
maamah take nema,hanya guda daya tilo da take tunanin zatabi don samun
warwarewar komai.
Daidai
lokacin da mota ke tsula gudu da ita saman kwalta,hankalinta yayi nisa yayi
kuma zurfi a tunanin tun sanda ta baro wajen boka. Kora yayi mata fata fata
akan kada ta sake zuwa masa muddin da maganar data shafi taurari biyu ne
sabreen da fu'ad. Ya gama aiki a kansu har abada saidai ta nemi wani.
Sanda ta
lallabashi da batun wata buqatar daban tazo da ita ba irin ta baya
ba.....buqatarta dankwafar da cikin sabreen yayita zama a mararta ba tare daya
girma ba bare a haifeshi,wannan kuma zai zama silar da zai zama karo na farko
kuma na qarshe data samu ciki da fu'ad din,a sanya masa shakka kan qaryar ciki
tayi dama tun asali.....maganar rabuwarsu kuma ita zataji da sauran.
Har ya
soma buga qasa yayi wani zabura da saida qoqunan gabansa gaba daya suka
hantsila,yaja baya yana gurnani da wasu surutai kafin daga bisani ya dubeta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 131
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
131
"Kinsan
aikata hakan daidai yake da kiran mutuwarki da kuma gaggauto da ajalinki
tu lokacin mutuwarki baiyi ba?"
Sosai abun ya daure mata kai itama,tana kuma buqatar qarin haske.
"Kamar yaya?,ban fahimta ba?". A fusace
yake.magana wannan karon fiye da fusatarsa ta dazu.
"Wannan yaran da suke cikinta......bake bama......duk
wanda keda qudurin cutar dashi to tabbas ajalinsa yake kira......fiddasu daga
mahaifarsu ko hanasu wanzuwa suyi rayuwa irin ta kowanne jariri kuwa,daidai
yake da kiran ajali yayin da yake nesa da ruhi.....ki fita daga harkar wadannan
taurarin......suna dab da karo da naki taurarin.......tazarar dake tsakaninku
kadance,faruwar hakan kuma daidai yake da LALACEWAR RAYUWARKI!.......SAURA
QIRIS!.....KI KAUCE KI BASU HANYA.....BA WANI ABU ME CUTARWA DA YA ISA YA TARE
HANYAR SHAWAGINSU!" ya fada a tsawace yana nunata da yatsa.
Tashin
hankali!,kanta taji ya wani irin sarawa.....muddin ya kasa mata wannan aikin
duk duniya bata jin akwai wanda zai iya yinsa
"Kayimin rai.....zan ninka maka abinda ya kamata
a......"
"Dakata!" Ya fada a gigice.
"Wannan aikin ba kudi yake buqata ba.......aiki ne na
tsira da rai........ran da muddin aka barshi ya dulmiya babu me iya fitowa
dashi........KIBAR DA'IRATA HAR ABADA....KARKI SAKE DAWOMIN DA MAGANAR
TSARARRUN TAURARI BIYU".
Wannan
tunanin yana mata shawagi kiran fareeda ya shigo,ta saka idanunta akan kiran da
wani irin yanayi,mamaki ya sanya batayi wani dogon nazari ba ta daga kiran tana
sakawa a kunnenta.
"Ina kika shiga fareeda..... Ko kina shirin janyewa ne
saga qudurinki?" Ta fadi tanajin kamar idan ta hada kai da fareeda din
nasara zata zo mata da gaggawa cikin sauqi,dole tana da buqatar me tayata
wannan yaqin.
Ba kalar
neman da bata yiwa zuwaira ba amma ta kasa samunta......duk inda take tunanin
idan taje zata sameta ta aika ba labarinta,abun yana daure mata kai.
"Ban fasa ba.....kuma sauka daga kan nufina
ba.....hasalima tsakiyar aikin da nakeyi aka samu matsala da kuskure".
Kanta ya sake sarawa,ta zauna sosai tana riqe wayar a kkunnenta sosai.
" Me ya faru kuma?". Sai data gyara muryarta da
kyau sannan tayi magana.
"Nasa anyi attacking na matarsa.....cikin rashin sa'a
aka sameshi.....yanzu haka anyi freezing komai na dukiyarmu......yasa kuma an
dakatar da dad daga muqaminsa......yana maganar saina fito nayi iqirarin nina
aika a kasheshi.....na bada haquri a media sannan zai sakar mana
komai.....abinda yasa na kiraki.....inaso ki sakashi ya warware komai......ya
janye kuma komai.....muddin wani abun ya sameni duk wani mmuradinmu zai tsaya
cak.....don ina da babban shirin da zai kauda mana damuwoyinmu ni dake gaba
daya".
Dif maamah
din tayi,kwanyarta suna juya mata maganganun fareeda. Haka kawai taji
hankalinta kamar ya kasa kama maganganun fareeda din,kaman akwai wani abu da ba
daidai ba.
"Fareeda.....bansan qasar da suka kaishi ba.....yanzun
haka matarsa ke dauke da cikin da nakejin gwara na nakasa da wanzuwarsa a tare
da ita.......bansan inda suka ajeshi ba".
"Taiwan......yana wani asibitu na Taiwanese a
taipei......ki kirashi tabbas zaki sameshi".
" Ki dakaceni tukunna.......fu'ad baya cikin mazan da
akewa gaggawa haka kuma su karba da sauri".
"Me kike fada mariya?!" Fareeda ta fada a
tsawace,a yanayin da take ciki bata qaunar sharhi qarin bayani ko
dako......isar da saqonta da cimma burinta kadai take da buqata.
"Kinsan a wanne yanayi muke ciki da har zaki saka
bataun JIRA a wannan zancan?......kinsan kowacce daqiqa guda da zata shude muna
sake shiga hadari ne nida duk wanda ya dangancemu?......buqata ta gaggawa
ce......kiyi hanzarin dakatar da d'anki daga aikata abinda yayi niyyar
aiwatarwa......idan kuma ba haka ba to tabbassss bazan shiga uku ni kadai
ba......zan shaidawa duniya da hannunki a cikin komai......dollars dina da kika
karba kuma.....kada ki manta akwai evidence na amount account details date da
time na yadda na saka miki komai.....saiki shirya maidosu" Daga wannan
fareeda ta yanke kiran.
Wani
sarawa kan maamah taji yayi......lallai idan fareeda ta ambaceta a wannan
badaqalar ba abinda zaya hana mutane aminta dasa hannunta.....musamman mutanen
dake da issue da ita irin ameenatu da sabreen.....sabreen din da har yanzu tana
qarqashin awa saba'in da biyun data bata,awannin da batasan ta yadda zata fiddo
fu'ad ba banda yanzun da kiran fareeda ya sanya tasan inda yake.
Karasashinta ya dawo da wani irin sanya ran lallai tana da
dama.....damarmaki har guda biyu.....damar sanyashi ya janye kaman yadda
fareeda ta buqata,a yadda duk wata kadara tata data mallaka ta narke daga auren
fu'ad da sabreen......da kuma neman hanyoyin da zata rabasu batajin tana da
adadin dollars din da zata maidawa fareeda kudinta.
Lalubar
number dinsa ta fara yi tana jin yadda kanta yaketa sara mata da ciwo. Kira uku
tayi,ana hudun sabreen data dauke wayar don ya sake samun nutsuwa taga kiran.
"Maamah" Da sunan yayi serving ba kaman sunan anni
da yake suna na daban cikin wayar tasa ba. Qaramin murmushi ta saki,sannan ta
taka zuwa bandaki a hankali ta maida qofan ta kulle.
"A yanzun yana buqatar hutu daga dukkan wata takura da
zullumi na rayuwa.....yana buqatar yin nesa da kowacce kalar damuwa"
Kalaman sabreen kenan da suka sauka a kunnenta suka sanya wayar hannun nata
kusan subucewa daga hannun nata,kanta kuma yayi wani dummmm na wucin gadi kafin
ta tattara qarfin halinta waje daya.
Magana
takeson mata amma ta kasa furta komai,wacce irin HATSABIBIYA ce yarinyar?,a
yanzun haka kenan tana taiwan tare dashi ta barta bata cikakken bacci?.
"Duk yadda kike tunanin cin nasara.....kina yiwa kanki
qarya ne.....ni mariya a duk sanda nayi nufin cimma nasara akan wani abu.....ba
wani wanda ko wani abu daya isa ya dakatar dani daga wannan nasarar....."
"Sai ubangijin da yayi ni yayi ki,ya kuma halicci
nasarar........shin da gaske ne kuwa?.....anya ke kika haifi muhammad da
musaddiq?" Sabreen tayi mata tambayar da bata taba tunanin zata iya mata
ita ba....amma yau ta tsinci kanta da tambayar tata.
Wutace
tsaf ta daukewa maamah tana jin jiri yana kamata daga zaune.
"Idanma ya tabbata ke dince.....to ki saka a ranki kin
haifawa masoyansu ne su.......sun tashi daga mallakinki.....sun tashi daga
ababen kulawarki,ubangji ya musu musaye da masoyansu na haqiqa....."
"Ki dakata da wannan shirmen......ki hadani da d'ana
dashi nake buqatar magana" Sabreen
bata tsaya sake sauraronta ba ta kashe kiran,ta kuma kashe wayarma gaba daya.
Iska me
zafi ta furzar daga bakinta,mamakin maamah yana sake kasheta,a yanzun dai ya
tabbata dari bisa dari......dukiya takeso......arziqin take da buqata bawai
'YA'YAN BA.
Mummunan
tashi hankalin maamah yayi,ta soma sake gwada kiran number amma a kashe.
"Allah ya tsine miki......muddin banyi sanadinki ba a
rayuwa nayi asara" Shine abinda maamah take maimaitawa sanda take yunqurin
sake maimaita kiran number fu'ad din ana gaya mata a kashe layin yake.
Sam
Allah ya dauke mata basirar kiran musaddiq......tunaninta yafi karkata ga ME
ZAI FARU bayan awannin da fareeda ta debar mata tana jiranta?.
*_Hajja_*
Tun sanda
suka gama wancan wayar da maamah ko sau daya taqi bawa kwanyarta hutu na neman
mafita da hasashen abinda zai wakana......hakanan ta gaza dauke kunnuwanta daga
jiran isowar jami'an tsaro gareta suyi awon gaba da ita kaman yadda take
hasashe,duk kuwa da bokanta ya shaida mata ba wanda ya isa ya shigo ya kamata
muddin ta tabbata a cikin gidanta,saidai idan qafa ta sanya ta fita.
Ta sake
amanna da maganarsa ganin kwana dayar har biyu shuru,sai wannan ya bata daman
zama tana tunanin matakin da zata dauka akan maamah.
Laila itace
burinta......laila da ita take kwana take kuma tashi,yantuwar laila shine
muradinta kafin ta waiwayo ga hanyoyin tozarta mariya.
Tsai tayi
da ranta tana bitar kalaman da sukayi musaya a wayarsu ta qarshe,ta tsinci
tsoro kadan da razana a muryar mariyan,ta yiwu akwai wani abu daban da batasan
dashi ba.....ta yiwu ba mmariya bace ta fidda hotonsu.....ta tabbatar tunda
hoton maqale yake da nata....duk da fuskarta bata fito sosai ba amma zai wahala
mariyan tabari ya fita. Wata shawara ta tsirga mata.....taji a wannan karon ta
shirya ayi tone tone tsakaninta da mariya muddin autarta zata dawo cikin
hayyacin rayuwarta,wayarta ta dauka kanta tsaye ta fara kiran layin wayarta.
Kamar ana
jira ta tsagaita da kiran fu'ad wani kiran ya danno mata waya. Hajja harira,ko
kadan kiran bai sakata fargaba ba har sai data daga wayar suka fara musayar
magana.
"Da baki wahalar da kanki kina tambayata meye yasa nayi
kiranki ba......fuskata da sunana sunyi tambari a bakunan al'umma da kuma
kowacce jarida......kina tunanin akwai wani faruwar abun kunya da zanyi shakkar
fitarsa?....abun da koda ya fita tawa kunyatar qarama ce akan ta mahaifiyar
data sadaukar da mutuncinta da rayukan 'ya'yanta saboda ta mallaki abun
duniya?". Kaman babu jini cikin jikin maamah haka takeji......a yanzu
takeson solving wannan issue din batabataso hajja ta afko cikin wannan
da'irar.....tanaso a sanda hajja zata buqaci a fafata yaqin ta gama da issue
din fareeda dana sabreen harma da ameenatu,a sannan zata gwadawa hajja yadda
ake wasan kura da rayukan dan adam.
"Hajja......karki tunkari.fadan da bazaki.iya qarasashi
ba......ki lallaba masarautar cikin gidanki dake gareki,ki qarasa mulkinki
sannu a hankali,ki kuma jirayi randa naga damar 'yanta miki d'iyarki"
Wata
dariya data saka numfashin maamah tsaiwa na wucin gadi ta saki,sai da tayi me
isarta sannan tace.
"A a'ah......mariyatul kibdiyya......wai ni bakisan
abokin mutuwa nake nema ba?....,to bari kiji.......daga yau zuwa gobe na baki
ki maidomin da d'iyata gaba na,ko kuma wannan boyayyar fuskar dake gefena a
bugun shafin farko na jarida da kowa keson ganinta ta bayyana kanta da
kanta.....aikin fahimta ko?" Daga wannan hajja bata jira komai ba ta kashe
kiran.
Daga
zaunen da take amma sai taji tana jin jiri.......me yasa komai yake neman ya
kwabe mata lokaci guda?,kowa adadin awanni yake deba mata cikin umarni da kuma
gadara?,wai me yake faruwa ne?.
Daidai
nan taji muryar driver dinta yana fadin.
"Mun iso gida.hajiya" Kanta ta daga tana kallon
gidan,batasan sanda suka iso ba kaman yadda batasan sanda suka shigo gidan har
ya iso parking lot ya tsaida motar ya kuma kasheta ba.
Hannu ta
saka ta bude murfin motar,a hankali taja jikinta tana fita a motar,saidai ko
Cilakken tsaiwa batayi ba ta yanke jiki ta fadi a wajen hankalinta yana
gushewa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 132
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
132
Da sallama
farouq ya shigo,sabreen dake tsugunne gaban fu'ad din tana gyara masa nails
dinshi na qafa duk da fes suke.....amma tsabar bayason tayi nesa dashi ya tsiro
mata aikin ta matsa kadan tana amsawa.
"Sannu da aiki addanmu" Ya fada yana jawo kujera
ya zauna yana dubanta. Murmushi tayi a kunyace tana amsawa.
"Yauwa BB....sannu da qoqari....Allah y qara
zumunci.....ya saka da alkhairi".
" Ameen dai.....dama wani abun saboda ke akeyinsa ai ba
don mutum ba" Ya qarasa fada yana jifan fu'ad da harara wanda yayi relax
abinsa jikin kujera kaman badashi yake ba.
Miqewa
tayi da zummar basu guri.
"Kin gama ne?" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi.
Kai ta girgiza tana satar kallon farouq tana masa alama dashi. Ya fahimci me
take nufi amma ya basar,don haka ta buda baki.
"Zanyi waya dasu huda kafin ku kammala". Agogo ya
kalla da narkakkun idanunsa.
" Minti goma ki dawo ki qarasamin"
"Okay sir" Ta fada a girmame ta qarasa tana daukan
wayarta ta fice.
Farouq
bai jira ta kammala fita din bama ya soma fesar da abinda ke ransa.
"Zuwa nayi na maka sallama". Dariya ya taso ma
fu'ad amma ya danneta,sai ya miqe sosai ya zauna yana ware idanunsa akan farouq
"Ina zaka kuma?"
"Gida zanje ayimin aure.....bazan zauna na mutu na
tashi a gafiyar lahira ba". Wannan karon dariya ta gasken gaske ya bawa
fu'ad,har wanda ke parlor din zai iya jin sautinta,kalan dariyar daya jima
rabonshi da irinta.
"Bafa inda zakaje dude.....ko zaka hadiyi zuciya saika
gama jinyata ka cikasa ladanka".
"Lada irin naka ne banaso......ina samun ladanka kaima
kana samun naka ladan ko?....bazan iya ba....ni yanzu wallahi kafi
qarfina" Kai ya jinjina yana shafa sumarsa. Da gaske yasan farouq aure
yakeso.....kuma koda shine yake a matsayin farouq din yana sanya auren mace
kaman sabreen bayajin zai iya haqurin da yayi ma.......baiga abinda zaiwa
farouq ba sama daya tabbatar da aurensu a daidai date din da aka saka.....baya
jin zai yarda ya zama silar daga bikin farouq koda na kwana daya ne.
"Ka yiwa pilot nassar magana......ayi booking barinmu
taiwan zuwa Nigeria.......inaso larabar nan mu koma gida". Waiwayowa
farouq yayi yana kallonsa da mamaki.
"Ina zakaje kana jinya?,ina zakaje bincike kuma bai
kammalu ba?". Murmushi ya saki me taushi yana duban farouq din,duba irin
na 'yan uwantaka ta jini me cike da dumbin qauna.
"Bincike ya gama kammala farouq......fareeda keda
alhakin komai......ta samu nasarar aiwatar da komai dinne ta silar maamah data
bata full details din......abu daya da ban sani ba shine.....bata da masaniyar
abinda fareeda zatayi dashi?,ko tana da masaniya?,tayi hakanne dukka cikin
tsare tsarenta data dauki shekara da shekaru tana gudanarwa?" Ya qarasa
maganar duk wata walwala da yake ciki tana sulalewa daga jikinsa. Ba farouq
kadai ba,hatta sabreen data dawo da niyyar daukan slipper dinta ta zagaya koda
veranda din dakunan saita tsaya tana komawa da baya. Wani irin tausayinsa yana
sasuqar zuciyarta. Yadda walwala tayi qaura daga fuskarsa karo daya ya tabbatar
mata a yanzu a rayuwarsa bashi da sauran wani ciwo daya wuce MAHAIFIYARSA. A
jikinta ta dinga jin cewa......She has to put in effort to help him overcome
his past,ya kamata ta sake matsawa sosai cikin rayuwarsa.....yana buqatarta
fiye da yadda take hasashen zai kasance.
"No dude.....no.....kada kayi wannan tunanin.....ko
yaya ne.....ko yaya kuke da maamah uwa ce.....bana tunanin kowanne kalan hali
ne da ita zata iya bada qofa ko daman rabaka da rayuwarka". Idanunsa da
suka sauya kala ya maida kan farouq yana dubansa.
"Farouq.....duk yadda zan gaya maka abinda ke nan
gurin..." Yayi nuni da qirjinsa da yatsansa.
".....ba zaka fahimta ba.......mun rasa
MAHAIFIYA.....MUN RASATA RASHI NA HAR ABADA......saidai na yadda nayi kuma
imani,yana cikin rashin cikar kamalar ni'imar mutum cikin
DUNIYARSA......cikakkiyar ni'ima tana lahira".
"Duk da haka dude please......ka ajiye wannan a
side"
"Na ajiye farouq......fareeda zata girbi duk abinda ta
jima tana shukawa.....she must pay.....bawai iya kaina kawai ba". Kai
farouq ya jinjina,wani aikine daya shirya gudanarwa da kansa,sai gashi fu'ad
din ya rigashi.
"But dude.....inaga kaman ka qarasa warkewa....."
"Noooooo......dole farouq dina ya shiga qwaryar manya
as soon as possible.....ta iya yiwuwa ya rage zargina.....ta iya yuwuwa kuma ya
daina katsemin muhimman lokuta na da DUNIYATA". fuskewa farouq din yayi
yana sosa kanshi
"Eh to.....kaman tafiyanma zaifi mana Alkhairi gaba
daya.....don bana tunanin idan ka zauna a nan dinma warkewar arziqi
zakayi,gadon ya muku kadan gwara a koma gadon gida". Toshe bakinta sabreen
tayi,salin alin ta debi kayan kunyarta taja jikinta tana barin gurin tun wani a
cikinsu bai ganta ba.
★Salati drivern ya
saki,hannuwansa bisa saman kansa yana sake sakin salatin gami da cewa.
"Ku kawo dauki bayin Allah......hajiya ta zube".
Dukka hankalin ma'aikatan gidan ya tattaru a kanta,saidai har matan ciki tsoro
da shayin dagata suke,basusan haqiqanin abinda zai biyo baya ba idan suka
dagata bayan ta farka.
"Dole haka za'a ceci ranta,kome zai biyo baya ai ba
za'a barta ta mutu ba ko?". Malam sa'adu me gadi ya fada.
"Matso ke raliya ki kama musu ita" Ya fadi yana
matsawa baya.
"Gashi ba kowa gidan Alhaji hamza ballantana muji ina
ake kaita" Malam sa'ad ya fada yana duban driver din.
"Kowanne asibiti ma kaita za'a yi tunda abune na
gaggawa.....ki shigo mu tafi" Yace da raliya yana shigewa cikin motar.
Tuqi yake a
gaggauce yana tsoron kada ta mace a hannunsa,babar babban mutum irin me jadda
ta mutu a hannunsa tabbas ba qaramin tashin hankali bane.
Tafiyar
minti shabiyar suka samu wani private suka tsaya a nan,aka dauko wheelchair aka
dauketa akai,har a sannan bata dawo daidai ba.
Sai da suka
kashe minti kusan sha biyar a kanta sannna ta farfado,suka cire mata oxygen
suka daura mata ruwa da suke saka ran minti talatin ya qare sannan likitan yace
zaije ya dawo kafin ruwan ya qare.
Kanta kawai
take mirginawa tana jin qirjinta yana mata wani ciwo,duk inda ta juya fuskar
raliya data drivernta kadai take gani,har bacci ya saceta.
Still data
farka din ba wasu sabbin fuskokin saisu din dai. Wani abu ya tsaye mata a
wuya,wasa wasa tana shirin kamanceceniya da tsintacciyar magen da bata da wani
gata. A hankali ta sauke dubanta kan wata mata dake kusa da gadonta,wanda su
biyu ne kacal dama a dakin. Yara hudu ne tsaye a kanta,tana zaune saman
gadon,daya a hannun damanta.....daya a hagunta,dayan yana tsaye saman kanta
yana bare mata ayaba yana bata tana ci,dayar tana saman kujera gaban gadon nata
riqe da robar yoghurt tana jira ya gama bata ta miqa mata.
Hira suke
a tsakaninsu,kowanne fuskarsa dauke da walwala duk da cewa jinyar mahaifiyarsu
sukeyi. Tana gama ci ya karbi bawon ya jefa a Dutsbin,zai karba yogurt din daga
hannun ta zaunen ta hanashi.
"Saika kwashe ladan duk kai kadai,nima inaso" Ta
fada tana kai roban bakin mahaifiyartasu.
Idanu
maamah ta dauke tana runtse idonta,wani irin bacin rai yana ratsata. Tasan koda
kwatar kwatar kwatar kudin fu'ad duka yaran matar basu kai ba.....amma yadda
suke tattalinta da nuna mata qauna da kulawa kadai abun kallo ne.....ita gata
ta qare da zama 'yar kallo,cikin rayuwar kadaici da rashin wani sashe da zai
tallafeka.
"Allah ya isa ameenatu.....Allah ya isa" Ta fada a
sarari tana ji har zuciyarta anni ta mata cutar da bazata taba iya wankuwa daga
ranta ba.....hakanan kowacce kalar fansa data shirya dauka ba zata iya ramawa
daidai da abinda tayi mata ba.
Daga raliya
har driver din da kallo suka bita,saidai babu bakin magana,daidai nan likitan
ya shigo.
"Ta farka ko?" Ya fada cikin kulawa yana dauko
file din gami da sake duba abinda ya rubuta,ya qara wasu rubuce rubucen sannan
ya ajiyeshi yana dubanta.
"Hajiya ki rage saka bacin rai a zuciyarki.....ki rage
saka damuwa a ranki,kina da hawan jini bai kamata ki dinga zama cikin damuwa
ba.......irin wannan gaskiya yana iya haifar da matsala kala kala,ba'ason
abinda zai dinga sanyawa jinin yana hawa haka ta farat daya....kuyi qoqarin
ganin ta kiyaye" Ya qarasa maganar yana dubansu raliya ganin maamah din
taja idanunta abinta ta kulle.
"Tom.....in sha Allah" Raliya ta fada a sanyaye a
ranta tana cewa mu asuwa?,indai taji da kunnenta ai shikenan mun kubuta.
"Kuna iya tafiya gida.....amma da zarar taji wani abu
daban ayi hanzarin dawowa,saboda yanzun takai matakin da dole a dinga yawa
checking up nata".
"Mun gode likita" Driver ya fada bayan ya karbi
takardar magungunan daya rubuta mata.
Yana
shirin tada motar ya dan waiwayo
"Ya za'a yi da magungunan nan hajjaju?,zamu siya ne a
hanya ko za'a kawo?".
"Kai sagiru" Maamah dake a qufule da yadda suke
jaddada mata cutar hawan jini ta kira sunansa.
"Naam hajiya".
"Ka fita daga ido na......hawan jinin banza hawan jinin
wofi?,maqaryatan banza wanda mutum baya ciwon Allah da annabi?,shekarata nawa a
duniya hawan jinin bai sameni ba sai yanxu ina fafutukar cika burikana?,Allah
ya tsinewa wanda ya fasa cewa ina da hawan jini.......hawan ruwa ne
dani.....bani takardar nan nan" Ta fada cikin fada tana miqa masa
hannunta.
"Hajiya......ki tsaya ki duba maganarnan,don bakiga
yadda kike bane dazu.....bai kamata ki wasa da magani ba....." Kai ta
jijjiga.
"Lallai sagiru wuyanka ya isa yanka.....ashe kana dab
da rasa aikinka" Ta fada cikin mamakin tsaiwa.musu da yayi da ita.
"Ka bata mana sagiru" Raliya tayi saurin tunasar
dashi,salin alin ya miqa mata yana cewa.
"Tuba nake,Allah ya baki haquri".
" Idanma hada baki kukayi dasu saboda ku manna min ciwo
ku kasheni to ta Allah ba taku ba.......rayuwa a duniya yanzu na farata,maqi
gani ya kauda idonsa" Ta fadi tana yayyaga takardar ta watsar ta window
tana cewa
"Muje gida" Tana jin lallai tana buqatar tayi
magana da fu'ad da gaske.
Ya gama
shirin kwanciya tsaf sanye da pyjamas masu taushi farare qal,yana zaune saman
yalwatacciyar sofa yana binta da kallo sanda take qoqarin gyara masa gadon don
yaji dadin kwanciya.
"Sabrrrr" Ya kirata da sautin da ya sanya taji
tsigar jikinta ta zuba. A nutse ta waiwayo tana kallon lumsassun idanunsa.
"Yau bazan kwanta kan gadon nan ba". Da dan mamaki
take kallonsa,kafin takai ga tambayarsa dalili sai musaddiq yayi knocking.
Sabreen ta sauka a nutse tana nufan qofan da dan mamaki,don yanzun sukayi
sallama dasu zasu wuce gida. Kanshi yadan rusunar yanajin nauyinta da tsoron
kada hamman ya fatattakoshi.
"Maamah keson magana da hamma" Ya fada yana miqa
mata wayarsa. Bin wayar tayi da kallo kafin ta matsa tana baiwa musaddiq hanya.
Dubanta yayi saita daga masa kai alamun ya shige,a sanyaye yake takawa ciki
itama tabi bayansa da nufin gama gyara gadon ta fita ta bashi waje don ya samu
amsa wayar sosai.
Wani yawu
musaddiq ya hadiye yana duban hamman nasa daya tsareshi da ido.
"Maamah ce tace lallai na kawo......" Hannu ya
daga masa yana amsar wayar,sai ya miqa masa yana fita daga dakin a gaggauce
yana jin bazai iya jiran ma ya gama amsa wayar ba ya karba sa hadu gobe,don
haka kai tsaye ya wuce inda cab ke jiransa.
Handsfree
ya sanya wayar,ya kuma ajiyeta a gabansa kawai yana zuba mata idanu,irin yadda
yakeyi idan ranshi yana bace kuma baya da buqatar amsa wani kiran amma tilas ta
sakashi amsawa.
"Ina kyautata zaton kana jina?,ko yanzun ma 'yar mulkin
taka ce ta daga kiran?" Tayi maganar da wata irin hasala da fusata.
"Muhammad fu'ad jadda ne" Ya amsa mata da wani
irin nutsuwa yana zubawa sabreen ido wadda ka ta ke duqe tana gyara bedsheet
din gadon da pillow case din.
"Naji dadin jin hakan......umarni ne daga uwa zuwa
shashan danta wanda baisan inda yake masa ciwo ba.........ka kama dukiyar
mahaifin yarinyar dake mutuwar sonka ka garqame.....ka masa sanadin aikinsa
duka saboda kana hannuwan mutanen da suke riqe da ragamar rayuwarka......sai
abinda suka ce.....ni mariya dana dauki cikinka daga gudan jini har zuwa
tsoka.....harka zama mutum.....saboda lalurar rayuwa ta nesantani daku shikenan
yanzun nice wulaqantatta a wajenka......to indai nice mahaifiyarka ina baka
umarni cikin qasa da awa daya komai na ambassador khaled ya koma kan aiki
daidai".
"Tom" Kawai yace da ita yana sanya dukkanin wani
qarfi na qwanjinsa dana ruhinsa yana danne zuciyarsa. Wasu irin abubuwa ke taso
masa......yana rantsuwa da ubangijin ka'aba......banda da gaske ya ratsa jikin
maamah ya bullo zuwa cikin duniyar da yake rayuwa a yanzu a cikinta......babu
wani halitta kaf duniya daya isa yayi masa quarter quarter abinda tayi masa a
yanzun. Hannunsa yake mutstsukawa yatsunsa suna wani irin qara,yana jin
wadannan mutanen guda biyu sun fara kai masa ko ina a rayuwarsa.
Kunnuwanta ne taji ba zasu iya dauke maganan maamah din ba,saita saki
gyaran gadon ta soma nufar qofa tana takawa a gaggauce.
"Sabreen.....dawo" Ya fadi kansa tsaye ba tare
daya damu maamah zata iya ji ba.
"Ina magana da kai kana kiramin sunan wannan
yarinyar?,annamimiyar karu....." Ya riga ya shanshano abinda take da
muradin fada,sai kawai ya sanya hannunsa da wani irin zafi ya datse kiran yana
kashe wayar gaba daya.
Da gaske
wani irin abu sabreen keji,wani yanayi taji yana tsarga mata,ba zata iya zama
ba da gaske,ba zata iya jura ba.....don haka ta sake takawa zata fita,sai kawai
ya sanya hannunsa me ciwon dake nade ya fusgota sai gata ta fado zuwa jikinsa
yasa hannuwansa duka biyun ya lullubeta cikin qirjinsa kaman ya manta ko baisan
ciwon dake hannunsa ba ko kuma wani sassauqan rauni ne da bashi da radadi ko
zafi ko kadan.
A zafafe
yake kiran wata number,tsoronsa a karon farko ya kamata ganin yadda numfashinsa
yake fita da sauri,zuciyarsa na wani irin bugawa.
"Haka fushinsa yake?" Ta tambayi kanta da
kanta,daidai sanda kiran ya shiga aka daga. Ko muryar dake wancan bangaren bata
jiba ya soma sauke musu umarni.
"Inaso a daren yau basai gobe ba.....fareeda khaleed
mustapha ta kwana a a cell......ba ita kadai ba,da duk wanda ya kawo wargi ko
yunqurin hana fita da ita" Abinda yace kawai kenan yayi wurgi da wayar.
Matseta
yayi so sai a jikinsa,yana daga idanunsa da suka kada suka sauya launi yana
zubesu cikin nata......
_tofa.....ran 'yan maza ya baci.....an manta da ciwon da ake
jinya......ko sabreen zatayi aikinta?🫣,zamu gani_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 133
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
133
Sasai taji
wani abu yana ratsa jinin jikinta game dashi......wani narkakken tausayinsa
yana taso mata yana kuma mamaye ilahirin jikinta. Ta yarda dari har bisa dari
cewa......da uwa irin maamah gwara ka rayu cikin maraici......da uwa irin
maamah gwara ka zamana cikin layin yaran nan da ko dumin iyayensu basuji ba
ubangiji ya karbi rayukansu......ta sake yarda da cewa.....komai ubangiji ya
tsarawa bawa tabbas akwai manufa da alkhairi a ciki.
"Ya zakayi haka?" Ta fada tana sake saka idonta
cikin nasa sosai tana kuma riqe da fuskarsa cikin tafukan hannayenta. Kaman
wanda yasha wani abu ya maku yake magana
"Ya bazanyi haka ba.....ta yaya zanyi wasa da
duniyata?.....ta yaya zan bari a taba duniyata?" Numfashi taja me zurfi
wanda ya shige jikinta da wani irin mahaukacin sonsa da kowacce safiya yake
qaruwa cikin ruhinta,ta sake bude idonta a kansa tana kallonsa.
Taga
abubuwa da yawa cikin idanunsa......giyar soyayya da qauna.....da kuma wani
irin fushi. Ji tayi kaman bata da wani sauran aiki daya rage mata a duniya a
yanzun banda ta kwaranyar da wannan fushin da kuma damuwar daga wannan ruhin
daya gama macewa a soyayyarta. Ba zato ba kuma tsammani yaji ta hade bakunansu
guri guda.
Wani irin
zazzafan kiss ta soma ajiye masa kafin ta tura harshensa cikin bakinsa ta soma
sarrafashi kaman yadda yake mata. Cikin qasa da second biyu kowacce wuta dake
jikinsa ta dauke,ya soma kokawar qwato numfashinsa,wanda bata daga masa qafa ba
ta fara aike masa da qarin wasu saqonnin da suka birkitashi......suka sakashi
ya soma mance wayeshi?,a wacce DUNIYAR yake?,meye matsalarsa a rayuwama gaba
daya?.
Tayi
masa ba zata ta qarshen qarshe......ta kuma tashi kansa da wasu irin zafafan
salon da suka saka har ya manta meye ma yakeyi?. Wani irin saqo take aike masa
me cike da jan rai......sai taji ya gaza jurewa ya juyeta ya maidata qasa.
Nutsuwarta
taso maidawa jikinta,ta dafe qirjinsa a sanda yayi mata rumfa tana kallon
narkakun idanunsa da suka sauya launi. Dubanta yayi shima yana neman qarin
bayani,saita masa nuni da hannusa me ciwo da ya dafesu ya aza masa nauyi kaman
ya manta yana da rauni.
"Kina tsoron jini ne?" Ya tambayeta ha tare daya
kalli inda take nuna masa din ba. Fuska tadan bata daban,ta sani ba'a fiya son
yayi wani aiki sosai da hannun ba,saboda a samu ya warke da wuri.....kuma
wannan fitinar da yakeso yayin tabbas zata iya maida ciwon danye.
"Alright" Ya fadi da hanzari cikin qasa da second
daya yana hautsinata ya koma qasan ita kuma ta koma sama ta maye gurbinsa.
"You're in charge now" Ya fadi yana dage mata
girarsa. Wani kunya ya kamata,ta cusa fuskarta cikin ni'imtaccen qirjinsa da
bata gajiya da wanzuwa akai.
"I give my self to you....i surrender to your
will....play your role well" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi.
Duk yadda
yake buri hakane ya kasance,duk yadda yake da buqata haka tayi masa. Abun ya
gigitashi ya sanyashi fita a hayyacinsa,wasu maganganun daya dinga yi sai
sukayi mata mugun nauyi,har ta dinga jin daga wannan ranar kaman ba zata iya
sake hada ido dashi ba.
Wani sabon
amarcin aka balle a asibitin tsakanin fu'ad da sabreen din,ba tare da kowa ya
kula da lalurar da yake tare da shi ba.
Hankalinta ya tashi bayan komai ya lafa da taga bandages din hannunshi
sunyi staining da jini.
"Ka gani ko?,dama bana gaya maka ba?" Ta fada a
narke muryarta tana rawa tana shirin sakin kuka. Hannun nasa ya kalla ya saki
murmushi yana jawota jikinsa sosai,duk qoqarin sauka da takeyi daga jikin nasa
amma ya hanata.
"Please stay with me.....i could use some relaxation
time......sai muyi wanka"
"Ciwonka fa?" Ta tambaya a mamakance tana kallon
fuskarsa da tuni ya maida idanunsa ya lumshe yana fidda wani sassanyan
murmushi.
"Forget about.....zasu gyara zuwa safe" Ta sake
motsawa zatayi magana ya dora yatsansa akan labbansa.
"Shshshsh" Yace da ita,dole ta maida kanta ta
kwantar,saidai hankalinta gaba daya yana kan ciwon.
Bayan sun
idar da sallar asuba,tana kammala azkar dinta ta koma toilet don yin fitsari
saiga jini. Ta razana sosai ta ware dukka idanunta tana duban jinin. Jikinta ta
dauki rawa gaba daya,bata da wani qwarin daga murya ta kirashi,tana ma ganin
kaman bata lokaci ne,sai kawai ta fito a toilet din da wani irin sauri.
Kansa ya
daga yana kallonta sanda ta fito din,sai shima ya ware idonsa yana dubanta
kafin ya miqe da sauri ganin yanayinta. Sosai ya riqeta yana tambayarta
"What's happening?.....relax.....gayamin" Pant
dinta kawai ta daga masa,sai ya zare idanunsa waje kaman zasu fado.
"Oh shit......subhanallah" Ya fadi yana jin gaba
daya ya gama firgicewa. Cikin kula da takatsantsan ya maidata gadonsa ya
kwantar da ita.
"Lemme call a doctor" Ya fada yana fita a dakin da
sauri don yana ganin tsaiwa kiransa ta landline ma bata lokaci ne.
Su biyu
suka shigo,shi da wata likitan mace daban,yanata masa magana akan hannunsa amma
bata wannan yake ba.
"Scan zamu fara yi mata don tabbatar da lafiyar babies
din" Likitan ta fada tana qarasawa gaban gadon sabreen din.
Maida
dubansa likitan yayi a kansa.
"Hannunka ya akayi yayi staining haka?" Ya tambayi
fu'ad din wanda hankalinsa duka yake kan sabreen wadda dr din ta fara jawo
na'urar scan wanda take a dakin permanently.
Kafin
yace komai anyi knocking qofar an turo an kuma shigo. Farouq ne shida musaddiq
dauke da breakfast da anni ke dafa musu.
Likitanne
ya amsa sallaman,farouq ya qaraso dakin fuskarsa dauke da alamun tambayar
abinda yake faruwa.
"Lafiya dude?" Farouq ya tambayi fu'ad yana
qarasawa kusa dashi. Bai amsa masa ba,ya taka ya matsa gaban inda su sabreen
suke ya jawo curtain divider ya rufesu daidai sanda yaji tana tambayar sabreen
din
"Kinyi wani aiki me nauyi ne sosai?" Amsa mata
tayi da a'ah....still ta sake tambaya.
"Ko kunyi mu'amala?". Shuru tayi tana jin kunya na
dawainiya da ita,fu'ad da hankalinsa ke wajen ya sauke hannayensa daya goya a
qirjinsa yana fadin.
"Kiyi checking baby din kawai madam"
"Okay sir" Ta amsa masa a ladabce.
Daidai
lokacin wani ma'aikacin jinya ya qaraso yana tura medication cart dake dauke da
bandages da sauran kayan dressing.
"Your hand sir" Dr din ya sake fadi yana duban
fu'ad tare da masa nuni da abun zama.
Sai daya
waiwaya zai zauna din suka hada idanu da farouq,kai ya dauke yana hade rai,sai
shima farouq din ya basar yana girgiza kai.
Ana mata
scan din likitan yana ware wancan bandage din a hankali,farouq yana daga zaune
a gabanshi yana danne dariyarsa. Ya wani maze sai cin magani yakeyi?,karon
farko da ya fuskanci fu'ad din baya son kallonshi. Koda ba'ayi bayanin komai ba
farouq din ya fahimci aika aika akayi a dakin a daren jiya,saidai fatarsa daya
babies dinsu ya zaman lafiya suke.
"Wow......unbelievable" Muryar likitan ta fita da
wani irin sound da yaja hankalinsu su duka. Kasa jurewa fu'ad din yayi,ya
dagawa likitan hannu.
"Wait..." Sai kawai ya miqe yana danne sauran
bandage din da ba'a gama cirewa ba.
Kai tsaye
ya kutsa tsakanin curtains din ya shiga.
"Triplets ne sir" Likitan ta sake fada da wani
kwantaccen murmushi saman fuskarta. Idanu kawai ya zurawa na'aurar qirjinsa na
harbawa,wani bahagon farinciki yana son bugar dashi. Zooming na scan din
tayi,sai gashi ya nuna wasu gurabe guda uku.
"Gasu a nan sir......congratulations" Ta fada tana
sakin dariya cikin nishadi.
"Alhamdulillah.......alhamdulillah" Farouq da
yakeji kaman yayi tsuntsuwa ya shigo a nuna masa shima ya fada yana murza
hannayensa bakinsa ya gaza rufuwa.
Idanunsa ya
lumshe sannna ya budesu,yana so yaji mafarki yakeyi ko kuma idanunsa biyu.
"Subhanallahi wabu
hamdih.....subhanallahilazeem,Alhamdulillah......alhamdulillah hamdan kaseeran
dayyiban mubarakan fihi....." Ya
fada yana yin qasa da kansa yana jin wani abu yana taso masa. Wanne abu zaiyiwa
Allah ubangiji da zai da dadawa Allah?,wanne abu zai yiwa Allah mafi soyuwa a
wajen ubangiji.....duk da ya ambaci wadancan kalmomin,masu sauqi a
harshe.....masu nauyi a mizani.......masoya a wajen Allah(subhanallahi wa bi
hamdih,subhanallahil azeem,kada ki wasa da yawan maimaitasu,kalmomi ne masoya a
wajen Allah,wato wadanda Allah yake sonsu qwarai,ga nauyi a mizani,zasu qarawa
ayyukanki nauyi ranar qiyama,ranar da ake auna ayyuka akan ma'auni).
"Thanks.....thank you so much" Ya fada yana isa
inda sabreen din take. Hannunsa ya dora saman kanta yana ranqwafawa a
samanta,sai a sannan ya dauke idonsa daga kan screen din yan jin kamar zaiga
yaran be baro baro a ciki. Idanunsu suka hadu waje daya,saita fara sakar masa
murmushi. Kai yake jijjigawa kawai ya kasa magana,sai ta miqa masa hannunta
shima kai tsaye ya bata nashi,ya sunkuya yana sumbatar mararta.
"You're my world sabbrrrr.......da nace ke DUNIYATA ce
da gaske ke din duniyata ce.......ya rabbb......ka tsaremin wannan baiwar taka
da irin tsaronka ita da duk abinda take dauke dashi......yadda mahaifanta suka
haifamin alkhairin rayuwata......ubangiji ka shimfida musu aljannarka cikin
qaburburansu........"
"Allah ya hada da abba daya zama nagartaccen uban daya
nunawa yaransa muhimmancin mace" Ta tari numfashinsa tana jin zuciyarta na
karyewa da irin addu'arsa akan mahaifanta wanda bata taba jin irinta ba. Wata
kyakkyawar runguma yayi mata wadda ta sanya likitan ficewa daga cikin labulen
ta basu guri. Wannan karon ba fu'ad kadai ba.....hatta da sabreen saida
fuskarta ta jiqe da hawayen farinciki. Ya fita jarumta a wannan karon,don shi
ya soma janye jikinsa yana goge mata fuskar.
"Kada ki tashi hankalin babies dinmu......ya isa.....is
okay ko?" Ya fada bayan ya gama goge mata fuskar ya sunkunya ya sumbaceta
a goshi.
"Sir......zaa qarasa duba ciwon?" Likitan yace
dashi,sai ya miqawa sabreen daya hannun nasa ya dagata ta zauna ya yaye labulen
bayan ya tabbatar ko ina a jikinta a rufe yake.
Hugging
nasa farouq yayi wanda ya kasa zama saboda farinciki,fu'ad ya dan bubbuga
bayansa yana murmushi
"Congratulations dude....." Kai tsaye ya taya
farouq din murna,don ya sani suna raye ko basa raye,zai amsa sunan mahaifinsu
ne kawai wanda yayi cikinsu,amma sunan uba farouq keda wannan matsayin.
"Thank you dude.....na gode" Farouq ya fadi
murmushi yana qin barin fuskarsa.
Likitan
yana duba ciwon daya doctor din tana sake yiwa sabreen bayani.
"Duka fetuses din suna lafiya qalau,ki zauna sosai ki
huta yau gaba daya,zai tsaya nan bada jimawa ba....sai prenatal medication
dinki da zaki ci gaba da sha da kula dasu.....ina miki fatan haihuwa sassauqa
da lafiyayyun Yara".
"Na gode" Sabreen din ta fada tana murmushi. A yau
din jinta take wata ta daban,jinta take ta musamman,yau ita sabreen itace a
mazaunin uwa?,wadda zata kawo wasu rayukan cikin duniya?,wasu halittun da suka
kasance jininta?,jinin muhammad fuad dukka a cakude a jikinsu?.
Duk bayan
minti daya sai ya daga kai ya kalleta,daga qarshe parlor suka koma don Dr din
ya qarasa dubashi,sai yake jinsa ba tsaro,gani yake kaman yana kalle masa ita.
"Amazing....haka kake da quick healing?" Likitan
ya tambaya da mamaki yana murmushi sannan ya dora.
"Nayi mamakin ganin saurin warkewar ciwon,kadanne ya
rage banda an bashi pressure me yawa ba da bazai fidda jini ba.....za'a maida
sabon bandage amma dan kadan.....please next time kada a matseshi da yawa hakan
zai bashi daman warkewa da wuri".
" Ai basai ka fada bama likita,ni nan zanwa tufkar
hanci" Farouq ya fada yana bubbuda hanci. Harara fu'ad ya watsa
masa,sannan ya maida harshensa zuwa hausa.
"Kada kiyi gigin cewa zaka kai qarata wajen
anni....muddin ka rabani da duniyata saina maida maka naka hannun agogon
baya" Ya fada sounding seriously.
Dariya
farouq ya tuntsure da ita,baisan ya akayi ya dagoshi haka da wuri ba
"Ko bankai qararka wajen anni ba nasan nayi dakai
ai" Ya amsa masa yana miqe qafafunsa nishadance yana duba saqon fannarshi
daya shigo masa.
Sai da
likitan ya kammala komai ya fice sannan ya kalli farouq.
"Bani abinci malam.....haka ake jinyar?" Ya fada
yana hararasa.
"Zan baka mana....kai banda ka fanshi kanki jiya zaka
sake ganin face din angon fanna ne?" Yadda yayi maganar ya sanya murmushi
subucewa fuskar fu'ad,yakau da kansa kawai yana murmushi.
Ya zuba
masa komai amma sai yaga yayi gefe da wani babban mug.
"Wancan meye a ciki". Da hannu farouq ya nuna
masa.
"Wannan?,maca and ginseng tea ne".
"Zubashi a nan" Ya fada yana nuna masa wani glass
mug. Nesa farouq ya qarayi dashi.
"Kai ina......kaida wannan ai ba yanzu ba
wallahi......kana wannan barnar xan barka kaci gaba da shan wannan?,kayi haquri
ku haifemin yarana lafiya....to daga nan har china kuje saikun dawo".
Idanunsa ya janye kawai bai ko musawa farouq ba ya dauki mug din daya zuba masa
normal black tea ya fara kurba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 134
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
133
Sasai taji
wani abu yana ratsa jinin jikinta game dashi......wani narkakken tausayinsa
yana taso mata yana kuma mamaye ilahirin jikinta. Ta yarda dari har bisa dari
cewa......da uwa irin maamah gwara ka rayu cikin maraici......da uwa irin
maamah gwara ka zamana cikin layin yaran nan da ko dumin iyayensu basuji ba
ubangiji ya karbi rayukansu......ta sake yarda da cewa.....komai ubangiji ya
tsarawa bawa tabbas akwai manufa da alkhairi a ciki.
"Ya zakayi haka?" Ta fada tana sake saka idonta
cikin nasa sosai tana kuma riqe da fuskarsa cikin tafukan hannayenta. Kaman
wanda yasha wani abu ya maku yake magana
"Ya bazanyi haka ba.....ta yaya zanyi wasa da
duniyata?.....ta yaya zan bari a taba duniyata?" Numfashi taja me zurfi
wanda ya shige jikinta da wani irin mahaukacin sonsa da kowacce safiya yake
qaruwa cikin ruhinta,ta sake bude idonta a kansa tana kallonsa.
Taga
abubuwa da yawa cikin idanunsa......giyar soyayya da qauna.....da kuma wani
irin fushi. Ji tayi kaman bata da wani sauran aiki daya rage mata a duniya a
yanzun banda ta kwaranyar da wannan fushin da kuma damuwar daga wannan ruhin
daya gama macewa a soyayyarta. Ba zato ba kuma tsammani yaji ta hade bakunansu
guri guda.
Wani irin
zazzafan kiss ta soma ajiye masa kafin ta tura harshensa cikin bakinsa ta soma
sarrafashi kaman yadda yake mata. Cikin qasa da second biyu kowacce wuta dake
jikinsa ta dauke,ya soma kokawar qwato numfashinsa,wanda bata daga masa qafa ba
ta fara aike masa da qarin wasu saqonnin da suka birkitashi......suka sakashi
ya soma mance wayeshi?,a wacce DUNIYAR yake?,meye matsalarsa a rayuwama gaba
daya?.
Tayi
masa ba zata ta qarshen qarshe......ta kuma tashi kansa da wasu irin zafafan
salon da suka saka har ya manta meye ma yakeyi?. Wani irin saqo take aike masa
me cike da jan rai......sai taji ya gaza jurewa ya juyeta ya maidata qasa.
Nutsuwarta
taso maidawa jikinta,ta dafe qirjinsa a sanda yayi mata rumfa tana kallon
narkakun idanunsa da suka sauya launi. Dubanta yayi shima yana neman qarin
bayani,saita masa nuni da hannusa me ciwo da ya dafesu ya aza masa nauyi kaman
ya manta yana da rauni.
"Kina tsoron jini ne?" Ya tambayeta ha tare daya
kalli inda take nuna masa din ba. Fuska tadan bata daban,ta sani ba'a fiya son
yayi wani aiki sosai da hannun ba,saboda a samu ya warke da wuri.....kuma
wannan fitinar da yakeso yayin tabbas zata iya maida ciwon danye.
"Alright" Ya fadi da hanzari cikin qasa da second
daya yana hautsinata ya koma qasan ita kuma ta koma sama ta maye gurbinsa.
"You're in charge now" Ya fadi yana dage mata
girarsa. Wani kunya ya kamata,ta cusa fuskarta cikin ni'imtaccen qirjinsa da
bata gajiya da wanzuwa akai.
"I give my self to you....i surrender to your
will....play your role well" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi.
Duk yadda
yake buri hakane ya kasance,duk yadda yake da buqata haka tayi masa. Abun ya
gigitashi ya sanyashi fita a hayyacinsa,wasu maganganun daya dinga yi sai
sukayi mata mugun nauyi,har ta dinga jin daga wannan ranar kaman ba zata iya
sake hada ido dashi ba.
Wani sabon
amarcin aka balle a asibitin tsakanin fu'ad da sabreen din,ba tare da kowa ya
kula da lalurar da yake tare da shi ba.
Hankalinta ya tashi bayan komai ya lafa da taga bandages din hannunshi
sunyi staining da jini.
"Ka gani ko?,dama bana gaya maka ba?" Ta fada a
narke muryarta tana rawa tana shirin sakin kuka. Hannun nasa ya kalla ya saki
murmushi yana jawota jikinsa sosai,duk qoqarin sauka da takeyi daga jikin nasa
amma ya hanata.
"Please stay with me.....i could use some relaxation
time......sai muyi wanka"
"Ciwonka fa?" Ta tambaya a mamakance tana kallon
fuskarsa da tuni ya maida idanunsa ya lumshe yana fidda wani sassanyan
murmushi.
"Forget about.....zasu gyara zuwa safe" Ta sake
motsawa zatayi magana ya dora yatsansa akan labbansa.
"Shshshsh" Yace da ita,dole ta maida kanta ta
kwantar,saidai hankalinta gaba daya yana kan ciwon.
Bayan sun
idar da sallar asuba,tana kammala azkar dinta ta koma toilet don yin fitsari
saiga jini. Ta razana sosai ta ware dukka idanunta tana duban jinin. Jikinta ta
dauki rawa gaba daya,bata da wani qwarin daga murya ta kirashi,tana ma ganin
kaman bata lokaci ne,sai kawai ta fito a toilet din da wani irin sauri.
Kansa ya
daga yana kallonta sanda ta fito din,sai shima ya ware idonsa yana dubanta
kafin ya miqe da sauri ganin yanayinta. Sosai ya riqeta yana tambayarta
"What's happening?.....relax.....gayamin" Pant
dinta kawai ta daga masa,sai ya zare idanunsa waje kaman zasu fado.
"Oh shit......subhanallah" Ya fadi yana jin gaba
daya ya gama firgicewa. Cikin kula da takatsantsan ya maidata gadonsa ya
kwantar da ita.
"Lemme call a doctor" Ya fada yana fita a dakin da
sauri don yana ganin tsaiwa kiransa ta landline ma bata lokaci ne.
Su biyu
suka shigo,shi da wata likitan mace daban,yanata masa magana akan hannunsa amma
bata wannan yake ba.
"Scan zamu fara yi mata don tabbatar da lafiyar babies
din" Likitan ta fada tana qarasawa gaban gadon sabreen din.
Maida
dubansa likitan yayi a kansa.
"Hannunka ya akayi yayi staining haka?" Ya tambayi
fu'ad din wanda hankalinsa duka yake kan sabreen wadda dr din ta fara jawo
na'urar scan wanda take a dakin permanently.
Kafin
yace komai anyi knocking qofar an turo an kuma shigo. Farouq ne shida musaddiq
dauke da breakfast da anni ke dafa musu.
Likitanne
ya amsa sallaman,farouq ya qaraso dakin fuskarsa dauke da alamun tambayar
abinda yake faruwa.
"Lafiya dude?" Farouq ya tambayi fu'ad yana
qarasawa kusa dashi. Bai amsa masa ba,ya taka ya matsa gaban inda su sabreen
suke ya jawo curtain divider ya rufesu daidai sanda yaji tana tambayar sabreen
din
"Kinyi wani aiki me nauyi ne sosai?" Amsa mata
tayi da a'ah....still ta sake tambaya.
"Ko kunyi mu'amala?". Shuru tayi tana jin kunya na
dawainiya da ita,fu'ad da hankalinsa ke wajen ya sauke hannayensa daya goya a
qirjinsa yana fadin.
"Kiyi checking baby din kawai madam"
"Okay sir" Ta amsa masa a ladabce.
Daidai
lokacin wani ma'aikacin jinya ya qaraso yana tura medication cart dake dauke da
bandages da sauran kayan dressing.
"Your hand sir" Dr din ya sake fadi yana duban
fu'ad tare da masa nuni da abun zama.
Sai daya
waiwaya zai zauna din suka hada idanu da farouq,kai ya dauke yana hade rai,sai
shima farouq din ya basar yana girgiza kai.
Ana mata
scan din likitan yana ware wancan bandage din a hankali,farouq yana daga zaune
a gabanshi yana danne dariyarsa. Ya wani maze sai cin magani yakeyi?,karon
farko da ya fuskanci fu'ad din baya son kallonshi. Koda ba'ayi bayanin komai ba
farouq din ya fahimci aika aika akayi a dakin a daren jiya,saidai fatarsa daya
babies dinsu ya zaman lafiya suke.
"Wow......unbelievable" Muryar likitan ta fita da
wani irin sound da yaja hankalinsu su duka. Kasa jurewa fu'ad din yayi,ya
dagawa likitan hannu.
"Wait..." Sai kawai ya miqe yana danne sauran
bandage din da ba'a gama cirewa ba.
Kai tsaye
ya kutsa tsakanin curtains din ya shiga.
"Triplets ne sir" Likitan ta sake fada da wani
kwantaccen murmushi saman fuskarta. Idanu kawai ya zurawa na'aurar qirjinsa na
harbawa,wani bahagon farinciki yana son bugar dashi. Zooming na scan din
tayi,sai gashi ya nuna wasu gurabe guda uku.
"Gasu a nan sir......congratulations" Ta fada tana
sakin dariya cikin nishadi.
"Alhamdulillah.......alhamdulillah" Farouq da
yakeji kaman yayi tsuntsuwa ya shigo a nuna masa shima ya fada yana murza
hannayensa bakinsa ya gaza rufuwa.
Idanunsa ya
lumshe sannna ya budesu,yana so yaji mafarki yakeyi ko kuma idanunsa biyu.
"Subhanallahi wabu
hamdih.....subhanallahilazeem,Alhamdulillah......alhamdulillah hamdan kaseeran
dayyiban mubarakan fihi....." Ya
fada yana yin qasa da kansa yana jin wani abu yana taso masa. Wanne abu zaiyiwa
Allah ubangiji da zai da dadawa Allah?,wanne abu zai yiwa Allah mafi soyuwa a
wajen ubangiji.....duk da ya ambaci wadancan kalmomin,masu sauqi a
harshe.....masu nauyi a mizani.......masoya a wajen Allah(subhanallahi wa bi
hamdih,subhanallahil azeem,kada ki wasa da yawan maimaitasu,kalmomi ne masoya a
wajen Allah,wato wadanda Allah yake sonsu qwarai,ga nauyi a mizani,zasu qarawa
ayyukanki nauyi ranar qiyama,ranar da ake auna ayyuka akan ma'auni).
"Thanks.....thank you so much" Ya fada yana isa
inda sabreen din take. Hannunsa ya dora saman kanta yana ranqwafawa a
samanta,sai a sannan ya dauke idonsa daga kan screen din yan jin kamar zaiga
yaran be baro baro a ciki. Idanunsu suka hadu waje daya,saita fara sakar masa
murmushi. Kai yake jijjigawa kawai ya kasa magana,sai ta miqa masa hannunta
shima kai tsaye ya bata nashi,ya sunkuya yana sumbatar mararta.
"You're my world sabbrrrr.......da nace ke DUNIYATA ce
da gaske ke din duniyata ce.......ya rabbb......ka tsaremin wannan baiwar taka
da irin tsaronka ita da duk abinda take dauke dashi......yadda mahaifanta suka
haifamin alkhairin rayuwata......ubangiji ka shimfida musu aljannarka cikin
qaburburansu........"
"Allah ya hada da abba daya zama nagartaccen uban daya
nunawa yaransa muhimmancin mace" Ta tari numfashinsa tana jin zuciyarta na
karyewa da irin addu'arsa akan mahaifanta wanda bata taba jin irinta ba. Wata
kyakkyawar runguma yayi mata wadda ta sanya likitan ficewa daga cikin labulen
ta basu guri. Wannan karon ba fu'ad kadai ba.....hatta da sabreen saida
fuskarta ta jiqe da hawayen farinciki. Ya fita jarumta a wannan karon,don shi
ya soma janye jikinsa yana goge mata fuskar.
"Kada ki tashi hankalin babies dinmu......ya isa.....is
okay ko?" Ya fada bayan ya gama goge mata fuskar ya sunkunya ya sumbaceta
a goshi.
"Sir......zaa qarasa duba ciwon?" Likitan yace
dashi,sai ya miqawa sabreen daya hannun nasa ya dagata ta zauna ya yaye labulen
bayan ya tabbatar ko ina a jikinta a rufe yake.
Hugging
nasa farouq yayi wanda ya kasa zama saboda farinciki,fu'ad ya dan bubbuga
bayansa yana murmushi
"Congratulations dude....." Kai tsaye ya taya
farouq din murna,don ya sani suna raye ko basa raye,zai amsa sunan mahaifinsu
ne kawai wanda yayi cikinsu,amma sunan uba farouq keda wannan matsayin.
"Thank you dude.....na gode" Farouq ya fadi
murmushi yana qin barin fuskarsa.
Likitan
yana duba ciwon daya doctor din tana sake yiwa sabreen bayani.
"Duka fetuses din suna lafiya qalau,ki zauna sosai ki
huta yau gaba daya,zai tsaya nan bada jimawa ba....sai prenatal medication
dinki da zaki ci gaba da sha da kula dasu.....ina miki fatan haihuwa sassauqa
da lafiyayyun Yara".
"Na gode" Sabreen din ta fada tana murmushi. A yau
din jinta take wata ta daban,jinta take ta musamman,yau ita sabreen itace a
mazaunin uwa?,wadda zata kawo wasu rayukan cikin duniya?,wasu halittun da suka
kasance jininta?,jinin muhammad fuad dukka a cakude a jikinsu?.
Duk bayan
minti daya sai ya daga kai ya kalleta,daga qarshe parlor suka koma don Dr din
ya qarasa dubashi,sai yake jinsa ba tsaro,gani yake kaman yana kalle masa ita.
"Amazing....haka kake da quick healing?" Likitan
ya tambaya da mamaki yana murmushi sannan ya dora.
"Nayi mamakin ganin saurin warkewar ciwon,kadanne ya
rage banda an bashi pressure me yawa ba da bazai fidda jini ba.....za'a maida
sabon bandage amma dan kadan.....please next time kada a matseshi da yawa hakan
zai bashi daman warkewa da wuri".
" Ai basai ka fada bama likita,ni nan zanwa tufkar
hanci" Farouq ya fada yana bubbuda hanci. Harara fu'ad ya watsa
masa,sannan ya maida harshensa zuwa hausa.
"Kada kiyi gigin cewa zaka kai qarata wajen
anni....muddin ka rabani da duniyata saina maida maka naka hannun agogon
baya" Ya fada sounding seriously.
Dariya
farouq ya tuntsure da ita,baisan ya akayi ya dagoshi haka da wuri ba
"Ko bankai qararka wajen anni ba nasan nayi dakai
ai" Ya amsa masa yana miqe qafafunsa nishadance yana duba saqon fannarshi
daya shigo masa.
Sai da
likitan ya kammala komai ya fice sannan ya kalli farouq.
"Bani abinci malam.....haka ake jinyar?" Ya fada
yana hararasa.
"Zan baka mana....kai banda ka fanshi kanki jiya zaka
sake ganin face din angon fanna ne?" Yadda yayi maganar ya sanya murmushi
subucewa fuskar fu'ad,yakau da kansa kawai yana murmushi.
Ya zuba
masa komai amma sai yaga yayi gefe da wani babban mug.
"Wancan meye a ciki". Da hannu farouq ya nuna
masa.
"Wannan?,maca and ginseng tea ne".
"Zubashi a nan" Ya fada yana nuna masa wani glass
mug. Nesa farouq ya qarayi dashi.
"Kai ina......kaida wannan ai ba yanzu ba
wallahi......kana wannan barnar xan barka kaci gaba da shan wannan?,kayi haquri
ku haifemin yarana lafiya....to daga nan har china kuje saikun dawo".
Idanunsa ya janye kawai bai ko musawa farouq ba ya dauki mug din daya zuba masa
normal black tea ya fara kurba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 135
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
135
So take ta
zama kaman kowacce mace.....wadda ke dauke da responsibility na mijinta,kula da
duk wani welfare nashi da al'amuran da suka shafeshi,bawai ta barshi shi yayita
hidima haka da ita ba,don haka koda suka qarasa bedroom din towel ta ajiye masa
sannan ta zarce toilet din.
Water
heater ta kunna wanda in minutes ta kashe kanta da kanta alamun ruwan ya
tafasa,saita kunna tap din duka guda biyu na famfunan,ta cika masa bathtub da
ruwan me dumi sosai sannan ta saisaitashi ta health faucet saboda kama ruwa da
sauransu.
Ta
kammala tana waiwayowa da nufin fita tace ta gama sai ji tayi an sake sama da
ita an tsumbulata cikin ruwan sannan ya biyo bayanta.
"Bansan sai yaushe zakiyi nauyi ba....kosai kin fara
turtsi bulli irin na masu ciki?" Ya fada yana qanqameta cikin ruwan.
"Me yasa da bakya hadamin ruwa me dadi haka?" Ya
sake fada yana sake matso da ita yana shanshana sumarta data fara jiqewa. Bare
baki tayi ta soma masa kukan shagwaba,akan meye zai jiqata bayan ba yanzu
zatayi wanka ba. Dariya ya dinga mata kafin daga bisani ya fuskanci kukan ya
koma na gaske ya lalace wajen lallashinta.
Mintuna
arbain kafin su fito,tayi daurin qirji da towel tanata goge kanta daya jiqe.
Curling iron din data dauko ya karbe,ya soma tsaga gashin yana nade mata shi da
style din da takeso.
"Hamma.....ana jiranka fa"
"Tare zamu sauka sabrrrr,bazan sauka na barki ba"
Karbe curling iron din tayi ta ajiye
"Mu shirya na rakaka kaci abinci ka fita.....kace kana
da hidiman bikin BB naka.....yaushe ka gama ganawa da mutane ka maida
hankalinka akai?". Hancinta ya lakace mata.
"Yes maaa.....da alama ina da personal assistant me
hazaqa,anya bazan sallami saddiq ba?" Murmushi ta saki tana cewa.
"Ba ruwana,kada yace nasa an koreshi".
Sai data
tabbatar ya qoshi sannan ta taka masa har inda yake ganin baqin da suka zama
dole,baqinsa na jikinsa sosai wanda ita kanta batasan da wajen ba sai a sannan.
Zata juya kenan daya daga cikin guard dinsa suka qaraso.
"Malam ne yazo"
"Har sai an nema masa izini?,kace masa ya shigo qasan
rumfar can" Ya fadi yana juyawa yana fasa shiga sitting room din. Hannunta
ya kama.
"Muje ku gaisa da malam.....mutumin kirki wanda ta
silarsa ne na samu ilimin addini". Bata musa masa ba suka taka zuwa
farfajiyar da aka qawata da kujerun zama.
Tun daga
nesa ta gane malam dinta,mutumin kirki na gasken gaske wanda kusan zata iya
cewa tafi fu'ad sanin hakan.
Mamaki
sosai malam yayi sanda yake zama saman dayan kujerun dake wajen. Ta zame tana
gaidashi kaman yadda fu'ad yayi.
"Ashe da gaske rumaisa take?,sanda take gayamin ke kike
auren muhammadu ba dauka shirmenta ne kawai.....muhammadu kayi sa'ar mata da
gasken gaske" Malam ya fada yana maida dubansa ga fu'ad. Sabreen fu'ad din
ya kalla sannan ya maida dubansa ga malam.
"Tana da tausayi da taimako......tana da yawan sadaka
da kuma kyauta,bata wata batayi sadaka ga mabuqata ba......marainiya ce
muhammadu......nasan halinka kai dinma.....muna da kyakkyawan zaton nagarta
daga gareka......ka riqeta hannu bibbiyu,lada biyu gareka,ladan riqon maraya,ga
kuma ladan kula da iyali".
"In sha Allah malam" Ya fada yana sadda kansa
qasa. Inama ace malam yazo a sanda yake tsaka da fara cusgunawa
rayuwarta?,inama ace malam yazo a sannan ya ceceshi daga feeling guilty da
yakeyi a duk sanda ya tuna yadda ya mu'amalanceta a baya?.
Duk da cewa
ba laifinsa bane.......yayi dukkanin binciken da zai yi a matsayinsa na dan
adam.....kuma abinda ya samu kenan. Da gaske ga a inda kudaden da duk take diba
sukafi tafiya kenan fiye da jikin 'yan uwanta,sai yakejin wannan din dama ce ta
sake samun wasu labaran a kanta ta wajen malam din.
Hira kadan
tayi da malam tana tambayarsa inna ta bada saqon gaisuwa ga rumaisa da shaida
mata sun dawo sannan ta koma ciki.
Da kanta
ta shirya abun motsa baki ta kawowa malam din,duk da ma'u tace ta barshi amma
tace sam malam yafi gaban haka.
Qarfe
tara tayi shirin bacci,don tunda ya fita ba sake jin motsinsa ba,ta tabbatar
zai wahala idan ba baqin bane suka sha masa kai. Ta dawo parlor din farko da
nufin daukan madarar shanu ma'u na fitowa a kitchen da alama ta gama komai na
yau sai gobe kenan.
Tana mata
sallama amma idanunta akan kwalin hannun mau,tsirfa da tsarabe tsarabe irin na
musu ciki haka kawai taji yawunta ya tsinke.
"Amma fa ma'u meye wannan?" Kallon farin box din
tayi tayi murmushi.
"Wallahi amna ce ta aikomin dashi,wani doughnuts ne da
ta taba ban guda daya ta yafi dani,sai tace zata sake sakawa a kawomin".
"Mu gani" Sabreen ta fada tana matsowa,bude mata
ma'u tayi take yawun bakinta ya qarasa tsinkewa gaba daya.
"Don Allah ma'u ko guda daya ne" Ta fada tana
narke fuska idonta akan doughnuts din da aka yiwa wankan madara.
Dariya ta
qwacewa ma'un,tasan halin ciki yafi gaban haka,bataga abinda zata samu ta hana
sabreen din ba,bare wannan da nan da nan idan sunason wani za'a sake kawowa.
"Jeki da kwalin gaba daya" Ta fadi tana tura mata
kwalin. Har wani dan tsallen murna tayi,ta amshe tana godiya ta haura saman
dashi.
Gudu gudu
ta gama shiryawa,ta ware gashinta saman bayanta ta haye sofa tana bude kwalin.
Lashe baki tayi tana jin kaman ya mata nisa ta tsaya bude ledar a daidai kawai
saita farke.
"Uhmmmnnnnn" Ta fadi saboda yadda wata lafiyayyar
madara ta hade da doughnuts din a bakinta
"Ya salammmm" Ta sake fada sanda tayi gutsira ta
uku,kawai saita kasa daurewa ta juya bayan kwalin ta kuwa dace da sunan
mamallakiyar abun.
*_Maman ummies delight_*+234 803 049 9555
A fili ta
karanta komai tana lumshe ido,saita rasa wanne zata fara kira a tsakaninsu?.
Landline
kawai ta nufa ta soma kiran amna.
"Addarmu"
"Ba wani addarmu......yanzu amna harki samo abun arziqi
irin haka amma ki kasa tunawa dani?". Tsam amna tayi tanaso ta tuna
meye,ita ta dauka ma complain zatayi akan sun sauka bata nemeta ba
" Adda mene?"
"Doughnuts mana.....doughnuts din maman ummi".
Dariya sosai ta zowa amna,duk yadda taso tareta kuwa sai data fito,karon farko
data fara yarda masu cikin ajinsu da zasuga sun fiya fi'ili da neman fitina da
gaske sukeyi bawai iya shege bane,yadda ta fadi doughnuts din maman ummin tar a
bakinta saika rantse ta santa farin sani,kaman ba yaune cin farko ba.
"To adda mu fara da bismillah mana.....dama anni ta
gayamin triplets ne,suna sauka albishir din data fara yimin kenan da alama da
abun take kwana tana tashi.....Allah ya bawa hamma juriya,ni dama guduwa zanyi
na barku". Baki sabreen ta kama
"Iyeeee,au gayamin kike aure zakiyi kenan" Kunya
ta kama amna kaman sabreen tana gurin.
"Ni na isa adda...."
"Yanzu mu ajiye wannan maganar.....ina za'a samu
doughnuts dinnan?,na kusa cinye wannan" Ido amna ta zaro.
"Tana kaduna fa?,amma saga kaduna zuwa kano kawo
doughnuts dinta kaman kina garinsu ne,sharp sharp ne.....idan ta kama sai asa
hamma ya tashi jet a karbo miki" Dariya sosai maganan ta bawa
sabreen,saidai da gaske dadin doughnuts din har cikin tsokokinta take jinsa.
"Seriously amna.....am addicted to it......zan samu
nayi breakfast dashi?"
"Lemme call her......zaki samu koda wajen 10 ne haka in
sha Allah.....ko duba flight din safe sai ayi idan akwai a sako miki.....amma
indai shi zaki koma ci hamma yana kwale kwale" Amna ta fada tana qyaqyata
dariya tayi kuma saurin katse kiran.
"Kada fa haka ta kasance" Ta fada tana raba ido
bayan ta lamushe taji bata gamsu ba. Ledar tabi ta tande madarar tasss ta saka
kwalin a gaba har tana fatan inama tana
sauran wani a ciki?.
Bata
ankara ba bacci yazo yayi awon gaba da ita sassaucin da aka samu kenan.
Qarfe sha
daya saura ya qaraso cikin parlor din,idanunsa a kanta,wani soyayyarta yakeji
tana sake ratsa dukka qasusuwansa. Bayanan da ya sake ji daga bakin malam sai
yakejin kamar ta cancanci sama da soyayyar da yake nuna mata.....kamar ta
cancanci sama sa wannan rayuwar da takeyi a yanzu.
Sai daya
kammala komai a hankali don kada ya tasheta,ya dawo ya zauna da wayoyinsa. Su
anni farouq da musaddiq duka yakeson kira,yanason komai ya kammala da wuri,don
kwanaki hudu ne kadai suka rage daurin auren.
Sai sannan
idonsa ya sauka kan kwalin,ya jawo ya dudduba yana mamakin yadda aka yiwa ledar
tasss,yadan girgiza kai ya kwashe ya zuba dustbin sannan ya dawo ya zauna yana
sake duban fuskarta. Wani kyau take qarayi masa kullum,hakanan ba qaramin kyau
bacci yakeyi mata ba,murmushi ya subucewa labbansa ya fara kiran farouq.
Kira
daya ya daga kaman yana kusa da wayar,muryarsa can qasa yayiwa fu'ad sallama.
"Are you okay?" Fu'ad ya tambaya tana tsayawa cak.
"Am okay dude"
"Ma sha Allah.....ka karba envelope"
"Na karba"
"Ka bude?"
"Na bude dude.....but I'm.....I'm speechless
dude.......rubutun jikin invitation card dina da ruwan gold na ainihi?"
Murmushi ya subucewa fu'ad.
"Kafi qarfin wannan dude......kada ka sake magana
akai.....akwai sadakin fannah a daga envelope din....have you seen it?"
"What?,dowry fa kake magana dude?......wannan gold din
ya ninka abinda suke karba a matsayin sadaki......babanta malami ne,kada yaga
mun zura da yawa fa".
"Fannah tafi qarfin haka a gurinmu....tunda takeson
wannan tsohon tuzurun namu,ta kuma amince zata zauna mana dashi da zuciya
daya.....sadakin mace baya yawa a musulunce,ko nawa aka bata yayi,saidai ma
yayi kadan,yadda kace babanta malami ne nasan yasan da hakan,sayyadina umar
yaso qayyadewa a zamaninsa,wata mata ta tunasar dashi annabi baiyi hakan ba,
sai ya qyale shima.... Ka fahimta?"
"Ya ilahi dude.....am speechless seriously"
"Zamuyi fada dakai......ina fata ka riqe data
din....kwana hudu......saura kwana hudu dude dina ya angwance" Sautin
murmushinsa ya riski fu'ad,hakan kuma ya masa dadi a haka sukayi sallama. A
duniya bayajin yana da wani abu da zai iya sakawa farouq dashi koda meye yayi
masa.
Musaddiq
ya kira wannan karon,shima dai kaman yana kusa da wayar ya daga. Muryarsa da
mugun sanyi ya amsa sallamar,still shima tambayarsa yayi lafiya yake?.
"I'm fine hamma"
"Maamah ko?" Shuru musaddiq yayi yana mamakin
yadda ya gano haka ta farat daya. Shurunsa ya bawa fu'ad tabbaci,ya sauke
numfashi.
"Idan ka dorama kanka daukan damuwoyinta ba inda zakaje
a rayuwa,zakayita zamane kamar a inda ta tafi ta barka ba tare da damuwan yadda
rayuwa zata kasance maka ba.....na kiraka na gaya maka,kayi magana da musaddiq
kai dashi ku duba gidajen nan dana bashi details dinsu ku zaba,za'a hade
bikinka sana farouq in sha Allah,so ka ajiye damuwan da bata cancanci damuwarka
ba.....ka fuskanci rayuwa da reality dinka.....but kada ka sake ka manta da
wannan......ka riqe mana amna sai mutuwa ce zata raba". Mutuwar daya fada
ta saukar masa da wani irin matsanancin faduwar gaba......ta kuma tuna masa da
maganarsu ta dazu da maamah.
"Mutuwa hamma?".
"Yes.....mutuwa,saboda ita kadaice ta isa ta raba
Soyayyar masoya" Shuru ne ya wanzu
tsakaninsa da shi,har sai da fu'ad din yace.
"Kana layi?"
"Inaji hamma"
"Good......komai da amna zata buqata ka rubuta ka
turamin.....bance ko sisinka ka saka a bikinka ba" Baima jira ya masa godiya ba ya katse,saboda
baya buqatarta,yanajin wani wajibinsa ne ya saukeshi.
Anni ce ta
qarshe daya kira,amna na kusa da ita ta miqa mata wayar.
Ban
gajiya suka yiwa junansu,sannan itama ya buqaci ta bada duk wani abu da take
buqata.
"Muhammadu kabar 'yan uwanka suyi wani abun
mana?" Murmushi yayi
"Anni sai idan bana raye.....ki fadawa amna ta rubuta
komai da take buqata na lefe.....idanma ba zata iya ba tazo nan gidan su hadu
ita da duniyat....." Saurin katsewa yayi bai qarasa ba,kunya ta kamashi ya
aza hannunsa aka yana sosa sumarsa. Murmushi me sauti ya qwacewa anni
"Ita da duniyarka ameenatu" Murmushi shima ya
saki.
"Su rubuta komai,bance ta dauke masa komai ba".
Kaman sauran bai jira ta masa wata godiya ba ya katse wayar,ya zubawa sabreen
ido wani abu yana yawo cikin ranshi.
Da alama
baccin ya mata dadi sosai,amma dole ya tasheta don akwai magana me muhimmanci
da zasuyi da bata buqatar takai safiya,yana ganin kaman tayi nisa.
Wayar anni
ta ajjiye gefanta,tana jin wani abu yana sauka a ranta. Tabbas fu'ad din wani
kyautar Allah ne a garesu,bawai don dukiyar da yake da ita ba.....aah....ta
jima da sanin haka tun yana fu'ad dinsa dan makaranta secondary school,fu'ad
dan bautar qasa. Wata irin zuciya ce shimfide a qirjinsa,wani irin dattako daya
girmi shekarunsa......wani irin halin girma me dumbin yawa.
"Tabbas mariya inda kinsan irin kyauta da alkhairin da
Allah yayi miki a rayuwa da baki gudu kin bar muhammad ba.....da baki gudu
kinbar musaddiq ba". A tattare dasu gaba daya tana ganin wata irin nagarta
ta musamman.
"Hammanki yace ki rubuta ko kije gurin addarki ki.masa
list na kayan lefe duka" Anni ta
fada tana nazarin amna data fahimci ta yawaita shuru shuru tun daga yammacin
yau din.
"Lefe ann?" Amna ta tambaya da wata sassanyar
murya
"Wani abun daban kikaji na fada?" Anni ta fada
tana nazarinta. Kai amna ta girgiza,haka kawai taji hawaye sun cika
idanunta,sai anni ta kasa jurewa.
"Meya kuma?"
"Tsoro nakeji anni......gabana yanata faduwa" Sai
hawayen da take maqalewa ya gangaro mata.
"Tsoro?" Anni ta maimaita,kai amna ta gyada mata.
Yankewa gaban anni yayi ya fadi,ta sauke numfashi tana ambaton sunan Allah.
"Tashi kije kiyi alawala,ki karanta hasbunallahu wa
ni'imal wakil qafa dubu kafin ki kwanta". Kai amna ta gyada sannan ta miqe
a sabule tana fita a dakin zuwa nata.
"Addanmu" Fu'ad dake tsugune gaban sabreen da
bacci yaketa danneta ya fada yana leqa fuskarta. Da qyar ta sake bude idon nata
a karo na uku.
"Adda sabreen.....tashi don Allah" A cikin baccin
taketa mamakin kiranta da adda din da yaketa yi,saita miqe tana daquna fuska.
"Hamma.....bacci"
"Zakiyi,na miki alqawari,amma kafin sannan jeki wanki
fuskarki ki dawo". A daddafe ta miqe saboda nauyin bacci,ta lalubi toilet
din ta shige.
Ba jimawa
ta fito,fuskarta tayi fresh da digo digon ruwa,idanunta sun dan tashi kadan
alamun bacci,ta zauna saman sofa tana dubansa.
Ajiye
abinda yakeyi yayi ya taso,ya iso gabanta ya tsugunna a hankali. Hannuwansa
yakai ya kamo tafukan hannayenta a tausashe.
"Adda sabreen" Ya maimaita fadi yana murmushi.
Idanu tadan ware tana dubansa wani malalacin murmushi yana qwace mata. Kai ya
jinjina mata.
"Kin bamu daman neman auren sister huda?.....kin bamu
izini mu nemawa musaddiq auren sister huda?".
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 136
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
136
Wani saukar ba
zata zancen yayi mata,wani irin zuwa ya yiwa kunnuwanta.
"Saddiq kuma?,saddiq dai hamma?" Ta fadi da sautin
muryar bacci da har yanzu bata gama warwarewa ba,banda ta zuba ruwa saman
fuskarta da sai tace cikin jerin gwanon mafarki kawai wannan maganar take
dibanta. Murmushi ya saki me sanyi yana jinjina mata kai.
"Eh......saddiq dinmu addanmu......inaso ya zama mijin
huda nan da kwana hudu,kaman yadda farouq zai zama mijin fannah in sha
Allah" A hankali ta daga ido tana sake duban fu'ad din,sai takeji kaman
wasa yake mata da hankali kawai ko tsokana,saidai kuma ko daya bataga wannan a
cikin idanunsa ba.
"Hamma.....huda fa?.....ka manta mudin ba kowa bane
hamma.... Mu din ba wasu madaukaka bane,ni din kawai a cikin family dinku ya
isa,basai huda ta shigo ba...."
"Shshshsh" Ya fada yana dora yatsantsa akan lips
dinsa. Bayason wannan karayar da take nunawa,bayason wannan raunin da yadda har
yanzu ta kasa jinta kaman kowa.....bayason yadda ta kasa daina tuna wacece ita
a baya
"Damu daku dukkaninmu abu daya ne yayimu.....jirgi daya
ne ya kwaso mu.....ki manta akwai wani lokaci da abinci da sutura suke gagarar
muhammad fu'ad?....ki manta akwai wani lokaci daya shude da yunwa take saka
musaddiq kwana yana kukan yunwa?,kin manta wani lokaci daya shude fu'ad dan
jari bola ne?......kin manta sanda saddiq ke kwana da yunwa saboda ba gatan uwa
a gefansa?,duka damu daku ki gayamin meye banbanci a ciki?" Shuru tayi
tana tuna komai kaman yadda yake tunasar da ita yanzu.
"Hamma.....amma huda batayi qanqanta ba?.....yanzu zata
gama secondary school fa......a haka an sanyata a makaranta da wuri kaman yadda
abbanmu yake mana....." Murmushi ya
saki yana dan jan kumatunta.
"Qanqanta?.....ke din kanki duka duka shekara nawa kika
bata?,banajin yakai biyar,ba gashi muna zaune ba?".
"Hamma karatunta fa?" Hannu ya sanya yana dungure
mata kai da sauri
"Lallai dai sai an ja mana aji kafin a bamu auren
sister huda.....lallai ko yaya wai sai an wajiga mu?.....me huda zatayi da
karatu duniyata?,ba huda ba.....ko wanda ke rayuwa qarqashin inuwar jadda
banajin zai buqaci karatu saboda ainihin buqata ta lalura.....saidai duk me
sha'awa yayi karatun don dai sunansa ilimi.....ba abinda huda zatayi da
takardu.....saidai.idan har tanason karatu saddiq bazai hanata ba.....za'a
dauko mata duk kalar malamin da takeso ya koyar da ita matakin ilimi daga na
college har zuwa university har PhD ma.......idan kuma makaranta takeso......ta
zabi duk makarantar da takeso a fadin duniya cikin jerin qasashe da muke dasu a
duniya 195 zuwa 200....kowacce take so zataje in sha Allah......sai me
kuma......a shirye muke mu karba duka qorafinki" Ya qarasa fada yana
tsareta da ido tare da jiran abinda zata sake fadi.
A hankali
ta jinjina kai
"Na amince hamma.....na bada izini bisa sharadi da
alqawarin zai bata dukkan wata kulawa data dace koda bayan raina". Wani
zazzaro idanu wajen fu'ad yayi yana dubanta.
"Kul.....karki sake zancan bayan ranki my
world......waye ya gaya miki fu'ad yana da sauran rayuwa bayan babu
taki?". Idonta ta maida ta lumshe a hankali tana murmushi.
" Zamu rayu tar in sha Allah......zamu kula da yaranmu
mu kuma basu tarbiyya tare" Ya fada yana sumbatar hannunta a tausashe.
"Na gode sosai duniyata.....na gode sosai da
sadaukarmana da daya daga cikin abubuwan da kike matuqar so a duniya.....kika
yarda ta zama abokiyar rayuwar saddiq"
"Kafi qarfin komai a wajena duniyata.....kafi gaban
haka muffin". Ta fada itama
harshenta da sautinta cike da qauna da soyayya.
" Bayan gidan malam......sai ina da ina kike kai
taimako?" Ya sake soko Mata tambayar da bata taba kawota ba. Fararen
idanunta ta daga ta kalleshi,sai kuma ta sauke idanun nata qasa tana jin
nauyinsa. Batason abinda zai sanya ya dauko mata wannan zancan na abinda ya
wuce a tsakaninsu.
"Ki bani dama.....inaso ki dore da aikin ladan da
kikayi niyya in a halal ways.......inaso na miqar dake kici gaba da abinda kika
fara a baya". Sake kallonsa tayi a karo na biyu......tana jin yana sake
shiga rayuwarta yadda ya kamata. Soyayyarsa tana sake hudata,wani mafarki ne
wannan nata,dasu take kwana dasu take tashi.....hayewar su huda kawai bai sanya
zuciyarta ta kwanta d'ari bisa dari ba.....bai sanya zuciyarta ta samu nutsuwar
da take yunwar samu ba. A yanzun a kuma wannan lokacin sai gashi ya gama qarasa
karanta tunaninta kafffff yana son xike mata ragowar gibin da ya rage.
"Me yasa a kowacce rana kake sake karantar zuciyata?,me
yasa a kowacce rana kake abubuwan da suke sake haukatani a kanka muffin?".
Idonsa ya lumshe yana budesu duka a lokaci guda. Yanason irin wannan
yanayin.....yana son irin wannan lokacin da zaiyi zaune kawai a gabanta yana
tana tona masa asirin zuciyarta.
"Sabrrrrr" Ya sake kiranta a tausashe.
"Haqqina ne.....kuma cikar kamalar kowanne d'a namiji
kenan,ya karanci wace matarsa.....me tafi so?,me tafi buqata?,me zaiyi ya
mallaketa?". Mallakar daya fada ta sakata fashewa da dariya tana zaro ido.
" Hamma.....mallakata kakeso kayi?"
"Nama mallakeki duniyata.....na mallakeki....kedin tawa
ce ni kadai har abada" Ya fada yana daga yatsunsa guda biyu.
"Gidan marayu.....gidan gajiyayyu.....yaran da iyayensu
suka mutu suka barsu kuma babu me tallafa musu irinmu" Takai qarshen
maganar muryarta tana karyewa.
"Ki zauna ki tsara dukkanin burinki akan wadannan gidajen". Ya fadi yana miqewa
tsaye. Wani irin sanyi taji yana sauka saman zuciyarta
"Ina fata ubangiji ya lullubeka da dukka
rahamarsa......ya yaye maka damuwarka.....ya kyautata qarshenka.....na gode da
karamcinka karimin mijina.....na gode da wannan halin dattako naka uban
'ya'yana". Murmushi me sanyi ya kubce masa,yanajin alfahari da wannan
addu'ar tata.
"Allahumma ameen matata 'yar aljanna.....amma saura abu
daya da baki roqamin ba". Idanunta ta juya,abinda ya sake tafiya sosai
dashi
" Me kenan muffin?"
"Baki roqi Allah ya qarawa wannan ameenatun so na
ba.....so nake ameenatu ta soni fiye da yadda takeson kanta,don kuwa ta samu
wanda zai kula mata da kan nata" . Kunya ta sakata sanya tafin hannunta ta
rufe fuskarta kafin tace.
"Inda ana iya bude zuciya ko qirji a nunawa
wani.....tabbas da na bude maka tawa zuciyar kaga abinda yake ciki a
kanka,wataqila zakafi gasgatani.....don maganar fatar baki tayi kadan"
Rasa me zaya ce mata yayi,sai kawai ya tsugunna yana kissinh forehead dinta a
tausashi.
Yana
dauke labbansa tana daga idanunta da sauri,sai ta soma rarraba idanun nata tana
a narke.
"Kai.......ina doughnuts dina?" . Dubanta yayi
"Wanne doughnut?". Ya tambaya yana tunanin ko
mafarki tayi a dazun kafin ya tashera.
Tambayar tata da yayi sai taji kaman zata saki kuka
"Doughnuts dina mana da ma'u ta bani......a nan fa na
ajjiye naci kadan na ajiye sauran". Qaramin murmushi yayi.
"Kin cinye madam....ni na tattara kwalin na zuba a
dustbin". Idanu ta waro waje tana dubansa sosai da salon rigima a
muryarta.
"Ka sakamin a shara?,wallahi ban cinye abuna ba,akwai
saura" Ta fadi tana miqewa zumbur gami da nufar dutsbin din. Da mamaki
yake binta da kallo ganin yadda ta bude dustbin din tana ciro kwalayen.
"Kai?,ka cinyemin?" Ta fada cikin sanyin jiki
hawaye yana taruwa cikin oily eyes dinta. Dariya ma abun ya bashi,ya daga
hannunsa alamun surrender yana dubanta.
"Innalillahi,Allah ba ruwana,sanda nazo ba komai a ciki
sai boxes din da leda". Dariyar tasa ta qular da ita,sai kawai ta fashe da
kuka tana sakin boxes din.
"Wallahi kaine.....kaine ka cinyemin kuma bazan yarda
ba" Mamaki sosai ya kamashi ganin yadda ta zube tana kuka bilhaqqi,hawaye
shabe shabe ta dage wai shine ya cinye mata. Da sauri ya isa inda take yana
miqa mata hannu.
"Yi haquri ki tashi.....eh na yarda nine na ci".
Ya fadi hakan don ya lura qaryata ba shine yaci din bama qular da ita yakeyi.
"Dama kai dinne ko?" Ta fada tana watsa masa
harara da jiqaqqun idanunta,sai ta sake fashewa da kuka sosai kaman wadda aka
yiwa dukan tsiya harda shashsheqa.
Ya rude
sosai don ta maida abun serious matter. Ya sulale ya tsugunna a gabanta yana
cewa.
"Am really sorry my world......taso muje ki gayamin a
inda aka siyo a sake nemo wani". Sai data galla masa harara sannan tace.
"Kaduna.....kaduna ne wajen maman ummi".
"Kaduna?" Ya maimaita.
"Eh" Ta fada cikin son jiran mutum yayi wani abun
ta sake barke masa. Kansa ya daga ya kalli agogo yana duba lokaci. Qarfe goma
na dare,wa zaya tasa zuwa kaduna yanzu. Idonsa ya mayar kanta,saiya taras ta
zuba masa ido tana kallonsa,dukkan alamu kuma sun nuna rigima ce a kwance idan
ya musa.
"Is alright.....bani details na masu abun".
"0803 049 9555,wallahi tunda ummee ta haifeni ban taba
cin doughnuts me dadin nata ba" Ta fada bilhaqqi da gaske har zuciyarta
tana jin tun kafin ya kawl ma yawunta ya tsinke. Idanu warwaje yake kallonta.
Tashin hankali!,ya fadi saboda yadda yaga tsaf ta haddace number,yaushe hakan
ta faru oho shima bai sani ba.
"Ina zuwa" Yace mata yana takawa a hankali yana
sauka qasan. Shi kam yasam yanzu ba lallai a bawa jadda wings daman tashi
ba,kafin ma su nemo umarni,pilot din ya isa su tashi ai asuba yayi,saidai duk
da haka bai fasa kiran number din ba.
Ainihin
sunan daya fito ameena sai yaji kimar me number ya qaru a idonsa tun ba'a daga
kiran ba. Bugu na uku aka dauka da cikakkiyar sallama ya amsa shima.
"Am sorry,na kira late at night......i don't know ko
matar aurece.....am sorry idan hakanne"
"Ba komai" Matar me kirki ta fada. Bayanin dalilin
kiran yayi sannan ya dora.
"If possible goben zan aiko a taho dake,kizo kiyi mata
sai a maidaki.....kiyi naming price dinki,kada ki damu ko nawa ne ki zaba i
will pay it". Murmushi tayi.
"Ba matsala.....ko goben da safen ma ana iya samun ko
pieces nawa takeso.....akai akai sai a dinga zuwa ana karba mata,Allah ya raba
lafiya,kowanne ciki da yadda yake zuwa ma mace,sai haquri". Yaji dadin
magananta sosai,don daga yanayinta ya fahimci ba yarinya qarama bace,yayi
godiya sannan ya kashe ya kira farouq.
Bugu daya
ya samu farouq,da alama bacci ya fara daukansa ma.
"Farouq akwai matsala fa" Maganan da ta saka
farouq miqewa ya zauna
"Me ya faru?" Ya tambaya. Ajiyar zuciya ya saki ya
masa bayani a nutse.
"I don't know ina zan samu doughnuts?.....kune masu
zuwa irin guraren nan".
"Ba damuwa......bari na duba wani guri kusa
damu......sun iya sosai zataji dadinsa".
"Thank you dude.....you save me" Ya fada yana dan
dafe goshinsa sannan suka yanke kiran.
Lallabata
ya dinga yi har aka gaya masa ga saqo daga bakin gate. Sanda yaje har farouq
din ya aje saqon ya juya,ya yaba masa sosai irin saurin da yayi don duka duka
mintuna talatin ya iso,ya tabbatar wannan gudun nasa ya zuba.
"Ga doughnuts din" Ya fada da murmushi yana aje
box din a gabanta. Da zumudi ta jawo ledar ta bude. Tun a yanayin packaging din
ta tabbatar akwai matsala,banbamce babance take gani iri iri da wancan,ta danne
tana bude doughnuts din.
Kanta ta
daga ta kalleshi,ya dage mata gira yana qoqarin lallabata,can qasan ransa yana
fatan kada ta ballo rigima kuma.
Kanta ta
mayar kai,ta gutsira tana kaiwa bakinta. Taunawa daya biyu ta furzar,muryarta
tana rawa ta kalleshi
"Wannan bashi bane.....Allah bashi bane".
" I know sabrrrr.........kiyi haquri kici wannan din,i
promise you da safe wancan din zakici as breakfast"
"Really?" Ta tambaya tana tsareshi da idanu.
"In sha Allah" Ya fada yana bata assurance.
Hankalinta taji ya kwanta,amma duk da haka ta ture wancan din
"Banasonshi....nata yafi dadi yafi madara" Dariyarsa ya boye,yana mamaki ashe da gaske
masu juna biyu suna haka?,idan madara takeso suna da ita kala kala har sai ta
ture,amma ya tabbatar yace tasha din ba sha zatayi ba.
★Tun sanda
amna tabar dakin sai taji ta gaza nutsuwa sam sam,hankalinta ya kasa
kwanciya,itama sai ta samu kanta da rashin nutsuwa da kokwanto.
Toilet ta
wuce,ta daura alwala,ta dawo ta shimfida abun sallah. Raka hudu tayi ta zauna
ta fara karanta hasbunallahu wani'imal wakil qafa dubu. Ko kadan batajin bacci
a idanunta,haka kuma batasan meye ya dauke baccin a idanunta ba.
Bayan ta
gama ta sake gyara tasbaharta. Bismillah hirrahamanir rahim 450 ta
karanta,sannan tayi salati 450 shima. Bayan ta gama ta karanta (Allazina qala
lahumunnasu innan nasa qad jama'u lakum fakshauhum fa zadahum imanan wa qalu
hasbunallahu wani'imal wakil zuwa
fanqalabu bini'imatimminallahi qafa 45(ko 450 idan zaka iya),ta sake karanta
salati 450,sannan ya azizu ya khafi ya qawiyyu ya ladifu 450,duk inda takai guda
100 saita tsaya ta jaddada roqonta ga Allah,neman tsari daga dukkanin wani mummunan
abu ko abun qi da zai iya samunta ko ya samu wani cikin ahalinta,ta sake
zurfafa addu'ar samun albarka da sanya albarka a dukkanin wadannan aurarraki da
akayi dama wadanda suka wuce.(addu'a ce me kyau da tsananin tasiri wajen samun
biyan buqata wajen Allah,in kin zama me riqe addu'a da barwa Allah lamuranki
kin huta da gasken gaske,shi zai miki komai daidai da yadda ya dace dake,sadaka
ce na baku sai a sanyani a addu'a,ubangiji ya bamu dacewa).
Shafa
addu'ar tayi tana jin wata nutsuwa tana saukar mata,ta miqe a nutse ta shirya
don wucewa gurin abba. Sai data gama shirin sannan ta zauna saman stool,ta debo
ruwa a wani babban mug ta soma karanta ayatulkursiyyu qafa ashirin da daya ta
fita da mug din a hannunta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 137
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
138
Zuwa takwas
da rabi na dare ya shigo gida. Tun kafin ya shiga din ya sallami kowa,don
ragowar lokacinsa yana jin cewa na duniyarsa ne.
Yau din
sai take jinta a cikakkiyar matar aure kaman kowacce d'iya mace. Ta shirya
sosai tayi kwalliya da wani farin tattausan lace,fari ne qal babu sirkin komai
a jikinsa. Ya kwanta mata sosai a fatarta,ba makeup a fuskarta,daga powder data
dace da skin dinta,sai wheat lips da ya sanya pink lips dinta suke wani glowing
me daukar hankali.
Sau daya
tak ya kalleta yaji tana son raba masa hankali,sai yake ganin kamar canzata
akayi daga fitarsa zuwa dawowarsa,kaman yadda yaji qamshin gidan gaba daya ya
sauya.
Qugunta ya
kamo,ya kasa cewa komai sai daya sada lips dinsa da nata,ya tsotse lips gloss
din da kyau kaman bata taba shafa komai akai ba da wani zazzafan French kiss.
Bakinsa ya
zare yana sauke numfashi,idanunshi akan fuskarta,yana jin yadda fatarta dama
kayam jikinta suke fidda wani daddadan qamshin turaren kabbasa. Idan baiyi
kuskure ba har gashinta data harshi baje saman kafadarta qamshin yake fiddawa.
"Those sweet lips sabrrrr....." Ya fada yana
zagaye yatsansa akan shape na lips din nata,yana jin wani shauqi yana fusgarsa.
Murmushi ta saki tana dan kauda kanta tanason ta karbi wayoyin hannunsa da wata
'yar kyakkyawar briefcase dinsa. Hannunsa ya sanya ya juyo da fuskarta da
sauri.
"Nooo......my lips missed yours sabrrrr......" Ya
fadi yana sake hade bakinsu guri daya.
Wani yanayi
ya fara saukar musu shi da ita,har qafafunta suka fara rawa ta fara jin ba zasu
iya ci gaba da daukarta. Shi dinma hakanne,don gaba daya jikinsa ya dauki shock
har sai da suka zube saman sofa sannan ya zare bakin nasa.
"Your lips are the ones.....i want to kiss
forever" Ya qarasa fada yana tura hancinsa wuyanta qamshinta yana bugar
dashi.
"Sabrrrr.....so kike ki haukatani da alama ko?" Ya
furta yana Dubanta da juyayyun qwayar idanunsa kaman wanda yasha wani abu.
Fiddo idanu waje tayi tana dubansa,hakan sai ya qara mata bala'in kyau saboda
yadda sukayi wani haske,eye lashes din kuma suka zame musu tamkar wani ado.
"Muffin.....me kuma nayi?.....idan na kasheka kuma na
zauna da wa?" Tayi maganar ne cikin wata irin shagwaba. Hancinta yaja
kafin ya lakuce mata kumatu.
"Fisabillahi zan fadi gaskiyata.....wannan qamshin
lallai idan kina tare dashi zanfi tape da taya maqale miki......komai kuma zai
iya faruwa ako ina sabrrrrr.......daga ina wannan qamshin?" Ya fada yana
kashe mata ido. Murmushi ne ya subuce mata sosai,harga Allah da farko ta dauki
turaren ne kawai saboda amna tace ta dauka,cikin irin turarukan da akayi musu
ita da huda wanda.ta bakinsa tasan huda sun iso,saidai tana sakawa a burners
dake lungu da saqo na gidan ta gama giving up.
Lumshe
idonta tayi wani farinciki yana saukar mata,ta bude idanun nata ta saukesu akan
kwalbar LAB_LAB da tayi amfani dashi,wanda daga saman kwalbar manyan rubutu ne
b'aro b'aro dake dauke da sunan INCENSE BY KABO DAUGHTER.
(Kunsan ni ma'abociyar son qamshi ce😄,na muku tallan
turarukan matar nan TASTED AND TRUSTED ne,duk irin turaren da kike siya ina
baki shawara ki gwada nata,yayi yayi yayi,zaki kuma bawa wani labari,muddin
kina da dama amma baki siya ba ina me tabbatar miki kin loser😂😂,confirmed🙌🏽🙌🏽,ba
kuma bala'in tsada gareta ba.....sai sirrin sanin kan turaren,nima dai 'yar
gidan malam shehu ce bare ace na manya muke using ahto😂😂,ki
gwada hajjaju zaki godemin,don tabbas idan me tsoron Allah ce ke kikayi
kabbasarta kika saka humra ko lab lab dinta ba zaki iya fita unguwa ba saboda
fitinannen qamshi suke bayarwa,ki gwada ki godemin +234 803 211 9803).
"Saboda kai ne
muffin......saboda kai ne". Idonsa ya lumshe yana sake zuqar qamshin,har
cikin zuciyarsa yake sauka,wani nutsuwa qamshin yake bashi,kamar wadda aka
tsoma a bahon turare.
"Kiyimin rai please sabrrr" Ya fadi yana sake cusa
kanta tsakanin dukiyar fulaninta.
"Name?" Ta tambaya tana murmushi.
"Don Allah kada ki bari wani yaji wannan qamshin idan
bani ba". Ya qarasa maganar yana dago kansa gami da sanya idanunsa cikin
nata don ta gane har ranshi,da gaske kuma yake maganar.
Tafukan
hannayenta dasu kansu qamshin suke ta saka tana dago kansa sosai. Zuwa yanzun
tuni ta fara fahimtar yanayinsa....da yayi magana ko baiyi ba....idan yayin
daga ina ta fito?.
"Muffin.....kana tunanin zanbar wani hanci ko wani d'a
namijin daban bakai ba ya samu wannan nutsatsen qamshin?.....har abada idan
kace bakaso ko farfajiyar gidan nan qamshin nan ya fita bazai fita ba......a
yanzun hatta da rai ka bani DUNIYATA......Ka bani rai tunda ka kusanto da
makusantana kusa dani......dame ne zan saka maka ni ameenatu?" Ta qarashe
maganar zuciyarta tana karyewa da wani irin rauni.
Idanunshi
cikin nata ya dora hannunsa saman mararta.
"Kin gama sakamin ameenatu.....kin gama sakamin
sabreena.....kin gamamin sakayya duniyata da kika bani iri.....yara uku
fa?,lokaci guda?,a qaramin lokaci har haka?,kika cikamin muradin
zuciyata?......abu daya ne ya rage kiyimin,karki guje ni tsanani ko
dadi.....karki bari tarbiyyar yarana ta zama abun Allah wadai......ki soni irin
son da ba wanda zaki bawa katankwacinsa.....that's all" Ya fada yana dage
hannuwansa sama.
Hannunta
ta saka daga qeyarsa sannan ta hade goshinsu guri daya suna musayar numfashi.
"Ka samu muffin.....ka gama samunsu.....amma zan qara
da addu'a ga Abba......mutumin da yayi sanadin haifamin irin wannan
mijin.....ubangiji ya jiqa kabarinsa ya kuma lullube kabarin nasa da dukkanin
wani nau'i na rahamarsa"
"Allahumma ameen" Ya fadi muryarsa qasan maqoshi
yana sake jin ta masa kima sosai.
"Abinci ko wanka?" Ta tambayeshi ba tare data
dauke goshinta a nasa ba still kuma tana zaune saman cinyarsa.
"Cin abinci sannan kazo kayi wanka yana raunana jiki my
world" Idanu ta fitar tana dubansa bayan ta janye fuskarta.
"Muffin.......da gaske komai naka dabanne,tsarukanka
dabanne kaman yadda naji ana gulmarka......kasan duk wani abu da zai kiyaye
lafiyarka"
"Wait" Yace yana hade ransa da wasa.
"Wake gulmata?,farouq ko?" Dariya sosai ta kubce
mata har tana sake riqeshi don kada ta fadi.
"Komai farouq?,komai farouq?.....BB ya kusa hutawa
dai,nasan fannarshi zata siya masa 'yanci". Murmushi shima yayi yana kama
hannunta suka miqe,shi kansa baisan ya wannan ranar zata kasance ba.....kowa ma
ya shiga uku.
Tsaf ya
janyeta suka shiga wanka kaman yadda rules dinshi yake,har ya fara zame mata
jiki,ya gaya mata sunna ce kuma bazai gaji da rayata ba,don duk wanda yayi koyi
da wani abu cikin abinda manzan Allah yakeyi da zummar koyin yake dashi,to
tabbas yana da ladan koyi dashi.
Cikin wasu
sauqaqan couples pyjamas suka shirya dukkanin farare da adon black wuya da
hannu da qafan wandon da bai qarasa idon sahu ba. Kamar wasu ma'auratan daga
wata qasar,suka sauka qasa tare.
Bayan
kammala cin abincin basu kwanta ba,dukka maganganu ne da shirye shiryen biki
yaketa fama. Itadai tana gefe tana kallon zallar aikin zumunci irin ma fu'ad
din,ta sake tabbatarwa bawai a banza Allah yaa sanya wannan dukiyar a hannunsa
ba(Tabbas idan har Allah ya baka wadata fiye da sauran abokai ko 'yan uwanka,to
ya baka ne don ka taimakesu,wala'alla duka harda arziqinsu ya saka a hannunsu
don ka zama.silar ciresu daga matsi ko matsala,Allah yana sonka da yayi maka
wannan baiwar,don zaka samu lada sanda kake basu ita ta hanyar data dace,don ka
zama kamar wakilin Allah a bayan qasa,idan kuwa ka riqe ka hanasu yana
kallonka.....tabbas! Kuma sai yayi hukunci akai, 'yan uwa dukiyarka kenan
fa.....inaga wanda zai danne haqqin wani?,ina ga wanda zai cinye dukiya ko
gumin wani?,Allah yasa mu dace,ya rabamu da taba abinda ba namu ba ya hayyu ya
qayyumu).
Ganin ta langabe
masa zata yi bacci ya katse maganan da yakeyi da kowa ya dubeta.
"Gate up ameenatu.....naga list na amna.....ke banga
naki ba" Ido ta zaro,cikin muryar soma jin bacci tace
"Muffin.......nawa name?"
"Naki lefan.....naki lefen sabrrrr" Ya fada yana
kama hannunta.
"Banda wanda akayimin hamma?" Ta tambaya tana dan
dariya saboda ta dauka zolaya ne. Kai ya girgiza.
"A yanzun ke din cikakkiyar zabin MUHAMMAD FU'AD JADDA
ce,sabon lefe sabon sadaki daga hannun jadda" Ya fada yana zame hannunsa a
nata. Qasa ya saka hannunsa ya fiddo wata kyakkyawar leda ya zube kayan ciki.
Kyawawan
akwatuna ne har guda shida masu daukan hankali,iya akwatun kawai abun kallo
ne,ba zaka gane kuma kallo ya koma sama ba sai daya bude abun ciki.
Wasu irin
sabbin designs ne na gold masu matuqar daukan hankali. Uku gold ne uku kuma
diamond,wanda ta gane haka ne ta qaramar takardar dake maqale a ciki. Uku ya
ware a ciki ya tura gabanta,ya bude wani jaka qarama dake gefan system dinsa ya
ciro sabbin rafas na dubu d'aya d'aya na dollars a miqe kar dasu ya dora a
sama.
"Wannan shine sabon sadakin ameenatu muhammad
jadda.....idan tana buqatar sama da haka tayi magana......wannan kuma" Sai
ya tura sauran boxes din
"Wannan kuma ladan rainon cikin da za'a yimin....duk da
nasan ban isa na biyasu ba.....duk boxes daya a madadin yaro daya
yake.....shima idan baiyi ba kiyi naming price dinki". Kaf jinin jikinta
taji ya daskare na wucin gadi,uwar dukiyar daya zube mata kawai take.kallo tana
jin zuciyarta tana raurawa,sarqoqi shida masu qololuwar darajar da batasan ya
zata kimanta kudinsu ba?,ga tsabar kudi daya kusa naira million dari da
sittin?. Tsoro ne kawai taji yana shirin kamata,tsoron ta yaya diyar ahmadu
kamarta zata mallaki dukiya dare daya irin wannan?.
Tana
shirin zamewa tayi kneeling a gabansa ya dagota.
"Kul karkimin godiya....karki qorafi,kinfi qarfin komai
da zan baki,don kema kin bani abinda ban isa ni kadai na bawa kaina ba......kin
soni da zuciya daya,kin tsallake duk wani gwaji da nayi miki da zummar gano
dukiyar kikeso ko bata gabanki,a yanzu ba abinda bazan iya sadaukar miki
ba...bare wannan da ba komai bane cikin abinda Allah ya mallakamin ba.....so
komai na dauka na baki kin cancanceshi ne,addu'arki da soyayyarki kadai su nafi
buqata a halin yanzu a rayuwata,Allah ya yimin komai". Qasa tayi da kanta
tana jin hawaye yana sauka a idanunta,sai ya buge da tsokanarta har sai daya
rakata daki,ya tabbatar ta kwanta ya lullubeta da duvet ya tofeta da addu'a.
Sai daya tabbatar bacci ya soma cin qarfinta sannan ya dawo falon ya zauna yaci
gaba da aikinsa.
★Sake juya
rubutaccen katin da yake hannunta tayi wanda akayi da zallar ruwan gold tana
bin kowanne ado na jiki da kallo. Ko ba'a gaya mata ba ta sani gold ne zube a
jikin katin daurin aure takarda maras daraja,ballantana zance yanata yawo anata
yamadidin bikin a lungu da saqo na qasar nigeria,tsakanin maiduguri da kano
kuwa dumin bikin ake ba'a cewa komai. Umar Farouq hamza kibiya zai auri fannah
maisharif babaghana .
Sake buda
katin tayi tana duba schedules din,duka a maiduguri ne za'a yi komai,shima abu
qwaya biyu ne rakkin sai daurin aure rana ta uku,kamu da za'a hada da zaman
ajo,sai bridal shower sai daurin aure,amma ita kanta tasan ace ma ba za'ayi
ta'adin dukiya ba qarya ne.
"Ranar juma'a kenan fannah zata shigo ahalin hamza da
ameenatu?" Ta furta ta daga kai tana duban wanda ke tsaye a kanta. Kai ya
jinjina mata
"Tabbas" Ya bata tabbaci ta cikin baqaqen
gilashinsa. Wani shu'umin murmushi ta aje tana ajiye katin.
"Na samu labarin kai tsaye zasu wuce da ita
gidanta.....sai washegari da ameenatu zata gudanar musu da walima haka
ne?". Kai ya sake gyada mata don bata tabbaci.
Wannan
karon qaramar dariya ta saki.
"Hakan nima yayimin.....amma kuma dan
jahannama.......bazan iya jiran washegarin ba......inaso ranar juma'ar ta zama
rana mafi muni da qunci a wajensu.....inaso ranar ta juye musu daga farinciki
zuwa baqinciki......inaso ta zame musu ranar tonon sililin baqincikinsu".
Kai ya jinjina yanajin hannunsa yana masa qaiqayi.
"Baki da damuwa......zamu ajiye musu tarihin da zai
zame musu abun lissafi da irga har qarshen kafuwar zuri'ar"
"Da kyau" Ta fadi tana cire sarqar gold din dake
wuyanta. Sarqa me tsananin kyau tsada da daraja.
"A auna maka ka saida.....ko nawa ta kama kudin naka
ne......bayan kudaden da zaku cajesu". Wata irin dariyar jin dadi ta qwace
masa bayan ya karbi sarqar,ko a hannunsa kawai nauyinta ya isa ya bashi amsar
kudade ne masu nauyi akan sarqar,baiyi wani mamaki ba ya juya ya fice yana jin
dadin yadda zai rabauta da riba biyu.
_uhmmmmm,zamu gani,waye zai rabauta?,waye zai fadi?,waye
zaiyi farinciki waye kuma zai shiga sasarin baqinciki?_
_Abinda ake gudu fa yana dab da faruwa.....abin boye fa yana
dab da fitowa fili_🥹
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 137
137
Dakin amna ta
tura ta shiga,komai yana kunne bata kashe ba,ita dinma tana saman abun sallah
da hijabinta a jiki,alqur'aninta da wayarta duka na yashe a gefe. Komai anni ta
tattara mata ta ajiye inda ya kamata,kafin ta qarasa inda take ta tsugunna tana
tashinta a hankali.
A firgice
ta tashi,saidai kuma ta farka tana fadin hasbunallahu wani'imal wakil(tana da
tsananin tasiri,ko iya ita kadai kike riqe,indai abu ya sameki saidai tsananin
qaddarar da take rubutacciya da bazata gogu ba).
Kama mata
anni tayi suka sauke tare kafin nutsuwarta ta dawo jikinta.
"Tashi kisha wannan" Anni ta fadi tana jin
tausayinta haka kawai yana tsarga mata. Maamah guba ce.....wata irin guba me
illata jiki da zuciya.....guba me hadarin gaske wadda ya kamata ka tserewa
gwargwadon tseren mutuwa........fuad wani irin ruhi ne me cike da tarin
alkhairi.....tsananin kirki kyautatawa da kuma sanin ya kamata. Haduwar guba
irin wannan da tsakakkakiya rai wani abune dake sanya rai da zuciya cikin
kokwanto me tarin yawa.......maamah lu'ulu'u ce a cikin juji.....kuma tamkar
ayar nan ce ta alqur'ani muraran da take fadin cewa "Allah yana fitar da
rayayye daga matacce suna fitar da matacce daga rayayye . Saidai abu daya data
sani......amna ba zata samu irin soyayyar data dace ba....mariya ba zata taba
marabtar amna a matsayin suruka kuma mata ga yaronta ba.
Koma meye
tayi accepting saboda girman fuad a gurinsu....yafi qarfin kowacce
alfarma,hakanan ya cancanci kowacce alfarma a gurinta,ya kuma isa da amna ta
kowacce fuska.
Rabi tasha
ta sanyata shafe jikinta da rabin sannan ta jawo qofar tabar mata dakin bayan
ta tabbatar ta sakeyin addu'o'i.
★Tunda asuba bata
koma ba,da kanta tayi qoqari da taimakon ma'u suka shirya abinci,saboda ya gaya
mata mali zasuje a ranar,zasu dawo kuma a ranar.
Ta langabe
masa tana nacin ya bari suje tare yace
"Aah my world.....bakiga yanayin da kike ciki
ba?....tafiyan awa goma zuwa da dawowa fa?....ban yarda a wahal da triplets
ba". Hakanan suka lalace wajen sallama da juna,kaman idan ya tafi bazai
dawo ba.
Duk da
farouq cikin shirye shirye yake gadan gadan,don kwanakin biki uku ne kacal suka
rage amma dashi akayi tafiyar. Yayi karamci ta hanyar dauko kawu rufa'i akayi
tafiyan dashi a matsayinsa na wanda yake tamkar mazaunin mahaifinta.
Zumudi da
farinciki da almarar yau zai shiga jirgi ya hana kawu rufa'i sakat,saidai yayi
qoqari qwarai wannan karon ya kama kansa ya nuna surukuta sosai,amma a qasan
ransa banda albarka ba abinda yake sawa sabreen da nemawa iyayenta rahamar
Allah.
"Rufa'i a jirgi,Allah me iko,da haka da haka fa wataran
sai umara ko aikin hajji?" Yayi maganar yana duban Jordan. Dariya farouq
ya saki,don yana daga kujerar baya ya kuma jishi. Shi haka kawai kawun yake
bashi dariya,musamman sanda ake cikin rigimar auren sabreen da fu'ad din.
"Ka fara kiran kanka kawu,hajjin bana da kai za'a yita
in sha Allahu,na baka kujerar hajji.....surukinka kuma fu'ad ya baka ta
umra". Wani farinciki ya sanya kawu miqewa tsaye zumbur yana kallon
farouq.
" Allaha akabar......yaro da gaske kake?,kace na fara
lallabikallahumma labbaik tun yanzu.....haihuwa me rana,sabreena kinyimin ranar
da ko d'iyoyin cikina basuyimin ba.....ubangiji ya kare gabanku da bayanku,yaro
Allah ya yiwa dukiya albarka,amma fa wani hanzari ba gudu ba....." Sai
yayi qasa qasa sosai da muryarsa yana sunkuyowa wajen farouq.
"Kana ganin me jadda zai bani kujerar umara
kuwa?". Duk yadda fu'ad dake tahowa gurin yaso danne dariyarsa ya kasa,sai
daya murmusa.
"Bayan wannan shekarar ma na sake baka guda daya wata
shekarar me zuwa kaida uwar gida". Muryar me jadda ta daki kunnensa. Banda
ya tabbatar da dattakonsa,banda kuma ya tabbatar baya magana biyu tabbas bazai
yarda ba,to amma ya sani cewa shi din kaifi daya ne,idan yace eh eh ne,hakanan
idan yace a'ah to a'ah ne. Sai daya dawo daga suman da yayi na wucin gadi
sannan yahau zuba godiya yana shirin zube masa.
"Karka tsugunna kawo,kun cancanci komai.....girmanku
ne" Fu'ad ya fada,abinda ya sanya mamaki ya sake kashe kawu rufa'i.
"Ko wanne irin halin kirki diyar nan takewa yaron nan
har haka yanzu?,ni na dauka wannan yarinya zatayi sati guda ma kuwa?,nayi
tsammanin in ta dade sati dayan taci gaba da tsalle tsallenta,sai gashi ta bada
mamaki?" Yaketa tadin shi kadai da zuciyarsa.
Sha biyu na
rana agogon mali qarfe daya agogon Nigeria suka sauka a Bamako senou
international airport. Kawu rufa'i yanata rabo idanu duk da ya kame kansa amma
al'ajabin duniya ya isheshi,kasancewar shi din idan yayi nisa lagos yaje sanda
mahaifinsu sabreen yana da rai idan ya aikeshi sari.
Sun isa gidan
momma bahijja,babban gida dake nuna wadatar da masu shi daidai gwargwado wanda
fuad din ya sake inganta rayuwar tasu silar su huda. Wani irin kyauta taban
girma,kulawa ta musamman da dauke dukka wani nauyi da dawainiya nasu.
Wani irin
saukan ban girma suka samu,fuad din tamkar rab'a yake,duk inda ya sauka saiya
jiqa wajen da damshi d alkhairi,don haka kusan kowa murna yake da zuwan nasa.
Bai bari iya su huda da momma bahijja kadai suke cin alkhairinsa ba,aah tun
daga maqota har dangi na nesa na sabreen alkhairinsa ya kai musu.
Awa daya
kacal aka basu huda.....komai na fuad kai tsaye yake yinsa,take ya nema
tattaunawa da momma bahijja da mijin momma din tunda auren zumunci ne,shidinma
kaman kawu yake a wajensu akan idan zai yiwu su biya sadaki a basu huda su wuce
da ita.
"To me ake jira?,me kuma za'a jira?,ga wakilin ango ga
na amarya?" Kawu rufa'i ya fada yana saba babbar rigarsa. Tuntuni
farincikin duniya ya isheshi ta yadda zai sake zama surukin JADDA,wani abu daya
tabbatar baiwa ce Allah yayi musu wadda shi bai taba kawowa ba,yaransa har biyu
cikin ahalin jadda?,tabbas arziqi yana masa sallama a bakin qofa.
Abinda ya
dinga daure masa kai yadda zama yayi dadi tsakanin fu'ad din da sabreen har ya
sake nemewa qaninsa jininsu?.
Ana dab da
kiran sallar azahar a alayin akayi sanarwar akwai daurin aure bayan an idar da
sallar azahar. Abun mamaki saiga mutane an taru ba laifi,don cikin masallacinma
cika akayi,ana idarwa aka daura auren SADDIQ HAMZA KIBIYA da amaryarsa HUDA
AHMAD wanda uban ango kuma uban amarya Alhaji Muhammad jadda ya biya sadakinta
akan 364,400CfA wanda yake daidai da
naira million daya kudin Nigeria. Ya kuma ajiye set na gold masu nauyin babban
gram da kudinsa ya tasamma wasu millions din.
A iya haka
kawai an tashi zancan,duk da hudan ba wani saninta sosai akayi cikin unguwar
ba,amma abun ya zama wani sabon labari.
Kasa cewa
komai huda tayi,yayin da momma ta soma qorafin abun yayi kurkusa da yawa,a dage
a basu koda sati biyu sai yazo ya dauketa,kafin nan sun shirya itama kuma ta
danyi taronta da dangin mamanta da suke nan.
"Kome ake buqata kwana hudu zuwa biyar zaa yishi in sha
Allah,tahowa kuma ayi list na adadin wadanda zasu zo Nigeria rakiyar amarya da
ganin dakin amarya,zan ajiye jirgin da zaiyi jigilarsu" Fu'ad ya fada.
To abune na
maza,su babu ruwansu,shi kansa mijin momma baiyi accepting maganarta ba,hakanan
kawu rufa'i da ya fara sintiri yanaso yaga momma ta kafe ya shiga ya gaya masa
shi uban huda ya lamunce,sai gashi salin alin ta saki ta basu huda din.
Abu daya
ya ragewa huda tashin hankalinta shine,tarkatosu da jadda yayi su duka,kuma sai
taji suna zancan da mijin momma cewa yace lallai shi zaa barwa auta.......nadra
kuma zata zauna hannun saddiq. Nan ma momma tace batasan zance ba,ita take
buqatar riqe yara tana kallonsu kaman 'yar uwarta. Kawu rufa'i fa akazo
wuya,fadi yakeyi
"Ni uban huda da nadra da haneefa na bashi su,duk inda
zai kaisu ya kaisu indai ba lahira bace,banda abun bahijja ke ba abun
alfaharinki bane?,ace wadannan yaran sun tashi qarqashin kulawar me
jadda?,akwai wanda ya samu ko zai samu gata duk ahalinmu da naku kuwa
irinsu?" Sauqin abun zance ne isu isu,ba wani bare a wajen bare kawun yayi
barin mutunci.
"Ni kaina banda na aurar dasu balaraba yace zai riqesu
bashi zanyi da gudun fanfalaqi ma kuwa". Wannan karonma sunci galaba a
kanta,hakanan tabar musu yaran suka tarkata suka wuce Nigeria dasu.
Suna sauka
ya sanya aka kaiwa anni su,ya tabbatar akwai tsarabe tsarabe na mata idan za'a
aurar da yarinya,duk da huda surukuwar anni ce,amma shi a duniya uwa ta gari
qwaya daya ya sani wato anni,don haka yakaita wajenta ya tabbatar zata hada da
amna duka ta sanya ayi abinda ya dace.
Itakam
anni mamakin me jadda ya cikata,komai nasa haka yake shirinsa katsam?,haka
shi.kuma yake daura aure?,indai waliyyai.sun sani ba ruwanshi da batun
mata,indai ma'auratan naso ya gama nashi hukuncin kenan saidai kawai aga
result,tana qare tunanin ta saki murmushi,ita kanta gidan da ya cika da
'yammata sai taji ya qara mata dadi,amma suna kwashe matansu zasu barta a kewa
sai ita kadai?,saita samu kanta da tunanin anya kuwa zata yarda ta bada su
nadra?.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 138
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
138
Zuwa takwas
da rabi na dare ya shigo gida. Tun kafin ya shiga din ya sallami kowa,don
ragowar lokacinsa yana jin cewa na duniyarsa ne.
Yau din
sai take jinta a cikakkiyar matar aure kaman kowacce d'iya mace. Ta shirya
sosai tayi kwalliya da wani farin tattausan lace,fari ne qal babu sirkin komai
a jikinsa. Ya kwanta mata sosai a fatarta,ba makeup a fuskarta,daga powder data
dace da skin dinta,sai wheat lips da ya sanya pink lips dinta suke wani glowing
me daukar hankali.
Sau daya
tak ya kalleta yaji tana son raba masa hankali,sai yake ganin kamar canzata
akayi daga fitarsa zuwa dawowarsa,kaman yadda yaji qamshin gidan gaba daya ya
sauya.
Qugunta ya
kamo,ya kasa cewa komai sai daya sada lips dinsa da nata,ya tsotse lips gloss
din da kyau kaman bata taba shafa komai akai ba da wani zazzafan French kiss.
Bakinsa ya
zare yana sauke numfashi,idanunshi akan fuskarta,yana jin yadda fatarta dama
kayam jikinta suke fidda wani daddadan qamshin turaren kabbasa. Idan baiyi
kuskure ba har gashinta data harshi baje saman kafadarta qamshin yake fiddawa.
"Those sweet lips sabrrrr....." Ya fada yana
zagaye yatsansa akan shape na lips din nata,yana jin wani shauqi yana fusgarsa.
Murmushi ta saki tana dan kauda kanta tanason ta karbi wayoyin hannunsa da wata
'yar kyakkyawar briefcase dinsa. Hannunsa ya sanya ya juyo da fuskarta da
sauri.
"Nooo......my lips missed yours sabrrrr......" Ya
fadi yana sake hade bakinsu guri daya.
Wani yanayi
ya fara saukar musu shi da ita,har qafafunta suka fara rawa ta fara jin ba zasu
iya ci gaba da daukarta. Shi dinma hakanne,don gaba daya jikinsa ya dauki shock
har sai da suka zube saman sofa sannan ya zare bakin nasa.
"Your lips are the ones.....i want to kiss
forever" Ya qarasa fada yana tura hancinsa wuyanta qamshinta yana bugar
dashi.
"Sabrrrr.....so kike ki haukatani da alama ko?" Ya
furta yana Dubanta da juyayyun qwayar idanunsa kaman wanda yasha wani abu.
Fiddo idanu waje tayi tana dubansa,hakan sai ya qara mata bala'in kyau saboda
yadda sukayi wani haske,eye lashes din kuma suka zame musu tamkar wani ado.
"Muffin.....me kuma nayi?.....idan na kasheka kuma na
zauna da wa?" Tayi maganar ne cikin wata irin shagwaba. Hancinta yaja
kafin ya lakuce mata kumatu.
"Fisabillahi zan fadi gaskiyata.....wannan qamshin
lallai idan kina tare dashi zanfi tape da taya maqale miki......komai kuma zai
iya faruwa ako ina sabrrrrr.......daga ina wannan qamshin?" Ya fada yana
kashe mata ido. Murmushi ne ya subuce mata sosai,harga Allah da farko ta dauki
turaren ne kawai saboda amna tace ta dauka,cikin irin turarukan da akayi musu
ita da huda wanda.ta bakinsa tasan huda sun iso,saidai tana sakawa a burners
dake lungu da saqo na gidan ta gama giving up.
Lumshe
idonta tayi wani farinciki yana saukar mata,ta bude idanun nata ta saukesu akan
kwalbar LAB_LAB da tayi amfani dashi,wanda daga saman kwalbar manyan rubutu ne
b'aro b'aro dake dauke da sunan INCENSE BY KABO DAUGHTER.
(Kunsan ni ma'abociyar son qamshi ce😄,na muku tallan
turarukan matar nan TASTED AND TRUSTED ne,duk irin turaren da kike siya ina
baki shawara ki gwada nata,yayi yayi yayi,zaki kuma bawa wani labari,muddin
kina da dama amma baki siya ba ina me tabbatar miki kin loser😂😂,confirmed🙌🏽🙌🏽,ba
kuma bala'in tsada gareta ba.....sai sirrin sanin kan turaren,nima dai 'yar
gidan malam shehu ce bare ace na manya muke using ahto😂😂,ki
gwada hajjaju zaki godemin,don tabbas idan me tsoron Allah ce ke kikayi
kabbasarta kika saka humra ko lab lab dinta ba zaki iya fita unguwa ba saboda
fitinannen qamshi suke bayarwa,ki gwada ki godemin +234 803 211 9803).
"Saboda kai ne
muffin......saboda kai ne". Idonsa ya lumshe yana sake zuqar qamshin,har
cikin zuciyarsa yake sauka,wani nutsuwa qamshin yake bashi,kamar wadda aka
tsoma a bahon turare.
"Kiyimin rai please sabrrr" Ya fadi yana sake cusa
kanta tsakanin dukiyar fulaninta.
"Name?" Ta tambaya tana murmushi.
"Don Allah kada ki bari wani yaji wannan qamshin idan
bani ba". Ya qarasa maganar yana dago kansa gami da sanya idanunsa cikin
nata don ta gane har ranshi,da gaske kuma yake maganar.
Tafukan
hannayenta dasu kansu qamshin suke ta saka tana dago kansa sosai. Zuwa yanzun
tuni ta fara fahimtar yanayinsa....da yayi magana ko baiyi ba....idan yayin
daga ina ta fito?.
"Muffin.....kana tunanin zanbar wani hanci ko wani d'a
namijin daban bakai ba ya samu wannan nutsatsen qamshin?.....har abada idan
kace bakaso ko farfajiyar gidan nan qamshin nan ya fita bazai fita ba......a
yanzun hatta da rai ka bani DUNIYATA......Ka bani rai tunda ka kusanto da
makusantana kusa dani......dame ne zan saka maka ni ameenatu?" Ta qarashe
maganar zuciyarta tana karyewa da wani irin rauni.
Idanunshi
cikin nata ya dora hannunsa saman mararta.
"Kin gama sakamin ameenatu.....kin gama sakamin
sabreena.....kin gamamin sakayya duniyata da kika bani iri.....yara uku
fa?,lokaci guda?,a qaramin lokaci har haka?,kika cikamin muradin
zuciyata?......abu daya ne ya rage kiyimin,karki guje ni tsanani ko
dadi.....karki bari tarbiyyar yarana ta zama abun Allah wadai......ki soni irin
son da ba wanda zaki bawa katankwacinsa.....that's all" Ya fada yana dage
hannuwansa sama.
Hannunta
ta saka daga qeyarsa sannan ta hade goshinsu guri daya suna musayar numfashi.
"Ka samu muffin.....ka gama samunsu.....amma zan qara
da addu'a ga Abba......mutumin da yayi sanadin haifamin irin wannan
mijin.....ubangiji ya jiqa kabarinsa ya kuma lullube kabarin nasa da dukkanin
wani nau'i na rahamarsa"
"Allahumma ameen" Ya fadi muryarsa qasan maqoshi
yana sake jin ta masa kima sosai.
"Abinci ko wanka?" Ta tambayeshi ba tare data
dauke goshinta a nasa ba still kuma tana zaune saman cinyarsa.
"Cin abinci sannan kazo kayi wanka yana raunana jiki my
world" Idanu ta fitar tana dubansa bayan ta janye fuskarta.
"Muffin.......da gaske komai naka dabanne,tsarukanka
dabanne kaman yadda naji ana gulmarka......kasan duk wani abu da zai kiyaye
lafiyarka"
"Wait" Yace yana hade ransa da wasa.
"Wake gulmata?,farouq ko?" Dariya sosai ta kubce
mata har tana sake riqeshi don kada ta fadi.
"Komai farouq?,komai farouq?.....BB ya kusa hutawa
dai,nasan fannarshi zata siya masa 'yanci". Murmushi shima yayi yana kama
hannunta suka miqe,shi kansa baisan ya wannan ranar zata kasance ba.....kowa ma
ya shiga uku.
Tsaf ya
janyeta suka shiga wanka kaman yadda rules dinshi yake,har ya fara zame mata
jiki,ya gaya mata sunna ce kuma bazai gaji da rayata ba,don duk wanda yayi koyi
da wani abu cikin abinda manzan Allah yakeyi da zummar koyin yake dashi,to
tabbas yana da ladan koyi dashi.
Cikin wasu
sauqaqan couples pyjamas suka shirya dukkanin farare da adon black wuya da
hannu da qafan wandon da bai qarasa idon sahu ba. Kamar wasu ma'auratan daga
wata qasar,suka sauka qasa tare.
Bayan
kammala cin abincin basu kwanta ba,dukka maganganu ne da shirye shiryen biki
yaketa fama. Itadai tana gefe tana kallon zallar aikin zumunci irin ma fu'ad
din,ta sake tabbatarwa bawai a banza Allah yaa sanya wannan dukiyar a hannunsa
ba(Tabbas idan har Allah ya baka wadata fiye da sauran abokai ko 'yan uwanka,to
ya baka ne don ka taimakesu,wala'alla duka harda arziqinsu ya saka a hannunsu
don ka zama.silar ciresu daga matsi ko matsala,Allah yana sonka da yayi maka
wannan baiwar,don zaka samu lada sanda kake basu ita ta hanyar data dace,don ka
zama kamar wakilin Allah a bayan qasa,idan kuwa ka riqe ka hanasu yana
kallonka.....tabbas! Kuma sai yayi hukunci akai, 'yan uwa dukiyarka kenan
fa.....inaga wanda zai danne haqqin wani?,ina ga wanda zai cinye dukiya ko
gumin wani?,Allah yasa mu dace,ya rabamu da taba abinda ba namu ba ya hayyu ya
qayyumu).
Ganin ta langabe
masa zata yi bacci ya katse maganan da yakeyi da kowa ya dubeta.
"Gate up ameenatu.....naga list na amna.....ke banga
naki ba" Ido ta zaro,cikin muryar soma jin bacci tace
"Muffin.......nawa name?"
"Naki lefan.....naki lefen sabrrrr" Ya fada yana
kama hannunta.
"Banda wanda akayimin hamma?" Ta tambaya tana dan
dariya saboda ta dauka zolaya ne. Kai ya girgiza.
"A yanzun ke din cikakkiyar zabin MUHAMMAD FU'AD JADDA
ce,sabon lefe sabon sadaki daga hannun jadda" Ya fada yana zame hannunsa a
nata. Qasa ya saka hannunsa ya fiddo wata kyakkyawar leda ya zube kayan ciki.
Kyawawan
akwatuna ne har guda shida masu daukan hankali,iya akwatun kawai abun kallo
ne,ba zaka gane kuma kallo ya koma sama ba sai daya bude abun ciki.
Wasu irin
sabbin designs ne na gold masu matuqar daukan hankali. Uku gold ne uku kuma
diamond,wanda ta gane haka ne ta qaramar takardar dake maqale a ciki. Uku ya
ware a ciki ya tura gabanta,ya bude wani jaka qarama dake gefan system dinsa ya
ciro sabbin rafas na dubu d'aya d'aya na dollars a miqe kar dasu ya dora a
sama.
"Wannan shine sabon sadakin ameenatu muhammad
jadda.....idan tana buqatar sama da haka tayi magana......wannan kuma" Sai
ya tura sauran boxes din
"Wannan kuma ladan rainon cikin da za'a yimin....duk da
nasan ban isa na biyasu ba.....duk boxes daya a madadin yaro daya
yake.....shima idan baiyi ba kiyi naming price dinki". Kaf jinin jikinta
taji ya daskare na wucin gadi,uwar dukiyar daya zube mata kawai take.kallo tana
jin zuciyarta tana raurawa,sarqoqi shida masu qololuwar darajar da batasan ya
zata kimanta kudinsu ba?,ga tsabar kudi daya kusa naira million dari da
sittin?. Tsoro ne kawai taji yana shirin kamata,tsoron ta yaya diyar ahmadu
kamarta zata mallaki dukiya dare daya irin wannan?.
Tana
shirin zamewa tayi kneeling a gabansa ya dagota.
"Kul karkimin godiya....karki qorafi,kinfi qarfin komai
da zan baki,don kema kin bani abinda ban isa ni kadai na bawa kaina ba......kin
soni da zuciya daya,kin tsallake duk wani gwaji da nayi miki da zummar gano
dukiyar kikeso ko bata gabanki,a yanzu ba abinda bazan iya sadaukar miki
ba...bare wannan da ba komai bane cikin abinda Allah ya mallakamin ba.....so
komai na dauka na baki kin cancanceshi ne,addu'arki da soyayyarki kadai su nafi
buqata a halin yanzu a rayuwata,Allah ya yimin komai". Qasa tayi da kanta
tana jin hawaye yana sauka a idanunta,sai ya buge da tsokanarta har sai daya
rakata daki,ya tabbatar ta kwanta ya lullubeta da duvet ya tofeta da addu'a.
Sai daya tabbatar bacci ya soma cin qarfinta sannan ya dawo falon ya zauna yaci
gaba da aikinsa.
★Sake juya
rubutaccen katin da yake hannunta tayi wanda akayi da zallar ruwan gold tana
bin kowanne ado na jiki da kallo. Ko ba'a gaya mata ba ta sani gold ne zube a
jikin katin daurin aure takarda maras daraja,ballantana zance yanata yawo anata
yamadidin bikin a lungu da saqo na qasar nigeria,tsakanin maiduguri da kano
kuwa dumin bikin ake ba'a cewa komai. Umar Farouq hamza kibiya zai auri fannah
maisharif babaghana .
Sake buda
katin tayi tana duba schedules din,duka a maiduguri ne za'a yi komai,shima abu
qwaya biyu ne rakkin sai daurin aure rana ta uku,kamu da za'a hada da zaman
ajo,sai bridal shower sai daurin aure,amma ita kanta tasan ace ma ba za'ayi
ta'adin dukiya ba qarya ne.
"Ranar juma'a kenan fannah zata shigo ahalin hamza da
ameenatu?" Ta furta ta daga kai tana duban wanda ke tsaye a kanta. Kai ya
jinjina mata
"Tabbas" Ya bata tabbaci ta cikin baqaqen
gilashinsa. Wani shu'umin murmushi ta aje tana ajiye katin.
"Na samu labarin kai tsaye zasu wuce da ita
gidanta.....sai washegari da ameenatu zata gudanar musu da walima haka
ne?". Kai ya sake gyada mata don bata tabbaci.
Wannan
karon qaramar dariya ta saki.
"Hakan nima yayimin.....amma kuma dan
jahannama.......bazan iya jiran washegarin ba......inaso ranar juma'ar ta zama
rana mafi muni da qunci a wajensu.....inaso ranar ta juye musu daga farinciki
zuwa baqinciki......inaso ta zame musu ranar tonon sililin baqincikinsu".
Kai ya jinjina yanajin hannunsa yana masa qaiqayi.
"Baki da damuwa......zamu ajiye musu tarihin da zai
zame musu abun lissafi da irga har qarshen kafuwar zuri'ar"
"Da kyau" Ta fadi tana cire sarqar gold din dake
wuyanta. Sarqa me tsananin kyau tsada da daraja.
"A auna maka ka saida.....ko nawa ta kama kudin naka
ne......bayan kudaden da zaku cajesu". Wata irin dariyar jin dadi ta qwace
masa bayan ya karbi sarqar,ko a hannunsa kawai nauyinta ya isa ya bashi amsar
kudade ne masu nauyi akan sarqar,baiyi wani mamaki ba ya juya ya fice yana jin
dadin yadda zai rabauta da riba biyu.
_uhmmmmm,zamu gani,waye zai rabauta?,waye zai fadi?,waye
zaiyi farinciki waye kuma zai shiga sasarin baqinciki?_
_Abinda ake gudu fa yana dab da faruwa.....abin boye fa yana
dab da fitowa fili_🥹
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 139
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
139
*_WEDDING
VIBES_*
*_KANO & MAIDUGURI_*
Idan aka
ambaci umar farouq kibiya,wani mutum ne me wasu irin halaye nagartattu,iya
mu'amala da mutane da kuma Tarin abokai,duk da kusan kowanne aboki da zai shigo
rayuwarsa yana qoqarin tantance cancantar wanzuwarka a rayuwarsa.
Bikin ya
karade kafofin sadarwa masu yawa,ya kuma shiga jerin sahun bukunkunan da kowa
yayi amanna zai bada wani irin salo me qayatarwa,duk da ba wani abu me yawa aka
tsara za'ayi ba.
Tun lahadi
ya yiwa maiduguri tsinke ta jirgin jadda wings,yayin da ya saukewa fuad saboda
yanayin hannunsa. Su ahsan da sauran abokansu sune suka zame masa groomsmen.
Duka komai
dasa hannun fuad aka kammalashi da wani irin dattako da nuna tsantsar 'yan
uwantaka,sunyi fuad din zai taho ranar zaman ajo sai kuma da farouq ya sanya ya
masa alqawarin zaije har gurin,saboda yasan halinsa,tun asali dama shi bameson
ire iren wadannan abubuwan bane.
★A nutse suke takowa zuwa farfajiyan da motocin da zasu masa
rakiya zuwa airport daga can su zarce Maiduguri. Hannunsa sarqafe cikin
nata,kwana biyu din da zaiyi sai yake jin kamar wanda zaiyi shekara biyu ne.
Ita kanta duk sai takejin kamar ta sake masa kuka,kewarsa takeji tun bai tafi
ya barta ba,duk da takan ji dama dama idan ta tuna in ya tafin itama zata wuce
gidan anni don shirye shiryen biki,wanda idan an dauko fannah an kawota nan
din,walima za'ayi gagaruma guda daya da anni ta shirya,zasuyi yini randa za'a
sauka da fannah,walimar kuma washegari ce,to amma ita din a yanzun ta zama
kamar auntyn amaren gaba daya da angwayen. Tuna su huda na tare da itan yana
rage mata wani kadaicin,duk kuwa da cewa ba wanda ya isa ya cike wannan gurbin
nasa.
Baiko kulaa
ko damu da mutane a wajen ba,ya ajiye mata tattausan kiss a goshinta bayan duka
sallamar da akayi a ciki.
"Saina dawo?,ki kulamin da kanki sosai,if possible ki
dawo gida ki kwana,banaso na tuna cewa baki dakinki kinji please" Kai
kawai ta iya gyada masa,don idan tace zatayi magana kuka ne zai qwace mata.
Har ya
fara takawa zuwa motar da Jordan ya bude masa ta jawo yatunsa,ya dawo da baya
yana kallonta da narkakkun idanunsa.
"Yadai?.....ko na fasa ne?" Kai ta maqale sannan
ta girgizashi.
"BB ne fa......idan banda BB dinne ba wanda zan bawa
aronka....."
"Nima banda ina kishin a kallemin ke.....banda ina
tattalin 'ya'yana ba abinda zai sanya na tafi na barki"
"To amma...." Ta fada tana turo baki ba tare data
qarasa magana ba. Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana kallonta,ya mata alama
daka akan ta fada.
"Banason ka kalli kowacce mace please...." Tayi
maganan tana juya masa baya alamun kunyarsa takeji. Qaramar dariya ya qwace
masa,yasa hannu.ya juyo da ita yana fadin.
"Say it mana.....Louder please!,with all your
might" Ya furta yana mata sassauqar runguma ta baya,yadda ta nuna kishin
na faranta masa kaman farincikin na neman masa yawa.
Kai tsaye
ta juyo ganin abun na masa dadi,ta saka idonta cikin nasan tana dubansa.
"Your eyes belong to me,don't look at any other women
please,na maka alqawari a karan kaina.....my gaze is fixed on you alone,bana
ganin kowai sai jadda na" Ta fada tana rungume Hannayensa". Sulalewa
yayi sai gashi saman gwiwarsa a gabanta,abinda ya sanyata zaro ido ta fara
kallon mutanen dake wajen.
Dukka
guards nashi sun juya bayansu,ba wani guda daya da yake kallonsu,saima kaman
katanga da sukayi musu ta yadda ba wani a farfajiyan gidan da zai ganin ainihin
abinda ke faruwa.
"Karki damu,My men are extremely competent" Yana
kaiwa nan ya kamo yatsuntsa masu kyau da taushi. Kafin yace komai wayarsa ta
dauki tsuwwa,yadan yamutsa fuska yana cirota a aljihunsa. CP ahmad nuhu ne,don
haka ya daga kai tsaye ya sanya a kunnensa.
Cikin ban
girma suka gaisa,kafin ya soma gabatar masa da bayanai.
"Sir dukkaninsu a yanzu sunyi taushin da kowanne
bayanai muke buqatar tatsa daga wajensu zamu sameshi in sha Allah,don yanzu
haka bibo da zuwaira ma mun samu dukkanin bayanan da muke da buqata,ban sani ba
ko zamu iya aike maka ta email?"
"Good job sir.....thank you,basai ka turo ba,don yanzu
haka mun fara hidimar bikin dan uwana.....but zuwa Monday dukka zamu zauna
dasu,akwai yiwuwar wanda za'a sallama a cikinsu.....thank you sir"
"Okay sir.....in sha Allah" Cp din ya fada suna
sallama cikin farinciki da mutuntawar yadda dukiyar FU'AD din bata sanya yana
musu kallon na qasa dashi ba. Ya basu
dukkan wani girmamawa da dama na gudanar da ayyukansu.
Kashe wayar
yayi duka ya sanya a aljihu don kada wani ya katse masa shauqinsa,sannna ya
sake riqo tausasan tafin hannunta da har yanzu yake jiyo wannan sassanyan
qamshin na jiya (incense by kabo daughter+234 803 211 9803 Da gaske turarenta
kwana yake a jiki,kama gida kuma da wuri yake,khumrorinta dukka na dabanne bare
akai ga turarenta).
"Ni muhammad FU'AD jadda,an halicci ruhi Zuciyata dama
gangar jikina gaba daya saboda ameenatu sabreen........har abada gangar jikina
da zuciyata sun haramta ga wata diya mace ba ita ba......mata gaba dayansu
wallahi wallahi kallon maza nake musu 'yan uwana,daga kanki an gama haifar wata
diya mace har abada,amana daya ce......kuma kin sameta,bana canza magana,bana
sauya alqawari" . Tasha jin ana cewa maza basu da magana daya.....ta gani
da idanunta yadda maza suke zama wasu ababen tsoro game da mata,amma a yanzun
saita samu kanta da amanna da maganganunsa.
Tana
tsaye har dukka motocinsu suka bar harabar gidan,sai ta juya ta koma a hankali
tana jin kaman ita kadai ce ta rage a duniya. Bata dauki lokaci ba itama sai
kawai ta shirya,ta yiwa securities din daya bar mata magana suka shirya motoci
ta fice zuwa gidan anni.
Ta samu
amare sunata wani glowing kaman wadanda anni ta dauka ta jefa cikin engine aka
sauyo mata da wasu,duk da dama daga amna har huda kyan fata garesu.
"Aah,mrs saddiq and musaddiq" Sabreen ta fada
cikin salon tsokana. Abun mamaki wai yau ita suke kunya,kowacce sai ta sadda
kai,saidai kuma yanayin amna data gani kaman ba yadda ta saba ganinta ba.
Duk da
akwai surukuta sosai tsakaninta da anni,amma ta dan sake wasu abubuwan da ba
zasu zamto zaqewa ba ta shiga anyi da ita. Lefen data gani wajen anni akwati
ashirin da hudu na huda ashirin da hudu na amna,guda biyu arba'in da takwas
kenan. Daki daban anni ta saka ta shiga tana nuna mata wasu designers akwatunan
guda sha biyu samfurin shekara mai zuwa,wanda akayi lunching nasu a dubai cikin
satinnan. Ita tsoro ne ma ya kamata da anni take gaya mata wai nata ne,ya ilahi
ina zatakai wadannan?,kada ya jawo mata baki fa na jama'a.
A daren
suna video call take jeranta masa kalaman godiya,kalaman da suka sake kashe
masa jiki da zuciyarsa,yaji kaman zai narke saman sofa din da yake kwance akai.
"Sabrrrr" Ya kirayeta,wanda kiran kawai ya gaya
mata yanayin da yake ciki.
"Anya ba gobe zan taho ba?,anya duniyata?". Dariya
ta qyalqyale masa dashi tana tsokanarsa.
"So kake BB da fannah suce nice na hanaka?,kayi haquri
please,awa arba'in da takwas ne kawai".
"Allah ka bani juriya" Ya fada yan lumshe ido,yana
jin wata kewarta tako ina,tattausan skin dinta me qamshi laushi da santsi.
★Randa FU'AD ya
sauka ranar fanna tayi bridal dinta,baije ba farouq ma bai matsa ba tunda yasan
bame son zuwan bane. A rana ta biyu ne akayi zaman ajo,wanda a wannan zaman
kudi sukayi rana.....dukiya tayi kuka da idanunta,ya nunawa BB dinsa qauna irin
wadda ta sanya farouq tara hawaye sosai a Idanunshi.
"Karka yadda kayi mana kuka gaban mata da tarin
mutane,idan kayi hakan bamu yafe maka ba.....wannan kukan ka riqeshi sai sanda
kuka kebe......idan ba haka ba za'a dauka lusari ta aura" Ya fada kadan a
kunnen farouq bayan ya gama zazzage pound cikin abinda aka ajiye saboda zuba
ajo din,don yana gama zubawa aka dauke abun,ya riga ya cika sai wani aka sanya.
Tofa......nan idanu dama hankulan 'yammata dama zaurawa masu lokaci yayo
kan FU'AD din,taron mayu bawai na maita ba......mayun mata.....ma'abota son
kyakkyawan namiji me abun hannunsa hankulansu ya tashi. Kowacce isassace me aji
tana jin takai,don me qaramin class ma baya suka dinga ja suna rufawa kansu
asiri,saboda sunsan kalar zaren ba kalar yadin bane......saidai su kansu
isassun sai rab'e rab'e,an rasa zaqaqura me qarfin halin tunkarar me jadda
din.....kwarjini yanata aikinsa.
Mota ya
koma yayi zamanshi suns hira da duniyarsa,video call kaman ko yaushe,ta daga
masa hannuwanta da sukasha wani irin jan lalle,tun daga tafin hannun har zuwa
bayan hannun nata.
"Ya salam" Ya fada yana jin wani abu ya harba a
jikinsa.
"Nawa me qunshin nan takeso a bata?".
"Anni ta biya mana ni dasu amna.....beside ma ai ka ban
kudin da zai isheni kalar kowacce hidima".
"No....kudin dana baki ban bakishi bane don kiwa kanki
komai ba,na baki shine don ki wata hidimar daban,zan saka miki a dollar account
dinki,saiki cire".
"Allah yabarmin kai jadda na.....Allah yajamin da ranka
uban 'ya'yana" Ta fada tana jin kanta yana fasuwa,bada komai ba kuma,da
zallar kulawa.....da kalar mijin kuma data samu.
Sanda
suka koma guest in dinsu farouq shine qarshen shigowa,bai kuma tashi shigowa ba
sai daya na dare. A sannan FU'AD yana zaune saman abun sallah yana
addu'o'insa,wanda duka ta neman dacewa da alkhairai ce duniya da lahira shida
'yan uwansa dama dukkan wani masoyinsu(harda ku fans na DUNIYATA😄🫶🏽).
Ido suka
hada FU'AD ya janye idanunsa yana hade rai.
"Wanne irin abune wannan?,zaka ajiye.mutane kuma ka
tafi,baka tashi shigowa ba sai tsakiyan dare kaman wani barawo?" Wani dariya sosai Farooq ya saki yana qoqarin
cire babbar rigar jikinsa.
"So sorry dude.....kasan abinka dame iyali kuma farin
shiga.....inacan ina lallashinta wai yatsunta sun gaji......ga tafiya kano gobe
donma flight ne.....".
" A gidan ubanwa ta zama iyalin naka?" Ya fada
adan fusace,don ya kira sabreen yaso suyi hirar dare bai sameta ba.
"Ka rabo mutane da iyalinsu kuma kazo ka
ajiyesu?". Ido farouq ya fiddo,yanason fashewa da dariya amma ya danne
"Ikon Allah....to ni me zan muku idan nazo din?,qarqari
muyi hira fa?,kuma yanzu tsakani da Allah saboda rashin imani wanda keda
sabuwar amarya ai abun a masa uzuri ne ko?.....to kuma ma naga wancan lokacin
naka daurin auren.....qasarma ka bari kaqi dawowa ka barni da amaryar da abokan
gaba daya.....wannan rashin adalci ne dason kai dude".
"Farouq....gori zaka yimin?....gate out please ka barni
naji da damuwana" Wannan karon duk
yadda yaso boye dariyar ya kasa,sai kawai ya saki abarsa yana nufar toilet.
"Bani nakar zomon ba.....ratayar ma ba'a bani
ba.....iyali me dadi.....ashe haka lamarin yake dama" Ya qarasa fada yana
shigewa gami da turo qofar.
Qwafa fuad
ya saki,sai kuma murmushi ya qwace masa. To meye ma laifin farouq a ciki?,ita
kanta sabreen din bata da laifi tunda tace masa zata aje wayarta dama,kawai dai
iya shegensa ne ya motsa,da alama kuma ramuwa yakeson yayi masa.
*_ALQAWARIN ALLAH baya tashi_*
"An daura
auren umarul farouq hamza kibiya,da fannah maisharif babaghana......jama'a kun
shaida?". Sautin daya sanya fu'ad sakin tattausan murmushi yana furta.
"Alhamdulillah......alhamdulillah"
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 140
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
140
Daga nan
inda yake yana hangen sadakin fannah dake bada tabbacin ta zama ta farouq dinsa
halak malak......hakanan yana iya hango farouq dake tsakiyar abokansa wanda
shigarsa bata da maraba data jikin fu'ad din,sak da sak kaman yadda sukayi a
bikin fu'ad din.
Lafiyayyen walima aka gudanar a gidan gwamnatin jihar borno bayan
kammala daurin auren da tarin abokansu masu jini a jika,wanda kowannensu wani
ne shi ta fannin ilimi da abun duniya.
Ana gamawa
fu'ad ya wuce masauki yabar farouq da tarin abokanshi,don shi bazai iyama
wannan iya shegen nasu ba,sun sanyashi a gaba sunata abubuwansu daya tabbatar
sai yayi trending a social media. Tunda akayi hotuna wajen reception din yayo
gaba,don akwai shirin da yakeso yayi.
Ruwa ya
fara watsawa ya fidda wayarsa,kai tsaye ya kira duniyarsa. Daidai lokacin tana
zaune suna kallon reception da daurin auren da ko awa guda ba'ayi da yinsu ba
amma har an warwatsa a media.
Kishin
fu'ad ke taso mata sosai saboda ganin tarin comment din yammata a kansa. Shi
kadai amma ya fita daban a cikinsu,komai nasa daban yake,wani irin kwarjini me
hade da nutsuwa da suka qarawa fuskarsa kyau da kuma kamala.
_"Lallai baaba ma da babansa fa.....duk kyan azurfa
bata kai ya gold ba.....the jadda.....guy dinnan daban yake fa🔥❤️🔥"_
comment din wata daya gilma kenan daya sanya zuciyar sabreen quntata,ta kuma
ture screen din daga fuskarta tana jan wani qaramin tsaki,can qasan ranta kuma
tana mita.
"Bansan me yake damun 'yammatan yanzu ba,kamar
mayunwata suke akan maza.....idan suka saka namiji a gaba baji ba gani?,ba
kunya ba aji ba kamun kai?" Daga huda har amna sun fahimci me takewa
qunquni,sai suka qunshe dariyarsu saboda zuwa yanzun suma suna jin tasu
soyayyar da angwayensu har cikin jininsu.
Kayanta
take hadawa dama,saboda tanason wucewa gida ne kafin su qaraso,tanaso ta kimtsa
ta tarbeshi da kyau,idan yaso gobe sai ta dawo gidan annin. Kiran wayarsa ya
sanya ta ajiye duk abinda takeyi,ta kuma daga kiran tana samun wajen zama.
"A ina kake?" Tambayar data fara masa kenan wadda
ta bashi mamaki.
"Na dawo guest house masauki.......me ya faru?"
Wata sassanyan ajiyar zuciya ta saki,tana jin dadi daya dawo din,at least ya
tsira daga kallace mata shi da wadancan mayunwatan 'yammatan sukeyi.
"People are commenting about you everywhere
You're all over social media muffin" Ta fada da wata
irin narkakkiyar shagwaba.
"What?" Ya fadi dariya nason qwace masa.
"Like nine angon?" Ya sake tambayarta.
"Am serous muffin" Ta sake fadi tana narke masa.
"Am all yours......am yours forever my World" Ya
fadi da wani irin calmness daya bawa zuciyarta nutsuwa. Ajiyar zuciya ta sauke
sannan ta soma gaidashi.
"Ya taron?"
"Alhmdlh.....but babu dadi coz bakya kusa dani".
"Nan da awanni kadan zamu kasance tare in sha
Allah" Ta fada tana bashi confidence.
"In sha Allah" Shima ya maimaita. Lafiyan yaranshi
shine next abinda ya qara tambaya,tayi murmushi tana dora hannunta saman
mararta data fara tasawa tana bashi amsa.
"They're fine.....suna gaida abbunsu.....sunyi missing
nasa"
"Me too my world.....akwai kyakkyawar gaisuwa
tsakaninmu idan na dawo.....so get ready,be at home as soon as possible"
"Yanzun nake shiri in sha Allah"
"But.....karkice zaki fita da mota daya....ki jira su
abdulgafar zasu kaiki har gida.....and nace su qara yawan security na
gidan". Ya fada da serious murya.
"I hope komai lafiya ko?" Kai ya jinjina,kawai
yana jin wani abu daban a jikinsa.
"Lafiya.....in sha Allah" Ya fada yana son
tabbatarwa da kansa haka.
Cikin nuna
tsananin kewa da qaunar juna sukayi sallama shida ita,kai tsaye kuma ya kira
abdulgafar.
"Zamu qaraso gurin qarfe biyar......get ready please,a
qara yawan security a airport da gida na harda gidan anni......har gidan
farouq.....if possible inaso kowa cikin ku ya zama ankare da kowanne
parts".
"As you wish sir" Ya fada cikin girmamawa.
"Ku rakata gida safely abdulgafar......bazan iya jurewa
ba if something happen".
"Bazai faru ba sir in sha Allah"
"Good abdulgafar" Ya fada yana yanke kiran.
Iska me
zafi ya furzar daga bakinsa yana dan wani gajeram tunani da shi kansa baisan na
meye ba,sake daukan wayarsa yayi ya tura rubutaccen saqo ga duk wani guard da
suke tare dashi a halin yanzu haka a maiduguri,sannan ya sauka yana laluben
wayar farouq don jin yadda zasu shirya tahowa kano kada lokacin tashinsu ya
fita.
★ Daga
samanta tana iya hangen yadda duk wani shige da fice yake gudana cikin gidan
hamza kibiya. Wani ajiyayyen qullutun baqinciki ne yake tsaye a wuyanta,shi bai
fita ba shi bai sauka ba. Idan akace mata a baya nasararta zatazo da irin
wannan salon tsaf zata qaryata......a irin wannan yanayin zata iya cewa bikin
d'anta akeyi.......amma koshi yaron nata bata samu martabar ganinsa ba bare ta
shiga lamarin bikin,balle kuma ta samu girma da daraja irin na kowacce uwa.
Agogo ta
kalla,tana jin ta matsu ta kuma qagu komai ya faru,tana jin a ranta afkuwar
komai din shine zai bawa abinda ya tsaya mata a wuyan damar fadawa.
Knocking
akayi sannan aka turo qofar dakin. Bata damu ta waiwaya kota tambayi waye ba
har zuwa sanda ta fara magana.
"Maamah ga abincinki fa,tun na safe bakici ba.....na
rana ma haka,ga na dare a hanya,kuma likita yace ki dinga kula da abinci ko don
yanayin ciwon...."
"Ciwon ubanki?.....nace ciwon ubanki?". Ta fadi
tana katse laila da dukka tashin hankalinta ya tattaru ga ganin alamun maamah
din tana cikin damuwa,tashin hankalin da takeji tana jin yafi wanda maamah
dimma ke ciki.
"Maamah kiyi a hankali ki daina fushinnan ko don
lafiyark......".
"Waini sa'arki ce?,to kiji na gaya miki na rantse da
Allah kika qara Dangantani da wani cutar hawan jini saikin gwammace uwarki
hajja bata haifoki na......idanma qullawa kukayi don ku cuceni ku kasheni
saboda ba idon 'ya'yana ko to?,to kunyi qarya kun kwana da yunwa,ni mariya
warki ce daidai qugun kowa.....ni mariya kuma ni kad'aice gayya......fita kiban
guri" Ta dakawa laila tsawa tsawar da har saidata zabura.
"Allah ya baki haquri" Ta fada ta juya tana fita a
dakin kaman zata kifa.
Fitar laila
sai ya zama kamar ta fita da iskar da take shaqa ne,take taji iska tana mata
kadan,wuyanta ya soma riqewa iskar bata samun daman isa ga hunhunta. A daddafe
ta samu waje ta zauna tana qara gudun fanka da Ac din dakin,wani irin haki yana
sarqeta. Likitan ya gaya mata,kada ta yarda ta fadi muddin irin hakan ya sameta
tana a tsaye,idan ba haka ba komai zai iya faruwa.
Ta kusa
mintuna talatin a haka kafin taji a hankali numfashinta yana daidaita har ya
koma normal. Wayarta ta jawo,ta kira number wayar da take sanya ran shigowar
kiranta tun dazu.
"Baki da damuwa.....muna ankare da kowa da kuma
komai.....ki jira jin sakamako daga yanzu zuwa gobe da safe"..
"Godiya nake" Ta fadi tana ajiye wayar tana kuma
sake jin relief sosai a ranta.
Cikin
wani irin mugun matakan tsaro jirginsu ya sauka,yayin da baqaqen motocin dake
dauke da tambarin JADDA kimanin ashirin sukayi convoy cikin wani irin tsari me
daukan hankali da kuma matakan tsaro sosai bisa umarnin fu'ad.
Lafiya
lau suka qaraso unguwar,suka kuma jera kansu zuwa kyakkyawa kuma makadediyar
harabar mansion House din alhj hamza kibiya.
Duk wani
dake da jibi da ahalin alhj hamza kibiyan yayi tattaki ya fito daga cikin
gidan,yayi tsaye a farfajiyar saboda girmamawa ga fannah,wadda aka fito da ita
nannade cikin wata lafiyayyar Cotton lafaya butter colour da ratsin maroon.
Yana
daga cikin motar amma yana iya ganin komai,yabi kowa da ido da yadda abun ke
kasancewa,sai yaji wani abu yana taso masa,don haka ya maida idanunsa ya
lumshe.
Lallai
babu wani babban arziqi a duniya irin uwa ta gari......babu wani babban jin
dadin rayuwa irin samun uwa ta gari.......alhmdlh yana godiya ga Allah a bisa
dukkan ni'imomin da yayi masa,kuma ya karba cewa tasa qaddarar tana kan
MAHAIFIYARSA tasa jarrabawar tana kan UWA da Allah ya bashi.
Amna
dake nade cikin tata lafayar sai wani irin farinciki taji yana lullubeta,tana
jin kamar suna dab da gina wani babban ahali ne,yau BB farouq dinta.....ya
saddik,ya musaddiq da hammanta dukkaninsu yana da matar aure,wadannan matan
kuma kowacce ana sanya ran zata basu baby,babies din da zasu taru su zame musu
wata tawaga kuma family na musamman.
Kasa jira
tayi a qaraso da fannah,saita taka da dan hanzarinta tana cimmata ta riqe
hannunta,abinda yasa matar dake riqe da fannah din sakin hannunta taja
baya,wannan ya bawa amna daman magana da ita qasa qasa.
"Welcome to alhj hamza family,welcome to jadda family
adda fannah......bansan ya kuke cewa adda da kanuri ba.....anyway muna miki
maraba".
"Na gode" Siririyar muryar fannah ta fita wanda ta
tabbatar ita daya ta jita.
Cikin
girma da martaba dangin anni dana abba suka amshi fannah aka qarasa ciki da
ita,bayan anyi addu'a an kuma bawa su anni amanarta,sai annin ta sanya aka ware
daki daban aka bawa fannah din ta huta suci abinci sannan sai a wuce da ita
gidanta,hakanan danginta suma aka basu wani dakin daban.
Sai data
tabbatar babu kowa a dakin sannan ta yaye lafayar dake kanta. Amna da huda ke
dakin,hudar da sam ta kasa sakewa,ta hana kowa ma ya ganta throughout saboda
surukuta da takeyi da dangin anni.
Musayar
murmushi sukayi,amna ta nuna huda.
"Wannan itace huda.....qanwar adda sabreen,matar ya
saddiq" Lokaci daya huda ta yiwa fannah,ta miqa mata hannu sukayi
musabaha. Ita da amna sai take jinsu karon farko kaman qannenta,don ta tabbatar
ta girme musu,saidai ba wani da yawa bane.
Qaramar
walima akayi cikin gidan,baqi sukaci suka qoshi suka huta,sannan anni ta bawa
fannah kyauta irinta surukuwa kaman yadda ta yiwa sabreen.
*_ME FARUWA!_*
Tun bakwai
da rabi aka soma shirye shiryen qarasawa da fannah gidanta. Musaddiq da saddiq
ne akan komai na game da shirya motocin da za'a dauketa a qarasa da ita ainihin
gidanta dake maqociyar unguwarsu.
Tunda aka
fara jera motocin daga harabar gidan zuwa qofar gidan amna ta kasa zaune ta
kasa tsaye. Tana bala'in son zuwa gidan ya farouq,wannan yana daya daga cikin
mafarkanta tun kafin tasan rayuwa zata juya lokutan aurensu guri guda,tun kafin
ta taba tunanin zata kasance qarqashin igiyar auren yaa musaddiq a wannan
lokacin.
Yadda
kowa ya shirya haka ta shirya,tanason ta tambayi ya musaddiq ko shi ya dauki
mota subi ayarin kai amare,a qalla tana tunanin bazai hanata ba,tunda zai
wahala idan ta shiga nata gidan ya barta fita da wurwuri,don musaddiq din wani
irin tsaro ne dashi tun wancan lokacin ballantana yanzu data zama mallakinsa.
Zaune
tayi tana gwada wayarsa,sai data kirashi a qalla sau hudu sannan ya daga.
"Ya akayi baby doll?" Cikin shagwabar nan tata ta
narkar da kai.
"Besty.......gidan amarya please,don Allah muje"
Idanunsa ya waro waje kaman tana gabansa.
"What?.....aah karmu fara haka dake babe.....zakije
amma bayan munyi wasu watanni" . Kukan shagwaba ta sakar masa wadda ta
qarasa susutashi,da qyar da ban baki ta shawo kansa.
"Amma kinsan anni zatayi fada ko?".
"Karka gaya mata please,nayi alqawari muna zuwa zamu
dawo". Shuru ya danyi,bayan wasu sakanni yace.
"Ban miki alqawari ba gaskiya babe... Kema amaryarce
kaman kowa,kodon kinga ban tada rigima a kaiki yau ba?"
"Am sorry besty....don Allah"
"Nace banyi alqawari ba,but ki jirani idan hali ya yiwu
zan miki magana saiki fito" A haka
suka rabu da musaddiq,duk sai taji ranta ya jagule,tunda taji ya fadi hakan
probability na rashin zuwanta yafi na zuwan nata yawa,saita buga tagumi tana
zaman jiran tsammani,har sanda aka shigo aka fita da fannah alamun tafiya
zasuyi.
Kasa zama
tayi,ta lafe a farfajiyar gidan tana ganin yadda motocin suke tashi suna
ficewa. Ta duba agogo,ta tabbatar tunda har musaddiq yakai wannan lokacin baice
ta fito ba to tayi loosing chance dinta,tabbas bazai kaita ba.
Hawaye
taji ya silmiyo mata,daya daga cikin talalar aure kenan,idan dane anni kawai
zata gayawa ta fice abinta.
Ko a
yanzun ma ji tayi ba zata iya haqura ba,tunda duka motocin gidansu ne zata iya
basaja ta bisu,idan an tashi dawowa da dangin amarya ta biyosu ba lallai a gane
ta fita harta dawo din,don haka ta silale a hankali tabi ta jikin motar dake
fita daga gidan ta saje a jikinta suka fice tare.
Sai
data fita din tahau raba ido,ba wata mota a wajen duka sun dauki hanya wata
nabin wata,caraf idanunta suka sauka kan wata baqa guda daya dake fake a
gefe,sauri take kada musaddiq ya cimmata yace ta koma gida,don haka bata lura
da number ba irin ta gidansu bane kawai ta doshi motar kai tsaye.
Sosai
abun ya musu dadi,ya kuma yi musu sauqi na ganin ta kawo kanta da kanta,sai ya
bude motar kawai yana jiran isowarta,wanda tana isowar ta bude bakinta da
zummar tambaya sai kawai ji tayi luuuu an jata cikin motar an maida qofa an
rufe. A gaggauce ta bude idonta tana son gani ko musaddiq ne yake mata
wasa?,saidai fuskar data gani din a gabanta ba wata alaqa ta kusa ko ta nesa da
imani a tare dashi bare a alaqantashi da sunan musaddiq ma.....kafin kuma ta
sake tantance komai,sun badeta da wani abu da ya sanyata atishawa,cikin qasa da
second biyu ta daina fahimtar komai.
_masu karatu kuyi haquri nayi baqi ne yau din,mu tara gobe
in sha Allah......sai ince kowa ya shirya,ranar da kuke jira ce ta tunkaro mu_
Sonso🫶🏽🥰🥰
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 141
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA
CLOSET........siya ko saidawa,reposting ko sari_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
141
Tsararren
gida ne da akayi masa wani irin qawataccen gini mai dauka hankali. Tun daga qofar gidan zuwa cikin
gidan dole ya burge me kallo saboda yadda komai yake a tsare da wani irin
yanayi me jan hankali. Komai favourite na farouq aka saka,fu'ad yayi masa ba
zata kaman yadda shima yayi masa.
A hankali
ta rufe turaren data gama fesa masa tana dubansa,yayi masifar kyau cikin wani
lallausan yadin vicuna da aka yiwa riga da wando da wata 'yar sama me kama da
alkyabba. Tsadajjen dinkin hannu da aka shiryashi da zare me daraja.
"Kayi kyau muffin" Sabreen ta fada tana lumshe
idonta gami da budesu akan fuskarsa. Hannunta ya riqo a tausashe yayi kissing
dinta
"Soyayyarki ce ta saka my world.....but bakisan kin
fini kyau ba?" Ido ta zaro waje kana ta saki dariya tana girgiza kai gami
da ja baya
"Zolayata kake muffin.....ta yaya haka zai kasance?,kar
ka tsaida BB hamma......yau ranarsa ce aje a miqawa sister fannah shi"
Murmushi ya subuce masa ya soma zura rufaffun takalmansa tana daga tsaye tana
morewa kallon abinta. Sai ya fito fes kaman wani shaihin malami.
Har bakin
mota ta masa tattaki,bayan ta tabbatar an saka komai a motar daya dace a kaiwa
amarya da angon. A yau kadai data sanya order Youghourt da sauran wasu snacks
daga wajen deeja beerva aka kawosu tsaf.......sai ta dinga jin sha'awar koyon
duka nau'in wadannan abubuwan. Ta duba handle dinta na tiktok da Facebook,ita
dai a rayuwarta zata iya cewa batasan mace kamarta ba. Komai ta iya,idan nace
komai ina nufin komai da komai din,kama daga kayan gashe gashe,girke
girke,kayan mata da na mazan ma da zaki hada da hannunki.....kayan
maqulashe,man kitso,man shafawa kai duk wani abu da dan adam zai buqata
musamman mace cikin rayuwarta. Hatta fannin gyara mu'amala da zamantakewar
auratayya ta hanyar shawarwari. Kai tsaye ta nemeta ta number dinta ta yanke
yin register da ita,kafin ta qara nauyi tanason ta zama cikakkiyar mace tako
ina,itama ta hada wadannan baiwawwakin.+234 907 927 4454
(Ba sabreen ba,ni kaina magana ta gaskiya na jima banga
mutum irinta din ba,akwai qaruwa sosai tattare da ita,in sha Allah bazan gajiya
da kawo muku duk wani mutum da zamanku tare dashi zai amfaneku kuda iyalinku
ba).
Home
service takeso sukayi tsada ta gama komai. Tun bata ganta ba kirkinta a iya
waya kawai yasa hankalin sabreen sake kwanciya da ita.
A nutse ya
kashe motar gaban gidan,duk da mai tsaron gate din gidan ya dage qofar tun
isowarsu.
Ango
farouq dake zaune a seat me zaman banza.....sanye da wata danyar dakakkiyar
shadda da iya kallo kawai da idanu zai ganar dakai kudin data lashe.
"Ya ka tsaya a nan kuma?". Girarsa kawai ya dage
masa yana zare key din.
"Muje na taka maka kawai.......sabrrrr tana
jirana"
"Muma dai Allah ya kawomu dadin abun ko?" Farouq
ya fada yana bude side dinshi ya fice.
Da ido
farouq yabi kyakkyawan kwandon da fu'ad ya dauko da kansa.
"Da alama wannan aikin adda ne ko?" Farouq din ya
fada yana jin wani girma da kimar sabreen suna hauha a ranshi.
"Eh.....ai ta rantse sai wannan tsohon tuxurun ya
morewa angwancinsa".
"Ta fiyemin kai ai hundred percent" Farouq ya fadi
yalwataccen murmushi na subuce masa.
"Thank god da babu yadda za'ayi dani ai" Fu'ad ya
fadi yana yin gaba yana barinsa da wani nannadadden kwali da shima ke cike da
tarkacen kayan qwalama.
A veranda
din farko fu'ad ya cake yana miqa masa kwandon.
"Meye haka dude.....ka qaraso ku gaisa mana"
"Da wa?" Ya fada yana zaro idonsa waje.
"Fannah" Ya amsa masa kai tsaye.
"Allah you're mad farouq.........kawai sai in shiga
gidan mutane kai tsaye har can ciki?.....kaga forget about it
please...........ka shiga da cikakkiyar sallama please.....don't forget to
recite addu'an da miji yakewa amaryarsa a daren farko......don't forget to pray
two Raka'at........fatan alkhairi ". Wani qaunar dan uwan nasa yaji yana
kamashi,sai kawai ya rungume fu'ad din cikin jikinsa yana fadin.
" Thank you dude.....thank you,Allah ya cika maka
muradinka".
"Kukan zakayi tun yanzun?,akwai sauran awanni" Ya
fada jin muryarsa kaman ta karye. Dariya farouq ya saki da risunannun idanunsa
yana janye jikinsa daga na fu'ad. Hannu fu'ad din ya sanya yadan daddaki
kafadarsa,ya zura hannunsa a aljihu ua fiddo wayoyin farouq din. Latsesu dukka
yayi ya kashesu sannan ya miqa masa su yana masa magana da ido akan
"Ka barsu a kashe,kada ka kunna". Sannan ya juya a
nutse yana fita a gidan gami da bawa guards umarnin su kulle ko ina a gidan.
Yana
takawa zuwa cikin gidan yana jin wani yanayi yana ratsashi. Wani yanayi daba
kowanne zai fahimta ba sai wanda yake a matsayi irin nasa.
Da
cikakkiyar sallama a bakinsa,tare da qarin addu'ar
"Allahumma adkhilni mudhkala sidqin,wa akhrijni
mukhraja sidqeen,waj'alni minladunka suld'anan naseera,rabbi anzilni munzalan
mubarakan wa'anta khairul munzileen" (Addu'ace me kyau ga amare ko angwaye
yayin shiga gida,ko idan kunyi sabon gida a sanda zaki shigeshi).
Yana yaye
curtain din falon duk wani colors da tsari na dream parlor dinsa ya
bayyana,lafiyayyen murmushi ya subuce masa.
"My dude.......miskili kafi mahaukaci ban haushi"
Ya samu kansa da yiwa fu'ad kirari qasan zuciyarsa. Kowanne taku nasa sai
yakejin wata rahama da nutsuwa tana saukar masa,wani irin farinciki yana
lullube ilahirin zuciyarsa.
Qawatattun
bedrooms din nasu har guda hudu ya dinga budewa daya bayan daya,sai ana biyar
din sannan ya ganta.
Nannade
cikin laffayar nan da zata baka tabbacin asalin kanuri dince ita,turararren
qamshinta daya dumame dakin kuma ya sake gaya maka still KANURI CE.
Sallama ya
sake jaddadawa,can qasan maqoshi ta amsa,saidai shi yaji abarsa,murmushi ya
sake subuce masa,sai kawai ya duqa yana sabule rufaffen takalmin Gaziano &
Glirling dake qafarsa,ya rage saura socks kawai wadda ita tayi masa jagoranci
har zuwa bakin gadon da take zaune.
Hannuwanta dake lullube da kyakkyawan zanen lalle ya kalla,baisan sanda
ya ajiye wayarsa da keys dinsa gefe ba,ya miqa hannu yana dora tafin hannunsa
saman nata tafukan hannayenta ba ya riqesu sosai. Wata sheshsheqa ya saki gami
da nannauyar ajiyar zuciya duka lokaci daya,wanda suka fito tare da kalmar
"Alhamdulillah". Karon farko a rayuwarsa da
hannunsa ya soma taba na fannah bayan ta zama halalinsa......karon farko da
sukayi kusaci da juna har irin haka,duk da yadda yake tsananin sonta,yake kuma
shauqinta,itama kuma haka,amma dukkaninsu sun killace hakan,sun kuma boyeshi
qasan ransu,ba wanda ya bari dan uwansa ya fuskanci hakan.(qalubale ga
matasanmu)
"Babarbariya ta" Ya fada a tausashe da wani taushi
da baisan yana dashi ba. Wani suna qwaya daya da ba soyayya ba da yake kiranta
dashi,yake kuma mata tsananin dadi.
"Taimaki wannan dan bawan Allahn a bude masa wannan
fuskar mutanen maidugurin ya kalla" Ya fada yana zamewa,sosai ya zauna a
gabanta gami da komawa kalar tausayi,ya koma kaman wani dan almajiri,sai
yakejin tun yanzun kaman zai fara sakin kukan da fu'ad ke cewa ya riqeshi
tukunna. Kafada ta maqale ba tare datace komai ba,sarai ya gani,duk saita
rudashi.
"Roqo nake badon halina ba" Ya fada yana riqe
hannayenta da kyau cikin nasa.
Murmushi
ya qwace mata,duk da fargabar da take ciki,sai ta zame hannunta daga nashi a
hankali ta sanyasu tana janye lafayarta baya ba tare data daga kanta ba.
"Kan uba!....subhanallah" Ya fada yana wani
wantsalawa cikin wani irin mamaki. Fannah ta shammaceshi,tunda suka fari
soyayyarsu har suka qare bazaice ga wani shape nata daya taba gani ba,koda da
wasa kuwa,a yanzun saiga wata ajiyayyar kyakkyawar halitta kuma dukka
mallakinsa ce?,yayi yadda yakeso?. Hannu ya miqa zai zame lafayar daga
kafadarta,yanason ya sake ganinta sosai sai ya janye hannun da sauri yana
murmushi,yana jin kaman wani shock ke jansa.
"Dan sake budemin please fannah.....i wanted to see you
all". Wuyanta ta langabe alamun aah,ai baibi ta kanta ba sai gashi ya dawo
gabanta. Hannuwansa duka ya sanya ya dagata,ya miqa hannunsa gefan qugunta inda
ta daure lafayar ya wareshi,ya kuma zarce da wareta gaba daya daga jikin nata.
Tsaf ya
ware kayarsa,sai yakejin wani abu yana ratsa sassan jikinsa.
"Subhanallazi lam yattakiz waladan wala saheeba"
Ya tsarkake girman zatin Allah a abinda idanuwansa suka gane masa karo na
farko(qalubale gareku mata,wata sai ran bikinta ma take fidda shape din gaba daya mazan duniya dana media su tayashi
kalla).
Ji yayi
idan ya qara koda second daya bai sanyata a jikinsa ba kaman zai mutu,sai ya
jawota gaba daya cikin jikinsa yana lullubeta da hannuwansa,qamshin jikkunansu
suna cakuduwa guri guda.
"Alhamdulillah,first halal hug" Ya fadi a bayyane
yana sake godewa Allah da yadda ya bashi iko ya tsare mutuncinsa.
Sai da yayi
da gaske ya zame jikinsa,don ya fahimci wannan al'amarin bame sauqi bane,idanma
har za'a biyewa ta zuciya da gangar jiki,tabbas dukka addu'o'innan da musulunci
ya koyar da sallolin ba zasu samu ba.
"Ki shiga toilet ki daura alwala,ki rage wannan nauyin
na jikinki kizo muyi sallah" Ya fada yana tattare mata lafayarta guri
daya. Dama gurin tsira take nema,don haka da sauri da sauri ta wuce bandakin ta
turo qofar.
Wani wawan
tsalle ya buga bayan ya isa dakinsa.
"Alhamdulillah" Ya sake maimaitawa yana sauraren
bugun da zuciyarsa keyi,sai ya miqe ya soma shima rage kayan nasa jikin sannan
ya wuce bandaki.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 142
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.....siya
ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashin da babu irinsa_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
142
Sai da suka tabbatar an kai amarya,an kuma dawo,kowacce mota an ajiyeta
a muhallinta sannan sukabar farfajiyar gidan shi da saddiq suna wucewa sassansu
da tuni kowannensu shima ya kwashe komai nasa banda furniture din ciki,aka kuma
shirya a tagwayen gidajensu masu tsananin kyau da fasali.
Saida
musaddiq din yayi wanka don yaji dadin jikinsa,ya kuma canza kayansa zuwa
sassauqar jallabiyya ta maza. Har zai tada sallah sai kuma ya fasa,ya koma da
baya yana dauko wayarsa da tunda suka gama waya da amna ya sakata a charge ya
kulle ya barta a dakin.
Yayi
hakanne don kada ta matsa masa da kira da magiya,taje ta karya masa zuciya yayi
abinda baiyi niyya ba. Sam bayajin zai barta fita a gidan,fita daya yakeso
tayi,daga gidan sai gidanshi a gobe in sha Allah.
Ya tarar
kuwa da miscal dinta har guda biyar.
"Rigimammiya" Ya fadi yana murmushi sannan ya koma
ya zauna yana yunqurin kiranta.
Kiran farko
aka gaya masa layin a kashe yake,mamaki yadan kamashi,don zai wahala ka kira
amna wayarta a kashe,tunda dai su ba rashin wuta sukeyi ba,inverter ne 24/7 a
gidan.
Sake
gwadawa yayi aka sake gaya masa hakan,sai ya haqura ya kira saddiq zuciyarsa na
raya masa tayi fushi ne dashi bai kaita ba,shi yasa ta kashe wayar don ta
rama,shikam bazai iya jura ba,gwara ya lallaso abarsa,
"Huda zaka kiramin,kace tace da amna ta bude wayarta
badon halina ba". Dariya saddiq ya bushe da ita.
"Man.....wannan karyar da kai haka?,'yan mazan anni na
dab da zubewa"
"C'mon saddiq.....zaka taimakamin ko na shiga gidan da
kaina na nemota?".
"Ni na isa?,bari na kira maka ita.....hold on kada ka
kashe". Ya fada yana hada conference call .
"Hubby..." Ta furta da shagwabar data sanya
musaddiq jin kunya ta kamashi.
"Love ya akayi?".
"Ina kewarka hubby"
"I know love......but mun kusa kasancewa da juna in sha
Allah,awanni kadan suka rage.....kina ina?" Ya tambayeta calmly.
"Na boye a daki hubby.....kunyar anni nakeji".
"Anni love?....." Ya fada dariya na subuce masa.
"Anni ai bata da surukai sai 'ya'ya,tasha fadin
hakan.....fell free please".
"I will tray hubby"
"Good girl....amna fa?"
"Tun dazun da muka karbi adda fannah ban sake ganinta
ba,ina tunanin tana wajen anni".
"Thanks......bari nayi wanka.....get ready zan kiraki
ki rage....." Bai qarasa jinsu ba ya yanke kiran,kada suje suyi masa
baranbarama a kunne.
Still ya
sake kiran saddiq.
"Ina kunyar tambayar anni please saddiq tambayar min
ita"
"A nawa?" Ya sake zolayarsa
"Ka fadi price dinka" Ya fada yana jin zaquwa.
"Bari na kira maka din sai mu tsadance" Ya fada
yana yanke kiran.
Minti
daya kacal saiga kiran saddiq din.
"Anni tace suna tare da huda,gashi kuma huda tace tana
wajen annin". Gaban musaddiq ne yayi wata irin mummunar faduwa,haka kawai
yaji fargaba tana ratsashi.
"Ya akayi haka?....amma,ina zuwa" Musaddiq ya fadi
yana yanke kiran,sai ya zura flip flops dinsa yana fita a dakin.
Kacibus
sukayi da saddiq wanda ya fasa wankan shima ya zura tasa rigar.
"Ko wani dakin ta shiga bacci ya dauketa" Saddiq
din ya fada shima yana jin haka siddan tsoro yana kamashi.
"Haka nake tunani"
"Muje cikin gidan" Saddiq ya fada yana yin gaba
musaddiq da yakejin kaman an sabule masa gwiwoyinsa ya bishi a baya.
Harabar
gidan ba kowa don kowa ya gaji ya wuce makwancinsa,baqi suna can shiyyarsu a
bangaren baqi na gidan,a haka suka kutsa sassan anni.
"Kira anni kice ta sauko" Saddiq yace da badawiyya
me aikinta,ta amsa da to. Harta fara haurawa saddiq ya dakatar da ita yace ta
dawo sai ya haura da kansa.
Ya samu annin
tana cire dankunnayenta da sarqa,saita juyo da mamakin ganinsa a irin wannan
lokacin tana kallonsa.
"Ya akayi saddiq?"
"Amna fa bata wajen huda anni,kota gaya miki tana wani
gurin?,dakunan wajen nan kuma mun duba kafin mu shigo,wayoyinta switched
off". Yankewa gaban anni yayi ya fadi,hannuwanta data miqa kunne don cire
dan kunnenta sai taji sun mata nauyi dole ta ajesu tana dubansa.
"Kun gama duba gidan nan gaba daya?". Kai ya
girgiza.
"Kusan ko ina dai anni" Hannu kawai ta miqa ta
dauki mayafinta ta yafa tana cewa.
"Muje". Tare suka sauko dashi,ta dubi musaddiq.
"Qarfe nawa ta kiraka kira na qarshe?".
"Takwas da rabi anni mukayi waya,tace zataje gidan BB
nace ta bari if possible zan dauketa na kaita taga gida mu dawo....idan bai
samu ba tayi haquri,na saka wayar charge saida muka gama komai na koma daki na
samu miscal dinta me yawa,na kira kuma wayar a kashe take". Wani abune ya
tsargawa anni,a jikinta kawai taji wani baqon abu yana shirin faruwa,don amna
bata taba irin wannan ba. Koda garden na gidan zata shiga saita gaya ma anni
ballanta ace ta fita ko tayi nisa da gida irin haka.
"Kiramin duk masu aikin gidannan" Anni ta buqata
tana duban badawiyya. Da sassarfa ta juya,ba jimawa sai gasu kafataninsu,annin
ta leqa daga qofar falon ta gaya musu,matan su bincike cikin gidan,mazan kuma
wajen gidan dama kewayensa,saita koma cikin falon ta zauna kawai tana jin
qafafuwanta suna dab da gagara daukarta.
Kimanin
mintuna biyar matan suka dawo,saidai kowacce abinda take gaya mata shine.
"Bamu ganta ba"
"Ba kowa a dakunan"
"Bata nan". Shuru kawai annin tayi tana jan
hasbunallahu wa ni'imal wakil tana dakon dawowar mazan.
Jimawa
kadan suka kammala nasu duban suma,har zuwa qofar gidan. Kasa tashi annin
tayi,don haka tace musu su shigo parlor din kawai.
" Mun duba duk inda ya dace ace mun duba din,tun daga
cikin gidan nan har street din daga farkonsa har qarshe amma bamu sameta
ba,bamu samu kuma komai nata ba"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,hasbunallahu wa
ni'imal wakil" Anni ta fada tana runtse idanunta,fargaba tana kamata.
Gaba
daya rasa abun yi tayi,hakanan kuma ta rasa abun fada kwata kwata,kwanyarta ta
daure tamau kamar bata tunani me kyau ba tunda take.
Fu'ad da
farouq dukkaninsu suna gidajensu da matayensu,abba kuma baya nan,a yadda sukayi
magana a safiyar gobe qarfe takwas zuwa tara jirginsu zai sauka. Kai ta
girgiza,ba wanda zata bari ya sani a cikinsu,ba wanda zata dagawa hankali.
"Anni ko su yaa fu'ad za'a kira?" Saddiq da tuni
hankalinsa yayi qololuwar tashi ya fada. Kai ta girgiza tana miqewa.
"Ban yarda ku gayawa kowa komai ba a darennan,don ba
abinda hakan zai amfanar saidai ku daga musu hankali,bayan koda sunzo ba zasu
yanke abun yanzu yanzu ba,sai wanda ya qaddara faruwar hakan ya qaddara
warwarewar lamarin...." Ta fada cike da tauhidi da qarfafa imaninta,duk
kuwa da cewa ita kadai tasan abinda takeji.
"Kuje kuci gaba da kula da aikinku....kuma ku wuce zuwa
safiya ko asuba muga abinda Allah zaiyi" Annin ta fada tana duban kowa.
Kowa din
ya juya ya fice,amma banda musaddiq dake qame a wajen,tamkar ma baisan abinda
yake faruwa ba.
"Musaddiq" Anni ta kirashi cikin dakiya. Kansa
kawai ya daga ya kalli annin,don yasan baida sautin da zai iya amsa mata.
"Kayi haquri kaje ka kwanta"
"Kwanciya anni?" Ya tambayeta kaman baya fahimtar
hausa.
"Ta yaya zan iya kwanciya bansan halin da take ciki
ba?,anni ina aka kaita?,waye ya dauketa?,me tayi musu?,me sukeso?,amna ce
fa?.....kwata kwata shekararta nawa?,waye ta tsarewa wani abu?" A nutse
anni ke karantarsa,ta fahimci kaman abun yanason fin qarfin kwanyarshi ne,don
haka ta kira saddiq.
"Ko baka kwanta ba kaje kayi addu'a musaddiq mu barwa
wayewar gari" Tsam.ya miqe ba tare
daya kalli koda saddiq dake jiransa ya tashi su tafi ba.
"Ina zaka?" Saddiq ya zaburo yana tambayarsa gami
da shan gabansa.
"Zan fita nemanta ne,tunda kai baka damu da ita
ba" Ya fada da alamun tashin hankali muraran akan fuskar sa. Kai saddiq ya
girgiza
"Akwai hadari a fitarka musaddiq,tunda ko su waye
sukayi hakan bamu sansu ba,bamusan dalilin daya sanya suka aikata hakan
ba,bamusan kuma meye manufarsu ko target dinsu ba".
"Ko report sai naje na shigar,ba zasu dauke mana
mutum.sukutum da guda mu kulle qofofinmu mu kama bacci ba kaman kaza suka
dauka" Anni ta fahimci da gaske
abun ya soma haurawa tunaninsa ne,don haka ta tako gabansa tana kiran sunansa.
"Kanason jefa amna a hadari bayan wanda take
ciki?" Kai ya girgiza da qarfi.
"Yayi....to kada ka soma wani motsi ko aikata komai har
sai munji daga bakin yayyenku.....qila fitar da zancan shine zai zama namu
kuskuren.....kayita karanta ya hayyu ya qayyumu birahmatika astagis".
Kafin ta dire ya kama,a hankali sai yaji hankalinsa yana daidaita,ya miqa hannu
ya kama hannun saddiq da kanshi yana cewa
"Muje".
A parlor
dinsu ya zaunar da saddiq shima ya zauna yana matsowa dab dashi,ya kalli saddiq
din sosai muryarsa tana Rawa
"Saddiq tsoro nakeji su waye?,tsoro nakeji karsu cutar
da ita,saddiq munaji muna gani a hannunsu zata kwana?,wanne irin gurin kwanciya
zasu bata?" Wanne kalan ruwa da abinci zasu bata?" Sosai saddiq ya
riqe hannunsa yana fadin.
"Kayita maimaita fadin ha hayyu ya qayyumu din kamar
yadda anni tace......bamu zalunci kowa ba in sha Allah ba wanda Allah zai
dorashi a kanmu".
Sun jima
yana riritar musaddiq kafin ya samo nutsuwarsa 'yar kadan,saidai ko cikakken
zama ya kasa bare ayi maganan kwanciya,kai kawo.kawai yake tsakanin qofa window
zuwa farfajiyar gidan,yana jin kamar ya zura da gudu ya tafi neman amanansa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 143
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
143
★A nutse
ya shafa addu'a daga sallar asubar da suka idar shida fanna din tasa,koda bai
kalli madubi ba yana iya jin yadda qwayar idanunsa suka tasa,wanda bana komai
bane saina kukan farinciki daya dinga yi a daren jiya. Yaso yayi haquri ya
kauda kai saboda walimar da za'a gudanar a yau,amma inaaaa.......ya gaza
jurewar,har sai da yakai ga inda zuciya ruhi da gangar jiki suke muradi.
Juyowa
yayi gaba daya gareta,tana zaune a takure,kanta a qasa tana duban yatsun
hannuwanta.
Ita dinma
fuskarta duk ta tasa,saboda kusan tare akayi kukan,tana yi yana tayata. Idanu
ya lumshe ya budesu yana jin nishadi yana saukar masa. Kullum cikin zulumin
yadda zai taddata yake,saboda ya sare da halayen 'yammatam yanzun duk da cewa
yana da cikakken yarda da dabi'unta,to amma wani lokaci abun ba'a kama bane ko
siffa.
"Taho nan flower" Ya fada da sassanyan muryarsa
yana miqa mata hannunshi. Bata wani musa ba ta miqa masa nata,don tana buqatar
inda zata jingina taji dadin zaman.
Jawota
yayi zuwa jikinsa yana rungumeta tsam,yana jin wata shaquwa tana tsaga
jikkunansu,yana jin kamar ta tabbata a rungume a jikinsa kaman haka.
Qoqarin
gaidashi takeyi,ya amsa mata yana shafa kanta ya amsa cikin kulawa. Sosai ya
dinga jero mata addu'o'i,kanta a qasa tana amsa masa da matuqar alkunya.
Mintuna kusan goma sha biyar suka debe a haka kafin ya gyara mata zamanta,ya
ciro alqur'ani guda biyu ya bata daya ya dauki daya.
"Ko na minti biyar ne flower,saboda mu bude wunin
rayuwarmu na farko da neman albarka". Ya fadi yana miqa mata. Rainon anni
ne wannan ta saba musu da farawa da qur'ani,kaman yadda yasan itama fannah din
'yar gado ce wajen iya sarrafa harshe a qur'ani.
(Ina kira a gareku iyaye,kiyi qoqari a mazauninki na uwa ki
wadata kwanya da harshen 'ya'yanki da qur'ani,su zama gwanaye wajen karanceshi
daga bango zuwa bango,idan da hali suna karantawa suna fahimtar ma'anar,saboda
hakan yana taimakawa wajen zaunar dashi a kansu yana kuma taimakawa wajen sake
jin asalin gard'insa da dadinsa. Allah ya sani ina mamaki naga babban mutum
babbar mace ko sangamemiyar buduwa musulma,amma ba zata iya karance miki
qur'ani daga bango zuwa bango ba,ko ba zata iya biya miki wani adadi me yawa
ba,don kwanyar da aka horata da qur'ani zaka sameta da kaifin basira da fikira
me tarin yawa,Allah ya bamu ikon tarbiyyantar da yaranmu akan hakan,ya shirya
mana zuria kafatanin musulmi Allahumma ameen).
Suna
kammalawa kira yana shigowa wayar tasa. Fannah ce ta miqo masa da hannu biyu ya
karba yana murmushi
"Allah yayi miki albarka" Saidai sunan daya gani
mamaki ya kamashi,baiyi zatonma zaa kirashi da safe da wuri haka ba shi yasa ya
bude wayar.
"BB ba'a ga amna
ba tun daren jiya......ga musaddiq nan ya rikice mana,kaman yanason rasa
nutsuwarsa,ka sanar da hamma don Allah" Abinda saddiq ya fada kenan yana
katse Kiran.
Innalillahi yakeso yaja,amma kuma bayaso yayi abinda zai tashi hankalin
fannah daga wayewar garinta a rana ta farko,ballantana yasan mata da rudewa
qwarai,dan qanqanin abu sai su maidashi babba,don haka ya miqe tsam da wayar
a.hannunsa yace.
"Ina zuwa" Ya soma takawa yana fita a dakin. Tadan
bishi da kallo kadan,sai kuma ta miqe tana ninke abun sallar da suka idar.
Wani dakin
daban ya bude ya shiga,sannan ya fara qoqarin kiran fu'ad yana kuma laluban
kayan da zai sauya a jikinsa,idanunsa akan agogo yana duba qarfe nawa.
Su dimma
rufe alqur'aninsu kenan,don a yanzun shine malaminta. Tayi sauka tun kafin
rasuwar mahaifinsu,tana da tilawa a kanta,amma sai yanayin karatunsa da
qira'arsa suke mata dadi,wannan ya sanya ya zame mata malami duk bayan sallar
asuba suke tilawar abinda ya sawwaqa tare.
Wani
lokaci ido take zuba masa idan yana karatun. Komai Allah ya bashi,duk wata
baiwa da take nuna cikar dan adam ya sameta,abu guda daya ne ya masa cikas da
naqasu shine MAHAIFIYA.
Kashingidar da yayi da wannan damar ta samu ta zame jikinta zuwa
kitchen. Wata irin mahaukaciyar yunwa take fama da ita a dan tsukinnan,ko cikin
dare ta tashi abinci takeci,ba jimawa kuma take rasa komai,cikinta yake yayewa
tasss kaman an mata yasa.
A
tsaitsaye ta hada oats ta madara tasha,kafin sannan saiga ma'u ta shigo.
A
mutunce suka gaisa,zuwa sannan ta fara gane inda sabreen tasa gaba na bawa
mijinta kulawa da karan kanta.
"Me zamu dafa?"
"Ummm.....bari muga.....bari na fara dafa masa paw paw
tea tukunna" Ta fadi tana nufar tsararren store dinsu.
Duk
kusan ganyayyakin da yakesha akwai a ciki,busassu anyi packaging nasa cikin
wani leda ta musamman da ake kawowa daga china. Packet na Paw paw leave din ta
dauko ta dawo,ta wankeshi da kyau ta tafasa ta juye masa cikin wani Traditional
English tea set sannan tace da ma'u.
"Ki fiddo naman kai bari naje na dawo".
Ta shiga
daidai sanda ya fito daga toilet yana goge ruwan alwala. Idanunsu suka gauraya
waje daya,kowannensu ya sakarwa dan uwansa lallausan murmushi.
"Barka da tashi sleepy head" Ta fada cikin salon
tsokana. Fadada murmushinsa yayi har fararen jerarrun haqoransa suna fitowa.
"Barka kade my super girl" Ya bata amsa yana
karbar tea tray din yana ajiyewa saman drawer. Hannunsa ya miqa mata yana
jawota cikin jikinsa,saidai kuma sulalewa tayi ta tsugunna tana gaidashi. Amsa
mata yayi cikin murmushi kafin ya miqa hannu ya sake jawota ya rungumeta
tsam,fitinannen qamshin kabbasarta na incense by kabo daughter daya hautsina
har cikin gashinta da kuma lab lab dinta suna tashi da wani sassanyan qamshi
daya manne a fatarta.
"Fatan shalelena ta tashi
lafiya.....addarmu.......matar babban yaaya" Yadda ya fadi maganan ya
sanyata tuntsirewa da dariya,ya sake kamota yana qanqameta a jikinsa.
"Ina yara na?,fatan sun tashi lafiya?" Ya furta
yana qoqarin dage rigar baccin jikinta. Da sauri ta damqe hannunsa tana duban
tsakiyar idonsa,sai ya dage mata dukka girarsa yana tambayarta why?,da wannan
kallon nasa.
"Ba bra a jikina".
" Good" Ya fada da hanzari yana daukanta cak ya
azata saman drawer din,sannan yasa hannunsa ya dage rigar har zuwa inda yakeso.
Da cikin
nata ya fara wanda ya fara turo kansa,ya aza dukkanin hannuwansa akai.
"Good morning my Angel's" Dubansa tayi.
"What?" Yatsansa ya dora saman lips dinsa
"Shshshsh" Ya fadi sannan ya maida hankalinsa kan
cikin.
"Eheeennnnn......hope you're doing well......am eager
to meet you my life.......have a nice and great day" Sai ya sunkuya yayi
kissing na cikin. Sama ya komar da fuskarsa tsakanin ababen dake matuqar janye
hankalinsa,qanqameshi tayi sanda yake cusa kansa a tsakiyar su,sannan ya sakar
mata wani kiss din me sanyi kafin ya janye fuskarsa da idanunsa suka fara canza
launi.
"Mun gama gaisawa.....me kike cewa?. Fuska ta bata.
"Son kai hamma.....son kai"
"Name?" Ya tambaya yana ware hannayensa.
"Angels hamma?......ni nafison baby boys.....masu kama
da kai.....masu quality dinka". Ta fada tana tura baki gaba. Kyau sosai
lips dinta sukayi masa,yasa hannu yana taba lips din murmushi na qwace masa,ya
motsa bakinsa cikin nutsuwa.
"Nafison baby girls masu tausayi irin naki......masu
tsananin zumunci irin na ummansu......masu qaunar 'yan uwansu.....kinsan ma
haihuwar diya mace falala gareta me girma fiye dana d'a namiji?" Kai ta
girgiza
"Na sani,idan aka haifi uku aka musu tarbiyya aka aurar
dasu zasu zama sanadin shigar mahaifansu aljanna,sannan haihuwar d'iya mace
tamkar shigowar haske biyu ne cikin gida,saboda zata jawo wani namijin shima ya
zama naku". Tafi sosai ya sakar mata yana murmushi
"Bravo alaiki...." Ya furta yana kissing tafin
hannunsa ya aike mata dashi.
"Duk da wannan?,duk da wannan my world kikeson
boys?" Kai ta gyada.
"Na rigaka addu'a fa hamma......inaji a jikina Allah ya
amsamin.......ina buqatar photocopies din muffin dina" Ta fada tana
tsiyaya masa ruwan gwadar ta miqa masa.
Karba yayi
yana dubansa,sai daya qare masa kallo sannan ya kalleta da lallausan murmushi
"Ya akayi kikasan ina sonsa?". Dukka girarta ta
dage masa tana nade hannayenta a qirji,hakan ya qara mata kyau sosai.
"Kana tunanin idan nace inasonka ina sonka ne da
wasa?......duk wanda nace ina sonsa......ina sonsa da gaske.....ballantana
kai...." Ta qarasa fadi tana nunashi da yatsa daidai sanda kira ya shigo
masa.
"Farouq?" Ya fada a mamakance,farouq dinne da kira
haka da sassafe?,cikin jikinsa yaji tabbas akwai wani abu daya faru,ya miqa
hannu yana daga kiran
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 144
*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada
munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR
GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN
HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road
kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a
duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
144
Shuru kawai yayi yana sauraren farouq har ya gama gaya masa
abinda zai fada din. Satar kallonta yayi sanda take qoqarin zuba masa wani tea
din.
"Ka kula please dude.....banaso adda taji maganar nan
ko don lafiyarta.....itama fanna din ban gaya mata ba,zan wuce gidan
yanzu"
"In sha Allah" Ya fada yana sauke wayar daga
kunnensa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Shine abinda
yaketa maimaitawa can qasan zuciyarsa kafin ya samu ya miqe tsaye yana duban
ta.
"Adamamin tea din nan,abba ne ya kirani yanzunnan wai
ya kusa sauka yanason nazo". Har ga Allah bata kawo komai ba,kawai
mamakinta shine abban ke nemansu da safe haka?,kuma shida farouq?. Ba huruminta
bane zafafawa kan sanin meye asalin ainihin kiran ba,don haka ta taimaka masa
ya sauya kayansa ya fice zuwa ma'ajiyar motocinsa,inda ya taso jordan suka fice
tare.
"La haula wala quwwata illa billah" Shine abinda
yake maimaitawa kawai akan hanya yana murza goshinsa. Wani irin tashin hankali
ne yaji yana lullubeshi,duk irin tsaron da ya saka.....duk yadda yake kaffa
kaffa amma daga gefe akwai wanda yake fakonsu?.
"Su waye?.....su waye?" Ya furta a dan zafafe yana
jinjina hannunsa yana duban titi,yana jin kamar ya tariyo daren jiya komai ya
wakana a idonsa.
"Waye ya rage?,waye yayi saura?" Ya fadi yanason
tunawa ko akwai wani abu daya bari wanda ya kamata yayi baiyi ba.
Wayarsa
ya fiddo ya fara qoqarin gwada number amna da kanshi,amma switched off ake gaya
masa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ya koma
maimaitawa. Anni kawai yakeji.....ko musaddiq zai biyo bayan anni ne wajen
shiga rudani,saidai ita anni ta fishi dauriya da dakiya.
Tun daga
harabar gidan daga kan fuskokin masu tsaron gidan ya karanci tashin hankali
b'aro b'aro. Jordan na fakashi ya sauka da dan sassarfa ya wuce cikin gidan.
Da
batulu ya soma cin karo,shugaban ma'aikatan gidan.
"Ina anni?" Ya tambayeta ba tare daya damu da amsa
gaisuwarta ba.
"Tana sama sir"
"Okay.......Inaso kowanne baqo a gidan nan a kula dashi
yadda aka saba,a kuma sallamesu ba tare da kowa yasan halin da ake ciki
ba......a shaida musu an soke walimar saboda annin batajin dadi,likita kuma
yace a barta ta kwanta ta huta sosai,saddiq zai sallami kowa,masu tafiya a
jirgi da masu tafiya a mota,inaso nan da azahar gidan ya zamana daga mu sai
mu,na tabbata ku kudai kukasan abun.....daga haka banaso labarin ya qara
gaba"
"In sha Allah yallabai za'ayi duk yadda kace" Ta
fada cikin girmamawa.
Yana
shirin haurawa saman yaji muryar farouq,waiwayawa kawai yayi ya kalleshi yana
amsa sallamar saiya juya yana haurawa saman. Hankalinsa duka yana kan anni,don
haka ita ya fara gani a sanda ya bayyana a parlor din saman.
Kallo daya
tak yayi mata yaga wata irin rama ta bayyana saman fuskarta,daga daren jiya
zuwa yau?,idan kuma abun ya shallake haka kuma fa?,fu'ad ya tambayi kansa da
kansa hankalinsa a tashe.
Sauke
dubansa ya sakeyi ga huda,wadda ke cure waje daya taci kuka har ta soma jin ba
dadi,saddiq na zaune kusa da ita,da alama qarfin gwiwar lallashinta yake neman
tattarawa kuma bai samu hakan ba.
Musaddiq
kuwa yana zaune kaman zane,ramarsa har taso wuce ta annin da wani taqi na
musamman.
Kallon da
yayi musu dukkaninsu a lokaci daya sai yaji zuciyarsa na nufin karyewa kaman
yadda ta anni ta karye. Ganinsu sun biyun sai takejin dukka qarfinta ya tattara
a nan....kaman sune duk wani hope nata a yanzun.
Fu'ad ne
ya lura da yadda jikinta ya soma rawa,ya qarasa da sassarfa ya riqeta yana
zaunar da ita. Komawa yayi gabanta ya zauna sosai yana tanqwashe qafafunsa.
"Kece qarfin mu anni.....don Allah ki sake bamu wannan
qwarin gwiwar koda karo na qarshe ne....koda shine alfarmar qarshe da zaki mana
mu 'ya'yanki". Duk yadda taso tsare hawayenta sai daya zarto,saidai tayi
qoqarin saurin daukeshi,banda su farouq da fu'ad din ba wanda ya gani.
"Allah shine qarfinmu muhammadu.....shine kuma zai
tsaya mana" Ta fada tana tattaro jaririyar dauriyar data rage mata. Saidai
shigowar abba a daidai lokacin ya sanya qwarin gwiwar nata ya sulale yabi
ruwa,don nufarsa tayi hawaye yana tsinke mata,fu'ad ya yiwa saddiq alama daya
sauko da huda ya juya yana sauka da sassarfa.
*_BAYAN MINTI TALATIN_*
Dukkaninsu
suna falon daya dauki shuru bayan gama tattaunawarsu akan al'amarin.
"Nayi alqawarin muddin ina numfashi......tsakanin yau
da gobe.....idan yayi tsanani zuwa jibi,tabbas da ikon Allah,da kuma girman
zatinsa amna zata dawo cikin ahalinta.....inason kowa a cikinku ya ajiyemin
wayarsa.....BB harda kai,kubar security code dinku akai basai kun cire
ba.....abu na biyu kowa inaso ya sanya ido akan motsinsa,da motsin duk wani
mutum da yake mu'amala dashi komai qanqantarta.....anni ki saka taki wayar a
ciki.....abba zanyi connecting kowanne kira da wayata basai ka bayar da taka
ba.....but kowanne saqo ko.kiran duk da nayi connecting ka kula sosai yayin
dagawa......zamuyi aiki da team dina na kwana biyu zuwa uku in sha
Allah" Yadda yace din duka hakan
akayi,har zai fita ya dubi huda.
"Bani taki wayar" Saboda wani tunani da yayi.
Throughout yau bayason yau sabreen tasan komai ko taji komai,idam ta yuwu ma
har zuwa sanda zaa kammala abun,saidai yasan abune me wahalan gaske,karbe wayar
hudan zai rage shigarta tashin hankali.
Wunin ranar
gaba daya bai zauna ba,dukkaninsu shi da farouq dinma,zirga zirga ce kawai ake
yinta a sirrance. Hankalinsa dukka yana kan wayoyin daya karba,wai ko zaiga
wani baquwar number ya shigo,saidai ko gilmawar saqo bai gani ba.
Zuwa
yammaci saqo da kiran sabreen ya cika masa waya,sai daya idar da sallar la'asar
ya ciro wayar sannan ya tuna tunda ya fita a gida bai kirata ba. Da sauri ya
maida kiran nasa zuwa ga wayarta,bugu daya ta dauka,muryarta duk tayi wani
laushi sosai.
"Am so sorry my world.....ayimin afuwa,munyi busy yau
sabgogi sun riqe muffin sosai".
"Hamma na dauka ka manta dani ne yau?,yau Walmar
anni,ga lokaci yana shirin kufcemin,na gama shiryawa ban sameka ba,kasan bazan
fita ba kuma bada izininka ba,still kowa a gidan na kira number dinsa bai daga
ba,hadda huda ma,lafiya kuwa hamma?". Yadda tayi maganar ya tabbatar
jikinta ya soma raya mata akwai matsala,muryarta tayi wani laushi.
"Na saka an tsaida walimar nan sabrrr...zazzabi ne ya
saukarwa anni,kinsan kuma tana da asthma.....so kiyi zamanki a gida.....i will
tray my best naga na dawo gida da wuri". Dan jim tayi kadan kafin tace.
"Anya baka boyemin wani abun hamma?,ko wani abunne ya
samu annin?". Murmushi ya saki me dan sauti na qarfin hali.
"Ba komai my world.....karki damu.....ki kulamin da
kanki,ki gaidamin yarana". Ya fadi yana katse kiran.
Lamo
kawai tayi saman gadon zuciyarta na wani bugawa,bugun sam ba daidai take jinsa
ba,hakan yana sake bata tabbacin akwai abinda yake tafiya ba daidai ba.
Tayi juyi
saman gadon har batasan adadinsa ba,a nan sallar magariba ta sameta taje ta
bada ita,tayi isha'i ta sake dawowa ta kwanta.
Indai
ciwon anni baiyi tsanani ba ai ya kamata ace ta samu koda mutum daya ya daga
kiranta,bawai kowa ta kira wayarsa zata yita ringing bai daga ba.....ciki harda
fuad din kansa.
Sanda tara
na dare yayi sai taji hankalinta ya soma tashi,kiransa ne ya bata relief dan
kadan.
"Am sorry....on my way dear,karkiyi kewata da
yawa". Maganan da sukayi kenan a taqaice.
Yana ajiye
kirannata wayar farouq ta dauki ruri. Da hanzarinsa ya ajiye tasa wayar y kuma
daga wayar farouq din yana kallon screen din.
Baquwar
number ce da babu ita a jerin lambobin kan wayar,baiyi jinkiri ba yayi hanzarin
hada abinda zai hada ya kuma daga kiran.
"Farouqu hamza kibiya haka ne?"
"Shine" Fuad ya furta kansa tsaye yana fatan hirar
tayi tsahon da yakeso.
"Yauwa......mune wadanda muka dauki qanwarka amna a
jiya........saidai kafin mu tattauna komai daku muna buqatar kudi naira billon
goma". Idonsa ya lumshe ya sake budesu,wani fushi yana taso masa yana
lullube zuciyarsa. Ashar yakeso ya fara sake musu a matakin farko,to amma kuma
har yanzu ba'azo gurin ba.
"Ba matsala.....zamu saka muku......amma idan munyi
hakan zaku sakar mana qanwa salin alin?".
"Me yuwuwa....duk da bamu keda wannan hukuncin ba,wanda
keda ikon fadin a saki ko a kashe daban.....wannan din ladan aikinmu ne muke
buqata daga gareku". Bakinsa yaji yana motsi,amma sai yayi qoqarin danne
zuciyarsa.
"Zamu biya mun amince......ku fadi inda za'a saka
kudin".
" Zamu saka" Ya fada yana datse kiran.
"Oh shirt" Fu'ad ya fada yana dukan seat din
motar. Qiris ya rage mintunan su cika.....baici nasara ba......
Bayajin
wannan daren yana da nutsuwar gyangyadi ko bacci komai qanqantarsa.....maganar
kisa suke fa idan ta kama?. Baiko jira Jordan ya gama tsaida motar ba ya bude
ya dira daga ciki yayi cikin gidan.
Baiko
tsaya tantance wanda yake parlor din ba ya ketashi ya wuce hallway,wannan qofar
dake a kulle kullum ya danna ya budeta yana kutsa kansa ciki.
Ajiyayyen gurinsa ne dake dauke da tarin na'urori,ba kuma kasafai ya
fiya shiga wajen ba sai ta baci ko kuma yana da babban aiki irin haka.
Gaba
daya qwayayen ya kunna ya kuma kunna kowacce na'ura ya saitata kan aiki,ba
dadewa komai ya daidaita,ya fidda gaba daya wayoyin ya zubesu ya riqe ta farouq
a hannunsa yana kwafe numbers din zuwa allon screen din dake gabansa.
Tiryan
tiryan ya soma kurdawa cikin bincikensa,saidai kaman yadda ya zata komai ya
tsaya daidai iya mintuna daya kashe kiran.
"Ya salam" Ya fadi yana jin wani zafi da fusata.
"Da gaske dai wani abu ya faru" Muryar sabreen ta
ratsa kunnensa. Da sauri.ya daga kai yana dubanta. Tana tsaye daga bakin
qofa,sanye da night wear baby pink masu daukan idanu masu hawa biyu,gashinta ta
sakeshi saman kafadarta,yayin da jaririn cikinta ya bayyana sosai ta cikin
rigar kasancewar ta lafe mata sosai a jikinta.
Duk da
yanayin da yake ciki na tashin hankali hakan bai hanashi hango kyawunta
ba......hakan bai hanashi ganin wani kwantaccen kyau daga gareta ba.
"Listen sab....."
"Karka rufemin hamma.....na roqeka" Ta fada
jikinta da muryarta dukka suna rawa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 145
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
144
"Is
alright......zo ki zauna" Ya fada yana tashi da kansa,ya kuma tarbota yaja
mata kujera ya zaunar da ita.
Ta bashi
dukkanin wata nutsuwa da hankalinta tana kallonshi.
"Kiyimin alqawari ba zaki daga hankalinki ba....."
"Nayi hamma.....nayi". Kai ya jinjina,ya sake riqe
hannunta sosai yana duban tsakiyar qwayar idanunta.
"Amna ce tadan bace jiya,amma yanzun haka ina kan gano
inda take"
"Amna ta bata ko kuma an saceta?,wanne ne daidai a
ciki?". Ta tambayeshi tana jin wata kaduwa tana kama ilahirin gabbanta.
Juya
maganar tata yakeyi a ransa,ya sake kallonta yana ganin yadda ta kafeshi da ido
kaman me tuhumarsa da aikata hakan.
" Kowanne za iya zama daidai....."
"Bazai zama ba.....inaji a jikina dauke amna akayi
intentionally.....wallahil azeem" Tana kaiwa nan saita rushe masa da kuka
gaba daya.
Rudewa
yayi,gaba daya kukanta ya dauke masa nutsuwa.
"Bamuyi haka dake ba sabreen.......karki cutarmin da
yara please" Ya fadi yana hade hannayensa guri guda gami da sanya nata
hannuwan cikin nasan🙏.
"Me yasa zaka boyemin hamma?......sai idan ta mutu
sannan zaka gayamin?,ina huda?"
"She's safe" Ya bata tabbaci. Kai ta girgiza,sam
hankalinta bai kwanta ba.
"She's not safe tunda aka dauki amna.....nadra haneefa
dukkansu suna cikin barazana"
"Like how?" Ya fadi yana dubanta da tarin tambaya
gami da zama sosai a gabanta sabanin tsugunnon dazu.
Tambayarsa
ta dawo da ita cikin hayyacinta. A hankali ta sassauta sautin kukan nata. Zato
bai zama gaskiya ba.....zatonta kuma a yanzu baida hujja ko dalili sai qwqwaran
zargi,tana gudun ta furta abinda idan yaje ya dawo zai zama ba gaskiya bane,da
wanne ido zataci gaba da kallonsa?..
"Kina da wani masaniya ko hasashe ne?" Kai ta
girgiza
"Babu....but duk wanda ya shiga ya dauki amna....nadra
dasu huda ba zasu gagareshi ba"
"A tsukinnan indai ba aljani ba,banajin akwai wani dan
adam daya isa ya keta tsaron da gidan yake dashi ya dauki amna.....ina kyautata
zaton fita tayi.....zan binciki duk wani CCT footages na gida.....naci alwashin
amna ba zata kwana uku ba cikin iyalinta ba". Wani irin abu taji yana yawo
da ita,ya jima yana qoqarin daidaita mata nutsuwarta,amma kuma hakan bai hanata
kwanan kuka ba,bisa sharadin itama gobe ba zata zauna a gidan ba,ya kaita gidan
anni.....anni bata cancani fuskantar wannan tashin hankalin ita daya ba.
★Taku biyu tayi ta
sake juyowa tana komawa bakin window din. Sake riqe wayar tayi sosai a kunnenta
tana jin wani farinciki yana yawo da ita,jinta take tamkar a saman gajimare.
Karon farko data fara kasancewa cikin sa'a a rayuwarta,karon farko data aiwatar
da wani aiki da yazo mata da nasara ba a karon farko ba sai wannan.
"Komai kakeso zaka sameshi tunda har ka cikamin muradin
raina,iya wannan nasarar daka tabbatarmin ta isheni farinciki......wannan
yarinyar dake hannunku kadara ce.....kadara ce me girman gaske,kada kuyi wasa
da ita har sai kun samu abinda kuke nema"
"Na sani hajiya,daga adadin abinda muka fara tambaya
kuma muka samu tabbacin samunsu nasan munyi babban kamu,munyi kuma babban aikin
da zamu fita daga talauci har abada".
"Qwarai da gaske" Ta fada tana jinjina kai.
"Ina yarinyar take?" Ta buqata ganin amna,ba bata
lokaci ya juya kiran video call ya kuma haska masa amnar.
Tana ya
she tun sanda suka sheqa mata abun bata dawo hayyacinta ba. Baki ta tabe
"Wai wannan abarce zata cakuda jinina da nasu?....kuci
gaba da aliyarta.....tabbas sai na sanya sunyi nadamar hada hanya dani da kuma
sanina koda sau daya ne a rayuwarsu" Ta fadi tana dauke idonta daga kallon
amna.
Kiran ta
katse tana sake murmusawa,idanunta kan farfajiyar gidanta.
"Wannan wasan zaiyi dadin kallo.....zan samu farinciki
matuqa idan naje idanuna suka ganemin jigatar da ahalin alhj hamza sukayi
tsakanin jiya shekaran jiya da yau" Ta fadi a ranta,sai kawai ta fada
wanka.
A nutse
ta shirya cikin qasaitaccen lace,lace ne na alfarma da ita kanta a jininta
tasan ba qananun kudade fu'ad ya sanya ya siya mata shi ba.
Laluba
ma'ajiyar sarqunanta tayi,duka gold sun qare sai fashions masu tsada. Su ta
sauko ta zuba tsakanin hannuwanta wuyanta da kuma kunnenta,ta bade jikinta da
turare,ta kuma dauko tsadajjen mayafinta mahadin lace din ta yafa.
Tunda
tazo gidan taga yadda anni da musaddiq ke a birkice idanunta basu huta da zubda
hawaye ba,ba iyasu ba.....hatta saddiq dimma da hudan gaba daya. Sak gidan ya
koma musu kaman gidan makoki,sauqin abun daya duk an sallami kowanne baqo ba
tare da an bari ya fahimci komai ba.
Duk yadda
anni keji daga qarshe ita ta koma lallashin sabreen,wani irin abu takeji daya
kasa tsarga mata,qaqqarfan zato da zargi maras iyaka dake mata kai kawo,wanda
tayi imanin wannan karon komai ya kawo qarshe muddin ya tabbata abinda take
zato dinne.
Cikin isa
da izza take takawa zuwa ainihin babbar qofar parlor din. Iska take zuqa sosai
d'ai d'ai tana fesarwa. A yau jin kanta dama duniyarta sabuwa takeyi,a haka ta
isa qofar falon annin ta turata ta shiga tana rangada sallama da muryarta data
fita fes.
Sabreen
ce mutum ta farko data fara daga idanunta ta kalleta,fes ta zube mata kallonta
sanda maamah din ke takowa zuwa cikin parlor din.
Kasa motsa
bakinta tayi bare ta amsa mata sallamar,sai idanunta da suka zuzzurma saboda
kuka data kafeta dasu.
Anni wadda ke
zaune saman abun sallah bayan ta idar ce ta daga idanunta tana amsa sallamar.
A mamakance
anni take duban maamah dake takowa parlor din,ci gaba da dubanta anni takeyi
haka kawai tana jin wani yanayi daban yana shigarta game da maamahn.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 146
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
146
Murmushi ta
saki tana sake takowa da wani irin qarfi da conference,laushin da take gani iya
idanuwansu da fuskokinsu wani nishadi yake bata.
"Barkanku da wannan lokaci" Maamah ta fadi tana
yiwa kanta da kanta wajen zama gami da harde qafafunta guri guda.
Idanu anni
ta sake binta dashi,tana so tace mata ta tashi ta fita idan ba alkhairi tazo
dashi ba,tana so tace mata ta fita salin alin bata buqatar dogon magana,tanaso
ta gaya mata ta nesanta fuskarta daga garesu muddin ba zaman lafiya ya shigo da
ita ba......saidai kuma shi wanda bai sonka,ba'a ko yaushe ba,ba kuma a kowanne
lokaci bane kake bashi daman da zai fahimci wani yanayi da kake ciki na
matsatsi ko tashin hankali ba.
"Mun yini lafiya ameenatu?,ya taro kuma ya tashi?"
Maamah tayi maganar data bawa anni mamaki sosai.
"Lafiya alhmdlh" Anni ta furta tana tsareta da
idanu. Wannan sauyawar yanayin daga Mariya baiyi mata ba,wannan sanyin da nuna
kirkin gaisuwar bai gamsheta ba sam sam.
"To ai haka akeso,yayi kyau....Allah ya
maimaita.....nace ba fada me ya kawo gaba ameena?,ina cewa duk tsiya dai nice
mahaifiyar musaddiq,har abada kuma tuwo sunansa tuwo,babu me canza masa
suna......ace an tashi bikin d'ana na ciki na amma bani da masaniya?,haba
ameena,son kan naki ai yayi yawa,ko a 'yan Allah ya sanya alkhairi ai nazo
ko?". Idanu anni ta dauke tana maidawa wani guri. Ko daya bata tsinci wani
abu me ma'ana a cikin zantukan maamah ba,hasalima ciwon kai kawai zasu qara
mata ba wani abu ba.
"Yanzunma bata baci ba.....baki kuma makara ba"
Annin kawai tace da maamah.
Wani
murmushi maamah ta saki tana dan doka hannunta saman kujera,a nutse sabreen ta
sake kai dubanta wajen tana aje wata qatuwar ayar tambaya a kai,sai kuma ta
sake maida dubanta ga maamah din.
"To Allah dai ya kyauta,amma ko don gaba ya kamata a
dinga sanin matsayin kowa".
"Idan kin gama zaman don Allah mariya in zaki fita ki
rufe qofar parlor din" Anni da takejin ba zata iya ci gaba da zama tana
sauraren soki burutsun maamah ba ta fada,don bata da juriyar zama sauraren nata
a yau.
"Kwantar da hankalinki ameena......tafiyar zanyi don
banga alamun ana maraba dani ba.....amma na miki uziri,duk da cewa idan naqi
fita a gidanma banyi kuskure ba,wanda ya gina gidan daga jikin mariya aka ciri
halittarsa ya zama gudan mutum abun mora a yanzu" Ta fada tana sake
hakimcewa alamunta suna nuna bawai tafiya zatayi yanzu yanzu ba kaman yadda
tace.
Ko sau
daya anni bata waiwayeta ba,ta dauki abun sallarta tana wucewa ciki.
Daga yadda
take bin anni da kallo tana sake sakin faffadan murmushi ya isa ya gaya maka
cewa batasan da wani mutum daban cikin falon ba. Wani abu daya sake qarfafawa
sabreen dukka wani zargi da tunaninta a kanta.
"Dariyarku takan zam kuka gaba,da nadamar me qin
gaskiya......" Furucin da ya fusgi hankalinta kenan,ta maida dubanta
sashen da sabreen ke hakimce qafa daya saman daya.
Wani
zazzafan duba take binta dashi,wani mayunwacin kallo me dauke da tarin
ma'anoni,wani irin kallo dake da wani irin zafi.....kallo ne na kota
kwana,kallo ne na ko a mutu ko ayi rai da wadannan fitattun idanun nata masu
zafi da basu da sauqi ko kadan.
Kallo
kallo akayi tsakaninsu na wani mintuna,cikin jinin jikinta maamahn ke jin bata
aminta da wannan kallon ba. Wani kallo ne da tafi kowa saninsa......tafi kowa
kuma sanin ma'anarsa......tafi kowa kuma fahimtar yaren dake cikinsa.
"Akwai wani yare da ba kowa yake fahimtar sa ba sai me
matsanancin hankali......akwai wani juyi da idan ya tashi juyawa yake watsi da
dukka wani abu dake kusa dashi ko nesa dashi ma......." Ta fada tana juya
idanunta sannan ta sake maidasu ga maamah
"Na jima ina gurnani......na dade ina gargadi.....na
dauki lokaci inata jirwaye me kama da wanka......amma inajin cewa lokacin yin
wankan gaba daya yazo don a batad da sahun wannan jirwayen.....jirwayen dake
cutar da farar tufa yake nakasa kuma lafiyar jiki......gargadi na qarshe da
bazan sake irinsa ba.....saidai fallasa ya biyo baya.....ruwan kura ne ta fiddo
ajiyayyen naman data aje....don kuwa yafi qarfin bakinta,kalar nama ne da bai
ciyuwa a gareta kasancewarsa me dauke da wata babbar guba.....a wannan karon
lokutan bada damar gaba daya awa biyu ne kacal....do or die" Tsam ta miqe
daga kujerar da take kai still idanunta akan maamah da wani zazzafan kallo tana
wucewa ciki itama.
Haka
kawai kowacce gaba ta jikinta tayi wani irin sanyi,bugun zuciyarta ya dinga
qaruwa da wani tsoro da batasan daga inda yake ba.
"Kada fa maganganunsa su tabbata.....kada fa lokacin da
yake maimaitamin ne yazo" Take fadi a Karan kanta tana jin wani irin
razanannen yanayi yana ratsata.
Fes
maganganunsa suke ratsata kaman a sannan yake furta mata su,tsoro ta sakejin ya
saukar mata,ta miqe da zummar barin falon sai taji jikinta ko ina ya dauki
rawa. Qoqarin daidaita kanta takeyi,batasan wacce irin matsoraciya ta koma har
haka ba,batasan dalilin da ya sanya take yawan samun rawar jiki ba idan tashin
hankali ya durfafeta(badai.baki yarda baki da hawan jini ba?).
"Ita din ba komai bace.....ba zata iya aikata komai ba
don bata da hujja" Abinda zuciyarta ta shiga maimaita mata kenan,abinda
kuma yadan bata nutsuwa 'yar kadan,saidai ta gaza samun irin nutsuwar da take
da buqatar samu.
K'arfe goma
na dare daidai take takawa a harabar gidan tana nufar motar da fu'ad ke zaune a
ciki yana jiran ta qarasl su wuce gida.
Ta madubi
ya hangeta,sai ya ajiye wayarsa da system din daya wuni dasu yana aiki ya bude
motara a nutse ya fito ya bude mata qofar yana jiran ta qaraso.
Tun bata
qaraso din ba ya karanci baqon yanayi a tare da ita,yadda yasan sabreen dinsa
ba haka take ba,duk da yasan dole akwai damuwa da dukkaninsu suke a cikinta,
Baice komai
da ita ba har ta qaraso,ta shiga ta zauna ba tare da tace masa komai ba,wannan
ma ya bashi mamaki,don komai runtsi.ba haka ta saba yi masa ba,sai ya rufe ya
zagaya ya shiga yana bada umarnin tashin motar.
Hannunsa
ya miqa mata,ta dubeshi sau daya ta miqa masa nata,sai ya jawota jikinsa ya
rungumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya.
"Ina cikin matsi da tsanani sabrrrr,bana cikin
nutsuwata da walwalata.....please karki bari ki wanzu cikin damuwar nan
kema,domin ke kadai ce kika ragemin da zan samu sassauci da ita".
Tausayinsa yayi tsananin tsarga mata,yana tare da abu mafi hadari da muni ba
tare da ya sani ba.....yana tare da halitta mafi zamewa rayuwarsa barazana ba
tare da yasan da hakan ba.
"Zamu kasance tare cikin tsanani da sauqi......zan zame
maka garkuwa alqawari ne wannan,your battle is my battle.....we fight
together".ta qarasa fada tana matse hannunsa da kyau cikin nata. Sosai
maganarta ta sake bashi nutsuwa,yadda ta sakashi a jikinta tana qoqarin bashi
dumi daga dumin jikinta ya tattaro hankalinsa dake son kaduwa waje daya.
"Thank you duniyata" Maganarsa ta qarshe kenan
shuru ya biyo baya.
Samansa
kawai suka haura shi da ita,don gaba dayansu ba wani me cikakken kuzari. Yana
ajiye wayoyin da yaketa dakonsu tun kiran jiya wayar farouq ta sake kadawa. Da
wani hanzari yakai dubansa ga wayar. Number jiya ce,don already ya riga yayi
marking nata,da wani irin zafin nama ya jona komai yana qoqarin turawa team
dinsa saqon kartakwana don buqatar kasancewarsu dashi koma saman minotti sofa
dinsa ya zauna yana aza kafatanin hankalinsa akan komai. A hankali ta samu
kanta da dawowa da baya,ta samu hannun sofa din da yake kai ta zauna tana jin
'ya'yan cikinta suna curewa waje daya.
"Mun sake kiranka a karo na biyu,kiran kuma da ba
lallai muyi na uku ba,zamu gaya maka inda zaka ajiye mana wannan
kudin....."
"Ni kuma a ina zan karbi qanwata?" Ya tambayesu
muryarsa a tsaye. Ya gama shirya komai,a yanzun bawai lallabawa yake buqatar
yayi musu ba,ko na bayan dama akwai gacin da yaso ya cimma shi yasa ya biyo ta
sigar lallami,a yanzun kuwa dole ya canza hannu ya gani ko zai samu kaiwa ga
wannan matakin.
"Au maganar karbar qanwarka ma kakeyi?.....muna maka
maganar kudin aikinmu?".
"Wanne aiki kenan kukayi?" Ya tambayesu cikin
salon rainin hankalin da yana sane ya tsiro dashi.
"Lallai kana buqatar mutuwar qanwarka a wulaqance kenan
a hannunmu".
"Da na sanya kunyi nadamar haihuwarku da iyayenku
sukayi,dana sanya kun gane duniya sashe biyu gareta". Shuru ya ratsa
tsakani kafin yaji an danqaro ashar
"Kuna tunani kuna da qarfin kudin da zaku iya kamamu
ko?,to zamu nuna muku kudinku bai isa ya saka muzo hannu ba.....don ita kanta
wadda ta bamu aikin me kudin kanta ce....kuma tana da nata ikon da ko kamamu
kukayi din a dole zaku sakemu".
"Au Allah?,amma ta kasa baku kudi wadatattun da zaku
rayu?,saita hadaku da aikin wahala aikin kidnapping?".
"Bayau muka fara mata aiki ba.....kuma wannan bazai
zama na qarshe ba,ko ta bamu ko bata bamu ba sana'a mukeyi,kuma ba zamu fasa
ba...koda ita ko babu".
"Koda ita ko babu din kuwa daga wannan karon ba zaku
sake zaluntar kowa ba.....daga wannan lokacin kun daina aikin ashshsha"
"Kaga dakata malam!" Ya daka tsawa daga daya
bangaren,tsawar da har sai data sanya fuad lumshe idonsa sannan ya budeshi,yana
ji a ransa inama ce gaba da gaba suke da wadannan qananun 'yan iskan.
"Bama doguwar hira da kowa faruqu kake ko wa?,kuma ba
zamu fara a kanka ba.......ka kawo kudi ko qarawa qanwarka tsahon kwana....ko
kaqi muyi kaca kaca da namanta kaman yadda hajiyarmu ta buqata daga nan zuwa
wayewar gari"
"Kuyi duk yadda kukeso" Ya fadi yana tsinke kiran
don ya kwashi mintunan da yakeso.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 147
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
147
"Ya
zakace musu haka?,ya zakayi haka hamma?" Sabreen data barke da kuka cikin
rawar jiki ta furta,sabreen din da baisan da zamanta a wajen ba sai a sannan.
"Ba zasu aikata ba.....kudi sukeso,sunsan kuma kudi ba
zasu karbu ba muddin suka tabata......sai hajiyar da....." Cak ya dakata
da maganar yana nanata sunan hajiyarsu da suke fadi.
"Hajiyarsu.....kasan wacece hajiyarsu?" Sabreen ta
fada tana miqewa tsaye cikin wani birkitaccen yanayi. Gaba daya ji takeyi tayi
loosing duk wani control nata da tunaninta......tana jin komai yazo
qarshe,komai yazo gaba.....tana jin ko na minti daya ba zata sake iya ci gaba
da rufe sirrin matar nan ba,duk wani signal ya kama ya kuma nuna
kanshi......sannan ya bayyanar da komai da komai.
"Nace kasan wace hajiya suke magana akai?" Ta
maimaita tana ware hannayenta gami da fiddo idanunta waje kaman wadda ta zare.
Bata jira amsarsa ba ta dora.
"Ba kowa bace sai MAAMAH!" ta fada da wata irin
tsawa da bata tashi tarwatsewa ba sai a tsakiyar kunnen fuad da wani irin
nau'in mafi munin sauti.
Idanunsa
da yakejin sun masa nauyi ya aza akan fuskar sabreen da wasu manya manyan
alamun tambaya a kansu.
"Maamah?" Ya maimaita sunan da salon tambaya.
"Eh maamah.......maamah itce ya dauke amna.....maamah
ita ta saka a dauke amnah!" Ta sake fada kuka me qarfi yana kubuce mata.
Daga zaune
da yake amma sai yaji kaman duniya tana zpagayawa ba daidai ba......kaman akwai
wasu sautuka da abubuwa da suke tafiya ba daidai ba.
"Kinsan me kike fada sabreen?....maamah fa?.....rashin
imani da qeqashewar zuciyarta har......" Bata jirashi ya qarasa ba wani
sashe na zuciyarta ya soma gaya mata cewa,kariya yakeson bata,qaryatata ita
kuma yakeso yayi.
"Abun nata baikai haka ba ko?,haka kake zato?.....kana
ina sanda ta tursasamin aurenka don kawai ta mallakeka......ta tsundumani a
rayuwarku don kawai na zama silar mallakarka gareta ta hanyar yin garkuwa da
'yan uwana......ta sanyani a kwanaki mafiya tsaho da tashin hankali a
rayuwata?......kana ina a sanda ta sake diban qannena ta riqesu don ta samu
damar cimma burinta a kanka da kaina......ta tirsasamin lallai saina shayar da
kai na kuma ciyar dakai da asiri?.....na tufatar da jikina da rigar da zata zama
silar soyayyarka a gareni?.mashkur......dama sauran wadanda suka kawowa
rayuwarmu farmaki kina tunanin yin kansu ne?.....fareeda data samu nasara a
kanka kana tunanin haka siddan ta sameta?......." Dora hannunta tayi saman
matashin cikinta.
"Hatta da wadannan yaran da basuzo duniya ba kana
tunanin sun tsira a hannunta?,banda kiyayewar Allah zuwa yanzu lissafin watana
nawa da barinsu akeyi.........ka duba wannan" Sai ta ciro wayarta daga
handbag dinta tana bude masa inda ta adana videos dinnan da sauri sauri ta
dangwarar masa ta juya da sassarfa tana fita a parlor din tana sauka qasa.
Wayar yabi
da kallo yana jin yadda jijiyar kansa ke wani irin harbawa. Yanajin kira na
shigowa ta wayarsa dama system din gabansa,wanda ya tabbatar team dinsa da suke
bincike tare ne suke kiran nasa,saidai baida wani kuzari ko kadan.
Hannu ya
sanya ya dauki wayartata,ya kuma bude video din da ta ajiye masa. Murya da
komai ya fita tassss.....baya buqatar neman qarin bayani,sai kawai yayi
connecting wayar da system dinsa,ya shiga aikin duba ingancinsa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Yaji yana
maimaitawa bakinsa yana rawa. Duk da ya jima yana hasashe.....ya jima yana
kwana yana kuma tashi da tarin tulin lissafin meye da meye maamah zata iya
aikatawa dama wanda ba zata iya ba?,amma sai ya samu kansa da jin komai sabo a
tattare dashi.....sai ya samu kansa da jin komai ya zame masa baqo.
Kaman wanda
aka yiwa allurar qaimi,sai ya zabura,ya hada connection da kowa dake cikin team
dinsa suka fara aiki akan kiran mutanen. Koda kowa ya gaji....koda kowa yana
ganin dare yayi a barwa safiya,shi bayajin zai iya hakan......baya jin akwai
abinda zai dakatar dashi daga lalubo maboyarsu daga daren nan zuwa
asubahi......baya buqatar a wuce haka.
Sanda
ake qwala kiran assalatu na farko signal ya harba sosai,kai tsaye kuma ya basu
daidai direction na inda network da layin yake motsawa.
"Alhamdulillah" Ya furta yana zarar wayarsa da
sauri. Jordan ya soma kira yace ya yiwa su abdulgafar magana......su hadu
yanzun a masallaci zasu fita ana idar da sallar asubahin.
Sai daya
tabbatar ya gama hada komai sannna ya miqe yana nufar toilet. Yadda yakejin
jikinsa kaman yana dab da kasa responding komai......amma ya gayawa kansa sai
ya qarasa aikin daya fara,don haka ya hada ruwa me zafi yayi wanka. Cikin baqin
shirt da wando ya shirya,ya jawo wani boots dinsa ya saka yana dora baseball
cap a kansa. Duk wani abu da zai buqata ya hada a back pack ya rataye,ya maida
baqin eyeglasses a idanunsa sannan ya fara saukowa a gurguje.
Har yakai
parlor din farko wani abu ya fusgi zuciyarsa,sai ya koma da hanzari yana dosar
dakunanta. Bai sameta asalin dakinta ba,sai a daki na biyu ya sameta.
Qudundune
ya sameta cikin duvet,da alama baccin me jima da saceta ba,don ga cups nan da
plate da tayi amfani dashi da sauran ruwa. Har ya qarasa gabanta bata motsa
ba,alamu sun nuna baccin daya dauketan me nauyi ne. Saman kanta ya tsaya yana
duban kyakkywar Fuskarta,wani matsanancin tausayinta ya saukar masa,ya tsugunna
a tausashe ya sauke mata kiss a goshinta don baiso ya tasheta,ya miqe a hankali
ya maida hankalinsa ga dakin.
Plates din
ya soma tattarewa da cups din,murmushi ya kubce masa. Da gaske ciki yana canza
hali da dabi'a,matar da daqyar sai yayi fama da ita take cin abinci,yau itace
anywhere anyhow kama abinci take bada wasa ba.
"Allah ya qara lafiya" Ya fada yana ficewa dasu ya
kaisu kitchen sannna ya fice daga gidan.
Cikin
dukkanin shirin daya kamata suka gewaye area din kafin su sanya kai zuwa
ainihin inda na'ura ke basu direction a kai.
Cikin qasa
da minti biyar suka nannade qofar gidan suka nadeta tsaf da wani irin qarfe.
Sake
kutsawa sukayi da wata irin sassarfa suna bada sanarwar suna qarqashin kamen
hukuma,kada kuma wanda ya motsa a cikin su.
Tun kafin
sukai ga qarasowa ciki sukayi surrender,ba yau suka fara irin wannan aikin
ba,saboda haka sun tabbatar da cewa sun riga sun kamu,tunda kuma suka kai ga
cimmasu har inda suke lallai ba makawa basu da sauran wani qofa na fita.
Qoqarin
dakatar da fu'ad sukeyi wanda shine na gaba sanda yake qoqarin doke qofar
dakin.
"Sir......it may b......." Bai iya bari sun qarasa
ba ya yiwa qofar wata Kyakkyawar duka data sanyata bude kanta da kanta.
Bindigarsa ya saita akan mutum na farko dake tsaye kafin sauran suma su saita
ragowan na dakin. Ya jima da koyar harbi da bindiga,ya kuma mallaketa da
license dinta da komai saboda dalilai na tsaro,amma ba kowa bane yasan da
hakan.
"Kowa ya cire abinda yake jikinsa,bindiga ko wani qarfe
ku zube a nan" Shugaban tawagar ya fada yana daka musu tsawa. Jordan ne ya
soke tashi bindigar sannan ya fara zagayasu daya bayan daya cikin qaqqarfan
takun nan nasa don tabbatar da kowa ya cire komai dake a jikinsa.
"Hamma....." Muryar amna ta daki kunnensa da wani
irin sauti galabaitacce.
Idanunsa
ya daga da zafin nama yana maidashi inda sautin yake. Amna ce ke takowa a
hankali jiri yana kwasarta daga wani daki dake cikin babban dakin. Maida
bindigarsa yayi da wani mugun zafin nama yana dosarta,wanda baikai ga isa ba
qarar sautin bindiga ya tashi a dakin.
Cikin
tsarewar ubangiji ya bashi ikon kaucewa ya kuma ture amna ya wuce ya bula bango
ya nutse a ciki. Cikin qasa da second biyu Jordan ya masa wani irin duka,ya
kama hannuwansa ya murdesu ya maidasu baya ya karbi bindigar,sannan ya daki
gwiwarsa ya zube a qasa.
"Zakasan kayi mistake........idiot!" Jordan ya
fada cikin tsananin fushi yana masa wani mummunan dauri.
Amna ya daga
da hannu bibbiyu,ya cire rigar daya dora daga saman rigarsa yana yafa mata
saboda yadda take gayarta haka,ba dankwali bare mayafi. Wani irin zafi
zuciyarsa takeyi,ya riqe amna da kyau suna takawa kafin ya kalli jordan
"A yau nakeso su fadamin waye ya sanyasu wannan aikin,a
yau basai gobe ba!" Ya fada da tsananin zafin zuciya.
Yau din ta
koma masa lovey dovey dinsa,ta koma masa amnansa sak ta shekarun baya,ta mance
da wani surukuta a tsakaninsu,ta lafe kanta saman kafadarsa tana rera kuka.
Ita kadai
tasan ya takeji a zuciyarta da qirjinta,nata duka me sauqi ne,tana tausayin
fu'ad ne a sanda sakamakon binciken ya fito sunan MAAMAH ya zama suna na farko
cikin wadanda suka assasa dauketa. A baya wani tsoron matar takeji......a
yanzun kuwa sai zuciyarta gaba daya ta qeqashe a kanta. Tayita kwanciya ne
bayan ta farfado saboda tsoro,saboda tanason ta tsira da mutuncinta. Tana
tsoron ta nuna musu ta warke batasan meye next step nasu ba.
Maamah tayi
waya dasu har sau ba adadi......taji kuma muryarta ta sake tabbatarwa da cewa
tabbas din itace. Abun ya matuqar bata mamaki ita kanta,ya kuma girgizata.
"Wacce irin zuciya ce a qirjinta?" Ta tambayi
kanta da kanta a mamakance.
Wani abu me
zafi da tauri ya dinga hadiyewa,kai tsaye ya bada umarnin wucewa da amna
asibiti don a duba lafiyarta.
Kasa zama
yayi ko tsaiwa waje daya,yana jin kaman ya sanya kai dakin da likitoci suka
rufu a kanta suna checking dinta. Bashi da wani qwarin gwiwar sanarwa kowa an
samu amna din har sai ya tabbatar da cikakken lafiyar amnan,har sai ya tabbatar
da cewa ta kubuta da mutuncinta da lafiya da kuma cikakken hankalinta.
A qalla sai
da suka kwashe awa guda kafin su fito,cikin lallashi Dr aswad yace mishi.
"Karka damu sir.....komai nata lafiya yake,ba wani abu
daya sameta,saidai jikinta da yayi weakening saboda hodar cocaine da suka shaqa
mata me yawa.......but shima idan tasha ruwa sosai jikinta zai koma normal in
sha Allah".
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya maimaita
yana jin zuciyarsa tana quntata. Cocaine kuma?,abar da yayi imani ko a ido aka
ajiyewa amna ita ba zatace gata ba.
Dakin ya
koma,tana kwance tana bacci,ruwan da suka saka mata saboda samun qarin kuzari
yana shiga jikinta. Wayarsa ya laluba ya fara kiran number abba.
Daidai
lokacin yake rufe shafin alqur'anisa,inda yakai qarshen suratu yaseen daya
dauki gabarar karantata tunda abun ya faru sau wani adadi. Ya samu wannan
sirrin daga bakin malam,wanda fu'ad ya raba kudi sosai aketa addu'a da kuma
roqon Allah akai.
Bismillah
yayi sanda yaga kiran daga fu'ad ne.
"Abba......an karbo amna,lafiyarta qalau
alhamdulillah,amma muna asibitinmu tana dan shan drip saboda jikinta ba
qwari"
"Allahu akhbar......alhamdulillah.....tabbas ubangiji
yayi gaskiya da yace ku roqeni zan amsa muku,Allah kaine abun godiya,sannu sa
qoqari muhammadu.......inajin bazan shaida musu ba sai wannan drip din ya qare
tukunna ta farka,ni zan taho,kafin sannan ina sanya ran qila ta farka".
"Hakanma yayi abba" Ya furta yana katse kiran.
Farouq ya kira da temporary line din da yake using nashi a kwana biyun.
Kalamansa dukka irin na abban ne......saidai ya cika da mamakin abinda ya sanya
fu'ad ya tunkari gagarumin aiki irin wannan bai gaya masa ba.
"Ba lokaci dude.....na matsu na dawowa da anni
autarta....besides ma waye zaiyi gangancin dauko ango ya sanyashi a hadari irin
wannan bayan bai gama tantance ma zaqin duniyar daya shiga ba?" Murmushi
ya sanya dole farouq din ya saki,sai ya yanke kiran shima murmushi yana subuce
masa.
Saidai
kuma cikin qanqanin lokaci murmushin ya tsaya masa cak,yaji gabansa yana
faduwa,sai ya sake lalubar number wayar CP.
Dab da
zata tsinke ya daga,yayi apologizing na fu'ad.
"Ba komai.....nace zaiyuwu zuwa nan da azahar na zauna
da dukka mutanen nan?".
"Yes sir......zai yiwu,a gida ko a nan?".
"If possible akaiminsu gida,zanwa abdulfattah waya ya
bude musu masauki.....waccan dayar matar dake wancan gidan....me take da suna
ma?"
"Bibo ko.....habiba mu'azu"
"Yes......itama a daukota,a hadamin ita a cikin
su".
"Okay in sha Allah" Ya fada suna yanke wayar.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 148
*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada
munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR
GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN
HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road
kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a
duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
148
Ba
jimawa sai ga abba,shigowarsa kenan farouq shima ya shigo,abinda ya sake zaunar
dashi suna tattauna yadda abun ya kasance.
"Amma don Allah me babban suna......zuwa yanzu ya
kamata ka daina tunkarar abubuwa haka kai tsaye,bakai kadai bane yanzun kaman
baya daka saba abunka gaba gadi,yanzun akwai nauyi akwai iyali da suka dogara
dakai".
"In sha Allah abba" Ya fada ne kawai,amma bayajin
akwai wani abu da zai hanashi sadaukarwa da iyalinsa ranshi da lafiyarsa muddin
yana raye din.
Lokaci ya
duba,bayason ya saba magana idan ya yita,don haka ya miqe yana duban abban.
"Abba zanje gida....don sanda na fita tana bacci
ne,yanzun haka nasan tana can da tunanin inda naje da kuma inda amna take"
"Maza ka koma kayi mata albishir,ubangiji yayi muku
albarka,ya kareku daga dukkan sharrin zamani.....ya tsare gaba"
"Ameen abba" Sai ya juya ga farouq yana bashi
hannu,shima bashi yayi sukayi musabaha suna duban juna,a tare a kuma lokaci
daya murmushi ya subucewa kowannensu. Farouq ya gode Allah da abba yake a
wajen,ya tabbatar da sai fu'ad ya taba masa iya shege komai qanqantarsa.
"Ka gayawa su musaddiq saisu dauko anni tazo ta ganta
itama hankalinta ya kwanta"
"In sha Allah oga" Harara yadan balla masa,yasan
da biyu ya fadi kalman oga din,sai ya juya yana fita a dakin.
Tunda ta
farka daga baccin takejin ta samu sassaucin qunci da bacin ran da takeji. Kai
tsaye daga gadon kitchen ta wuce saboda yadda yunwar data tasheta a baccin ke
neman sabautata. Koda ta duba agogo sai taga ashe ta zarta lokacinta ne. Tana
cin abincin tana sake sallamawa lamarin ciki,tayi imanin banda cikin a yanayin
da take ciki a yanzun ba abinda zai sanya ta iya sakawa cikinta abinci.
Tsaf ta
cinye ma'u na satar kallonta.
"Ko a qara miki?" Kai ta girgiza.
"Doughnuts dina kawai nakeso......ya qare ragowan na
cinye yanzu da tea,don Allah ma'u ki sakamin order,kwali sha biyu nakeso"
Ta fada tana goge hannunta da towel jikinta sam ba wani kuzari sannan ta juya
tana fita a kitchen din ma'u ta bita da kallon mamaki.
Eh dole ace
ciki yana saka wasu hauka,batasan ya zatayi da doughnuts kwali goma sha biyu
ba,doughnuts din matar da madarar ciki kawai ta isheka ta sanya kaji ka qoshi
koda kuwa rabin guda daya kaci,ba qaramin jarumi bane wanda zai iya cinye guda
uku ba,komai cinka kuwa idan har kaci ukun nan ba sauran space nacin wani
abincin saboda ka gama qoshi.
"Allah ya raba lafiya" Ma'u ta fada tana jawo waya
ta soma lalubar number wayar maman ummee kada a samu akasi.
Wata
lafiyayyar kasala ta saukar mata,sai kawai ta yada zango saman sofa din falon.
Zuciyarta na cike da mamakin yadda bataji motsinsa ba ko kadan......hakanan
kuma bataga alamun ma ya nemeta ba.
"Kodai da gaske yana shirin rejecting maganata da kuma
qaryatani kaman yadda mamansa tasha shan alwashin hakance zata faru?"
"Ga alama kuwa.....ya fara doubting akan abinda kika
fada". Fada ne ya kacame tsakanin sassan zukatanta guda biyu,daga qarshe
taja qaramin tsaki,ta jawo landline ta soma neman number gidan anni saboda tata
wayar a hannunsa ta barta.
Daya daga
cikin masu aikin ce ta daga,cikin girmamawa ta gaida sabreen.
"Hadani da huda ko.nadra ko haneefa"
"Okay maa" Ta amsa mata a ladabce. Dukkaninsu ta
kawo mata,suka bata lokaci sosai suna hira kafin suyi sallama.
Daki ta
koma donyin wanka,sai a sannan ta lura an kwashe duk wani datti kwanuka data
zubar. Mamaki yadan kamata,amma saita samu assurance na shine ya shigo din ya
fidda kayan.
Tsaf ta
gyare dakin,ta wadatashi da qamshi daya qarawa dakin wani irin sukuni da
nutsuwa,sannan saita wuce tayi wanka. Tsaf ta shirya cikin wata chiffon gown
maras nauyi,ta lalubo Malaysian hijab ta saka sannan ta fita.
Kaman ba
zata haura saman nashi ba amma ta daure. Tasan bai kamata ta barshi haka bata
gyara ba,kaman yadda bai kamata ta bari wani ko wata su hau ba.
Tsaiwa
tayi tana qarewa parlor din kallo. Komai yana nan a zube inda yayi amfani
dashi,da alama ma a nan parlor din ya kwana,saita taka tana tattareshi tsaf,ta
kuma sanya vacuum cleaner ta tsaftace saman dukka ta gyare masa toilet din.
Sanda ta gama azahar ta kawo jiki,cikinta kamar an mata yasa,dole ta sauko
dining din qasa neman abinci.
Tunda
lalurar nan ta kamata ma'u ta haddace,bata taba barin dining din wayam ba
komai,kaman yadda bata barinta ta dawo sake cin abinci ta samu maimaici.
A nutse ta
zauna ta zuba da nufin soma cin abincin amma kuma sai taji ta kasa. Azahar ta
sako jiki sosai,ina yaje?,abunda tun fara shaquwarsu bai taba faruwa ba.
Ta juya
abincin har batasan sau nawa ba amma ta kasa kaiwa bakinta,kaman ahakan ake
jira ya faru sallamarsa ya ratso parlor din.
Duk da
hautsine yake amma kallo daya tayi masa shigarta taji ta burgeta ta masa mugun
kyau. Baqi da baqi a jikin fari,saidai duk da hakan saita wani basar ta dauke
kanta tana amsa masa sallamar tan jira taga da wanne irin yanayi ya dawo gidan.
Tsam ta
miqe sanda taji alamun takowarsa nan dining din,ta tura kujerar tana nufin
wucewa,saiji tayi anyi mata wata Kyakkyawar damqa na tare da bata lokaci ba
kuma ya mata wata Kyakkyawar runguma da ta sanya qamshin turarensa mai matuqar
sanya nutuswa isa ga hancinta.
Saman
wuyanta ya aje fuskar ta,kullum alfahari yake d wannan qamshin nata da yasha
banban dana kowacce mace.
"Kina bisa wuyana oum triplets......a yafemin,na leqo
kina bacci,banaso kuma na katse wannan daddadan baccin nan.....yaya babies
dina" Ya fada yana zamewa ya duqa a gabanta yana yaye rigarta.
Maganganunsa daya saba yi da cikin nata yayi da nufin da yaransa yake
magana,ta dauka zai tashi kaman yadda ya saba,sai kawai ya jawota yana
tsokanarta ta cibiyarta. Janyewa tayi da sauri ya saki dariya.yana miqewa.
"Anga amna"
"Serious hamma....serous?" Girarshi ya dage
mata,saita sauke ajiyar zuciya tana fadin
"Alhamdulillah alhamdulillah.....please hamma"
"Bani hug daya kawai ya isa tukucin yi miki
albishir......tausar dare kuma itace tukucin kaiki wajenta"
"Zanyi hamma zanyi wallahi" Ta fada tana dan
qaramin tsalle. Riqeta yayi da kyau yana duban tsakiyar idanunta,da wata
muryarsa can qasan maqoshi yace.
"Bi a hankali.....yarana" Ya qarasa fada yana dora
hannunsa saman cikinta. Kunya ta kamata,ta kuma sanyata janye idanunta da
sauri,daidai sanda kira ya shigo masa.
Bai fasa
sakata a jikinsa ya matseta ba sannan ya amsa wayar da cp ne ya.kirashi.
"Thank you.....gani nan fitowa" Sai ya katse wayar
yana dubanta.
"Zanga baqi my world.....zan dawo shortly in sha
Allah....ki kulamin da kanki" Ya fada yana kissing kuncinta duka biyun ya
juya yana fita farfajiyar gidan.
Daki ne
yalwatacce da aka shimfideshi da lallausan carpet milk color kaman kalan
labulayen dakin.
Daga
damansa bibo ce ita da zuwaira,sake maida dubansa yayi ga gabansa,mashkur ne
shi da dan uwan tasa ta'asar.....mashkur din da gaba daya ya fita a
hayyacinsa,tsufa sosai ya kamashi,wani irin tsufa na qarfi da yaji wanda
wawulonsa ya sake tsananta munin abun.
Sauran duka
ya bisu da kallo,amma kowannensu munin fuskar mashkur ta zarta munin da yake
gani a fuskokinsu,bawai muni na fuska kawai ba.....aaah muni na zuciya.
Ma'aikatan
gidan jaridar ya fara nunawa.
"Wadannan na gama da case dinsu......aje a hadasu da
diyar ambassador......ranar shiga kotu a hadosu tare qarqashin shari'a guda
daya,lawyer na zaiji da komai".
"Wayyo Allah.....mun shiga uku,don Allah sir kayi mana
afuwa ka yafe mana,wallahi bamusan a kanka tace a buga labarin nan ba".
Wani banzan kallo yayi masa.
" Okay,idan wanine bani ba kenan zaku iya tozarta masa
iyali,idan wani ne bani ba kenan zaku iya wulaqantashi ku wulaqanta aurensa da
shaidar zur.....CP.....bana son sake jin muryarsa a nan wajen" Ya fada
yana takawa ya jawo wata kujera.
Kiiiii ya
ajiyeta gaban bibo wadda jikinta ketsa tsuma,ya koma ya zauna sosai yana dora
qafarsa daya kan daya.
"Nutsu sosai.....labari zan baki sannan na
sallameki".
"To....to Allah yayi albarka".
" Ameenatu ahmad sabreen takai budurcinta gidan
mijinta,wanda ni Muhammed fuad jadda na karbeshi da kaina....kuma mutanen dake
rayuwa damu suka shaida hakan a lokacin". Dif wuta ta daukewa bibo duk
yadda takeji da tsageranci sai taji maganar ta girmeta.
"Ke din uwace ko?,a kamatance bai dace na gaya miki
haka ba ko?,saidai kash.....nidin bana yafiya bana kuma ragayya ga duk wanda
yace zai taba rayuwar duniyata.....sabreen,a inda kuma aka samu akasi
shine.....tuntuni kika sanya qafa kika take wannan girman daya kamata ki
samu......to ina me!miki albishir.....sabreen takai bantenta......ba wani
matsiyaci ko lusarin daya samu damar tsallake wannan shingen......yadda kika
dinga yada jita jitan mutuniyar banza ce......na baki dama na biyu kisan yadda
zaki wanke wannan sunan daga kanta....ki maida gurbinsa da kyakkyawar
shaida,idan hakan bata kasance ba kuwa,a karo na biyu idan na daukoki batar
dake zanyi bat.....a bude mata ta tafi gida". Bata tsaya tunani ko
waiwayen tazarar nisar tafiyar da zatayi a qasa,ba tare da abun hawa ko kudin
mota ba ta fice,tunda har ta samu nasarar shaqar iskar 'yanci kuwa......bataga
abinda zai hanata hada lecture din wayar da kan al'ummarta kan muhimmancin
mutuncin da sabreen ke dashi ba.
Idanunsa
ya ware akan mutum uku.....mutum ukun da yakejin laifinsu yafi na kowa girma,ya
sake aza idanunsa akan zuwaira wadda daga ita har bibo sunyi wani zuzzurmawa.
Duk da ajiya ce kawai akayi musu irin ajiyar da take daidai da aljannar kare.
"Kamata yayi kema a hadaki da wadancan.....sashen
manyan laifuka ko?..." Kuka ta fashe dashi tana hurwa tana neman agajinsa.
"Ki rufen baki,don duk yadda raina yakai ga baci bazan
iya zabgawa fuskar dakeda furfura mari ba,koda furfurar ta banza ce" Gum
ta koma tayi sannna ya bude idonsa yana sake dubanta.
"Kina gidana kina qarqashin inuwata amma kina neman
hanyar da zaa shigo a keta haddin iyalina?!.....abu guda ya rage miki ki
gayamin......waye ya sanyaki boyesu a dakinki kika fiddosu da dare zuwa sassan
matata!!!". Wata bahaguwar tsawa daya sauke mata sai data tattara gudawa
me yawa a cikin mashkur,ya rasa wanne.ibtila'i da bala'i ne yake hanashi furta
masa sunan.matar kowa ma ya huta?,fatansa daya wannan tsohuwar ta kira
sunanta,wataqila ko kwatance da ka yayi akan shima ita ta dauki.nauyinsa duk da
akwai nasa shirin.
"Mmm.......maamah ce" Sunan ya saukar masa cikin
ba zata. Fuska ya yamutsa yana dubanta.
"Wacce kenan?"
"Hajiya maamah.....mariya mahaifiyarka" Komai ya
tsaya masa na wasu daqiqu,sai daya koma daidai kuma kwanyarsa ta cika da wasi
wasi.
"Cp.....janye matar nan,a hadata da wadancan
mutanen". Kallo daya ya yiwa mummunar fuskar mashkur,wadda ta jima da
tashi daga kyakkyawa zuwa asalin mummuna.
"Mariya ce nima!.....maamah ake ce mata" Ya fada
da sarqaqqiyar muryarsa da bata fita yanzu tartar saboda fitar haqora sha biyar
daga bakinsa.
Kaman ya
dauki takobi ya jefeshi dashi haka yaji,duk wani jini dake jikinsa yaji yana
neman daskarewa,kwanyarsa kuma tana shirin yi masa formatting da karan kanta
irin na kota kwana,saidai kiran wayarsa yaso maida komai muhallinsa,ya daga
kiran bawai don yana gane waye ke kiran nasa ba yana komawa kaman wani
shashasha.
"Jordan ne sir.......sir an jona musu na'urar fidda
bayanai cikin sauqi,sun kuma yi bayanin komai...."
"Me aka samu?" Ya tambaya cikin sarewa da jin
komai.
"Am sir.....kayi haquri.....gaskiya bayanansu na qarshe
kaman na'urar ta samu matsala.....sunce zaa sake bincikawa"
"Jordan please tell me.....ka gayamin ko waye ya
sanyasu.....bana buqatar jinkiri a daidai wannan lokacin".
"Sir....sir" Sai ya kama inda inda.
"Tell me nace!" Ya fada a tsawace.
"Mariya......mariya ce maamah". Iya abinda fuad
yaji kenan wayar ta sulale daga hannunsa ta fadi qasa.
Bai sani
ba......jijiyoyin hannunsa ne suka daina aiki yadda ya kamata ko kuma
qwaqwalwarsa ce?!.
Tashin hankali!
Allah ka rabamu dashi!
Me karatu sai ince muje
mu qarasa
Hugumanku ce
Na gode
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 149
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA
CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da
babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu
ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
149
Kowacce gaba
ta jikinsa sai yaji tayi wani irin sanyi,sai ya dinga jin kaman bashi da wani
sauran damar ya motsa ko ya sakeyin kuzari a daidai wannan lokacin.
"Mariya ce.....maaamah ce......itace" Sautukan
suka dinga haduwa suna masa amsa kuwa a tsakiyar kansa.
"Are you okay sir?" Muryar cp tayi kutse cikin
tunaninsa,wanda yaga lokaci daya fu'ad din yanayinsa ya sauya,wuta kuma ta
dauke masa. Da qyar ya iya daga idanunsa ya kalli cp saboda wani dan banzan
ciwon kai daya saukar masa lokaci guda.
"Yes.....am okay,akwai wadanda sukayi kidnapping 'yar
alhaji hamza kibiya......za'a canzasu daga can inda suke a kawosu nan a
hadesu......duk yadda ta kama ayi musu hukunci".
" Ma sha Allah....sunzo.hannu kenan?" Kai ya
jinjina masa kawai. Bayason doguwar magana sam sam,don shi kadai yasan yadda
kansa yake masa wani irin bala'e'en ciwo,yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa da
wani irin mahaukacin fushi da yake tsoron kada ya illatashi shi a karan kansa.
Da zafi zafi ya fita a gurin,ya samu abdulgaffar suna tsaye suna dakon
fitowarsa. Hannu kawai ya miqa masa
"Bani key" Ya fada ba tare daya dubu abdulgaffar
ba. Baki ya saki yana kallon boss din nashi,baisan meye haka da zafi ya
tunzurashi ba ko kuma ya sauyashi.
"Sir.....muje na kaika duk inda zaka je.....like kaman
baka cikin mode din da za'a barka kayi driving".
"Just give me the keys abdulgaffar.......ko mutuwa
zanyi a hanya kana da asara?........wanda ya kawoni duniya ma bashi da asara
ballantana kai!" Ya fada da wata irin tsawa data bashi matuqar mamaki.
Salin alin ya miqa masa key din,saidai kuma ya yiwa sauran team nashi alama da
ido,don haka fu'ad din yana tada motar yana fita suka bishi a baya cikin salon
da bazai gane shi suke ba. Suna matuqar qaunarsa da kula da dukka abinda zai
cutar dashi,suna matuqar jinsa a jiki irin kusa kusannan,suna jinsa tamkar wani
babban yayansu da yake da ruwa da tsaki a rayuwarsu,inda suna da hali tabbas ba
zasu bari ba ko quda me cutarwa ya sauka a kansa ba.
Wani
mahaukacin gudu yake zubawa wanda ya sake tabbatar musu da ba lafiya
ba,hankalin abdulgaffar akan motar yana duban wanda ya bawa yayi driving.
"Ka kula sosai,kada ka matsi bayansa da yawa kada kuma
ka bari ya kufce mana" Ya fada yana gyara zaman Bluetooth din kunnensa
yana magana da na motar baya.
Shi kansa
yasan gudun da yakeyi ya wuce qa'ida.......amma a irin zafi da bugun da tasa
zuciyar takeyi sai yakejin ba wani gudu yake ba shi din. Idanunsa fes bisa
kwalta amma tunaninsa yayi nesa sa gangar jikinsa. Baisan kuka yakeyi ba saida
yaji iska na fifita hawayen daya silmiyo masa,karon farko tun bayan tafiyarta
ta barsu.....karon farko tun bayan wasu shekaru masu yawan gaske da ya share
wani abu bai sakashi kuka ba......a yau a zagaye na biyu ta sake zama silar
kukanshi. Hannunsa daya ya saki dava steering din,ya shafo hawayen yana kallon
su,a wannan lokaci yana jin ta gama sanyashi kuka......yayi kuka qarshe a rayuwarsa saboda ita. Tsananin
kunyar anni da abba yakeji,da wanne idanu zai kallesu ya shaida musu
mahaifiyarsa ce ta aikata ma diyar cikinsu autarsu haka?,da wanne bakin zai
musu bayani?,wanne shine kalar sakayyar da suka cancanci su samu makwafin
alkhairin da sukayi mata?.
Wani
birkitaccen parking yayi qofar
gidan,parking din da ya tada qura,ya kuma ja hankalin malam sa'adu dake zaune
daga cikin gidan a bakin qofa yana jan tasbaha.
Da
sassarfa yake takun nasa,kaman me gaggawar cimma wani abun. Security na farko
ne ya hangoshi,ya kuma taso ya bude masa da sauri kafin yakai ga qarasowa.
Kusan ba
sosai yake gani ba,fatansa kawai ya cimmata......fatansa kawai ya isa
gareta......ya kuma tambayeta dukka akan me?,me yasa?.
Da sauri me
aikinta dake saukowa daga samanta taja baya tana zubewa sanda taga shigowarsa.
"Barka da warhaka yallabai?" Sam ba gaisuwarta
bace damuwarsa,bai kuma damu ya amsa ba
"Tana ina?" Ya tambayeta kai tsaye yana jin
jikinsa ko ina yana rawa.
"Tana sama" Ta amsa masa tana rabewa ganin yadda
ya nufo saman da sauri bata ko dire statement dinta ba.
Matakala
bibbiyu ya dinga hadawa har Allah ya kaishi saman. Dab da matakalar qarshe
sautin muryarta ya sauka a kunnensa.
"Ta yaya akayi saken da har wani yasan inda suka
boyeta.....wanne irin hauka ne wannan?,baisan muhimmancin yarinyar nan a
hannuna ba?,subucewarta da kuma kamasun da akayi yasan irin asarar da zai
jawomin?.....bani da haufi akan zasu iya fadar sunana......duk da boka baiyi
aiki a kansu ba amma kudin dana musu alqawari da alqawarin dana musu akan koda
tsautsayi ta gifta zan fiddasu....iya wannan bazai bari su fadi sunana ba"
Ta furta cikin bawa kanta tabbaci da yaqini da gaibu da qaryar daka iya fidda
bawa daga ainihin imaninsa.
Wani abune
ya fusgeshi sosai,da sassarfar data jawo hankalinta daga wayar da takeyi. Wani
irin duba take masa me cike da tsoro da kokwanton ya jita ko bai jita
ba?,zuciyarta gaba daya ta kasa bata nutsuwar bai jita din ba saboda wani irin
kallo dake fita daga idanuwan da suka sauya launi suka jirkice,daga fararen
qwayar idanuwa zuwa kalar makuba kaman an diga jini.
"Why maamah.....why amna?!" Ya furta da wani irin
sauti me cike da razani mamaki dake cakude da karyewa yana wara hannuwansa da
kuma watsasu kaman wanda yake dakon kama wani abu.
Wani irin
shock taji,wanda ya kusa sanya numfashinta dakatawa na wucin gadi.
"Me yasa maamah?.....me yasa?,idan ni
kinyimin.......d'anki ne.....idan kin yiwa musaddiq.......d'anki ne......amma
amnah fa?!" Ya fada da wata irin murya dake neman fara rawa saboda
tsananin sarewa da dukkan komai,ya kuma qarasa maganar yana nuna waje da
yatsarsa.
"Me amna ta aikata maamah.....meye laifinta?" Ya
kuma fada da yanayin mutumin da ya soma zarewa.
"Idan kika bada kai bori zai hau.....idan kuma baka iya
kama barawo ba saishi ya kamaka" Wani sashe na rubabbiyar zuciyarta ya
sake bijiro mata da wannan shawarar,shawarar data qarfafi dukkan gabbanta,ta
soma qoqarin tattaro kowacce nutsuwa tata,sannan kuma ta hana kanta shiga
d'imuwa.
"Kai fu'ad.....kalleni nan da kyau,idan kana cin qasa
ka kiyayi ta shuru....ni dinnan nice uwarka,baka da sama dani.....ohhhh,wato
kaje an karanto maka abinda zakacemin da kalar rashin kunyar da zaka
yimin.....dukka ameenatu ta yo maka katunsa shine zakazo ka saukemin?!"
"Ameenatu ameenatu dai?,ameenatun da batayi miki komai
ba face alkhairi?,ameenatun da ta rungumi yaran da kikaji cewa baki
buqatarsu?,ameenatun data yarda ta zauna ta kashe tata rayuwar saboda ta
'ya'yan da kika watsarwa duniya?,akwai wani alkhairi sama da
wannan?,akwaishi......wata can daban tayi abinda uwa ta gaza yi?,wata can daban
tayi abinda uwa take ganin ya zame mata babban aiki?" Ya qarasa fada yana
zuba mata ido,qirjinsa yana sama da qasa yana jin kamar ciwon zuciya ne yake
shirin kamashi.
"Kin dawo kin sake kashemu a karo na biyu bayan wancan
kisan da kika yiwa rayuwarmu.......me mukayi miki haka?,laifinmu ne da kika
haifemu alhalin baki buqatarmu?" Ya fada a tausashe da wani irin rauni
daya sanya idanunsa fitar hawaye
"Daga kowanne bangare......cikin binciken kowanne laifi
Maamah dai mahaifiyar fu'ad?,mahaifiyarsa?.....maamah dai?,wadda tayi silar
zuwansa duniya?,maamahn ita ta dauke amna?,amna diya ga hamza kibiya?,mutumin
daya zame musu uba......bango madafarsu?,ya tallafesu a sanda duniya tayi watsi
dasu,ya rungumesu,a sanda ita da take Mazaunin uwar data kawosu duniya ta sanya
qafa tayi wancakali dasu?.....ya rungumi farincikinsu da baqincikinsu?,ya rabu
da duk wanda zaice baya sonsu?,ya qara zafin nemansa saboda su.......yayi musu
riga yayi musu wando?,yayi kawar da dauda da duhun jahilci daga qwaqwalensu?,ya
daga darajarsu a idanun duniya ta hanyar haskasu da hasken ilimi?,ya maidasu
mutane ta hanyar basu ilimin addinin islama?,ya karbesu a matsayin 'ya'yan da
shine yayi silar zuwansu duniya bawai uban riqo ba?,yayi musu gatan da ko
'ya'yan cikinsa bai musu ba?.....amnan dai itace d'iya ga
ameenatu......ameenatun data dawowa auren hamza saboda yaran?,ameenatun data
sadaukar da duk wata kulawa da lokacinta akan yaran?,ameenatun da bata yarda da
wani abu me cutarwa ya rabesu ba?,ameenatun da idan kanaso kaga
farincikinta.....ko kaga kirkinta ka yabi musaddiq.......ka yabi
fu'ad......idan kanaso ku bata alaqarku taja baya ka zagesu ko ka
kushesu.....ameenatun da ta sadaukar da lafiyarta saboda su su rayu cikin
aminci?,taqi kwanciya ta huta sabodasu?,taqi ci saboda saboda basuci ba?,taqi
sha saboda basu sha ba?......" Ya sake tsayawa saboda yadda numfashi ke
masa wahalar shaqa.
"Laifin ameenatu rainon 'ya'yanki da tayi......laifin
ameenatu inganta rayuwar 'ya'yanki.....idan duka haka ne ita kuma SABREEEN
FA?!". Wannan tambayar daya jefa mata tafi kowacce gigitata. Sabreen?,ya
tabbata ta qarasa bude mata aiki kenan kaman yadda taci alwashi?.
"Ni na kawota rayuwarka.....kuma a yanzu bani da
buqatar kasancewarku......na nuna maka ta dukka hanyar data kamata amma saboda
banda kima da martaba a idanunka ka gagara fahimta".
"Sai hakan yanzama license ya zama halaccin da zaki
tura wani d'a namiji gidan aurenta.......dakin da d'anki ya gina saboda matarsa
ta sunnah?.....yaje ya keta hurumin ubangiji?,.......kin auramin sabreen saboda
ki.mallaki fu'ad......fu'ad din da bai mallaki wuta ko aljanna ba......fu'ad
din da bai mallaki rayuwa ko mutuwa ba.......bai mallaki komai ba face wata aba
da ake kira DUKIYA wadda ka iya zama fitina da jarrabawa ga bawa.......".
Yana kaiwa qarshe ya jawo littafi da abun rubutun daya gani ajiye a gefe,ya
jawo side table ya ajiye a tsakaninsu ya daga idonsa yana kallonta duba na kai
tsaye.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 150
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA
CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da
babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu
ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
150
"Na
baki dama......daga farkon littafin nan har bangonsa ki rubuta adadin kudin da
kikeso......na baki dama ki rubuta adadin alatun rayuwar da kikeso......na baki
dama ki rubuta tsarin rayuwarki na shekaru dari nan gaba idan har zaki kai
sannan......ni kuma zan tabbatar miki da wannan mafarkin,muddin zaki zare kanki
daga rayuwarmu.......muddin zaki fita salin alin daga rayuwarmu......muddin
zakiyi nesa da rayuwarmu......indai kin amince zaki bar iyalin ameenatu su rayu
cikin salama su kuma zauna lafiya........ina fada miki hakanne cikin harshe na
girmamawa.......ina gaya miki hakanne saboda har yanzu sunanki
MAHAIFIYARMU.......Duk da girman abubuwan da kika aikatawa mutanen da basuji ba
basu gani ba......ina gaya miki wannan zabinne saboda shine zaifi mana sauqi mu
dake" Ya qarasa maganar yana jin wani mulmulallen dutsen wuta yana tsaya
masa tsakanin wuyansa da qirjinsa yana qoqarin turashi da qyar. Fata yakeyi
inama ace wani ko wata ce can daban suka aikata musu wannan abun ba maamah ba?......inama
ace wasu mutanen ne daban keda alhakin dukka wadannan abubuwan ba maamah ba?,ya
rantse da Allah da sai ya ganar dashi kuskuren bari da yayi uwarsa ta haifesa
zuwa gidan duniyar ma gaba daya.
"Fu'ad!.....ni kake gayawa wannan maganar?,ni kake cewa
zaka rabu dani saboda ameenatu?" Ta tambaya tana jin wani irin tashin
hankalin jahiltar matsayin ameenatu da tayi a baya. Ashe har zai iya katse
alaqar uwa tsakaninsu saboda ameenatun dai?.
"Fu'ad!.....ka saurareni da kyau!......."
"Jaffal qalam" Ya fada yana miqewa daga gabanta.
Zuciya da shaidan dukka suna kusa,duk sanda zai kalli fuskarta fuskar
mahaifinsa yake kalla a tayi watsi dashi cikin tsananin ciwo bayan ta gama
illatawa luguiguita lafiyarsa cikin mugunta.......duk sanda zai kalleta saiya
tuna sanda take cida Mahaifinsu da abubuwan da aka hanashi ci ko sha saboda
hakan zai iya zama sanadin komai.....ciki harda MUTUWARSA.......duk sanda ya
kalleta saiya tuna sanda JADDA ta mutu saman cinyarsu saboda rashin gata suka
kwana da gawarta ba wanda ya ko leqosu sai bayan wayewar gari......duk sanda ya
kalli fuskarta sai ya tuna sanda musaddiq ke kwana yana kuka harda shidewa
cikin kewa da qauna yana kiran sunanta.....burinsa shine kawai ya
ganta......har yanzu kunnuwansa sun gaza manta yadda aka saka abun rushe gini
ake dukan ginin gidan da mahaifinsu ya wahala da dukka qarfinsa ya ginashi don
su rayu a ciki......ta badashi a mazaunin jingina ta karbi kudaden ta nausa
zuwa duniya
"Wannan dama ce a wajenki cikin girmamawa da kuma baki
abinda kiketa harin mallaka din tsahon shekaru kina fadi tashi.....ki
rubuta!....ki rubuta!!.....ki rubuta!!!!....ki gayyato wasu ma su tayaki
rubutun?!!!,wannan damar ce kawai ta rage......'yanci muke nema!!!!,yanci muke
buqata....." Sai ya hade hannayensa alamun roqo
"A wannan karon da kanmu muke roqarki ki tafi ki barmu
kaman yadda kikayi a baya". Sai ya fara tafiya da baya da baya idanunshi a
kanta yana barin falon. Irin kallon da ya jima baiyi mata irinsa ba. Ya dade
rabon daya sanya idonsa cikin nata,ya dade rabon daya iya daga kai ya
dubeta,tana hango abubuwa da yawa cikin idanunsa.
"Idan kika rubuta hakan yana bawa ameenatu tabbacin
kinbar mata su dama dukkan wata dama ko matsayi da zasu sake takawa a
gaba.....kinbar mata su da dukka wani arziqi da zai sake habaka
nasu......kinbar mata dukkan wata alfarma ta amsa sunan UWAR ME JADDA har
abada......iya abinda kika samu daman rubutawa shine kawai naki rabon har
abada.....baki da wani sauran dama ko rabo a jikinsu saidai idan sun rigaki
MUTUWA" Maganar da shaidaniyar
zuciyarta ke gaya mata kenan sanda yake dab da fita a falon,abinda ya sanyata
zabura ta miqe,sai wani irin jiri ya taso mata,amma cikin tsananin taurin rai
dana zuciya ta cije ta kuma soma takawa tana binsa da hanzari gami da qwalla
kiran sunansa.
Turus yayi
ya tsaya gaban gate din gidan yana kallon tarin 'yan press da suka cika qofar
gidan maqil.
"Da gaske ne kenan yallabai.....mamarka itace tayi
kidnapping d'iyar alhaji hamza kibiya dake kwance a asibiti a yanzu tana
jinya?,yanzu haka ma akwai d'iyar qawarta a cikin gidan nan da tayi!kidnapping
nata tsahon watanni ba'a sani ba me suna laila?" . Wani abu yaji yana
neman kayar dashi,abu daya ya saka masa sassauci ganin yadda dukkaninsu suka
sauke cameras dinsu a kanshi cikin nuna masa girmamawa.
Kasa
magana yayi cikin tsananin mamakin yadda akayi!maganan ya fita?,waye kuma ya
gayyatosu?,amsar da ya sameta kai tsaye daga bakin wani dan jarida.
"Mun samu half details na cikakken labarin daga wajen
aminiyarta hajja harira......ta kuma bamu tabbacin zamu samu full din daga
bakin hajiya mariya ahmad" Ya qarashe fadi sanda maamah ki fitowa da
sassarfa tana qwala kiran sunan fu'ad din.
Waiwayawa
yayi ya zube idanunsa a kanta a sanda sam bata lura da taron da dama ita suke
kwadayin gani ba.....malam sa'adu ya tsaidasu da qyar ba,sai kawai ya dauke
kanshi ya kuma dubesu da dakakkiyar muryarsannan dake qara masa kwarjini,wadda
a yau take cakude da bacin rai yace.
"Ku bani hanya....bani keda labarin ba". Tsakiya
suka buda masa ya fara wucewa da sassarfa,bayajin akwai wani abu da zaiyi
mata.....ba wani abu da yayi saura da zai iyayi mata shi
"Fu'ad......a matsayina na mahaifiyarka ina me baka
umarnin........"
"Yauwa.....shikenan ma.....gata nan ta fito" Yaji
muryoyin wasu a cikin su suna fadi gami da kunna cameras dinsu suka saitasu
sannan sukayi kanta.
"Kada ki damu,wataqila sun soma fahimtar kece mahaifiya
ga fu'ad din.....girman ya fara dawo miki,wataqila ameenatu ta sallama ne"
Wata zuciyar ta gaya mata,don haka ta dake tana dubansu sanda suke yowa kanta
yuuu.
"Ranki ya dade......samun tabbaci da neman sahihancin
rahotanni yasa mukazo gareki.....da gaske kece mahaifiyar muhammad fu'ad
jadda?.....mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources?" . Wani
murmushin alfahari ya kubce mata,murmushin da ya dusashe duk wani bacin rai da
tashin hankalin data tsinci kanta yanzu yanzu a cikinsa.
"Qwarai da gaske.....nice"
"Ma sha Allah......kina tare da laila d'iyar qawarki
kenan?". Da farko tambayar ta mata banbarakwai,amma zuciya batan basira da
neman suna suka gina mata tunanin wataqila suna kallon ita din uwar kowa ce da
take riqon yara turmus,don haka ta daga kanta kawai tana cewa.
"Eh haka ne".
"Yauwa.....mun samu cikakken labarin
qawancenku......yadda kikayi silar hada auren d'anki da matarsa ta yanzu
sabreen da dukkan wasu hujjoji na riqe qannenta a bisa cikar wannan buri
naki.....kidnapping diyar alhaji hamza da kidnapping tata d'iyar wato laila da
a yanzu kika bamu tabbacin kuna tare....". Wani jibgigen abu ne taji ya
saukar mata tsakiyar kanta wanda ya sanya numfashinta yaso riqewa iya wuyanta.
Ita hajja
zata yiwa haka?,ita hajja zata wulaqanta?,ita hajja zata jajibowa taron manema
labarai?,ita hajja zata tonawa asiri?,ya akayi ta manta da ita bata sanyata
mutum ta uku daya kamata ta shafe labarin su ba,me yasa bata b'atar da ita
ba?,me yasa ta barta taci gaba da shaqar iskar 'yanci?.
Juyawa
tayi kawai don komawa ciki,saboda tana jin bai kamata tace komai ba gudun
tonuwar asirinta gaba daya wanda ta fahimci fiye da rabinsa ya yaye.
"Ranki ya dade ya zaki koma kuma?" Zaqaqurin dan
jaridar ya fada. Waiwayowa tayi ta zube masa wani kallo.
"Ni ba uwar qaramin mutum bace,bani da lokacin magana
daku kai tsaye haka.....idan ka matsa kuma kasan waye d'ana,ba aikinka kawai
zaka rasa ba.....har....." Sai kuma ta dakata tana kwabar kanta duba da
irin cameras din dake fuskantarta. Kallon kallon suka farayi tsakaninsu,don
kowa da abinda ransa ke raya masa da yanke maganar da tayi bata qarasa ba.
Ganin ta dauke musu wuta gaba dayansu saita taka tana komawa ciki cikin jan
qaqqarfan tsaki.
"Akwai batun aika b'ata gari da kikayi gidansa don yiwa
matarsa fyade da sunan baki sonta.......wannan batun gaskiya ne?". Wani
irin suka maganar tayi mata a qirjinta,har batasan sanda ta saka hannu ta dafe
saitin zuciyarta ba. Haki ta soma yi tana jin kamar qafafunta ba zasu dauke ta
ba,dole ta fara kiran sunan laila saboda tasan duk 'yan aikinta yau basunan
cikin mancewa da tarin 'yan jaridar da suke neman tabbacin lailan tana tare da
ita kaman yadda cikin rashin sani ta basu tabbacin.
Kome
takeyi,komai girman bacci ko uzurinta muddin maamah ta kirata saita bar komai.
Kaman yanzun da take zaman cin abinci haka ta watsar dashi ta kwaso da gudu.
Fitowar tata ta sake maida hankalin mutane kan laila din da dukkanin kamanninta
da hajja harira da suka fito.
"Lafiya maamah?,me sukayi miki?,me ya faru?".
"Kamani muje ciki" Ta bata umarni a tsawace,abinda
ya sanyata kamata dukka jikinta suna rawa.
"Da gaske kece diyar hajja harira?" Wata cikin su
tayi caraf ta jefa mata tambayar sunason tabbatar da maganar juya mata hankali
da sukayi.
"Eh 'yarta ce......amma yanzun daidai nake da baiwa
wajen maamah......yadda takeso take buqata haka zanyi,koda ya kama na rabu da
ita hariran"
"Ke laila kama bakinki mu wuce ciki!" Maamah ta
fada da hanzari gudun kada tsananin mallaka ya sanyata nunawa duniya abinda zai
sake zame mata abun fada.
"Laaaaa haila
ha'illallahu.....muhammadurrasulillahi" D'aya daga cikin mata 'yan jarida
dake wajen ta kasa daurewa abinda ya farun ta saki kuka tana tafa hannu.
"Wallahi 'yar hajja harira ce,da gaske ne,da gaske
aikin juyar da hankali tayi mata bayan tayi kidnapping nata......da gaske
ne,gashinan diya tana neman mancewa da uwarta?" Wannan kalaman sun sauka
daidai kunnen maamah,wanda hakan ya sanyata runtse ido,tsananin jin zafin hajja
yana sake ratsata tare da alwashin daukan fansa a tare da ita.
"Ki gayawa malam sa'adu ya fidda mutanen nan,idan ba
haka ba zai fuskanci fushi na" Umarnin data bawa laila kenan,ta kuma saka
kunne tana jiran daina jiyo hayaniyarsu daga nan inda take.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 151
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA
CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da
babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu
ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
151
Tsahon mintuna
talatin ta sauke idonta akan takardar da fu'ad ya ajiye mata,ta zubawa littafin
idanu tana lissafa adadin yawan shafukan da yake dasu. Ya fadi cewa zata iya
cika littafin harma ta qaro wani....tayita rubuta dukkanin abinda
takeso.......wannna babbar dama ce a gareta kenan na zama Mulitibillonier?.
Murmushi ta saki ta soma yunqurin daga hannunta ta miqashi don dauko
littafin,amma abun mamaki sai taji hakan ya gagara. Ta sake yunqurawa a karo na
biyu da zummar gwada daukar nan ma shuru ne hannun yaqi sarrafuwa.
A zabure
ta maida dubanta ga hannun nata cikin wani irin kidima da dimuwa tana kallonsa.
Hannunta ne dai......hannunta ne data sani shekara da shekaru......hannunta ne
da ba wani abu daya canzashi.........amma meye ya kawo qin daguwarsa?.
A karo na
uku ta tattaro dukkanin qarfinta zata dagashi ya sake motsuwa koda wasa,a
birkice ta maida hankalinta kan daya hannun tana qoqarin motsashi shima.
Still
shima abinda dan uwansa yayi shi yayi mata. Matuqar qololuwar tashin hankali
taji ta shigeta,wani irin mahaukacin gumi ya yanke mata.
"Me hakan yake nufi kenan?,wani ne yayi min asiri?,ko
wani ne yayi min tsafi?" Ta tambayi kanta da kanta.
"Kai inaaaa.....a irin wannan lokacin?,a lokacin da
dama tazomin?" Ta sake tambayar kanta a fili kaman wata tababbiya.
"Bazai yuwu ba" Ta fada tana qoqarin miqewa don ta
gani ko qafafunta suna aiki?.
Miqewar
datayi aniya jikinta ya gaya mata bashi da wani sauran motsi me qarfi,qafafun
suma suka shaida mata basu da wani sauran qarfin da zasu dauki nauyin gangar
jikinta ta hanyar warbar da ita ta zube a qasa tana kifawa saman fuskarta.
Wani irin
matsanancin ciwon kai yakeji,wani irin yanayi da yakejin kamar jikinsa yana dab
da gazawa. Yana dafe da kanshi tsahon mintunan da suka dauka suna tafiya a
motar,har zuwa sanda ya buda bakinsa a hankali yayi magana da driver din
"Badawa zaka kaini......ba gida ba" A yanzun ba
abinda yafi buqata irin ya kebe,so yake ya kebe shi daya,bayason magana da kowa
bayason kuma hayaniya.
Karya kan
motar yayi suna komawa daya hannun. Tafiyar mintuna ashirin ta kaisu m,already
yasan gidan,gida ne madaidaici daga waje,saidai kuma daga cikin yana da yalwa
da wani irin yanayi da aka tsara me tsananin burgewa. Yakan jima baizo gidan
ba,yana ma mantawa dashi sau tari,saidai duk sanda yake buqatar ya kebe ko ya
huta a nan din yake zama har zuwa sanda ya gamsu da yanayinsa ya koma normal
mode dinsa.
Tun a
parlor din ya zube,karo na farko da yaji yana buqatar yayi kuka,karo na farko
da ya buraci inama ace shi din yana cikin sahun mutanen da hawaye ke fita a
fuskarsu da wurwuri?. Hawaye yake da buqatar ya zubar sosai saboda qirjinsa
dama zuciyarsa sun gaji da daukan abinda suke dauka din. Koda zai iya hana
kanshi fitar dasu to ba a irin wannan lokacin ba,a yanzun kuka yafi buqatar
yayi bawai yaci gaba da nuna jarumtarsa ba.
"Astagfirullah ya Allah......astagfirullah" Shine
abinda labbansa dake motsawa suke maimaitawa yana jin yadda qirjinsa ke sake
suya idanunsa suna sake d'aurewa da wani irin zafi da kuma radadi.
Wani sabon
babi ya bude na tariyar rayuwarsu,tun daga sanda ya bude idanunsa ya zama mutum
cikakke zuwa yanzu. Bai tsinci komai tattare da maamah ba banda haihuwarsu da
tayi......ko a sanda take rayuwa tare dasu,yadda take mu'amala dasu haihuwarsu
ta zame mata kaman wani nauyi wahala ko dawainiya.....abbansu kusan shine komai
nasu......abbansu shine duk wata wahala da dawainiya tasu,abbansu shine
wankansu abincinsu,shirin makarantarsu da komai na dawainiya......yayi a gida
ya fita yayi a waje ya kawo musu. Zuwa yanzu baisan sadaqaul jariya na abubuwa
daban daban dubu million nawa yayi saboda shi ba......yana fatan ko a ina yake
ya bishi cike da samun salama cikin kabarinsa da rayuwarsa ta barzahu.
Da
taimakon ambaton sunan Allah da yakeyi ya samu nutsuwa ta fara dawo masa. Yayi
amfani da wannan damar ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala. Dawowa yayi ya
kunna ya kunna TV din dake kashe,ya lalubi tashar saudi qur'an ya qaro volume
din ya karade parlor din gaba daya.
Cikin
kujera ya nutse,idanunsa a lumshe yana sauraren karatun gami da bin ayoyin tare
da shaik abdurrahman assudais. Yana karatun yana fahimtar ma'anar ayoyin,abinda
ya sake taimakawa wajen bawa zuciyarsa da ruhinsa nutsuwa.
A nan gurin
yayi sallar la'asar,magariba ma ta ruskeshi duka ba tare da ya sani ba. Itama
magrib din a nan yayita,ya jima saman abun sallah yana addu'o'i har baisan
adadin lokutan daya shafe ba,yadai duba ya tarar da lokacin isha'i har ya
shiga.
Isha'i
dince ya fita a daddafe zuwa masallacin dake cikin layin cikin shiga ta bad da
kama,baya son kowa ya tsaidashi don bazai iya dogon magana ba. Ana idarwa ya
taso shida jordan sukayo gida,jordan din ya dan dubeshi cikin matuqar jin
tausayinsa qauna da kuma kulawa.
"Sir......ko za'a aika a karba maka abinci gurin
madam?,if not a maka order daga wani eatery din?". Kai ya girgiza,a halin
yanzu bayajin yunwa,still kuma bayaso ma sabreen ta ganshi a yanayin da yake
ciki. Tashin hankalin da take fuskanta ita kanta yayi yawa,tunda ta dauki cikin
nan bata huta ba,tana stressing kanta da yawa akan duk abinda ya
shafeshi......is over,ya kamata ta huta hakanan,ya kamata ta samu peace of
mind......yana shawarwarin yin nesa da ita har sai abubuwa sun lafa,shi kansa yana
jin zaya dauki hutu har sai komai ya koma daidai.
"Sakamin order lite abu please" Yace da jordan din
yana wucewa cikin gidan.
Saman
sofa ya zauna,ya dauki wayarsa dake yashe a wajen wadda sam yama mance da ita.
Saqonni da miscalls rututu,amma duka na sabreen din yafi yawa. Ya saki dan
qaramin murmushi bayan ya gama karanta wani saqonta na qarshe.....finally ya
samu wata kyakkyawar zuciya data damu dashi da gasken gaske,finally ya samu
wani ruhi dake craving for him.......finally ya samu wannan madadin da yake
qishirwar samu.
_"na kiraka na maka saqo har sau babu adadi amma babu
guda daya daka amsamin.....tom.....Even if you're ready to live without me,I'm
not ready to let go,ko yaushe zan kasance a tare da kai,koda hakan baida tsada
ko daraja a wajenka,bana saba alqawari,forever. Yours mom of triplet"_
Har tsakiyar
zuciyarsa yaji saukar da saqon yayi masa. Wata soyayya ta musamman tana sake
huda zuciyarsa,qaunar 'yan tayi guda uku dake kwance a cikinta suna sake
lullubeshi.
_You're the missing piece that makes me whole,without
you,life wouldn't be the same,forever with you is where i want to be.....you're
my forever adda sabreen......am safe.....karki damu da yawa,ki bani aron
wadannan awannin,zamu kasance tare da juna in sha Allah,ma'u zata kasance tare
da ke,ayimin afuwa"_ sai kawai ya tura mata,yana buqatar isashen time da
zaiyi healing daga nan zuwa safiya,bayaso ya jefata a damuwarsa,wadda batasan
sadda ta samo asali ba,yana ganin kamar yin hakan rashin adalci ne kawai.
Yanaso
yaji muryarta shima......yana kewar wannan lallausan sound din nata wanda koda
fada takeyi ko masifa laushinsa sai ya bayyana,but definitely idan taji
muryarsa saita gane damuwarsa.
Cikin
taqaitaccen zaman kusa da kusa da sukayi da juna,yana mamakin yadda take da
saurin karantarsa,sauyawarsa ko damuwarsa,walwalarsa ko akasinta.
Abu daya
daya sani shine baiwa ce,ba duk namiji Allah kewa baiwar mace me kula da dukka
damuwarsa da matsalolinsa ba.
Sauran
kiran da saqon nasu farouq ne,duka sai ya share,saidai akwai saqo guda daya
daya dauki hankalinsa.
"Maamah is sick,she was admitted to the hospital"
Idanunsa yaja ya lumshe,baisan me zaice ba?,me zaiyi?,sai kawai ya kashe wayar
gaba days ya cillata gefe.
Ya samu
yaci abincin kadan,sai ya maida hankalinsa kan tataccen ruwan blood orange
natural da aka hado masa dashi,da kuma wadatar kayan fruit,cherry pear jujube
sai gooseberry da suka hado masa dashi. Dasu ya danyi fresh up,yadan jira
abincin ya narke kadan sannan ya wuce bedroom Kai tsaye.
Duk wani
haske da komai da zai bashi sauti sai daya kasheshi,ya zamana daga zallarshi
sai sautin alqur'ani da yake tashi kadan kadan ta wata qawatacciyar fitila dake
tsakiyar gadon,wadda ke zuwa da qaramar fanka me bada sanyi kwatankwacin na ac
da Bluetooth da zaka iya using nashi,sai ya kashe hasken fitilar dake jikin
yabar iya sound din.
Yayi lamo
saman gadon kaman dazu yana bibiyar karatun,bai tashi gane kuskurenshi ba sai
da bacci ya qauracewa idanunshi fafur.
Juyi ya
dinga yi saman gadon shi kadai yana jin yadda kadaicinta yake neman
hallakashi,kowanne sashe a jikinsa sabreen din yake buqata,kowanne bangare na
jikinsa kewarta yakeyi.
"Ya salam ya al-hadi". Yana sawwara ta yadda zai
iya yin nesa da ita dalilin tafiye tafiye na kasuwanci......ta yaya hakan zata
yiwu?" Ya tambayi kansa da kansa.
Daga
qarshe dai ya tabbatar hakan bame yiwuwa bane,ya tashi zaune yana duba qaramin
kyakkyawan agogon dake saman side drawers na gadon.
"Oops" Ya furta yana dafe goshinsa,dare yayi,yayi
imanin zai wahala idan bata fara bacci ba yanzun,idan kuma har ya zama silar
tadata a baccin bazai yafewa kansa ba,sai ya maida kansa ya cusa tsakiyar
pillow din yana qagara asuba tayi.
★Tunda ya dawo
sallar asuba ya wuce gym,yana fatan hakan ya dawo masa da kuzarinsa daya rasa a
kwanakin nan saboda tashe tashen hankulan da suka durfafoshi. Waya ya dauka kai
tsaye ya kira Jordan ya bashi umarni ya koma gida ya dauko masa duniyarsa. Yana
so nan din ya zame musu wani kebantaccen guri da ba kowa bane yasan da
zamansa,da qwaqwalensu zasu huta na koda kwanaki uku ne kafin su koma cikin
jama'a.
Sanda ya
kammala shiryawa cikin sassauqar shirt da trouser sai ya wuce parlor. Da kansa
ya shiga kitchen ya tafasa madarar shanu fresh one da turmeric dan kadan ginger
da cloves ya dawo falon yana sipping kadan kadan yana kamo tashoshin daya saba
kalla a lokuta irin wadannan da ake labarai na qasa.
Tashar
farko cikin headline na news din hoton maamah ya gifta da anyo briefing na case
dinta daga qasa. Zuciyarsa ta motsa tana bugawa da wani irin yanayi,sai kawai
ya matsa remote din yana canza tasha.
Channel
din daya kama sun fara news tuni,the next abinda ya faru shima dai hoton maamah
ne da title tafka tafka na zargin kidnapping.....wannan channel din sun samu
nasarar saka wani d'an yanki na tambayoyin da 'yan press din sukayi mata a
Farfajiyar gidanta,wanda kusan duk me hankali idan ya kalla yasan maganganu ne
kama kai.
"Subhanallah" Ya fadi yana sauke canza channel.
Already su
sun gama,saidai.maimaicin kanun labarai da shima hoton maamah dana hajja harira
harma dana fareeda da suka cika screen din. A nan ma baida buqatar yaji
komai,yasan tunda haka ta faru duk inda zai kunna ma abinda zasu nuna masa
kenan tamkar sunsan yana da alaqa da ita.
Wani zafi
zuciyarsa ke mass,wani irin kud'a da quna take masa. Ya dauka ko meye maamah
tayi....kuma ko meye akayi mata ba wani sauran abu daya rage da zai tada masa
hankali a kanta ko ya qona masa rai,sai gashi bayyanarta a screen na TV dinsa
yana neman hana mishi nutsuwa.
Har addu'a
yakeyi......har fata yakeyi ta zabi adadin abinda take buqata daga
gareshin.....mutanen dake kewaye dashi a yanzun,mutanen da yake rayuwa dasu a
yanzun suna da matuqar muhimmamci a tattare dashi,mutane ne da bayajin idan
wani abu maras kyau ya samesu ta sanadinsa.....ko ta sanadin arziqinsa lallai
ba shakka bazai yafewa kansa ba,bazai iya jurewa ya rasa koda rai guda daya a
cikinsu ba. Koda maamah ta karbi abinda takeso ta koma inda ta fito,har kullum,muddin
da numfashi a gangar jikinsa bazai fasa mata addu'a ta shiriya ba darajar
haihuwarsu da tayi.
Idanunsa
basa wajen,amma tsaiwarta a bakin wajen yaji a jikinsa,don haka ya daga
risunannun idanuwansa yana dubanta.
Tayi wani
irin kyau da shigar mutanen turkey,wasu irin riga da wando da dan hijab dinsu
me suturce jiki. Ya sauke idanunsa akan cikinta,sai yaga kaman ya qara
tasawa,kaman ya qara girma a kwana daya tak da yayi bai ganta ba. Wani sanyi da
rahama yaji yana sauka a zuciyarsa,sai ya miqa mata hannuwansa yana lumshe
idanunsa,abinda ya bata tabbacin lallai yana buqatarta kusa dashi.
A nutse ta
tako,wanda tun kafin ta iso inda yake qamshin nan nata,qamshin kabbasar nan
tata ya soma kasheshi daga inda yake a zaunen(incense by kabo
daughter....duniya ne sis,ki gwada ko sau daya,basai nace miki gobe ki koma
ba,wannan tasted and trusted ne,bawai just normal tallan da bakasan ya kan abun
yake ba(+234 803 211 9803).
Kasa dauke
idonsa yayi daga kanta saboda wani salon tafiya da takeyi da yake fusgar
hankalinsa,har ya qagu ta qaraso inda yake ya shaqi ni'imtaccen qamshin nan da
yakejin inama kowanne second da zai shude a rayuwarsa zai samu daman shaqarsa?.
Kaman
tasan da hakan,tana zuwa dab dashi saita cake ta tsaya,ta yamutse fuska,ta turo
lips dinnan nata ta kuma juya masa qeya.
Ya masa
nisa ya tsaya tambayarta abinda ya faru,don haka kanshi tsaye ya miqe,ya taka
ya zagayo gabanta. Tsaiwa yayi yana duban kyakkyawan fuskarta data soma nuna
yanayi na masu ciki,yasa hannuwansa duka biyun ya kama kunnensa.
"Na tuba......bazan qara ba" Kafadarta ta maqale.
"Ni saidai kayimin tsallen kwado".
"Done madam" Ya fada yana dan ja da baya still
idanunsa a kanta.
Hannuwan
rigarsa ya tattare,ya durqusa a nutse ya tattare qafafuwan wandonshi,sannan
yayi bismillah ya tsugunna ya fara.
Da idanu
take binsa,tanaso taga alamun ya gaji amma saita lura kaman ko a jikinsa. Bata
rai tayi ta soma buga qafa.
"Ni ban yarda ba Allah.....so nake ka gaji fa".
Murmushi ya kubce masa,da gaske mata rigimammu ne,suna kuma rigimar da ba
dalili,musamman masu juna biyu,don haka yana kaiwa qarshen bangon ya zube
warwas yana numfarfashin qarya gami da jujjuya kanshi.
Dariya dole
ta kubce mata da abinda taga yana yi din,ta qarasa gabansa tana dan dukan
qirjinsa a tausashe.
"Wannan duka cuwa cuwa ne......kawai yi kayi kawai
badon haka bane". Dariya me siririn sauti ya saki,sai kawai ya jawota
jikinsa,yayi mata kyakkyawar runguma yana fadin.
"Na gaji da wannan qwalelen da kikemin,qamshi duka ya
buwayi hancina,amma kin hanamini jinsa yadda ya dace?,haka akeyi?" Ya
qarasa fadi yana yaye hijabinta ya salubeshi ya wurgar gefe sannan ya cusa
fuskarsa tsakanin wuyanta da qirjinta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 152
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
152
★K'arfe goma
da rabi na safe motocinsa suka shiga farfajiyar harabar asibitin. Shi da
duniyarshi ne,wadda tayi kyau abinta cikin wata tsadajjiyar cotton lace lafaya
me asalin tsada da taushi. Butter color ne da aka yiwa adon maroon da
golden,wannan ya saka takalmi da handbag da earrings data sanya duka suka
kasance maroon color,kalar daya zauna sosai a farar fatarta dake glowing saboda
cikin dake manne a jikinta.
Wani
lafiyayyen yadi ne a jikinsa fari qal me taushi,wanda baida kauri ko nauyi ko
kadan,hasalima kana iya hangen fara qal din vest din dake sanye a qasan rigar.
Kusan komai nasa fari ne yau,hatta da takalmi da kuma agogon da yayi amfani
dashi dukka farare ne,sai wata hula saman kanshi irin ta mutanen qasar Morocco
wadda itama fara ce kaman kayan jikinsa.
Tunda
suka fito daga gida take satar kallonsa,ya mata wani irin fitinannen kyau kamar
yau ta soma ganinsa,sun maidashi kamar wani jarumin fina finan india.
Waiwayowa
yayi gareta sanda motar ta qarasa tsayawa sai suka hada idanu. Ta janye
lumsassun idanunta daga kanshi tana sauke boyayyen murmushi da wata 'yar kunya
can cikin idanunta.
"Sabrrr" Ya kirata a tausashe da wani kwantaccen
sauti yana dubanta duk da data dauke fuskarta a wajen.
"Na'am" Ta amsa masa ba tare data waiwayo ba.
"Sabrrrr" Ya sake fadi yana jin shauqin kallonshi
daya samu tana yi.
"Na'am hamma" Ta sake amsa masa still ba tare data
waiwayowa din ba.
"Please mana sabrrr" Ya fadi a shagwabe har abinda
ya fusgi hankalinta ta waiwayo tana sakin dariya.
"Hamma shagwaba?" Ta fada pink lips dinta dake
qyallin man lebe yana fadada da fara'arta. Girarsa dukka biyun ya daga mata
yana duban qwayar idanunta.
"Kina kallona ina jin dadi.....kuma sai kawai ki dauke
kanki?". Murmushi ta sakeyi,a hankali ta motsa labbanta.
"Kayimin kyau muffin,kayimin kyau sosai......kyanka da
kamalarka suna sake tsananta kishinka a raina.....wani lokaci ni kadai ina
tunani......ina tunanin ranar da zaka raba wannan soyayyar......wannan
qaunar......wannan kulawar......wannan jikin........wannan baiwar da wata diya
macen......iya tuna haka kawai idan nayi sai naji kaman zan zauce,sai inji
kaman numfashina zai tsaya,sai naji komai ya dainamin dadi.....kokwanto me yawa
sai ya cika zuciyata......iya tunawa kadai idan nayi nakejin haka.......ta yaya
zan iya fuskanta da d'aukan haka a gaske?" Ta qarasa maganar tana maida
dubanta cikin idanunsa.
Idonta
kawai ya kalla ya fahimci ainihin zallar gaskiyarta......idanunta kadai sun
gaya masa da gaske take......duk abinda take fada din ainihin gaskiyarta kenan.
A
hankali ya miqa hannunsa daya ya kamo fuskarta yana dubanta da kyau,yanayin
fuskarsa ya sauya zuwa ga yanayin wanda zaiyi magana me muhimmanci.
"Kin aminta daga wannan tsoron,kin aminta daga wannan
firgicin har abada.......bazan taba iya jurewa ba naga ruhin da yake tsananin
sona yana wahala har haka akan abinda nake da ikon yi masa ko bashi
ba......sabreenn,mace daya tak qwaqwqqara na roqi Allah ya
bani......nagartacciyar mace na nacewa Allah da roqo ya bani,koda zanci wahalar
samu ko nemanta.....koda zan jima banyi aure ba amma dai ta gari
nakeso......nasha wahalar.....na kuma fuskanci qalubale.....kuma Allah ya bani
ke.....ke kadai kin gamsar dani,bana buqatar qari......kece reality
na......bana buqatar gaibu.....muhammad fu'ad naki ne ke kadai har
abada........muddin kina nan a sabreenn dinnan dana sani baki sauya hali da
dabi'a ba....."
"Koda na tsufa?". Ta fada idanunta suna rau rau da
cika da hawayen farinciki
"Ko deboki akeyi a shanya a rana sai yamma tayi a
maidaki daki.....ballantana ma ina miki kyakkyawan fatan tsufa me kyau.....baka
mummunar tsufa....baka tsufan banza muddin ka riqe Allah kayi rayuwa irin wadda
Allah da manzonsa suka tsara".
"Haqiqa ba wata kyauta da zaka bani a rayuwa bayan
wannan......ba wata kyauta da tafi wannan.....ka amintar dani daga tsoro
na.....na gode.....na gode".
"Ni banason godiyarki" Ya fada yana zare jikinsa
daga rungumar data masa,ya kuma zura qafafunsa ya fita waje,saidai ya babbake
bakin qofar motar ya zube hannayensa a aljihun rigarsa ya zube mata fararen
idanunsa.
"Me kakeso hamma?" Ta tambaya a sanyaye. Yadda
tayi sanyin ya bashi dariya,ya kalli qasa ya dara kadan sannan ya dubeta.
"Kici gaba da haifamin yara turmus....bibbiyu uku uku
hurhudu harma biyar biyar". Idanu tadan waro waje kafin murmushi ya subuce
mata,kyau tayi masa sosai,sai ya miqa mata hannunsa yana duban idanunta.
"Me kika ce?" Dora hannun nata tayi saman nasa ya
taimaka mata ta fito sannna ta amsa masa.
"Ka tayani da addu'a Allah ya bani masu sauqi,kuma
Allah ya bani ikon tarbiyyantar dasu"
"Zakk iya in sha Allah......am by your side.......na
tsaya miki akan komai sabreen,na tsaya miki,duk wani kalar jin dadi kulawa da
riritawa kikeso....duk wani kalar rayuwa ko kalan abu da kikeso a rayuwa umarni
kawai zakiyi yazo gareki......kaman yaddana taba yowa kaina alqawari saina
cikashi in sha Allah.....zan maida matata ta zama sarauniya cikin mata....zan
sakata da kanta ta dinga jin ita din ta dabance a cikin mata....zata zama wata
gimbiya tauraruwa me haskawa.....shalelen mata wadda mata zasu dinga jin duk
ita suka rako duniya....komai mulkin mace dukiya ko nasabarta idan tazo inda
kike zataji ta koma tamkar baiwa a gabanki......abu uku zuwa hudu ne kawai nake
buqata. Ki soni har abada har Qarshen numfashi so na fisabilillahi.....wuya ko
dadi kar ya zama silar rabuwarmu.
"Na biyu kiyita haifamin yara kina basu
tarbiyya,sahihiyar tarbiyya data dace da addini."
"Na uku ki bani kulawa.....idan zai yuwu ki fifitani
sama da kowa harda yaran da zamu haifa ma". Wannan gabar sai data sakata
sakin dariya.
"Daddyn yara yada haka?" Sassanyan Murmushi daya
qara masa kwarjini da kyau ya saki,kafin ya bata amsa wannan karon sai daya
jawota jikinsa suna iya jin hucin numfashin juna.
"Saboda shi daddyn yafi yaran son mamar tasu.....sannan
shi daddyn yafi yaran sanin tsadarta da kuma darajarta......abu na qarshe shine
ki tsaremin kanki.....ki tabbata a matsayin DUNIYAR MUHAMMAD FU'AD JADDA har
Qarshen rayuwarmu". Tun b'a je ko ina ba da wannan kalaman nashi na qarshe
ya qarasa tashin kanta. Tun ba'aje kuma ko ina ba ta dinga jin kaman zata narke
da wata irin soyayya da qauna me tarin yawa. Tun a nan wajen tasan tabbas tayi
sa'ar miji.....an haifota cikin sa'a.....kalar sa'ar da sai mace me tsananin
sa'a take samunta.
Baya yaja
kadan,yasa hannuwansa yana gyaggyara mata lafayar jikinta.
"Banaso ko ina ya fito.....komai nawa ne.....you're
mine and only mine,all rights reserved".
"Kowa ma ya sani.....basai ka yita maimaitawa ba
yallabai" Muryar farouq ta sauka daga bayansa.
Baiko
waiwaya ba,kaman ma bai fahimci farouq dinne ba yaci gaba da gyara mata
lullubin,a nutse yace.
"Har yanzu ba zaka daina yimin kutse ba kenan
farouqu.....wannan....." Bai qarasa ba saboda idanun da sabreen ke juya
masa tana masa nuni da bayansa. Da ido shima ya tambayeta,tayi qasa da muryarta
kamar me rada.
"Like kaman shi da fannah ne hamma" Shuru ya danyi
sannan ya dage girarsa yana sauketa,yaja da baya daga gabanta sannan ya
waiwaya.
Fannah
dince,tana a gefensa kanta a qasa,kunya kaman zai kasheta. Tasha labarun
soyayyar sabreen da dude enshi,amma bata dauka haka sukejin DUNIYOYIN nasu daga
su saisu ba sai a yau din. Tun daga nesa data hangi yadda guard dinsa sukayi
musu qawanya take mamaki,ta dauka zallar tsaro ne suke bashi,ashe su suna
qarfafa tsinkar fule da fulawar da akeyi ne daga tsakiya. Abun ya bala'in
burgeta,sun kasheta sun kuma tashi kanta,har ta dinga murmushi duk da kunya da
nauyin FU'AD da take danji,don yana mata kwarjini sosai.
"Qaton banza......ka taho da diyar mutane amma ba
zakamin magana ba?" FU'AD ya fada yana hade girar sama data qasa shi a
dole babba. Fannah ta qwaci farouq da dariya ta hanashi bashi amsa.
"Barka da yamma hamma". Qasan ranta tana mamaki
dama yana taba barkwanci haka?,idan kaga face nashi a news ko a news paper ko a
wani taro na kasuwanci ba zaka dauka yana murmushi bama bare akai ga
barkwanci,kaman bashi ba.
"Barka kade amarya.....ya baqunta da sabon guri?"
Ya fada cikin kulawa da girmamawa.
"Alhamdulilah hamma....yame jiki?,Allah ya qara lafiya
yasa kaffara ne" Fannah ta hada duka ta fada don kwarjininsa ya mata yawa.
"Ameen" Ya furta yana jin kalmar kaffara din data
fada tayi daidai da a roqawa maamah ita din.
Gaba yayi
suna jerawa da farouq bayan fannah ta qarasa wajen sabreen suka jera suma suna
gaisawa. Karon farko kenan da suka fara ganin juna face to face,saidai
kowaccensu yanayin nutsuwar dayar tayi mata.
"Ayi mana afuwa,bamu samu haduwa ba,yanayin yazo da
ciwon boss,ba daman nayi nisan zango na barshi,sai yau Allah yayi muka
hadu" Sabreen ta fadi tana dan murmushi.
"Aiba komai.....ana tare ai,shekaru masu yawa a gaba
muna fatan hakan,yana da kyau a kula da boss sosai ai.....kema kuma dole ki
rage zirga zirga ai saboda naki yanayin" Fannah ta fada tana murmushi.
Mamaki yadan kama sabreen,wai cikinta ya soma fitowa ne?duk da fannah din
midwifery ta karanta dama,saita dora hannunta saman cikinta.
"Cikin 'yan uku daban yake ai adda.....sauri girmansa da kuma yawan satittikan da yake
dauka a haifeshi,baya kaiwa dadewar cikin twins ko single baby" Ta fada da
muryarta maras hayaniya. Kai sabreen ta girgiza,bayanin na fannah ya gamsar da
ita,ta kuma fahimta,da alama kuma zata amfana da ita sosai.
A hankali
suke takowa shida farouq din suna tattaunawa.
"Mun jima a asibitin,gida zamu wuce.......amma kunyi
cikakken magana da likitan da yake ganinta?" Farouq ya tambaya da dan
alamun damuwa kan fuskarsa.
"Banganshi ba.....bansan wanne likita ke ganinta
ba.....sai yau na samu shigowa asibitin".
" Why?" Farouq ya tambayeshi yana nuna rashin jin
dadinsa,duk kuwa da cewa yasan komai,saidai muddin dai maamah tana
raye....muddin dai maamah din sunanta mahaifiyarsu ko sau daya bayajin akwai
Randa zaice yayi mata wani rashin kirki ko me tayi.
"Farouq.....Allah ne ya kiyayeni......da taimakon Allah
da taimakon sabreen,banda hakan nima da tuni yanzu ina nan inata checking BP
na......saura kadan jinina ya hau,ciwo zuciyata ta dinga yi,banda dauki da
Allah ya kawomin na bani mace ta gari......hutawa nayi na kwana uku
farouq,bansan da wanne fuska zan kalleku ba kuda anni.....mahaifiyata ta zama
silar da saura kadan anni ta rasa diyarta......wannan sakayyar ya kamata ta
samu ta bangarenmu?" Ya qarashe maganan da alamun abun yana masa mugun
d'aci.
"Dude.....na taba zaginka?.....inajin zan fara wannan
karon" Farouq ya fada ba tare daya dubi FU'AD ba.
"Ashe har akwai banbanci tsakaninmu da ku?,ashe har
akwai abinda zamu yiwa anni ta tsanemu kenan indai zata tsaneku ko.taji
haushinku akan abinda baku kuka aikata ba.....ka saka a ranka ma tun wuri ka
sake gayawa kanka cewa....ni dakai mahaifa daya muka kwanta aka haifomu
tare,kaman yadda musaddiq da saddiq suka kwanta mahaifa daya aka haifosu
tare......har abada ba wani banbanci". Shuru kawai FU'AD yayi,har abada
baisan da meye zaiwa wadannan bayin Allah sakayya ba.
"Ya kamata ka duba yanayin jikin nan nata da kyau,anni
nata yimin fada tun jiya......ina ganin ma kamar qasar ya kamata a fidda
ita....saidai kaje zaka gani,hawan jini yayi mata mummunar kayarwa" Ya
qarasa fada da sautin jimami a muryarsa. Kai ya kada yana nazarin abun,hawan
jinin da baida labarin sadda ta sameshi,ya sake kada kai yana tuna wata kalma
data taba fadawa abbansu randa ya dawo result din kamuwa da hawan jini.
"Kadanma ka gani......shi talauci in gaya maka idan ya
samu ciwo yaga gurin zama kenan....duk talaka da hawan jini yake qarewa,kaga
somi somin daukan hanyar mutuwa kenan,ciwon qoda,hanta,zuciya,lalacewar hanji
duka daga hawan jini yake farawa......bari na fara tanadi don kaina" Tayi
maganar tana miqewa abinta ta barsu a dakin da takardarsa da magungunansa a
leda.
Bai amsawa
farouq ba,illa wani nannauyan numfashi daya sauke bayan ya gama tuna wannan,sai
shima farouq din bai sake cewa komai ba. Ya sanshi,a dabi'arsa ba komai yake
baka amsa ba,idan kuma kaga bai baka amsar ba to lallai baka da buqatar bada
amsar ne.
Dab da
zasu shiga reception na asibitin da zai sadasu da sassan asibitin,sanda guard
dinsa ke clearing masa hanya ya tambayi farouq.
"Inasu saddiq?" Harara ya balla masa.
"Zama zasuyi jiranka?,kwanan amna daya a asibiti abba
yace kowa ya dauki matarsa su wuce gida". Ido yadan fitar.
"Me yasa abba bai bari amna jikinta yayi qwari
ba?" Ido farouq ya zuba masa sannan ya bushe da dariyar mamaki.
"Kana tsoron kada ayiwa qanwarka abinda ka yiwa diyar
mutane ko?,to abba yace ta qarasa warkewa a dakinta..
..kaga malam ka barshi shima ya shana......wannan lamari
baya buqatar shamaki ko shishshigi fa" Farouq ya fada yana dan shafa
gemunsa cikin nishadi. Dunqule hannu FU'AD yayi yakai masa duka
"Sai yanzu kasan haka kenan?"
"Fes kuwa" Ya amsashi yana dariya. Mur FU'AD yasha
ganin su sabreen sun kusa da inda suke,farouq kuma yaja tunga.
"Wucewa zamuyi gida.....zamuzo muku ziyara once kafin
mu wuce honeymoon" Ya fada cikin salon tsokana yana bawa FU'AD hannu.
"Sai kunzo....Allah yasa muma ku samemu" Ya amsa
masa yana bagararwa.
"Iyeeee.....lallai mutumin nan.....baku gaji ba?"
"Kai ka sani" FU'AD ya fada yana danne murmushin
daya taso masa.
Tsayata
yayi a bakin qofar amenity din,suka gama sallama da fannah,sukayi exchanging
phone numbers sannan ta tako ta sameshi. Hannunsa ya sanya cikin nata ya riqe
gam kamar wadda za'a qwacewa ita,har sai data daga idanunta ta kalleshi suka
hada idanu,idonsa ya dauke,sai mamaki kadan ya kamata,kaman ya manta gaban
surukarta maras lafiya zasu shiga?,bazaiyi alkunya tafin hannunsa cikin nata
ba,ta bishi kawai yana tura qofar gami da sanya qafarsa a ciki.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 153
*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada
munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR
GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN
HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road
kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a
duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
153
Har yanzu da
take zaune saman wheel chair din bata daina qoqarin motsa kowacce gaba ta
jikinta ba,duk da hakan baida wani amfani ko qanqani a tattare da ita,kaman
yadda bai kawo wani ci gaba a yanayin da takejin jikinta ba. Ta sake tattara
duk qarfinta a karo na babu adadi don ta samu koda bakinta ne ta motsa tayi
magana,amma kamar dai mintunan da suka shude ko motsi bakin baiyi ba bare akai
ga fitar wani sauti.
"Innalillahi......na shiga uku!" Shine abinda ta
furta cikin zuciyarta,don babu damar yin magana a bayyane bare wani yaju
furucin nata.
"Wai da gaske ne?,da gaske ne ni mariya?,bazan iya yiwa
kaina komai ba?,da gaske ne ni mariya bazan iya tafiya ba?,da gaske ne ni
mariya bazan iya yin magana da kowa ba bare a jini ko a fahimceni?"
Tambayoyin kenan da suka cika mata kwanya da qirji tsahon kwanaki ukun
kenan,kuma bata da wani me iya jin tambayoyin bare ya amsa mata.
Tun daga
kwanaki ukun zuwa yau ko sau daya bataji ta gamsu ko ta nutsu da maganganun
likitocin ba da suketa maimaita maganar hawan jini ne wai ya kamata ba. Tafi
amincewa da cewa tabbas wannan abun daya sameta jifa ne......asiri ne kawai
akayi mata saboda kada taci arziqin d'anta. Mutum biyu take zargi,hajja harira
ko ameena hamza kibiya.
Duk duniya
wadannan mutanen biyu bata da wani abokan adawa sama dasu,bata da wani abokin
takun saqa sama dasu. Duk da kuma tana zargin ameena din,amma zargin nata yafi
qarfi akan hajja.
"Na rantse da Allah na warke hajja bazaki sha ba.....ba
zaki tsira ba....ko ke ko ameena duk wanda yake da hannu cikin maida rayuwata
abun tausayi cikin qididdigaggun daqiqu" Taci alwashin cikin ranta tana
jin wani abu yana tokare mata a wuya me tsananin zafi.
Checking
nata likitan yakeyi yana rubuta bayanan cikin folder dinta yana hada mata da
bayanai duk da yasan bawai zata iya bashi amsa bane,amma yasan tana ji tana
kuma fahimta,maidawar ne ba zata iya ba. Duk abinda yake fadi sam bata bashi
hankalinta bama bare ta tantance ma'anarsa,a nata ganin maganin warware sihiri
tafi buqata fiye da wadannan tarkacen na'urorin da aka zube mata aka. Tayi
imani ba wani hawan jini daya sameta,kawai komai da akeyi din wani bata lokaci
ne na daban,tunda ko hanyar bakin zaren bata ganin alamun daukoshi.
Kaman
kowanne kebantaccen dakin asibiti me cike da tsari shima haka yake. Gadaje guda
biyu qananun sofas guda uku da plastic chairs guda biyu suma.
Yadda
idanunsu suka sauka a kanta haka itama idanunta suka sauka a kansu. Wani
zazzafan abu ya taso ya lullube mata zuciya.
Sosai ta
kafe sabreen da idanu tana dubanta ba tare data dauke dubanta daga kanta ba ko
na second guda. Ita kadai tasan me takeji akan yarinyar......tana kallonta a
matsayin silar komai.....tana dubanta a matsayin wadda ta assasa mata dukkan
wata musiba da take ciki. Gaba daya maganganu akanta da boka ya gaya mata suka
fara dawo mata d'aya bayan d'aya.
"KINYI KUSKURE!" Kalmar farko da ya fadi mata
kenan a kanta,ashe tabbas da gaskiyarsa......da gaske yake kuskuren tayi.....to
amma koma meye wannan kuskuren zata tabbatar ta maidashi kansu muddin lokaci da
dama suka sake waiwayarta.
Abubuwa ne
da yawa suke yawo a zucoyarsa da idanuwansa sanda suka iso gabanta. Kallon da
take binsu dashi tana raba idanunta tsakanin fuskarsa da tata kadai ya gaya
masa komai. Akwai maganganu masu yawa saman harshenta,akwai saqonni masu nauyi
cikin zuciyarta wanda dama bata bata daman furtasu ba......saidai duk wani
yanayi nata.....duk wani motsi nata karantaccen abune a wajensa da koda da
idanu tayi magana zai wahala ya gaza fahimta.
"Sannu" Ya furta mata yana dubanta. Ido ta lumshe
sannan ta budesu,qwaqwalwarta na dawo mata da haduwarsu ta qarshe. Maganganunsa
da sam basuyi mata ciwo ba kaman yadda babbar damar daya bata ta kubce mata
tayi mata ciwo......wata irin gagarumar dama da bata tunanin zuwanta da
subucewarta haka lokaci guda ba.
"Barka da zuwa sir" Likitan ya fada cikin
girmamawa.
Waiwayawa
fu'ad yayi ya kalleshi.
"Yauwa sannu da qoqari" Ya fadi yana jawo kujera
gaban gadon maamahn.
Sabreen ya
waiwaya ya kalla sannan ya kalli kujerar.
"Zoki zauna" Ya fada cikin nuna kulawa. Nauyi abun
yayi mata,sai takejin kamar idanuwa ne da yawa a kansu. A darare ta matso tana
tsarkake sunan Allah ta zauna,tasbihin da tunda ta shigo dakin takeyinsa da
kallo daya data yiwa maamah. Tsaf kamannin maamah din suyi wani irin
juyewa,qasa da awa saba'in da hudu kacal?,iya wannan ya ishi bawa girmamawa ga
ubangijinsa da kuma sallamawa lamarinsa. Tsoron Allah taji yana sake
shigarta,wani bangare na tausayin maamah din ya karyo mata.
"Sannu.....ya jikin?,Allah ya mayar kaffara" Ta
furta a hankali tana son karantar yanayin kallon maamah din a kanta.
Kafe
sabreen din tayi da idanuwa,tana jin wannan dubiyar da addu'ar gaba daya akwai
isgili a cikinta. Akwai maganganu masu yawa data jima tana tanadin gaya
mata,akwai maganganun data tanada saboda rana irin wannan.....ranar sa sabreen
din zata tona mata asiri,ta kuma yaye lullubin sirrin dake tsakaninsu wa
fu'ad......a ranar ta tanadi abubuwan fada masu yawan gaske a kanta. Saidai
kuma ranar tazo mata da wani babban akasi......akasin da babu daman cewa komai
gareta,sai kallo da da idanu,dukkan wasu kalmomi nata suna mata kai kawo
tsakanin qirjinta da wuyanta amma fitarsu ya zame mata wani jan aiki.
Kallon
fuskar sabreen din kadai wani gagarumin baqinciki yake ajiye mata,saidai sanda
ta dauke idanun nata da zummar kauda kanta sai suka fada kan dan matashin cikin
dake kwance a jikinta wanda batasan sanda har ya fara bayyana kansa ba.
Kulle
idanun nata tayi tana jin yadda bacin rai yake hautsinewa a qirjinta yana kuma
bin kowanne sashe da jini ke gudanar mata yana aike mata da saqo kowanne sashe
na jikinta. Batajin zata iya ci gaba da kallonta zaune haka a gabanta,inda tana
da baki da zata gaya mata cewa ta tashi ta matsa daga gabanta ne,amma bata da
wannan damar yanzu haka banda ta kulle idanun.
Sallamar da
aka sakeyi ita ta tilasta mata sake bude idanun nata. Musaddiq ne a gaba,amna
na biye dashi a baya sanye da baqar abaya data fito da hasken amarcinta da
kyau,duk kuwa da 'yar rama kadan dake tattare da ita. Kallo daya tak zakayi
mata ka karanci a tsorace take,tana daga bayan musaddiq din,duk inda ya tsoma
qafarsa ya dauke nan yake ajiye tata. Hannunta riqe da nashi hannun daya bar
mata shi ta baya a haka suka shigo.
Kan
hannun nasu idanunta suka fara sauka,wannan karon yunqurin miqewa tsaye tayi ta
gwada tata jarumtar na UWA kuma wai MAHAIFIYA,saidai kuma kash......ba wani abu
nata daya motsa balle akai ga batun tashin. Gumi sosai ya dinga karyo mata
saboda abinda takeji a zucoyarta,bala'i da masifa ne fal idanu da
zuciyarta,donme musaddiq din zai debo mata diyar alhaji hamzan yazo mata da
ita?,auren da sukayi kadai bai ishesu ba?,har sai sun qara qunsa mata baqincikin
ganin kasantuwarsu a tare?.
"Akwai buqatar ki saka nutsuwa da kauda duk wani bacin
rai daga zuciyarki don a samu a ceto lafiyarki yadda ya kamata" Likitan ya
furta yana dubanta,gumin dake fita a fuskarta kadai ya gaya mishi akwai wani
abu daya motsa zuciyarta,duk da baisan ainihin meye ba.
Tana
labe a bayansa suka qarasa gabanta,ya gaidata gami da yi mata sannu. Leqowa
amna tayi daga bayansa tana mata sannu itama,suna hada idanu ta koma bayan
mijinta ta lafe. Ko kusa ko alama bata qaunar ganin matar,anni ce ta kirata ba
tare da sanin musaddiq din ba tayi yaqi da ita akan ta bishi idan zaije ta
dubata.
"Komai lalacewar tuwo ba'a sauya masa suna.....musaddiq
baida wata uwa bayan mariya,koda ya nuna miki baya sonta wannan wani yanayi ne
ya kawo haka.....batun abinda tayi miki kuma darajar addu'a bata samu galabar
komai a kanki ba,sannan kuma hakan ya zame mata wani sanadi ne na tonuwar
kowanne sirri....kina tunanin ke kika yiwa kanki haka?,ko kadan,darajar addu'a
ce da duban zukata da Allah S W T yayi". Wannan maganar ita ta sanya amna
yin qundumbala ta biyoshi.
"Any progress?" Fu'ad ya tambaya yana duban
likitan. Ajiyar zuciya kawai ya sauke sannan yace.
"Idan zai yuwu muje muyi magana daga office ko?"
Juyawa fu'ad yayi ya yiwa musaddiq inkiya,shi kuma ya waiwaya yana duban amna.
Muryarsa can qasa cikin sigar lallashi ya fara magana.
"Calm down dear......ga adda sabreen ku zauna tare da
maamah......ba abinda zai sake faruwa,yanzun zamuje mu dawo.....okay?" Ya
fadi yana dage mata dukka girarsa gami da riqe fuskarta tsakanin hannuwansa.
Kai ta gyada masa,sai ya sake mata murmushi yaja da baya yana juyawa gami da
bin bayan fu'ad. Saura kadan numfashinta ya qwace mata,wani tashin hankali ya
sake sauko mata.
"Shima musaddiq din haka yake?" Maamah ta tambayi
kanta. Wani irin yanayi ne da batasan musaddiq dashi ba,soyayya muraran da mace
a gabanta?.....wacce irin baqar rana ce wannan take gani?. Dukka yaranta guda
biyu da iyasu ta mallaka a duniya,kowannensu ya dulmiya cikin soyayyar wata
diya macen daban ba ita ba?,wani irin so me zurfin da bataga kwatankwacinsa a
kanta ba a cikin idanunsu?.
Shuru dakin
ya dauka,sabreen tayi qarfin halin sakin murmushi ta kalli amna.
"Ga guri ki zauna amarya.....kada angonki yazo ya
tuhumeni na bar masa me a tsaye" Ta fadi tana ganin yadda amna din taqi
sakewa. Ita kanta ta zama tamkar baquwa a gurinta. Murmushi ta maida mata,ta
tako a nutse ta samu gefan sabreen din ta zauna tana qoqarin sakin fuskarta.
Ashar
maamah keda muradin narka musu ganin suna hira qasa qasa a gabanta amma bakin
yaqi buduwa,game kula kuwa zaiga yadda idanunta suka kada sukayi jajur,daga
amna har sabreen ba wanda ya kula a cikinsu,don sabreen din nata qoqarin jan
amna da hirar da zata sakata sakin jiki.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
154
"Shekararta nawa tana fama da hawan jinin nan sir?" Likitan
daya gaji da ganin abun mamaki tsakanin kwanaki ukun ya tambayi fu'ad.
Kafadunshi duka biyun ya dage yana son gano dalilin tambayar.
"Ba wasu shekaru bane,idan ya dade wata daya....."
"Hamma duka baifi sati uku bafa" Musaddiq ya fadi
yana duban fu'ad. Dauke dubansa fu'ad yayi ya maida ga likitan alamun
"Kaji amsar tambayarka?".
Kai ya
jinjina cikin matsanancin mamaki. Tunda yake kaf a tarihin aikinsa bai taba
ganin mutumin da jininsa yahau har haka kuma yake iya ci gaba da rayuwa ba.
Matakin hawan jininta yakai mataki na qarshe,wanda daga wannan stage din saidai
mutuwa bama stroke ba.....uwa uba kuma tun a kwanakin da aka kawota yake ta
qoqarin ganin jinin ya sauka amma yana nan a inda yake,ba wani ci gaba. Ya
gwada duk wata basira tashi da dabarun aiki amma abun ya cimma tura.
"Sir......munyi mata dukkan abinda ya dace amma ba wani
ci gaba ko nasara koda alamunta kuwa,abinda yafi bani mamaki shine......yadda
hawan jinin yayi mata wata mummunar rafkiya karo daya,nayi zaton tsohon ciwo ne
ma,sa'annan duk wani hanya na sauke jinin wallahi yaqi sauka,abinda yake dada
bani tsoro shine,ci gaba da qin saukar nasa zai iya zame mata sanadin matsaloli
kala daban daban,don a yanzun haka tsoro nake kaman qodarta tana son
harbuwa,bansan me yake faruwa ba,nidai ban taba cin karo da case me kama da
nata ba tsahon shekarun dana dauka a bakin aiki.......amma abinda nake
tunani.......anya ba wani abu babba data sanya a ranta?,ko wani goal da takeso
ta cimma a rayuwarta?,wani matsala dake bata mata rai?". Wani murmushin
takaici ne ya qwacewa fu'ad,wanda tunda suka shigo office din yana tsaye kawai
hannayensa zube a aljihun wandonsa.
Likitan
yayi tambaya a muhallinta,duk duniya shike da amsar wannan tambayar tasa,saidai
abune da bai shafeshi ba,koda ya shafeshi ma labarin zai zame masa wani baqon
labari da ko a duniyar hikayoyi bai taba jin irinsa ba. Uwa nason mallakar d'a
kota mallaki abinda ya mallaka kota halin qaqa?,uwa nason tarwatsa rayuwar
'ya'yanta ta hanyar rabasu da abokan zamansu?......rabo na jikokinta dake manne
a mahaifar surukarta kuma fatanta yabi rariya?,BURIN UWA TARWATSA RAYUWAR
'YA'YANTA ta rabasu da uwa da uban goyonsu da suka zamewa rayuwarsu
suttura?,wacce irin uwa kenan wannan?,baya ga wasu boyayyun al'amura da fadinsu
ma baida dadi koda a baki ballantana ga kunnuwa?.
"Me take buqata?,me ya kamata ayi?" Ya yankewa
likitan dogon tunani da zallar mamakin daya fada
"Tana buqatar kulawa ta wurwuri......kulawa ta gaggawa
saboda gudun rasa wasu bangarori na jikinta,kamar idanunta kunnuwanta ko qoda
ko kuma hanta".
"Yanzu me kake gani za'ayi?" Ya sake tambayar
likitan,yana jin wani tsoron girman Allah yana kamashi. Amsa kuwwar muryarta
yakeji a shekarun baya yanzu haka.
"Shi hawan jini ai baka rabuwa dashi sai ya lalata maka
ji gani qoda ko hanta.......kai kam gaskiya kaman bakayi sa'ar rayuwar duniya
ba?,daga wannan sai wancan?" Tayi maganar tana tsaye a kan abban nasa
sanda duniya tana tsaka dayi mata zaqi da gard'i. A lokacin shi kuma yana
tsugunne a gabansa yana qoqarin ballo masa magungunansa saboda hakin daya
sarqeshi ba qaqqautawa.
"Ina ganin me zai hana ku fita da ita waje?,suna da
kayan aikin damu bamu dasu,zasu sake bincikarta sosai ko akwai wani abun daban
da yake jawo wannan matsalar bayan......."
"Kayi magana da dukka asibitin daya dace ace an kaita
din,ka tura adadin abinda za'a buqata daga dawainiyar asibitin da komai ka
sanarmin ta waya" Ya fada kawai a gajarce.
Yana ji a
jikinsa komai daya kama na neman lafiyarta zaiyi mata shi,bayan ya tanqwara
zuciyarsa wadda kowanne taqi tana tuna masa da yanayin nata action din akan
mahaifinsa sanda yake jinyar ajali. Ya sani idan zai biya ta wannan ko
paracetamol maamah bata cancanci tasha ba ta hannunsa.....to amma har yanzu
huduba da tarbiyyar anni tana yawo a jininsa.
"Uwa uwa ce fu'ad,duk lalacewarta ba wata
madadinta" Wannan maganar ya jima da haddaceta daga bakin annin.
★Cikin sati
guda komai ya kammala na fitar da maamah din qasar Egypt. Fu'ad da kansa yace
musaddiq yayi zamansa su samu hutu sosai da amna,don itama amna din har yanzu
yana ganin kaman bata gama sakin jikinta ba bata warware gaba daya ba. Sanda
yake shirin tafiyar sabreen ta sameshi a daki,ya daga kai daga abinda yakeyi
yana dubanta. Sosai cikinta yake sake bayyana kanshi kowacce rana. Sosai cikin
ke qara mata wani kyau,shi kansa zamanta a jikinta kyau yake mata. Hannuwansa
ya harde yana kallonta da sassanyan murmushin nan nasa. A kwanakin gaba daya ta
sake sauya masa,wani abu me sunan tattali da kulawa da bai sanshi ba yake samu
daga gareta. Wani irin respect take bashi,bai taba jin bashi respect yana
burgeshi ba kaman a kanta,ta maida kanta qasansa sosai,komai zatayi tana nuna
ita din a qarqashinsa take,ita din mallakinsa ce.
"Sun hanaki bacci halan so abbee dinsu suke jira yazo
tayasu hira" Ya fada yana bude mata hannayensa. Bata tsaya wani bata
lokaci ba ta taho ta fada ciki,ta kuma lafe abinta. Ba wani guri da takejin
tsananin aminci kaman qirjinsa,ba wani guri da take ji take kuma samun
cikakkiyar nutsuwa irin qirjinsa,wani guri ne na musamman da takejin duk duniya
bata da kamarshi.
"Na gama shirya nawa kayan fa hamma" Ta fada a
shagwabe. Dan dagata kadan yayi daga jikinsa yana duban fuskarta.
"Zuwa ina kenan adda?".
" Egypt mana" Ta fada a shagwabe tana maqale
kafada. Kai ya girgiza yana sakinta sannan ya fara takawa yana barin wajen
"No.....zaki zauna a nan har mu dawo,kinsan yanayin da
kike ciki ai ko?,ko kin Manta wani hutun nake shirin baki ma?". Batace
masa komai ba har ya qare zancen,saita sauke hannayenta data harde a qirjinta
tana takawa a hankali zuwa inda yake zaune yana basarwa ta hanyar qirqirar wani
aikin.
Dab dashi
ta zauna har jikinsu yana gogar na juma,tasa hannunta ta jawo fuskarsa zuwa
inda take kaman yadda shima yakeyi mata.
"Nasan me kake tunani,nasan abinda yasa ka fadi haka
kuma.....amma kada ka manta.....har yanzu maamah uwa ce.....kuma nidin nayi
alqawarin riqe hannunka gam,zamuyi tafiya bisa tafarkin rayuwa a tare,da dadi
ko babu dadi right?". Kansa ya daga a hankali yana dubanta,ya rasa wadanne
irin mutane haka Allah yayi masa rahama da ni'ima dasu?,sam basa duba sharri
sai alkhairi a tare dashi,duk da irin uwar da Allah S W T yayi masa jarrabawa
da ita.
"Koda maamah zata kasance me laifi a waje na.....nikam
na yafe mata,har abada babu wata uwar da zata iya haifamin muhammad jadda sai
ita.....ta kuma haifamin din,ina da abinda zan iya saka mata dashi?".
Idanunsa ya lumshe kawai yana jin yadda soyayyarta ke tsatstsaga jikinsa.
Addu'ar mace ta gari da yayi Allah ya bashi ma sama da abinda ya roqa din,yana
jin kunyar idanun kowa......yana jin kunyar sanyasu su yiwa maamah wani hidima
bayan dukka tarin sharrance sharrancenta a garesu,wanda har zuwa yanzu shikam
yana ji a a jikinsa maamah din bata hau sirad'al mustaqeem ba da gasken gaske.
Hannunta
ya riqe sosai cikin nasa da wani irin taushi.
"Na gode sosai my world......na gode duniyata".
Murmushi ta sakar masa
"Ba godiya tsakanina dakai.....kome nayi maka kafi
qarfinsa a wajena".
Tafiyar
sai ta kasance me sassauci a tare dashi,don kasancewar sabreen a tare dashi
cikin kowanne motsi a rayuwa ba qaramin qarfafa masa gwiwa yakeyi ba. Sun isa
Egypt bisa jagorancin Dr awwab,an kuma gabatar da maamah ga qwararrun likitocin
asibitin,wadanda suka dauki kwanaki suna dukkan bincike da gwaje gwaje.
To sakamakon
dai guda daya ne,hawan jini ne me tsanani da har a Egypt dinma dai bai sauka
ba,sai kuma wani abu data qulle a zuciyarta da suke ganin kaman shima yana
barazanar taba lafiyar zuciyarta.
Sabreen
ta girgiza matuqa,jikinta kuma ya sanyaya,ta qara cika da mamakin maamah,ta
kuma sake sallamawa lamarinta,ta qara yarda da imani da yaqinin lallai wanda
Allah ya shiryayye......ba wanda kuma ya isa ya shiryar da wanda Allah ya
batar. Daga idanun maamah da kallon da take binta dashi duk da kalar hidimarta
gareta ta karanci ba wani rusunawa ko nadama a tattare da ita......qaddararren
ciwon daya zama jarrabawa game hankali ne kawai yayi mata cikas ya hanata duk
wani sukuni.
Daga
qarshe sun yanke zasu ci gaba da bata kulawa har na tsahon wata guda suga
abinda hali yayi. Da taimakon qwararun nurses dake kula da maamah din aka soma
dorata akan magunguna da therapy kala kala. Duk da akwai masu kula da ita din
sabreen bata zauna ba,saidai ko yanzun sabreen ce zata bata abinci ba zata
karba ba. Da idanu take kafeta,wani abu yana sake mata ciwo,duk sanda ta
kalleta zuciyarta tana gaya mata.
"Yarinyar tayi winning a kanki,ke gaki a zaune saman
wheelchair ko yatsarki baki iya dagawa". Rana ta farko da zuciyarta ta
gaya mata haka bayan sun gama zama da ita ne sun wuce masaukin da suke kwana.
Kuka sosai
ta dingayi,hawaye shabe shabe daya na bin daya,hawayen zallar baqinciki faduwa
da kuma asarar da tayi.
Hakanan
nurses din dake kwana da ita suka taru a kanta suna lallashinta,amma taqi
tsaida hawayen tamkar ma suna tunzurata. Haqurin da suke bata ma sake bata mata
rai yakeyi,ta rantse inda bakinta yana magantuwa su kansu da sai sunji magana
iya magana.
Jirigi
guda musaddiq da amna,farouq da fannah......saddiq da huda wadda ta soma
murjewa ta fara qiba suka shigo Egypt duba maamah din.
A ranar
taga baqar ranar da zata iya cewa kaf fadin rayuwarta bata taba ganin irinta
ba. Kowa yana zaune da qugunsa......yana takawa da qafafunsa....hannu kai da
qafufuwansu dama bakunansu gaba daya suna aiki amma banda ita?,banda nata?,ita
kadai dai komai a kanta ya qare?. Wannan tunanin ya sake sakawa ta dinga fitar
da hawaye,har numfashinta ya sarqe saida likita ya shigo ya mata allurar bacci.
"Har yanzu akwai wata danqararriyar damuwa a
ranta.....kuma indai bata cireta ba treatment dinmu bazaiyi aiki ba,jininta
bazai taba sauka ba.....tana da ciwon tun asali tayi wasa da magungunanta har
sai daya zame mata haka,qodarta ta fara nuna alamun failure.....duk yadda
zakuyi ta cire damuwa a ranta". Bayanan da likitan yayi musu kenan.
Dukkaninsu sunsan wani abune me suna gaibu tilasta maamah ta cire damuwa a
ranta,damuwar da dukkaninsu suka kasa gane ta meye idan ka dauke fu'ad sabreen
da musaddiq.
A nasu
hasashen it's high time ace maamah ta cire komai a ranta,so ba damuwar
dabi'unta bane na baya,saidai fu'ad sabreen da musaddiq sunsan cewa HALI ZANEN
DUTSE......BARIN HALI KUMA SAIDAI MUTUWA.
*_TURQASHI.....WAI ME KARATU NACE BA.....WAI SAI YAUSHE NE
MAAMAH ZATASAN ANNABI YA FAKU?,SAI YAUSHE NE HALINNAN ZAI CANZA?_*
155
★Cikin wata
gudar nan da suka dauka mata ba wani kalar treatment da ba'ayi mata ba. An
kashe kudi sosai anyi amfani da engine da fikira da fasahar dan adam a kanta
amma ba wani canji ko qanqani da aka samu. Duk wata lalurarta saidai ayi
mata,bata tsinanawa kanta komai don ko yatsanta bata mallaka ba,bata isa ta
juyashi ba bare sauran sassa na jikinta. Idanu da kunnuwan ne kawai suke
aiki,banda su za'a iya cewa komai a jikinta ya tsaya a aiki idan ka cire ZUCIYA.
Wannan
zuciyar dai da annabi yake mana gargadi da jan kunne a kanta,wannan zuciyar dai
da yake gaya mana idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan ta baci dukkan jiki
ya baci. Wannan zuciyar dai wadda da ita ake gwada nagartar bawa.....wannan
zuciyar dai wadda da ita ake ganin qarfin mutum,ba qarfi na jiki ba ko qarfi na
dukiya ko qarfi na mulki ko qarfin iko ba.
(Ubangiji don girman al'arshinka kasa mufi qarfin
zuciyarmu,ya Allah kasa mu mallaki zukatanmu don hasken fuskar manzan
Allah,wallahi wallahi duk wanda kaga yayi qarko to tabbas ya mallaki zuciyarsa
ne......yafi kuma qarfinta,ya haneta aikata abubuwa masu yawa daba daidai
ba,dukkaninmu kowa yasan daidai yasan kuma ba daidai ba,kubutacce a cikin mu
shine wanda ya mallaki zuciyarsa yaji tsoron Allahnsa akan komai na duniya da
lahira,yake kuma aiki da nasa hankalin).
Dole
hakanan don ba yadda za'ayi mata suka tattara suka koma gida nigeria da sauran
tarkacen kayan therapy din da za'a iya siya mata,wadanda zasu dinga motsa mata
gabbanta,kaman yatsun hannu da sauransu.
Ma'aikata dole ya sanya aka samo masa ya dauka,wadanda zasu kula da ita
da komai nata. Wankanta,cin abincinta,sallarta tsaftar kanta data jikinta.
Already tana da masu aiki dake tsaftace gidan suyi girki,akwai guard kuma a
gaban gida da farfajiya masu kula da gidan gaba daya.
Rayuwa
duk yadda kayi haka za'a yi maka,Allah da kansa yace wadancan kwanakin sune
muke juyasu tsakanin mutane,kwatankwacin karin maganar bahaushe da yake cewa
YAU GAREKA GOBE GA DAN UWANKA.
Wata
babbar dama ce ta samu ga wadannan ma'aikata da aka dauka,sabbi da kuma wasu
daga cikin wadanda suke cikin gidan. Bude cin karensu babu babbaka sukayi,kowa
yayi abinda yakeso a sanda yakeso,a kuma yanayin da yaga dama. Bata da bakin
magana sai idanu,sai tarin baqinciki da takeji kaman zai kasheta.
Idan
tayi bayan gida ko fitsari,muddin fu'ad ko musaddiq basa nan sai ta gane
kurenta. Don zasu barta da abinta sai sun gama sharafinsu sannan suzo su wanke
su gyarata bayan sun gama tsaki toshe hanci da harara da baqar magana. Tanaji
tana gani duk wani abu da yake mallakinta ita keda iko dashi sunayin yadda
sukaga dama,da sunji alamun zuwan musaddiq ko fu'ad harma da
sabreen......yanzun nan zasu dawo gabanta su zauna suna nan nan da ita. Takan
yawaita kallon fu'ad din,tanason gaya masa irin abinda suke aikata mata amma ba
wannan damar,ba bakin magana,tana ji tana gani zasu gama abinda zasu yi mata su
fice,su kuma su dora daga inda suka tsaya.
Duk
abinda mutum yake akwai ranar da dubunsa zata cika,khairan au
sharran......muddin kaga ka dade to Allah yana qara maka lokaci ne yaga ko zaka
tuba?,ko zaka gyara kurenka?.....ko zaka gano kanayin ba daidai ba?....kaman
yadda bahaushe yace komai nisan jifa qasa zai fado.....komai girma gona akwai kunyar qarshe.
A irin
wadannan ranakun Allah ya kawo sabreen katsam. Basuyi zaton zuwanta ba,don ba
lokacin zuwan nata bane. Yanayin da taga sun watsar da maamah din ya daga
hankalinta sosai. Hawaye kawai ta dinga yi tsoron Allah ita kanta yana sake
shigarta,wato dan adam ba kowa bane.....kaman yadda yake ba'a bakin komai ba.
Girman kai dagawa da mugunta dukka idan kaga mutum yana yi Allah ne ya ara masa
lokaci,dama ce wadda idan yaga dama ya qwaceta shikenan ta tafi kenan har gaba
da abada.
Ko a
mafarki akace mata maamah din zata dawo haka ba zata gasgata ba......ko da wasa
aka ce mata akwai lokaci me zuwa kaman haka ba zata yarda ba......matar dakeji
da dukkan wani izza taqama da gadarar qarfin iko,yau gata zaune waje daya,ko
ruwa bata isa ta bawa kanta ba idan ba'a bata ba.
Kaf
ma'aikatan gidan ta tattara,bayan ta gama jin ta bakin amintaccen malam
sa'adu,wanda ya gama karantar halin kowa. Da kanta ta yanke hukunci ta sallami
dukkan wanda lambarsa ta fito na baqin hali da mugunta. A ranar tayi kuka tayi
kuka,kukan tausayin kanta a matsayinta na 'yar adam wadda itama haka tana iya
kasancewa a kanta. Tun fu'ad na lallashinta har ya rasa ta ina zai bullo mata.
Ya dafe habarsa kawai yana kallon yadda tasa ciki a gaba tana kuka. Kuka akan
maamah?,duk sanda ya tuna da wannan abun yana bashi mamaki.
Baiyi
zaton koda mutuwa maamah tayi ba hakan zai d'a d'a sabreen da qasa ba
"Ya ilahi......wacce irin zuciya ce da ita?" Ya
tambayi kansa da kansa yana sake jinta har cikin qasusuwansa. Ya tabbatar
kyakkyawar zuciya kawai baiwa ce......baiwa ce da ba kowa Allah yake yiwa ita
ba,baiwar da tafi duniya da abinda yake cikinta alkhairi.
"Ya isa haka sabrrrr.......ya isa.....babies dinki
karsu dauka nina taba musu maamah fa" Ya fada cikin damuwa. Shi kansa ba
jin dadin ganin maamah a haka yakeyi ba,to amma yasan cewa duk wani abu daya
dace suyi mata sunyi mata shi,hukuncin Allah ne kawai yake aiki a kanta.
Duk runtsi
duk yanayin aikinsa sau biyu shida musaddiq suke zuwa,da safe da kuma yamma
wani kuma yaje da dare. Har yanzu wannan ruhin da wannan zuciyartata basu gama
yin laushi ba,abinda yafi komai dagawa fu'ad din hankali kenan. Idan kaga tana
gumi sosai to musaddiq yaje shida amna,ko ta ganshi tare da sabreen ko kuma ta
zubawa cikin jikin sabreen din idanu.
A yadda
sabreen ta damu da maamah yayi tsammanin zuciyarta zata sanyaya da dukkan
komai. A yadda ta wahal da amna ta nemi rayuwarta ya zaci yanzun zatayi nadamar
aikata mata abinda ta aikata mata. Kai tsaye ya hana musaddiq zuwa da amna
kwata kwata,don itama 'yace me cikakken 'yanci da iyayenta ke matuqar
qaunarta,bai kamata a dinga razana rayuwarta da qananun shekarunta ba ta hanyar
zuwa da ita inda takeji kullum bata da security.
Wannan
karon saida sukayi bincike sosai kafin daukan masu mata hidima,asalin garinta
na haihuwa suka shiga tushenta,suka samo amintattun mata da suke da dangantaka
da maamah din. Wasu ma cousins dinta ne......amma yanayin rayuwa ya sanya duk
suke kaman sun girmeta. A asali nutumin karkara mutum ne me karamci mutunci da
kuma martaba dan adam......mutum ne me juriya da amana,har yanzu akwai ire
irensu.....cikin taimakon Allah suka samo mutum shida a cikinsu. Uku mata uku
maza,da farko ma sunce kyauta zasu kula da ita,saboda Allah saboda kuma girman
zumunci. Basuyi fushi ko zuciya da yadda ta watsar dasu ba,saidai fu'ad bai
yarda ba,ya yankawa kowannensu albashin da iyalinsa zasu rayu cikin wadata da
nutsuwa.
A duk
sanda yaje dubata,ya cire duk wani shiga nashi na office don gyarata ko mata
wata hidima mamaki sukeyi. Babban mutum kamarshi?,wanda bai rasa komai ba?,amma
yana iya tsaftace qazantar mahaifiyarshi?,ko yayi mata brush?,ko ya azata saman
keken dake mata massage da sauran exercise na jiki?.
Abu daya
da yakan tuna a ko yaushe a kanta shine girman haqqin uwa......uwa uba kuma
maamah din a yanxun abar tausayi ce ita,koda ita batasan hakan ba,koda har
yanzu zuciyartata batayi laushi ba.
Daya daga
cikin ranakun da suka sake sanyaya jikin sabreen game da maamah. Ranar wata
Wednesday ne,ranan kwanaki biyu suka rage ita da fu'ad din su koma madeena umra
da kuma duba lafiyarta dana babies dinta,a asibitin da fu'ad yayi mata register
na komai. Burinsa a duniya a haife masa yaran a garin manzon rahama annabi
Muhammad,garin da jikin masoyi farin haske farin jakada yake kwance a ciki wato
madeena.
Tazo ta
samu masu kula da ita sun gama mata komai. Ta qarasa kujerar dake gefan
wheelchair dinta suna gaisawa da ma'aikatan,idanunta yana kan maamah din. Ta
rame sosai,duka idan ka kalleta ba zakace mariya bace.
Kwanakinnan da cikinta ya sake turowa ya fito sosai bata kallon nata.
Kallo daya tak idan tayi mata to koda awa nawa zatayi da ita ba zata sake daga
idanunta a kanta ba.
Zama
suke na kaman qawaye da masu aikin,don haka yawancin lokuta idan tazo cewa take
su zauna ayi hira,a nata lissafin wai ko hirar zata daukewa maamah din kewa.
Yanzun ma
hira sukeyi lokaci lokaci suna kallon wani hausa film. Sunason kallo sosai,kuma
bata hanasu ba indai sun gama duka ayyukansu.
Musaddiq ne
yayi sallama,suka amsa masa,ciki harda sabreen cikin mamakin jinsa a irin
wannan lokacin. Kwata kwata ba lokacin zuwansu bane,saidai kafin ta dauke
idanunta amna ta biyo bayansa.
Doguwar
riga ce a jikinta da qaramin hijab,kallo daya tayi mata taga kaman ta fada.
Yau din ba
wannan tsoron sosai a tattare da ita,ta tako kaman yadda mijinta yayi ta qaraso
gaban maamah ta gaisheta ta kuma dubata sannan ta matsa gefe kusa da sabreen ba
tare data damu da ko idanu maamah din bata daga ta kalli amna ba.
Sun gaisa
da sabreen kafin amnan tayi shuru. Sabreen ta daga kai ta kalleta da dan
mamaki. Amna ba kasafai zata zauna tayi shuru haka ba,abune me wahala musamman
idan akwai sabo tsakaninku. Dan tabota tayi,ta daga kai ta kalleta,sai ta sake
mata murmushi,itama amnan ta maida ma sabreen
"Lafiya kuwa auta?" Sabreen ta tambaya. Kaman
jirar tambayar aman da ya taso mata yakeyi sai ya qarasa fitowa zuwa sarari.
"Subhanallah" Sabreen ta fada a rude ta miqe tana
riqe amna din dake sake galabaicewa.
Kaman
ya mance a inda yake,gaba daya yayo kan amna din yana rungumeta ta baya hadi da
riqeta sosai hankalinsa yana tashi. Sannu kawai yake jera mata,har zuwa sanda
ta kammala aman,daya daga cikin masu aikin maamah din tuni harta dauko kayan
aiki tahau gyara gurin,sauran kowacce sai jera mata sannu suke cikin kulawa da
tausayawa.
Idanu maamah
ta zuba mata tana jin qwayar idanun dama kewayenta gaba daya sun budade da
yaji,tamkar an damqi garin yaji an watsa mata. Wani lafiyayyen gumi ya soma
karyo mata,ta kasa dauke idanunta daga kanta zuciyarta na wani irin mahaukacin
bugawa.
"Da ka sani musaddiqu ai baku fito haka nan ba"
"Daga asibiti muke......tun shekaran jiya bata da
lafiya taqi kuma yarda aje asibitin saboda tsoron allura......ganin ban samu
shigowa da safen ba sai nace bari mu shigo mu gaida maamah saimu wuce
gida" Ya amsa mata yana goge mata jiki da tissue.
"Allah ya sawwaqe.......Allah ya inganta......mu saidai
mu tayaku da addu'a ai,shekara ashirin rabona da haihuwa yanzu haka" Ta
fada cikin raha tana murmushi.
Murmushi sabreen ta saki,sai a yanxun ta gano bakin zaren,wato shima
musaddiq yayi nashi aikin. Murmushin da yazo wuyan maamah ya tsaye mata,sai
taga kaman dariya sabreen take mata,kaman sabreen tana gaya mata KE DIN LOSER
ce,kowa yaci nasara a kanki,abinda ya sanya wani tari ya sarqeta ta soma
qoqarin zamowa daga saman wheelchair din saboda yadda zaman ya gagareta.
156
"Subhanallah" Musaddiq ya fadi da sauri yana isa gareta ya
tareta kafin takai qasa. Hawaye ne suka qwace mata,inama ace tana da ikon
tureshi,ba shakka da sai tayi masa mummunar turewar da bazai sake sha'awar zuwa
kusa da ita ko kawo mata dauki ba.
Ciccibarta
yayi yana maidata saman wheelchair din sannan ya daureta da belt din da suke
jiki. Komawa yayi gabanta ya zauna yana duban fuskarta yana kallon gumin da
yake tsatstsafo mata. Ba ita ba.....shi kansa radadi zuciyarsa take masa,saidai
akwai banbancin radadin da yakeji da kuma wanda ita yakeji. Ita nata radadin na
baqincikin rayuwar wasu ne,qyashi da kuma baqar hassada. Yayin da nasa radadin
ya ta'allaqa ne da yadda kullum zuciyarta ke sake gurbacewa,duk da irin yanayin
da take ciki,duk da irin qalubalen da take fuskanta amma hakan bai sanya ta
haqura ta ajiye koma meye da yake zuciyarta ba.
"Maamah" Ya kira sunanta kai tsaye da wani irin
sauti bayan ya yiwa masu aikin alamar su fita. Jajayen idanunta ta daga ta
kalleshi dasu,tana da magana fal bakinta saidai ba damar hakan.
"Kiyiwa Allah.....kiwa manzon Allah......na roqeki ko
meye muka yi miki a rayuwa.....ba domin kanmu ba don lafiyar jikinki ki manta
da komai........ki duba girman Allah ki sassautawa zuciyarki......haba
mana!" Ta furta da wani irin bacin rai da yakeji yana taso masa.
Idanu tsaf
ta zuba masa,abinda ke nuna inda bakinta a bude yake tabbas da yaji
maganganu,saidai ko a iya kallonta a kansa kawai ya shaida masa maganarsa ta
shigeta da wani kalar mamaki.
"Ba wanda ya isa ya canza qaddarar wani.....ba wata
qaddara da zata sauya kanta da kanta sai wadda ubangiji da kansa yaso
sauyata.......ba wani dan adam da zai tsarawa wani rayuwarsa......kowa da yadda
Allah ya tsara masa.... Me yasa ba zaki hutar da zuciyarki ba?" Ya sake
fadi yau din yana jin zuciyarsa takai maqura.......a yau din yana jin yana
yanke dukkanin tsammaninsa da sauyawar halaye da dabi'un maamah.
"Ki yafe mana idan mun miki wani abun.....me zaki ragu
dashi?" Ya qara tambayarta yana kallonta. Ba amsa,amma still hawayen basu
daina fita ba
"Ko bayan an cuceka ka yafe.....ba zaka ragu da komai
ba sai qaruwar daraja a gunka......ki yafe mana indai mun miki laifi muddin
kedin ke kika haifemu" Ya qara fada yana hade hannayensa waje daya alamun
roqo.
"Indai kun yadda ni din nice na haifeku me yasa ba zaku
yimin abinda nakeso ba?,indai kun yarda nice na haifeku me yasa ba zakubi
umarnina ba?,me yasa ba zaku kwanta nayi muku mulki irin na isassun iyaye
ba?,me yasa ba zaku fahimci asiri akayimin ba?,me yasa ba zaku gane ba hawan
jini bane wannan?!" Wadannan sune kalaman da suke ta kokawa a qirjinta
suke koma neman hanyar da zasu fidda kansu,saidai kuma ba wannan damar,illa
hawayen baqincikin rashin samun damar magana da batayi ba da suka sake wanke
mata fuska.
Tsam ya
miqe kawai,ya kama hannun amna da jikinta ya sakeyin laushi qwarai bayan aman
da tayi,ya miqa mata takalminta ta sakawa qafafunta suka fice a parlor din
sabreen da maamah na binsu da kallo,kowa da mabanbancin yanayi cikin zuciyarsa.
Tausayin
musaddiq da hammanta kullum take kwana take tashi,bata tunanin duk yadda sukaso
maamah ta shiryu idan har ubangijin daya halicceta bai shirya mata hakan ba
saidai kowa yayi haquri. A zuwan da take dubata da duba yanayin gidan da masu
kula da ita.....ba kalan lokutan da bata kebe ba zaune da ita,daga ita sai
maamah din ta karanta mata dukkan kalar wata nasiha me ratsa jiki da
zuciya......amma bata taba ganin alamun rusuna ko sanyi daga idanuwanta ba.
★"laila"
Hajja harira ta sake kiranta karo na biyu. Daga kai lailan tayi wadda ke zaune
qasan carpet din dakin ta kalli mahaifiyar tata.
"Na'am hajja" Ta fadi dukkanin wani lungu da saqo
na zuciyarta dama gangar jikinta suna azalzalarta,tana jin kaman wuta ake
hurawa sassan jikinta dama zuciyarta.
"Wacece ni?"
"Mamana ce" Ta amsa mata Kai tsaye idanuwanta kafe
a kanta.
"Alhamdulillah" Hajja ta fadi tana sakin murmushi.
Cikin zuciyarta cike fal da godiya ga bokan da yayi mata aikin farraqu tsakanin
maamah da laila,ya gaya mata cewa wannan din qaramin aiki ne da zai iya
aiwatarwa,ya mata alqawarin sai yazo duk duniya ba wanda laila taqi jini taji
koda sunansa sama da hajiya mariya.
"Zaki koma wajen maamah mariya?" Hajja ta gwada
tambayar laila. Shuru ta danyi na wasu sakanni,sai kuma ta girgiza kanta da
qarfi.
"Bana so,bazan koma ba,ina wurin hajja na". Ta
fadi bawai don tana nufin abinda ta fada din bane da gaske har zuciyarta.
Da dariya
ta qyalqyale sosai,farinciki yana cikata,lallai laila dinta ta dawo,ta dawo
hayyacinta.
" Na godewa Allah daya dawomin dake hayyacinki
laila" Murmushin qarfin hali ta sakarwa hajjan,tanason ta sake bata
tabbaci da yaqinin ta warke don ta ware mata takunkumin hana fita da sanya masu
gadi su hanata fita ko nan da can. Ba abinda takeso irin taje wajen maamah,ta
duqufa tayi ta mata bauta iyakar qarfinta.
"Na warke hajja in sha Allahu,kawai zaman cikin gidan
nan ne hajja na gaji.....ko cikin layinnan kya barni na tattaka da qafafuna
ko?" Ta fada a shagwabe kaman yadda take mata a baya.
Fuska
hajja tadan bata tana dubanta.
"Aah......ba yanzu ba laila,matar nan makira ce,duk da
ance tana can tana jinya amma ba Allah a ranta,kina kallon yadda take
kidnapping 'ya'yan jama'a fa?" Hajja ta fadi tana nunawa laila girman
ta'addancin maamah.
Wani irin
tashin hankali da kuma bacin rai ne suka bijirowa lailan,ta tabbatar yau ko
gobe Hajja ba zata barta ta fita ba bare ta koma wajen maamah,kenan ba amfanin
rayuwarta ba tare da maamah ba?". Ta yiwa kanta wannan tambayar.
A take taji
indai za'a yanke alaqarta da maamah bata da wani amfanin rayuwa,don haka ta
miqe tsam.
"Bari naje kitchen nasha ruwa"
"Ki tahomin dashi" Ta fada hankalinta kwance don
tasan a kitchen din dai ba wata hanyar fita daga sassan ma bare akai ga gidan.
Idanu kawai
take warawa sanda ta shiga kitchen din,gaba daya kwanyarta a birkice take,neman
abinda zatayi amfani dashi kawai take yi idanunta suka sauka kan gas.
Da sauri ta
qarasa wajen,ta saka hannu ta kunna dukka makunnansa guda hudun da yake dasu.
Fita ya fara yi sosai,kafin kace meye wannan warinsa ya mamaye kowanne sashe na
part din hajjan.
Hancinta
sosai hajja ta dinga budewa tanason tabbatarwa warin gas dinne?. Da wani irin
sauri ta duro daga saman gadon tayi kitchen da mugun sauri. Duka masu aikinta
ba kowa yau ballantana tayi tunanin wani ne a cikinsu,laila kawai tasan ta
shiga kitchen din.
Cak ta
tsaya daga bakin qofar falon,qafafuwanta suna rawa zuciyarta na wani irin gudu
mara fasali. Laila ce tsaye a kitchen din riqe da lighter,idanuwanta fes kan
hajja dake tsaye daga can bakin qofar kitchen din.
"Laila.....laila baki da hankali ne!!!" Hajja ta
fadi a birkice ganin lailan tana qoqarin motsa yar robar data tare bakin
lighter din wadda ita zata bata damar tashi. Wani kalar murmushi ta saki tana
duban hajjan
"Kina tunanin zan iya rayuwa ba tare da umarnin maamah
ba?,ko kina tunanin zan iya rayuwa a inda babu ita?.....sai watarana
hajja" Laila ta fada cikin qwarin
gwiwa.
A gigice
hajja ta bude baki tana son gaya mata cewa.
"Kada ki kunna laila.....indai mariya c na bar mata ke
har abada,ki hada kayanki ki koma gareta" Saidai dukka wadannan kalaman
basu samu damar fita daga bakinta ba sai hucin tsananin atsabar zafin wuta da
qarar bindigar fashewar tukunyar gas din da suka cakude waje daya aka wullota
waje,wanda daga nan bata sake sanin abinda yake faruwa ba.
Qarar
fashewar taja hankalin sassan matan 'ya'yanta da masu gadi dake waje,kafin
balbalin wutar ya tashi hankalin kowa suka nufo sashen hajja din.
Duk
saurinsu turus kowa yayi,saboda wata irin muraddiyar wuta ce me azabar duhu da
Zafar tana harshe ke cin kowanne sashe na hajja din. Babban sashe da yafi na
kowa cikin gidan girma kyau da tsaruwa,sashen da idan ka kalleshi ka kalli na
matan 'ya'yanta saika dauka su din duka sashen ma'aikatan gidanne wato boys
quarters,duk kuwa da cewa mudin na mazajensu ne,dasu akayi wahalar nema da kuma
samu.
Tashin
hankalinsu waye da waye a ciki?,suna tsaka da son tantancewa sukaci karo da
hajja yashe a qasa,wadda babban jikanta ne kawai ya iya gane itace,saboda shi
dinma ya shiga dazu kai mata wankinta ya gane atamfar jikinta,fuskarta kaf da
kafadunta zuwa qirjinta sun koma jazur kaman an shafeta da jar hoda saboda
yadda wutar ta kwaye asalin fatarta.
"Na shiga uku......wayyo Allah na..... Wayyo
laila......laila kada ki mutu ki barni......laila bansan kanki abunnan zai koma
ba,wallahi laila bake nace a bawa kici ba......laila don Allah ki fito
laila......naci buri a kanki,na shiga uku" Sune maganganun data dinga fada
tana ihu tana kururuwa gami da zabura,azabar zuciya dana gangar jiki duka sun
isheta aka wuce da ita asibiti cikin ambulance bayan anyi kiran fire service
suzo su tsaida watar kada ta soma lasar sassan gidan.
Abun kamar
film kamar almara,ana fita da hajjan sanda wutar ta cinye sassan
sarai,surukanta dukka dake tsaye a wajen sai kowacce ta dafe kanta.
"Wayyo Allahna.....wash Allah na.... Wayyo kaina"
Shine abinda suka fara fadi a jejjere,kafin kace meye wannan sai gasu duka su
ukun a zube warwas a qasa sun sume.
Akwai
wani malamin makarantar almajirai dake a wajen,kallo daya yayi musu yace basai
an kaisu asibiti ba,babban falon gidan yasa aka ajiyesu,ya karbi ruwa yayi musu
tofi sosai ya bawa mazajensu yace a yayyafa musu idan sun farka a bawa kowacce
tasha.
Cikin qasa
da minti biyar sai gasu a zaune,kowaccensu kuka takeyi wiwiwi
"Wallahi saika sakeni......wallahi bazan sake zaman
bauta ba..... Idan ta dawo kuma me ya rage mata?,inajin sujjada zata saka mu
koma yi mata" Shine abinda matan kowacce ke gayawa mijinta cikin kuka.
Duka falon sai ya rikice,ga gobara a waje ga tashin hankali a cikin gidan,su
kansu mazan a rude suke,don sam duka abinda matan ke iqirari akai ba wanda
yasan anyi a ciki.
Gyaran
murya malamin yayi ya kuma nemi su bashi hankulansu. Bayani ya musu me ratsa
jiki game da lamarin,kusan abune da kaf unguwar ake magana akai yadda take
bautar da uban kowa cikin gidan,kusan duk me hankali yasan aikin sihiri ne.
"Indai har zaku yarda da shawarata ku yafewa mazanku,ku
sake sabon zama dasu don ba cikin hayyacinku dukka kuke ba,wataqila wannan
gobarar ta qone duk wani binne binne ne shi yasa komai ya warware kansa.....sai
ku bita da addu'a Allah ya bata lafiya ya sake fahimtar da ita ainihin
rayuwa.....". Da wannan bayanin nasa ya kashe wannan qurar,hankula kuma
suka koma kan wutar dake ci wadda an fara samun daman kasheta.
157
★Tana
kwance saman kyakkyawan gadon,sanye da fara qal din abaya har veil din da tayi
rolling dashi,kaman yadda siraran abun hannun azurfa da zobensa da set din dan
kunnensa suka sake qawata mata shigar tata.
Duk da
tsufa da nauyi da cikinta yayi hakan bai hanata ado ba......duk da yadda take
komai da qyar amma bata yarda ta bari tayi mummunan kama ba.
Ko a
yanzunma akan gadon scanning take,daga daidai kanta kuma muhammad fuad jadda
ne. Sanye yake da farar jallabiyya ta maza saqar morocco wadda ya yiwa ado da
farin hirami daya zauna sosai a kansa,saika rantse da Allah dan asalin qasar
saudiyyan ne. Wani irin ajiyayyen kyau na musamman shigar tayi masa,jikinsa da
fatarsa dukka suna nuna zallar hutu da jin dadi gami da cikakken sukunin rayuwa
da Allah ya bashi. Saman kujera hake,hannunsa cikin tsakiyar tafin hannunta,ya
sarqafe yatsunta cikin nasa.
Daga
shi har sabreen din idanuwansu suna kan allon computer din,wanda balarabiyar ke
yawo da kan na'urar saman cikin sabreen din da yayi wani irin girma.
Sai data
kammala scan din tsaf,sannan ta dora hannunta saman board din computer ta danna
tana maidashi 3D scan gami da cewa cikin harshen larabci.
"Sa'ureekum shai'an" Ta fada tana murmushi.
"Na'am" Ya fada yana matse hannun sabreen cikin
nasa. Maida mouse din tayi saman cikin sabreen din,ta matse hoton cikin take
yara guda uku suka fito sosai.
"Allahu akhbar.......subhanallah" Fuad ya fada
muryarsa tana rawa. Damqe hannunsa sosai sabreen tayi itama cikin nata,ta kasa
magana kaman yadda fuad shima ya kasa cewa komai face tasbihi ga Allah buwayi
gagara misali. Yaran na kwance irin kwanciyar jarirai uku cikin
mahaifiyarsu,kamanninsu sosai ya fito,har ya dinga jin kaman ya saka hannu ya
daukosu.
Cikin
qwarewa take juya na'urar tana zoom in musu yaran daya bayan daya. Qosassu kuma
lafiyayyu ko a ido,wanda ko daga yanayin girman cikin sabreen din shi kansa
yasan qosassunne,duk da akance abun ba daga girman cikin bane.
Murmushi ya
subuce masa wanda ya taho da taruwar hawaye cikin idanunsa ganin daya daga
cikin yaran da tayi zoom in din babban yatsansa na cikin bakinsa kaman me shan
hannu.
"Astgafirullah......alhamdulillah......subhanallah
walhamdulillah wallahu akhbar" Abinda ya dinga fadi kenan,yana jin kaman
kada ta daina nuna masa fuskokinsu,saidai kuma dole saboda ayyukan da suke
gabanta.
Sauke
na'urar tayi itama murmushi yana qwace mata,ita kanta yaran sun burgeta,ta kuma
jima bataji jariran da taji tanason ta gansu fuska da fuska ba irin yaran. Bata
sani ba,ko hakan yana da alaqa da yadda ma'auratan suke burgeta?.
Zata iya
cewa tsahon shekarun aikinta,taga spouse kala kala,amma ba wadanda sukafi
burgeta tare da qara mata son yin aure a kurkusa irin sabreen din da fu'ad. Da
fari ma ita sam bata yarda daga nigeria suke ba,na farko dukkaninsu sunayensu
batayi tunanin akwai masu irin sunan a bahaushiyar qasa ba,na biyu kuma yadda
fatarsu keda wani irin haske da kadan tasu ta dara nasun,uwa uba yadda sukejin
labarin Nigeria da yadda 'yan qasar suka zubda kansu a qasar saudiyya yadda ake
binsu ana kamesu kaman kaji ko awaki,bata dauka akwai mutane masu qayatarwa da
burgewa kaman wadannan mutanen ba,sam bata zaci zaa samu mutum irinsu a Nigeria
ba.
Hannun
sabreen kawai ya juya ya dinga kissing,har sai da dariyar likitar ta dakatar
dashi.
Da kansa
ya taimakawa sabreen din ta zauna sannan ta miqe tsaye,ya gyara mata rigarta da
mayafin saman kanta,sannan ya taimaka mata ta zauna saman kujera tayi relaxing
sosai,daidai sanda likitar ta dawo dauke da takardu zuwa gabansu.
"Cikinta yanzu haka yana sati na talatin da uku,kuma
yawanci 'yan uku bama bari su haura sati na talatin da hudu saboda
nauyinsu......don haka ina tunanin mafi kyau sati me zuwa ayi mata CS a
ciresu". Murmushi ya sake kubce masa,wannan nesar tazo kusa kenan,wannan
lokacin na haduwa da yaranshi yayi kenan. Already sun yanke ayi mata CS
din,saboda haka kawai yake tsoron tayi naquda,gani yake kaman zai rasata,tun
randa sukazo anti natal suka samu wata mace ta rasu gurin haihuwar twins dinta.
Koda ya shawarci sabreen din bata qi ba,don ita don ta ita bata da wani
zabi,kome ya yankewa rayuwarta tasan bazai cutar da ita ba. Likitar kuwa dama
kai tsaye ta gaya masa cewa.
"Ba kasafai muma muka fiya so ko barin me haihuwar fari
triplet ta haihu da kanta ba,akwai risk,CS is the best idan har ma'aurata sun
amince.
"Ba matsala,Allah yasa ayi a sa'a.......a turamin komai
da asibiti keda buqata na komai da komai din,zamu shirya zuwa sati dayan in sha
Allah".
"To yayi.....zaku zo a day kafin ranar aikin,don bayan
asuba koda sassafe zamu shiga da ita".
Shi da
kansa yayi driving nasu dama zuwa asibitin,yanzunma shi dinne,don wannan karon
kwata kwata daga Jordan dan amanarsa sai abdulgafar,da iya mutanen daya taho
kenan.
Wani
rayuwar 'yanci yake abinsa cikin garin madeena,kusan kullum saisun fita shida
ita,strolling ko a mota,suci abinci su dawo gida bayan sun zazzagaya garin. Ya
lura yadda yake qaunar madeena haka ita dinma,yanayin garin da calmness dinsa
yana sakata nutsuwa sosai ya lura da wannan,don haka a yawan lokuta ma ba hira
suke ba,suna tafiya ne kawai a low speed tare da madaidaiciyar qira'ar daya
daga cikin malamanmu na addini,sai kaga duk jikinta yayi weak wani kwanciyar
hankali tana ratsata.
Yanzunma
hakan yayi mata,saidai suna fara tafiya tace
"Hamma"
"Na'am adda sabreen" . Yadda ya fada din ya sakata
sakin murmushi,muddin zata ce masa hamma,to shima fa zaice mata adda sabreen.
"Umra nakeso nayi......". Kallonta kadan yayi
sannna ya maida hankalinsa kan titi.
"Yaushe kenan?".
"Kafin ayimin Cs.....ban sani ba ko itace ta
qarsh"
"Ameenatu!" Ya kirata da wani irin sauti kaman kan
motar zai subuce masa kafin ya daidaitata.
"Don Allah ki rufan asiri karki qara fada,kinsan tsarki
da darajar garin nan kuwa?,kinsan ko ina kayi addu'a indai a cikinsa ne ta
musamman ce?,kin sani ko muna tare da mala'iku?" Ya qarasa fada kaman
zaiyi kuka. Sanyi itama jikinta yayi,sai tayi qasa da kanta tana fadin.
"Kayi haquri,bazan sake ba in sha Allah" Shuru
yayi kaman bazai amsa ba kafin ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya.
"Allah yayi miki albarka,ya rayamu a tare"
"Ameen" Ta amsa tana satar kallonsa tausayinsa
yana ratsata.
Hanyar
komawa gida taga ya canza sai kuma yace mata.
"Jibi in sha Allah zamuje kiya umra......amma muje in
nuna miki wani abu" Kai ta
gyada,sai ya qaro sautin qur'anin kadan yaci gaba da tuqin a nutse.
Sosai
karatun yake ratsata,qasan zuciyarta kuma tana jaddada godiyarta ga Allah.
Haqiqa tasan bata da haufi.....bata kuma da tsoron kalar uban data zabawa
'ya'yanta. Nagartar fu'ad kawai wata baiwa ce me zaman kansa,ballanta zallar
tausayinsa da jin qansa akan 'ya'ya mata......especially matarsa. Ita kadai
tasan wanne irin kalar miji take aure.....a father...a mentor.....uwa uba
Selfless partner ne. Batasan yawan addu'o'i da take sha ba daga wajensa.....ita
take dauke da cikin kawai,amma ya fita damuwa da kan kanta. Bai taba barinta ta
kw ata ba addu'a ba alwala ba,bai taba barinta tana kallace kallace ko jin kade
kade ba,duk da dama ita din ba gwanarsu bace,saidai akance dan adam ajizi. Da
yawan lokuta yakance.
"Tun a ciki kana iya koyawa yaranka dabi'a me kyau da
maras kyau.....tun a ciki kana iya debewa yaranka albarka kana kuma iya sama
musu albarkar.....me ciki kullum so ake ta zama cikin d'a'a da bin Allah.....ta
zama very attached to her rabb,yawan sadaka.....yawan kyauta,karatun qur'ani ko
sauraronsa,ambaton Allah da istigfari,ta guji gulma zagi mugunta tuggu makirci
da qarya......wannan zai sanya ta samu nagartattun yara in sha Allahu".
Kai ta jinjina,kuma tun daga wannan lokacin bata sake bari ya mata gyara akan
duk yadda yakeso ta kasance ba.
Bata tashi
bude idanunta ba sai a gaban wani gida,wani irin qawataccen gida daya fusgi
hankalinta tun a waje. Ya bude mata motar ta fito,suka zagayo a tare,sai yayi
tsaye gaban gidan yana zura hannunsa a aljihun rigarsa ya fiddo key.
"Wannan gidan na siyeshi ne da sunan
yarana......mallakinsu ne halak malak cikin wannan garin na madeena,ya Allah ka
shaida" Yayi maganar yana damqa maqullin a hannun sabreen.
"Bude mana" Ya furta yana sakin murmushi. Sanda
take budewa dukka hannunta rawa yake,idan tace bata taba ji ko ganin matar data
samu tsananin soyayyar miji ba irinta batayi qarya ba.
"Kawo nan raguwa ce ke wani lokacin" Ya fada yana
tsokanarta sanda ya bude gidan.
Da
bismillah da kuma sallama suka sanya qafafunsu. Tun a parlor na farko tasan sun
shigo aljannar duniya ne kawai,wani irin gida me cike da tsari da nutsuwa ta
daban.
Tiryan
tiryan yake nuna mata kowanne sashe na gidan har zuwa sanda sukazo kan daya
cikin bedrooms biyar da gidan yake dasu.
Murmushi
ya sakar mata yana mata nuni data bude dakin,ta maida masa sannan a hankali ta
saka hannu ta murda handle din ta tura.
"Wow......ya subhanallah" Ta fadi tana ware
idanunta da kyau. Wani irin lafiyayyen dakin yara ne dake dauke da wasu irin
designers gadaje masu dan karen kyau. Komai na dakin an shiryashi da wani irin
hikima da tsari me tafiyar da hankali. Komai na dakin guda ukune tabbacin ana
welcoming yara uku kenan. Curtain rug da duk wani furniture na dakin abun kallo
ne.
Bango zuwa
bango na dakin dauke yake da frames masu rubutattun ayoyin qur'ani na tsari
kala kala,sunayen annabi da sunayen Allah.
Daga cikin
dakin akwai wata qofa,banda tasan cikin gida suke ba abinda zai hana ta kira da
dakin baby shop. Komai akwai a ciki,babu ce kawai. Tarkacen kayayyaki Cots,baby
bassinet,portable cribs kala kala. Kayan sawa kuwa cikin wasu irin kwalaye na
alfarma suke me dauke da wani tambari na musamman da zai tabbatar maka musamman
aka yosu. Tun idanunta na iya fahimta har ta daina gane wasu kayan ma,don wasu
abubuwan ko sanin mene ne batayi ba ballantana amfaninsu. Idan tace babu ce
kawai babu cikin abinda ya shafi tarkacen jarirai sabuwar haihuwa batayi qarya
ba,tun daga nan ta sallama,ta yadda lallai 'YA'YAN GATA zasu shigo duniya.
Fuskarta
kawai ta rufe da tafukan hannunta kuka yanaso ya qwace mata,komai tana kallonsa
ne kamar a mafarki ba a zahirin rayuwa ba,sai ya jawota ya sanyata cikin
jikinsa yana bubbuga bayanta.
"Wanne irin so kake musu haka hamma?"
"Beyond imagination sabreen.......ina dreaming gina big
family duniyata.......inaso nayita tara yara nayita tara yara,wadanda zasu
zamemin sanyin idaniya" Ya furta yana hadiye wani abu. Shuru kawai tayi
tana sauraren bugun zuciyarsa,ta wani bangaren kuma zuciyarta ta cika da tarin
addu'o'i da fatan samun rayyayun 'ya'ya masu albarka.
★ *_LOKACI TAMKAR TAKOBI YAKE_*
Kamar yadda yayi
mata alqawari ya cikashi,kwanaki biyu rak suka sauka a makka ta sauke umrarta a
ranar. Tayi matuqar qoqari shi kansa ya yaba,duk da nauyin da cikinta yayi amma
tayi addu'o'i sosai tayi ibada a kwana biyu kacal da sukayi. Ranar da suke
sanyan rai zasu dawo sai ga uban 'ya'yan BB farouq da amarya fannah.
Dukkaninsu
sunyi wani irin kyau shi da fannah din,sunyi bundum abinsu gwanin sha'awa. Yayi
mamakin saurin qarasowarsa,don dai kawai ya gaya masa saura kwana biyar ayi CS
din sabreen baiyi zaton zai taho da wuri haka ba.
"Dole muzo mu yiwa adda addu'a,sannan so nake a
matsayina na uban 'ya'ya na riga kowa daukarsu" Murmushi fu'ad yayi,yana
jin wannan qaunar har cikin jininsa,farouq na dabanne a rayuwarsa.
Su suka
tsaidasu suma saida suka sauke tasu umarar,sannan suka tattara suka wuce
madeena.
A kwanakin
sosai sabreen taji dadin zuwan fannah,ta qarfafa mata gwiwa sosai ta kuma bata
shawarwari a matsayinta na wadda bangaren ta karanta. Akwai fargaba kadan da
takeji,amma tana dannewa saboda fu'ad din. Dukka tunaninsa da hankalinsa yana
kanta,burinsa na duniya gaba daya ya tattara a kanta da abinda yake cikinta. Ta
san ko yaya ne sai damuwar ta tabashi,shi yasa taketa qoqarin nuna komai normal
ne.
Ranar da
zasu wuce asibiti da azahar,ko kara fu'ad qin yiwa fannah yayi,ya hanata hada
kayan tafiyar,sai list data musu ya zage da kanshi ya hada komai.
"Zo mu tafi daki abunmu.....muje na baki labari me
dadi" Farouq ya fada yana janye fannarshi.
"A dawo lafiya......Allah ya bada lada" Fu'ad yabi
farouq dashi ba tare daya kalleshi ba,don idan kaga yadda yayi maganar zaka
dauka badashi yake ba.
Qaramar
dariya sabreen tayi,kominsu yana burgeta,tsakanin farouq da fu'ad ba wanda ya
isa ya shiga,idan ka shiga ma zaka fice da qafafunka don kunya zasu baka.
Ba'a wuce
awa daya ba ya dawo ya janye dude dinshi,can ta hangosu suna qus qus kafin ya
juya ya fice. Idanunta ta lumshe,tana jin wani sanyi qasan ranta,koda ta mutu
wajen aikin,fu'ad yabi bayanta,tayi imani da Allah muddin farouq yana raye
yaransu ba zasu tashi a maraici ba,yaransu ba zasu wulaqanta ba,yaransu ba zasu
fuskanci kalar rayuwar da ita da abbensu sukayi a duniya ba.
Sallamarsu
anni kawai sukaji,anni huda da saddiq. Mamaki ya kama sabreen har ta gaza
daurewa,ta taka a hankali ta isa ga anni,sai annin ta rungumeta tana mata
sannu,lamarin da ya sanya sabreen din sakin kukan da batasan meye dalili ba.
158
Hannu anni
ta dora saman bayannata tana shafawa a hankali gami da fadin
"Ya isa haka mana.....kukan na mene ummmm
sabreen?,habba addarsu.......bakya gani duka qannen naki suna kallonki?"
Annin ta fada cikin murmushi. Kunya kadan ta kama sabreen,saita boye fuskarta
saman kafadar annin tana murmushi.
Qarfe
takwas na dare suka shirya suka wuce asibitin bisa jagorancin tuqin BB
farouq,wanda a yau yake jin kansa kamar yafi kowanne mutum farinciki a duniya.
Shi yake driving din fu'ad yana gefansa,a haka suka qarasa asibitin.
An
shirya mata lafiyayyen daki kafin isowarsu wanda aka zuba komai da zai sakasu
su jisu comfortable sosai.
Sosai
qwalla ta cika idanunta sanda ta bude qofar dakin,wanda aka tsarashi da gadajen
jarirai har guda uku,gadajen da taji zuciyarta na bugawa,yaran zasu hau?,ko
gawarsu ce zata hau?,zata bude ido ta gansu su duka ukun akai?,ko kuma za'a
rasa wani ko ita a rasata?,dukka wannan Allah shi ya barwa kansa sani.
Sukam
gaba daya tsarin dakin ya burgesu,sunbar anni a gida saboda yanayin tafiya da
zaman jirgi,don haka har huda da fannah suka samu sakewa abinsu. Huda kam kaman
taso tafi kowa gaza boye farincikinta,idan triplet sukazo zanyi kaza......ni
zanyi kaza.....ni zanyi kaza,har tana dariyar sai ta riga haneefa da nadra
daukansu.
"Idan kika kira kika tsokanesu fa zan iya daukanki mu
koma salin alin.....musamman kika saka mana haneefa auta kuka" Saddiq ya
fada qasa qasa yana jifanta da wani irin kallo da kana gani kasan na shauqin
soyayya ne.
Kukan
shagwaba ta saki masa,Allah yasa fu'ad a lokacin ya fita magana da likita.
Kunya ta kama sabreen,sai dauke kai tayi tana ajiye kayan kunyarta,sai yanzu ta
fahimci haka sukeyi ashe suma?,kuma ko yanxun ba fasawa akayi ba. Fu'ad din
baya gane kowa baya jin maganan kowa bare ya fahimta a sanda suke tare da ita.
Tana
jinsu ta gama,ya lallashi abarsa,koda ta dawo kusa da sabreen harara ta balla
mata.
"Ke bakijin kunya ne?,wannan tabarar da kikeyi ko
haneefa sai haka". Dariya sosai ta ballewa hudan,tadan matsa baya kadan.
"Adda.....bamayin komai fa a kanku keda hamma......adda
kinsan kuwa yadda kuke komawa keda hamma?.....wallahi idanunku ma narkewa suke
su juye idan kuns tare,har wani laushi jikinku yakeyi baki taba lura ba?"
Daquwa sabreen ta watsawa huda da sauri.
"Qaniyarki huda.....kakarki ce ni?"
"Barta ta fadi fa......sister gaskiya ta fada,Allah na
tuba waye yayi yaku?,har yanzu gani nake BB bai kamoku ba,in kuna wani abun sai
inga tabbas mu dukka 'yan koyo ne" Cewar fannah tana dariya bayan ta gama
duba bayanan asibitin da yadda zasu gudanar mata da aikin. Kai kawai sabreen ta
girgiza,bata iya ce musu komai ba don bata da abun cewar. A fakaice take bin
huda da kallo,ranta fari tas tana godewa Allah,tana tuna shekarun
baya......tana tuna nasir,wanda tabbas inda yakai ga cimma gaci qila yanzun
huda ba'a wannan matsayin take ba. Yadda ta mori miji haka tayi imani huda ta
mora,ta lura da yadda hudan ke qara mulmulewa abinta,jikinta kuma ya bata juna
biyu ne,fadi ne kawai basuyi ba saboda kunya,uwa uba kuma sai Allah yayi mata
baiwar juna biyu maras laulayi sam sam sam,kawai dai ya sakata mugun cin da ya
sanya taketa qiba. Amna ce tayi fama da laulayi,yanxunma dai daya girma sai a
hankali,abinka da auta shagwaba ga quruciya,duk da shekarunsu kusan daya da
huda amma rainon ma ba daya bane,amna bata saba da wahala ba,huda kuwa ta daku
da wuya iya wuya,qilan ma shi yasa yazo mata ba'a wani kayan wahala ba,duk da
cewa asali halitta halitta ne.
Aikam
zancansu dutse,don sanda fu'ad yake shigowa dakin duka kasa zama suyi,kowa yaja
matarsa,daga qarshe ma sallama sukayi musu akan gobe zasu dako sammako don ayi
aikin a gabansu.
A hanya
suke gulmarsa,fannah tace.
"Kasan Allah mine......nasha gulman dude dinka,nakance
wadda ta aureshi zata wahala,miskilancinsa yayi yawa,duk yadda kuke dashi sau
daya ya taba rakoka zance,koda yaxo ma sai naga magana wahala take masa,nace
wannan ina za'ayi walwala a gidansa?,ashe expert ne......Shahrukhan
ne" Dariya sukayi gaba dayansu.
Huda ta karba itama.
"To ai har yanzu adda fannah....." Harara fanna ta
aika mata.
"Nifa ba fulbe bace.....ki daina kirana da addan
nin.....bayinmu fulani ke amfani dashi" Dariya ta sake sosai.
"Adda kin riga fa kin shigo cikinmu,kema kin zama
bafulatana daga yau......" Jujjuya kai fannah tayi alamun ya zata
iya?,anfi qarfinta.
"Ko yanzun ba boss yake,yanzu fitowarmu daya shigo yana
taku yana shan qamshi in ke baquwa ce ba zakice haka yake ba.....amma yana isa
gurin matarsa ya koma wani mutum na daban" Huda tace tana dariya abinta.
Da irin wannan hirar ta qawatacciyar soyyarsu suka qarasa gida.
*WELCOME TO THE WORLD*
*_The jadda's triplet_*
*_a bundle of joy_*
*_three little miracles_*
Idanunta
tsakiyar nashi,ta kasa banbance tsakanin ita dashi waye yafi wani fargaba,waye
yafi wani tsoro?,waye yafi wani shiga yanayi na zaquwa da kuma shauqin ganin
yaran da har a sannan basusan wanne jinsi bane?.
Cikin
tsararren dakin aiwatar da tiyatar,kwance saman gadon wanda likitoci ke kewaye
da ita. Aikinsu suke daga qasanta,sun saki koren labule daga saman cikin nata
zuwa kanta bata tare dasu......amma muhamma fu'ad jadda.....rauninta kuma
qarfinta yana tare da ita.
Yana zaune
daga saman kan nata saman kujerar da tsahonta yakai daidai kanta,sanye yake da
wasu kayan green color shima da irin hular dake kawunan likitocin. Hannunsa
cikin nata hannun,ya sarqafe yatsunsu guri guda,idanun kowannensu cikin na dan
uwansu.
Qur'ani
yake karanta mata qasa qasa,cikin wani irin daddadan sauti daya sanya hatta da
likitocin sauraronsa babu shiri,idan kaji sunyi magana ya kama ne. Sosai
takejin wani nutsuwa yana saukar mata,idanunta kan labbansa dake motsawa cikin
gwanancewa da qwarewa cikin karatun qur'ani me girma.
Daidai
sanda yakai kan ayar qarshe ta cikin suratu yaseen
"Innama amruhu iza arada shai'an an yaqula lahu kun
fayakun,fasubhanallazi bayadihi malakuti kulli shai'in wa'ilaihi
turja'un". Sound din kukan baby na farko shine ya biyo bayan saukar nashi
muryar.
Sake
sarqewa idanuwansu sukayi cikin na juna,zukatansu na wani irin bugawa da wani
irin madaukakin farinciki.
"Second baby" Muryar likitar ya baqunci kunnensu
da kuma wani sabon kukan jaririn.
"Third one" Suka fadi sanda sabreen din ta sauke
wani nishi saboda fitar yaron daga cikinta da ya sanya qirjinta fadawa
sosai.(wannan wani irin yanayi ne da kowacce uwa da aka taba yiwa CS ta
sanshi,wani yanayi ne da bakya taba mantashi,ya Allah ka taimaki duk wasu uwaye
musulmi,wanda CS ya zame musu abu na ko yaushe yayin haihuwa ya rabbi ka basu
da sauqi,ka tsallakar dasu dukka wani hadari da wata wahala dake cikinsa,masu
haihuwa da kansu don isar annabin rahama ka basu naquda me sauqi,masu neman
haihuwa ya Allah don hasken fuskar manzan Allah ka azurtasu da ita,ka basu masu
albarka wanda zasu iya dasu ameen).
(A wannan gabar nima nake barar addu'arku da bakunanku masu
albarka😄,Allah ya azurtani da twins ko triplet nima🙏🏽🙏🏽,the
dream of my life,ina fatan zaku sani a addu'arku,akwai wadanda suke qasa me
tsarki duka ina fatan zaku jefani a Addu'arku,na gode).
A lokacin
fu'ad ji yake kaman bazai iya jira su zagayo da yaran su nuna musu su ba,duk da
yasan definitely zasuyi hakan. Bai jima da sauke tunanin ba kuwa mutum uku suka
daga musu yaran yadda mahaifiyarsu ta haifesu suna tambayar sabreen meye gender
dinsu.
"Boys" Ta fada muryar ta na rawa da wani irin
narkewar zuciya. Shikam kasa magana fu'ad yayi,sai sake damqe hannunta da yayi
cikin nasa,ya maido idonsa cikin nata yana dubanta da wani kasantaccen shauqi.
"Thanks hamma......na gode sosai hamma......inama
ummeena tana raye?,ka bata jikoki da jinsin da har ta mutu ake mata gorin bata
haifa ba.......ka bani wata kyauta da bazan taba iya mancewa da ita ba".
Hannu ya dora saman lips dinta yana fadin.
" Shshshsh.....ki huta my world......ki huta
duniyata" Ya aza hannunsa saman kanta yana shafa mata a hankali. Bayaso
taci gaba da magana,don ya tabbatar muddin zataci gaba din to tabbas zata karya
masa zuciya ne,zuciyarsa a kusa take da sakin kukan farincikin da a yau bayajin
yana da nutsuwa idan bai dangana da masallacin ma'aiki ya miqa godiyarsa ba.
Yana iya
hangen yaran bayan an gama tsaftacesu an kuma shiryasu cikin kayan
jarirai,kowannensu ya cika kayansa,kaman ba jiriri ba,abinda yake bashi mamaki
yadda cikin duniyarshi ya dauki manyan yara kaman haka,yana hangensu suns
wutsil wutsil,yana jin shauqinsu daga nan inda yake zaune,amma kuma bazai iya
sakin hannunta ya barta yaje wajensu ba. Tana ankare da hakan,saita saki
tattausan murmushi ta kuma matsa hannunsa,wanda hakan ya jawo da hankalinsa kanta
"Tashi kaje hamma....tashi kaje wajensu" Kai ya
girgiza mata yana sakin murmushi,qwalla cike da qwayar idanunsa.
"Bazan iya motsawa daga inda duniyata take ba....until
you feel okay"
"Am okay hamma.....am okay" Ta bashi
assurance,amma sai ya maqale kafadarshi yaqi tashi.
Cikin minti
arba'in gaba daya aka kammala gyarata tsaf ita da yaran,sannan aka tura gadonta
zuwa dakin da zata huta.
Tsaiwa
nurses din kawai sukayi da yaran suna dariyan ganin drama din da akeyi
tsakaninsu BB farouq huda anni saddiq harda fannah ma. Shidai abba Alhaji hamza
kibiya da isowarsa kenan asibitin baya yaja ya tsaya yana dariya,don baisan shi
kansa ya zaiyi musu ba,kowa so yake shi za'a fara bawa,wannan ya sanya kawai
suka zarce wajen Alhaji hamza suka miqa masa daya,sauran biyun wuka sanya masa
su kan cinyarsa.
"Shikenan sun raba rigima ko?" Abba ya fada yana
dariya gami da zube idanunsa akan yaran.
159
"Ma
sha Allah,tabarakarrahman.......alhamdulillah.....alhamdulillah" Abban ya
maimaita yana jin wani qaunar yaran sabuwa fil tana taso masa. Har ransa
yakejin alfahari da samun yaran,har cikin jininsa yake jinsu tamkar amna ko
farouq ne ya haifesu,wani irin rahama yaji kaman ta sauka a family din
nasa,samun qananun yara har qwaya uku a lokaci daya,a sanda suke kewan yara
qananu din. Baisan wani abu da yakeso yake kuma matuqar alfahari dashi ba irin
iyalin nasa......irin family din nasa ba,wani baiwa da kyautar ahali Allah yayi
masa,badon yafi kowa wayo ko dabara ba.
Addu'a
sosai abban ya dinga musu a sarari a bayyane,su anni suna amsa masa da
ameen,duk kuwa da cewa kowa ya qagu abban ya gama ganin yaran ya basu su.
Na
hannun nasa da suka ce masa shine babba ya juya,yayi masa kiran sallah a
dama,sannan yayi kasa iqama a hagu,bai ambatar masa sunansa ba,don shi din ba
mutum bane me yawan kutse ga al'amarin yaran sa ba,muddin basu sabawa al'ada ko
addini ba yana barin kowa ya zabi abinda yakeso ne.
Anni ya
fara miqawa sannan ya dauki na biyun ya maimaita masa abinda yayiwa na farko ya
sake miqawa anni,wadda ita kuma ta miqawa huda na farkon. Tana ganin irin
zaquwar da huda ke ciki,ta kasa zama ta kasa tsaiwa. Hannu biyu anni ya
karbeshi shima,sai ga hawayen da taketa riqewa sun soma diga saman lallausan
abun daukan jariran,sai sautin kukan huda itama ya soma tashi.
Murmushi abba
ya saki yana tsokanar annin.
"Da alama wannan kukan za'a yimin tawaye kenan,banda
haka nine ya cancanci nayi kuka ai,nida aka yiwa kishiyoyi?,har uku rigis a
rana daya a lokaci daya?,to ki daure zuciyarki dai karsuce matar tasu raguwa
ce" Ta tsakiyar hawayen nata murmushi ya subuce mata,daga ita sai Allahnta
su kadai sukasan irin farincikin da yake dawainiya da ita,yaran wani baiwa ce
da rahama daga ubangiji zuwa garesu,lallai bawa ya kamata ya zama me yawan
imani da qara girmama zatin mahaliccinsa.
Duk
wanda ya dauka kaman kada ya sauke a cikinsu,sun karade wajen har basa ganin
wani bare a wajen,ganin yara uku ya janyo hankulan mutane,duk wanda zai wuce
sai ya tsaya ya kalla ya musu addu'a kuma.
"Wai ina muhammadu ne?" Abba da baiga fu'ad ba tun
zuwansa gurin ya tambaya.
"Yana can wajen matarsa......inajin ko yaran bai dauka
ba" Anni ta fada tana nannade yaro daya da yake hannunta.
"An kaita dakin hutu ai,inaga ya kamata sukai masa
yaran.......kai saddiqu" Ya kira saddiq da suka lafe shida hudarsa suna
tattauna yadda nasu yaran zasu kasance kyawawa kamar haka,sun saka yaro daya
dake hannunsu a tsakiya sunata murmushi kaman wasu shashashai. Kai anni ta
dauke tana sakin murmushi gami da girgiza kai,daga hudan har saddiq din akwai
wauta tamkar 'ya'yan fari. Saida zamansu ya miqa ta fahimci lallai halayyarsu
ta dace da juna sosai,shi yasa har yau bata taba jin kansu ko cikinsu ba.
"Karbeshi kuje kukaiwa babbansu su"
"To abba" Ya fadi yana sanya hannu ya karbeshi
daga hannun huda,ji tayi kaman kada ta bada shi,shima ya karanci haka,sai ya
saki murmushi murya qasa qasa yace
"Namu yana hanya in sha Allah". Murmushi ta saka
cikin tsananin jin kunyarsa ta kauda kanta,tana ganin kamar su anni zasuji
abinda ya gaya mata.
Dashi
da BB farouq suka isa dakin,farouq yara biyu ne saman kafadarsa,yayin da saddiq
din yake dauke da guda daya.
Wani irin
nutsatstsen yanayi dakin ke dashi,ba yawaitar haske kuma ba yawaiyar duhu,wataqila sun barshi a
hakanne saboda cikakken bacci da sukeso sabreen din ta samu.
Yana zaune
gaban gadon saman wata farar kujerar,hannunsa cikin tsakiyar nata hannun,ya
tattara dukakanin hankalinsa a kanta cikin matsananciyar kulawar da ko cikakken
motsi baya so tayi.
Da alama
magana sukeyi qasa qasa,wanda a tsakaninsu ne,don kana dakin babu lallai ka iya
jin komai. Motsin shigowarsu ya sanyashi daga kanshi,ya zube idanunsa akan
yaran dake hannunsu yana jin wani irin abu me nauyi na sauka a qirjinsa.
Cakudadden farinciki ne daya gauraya da nutsuwa da godiya da rahamar
Allah a kanshi.
"Wannan duniyar taka ba zata taba barin yarana suyi
farinjini a gurinka ba da alama......kawai dadin abun......uba da yawa maganin
kukan d'a" BB farouq ya fada yana isa gabanshi ya jeresu daga gefen
sabreen din duka su ukun.
"Minti kadan na baka ka gama kallonsu zanzo na debe
kayana" Farouq ya fada da wani irin cin serious harda duba agogon
hannunsa. Murmushi kawai faud ya saki,zuciyarsa na karyewa,nauyi da kunyar
ubangiji tana kamashi,yana jin kaman baiwa Allah komai ba daya cancanci irin
wannan kyautar da baiwar ba.
Har yayi
taku biyu farouq din ya dakata,ya waiwayo yana dubansa.
"Ko barka kayimin ba.....kuma duk wanda baimin barka ba
yana cikin black book dina"
Murmushi ya sake qwacewa fu'ad,ya motsa labbansa a nutse.
"Congratulations BB farouq......ina tayaka murna da
samun 'ya'ya da kayi". Wani ni'imtaccen murmushi ya bayyana a fuskar
farouq din,sai kawai ya dawo da dan sassarfa,kafin yakai ga qarasowa kuwa fu'ad
ya rigashi miqewa suka rungume juna sosai.
"Barka da arziqi dude......ina maka fatan alkhairi,ina
tayamu murna mu gaba daya.....Allah yasa mu da musulunci gaba daya muyi
alfahari dasu"
"Ameen dude......ameen na gode" Fu'ad ya fada yana
jin jinin 'yan uwantaka yana yawo a jikinsa. Zare jikinsa farouq yayi,yaja da
baya yayi saluting sabreen da sai a sannan ya lura idanunta biyu.
"Well done addarmu......" Ya fada yana qamewa.
Murmushi ta saki idanunta na lumshewa saboda nauyi da sukayi mata,ta girgiza
kai murya can qasa ta furta.
"Na gode BB". Gira ya dagawa faud tare da babban
dan yatsansa sannan ya juya yana fita.
Da fari
idanu suka zubawa yaran su duka shida ita,dakin yayi tsit sai qarar na'urar
kadan kadan. Gaba dayansu bacci sukeyi,sunyi wani irin matuqar tafiya da
zukatansu da wani qaqqarfar soyayyarsu data fusgi zuciyarsu lokaci guda.
Tare suka
kai hannuwansu kan yaran,sai suka kalli juna kuma kowannensu ya sakarwa dan
uwansa murmushi. Tsam fu'ad ya miqe tsaye,ya gaji da bugawar da zuciyarsa
keyi,ya dauki.yaron farko ya mannashi a qirjinsa sosai yana jin dumin jikin
yaron da qamshin sabbin tufafinsa.
"My heart beat" Ya furta a sanyaye har na tsahon
second sittin sannan ya daukeshi daga qirjin nasa ya maida dubansa kan
fuskarsa.
"Wannan hamza ne.....hamza ne wannan,jarumin sadaukin
nan,baffan manzan Allah......kuma ubana abbana daya bani sabon ruhi da sabuwar
rayuwa" Yayi maganar daga qasan zuciyarsa yana jin soyayyar yaron.
Idanunsa
ya cire ya maida kanta,tana daga kwnace tana kallonsu da wani azababben kallo
me cike da qauna. Rayuwarta take gani a tattare dasu,ruhinta dama komai
nata.......daga sabreen ita daya ya daga darajarta ya maidata me rassa har uku.
Kadan ya
Matso gareta,ya manna mata yaron itama a qirjinta.
"Ki masa addu'a.....hassan shine hamza"
"Allah kasa ya biyo halin asalin me sunan"
"Ameen" Ya amsa yana lumshe ido.
Juyawa yayi
tana nufar gadonsu,ya kwantar dashi sosai yana gyara masa lullubarsa sannan ya
dawo kan yaro na biyu.
"My world......dukkansu kamarsu daya.....kama suke da
juna ta sosai da sosai......kinga har wani digo dake fuskarsu ma iri daya
ne" Ya furta yana dubanta. Ajiyar zuciya ta sauke,ta gani itama,ta gani
fadi ne akwai batayi ba.
"Wannan babban aminina ne,dan uwana kuma
masoyina.....umar alfarouq" A
wannan karon ita kanta saida murmushi ya subuce mata
"Wai Allah hamma......zaka kawo rigima fa.....tabbas BB
bazai boye soyayyar hussain a zuciyarsa ba".
"Na sani ameenatu" Ya amsa mata shima yana
imagining fuskar farouq,don ba zata yayiwa kowa,shi kansa baisan gender na
yaran ba sai bayan an haifesu bare wani yaji sunan da zai sanya musu.
Shima sai
daya mannashi sosai a qirjinsa sannan itama ya saka mata su,ya kuma sanyata ta
masa addu'a kaman dan uwansa sannan yaje ya hadashi da dan uwansa ya dawo kan
na ukun.
"Gamboliya gambo" Ya furta da wani irin nishadi a
muryarsa daya sake saka sabreen din ita kanta a nishadi,duniyar duka sai take
jinta kamar tasu ce su biyar dinnan suda yaransu.
"Shi wannan......abbana ne......sanadi
na.......masoyina almustapha muhammad jadda" Ya qarasa fada yana kissing
nasa sannan ya maidashi qirjinsa yayi masa kyakkyawar runguma. Tana iya hangen
hawaye qasan idanunsa,wanda ta tabbatar na rauni ne. Wani tsohon miki ko rauni
dake danqare qasan zuciyarsa.
Tanaso
ta sassauta masa don haka tagi gyaran murya kadan,sai ya ware idanunsa da suka
canza launi akan fuskarta.
"Amma hamma.....anya ba za'a samu jam'iyyu
ba.....zakaso abba da yawa fa....." Murmushi ya qwace masa,ya dauke
almustapha daga qirjinsa yana cewa.
"Wadannan dukkaninsu masoyana ne......idan kika cire
daya daya daga cikinsu to tabbas babu fu'ad......tarihin muhammad jadda bai
kammala ba,bazai kuma taba zama kammalalle ba". Ta aminta da maganarsa
dari bisa dari,ya matso ya aza mata almustapha din saman qirjinta,shima ta
bishi da addu'a.
Dawowa
yayi saman kanta,yana shafa doguwar sassalkar sumarta a hankali.
"Kiyi bacci my world.....yi bacci duniyata.....kin
cancanci ki huta,kiyi bacci me dadin gaske,mijinki yana daga bakin qofa yan
gadinki,ko yatsarki kika motsa zan jiki......ki raya a ranki duk duniya ba wata
mace me gatanki......ke 'yar gatan mijinki ce......mata tabbas rakiya sukayo
miki zuwa duniya". Wani sassanyan ruwan nutsuwa maganarsa ta sakar mata a
tsakiyar zuciyarta,ta lumshe ido tana sakin murmushi bar batasan sanda baccin
yayi awon gaba da ita ba.
Ai duk
yadda sabreen ta wassafa za'a sha drama da farouq sanda yaji an masa takwara
abun ya wuce nan. Gaba daya farouq ya koma qaramin nanny........dariya kawai
data sha banda Allah yasa tana qoqarin kiyayewa saboda dinkinta ma da batasan
adadin yawanta ba. Duka sunqi gida,asibitin ya zame musu a kwanaki hudun da
sukayi,kafin likitoci su taru suyi qaramar walima cikin asibitin da yaran da
iyayensu dasu anni,sannan aka musu takardar haihuwa,da shaidar zama cikakkun
'yan qasa......daga bisani kuma suna shirin tafiya saiga galla galla motoci na
billions of naira guda uku kyauta daga masarautar saudiyya,saqo daga sarki
abdul'azeez zuwa ga d'iyoyin muhammas fu'ad da aka haifa a qasarsa.
Labari
ne daya zama abun dauka ga kafafen yada labarai na qasar saudiyya,labarin kuma
ya lula ya dira kai tsaye akan akwatin talbijin din da aka kunnawa maamah
saboda debe kewa da zaman tunani.
Tana daga
zaunen jikinta dukka ya dauki kyarma. A sanda sukayi waya da fu'ad din don yaji
lafiyarta,ya gaya mata sabreen din ta haihu,amma batasan me ta haifa ba,mace ne
ko namiji,in fact ma ita bata dauki abun serious ba,sai yanzu da idanunta ke
nuna mata kyawawan yaran tamkar photocopy na muhammad din sanda ta haifeshi
akayo aka manna musu.
Maida
idanunta ga rubutun dake wcewa tayi.
"Yara maza!!....Yan ukun shahararren attajirin dan
kasuwar sarrafa gold da diamond da qasar saudiyya garin madeena ya zame musu
mahaifarsu".
" Tayi nasara a kaina......taci nasara kaman yadda boka
ke gayamin,dukiya ta zama tata......Muhammad fu'ad ya zama nata" Abinda
take maimaitawa kenan jikinta dukka yana rawa kamar wadda aka sawa shocking.
Gumi kuwa tuni ya jiqa gaban cotton gown din dake a jikinta,numfashinta tana
jin yana mata nauyi har tana zuqarsa da qyar.
Tashinsu
kenan a wajen masu kula da ita zasuyi sallah wasu kuma su hada mata abincin
rana,me sallar tana dawowa ta sameta a haka tana qamewa kamar wadda aka hadawa
shocking.
Hankali a
tashe ta dauki wayar da fa'ad ya nuna musu yadda zasu kira likita,musamman aka
hadata kawai saboda yiwa likitan kiran gaggawa.
He's always
available likitan,saboda albashi kawai jadda ya yanka masa yake biyansa
monthly,ko yayi aikin duba maamah ko baiyi ba,kawai buqatar fu'ad din shine ko
yaushe ya zama available duk sanda aka kirashi.
Ba jimawa ya
iso,ya kuma bata dukka taimakon da zai bata aka samu ta dawo da qyar,saidai
danci gaban da ake sanya ran samu komai ya dagule ya koma baya.
Shi mamaki
matar take bashi,ba abinda ta rasa na kulawa daga 'ya'yanta,jin dadin rayuwa
iya jin dadi,amma taqi kwantar da hankalinta ta warke.
Guri yasa
aka basu daga shi sai ita,da zuciya daya yakeson mata fada wala'alla zataji.
"Hajiya.....kiyiwa Allah ki rufawa kanki asiri kaman
yadda Allah ya rufa miki......ko kinaso kikai kanki lahira ne?,kina sha'awar
kwanan kabari da maqabarta?,wacce irin damuwa kike da ita haka a zuciyarki data
hanaki sukuni?,anya ba ciwon hassada bane silar damuwarki?,to amma idan
hassadar ce ma waye zaki yiwa ita?,mutum nawa kikafi a rayuwa amma ke baki gani
ba?,to na rantse da Allah muddin baki sassautawa wannan zuciyar taki ba zakita
shan wahala ne,ana aiki yana dawowa baya ba wani ci gaba" Ya fada cikin
jin haushinta da takaicinta ya miqe yana barin parlor din bayan ya ajiye duka
magungunan da zasu bata.
160
Idanunta
suna kan likitan har zuwa sanda ya kammala ficewa. Numfashi taja sosai tana
saukeshi,wani bacin rai yana qoqarin taso mata amma tana danneshi.
"Ba yanzu ba mariya......ba yanzu ba,ki danneshi don ki
samu lafiya......ki danneshi don jikinki ya daidaita,akwai abubuwa da dama da
kike buqatar aiwatarwa,lafiyarki kuma ita ce jagora,idan babu ita ba abinda
zaki iyayi" Ta yarda da wannan
sashen zuciyar dake mata wannan bayanin,ta aminta da abinda yake gaya mata.
Maganganun likitan sun tsaye mata a rai,lallai ne baisan wacece ita
ba.....baisan wacece mariya ba,wato kawai idan baka da lafiya sai abinda ka
gani?,idan ba zaka iya yiwa kanka komai ba......idan ba zaka iya cewa komai ba
kawai sai abinda ka gani?. Maganar da take nanatawa kanta kenan tana tuhumar
wannan ciwon.....ciwon da yayi mata dirar mikiya a sanda ya kasance takun taqi
kadanne tsakaninta da arziqinta,takun taqi kadanne tsakaninta da cikar burinta
fa......to kuwa me zai hana su kasa fahimtar asiri akayi mata ba hawan jini
bane.
Duk inda
ta juya ya waiwaya fuskokin yaran take gani,ba daman ta rufe idanunta sai taga
yaran guda uku sak masu kama da fu'ad,ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana jin
wani razana yana kamata.
Fu'ad ya
riga daya samu magada,ko mutuwa yayi a yanzu ba a abinda mutuwarsa zata qara
mata illa tsira da kaso daya bisa shida na dukiyarsa.......babban sake da
kuskuren shine barin yaran suka iso duniya.....kuma duniyarma ta shaida.
Ko sanda
ta samu bacci yayi awon gaba da ita su ta dinga mafarki,a mafarkinma su shida
suka koma,wani akan qafarta wani a bayanta,wani a zaune saman kanta,wani a
gefenta haka dai,na saman kan nata ne ya sheqo mata kashi daya rufe fuskarta da
jikinta gaba daya,abinda ya sakata farkawa kenan.
Jikinta
rawa yakeyi sosai,ta jiqe da gumi cikin tashin hankali,takai idanunta inda su
sahura ke bacci,tanason tashinsu amma bata da wannan ikon.
"Meye fassarar kashi a jiki?,anya ba ajalina aka haifo
yaran nan suyi ba?" Ta tambayi kanta da kanta can qasan zuciyarta. Juya
mafarkin taci gaba dayi da ma'anoni daban daban,hankalinta kuma yana sake
tashi,har sanda Allah ya tashi sahurar ta dubata ta bata ruwa ta sake gyara
mata kwanciya. Tanata kallon sahurar,tanaso ta tambayeta fassarar mafarkin
kashi,amma ba bakin magana,haka ta maida idanunta ta kulle tana jin zuciyarta
tana mata quna,tana Allah wadarai da rashin damar yin magana da bata dashi.
"Mafarkin kashi fa arziqi ne....alheri ne" Wata
zuciyar ta gaya mata tana tunasar da ita shekarun baya can sanda fu'ad yana
yaro. Tasha yin wannna mafarkin a kanshi,duk sanda ta farka kuwa an yita tafka
tsiya kenan ita da abbansu.
"Ni wannan yaron bansan meye tattare dashi ba......kai
baka da aiki saidai ayita mafarkin ka shafe jikinka da kashi koka shafeni?,inda
Alla yake taimakona wankewa nake zuwa ni nayi a mafarkin ina dalili?,kai kuwa
kaida Musaddiq duk yadda zan jaku ku wanke qi kukeyi.....kashi ai masifa ne
qazanta ne". Tofa a ranar haka zata yita maganganu,hantara da kyara kuwa
ranar fu'ad ya gamu dashi kenan har sai ya fita a gidan ya wuni a layi sannan
hankalinta yake kwanciya. Ba fadan da abban baiyi mata ba amma bata ji ba,dole
ya kawo idanu ya zuba mata,shi kuma bai taba gaya mata cewa ana tunanin arziqi
bane.
Abun ya
tsaye mata akan jariran,tanason gasgatawa amma kuma tana qaryata hasashen nata.
★Sati biyu
sukayi a madeena kaman yadda fu'ad ya tsara. Cikin sati biyun yake sanya ran
sabreen taji qarfin jikinta,hakanan yaran sun sake qwari.
Hakanne
kuwa ya kasance,zuwa lokacin sabreen din ta warke sosai saboda irin kulawar
data samu daga kowanne bangare,duk da cewa anni tun suna da sati guda ta koma
Nigeria. Tana da buri sosai na hadawa yaran gagarumar walima,saidai taje ta
tarar amna ta gama shirya komai da taimakawar musaddiq. Wani irin gagarumin
suna da akayi sati guda ana shelarsa,sunan da duniya ta jima bataga irinsa ba.
Cikin sati
gudar nan fadin irin dukiyar da fu'ad ya sadaukar ma bata baki ne,irin yawan
kyauta da yayi abun ba'a cewa komai,mutane da dama ya fidda da prison,mutane
masu yawan gaske ya biyawa bashi,mutane masu yawa ya siyawa gidajen zama,mutane
masu yawa ya dauki nauyin aurar da 'ya'yansu,a cikin dangi kuma ya sake ninka
adadin mutanen da ake bawa kujerar hajji da adadin ninki uku. Mutane da yawan
gaske ya dauka nauyin maganinsu da samar musu lafiya,hakanan ya qara yawan
adadin marayun da nauyinsu ke wuyansa. A sannan sai ya ke qara jin yana da kyau
idan sabreen ta koma hankalinta su zauna,foundation yake da sha'awar ya bude
mata saboda taimakon iyayen marayun da marayun kansu.
Yayi
kyautar kudaden da shi kansa baya lissafawa. Duk duniya sai data shaida
muhammad jadda an haifa masa abinda yafi so.....muhammad jadda ya samu abinda
yafi qulafuci,duka kuma yayi ne saboda nunawa ubangiji godiyarsa a gareshi.
Kwanaki
uku kawai da suka rage suna suka baro birnin madeena da boundles of joy
dinsu,suka sauka kanon Nigeria.
Tun a
airport tasan lallai haihuwa wata baiwa ce,wata abace ta daban dake cike da
ni'ima baiwa da kuma tarin albarka da bata da iyaka.
Tamkar
tawagar matafiya haka sukayi zuga zuwa gida,ko dama fu'ad din idan yana qasar
motocinsa sukan kasance ne cikin convoys koda yaushe......saidai a yanxun yawan
adadin ya ninku.
Sanda
suka isa gida ma mutane 'yan sannu da zuwa da barka suka samu,saidai kusan duk
wanda ke cikin gidan me fada aji ne,don haka cikin gayu da nutsuwa komai ke
gudana,don sai data shiga daki ta sake wanka ma,aka warware yaran suma aka
sakeyi musu wanka aka shiryasu cikin wasu lausasan kaya masu zuwa complete set
dinsu ruwan sararin samaniya me haske. Nannys ya dauka musu qwararru tun daga
madeena din,wadanda raino suka karanta gaba daya. Salwa da sameena,ba cikakkun
larabawa bane,saidai acan aka haifi iyayensu suma aka haifesu,har kuma suka
soma girma a yanxun,don kowacce tayi shekara kusan talatin da biyar biyar.
Asalin kakanninsu 'yan nigeria ne......mata ne kamilallu da suka san
rayuwa,sukasan kuma raino da abinda ake nufi da tarbiyya.
A iya
rayuwarta idan aka gaya mata akwai ranar da rayuwa zata sadata da manyan mutane
irin wadannan zata qaryata.....mummunar qaryatawa kuwa,don tasan tabbas
wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa idan har ba ta dalili ko silar fu'ad din ba.
Allah ya
zuba mata wani iri kwarjini da cika ido
sabreen din tun asali,tana kuma da wata irin nutsuwa da kamewa......wannan ya
sanya ta saje sosai a cikinsu.
Irin
gifts din data karba a ranar kadai sai daya sanya kanta ya kusa kullewa. Da
gaske masu kudi suna sha'aninsu,da gaske masu arziqi suna sha'aninsu......da
gaske rayuwa mataki mataki ce. Gifts data samu a yau idan a rayuwarta ta baya
aka gaya mata ana kyauta da irin wadannan kudaden ko kayan zata qaryata,zata
kalli wanda ya bata wannan labarin tace masa ya rage qarya......ya kuma ji
tsoron Allah,sai gasu zube a wani daki daban,wanda ma'u tace a nan zata tarawa
yaran komai nasu.
Ana
magariba ta rufe ganin kowa don tanaso ta bawa fu'ad lokacinsa.......tanaso ta
bashi kulawa kaman yadda ta soma tsarawa rayuwarta. Yaran ta sama su salwa suka
sake daukewa,aka sake fesa musu wanka da wasu baby set din da akayi musu order
dinsu musamman daga wani babban kamfani dan qasar turkiyya. Akwai wani tambari
na musamman jikin rigunan dake dauke da THE JADDA'S jikin rigar Kowannensu,hula
da takalmi da safan hannu dana qafa duka irin guda sak da kayan da abun daukan
nasu dake da adon gold a jiki.
Daga
wanka ta fito itama,wanda take lullube wajen dinkin da wani leather haka tayi
wankanta sannan ta tsane jikinta da kyau kafin ta bude.
Tururin
zazzafan ruwan dake tashi da wani sassanyan qamshin turaren wanka na incense by
kabo daughter jikinta yake fiddawa. Wani irin nishadi takeji......tana masifar
son qamshi har batasan waye yafi wani ba tsakaninta da fu'ad din. Duka gidan a
dumame yake da qamshin incense by kabo daughter,wanda kowanne sashe da daki na
gidan qamshinsa daban yake fiddawa.
Manyan
mahaukatan botikai tasa akayi mata kusan kala goma,kowanne kuma qamshinsa daban
yake fiddawa.
Kanta
ta busar ta kuma turareshi da kabbasar gashi duka daga kamfanin incense by kabo
daughter,ta tajeshi tana qoqarin kameshi da banda taji an riqe hannayenta a
tausashe ta baya.
Murmushi
ya subuce mata jin yaqi magana,ya kuma tsaya cak yaqi ya bata alamun da zata
gane shine. Motsa labbanta tayi a hankali tana dora hannunta ta baya saman
nashi.
"Koda bayan na dauki shekaru da mutuwa ne......koda
bayan na zama qasusuwa ko qasa cikin qabarina......muddin zaka wuce ta gurin
zan fahimci cewa kaine ka wuce,don takun takalmanka zai zama ya fita daban dana
kowa". Wani irin abu yaji yana ratsashi,sabreen dinsa ta fita daban da
kowa.......ta iya kalaman da suke sanyashi kullum kwanan duniya yake jin kansa
yana sake kumbura,kullum kwanan duniya yakejin yafi kowanne d'a namiji sa'ar
mace.....kullum kwanan duniya yakejin ba za'a sake haifan mace kamanta ba.
Juyo da
ita yayi suna fuskantar juna,idanunsa cikin nata yana ganin ta sake masa wani
ajiyayyen kyau.
"Na dauka zaki tsorata ai" Ya fada a tausashe yana
sanya hannunsa ya matsar mata da wani siririn gashi daya fito ta gefen fuskarta
gefe. Murmushi ta kuma sakar masa tana juya idanunta.
"Tsoro?" Ta tambayeshi tana murmushi,sai kuma ta
miqa hannunta gefan fuskarsa tana shafa kwantacciyar sumar dake wajen.
"Wannan jarumin mazan......wannan uban na 'yan ukun nan
masu sunaye masu daraja......ya fidda kalmar tsoro kwata kwata daga rayuwar
marainiyar nan.....ya cikata da qauna da aminci da soyayya.....ya sanyata cikin
wata masarauta dake cike da tsaro......ya kewayeta da amintattun mutane......ya
kuma sake bata wasu ruhikan har uku da zasu rayu da ita" Kasa magana yayi illa jawota da yayi ya
rungumeta tsam cikin jikinsa.
"Me zan mallaka miki my world......me zan miki da zai
sake fahimtar dake girman matsayinki a raina.....me zan miki?".
"Kaci gaba da sona saboda Allah,kaci gaba da qaunatata
don girman zatin Allah,ka kula dani......ka kula da yayana da
rayuwata.....sannan ka rayu dani ni kadai". Dagata yayi.yana murmushi gami
da duban fuskarta,kafin yace komai ta rigashi.
" Ina da.tsananin kishi.....amma akanka
kadai.....banajin zan iya rabaka ko sharing dinka da wata".
"Kin riga kin sameni.....kin sameni har abada ke kadai
sabreen.....xanta maimaita miki hakan har sai ranar da kika gamsu dari bisa
dari".
"Na yarda dakai" Ta furta tana kallon tsakiyar
idanunsa
"Na yarda dake fiye da yadda kika yarda dani" Ya
fadi yana sauke mata tattausan kiss.
Knocking
din qofar shi ya maida hankalinsu kan qofar.
"Xan iya shigowa hamma?" Muryar amna ta qaraso
dakin bayan tadan buda qofar kadan
"Bismillah" Ya fadi yana takawa zuwa qofar dakin.
Babies biyu
ne rungume a kafadarta,ya miqa hannu ya karbi daya yana tayata dashi. Tare suka
shigo dakin,ya qarasa gaban sabreen ya tsugunna zai miqa mata shi,kaman yasan
an iso gaban mamanshi ya saki kuka.
Murmushi ya
saki yana bude fuskarsa,ya kalleshi da kyau sannan ya daga kansa yana dubanta.
"Farouq ne......" Murmushi itama tayi tana maida
kallonta kan fuskarsa.
"Gyara zaman na baki shi". Saman cinyarta ya dora
mata shi sannan ya saka mata pillow yadda zata jita comfortable. Baya ya koma
ya zauna sosai yana kallonsu cikin burgewa,yadda take shayar dashi hamza yana
gefanta hannunta saman sumar kan hamzan.
"Hamma" Ta kirashi a shagwabe.
"Giwar hamma" Ya amsa mata har cikin ranshi yana
jin ta cancanci wannan sunan.
"Nifa na shirya"
"Zuwa ina?" Ya tambaya yana kallonta.
"Zamuje ni dakai mu kaiwa maamah yaran nan ta
gansu......bata gansu ba bata sansu ba". Shuru ya danyi yana juya
maganarta,hakan ya kamata suyin,to amma shi yana tsoron dabi'ar maamah,baisan
da wanne irin kallo zata dubi yaran ba,yana tsoro kada kallonta kadai ya cutar
masa da yaran. Saidai kuma ya tabbatar sabreen din tana da zurfin tunani da
hangen nesa,ba zata yi abinda zai zamewa yaran cutarwa ba......hakanan ya yarda
da ita dari bisa dari.....
161
"Is
okay" Ya fada a taqaice yana miqewa
"Bari na watsa ruwa kafin lokacin ki sallami sojojina
ko?abbana ne kawai ba'a kawo ba" Ya fada yana kashe mata ido daya. Rolling
nata idanun tayi tana murmushi.
"Ba laifi"
"Wannan abun yana kasheni my world......anya zaki
taimakamin na barki har ki warke?" Ya fada yana karya wuya. Yadda yayi
wani kalan tausayi ya sakata sakin dariya
"Eh to,ai anni tana nan dai......sannan momma ma gobe
zata iso". Sarai ya fahimci me yake nufi,sai yadan bata rai,ya tako zuwa
kusa da ita.
"Karki yadda a zame mana katanga tsakaninmu......bazan
iya jurewa ba,idan kuma har na gaza jurewar komai ma zai iya faruwa" Ya
qarasa maganar yana aje mata wannan zazzafan kallon nasa da taji ya tsarga mata
itama tun daga tsakiyar kanta har tafin qafafuwanta. Daidai sanda kira ya shigo
wayarta,ya matsa a hankali ya dauko mata wayar.
"Bibo da yarinyarta sunzo,saidai na hanata ganinki,don
har yanzun ban gama nutsuwa da ita ba,bazan kuma bari kowanne abu da ban gama
nutsuwa dashi ba ya iso gareku" Ya furta yana saka mata wayar a hannunta.
"Na tabbatar maka bibo tayi nadama zuwa yanzu,don ba
komai yake damunta ba tuncan baya sai kishi da hassada"
"Zan duba na gani" Ya amsa mata yana takawa a
hankali zai fita a dakin,ta maida kallonta kan wayar.
Kawu
rufa'i ne,ta dan saki murmushi tana daga kiran.
"Sannu d'iyar arziqi......sannu d'iyar
albarka......wadda aka haifa tsiya tana bacci". Dariya sosai kawun ya
bata.
"Ina wuni kawu barka da dare"
"Barkanki kadai,an samu kai qalau?"
"Alhamdulillah kawu"
"Ubangiji ya rayasu yayi musu albarka......ai nace
kinyimin daidai da kika bugo yara uku tun a karon farko......wa yaqi
arziqi?,waye zaiyi sanya a gidan arziqi?,ina me miki wasiyya,duk sanda kika
tashi haihuwa dinga ajiye masa hudu hudu uku bibbiyu,idan da hali karkiyi d'an
d'aya ma sam". Dariya ce taso kubce mata,amna ta danneta,saidai hakan ya
nuna a muryarta.
"To ai kawu abun na Allah ne,shi yake bada iya adadin
da yakeso".
" Eh amma ai yace ku roqeni zan amsa muku ko?,qarshen
watannan zamu shiga qasa me tsarki,farouqu xai fara cika alqawarinsa.......zam
zage nayita roqo miki.haihuwar haka haka din" Wannan karon saida tayi
dariya sosai.
"Kawu Allah ya bamu masu albarka wadanda zamu iya
dasu".
"Ke!,kana da wadata da arziqi irin na mijinki harka
dinga tunanin kalar yaran da zaka iya dasu?,yo ko yawan taron arfa kika haifa
masa ai yana da abinda zaiji dasu". Kai ta girgiza tana murmushi.
"Kawu......tarbiyya ba'a nan take ba,kace ameen
kawai"
"To ameen sarkin tsari......nace ba?" Ya fada yana
komawa serious.
"Ina jinka kawu"
"Ina iya tahowa zaman dab'aro?". Idanu sosai
sabreen ta bude dariya tana son qwace mata.
"Kawu kaifa kawuna ne,kuma namiji ne kai,ai mata suke
zaman dab'aro,inama laifin ace inna A'i?(matarsa)".
"Ke komai yanzu a zamanance akeyinsa,ta yaya zan turo
A'i gani?,bayan ba abinda bazan iyayi miki ba?,ni damuwata na kula da d'iyar
ahmadu,na rama halascin da ya yiwa rayuwata" Ta fuskanci da gaske kawu yake,saita gyara
muryarta.
"Kawu kada ka damu,mun dauko masu kula da yaran
musamman,sannan kuma ga masu aikin gidan na ainihi".
"Duk da haka ba za'a barki haka ba,xan aiko A'in ta
zauna miki kona kwana arba'inne na al'ada"
"To kawu Allah ya saka da alkhairi ya qara
zumunci" Ta fada tana jin dadi qasam ranta. Ko ba komai zata ce ga wani
daga dangin mahaifinta,duk da zuwa yanzu 'yan uwa ne kowa keta kutsowa da
b'arkowa don nuna kulawarsa da bajintarsa akan haihuwar,tun suna madeena ma
kafin sukai ga dawowa.
Wayar ta
sauke tana murmushi sanda take tuno baya,drama dinsu da kawu wadda kusan kullum
sai an yita,rayuwa kenan.....komai yayi farko said qarshe,kuma dukkan tsanani
yana tare da sauqi tabbas.
Farouq
yayi bacci,saita ajiyeshi kusa da dan uwansa hamza,ta miqe ta soma
shiryawa,tana yi tana duban fuskokinsu. Ita kadai murmushi yana subuce
mata,tana jin qaunar yaran har a cikin jininta. Duk sanda ta kallesu su ukun a
jere reras saita samu kanta cikin mamakin yanzu wadannan din daga jikinta suka
fito?,yanxu wadannan din 'ya'yanta ne?,mallakinta ne?,yanzu wadannan din
jininta ne?,jinin muhammad fu'ad ne?.
Sanda
ya shigo tsaiwa kawai yayi yana qare mata kallo,tayi wannan sassanyan kyau
cikin shigar atamfar data yafawa mayafi onion color. Sautin sauke ajiyar
zuciyarsa shi ya dawo da hankalinta,tadan juya ido a shagwabe
"Ka tsoratani hamma.....ka iya sanda ka tsaya kayita
qaren kallo.....so kake kyauna ya qare?". Bai amsa mata ba har sai daya
iso inda take,ya rungumeta ta baya sassanyan turarukansu suna gauraya waje
daya.
"Bakisan kina sake qara shekaru kina sake qara kyau a
waje na ba?,tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qagi wannan halittar ya kuma
mallakamin ita a matsayin halaliyata......kuma uwar 'ya'yana" Luf tayi
itama a jikinsa,tana jin yadda soyayyarsa take hudata tako ina.
Mota uku
kawai tayi musu rakiya zuwa gidan maamah din,wadda tun a bakin gate masu da
guards na gidan suka taso,kowa barka yakeyi masa da nuna farincikinsa.
Shi ya
dauki farouq da hamza,ita kuma abba ne a hannunta wato almustapha. Yana gaba
yayi sallama tana biye dashi. Mutum daya suka samu a parlor din wato saratu,ta
miqe tana musu sannu da zuwa,ta kuma karbi yaro guda daga hannun fu'ad din tana
musu barka da addu'o'i sosai.
"Yanzu muka kai hajiya
ciki,munga kaman ta gaji da zaman bacci takeso tayi"
"Har yanzu ba batun magana?". Kai saratu ta
girgiza cikin jimami.
"Ba abinda ya canza har yanzu" Shuru kadan yayi
yana juya al'amarin,a irin kulawar da take samu physically and mentally yaci
ace an samu ci gaba sosai,amma yana mamakin yadda komai yaqi canzawa koda
qanqani kuwa.
Daga
saman gadon da take zaune jingine da fuskar gadon ta daga idanunta sanda suke
sallama cikin dakin. Idanunta ta zube fes a kansu kowanne dauke da yaro guda.
Saratu ce ta fara isa gefanta ta aje hamza tana juyawa ta fice a dakin.
Da wani
irin kallo taci gaba da binsu ba tare data dora idanunta akan yaran ba da
takejin ba zata iya kalla ba,zuciyarta ta fara zafi tana jin gumi yana fara
keto mata.
Kaman
hadin baki suka isa gabanta a tare,fu'ad ya ajiye mata farouq a gabanta,ya
karbi almustapha ya ajiyeshi shima kusa da farouq,ya dawo da hamza kusa da yan
uwansa still idanunta akan fu'ad din yake. Yatsarsa ya sanya ya nuna hamza.
"Ga hamza......wanda ya zamemin tsanin zama muhammad
jadda din da ake kirana dashi a yanzu,hamzan daya bani dakin kwana......ya bani
sabuwar rayuwa,ya bani sabon ahalin da zan rayu dasu,na kuma kallesu a mazaunin
nawa,ya kashemin kudinsa,yayi amfani da lafiyarsa don sama mana abinda zamu
rayu dashi cikin aminci.......ga farouq,wanda ta sanadinsa nakai ga hamzan daya
zama qashin bayan ilimina da tarbiyyata gaba daya........ga kuma
abbana..." Ya nuna almustapha yana tsagaitawa wanda da alama wani abun ya
hadiye.
"Abbana.....sanadi na......abbana da bani da wani abban
daya haifeni wanda zai sake maimaituwa irinsa sak" Yana kaiwa nan ya miqe,ya damqi hannun
Sabreen
"Gasunan maamah.......gasunan ki kallesu,kiga waye
bakiso a ciki?,waye yayi miki wani laifi na rashin kyautawa?.....ki.kallesu
jikokinki ne......yaran da suka fito daga tsatson fu'ad.....dan da kika dauki
cikinsa wata tara,d'an da kikayi naqudarsa tsakanin mutuwa da rayuwa" Yana
kaiwa nan ya fara jan sabreen din suna fita a dakin.
Bugawa
kawai zuciyar sabreen takeyi,don tace akai mata yaran ba hakan yana nufin su
fita a dakin subar mata su ba,zuciyarta ta kasa nutsuwa ko amincewa da hakan
"Hamma......"
"Shshshsh" Kawai yace da ita da qarfi.
"Hamma yara na....." Ta sake fadi a gigice wanda
sautin da reaction din yakai kunnen maamah dake zaune a dakin.
Suna fita
a dakin ya kama kafadunta dukka biyun ya riqeta da qarfin gaske.
"Relax sabreen.....ba abinda zai faru......ba zata
iyayi musu komai ba......inason zamansu a dakin ya wanke duk wani daci da
tsanarsu da zata iya ji a nan gaba......ban isa na sanya ta soki ba kota
soni......amma definitely!.....dole!......dole taso wadannan yaran" Qwarin
gwiwar da take gani tsakiyar idanunsa shine ya bata relief,ta bishi xuwa falon
suka zauna.
Tana iya
jin zaman yaran kusa da ita har cikin jikinta,tana iya jin wanzuwarsu sosai a
tattare da ita,saidai kuma ta gaza daga idanunta ta kallesu. Zafi takeji a
ranta,zafin sabreen sosai takeji,tana ganin kamar itace silar komai da komai.
Sun dauki
mintuna masu yawa a haka,iyayen basu dawo sun daukesu ba,abinda ya dinga bata
mamaki kenan. Me yasa suka iya dauke idanunsu akan yaran?,me yasa suka iya bar
mata su suka fice abinsu?. Motsin da hamza ya fara yi shine ya fusgi hankalinta
ba tare data sani ba takai dubanta kansu.
"Subhanallahi" Ta fadi a ranta tana mamakin zallar
kamannin dake fuskar yaran. Kamannin da suka tuna mata da fu'ad din sanda yake
tsumman goyo kaman haka. Idanu ta zuba masa shi kuma yana ci gaba da motsinsa,a
hankali har ya fara qushin qushin din kuka,abinda kuma ya tashi sauran 'yan
uwansa kenan.
Mutsu
mutsu suka fara yi su duka ukun,kafin kuma a hankali su kece da kuka.
162
Hannun
fu'ad ta riqe da kyau tana ji kaman ana matsa zuciyarta sanda sautin kukan nasu
ya isa ga kunnuwanta. Jikinta duka ya dauki rawa,ta daga idanu tana kallon
fu'ad. Qin kallonta yayi,kuma kaman ta fahimci yana sane yaqi kallon nata,sai
kawai ta sadda kanta qasa tana sake jin yadda zuciyarta ke tsananin bugawa.
Cika
mata kunne sosai kukan nasu yayi.
"Ya isa....kuyi shuru" Ta fadi tana jin ciwon
yadda furucinta baya fita a sanda ta yishi,saidai kuma ga mamakinta sai
almustapha ya fara rage sautin kukansa,a hankali dukkaninsu suka rage kukan
kafin kuma suyi shuru. Mamaki taji ya kamata,ta sake xuba musu idanu wanda
kaman sunsan da hakan sai hamza ya soma bude idanunsa. Tarwai qwayar
idanunsa,kai ba zakace jariri bane dan sati biyu kacal,tana waiwayawa ga sauran
suma duk idanunsu sun bude,kuma ita suke kallo.
Batasan
me yasa ba ta samu qaramin murmushi ya subuce daga fuskarta,ta samu kanta da
yunqurin miqa hannunta ta kamo hannun koda d'ayane a cikinsu.
Cikin wani
irin ba zata da mamaki sai ga hannunta ya motsa,ta maida dubanta ga hannun,ta
sake gwada dagashi xuwa gaba,ga tarin mamakinta sai hannunnata ya isa ga
almustapha ta riqe yatsunsa hannun nata yana wani irin kakkarwa.
Wani abu
da batasan meye ba ya soma ratsa zuciyarta,hawayen da batasan daga ina suke ba
suka tsinke mata.
Wacce irin
baiwa ko hukuncin Allah ne tattare da yaran?,abinda ta dinga maimaitawa kanta
da nacewa da tambaya kenan idanunta akan fuskokinsu dukka su ukun. Sun zame
mata waraka daga wani bangaren ciwon ta kenan?. Tambayar da tana ajiyeta fu'ad
ya murza qofar ya shigo a hankali shidaya,don gaba daya sabreen ta gaza miqewa
bare tayi jarumtar biyoshi,kawai zuciyarta tana gaya mata shikenan,shurunsu
wani abun ne maras kyau ya samesu.
Hannun
nata yabi da kallo yana mamaki shima wanda har yanxu yana cikin yatsun
almustapha,ya qarasa gabanta ya tsugunna yana duban hannun yana kuma duban
yaran.
"Hannunki ya motsa yau?" Ya tambayeta,saita gyada
kai a hankali hawaye yana silmiyo mata daga idanunta. Qasa yayi da kansa yana
tasbihi ga Allah,sun jima a haka sannan ya fiddo wayarsa.
"Ubangiji ya tabbatar da lafiya" Ya fadi a taqaice
yana kiran sabreen zuciyarsa ta nauyaya da girman zatin Allah.
Tana
kallo suna ficewa da yaran a dakin,sai ta samu kanta da gaza dauke idanunta a
kansu har suka kammala ficewa. Tafi qarfin awanni uku bacci bai dauketa ba,tana
jin kamar dakin nata ya koma kango bayan fitar tasu,kamar ba wani abu daya rage
a dakin sai ita kadai.
Abun
mamakin shine,kwana tayi tana mafarkin yaran,cikin mafarkanta na daren gaba
daya sune kewaye da ita,harda wanda suke magana da ita,saidai ta kasa bambance
me suke fadi.
Ajiyar
zuciya kawai ta dinga saukewa sabreen din tana tariyo abinda fu'ad ya gaya mata
na yadda ya shiga ya samu maamah din.
"Ya Allah.....ka jefa matsananciyar soyayyarsu a
zuciyarta ninkin ba ninkin yadda ta tsani mahaifiyarsu" Ta samu kanta da
wannan addu'ar.
*_NAMING CEREMONY_*
Katafaren
kuma qawataccen guri ne na alfarma,aka aka shirya sannan aka tsarashi musamman
saboda gabatar da radin sunan. Komai na gurin kusan fari ne,farin ma irin qal
dinnan me daukan hankali da kuma daukan idanu. Tun daga farkon shiga gurin har
zuwa ciki wasu irin manyan hotunan ne na jiraran design daban daban suke
welcoming naka.
Kana shiga
gurin zakasan guri ne bana wasa ba.....guri ne da akayi barin dukiya,irin barin
da zai gaya maka ba'asan zafin kudin ba,don an nemesu a sanda ya dace an kuma
tarasu.
Komai a
tsare yake,don guri na musamman aka tanada saboda ajjiye yaran. Kowa xai qarasa
ya gansu,me buqatar basu gift ko wani abu makamancin hakan amna da huda suna
kusa,don sune iyayen yaran gaba daya.
Cikin
tsari aka soma gudanar da taron,sabreena maman yaran wadda ta koma hajiya
sabreen,tayi wani irin razanannen kyau cikin wani dan banzan lace da aka warewa
milliyoyin kudi aka bada order saqashi a india. Ba iya lace din jikinta kawai
ba......hatta da lace da atamfofi da manyan luxury warmers da aka raba a gurin
duka container guda akayi musu.
Tun kana
lissafa adadin kayan ciye ciye da shaye shaye da aka tanada a wajen zaka gaji
ne kawai,don kuwa tsarin serve yourself kawai akayi,debi da kanka,kaje ka zaba
ka zuba koka aika a debo maka,ko ka kira daya daga cikin ma'aikatan dake wajen
ka bashi order din abinda kake da buqatar ci.
Guri na
musamman aka tanadarwa jama'ar DUNIYATA,don a idanun sabreen mutane ne masu
kima mutunci da daraja,wadanda suka taimaka qwarai wajen bawa dangantaka dama
soyayyarsu gudunmawa.
A gurinne
fannah ta gabatar da kyautar da BB ya yiwa takwaranshi,wato kyautar sabon
company dinsa na sarrafa auduga da fiddashi qasashen waje.....daukan nauyin
duka wani abu da ya shafi rayuwarsa,tun daga karatu lafiya sutura da
sauransu,yace kawai abbanshi ya zuba masa idanu,don shi aka haifawa umar din.
Bama umar duka ba.....dukkanninsu yana jinsu a zuciyarsa,saidai yace bazaiyi
qarya ba umar din na dabanne a wajensa.
Abba baiyi
qasa a gwiwa ba shima ya aiko da nashi saqon ta hannun amna,estate guda ne me
dauke da gidaje dari ya mallakawa nasa takwaran. Ihu aka dinga yi a
wajen,saboda yadda abun ya qawatar da mahalatta taron,wato dai gasa ce ta
gasken gaske tsakanin kowa da takwaranshi. A sannan fu'ad din yana daga can
gidan hutawarsa,yana kallon yadda taron yake gudana kamar a gabanshi,ta hanyar
cameras da ya saka aka zuba sosai a wajen,aka kuma miqa ragamar monitoring
dinsu a hannun qwararrun security dinsa. Saidai duk da haka yaji yana sha'awar
zama,yayita kallon duniyarsa da yanzun ta rarrabu da wasu hadakar qananun
duniyoyin har guda uku.
Murmushi
ya saki yana gyada kai,shi za'a yiwa wariyar launin fata kenan a ware masa
abbansa?,kawai sai ya dauki waya ya kira musaddiq da nashi saqon.
Sanda
musaddiq ke sanar da bada kyautar JADDA WINGS ga almustapha kusan kowa sai da
yaji shock,kafin daga bisani gurin ya kaure da tafi.
"Sannan nima ina gabatar da tawa qaramar kyautar
motar" Ya fadi yana fiddo maqullin motar daga aljihunsa ya dagashi sama ya
kuma isa gaban abban nashi almustapha ya ajiye. Motace me bala'in tsada new
model,wadda har yanzun ko cikin masu kudi ba kowa bane ya samu nasarar
mallakarta ba. Tabbas abban abba ne,kusan yafi kowa a cikinsu tashi da
gwaggwabar kyauta.
Kafin
abar gurin fu'ad ya sanya qaramar musabaqa ga yara masu haddan qur'ani a
wajen,daga shekara goma sha biyu zuwa qasa,koda izu uku ke gareka kuwa. An
gwabza musabaqa me kyau,abinda ya sake janye hankalin sabreen taji a duniya
bata da burin daya wuce yaran nata su zama mahaddatan alqur'ani.
Sai da aka
kammala komai sannan anni itama ta gabatar da nata kyautan. Motoci ne masu kyan
gaske guda uku iri daya sak,dukkaninsu farare qal,amna kuwa wani babban box ne
da ba wanda yasan ainihin meye a ciki. Fannah ma ba'a barta a baya ba,itama da
nata gift din,haka dai kusan duk wanda yazo wajen da nasa alkhairin da zai
gabatar,
Muhammad
fu'ad jadda ba qashin yarwa bane,komai arziqinka komai kuma babunka ba zaka
taba cewa baka amfana dashi da komai ba,wannan ya saya ma yaranshi dama matarsa
wata irin soyayya da qauna.
Taro ya
tashi lafiya,yara kuma sun tabbatar da sunayensu na ALMUSTAPHA MUHAMMAD
JADDA(FAWAD). HAMZA MUHAMMAD JADDA(FAUZAN). da babban aboki amini kuma dan uwa
UMAR MUHAMMAD JADDA(FAWWAZ). Yaran sunzo da wani irin yanayi a dangi gaba
daya,yan uwa dama wadanda ba 'yan uwa ba kowa ya tafi da fawwaz fauzan da fawad
a bakinsa.
Kusan
gaban idanunshi aka gama komai,koda ya dawo gidan wajen sha biyun dare yayi
mamakin haurowarta samanshi batayi bacci ba.
Daga qofa
ta tsaya ta langabe kafada,ya saki murmushi yana cewa.
"Qaraso ciki........kinsa yau duka kishi ya
kamani......na kasa sukuni sam". Ido ta zaro,ya sakata sakin murmushin da
bata shirya ba.
"Hamma.....kishin me?,duka mata ne fa a wajen,yaran
dake wajen under age ne fa?". Idonsa ya lumshe yana duban dukiyar
fulaninta da suka tutturo kaman suna tsokanarshi ne ma,lafiyayyar farar fatarta
dake samun kulawa tana sake qawata su,uwa uba kuma yanayin rigar da tayi amfani
da ita V neck ne da aka shimfidawa lace.
Wani abu
ya hadiye a maqoshinsa kawai ya miqa mata hannu,tana mamakin maganarsa ne,don
haka sam bata lura da mayataccen kallon da yake watsa mata ba.
Tanata
masa surutu na labarin taron suna,har sai da yayi mata wata kyakkyawar runguma
sannan hankalinta ya dawo jikinta,dif surutun ya dauke,shuru ya wanzu a
dakin,sai sautin bugawar zuciyoyinsu. Duk wani gaba ta jikinsa sai data amsa,ya
sake cusa hancinsa cikin jikinta yana jin qamshinta yana birkitashi.
"Sati uku adda na......sati uku da haihuwan su fauxan
right?" Kai ta gyada masa,sai shima ya jinjina kansa yana dan zame jikinsa
kadan daga nata.
"Naga kaman kinyi sallah daxun da asuba ko?".
Qirjinta ya buga tsoro ya saukar mata.
"Hamma.....nayi sallah......amma fa three
weeks....." Yadda ya zuba mata jajayen idanunshi ya hanata qarasa
magana,ta maida abinda takeson cewa.
163
"Yayi
wuri?,nasan haka zakice.....amma bakisan me nakeji bane sabrrrr".
" I know hamma......na sani,ba wani motsinka da zan
kasa gane manufarsa.......I will always be ready to accept you.....amma yanzu
hamma,dr tace ina buqatar time kafin wannan abun,yana da kyau nayi healing
sosai". Zame jikinsa yayi yana lumshe idanunsa ya koma wata kujerar daban
ya zauna yana dafe goshinsa. Tausayinsa taji ya kamata,ta tako a hankali zuwa
gabansa ta tsugunna tana dora hannuwanta saman cinyarsa.
"May I help you?.bette" Idanunsa da suka sauya
launi ya bude a hankali yana kallonta,saita sake gyara tsugunonta
"I will help you to feel better" Idanunsa ya ware a kanta yana dafe
hannuwanta.
"No.....ba abinda hakan zai qara bazai magani
ba.....komai zai iya faruwa don qishirwa kawai zaki qaramin......dawo nan ki
zauna muyi hira" Abinda yace kenan da ita yana ture mata pillows din da
suke gefanta.
Hirar kuwa
tayi masa sosai,ta dinga bashi labaran abinda ya faru a wajen. Tun yana tsume
har ya ware,ya soma dariyan abubuwan da take bashi labarin,qarshe dai a nan
suka bingire yana rungume da ita,basu tashi farkawa ba saida kiran wayar tashin
triplet ya farkar dasu.
★Sannu a
hankali kwanaki suka dinga tafiya,abubuwa da yawa sun lafa kuma sunyi
sanyi,kaman darajar haihuwan yaran yazo musu da abubuwa ne masu yawa.
Amna da
fannah harma da huda dukkaninsu goyon ciki sukeyi,amma hakan bai rage musu
kwadayi ko sha'awar yaran ba. Babu wanda ke iya kwana biyu cikakke ba tare daya
kira yaji lafiyar yaran ba. Farouq kuwa da aka jarabceshi da son takwararsa
gidan ya zame masa kaman hanyar wucewa,sai aiki yayi mugun cude masa yake kwana
uku bai shigo gidan yaga yaran nashi ba,ya kuma kebe takwaransa sunyi ganawa ta
daban da sauran.
Ta
bangaren maamah kuwa.....tun ranar daya kai mata yaran suka kasa bacewa daga
idanu da kunnenta. Cikin awanni ashirin da hudu na yininta kowanne awa bata
rufewa ba tare data tunasu ba. Sannu sannu sai takejin kamar tanason ta sake
ganin yaran,kaman tana kewarsu,idan tana dakin bata da aiki sai kallon muhallin
da ya kwantar dasu a waccan ranar. Wani abu takejin kamar yana shirin kamata me
kama da hauka hauka akan yaran,tana yawan jin irin kukan da sukayi a waccar
ranar,tana yawan jin muryoyinsu kaman suna wajen.
Daga
qarshe dai ta fahimci son ganinsu takeyi,saita ta rasa kuma yadda zata fahimtar
dasu saratu tanason ta sake ganin yaran,don iyasu kadai kawai takeson gani
banda mahaifiyar tasu.
A
hankali sabreen din cikin salo da hikima ta soma gyaran jikinta ta hannun
dattijuwar matar nan da tasan jiya tasan yau kuma har gobe ake tafiya da ita
wato Bgawos kitchen and aphrodisiac. Ingantattun kayan gyara natural na matan
da suka jima a duniya kusan shekaru hamsin.08127084190/08104553105(tasan sirrin
gyara sosai,gyara irin na dauri na tsaffin mata bana zamani ba,bana gama garin
masu magungunan matan yanzu ba,bama gyaran kadai ba,hadda duk wani nau'in
abinciccika,na biki ne suna taron sauka walima da sauransu,ko kuma kawai akwai
ranar da zaki tashi bakya sha'awar shiga kitchen?,kinaso kuma abincin gidan ki
ya zama ready a tsaftace kaman ke kika shiga kitchen din kikayi da kanki?,karki
tsallake wannan).
A jikinta
kawai taji canji me matuqar yawa,ta sake jinta tana sake kintsuwa tako ina. Har
ta soma gyaran jiki ta watsar,don ta tsorata sosai ranar da fu'ad ya rutsata,da
qyar tasha,amma daga qarshe ya gaya mata yana lissafe da satittikan da suka
rage.
Tunani ta
shiga sosai na yadda zata kubce masa,tanaso ta sake warkewa sosai,uwa uba kuma
sunyi hira da fannah,har suka gangaro kan tsarin iyali.
"Muddin period dinki ya dawo to duk sanda kuka kasance
tare xaki iya daukan wani cikin" Idanu sabreen ta waro waje.
"Ciki fannah......" Ta danyi dariya.
"Satinsu fauzan nawa?" Dariya fannah tayi.
"Shi ba ruwansa da satin yaranki nawa......indai har
period ya dawo daidai shikenan magana ya qare"
"Fannan BB...." Sabreen ta fada tana cin serious.
"Adda sabreen" Ta amsa mata tana dariya qasa qasa.
"Kibar zancan nan tukunna......me zaki bani na gyara
tsarabar bare bari" Gyara zama fannah tayi.
"Kamar kuwa kinsan mu bare bari ba wasa bane" Sai
suka saki dariya a tare.
"Bari na gutsira miki kadan.....ki samu 'ya'yan
habbatussauda da dabino ki dinga ki tsaga dabinon ki cire qwallon ki zuba yayan
habba din ki dinga taunawa kullum safe da dare". Da daya da daya ta dinga
bata sirrikan da na barebari ne,ita kanta ta qaru ta kuma sallama (sai damu
wallahi😂🥱).
A tsorace
take har zuwa sanda suka cika sati shida,ganin sun tsallake ranar baice mata
komai ba,don washegari qaramar tafiya ta kamashi zuwa branch dinsa na lagos,don
haka kawai tayi amfanin da wannan damar ta tayar da yawon arba'in.
Dabara
tayi,ta kira anni tace mata tana son zuwa din,amma bata samu hamman ba,tunda
tasan wani lokaci idan tafiya me muhimmanci wadda take ta gaggawa irin haka ta
taso masa yakan saka layinsa a flight mode ne
"Yana da kyau ai,ko don a sake ganin 'yan uwa,zan gaya
masa da kaina" .
Hankali
kwance tahau shirinta,so samu ma ta wuce mali wajen mommanta,to amma mali din
tasan tayi nisa ta tsallake zuwa can,don haka kawai saita shirya zuwa abuja
gidan yayan ummeenta da bai jima da dawowa Nigeria ba,ta shirya su fauzan duka
da masu aikinta,ta siya musu ticket suka wuce abinsu.
Sanda
anni ta gaya masa harda 'yar mitarsa,yana tunanin cikin kano ne zasuyi
ziyaransu gidan kawu rufai da gidansu da sauran wajen 'yan uwa su dawo gida su
kwana.
"Anni kina ganin ba zata debowa yaran nan iska ba?,40
days fa kawai sukayi,nima kwana uku kawai zanyi fa na dawo,meye na fitan?"
Ya kasa boyewa sai daya furta.
"Banda abinka fu'ad ai sada zumunci ne,kuma a al'ada ai
dama ana yin wannan zagayen,kaman ba gajiya ne da kuma nunawa dangi lafiya kuke
ne" Shuru ya danyi,dondai anni
ce,yana kuma kunyar jayayya da ita.
"Shikenan,Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen ameen" Anni ta amsashi suka dan sake
tattaunawa sannan suka shiga wani maganan na daban.
_Yawon arba'in ko?....hmmmm😂😂......._
_get ready muna pages din qarshe ne fa in sha Allah_🥰🥰🥰
★Kwanansa uku a
lagos,kwanan sabreen biyu a Abuja ya dawo kano. Har ya iso gidan baiyi wani
tunanin abuja ta tafi ba,sai bayan ya shigo ne yadda gidan yayi masa shuru da
yawa ya sakashi ya fara kokwanto. Tun a parlor na biyu ya soma da duba kitchen.
Ba alamun dazu ko jiya anyi amfani dashi,kai tsaye kawai ya wuce bedroom dinta.
Yadda
yaga komai a killace ya bashi amsar cewa ba mutum a gidan,mamaki ya sanyashi
zama gefan gadon nata,yana kallon inda aka shirya qananun gado saboda su fauzan
idan a dakin zasu kwana.
Sai
lokacin yayi noticing wani abu,tunda ya tafi shi yake kiranta,idan ya kunna
wayar yana tunanin zai samu saqonta ko miscal dinta sai ya tarar wayam,idan
kuma ya tashi kiran nata sai ya kira sau nawa ana gaya masa isn't reachable,sai
daga baya ya sameta. Jiyama kwata kwata basuyi waya ba,don ya shiga cikin
qaguwar kammala aikin daya kaishi ya juyo gida.
Ya manta
rabon da yayi nesa da ita har haka.....bare su yaran da dama bai taba nesa dasu
ba sai a wannan karon.
Koda ya
ciro wayarsa sai ya rasa waye zai kira?. Anni dai ya tabbatar bada cikakken
saninta akan baisan nesa zasuyi ba akayi tafiyar ba........ita kuma sabreen ya
kirata yace mata me?.
Wani
mummunan baci yaji ranshi ya soma yi,zuciyarsa ta soma tafasa sosai,sai kawai
ya fara maimaita
"A'uzubillahi minashshaidanir rajeem.....innalillahi
wa'inna ilaihi raji'un". A hankali a hankali yaji zuciyarsa tana yin
sanyi,gefe guda kuma yana tunawa kansa maganganun malamai da yawa da kuma
abbansa,hadisin manzan Allah S A W da yake gayawa maza su waye
mata?.....karkatacciyar halitta da aka halicceta da qashi mafi karkacewa na
haqarqari,da wannan ya danne zuciyarsa badon ranshi ya daina baci ba.
Samansa ya
haura yayi wanka,ya dawo ya shirya cikin shigar wani tattausan yadi ruwan
sararin samaniya,kawai sai ya dauki key da wayarsa ya fice a gidan,duk da cewa
yunwa yakeji.
Da
kansa yake driving,kanshi cunkushe da tunanin ina zata je?,ina zataje da har
bai sani ba?,ya miqa hannunsa ya dauki wayarsa da daya hannun dayan kuma yana
riqe da steering ya soma kiran anni.
Bugu uku
annin ta dauka,yana iya jin maganarta da su nadra,yaran da qiri qiri tace nata
ne.....bama tun ya zu ba,tun a baya inda tasan dasu da tuni sun jima da zama a
hannunta,dole kowa dake da kwadayin daukarsu ya haqura yabar mata su.
"Barka da dare anni" Ya furta muryarsa ba wani
karsashi yana rage gudun motar.
"Barka kade me babban suna,abban abbobinsa" Ta
fada da dan tsokana kadan a muryarta. Duk yadda yakejin muryarsa a jagule saida
sabon sunan data sanya masa ya sakashi sakin murmushi.
"Mun yini lafiya?"
"Alhamdulillah.....ka dawo ne?". Sai daya hadiye
wani abu sannan ya amsa mata.
" Na dawo dazun,bai wuce awa daya ba".
"To ma sha Allah,Allah ya bada abinda akaje nema da
nasara me yawa"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Sai kuma ya danyi shuru.
"Da wani abune?" Ta tambayeshi,kaman yadda ta saba
da saurin gano damuwarsa tun baikai ga furtata ba.
"Cewa nayi anni......wanne waje ne su fauxan suka
je?" Banbarakwai anni taji maganar
"Abuja mana.....ina cewa kun fara magana dama tun kafin
ka tafi?". Kai ya girgiza a hankali,ya fahimci inda maganar yanzun ta
dosa. Idan ya cewa anni baisani ba hakan bai dace ba,zai zamana kaman ya nunawa
anni wani laifi nata da wala'alla zai saka annin jin wani iri a kanta,don haka
sai kawai yace.
"Ba komai anni......na dauka sun canza booking ne"
"Aah abujanne dai,gidan uncle mubarak ko".
"Ba matsala.......sai na shigo".
"To Allah ya kawoka lafiya" Har zai yanke kiran ta
rigashi.
"Me kaci daka dawo?" Tayi tambayar ne don bata
gamsu da yanayin muryarsa ba,kuma wani tunani ne yazo kanta a sannan.
"Ba komai anni....amma zanci".
" Ka qaraso ga favourite dinka anyi".
"In sha Allah,godiya nake" Ya fadi yana yanke
kiran.
Cilla
wayar yayi seat me zaman banza yana jin wani bacin rai yana taso masa. Duk wani
dalili na kiranta yakejin babu shi yanzu a tattare dashi. Gudun na meye?,kaman
wadda yake sarar naman jikinta?,ko soyayyar daya bata ne ta mata yawa takeson
ta fara karya alqawarinsu,ta kuma fara wahal dashi kaman yadda sauran mata
sukeyi a sanda suka samu soyayyar d'a namiji yadda sukeso?. Shikam yana jin
bazai dauki irin wannan ba,ya tsare mata dukkan komai,itama ya kamata ta tsare
masa.
_hausawa sukace zo mu zauna zo mu saba,ran maza ya baci_
_wanne hukunci kuke ganin ya kamata jadda ya yiwa sabreen?_😂😂
164
Karya kan
motar tasa yayi zuwa unguwar tasu,yana jin ya kamata ya duba maamah,duk da ko
bayan ya tafi kullum sai ya kira yaji ya suka kwana,ya kuma suka tashi.
Tun daga gate
masu aikin gidan suke gaidashi,har zuwa sanda ya isa qofar parlor din.
Takalmansa ya cire,sam bashi da wannan dabi'ar na shiga guri da takalmi,duk da
girman daraja da matsayin da Allah ya bashi,ya sanya kansa a parlor din a nutse
bakinsa dauke da sallama,duk kuwa da yadda zuciyarsa ke a matuqar b'ace.
Muryarsa
ta sanyata daga kanta da sauri daga karbar madarar da saratu take bata.
Idanunta ta kafe a kansa kafin ta maida dubansa zuwa ga bayansa kaman me neman
wani abu. Ita shima yake kallo,yana mamakin yadda taketa kallon bayansa
din,kwanyarsa nason lalubo masa dalilin kallon.
Bugun
zuciyarta yadan qaru,sai taji zuciyarta tana dan washewa daga sanda yayi
sallama a parlor din. Can qasan ranta ta samu kanta da fatan Allah yasa tare
yake da yaran,Allah yasa tare suke,saidai duk walwalar da taji ta sauko mata
sai taji tana komawa sanda ya qarasa shigowa falon,ta kuma fahimci shi kadai
ne.
"Kawo na qarasa bata" Fu'ad yace da saratu sanda
ta gama gaidashi yaja kujera ya zauna daura da maamah din. Amsa masa tayi cikin
girmamawa,ta miqa masa hade da dan qaramin towel sannan ta miqe tana basu guri.
Duk sanda
ya miqa madarar bakinta sai yaga ta kafeshi da wani irin kallo,ya kasa gane
abinda yasa take binsa da kallon,saidai yasan cewa lallai akwai wani abun a
qasa.
Wani irin
boundaries takeji tsakaninta dashi,zamansa kusa da ita yana shayar da ita
madarar sai taji kamar ana sauyata ana kuma sauya jiki da zuciyarta. Fuskokin
yaran guda uku take gani a tasa fuskar,tanaso tace masa ina suke?,tanaso tace
masa ina ya barsu?,tanaso tace masa yaje ya dauko mata su amma kuma ba halin
hakan,ba kuma bakin hakan a tare da ita.
"Akwai wani abu da kike buqata?" Ya tambayeta
ganin yadda kallon yaqi qarewa yana kallon hannuwanta. Kai ta girgiza masa a
hankali,amma still bata daina kallonsa ba.
"Zaki iya rubutu?" Ya tambayeta bayan ya gama
kallon hannunta guda daya wanda tun wancan ranar yaci gaba da motsi. Kai ta
daga masa a hankali tana jin zuciyarta tana tsinkewa. Kowa da yake tare da ita
ya gaza gano mata hanyar fadin abinda yake bakinta amma gashi daga zuwansa har
ya gano hakan.
Tana ji
yana kiran saratu,sannan ya sakata taje ta dauko memo da sticky notes a ajjiye
mata koda yaushe a kusa da ita.
Sanda
ta kawo din sai ya ciri sticky notes din guda daya da a biro ya dora saman
cinyarta
"Write it down" Ya fada a nutse yana kallonta.
Gabanta ne ya fadi,jikinta kuma dukka yayi sanyi tana jin wani yanayi daya
haifar mata da fara rawa da jikinta yayi. Sauke biron tayi tana jin ba zata iya
rubuta komai ba. Tana jin kunyar tambayarsa yaran duk kuwa da yadda take
bala'in son ganinsu......ba abinda ya dawo mata a lokacin sai gamuwarsu ta
qarshe,daya ajjiye mata abun rubutu kaman haka,yace kuma ta rubuta dukka adadin
abinda takeso zai bata don ta rabu da rayuwarsu har abada,kenan hakan yana
nufin inda ta rubuta din sun rabu?,inda ta rubuta din da yanzu ko dan tsako
bata dashi wanda zai zauna haka a gabanta ya damu da damuwarta?. Ga dukiyar ga
komai tana gani......amma kuma bata wani jin d'andanonta sam a tattare da ita.
Lumshe
idanunta kawai tayi tana maida bayanta jikin kujera ta jingina,yadan tsaya yana
kallonta saiya kalli saratu.
"Idan bacci takeji a maidata daki a gyara mata gun
kwanciya.....ni zan wuce,sai da safe idan Allah ya kaimu"
"To ranka ya dade....Allah ya tashemu lafiya".
Kai tsaye
gidan anni ya wuce,ya sameta da 'yan matanta guda biyun,nadra da haneefa.
Abinci sukeci,kai tsaye nadra ta shirya masa nasa abincin sannan sukayi qoqarin
tashi su basu waje shida anni.
"Kuyi zamanku" Fu'ad ya fadi yana ganin fuskar
haneefa kamar sabreen ce a wajen saboda kamannin da suke da ita.
Sosai
yayi qoqarin share damuwarsa ta hanyar sakewa yayi hira da anni,saidai suna
tsaka da hirar kiran sabreen ya shigo wayar annin.
Bai sake
cewa komai ba yaci gaba da cin abincinsa,saidai kuma yana iya dauko sound dinta
ta cikin wayar. Abinda ya sake quleshi yadda yaji tana hira hankalinta
kwance,suka gama maganganun da zasuyi da anni su haneefa suka karba suma suka
dora.
"Lafiya dai ko Muhammadu?" Anni tace dame babban
suna wanda har ya kammala cin abinda zai iya ci ya miqe. Murmushi ya qirqira.
"Ba komai anni......" Bata gamsu ba sam sam,saidai
daga kiran da sabreen tayi kawai taga fuskarsa ta sake canzawa,amma kuma bataso
ta zama me yawan sanya kai akan mu'amalolin gidajensu. Koda matsala ce tafison
su koyi kasheta da kansu da kansu,hakan zai koya musu jarumta da kuma dabarun
xama da juna da kuma sake samun shaquewa sosai da juna.
Ya
yiwa anni sallama ya fito zuwa parking lot na gidan farouq ya shigo shida
fannah. Fanna ta gaidashi ta wuce ciki,shi kuma farouq din yayi tsaye daga
wajen motar fu'ad na daga ciki ya zuro qafafunsa waje.
"Inata tunanin kiranka ai" Fu'ad ya fadi yana dan
shafa sumarsa,don duk yadda yakeso yayi avoiding damuwar amma har yanzu yana
jinta cikin kansa.
"Lafiya kake dude?" Farouq ya tambayi fu'ad din.
Kaman zaice wani abu sai kawai ya basar,yanason koma meye ya ganar da ita
kurenta da kansa,basai wani ya ji ba.
"Share kawai......hannu nakeso ka sakamin a
nan" Ya qarashe maganar yana miqaqa
farouq din. Karbar takardar yayi yana dubawa.
Takardar
mallakar wani tafkeken fili ne me fadin qafa da tsaho me yawan gaske. Daga kai
tukunna farouq yayi ya kalleshi.
"Wanne company ne haka zai sake lashe girman filin
nan?" Murmushi fu'ad ya saki a
gajiye.
"Ba wani company.........mafarkina nakeso na cika na
gina mana gida guda daya amma me gidaje sassa daban daban a ciki,wanda zai
qunshi duk wani jinin jadda......ina mana sha'awar mu rayu tare yadda yaranmu
zasu tashi da zumunci fiye da namu in sha Allah". Kai farouq ya
jijjiga,sai ya maida file din ya rufe.
"Wannan burina ne.....ni na tanadar mana wannan
filin,bazan kuma bari ka rigani ba......kayi haquri ayi amfani da
nawa" Kai fu'ad ya girgiza yana
dage glass din motarsa
"Is too late dude........saidai ka dauki wani abun
daban........amma wannan kam na riga na gama dashi,already ma yau nayi
requesting ma wani company daga china zasu zo su fidda komai yadda nakeso ya
kasance......idan ka saka hannun ka ajjiye documents din a hannunka,saida
safe" Ya fada duka a dunqule yana jan murfin motar ya rufe abinsa sannan
ya tashi motar da gudu yana fita a gidan.
Da kallo
farouq ya bishi har ga bace masa,sai kawai ya jinjina kai yana maida dubansa ga
file din,sannan ya fara takawa yana wucewa cikin gidan.
Ko sanda
yaje lagos baiyi baccin wahalar da yayi ba a daren. Lagos yasan baqon guri
yake,gurin da ba iyalin nashi,amma anan gurin a yanzun yasan cikin gidanshi
yake,saidai ya kasance shi daya,don haka tunda asuba ya lalubi pilot nashi yace
ya nema musu izinin tashi zuwa abuja a yau din.
Sai wajen
bakwai na safe ya kirashi,a lokacin yana cikin gym,ya sauko daga saman machine
din da yake kai ya dauki wayar yana duba kiran. Zama yayi yana goge gumin
jikinsa da qaramin towel.
"Sir......mun samu izini,amma qarfe biyu daidai na rana
suka bayar"
"Good.....hakan yayi,zan kasance a airport din one din
in sha Allah"
"Yes sir" Ya amsa masa suna ajiye wayar gaba
dayansu.
Cikin
wani baqin lafiyayyen yadi me tsada da aka yiwa dinkin kaftan ya shirya.
Hularsa zuwa takalminsa dukkaninsu gray color ne,sosai yayi wani wani irin
azababben kyau,kalar baqin kayan saman farar fatarsa ta zama wani abun kallo na
musamman. Haibarsa da kwarjininsa sun ninka na koda yaushe saboda rashin
walwalar dake shimfide saman fuskarsa.
Shi da
saddiq kawai suka tafiyar,sai jordan daya zama kaman aljihunsa saboda
jajircewarsa da kuma qwarewarsa a aikinsa da kuma kula dame gidan nasa.
Kasancewar
juma'a ce,sai daya tsaya central mosque sukayi sallan juma'a. Yadan samu delay
kafin subar masallacin,har la'asar saboda a ranar ana wani taro a nan a buja
daya shafi qasa,kuma manyan mutanen daya jima basu hadu ba suka tsareshi a
wajen.
Daya daga
cikin drivers dinsa ne ya iso da daya daga cikin motocinsa dake ajjiye a
katafaren mansion dinsa na nan abujan qirar Lamborghini. Kai tsaye jordan ya
karbi driving din daga hannunsa suka qarasa zuwa cikin maitama. Plate number
dake jikin motarsa kadai ya sanya me gadin bude musu qofa,Kai tsaye jordan ya
qarasa parking space na gidan ya ajiye motar.
Bai fita
a motan ba,har sai da daya daga cikin ma'aikatan gidan ya sanar da safuura
matar uncle din sabreen zuwan fu'ad din.
Tana
kitchen tana hada abincin daren me gidan,tuni ta saki girkin tana cewa.
"Ku bude masa seating room maza akai masa drinks da
abinci,me gidan baya kusa,bari nazo mu gaisa". Fu'ad sunanshi kirkinsa
dama kamanninsa duka ba baqinsu bane,wannan ya sanya suke matuqar girmamashi da
yadda kuma ya riqe sabreen dama 'yan uwanta da kyau,duk da ba gazawa sukayi
wajen riqesu ba.
Daidai
lokacin fitowar sabreen kenan daga wanka bayan ta murje hadin dilka dana gyaran
jiki da akayi mata,tun daga ranar da tazo mummy safuura ta soma gyarata ta ciki
da waje.
Idanunta kan babbar TV plasma dake maqale a bangon dakin tana kallon
waqar dani kake kama. Sosai waqar ke shiga ranta da wani irin yanayi daya sanya
zuciyarta tayi wani irin laushi,zuciyar kuma ta fada wani matsanancin kewa da
begen mamallakinta wato muhammad fu'ad jadda.
Ajiye
towel din hannunta tayi ta taka zuwa gaban mirror tana duban wayarta dake ajiye
a kai. Yawancin lokuta tunda tazo a kashe take barin wayar,saboda tana tsoron
ya kirata yaji inda take yace ta dawo gida. Tanason tadan sake samun lokaci
kadan,duk da tayi kewar komai daya shafesa kewa bana wasa ba,amma a yau din sai
take jin haqurinta ya gaza,koda muryarsa tana da buqatar taji.
Kunna
wayar tayi sannan ta zuba numbers dinsa da tuni ta jima da haddacesu,kiran ya
fara gangarawa yana shiga wayarsa dake hannunsa a daidai wannan lokacin da suke
gaisawa da mummy safuura.
Fuskar
wayar kawai ya kalla,yadan zubawa kiran idanu yana mamakin ya akayi ta kirashi
a daidai irin wannan lokacin?. Yasan tabbas batasan yazo ba,don ga mummy din a
zaune a gabansu ballantana yayi tunanin itace data shiga ciki ta gaya mata.
Kife fuskar
wayar yayi,har ta gama rurinta ta katse ba tare ma daya sani ba.
Da dan
mamaki ta sake daukan wayar tana sake kira,ta saka a handsfree ta ajiye tana
jin yadda bugun zuciyarta ke daduwa. Still bai daga ba,abinda bai taba faruwa
ba kenan a tsakaninsu. Komai yawan aiki ko uzurin dake gabansa kiranta na
dabanne,to amma batasan wanne irin aiki ya samu da yawa haka a lagos din ba,don
haka sai ta ajiye wayar ta miqe da nufin shiryawa,idanunta kan su fauzan dake
bacci dukkaninsu su ukun abinsu.
165
Tana
bude luggage dinta hamra diyar mummy safuura ta tura qofar dakin da sallama ta
shigo.
"A tashi HAMFAAL(hamza/farouq/almustapha)". A
marairaice Sabrina ta dakata da daukan kayan da take shirin yi ta dubi
hamra,don tunda taji tace hamfaal to dukkaninsu take nufi.
"Amma dai antynsu fawad ayimin rai don Allah......ina
shirin karance littafin girke girken nan yau duka gaba dayanshi zaki jiqamin
aiki?" Dariya sosai hamra tayi,don ita sam bata ma qaunar yaran suyi
bacci. Bata gajiya da rainonsu,zuwansu ne yasa ta fara jin gidan nasu a
mazaunin gida sosai.
"Ayyah.....yau ba laifina bane......daddynsu ne yazo
ganinsu". Dum!,taji qirjinta ya buga,gabanta yayi wani wawar faduwa,tsoro
kuma taji ya saukar mata. Ta fidda idanu waje tana tambayar hamra.
" Please hamra......banason wasa"
"Serious adda......yana seating room,yanzun suka gama
gaisawa da mummy" Ta fadi tana takowa ciki saboda shigowar me aikinsu da
zata tayata daukan yaran.
"Gasunan.......ga abun daukansu can" Sabreen ta
fadi tana nuna mata tattausan abun daukan guda uku farare qal dake ajiye a
gefe.
Tsaf suka
nadesu suka fice dasu,saita bisu da kallo har suka bacewa ganinta sannan ta
maido dubanta cikin dakin tana sauke nannauyan ajiyan zuciya.
Tsoron
yadda zata tunkareshi takeji sosai,amma dole haka ta qarfafa gwiwarta ta som
shiryawa cikin mutuwar jiki da rashin kasala.
Dukkanin yaran ya aza saman qirjinsa ya rungumesu yana shaqar daddadan
qamshinsu daya cakude dana mamarsu da yake iya jiyowa cikin jikkunansu
(Shi yasa wannan yake zama babban abun kaico ga macen da
take jego amma wai don wani kayan takaici da baqinciki ka rasa qamshi a
jikinta,to wannan qarnin da qarin da kikeyi haka jikin yaronki zai zama,kada
kiji haushi kada kuma kiyi mamaki idan kikaga yaronki sam baida farinjini duk
da kuwa kyakkyawa ne,hakanan kada kiyi mamakin ganin ana rububin daukan yaron
wata kuma bayan baikai yaronki kyau ko saka sutura me tsada ba,don Allah mu
kula da wannan,qamshi rahama ne,koda kuwa iya keda hancinki ne ma 'yar uwa😂😂).
Bugawar
zuciyarsa ya canza sosai daga dumin yaran kawai,sai a lokacin ya sake fahimtar
yayi kewarsu bata wasa ba.
Ajiyar
zuciya a jejjere ya dinga saki kafin daga bisani ya saukosu. Saddiq ya karbi
abbanshi hamza. Da fuskarsa da tasu ya manne guri guda,ya basu tattausan kiss a
goshinsu.
Cikin wani
tattausan milk material ta shirya,tayi wani irin sassanyan kyau,jikinta na
fitar da tattausan qamshin nan nata na incense by kabo daughter da yafi qauna.
Glowing kawai skin dinta yakeyi na masu danyan jego,ga cikakken hutu ga kuma
gyara da takesha,wanda hatta da abun shanta mummy safuura na daban take bata na
gyaran mata. Kanta ba dankwali sai qaramin mayafin material din data yafa saman
kan nata,wannan ya bawa sumar kanta me sulbi daman fitowa ta gaban goshinta.
A
parlor ta samu mummy safuura,saita nuna mata wani kyakkyawan glass bowl me
murfi
"Dauki wannan ki tafi masa dashi......."
"To" Kawai tace da mummy a sanyaye.
Tun
daga qofar setting room din ta lura ba alamun takalmin mutum ko daya,saidai duk
da haka bata kawo komai a ranta ba ta taka a hankali ta shiga parlor din.
Wayam ba
kowa cikin setting room din,sai tattausan mayataccen qamshin nan nasa. Bugawa
zuciyarta ta dinga yi d'ai da d'ai d'ai,indai batayi kuskure ba a nan din hamra
ta fadi mata an saukesu,to amma ina suka shiga?.
Mugun
sanyi jikinta yayi,tayi taku biyu tana isa saman daya daga cikin kujerun ta
zauna sannan ta ajiye bowl din hannunta. Wayarta data fito da ita ta zaro ta
soma kiran mummy safuura. Bugu biyu ta dauka
"Ya akayi sabreen?".
" Mummy.....banga kowa a seating room din ba.....ba
kowa" Ta qarasa fada a sanyaye.
"Kaman yaaya?,yanzun hamra ta baro parlor din fa"
Mummy safuura ta fadi da dan mamaki a muryarta.
"Alla ba kowa mummy" Ta sake fada tana dora tafin
hannunta saman goshinta,tsoro yana kai kawo a zuciyarta bayan wani hasashe da
zuciyarta tayi mata.
"Bari ina zuwa" Mummy ta fadi tana cike da
kokwanton abinda sabreen ta fada. Wayar ta ajiye,tana shirin miqewa daya daga
cikin yaran gidan ya shigo. Fuskarsa washe da madaukakiyar fara'a,hannunsa riqe
da rafas na dubu daya sabbi kar a miqe.
"Mummy.....baqonku ya tafi.......yace a baki haquri
sauri yake,lokacin tashin jirginsu yana dab da qwacewa,yana gaidaki da kyau,ya
mana kyakkyawar sallama,yau duka mu masu aikinki muna cikin alheri dumu
dumu,yace a baki wannan" Ya fada yana miqa mata envelope din dake daya
hannun nashi.
"Waya bawa yaran ya dawo dasu?" Ta tambayeshi tana
miqa hannunta.
"Gaskiya dasu naga sun fita......ba da mamarsu suka
tafi ba?" Batasan amsar da zata bashi ba,sai kawai tace dashi
"Madalla.....ka dubamin idan uba ya gama wanke
motarnan" Ta fada tana karbar envelope din.
Budeta tayi
a hankali,saiga sabbin dollars a ciki miqaqqu. Ido tadan fitar cikin mamaki,me
yasa sam mutumin nan bai iya qaramar kyauta ba?.
Komawa
tayi ta zauna tana ajiye envelope din a gefanta,mamaki yana cikata. Ya zaiyi da
yaran daya tafi dasu?,bai tsaya koda ganin mamansu ba?,bai kuma gaya mata zaije
dasu ba?,kada dai ya zamana sabreen yaji tayi ita ta amsheta bata sani ba,ko
kuma wasa takeyi da aurenta?. Kai tsaye ta dauki waya ta kira sabreen.
"Dawo ciki ina parlor" Bata ko iya amsawa mummy
ba,ta kashe kiran kawai ta miqa bata ko bi takan furar data ajjiye ba ta fice.
'"Zauna a nan" Mummy safuura tace da sabreen tana
nuna mata gefanta. Sam fuskarta ba alamun wasa a ciki.
"Sabreen" Ta kirata a tsanake.
"Na'am mummy" Ta amsa mata kowacce hanta dake
cikinta tana kadawa.
"Ki gayamin gaskiya,da iznin mijinki kikazo nan koba da
izininsa ba?" Shuru tayi tana juya maganar mummy,nadama da tsoro suna
cikata.
"Ki fadamin gaskiya,don kinfi kowa sanin halina bani da
sauqi,ba ruwana da wai kedin 'yar 'yar uwar mijina ce.....bata yadda za'ayi
baban yarannan yayi tattaki yazo har nan,ya kuma dauke yara ba tare da sanin
mahaifiyarsu ba" .
Wannan
abun wani baqon abune wajen sabreen
din,ballantana ita din da sam sam bata son tashin hankali ko kadan.
"Da saninsa,saidai baisan nan zamuzo ba,kuma har mu
kwana" Take ran mummy safuura ya baci sosai,ta zubawa sabreen idanu tana
jin kaman ta rufeta da duka.
"Me yasa?" Ta tambayeta a taqaice,irin taqaicewar
data nuna mata batason wani dogon sharhi ko dogewa.
"Mummy tsoro nakeji".
" Wani irin tsoro kuma?" Ta fada tana zare mata
idanu waje.
"Ciki mummy,inaso na huta......shi kuma haihuwa yakeso
akai akai".
"Haihuwarce ke bakiso saboda mamarki kuda yawa ta
haifa?". Kai ta girgiza saboda tasan magana mummy ta gaya mata a fakaice.
"Hutawa kawai nakeso na danyi mummy sab....."
"Gafara can dalla ki rufemin baki malama,"Amma ban
taba raina wayonki ba irin yau sabreen......ni'imar da Allah yayi miki kika
sanya qafa kike shureta?.......ashe baki da hankali ban sani ba?,idan muhammad
jadda beso haihuwa a dukiya da lafiyar da Allah ya bashi ba......ki gayamin me
zaiso?,sometimes mata ku kuke kirawa kanku kishiya wallahi" Idanu a waje ta daga kai tana duban mummy jin
ta ambaci kishiya.
"Yes....kishiya,ga abinda mijinki yakeso amma ke kullum
kina opposition party nasa.....me zai hana ya nemo wadda ra'ayinsu da komai
nasu yake daidai?......to wallahi bari na rantse miki,nima yau dinnan basai
gobe abbanku ya dawo ba,ba zaki sake kwanar mana a gida ba.......sauqinki daya
na sakaki a jirgi na maidaki gida a ranar yau,muddin kika sake ya dawo yaji
abinda ya faru saikin gwammace bakizo abuja ba....zan rufa miki asiri bazan
gaya masa ba,shine kawai abinda zan iyayi miki" Kuka sosai ya qwacewa sabreen,komai
ya dagule mata cikin lokaci qanqani. Kafin mummy ta nema musu ticket a gama
komai nononta duka ya ciko yanata damunta,alamun dake nuna mata tabbas su
fawwad sun tashi.
"Me zai basu idan sun farka suna jin yunwa?,ta yaya zai
iya kulawa dasu?" Tambayar data dinga yiwa kanta kenan,harta kasa jurewa
ta tambayi.mummy safuura.
Duk da
yadda tayi laushi lokaci guda ta bata tausayi amma saita jefa mata harara sanda
take hada mata sauran kayanta.
"Ke kika sani,ban sani ba" Ta fada cikin jin
haushi.
Haushin
kuma bai hanata ta hadawa sabreen din komai ba
"Idan kinje kin nutsu kinwa kanki fada na miki
bayani". Abinda kawai tace da ita kenan. Da kanta ta dauketa a motarta har
airport,bata kuma dawo ba sai data tabbatar da jirginsu ya tashi qarfe takwas
na daren ranar.
K'arfe
tara da minti ashirin da uku daidai na dare cave din airport ya saukesu a qofar
gidan muhammad fuad jadda. Karon farko da taji tana fargabar shiga gidan,abinda
bata taba ji ba tun bayan data amsa cikakkiyar sunan matar muhammad fu'ad
jadda.
Bata
sake fahimtar waye take aure ba......bata sake fahimtar girman matsayin da
Allah ya bata ba sai da suka tasamma shiga unguwar.
Tun a main
get na shigowa unguwar suka fara fama da tambayoyi na securities dake tsaron
kowanne gate na unguwar. Yawancin gurare saita laqo tayi magana sannan suyi
salute nata su dage musu su wuce,abinda bai taba faruwa ba kenan,don duk inda
zasu plate number din motocinsu ne kadai amsarsu,amma yau din sai da tasha
bayani kafin su samu su iso qofar gidan.
Gaba
daya masu gadin gidan mamaki ya kamasu ganin madam guda a cab. Cikin rawar jiki
da kuma girmamawa suka bude motan suka shiga fidda luggage dinsu zuwa cikin
gidan.
Tun a
veranda ta sallami nannies dinsu fawwaz,cikin fargaba ta dinga takawa zuwa
cikin gidan,tana jin kamar ta kirasu su tayata bawa fu'ad din haquri.
"Barka da dawowa......tun daxu nake zuba idanun ganin
fitowarki ai" Muryar ma'u ta sauka a kunnenta.
Dukka
dauriyarta ta tattaro ta sakar mata murmushi
"Yauwa ma'u......ashe kina ciki"
"Eh na shigo ne na zare socket na freezer dincan,kayan
ciki duka sun qanqare,kada mu tashi girki gobe qanqara ta hana ciro
komai......ya hanya?,dazun na dan jiyo qushin qushin din mutanen nawa".
Dan murmushin yaqe ta saki,ta san tana nufin su fauzan ne.
"Kinsan basa rabo da rigima idan sukaso,duka su ukun
saisun hade maka kai" Dariya ma'u tayi.
'"Ai inajin sai wajen gobe zamu hadu dasu,Allah ya huta
gajiya uwar dakina"
"To ma'u na gode".
"Ba'a buqatar komai ko?" Ma'u ta tambaya.
"Babu ma'u,bari na qarasa ciki" Da haka sukayi
sallama ta wuce parlor na biyu kai tsaye ya doshi hallway dinta.
166
Wata
matsananciyar kewar yaran takeji tana damunta,tanajin kaman ba awanni kadai ta
dauka bata gansu ba,ji take kaman shekara bata gansu ba,wani qaunarsu tana sake
taso mata kaman ba zata iya qara minti daya cikakke bata gansu ba.
Kai
tsaye dakinsu dake hallway din ta bude,bata gansu ba a ciki,hakan ya bata
tabbacin suna samanshi kenan.
Kaman ta
wuce dakinta amma sai taji ba zata iya ba,ta soma takawa zuwa saman nasa tana
qoqarin dake zuciyarta..
Ta kusa
minti uku bakin smart door din sannna ta matsa inda tayi scanning nata,kai
tsaye kuma ta bude kanta da kanta tana bata daman shiga.
Scenes
din watannin baya da suka shude ne suka shiga dawo kata kanta sanda ta hangeshi
zaune saman minotti sofa dinsa.......watannin da take a matsayin sabreen dinta
ta ainihin,wannan sabreen din wadda babu qaunar Muhammad fu'ad ko qanqani cikin
rai da zuciyarta.
Yana
zaune gabansa ya bude apple system dinshi har guda biyu,da alama kuma aiki
yakeyi sosai,koma ya jima a zaune a wajen,don ya saye idanunshi da farin glass
din nan nasa dake bada kalan light blue sama sama wani lokaci wanda ke taimaka
masa wajen zuqe hasken screen din.
Kansa ya
daga a nutse yana gyara zaman glass din a fuskarsa,lokaci guda kuma ya dauke
idonsa daga inda take a tsaye ya maida idanun kan screen din yana taba
Bluetooth din kunnensa
"Am hearing you" Daya fada shi ya alamta mata cewa
waya yake amsawa.
Duk da haka
bata fasa sallama ba don tasan ita din me laifi ce,ta taka a nutse tana shiga
ciki idanunta nakan wani irin gado dake wani shiyya daban na parlor din. Kaman
gado kama lilo haka aka tsarashi,amma idan kakalli cikinsa sosai zaka fahimci
gado ne na 'ya'yan gata wanda aka yi masa lafiyayyar shimfida me tsananin
taushi.
Gaban
gadon ta tsaya tana qare musu kallo,sai wani tausayinsu taji yana ratsata.
Kayan jikinsu na dazun yanzun ba sune a jikinsu ba,an canza musu su zuwa kayan
bacci masu taushi na jarirai farare qal dukka iri daya,hatta da socks na
qafansu dana hannunsu,sai suka sakeyi mata kyau,taga kaman sun qara girma akan
girman su na dazu.
Kewarsu
takeji sosai,don haka ta miqa hannu don fara daukan almustapha.
A qirjinta
ta sakashi,ta rungumeshi sosai tana shafa kan fawwaz. Ta jima a haka kafin ta
sanya fawad a kafada daya,fawwaz a daya kafadar,ta fara takawa a hankali tana
sauka dasu. Sai data kwantar dasu sannan ta dawo ta dauki fauzan.
"Kinci darajar ma'aiki daya hana raba uwa da
d'anta......banda hakan da daga yau ba zaki sake dora hannunki kan yara na
ba" Maganar daya fada kenan wadda ta sanyata tsayawa cak. Batayi tunanin
ya gama wayar da yakeyi ba,a sanyaye ta juyo zuciyarta na bugawa,saidai kafin
ta gama ajiye kallonta a kansa tuni har ya wuce dakinsa abinsa.
Jikinta a
mace ta gama shirin kwanciya tana juya maganarsa a ranta. Tayi fakare tana jira
taji ko zataji shigowarsa?,don ko dakin bata kulle ba,hakanan su fauzan duka
akan gadajensu ta kwantar dasu,saidai harta gama zaman jiransa bacci yayi awon
gaba da ita.
Koda ta
tashi har an gama sallar asuba. A gajiye ta miqe tana duba ko ina na dakin,ba
alamun ya kwana a dakin,a haka taja jiki zuwa toilet tayi wanka sannan ta hada
da alwala ta dawo ta bada farali.
Shiryawa
tayi cikin sassauqar doguwar riga data mata kyau ta fidda quruciyarta. Qarfe
bakwai da ashirin ta wuce zuwa kitchen da nufin shirya masa breakfast,don bata
da scheduled dinsa na satin gaba daya,amna ta tabbatar dole zai buqaci
breakfast din.
Kafin ta
kammala har ma'u ta gyara su fauzan gaba dayansu,sai ta shiga wuce daki kawai
ta gyara jikinta.
Kwalliya
tayi sosai data dace da safiyar,ta wadata jikinta da sassanyan qamshin nan da
tasan yana masifar so. Bata ma dauki su fauzan ba kai tsaye ta wuce zuwa
samanshi.
Koda ta
samu daman shiga parlor din bata wani ji motsinsa ba,don haka ta wuce zuwa
master bedroom dinsa. Tun a nan ta fahimci tuni ya fita,don ga alamu nan sun
nuna,comb dinsa da towel dinsa,da qaramin cup da yasha ruwan dumi duka saman
mirror. Zama tayi gefan gadon tana maida numfashi,hakan yana nufin yayi fushi
sosai da ita kenan?.
Wayarta ta
bude ta soma kiran numbers dinsa,saidai kowacce gaya mata akeyi a kashe
take,dole ta haqura da neman nasa ta sauko qasa saboda kukansu fawwaz da yayi
mata maraaba.
Tana
shayar da yaran amma duka hankalinta yana kan tunaninsa da tunanin abinda ya
faru. Duk hankalinta a jagule yake gaba daya,ta dinga gwada kiran number dinsa
amma bata shiga,tun tana sanya rai harta haqura ta daina neman nasa,sai gajeran
saqo data tura masa,wanda shima har magariba tayi bata samu amsa ba.
Magariba
ta wuce,isha'i ta shigo itama ta wuce,shuru ba shi ba wayarsa ba dalilinsa. A
haka ta samu su fauzan dukkaninsu sukayi bacci,don dama idan sun jima sukai
bayan ishai'i,idan kuma suka kwanta matuqar sun tashi to yunwa ko qishirwa ya
tashesu,basa farkawa yawanci da safen ma,sai sukai bakwai da rabi har takwas
suna bacci abinsu.
Baccinsu
ya sake sakata ta dan qar samun nutsuwa. Wannan karon koda ta kirashi wayar
yana shiga,amma haka ta qaraci b'urarinta ta katse bai amsa ba.
Dole ta
ajiye komai gefe,ta qarfafa jikinta ta shiga wanka. Saidai duk wata laka ta
jikinta an zare mata ita. Batajin sam sam zata iya ci gaba da karbar wannan
hukuncin nasa,batasan haka ya iya hukuncin 'yar shariya me ciwo ba sai yanzu.
Zaifi mata sauqi ya kulata,yayi mata fada ma,idan ta kama ma ya zaneta ko ya
zageta zaifi sauqi.
To yau
kam ma duk wani shirinta bata samu ganin shigowars gidan bama kwata kwata. Har
sha daya na dare idanunta biyu,batasan kuka ta fara yi ba saida taji damshi
saman fuskar fawwaz dake shan mama wanda ya tashi a sannan,daga qarshe ma tana
tsaka da bawa fauzan mama bacci yayi gaba da ita,wanda a sannan sha biyu saura
na dare.
Washegari
taga alamun gidan ya kaana,saidai duk saurint na ta sameshi bata iskeshi ba.
Wunin ranar gaba daya dauriyarta a ya qare,wuni tayi a daki ma'au nata
cigiyarsu,don batason ta fito ma'u taga canji a fuskarta ta zargi wani abu.
Ranar ta
rantse ba zatayi bacci ba sai taga shigowarsa,koda zata kwana ne a zaune,don
haka koda goma na dare yayi ta tabbatar yaran sunyi bacci,goma da rabi ta sauya
kayan bacci.
Lafiyayyun
kayan barci ne masu wani irin sulbi da yauqi,wadanda ta siya a HUGUMA CLOSET da
sukazo kai tsaye daga Dubai. Suna da wani irin bin jiki da daukan
hankali,lingerie ne sosai na isassun mata.
Curling
iron ta saka ta zauna ta yiwa gashinta wani irin nannadewa kaman
macaroni,sannna ta tattarashi zuwa left side na kafadarta gaba dayanshi. Daga
daya side din tadan tareshi da mabanbanta shapes na hair clips. Tattausan lips
nata ta wadata da lips gloss daya qara masa kyau da sheqi,ta wadata kowanne
part na jikinta da kalar turaren da musamman aka yishi saboda gurin,wannan
turarrukan ta sansu da amfaninsu ne a wajen mummy sultana mummyn twins BATOUL
DA BENAZEER(Gudun k'addara).
K'awace ta
mummy safuura,ranar da suka isa abuja tazo mata a gaggauce da nata twins din
din batoul da benazeer,wadanda aketa shirye shiryen bikinsu dukka su biyun,duk
da bikin saura watanni shida,amma tsananin gata idan kaga yadda aketa shiri
saika dauja gobe ne ko jibi.
Ita kanta
ko yaya ta motsa qamshin jikinta burgeta yakeyi,ta tsaya gaban madubi taga
yadda ta ajiye wani sassanyan kyau,ta gamsu da kanta da kanta,don haka saita
tofe su fauzan da addu'a ta kuma wuce zuwa parlor na biyu.
Ba sabonta
bane kallo,amma yau da kanta ta kunna Tv din,ta kuma kamo tashar tumbin giwa
ind suke wani hausa series.
Rabi da
rabin hankalinta yana kan wayarta,batasan adadin saqonnin data aike masa a
kwanaki ukunnan ba,amma ko qwaya daya tal bata samu amsarsa ba. A baya ta shiga
tsanani na rayuwa da barazana kala kala,amma bata taba jin tsananin da yakai
mata wannan wahala ba. Bata taba jin nutsuwa da lafiyar zuciyarta tana mata
barazana ba irin na wanann lokacin. A wannan lokacinne take tabbatar da ma'anar
TASHIN HANKALI da kuma rashin sukuni da gasken gaske.
Ba fahimta
take cancan ba,saita yanke kiran fannah kawai suyi hira.
A qalla sun
kusa awa daya da fannah din,har sai da taji farouq ya iso kusa sosai,tana jinsa
yana saka fannah din dariyar da bata shirya ba,dole ta yanke kiran. A gogo ta
kalla,taji kewar nata mijin yana saukar mata,banda wannan matsalar data faru a
tsakaninsu da tuni zuwa yanzun shima yana tare da ita,ta sauke idanunta tare da
ajiyar zuciya zuwa saman Tv din,daidai sannan ya murxa handle din qofar parlor
din ya shigo da sallama muryarsa can qasa,yanajin kowacce gaba ta jikinsa a
mugun jigace.
Idanunsa
da sukayi laushi qwarai su ya fara zube mata,tayi masa wani irin fitinannen
kyau,ya sauke dubansa kan gashinta da yasa kwalliya da wani irin salo,salon da
hatta yanayin zamanta saman kujera yau din na musamman ne.....
Cikin
wani irin hanzari ya dauke kanshi daga dubanta sanda ta daga risunannun
idanunta zuwa kanshi. Yadda ya dauke kan baima ko nuna ya ganta ba ya mata wani
irin ciwo,duk da haka ta daure tace masa.
"Sannu da zuwa".
"Yauwa " Ya amsa still ba tare daya kalli sashenta
yana takawa zuwa hallway din.
Idanunsa ya
lumshe,yana jin wani abu yana harbawa zuwa kowanne sashe na jikinsa. Ta masa
kyau iyaka,ta fusgi hankalinsa qwarai,saidai har yanzu yana jin tasirin
fushinnan da yakeyi da ita. Ta dauka masa yara sun fita daga gidan daya
killacesu ba tare da yasan adadin nisan da zatayi ba,ta dauka masa yara ba wasu
cikakkun masu tsaronsu......uwa uba ta taba masa martabar igiyar
aurensa......tayi nisan da bai kamata ace ta yishi ba tare da muharraminta
ba.....ba kuma tare da izininshi ba.
Idan har
ya sake mata haka da yawa gaba yana da guarantee din me zaya faru?. Iyali suke
tarawa shida ita,fata yake kuma su gina iyalin da kowa zasu zame masa abun
alfahari. Babban abun dake mintsinar zuciyarsa shine......tsoronsa daya karanta
cikin idanunta tun wancan ranar,to meye yake mata a shimfidarsu da zai sanyata
gudunsa har irin haka?.
Ya
sani......duk duniya ita zata fadi wayeshi a wannan fannin.......tafi kowa
alfahari dashi........wani irin yanayine da take ji dashi cikin rayuwar
aurensu,amma dare daya saita nema sauya hali?.
Alqawari
ne ya yiwa kansa tun first night nasu......bazai sake kasancewa da ita ba ta
wani yanayi na daban har sai da shauqinta da cikakkiyar amincewarta,koda kuwa
son kusancinsa da ita zai masa mene ne.......bare a yanzun da yake cikin fushi
da ita.......banda wannan kallon daya mata na yanzu da yake shirin wargaza masa
lissafin da baiyi niyyar wareshi a nan kusa ba.
Dakinta ya
wuce kai tsaye,kaman yadda ya saba shiga ya gansu suna bacci batasan ma shigar
tasa ba bare fitowarsa. Ya qarasa gaban gadon,ya riqe yatsun yaran
idanunsa a kansu. Wani sanyi yaji
zuciyarsa tana yi.......da gaske da ake cewa yara sanyin idaniyar iyayensu ne.
Yana iya
jinta sanda ta tura qofar dakin ta shigo yana tsaka da musu addu'a,bai waiwayo
ba,bai kuma tsaya da abinda yake ba har ya gama tofesu da addu'ar sannan ya
juya a hankali da zummar fita a dakin.
Dab da
zai isa bakin qofar tasha gabansa,ta shiga ta tsakanin hannayensa ta tsaya a
tsakiyarsa tana lalubar qwayar idanunsa ta saka nata a ciki.
Narkakkun
idanun nan nata da suke kasheshi......narkakkaun idanun nan nata da suke zare
masa dukka wata laka tasa,su kuma kashe wutar fushi dake ruruwa a
zuciyarsa,idanun da har yau wani haske da qyalli suke kasa kaman ranar farko
daya fara ganinsu.
"Zan wuce a gajiye nake.....bacci nakeji". Ya fada
da wata maqalalliyar murya daga can qasan maqoshinsa,muryar da takeso lallai
saita tona asirin dake danqare a zuciyarsa da gangar jikinsa.
Qwalla sosai
ta cika fararen idanunta,ta koma masa kaman wata yar shekara goma saboda yadda
ta maqale.kafada.
"Zakaje ka kwanta kayi bacci ko?,sabreen ita kuma ta
mutu?". Sai kawai ta fashe masa da kuka.
Cije
labbansa yayi,yana jin yadda kukanta ke huda masa sassan jiki yanason
kassarashi da kassara qarfin qwanjinsa dana zuciyarsa. Ya dake sasai yana
fadin.
"Nifa ba kuka na tambaya ba,hanya nakeso a
bani......zancan sabreen ta mutu kuma ai bai taso ba.....ki bani hanya
please" Ya fada a dake yana basarwa,yana fata ta matsa ta bashi hanyar
kafin ya qarasa karyewa daga hawayen dake fita a fuskarta.
_Wato dai da gaske kai ragon namiji ne indai akan sabreen
ne?,zamu gani,zaka iya daurewa?😂😂_
167
"Hamma" Ta sake kiransa muryarta a karye da sautin kuka.
"Am really sorry hamma......Allah bazan sake ba"
Tun daga tsakiyar kansa har tafin qafarsa yaji kiran sunanshi da tayi,zuciyarsa
tayi sanyi amma tana gaya masa ba yanzun ba......da sauran karatun.
"Naji na haqura.....matsa na wuce" Ya sake fadi
yana kuma tsare gida. Fararen idanunta da suka dan surka kadan saboda kuka ta
daga ta kalleshi,shima idanunsa suna kanta,amma koda ta kalleshin sai ya dauke
kansa,saboda tsigar jikinsa ya da yaji gaba daya ta tashi.
"Hamma baka haqura ba....."
"Goyaki kikeso nayi?,shi zai tabbatar miki na haqura ko
kuwa yaya?". Yadda yayi maganar da wani basarwa sai ya karya mata
gwiwa,gaba daya sai taji kaman ya tozartata da yadda yake qoqarin tankwabe
rarrashin da take masa.
"Bani hanya please" Ya sake fada yana kuma hade
gira.
A hankali
ta janye jikinta ta bashi waje,ya taka hankali kwance kaman wani abu be
tsikareshi ba ya fice a dakin.
Sulalewa
tayi a wajen,sai wani sabon kukan ya
tsinke mata. Tsoro taji yana shigarta,tsoron kada ya zamana fu'ad ya fara
juyawa daga muhammad din data sani......zuwan mazajen yau da mata ke complain a
kansu. Idan haka ta kasance a kanta bata jin zatakai labari.....don ta
ta'allaqa dukka burinta da fatanta a kansa,ta karkatar da akalar rayuwarta a
kansa,ta saka buri me yawa kuma akan nasa.
Tas
taci kukanta ta godewa Allah,sannan ta miqe tana qarfafawa kanta gwiwa. Ta
shirya abincin duka cikin wani kwando na daban ta haura masa sama dashi. Ba
kowa a parlor din,tafi sanya ran wanka ya shiga,don haka ta jera komai tsaf
saman dining ta wuce bedroom dinsa.
Kai
tsaye ta murza handle na toilet din ta shige abinta gaba gadi. Cikin Jacuzzi ta
hangoshi,ya sakarwa kansa ruwa wanda yake wanka duk kumfar daya sabawa jikinsa.
Idanunta ta Maida ga bathtub din data cika masa d ruwa da kuma sassanyan
turaren wanka,ba alamar ya taba ruwan ma bare akai maganar yayi wanka
dashi,saita hadiye abinda ya taso mata ta nufi jazucci din kai tsaye.
Zuge
qofar tayi,ta taka a nutse tana shigewa ciki. Ya ganta sarai amma bai waiwaya
ba,yaso ace sanda bai shiga azumin fushi da ita ba ta kawo kanta a irin wannan
lokacin,lallai da ya samu ganima.
Yana
jinta ta gama tsokane tsokanenta bai nuna yasan tana ciki ba,ya gama ya nannade
jikinsa da towel ya fito. Tana tsaye a nan kamar wata hoto har yabar toilet
din,ranta taji ya soma baci,to amma ya zatayi?,duk ita ta jawo,ta tabbatar
fushinsa lallai ba abu bane me dadi,tunda ya gwada mata ta gani.
Ko data
zuba masa abinci ma cewa yayi ya qoshi baya buqata,ta san halinsa koda yana
buqatar abincin ma ba lallai yaci,zaice bazaici abinci bane late,don haka ta
shiga kitchen ta hada masa fruit salad me kyau da nau'un fruit din da basu da
matsala ga lafiya da dare,a cisu kuma a kwanta.
"Ajiye a nan xanci" Ya fada kawai yana duba wasu
file. Ajiye masan tayi,ta kuma sauka qasa tayi shirin bacci.
Still
cikin wasu red night gown ta shirya,ta saki gashinta kafadunta yanzun bayan ta
tajeshi daga curling nashi da tayi a dazu.
Sanda
take kawo yaran zuwa gadonsa dake gefan dakin,yana kwance cikin duvet a
qudundune amma tun shigowar farko sassanyan qamshinta ya ruskeshi har inda yake
din.
Wata
wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa,bai taba kawowa zai iya jure
wadannan kwanakin ba.......bai taba zaton yana da haquri a kanta har haka ba
sai yanxu.
A nutse
ta gama komai,ta sake musu addu'a,ta shiga toilet nashi tayi brush sannan ta
hauro gadon tana rage hasken qwayayen dakin.
Ya jita
kusa dashi sosai,amma bai taba kawo zatayi abinda tayin ba a yanzun. Wata
kyakkyawar runguma tayi masa ta baya,cikakken dukiyar fulaninta da shayarwa
tasa y qara cika ya tokare a bayansa.
Saura
kadan numfashinsa yayi qaura daga gangar jikinsa,wasu irin kaifafan kibiyoyi ta
sakar masa wanda suka ratsa sassan jikinsa d wani irin matuqar sauri suka aike
masa da wani nannauyan yanayi daya sakashi takure jikinsa ba tare daya shirya
hakan ba.
Matseshi
tsam tayi ta baya,tana bashi wata kyakkyawar runguma. Har cikin jininsa sai da
yaji yadda dumin jikinta da tudun dukiyar fulaninta ya zauna sosai saman fatar
bayansa.
Sosai ya
riqe numfashinsa don hana kansa jin abinda yakeji yana masa yawo a jiki,amma
yadda zuciyarsa ke bugawa da sauti ya sanya ta kasa aiwatar da hakan,ya kamo
numfashin da qyar sannan ya tattaro juriyarsa yana dan zamewa.
"Stay away please" Ya fada da wata irin
kasalalliyar murya.
Maganan
tashi tazo mata a bazata,tsam tayi da ranta tana dakatawa da komai,tana jjn
yadda zuciyarta ke bugawa da sauri,tana kuma jin yadda itama a yau din take jin
ta dokanta dashi.
"Hamma" Ta furta a sanyaye. Qarasa janye jikinsa
yayi,sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana dubanta
"I'm not in the mode,im feeling off" Ya furta
muryarsa tana qara yin can qasan maqoshinsa. Idanunta da suka fara lumsheea ta
ware tana kallonsa. Yau ita jadda yake cewa he's off?,off for what?.
Tana tsaka
da wannan tunanin ta ganshi ya dauki babban blanket nasu da pillow ya aza saman
sofa ya kwanta abinsa ya lulluba har saman kansa.
Baki ta
sake kawai tana kallonsa,abun gaba daya ya bata mamaki,yau ita abben su fauzan
din ke yakicewa?,ita din yake dodging?. Wani matsewa zuciyarta dake qirjinta
tayi,sannan a hankali wani hawaye me dumi taji kawai ya sauko mata saman
fuskarta.
Da
hanzari ta sauko daga saman gadon kai tsaye,ko bedroom slippers dinta batayi ta
kai ba ta soma fita a dakin da sassarfa.
Komai da
takeyi yana jinta,bai kuma motsa ba har sai da yaji fitarta,kunne ya kasa
sosai,kusan mintuna biyar sannan ya yaye duvet din ya sauka a hankali yana fita
a dakin.
Bata duka
bedrooms din hakanan bata parlor din,abinda ya bashi tabbacin sauka tayi gaba
daya daga sassan nasa.
Wani
qaramin murmushi ya saki,qasan ranshi yana fadin ashe babu dadi. Maida qofar
parlor din yayi ya kulle abinsa ya koma bedroom din duk da yadda zuciyarsa ke
jin matsananciyar kewarta.
Yaran gaba
daya ya sauke daga nasu gadon,ya maidosu kan gadon nashi,ya bajesu ya shige
cikinsu abinsa ya kwanta sosai yana sakin ajiyar zuciya,yana kuma jin kusancin
dake tsakaninsa da yaran.
Kwata kwata bacci qaurace mata yayi,batajin zata iya jurar wannan abun.
Yayi mata komai zata jure amma banda nesanta kanshi da ita,ita kanta cikin
tsananin buqatarsa take,don ya riga ya horata ta wannan fannin ya kuma maidata
irinsa. Abu daya ne ya sanyata ta guje masa stitches nata na CS dinta da take
ganin kamar zai farke.
A haka
bacci barawo ya lallabo ya saceta,cike da fata da sanya ran zai shigo har dakin
ya nemeta,ko don saboda yaran ma. Sam baccin baiyi wani tsaho ba ta farka
firgigit,ta shiga buda idanunta sosai tana sanya ran ganinsa ko yaran ko alamun
ya shigo ya fita,amma bataga komai a ciki ba.
Ranta taji
ya bacu,zuciyarta ta quntata,sai ta shiga toilet tayi fitsari ta daura
alwala,ta dawo tayi nafila raka'a shida. Tana saman abun sallan tana
addu'o'inta wani baccin ya sake waftarta,wanda shine bacci mafi tsaho da
tayi,don bata tashi farkawa ba sai da akayi kiran farko.
Yanzunma
bataga alamun ya shigo ba,kawai sai wata qwalla ta cika mata idanunta. Dama
yake da ciwo kayi abandoning mutum?. Yaran sun tsaye mata a rai,tasan zai
wahala ace duka tsahon daren ba wanda ya nemi nono,kawai saita sauka daga kan
abun sallar ta soma takawa a hankali ta fice a dakin.
A
Hankali ta bude qofar bedroom din,mamaki da haushi ya cikata fam kaman zata
fashe. Wato shi ya sanya yaranshi a gaba abinsa suna sheqa baccinsu ko a
jikinsu?,ita gata nan wahalalliya ta hana kanta da kanta sukuni duka saboda
yaran da nasa tunanin,kawai saita saki kuka me sauti,kukan daya tasheshi ya
kuma saka yaran motsawa,daya bayan daya suka farkawa tarwai abinsu,sai kuma a
sannan suka fara neman abincinsu ta hanyar fara cilla qafafu suna son fara
sakin kuka.
"Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma amatana wa
ilaihinnushur" Ya fada sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana
dubanta inda ta zauna gaban gadon tana musu kuka.
"Me akayi miki?" Ya tambayeta hankali
kwance,tambayar data sakata sake masa hararar da batasan tayi ba,sai ya dauke
kansa kawai yana sauka daga gadon a hankali ya wuce toilet don daura alwala
yayi raka'atanil fajr kada ta subuce masa. Rigima ce fal idanunta yake
hanga,shi kuma indai wannan rigimar ce a shirye yake da ita,ya fita jinta ma.
Ko kafin
ya gama alwala ya fito dakin duka ya karade da kukansu su ukun,ga mamar tasu
zaune a gabansu itama tana hawaye sosai.
Tausayi da
dariya abun ya bashi duka lokaci daya,ya dake yana zura jallabiyyar jikinsa da
sauri bayan ya tsane ruwan gargasarsa.
"Baki gani kuka suke kika zauna kika sakasu a gaba kina
kallonsu?". Kaman jira take yayi maganar ta miqe tana nufar qofar,kuka
takeyi sosai,sai ya qarasa yasha gabanta yana duban idanunta.
"Hamma raino kawai na iya dama?".
"Ni me nace miki ne Sabreen?,me kikeso kuma
ehmmm?" Yayi maganar da alama shima ranshi ya fara baci. Ta kalleshi sosai
ta kuma fahimci kukan yaranshi ke dagula lissafinsa,kenan yafi jin kukansu a
ransa sama da nata?,wannan ya sanya ta soma neman hanyan fita kawai.
Hannu daya
ya sanya ya jawota baya kafin ya saka hannuwansa duka biyun ya dauketa cak yana
lullubeta a qirjinsa yana jin yadda sassanyan qamshinta ke bulale masa
hanci,bai kuma direta ko ina ba sai tsakiyar gadon. Haurawa saman gadon yayi ya
dauko farouq da nasa kukan yafi na kowa ya aza mata saman cinya,ya kuma tsare
ta da idanun nasa. Zuwa yanzu qwayar idanun nan sun kuma na muhammadun sosai,me
babban suna kuma shugaban kamfanonin jadda.
168
"Feed
him" Ya bata umarni nakai tsaye da husky voice dinsa. Duk wani annurin
fuskarsa yana daukewa,kukan yaran yana jinsa kamar d'igar ruwan dalma saman
tsokar zuciyarsa.
Umarnin
ya zarce har cikin kwanyarta,saita soma nuqu nuqun fidda maman. Gani yake bata
masa lokaci takeyi shida yaran gaba daya,don haka ya buda hannayenta kawai ya
balle duka button din rigar tata ya zameta daga kafadunta.
Cikakkun
dukiyar fulaninta da suke a tsaye,sun cika sosai irin na masu shayarwa ya
bayyana,abinda yayi nasarar karya alwalar da yaketa faman tattalawa kenan.
Hannunsa ya miqa cikin dakiya ya dagoma fauzan abincinsa,nan da nan ya kama,sannan ya saki ya koma wajen su
fawwaz da kukan nasu ya sassauta.
Bai nuna
yaga hawayen da take zubarwa ba sam,yaci gaba da bata yaran suna sha,har sai
kowannensu ya qoshi sannan ya janyeshi. Suna sha yana karbarsu daya bayan daya
yana sauka dasu. Batasan inda yake kaisu ba,amma haka yake dawowa hannunsa babu
su.v
Almustapha ne qarshe,don kusan ya fisu haquri,sai daya tabbatar shima ya
kama sannan ya tashi yayi raka'atanil fajr din. Sanda ya idar ya gama sha
shima,ya miqa mata hannuwansa yana kallon fuskarta da tayi ja saboda kukan da
tayi. Miqa masa shi tayi shima,sai ya karbeshi ya kuma ajiyeshi a gefe.
Hannunsa yasa yana maida mata rigarta yadda take duk da qoqarin maidawa da
takeyi da kanta.
"Ka barmin abata zan mayar" Ta fadi cikin rawar
murya. Wani kallo ya jefeta dashi.
"Ina ruwanki?,wannan din ba jikinki bane.....jikin
muhammad jadda ne.....naki jikin gashinan" Ya fadi yana nuna kansa da
kansa da yatsa.
Wani abu me
sanyi taji ya sauka a zuciyarta,har sai data lumshe idonta kadan,ya kammala
maida mata ita tsaf,ya saka hannu ya dauki almustapha fawad yana tafiya qofa.
"Kiyi alwala kiyi sallah.....zanje sallah na dawo"
Ya qarasa maganar yana qarasa fita. Tsaiwa yayi yayi locking qofar da new
password ta yadda ba zata iya fita ba,sannan ya gangara ya miqawa salwa fawad
yace a gyarashi shima kaman sauran 'yan uwansa sannan ya wuce masallacin.
A sanyaye
tayi alwalar tayi sallar,tayi addu'o'inta kaman yadda ta saba. Idanunta sun
mata nauyi sosai,kuma da alama rashin bacci ne isashe na kwanakin,don haka sai
kawai ta koma toilet ta hada ruwa me dumi sosai tayi wanka,ta kuma nade kanta
da jikinta da towels dinsa wadanda qamshin jikinsa ya kamasu sosai. Idanu kawai
take lumshewa,wanxuwar towel din me manne da qamshinsa sai ya xame mata kamar
shine nannade a jikinta. Wani irin azababben shauqinsa takeji ta kowacce
fuska,tana jin kaman takai kanta gareshi ta roqeshi.
"Wanne irin abune wannan?" Ta tambayi kanta da
kanta sanda tayi zaune saman stool a gaban madubi. Hirarta da fannah ta dawo
mata fes a kanta.
"Wata macen sai ta fara haihuwa take zama cikakkiyar
mace me cikakkiyar buqatar namiji..sai a sannan komai nata yake qosawa yake
kuma bunqasa" Dauke hawayenta tayi da yatsanta,tana raya cewa wataqila ita
din tana cikin irin wadannan matanne.
"Kamar ke kadai keda idanun kuka?,bakisan ni ya kamata
na zauna nayita sheqa kuka ba?" Taji maganar sa daga gefanta wanda harga
Allah batasan da shigowarsa ba.
"Taso kizo nan" Ya bata umarni kansa tsaye yana
nuna mata daura dashi.
Da kallo
yake binta sanda take takowa inda yake. Duk da yake shi ba ma'abocin kallon
mata bane amma yayi imanin samun takun isa a wajen diya mace irin na sabreen
dinsa zaiyi wahala,kaman yadda qirar jikinta tasha banban data dubban mata,don
ko a yanzun da take tafiyar saika rantse ba wani yaro daya zauna a cikin ta
tsahon wata tara,sai cika da komai nata ya sakeyi. Duk da yanayin halitta ma ya
lura macace me gyara sosai(idan kina da kyau ki qara da wanka,karki yadda ki
zauna a wargaje waike jego kike ko kin tara yara sun miki yawa,xaki banu zaki
lalace fes wallahi).
"Sabrrrr.......don ni bani da gata?,don ni bani da
wanda zan gayawa damuwata......don ni namiji ne bani da idon kuka?" Yafada
da wata raunanniyar muryar data tilasta mata daga idanu ta dubeshi. Wani irin
tausayinsa daya tsarga mata ya sanya hawaye taruwa a idanunta. Miqewa yayi,da
alama baiso maganar ma tayi tsayi can.
"Alqawari nayi,tun a wancan daren bazan taba koda
yatsarki ba muddin zamanmu sai kina cikin yanayin".
" Ina ciki wallahi" Ta furta da wani irin sauri
bayan ta yiwa kanta kyakkyawar masauki a qirjinsa tana cukuikuyeshi. Dariya ta
kusa kubce masa duk da yadda sanyin hawayenta daya sauka budadden qirjinsa da
wuyan rigan ya zama V shape ya taba zuciyasa sosai.
"I can't live without you.....You're my
everything,without you,I'm lost,i need you now and forever,you're irreplaceable
hamma........ka yafemin hamma.....bazan sake ba hamma......na tuba" Ta
qarasa fadi tana sakin masa wani kukan kisisina me tsayawa a zuciya.
Hannunsa
har rawa yake sanda ya riqeta,ya sake mata wani tsatstsauran riqo yana sanyata
tsakiyar qirjinsa yayi mata kyakkyawar runguma. Kasa magana yayi,kasa cewa
komai yayi,kaman yadda shirunsa ya isheta amsa ta hanyar bugun da zuciyarsa
takeyi.
Ta yarda ta
kuma amince tabbas taso ta zalunceshi,jikinta ya sake sanyi da kalar soyayyar
da yakeyi mata.
"Dukka wannan bugawar da Xuciyar nan takeyi tana yine
saboda ke.....ke kadai sabreen,ban taba koda sha'awar daga kai na kalli wata
macen ba bare har naji ta fusgi hankalina na ko ta dace da rayuwata ba
bayanke".
"Nayi maka alqawarin xame maka aljannar duniya koda
shine xai kawo qarshen bugun zuciya dana numfashina" Lafaxinta na qarshe
kenan daya iya tantancewa,ya dauketa cak ya ajiyeta inda yafi wayo sannan ya
fara rabata da towel din jikinta.
Wata irin
sassanyan safiya ta bashi.....wata irin safiya me tsayawa a Xuciyar masoya.....
"Can i have you for breakfast today?" Ya fada da
wata narkakkiyar murya dake wani irin rawa.
Yana dire
tambayar ta tabbatar masa da abinda yake buri,abinda yake fata yake kuma
tsananin buqata. Shi da ita kowannensu da zafinsa yazo,shi da itan gaba daya ba
wanda bai gigita dan uwansa ba da wani irin zazzafan salo daya sake tabbatar
masa itace DUNIYARSA shima shine DUNIYARTA. Gaba daya ta canza masa,ta kuma
caza masa kwanya,yana jin tamkar yaune ranar farko a rayuwarsa daya fara
kasancewa da ita. Ta gigita duk wani tunani nasa......ya sake fahimtar cewa
lallai macen datasan kanta haihuwa ko shekaru basa saka kimarta zagwanyewa,a
yanzunne ya sake gamsuwa da lallai sabreen dinshi ta zama cikakkiyar mace.
Tana
kwance luf saman qirjinsa sanda komai ya kammala,kalar alqawuran da yake
zayyano mata ya sanyata sakin wani sassanyan kuka,nan ya sake lalacewa wajen
lallashin kayarshi.
Sanda taga lokaci bayan ta kalli agogo batasan sanda ta wantsalo daga
gado ba ta nufi bandaki tana fadin
"Su fawad" Miqewa yayi ya bita toilet din da
towels dinsu.
"Ina da nufina dana daukarwa su fawad nannies,kwanan
nan kuma zan qara guda daya kowacce taji da guda daya,lokaci na lokaci na
ne.....banaso nayi sharing nasa da kowa"
Yaso ya bata dariya,saboda yadda yayi maganar da gaske.
"Ayi musu afuwa naje na dubasu,don zuwa yanzun ya
kamata ace an dubasun" Bai amsa mata ba ya turata cikin bathtub din kawai
yana sake maqale mata.
Tsaf ta
shirya cikin atamfa riga da zani,shigar data jima bata yita ba. Shi kansa yau
din saita masa kyau sosai,ta maqala wasu sabbin design na earrings na gold
marasa nauyi a kunnenta da siriryar sarqarsu saman dogon wuyanta,abinda ya sake
mata kyau kenan.
Ido ya
saka da baki yana kallon kyakkyawan
dokin wuyanta,tunda aka fidda design din shi sai yau yaga kyansa saman
wuyanta,ya tako a hankali ya sumbaci wuyanta nata,abinda ya dauke mata wuta na
sakanni.
"An bani izinin sauka na dubasu?".
"An baki duniyata" Ya fada cikin kulawa da shauqin
qauna.
Basa
dakinsu koda ta duba,don haka saita yanke duba parlor dinsu.
"Salwa.....Allah yasa ba rigima suke miki b......"
Bata samu daman qarasa fadin abinda yake bakinta ba komai ya maqale mata yadda ta zuba mata idanu itama haka ta zuba
mata,cikin wani irin kallon me cike da matsanancin mamaki da gigita.
Maamah ce
zaune saman wheelchair dinta,an dora mata farouq fawwaz da almustapha fawad
saman cinyar tata. Yatsanta cikin nasu yatsan tana tabawa a hankali,duk da
bacci sukeyi amma idanunta yana kansu gaba daya.
"Ba wata rigima hajiya......tun dazun suna hannun
kakarsu,har sukayi bacci.......fauzan ne ma yaqi zama gashican an goyashi"
Salwa ta bawa sabreen amsa.
Maamah ce
ta fara cire idanunta akan sabreen din sannan itama sabreen din ta dauke
kallonta daga kanta cikin matuqar mamaki jikinta yayi wani mahaukacin sanyi.
"Tun yaushe tazo?" Ta tambayi salwa da harshen
larabci data tabbatar maamah bataji murya qasa qasa
"Mintuna kusan arbain kenan,a rubutunta tambayeni ma
haka kuke barin yaran a qasa gurinmu kuna sama?" Salwa ta fadi tana
murmushi. Ta fada ne saboda yadda taga maamah din tana qarewa yaran
kallo,kallon dake nuna zallar qauna da shauqi da kuma kulawa. Tunda tazo
idanunta yana kansu,bata kuma saukesu ba ko sau daya.
Kai sabreen ta jinjina,abun yana sake fadada mamakinta.
"A samo mata abinci da abinsha" Ta fadi tana maida
hankalinta kan maamah tana takawa cike da qwarin gwiwa.
Ganin
maamah a gidan nata ba abu bane me sauqi,ba wani abu bane da zatayi zaton zai
kasance haka a nan kurkusa ba.
Gabanta ta
qarasa ta kuma tsugunna tana fadin
"Sannu da zuwa maamah......barka rana,ya jikin?,Allah
ya qara lafiya". Wani kallo ta dago ta dan watsa mata. Da tana da iko zata
tambayeta ne uban me sukeyi a sama kusan sama da awa daya suka bar kula da yara
hannun masu aiki?,haka sukeyi kenan cikin gidan?,shi ya ajiye fita office ita
ta saki ragamar gida kamar su kadaine suka rage a duniyar?,kaman ba wani abu me
rai da yake rayuwa a duniyar saisu?.
Saidai ba
wannan damar,sai dai kallon tuhumar data gabatar mata tana jin ya kawo mata dan
sassauci a zuciyarta. Sarai taga kalar kallon,to amma ita kanta tasan yasha
banban da kallon qiyayya da takeyi mata,wannan din akwai sassauci qwarai a
cikinsa,duk da cewa akwai alamu na jin haushi a cikinsa da batasan haushin meye
ba?,sai daga baya zuciyarta ke raya mata na barin yaranne a hannunsu salwa?.
Saida
salwa ta kawo komai sabreen ta jera mata a gabanta,sannan ta umarceta ta karbi
yaran ta bata abincin taci,amma qememe taqi bayar da yaran.
Sanda
fu'ad ya sauko ana wannan drama din,don sabreen ta haqura ta koma gefe tana
kallon ikon Allah,yadda ta tattara dukka hankalinta akan yaran,kamar bata da
wani sauran abu me muhimmanci a duniyarta sama dasu,duk kuwa da cewa ita din
daga wannan kallon guda biyu bata sake samun wani kallon ba.
Shima nasa
kallon aka aje masa,sannan ta kauda kanta bakinta yana motsawa kaman meson yin
magana amma kuma ba dama. Mutuwar tsayen da yayi yafi na sabreen,don har sai da
maamah din ta sake daga idanu ta kalleshi tana masa nuni da ya zauna ya tsaya
mata a kai.
Kaman yadda
sabreen tayi mata shima still hakan,saidai shi dinma ba wani muhimmanci ta
bashi ba. Ganinta riqe da yaransu kuma gudan jininsu cikin hannuwanta da wata
qauna data gaza boyuwa daga cikin qwayar idanunta yafi komai yi musu dadi shida
sabreen din. Suna zaune zaman kurame kawai,amma lokaci lokaci suna satar kallon
juna shida sabreen din,har zuwa sanda tayi alama da hannu aka bata abun rubutu.
"Ka kiramin driver ya maidani gida,kada ku sake barin
yara har tsahon sama da awa a hannun masu aiki ba tare da kuna zagayosu kuna
dubasu ba" Iya abinda ta rubuta kenan da rarrababben rubutunta.
Ya dauka
idanunsa ne suke masa gizo ko suke nuna masa ba daidai ba,sai kawai ya miqawa
sabreen din paper ya qarasa ya karbi yaran ya ajiyesu sannan ya tura wheelchair
din da take kai da kansa.
Sanda
yake turata da kansa sai taji wani abu yana sauka saman zuciyarta,tana iya
qididdige takunsa da kuma yadda yake tura kujeran cike da karsashi,sai takejin
kaman ba'a taba tafiya da ita saman wheelchair din irin haka ba.
169
Koda suka isa key ya karba hannun driver din,yace su biyoshi a daya
motar. Shi yayi driving nata har gida,ya kuma danganata da bedroom dinta.
Tsugunnawa yayi a gabanta a hankali,yana jin wani abu me kama da qaqqarfan
farinciki yana dawainiya dashi.
"Zan koma......ba wani abun?" Kai ta girgiza masa
alamun ba komai,sai ya miqe a nutse yana furta.
"Sai da safe,Allah ya huta gajiya" Ya fada yana
dan rage Ac din dakin. Idanunta ta lumshe,wasu hawaye masu dumi suna silmiyo
mata wanda ba nace ga dalili ba,ta miqa hannunta da qyar dake yawan yo mata
nauyi tana goge hawayen fuskarta.
Riqe da
paper din kuma a inda ya barta ya sameta a zaune tsakanin yaqini da kokwanto.
Cak ya dagata yana juyi da ita sannan ya direta yana duban tsakiyar idanunta.
"Na gode sosai duniya.....na gode da tayani siyawa
yaran nan soyayyar maamah......koda ni ko ke mun rasa soyayyarta.......soyayyar
da zata bawa su fauzan ta ishemu". Da mamaki take kallonsa,sai ya lakace
mata hanci.
" Ko an gaya miki bana sane da boyayyar addu'ar da
kikewa iyalinki.....ni number one,addu'ar kariya samun nasara da cikakkiyar
lafiya,yaranmu shiriya da zama nagartattu.....sai samun qauna daga wajen
kakarsu" Kunya ta kamata,ashe dukka
kukenta da fatanta cikin sallolinta na dare fakare yakeyi mata?.
★Cikin kwanakin
kwanciyar hankali da nutsuwa ta samu ga kowa,ci gaba ta fuskokin rayuwa kala
daban daban.
Wata irin
soyayya ake murmushewa cikin gidan me jadda me license,irin soyayyar da yaran
da suka fito ma daga jikinsu saidai a sanmusu. Tsakanin DUNIYOYIN guda biyu
wani irin dangantaka ce me qarfin gaske.....wadda ta gwada musu lallai WA YASAN
GOBE? banda Allah?. Wata irin DANGANTAKAR ZUCI me tsakanin qarfi da power,wadda
take sake basu yaqinin ABADAN ba wanda zai iya rayuwa ba dan uwansa. Sau da
dama idan suka zauna labarin rayuwrsu ta baya suna jinjina lamarin ubangiji kan
yadda ya tsara KUNDIN QADDARAr junansu,wani ALQAWARIN ALLAH ne wanda baya
tashi. Komai na sabreen din tana qoqarin saitashi ya zama daidai da ALQIBLAr
fu'ad din,komai nata tana qoqarin ganin bai saba da muradi da abinda me jadda
yakeso ba. SIRADIN RAYUWArta kaf akan gidanta ne da yaranta,ta zage sosai wajen
koyan abubuwa da dama da zasu maidata cikakkiyar matar gida,irin matar gidan da
soyyayarta da kulawarta ke tsayawa a zuciyar mijinta.
Duk wata
DABI'AR ZUCIYA da tasan zata kawo rauni a mu'amalarta da fu'ad tayi qoqarin
nesanta kanta da ita,ta sake qoqarin zame masa GURBIN IDO ta fannin mahaifiya
dama mu'amalarsa tako da yaushe. Kusan duk bayan kwana uku ko zataje ko
bazataje ba ta koyawa faud daukan yaran bayan sallar ishai suje su gaida
maamah. Hakan yana sanya maamah cikin farincikin da har baya kasa boyuwa saman
fuskarta,tana jin yaran a jikinta qwarai,can qasan zuciyarta kuma idan ta kalli
mahafinsu takanji kaman ta zama butulu KUFAN WUTA a wani zamani can baya daya
wuce. Tun zuciyarta bata gaya mata harta fara gayawa kanta da kanta cewa A
RUBUCE TAKE qaddarar kowanne bawa,ba wanda kuma ya isa ya sauya qaddarar wani
face marubucin qaddarar.
Sabreen
zata iya cewa ita din tana daya daga cikin matan da suka qaryata kalmar nan ta
NAMIJI TABARMAR K'ASHI. Mu'amalar fu'ad da komai nasa na musamman ne kuma ya
banbanta dana sauran maza. Duk da cewa GUDUN K'ADDARA GUZURIN TARAR DA ITA amma
tayi imanin cewa addu'a tana iya sauya qaddarar bawa......tana fatan yadda ko
yaushe ta sanya goshinta a qasa take roqar Allah madawwamiyar lafiya da zaman
lafiya a gidanta.......ta kasance ita daya a rayuwar fu'ad din a matsayin matar
aure,tana da yaqinin Allah bazai juyar da addu'arta ba duk da tabbacin data
samu daga bakinsa.
★Cikin dim
light din dake kai kawo a dakin ta qaraso gabansa,sanye da wata sassalkar rigar
bacci data qawata surarta dama fatar jikinsa. Duk da sau daya ya daga kai ya
kalleta amma sai data fusgi hankalinsa,ya kalli agogo ya maida dubansa kanta
sanda take tsugunne gabansa tana zuba masa hadadden kunun ayar data koya,kunun
da tunda ta koyeshi ya zame masa JARRABI kullum sai yasha shi.
Sai data
sake masa murmushi sannan ta miqa masa cup din,ya miqa hannu da nufin karba
yana cewa.
"Inda malami kika saka yayimiki aiki akan soyayyarki a
zuciyata,tabbas dana qara masa kudi ya qara tsananta aikinsa,don nasan babu me
mace irin tawa a duniyar nan".
" Hamma....sonkai?" Ta fada da muryarta me
sanyi,wadda shi daya take maidawa ita haka a kebantaccen guri irin wannan. Zai
bata amsa zafin da bayan hannunta yayi ya dauki hankalinsa.
"Subhanallah.....zazzabin nan wai bai tafi ba?" Ya
tambaya cikin tsananin damuwa yana ajiye cup din hannunsa.
Kai ta
gyada masa a shagwabe
"Bai tafi ba hamma....."
"Bari na yiwa doctor mubeena waya ta shigo ta
dubaki......zazzabin nan ya isa haka nan". Tasan koda tace masa ya bari
bazai bari ba,yana damuwa da ciwonta fiye da yadda ita take damuwa da kan nata.
Sannu
kawai yake jera mata,tayi tayi ka yasha kunun yace ta maida fridge.
Baa
rufa awa ba doctor mubeena ta iso da kayan aikinta,kai tsaye suka wuce dan
qaramin dakin daya zuba qananun kayan aiki a ciki saboda lafiyar iyalin gidan.
Shi da
ita duka idanu suka zuba mata sanda take duba gwajin data mata saboda ganin
murmushi yana fita kan fuskarta.
"Mr and mrs jadda......congratulations,madam nada juna
biyu". Banda yasan doctor mubeena na tsananin girmamashi da sai yace tana
wasa da hankalinsa ne,saidai duk da haka sai daya ce.
"Say it again please".
"I said madam nada juna biyu......she's pregnant".
Suratul ikhlas kawai ya hau karantawa qafa uku,daga nan ya miqe ya sunkuci
matarsa,daukan data saka Dr mubeena soma hada ya nata yan nata ta basu
waje,saidai tana iya hangen tsoro sosai fuskar sabreen.
Abinda kawai
yake yawo a kanta shine watansu fauzan hudu,cikin week dinma duka duka aka fara
koya musu zama......likita yace aqalla tayi shekara daya so samu har biyu bata
dauki wani cikin ba saboda ta warke yadda ya kamata,yanzu kuma dr mubeena na
gaya mata juna biyu ne da ita?.
Cikin qasa
da mintuna biyar dukka wannan tsoron yabi ruwa,cikin daqiqa kadan komai ya
kwaranye daga zuciyarta. Yadda idanun fu'ad ke fidda qwallar
farinciki......yadda bakinsa ya gaza hutawa dayi mata addu'ar
"Ke 'yar aljanna ce in sha Allahu sabrrrr.......ke
alkhairi ce sabrrrr......don Alla ki gayamin me kike da burin mallaka a
rayuwarki bayan gidan marayu da gajiyayyu da tallafawa marayu?". Kai ta
girgiza a hankali,lallai ta jahilci irin tsananin son da fu'ad yakewa haihuwa.
"Babu.....babu muffin,iya wannan qaunar da soyayyar da
wadatar......iya wannan shauqin na samun iri daga jikina ya isheni farinciki
har qarshen rayuwata". Ta furta maganar da dukka zuciyarta tana tuna wata
mata da mijinta yayi mata duka ya watsota waje ya kuma saketa dukka a
iqirarinsa na ta fiya haihuwa......da an tabata sai ciki.....dukka ubangiji ita
bai jarabceta da wannan ba?.
Wani irin
dare ne da bacci ya gagari idanun fu'ad,yayi sallah yayi addu'a har baisan
iyaka ba. Itama da take kwance lamo kawai tayi,zuciyarta na sake cika da
mamakin yadda yake tsananin son haihuwa,saita samu kanta da maimaita.
"Alhamdulillah......alhamdulillah" Har sau babu
adadi.
★Cikin
lokacin wani kulawa yake bata data ninka ta baya,yana gida ko yana office dukka
yana kula da motsinta. Ya sake qaro mata aminttatun masu aiki da suka sanya
komai ya sake zame mata da sauqi,goyon ciki me 'yanci,kuma Allah ya bata da
sassauci akan nasu fauzan,duk da cewa har a lokacin tana shayar da yaran,yace
bai yarda ta yaye masa yara ba,idanma biyanta ne shi zaiyi a barsu susha nono
su qoshi ko don saboda ginuwar kwanyarsu yadda akeso.
To shi
ciki dai d'an duma ne inji hausawa,a hankali jikinta da dabi'unta suka fara
nunata,duk da yadda take gocewa shiga cikin mutane don kada su fahimci cikin.
Kunyar cikin take sosai,sau tari idan shagwabarta ta motsa sai tayita masa
rigimar banza akai.
"Hamma don Allah kada ka gayawa kowa.....don Allah
hamma kada ka fada,yayi wuri fa hamma.......duka duka watansu fawad nawa
ne?,Allah kunya nakeji"
"Sabrrrr" Ya kirata kai tsaye a lokacin tana saman
cinyarsa yana raba mata doguwar sumarta biyu hagu da dama don ta dameta.
"Wallahi wallahi ko cikin shege nayi miki bazan boye
samuwarsa ba.....kuma zanso abina fiye da tunaninki,ballantana 'ya'yan halaliya
'ya'yan so". Yadda yace 'ya'yan so din har tsakiyar zuciyarta,tun daga
ranar saita daina cewa komai akai,ta kuma tayashi da duk yadda yakeso.
Tasha
tsokana sosai wajen fannah wadda itama nata cikin ya fara girma,amna da huda
kuwa dukkaninsu yaya take a Wajensu,ba tsokana sai gulmarta a boye,uwa uba suma duk ta kansu sukeyi don
cikinsu ya tsufa sosai.
Wata tara
da bikinsu amna amna din ta dire nata yaron namiji. Maamah bata sanu ba sai
bayan kwanaki bakwai,tana zaune saman wheelchair dinta sanda musaddiq ya ajiye
mata goro da alewar radin suna. Hamza ya saka shima still saboda nuna yabawa
bisa hidimar abban a kansu,sun masa laqabi da HILAL. Ba wani feeling data samu
zuciyarta a ciki akan haihuwar,so ko qi itama bata san wanne layi take kai
ba,saidai bata wani dorawa kanta tsananin tunani akan komai ba ta ajiye
maganan,duk da lokaci lokaci idan aka kawo mata su fauzan yaron yana fado mata
a rai.
Tsakaninsu
da huda wata biyu kacal itama ta dire nata sojan. Saddiq ya nuna kara sosai,ya
sanya masa sunan mahaifinsu sabreen wato ahmad,suna masa alkunya da NASEEM.
Ta kowacce
fuska anni jinta take cikin alkhairin ubangiji,saidai a yanzun kwadayinta a
samu 'yanmata kuma,don tana fatan samun garabasar nan na wanda ya raini diya
mace biyu ya aurar dasu na alqawarin aljanna kai tsaye.
Irin girman
da nauyin cikin ya sanya fu'ad wucewa da ita a wata tafiya da yayi zuwa spain
ya tafi da ita. Bawai don yana da nufin tayi anti natal nata a can ba,saidon
kawai a duba mishi ita duk da bata da matsalan komai,saina wani irin cin abinci
da takeyi,abinda shi kuma yakeyi masa dadi sosai,har yakan zauna yana kallonta
abinsa.
Scan din
farko ya nuna twins ne a cikin nata. Wani iri ya dinga ji,tsoron Allahnsa yana
sake kamashi. Dukka cikin addu'arsa ba wadda bai gani ta tabbata ba.....shin
cikin ni'imomin Allah wanne ne a ciki zaiyi inkari?.
_Allah ka wadatamu da dukka ni'imominka na zahiri dana
badini,ya Allah karka jarabcemu da gushewar ni'imominka a kanmu_
_on our way to the last episode's in sha Allah_👏🏽👏🏽😄😄😄
170
Tattalinta
ya dinga yi,nan nan da ita yakeyi,baya yarda komai ya taba walwalarta ko kuma
jin dadinta.
Duk wani abu
da yasan zata iya buqata ya ajiyeshi......komai da yasan zata iya nema kafin ma
takai ga tambaya ya tabbatar da samuwarsa.
Bata aikin
komai,ba aikin fari bare na baqi,komai nata dana yara tana da amintattun masu
aikin da take jinsu kaman 'yan uwanta na jini,musamman da suka kasance kusan
dukkaninsu marayu ne wadanda basu watsar da maraicinsu ba.
Duk
wannan gatan data samu.....duk wannan kulawar bata sanya ta saki hidimarsa ki
qwaya daya ba. Yayi yayi ta barshi amma ita kanta tasan ba abu bane me yiwuwa
tabar kula da mijinta,sai ya qyaleta a bisa dole,amma duk wani motsi nata da
zatayi shike tayata,shike kama mata. Misali wani lokacin yakan yi mata wayo ya
rigata tashi da safe. A kitchen din sama zai hada breakfast abinsa ya aje mata
nata,ya hada ruwan wankanshi da kanshi yayi,ya watsa undies dinsu cikin washing
machine ya wanke musu,ya kwashe komai dake tsananin parlor zuwa Bedroom din da
suka bata. Idan ta farka saidai ta taras da sauran aikin,wanda baya wuce shayar
dasu fauzan da kuma qarasa kintsa saman nasa,sai tayi wanka shikenan ta zauna
cikin masu aikinta.
Idan ta
gaji tana buqatar fita shike katse komai nasa ya dawo ya fita da ita,idan ma
qasar ko garin takeso su danyi balaguro daukanta yake ita da duk wanda takeso
su wuce suyi iya kwanakin da takeso.
Irin gatan
da yake gwada mata saita dinga jin kaman ya mata yawa,kaman bata cancanci
tattali irin haka,ranar data fara magana a kai suna tsaye ne saman balcony na
wani qawataccen madaidaicin gida daya siya a dubai a satin. Gidan yana area me
tsada ne wanda yake da clear view na garin dubai da guraren kallo masu kyau.
Ta baya
ya rungumeta yana dora hannunsa guda daya saman qaton cikinta. Ta miqa hannunta
ta bayan itama ta shafo sajensa tana sakin murmushi.
"Tunanina kike?" Ya furta a tausashe,saita gyada
masa kanta.
"Ya akayi kasan sirrin zuciyata".
"Ruhi daya......zuciya daya.....qwaqwalwa
daya.....gangar jikince kawai guda biyu,to menene zai boye a wajena?" Ya
qarasa maganar yana tura mata wani file ta gefan cikinta. Murmushi ta saki tana
jin maganarsa ba wani kuskure ko gyara a ciki,ta karbi file din ta bude.
Takardar
shaidar mallaka ce ta wannan gidan da suke ciki,wanda ya rubuta da sanya
hannunsa da komai kan ya mallaka mata gidan. Ganin komai take kamar a
mafarki,batasan adadin gidaje da estate nawa ya mallaka mata ba.......amma
wannan ya zama na daban. Mallakar gida sukutum da guda a dubai?,abun sai kanta
ya kasa dauka,don a satin a gabanta ya bada izinin tura Dirham's masu nauyin
gaske ga kamfanin da sukayi cinikayyar gidan.
A nutse ta
juyo suna fuskantar juna,hannunta yayi sanyi sosai ta riqe nasa hannun.
"Hamma.......wannan kyautar tayi girma da yawa,wannan
gatan yayi yawa". Sassanyan murmushin nan nasa ya saki,ya kama qugunta ya
riqe yana mata wani tattausan kallo kaman zai hadiyeta.
"Me akayi ma my world?,wannan gidan wai?,kinsan gidaje
na nawa a qasar nan?,wannan din kuma dama tun asali saboda ke aka
siyeshi.......sabreen" Ya kirata da wani sound yana kama fuskantarta cikin
hannunsa.
"Na'am muffin" Ta amsa masa idanunta suna cika da
hawayen farinciki.
"Komai na fu'ad naki ne.....komai na muhammad jadda kin
cancanceshi.........gata kuma ban nuna miki komai ba sabrrrr.......bana buqatar
komai a wajenki illa ki cikamin gida da yara......ki cikamin gida da zuri'ar da
zasu zamemin ababen alfahari.....haihuwa nakeso kiyita yi......ni kuma nayi
alqawarin bazan barki kisha wahalar komai ba banda ta basu tarbiyya".
Rungumeshi ta matso zatayi amma cikin jikinta ya tokaresu,sai taja baya
kadan,yana dariya ya nuna cikin da yatsarsa,sannan ya juyata yana baga kyakkyawar
runguma ta baya.
★Wata
takwas da sati biyu wanda yayi daidai da shekararsu fauxan daya da wata daya
akayi mata wani CS din a garin madeena.
Kyawawan
'yan biyu ya haifa dukkaninsu maza. Manya manya har sunfi su fawad girma da
wani irin kyau me daukan hankali,don kuwa kamanninsu bangare biyu suka
debo,fu'ad din da sabreen din,saika kasa tantance da wa suke kama?.
Kasuwar
'yan uku ta tsaya,kowa so yake a bashi yaran,duk kuwa da cewa dasu aka tafi
karban haihuwar 'yan uwansu. Amna naso,huda naso,fannah da farouq dinta
sunaso,ga maamah a gefe da sai a ranar tayi kukan rashin magana da bata iyayi.
Kuka tayi sosai me yawa,don kuwa taso tana da baki,da tabbas ko fu'ad baya so
sai ta karbi wadannan yaran.
Wani irin
kwarjini yaran ke dashi kaman ubansu ya roqa musu,ga wani irin energy da suke
dashi da wani girma kai zaka ce shekara biyu suke ba daya ba. Bugu da qari
kowannensu tafiya yake sosai,don tun suna wata bakwai suka fara miqewa,yanayin
kulawar da suke samu ya sanya ba wani wanda yayi wani abu wai kashin
haqori,banda zazzabi da sukayi na wasu kwanaki,sai bullar haqora kawai a
bakinsu.
Energy
dinsu ya sanya suke da fitina,haka suke fafatawa da anni. Gidan su kuwa tuni
fu'ad ya sanya an dage komai sama wanda zasu iya jawowa ya illatasu,wanda bazai
dagu ba yasa an daukeshi anyi replacing da wani abun na daban. An kwashewa
sabreen flower verse dinta da yawa da take ado dasu,a ranar ta dinga fushi tana
tura baki gaba.
"Tsakani da Allah......haka kawai a hana mutum
ado......". Duba daya yayi mata ya dauke kai yana ci gaba da yankewa
fawwaz farce sanda yake bacci saman cinyarsa.
" Yara dai da gidansu ba wanda zai hanasu sakewa,ni ba
ta flower vase dinki nake ba.....ta lafiyan yarana nake,inda bazai cutar dasu
ba zan bar musu suyita fasawa......qarqari ace dai mu biya ko?,mu kuwa baza'a
mana gorin biya ba". Mamaki ya cikata,tayi sakato tana kallonsa yadda ya
basar yana wani shan mur,ta danne dariyarta tana sake daure fuska
"Amma dai ba haka akewa yaro tarbiyya ba,a barshi idan
ya fasa a zane masa hannu don yasan ba abun tabawa bane". Nail cutter din
ya subuce a hannunsa,ya waro ido yana dubanta.
"Du me?,ke waye ya dakeki?,ashe kina so anni da abba su
shigo sulhu kenan......wa yace miki akwai duka cikin tarbiyya?,wait.......tsaya
ma......bakisan yaro muddin ba'a barshi yayi wasa yadda ya dace ba hakan yana
zame masa naqasu a gaba?,ina manya da zakiga sun girma suna wasanni kaman
yara?,har wata tsokanar idan sun maka ya baka haushi?,alhali bawai tarbiyya ne
basu dashi ba?,to yawansu rashin barinsu suyi wasan da zasu qoshi ne".
Dole dariya ta subuce sabreen ganin yadda ya gyara zama yake mata jawabi bilhaqqi
da gaske.
"Malam hamma....ban taba jin karatun nan ba sai a
kanka".
" Zaki jine da kyau.....nidai na fada abar yarana suyi
yadda sukeso". Ya fada yana ci gaba da yanke masa farcen
"Hamma" Ta kirashi a tausashe,kai ya daga ya
kalleta ganin yadda ta kirashin.
"Ina gudun kada soyayyar yaran nan ya rufe maka ido ka
kasa tayani basu tarbiyya me kyau". Wani murmushi ya sakar mata yana ci
gaba da aikinsa.
"Zaki gani.....Allah ya bamu aron rai" Abinda ya
fada kawai kenan. Shi kadai daga shi sai Allahnsa sukasan irin burin da yaci
akan yaran,shi daya yasan kalar rayuwar da yayi musu tanadi.....ba iyasu fauzan
ba,dukka yaran da zai samu daga nan har ya qare rayuwarsa.
Ranar da
zasu bar asibiti zuwa gida tana zaune suna hira da huda dake rungume da babynta
wanda ya gama rigima bacci ya soma daukansa taji sallamar kawu rufa'i.
Farar
jallabiyya ce a jikinsa harda hirami,ga wani farin carbi a hannunsa.
"Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu
yake d'iyar aljanna mabudin arziqin ahalinta gaba daya". Bushewa da dariya
huda tayi tana kallon kawun. Gaba daya ya canza,quruciyarsa kuma sai dawowa
takeyi saboda wadatar daya soma tsumbula ciki.
"Kawu waye ya kawowa madeena?,kamar bakafi wata shida
da komawa bafa" Huda da dama can tasu bata jiquwa ta furta.
Harara
ya dalla mata yana neman wajen zama gami da kalmashe carbinsa.
"Ni yanzu har ayimin maganar hawa gajimare da
sauka......mutumin da yake da suruki irin me jadda gidan gold da diamond?,to
bari kiji yarinya,a yanzu haka aminaina guda biyu dukkaninsu hajjin bana dasu
Zamuyi gaba daya,albarkacin me jadda.....albarkacin d'iyar da aka haifa tsiya
tana bacci kariris". Neman wajen zama huda tayi saboda kada dariya ta
kayar da ita,kawun ya gama bata amsa daidai da ita,saiyayi banza da hudan yana
maida hankalinsa kan sabreen.
"Sannu d'iyata.....sannu 'yar nan.....ashe ni ahmadu da
fateema suka haifawa ke ban sani ba?" Ya qarasa fada yana matse hawayensa
da wasu sabbin qwalla da suka fara taruwa lokaci guda.
"Dama na dade inaji a jikina zanyi kudi.....na dade
inaji a jikina zanyi arziqi ashe ta sanadinki ne,ubangijin al'arshi yayi miki
albarka,dukka gidanku yanzu ya koma qarqashin kulawarki,masoyanki da
maqiyanki,harda 'yan uwanki na dakin aure,Allah ya qara miki riqonda zumunci da
kuma zuciyar yafiya da afuwa"
"Ameen ameen kawu" Sabreen ta fada tana murmushi.
Gaba daya kawun nata ya canza kaman bashi ba,wata kamala duka ta saukar masa,ga
alamun jin dadi da hutu duka tattare dashi.
"Amma 'yar nan ya akayi haka?" Ya fada yana gyara
muryarsa. Kai ta daga tana dubansa
"Me akayi kawu?".
" Kinyi qoqari dai.....amma ci gaba ya kamata a samu
ai,'yan hudu ya kamata kiyi wannan karon,amma sai aka koma baya kikayi
biyu,maimakon ki maimaita ukun?,kinsan innarmu sai da tayi 'yan uku da 'yan
biyu kusan kashi biyar,duka rasuwa sukeyi,ni kadai da dan uwana ahmadu ne muka
zauna,don ko babanki ai tagwaye ne,ni kuwa mu uku ta haifa,amma ni duka na fisu
qwarin qashi ni kadai na zauna".
"Kaine dai Allah baiyi niyyar kashewa ba kawu ba
wayonka bane" Huda data goya baby naseem da baby carrier ta fada duka
cikin salon tsokana.
Daquwa ya
watsa mata yana dubanta.
"Kinci ubanki.....banda kinci darajar mijinki da ya
bani kyautar gida harda mota satin nan daya wuce yau da sai na karbi goyon na
aza a bayana naci qaniyarki sannan na baki danki ki cigaba da tafita"Daga
huda din har sabreen sai a sannan sukasan saddiq ma yayi kyautar,ba zatar data
kashe rigimar kawu da huda ya koma maganar da sabreen.
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 171
*_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_*
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1
171
"Allah
ya sambada miki albarka,don Allah.........don Allah ki daure wata shekarar
warhaka ki sake tunkudo wasu hudun" Ido ta zaro da mamaki
"Da gaske fa kawu kake?".
" To me zaki tsaya jira?,banda rainon cikin bakisan
wahalar komai ba?,shi kuma iri kawai yakeso,ai faduwa tazo daidai da zama"
Ya fada yana leqa fuskokin yaran.
"Tubarkallah wallahi.....haihuwar masu kudi daban data
talakawa,su kansu yaran daban naku suke da namu".
" Wallahi idan banbar dakin nan ba sai kawu ya sanya
cikina ciwo.....adda bari naje nima nayi sallah a masallaci" Huda ta fadi
tana fita ta barsu.
Wannan karon
halastacciyar walima jadda ya fara hadawa a birnin madeena. Walimar maza daban
mata daban. Jirginsa daya siya bayan wanda yayi kyautarsa na JADDA WINGS 002
kawai ya bayar akayi jigilar 'yan uwa da suke cikin list na zuwa umra a wannan
watan aka gabatar da walimar tare dasu,ciki harda maamah,wadda akan idanunta
aka gudanar da komai.
Duk wani
motsi na yaran nan guda biyar akan idanunta yake,ta saka damuwa sosai a kansu
tana ganin kamar zasu bace ko zaa daukesu,saidai tana komawa daidai duk sanda
ta tuna amincin da garin yake dashi.
Wannan
karon Sabreen itama ta samu mahaifinta,wato AHAMD(Amaan),dan uwanshi kuma yaci
sunan muhammad da kanshi wato takwaran babansa (AMEEN).
Tuburewan
tsokana Sabreen tayi.
"Hamma wannan son kai ne.....ni me yasa ba'a fara jira
an saka me sunana ba?" Ta fada tana turo baki gaba. Dariya ya saki yana
murza yatsunta sanda take zaune tana shayar da muhammad ameen din.
"Ki haifomin baby girl ki gani DUNIYATA.....ke kika
mana addu'an boys,gashinan ta shafi kowa cikin familyn jadda,duka maza suke
haifa mana,muna da kwadayin mace dukkaninmu amma bansan kusancinki da Allah ba
da addu'arki ta riga tawa tafiya ba.....at first nafison na samu daughters so
samu.....don na basu tarbiyya na aurar dasu,na kuma rabauta da rabon aljannar
da manzon Allah ya yiwa duk wanda yayi irin wannan aikin alqawarin samu".
Dauke kai tayi tana sake tsuke bakinta cikin shagwabar nan da bata jin ta girma
da yinta,kamar yadda shima baya ganin ta girma dayi masa ita.
"Amma dai it's not fair hamma......sai a jirani sai
sanda aka samu baby girl din aka saka ameenatu".
"Ameenatu ta zama wajib akan dukka diya mace ta farko
data fito daga tsatson jadda......take it easy maa.....ki qara himma next year
by now ki ajiyemin girls" Idanu ta zaro ta bishi dasu,sai ya jinjina mata
kai cikin bada tabbaci.
"In sha Allah" Ya fada da yaqinin daya sanyata
bata sake cewa komai ba.
Sabreen
bata yarda ta koma ba saida jini ya dauke mata,ta sauke umra. Addu'a tayi me
tarin yawa akan rayuwarta data zuri'arta,addu'a ce me yawan gaske akan zaman
lafiyarta dana familynta gaba daya,qannenta 'yan uwanta dama duk wanda yake da
jibi dasu. Ta dade gaban dakin Allah tana neman me kyau a duniya me kyau a
lahira(Rabbana Aatina fiddunya hasanatan wafil Aakhirati hasanatan wa qina
azabannar/addu'a ce wannan me matuqar muhimmanci,ku dage kada kuyi wasa da
ita). Ta roqi Allah dawwamammiyar soyayya a zuciyar mijinta,da kariyar Allah
daga jinsa ganinsa da zuciyarsa dama al'aurarsa akan kowacce diya mace idan ba
ita ba.
Cikin
wani irin aminci sakewa da walwala take kula da yaranta dukka guda biyar din.
Tana da wadatattun masuyi mata hidima,yayin da ita kuma ta tattara damuwarta
dama kulawarta dukka akan mijinta.
Sai data
warware sosai sannan yazo mata da komai da komai na kammaluwar ginin gidan
marayu maka maka har guda uku a arewacin Nigeria,da kuma gina sabuwar
foundation ta kula da marayu da zawarawa da yara marasa galihu.
Kukan
farinciki sosai ta dinga yi,saboda cikar ragowar burinta kenan a rayuwa. Wani
irin katafaren gida ne da aka tsarasu bisa tsarin ginin unguwa guda wato
estate. Da makarantunsu tun daga primary har zuwa secondry,jami'a kuwa a qasar
waje yayi planning ya dinga turasu qasashen musulunci,don yana sanya ran a can
zasuyi karatu me kyau,ba tsangwamar mutane ba takurawarsu.
Komai an
wadata gidajen dasu,abinci sutura wutar lantarki da kayan more rayuwa cikin
kowanne gida da dakuna. Cikakken tsaro da tsari na addinin musulunci wanda aka
ginashi bisa jagorancin malam da a yanzun shine babban me bawa jadda shawara
akan duk wani abu daya shafi zakka da harkokin addini cikin rayuwarsa.
"Wannan gidan da komai dake cikinsa kuma mallakin su
ayshatu ne......na kusa dashi kuma na JIB ne,sai kuma guda dayan na
busari" Ido ta waro tana mamaki,ya akayi yasan su jib?.
"Maida idon ranki ya dade don ban gaji da kallonsu ba
daga nan har qarshen rayuwata......karki ce komai,tun daga randa na sameki
cikakkiyar mace na bibiyesu na kuma jawosu cikin rayuwata,yanzu haka busari
shine shugaban drivers na kamfanina,Jib kuma yana jagorantar sashen tsaro na
daya kamfanina dake lagos" A ranar
idan farinciki yana kisa tabbas ta tabbatar sai buzunta. A yadda abubuwan
sukazo tana buqatar ma'aikata ita kanta,tana buqatar su zauna su qarasa tsara
komai kafin ranar da zaa qaddamar da qungiyar da kuma qaddamar da gidajen
marayun dake kano kaduna da abuja.
Sosai ta
tsananta bincike cikin danginta na uba harna uwarma,ta kuma zabi amintattu da
zasu dinga gudanar da komai,nata aikin kawai tana daga cikin gida xatayishi
cikin system sai waya idan ta kama,sai kuma ziyara da duba gidajen lokaci bayan
lokaci da zata dinga zuwa,da kuma wani taron idan ya kama,kamar ganawa da
ma'aikatanta da sauransu.
Abinda ya
bata mamaki shine,albashin da fuad ya sanya mata na million din kudade. Abun ya
qarasa kasheta da mamaki,itace shugaba,yayi dukka aikin ya mallaka mata,ya bata
dama ta sakawa kowa albashinsa kuma zata dinga biyansa......sannan ita kanta
kuma ya yanka mata albashin miliyoyin kudaden da batasan ma me zatayi dasu ba.
Kuka kam
wannan karon barinta yayi tayi abinta,ta shimfida fuskarta saman kyakkyawan
qirjinsa tayi kukanta yadda takeso ta kuma zarce da godiya ta baki da kuma
godiya ta aikace. A ranar ta saje yarda da kanta,ta haukatashi da wani irin
salo......ta sake godewa Bgawo's kitchen and aphrodisiac. Mama macace
dattijuwar qwarai data iya gyara a gargajiyance,saboda cikar hankali da
shekarunta da takai matakin dattijantaka,bata taba ganin gyara irin nata
ba,gyara na dattawan tsofaffi da babu side effects akai sai tsimuwa da jikinki
zaiyi da kyau,wanda sun shigo duniyar gyara ne saboda bada gudunmawa ga matasan
mata dake tasowa cikin rayuwar aure a yanzu.08127084190/08104553105.
Yana jinta da
kima a rayuwarsa fiye da duk wani abu me kima daya mallaka......yana jinta a
matsayin abu mafi tsada da daraja a rayuwarsa,don haka komai nata ya zama na
daban kuma na musamman.
Wani tsaro
yake bata,guards ya samar mata na musamman,wadanda suke tare da ita a duk sanda
zata fita ko zata tafi zuwa wani gurin. Ya samar mata 'yan sanda mata biyu
jajirtattu da zasu kasance da ita a motor din da take ciki,bayan 'yan aikinta
dake kula da lamarin yaranta,sauran motocin kuma duka guards dinta ne. Cikin
lokaci qalilan Sabreen din ta zama wata me tsada,komai nata kuma ya kuma sake
zama na musamman,ya canza mata mota tata ta hawa da duka sabbin motocin da masu
tsaronta zasu dinga using.
*_BAYAN WASU SHEKARU_*
*JADDA'S VILLA*
JADDA'S
VILLA shine sunan dake rubuce b'aro b'aro daga tsororuwa babban ginin gidan.
Rubutun an yishi ne da ruwan GOLD jikin wani qawataccen allon qarfe da aka yiwa
wani irin design me azabar kyau da daukan hankali.
Wani irin
shimfideden gida ne,wanda a qalla ya qunshi maka makan mansions a cikinsa guda
shida. Kusan komai na gidajen iri daya ne,saidai banbancin girma da wani gidan
yafi wani yawan dakuna da kuma qawatuwa da kayan alatu na rayuwa,daidai da
yadda mamallakan gidan suke da buqata.
Idan ka
kira JADDA VILLA da aljannar duniya sam sam bakayi laifi ba,don inda akwai
sunan da yafi haka nuna tsananin tsari da cikar suffa da haibar gida ya
cancanci ka bashi.
Gidane
daya mamaye jadda street gaba daya daga hannun dama,sai hannun hagun dake dauke
da qawatattun gidajen hamshaqai masu fada aji cikin unguwar da sai ka isa wane
zaka mallaki gida a cikinta cikin birnin tarayyar abuja.
Ba
gidan kawai ba,unguwar kanta sai kabi matakai daya bayan daya kafin ka samu
nasarar shigarta,bayan kuma ka shiga din zai zame maka barazana hanyar shiga
JADDA VILLA. Birnin da ya shiga bakunan manyan masu kudin da suke ganin wuyansu
yayi kauri a duniyar naira.....birnin daya girgiza zukatan al'umma da dama ciki
harda manya manyan masu kudi na qasata dama qasashen duniya gaba daya.
Manyan
gate gate guda biyu da matsakaici guda daya dukka saika wucesu kafin kakai ga
shiga BIRNIN JADDA kaman yadda aka rubuta daga cikin gidan gate din farko.
Daga
can cikin daya daga cikin gidajen dake cikin jaddas villa din,cikin tsakiyar
wani qawataccen courtyard da aka shimfida hikima wajen gini da tsarinsa.
Qawatattun shuke shuke ne masu dauke da mabanbantan furanni masu launikan dake
kiran butterflies zuwa garesu,daga qarqashin shukokin wata 'yar qwarya qwaryar
qorama ce ta zamani da aka qirqireta saboda wucewar wani ruwa me tsananin
hasken da kake iya hangen wasu irin mulmulallun stones masu daraja da tsada
dake zuwa a oval shape,amma suna da nau'in kaloli daban daban,kaman yadda
madaidaita da qananun kifayen dake yawo a ciki suke da wadannan launikan.
Wasu
irin Kujeru ne sirara masu taushi aka qawata courtyard din dashi,wadanda suke
farare qal,kaman ba'a tsoron kai kawon yaran da gidajen suka mallaka,yaran da
suka tasamma rai ashirin da shida.
Zafin rana
ko sanyi duka basa rabar wajen,guri ne na musamman da kowanne gida daka cikin
gidajen jadda villa aka tanadar dashi bisa tsari na musamman dake iya daidait
weather na wajen. Idan zafi ne weather wajen na fidda iska me kyau da dadi,idan
sanyi ne weather din wajen na bada temperature da zata dace da yanayin da mutum
yakeso.
Saman
daya daga cikin kujerun dattijuwa anni ce,sanye da wata sassauqar riga mara
nauyi ruwan madara,wadda take hade da hijabinta asalin saqar qasar Indonesia.
Daga
gabanta kuwa yara ne matasa maza da mata kusan guda biyar,masu kamanceceniya da
juna,wasu kamanninsu sun fita sosai......wasu kuma kamanni ne na baya baya.
Daga gefan daman annin wasu yara ne guda biyu da duka duka shekarunsu ba zasu
haura takwas da tara ba,dukkansu share hawaye sukeyi fararen fuskokinsu sunyi
jajur.
"Kowa ya gama bayaninsa?"ta fada tana duban
fuskokin su daya bayan daya. Da fari gurin shiru ya dauka kafin daga bi sani,ta
sake bin fuskokinsu da kallo tana sake maimaita tambayarta. Kai suka gyada daya
bayan daya.
"Da kyau" Ta fada cikin cikakkiyar nutsuwarta
dinnan tana ajiye littafin hallul masa'eel dake hannunta a gefe.
"Ameen" Ta kira sunansa kai tsaye. Yaro da yaci
sunan muhammadun ta hanyar fadin gaskiya akan komai da aka tambayeshi,koda
hakan zai ja masa duka......yaron da kusan halayensu suke kamanni iri daya dana
MUHAMMAD SAUBAN(Ku ajiye wannan sunan a next novel nawa idan rai yakai mana😄😄).
Sauban din da shike binsu muhammad ameen da ahmad amaan.......amma halayensa
sak irin na mahaifinsa......halayensa sak irin na ameen......shekarunsa duka
duka basu wuce goma sha biyu ba......amma wani irin girma da dattako gareshi.
"Me ya faru ameen?" Anni ya qarasa tambayarta.
Bayani yayi mata na iya abinda ya sani,ya qara da cewa.
"Amma a gaban sauban akayi.....ki tambayeshi". A
nutse ta waiwaya ga sauban din,wanda yake zaune shi daya saman kujerar da babu
kowa kusa dashi. Ita kanta kujerar tayi dan nesa kadan dasu,kunnuwansa manne da
headphones wanda ko daga nan kana iya jin sautin qira'ar qur'ani na fitaccen
shaik dinnan wato maheer almu'aiqaly.
Duk wanda
yasan sauban ya sanshi da yawan sauraren karatun shaik maheer duk sanda yake
kebe shi kadai,wannan ne anni take kyautata zaton sanyashi ya zama na daban
cikin 'yan uwansa......hasken alqur'ani kuma take tunanin ya qara sanyashi me
tsananin nutsuwa,duk da tarin zuciya da yaron yake dashi.
"Sauban" Ta kirashi tana yafitoshi da hannu. Kallo
daya ya yiwa annin ya saka hannunsa ya cire headphones dinsa sannan ya taso ya
qaraso wajen
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
__________________________
*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada
munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR
GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN
HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road
kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a
duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 172
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA
CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da
babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu
ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
172
"Me
ya hada arham da ahsan?". A nutse ya zube kyawawan idanunsa masu girma
kaman na mamanshi akan dukkaninsu,sai ya matsa a hankali ya zauna gefen anni.
Baiji
tsoron idanun kowa ba ya zauna ya yiwa anni bayani filla filla har yakai
qarshe.
" Haka akayi?" Ta sake tambaya,dukka wajen ba
wanda ya musa banda hilal da yayi shuru. Maida dubanta tayi ga hilal.
"Allah yana cewa cikin qur'aninsa,yaku wadanda kuka
bada imani da Allah.....idan fasiqi(mutum)yazo muku da labari,to kuyi
bincike,gudun kada ku afkawa wasu mutane bisa jahilci(rashin sani dalilin
rashin bincikenku).saiku wayi gari kuna masu nadama.......a duk sanda wani
mutum yazo maka da labarin anyimin kaza,ko wane yayi maka kaza,ko kaza ya
faru,dole ne akan musulmi ya nemi hujja ko dalili na abunnan ya faru,dole
ne......muna da wata dabi'a ta saurin yanke hukunci,da daukan zance daga bakin
mutumin daya fara zuwa mana da labarin wane yayimin kaza,wane ya batamin ko
yayimin ba daidai ba.....nan da nan wannan daya fara zuwa da labarin saimu
dauka shine me gaskiya,bisa jahilci irin namu na neman jin ba'asi daga bakin
wani sashen,wanda muddin zaka kasance mutum irin wannan a rayuwarka,za'a yita
sanyaka batawa da mutane masu daraja da kirki.....zaka yita fada da mutanen da
basuyi maka komai ba.....za'a sanyaka ka yita yanke alaqa da mutanen da
alaqarku keda matuqar amfani a duniyarku da lahirarku.......wannan ba halin
musulmi na kirki bane a matsayinka na babba hilal.....ba kuma dabi'ar qwarai
bace.....ba dattako sam a cikin ta,dukkaninku daga yau na horeku da zama masu
bincike".
"In sha Allah anni" Ya fada yana saukar da kansa
qasa. Waiwayawa tayi ga yara biyun dake gefe tana dubansu.
"Faarees da ra'ess ya tabbata kunyi qarya.....ku bawa
Aadeel haquri,sakamakon qaryarku kuma wannan satin gaba daya kada naga uniform
dinku a wash room,da kanku zaku wankesu duka satin nan.....sannan idan ummenku
ta dawo......kune na qarshen zabar tsaraba har sai kowa ya dauka nashi" Ta
fada tana nunasu da yatsa.
Haqurin
data buqata suka juya suna bawa wanda ake kira da Aadeel din haquri,ta kallesu
daya bayan daya still tana cewa.
"Ku kyautatawa junanku......kyakkyawar mu'amala itace
mutum......girmankai na shashasha ne maras wayo.....hassada ta maras rabo
ce,don tana cinye kyawawan ayyuka kaman yadda wuta takejin yayi.......shi kuwa
sharri dan aike ne,daga inda aka aikashi duk daren dadewa nan zai
dawo......alkhairi kuma danqo ne baya faduwa qasa banza.......komai dadewa ka
shuka alkhairi shi zaka girba,kaman yadda komai dadewa idan ka shuka sharri
cuta ko ha'ince sai ka girbeshi.....kyakkyawar dabi'a jari ce da babu kamarta,wadda
duk dukiyar gidanku bata isa ta siya maka ita ba......hakanan duk talaucin
gidanku idan ka sameta kaiba talaka bane har gaba da abada".
Ire iren
kalmomin kaka ta gari kenan a duk wani zama da zai hadata da yaran,bakinta sam
sam baya gajiya da furta wadannan kalmomin a kansu,har sun fara haddacesu tun
basusan ma'anarsu ba,zuwa yanzu kuma wadanda suka fara girma a cikinsu sun
haddacesu tas a kansu.
Basu fita
a wajen ba saida kowa ya gaisa da kowa,kowa ya koma yanayinsa na dazun sannan.
A sanda suke fita a lokacin sauban ya koma inda ya taso,ya maida headphone
dinsa saman kansa yayi playing karatun yana ci gaba da ji hadi da lumshe ido.
Kammaninsa da dabi'unsa kamar babansa,duk wani harka ta hayaniya ko fada
babu shi a ciki,kaman ya yiwa kansa rigakafi daga fushi da zuciyar da yasan
yana da ita.
Dauke
kanta anni tayi daga inda yake murmushi yana subuce mata. Tana ji a jikinta
anya sauban din ba shine wannan HASKEN da take gani tsakanin iyalinta
ba?,wannan mai riqon addinin ma'abocin cikakken ilimi daya haura na saura?.
"Allah kayi mana zabi da mafita mafi alkhairi" Ta
fada a nutse tana jawo hallul masa'il dinta tana dubawa.
Tsaiwa
Amaan yayi yana hango abokin tagwaitakarsa wato muhammad ameen dake fitowa daga
sassansu. Sanye da fararen kayan da aka yiwa ratsin baqi sak irin kayan dake
jikin Amaan din.
Shima gunsa
ya nufo kai tsaye yana dubansa.
"Abbee fa ya shigo yanxun......kuma naga ya
shirya.....ina kuma kyautata zaton ummee zaije daukowa daga airport......na
tabbatar dukkaninsu sun manta da yaune wedding anniversary dinsu,15yrs"
Ameen ya qarasa fada da faffadan murmushi daya qara masa kyau,yana kuma d'age
dukka girarsa sama.
"Na tuna......akwai wani abu ne?"
"Yes" Ameen ya fada ya fada yana dariya.
"Ya kamata muyi wani abu,yadda naga abbee yana wani
shiryawa yanata duba mirror kaman wani dan saurayi,dolen saiya burge
duniyarshi". Dariya suka saki lokaci daya,amaan yace.
"Babu ruwana idan ummee ta jika.....let's go,mintunan
zuwanshi da dawowarsa basu da yawa" Hannun juna suka riqe suna
hirarrakinsu,wanda kana kallo zakasan akwai shaquwa da qaunar juna me tsananin
gaske.
Ita
kadai yau take zaune saman wheelchair din nata,kusan awa biyu kenan. Mutum daya
take sanya ran shigowarsa kaman yadda ya saba......yaro guda dayan da take
mamakin yadda yafi kowa qulafucinta a gidan da qoqarin kula da duk wani motsi
nata......yaro guda dayan da ita kanta yafi shiga ranta sosai wato sauban.
Jifa
jifa tana jin motsin yaran,guje gujensu kasancewar weekend ce.....amma yau ko
wasan kaka da jikan data jima tana nuna musu bataso ba wanda ya leqota yayi
mata,duk sai ta jita ba dadi.
Sabreen ce
ta fado a ranta,ba yadda za'ayi duk wuya.....duk runtsi idan tana nan ta barta
ta zauna shuru haka,koda kuwa bata buqatar komai zata umarci biyu ko uku cikin
haihuwa yara rai goma da Allah ya bata wani yazo ya zauna kusa da ita.
Wani abu
ta hadiye,karon farko da taji tana dokin ta dawo daga tafiyar kwanaki ukun da
tayi zuwa qasar saudiyya.
Daidai
nan yayi sallama,sanye da dinkin kaftan da aka yishi da wani fari qall din yadi
me daraja. Dinkin babbar riga ne da 'yar ciki dinkin da aka zamanantar dashi,ya
kuma sake maida fuad din kaman wani qaramin matashi.
Baiyi
amfani da hula ba,sai farin rawani daya nada saman farar hular kanshi,sai ya
fito kaman wani basaraken malami.
Duk da ya
dubata dazun yanzun bai gaza wajen dawowa wajenta ba,ya tsugunna ya gaidata,ta
amsa masa da sautin da ba kowa yake iya fahimtar abinda take fadi ba idan ka
dauke shi da Sabreen da suke iya fahimtar kusan komai tace.
Nasarar
fara fitar sautin nata ma gaba daya ya samo asali ne daga Sabreen,wani umra da
sukaje,ta samu daman tara roba wajen indararon ka'aba ta tari ruwan saman dake
sauka ta saitin wajen,ta kumayi tofin addu'o'i sosai data samu daga wajen
mallam,ta durfafi bata.
Wani abu
ne daya tsayewa maamah din a rai,har yau ta kasa mantawa da abun,duk da sai
bayan nasarar ta samu takejin daga ina ruwan ya fito,basu gaya mata ba gudun
kada taqi sha.
"Yau zata dawo?,daukota zakaje kayi?" Ta
tambayeshi sanda ya miqe yana soma takawa da murdadden harshenta.
A
mamakance ya juyo yana duban maamah din,wai yau ita ke tambayar dawowar
Sabreen?,wani farinciki yana sauka a zuciyarsa ya gyada mata kai.
"Eh,saura mintunan kadan jirgin ya sauka".
"A dawo lafiya" Ta furta tana jin wani dadi yana
mamayeta .
"Allah yasa" Ya amsa wata qwalla tana cika masa
idanu. Yau maamah ke masa addu'ar da alamu sun nuna kai tsaye suna fita ne daga
zuciyar ta?.
Sai daya
tsayar da jordan cikin motar ya daidaita kansa,ya kalli fuskarsa yaga ta koma
ainihin mode dinta sannan yace suje. Bayason yaje da wani sauyi ko kadan saman
fuskarsa,don yasan abune da tana masa kallon farko zata karanci hakan,shi kuma
duka yau din yana buqatar kyakkyawan yanayi shida duniyarshi,wadda yayi missing
nata tsahon kwanaki biyar kenan.
Cikin
hukuncin Allah JADDA MAJESTY JET ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama
na Nnamdi Azikiwe dake abuja.
Mintuna
kadan kafin jirgen ya sauke matakalarsa a hankali,tsakanin wasu mintunan kuma
mutanen dake da iko da jadda majesty din suka fara fitowa.
Da farko
wasu matane guda biyu masu baqar fata,giant dasu,sanye da baqaqen abayas da
mayafinta wanda sukayi rolling,sannan kuma suka manne idanunsu da baqaqe
glasses.
Mata
biyun dake bayansu su dinma abayanne a jikinsu,saidai tasu ruwan wine color ne.
Daya janye take da wata qaramar luxury luggage,yayin da dayan ke dauke da wata
kyakkyawar jaka.
Kyakkyawar halittar dake takowa daga tsakiyarsu ta dushe kowacce diya
mace dake tafiya tare da ita.
Mistress ameenatu ahmad mrs muhammad jadda......the lady of the house
itace ke takawa d'ai d'ai cikin wani yanayi da zai tabbatar maka da cikar
kamala da nutsuwa gami da kammaluwar hankali da nutsuwarta waje guda.
Sanye
take cikin wata Turkish gown ta wani lafiyayyen material,rigar ta bude sosai
daga qasa,armless ce butter color me adon gray color da wasu manyan flowers
masu ban sha'awa,wadda aka yiwa top gray color me dogon hannu da kuma sarqarta
a jikin rigar ta yadda basai ta buqaci wata spare sarqa ba.
Tayi
rolling kanta da gray color din wani exclusive veil,qafarta na sanye da wani
high hill daya kasance mahadin qaramar handbag din hannunta da batafi taci
qananun abubuwa ba sai tsananin tsada da jakar ke dashi.
Rungume
take da wata baby girl wadda ke sanye da gown armless fara qal data kasance
mahadin takalmin qafarta da kuma dan crown din dake saman kan yarinyar wanda ya
hana sassalkan dogon gashinta bazuwa zuwa sassan fuskarta.
Wani irin
kamanni ne tsakanin ta da yarinyar na sak da sak.......abinda kawai ya banbanta
su shine kasancewar yarinyar 'yar kululluba da ita.
Ameenatu
muhammad jadda kenan IFFA......shalelen family din jadda....diya mace qwaya
daya da suke da ita cikin villa din tasu. Chubby din abbee......chubby din
anni......kuma chubby din triplet da twins na jadda villa.
Cikin
kyakkyawar nutsuwar nan tata Madame kuma duniyar muhammad jadda wato ameenatu
ahmad ke sauka da takalmin ta me tsini wanda zakayi tsammanin ba zata ita
tafiya dashi ba,saidai caf caf take takawa da abinta cikin sani kan ado da gayu
daya ratsa jini da jikinta gaba daya.
Wani
fitinannen qamshi take fiddawa wanda ya huda jikinta,irin qamshin da sai kazo
kusa da ita kake iya jinsa a duk wani motsi da zatayi.
Dawowarta kenan daga qasar saudi Arabia,bisa gayyatarta da sukayi don su
karramata da lambar yabo da kuma girmamawa ta musamman kasancewar gidan
marayunta gida na farko da kaf nahiyar africa dama wasu qasashen qetaren babu
koda kwatankwacinsa.
Gida ne
daya fara bawa yara feature me kyau......ya fara inganta musu rayuwa da inganta
mafarkansu bisa jagorancin me gayya me aiki muhammad fu'ad jadda mamallakin
kamfani guda daya da baida kishiya dake sarrafa gold da Diamond a qasash kusan
arba'in cikin qasashen da muke dasu a duniya sama da guda dari biyu.
"Karbeta najma.....tayi bacci" Sabreen ta fadi a
nutse tana miqawa nanny dinta ita gami da gyara rolling dinta daya dan
cukuikuye.
"Sarkin rigima" Nanny din nata ta fada tana
rungumeta a kafadarta
"Kunfi kusa,fadanki dana iffa ko waye ya shiga ma kunya
zaiji" Sabreen ta fada tana murmushi.
Murmushin
daya samu isa ga idanuwan Muhammad fu'ad dake zaune cikin mota,ya kuma kori
Jordan ya saita madubinsa yana qarewa duniyarsa kallo abinsa.
Sam bata
ganshi ba,bata kuma san yana mata kallon qurillar nan tashi ba,duk da cikin
jikinta tana jin kamar wani kusanci yana wanzuwa tsakanin zukatan guda biyu.
"Welcome maa" Shine abinda dukka ma'aikatan da
suka rako boss jadda suke fada cikin rusunawa da girmamawa,yayin da ita kuma
take amsawa cikin nuna kulawa da tambayarsu aikinsu.
Abun yana
bawa fu'ad mamaki sosai.....gaba daya ta zama tamkar wata uwa tsakanin kowanne
ruhi dake rayuwa cikin jadda's villa. Ba iya yaran gidan su huda amna dasu
saddiq ba......tsakanin kowa da kowa ma,muddin kana kwana kana tashi a jadda's
villa.
"Wannan tsadajjen murmushin rabonshi da akeyi ya isa
haka please" Ta tsinci lallausan sautin nan nasa cikin kunnuwanta a sanda
ya fito daga motar yana bude mata murfin motar yana kuma gyara babbar rigarsa
da daya hannun.
"Wow" Ta fada da wani boyayyen sautin da labbanta
ne kawai zasu gaya maka abinda ta fada,tana fidda idanunta waje dukka a kansa.
"Muffin......ka koma exactly ranar da ka zama angon
ameenatu sabreen.......sak irin shigar".
" Har yau har gobe har kullum ma cikin taya kaina murna
nakeyi da mallakar mace irinki......ki taimakeni ki sakayamin kanki cikin motar
nan kafin mazan dake airport dinnan kaf su qarasa kallemin ke" Kai ta
girgiza tana dariya sanda ta fara takowa cikin jan aji.
"Hammana yaushe xai canza ne?baya kallon madubi yaga
yadda ya fara zama babban mutum?,babban mutum din daya ajiye yaran da sati me
zuwa zasu kammala secondary school dinsu?"
"Fu'ad bazai taba canzawa ba.....kishinsa da soyayyarsa
game da Sabreen suna nan kaman yau aka ginasu" Ya amsa mata yana rufe
motar,ya zagaya ya shiga nasa side din.
_wacce addua kuka yimin littafinnan yaqi kammaluwa a yau?_🥹🥹🥹🥹
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada
munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR
GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN
HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road
kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a
duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 173
*_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_*
*follow us diaries*🥰🥰👏🏽👏🏽
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1
173
Wani
ajiyar zuciyar numfashi ya sauke yana lumshe ido gami da sauke nannauyan ajiyan
zuciya.
"Sai yanzu zuciyata zata koma aiki daidai......welcome
home your royal highness" Ya fadi cikin salo na girmamawa yana hada
hannuwansa guri guda. Murmushi tayi tana girgiza kai,kullum sabuwa ce a wajensa
kaman yadda yake sabo a wajenta.
"Giya nake roohi......hayaty kulliha" Ido ya fidda
waje yana tashin motar tasa.
"Wannan ranks din nifa bana gane musu sosai
yanzu.......jira nake naga nan gurin ya tasa" Ya fada yana taba lafaffen
cikinta kaman bata taba daukan ciki ba.
Itama waro
idon tayi tana kallonsa. Mamaki yake bata yadda har yanzu 'ya'ya basu isheshi
ba,yara goma cas tara dukkaninsu maza mace daya?,me kuma yake da buqata?.
"Muffin......fauzan fawwaz da fawad ba graduation dinsu
next week immediately ana gama bikin nadra da haneefa?". Dubanta kadan
yayi sannan ya tada motar hankalinsa kwance.
"What's that supposed to mean? And what's the
point?......kin daina haihuwa?". Ganin yadda yayi maganan yana nuna da
gaske yake fadi,saita karya wuyanta tana narke masa.
"Hamma......yanka sau hudu fa?...."
"Yanka hudun yana nufin kin gama?" Ya sake tambaya
yana tsume fuska. Sosai tayi calming down kanta tana saukar da kanta.
"Ni na isa?" Ta fada a sanyaye. Wani abu data lura
dashi yana da bala'in son tara yara,Allah ya taimaketa ya dinga bata bibbiyu
har sau uku bayan ukun farko da tayi,iffa ce kawai tazo ita daya abinta,shi
yasa idan suka tashi tsokanarta suke cemata me baqinjini,ita ba wanda ya
rakota,su kuwa saida suka rako juna,duk da cewa a zahiri kusan farinjininta
daban yake,kowa yasan wannan,farinjinin diya mace cikin yara maza.
Shurun da
tayi ya sanyashi satar kallonta kadan sannan ya kauda kai,bayason damuwa a tare
da ita sam sam,don ta gama yi masa komai a rayuwa.
"Bani labari.....How'd the trip go?". Numfashi ta
sauke tana son wadata fuskarta da murmushi,saidai kafin tace komai ya sake
magana.
"Banga mamana bafa.....a ina kika barta?"
"Tana hannun Nan najma(kaman yadda iffa din take
kiranta)" Kai ya gyada
"I missed her so much......da safen nan abinci sam
bayamin dadi idan na kalli gurin xamanta naga bata nan". Baki Sabreen ta
tura tana bata fuska.
"I don't know me yasa kakeson min kishiya da iffa
ne.......zan bayar da ita fa?". Ido ya waro kaman zai saki steering motar
yana dubanta.
" What?,yarona ko daya bazan iya badawa ba koda cikin
gari ne dani......in fact ma ni koda mutuwa nayi ban yarda a rabamin yara ba
bare ina raye".
"Mu ajiye batun mutuwar nan hamma....." Ta fada
tana maida aljihun motar data bude ta dauko mint sweet ta saka a bakinta.
"Komai ya tafi daidai hamma......kuma dukka lambobin
yabo dana karramawar da suka bayar naka ne....kaine ka cancancesu......ni 'yar
tayi ce,Allah yakai kadan kabarin abba.....sun saka kudade masu yawa a asusun
gidan,duk da nace bamu da buqatar wannan,amma sunce zasuyi don neman
lada,sannan cikin daliban da muke yayewa duk shekara,a dinga ware mutum
goma,maza biyar mata biyar yearly zasu dauki nauyin karatunsu har zuwa
degree,har masters ma idan suna buqata har sama da hakan". Kai yake
jinjinawa,ya jima yana ayyukan lada dana alkhairi kala daban daban,amma wannan
din yafi kowanne yi masa dadi da qara masa walwala da nishadi. Uwa uba kuma
wani abu daya lura dashi,tun daya sanda gidan ya fara aiki dukiyarsa kaman amai
take,wani irin mahaukacin hauhawa takeyi,wani irin bangajejen budi yake qara
samu da shi kansa kai tsaye yanzun bazaice ga adadin abinda ya mallaka ba.
Ci gaba
sukayi da tattaunawa shi da ita da wani irin yanayi da zai gaya maka zallar
soyayya da tausasawa da jin qaine ke wanzuwa tsakanin ruhi da zukatan wadannan
masoyan.
Suna isa
ya karbi mamarshi ameenatu iffa,don ta farka a sannan. Ita dinma da gudu ta
nufoshi tana fadin.
"Miss you abbee...."
"Mamana.....My incomparable mother.....a mother without
equal" Ya dagata yana juyata abinsa,ba ruwansu shi da ita da al'ummar dake
farfajiyar gidan,wadanda kusan dukansu sun fito ne saboda tarbar Sabreen
din,wanda wasu lokuta suke mata title da THE MISTRESS OF THE VILLA.
K'ananun
shekaru gareta amma ta zama babbar qarfi da yaji cikin gidan,duk da ta tasamma
shekaru arba'in daidai a duniya......amma tsananin kula da kai da gyara jiki da
kuma shan natural abubuwan gyara ga diya mace ya sanya zaka yita daukanta a
shakarunta ashirin da biyar ko da takwas take. Bugu da qari idan ka kwatantata
da su anni da suka kasance manya a gidan,ba laifi idan ka kirata da yarinya.
Kusan duk wani dawainiya da matsaloli da zaa kaiwa annin ta hana isarsu
Gareta,ballantana maamah da ba cikakkiyar lafiya gareta ba,yau da lafiya gobe
babu.
Girman ya
karbeta da kyau,yadda ta tafi dashi kuma cikin adalci da mutuntawa ya sanya
kowa yake biye da ita da tarin qauna.
Ko a wajen
bata wuce ba sai data duba lafiyar duka ma'aikatan,fuad na biye da ita dauke
iffa yanata shan surutu,daya hannun nasa kuma handbag dinta ce. Wannan dabi'ar
tasa kowa dake jadda villa ya santa,tun suna kunya har ya zame musu jiki. Ko
zaman kwana uku kawai kayi cikin villa din zakasan cewa akwai wata mahaukiyar
soyayya irin ta hanta da jini a tsakaninsu.
Tare suka
jera cikin gidan bayan gamawa da ma'aikatan yana tsokanarta.
"Hajjaju da kanta......yau masu gidan sun dawo kowa ya
shiga saitinsa" Yayi maganar yana maqalewa a bayan fuskar iffa yana mata
gwalo. Murmushi ta saki tana mintsinar hannunsa.
"Ka daina mantawa fa da cewa yanxun baban samari ne
kai.....in suka ganka kana tsokanar ummensu tabbas xakaji kunya".
"Suma sun jima da sanin cewa ba'a raba hanta da
jini......yadda nakeso susan zallar madarar soyayyar dake tsakanin abbeensu da
ummeensu alhamdlh sun fahimta" Kai
ta gyada,ita kanta tasan da hakan,hakan kuma ya taimaka sosai wajen bawa yaran
qwaqwalwa da rayuwa me kyau,hakanan kuma suma sai suka tashi da qaunar junansu
sosai.
"Banga kowa ba cikin dukka yaran gidan nan
ba.....sauban dai ancemin yana gurin anni".
"Kin rigani fade ne......duk da kaman su nadra sun tafi
siyayya dasu sahl samr suhail duka sun bisu". Murmushi ta danyi tana
jinjina kai,tana sake jin rayuwarta tayi mata dadi idan ta tuna yau zata aurar
da nadra da haneefa gaba daya,ragowar abinda ya rage mata kenan take addu'ar
Allah yakai mata ranta.
"Kaman yaushe zaku fara bikin nan?" Fuad ya
tambaya sanda suke dab da isa sassan maamah. Umarnin anni ne,duk sanda suka
dawo daga wata tafiya ko kuma suka tashi da safe zasu shiga su gaisa ita ta
yafe zuwan farko,su fara zuwa wajen maamah tukunna su dubata.
"Don itace me lalura,tafi buqatarku a akaina,ni da
lafiyata har yanzu da sauran qarfina.....kuma alhamdulillah zan iya yiwa kaina
komai"
"Hamma abubuwa kadan zasuyi fa......zasuyi the day of
qur'an da dalibai da malamansu na mu'assas.......then zasuyi bridal
shower.......sai waleema da anni ta shirya shikenan,dukkansu suda mazan basason
dogon biki". Kai ya jinjina,yana jinjinawa yaran,suna da wani irin hankali
da nutsuwa na daban,komai nasu moderate ne,shi yasa ya yuwa rayuwarsu wani
tanadi na musamman da ba wanda ya sani sai ranar da aka daurawa kowaccensu
aure.
"Ma sha Allah.......Allahumma barik" Ya furta suna
sanya qafa makekiyar balcony din da zata sadaka da falon.
Idanunta
akan tashar saudi sunnah da suke hasko masallacin ma'aiki tare da karanto
hadisansa masu tsarki girma da alfarma,zuciyarta takejin tana tsananin kewa da
qishirwan gurin,kaman bata taba zuwa ba tunda take a rayuwarta. Sukanje tana
bin jama'ar gidan da suke da kebantattun lokuta da jirgin jadda majesty jet
yake jigilar kowacce halitta dake birnin jadda villa din bayan kowanne hutun
makaranta da za'ayiwa yaran. Wannan damar suke amfani da ita suke ziyartar
fauzan fawad da fawwaz dake karatunsu a madeena king Abdul'azee international
School wadda suka kammala kuma za'ayi bikin yayesu sati me zuwa.
Kaman
saukar nannauyan dutse daga qirjinta haka taji sanda sukayi sallama a tare,ta
motsa bakinta tana amsa musu da sautin da ba'a fahimtar abinda take fada sosai
sai wadanda suke da matuqar ganewa kaman sabreen din,don shi kansa fu'ad din
sometimes sabreen ce ke gaya masa abinda tace din.
Idanunta
ta janye a kansu tana maidawa kan yarinya ta biyu da Allah ya jarabceta da
masifar son yarinyar......yarinyar da duk gidan kowa qaunarta yakeyi saboda
kasancewarta jika diya mace qwaya daya kaf cikin jikokin gidan ashirin da wani
abu. Ameenatu iffa ta sakarwa maamahn murmushi tana zamewa daga jikin fu'ad ta
tsallako da gudu tayo wajen maamah.
"Har yanzu baki tashi kin fara tafiya ba?,kikace zaki
fara tafiya kafin mu dawo?" Ta fadi cike da quruciya cikin maganarta.
Murmushi kawai maamah din ta sake,yarinyar ta tattaka qafafun maamahn ta haye
cinyarta tayi dare dare tana bata labarin su hamma fauzan suna gaisheta.
Tayi kewar
'yan ukun sosai,su na dabanne a zuciyarta,duk da gidan cike yake da tagwaye
amma nasu qaunar daban yake. Har yanzu
suna iya kira video call su dukka ukun su sakata a gaba da hirarraki har
sai sun sakata dariya sanna,har zaman jiran kiransu takeyi kulli yaumin,koda
basu kira ba zata sanya a kira mata su.
"Barka da warhaka maamah.......ya qarfin jikin?".
" Alhamdulillah " Yau sautin amsa gaisuwar sabreen
din ya fita da kyau har sai da sabreen ta daga kai ta kalleta a mamakance.
"Ya taro?" Ta fada da sarqaqqen harshenta.
"Alhamdulillah.....mun kammala cikin nasara"
"Allah ya taimaka" Ta sake fada da qyar tana
fuffusgo kalmar.
"Ameen" Sabreen ta amsa tana sadda kanta tana
tattalin hawayen farincikin dake son ballewa cikin idanunta.
Kamar
yadda maamah ta zata din,sabreen din saidata tabbatar komai yana tafiya daidai
a sashen,daga masu kula da ita har kalar abincin da ake bata sannan suka wuce
sassan anni.
Suna
zaune da mutuminta sauban a courtyard din da ya zamana shuru saboda fitar duka
yaran da rashin motsinsu wanda anni batasan me ya kawo hakan ba.
Murmushi
ya sakarwa ummeen nasa da abbeen nasa,ya zare headphones din ya ajiye ya tako
da nutsuwar nan tasa yana fadin.
"Sannu ummee.....abbee sannu" Ya fada yana kamo
iffa wadda tayi tsalle ta daneshi. Akwai sabo sosai tsakaninsu,don wani irin
sassanyan kulawa yake bata ta hankali.
"Anata karatun sauban?" Sabreen ta fadi bayan ya
gama gaidasu,fu'ad ya dora hannunsa saman kansa. Yana jin yaron sosai a jininsa
saboda yadda yake da maitar karatu,yana da buri sosai akanshi,kowanne yaro
nashi yana bashi karatu daidai da abinda ya fuskanci yafi karkata
akai.....kaman yadda ta fannin neman kudi ma yayi alqawarin zaibar kowa yayi
kalar neman kudin da yafi sha'awa muddin bai sabawa addini ba.
Da wani
irin alfahari qauna da soyayya anni ke kallonsu a gabanta,har suka gama gaisawa
suka fara taba hira
"Kije ki huta takwara,anjima akwai general dinner a
babban dining room na gidan nan,sai a qarasa hirar a can" Murmushi tayi a
kunyace sannan ta miqe,fu'ad ya tayata da jakar suka rankaya dukkaninsu wannan
karon har sauban suka fice.
Tun kafin
sukai ga bude qofar sassan taga kaman parlor din farko yayi duhu da
yawa,bangaren sitting room ba ba wani wadataccen haske. Tanata so tayi magana
amma kuma Allah bai bata iko ba har sai da suka shiga parlor din.
Duduun ba
wani haske,abun da ya basu mamaki kenan daga ita har fu'ad din,ta bude baki
zatayi magana fitilan farko ta kama. Harafin H ne tafkeke,mamaki ya
cikata,zatayi magana A ta bayyana,da wani irin sauri P ta bayyana a jejjere
ragowar suka kama suka bada cikakken sunan HAPPY WEDDING ANNIVERSARY.
Baki sake
take kallon harufan,ta juya a hankali da zummar yiwa fu'ad magana ko yaga
abinda take gani,sai gaba daya wutar falon ta kunnu hade da wasu abubuwa masu
walwali da suka soma bude kansu da kansu daga jikin fitilun suna watsuwa a
kansu,lokaci guda kuma muryoyin zuria'ar yara na jadda din ta hadu wajen fadin
"Happy wedding anniversary" Sai a sannan suka
ankara da komai da tsananin mamaki. Ameen,Amaan,hilal dan huda na fari,naseem
dan amna na fari,sai yaron wajen farouq na farko shima Aleem,sai tagwayen
sabreen na biyun masu bin su ameen Aabid da Aadil,sai wasu twins din masu binsu
Aadil din,irfan da farhan wadda ameenatu iffa ita ta zama cikon ta gomansu.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN
NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA
MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU
DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA
DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN
DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA
WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA
INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN
BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 174
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA
CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da
babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu
ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
174
Yara
ashirin da daya ne idan ka dauke mutum biyar dasu nadra suka fita siyayya
dasu.......sai fannah da huda dake tsaye
a bayan yaran da alama su suka tayasu hada wannan surprise din. Inda Allah ya
kawo ma sauqin abun amna bata nan,tare suka fita siyayyar dasu nadra tabbas da
abun sai yafi haka.
Kasa
magana sabreen tayi,harga Allah tana sane da yau dinne suka cika shekara goma
sha shida da aurensu,amma bata kawo zatayi wani abu da wani zai gane ba illa
tsakaninsu ita dashi,sai gashi yaran sun rigata aiwatar da komai.
"Ku ko?" Sabreen ta fada tana nuna fannah da
huda,fanna din da amnar da dukkaninsu zuwa yanzu tana jinsu tamkar uwa daya uba
daya suke. Tana nunasun da yatsa tana murmushi sai kuma kukan farinciki ya
barke mata,ta aza kanta saman kafadar fu'ad din tana matsar qwalla.
Irin wannan
soyayya da suke gwada mata batasan wacce iri bace,bama ita ba.....kusan
dukkaninsu ba zaka tantance wane da wane ga daga inda suka fito ba. Rankatakaf
jikokin gidan dama iyayensu kallon uwa suke mata,kuma hakan baya rasa nasaba da
yadda ta riqesu kaman ciki dayan suma fito.
A cikin
yaran ba wanda bata taba rainonsa ba,duk itama tata bataliyar,duk kuma da cewa
kusan kowanne yaro yana da nanny dinsa a gidan,sai wanda suka kai shekarun
girma irinsu ameen sannan ake barinsu su koyi rayuwa da hidimar rayuwar data
zamewa kowa ya koyi yiwa kansa.
Idanun
yara kawai ya hana ya rungumeta,amma qasa qasa yake fadin.
"Karki bata fuskarki,karki kashe mana farincikin
yau" Ya fada yana dan bubbuga bayanta.
"Kita fatan muci gaba da irga wadannan shekarun
tare" Abinda ya rada mata kenan.
Qaramin
walima akayi a gurin da kayan maqulashe kala kala,kuma abunda ya bata mamakin
shine,koda autar gidan iffa wadda tare suka shigo gidan sun tanadar mata gift
din da zata bawa daddy jadda (yadda gidan suke kiransa kenan in general idan
ba'a sassansa bane).
Farinciki
da walwala ne kawai ya wanzu a gurin,inda daga qarshe dai bata haura samanta ba
kota wuce sassanta ta lalace a nan tana tsakiyar family din nata suka zarce da
hirarrakin bikin da zaa fara jibi jibi.
Wayarta ta
ciro da zummar kiransu nadra taji inda suka dade haka da yawa sai taci karo da
tarin miscal din jadda. Ta zaro ido tana mamakin tun yaushe yaketa kira bataji
ba?,saiga shigowar wani kiran nasa.
"Sabrrrr" Kawai ya fada a narke,take ta fahimci
yana buqatarta a kusa dashi.
"Banda abun hamma.....awa daya kawai ya rage ayi
magriba fa?" Ta fada cikin mita tana tura katafariyar qofan master bedroom
dinshi.
Bata
gama ajiye qafarta taji an ficikota ciki,a zafafe ya manne bakinsu guri daya ba
tare daya jira komai ba.
Har
kullum har ko yaushe har kuma abada mantawa takeyi da shekarun dake wuyansu
idan suna tare da jadda din. Wani irin mutum ne dake da baiwar narkar da
zuciyar diya mace ya kuma mantar da ita komai. Abinda yayi imani dashi
shine,yadda kowacce diya mace a kullum take fadi tashin neman hanyoyin faranta
ran namiji da burgeshi,haka ya kamata kowanne namiji shima ya kasance cikin
sanin hanyoyi da salon mallake zuciyar matarsa......wannan dabi'ar tasa ta sanya
yayi zarra a zuciyar sabreen din.
Sai data
tabbatar ta samar masa da nutsuwa sannan ta baiwa kanta hutu tana aje
numfashi,ya birkitota yana maqaleta a jikinsa bayan sunyi alwala sun dawo.
Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kafin daga bisani taji saukar numfashinsa a
hankali bacci me cike da nutsuwa yayi awon gaba dashi.
Sai bayan
sallar isha'i ta samu saukowa daga wajensa,a lokacin ya fita sallar isha'i,da
wannan damar ta samu tayi wanka tayi kwalliya kuma cikin atamfa kaman yadda ta
saba idan zasuci abinci nasu duka.
D'as d'as
take takawa kaman ba wannan jikin bane ya fidda rai goma ba,har ta iso babban
parlor din da anan aka gina katafaren dakin cin abinci.
Ta samu
kowa yana gurin,kowa kuma yasan mazauninsa yana kai a zaune,sauran wadanda basu
hadu ba sai a sannan irin musaddiq saddiq da farouq duka a nan suka gaisa suna
tayata murnar ci gaban da aketa samu.
Kowa ya
hallara kuma faud din ake jira,shine qarshen shigowa,yana takowa a nutse da
wata irin haiba da kwarjinin da ya qara yawa sanadin shekaru da kuma riqo da
addini da yake dashi,kwarjinin da yake hana mutum musu dashi ko yin abu ba
daidai ba,kwarjinin da hatta sabreen a yawancin lokuta yakan daketa duk kuwa da
cewa dazu dazu suka rabu a daki cikin wani sirrintaccen yanayi,amma yanzun data
kalleshi kwarjinin nan ya dawo fes saman fuskarsa.
Kusan
yara yaran a tare suka gaidashi,su sabreen huda fannah da amna suka fara
serving na kowa da kowa a nutse ba wani hayaniya kaman ba taron mutum kusan
talatin ba.
Cikin qauna
da tsabar sabo da juna suke cin abincin,hirarraki suna gudana a tsakaninsu. Har
yau har kuma gobe yana maintaining class dinta a idanunsa,bata duba an dade
tare.....an jima da juna ta dinga wasu abubuwa da babu aji sam cikinsa a wajen
diya mace( mata yana da kyau ku kula da wannan,stay classy please,karki dinga
abu gaban miji wargazaza koda shekara dubu kukayi ki tabbatar masa ajin nan fa
akwaisa,idan ba haka ba ya hango wadda bata kaiki ba nata ajin ya dinga dibansa
yana burgeshi).
Shi dinma
satar kallonta yakeyi,yanason gano meye ya banbantata da sabreen din shekaru
goma sha baya?. Ya dade yana against in din maza da yawa akan suna da babban
laifi da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen wargajewar matansu,mace 'yar
tattali ce.....'yar a bata kulawa ce,mace tamkar fure take,dole idan anaso aci
gaba da ganinta sharshar a tsaya mata da ban ruwa,wato cima sutura muhalli abun
sha me kyau,a debe mata damuwa daga zuciyarta.
Ta samu
daman zama da amaren nadra da haneefa har kusan sha daya na dare,don shima sun
kebe dasu musaddiq suna tasu tattaunawar,har suka kammala ya dawo ta parlor
din.
Daga
tsaye yake dubanta da lumsassun idanunsa,hannayensa cikin aljihun rigarsa.
"Madame.....baa kammala bane?".
"Saura kadan hamma" Agogo ya kalla sannan ya sauke
dubansa.
"Kubar addan nan ta huta mana.....da safe sai a
qarasa" Dariya nadra da haneefa suka saki suna miqewa gami da tattare
kayan da take dubawa,haneefa tace
"Hamma babu ruwanmu fa,tun dazu mukace mata xamu qarasa
gobe tace yau xaa gama.....saida safe" Ta shilla da dan qaramin gudunta
tana bin bayan nadra da tuni ita ta fece.
Ta dawo da
idanunta daga kan haneefa tana murmushin wai auta itace yau da aure?,saiji tayi
kawai anyi sama da ita.
Wutsil
wutsil ta fara yi da santala santalan qafafunta kamar qaramar yarinya.
"Hamma......please mana,kada wani ya ganmu mana?".
"Who cares?" Tunda taji ya fadi haka tasan zai
wahala ya sauketa idan ba fita sukayi ba,don haka ta kwantar da kanta saman
qirjin da duk duniya yafi mata ko ina dadi da samun cikakkiyar nutsuwa.
★Kwanaki uku
kacal da dawowarta aka fara bikinsu nadra din,iya events din data fada din
kusan haka aka yisu. Saidai fa tun ranar bridal shower fu'ad din bai sake
barinta taje komai ba,saboda wani irin sassanyan kyau da tayi me daukan hankali
cikin wata butter color gown ita da iffa da tayi order dinta tun daga
Egypt,tana yawo kuma da tag din bride sister daya sake bata ranshi. Lallaba
kayanta kawai takeyi,tasan halinsa sarai a kanta baida sauqi,ta samu ta saukeshi
ta kuma kiyaye dukka dokokinsa har aka gama bikin lafiya. Saidai ko bayan bikin
still mitar bridal shower day din ya dinga mata,saida ta samu ta bashi wani
zazzafan dare guda daya sannan ta wanke kanta.
*_GRADUATION DAY_*
*@KING ABDUL'AZEE INTERNATIONAL SCHOOL*
Triplet
din 'yan qasa nigeria kuma haifaffun qasar madeenatul munawwara......wasu irin
yara ne da sunansu dasu kansu sukayi fice cikin makaranta dama wajenta. Bawai
don kawai farinjinin 'yan uku ba.....aah hatta da kaifin basira da Allah ya
zuba musu,matsanancin nutsuwa da sanin ya kamata.....inda daga qarshe kuma suka
zama dalibai madiya hazaqa da qoqari cikin daliban da makarantar ta fitar.
Sanda
makarantar ta tasosu ta tsaidasu saman stage tana wassafa kyawun dabi'u da
hazaqar yaran sai sabreen ta kasa daurewa,ta kifa fuskarta tsakanin tafukan
hannayenta tana jin wani irin alfahari da yaran da kuma qaunarsu tana
ratsata.......wani irin farinciki da batasan yadda zata misaltashi ba na kyauta
da baiwar yaran da Allah yayi mata,wanda a yanzun haka cikin amsa kuwwa ake
sanar da kowa cewa su din cikakkun 'yan qasa ne.....gwamantin saudiyya kuma sun
dauki nauyin komai da komai nasu saboda girmamawa da jin dadin yadda suka zauna
da kowa cikin makarantar dama qasar lafiya.
Da
qyar ta iya isa tsakiyar yaran nata don karba musu kyaututtukan karramawa da
suka samu,duk da jikinta a lullube yake kirif,baka ganin komai nata sai
zagayayyar fuskarta,amma duk da haka wasu sun cika da mamakin cewa itace
mamansu. Tun tana iya amsa har gifts din sukafi qarfinta saida jadda dake sanye
cikin wata rantsatsiyar shadda ya tako da sanyin nan nasa da nutsuwarsa ya
tallafeta da wasu kayayyakin.
Ranar wata
rana ce da bazata gushe ba a zukatansu,cike da tarihin da bazai kankaru ba
cikin rayuwarsu.
Already
sun tsara ana kammala taron zasu koma makka su sauke umra gaba dayansu,saboda
nuna godiyarsu ga Allah da kuma sake roqon ubangiji ingantacciyar rayuwa me
dorewa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI
WANNAN NUMBER_*
08187255862
*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada
munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR
GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN
HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road
kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a
duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 175
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA
CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da
babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu
ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*👇🏾👇🏾👇🏾
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1
__________________________
175
A maimakon
jirgi a babbar lafiyayyar mota suka taho zuwa makka. Wata irin tafiya ce ta
iyali me dadin gaske,hirrraki da labarai duka sun cika motar dake dauke da
JADDA FAMILY.
Saidai
duk da hakan daga can seat din baya ita da fu'ad ne zaune,tadan dora kanta
saman kafadarsa tana jin kasala da wani saqe saqe da cikinta yayi mata wanda
batasan Meye dalili ba.
A fili
kuwa hotunan graduation din take kalla daya bayan daya. Duk inda zata wuce
fu'ad da yaran sai tayi zooming ta kallesu sosai,tana jin kaman ba yaranta
ba,kaman wani imagination ne a cikin duniyar mafarki ma,har sai da fa'ad daketa
sauraron shirmen yaran daga gaban motar yana murmushi kadan kadan ya ankara da
ita.
"Kina mamaki ne?" Kai ta daga ta kalleshi sannan
ta maida saman kafadarsa.
"Ina mamaki mana hamma......yau sabreen da kowa ke mata
kallon KARUWA da yara irin wannan?,sabreen din da kowa ya gaza janta a jiki
yaji meye damuwarta,meye kuma uzurinta yau ita keda yarannan?......sabreen din
da tafi kowacce yarinya nutsuwa da hankali saboda ita din rainon ummee ce yau
ta zama haka meye sila?,ba hujja ba dalili sai yanke hukunci babu
bincike". Bata tsaya jin ta bakinsa ba ta dora.
"Alhaji ahmad me citta shine asalin sunan
mahaifina,wanda ya shahara da sana'ar saida citta kanunfari da sauran kayan da
suka danganci wannan da wasunsu ma daga qasar larabawa ake shigo musu dasu.
Abbana ya auri ummeena ne a sanda yake da matan aure biyu da yara mata goma sha
biyar,ummena ce ta uku,mace me tsananin haquri da kawaicin daya sanyata taci
nasarar zama da sauran matan abbana,wanda cikin su take da babbar abokiyr adawa
wato bibo,wadda ita ummee ke bi. Abban mu ya tsaya sosai a kanmu,shanmu cinmu tarbiyya
da iliminmu,don har yanzu tasirin dagewarsa ce a jikina na ilimin dana samu
daga private school daya sakamu me tsada,tun daga matakin free nursery har
secondry,duk da cewa ina js 3 abbanmu ya koma ga Allah,ummenmu itace ta jajirce
naci gaba da wannan makarantar har na shiga ss3 second semester,a lokacinne
Allah yayi mata rasuwa,a lokacinne asirinmu ya tonu,maraici kuma ya afko.mana
gadan gadan,ummenmu ba 'yar qasar nan bace,don haka bamu da kowa a kusa damu da
zai tallafemu. Sh momma sunso tafiya damu amma kawu ya saka kuka,wai ya za'a
tafi da zuri'ar ahmadu yana raye?,shi yayi alqawarin kula damu kaman yadda
abbanmu ya kula da rayuwarsa. Abbanmu ne ya riqeshi bayan rasuwar iyayensu tun
auren abban ma na fari,bai kuma qyale kawu ba sai daya aurar dashi ya hadashi
da jari yana saka ran wasu halayensa da bayaso zuwa sannan kawun ya dainasu. Da
wannan yaqinin suka barmu hannunsa,ashe kuma lokaci lokaci suna masa aike da
sunanmu,amma ko labari bai taba bamu ba bare muga abinda suka kawo.
....... Tom ko bayan mutuwar abba kowacce mace ita ta koma
hidimar kanta da kanta,to yanzun da bamu da uwa sai ya zamana ba wanda ya damu
damu,ba wanda yake dubamu,ba wanda yake damuwa da munci bamu ci ba,munsha ko
bamu sha ba,mun tashi lafiya?,waye baida lafiyar?,dukka ba wanda ya saka hakan
a tsarinsa. Da farko na dauka abun na wasa ne,na dauka zasuji qanmu,saina fara
nema mana abinci daga dakunansu kafin na fahimci ba wanda zai iya cida mu,don
da zagi nake fita a dakin da qyama da tsangwama,daga bisani dole na koma
roqarwa su huda a maqota,donni ban damu naci ba,muddin sukaci shikenan tawa me
sauqi ce,zan iya kwana uku ma banci komai ba,saidai nasha baqin ruwa na kwanta.
Sannu a hankali suma maqotan suka fara hanani,sai ya zamana mun qarasa
galabaicewa,ciwon yunwa yanason kama huda da haneefa da bata gama sanin ma me
ake ba idan yunwar taji ba. Ba wanka ba wanki don ba wanda zai bamu
sabulu,saidai da yake ummenmu ta saba mana da tsafta hakanan mukeyi da zallar
ruwa.
Maqociyarmu kuma qawa ga bibo ita ta fara bani shawara.
"Kina da kyau sosai sabreen,kaf gidanku ba yaro me
kyanki.....me zai hana ki tallata hajar jikinki?,wallahi abinci ma saikun bawa
wani" A ranar hankalina yayi mugun tashi,mukayi uwaka ubaka da ita,kaf
kimarta ta zube a ido na,ita kuma ta kamani tamin shegen duka akan na mata sata
kuma na mata rashin kunya. Ba wanda ya damu yaji ba'asi saboda basa sonmu bamu
da gata,saima tayata da bibo tayi,haka nayi kwana uku kwance ina zazzabi ba
magani a dole na warke. Sanda naga yunwa na neman rayuwarmu saina fara da tambayar
alhaji baqo,aboki na kusa ga mahaifinmu wanda nake kyautata zaton zai iya
taimaka mana" Shuru tayi tana hadiyar wani abu me ciwo.
"Saidai abun mamaki abinda kuma ko yau na tuna yakemin
ciwo,ya nemi yaci amanar amintaka,ya nemi na bashi mutuncina yaci gaba da ciyar
damu duka. A nan ne naci masa mutunci saboda mamakin daya bani,kamar yadda
mukayi da waccar matar shima duka yayimin ya hadamin da sharri,abu na farko
daya fara qeqasarmin da zuciya,na fahimci kaman ba wanda zaiji tausayinmu a
unguwar,binda yasa na kasa mantawa ko yafewa,na koma na kunna masa gobara a
dakinsa data jaza masa asara me yawa,ya gano nice,yace zai kaini ga 'yan sanda,na
gaya masa ina da shaidar cewa muddin ya aikata haka ni kuma nizan babbake
gidansa duka da 'ya'yansa da matansa,abinda ya sakashi haqura kenan,tun daga
ranar idan na ganshi sai tsaki habaici da tsartar da yawu,sai duka ya tsargi
kansa yana tsoro kada na tona masa asiri,sai ya koma kaman sirikina. Daga nan
saina fara yawon nema mana abinci,duk da ba cikin kyakkyawar kama nake ba,amma
duk wanda ya ganni ringidi ringidi zai jani ya kaini gun cin abinci a
zubamin,saina juyewa su huda a leda,sukance ki cinye,indai kin bamu hadin kai
lallai abinci saikin ture. Mutun na farko daya fara nunan me hakan yake nufi na
samu na gudu ina zaginsa,akayi na biyu na uku na hudu na biyar shida har
goma,duk wanda yaga bazai samu abinda yakeso ba saiya qwace abincinsa. Maza da
yawa haka muka dinga yi,abinda ya sake dasamin duniya ba imani.....babu me
taimako don Allah sai don wani abu na daban,dana fahimci haka saina fara
tunanin ta yadda zan amfana da kudadensu ba tare da mutuncina ya tabu ba.
.....salis shine
mutum na farko dana fara gwada hakan a kansa,na saka masa maganin bacci a
lemo,na kuma debi kudade masu yawa na gudu. Wannan kudin su suka fara canza
rayuwata,na siya mana abinci me yawa,suturu da komai na fara kwalliya muka fita
daga qazanta.
Da bincike
salis yasa aka samoni,aka kamani,kamun da dashi bibo tayi amfani ta fara
bugamin tambari da batamin suna,tunda tana baqinciki kwana biyu muna cikin
abinci da duk kayan wadata na rayuwa,saita saka idon lallai sai tasan inda na
samo,saiga case din salis.
Sanda ake
tuhumata na kasa bada amsa,na tsinci dai wata murya tana cewa.
"Ku saketa fa,nine shaida bata da laifi,ya cinye
kudinsa ne kawai zai laqabawa wata" Wani matashin dan sanda ne ya fadi
haka. Wannan shine jib,silar haduwarmu kenan,mayen computer na gaske da salis
da yake kawunsa yaqi taimaka masa da registration a shekarar qarshe da yake
ciki saboda rashin kirki,wannan ya sanyashi rasa damar karatunsa,da cuku cuku
ya samu aikin dan sanda da qaramin albashin da bai wuce ladan ganin ido ba.
Haduwarmu
uku da jib magana ta hadamu. Shima maraya ne,banda wanda nake gayawa damuwata
amma ganin kirkinsa da yadda da nayi da nutsuwarsa a ranar mukayi dogon hira
dashi.
"Basa taimako Don Allah,ni shaida ne.....amma idan basu
taimakemu don Allah ba,zamu diba ta qarfi da yaji" Da taimakonsa muka soma
gudanar da plan dinmu,ranar farko na fadi,aka biyo sawunmu,Allah ya hadamu da
busari ya daukoni kyauta,wanda tun daga ranar ya zama dan adaidaita sahuna,daga
baya bayan uban gidansa ya qwace abun hawansa,na hada dukka kudina na siya masa
wata,sanadin haka kwananmu biyu ha abinci,saboda shi dinma marayanne,kuma shike
daukan nauyin tsohuwar mamarsa wadda shi kadai Allah ya bata a duniya"
"Sannu a hankai aikinmu ya dinga tafiya daidai,indai
zan fita sai nayi nasara,ina yin nasara ina gane cewa maza babu Allahba
ransu,wasu mazan sukan daukaki matan bariki su wulaqabta iyalinsu,wasu mazan
kuma saidai ki bada jikinki su baki kudi,don haka mukayi tsare tsaren da duk
wayonka bani zuwa gurin da kakeso,saidai na sameka a guri public mu qarqareta a
nan,na zare kudin ta hanyar taimakon jib dake sarrafa na'uarar,daga ranar kuma
ba zaka sake jina ko ganina ba,bazan sake kuma zuwa duk wani guri da muka taba
haduwa dakai ba. Nasha samun barazana amma Allah ya kiyeyeni,ban taba yarda ko
farcena wani namiji ya tabamin ba duk kuwa iya wayonka,wanda ni nasan hatsari
na saka kaina me girma,ba wayona ko dabarata bane kuma ya qwaceni ba,zuciyata
akwai Allah ya duba.
Duk namijin
da zan hadu dashi ina fara karantarsa,adadin son matanka da
fasiqancinka.....adadin barnar da zaka gani a dukiyarka......akwai nutsasun
maza daidaiku dakeson aurena da tun tafiyar farko nake zamesu daga gareni
saboda basu cancanci na cutar dasu ba,amma kuma bani da wani nufin aure kai ko
sha'awa ma baya bani.....mazanma dukkaninsu haushi suke ban,saina sallamesu
salin alin duk iya nacinsu kuwa.
Yadda nake
shiga me kyau nake fita da yadda duk wata buqata nake sauke mana ita ba tare da
anga ina sana'ar komai ba sai bacin suna yahau kaina......yayin da shaidar zur
dasu bibo ke qarawa 'yan waje ya sake basu qwarin gwiwar yadda da komai a
kaina,ban damu sosai ba sai dana qara hankali,amma damuwata ta dadu qwarai
sanda naga suna qoqarin brainwashing ma su hud akan qazafin karuwanci da zina.
Kudi suka
fara shigowa har suka fara fin qarfin buqatuna,sai a sannan na lura akwai tarin
marayu a unguwanni daban daban,mabuqata marayu da iyayensun harma da marasa
qarfi......saina saka marayu guda hamsin nauyin su saman kaina,duk wani abu da
zan samu kuma kasonsu yafi nawa yawa,a haka na dinga kula dasu da nawa
qannen......har xuwa sanda na hadu da mika'il komai kuma ya faru" Ta qarasa maganar tana sanya gefan mayafinta
tana share qwallar data jiqa mata fuska.
"Ki yafemin......ki yafemin sabreen don girman
Allah......ku tayani roqar anni ta yafemin" Muryar maamah data sauka musu
a baza wadda ta saka sabreen sake sakin kuka.
Ashe dama
akwai rana irin wannan da zatazo?. Sautin kukan ya taso anni tana dubawa ko
cikin yaranne suke rigima,saidai sanda ta kawo qarshen motar taga sabreen ce
saita zauna a wata kujerar tana shirin tambaya,amma yadda maamah ta riqe
hannunta gam cikin nata ya tsoratata ya kuma bata mamaki.
"Ameenatu ki yafemin........ki yafemin,iya abinda zan
iya cewa daku kenan....kunyimin halaccin da bazan iya biyanku ba amma baqar
zuciya da shaidan gaba daya sun sanya idanuna rufewa,kin yafemin don girman
zatin Allah ta yadda idan na tashi mutuwa zan mutu cikin salama". Sosai
qirjin fu'ad yayi nauyi saidai wani farinciki kebantacce yana dawainiya dashi.
Har yanzu ya daina jin sautin kukanta na daren jiya,sanda ta sanyasu a gaba
shida musaddiq akan su yafe mata. Wani irin kuka dake dauke da zallar nadama cikin
ido murya da kuma lafazinta. Daga shi har musaddiq ba wanda baiyi kuka
ba......wani hukuncin Allah da lamari na uwa kuma.......cikin awanni biyu kacal
da sukayi zaune da ita tana qoqarin basu labarin komai da hardaddiyar muryar
ta,saiga zukatansu dukka sunyi wani irin sawai. Basu bar dakinba saida tayi
bacci tsakanin qafafunsa shida musaddiq,wanda ko bayan sun fito a dakin shi da
musaddiq din ganin komai suke kaman mafarki,sai suka samu kansu da rungume
junansu. Fu'ad ke lallashin musaddiq
"Ba abinda yafi qarfin addu'a......ba wani lamari da
yafi qarfin Allah,alhamdulillah da Allah ya qaddara mata shiriya tunda sauran
damarta" Wadannan kalaman su suka tsagaita kukan musaddiq.
"Anni ki roqamin hamza ma......na cutar da mutane da
yawa ta fuskoki da dama......amma yanzu kune nake gani kune tare dani ku kuka
rage.....ku yafemin naji dana sauran mutane.....hajja da laila dukkaninsu babu
su bare na nema yafiya a garesu........fareeda ta haukace bata da cikakken
hankalin da zamu yafewa juna nida ita".
"Allah ya yafe mana gaba daya" Cewar sabreen
qwallar farinciki na fita a idanunta.
"Allah ya tabbatar damu kan hanya
madaidaiciya.....Allah ya kyautata qarshemu" Anni ta qara da wannan tana
goge Qwallar farinciki da Allah ya qaddarawa maamah shiriya bata mutu da
haqquna ba saina wadanda suka rigata gidan gaskiya.
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 176
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA
CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da
babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu
ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_____________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1
176
Zuwa
yammaci sun daura niyyarsu suka kuma fara gabatar da umarar wanda cikin awa
biyu suka sauketa.
Itakam
sabreen kusan duk sanda sukazo tana yin nesa ne da ayarin familyn jadda,don
tana jin kamar tafi kowa yawan buqata a cikinsu.
Sau tari
bata sake haduwa dasu sai a masauki. Abinda ya gudana kenan yau dinma,don bata
tashi komawa hotel dinsu dake daura da harami ba sai tsakiyar dare.
A gajiye
ta bude dakinsu wanda yake cikin jerin dakuna mafiya tsada dake hotel din da BB
farouq ya kama musu. Kowa da iyalinshi,sai kuma babban daki dake dauke da
bedroons guda biyu,anni ta dauki daya maamah ma ta dauki daya da jikokinsu da
masu aikinsu.
Da sallama
ta shiga dakin,muryarta can qasan maqoshinta da wata irin gajiya a jikinta.
Yana
zaune da farin soft and cotton shirt me zagayayyen wuya,sai boxer da bai qarasa
idon sawunsa ba.
Littafine
a hannunsa wanda yake bayani akan hajji da umra da kuma falalar madeena yana
dubawa,ya daga kai a nutse yana amsa mata gami da zuba mata narkakkun
idanuwansan nan. Qafafuwansa ya janye yana gyara mata pillow din dake wajen,da
idanu ya mata nuni tazo ta zauna,saita qaraso tana zubewa saman kujerar.
Hannu ya
miqa ya zare mata hijabin jikinta bayan ya karbi handbag dinta da carbinta ya
ajiye,ya zare mata hular saman kanta,wanda hakan ya bawa gashinta me sulbi
daman bajewa.
"Yanzun nan nake shawarwarin binki.......daren yayi
yawa duniyata......me kiketa roqa hakane wanda Allah bai baki ba?" Ya
qarasa tambaya da murmushi kan fuskarsa yana miqa mata ruwan daya tsiyaya mata
a cup.
Sai
data maida masa murmushin sannan ta karba ta shanye,ta ajiye cup din tana
dubansa.
"Na godewa Allah......na gode duniyata......haqiqa
Allah yayimin komai tunda ya bani kai......saidai 'ya'yanmu....uwa bata da wani
sauran bacci a sanda ta tara zuria,kullum addu'arta shine yadda zasu samu
rayuwa me kyau,ba irin rayuwar da iyayensu sukayi ba suka tsallake da
qyar".
"In sha Allah.....tun basuzo duniya ba tun iyayensu ma
basu hadu ba muke roqa musu rayuwa me kyau......ubangiji yaji kuma ya karba da
yardarsa" Kai ta gyada cike da gamsuwa,yayin da shi kuma ya miqe ya wuce
toilet.
Ruwa me
dumi sosai ya hada mata,ya dauko mata towel ya fito.
"Oya zaki wanka ki dawo ki kwanta ki huta,kin gama
hidimar biki kikazo kikayi tasu fauzan.......ga kuma zaman mana addu'a dana
tabbatar idan ba nigeria muka koma ba bazai barki ki huta ba". Murmushi
tayi idanunta suna lullumshewa saboda tsananin gajiya,ta miqe da qyar ya
taimaka mata ta cire kayan jikinta ta karbi towel din tana wucewa bandakin.
Dumin
ruwan ya hanata gama wankan da wuri,har sai da ta gasa jikinta sosai sannan ta
fito,ta daura alwala ta tsane jikinta sosai,saita cire wata doguwar riga daya
zaba mata me taushi dake jikin hanger ta zura sannan ta tako a nutse ta fito
tana qoqarin daure gashinta da yayi mata damshi saboda ruwa daya taba.
"Hamma yau ko yatsana bazan iya dagawa ba......am
really tired" Ta fada tana jin idanun suna mata nauyi sosai. Shuru taji
bai amsa mata ba,bayan tana hango qafafunsa daga qasan idanunta yana daga
tsaye.
"Hamma kaina ya jiqe,bazan iya busar dashi ba saida
safe" Ta fada tana hayewa kan gadon,burinta kawai taji jikinta saman
gadon.
"Meye wannan?" Tambayarsa ta ratsa kunnuwanta gami
da saukar wani abu a jikinta sanda take shirin kwanciya.
Birkitacciyar fuskarsa ta kalla,yadda taga ya hautsine ya sanyata bin
abinda ya jeho din da kallo da sauri.
Tablet ne
na family planning wanda har ansha rabinsa. Saita saka hannu ta dauka gabanta
yana wani irin bugawa,ta miqe da sauri da maganin a hannunta a rude ta sauka
daga saman gadon.
"Magani ne hamma......"
"Na tsarin iyali ko?!" Ya fada da wata
gigitacciyar murya dake nuna tsananin fushin dake sauka saman zuciyarsa.
"Eh hamma.....amma ka tsaya......"
"Na tsaya sabreen?,na tsaya kiyimin me?" Ya
tambayeta qofofin hancinsa da jijiyoyin kansa suna budewa.
"Na tsaya ki gayamin ke kika tsaida haihuwa hakanan tun
daga kan iffa?,na tsaya ki bani labarin yadda kika fara shan maganin
planning?,ko na tsaya ki gayan kin gaji da haihuwa?"
"Duka ba haka bane hamma!" Ta fada itama da muryar
data dagu fiye da dazu. Kalamansa gaba daya sun firgitata da wani irin
tsoro,lafaxinsa gaba daya ya gama rudata.....ya zaiyi hukunci irin haka?.
"Duka ba haka bane to yaya ne?,kin taba samun tazarar
haihuwa irinta iffa?,ko kin taba kaiwa haka?,shi yasa nayita tambaya ba bayani
gamsashe?,ko shi yasa naketa magana ke sam ba damuwa a lamarinki!!!" Ya
qarasa fada da wata tsawa data sanyata danne kunnuwanta tana fadin.
"Ya isa hamma!!" Ta fada da murya me qarfin gaske
saboda tsoratar da tayi.
"Tsawa kikeso kiyimin?" Ya tambayeta yana nuna
qirjinsa da yatsansa.
"Kiyi kome kikeso sabreen.......sonki da nakeyi ne ya
jawomin......ki jani da duk kalar abinda kikaga dama.....kiyi duk yadda
kikeso!" Ya fada yana wurgar da daya kwalin dake hannunsa a qasa.
"Karka qarayimin tsawa hamma" Ta fada tana jin
fushi ya fara taso mata.
"Karka qara zargina akan abinda ba haka yake
ba......idan ba haka ba..."
"Ba zaki yafe ba?".
"Basai na fada da bakina bama......na gaji hamma na
gaji,wanne irin 'ya'yane ban haifa maka ba?,wanne irin baiwa ce Allah bai mana
ba na 'ya'ya,samun tazara tsakanin haihuwa da wata haihuwar lallai sai ace sai
ya zama daidai dana baya!......ana yiwa Allah dole ne?,idan kuma yace gaba daya
ka gama haihuwa fa?!" Ta qarasa fada kuka yana qwace mata.
Wani
malulun bacin rai ya taso ya saukar masa,donme zatace idan ya gama haihuwa fa?.
"Ban gama haihuwa ba sabreen.......saidai idan kece
zakiyi silar faruwar hakan"
"Eh nice din.....nice hamma" Ta fada itama a
fusace cikin gajiya da jin bayanansa.
"Okay.....okay.......yanzu kika fitomin a mutum.....kin
tabbatar min da abinda nake zargi kenan".
" Ba zargi dama kakeyi ba.....kana cusamin laifin da
bansan dashi ba......ko meye kake tunanin na aikata na aikata hamma!" Ta
fada da wani irin kuka.
"Don kin aikata sai me?,saboda kinga na damu
dake?,saboda ina sonki.......saboda kina ganin bazan iya rayuwa ba tare da ke
ba?........idan na daina sonki shikenan?" Ya fada da salon tambaya yana
dage mata girarsa dukka biyun gami da bude idanunsa da suka sauya launi.
Wani irin
abu taji kaman an jibga mata a saman kanta.
"Kana zaton nima bazan iya rayuwa babu kai ba?,bazan
iya rayuwa ba soyayyarka ba?......ka daina sona din fine......sai me?" Ta
fada da qarajin kuka. A gaggauce ta juya ta fusgu hijabin data cire dazu ta
maida,ta juya ko wayarta dake kuwwa bata dauka ba illa jakarta data ajiye ta
fice a dakin a gaggauce.
"Kiyita tafiya.....zan iya rayuwa nima ko babu ke"
Ya fada a birkice kaman wanda zai zauce.
Komawa
yayi ya fada saman gadon yana jin wani irin bacin rai yana saukar masa. Tayi
masa laifi kuma sannan ta fishi fushi?,ya samu yara alhamdulillah amma arziqin
da Allah ya bashi yana jin yana buqatar qarin wasu......yanason ya gina family
din da aka jima ba'aga irinsa ba......yanaso ya gogewa maamah gorin yawan
haihuwar da tace asali dangin babanshi na dashi,haifarsu su biyu da tayi daga
jikin ubansu ne.
Wani irin
duhu da qunci dakin yaji yayi masa,tsahon awa guda da wani abu yana zaune guri
daya batare daya ko motsa ba. Sake maida dubansa yayi ga sachet din maganin,ya
saka hannu ya daga yana sake karantawa sai yayi jifa dashi wanda kai tsaye ya
sauka a bakin qofa. Hannu bibbiyu ya saka ya dafe kansa yana jin yana wani sara
masa,yaushe sabreen ta fara sha?,wanne lokaci ta dauka tana sha?,kada ya zamana
ta illata mahaifarta fa?.
Juyi
kawai ya dingayi tsahon awa uku,sai daga bisani a hankali hankalinsa ya dawo
gangar jikinsa,ya miqe ya shiga bandaki ya daura alwala. Saman abun sallah ya
zauna yana karanta wasu addu'o'i hadi da sunayen Allah,A hankali sai yaji
zuciyarsa tana saukowa tunaninsa yana daidaita.
Sannu
sannu sai komai daya faru tsakaninsu ya dawo masa fes cikin kanshi,wani sashe
na zuciyarsa ya dinga masa zafi.
Kwanciya
yayi niyyar yi kafin ayi kiran sallar asuba,amma sanda ya isa gadon da zummar
kwanciya sai maganarta ta fado masa.
"Hamma na gaji.....bacci nakeso nayi". A nutse ya
sauka daga saman gadon,ya koma saman kujera da nufin kwanciya,nan ma sai yaji
ya kasa.
Da daya
da daya ya dinga sauya guraren kwanciya amma ko ina ya sanya kai sai yaji ya
kasa,sannu a hankali ya fahimci zuciyarsa na neman 'yar uwarta ne.....zuciyarsa
na neman mahadinta. Duk yadda yaso ga kafewa wajen fita nemanta amma sai
zuciyar taqi bashi hadin kai,daga qarshe dai ya fahimci ba wata mafita da yake
da ita illa ya fita ya nemo duniyarsa.
Yana
miqewa ana kiran sallar farko,don haka sai kawai yayi alwala,ya zura riga ya
sanya flipp flops dinsa ya murza qofar zai fita a dakin.
Farouq
ya samu daga bakin qofar dakin
"Yauwa dude......dan yiwa adda magana please ta miqo
maganin fannah,jiya ta manta maganinta a jakarta duka biyun.....kasan ba'ason
fashin shansa" Farouq yayi maganar hankalinsa yana wani gurin bai bada
hankali ga fuskar fu'ad ba.
Wani
irin sanyi jikinsa yayi kaman an watsa masa ruwan qanqara,ya juya gwiwarsa a
sabule ya koma dakin ya hada kan magungunan ya bawa farouq. Sanda farouq din ya
wuce sai yaji kaman bazai iya sake taku ko guda daya ba,sai a sannan tunaninsa
ya dawo,fannah tana shan maganin planning saboda matsala da take da ita a
mahaifarta,dole take shan maganin sabida akwai buqatar ta huta sosai tsakanin
kowanne ciki.
Sam bai
kawo hakan a ransa ba,ta yaya ma zaiyi tunanin maganin fannah zai shigo jakar
sabreen?.
Yana
rangaji haka ya dinga takawa har yakai masallacin harami,daidai lokacin da ake
dab da tada sallar,yayi raka'atanil fajr yabi jam'i aka tayar da sallar.
Koda aka
idar zama yayi yayi addu'o'i sosai,yayi istigfari akan zato da kuma yanke
hukunci ba tare da bincike ba. Ya jima sannan ya miqe ya fara zagayawa guraren
da yasan tafi zama ko zai ganta,amma har ya gama zagayensa ya koma duba guraren
da ba wajen zamanta ba baiga koda me kama da ita ba.
Zuwa sanda
rana ta fito ya gaji sosai,dole ta sanya ya koma masauki. Ya samu yaran duka
sun gama shiryawa,kowannensu kuma ummeensa yake da buqatar gani,musamman su
fauzan dake jiran fitowarta su duba gifts da suka samu kafin su wuce harami.
Baisan
amsar da zai basu ba,saidai kawai ya zauna cikinsu ya sadaukar musu da wannan
lokacin,amma dai duk da haka hankalinsu yana kan uwarsu.
Har azahar
shuru bata ba dalilinta,ga anni na nemanta,maamah ma da bata iya magana sosai
sau uku tana tambayarsa.
Zuwa
la'asar hankalinsa ya tashi,don masu neman nata suna qara yawa ne,iffa ma dake
da shekaru biyar neman ummenta takeyi bare sauran da suke da hankali.
Ya kasa
gayawa kowa abinda ya faru,yadai ce musu tana masallacine kawai. Sannu a
hankali hankalin anni yakai kai,saboda yaran da suka matsa da qorafin taje ta
dade a masallacin.
Zaman
jiransa sukayi har yaran sukayi bacci bai shigo ba,yana can yana dubata a ciki
da wajen masallacin. Bai shigo ba sai daya baza masu duba masa ita,wai ko
madeena ta koma daya daga cikin gidajensa?,saidai acan dinma duka daya ne bata
koma ba ba wanda yaga gilmawarta.
Nigeria
ya karkata kiran nasa,tsakanin abuja lagos da kano,can dimma duka daya,don bata
je musu ba.
"Innalillahi wa inna ilahi raji'un" Kawai shine
abinda ya dinga maimaitawa,a rayuwarsa wannan shine ainihin color din tashin
hankali tsurarsa daya taba gani ido bibbiyu.
Yana
kallon wayarsa na ruri da numbers na anni da maamah,kowacce kiranta yana
katsewa na 'yar uwarta yake fadowa,amma ya gaza daga koda yatsansa ne bare ya
amsa musu.
A
jikinsa yake jin bazai iya komawa masauki ba,idan ya koma da anni da maamah da
dukka yaran me zaice musu?,sai kawai ya wuce bandaki ya sake alwalarsa ya dawo
gaban ka'aba yayi salla raka'a biyu ya sake istigfari sannan ya zauna ya
durqushe yana roqon Allah cikin qanqan da kai da neman afuwarsa da agajinsa.
*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada
munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR
GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN
HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road
kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a
duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓
𝐀
_Zafafabiyar_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 177
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA
CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da
babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu
ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1
177
Baisan adadin lokutan daya kwashe a wajen ba,baisan mutun dari nawa ne
suka zauna suka kuma tashi ba a wajen. Har zuwa sanda ya soma jin wani siririn
sautin kuka daga gabansa.
Guri ne da
mutane masu damuwa da buqatu kala kala ke zuwa,don haka baiko dago ba yaci gaba
da abinda yakeyi,saidai kukan dayaci gaba da tashi ya fusgi hankalinsa don
sautin Sabreen yake ji sosai.
A
hankali ya matsa zuwa gaba,ya kuma daidaita zamansa daidai da inda ta zauna.
Jin mutum kusa da ita sosai ya sakata daga kanta,idanunsu suka gauraya dana
juna,take kowannensu wani qaqqarfan abu dake riqe da zuciyarsa akan dan uwansa
ya motsa.
Fatali tayi
da abun,ta kuma yi zumbur ta miqe kamar wadda cinnaka ya cijeta,saidai ko gama
daidaita batayi saman qafafunta ba shima ya miqe,hakan ya sanyata ta fara
hanzarin barin wajen,don tabbas inda tasan zai fito da tsakiyar dare irin haka
ita ba zata fito ba.
"Sabreen" Ya dinga kiranta da tausashiyar murya
sanda suka fita a haramin gudun kada ya janyo hankalin jama'a kansu.
Kaman ba
zata amsa masa ba........amma wata raunanniyar zuciyar ta gaza jure jin yadda
yake jera kiran sunanta da wata irin sassarfa wadda tafi qarfin tata
tafiyar,saboda qoqarin tsere masa da takeyi sai data hada da gudu gudu.
"Ki dakata sabreen".
" Bana buqatarka" Maganar data cake masa a
tsakiyar qirjinsa kenan. Bazai iya jure jin sake fitar wata magana haka daga
bakinta ba,don haka yayi taku uku qwarara sai gashi a gabanta,baiyi wata wata
ba kuma ya dagata cak kaman yadda ya saba yi mata. Ya raina jawota da hannu
daya ko dagata kaman yarinya qarama,saita fara wuntsila qafafunta tana magana
cikin kuka.
"Ka saukeni......bana buqatarka,kace ka daina sona
fa.....kai kacemin na tafi.....na tafi kenan bazan dawo ba,kuma nima na daina
son......." Ai bai iya bari ta qarasa ba ya manne bakinsa da nata,wanda
cikin second kadan qafafunsa suka soma qoqarin kayar dasu saboda wasu irin
taurari da suka soma kewaya jininsa.
Sauketa yayi ya hadeta da bangon wani gini dake kusa dasu,ya sake
lalubar bakinta ya shigar dashi gaba cikin nasa yana aike mata da wani irin
zuzzurfan kiss.
Hawaye
kawai takeyi,ta kasa hanashi,ta kuma kasa tsaidashi,kaman yadda zafin
maganganunsa suka kasa cirewa daga kanta.
Sai daya
galabaitar da ita gaba daya,ya kuma zare duk wani tasirin fushi da yake iya
hanga sannan ya zare kansa daga gareta.
Hannunta yaja ya zaunar saman wata concrete chair dake wajen shi da ita duka
suna sauke numfashi kaman wadanda sukayi tsere.
A madadin
ya zauna,sai ya zame yana tsaiwa saman gwiwoyinsa. Hannunta ya kamo ya sanya
tsakiyar nasa hannun.
"Sabrrr" Ya kirata da wani irin taushi daya sanya
taji wani sanyi ya sauka tun daga tsakiyar kanta har tafin qafarta.
"Sabrrr" Ya sake kiranta wannan karon saita lumshe
masa kyawawan idanunta kawai da suka sanyashi yaji kaman ya hadiyeta ya huta
"Ki amsamin don Allah.......kice na'am hamma idan baso
kike na zauce miki ba".
" Hamma" Ta furta tana ware idanunta da suka wani
zuge saman fuskarsa. Sosai yaji abun ya sokeshi,me ya shigeshi ne haka jiya?.
"Please forgive me my world......forgive me.....am mad
duniyata.......i hurt your feelings......ki yafemin......bazai sake faruwa
ba,ke na batawa amma ni na karbi hukuncin,'ya'yanki da iyayenki da qannenki
dukka sun zuba mini ido ja fiddo musu madame dinsu......in fact ni kaina
zuciyata da kanta fushi take dani,don na haramta mata ganinki.....na haramta
mata kasancewa dake". Yayi dukka maganar yana dora hannuwanta saitin
zuciyarsa dake fama gudu.
Hannunsa
guda daya ya zame a nata,ya danganashi da saitin ka'aba sannan ya fara magana.
"Ni muhammad fu'ad......daga rana irin ta yau nayi
alqawarin bazai sake bari hawayen bacin raina ya zuba a idanun ameenatu na
ba.....idan har kuma hakan.......".
Da wani
irin sauri ta zame daga inda take zaune tana riqe dukka hannayensa biyun tana
girgiza masa da sauri.
"Kada kayi haka......kowanne zaman aure dauke yake da
qalubale.....komai dadi kuma wataran sai an bata ran juna......nima ina bata
maka rai fa hamma......sau nawa ma......amma saika dinga yi kaman ma ban bata
maka ba......kawai abu daya ne banaso ka sake fada don Allah". Ta fadi
hawaye yana silmiyo mata,da alama maganan ita daya tayi mata ciwo fiye da
sauran komai. Kafin ma yaji abinda zata ce din ya dora kanta saman qirjinsa
yana lallashinta
"Mene ne?,me na fada sabrrrr?".
" Kada ka sake cewa zaka iya rayuwa babu ni......don
wallahi ni bazan iya rayuwar da babu kai a cikinta ba". Wani abu me nauyi
yaji ya sake sauka saman zuciyarsa game da ita,ya runtse idonsa sannan ya
budesu.
"Sabrrr" Ya sake kiranta a tausashe.
"Na'amm hamma"
"Adda na" Ya sake kiranta yana jin kaman ya maida
agogo baya ya shafe abinda yayi mata.
"Muffin" Ta motsa labbansa tana kiransa da sunan
da yafison ji a bakinta sama da kowanne suna
"Wallahi Allah mugun maqaryacine ni indai akan wannan
ne......zan iya rayuwa babu ke?,ko na daina sonki?,babbar qarya ce wallahi
wallahi da babu ta biyunta a duniya".
Sam sam
ta mance da mode dinta sai wata irin dariya data kwashe da ita. Yayi matuqar
bata dariya yadda ya taqarqare yake siffanta kansa da siffar da tasan yafi
tsana guda uku a rayuwarsa. QARYA YAUDARA DA HA'INCI.
"Mijina ba maqaryaci bane......ban taba ganin mutum me
gaskiya irinsa ba........a shekara goma sha shida ban taba tuna wata tana daya
batamin rai ba koda sau daya kuwa.....don me bazan masa shaida ta cikakken
adali ba?,tabbas dana zama cikakkiyar butulu kuwa idan na tuhumeshi akan wannan
laifin qwaya daya". Dagata yayi cikin jin alfahari da ita,ya kalli
fuskarta sosai ya sumbaci goshinta.
"Allah yasa ke matatace har a aljannah".
"Haka nake fata ka zama mijina har aljanna.......amma
akwai albishi daya" Ta fada tana murmushi.
"Wanne kenan?" Ya fada yana dubanta cikin zaquwa.
"Allah karimi ne me karamcin da babu irinsa kaf a
halittun duniya.......Allah me boye baiwarsa ne ga bayinsa duk yadda yaso yayi
hakanne zai faru.......bayan na fito sanda gari ya waye jiri ya daukeni,daga
haram suka kaini asibiti don na huta,sunyimin gwaji abun mamaki sun tarar da
cikin da ake rigima a kansa a jikina......kasan watansa nawa hamma?" Ta
qarasa fada a mugun sanyaye tana aza hannunsa saman cikinta. Kai ya girgiza
yana jinsa kaman a duniyar mafarki.
"Wata uku hamma amma dukanmu bamu sani ba.....dama haka
yana faruwa?" Wani irin rauni ya kamashi,ya daga tafin hannunta ya sanya
saman bakinta wai yana qoqarin controlling farincikinsa kada murna tasa ya
furta abinda bai dace ya fada ba.
Sai bayan
wasu wasu sakanni ya iya magana da muryarsa me rawa.
"Yana iya faruwa saboda haka Allah yaso ya
kasance.......astgafirullah......Allah ka yafemin bisa gaggawa da shishshigin
da na yiwa lamarinka......tashi na maidaki cikin ahalinki don basu da wata
madadinki" Ya fada yana dagata zuwa jikinsa gaba daya.
"Da alama su suka sanya sabrrrr dina me ma'anar sunan
haquri ta zama mafadaciyar qarfi da yaji?" Kunya ta kamata,ta shige
jikinsa sosai yana boye fuskarta,ga kunyar albishir din da takeson yi masa.
"Hamma two embrayos........ina fata su zama dukka baby
girls,abinda na zauna na yita roqa maka kenan......sunan waye da waye zaka
saka?".
" Sunan maamah.......da kuma nagartacciyar surukar data
haifamin wannan DUNIYAR TAWA" Ya qarasa fada yana matse hancinta me kyau.
Dariya ta saki har fararen haqoranta suna bayyana,tana wassafa kuma irin
soyayyar da yarinyar me sunan umminta zata samu daga gareta.
"Godiya ga Allah daya bani DUNIYATA na haqiqa......ya
fiddani daga wancan DUNIYAR me cike da rudani" Tayi maganar ne a zuci
batasan ta fito ba har sai da suka hada idanu ya kashe mata ido daya,kunya ta
sakata cusa kanta cikin qirjinsa tana boye fuskarta gami da shaqo tattausan
qamshin nan nasa daya mata wani irin dadi kaman bata taba jin qamshin ba sai
ranar,da alama za'a fafata kenan,da alama kuma wannan cikin meson zuminci da
babansa ne,don dama tanata mamakin yadda cikin watannin ta sake zama very
addicted da lamarin.
*_Tammat bi hamdillah_*
*_Alhamdulillah alhamdulillah,Allahumma lakal hamdu fil ula
wal Aakhira_*
*_lallai a rayuwa komai yayi farko yana da qarshe,doguwar
tafiya me cike da tarin qalubale masu dadi da sauqi dalilin SUPPORT NA MASOYA_*
*_sau tari wata rayuwa na zame maka mabudin alkhairan da
bakayi zato ba🥰_*
*_sau tari wasu dalilan ma zame maka falala me tarin yawa
cikin hikimar gwani na gwanaye wajen iya tsara rayuwa da dukkan hukuncinsa da
iyawarsa_*
*_wata DOGUWAR TAFIYA da inajin bamu taba irinta ba😄,wadda
a zahiri bazai yuwi nayi shuru ban yaba muku ba ku kanku_*
*_kunyi yawan da bansan wasu bama a cikinku......masoyan da
suka dora dambar bibiyar SAFIYYA HUGUMA badon tafi kowa ba.....ba kuma don tafi
kowa iyawa ba,sai don saboda soyayya da qauna data zama SILA_*
*_INA MUKU FATAN ALKHAIRI DA DUKKA FURUCIN BAKINA......INA
FATAN ALLAH YA SAKE SADAMU A TAFIYA ME DADI IRIN WANNAN CIKIN QOSHIN LAFIYA
AMINCI QAUNAR JUNA DA SUPPORTING JUNA_*
*_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU A DUK INDA KUKE AREWABOOKS
FOLLOWERS_*
*_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU 'YAN WHATSAPP.....INA FATAN
ALLAH YA AMINTAR DA KOWANNENKU YA YALWATA ARZIQINSA DON ALFARMAR SHUGANA S A
W_*
*_NAJI DADIN WANNAN TAFIYA MATUQA,NA SAMU SUPPORT DA SHINE
QASHIN BAYAN NASARATA A WANNAN TAFIYA DAGA GURIN MABANBANTAN MUTANE,UBANGIJIN
AL'ARSHI YA DAFA MANA GABA DAYA_*
*_AMANA/GASKIYA/ADALCI/DATTAKO/KAWAICI SUNE TUSHEN KOWACCE
NASARA_*
*Darasin DUNIYATA*
*_KOWACCE RAYUWA AKWAI NATA KALAR QALUBALEN,BA KOWANNE MUTUM
BANE ZAKA GANI CIKIN INUWAR DUKIYA KA DAUKA SHIKAM BAIDA MATSALA BA,BA KOWANNE
MUTUM ZAKA HANGA KA DAUKA YA SAMU DUKKAN WATA WATA NI'IMA TA RAYUWA BA_*
*_KAYI RAYUWA IYA MATSAYINKA......KADA KAYI MIQAR DA ZATA
WUCE TSAHONKA,DUK GAGGAWARKA RABONKA SHINE NAKA,BA ZAKA TABA CIN RABON WANI
BA_*
*_BAWA BAI ISA YA YIWA KANSA ARZIQI BA,SAI ABINDA BUWAYI
GAGARA MISALI YA HUKUNTA MAKA_*
*_KE UWA!.....BAKI DA KAMAR 'YA'YANKI.....SUNE
RAYUWARKI.....KIYI AURE AMMA KARKI YADDA KI FIFITA KOMAI NAKI SAMA DA
TARBIYYARSU DA KUMA RAYUWARSU_*
*_AIKATA ALKHAIRI KA WUCE ABINKA KA BARSHI AGUN,ZAI CIMMAKA
WATAN WATARANA.....KAMAN YADDA IN KAYI SHARRI HAKA WATARAN ZAI DAWO MAKA_*
_Kusakurai da aka samu a ciki da abinda bai kammalu ba
ayimin haquri,na rubutu matuqa har naji rubutu ya ginsheni😂😂😂_
_wanda na batawa ya yafen,na yafi kowa,kuskuren ciki
ubangiji yayi afuwa,ya tattaramu a ladan,ya bamu ikon daukan me kyau a labarin
mu watsar da shirme_
Every conclusion sparks a new inception
Nothing lasts forever
Every dawn has a dusk
Ending are part of beginnings in sha Allah
_subhanakallahumma wabi hamdika ashahadu an la'ilaha illa
anta,astagfiruka wa'a tubu ilaika_
_Allahumma salli wa sallim ana nabiyyurrahmati_ S A W
08187255862