*A D U N I Y A T A* 🌎
*_H U G U M A_*
*_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_*
*lace*
*kowanne nau'in shaddodi*
*yadika na maza da mata*
*mayafai*
*lafaya*
*takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana*
*sarqoqi da agoguna*
*under wears*
*abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza*
*_Akwai group na musamnan saboda nasu buqatar kayan kitchen HUGUMA UTENSILS UNIVERSE_*
https://chat.whatsapp.com/EzM8Qst8A2XAevw3akx5ub
*_Duniyar kwatalle kitchen din amarya da uwargida_*
*_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?,sallah tana matsowa,azumi na tunkarowa?_*
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
__________________________
Page 01
*_The gateway_*
"Maaaam.......don Allah maama,abbee bashi da lafiya sosai kin sani maama......idan kika tafi waye zai kula damu?,idan kika tafi maama waye zai kula da abbeee?" Muryar yaron da gaba daya bazai haura shekara goma sha uku ba kenan take fita cikin wani irin sanyi da matsanancin rauni wanda koda ba'a gaya maka ba.....koda kuma baka kalli fuskarsan nan dake jiqe da hawaye ba.....koda baka kalli hannuwansa dake rawa ba wanda ke tallafe da mujinyacin dake zaune tsakanin cinyoyinsa ba zaka fahimci yana cikin matuqar kaduwa razani tare da zallar firgici.
Idanunshi qur bisa kanta yana fatan jin qididdigaggun kalmomin
"Na fasa tafiya" daga bakinta,duk kuwa da cewa ba wani abu guda daya tal da ya bashi alama komai qanqantarta da take nuni da zata iya janyewar. A maimakon haka ma,sai sake gyara yafen mayafinta dake saman kanta tayi,ta duqa tana cusa ragowar kayanta da basu samu gurbi ba cikin baqar jakar gabanta.
"Don Allah mariya.......ba don ni ba......ko don yaran nan,kiyi haquri......ki zauna ki rungumesu,ni tawa me sauqi ce,ina da tabbacin kwanaki qalilan ne suka ragemin,su din dai sune abun dubawar......" Mutumin da rashin lafiya da kuma talauci sukayi gamayya da matsin rayuwa suka yiwa kowanne sashe na halittar jikinsa illa. Yayi maganar da qyar yana fidda numfarfashi kaman numfashin nasa zaya qwace daga tsakanin qirjinsa zuwa hunhunsa.
Dauke dubansa yayi daga kan fuskar mutumin da yake MAHAIFI a gareshi ya maida kanta zuciyarsa na narkewa da wani irin tausayin kansu gaba daya idan ka debe ITA!. Bugun zuciyarsa na sake daduwa da tsananin tashin hankali da tausayin na daban kamar zai fasa zuciyarsa ta tsage. Ya jima yana begen jin fitar wasu kalmomi daga bakin mahaifinsu wanda a qalla yau kusan kwanaki goma cif kenan baya um baya um um. Ya kashe darare masu yawa yana kasa kunnen yaji wani abu daga bakinsa.....sai gashi a yau bakin ya budu,amma kuma sun budu ne saboda tsananin bala'i da firgici da take shirin jefa rayuwarsu,bawai ya budu bane da zummar musu magana da kyawawan kalmomin nan da baya rabo dasu a kansu.
Idanunsa cike da fatan zuciyarta zata rusuna daga kalaman mahaifinsu.....kodon kalmar mutuwa daya ambatarwa kansa wadda ta zama daya daga cikin dalilan da ya sanya yaji inama baiyi maganar ba,inama shuru yayi da bakinsa duk da tarin buri da begen yaji yayi maganar wanda ya cika zuciyarsa. Yana tsaka da wannan shawagin cikin zuciyar zato da fata ya sake jin busashiyar muryar mahaifin nasa mara amon sauti yana sake tattara dukka juriyarsa yana fadin
"Mariya......idan kika tafi waye zai kula dasu?" A fusace ta waiwayo ta watsa masa wani irin kallo tana rataya jakarta bisa kafadarta
"Dasu nazo?,ai dama a nan na samesu kuma a nan din zan barsu,dan da uwarsa ke mutuwa ma randa ta haifeshi yanzu haka suna rayuwa sunfi miliyan bare wadanda suka kai shekara sha uku da takwas" tana kaiwa nan ta soma daga qafafunta tana baiwa dakin takun bankwana,abinda ya bashi tabbacin da gaske fa take!
Ba zata rusuna ba!.
Da alama kuma ba abinda zai sanyata rusuna din!.
Baisan wanne tunani ya kamata yayi ba,don a sannan qwaqwalwarsa tayi qanqanta da daukan dukka wadannan abubuwan bare har ya rarrabe hukuncin daya dace da wanda bai dace ba,sai ya tsinceshi a gabanta,riqe da qafafunta yana qaramin kuka da iya dukka qarfinsa a shekarunsa.
Dubansa tayi kaman zata qwace qafar,sai kuma ta saka hannu ya dagoshi ta maidashi ta zaunar tana cewa
"Nan din shine dolenku,a nan zaku zauna da dadi ba dadi,da wuya ko babu,idan nace nima zanci gaba da zama,dukkanmu ni daku za'a yi haihuwar guzuma ne ni kwance ku kwance babankun ma haka,gwara na matsa kadan,wataqila rabon yana a gaba".
Cak maganar ta yiwa zuciyarsa tsaiwar mashi. Idanuwansa suna iya hangen mahaifinsa yana runtse idanunsa. Sai ya zare nasa idanun yana maidawa kan yaron daya yunqura zaibi bayanta bayan fitarta qofar dakin.
Wata gigitacciyar tsawar data girmi shekarunsa ya daka masa
"Dawo ka zauna!......zamu rayu.....zamu rayu da mahaifinmu!.......zamu rayu da wuya ko da dadi!.......zamu rayu da farinciki ko babu!.......mu din dolen junanmu ne yanzu!......bamu da kowa sai kawunanmu sai mahifinmu!" Ya qarashe maganar yana numfarfashi qirjinsa yana dagawa sama da qasa.
Cak ta tsaya,ta kuma waiwayo,idanunsu suka sarqafe guri guda. Ba sanin shekara daya ko biyu tayi masa......ba kuma sanin shanu tayi masa ba.......tasan dabi'unsa dake zubi da dabi'un mutumin daya dauki wani dogon xango xamani ko kuma qarni cikin sararin duniya...... dabi'un da sukan jefata duniyar mamaki a wasu lokutan..... Amma ko a shifcin qwaqwale bata taba tunanin fitar wadannan kalamai masu tsananin zafi daga harshensa ba. Kalaman da suka jeru da kyau!. Suka kuma isar da saqo tamkar dai ya jima yana ajiyarsu......kamar kuma rubuta masa su akayi ya dauki dogon lokaci yana gwajin yadda zai furtasu.
Yadda ta zare idanunta daga kanshi haka ya zare nasa. Sai ya maida dukka yunqurinsa wajen qoqarin kwantar da mahaifinsa yadda zayaji dadin kwanciyar. Jikinsa ya qara nauyi ya kuma sake sosai. Saidai duk da haka numfashi na fita ta qofofin hancinsa,abinda ya sanya sam tunaninsa bai kai kan komai ba.
Bashi da wani sauran FATA a kanta......amma kuma hankalinsa ya gaza daukewa daga kanta,yana lissafe da takun takalminta sanda take ficewa daga cikin gidan nasu. Fitar da har yanxu ta kasa barin qwaqwalwarsa. Fitar da har yanxu take masa matsanancin ciwo......fitar daya alaqantata da sila kuma MABUDIN afkuwar kowanne irin tsanani da matsin rayuwa.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*🌍
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
Page 02
Idanunsa da suka qanqance suka kuma sake shigewa ciki saboda tsananin kuka tashin hankali da firgici ya bude. Ya jefa idanunsa gefansa hannun hagunsa,ya kuma aza idanunsa saman shimfidaddiyar lamusashiyar shimfidar. Shimfidar da kwanaki uku kenan da matuwar mamallakiyarta, shimfidar da kwanaki uku da suka gabata iwar haka suna tare da me shimfidar. Kaka a garesu,mahaifiya ga mahaifinsu wadda ta zame musu bango jigo kuma majingina a garesu bayan rasuwar mahaifinsu.
Har yau ya kasa sanya hannu ya tattare shimfidar,hakanan babu wanda ya damu ya dauke ta. Yo ina aka damu dasu ma ballantana abinda ke cikin gidan?. Su din ba wasu bane,basu da abinda zasu bawa jama'ar zaman makoki,basu da gata basu da wani tsayayye da zai tsaya ya tayasu jimamin rasa kakar tasu da suka zauna da ita shekaru uku cikin tsanani da kuma zazzafar gwagwarmaya irin wadda ke xamantoww tsere ne tsakanin tsanani da kuma sassauci cikin tsananin.
Hawayen nan daya kasa yankewa daga idanunsa ne suka sake bullowa. Har yau gani yakeyi wasa ne,har yanxun gani yake JADDA zata dawo. Shudewarta ya dawo masa da mikin rasuwar mahaifinsa,sai yakejin kamar yau ne ya rasu,kamar a yau ne yayi bankwana da duniyar,kamar a yaune MAAMA ta sanya qafafu ta fice ta barsu,tafiyar data xama wani yanki na tunzura yanayin rashin lafiyar abbee......tafiyar kuma data zaman kamar ta tafi da ruhi da kuma rayuwarsa. Hannunsa daya ya sanya ya riqe wuyansa da kyau kamar yana shirin shaqe kansa. Wasu murtuka murtukan jijiyoyi suka fito bisa saman kansa da goshinsa sukayi layi rad'a rad'a. Kalar da idanunsa yayi ya sake ninkuwa da kalar jaa ainun,kuka da hawaye me zafi ya sake yanke masa,matuqar maqurar qiyayyar jinin mahaifiyarsa yana tsartuwa cikin kowanne sashe da lungu na gangar jiki da zuciyarsa.
"Hamma.....ham" yaron daya fado dakin ya dakata da kiran da yake jera masa. Cikin wannan yanayin ya waiwayo yana kallonsa,sai yaron ya dan ja da baya,don ya tsorata ainun da yadda yaga fuskarshi ta sauya. Yanayi ne dake sanya masa tsoron hamman nasa sosai da sosai,duk sanda ya ganshi a irin haka sai ya dinga ganin kamar ba hamma dinsa ba.
Ya lura da hakan shima,wannan ya sakashi zare hannunsa daga wuyansa yana tattaro wani irin yawu me tauri da kauri yana hadiyewa da qyar kamar me hadiyar duwatsu. Yakai zuciyarsa cen nesa,ya kuma gyara harshensa sannan ya jefa masa tambaya
"Menene?" Murya da jikinsa suna danyin rawa ya soma fadin
"Abba ne......abbansu farouq ne yace kazo yana soro" idanunsa ya sauke yana jin wani kaso na rahama da sassauci suna sauka a zuciyarsa. Mutum qwaya daya tak a duniya da ganinsa ko jin kiransa yake shaida masa zuwan alkhairi sauqi sassauci ko rangwame daga dukkan wani hali da suke ciki.
Yana tafe amma yana jin kaman ba'a kan qafafunsa yake tafiya ba,yana tafe yana jin kamar tsakanin sama da qasa yake,saboda tashin hankali yunwa harma da qishi. Ko sau daya bayan rasuwar ya gaza kai qwayar abinci bakinsa daga abincin da maqota ke saka musu jifa jifa. Yana daddafe da bango yana wulga idanunsa ga sararin tsakar gidan nasu daya zama kamar filin sukuwa......ya zama fetal ya sake fadi,abinda ke alamta masa cewa lallai sun sake rasa wani bangon kuma madaafa.
******Dattijo me cikar kamala wanda duka duka shekarun haihuwarsa a duniya ba zasu haura arba'in da biyar ba. Amma alamu sun nuna muraran shi din me ginanne kuma lafiyayyen jiki ne dake iya cinye shekaru.
Yana sanye da yadin kufta da yasha aikin hannu wanda ya qara masa cikar kamala. Ya tura hularsa baya,qafarsa sanye da slipper dan madina,wanda ke zamantowa daya daga cikin dabi'unsa a lokuta da dama idan zaya fito guraren da bai wuce masallacin cikin unguwa ba ko wata unguwata kurkusa a cikin abun hawansa ko a qafa.
A raunane suke kallon juna shi da shi,ganinsa sai ya sake sakawa zuciyarsa wani raunin,yana shirin duqawa ya gaidashi ya tallabeshi
"Tashi tashi......sannu da qoqari,sannu da haquri......akwai wai abu da kuke buqatar dauka ta cikin gidan?" Ya tambayeshi yana dubansa. Bai gane komai abban yakeson fada ba,don haka ya dubeshi sosai.
"Gida na zan wuce daku,ba za'a barku ku dinga kwana kuna tashi gidan da ba kowa a cikinsa ba saiku kadai"
Muryar nan data nuqu qwarai cikin wahala da gararanba ya bude
"Sai kayan sawarmu"
"Dauko abinda ya sawwaqa a kulle gidan" yayi maganar yana kama hannun qaramin qanin nasa dake kusa dashi.
Sanda yake hada kayan kudu da yamma gabas da arewa na zuciyarsa a cakude yake da tunani. Zasu koma gidan abba?. Gidansu farouq?. Tabbas su farouq 'yan gata ne gaba da baya,saidai wani irin gata suke samu dake da wani wawakeken gibi da kuma naqasu. Gatan daya rasa wani bango kuma jigo a cikinsa,gatan da wani lokacin yakan juya musu da wani irin launi mara armashi. Wani gata da bai amsa sunansa ba a lokuta masu yawa,su din sukan zama har sun darasu samun wani abu guda daya,duk da tarin nasu naqasun rashin wadata da sukunin rayuwa. Sun darasu samun 'YANCI SAKEWA DA KUMA WALWALA. kenan zasu rayu tare da momy?,zasu zama qarqashin inuwa da mulkinta kamar sauran yaran?.
Sakin ragowar kayan hannunsa yayi ya sulale ya zauna a qasa. Iya wannan tunanin kadai ya karya duka sauran guntun karsashinsa.
Tunaninsa ya dinga rarrabuwa,a haka dai gatane suka sameshi saboda abban wani irin dattijo ne me fafutukar taimakawa da tallafawa sukkan me rauni. Tun zamanin da mahaifi da mahaifiyarsu ke rayuwa tare hannuwansa da aljihunsa harma da lokacin cikin hidimta musu suke. Shudewar uba a garesu ya sanyashi sake ninka alkhairinsa. Ya sanya hannu bibbiyu ya tallafi rayuwarsu data jadda,a yanzun kuma yana shirin maida nauyin kacokam bisa wuyansa.
"Idan ba zaka iya shirya kayan ba fito hakanan a barsu zuwa gobe ko?" Muryar abban ta baqunci kunnensa,wanda dole ta sanyashi miqewa ya debi iyakar abinda zai iya. Ya janyo qafafunsa yana fita daga dakin,idanunsa na rarrabuwa a sassannin da suka qaraci dabdalar rayuwarsu suda jadda bayan shekaru uku da rasuwar mahaifinsu. Abinda ya dunqule waje guda ya bashi adadin shekaru SHA BIYAR a duniya.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*🌍
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
Page 03
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
______________________________
Yana riqe da hannunsa tsam cikin nasa cikin tausayi da nuna kulawa. Yayin da yake biye dasu a baya,rungume da kayansu jikin qirjinsa, wanda ke dauri a wani yalolon mayafi.
Duk taku daya yana yinsa ne tare da bugawar zuciyarsa,wani irin shakkun shigarsu gidan yana mamayar zuciyarsa,dukkan sarewa da kuma rauni tare da rashin tabbas suna cikashi. Daidai sanda abban ya waiwayo a nutse,lokacin da suka kawo bakin gate din gidan.
Murmushi ya sakar masa a hankali da mufin kwantar masa da hankali,ya fahimci akwai anunuwa da yawa dake kai komo a zuciyar yarin game da shigarsa gidan. Shigarsa gida wani tsohon labari ne daya jima da shudewa,a qalla shekaru kusan biyu cur kenan yanzu ake magana.
"Ka saki jikinka,hakan shine zai sanya dan uwanka shima ya saki jikinsa,ka dauka a ranka tamkar mahaifinku ne ya dawo,zan zame muku uba bango kuma majingina muddin numfashi yana yawo a gangar jikina,kasa a ranka a yanzun baku da sauran matsala ko maraici kaji?" Abba ya furta yana dora hannunsa saman kanshi,qauna da tausayinsa yana ratsashi.
Ya jima yana kallon yaron a mabanbantan ranaku lokutta da kuma gurare cikin unguwar. Ya jima da sanin cewa yaron ya fita daban cikin sauran yara,komai nasa na dabanne,nutsuwa da hangen nesansa kawao zai sanya kayi tunanin ya girmewa shekarunsa. Bai taba ji ba,bazai kuma taba iya tuna wani lokaci da yaji wani yayi kusa dashi cikin unguwar bisa rashin gaskiyarsa ba,muddin kaji wani koke a kansa to lallai ba shakka taboshi akayi,an shiga gona ko huruminsa.
Duk sanda ake irin wannan case din a mafi yawan lokuta yana tare da mahaifinsa,yakance
"Ka barni nayi masa hukunci koda shine da gaskiya,ya cika zafin rai,ya fiya taurin kai da kafiya,wannan duka ba dabi'u bane masu kyau,ya kamata ya sauya saboda rayuwa".
Murmushi abban yakan saki,ya kuma maida dubansa ga fuskar yaron kafin ya bawa mahaifinsa amsa
"Ka godewa Allah,ba'a taba kawo maka qararsa akan rashin gaskiyarsa ba,koda kuwa an kawo qarar zaka sameshi ne ame gaskiya,shin me kake nema ko fata sama da haka?". Mahaifinsu mutum ne me tsananin kawaici,kanshi kawai yake kawarwa yana murmushi. Abban ya wuce komai a wajensa,maqoci ne me nagartar da samun irinsa yake wahala,don haka ne yake bashi dukkan girma,ba kuma wai don arziqi ko dukiyan daya mallaka ba,a'ah,don kawai ya cancanci hakan.
"Kana jina?" Abba ya sake fada don maido hankalinsa kansa,sai ya gyada kansa a nutse shima yana duban abban
"Yauwa,muje ciki,dukka su saddiq ma suna ciki na tabbatar yanxu" Bai musa ba yayi gaban abban yana biye dashi yana tsokanar dan uwan nasa daya sake sosai,farinciki ne ma kwance akan fuskarsa,da alama quruciya da rashin sanin cikakken ciwon kai ya sanya ko kusa ko alama baya hasashe ko hangen abinda kan iya faruwa,ko a kusa ko a nesa,me kyau ko akasinsa a kansu da rayuwarsu dama DUNUYARSU gaba daya.
Ci gaba sukayi da tattaki cikin harabar gidan,yalwatacciyar haraba dake shimfide da interlock. Kana ma gidan kallo daya zakasan akwai sukunin rayuwa a cikinsu,duk da ba zaka kirayeshi da wani MAHAUKACIN ME KUDI BA amma tabbas yana cikin jerin MASU KUDI ARZIQI DA WADATAr daya tserema neman komai na biyan buqatar rayuwa,kamar yadda ya tserema RASHI ya masa tazara irinta HAIHATA HAIHATA.
"Bude mana" Abban ya furta sanda yaga yaja ya tsaya ba tare daya buda qofar falon da zata sadaka da ainihin cikin gidan gaba daya ba. Matsawa yayi gaba kadan,ya murda qofar ya kuma tura,sannan ya saka qafafunsa cikin falon dake gauraye da sanyin Ac.
Ita dince dai,itace mace ta farko da idanunsa suka fara tozali da ita. Bai sani ba,tsabar yadda ya washeta ne,yake kuma qyamatar shiga cikin dukkan lamuranta ne kamar yadda take nuna qyamata da qin jininsu qarara a fili?,wannan shi ya sanya ta zama mutum na farko daya fara gani?.
"Kai dakata!,ina zaka je?,wajen wa kazo?,wai ban hanaku shigowa gidan nan haka gaba gadi ba kamar gidan tsohonku?,me ma ya kawowa da wasu tsummokara a hannu?"
"Nine na kawoshi" Abba dake bayansa ransa na quna da jin kalamanta ya furta. Sak ta danyi,duk da bawai ta razana bane da jinsa,sai tsabar baqinciki da kuma zato daya soma zuwa ranta
"Lallai kawai bala'i cikin gidan nan" Ta raya a ranta tana sake tattara dukka girarta waje daya ta hade,babu rahama ko qanqani saman fuskarta.
Yaron dake zaune a rakube daga qasan carfet din ya sake tattare jikinsa waje daya,alamu dake bayyana lallai ya shiga taitayinsa da sauyawar yanayin nata.
"Laaaaa......kaine kuma yau?ashe zaka sake shigo mana?" Yaron dake fitowa daga kitchen din gidan ya furta,fuskarsa na juna tsantsar farinciki,kamar yadda ya bada dukka hankalinsa akan wanda ya jefawa tambayar,hannunsa dauke da tray,daga hannun nasa har zuwa qafafunsa ya tattare bakin wando da kima rigar tasa.
"Kai me yasa baka da hamkali ne?,zaka zo ka ajjiyemin ko kuwa?" Hamshaqiyar matar dake zaune saman kujerun falon ta sake ma yaron tsawa,wanda tamkar ma ya manta da abinda ya fito dashi daga kitchen din,kaf hankalinsa ya tafi ga baqon yaron daya shigo din,wanda a idanu shekarunsu tamkar daya suke.
Juyawa yayi xuwa gareta don aje mata tray din,hakan bai isheta ba ta bishi da wani mummunan kallo,idanunta kamar zasu ciro su fado qasa
"Shashasha,kamar wani wanda yaga qanin ubansa,sai nayi maganinku" Ta furta cikin fushi. Daga baya baya kadan ya ajiye tray din yana fatan kada hannuwanta yakai kansa,duk da yasan hakan zaiyi wuya,ko don wanzuwar mahaifinsu a wajen
"Musaddiq......maza karbi kayan hannunsa ku wuce dakinku dukkanku" Zumbur yaron dake a zaune rakube tsakanin kujerun ya miqe. Bai jira kowa ba a cikinsu yayi hanyar dakinsu,saidai yana tafe yana dan waiwaye.
A sanyaye ya sakarwa musaddiq kayan hannun nasa,yana qoqarin maida masa martanin murmushin da yaketa faman yi masa tunda sanda yayi tozali dasu
"Muje ko?" Ya sake fadi yana kama hannunsa.
Bai musa ba ya soma bin bayansa,don zamansa a falon yayi imanin sam bazai yiwu ba koda abba bai basu umarnin wucewa ciki ba.
Zazzafa kuma tozartaccen kallo take binsu dashi,zuciyarta na mata wani irin suya,bacin rai da takeji kamar zata yi aman zuciyarta.
Debe idanuwanta tayi daga kansu tana jan qaramar qwafa qasan zuciyarta,ita daidai take dasu,babu wanda ta shirya bari ya takura rayuwarta ko ya quntata ta.
Duk wani motsi nata yana karance da ita,har zuwa sanda ya daidaita zamansa saman kujerar sannan ya dubeta yana kiran sunanta
"Asama'u" Kallonsa kawai tayi ba tare da tace komai ba
"Ga yara nan na kawosu,yara ne kuma da kin sansu bawai baqi bane a wajenki,kin kuma san basu da wata matsala ko aibu ko wani abun fada cikin unguwar nan......alqawari ne da na yiwa kaina tsakanina da ubangijina,na kuma cika alhamdulillah,ina fatan zaki tayani riqesu bisa amana ko don maraicinsu".
Wani kallo takeyi masa ranta cike fal da mamaki,ta karkace tana dubanss tare da tattara abinda zata ce masa
"Yanzu bayan naka yaran har yaran maqota kakeyimin kalensu?" Ta aje maganar tana jin zafi cikin ranta da zuciyarta. Tana jin ta quna bata tsoron qauri,ta soma gajiya ta kuma soma qosawa tare da debe haso hadi da tsammani na samun shimfidaddiyar rayuwar data jima tana mafarki gami da shimfidawa cewa zata samu cikin gidan.....
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
*PAGE 04*
A nutse ya daga kai ya watsa mata wani irin kallo. Yau ta fara fadin hakan,amma kuma ya dade yana karantar hakan daga dukka ayyukanta da motsinta.
"Nayi tunanin akwai dattako fahimta da kuma qaunar juna a tsakaninmu da har yarana sukafi qarfin kice riqonsu kikeyi,na zaci cewa kina ji a jikinki da zuciyarki kina rainkn 'ya'yan da kika haifa ne a cikinki?" Wani abu ne yazo yayi mata tsaye a wuya,ta juya kanta gefe guda tana tattaunawa da zuciyarta kan
"Har abada 'ya'yan riqo ba 'ya'ya na bane,'ya'yan wasu ba zasu taba zama 'ya'yana ba.....banda qaddara me zai hadani da riqon 'ya'yan wasu?" . Idanunsa a zube fes a kanta,ya gyara zamansa sosai yana sake ci gaba da kallonta
"Inaso ki cire a ranki riqo kikeyi.....ba 'ya'yana na cikina bama.......hatta yaran dana kawo yanzu,inaso ki ji a ranki Tamkar suna rayuwa ne cikin gidan mahaifinsu a gaban uwa da kuma ubansu". Dukka haqurinta ya qare,ya tuqeta ta kuma kai bango,tana jin ba zata iya ci gaba da zama tana sauraronsa ba,don haka ta miqe tsam,ta kuma gegara ta gabansa tana barin falon.
Da ido ya bita har zuwa sanda take shirin bacewa ganinsa. Ya jima yana ganin alamun da suke alamta masa akwai matsaloli masu yawa cikin rayuwar su farouq,amma yayita qaryata hakan gudun kawo damuwa da matsala cikin zaman uwar wani da d'an wani wanda keda wuyar sha'ani,sai gashi a qanqanin lokaci komai yana bayyana kansa daki daki.
Numfashi ya zuqa ya fesar yana rufe idanunsa,qoqari yake ya saita kansa yana tunanin hanyar da zai daidaita komai.
Tray din da faruqee ya ajjiye yabi da kallo,a dawowarsa daga lagos wannan karon ya fahimci kamar ma suke yiwa kansu girki harma su hada da ita idan ta kama,babu sakewa babu walwala sam tattare dasu. Ya lura da raguwar kuzarinsu kyara da kuma hantara daga gareta,saidai dukka ya kauda kai don bai kamaci a karon farko ya fidda soyayyar yaransa kai tsaye daga zuciyarsa har haka ba,bayaso yabar wani tabo ko targaden da zai kasa gyaruwa tunda wurwuri haka.
Da idanu kawai yake bin dakin da kallo sanda Faruqee yaketa masa bayani zuciya da fuskarsa cike da zumudi da farinciki.
"Kayi shuru?,ka tsaya a bakin qofa,ko dakin baiyi bane na gayawa abba a qaro wasu abun?" Faruqee ya fada jikinsa yana sanyaya da yadda yaga fuskarshi. Don a yadda ya zata zayaga farinciki sosai a fuskarsa kaman kwatankwacin nasa farincikin na dawowarsa cikin gidansu,farincikin samun aboki me hankali irinsa,farincikin samun aboki da yayi daidai da shekru da hankalinsa,ba aboli irin qaninsa ba da sam.baya gane wsu abubuwan saboda sabanin mizanin hankali da fahimta dake tsakaninsu.
Karon farko yayi qoqarin sake fuskarsa da kyau yana kallon faruqee. Dakin gata kuma dakin yaran gata irin wannan da shi din bai taba samun kwatankwacinsa ba ta yaya zaice baiyi masa ba?. Dukka alatu da yayi saura a dakin bashi yake daukarsa ba.......duk da qarancin shekarun daka iya dakusar da tunanin yaro a sannan......amma shi sun bawa qwaqwalwarsa damar budewa da yin tunani me nisan zango akan
"Wacce irin rayuwa zasu fuskanta a matsayinsu na agola bayan su kansu tsatson gidan basu tsira ba?,mene ne makomarsu?,meye farko da kuma qarshensu?" Tarin tambayoyin da baisan ta ina zaa fara sauke masa su ba
"Nayi murna farouq" Ya furta a sanyaye,sunan da shi daya yake furtashi daidai yadda yake,don har yau bai taba kiransa da faruqee ba.
Yadda qanin nashi ya zuba masa idanu ya sanyashi qoqarin sakewa,ya qaraso ainihin cikin dakin kamar yadda sauran suka kai ga shigowar.
Qoqarin kauda komai ya dinga yi daga zuciyarsa,yana zaune daga falon yana iya jiyo muryoyinsu sama sama,saidai har yanzun baiji tashi muryar ba. Baiyi mamaki ba,don ya sani,yadda komai nasa ya fita daban daga cikinsu,haka dabi''arsa da halayyarsa ma ta zama daban.
Abincin yaja ya soma ci bawai don cin abincin yana masa dadi ko yana burgeshi ba. Tunaninsa yayi zurfin da har ba komai dake wakana cikin falon yake ganewa ba,bai taba zata ba,bai kuma taba kawowa rabuwa da rabi'atu zai iya zame masa qalubale ba sai yanzun da dukkan alamu suka fara bayyana kansu. A karon farko har yaji ya fara tuhumar kansa da kansa,tare da nacin son gano meye ainihin laifin rabi'atu ne har ta cancanci a saketa?.
Baici da yawa ba ya ture,ya miqe yana irgen lokaci,sai ya juya ya fara takawa zuwa dakin yaran.
Dukkansu sunyi shirin bacci amma bandashi,yana zaune gefe daya na gadon farouq,ya goye hannayensa a qirjinsa tamkar wani babba da yayi nisa cikin nazarin wani abu.
Motsin abban ya sanyashi waiwayowa,da sauri ya sauke hannayensa yayi qasa da kansa yana niyyar zamowa daga saman gadon
"Yi zamanka me babban suna......tunanin me ka zauna kana yi?,duk 'yan uwanka sunyi shirin kwanciya banda kai?" Farouq dake zaune tsakiyar gadon yayi hanzarin karbar maganar dama tana damunsa tun dazu
"Abba yaqi ya canza kaya,na bashi kayan bacci yaqi ya saka tun dazu" Hannu kawai abban ya miqawa farouq din,sai ya saka masa kayan baccin dake gefansa.
Kayan abban yabi da kallo yana jujjyasu a hannunsa,sannan ya maida dubansa zuwa jikinsu dukka su ukun dake sanye da wasu kalolin kayan.
"Amma faruqee ban gaya muku a bada kayan nan ba dukansu?,ina kayan dana kawo muku wancan tafiyar da nayi?" Ya qarasa tambayar yana maida idanunsa kan saddiq qaninsa.
Har wani juyawa saida cikin saddiq din yayi,saboda tunawa da yayi da kakkaifan warning din da suka samu daga wajen matar gidan akan batun.
"Abba,dukka mama ta karbesu,ta kuma gargademu kada mu sake mu sanar dakai,idan ba haka ba saita tsoma kawunanmu a ruwan zafi" Ba abba kawai ba,hatta me babban sunan saida maganar ta ratsashi duk da qananun shekarunsa,amma zuwa yanzu ya dade da yiwa kansa karatun qalubalen da suke shirin fuskanta
"Ruwan zafi?" Abba ya furta cikin tsananin kaduwa da mamaki,sai faruqee ya gyadawa abban kai. Maganar ta ladabtar d abba ta sanyashi samun waje ya zauna. Yana tsoron ci gaba da wannan tafiyar tasu......yana tsoron garin neman lada ya rufta ya buge d wucewa jahannama,ya debo marayun Allah da nufin basu rayuwa me inganci,muddin Mariya bata goya masa baya ba meye makomar yaran?,ya gobensu zata kasance?. Tambayoyin da suka dinga karafkiya kenan a kansa.
Indai haka ne ya zama dole yayi jan ido,ya zama dole yayi wuta wuta akan gidansa da iyalinsa. Ya sauke dukka nauye nauye haqqunan da suka zama wajibi dama wadanda basu zama wajibi bs,ya zama dole to itama ta bishi yadda ya kamata.
"Ba komai,tashi me babban suna ka shirya,idan kun kammala ku kashe kayan wuta gaba daya kuyi addua ku kwanta" Yayi maganar ne yana sake nazartar dakin tare da kallon guraben da ga siya ma yaran abubuwa da dama ya ajjiye saboda jin dadin Rayuwarsu a yanzu ba komai a wajen sai gurbinsu.
Sai daya kammala komai daga ainihin dakinsa sannan ya zarce dakin mariya. Ta gama shirin kwanciya tsaf tayi rub da ciki tsakiyar gado tana latse latsen waya. Fuska a hade ta daga kai ta kalleshi sau daya saita dauke kan nata ta maida ga wayarta tana sake tsuke fuska.
"Tashi zamuyi magana" Ya fada cikin yanayin dake tabbatar mata da gaske yake,da kuma zafinsa ya shigo. Sai da tayi kamar ba zata tashi ba sannan ta miqe ta zauna sosai tana gyara wuyan rigar baccinta tare da tsuke fuska da kyau.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
Page 05 last free page
"Asama'u" Ya kirayi sunanta da wani irin yanayi da har cikin zuciyarta ta tabbatar cewa......dukka maganar da zata gita yanzu haka daga bakinsa ,yankakkiyar magana ce wadda babu janyewa a cikinta ko kuma wani sauyi bare sassauci
"Ban rabu da mariya ba don na auro wata matar tazo ta azabtar min da 'ya'ya ba,ina tsananin qaunar 'ya'yana fiye da soyayyar da nake yiwa kaina,duk soyayar da zaki gwadamin bata da alfanu rana ko kuma fa'ida a gareni muddin ba zaki so 'ya'yana ba......asama'u,na rantse da Allah,dai dai da rana guda na samu wulaqanci cin amana ko tsanantawa diyoyina bisa ganganci bawai kuskure ko ajizanci irin na dan adam ba bazan raga miki ba"..... Wani dum taji har tsakiyar kabta,batabtaba kawowa dukka maganganunsa zasu kai har wannan iyakar ba,bata tana tsammanin abun yayi zurfi haka haka ba,da ake gaya mata yana da son yara batabtaba kawowa yakai har wannan bigiren ba.
Zuwa sanda zatakai qarshen tunaninta shi din ya jima da miqewa yana kallonta
"Bazan fasa tafiye tafiye na wajen neman halak da neman abinda zan rufawa kaina da iyalina asiri ba......ba kuma zan kwashe diyoyina na kaisu wanin guri ba,gaki gasu nan asamau,dukkan abinda kika qudirta yi kada ki fasa koki sauya ra'ayi" Ya qarashe fadi yanajin wani irin daci saman harshensa,bai kuma dakata ya saurareta ba ya juya a nutse yana barin dakin nata.
Har sanda ya bacewa ganinta bata dauke dubanta daga bakin qofar dakin ba,ta qanqance idanu tana kallon qofar tare da jin dacin kalamansa suna gauraya kowanne sashe na jikinta. A taqaice dukka bayanansa suna auna mizani da kuma adadin iya matsayinta kenan a wajensa?. Bata shigo gidansa don ta fita ba,don muhallin dame muhallin duka sunyi mata,amma kuma bata shigo bautar d'an kowa ba,hakanan bata shigo don a takata ko aci mata zarafi ba bare kuma a hanata sakewa.
Shawara take buqata kawai a yanzu hala,don gaba kura ne baya sayaki,ta kula dasu ko ta barsu komai ta fanjama fanjam?,to amma fisabilillahi zai yiwu kuwa ace ta buge da bautar d'iyoyin da ba ita tayi Jigilar daukar ciki da kuma rainonsu ba?.
Matsawa tayi kusa da wayar landline dake gefan gadonta,ta latsa lambobi tana fatan sashen kamfanin sadarwar ya sadata da matar data kira take mararin magana da ita. Ba'a dauki dogon lokaci ba sukayi mata hakan,saita qarasa sauke dayar qafar tata qasa tana zama sosai yadda zatafi jin dadin amayar da abinda ke cikinta.
Yanayin yadda suka gaisa kadai zai gaya maka akwai shaquwa me zurfi da tsohuwar sanayya a junansu.
"Ya nake jinki haka sama sama?" Daga saya bangaren ta tambayeta. Sai data aje dogon tsaki sannan ta fara magana,zuciyarta cike da wannan bacin ran da batasan ranar da zai wanke daga zuciyarta ba
"Barni kawai......dukka shirina har yanzun bai tafi a yadda na jima ina tsarawa ba"
"Wani abunne kuma?" Kai ta rausayar tana jin kamar ta qifta idanuwanta ta budesu ta tarar babu kowa tsakiya da gefannin rayuwarta da mijinta,daga ita saishi
"Yarannan haleema......bayansu ya sake kwasomin riqon marayu,bayan wadannan din har yanzu ban gama da matsalarsu ba......" Daki daki ba tare data rage komai a abinda yake faruwa ba ta shimfida mata,sannan ta dora da fadin
"Inajin kamar naje gurinsa ayita ta qare haleema,na meye zaa dinga doramin nauyin da bai zama wajibi a kaina ba?" Ajiyar zuciya haleeman ta sauke
"Ashe qarya kikeyi,baki shirya zaman auren ba" Haleema ta katsi numfashinta sanda taji tana shirin sake dorawa da wata mitar
"Kamar yaya?,ya zakice haka bayan kinsan komai?" Ta tambayeta tana tsuke gira tare da mamakin amsar data bata
"Eh to ai dole nace haka,wani lokaci sam baki da wayo asama'u,yaransa biyu da yake mutuwar so ki gaza riqesu?,bakisan ta hanyar riqon da zaki musu bane zaki samu fiye da abinda kike hange ko hasashe daga jikinsa?" Ta qarashe maganar da sigar tambaya,tambayar data dauki dukka tunanin asama'u ta jefashi wani guri me nisa
"Amma haleema,saina zama baiwar yara har hudu?" Ta yiwa haleema tambayar tana jinjina girman abun,tamkar wadda aka dorawa nauyin wanke kashinsu da fitsarinsu gami da ci dasu tsahon kowacce rana da wuni na rayuwarta
"Bance haka ba,ban kuma goyi bayan hakan ba,yaransa sune dolensa,su zaki kama ki riqe,saura kuwa wannan baida hurumin tilasta miki zama dasu,idan ma baki riqesu ba bakiyi laifi ba,kedai yaransa su zama makamin zamanki a gidan,yo asama'u kona ganin ido ne ke ba zaki iya ba?.......".
Dadewar da sukayi saman waya sa haleema iya adadin karatun data samu daga gareta,ta kwanta ne tana juyawa tare da tauna yadda zata dauki shawarwarin haleema tayi aiki dasu,ta yaya zata danne zuciyarta da dukka wani abu da takeji tayi yadda haleema ta kwatanta mata?.
*_W A S H E G A R I_*
Dukka su hudun suna zaune a gabanshi,yana jansu da hira cikin yanayin da zakayi tsammanin shi din wani babban yayane a garesu bawai uba ba.
Da idanu yake karantarsa,har yanzu dai bai sake ba kamar yadda ragowar 'yan uwansa uku suke a sake. Har yanzu a darare yake,dararewar data sanyashi yaji a ransa akwai abinda ya hanashi sakewar.
Har cikin rai da gangar jikinsa a yanzun da suke gabansa yake jin kamar dukka su hudun mallakinsa ne,shine ya haifesu. Inda yana da iko tabbas zai maida agogon rayuwarsu baya ya mantar da al'ummar da suka sanshi dama na unguwar cewa shi din ba shine ya haifesu su biyun ba.
Tun daga nesa da take takowa cikin falon idanuwanta yake kansu. Sunyi wanka dukkaninsu sun kuma shirya cikin shaddodinsu masu kyau,wadanda tayi imani cikin sabbin kayan daya saba tahowa da yaranne. Sake maida idonta tayi a kansu,a nutse yake qwarai fiye da dan uwansa,ba wani karsashi a tare dashi ko kuma rawar kai,saidai kuma haka siddan takejin muguwar matsananciyar tsanarsa shi da dan uwansa.
Ta yaya tun bata aje nata yaran ba ace wasu yaran sun shigo sun sake cinye gurbi da muhallin mutum biyu bayan gurbin mutum biyun da yaran gidan suka cinye?. A yanzun idan har ta soma aje nata yaran kenan saidai su tashi daga na biyar?,ya za'ayi ta bari haka ta kasance?.
Sai data iso dab dasu sannan ta iya controlling kanta tayi sallama. Dukkansu suka daga kai suna dubanta banda abba da ya kauda nasa kan kadan gefe don da haushinta ya kwana.
Qoqarin gaidata sukayi,ta amsa tana binsu da kallo daya bayan daya,wannan ya sanya kowa ya sake kama kanshi a cikinsu,bansa me babban suna wanda tun daga kallon farko bai sake daga kansa ba bangaren da take.
"Ina kwana abba?" Ta gaidashi cikin matuqar qoqarin daidaita kanta idanunta zube kan kayan breakfast dake gabansu.
"Lafiya lau" Ya amsa mata a taqaice yana rufe plate din fried egg din daya gama ci.
"Yau nayi bacci me nauyi ban samu tashi na hada abincin safe ba"
"Eh laraba tayi.......don dama fita nakeso muyi" Ya amsa mata yana miqewa.
"Ina haka da safiyar nan?" Tayi masa tambayar cikin son sanin komai
"Makarantarsu Faruqee,inason na yiwa su me babban suna registration,next week idan Allah ya kaimu su koma tare baki daya" maganar tayi mata kama da almara ko kuma ba zata. Tana tantamar akwai hikima ko hankali kuwa cikin maganganun abban?,ta yaya zai dauki yaran maqota ya kaisu makaranta me kudade masu ciwo haka?,makarantar dako yaran cikinsa da taji nawa ne school fees dinsu saida taji kishi da baqincikin abun?,ta kuma bashi shawara a fakaice ya kusa sau biyar akan ya sauya musu da wadda bata kaita ba.... Ko don yadda shima wani lokaci ta lura kaman yawan school fees din yana dan takurasa?.
Abinda ya darsu a ranta me girma ne,tana da abubuwan da takeson ta fadi masa amma girman bacin rai da kuma abinda ya tsaya mata a wuya ya hanata cewa komai har suka tarkata suka fice daga falon.
Idan nace ta samu nutsuwa tun daga fitarsu har dawowarsu to zance ne kawai. Sanda suka tashi dawowa din kuma sun dawo da dukka tarkacen kayan amfani na buqatar rayuwa na yau da kullum. Komai hurhudu ya siya,amma kaf cikin siyayyar bataga tsinke nata ba
"Somin tabi kenan hatsin gara a buta......tun yanzu?" Wani sashe na zuciyarta ya ayyana mata. Ai juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Tun a rana ta farko ta soma karantar iyakokinta?,dukka kuma akan yaran da suka kasance tamkar wata tsintacciyar mage?. Yaran da basu da GATA ASALI ko wani GALIHU?. Ita kuwa asama'u yaushe?,yaushe zatayi wannan SAKEN?. Muddin bata bazama su ba lallai anyi asarar haihuwarta,muddin bata ganar dasu kuskuren maida UBAN WANI NASU BA bata cika MACE BA....
*_BAN TABA KOMAI BAFA CIKIN LABARIN......BAN FARA KOMAI BA A CIKI_*
*_zazzafan labari ne tsakanin SABREEN DA MUHAMMED FU'AD_*
*_BANBANCIN RA'AYI TSARI DA AQIDA_*
*_MUMMUNAN ZATO DA GURGUWAR FAHIMTA_*
*_TA YAYA RUWA DA WUTA ZASU HADU GURI DAYA?_*
*_ZALLAR QIYAYYAR MAHAIFIYA HALITTA MAFI SOYUWA A DUNIYA_*
*_BAHAGUWAR BIYAYYA BISA TILASHIN ZUCIYA BA DON RAI YANA SO BA_*
*_GWANA KUMA QWARARRIYA WAJEN SACE ZUKATA DA ALJIHUN MAZAJE DAMA ASUSUNSU GABA DAYA_*
*_KARKI SAKE AYI BABU KE_*
*_WANNAN SALON YASHA BANBAN DANA SAURAN_*
*DUNIYATA(MUHAMMAD JADDA)*
*DUNIYATA(SABREEN)*
_GA HANYA MAFI SAUQI DA ZAKI KASANCE DA ZAFAFABIYAR FAMILY IN SHA ALLAH_👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
Page 06
___________________________
*_TURQASHI_*
*_BIGI SAI BIGI_*
*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*
*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*
*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*
*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*
*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*
*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*
*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Instagram handle_incense by kabo daughter*
*Facebook_kabo daughter*
*Twitter_kabo daughter*
__________________________
Tayi zaune kawai saman kujerar falon tana duban kowa d'ai d'ai da yadda yaran keta walwalarsu da sabgoginsu. Ta yita juya zancan haleema a ranta,anya zata iya kuwa?,zata iya jurewa?,daga bisani data tabbatar muddin taci gaba da zama a wajen zata karya dukka tsarinta saita yunqura kawai ta miqe tana bar musu falon.
Cikin satin ya tabbatar yayi musu dukkan abinda ya dace,ya kuma sauke duk wani abu da uba zai saukewa 'ya'yansa,tun daga suturunsu xuwa takalmansu,kayan makaranta hadi da jaka takalmi da duk wani abu daya zama dole ga dan makaranta.
Zai iya cewa Kansa da kansa sauyi ne na dare daya yazo cikin rayuwarsu,duk kuwa da cewa har yanzun.....daidai da second dayahasashe,koda da wasa irin na qwaqwalwa zuciyarsa bata taba hasashen ta manta da abubuwa guda ukun nan da suka shafi rayuwarsa ba......suka shigeta da wani irin yanayi,yanayin daya tilasta canzawar zubi da kuma tsari na dukkan feeling na zuciyarsa da gangar jikinsa.
Abbansa
Jadda
Da kuma uwa uba mahaifiyarsa da zuciyarsa ke mata wani irin bahagon kallo.
Halitta mafi girma da daraja cikin rayuwarsa......amma kuma dukkan wani matsayi da girman suna da halittar ta mallaka baya jinsa ko dis cikin jininsa da zuciyarsa.
Eh tabbas......a tsukin kwanakin rayuwarsu tayi wani wawan sauyi,saidai nashi sauyin ya tsayane cak iya zahirinsa. Darare da yawa suna wucewa cikin idanunsa. Alfijir dake cikin kowacce asubahi da Ubangiji ya halittama kwanakinmu sun sha ketowa ta cikin qwayar idanunsa. Ta tsakiyar qwaqwalwarsa yana jin kamar an tsatssagarta da wani abu me kaifin tsini
"Me yasa maama taqi zama damu?,me yasa ta kasa jurewa lalurar Abbey?"
"Saboda bashi da komai yanzun,saboda shi talaka ne" Amsar da kullum yakeji ana rada masa kenan cikin kunnuwansa. Sau tari yakan sanya dukka tafukan hannayensa ya toshe qofofin kunnuwansa wai ko zasu daina jiyo masa wannan amsar......waiko amsar tambayarsa zata iya sauyawa?.....saidai aah,koda wasa bai taba jin amsar nan ta sauya ba. Tun baya daukar gaskiya ake rada masa ana kuma sake jaddada masa har zuciyarsa ta gamsu da hakan.
"Indai haka ne maama ita tayi silar mutuwar Abbey......indai haka ne maama itace tayi ajalin jadda" Abinda yake gayawa kansa kenan a duk sanda ya kalli fuskarsa dake dauke da qananun shekaru
"Amma ta yaya ta kashesu?" Tambayar da daya kasa lalubo amsarta,saidai yasan koda duniya zata taru ta hanashi wannan tunanin bazai taba kankaruwa daga qwaqwalwarsa ba har ABADA.
*******
Safiyar litinin ce dake dauke da yawaitar hazo da kuma lullumin sanyi daya soma tun a daren shekaran jiya. Cikin dakin nasu a cikin su hudun kowanne shirin tafiya makaranta yake yiwa kansa don ba wanda baya iya yiwa kansa da komai da komai a cikinsu,daga su Faruqee da suke 'yan gidan,har su da suke baqi ko kuma ace 'YAN RIQO. Kusan za'a iya cewa banbancinsu dasu Faruqee din shine,mamarsu da babansu dukkansu suna a raye,sannan komai tsanani suna da gatan dangi da kuma muhallin da zasu kwana a ciki. Amma ta fuskar samun cikakken gata da kulawa na iyaye,sun tashi kusan a mizani guda,don sun rasa kaso tamanin a cikin dari sanadiyyar RABUWAR AUREn mahaifansu.
"Ya kamata kayi ka gama,wannan laqai laqai din naka ba abinda zai haifar mana sai bata lokaci,kasan dai abba ya koma a motan haya zamu je yau" Faruqee dake saba school bag dinsa yace da saddeq dake kurba shayin da Faruqee ya hado musu dukkansu suka gasa cikinsu.
Kusan ya zame musu jiki,duk randa mahaifinsu ya sanya qafa ya koma Lagos lunch box dinsu yakan koma hoto,zancan breakfast kuwa saidai da tsananin rabo Faruqee ya faki idanunta ya hada musu tea susha su wuce kaman yau. Tasha kamashi bayan anyi hakan,tasha gargadarsa amma a banza wai man kare,gobe ma sai ya qara. Tun tana hukuntashi ta hanyar duka har yakai shekaru sha biyar. Tayi niyyar masa wani wawan duka,amma da yake ance qashin namiji dana mace ba daya bane saita samu targade a hannun nata madadin shi yaji rauni.
Yayi dariyar ranar kaman ba gobe,ya dinga maimaitawa qaninsa
"Alhakina ne". Hakanan taji jiyyar hannun nata ba tare da kowa ya sani ba. Tun daga ranar ta canza kalar horo,saita hadashi da aiki me tsanani,kota hanasu abinci a ranar gaba daya. Irin wannan horon yafi mata dadi idan ya zamana abba baya gari,idan kuwa yana nan abubuwa da dama saidai tayi haqurin dole ta tarasu sai randa ya wuce.
Saddiq da musaddiq ne a gaba,sai shi da Faruqee a bayansu.
Kana musu kallon farko zasu burgeka,ka kuma dauka set din tagwaye ne guda biyu,don dukkansu kusan sa'annin junansu ne. Yanayin zubin kyan halitta da suke dashi,ga kuma wadatacciyar tsaftar uniform da Faruqee bai yarda wahalar cikin gidansu ta sanyashi qazanta ba.
Ba wanda gabansa bai fadi ba cikin su ukun bayan ratsowarsu ta falo da zummar fita daga gidan idan ka dauke me babban suna da ya dauke idanunsa daga kanta tuntuni.
Qafarta daya saman daya tana karkadata a hankali,kamar yadda ta zube musu idanunta tana binsu da kallo kamar qwayar idanun nata zasu zuba a waje.
A darare dukkansu suka gaidata,saidai idanunta suna kanshi ganin yadda ya gaidata hankali kwance,sam kuma kwata kwata babu wannan razani da kuma d'ar d'ar dake kwance a fuskokin 'yan uwansa dake takawa cikin sanda suna fatan wucewa daga falon lafiya.
"Zo nan dan qaruna!" Ta furta da wata kakkausar murya tana sake jin haushi da tsanar yaron. Dukkansu suka waiwayo,ta sake binsu da ido
"Duk ku dawo nan" Ta kuma fada tana gyara zamanta.
Ba wanda ya musa mata suka tako dai dai da dai dai suka zube saman carfet din
"Kai don ubanka waye yace ka shiga kitchen ka taba madarar gidan nan?" Ta jefawa Faruqee tambayar tana watsa masa zagi da hannayenta.
Kiran uban da tayi shi ya sauka har tsakiyar zuciyarsa ya sosata. UBA wani abu mafi daraja da yake ganin kimarsa cikin DUNIYARSA fiye da uwa,ubansa da kuma ABBAN Faruqee mutane biyu da basu da tamkar da bayajin zai iya jurewa zaginsu. Idanunsa ya maida ya lumshe yakuma yi qas da kansa yana hadiyar wani abu me tauri da zafi tamkar shi mama ke tambaya. Wai haka iyaye mata suke ne marasa tausayi?,marasa imani?,me yasa iyaye maza yaketa gani da tambari da dukka wani tabo na tausayawa 'ya'ya?,me yasa kalmominsu suke tsauri akan 'ya'ya cikin rashin tausayi da kyautatawa?.
"Makaranta zamuje,kuma yunwa mukeji"
"Ubanka nace......saboda ubanka ne ya kawo madarar shine kake ganin kana da right na shigarmin kitchen yadda kakeso?"
*_Dukkan godiya sun tabbata ga Allah_*
*_yadda muka fara lafiya Allah yasa mu gama lafiya_*
*_kusa kurai da zaa gani a ciki ajizanci ne irin na dan adam,da fatan za'ayi afuwa a kau da kai_*
*_Don Allah don Allah ina roqo da fatan zaku zama masu uzuri a gareni,saboda yanayin sabgogin rayuwa,kowa ya sani yau da gobe tana iya sauya bawa daga ainihin yadda aka sanshi_*
*_duk sanda kuka samu wani sauyi tattare dani game da tsaiko na posting,tsahon pages da sauransi,ina kyautata muku zaton soyayyarku gareni zata sanya ku zama masu yimin uzuri_*
*_ina godiya qwarai game da yadda bakwa gajiya da bibiyata,da bibiyar zafafa biyar gaba daya_*
*_alkhairin Allah yakai muku a duk inda kuke,tare da fatan ubangiji zai tsareku kuma daga dukkan abunqi_*
*_na gode qwarai,kuma in sha Allah a duk sanda dama ta samu zaku samu komai fiye da yadda kuke so ma cikin wannan tafiya ta DUNIYATA_*
*_LABARIN ZAI TABO BOYAYYAR MATSALAR DA MUKE FAMA DA ITA,na muku alkawarin nishadi da sassanyar soyayya kan bigiren salon da kukafi so😍🥰_*
*MU KASANCE TARE IN SHA ALLAH DAGA FARKO HAR QARSHE*
*HUGUMANKU CE*
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
Read My Book "DUNIYA TA🌏" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
________________________
Page 07
Dif sukayi dukkansu,ba wanda ya iya tanka mata a cikinsu. Daga can qasan zuciyarsa yake jin wani irin zugi fushi da kuma radadi,don meye zata dinga zagin iyaye a gaban 'ya'yansu?,shi abban me yayi da har ya cancanci a zageshi?.
"Badai makaranta zaku ba?,ku tashi ku bacemin da gani". Kaman dama suna jiran wannan umarnin ne daga gareta dukkansu suka miqe din kusan lokaci guda,kowa yana yunqurin barin gabanta kamar yadda ta buqata
" Harda su kaza a cin danqo?" Ta furta tana kama haba idanuwanta a kansa
"Kai dan qaruna ina zakaje?"
"Makaranta mana maama,ko kin manta tare muke zuwa?"
"Na manta uban masu gida,saika karanta min,don ubanka da can makarantar suka damu da zuwa?,shine yanzu saboda wuce gona da iri da samun waje har suke rawar jikin tafiya?.to wallahi kuda makaranta saidai idan anfi qarfina" Ta fada tana kada hannu da kyau cikin hargagi tana nunasu da yatsa.
Hukuncin nata yazo masa a bazata,don bai taba tsammanin zatayi hukunci me tsauri har irin haka ba. Yaji abun ya taba ransa qwarai,domin a yanzun bashi da wani buri daya rage masa saina KARATU. KARATU shine cikar burinsa qwaya daya tal daya rage bai qarasa mutuwa daga zuciyarsa ba,yana jin zai iya bada kominsa don yayi karatu,zai kuma iya jure dukkan wata wahala tsanani ko tsangwama saboda karatu. Ko a yanzun yana daya daga cikin abinda ya sanya zuciyarsa ke qarfafa,tana sake jadda masa zai dauki komai ya kuma jure komai din saboda ingantaccen ilimin da yake hangowa zaya samu. Dole ya daga idanunsa da suka fara sauya launi ya kalleta dasu
"Kalleni da kyau......ba wani karatu da zakuyi cikin gidan da ba na ubanku ba,idan kuma kallon mamaki kake yimin ai uwarka yafi kamata ka yiwa wannan kallon,ita kanta ta kasa jurewa zama daku sai ni da bani da galihu akeson hadani da alaqaqai,to wallahi yadda ban samu yadda nakeso ba,haka kuma ba zaku samu ba......."
"Me kikeso ayi mama?" Ya furta tana aje numfashinta daga tijarar da takeyi. Tsananin mamakin yaron takeyi yadda yakeyin komai cikin dakiya da taurin rai dana zuciya
"Ko baka tambaya ba ai zan gaya maka kuma dole kabi,ka sauke wannan munafukar jakar ku wuce ciki,sudai da babu yadda zanyi dasu gidan ubansu ne saisun dawo,a sauka lafiya" Ta fadi tana nunawa su Faruqee hanya da yatsa.
"Mama.....amma" Zakayimin shuru ko sai ka jawo kuma na hanaku?" Wani dunqulallen abu ya hadiye can qasan ransa yana jin kamar ana masa suya
"Kudin mota"
"Kudin ubanka dai,sayyadarku zaku taka sisi bazan bayar ba" Ya fada tana zazzare masa idanu hadi da dukan hannun kujerar da take kai
"Ku tafi Faruqee don girman Allah" Ya furta da rinannun idanunsa da kuma muryarsa da tayi laushi qwarai yana duban Faruqee din,don kunnuwansa sun soma gajiya da jin zagin da take nausawa bawan Allahn da baisan hawa ba baisan sauka ba.
Kallon kallo suke ma juna shida Faruqee din,kowanne cikinsu zuciyarsa cike take fal da zallar bacin rai daya haurawa shekarunsu. A zahiri tausayin me babban suna shi yafi rinjaye a zuciyar Faruqee. Ba yau ba ba kuma jiya ba ya sani......muddin ka ambaci kalmar UWA ko mahaifiya a gabansa takan zame masa kamar tabo ko kuma ciwo koda ba dashi kake ba,ballantana a yanzun da aka kirata muraran.
Abun ya jima da zame masa kamar wani ciwo,tunda zancan ya bulla cikin unguwa sai ya zama abun yamadidi da magana tsakanin maqota da mazauna unguwar. Sam baa tallafi rayuwarsu ba,ba'a agajesu ba,ba wanda ya waiwaya ya dubi tsanani bayan tsananin da suke ciki,ba wanda ya bawa rayuwarsu tallafin da zai rage musu radadin da sukeji,a maimakon haka,sai suka debo DAFI na cecekucen maganganu akan rayuwarsu suka sake watsawa ciwuka da raunukan dake ciki zukatansu shi da d'an uwansa.
"Kaje Faruqee" Ya sake maimaita masa yana tsareshi da ido. Ya karanci komai ta cikin idanunsa,ya karanci abinda yake nufi da maganarsa,don haka bai qara koda minti daya ba ya kama hannun musaddiq suka suma takawa suna barin falon.
"Na dawo gareka" Ta furta cikin izza da dagawa tare da jinta can saman qololuwar isa da kuma 'yanci
"Ka koma ka zare wadannan kayan,don basu dace da agola irinka ba,tabbas da 'ya'yan da mahaifiya zata wofantar dasu,ta tsallakesu ta gudu ta barsu to ba'a banza ba......don haka banga dalilin da uwar data haifeku bata tausaya muku ta zauna daku ba ni zan tausaya muku ba......tunda kun iso inaga ya kamata me mana wanki da guga ya tafi hutu hakanan,ka shiga dakin ajiyar kayan wanki ka debo duk kayan da ka gani ka fita dasu bayan gida wajen fanfunan can ka wankesu......wallahi wallahi kace zaka saka iskanci a aikin kaga ikon Allah,banaso kuma azahar tayi maka baka kammala ba". Baice komai ba yakau da kai ya soma takawa yana komawa dakinsu ranshi yana wani irin tafasa da suya. Tsanar maama tana sake wani mahaukacin tasiri cikin ransa. Inda bata tafi ta barsu ba duk tsanani duk wuya,komai girman talaucinsu sunfi gaban a goranta musu,don da iyaye ake ado,sune abun adon diyoyinsu.
Me yasa ta aikata hakan?,me yasa ta kasa jurewa?,tsabar son kai ne irin na jinsin DIYA MACE da ya tabbatar a yanzun haka halittarsu take?.ko kuma son duniya da qyale qyalen cikinta ne ya rudeta?. Me yasa batayi haquri ba kaman yadda Abbie ya dinga kira mata?. Har yau har kwanan gobe sashen qwaqwalwarsa da ya nadi muryar Abbie ta qarshe.....magiyar Abbie ta qarshe akan roqarta ta zauna ya gaza goge su......ya gaza goge wannan rarraunan sautin nasa daga nemory dinsa. Abinda ke sake aza masa wata mahaukaciyar wuta,tare da dasa masa fara kallon halittar diya MACE a baibai.
Yana cire kayan saddiq yana kallonsa,a duk sanda zuciyar dan uwansa ta motsu shine mutum na farko dake fara fahimtar hakan. Ya kammala cire kayan tsaf ya musanya dana gida sannan ya juya ya adana na makaranta yana musu kallon tsanaki,dukka ruhinsa da zuciyarsa tana makarantar,yana wassafa malami na farko ya fita zuwa yanzu,malami na biyu kuma na dab da shiga ajin komai yana ciki.
Hannu ya sanya ya share fuskarsa yana qoqarin lanqwasa zuciyarsa. Farat daya qaunar da yakewa karatu ya ninku a zuciyarsa ganin abba ya bashi dukkan wata dama da zaiyi karatun,sai gashi farat daya tana nema ta zama silar da zaiyi nisa sosai da MAFARKINSA?.
_________________
*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*
*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*
*_NA GWADA NA GANI_*
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*
*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*
*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*
*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*
*_ME KIKE JIRA?_*
*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*
*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*
*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*
*_zaki dariya za kuma ki godemin_*
*_gani ya kori ji_*
*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
_________________
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 08
__________________________
*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*
*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*
*_NA GWADA NA GANI_*
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*
*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*
*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*
*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*
*_ME KIKE JIRA?_*
*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*
*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*
*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*
*_zaki dariya za kuma ki godemin_*
*_gani ya kori ji_*
*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
___________________________
"Hamma" Ya tsinkayi muryar saddiq tana kiransa,sai ya waiwaya ya zubawa qanin nasa ido
"Wai sai yaushe maama zata dawo?,yaushe za'a daina yi mana gori?" Tambayar ta tsinka zuciyarsa sosai ta kuma sake yi masa tabo. Ya zuba masa idanu sosai,kamar bazai ce komai ba sai ya motsa labbansa
"Duk tsanani duk wahala.....kada ka sake zancanta sadiq,ta tafi kenam,ba kuma zata sake waiwayomu ba.....ni zan tsaya dakai a kowanne yanayi da.mataki na rayuwa,bazan bari kasha wahala ba in sha Allahu,bazan bari ka zubda hawaye irin wanda na zubar ba.....kayimin alqawari ba zaka sake zancan maama ba?" Ya qarashe maganar yana ritsashi da idanu.
Kai ya jinjina a sanyaye yana maida jikina ga bango ya jingina,wani abu sosai yaron yakeji da baisan yadda zai fasalta shi ba
"Ka cire uniform din" Ya bashi umarni ya sanya kai yana nufar qofa bayan muryar mama ta karade ilahirin gidan ta cimmasa har dakin nasu
"Yaaya zan tayaka wankin" Sadiq ya fada a gaggauce
"Aah banaso,kayi zamanka" Ya amsa masa yana qarasa ficewa.
Tun daga wannan rana ta sauya lokutan zuwansu makaranta zuwa lokuta na bauta da wahalar ayyukan gidan da basu ratayu a wuyansu ba. Duk wani aiki ta kallafa masa,har takai ta bawa ainihin masu gudanar da aikin hutu tace saita nemesu,hutu ba tare da an yanke musu albashi ba.
Dukka yawa da azabar aikin aikin banza ne a garesa idan aka kwatantashi da maganganu masu dafi da take jifansu dashi. Duk kalmarta guda daya me tsananin guba ce tana kuma same zuba masa dafi da guba me daci ne cikin zuciyarsa. Rashin ko inkula dinta a kansu da dukka dabi'unta basi fiya bashi mamaki ba,saboda ya riga da ya yiwa mata kudin goro gaba daya,tunda ya fara ganin sample daga kan mahaifiyar data tsugunna ta kawoshi duniya kuma. MATA BASU DA IMANI,BASU DA KIRKI,BASU DA TAUSAYI,BUQATAR KANSU CE A GABA DATA KOWA.
Wannan shine rubutaccen abu daya zauna radam cikin kwanyarsa da zuciyarsa,wanda baya jin akwai lokacin da zaizo wanda wannan zai wanke daga cikin kundinsa.
Duk yadda Faruqee ke cikin tsananin fushi da daukar alwashin sai ya gayawa abba idan ya dawo,in yaso ta kamashi ta gutstsira namansa ta kacalcala amma me babban suna ya danneshi ya kuma haneshi
"Maama ma data haifemu ta gujemu,ta gaza tausaya mana?,ta kasa haquri damu?,ina ga mama......mu din ba dolenta bane Faruqee,iya abinci da take sawa ana bamu da gurin kwana ma kawai tayi qoqari"
"Abincin nata ne?,ko gurin kwanan nata ne?,sannan shi kansa abincin waye yake qoshi?,bayan store din gidan nan cike yake da kayan abinci?" Qaramin murmushi ya saki. Duk da qarancin shekarunsa amma kwanyarsa tana aiki yadda ya kamata. Dukka wannan bai cika masa ciwo bafa,abinda maama tayi ya danne dukka wadannan ciwo da zafi da kuma tsaiwa a zuciya. Abu daya ne yakejin yana dab da kasa jureshi,hanashi zuwa makaranta......yana qaunarta yana qaunarta yana qaunarta har baisan iya adadi ba. Abu na biyu indai saddiq dinsa yana lafiya to komai me sauqi ne.
A haka suka debi wata guda cur babu abinda ya sauya. Yadda kowacce safiya da ubangiji zai bullo da ranarsa haka zata fidda wani sabuwar muguntar don quntatawa cuzgunawa a garesu. Duk fushi zafin zuciya da rashin daukar raini irin nashi bai taba daga kai ya kalleta bare ya tanka mata ba,yana duba cewa ta girme masa,gaba take dashi,a qalla ta ninka shekarunsa sau biyu. Duka duka shekarunsa sha shida basu kai adadin shekarun da zai tsaya yana jayayya da babba ba.
A hakane ALHAJI HAMZA KIBIYA ya waiwayo gida cikin iyalansa.
Yaran suna ranshi matuqa,babu kuma ranar duniya da zata bullo ta bace bai tambayeta su ba idan suna waya,amsar kuma daya ce suna lafiya lau. Koda ya buqaci magana dasu tana gabatar masa ne da wani uzurin a kansu.
Wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi. Sanda ya sanar da dawowarsa kaf ta hadasu ta musu mummunar jankunne data tsoratasu ainun. Saidai ko kadan shi bai tsorata ba,don ba komai yake bashi tsoron ba,bare a yanzun da zuciyarsa ke qarasa bushewa da qeqashewa akan komai na rayuwa.
Yadda aka saba haka ta sakar musu,sukaci gaba da zuwa makaranta abba yana kaisu da kanshi kamar yadda yakeyi idan har yana gari.
Ya tsumu sosai,zuciyarsa kuma ta cika da takaici da bacin rai me yawan gaske sanda ya isa class dinsu yaga yadda aka tsere masa a karatu. Kusan ranar duka ya qarar da ita wajen bibiyar dame dame akayi da baya nan?,ya karbi note books na classmate dinsa da dama ya taho dasu gida .
Da yake abba yana nan akwai isashen lokaci 'yanci da kuma hutu,babu tarin aikace aikacen nan marasa dalili marasa kuma tushe ballantana makama,sai ya zauna ya qarar da dukka wuninsa a daki wajen ganin ya daidaita karatunsa dana 'yan uwansa.
Bashi da matsala da saddiq,don ajinsu daya da musaddiq,kuma duk sanda suka dawo gida Faruqee yana hadasu su sake maimaicin karatu tare ta yadda zai zamana ba'a wuce saddiq din ba.
Yana da wata irin baiwar basira ta gasken gasken,sharp brain dake da saurin koyo da kuma riqe abu tun yana dan mitsitsinsa ballantana a yanzun da yake shirin fara shiga shingen samartaka,danyan jini yana zagayawa da gudu a jikinsa. Wannan ya taimaka cikin sati gudan da abba ya musu hutu ya gama kammala komai,ya kuma tarar dasu tamkar dama dashi ake karatun. Sai a sannan ya samu sukuni ya soma dawowa daidai. Saidai kuma a satinne qarshen satin,a yammacin juma'a abban ya tattara ya koma lagos,abu guda daya dake alamta musu zasu koma RAYUWAR GIDAN JIYA kenan cikin gidan.
*********
*_MONDAY_*
Tushen aiki,bai sare ba ya shirya tsaf kamar yadda su Faruqee ke shiryawar,yana shirin Faruqee na rantse rantse da cewar ba abinda zai hanasu fita a makaranta yau din. Ya lallaba kitchen ya hada musu tea kaman yadda ya saba ya dawo ya bawa kowa,saidai ya tsallake me babban suna don yasan bazai sha ba,don kuwa tun daga wancan ranar data zagi abban bai sake ci ko shan wani abu da Faruqee zai dauko musu ba,ya tsani zagin iyaye matuqa,mutum ne kuma me fushi da gudun zuciya,wannan ya sanya yake takatsantsan,akan komai bai fiya zura jikinsa ba.
Fitowa sukayi kamar wancan karon,saidai a yauma sun sameta hakimce a falon. Idonsa yadan lumshe yana addua daga qasan zuciyarsa. Ya tabbatar wannan zaman ta yishi ne saboda su,son a lokutan da abba yake gari kwata kwata nasa ganin qyallinta sai kusan shada zuwa sha biyu na rana.
"Eh......wato akuyar daure an samu sake,to kuzo nan" Faruqee ne na farko daya fara cakewa guri daya,amma ya kama hannunsa ya jashi suka qarasa wajen.
"Me zakuyimin ku?,tunda kuna da uba ya daure muku gindi?,ku tashi kuban waje,ku kuma ku koma ta inda kuka fito a cire uniform azo a kama aiki ko?" Cikin tsananin bacin rai Faruqee ya miqe yana nufar hanyar fita yana kuma qananun maganganu qasa qasa
"Zagina kekeyi farouqu?,ka kuskura ka zageni ubanka zanci wallahi la'ada waje" Ta furta da hargagi tana nunashi da yatsa sanda suke kusa da ficewa daga falon. Abinda ya sanya me babban suna miqewa yana jin nauyi da kuma zafin zaginnan. Ko meye zatayi me ya gamo da iyayensu?,me su sukayi mata idan su din masu laifi ne a gareta?.
"Don Allah mama ki barmu muje muma,idan mun dawo zamuyi miki duk aikin da kikeso"
"Kai.....wasa nakeyi dakai?,zaka tashi ka bani waje ko sai na zagi uwarka mara daraja da ubanka dake qarqashin qasa?" Kamar saukar mashi haka kalamanta suka soki zuciyarsa,har sai daya kasa jurewa ya waiwayo yana dubanta.
"Don Allah mama ko meye,ko meye mukayi miki ki mana hukunci ba tare da zagin iyaye ba......"
"Ubanka da uwarka,shegen yaro me tsaurin ido,kaci ubanka" Ta fada har tana zullo tare da watsa masa daquwa. Ta jima da tsanar dama wannan kamewar tasa,ta jima da tsanar yadda yake da dauke kai da rashin hayaniya akan komai da zatayi masa,duk yadda takai ga tama masa wajen bashi baqin kashi da baqar wahala don ya magantu dukka ya shanye sai a yau din.
Cikin qasa da minti guda launukan idanunsa suka sauya,baice qala ba amma kunnuwansa suna suna iya jin zafafan muggan kalaman da take jifanshi dasu. Ya tako a nutse ya iso gaban saddiq dake durqushe a gabanta ya sanya hannu ya damqi hannunsa ya tasheshi tsaye,abun sai ya masa kamanceceniya da sanda saddiq din ke tsananin roqon mahaifiyarsu akan kada ta tafi ta barsu.
Bai waiwayeta ba,bai kuma dakata ba ya durfafi qofar fita daga falon kanshi tsaye,ba tsoro ba shakka ba kuma shayi
"Ina zakaje,bance ba zakuje makaranta ba?" Ta furta da qaqqarfan sauti. Bai dakata ba bai kuma waiwayo ba ko ya nuna yasan tanayi har ya fice daga falon. A yau ta rushe dukkan wani ragowar kara da dagin qafa da yakeyi mata. Baya wasa da kalmar UBA sam a rayuwarsa,IYAYEN MA guda biyu,abba da Abbey.
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
________________________
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 09
Ko Faruqee baisan da zuwansa makarantar ba sakamakon banbancin abinda kowannensu yake karanta,har sai sanda aka fito break.
Har a sannan ranshi a jagule yake,bacin rai kowanne second yana sake motsa zuciyarsa. Faruqee ya sameshi daga bayan makarantar zaune qasan bishiya saman rairayin dake wajen,hannunsa riqe da busashen siririn reshen bishiyar yana tona qasa dashi,ya kafe qasar da idanu kamar me nazarin samar da wani abun amfani daga gareta. Ta gefansa ya zauna,yayi masa tambayar duniya akan ya akayi ya taho makarantar amma ya gaza cewa komai. Na Faruqee ba,tunda ya shiga class din baiyi manana da kowa ba,don bayajin koda ya bude bakinsa akwai wasu kalmomi da zasu iya fita daga cikinsa. Dole Faruqee ya haqura ya kuma tayashi zaman shurun,don dukkansu dama babu me 'yanci ko damar yin break,to inama kudin?,dukka dana transport din da komai ta hada ta kalmashe.
Sai a hanyar komawa yaji komai daga bakin saddiq. Qwafa yaja yana girgiza kai
"Duk yadda kake tunanin matar nan ta wuce nan,duk kuwa yadda zan fasalta maka,ta samu sassauci ne daga garemu shi yasa take abinda taga dama,ace mutum ya shiga shekara ta sha biyar,kana girma amma baka da 'yanci?" Shikam baima iya cewa komai ba har zuwa sanda qafafunsu suka maidasu gida.
Sai da suka gilma ta gaban gidansu kafin su cimma gidan RIQOnsu a yanzu,idanunsa zube bisa fuskar gidan dake garqame da kwado. Take yaji wata matsananciyar kewar gidan da kewar Abbie da jadda suka saukar masa. Duk da suna rayuwa ne cikin matsakaicin matsayi na rayuwa,amma rayuwarsu rayuwa ce me 'yanci da kuma dadi. Duk da suna rayuwa da maama cikin wani baqon hali da murdaddiyar dabi'a.......hakan yafi musu sauqi a kan rayuwarsu ta yanzun cikin gidan RUQO.
Ya janye idanunsa sanda ya dubu daidai wajen da mahaifinsa ya dogaro da qyar ya biyo bayan maaman yana cike da fatan zata dakata daga aiwatar da qudurinta nayin nesa da rayuwarsu,wani zafin akan na dazu ya sake yunqurowa ya mamaye zuciyarsa.
Daga saman balcony din da zata sadaka da ainihin falon suka sameta a zaune ta hakimce. Faruqee ne a gaba,musaddiq yana biye dashi,sai me babban suna da ko qaunar hada idanu da ita bayayi. Zuciyarsa yadda take a zafafen nan tana ayyana masa abubuwa masu dama a kanta.
"Idan ka kuskura ka qaraso na saina sanya an maka dukan tsiya......baka isa ka shigamin gida ba tunda kai din tantiri ne mara kunya.....nan gaba kadan shaye shaye zaka farayi da daba,kaga kenan ka samu hanyar da zaka hallakani a banza" Ta fada tana miqewa tsaye.
Dukka su hudun sukayi carko carko suna dubanta da jin kuma wani sabon bala'in daya tunkarosu kuma bayan na dazu da safe.
"Kai har ka isa na fadi magana ka sabamin bare ka maidamin?,don an zagi uwarka da ubanka,su su waye da ba za'a zagesu ba?,wato gaka kai me zuciya ko,to an zagesu din na kuma zagi banza da wofi".
Da qarfi ya damqi hannun saddiq ya kuma soma ja da baya yana janye jikinsa daga wajen
" Yauwa gwara daka fahimta,don wallahi kabar gidan nan kenan,tun yanzu kana tsayarmin ina ga nan gaba idan ka gama zama balagagge?".
Da sassarfa Faruqee da har ya isa bakin qofar falon ya soma saukowa yana takowa zuwa garesa ganin suna nufar gate din fita daga gidan yana qwala masa kira da niyyar tsaidashi
"Aisai ka bishi kaima don ubanku,na fiku iskanci qananun balagaggu" Ta furta tana komawa saman kujerar ta zauna
"Bar nan gurin" Ta kwatsawa musaddiq daya mace a wajen saboda tsoro da mamaki tsawa,baiyi wata wata ba ya juya shima yabi bayan 'yan uwansa.
Bai iya tsaidashi ba har sai da suka isa qofar gidansu dake garqame. Sai sukayi carko carko suna kallon kallon shi dashi. A yadda ya hangi kwantaccen fushi da bacin rai akan fuskar me babban suna sai ya rasa da wadanne kalmomi zai iya shawo kan me babban suna?,wacce kalma ce zatayi masa aiki?.
"Kayi haquri kazo mu koma,tunda gidan abba ne ba nata ba bata isa ta hanaka zama ba,yau ko kasheni zatayi saidai ta kasheni" Wani irin kallo ya yiwa Faruqee,ga mamakinsa murmushi ya gani ya subuce masa.
Da wani irin zafi ya waiwaya ya dauko dutsen dake yashe gefan malalen simintin dake gaban gidan nasu,har tsoro ya kama Faruqee yaja da gefe,sai yaga ya doshi qofar gidan,ya kama kwadon dake jiki ya fara bugeshi baji ba gani.
Tsakiyar azahar ne,wannan ya sanya ba yawaitar jama'a a layin bare a samu me dakatar dashi. A yanayin da yakejin zuciyarsa da kansa a ciki,bayajin akwai ma wanda ya isa ya dakatar dashi din sai MUTUM DAYA TAK A DUNIYA.....ALHAJI HAMZA KIBIYA.
Zare kwadon yayi ya watsar gefe,kansa tsaye kuma ya soma cusa kai cikin gidan ba tare daya damu da yana datti ko qurar data lullube qofar ba.
Wannan shine mafarin komowarsa gidansu......tushensa......asalinsa da yaji yafi masa kwanciyar hankali sau dubu akwan kwanansa cikin babban bedroom din gidan alhj hamza dake dauke da wuta 24/7 da kayan alatu na rayuwa.
Tun a asalin halittarsa shi jajirtacce ne tsayayye da bai yarda da faduwa ba......sanda komai ya dinga faruwa kuma daki daki,sai zuciyarsa ta qara qeqashewa ta kuma tsaya kyam......ya karantawa kansa da kansa cewar shine uwa kuma uban kansa da dan uwansa sadiq.......shine gatan kawunansu,ya fidda kowa daga cikin zuciya rayuwarsa dama hasashensa. Wannan ya sanya tun rana ta farko da suka dawo gidan bai kuma karbar koda ruwa daga gidan alhj hamza ba. Duk da yadda ran Faruqee ke baci da yadda yake wofantar da komai da ya kawo musu din kuwa koda ruwan sha ne. Da kansa ya tsaya,sadiq na debo ruwa shi kuma yana wanke komai da yayi saura na gidan wanda zasu iya amfani dashi. Cikin kwanaki uku kacal ya fara Qwadago.
Duk wani aiki da zai samar masa kudi......komai wuyarsa kuwa muddin halas ne yana karba yayishi hannu bibbiyu. Da wannan din ya dogara.....da dan abinda yake samu din ya dauke musu abinci dama abin sha......idan faraga ta samu harda kudin transport na makaranta koda na zuwa kadai ne banda na dawowa.
Sauyawar yanayi da kuma tsarin rayuwarsa ya sake canxashi gaba daya. Yana tsananin son karatu kowanne iri ne,na addini dana boko gaba daya
*_TURQASHI_*
*_BIGI SAI BIGI_*
*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*
*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*
*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*
*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*
*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*
*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*
*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Instagram handle_incense by kabo daughter*
*Facebook_kabo daughter*
*Twitter_kabo daughter*
________________________________
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 10
Baya wasa da islamiyya,amma wahala da nauyin kansa dana saddiq ya sanya ya sallamawa zuwa islamiyya. Duk da haka bai sare ba,ya lalubi makarantar magariba ta manya ya soma zuwa don karantar litattafan addini,duk kuwa da nisan zangon tafiya dake a tsakaninsu.
Su kansu ba 'yantattun 'ya'ya bane cikin gidan mahaifinsu......amma duk da wannan ya gaza barin me babban suna yakuma qyaleshi kamar yadda ya fuskanci yana da muradin hakan. Duk da basu da 'yanci ko fada aji a gidan......amma hakan baya hanashi dauko abinci daga cikin nasa kwanon data qayyade musu cikin gidan ya kawo don suyi tarayya suci tare,amma koda wasa me babban sunan bai taba dangwala yatsarshi a ciki ba.
Abun yana ma Faruqee zafi da ciwo matuqa,har daga qarshe hakan ya sanya suka samu sabani
"Don mama tayi maka laifi ai ba abincinta bane,abincin abba ne wanda har yanzu a nasa zaton kuna cikin gidansa ne cikin aminci bisa kulawarta,iyakarta da abincin nan tazo ta diba itama taci,don ko dafawa ba ita ke dafawa,larai ce......kuma ita ke qaramin yawan abincin a boye ba tare da saninta ba,to indai bawai nima gaba da fushi kakeyi dani ba banga abinda zai hanaka ci ba.....idanma kai ba zakaci ba....kada ka sake hana saddiqu yaci,kai ka zauna haka can ta matse maka". Busashen murmushi ya saki yana jin yadda cikinsa ke qugin yunwa,don yau ba wani abun kirki ya samo a aikin ba,wannan ya sanya basu wani qoshi ba wunin ranar sur.....ga kuma tafiya makaranta a gabansu gobe juma'a.
Yadda Faruqee yayi fushi ya kuma dauki zafi da abun ya sanya yake barin saddiq din suna hadaka dashi. Shikam yasan bazai taba iya sanya abincin cikin bakinsa ba. A duk sanda yayi yuqurin hakan sai maganganunta su dawo musu kar kar cikin qwaqwalwa
"Tunda uwarka ta zube ku ta tafi ta barku,banga uban da zai iya zama daku ba......uwarku ma ta barku ballanta wani?" Aduk lokacin da zai tuna da irin wannan maganar a take yakanji komai ya fita a kansa ne,tsananin baqinciki ya mamaye walwalarsa,wata irin wuta me zafi na taso daga qasan zuciyarsa da ruhinsa dangane da imaninsa. Ta wani fuskar da mama da sauran 'yan unguwa dake jifansu da muggan kalamai sai yaji sam baya jin zafinsu ko kadan,da uwa da uba da kuma dangi ake ado,su kuma basu da ko guda daya!. Ya tabbata lallai su din cikakkun marasa gata da galihu ne,kuma kowanne suna aka kirayesu dashi sun cancanta.
Yayi imani inda har jadda tana raye.....koda sunfi kowa talauci da matsin rayuwa......to babu shakka zasu zamo na sahun gaba gaba wajen zama yaran da sukafi kowa samun gata na kulawa da soyayyar kaka. Saidai Allah baya barin wani don wani yaji dadi,ya tabbatar haka ubangiji ya tsara musu tasu DUNIYAr,haka kuma yaso ganinsu a cikinta.
A wannna tafiyar abba yayi nisan kiwon da ya jima baiyi irinsa ba. Yana rayuwa bisa yaqinin lallai gidansa da marayun Allahn daya dauka riqo suna lafiya,tunda duk sanda zaya kirata hakan take gaya masa,sannan lokaci bayan lokaci tana hadashi da musaddiq,shima kuma
"Lafiya qalau muke abba" Shine amsar da yake bashi bisa jagorancin mummunan gargadi da idanuwa da maman take aike masa duk sanda suke wayar. Faruqee ne bata taba yarda ta bawa wayar ba,sai a wani yammaci da abban yace ya jiyo muryarsa ta hadasu.
"Lafiya amma ba qalau ba amma.....muna buqatar ka dawo a kusa abba" Bata iya barinsa ba ta fusge wayar daga hannunsa cikin hanzari ganin yana niyyar sauka daga layi.
Maganar ta tsayewa abban a rai,ta kuma sanyashi yaji dukkan hankalinsa yana tarkatowa yana yowa gida. Duk kuwa da akwai sauran abu daya tsara zaiyi a can din,amman sai yaji komai ya fita a kansa tahowarsa gida ce abu na farko da yake kwana yana tashi dashi.
*******Kusan dukkansu jan qafafunsu sukeyi,zafin rana yunwa ga gajiya dake tattare dasu. Akwai nisan tazara me dan dama tsakaninsu da makarantar wanda suke shanyeta a qasa daga tafiya zuwa dawowa. Babu ranar hutu a garesu idan ba asabar ko lahadi ba. Ga me babban suna kuwa,baya gane asabar ko lahadin cikin rayuwarsa da DUNIYARSA. Rayuwar tasa gaba daya a birkice take,bashi da wata dogon hutu daya wuce makaranta zuwa neman kudin abinci.
Yayi wani irin duhu,dukkan hasken fatar nan da suka gado babu shi,ya rame daga ainihin halittarsa zuwa wata halitta ta daban.
Tun daga nesa ya soma hangen wani abu da yayi matuqar girgiza hankali da kuma tunaninsa,ya sanya dukkan wani tunani nashi ya fara sauka daga kan layi,ya kuma daina gane me Faruqee daketa faman bashi labari yake fadi.
Wata qurace take tashi daga wani sashe na gidansu gami da qarar zubewar bulalluka. Gefe guda akwai tsaiwar tsirarun mutane da kuma yara wadanda basa raina abun kallo,hakanan basa bari abun kallon ya wucesu kamar qanqantarsa.
Zame hannunsa yayi daga jikin na Faruqee,a gaggauce da kuma hanzari ya soma tattaki har zuwa inda aikin ke gudana.
"Gidanmu ne fa.....me yayi ake rusheshi?" Ya furta bayan ya tabbata ya tsaya gaban mutanen dake gabatar da aikin futu futu cikin qasa da qura.
Dukkansu suka waiwayo suna dubanshi,kafin daga bisani wani dan tsamurmurin mutum dake sanye da milk riga da wando na shadda,da kuma babbar riga ta koriyar shadda gami da baqaf hula daya karkatata gefe ya qaraso gabansa yana dubansa. Bakinsa cike da gashin baki,kai kace daya daga cikin qabilun da suka shude ne shekaru aru aru.
"Yaro me kake cewa?" Ya fadi yana saba babbar rigar da a zahiri an tafka babbar asara wajen ware shaddar aka masa rigar da ita gaba daya,don kuwa yadin ya masa yawa,alamu ma suna nuna kamar rinjayarsa takeyi
"Gidanmu ne nace,me yasa kuke rushe mana gida?" Ya sake jefa tambayar ga mutumin yana tsareshi da ido da zummar jin ba'asin maganar.
Qaramar dariya yadan saki yana sosa gashin bakinsa da alama qaiqayi yake masa.
"Yaro man kaza......kai!bakasan tsohuwarka ko ince uwarka ta karbi rabin kudin gidan daga hannun matata ba sanda zata bar garin?". Fuska da idanu gaba daya me babban suna ya yamutse yana duban mutumin cike da zallar mamakin da kwanyarsa ta gaza dauka.
" Ko da yake ma.ba fahimta ai zakayi ba,wannan zancan na babanka ne inda yana raye,ba abinda zaka gne yaro" Yana kaiwa nan sai ya juya yana dubañ mgainan
"Kuyi ku raba ku zagaye mana haqqinmu" Da hanzari yasha gaban mutumin jin kalaman da yake sake maimaitawa
"Kada su sake taba mana gida,don nan vidan ba gudan mamata bane da zata saidashi,gidan mahaidinmu ne daya ginashi da guminsa,ta nemeta ta biyata kudinta amma mu ba ruwanmu" Tsaiwa yayi yana qanqance idanu hadi da duban me babban suna
"Kai wannan yaron da alama zakayi tsaurin idanu,da alama dai abinda ake fadi a kanka gaskiya ne......to ai ko kai yanzu ba zakace ga inda uwar data haifeka take ba,tunda ta bazama yawon duniya ta watsar daku.....". Kalmar ta sokeshi qwarai kamar kowanne lokaci. Duk a iya adadin fadar da akeyi bai taba yunqurin kare musu jifan da ake musu da kalmar ba,amma a yau din sai yaji koda sau daya yana da sha'awar huce musu wannan takaicin shi da saddiq.......yana da marmarin maida martani koda sau daya ne tak......amma baya sha'awar bata kariya ko wanketa daga muggan kalaman mutane a kanta,don bashi da abun cewa a kanta,kwata kwata dukkan wata soyayya qauna ko tausayi na fil'azal a tsakaninsu yanxun baya jin akwai burbushinsa,abinda ya sani kawai ya kare kansa ya kare saddiq dinsa
"Ba abunda ya shafemu da inda taje ko inda take.......kaman yadda ba ruwanmu da karbar kudinku da tayi don nan gidan mallakin mahaifinmu ne mallakinmu......abinda muka sani kawai shine mu din halastattun 'ya'yane da aurar ya samar......"
Daya daga cikin ma'aikatan wanda kuma gidan su yake ta qarshen layinsu wanda ke tsaye gaban tsani ne ya bushe da dariya
"Dame kwado yafi gaya ku da shegun?,dame kuka fisu?" Yana kaiwa nan ya dauki qatuwar gudumar da suke dukan saman ginin da ita ya soma taka matattakalar tsanin yana hayewa da zummar ci gaba da aikinsa na ragargazar ginin da mahaifinsu ya kwashe lokaci yana zuba kudadensa wajen qawata musu shi. Ya sadaukar da kudi da qarfinsa wajen samar dashi,ya sanya burinsa akai na ganin sun rayu a cikinsa cikin aminci da kwanciyar hankali.
Kwata kwata kasa jurewa yaji yayi da mummunar kalmar da yaji ya jefesu da ita. Sanda ya daga gudumar zai doka......daidai lokacin ba tare daya ankara ba ya sanya hannu ya fusgoshi sai gashi qasa warwas!. Abinda ya sanya dukka jama'ar dake tsaitsaye a gefe tun dazun basuyi magana ba yunqurowa,masu salati sunayi masu yunqurin tayar da babba magini sunayi.
Wani irin mamakin sauyar rayuwa da mutanen dake rayuwa a cikinta ya kamashi. Da idanu yake binsu
*_TURQASHI_*
*_BIGI SAI BIGI_*
*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*
*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*
*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*
*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*
*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*
*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*
*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Instagram handle_incense by kabo daughter*
*Facebook_kabo daughter*
*Twitter_kabo daughter*
*D U N I Y A TA*
*_H U G U M A_*
PAGE 11
_____________________________
*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*
*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*
*_NA GWADA NA GANI_*
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*
*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*
*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*
*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*
*_ME KIKE JIRA?_*
*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*
*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*
*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*
*_zaki dariya za kuma ki godemin_*
*_gani ya kori ji_*
*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
___________________________
Daga sanda ya jawoshi ya maidoshi qasa......daga sannan yaga iya yawan adadin mutanen dame wajen wanda sam baiyi zaton sunkai haka ba,bai dauka suna da yawa haka ba.....amma duk da wannan yawan nasu babu wanda yayi yunqurin yin wani anu guda daya sanoda ceton rayuwarsu da cetin ginin gidan dashi kadai suma!mallaka a rayuwarsu wanda zasu nuna suce ya fito daga jini da gumin mahaifinsu?. Me yasa al'umma ta sauya?,ya dinga duban fuskokin masu luguiguita zancan da kambama abinda ya aikata din,dukkansu suna tsaye sanda ake himmar rugurguza mafaka guda daya tasu da tayi saurs,ba wanda ya tallafa,ba wanda ya dakatar. Kusan dukkansu fuskokinsu bayyanannu ne a idanunsa,fuskokin daya saba gani sunzo neman taimako wajen mahaifinsu,wanda bai taba gazawa ba da taimaka musu da abinda Allah ya hore masa,amma yau tsantsar butulci irin na dan adam sune suka juye suna masu tsaiwa suna kallon wasy na shirin zaluntarsu.
A sanda yayi nisa da wannan tunanin a lokacin babba yayi amfani da wannan dama yakai masa duka,dukan da yazo masa a bazata banda jin hucin wucewarsa da yayi da hucin hannun Faruqee daya tare masa dukan. Yaja baya yana maida hankalinsa jikinsa,sai ya taka dutse ya kuma yi taga taga ya fadi da baya,wannan ya sanya babba ya sake yunquro masa da nufin turmesheshi cikin baraguzan ginin gidan da suka fara saukewa,sai Faruqee shima ya taso ya rufa masa baya da zummar baiwa me babban suna din dauki.
Cikin zafin nama fushi da kuma taurin kai gami da kafiya da taurin zuciya Shima ya yunqura ya miqe yana jiran qarasowar babba. Idanunsa a lullube suke da bacin rai,baya hangen nisan tazarar shekaru da kuma girman jiki dake tsakaninsa dashi.
"Kai.....kai......dakata.....meye hakan?" Muryar nan me cike da kamala tausayi da dattako ta ratso gurin. Kowa ya tsaya ya waiwaya yana duban saukowarsa daga motar zuwa takowarsa cikin fusassun duwatsun gurin. Alhaji hamza kibiya ne idanunsa na kai kawo tsakanin Faruqee me babban suna da kuma ginin gidan nasu.
Mutum ne me cikar kamala da dattako,wanda ya riqe mutuncinsa da kyau. Yana daya daga cikin dattijan unguwa dake bada Umarni ko shawara abi,musamman da yake yana da abun hannunsa wato kudi abokan tafiya.
Kunya tadan kama manyan dake wajen da basu hana ba sai tsaiwa kallo da sukayi,wanda sun tabbatar idanuwansa sun gansu gaba daya.
Bai tsaya sauraren barka da zuwan da suke masa ba,sai qoqarin qarasawa gabansu kawai da yakeyi bayan yace da saddiq da musaddiq su tsaya daga baya,wanda dukansu suka tsorata tun farkon rigimar,to amma basu dame kawo musu dauki bare suyi hanzarin garzayawa su kirashi ko zai cecesu.
Ta gefan babba dake tsaye yana kade jikinsa cikin jin nauyi yana kuma huci qasa qasa ya wuce,ya qarasa inda me babban suna ke zaune warwas ya miqa masa hannu ya tasheshi tsaye.
Yana tsaye a gabansa ya bashi handkerchief yana karkade jikinsa. Idanun alhaji hamza a tsaye sosai jikin uniform din nasa da suka fara alamta masa wani abu.
"Me yake faruwa a nan ne?" Ya watsa tambayar ga tsamurmurin mutumin daya lura kusan shine baquwar fuska a wajen.
Baiyi qasa a gwiwa ba ya kwararowa alhaji hamza bayani kaman yadda ya yiwa me babban suna,bayanin da maimaicinsu yake sanyashi jin kamar ya rufe idanunsa ya budesu ya ganshi ba'a wajen ba,kamar ya rufe idanu ya kuma budesu ya tsinci kansa haihuwar wata uwar daban ba maama ba......kaman ya tsugunna qasa ta hadiyeshi ya huta.
Sai daya kammala bayaninsa gaba daya sannan alhaji hamza ya gyada kai
"Nine a matsayin wakilin yaran nan,kuma bana nan,yanzu haka shigowata garin kenan,inaso a dakatar da aikin nan,ka kuma sameni gobe mu zauna muyi magana akan batun da kazo dashi,ina da buqatar qwaqwarar shaida da hujja ka taho da ita,idan ya tabbata da gaskiyarka,zaku fadi iya kudin data karba zan biya na fansarwa yaran gidan da suka gada,idan kuma aka rasa daya daga ciki kasan qarshen case din basai na qarasa ba" Abba yayi magana yana janye hannun me babban suna sunayin gaba. Ko daya bai amsa maganar mutanen ba,wanda ba abinda ransa keyi game dasu sai baci da soyuwa. Rayuwa ta lalace,DUNIYA ta zama wani abu na daban?,babu me kawar da barna?,babu me rungumar dan wani?,kowa nasa ya sani.
A baya suka bishi yana riqe da hannun me babban suna ba tare da yace komai ba.
Motarsa ya qaraso da ita bakin gate din gidan nasa sannan ya kulleta,ya soma takawa zuwa ciki yana kiran Faruqee. Cak ya tsaya daga gate din gidan shida saddiq suna kallon abba Faruqee da musaddiq suna wucewa zuwa ciki.
"Me babban suna" Abba ya ambata sanda ya sanya qafarsa ta farko cikin gidan
"Abba baya shigowa gidan mu yanzu" Musaddiq ya fadiwa babban qasa qasa yana tsoron kada mama dake can ciki ta jiyoshi. A mamakance ya kalli musaddiq sannan ya waiwaya ya kalli me babban suna dake tsaye daga baya kansa a qasa.
Yana jin nauyin abba qwarai,yana kuma jin nauyin saba umarninsa,amma bayajin qafafunsa zasu sake taka wannan gidan har abada kamar yadda yaci alwashi.
"Faruqee meye haka?" Abba ya tambayi farouq cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa
"Abba ya koma gidan su,mama ta koreshi". Wani abu yaji ya sauka tsakiyar kansa har kaman qafafunsa suna neman yin rawa.
" Ya salam ya Allah" Ya fada a fili,tun yaushe ta aikatawa.marayun Allah haka?,ashe shi yasa hankalinsa yayi qololuwar tashi sanda ake taba ginin gidan nasu tunda yana kallonsa a mafaka guda daya duk duniya data rage musu?,ashe shi yasa yaji ya kasa samun nutsuwa kwata kwata a kwanakin?.
"Muhammadu" Abba yakirayeshi kai tsaye da cikakken sunansa da ba kasafai yake kiransa dashi ba.
Kansa ya daga,suka hada idanu da abban da idanunsa da suka jajur
"Zoka wuce muje ciki" Ya sake bashi umarni nakai tsaye.
Umarninsa dai dai yake da umarnin mahaifinsa da yayi silar kawoshi duniya,tabbas idan zaiyi musu da gardama wa mahaifinsa to la shakka zai yi wannan wa abban. Amma fa tabbas inda ya san abban zai ankara d wuri akan baya biye dashi,allai da yayi nisa da gurin tunda wuri,tun gabanin yayi masa umarnin shiga gidan irin haka.
A gaba ya jeresu yana biye da bayansu har zuwa sanda suka isa ainihin falon gidan. Daidai sanda take fitowa daga kitchen hannun ta dauke da jug data tanadarwa abban lemo,haka kuma tasha ado da lace bakinta ya cika taf da lipstick ja shar dashi.
Har cikin zuciyarta takejin bala'i da masifa suna tsarga mata. Yau kam dukkan juriyarta da karar da take masa ta qare muddin dai yace dawowa yayi da yaran nan masu zubin mayu. Iya zamanta da yaranshi ma ya isheta jarrabawar rayuwa bare ya qaro mata yaran da batasan matsayinsu a gidan ba,suba agololi ba,su kuma ba yaran masu gida ba.
A gaggauce ta isa dining ta ajjiye jug din idanunta bisa fuskarsu
"Ku kuma daga ina?,daga dawowarsa shine kuka biyoshi saboda tsabar maita?" Ta furta tana zazzare idanu hannuwanta riqe da qugunta.
"Ya isa da Allah asama'u" Abba ya fada da hanzari yana daga mata hannu,don wasu maganganun bai dace ace an yisu gaban yaran ba,koda saddiq da musaddiq basu da shekaru sosai,ai Faruqee da me babban suna zuwa yanzun sun fara kammala hankalinsu tunda sun shiga shekara ta goma sha biyar.
"Ku wuce dakinku ku canza uniform"
"Ba inda zasu a gidannan dai wallahi,basu da daki kuma basu da matsugunni tunda dai bakai ka haifesu ba.....danginsu ma sai watsar dasu wai ballantana kai abba?" Ta fada tana sake matsowa hanyar da zasu wuce zuwa dakin
"Abba babu kayansu ko daya a gidan nan fa.....baka dade da tafiya ba ta koresu,tunda.ka tafi suma suka koma kwana a gidansu" Faruqee ya fada gaba gadi,yana jin cewa shima yau yakai bango,komai ta fanjama fanjam.
"To baqin munafuki,na koresu din,kuma wallahi wallahi koni ko su a gidan nan" Maganar faruqee ta dagawa abba hankali. A cikin gidan da bashi da maraba da kango suke kwana?,gidan dake cike da memories na iyayensu da suka gushe?,ta yaya suke iya bacci su biyu rakkin wanda har zuwa yanzu ba wanda yakai shekara sha bakwai ma bare sha takwas a tsakaninsu?.
"Abba abinci ma aiki me babban suna yakeyi a tasha kullum yana kawo musi gari ko dan wanke" Musaddiq ya fada a dan tsorace yana satar kallom fuskar mama bayan ya riqe hannun mahaifinsa da kyau yana boyewa a jikinsa.
Sosai maganar ta dakeshi,zaka fahimci hakan ta yadda kalolin idanunshi suka sauya duk kuwa da tarin haqurinsa. Farat daya yaji asama'u ta fita a kanshi gaba daya. Duk matar da zata iya yiwa maraya haka tabbas ya sani nashi yaran ba zasu tsira ba wadanda suke da uwa da uba,Allah ne kawai mafi sanin haqiqanin abinda su kansu su musaddiq din suke kwankwada daga hannunta idan baya nan.
Bai taba barin garin ya tafi gurin neman kudinsa hankalinsa a kwance ba tun daga ranar daya saki mariya. Tun daga ranar daya rabu da mariya bai sake samun nutsuwa cikin gidansa ko aminci akan 'ya'yansa ba.
"Asama'u?,bakya tsoron fushin Allah kike cutar da marayin Allah?"
"Ni babu abinda Allah zaiyimin,don su din ba dole na bane,wadanda ma suka zame musu dole sun yakicesu sun zubda bare ni da aka tsinceni da haqorana talatin da uku.....don haka wallahi bazanyi riqonsu ba,yaranka dai ba yadda na iya dasu saboda ubansu nake aure"
*_TAFIYA DA GWANI ME DADI_*
*ZAFAFA BIYAR*❤🔥🥰
*zafafa biyar*❤🔥🥰
*ZAFAFA BIYAR*❤🔥🥰
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA*
_FITATTUN GWARAZAN MARUBUTAN LITATTAFAN NAN NE MASU DAUKE DA SALON LABARAI IRIN DABAN DABAN BISA TSARIN TAFIYA DAYA SUKA SAKE YUNQUROWA☺️😇_
_WADANDA SUKA SABA GABATAR MUKU DA QUNSHIN ZAFAFAN LITATTAFAI DA LABARAI MASU TAFIYA DA HANKALI DA TUNANI_
*_IRINSU_*
BURI DAYA
INAYA
AMEENATU
DALAAL
BAQON MUNAFUKI
KAIMIN HALACCI
TSUTSAR NAMA
WUTSIYAR RAQUMI
BAQAR INUWA
SIRADIN RAYUWAR BILKISU
TABARMAR QASHI
KUFAN WUTA
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
___________________________
PAGE 12
"Qarya kike,wallahi tallahi yarana dinma ba riqonsu kikeyi ba,koda basu taba gaya min ba amma na tabbatar ba irin riqon uwa da 'ya'yanta kike musu ba.....irin riqon da mukayi alqawarin zakiyi musu" Qaramar shewa tadan saki tana tafa hannuwanta hadi da qare masa kallo tsaf ido cikin ido
"Dama waye yace maka uwar wani zata iya riqon dan wani tamkar nata?,au ashe bakaji abinda bahaushe ya fadi ba kenan,riqon uwar wani da dan wani ai sai Allah" Mamakinta ne ya qarasa kasheshi,ransa yakai qololuwar bacin da har ya mance da yara ma a wajen
"Haka kika ce?,to bari kiji na gaya miki......muddin ba zaki riqe wadannan marayun ba saidai kisan inda dare yayi miki" Idanu ta fidda tana kallonsa cikin maqurar mamaki,wato ya fifita matsayin yaran a kanta kenan?,ta yaya zata ma zauna ta karbi wannan fifikon?,ya za'ayi ma tayi sake har yaga warginta haka?,a gaban yaran ya kafa mata irin wanna sharadin?,ai duk yadda taso ga son zama dashi ba zata karba irin wannan mulkin qarfa qarfan ba.
Hannayenta ta sake hadawa ta tafa ta kuma riqe qugunta da kyau tana dubansa
"Wallahi kaji na rantse bazan riqe su ba,har nakanma na gaji ai bamuyi abinda zanzo nayi kenan cikin gidan nan ba"
"Tunda kuwa kikace haka saidai ki qara gaba" Gabanta yadan fadi,amma batajin zata bari ya gano lagonta
"Hakan shi yafi sauqi,amma bazanje nayita zama da dakon aurenka ba,ka gayan meye matsayin tafiyar tawa idan na yita?" Ta kuma tambaya tana watsa hannuwa
"Na sakeki saki biyu"
"Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" Me baban suna ya furta yana saka hannuwansa dukka biyu ya toshe kunnuwansa,sannan ya koma ya sulale yana zama tsakanin kujerun falon.
"Tafi nono fari,sai me?,dadin abun ai ba kai kadai bane namiji" Ta qarasa fada tana ture kujerun dining din ta sauka a gaggauce zuwa dakinta gabanta yana wani irin bugawa da sauri da sauri.
Daga su har abban ba wanda ya iya cewa komai,falon ya dauki shuru kawai sai motsinta daga can uwar daki tana hada kaya gami da sakin maganganu wanda basa iya jin ainihin me take fadi.
Mintuna goma kacal ta fito janye da akwatunta da qaramin mayafi yafe a kafadarta. Daga inda yake ya daga rinannun idanunsa yana kallonta. Abba ya saketa ne saboda su,me yasa abban zai saketa saboda dalilinsu?. Fitowarta sai tayi masa kama da fitowar mahaifiyarsu sanda take shirin barin gidan mahaifinsu.
Me yasa ake tafiya ne ana barinsu?,farinjini ne basu dashi ko kuwa?,ko wani maqalalle kuma boyayyen abune dasu?,me yasa iyaye mata basa tausayinsu saidai maza?.
Baisan yaushe ya yanke wannan hukuncin ba,shidai ya tsinci kansa a gaban mama ne,cikin matuqar tashin hankali da karyar da muryar yake fadin
"Don Allah mama kiyi haquri,kada ki tafi saboda mu......"
"Na rantse da Allah zan zabga maka mari idan baka bani hanya ba,munafukan banza da wofi wadanda babu alkhairi sam a jikinsu sai masifa da balai nau'i nau'i,ai daya sakenin sai ku ya aureku,gaku nan gashi,kara da kiyashi daukan mara sani" Sai ta wuce abinta ta barshi da zafafan maganganun daya gaza mancewa dasu.
"Dawo ka zaun me babban suna,waye yace maka ka bata haquri?,waye yace maka zan iya zama da ita bayan bata sonku?,ba zata iya zama daku ba?,ba zata iya haquri daku ba?......in sha Allah na muku alqawarin dawowa da mamanku nan da sati guda kacal" Maganar data Haifar da wani irin farinciki mara misali a zuciyar faruqee musaddiq harma da sadeeq din da baima mamansu musaddiq din farin sani ba. Yayin da me babban suna yake binsu kawai da idanuwa,don kunnuwansa da zuciyarsa harma da qwaqwalwarsa sunyi nisa qwarai da abinda ke wakana a falon.
Jarin maganganun mutane masu tsananin dafi daya soma girma da jinsu yaketa aunawa. Kullum kwanan duniya wayewar gari zuwa faduwar rana sai yaci karo da wata mummunar kalma da zata zamewa zuciyarsa tabo wadda ta shafesu da mutuncinsu,duk kuma MAAMA itace sila,dama uwa tana iya zama silar bacin suna da rayuwar 'ya'yanta?. Tambayar da amsarta ta kasa samuwa a gareshi kenan,musamman lokacin da MARIYA mahaifiya ga faruqee da musaddiq ta dawo ainihin dakin aurenta da zummar riqe yaranta harma da marayun Allah MUHAMMAD DA ABUBAKAR SADDIQ
***************
Faffadan tsakar gida ne ma'abocin yalwa da kuma tarin dakuna da zasu nuna maka yawan adadin mazauna gidan dake cikinsa.
Tun daga qofar gida,zauruka guda biyu masu girma har zuwa farfajiyar gidan da wani filin tsakar gida da gidan ya mallaka zakasan cewa asalin ginin gidan anyi gine na masu wadata a wani qarni can baya daya shude.
Duk kuwa canzawar siffar ginin zuwa zubin ginin daya dauki shekaru,amma yanayin yadda akayi zuba ginin da kyakkyawan tubali hakan ya hanashi muguwar lalacewa ko muzanta daga suffar kyau zuwa ta tsufa.
Dakuna guda hudu manya manya gidan ya mallaka lailaye da siminti da tsakar gidan ya wadatu dashi da fulasta wadda ke nuna yau ta jima da samuwa a jikin ginin gidan. Kafin idanunka yakai ga duqurqusar matakalar bene dake qarshen qofar daki na hudu a jerin dakunan gidan. Rijiya ce da aka dan dagata kuma aka rufeta da murfi na langa langa. Idan ka sake kai dubanka kuma can zuwa sashen hannun hagu na gidan,bayan ka wuce bishiyar mangwaro data samu muhalli na dindin da Tsakiyar gidan,kai tsaye kana iya hangen qofar da tafi kama data makewaye,da kuma qofar babban kitchen na gidan daya hada kowa da kowa.
Akwai gurabe daga jikin bangon gidan da zai sanyaka ka fahimci a baya akwai wasu shuke shuke da sukayi zamani daga bangwayen gidan,saidai yanzun babu ko wanne tsiro idan ka cire bishiyar dake a Tsakiyar wadda gushewarta ita din ba abu bane me sauqi.
A tsaftace gidan yake ba laifi,wanda kusan gado ne da kuma asali da tsafta daya samo cikin gidan koda kuwa bayan gushewar me gidan da rasuwar mace daya cikin matan aure uku da ma gidan ya mallaka a lokacin rayuwarsa.
Safiya ce sosai,kusan qarfe bakwai da rabi na safe agogo ya nuna a daidai lokacin. Kowacce qofa ta gidan a sakaye take,sai wata qofa guda daya qyaure ta ya banbanta da sauran qyamaren gidan kafataninsu.
Ba zaka gama fahimtar yadda banbancin yake bai tsaya daga qyauren kawai ba.....aah,har sai ka samu nasarar kutsa kanka cikin ainihin falon dake hade da uwar daki kaman kowanne daki na gidan.
Kyawawan labulaye ne da aka yiwa dakin qawanya dasu ruwan toka wadanda sukayi daidai da sofas guda biyu dukkansu 3sitter da aka gewaye falon dasu hakanan suka dace da lallausan daddumar da aka shimfida a tsakaninsu qirar qasar turkiya.
Akwai lausasan pillow guda hudu manya dake zube a qasa dukkaninsu kala daya da labule zuwa kujerun. Daga bangon dakin ta fuskar hagu kuwa,bango ne da yasha wallpaper me kyau aka kuma yiwa TV plasma me matsakaicin girma da reciever dinta mazauni na daban. Gaba kadan dasu 'yar madaidaiciyar AC ce ta tsaye wadda ke amfani da hasken rana da aka yiwa kafatanin dakin wayarin dinsa. Wannan ya sanya koda babu wuta ko ina cikin gidan,koda babu wuta ko ina a unguwar wannan dakin baya rabo da ita. Akwai freezer madaidaiciya itama data dace da tsarin dakin,sai manyan frames masu daukan hankali biyu masu sunayen Allah da ayoyin tsari,biyu kuma masu dauke da zanen nature me kyau. Sassanyan qamshin turaren icce dake zama a daki ya kama labulaye da kujeru da kyau falon yake fiddawa ya zarce kuma har uwar dakin,wanda ya cakuda da qamshin turaren daya zamewa mazauniyar dakin lazim amfani dasu.
Labulen bedroom din aka daga,sannan kuma a hankali ta bayyana hannunta riqe da hijabin yarinyar dake tsaye cikin uniform.
Matashiya ce wadda duka duka a qiyasce shekarunta ba zasu haura ashirin da biyu ke takowa a kasalance.
*_TURQASHI_*
*_BIGI SAI BIGI_*
*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*
*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*
*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*
*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*
*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*
*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*
*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Instagram handle_incense by kabo daughter*
*Facebook_kabo daughter*
*Twitter_kabo daughter*
__________________________
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 13
___________________________
*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*
*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*
*_NA GWADA NA GANI_*
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*
*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*
*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*
*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*
*_ME KIKE JIRA?_*
*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*
*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*
*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*
*_zaki dariya za kuma ki godemin_*
*_gani ya kori ji_*
*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
________________________
Sanye take cikin lallausar doguwar rigar bacci me kauri me gajeran hannu off white wanda ta tsaya daidai idon sawunta.
Zaka iya kiranta doguwa saidai ba cancan ba,irin tsahon da yayi daidai da tsahon da za'a iya kiran diya mace doguwa,wanda siririn jikinta ya sake taimakawa wajen bayyanar tsahonta,muddin kuma ta samu damar mujewar jiki ko ta dan qara qiba to tsaf tsahon zai shanye da ba lallai a iya ganinsa ba.
Tana da wani irin launin fata,fari me cakude da sirki sirkin ja,fara ce tas irin hasken fatar da kana kalla zakasan ba zallar hausa fulani bace,lallai ita din ruwa biyu ne halittarta ya hada nasaba da wani yaren(half cast).
Ma'abociyar yalwataccen gashi me santsi da tsahon da kana iya hangensa ta cikin hular bacci dake kanta,a cukurkude kuma a daure cikin siririn band. Yanayin zubin idanunta shike fusgar hankalin maza da dama,bama maza kawai ba,harda mata 'yanuwanta suke kallonta a matsayin me tsananin kyau,duk kuwa da cewa ita din kanta ta sani,ba wata me mugun kyau bace na azo a gani,amma batasan meye yake janye hankalin mutane haka a kanta ba?. Tun tana mitsitsiyarta wannan abun yake tare da ita,FARINJINI
....wanda a sanda take da gatan uwa mahaifiyarta ke yawaita tofeta da addu'a ko yaya ne idan zasu fita.
Mata ukune cikin falon,matashiya ta biyu wadda shekarunta zasu iya kaiwa sha shida na zaune dirshan saman lallausan carfet din nasu daya wadatu da tsafta,hannunta riqe da cup na tea,daga gefanta kuma bowl ne dake cike da chips. Sanye take da uniform irin na sauran 'yan uwanta dake alamta maka ta kammala nata shirin zaman tsimayinsu take bayaga breakfast data kasa kammalawa har yanzu. Yanayin yadda take cin abincin kawai zai gaya maka bawai dadin abincin takeji ba,idanma ba haka bane to lallai akwai abinda yake damunta.
Ta biyun na gefan kujera tana qoqarin saka fara qal din sucks dinta. A qiyasce nata shekarun na haihuwa zai wahala ya wuce sha uku. Sannan qaramar data isa gareta tana gyara hijabin hannunta tana qoqarin sanya mata fuskarta shimfide da wani sassanyan murmushi nata shekarun tsakanin tara zuwa goma suke.
Idanunta akanta da wani irin kallo na tausayi da rahama,zuciyarta na sake narkewa cikin tausayinsu gami da jin qwarin gwiwar basu kariya da samar musu da komai na buqatar rayuwa duk rintsi,komai wuya komai dadi. Wanzuwarsu a yanayi na farinciki yafi komai dad'ad'a mata rai da sanyata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali duk kuwa da irin birkitacciyar rayuwar da take fuskanta,wadda bata da dadi sam sam ballantana ban qaye.
"A'ah.......kaga haneefata anyi kyau" Ta fadi da sassanyan muryarta me wani irin amo me dadi da daukan hankali idanunta saman fuskar yarinyar data kira da haneefa......yarinyar da ake cewa duk cikin qannenta ba wanda ke kama da ita irinta,duk da ansha cewa haneefan ta fita kyau,hasken fata kawai zata darata dashi.
Dariya haneefan ta saki ta daga hannunta zuwa ga 'yar uwartata alamun su tafa,sai ta daga nata dogayen yatsun ta bata suka tafa din.
Batasan wanne irin son karatu Allah ya dorawa qannen nata ba,wadda karatun bai fiya damunta ba huda ce,saidai a sannu da tayi tsaiwar daka a kanta yanzun abun ya shiga jikinta itama. Hudan ma bawai karatun bane bataso,a'ah,kawai hankalinta yafi karkata zuwa ga wasu bangarori. Kaman koyon abubuwa na qirqire(creatives),irinsu zane zane,dinki,decorations da sauransu. Bata jin akwai wanda zata matsawa kan abinda yakeso yayi muddin bai kaucewa hanya ba.....to amma kafin sannan tana da buqatar suyi karatu.......tana da buqatar su karantu da kyau ta yadda koda bayan ranta sun zarcewa raini da wulaqanci......tana da buqatar suyi karatun da duniya gaba daya zata tabbatar sun gagari rainin me raini ta fannin ilimi.....tanaso suyi irin nau'in karatun da hattana da maqiyi babu yadda zaiyi zai sallama cewa eh lallai......jinin hindu sun zama wasu taurari na daban a cikin familynsu gidansu dama unguwarsu gaba daya......zata nunawa wadanda suke ganin ba zasu iya ba.....ba zasu kai ba......zasu tozarta cewa......zasu iya iya.....za kuma sukai labarin da su basu kai ba.
A nutse ta waiwaya ta kalleta. Tadan zuba mata idanu na second tana nazarinta. Tun tuntuni ta fahimci akwai kwantacciyar damuwa a qasan ranta,kasancewarta mutum me wani irin kakkaifan hange da saurin gano abu. Kaifin fikirarta ya fita daban dana dukkan wani yaro dake cikin gidan,don haka take saurin fahimtar kowanne motsi taku da kuma sauyawar yanayin qannenta.
"Huda......wai baki duban lokaci?" Batace komai ba huda din,saita zare cup din bakinta ta direshi tana niyyar miqewa,abinda ya sakata maida idanunta ga cup din kenan. Ko rabin tea din bata sha ba,ta sake maida kallonta a kanta
"Kin qoshi kenan?" Kai ta jinjina mata kafin tace
"Banajin yunwa dama kwata kwata" Kyawawan idanun nata masu wani irin shape ta lumshe,can qasan zuciyarta tana furta
"Alhamdulillah,astgafirullah" A duniya daya daga cikin sauti da take matuqar son ta yita ji kenan daga harsunan qannenta
"BANA JIN YUNWA" Sauti mafi dadi kenan daga bakinsu zuwa kunnuwanta.
Waiwayawa tayi gefanta ta kalleta sanda ta kammala saka takalmi da socks dinta
"Nadra......shiga daki gefan katifata ki daukomin jakata na sallameku......yau din kamar babu me laka a jikinku"
"Tom" Ta amsa tana saukowa daga saman kujerar da saurinta ta wuce dakin. Sanda take maido dubanta cikin falon sai suka hada idanu da hudan. Huda ta janye daga kallonta,sai ita din taci gaba da kafeta da kallo tana dubanta
"Huda"
"Naam" Ta amsa mata ba tare da sun hada ido ba
"Wai meke damunki?" Ta jefeta da tambayar tana kebe baki......harta bude baki zatayi magana ta dakatar da ita a tsaurare
"Karki soma cemin ba komai.......na gani a idanunki da motsinki......"
"Gida......"
"Ba damuwar mutanen gidan nan ba?" Ta jefa mata tambayar tana duban idanunta,a yanzu akwai sirkin bacin rai kadan a maganarta da idanun nata
"Yaushe kika fara saka maganarsu cikin ranki?" Ta kuma tambayar tata tana kallonta
"Ashe har yanzu baki saba da halayyarsu ba?,bakisan yadda zaki zauna dasu ba?,huda ina duk qoqarin da nake a kanki ke da kike babba ki fahimci yadda zaki zauna da kowa a cikinsu?"
"Anty bakisan me suka ce ba a kanki.....bakisan me suke fada ba kullum" Ta qarashe maganar muryarta tana raurawa sosai da alamun zuciya da ruhinta gaba daya sun sare.
"Kome zasu fada huda su fadi,indai a kaina ne karki azawa kanki damuwa.......kome ma zakiji sun fada,ba wani baquwar kalma da zakiji daga bakinsu ko sabon abu.....me yasa sai yanzu zaki fara sawa kanki kina damuwa?" Ta qarashe da sigar tambaya. Qasa tayi da kanta ba tare data amsa mata ba,ita kanta batasan me yasa sai yanzun abun ke damunta ba duk da sun share shekaru dasu a haka.
Daidai sanda nadra ta qaraso ta miqa mata kyakkyawar hand bag din nata fara tas me adon brown duka jikinta dake dauke da tambarin kamfanin Gucci.
Idanunta masu sheqi ta juya zuwa ga nadra,ta saka hannu ta karbi jakar tana qoqarin zugeta.
"Anata kiran wayarki tunda na shiga" Nadra dake goya jakarta ta fada.
"Okay,barta" Ta amsa mata a taqaice,don ta tabbatar a cikin mutum biyu daya ne yake kiranta,tafi kuma gasgata zatonta akan dayan.
Zip din da take ajiye canji ta zuge,ta fidda kudin ta lissafa daidai yadda tasan zai ishesu break da kudin mota,saboda yau din basuyi abinci yadda suka saba ba kasancewar kayan abincinsu ya qare.
Daga bakin qofar falon nasu tayi tsaye hannayenta goye a qrijinta tana dubansu har suka kammala ficewa daga gidannasu,sai taja Qaqqarfar ajiyar zuciya tana sauke hannayen nata ta juya a hankali don komawa falon don kwata kwata bata samu isashen bacci ba a jiya,tanaso ta runtsa sosai sannan ta shiga kasuwa tayi musu saye saye
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 14
________________________
*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*
*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*
*_NA GWADA NA GANI_*
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*
*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*
*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*
*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*
*_ME KIKE JIRA?_*
*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*
*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*
*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*
*_zaki dariya za kuma ki godemin_*
*_gani ya kori ji_*
*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
_________________________
Saidai dai dai sanda ta saki labulayen da zummar shiga ciki din taji sallamarsa ta karade tsakar gidan. Qaramin tsaki taja,tabbas tunda aka jishi da sassafen nan kamar haka to ba a shakka wata tijarar yazo yi,ko kuma akwai abinda ya hadoshi da wani. Idan da sabo zata iya cewa sun saba da halayyarsa,macce daya ce cikin gidan suke dasawa har baka iya jin kansu. Har gwara ita tasan maganinsa,ta kuma san ta yadda take bulloma tsiyarsa,duk da bata taba tsaiwa ta kulashi ba anji muryarta a matsayinsa na qanin mahaifi a gareta.
Sakaya qofar kawai tayi ta sake zuge labulen sosai sannan ta wuce uwar dakin ta yadda ba zata tsaya bata lokacin jin meke faruwa a tsakiyar gidan nasu ba,domin ita din tana cikin jerin sahun irin mutanen nan ne dai basa shiga abinda bai shafesu ba,wanda ya shafesun ma sai tura takai bango,bata da magana sam sam bare hayaniya. Wannan hali nata da siffarta ta sanyi da sauqin hali da kuma yauqinta ya sanya da yawa suke mamakin WANNAN DABI'A TATA......Dabi'ar da har yanzu su kansu basu da cikakken yaqinin a kanta,duk da cewa suna kallon gamsassun hujjoji ai sun gama bayyana a fili a game da ita.
Babban bedroom ne qwarai wanda iya dauke gado da wardrobe guda bibbiyu,sai dressing mirror guda daya. Duk da cewa wai daga bacci aka tashi amma dakin neat yake,komansa akan tsari,ga kuma wani sassanyan qamshi da yake fita kaman dai yadda falon yake.
Daya gadon da yake shine qarami ta nufa,wanda ke lullube da lallausar shimfida da tattausan blanket peach color. Tun batakai ga zama ba rurin da wayarta keyi ya cika mata kunnuwa,sai ta haye saman gadon ta lalubo wayar ta cirota daga gefan pillow dinta.
Iphone 15 ce dake dauke da wata irin cover me kyau data dace da wayar da kuma me wayar gaba daya,ta zubawa sunan dake yawo saman screen din idanu
*_ibraheem_* ya nuna mata. Wani gajeran murmushin gefan baki ta saki dake cakude da wani emotion. Siririn tsaki taja saman harshenta,ta fara qoqarin rejecting kiran
"Done and dusted.......an gama da shafinka tun a jiya" Ta fada qasan ranta tana tuna yadda al'amura suka tafi mata successful kaman yadda aka saba.
Sai data tabbatar tayo blocking ta kuma shafe duk wani abu daya shafeshi cikin wayar,bata bar hujja ko qarama ba da zata nuna tsohuwa ko sabuwar alaqa ko kuma mu'amala tsakaninta dashi ba. Ta sake bin wayar ta tabbatar komai ya koma kaman da,sannan ta duba wata ma'ajiya ta daban ta lalubi wata number ta kira ta kara wayar a kunnenta.
Bugu biyu aka daga ana sallama cikin zaquwa da zumudi
"Ina fatan saqon ya riskeki?" Tayi tambaya zuwa ga daya sashen
"Ya riskeni qwarai kuwa tun a daren jiya.......ina godiya......na gode sosai,ina me baki haquri kuma akan sabanin Fahintar da nayi miki a farko.....gashi kuma ko sunanki ma ban sani ba"
"Ba buqatar hakan......infact ma daga yau ba zaki sake samu na ko jin muryata ba......abinda na baki kiyi qoqarin tattalashi,ki kuma boyeshi daga sanin mijinki.......abu na qarshe saiki tayashi jiyya.....kinsan yadda zaki sanya masa tawakkali cikin zuciyarsa,don nayi imani ya zuwa yanzu zaiyi wahala bai zauce ba,na barki lafiya" Ta yanke kiran ba tare data barta tace komai ba,duk da tarin abubuwan fada masu yawa da take dasu take kuma son gaya matan.
Itama goge number dinta tayi ta kuma sakata a sahun sauran tarin lambobin dake akwatin katangewa dake cikin wayarta. Layinta layi ne dake da wani irin tsaro na musamman,wanda ba kowacce number da bata yarjewa bace take iya samunta. Tana da ire irensa sunfi guda ashirin,duk kuma sanda take da muradi ra'ayi ko kuma buqatar hakan ya taso tana iya sauke wanda taga dama ta dora wani.
Tana shirin shigewa duvet ta kwanta wani kiran ya sake shigo mata. Batason takura sam,sai taja tsaki tana kallon fuskar wayar.
Shine din dai,batasan me yasa ya matsa da yawa ba,bataso a yanzun akwak enough kudi a hannunta,tanaso taje hutu koda na taqaitaccen lokaci ne kafin ta fada zuwa wani agenda din.
"Tsautsayi da alama keta kiranka" Ta furta qasa qasa ta jawo wayar tana rejecting kiran shima sannan ta kashe kiran gaba daya ta jefar da wayar. Kanta ta mayar ta qudundune sosai cikin blanket din,saidai ko minti biyar bata yi ba cikakke ta miqe zumbur kamar wadda aka tsikara,ta sauko daga saman gadon tana qoqarin daure gashinta me santsi dake rufe gefan fuskarta.
Kyakkyawar drawer dinta ta bude banqaran hijabs,ta fidda wani qaramin farin hijab cikin jerin hijban da take amfani dasu a lokaci irin haka idan zata shiga wanka. Sama kanta ta zurashi,wanda wannan ya fidda kyakkyawar fuskarta tsakanin hijab din,ya kuma fidda wata sihirtacciyar kama akan fuskar tata. Towels dinta ta nufa ta zari guda daya,sannan ta matsa gefan daya drawer dinta ta jawo ta can qarshe ta fidda set na kayan wankanta dake cikin wani dan kyakkyawan kwando kaman kwandon kaba,ta rataye toweldon saman kafadarta ta fara takawa a hankali tana fita a dakin tare da sake gauke fuskarta da kyau wanda kusan haka dabi'arta take duk sanda zata fita zuwa ainihin tsakar gidan nasu,duk da dama ita din ba matum bace data cika fara'a.
Duka duka mutanen dake sabgarsu a safiyar ranar cikin sararin tsakar gidan ba zasu wuce mutum biyar ba. Dukkaninsu kuma mata ne da a shekaru suke qasa da nata shekarun idan ka dauke mutum daya dake ta bakin kitchen dinsu,zaune saman kujera 'yar tsuguno tana ta kokawa da wutar ice da take qoqarin kunnawa hayaqinta yana dawo mata cikin idanu yana sake tunzurata da hasalata.
Duk wanda suka hada ido dashi sai ya janye dubanshi daga kanta kamar yadda itama kusan haka take musu,duk kuwa da cewa wasunsu suna son tankawa a gareta kaman yadda a wasu lokutan yake kasancewa,saidai wanzuwar ta bakin kitchen din ya sanya ba wanda yayi gigin aikata hakan a cikinsu.
Bata dakata ba har ta isa bakin makewayensu da ko yaushe yake cike da tsafta da kulawa,ta xare towel din wuyanta ta azashi saman qofar bandakin idanunta nakan shaheed,yaron da aka kawoshi yaye daga gidan mahaifansa zuwa gidan kakanninsa. Yaron yayarta ne,yayarta ta kusan biyar,d'iya a wajen gwaggo mace ta biyu a wajen mahaifinsu.
Ido suka hada da yaron,sai ya sakar mata murmushi,a hankali itama ta motsa bakinta tana maida masa martani. Tana da wani boyayyen soyayya ta yara a zuciyarta,saidai zuwan yaron sai ya zame mata kamar wani mabudi ko kuma wanzuwar sabon abu da bata saba gani ba cikin gidan wato murmushi kowacce safiya a tsakar gidan mahaifinta wanda ya jima da shudewa tun bayan gushewar mahaifiyarta.
Tanason yiwa yaron magana,amma tayi imani rayuka zasu iya baci daga qarshe,dole ta kauda kai,ta sirka ruwan zafin data fito dashi ta fada wankan.
Kafin ta kammala taji masu buqatar shiga bandakin da yawa,masu qananun mitoci da qorafi duka sunayi,wasu su juya wasu su zauna suna dakonta gami da ci gaba da yasar da maganganun da tayi imanin da biyu suke yinsu kamar yadda suka saba.
Zuwa yanzu ta fara tunanin yadda zata maida qaramin dakin dake kusa da dakinsu toilet. Daya daga cikin dabi'a daya ta gidansu data tsana kenan,sharing toilet.
Gini ne irin na da wanda duk yawan jama'ar gida suna hadaka ne a bandaki qwaya daya tal!. Zata iya cewa da sauqi nasu tunda akwai wadatar tsafta.
Ko data fito babu wanda tabi takai,sai data kammala uzurinta na daura alwala a nan bakin famfo sannan ta tattaro kayanta tana barin wajen. Sai a sannan ta kallo mata biyun dake zaune daga bakin bishiyar.
Daya ta girmi daya a shekaru,saidai dayar ta dara dayan jiki. Sun kalleta sun kuma dauke idanu kamar basu ganta din ba. Ba abinda ya dameta da hakan
"Ina kwananku?" Ta furta da muryarta me laushin nan tana yin gaba ba tare da tayi koda yunqurin tsaiwa ba da salon gaisuwar da duk safiyar duniya bata daukewa kowacce cikin su ukun ba muddin zasu hadu a farfajiyar gidan.
Amsa mata sukayi kaman yadda suka saba din,can qasa suna kuma binta da wannan kallon dake dauke da tarin ma'anoni can qasan ransu,wasu.
sun furta su sun kuma bayyana,wasunsu kuwa an barwa zuciya AKWATIN SIRRI.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
PAGE 15
A nutse take ratsa falon harta cimma uwar dakin nasu. Duk takunta guda daya sauke qafarta da dauketa zuciyarta cike take da kewa. Wata qatuwar kewa data zamewa kowanne motsi na rayuwarta lazim. Kewa ce da zaiyi wuya ita iya barin gangar jiki. Kewar mahadin rayuwa jigon rayuwa mahadin numfashi wato MAHAIFIYA.
Duk yadda lokaci yakai ga wulwula gudu,duk yadda zamani yakai ga fara yin tsaho da nesanta bawa daga dukkan tunani radadi da damuwoyin abubuwan da suka shude amma ya gaza yin nasara a kanta ta wannan fannin. Mahaifiya daban take cikin rayuwar 'ya'yanta,babu ma ya mahaifiya irin tata......jajirtacciyar uwa data zamewa maraicinsu sutura,ta zame musu bango abun dafawa,ta hana musu kuka akan rashin mahaifinsu.....sai gashi a yanzun suna kuka.....irin kukan da kunnuwa ba zasu iya ji ba,idanuwa ba zasu iya gani ba.......ta saka dukkan wani qarfi da iyawarta ta tare wannan shingen maraicin......tozarta da wulaqantar rayuwa dake shirin danne musu numfashi har ya zuwa lahirar duniyarsu.......tallafewar data sabbaba mata tarin ciwuka.......nauyi me yawa a qirjinta da rayuwarta......ya kuma bude mata qofofi masu fadin gaske cikin rayuwarta......ya maida JARUMA a mafi yawan lokuta.....wani lokacin kuma MAFARAUCIYA dake bude dukkan qarfin qwanji dana zuciyarta don cimma burikanta.
Ya dasa mata abubuwa masu yawa cikin ZUCIYARTA ya kuma sanya dolen dolen ta sauya akalar rayuwarta ta fanni da dama. Ta koma tamkar tarwada me wahalar kamawa cikin ruwan da take ninqaya. Ta kuma koma tamkar hawainiya dake canza kala a duk sanda taso hakan,ta bace ta kuma saje da duk yanayi ko launin da takeso ko kuma taga dama.
Tana da tarin sunaye masu yawa da a duniya a yanzun bayan ainihin sunanta na yanka SABREEN. Sunayen da ba'a yiwa yanka ba don tabbatuwar samuwarsu a kanta.
Akwai idanuwa bakuna da hankula masu zafi da batasan adadinsu ba a kanta. Kowanne kuma da irin nashi kallon.....hasashen da furucinsa dangane da ita.
Karon farko ta sakarwa fuskar nan tata murmurshi data fito tawai bisa fuskar madubin dame gabanta duk kuwa sa siririyar qwallar dake kwance cikin qwayoyin idanunta masu sheqi kaman an diga ruwan zaiba. Karaya da kuma qwarin gwiwa na karakaina tsakanin qirjin nata,saidai ko sau daya bata aminta ta dauki FADUWA TSORO ko kuma ja da baya ba.
K'aramin towel da yafi kama da handkerchief ta sanya ta tsane qwalla don kada ta bata daman fitowa,ta miqa hannu ta jawo stool ta zauna a kai tana saka hannunta tana kokawar daure sassalkan gashinta dake qoqarin kwancewa daga daurin farko datayi masa.
A nutse ta jawo set na kayan shafarta da take amfani dasu. Skin care product ne da suke mahadi da shower gel cream da sauran tarkace,wanda kudinsu duka zai tasamma dubu arba'in.
Kudi ne me nauyi da ciwo a wajen me qaramin qarfi,to saidai ta wajenta amfani dasu sun zame mata jiki kaman yadda suka zame mata wajibi. Tana son ado,tana qaunar tsafta da qamshi,wanda da a baya bata basu muhimmanci ba,saidai daga bisani ta gama karantunta tsaf......ta fahimci kowanne taku a rayuwa akwai abokin yinsa.....akwai sauyawar yanayi da ta zamewa jiki da rayuwa dole......dole sai an aiwatar da wasu abubuwa ake samun wasu abubuwan,dole sai an gusa koda da taki daya ne sannan ake samun wasu sabbin damarmakin suke shigowa rayuwar dan adam.
Gayunta na daya daga cikin abinda ya sake sama mata MUMMUNAR SHAIDA da kuma mummunan zato daga bakunan mutane da dama. Zaton daya kamata ya qona mata rai.....ya sanyata fidda qwalla masu zafi.....a maimakon hakan saidai kawai ta murmusa,ta kuma motsa ta barka a wajen da salon abun nan dake nuni da BANI DA LOKACINKI/KA.
Tsaf ta duk wani shafe shafe nata,ta kuma gyars gashinnan me tsanani yauqi sheqi da tsaho,ta dameshi cikin ribbon me dan girma,abinda ya sake bawa ainihin kamanninta fita ras kenan.
Koda ta bude ma'ajiyar kayanta tsaiwa tayi tana tunanin suturar da zata dace da jikinta a wannan lokaci. Shaqe take tafff da tarin suturu na alfarma,masu tsadar da koda ba'a gaya maka ba kai kanka ka sani. Suturun da a tashin farko xakasan sunfi qarfin wanzuwa cikin wannan wardrobe din.....kaman sunfi qarfin ma ace akwai wani cikin gidan daya mallaki masu darajarsu.
Juya zagayyayun idanunta tayi tana dan lumshesu kadan zuwa bangaren abaya. Sai data gama nazarinta sannan ta jawo daya daga ciki. Egyptian abaya ce me asalin daraja da kuma kyau wadda kudinta ya tasamman dubu arba'in da 'ya'ya. Sam sutura me tsada ba damuwarta bace,tana iya mallakarta a duk sanda tayi marmari ko kuma muradin hakan.
Da sanyinta dinnan da yake cikin halittarta take daura belt din da abayan yazo dashi bayan ta saka ta farko ta kuma dora alkyabbar da abayar tazo da ita. Siririn mayafi ta zaba daya dace da rigar tayi rolling me kyau da ma'ana,take zagayyar fuskarta ta fito cif tsakiyar veil din,sai ta kuma duba handbags dinta dake rataye sama da goma sha biyar kowacce da takalminta mahadi a qasanta.
'Yar qarama ta dauko qirar kamfanin D&G da takalminsa,ta natsa gaban madubi ta dauki turarenta ta bintike kan ta feshe jikinta dashi,sannan ta zari wayarta ta jefa a jaka tana duba agogon dake daure a tsintsar hannunta ta doso falon.
Jakar ta ajjiye tana jawo tea flask dinsu tana qoqarin budewa. Bata fiya son cin abinci da wurwuri da safe ba,to amma kuma tana tunanin zaiyi wahala idan ta fita din ta iya tsaiwa taci komai tasan halin kanta da kanta sarai.
A tsaitsaye take kurba kyawawan idanunta zube fes saman qaramar waya me keypad data dora saman cinyarta tanata qoqarin kiran wata number.
Bugu biyu aka dauka,muryarsa ta bayyana cikin wayar da wani irin shauqi da doki
"Da wacce irin saa yay na wayi gari ne?,ya Allah" Ya fadi yana zama gefan gadon bedroom dinsa.
Taqaitaccen murmushi me qaramin sauti ta sake tana kai cup din bakinta,can qasan ranta wani abu yana yawo gami da kai kawo a ciki. Gaba daya ta manta da rayuwarsa,taso kuma ta gogeshi a babin rayuwar tata gaba daya,to amma data tuna wani abu,sai take ganin ya kamata ko yaya shima a bashi darasi.
"Ina kika shiga don Allah,ina kika boye hanan?"
"Dukka wadannan tambayoyin basu kamaceka ba,tunda dai gani din na kuma kira ai sai ka ajjiyesu ko?"
"Haka ne ranki ya dade" Ya amsata da sauri ba tare daya damu da yadda matarshi ke tsaye saman kanshi tana dubansa cike da qunar zuciya da kuma takaici ba.
"Zaka iya samuna nan da mintuna goma a gaban flavours na gadon qaya?" Ta jefa masa tambayar tana ajiye cup din hannunta,daidai sanda yaron ya daga labulen falon bayan ya turo.qofar ya shigo. Washe mata baki yaron yayi,abinda ya sanyata murmusawa tana miqa masa hannunta dake daure da agogon fatan daya kwanta a jikinta sosai,gefe guda kuma tana sauraron amsarsa
"Ko mintuna biyar kika ce zanyi qoqarin kawo kaina"
"Yayi,saika qaraso" Ta amsa masa tana dan kauda wayar ba tare data kashe kiran ba.
"Wace tayi kiranka?,ina zaka je?,wallahi baka isa ka fita a gidan nan ba" Sautin muryar matar ya ratso ta cikin wayar. Lafiyayyen zagin da taji ya fita a bakinsa ya sanyata datse kiran ba tare data shiryawa hakan ba,ta lumshe ido tana jin yadda qirjinta yake quntata
"Har yanzu yana nan a yadda yake......har yanzu babu wani abu daya sauyashi" Kalaman dake karakaina a kwanyarta kenan
"Am sorry.....am sorry" Ta fada murya can qasa tana motsa labbanta.
Sanyin hannun yaron daya taba nata hannun ya sakata bude idanunta. Har ya qaraso inda take ba tare data ankara ba
"Antyn huda" Ya kira ta da sunan daya saba kiran nata
"Kaci abincin safe?" Ta tambayeshi tana dubansa. Girgiza kai yayi da sauri,sauta juya gefanta tana masa nuni da doguwar yatsarta
"Dauko wancan plate din ka cinye duk abinda yake ciki na barmaka" Da zumudinsa ya juya din yana nufar wajen. Zama yayi sosai bayan ya bude yaga abinda ke cikin,soyayyen chips da ragowar soyayyen qwai,ya fara kaiwa bakinsa yana murmurshin jin dadin garabasar daya samu.
Qananun surutai da muryarsu tun kafin sukai ga isowa falon shine yaja hankalinta. Ta kafe qofar falon da kallo har zuwa sanda suka yaye labulen suka bayyana,yana gaba tana binsa a baya......
*_TURQASHI_*
*_BIGI SAI BIGI_*
*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_TASTED AND TRUSTED_*
*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*
*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*
*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*
*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*
*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*
*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*
*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Instagram handle_incense by kabo daughter*
*Facebook_kabo daughter*
*Twitter_kabo daughter*
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
PAGE 16
___________________________
*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*
*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*
*_NA GWADA NA GANI_*
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*
*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*
*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*
*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*
*_ME KIKE JIRA?_*
*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*
*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*
*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER*
*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*
*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*
*_zaki dariya za kuma ki godemin_*
*_gani ya kori ji_*
*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
_________________________
Idanunshi a kanta sanda yake shigowa zuwa cikin ainihin falon da yake da banbamci da sauran faluka dake gidan. Itama shi take kalla,kaman yadda suma bambanta a kamanni da mahaifinta haka suka bambanta a halaye da kuma dabi'u.
"Kai....kai,ubanka.....cireshi daga bakinka......tashi!" Matar dake biye dashi a baya ta furta a zabure bayan shigowarta dakin,idanunta kuma suka fada akansa sanda yake cin Chip's din hankalinsa kwance. Debe idanunta tayi daga kansu ta maida kan yaron da ya tsorata sosai saboda yasan halinta,ba shiri ya miqe tsaye har farantin chips din dake saman cinyarsa ya fadi,tsirarun dankalin ciki da yayi saura ya tarwatse a wajen.
Gewayesu yayi da gudu gudu zai fice yana matsawa daga wajenta amma duk da haka bai tsira ba,bayan uwar harara da take narka masa sai data bishi da ranqwashi tana cewa
"Bansan inda ka dauko kwadayi ba don ubanka,saidai daga can bangaren uban naka,don mu nan ba makwadaita bane,masu kwadayin ma addu'ar shiriya muke musu.....ba zaka jazamin masifa ba......cin abincin da aka da kudin haram?,ina zamana lafiya?,to muddin zaka ci gaba da shigowa dakin nan kuwa sawuna a likkafa zan maidaka gidan naka uban" Tayi maganar tana daga tsaye tana kallon qofar da tuni ya riga ya fice daga ita.
Dauke dubanta tayi daga kanta,don gugar zana irin wannan tash ba kasafai ta fiya damunta ba. Idan d sabo ta jima da sabawa da ita din,ta kuma zame mata jinin jiki.
"Ni zan fara gaidaki ko kece zaki fara gaidani?" Muryarsa ta dawo da hankalinta daga duniyar tunanin data fara nausawa. Fararen idanunta ta aza a kansa,mutumin dake a mazaunin mahaifi a gareta.....wanda ya kamata a ce a yanxun basu da tamkarshi,koda baiyi ya mahaifin nasu ba.....amma ya zamana ya toshe wani babban kaso cikin gibi da rayuwarsu zata samu.
Qaramin bakinta ta motsa wanda sauri yakan kira da shegen bakin rashin d'a da rashin mutunci,da wannan muryartata da sautinta ke cike da sanyi da nutsuwa tace
"Ina kwana kawu?"
"Lafiya qalau na kwana,sai uban baqinciki da takaicinki dake shirin hallakarmin da rayuwa" Ya furta cikin hargagi tamkar dama yana jiran ta gaidashinne.
Har yantsu dogon yatsanta yana saman labbanta,yayin data kafe mutumin data kira a dazu da kawun nata da idanunta,tana dan motsa yatsan nata saman lebenta tana kuma nazarin fuskarsa furucinsa dama motsinsa.
Ko sau daya bata taba ganin mutunci kima da martabarsa ba......daidai da misqala zarratin bata taba daukarshi da wani babban matsayi ba......abu daya ta sani,komai lalacewar fura tafi kashin shanu......komai kashinsa da zabgewa gami da lalacewar martabarsa a idanunta sunanshi kawunta kuma qani ga mahaifinta.
Maida idanunta tayi ta lumshe kawai kaman yadda ta saba masa a yawancin lokuta......tasan me ya sanyashi wannan zuwan,wani boyayyen buqatarsa ne dake a qasan rai da bai samu biyanta ba. Ta tuna haduwarsu ta qarshe dashi a wancan satin daya wuce. Dama ta sani ba zai haqura ba.....shine zai fake da wasu abubuwa wanda shi kansa ba kubuta yayi daga su ba.....yazo ya samu wannan matar da qiyayyarsu ta jima da yin tsiro da jijiyoyi a cikin jikinta. Takai qarshen maganar sanda take bude idanunta saman fuskar bibo.
Haduwa idanunsu sukayi waje daya da nata,ta juya qwayar idanunta tana watsa mata wani kallo
"Ki dain kallona da wadannan tsayyayun idanun naki na rashin kunya masu kama da idanun mage.......kai ya kamata ka tsaya a kanta saboda tana jawowa bawan Allah zagi,wanda ya jima da mantawa ya zauna a duniyar.....amma ina kyautata zaton kullum ta Allah sai mala'iku sun tadashi zaune sun nuna masa qazantar da d'iyar cikinsa ke aikatawa. Ya rasu yabar yara sama da goma sha takwas amma ba wadda ke hana masa kwanciya lafiya a kabarinsa sai ke?,ai wallahi Allah wadai da haihuwar d'iyoyi irinki.....indai haka haihuwar take gwara mutum ya zauna a haka" Tana maganar tana jujjuya hannunta guda daya gami da yarfeshi,idanunta a kafe saman fuskarta,kaman yadda itama tunda ta fara maganar ko sau daya bata dauke dubanta daga kan bibo ba.
Maganganun nata sunkai mata iyaka,tana jin ta gama daukar iya abinda zata dauka a iya wunin yau,saboda haka a nutse ta sauke qafafunta qasa ta miqa hannunta ta dauki handbag dinta ta miqe tsaye tana gyara rolling din mayafinta
"Fita zanyi,kuma ina da buqatar na kulle mana dakin kafin na fitan,idan ba damuwa ko zamu koma tsakar gida mu qarasa maganar a can?"
"Kaji ko?......dama ai na sani,babu wani sauran wanda take gani da kima a duniya.......yau koda fadima zata dawo duniya bata isa ta juyata ba bare alhaji" Tayi saurin cafe zancan.
Wani irin juyowa tayi gareta ta zube mata manyan fararen idanunta
"Kaman bakiji me nace ba ko?,nace muje tsakar gida mu qarasa......bankai ga furta cewa banda lokacin sauraro ba" Ta mata maganar dalla dalla tana kallonta.
Sosai bibo ta kafeta da kallo,har yanzu babu abinda zai sauyata......wannan rashin shakkar da rashin tsoron suna nan rubuce baro baro cikin ayyukanta da dukka motsinta,dakiyarta da shariyarta da daukan abu me zafi ta wulwulashi ta sauya masa mizani idan taso.
"Idan ta fito kawu qofar kawai zakaja jam lock din zai shige,ka sameni a qofar gida muddin baka wuce minti biyar ba" Tayi furucin sanda take takawa zata fice a falon tana riqe da vail din abayarta daya zame tana qoqarin mayar da rolling dinta yadda yake.
"Tashi muje na sameta a waje din inji da wacce hujjar zata kare kanta kuma" Ya furta dukka jikinsa na nuna zumudi da qaguwar yaga ya bita.
Da kallo bibo ta bishi tana daga zaune a kujerar ba tare data motsa ba baqinciki yana kasheta. A yau tana jin kaman ta tashi ta rufe rufa'i da duka. Yau ya tabbata mara amfani kwata kwata a garesu gaba daya.
"Ko nayi gaba kya rufe musu dakin?" A zafafe ta miqe tana gyara daurin dankwalinta
"In zauna inyi me a nan?,Allah ya sawwaqe,ai ni tawa son zuciyar bai fara sauka har takan kayan haramun ba" Ya jita sarai,ya kuma san da biyu take maganar,saidai a yanzu baya jin yana da lokacinta,dukka tunaninsa yana ta'allaqe akan sabreen. Yasan halinta sarai,muddin ya haura mintunan data dibar masa,yayi imanin da gaske zai iya zuwa ya tarar ta wuce din abinta.
Tana rungume da hannayenta sanda take tsaye a qofar gidan nasu ta bashi baya. Fuskar nan dake shimfide da wani irin kwarjini yau din cakude take da ninkin rashin fara'a da walwala na tun asali da aka santa dashi. Har tsakiyar zuciyarta takejin wani abu yana tsikarinta duk da yadda iskar dake yawo sararin subhana ke kada doguwar riga da dan mayafin saman kanta tana watsa daddadan qamshin turaren dake tashi a jikinta. Turaren da ita kanta yake sanya mata nutsuwa da kwanciyar hankali,dadinsa ya sanya ta zabeshi a matsayin turarenta na dindindin,duk da batayi tunani matsayinta zaikai a nan kusa ta mallakeshi ba.
Ta kalli agogon hannunta,yaci mintuna hudu cikin minti biyar din data bashi,don haka ta fara takawa sannu a hankali tana matsawa daga gaban gidan nasu.
Tun batayi nisa ba ta jiyo taku da kuma muryar kawun nata,bata da buqatar kallon fuskarsa ko doguwar magana ta hadasu,buqata gareshi zata sallameshi.....kamar yadda tun tale tale.....kaman yadda tun can baya bashi da amfani a garesu a yanzun ma bata tunani akwai wani sauran amfani da yake dashi a rayuwarsu,don haka ta sabule jakarta,ta zuge ta zaro wani abu daga cikin kudin da yayi saura a ciki ta dunqule a hannunta tana jiran isowarsa
"Ke sabreena......sabreen" Ya hada da qwala mata kira tamkar ya bata bashin kudi tana kuma shirin gudar masa dashi. Ranta ya sake baci,ta tsani kwakwazo,a banza ma idanun 'yan unguwar da dukka kunnuwansu harma da hankulansu suna kanta,kowanne motsi ko taku nata a biye suke dashi,sauraro suke.....jira sukeyi na samuwar dukkan wata dama da zasu samu abun magana a kanta. Wannan ya sanya tadan saurara daga tafiyar da takeyi tana dakon isowarsa. Ko a sannan tana iya ganin idanun tsirarun mutanen unguwar da suka samu sararin fitowa da safen kamar ita yana karakaina a kanta.
Irin wannan kallon nasu gareta ya zama tamkar jarrabi ko masifa cikin rayuwarsu. Akwai abubuwa da yawa tasan da akeson gaya mata amma babu wannan fuskar. Bataga dalilin zallar rashin adalci irin nasu da suke gwada mata ba suke kuma gwadawa rayuwarta ba. Sun sany hannu dukka da qafafunsu sun tankwabeta sun kuma tankwabe rayuwarta a sanda take da tsananin buqatarsu......a yanzu kuma data yankema kanta bata da buqarsu.....a sannan su kuma suke qoqarin dawo da ita su dankwafar da ita.....suka kuma fidda makamansu da harsunansu wajen illata mata gangar jiki da zuciya.
"Me na samu?" Ya iso gareta yana tambaya sanda motar da take da tabbacin waye a ciki ke dab da isowa inda take. Kowanne mutun da zatayi mu'amala dashi ko kuma tayi mu'amala dashi din......sau daya tak take masa wani karatu a taqaitaccen lokaci.......fahimtar waye kai?......meye qudurinka.......meye motsinka?.....mene manufarka......da sauran dukkan wani abu daya shafi rayuwarka yana zama RUBUTACCE cikin shafin qwaqwalwarta. Bata fiya manta abu ba,haka bata missing target saidai idan bata nufaci abu ba.
Ta baya ta miqa masa kudin sannan ta fara takawa zuwa ga motar da tuni ta iso inda suke harma ta samu wajen tsaiwa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 17
daga inda yake a zaune din yakejin kamar gilashin window din motar ya masa shamaki daga kallonta duk da yadda yake tarwai yake kuma iya baka daman gano komai dake ta wajen motar......duk da haka yana jin kamar ya rage ma idanunsa armashin kallonta,don haka ya kasa haqurin isowartata,ya sanya hannu ya sauke dukka gilashin nasa qasa.
sau daya tak ta taba ganinsa ido da ido,amma ta haddaceshi tsaf,tun daga abun hawansa har zuwa halayya da kamanninsa.......
Kakkaura kuma faffada da zaka iya kiransa me jiki saidai bai cancan ba. Maabocin iya ado sosai da murza hula ta zauna a kansa kamar shi yake saqa ma kansa ita. Yadda turarensa da shigarsa keda kyau da tsari haka ma kalaman bakinsa,saidai kash!.....daidai da wucewar daqiqa guda bata taba jin wani abu me kama da SO K'AUNA KO BEGE nashi ya tsartu a ranta ba.
Waishin mcikina meye SOYAYYA ne?. Ita kanta jerin kalmar SOYAYYA da yadda mutanen duniya suka daukaketa na daya daga cikin abinda ke sanyata dariya koda bata shiryawa hakan ba. SHIRME shine cikakkiyar ma'anar da take ganin yafi dacewa da a kirata ko kuma CUTA,idan akwai sunan da yafi haka lalacewa ma a nata ganin daidai ne a kirata da wannan sunan.
Yadda yake tsareta da kallo ya sanya qirjinta ya dinga suya duk kuwa da cewa ta saba da irin wannan shegen kallon. Kwarjininta na daya daga cikin abinda ya sanya take tsira daga guba da dafin MAZA duk kuwa da cewa ita da kanta take tsalle ta afka tsakiyar tarkon bisa tsananin lissafinta,ta kuma samu sa'a da nasarar zame kanta cikin SALO da kuma qwarewar iya wasa.
Da hanzarinsa ya fito ya zagaya don bude mata qofar motar,hakan ya bawa kawu dake lafe yana kallon komai qare masa kallo.
"Iya shaddar jikin yaronnan kawai ta isheni jari wallahi,wannan tsinanniyar yarina,yanzu meye aibun wannan da ba za'a aureshi ba?" Ya tambayi kansa da kansa yana naniqe da kudin hannunsa.
Idanunsa ya aza a kanta bayan ya bude mata motar,sai ya sakar mata murmushi,tadan lumshe ido tana qaqalo nata murmushin cikin dauriya da son maida masa. Gefe guda zuciyarta na cike fal da qarin wani mamakin akan D'A NAMIJI. ta tuna kalamansa akan matarsa dazun dazun nan,amma a yanzun gashi a gabanta ita kamar zai narke. Ta yaya zata yadda tayi aure a duniya?,ta yaya zata bari zuciyarta ta kamu da soyayyar wani namiji?,yaya za'ayi ta banzatar da lafiyar zuciyarta cikin soyayyar wani?,soyayyar halittar da babu tausayi ko jin qai a tare dasu?,halitta mafi son kai cikin halittun duniya gaba daya?,halitta me tsananin mugunta da son cutar da halittar mace 'yaruwarta?.
Ba zata iya sadaukar masa da murmushinta na dogon lokaci ba,duk kuwa da cewa fake smile ne,don haka ta zame jiki ta shige cikin motar ya mayar ya kulle yana sauke ajiyar zuciya. Yana jin duk duniya ba wanda ya kaishi sa'a a yau din. Yana jin kamar duka ranar tashi ce.
A kujeran driver ya zauna yana qoqarin tayar da motar amma duka ido da hankalinsa yana kanta
"Ina muka nufa my life?"
"My life?" Ta sake jaddada maganar a ranta
"Ko ina ya baro matarsa ta sunna da har ita ya danqara mata wannan sunan?" Wannan ba baqon abu bane a wajenta,saidai har yanzun mamaki da lamarin maza bai gama sakinta ba.
"SAMHG store" Ta amsa masa a nutse tana gyara agogon hannunta daya goce
"An gama ranki ya dade" Ya fadi cikin zumudi yana tayar da motar.
Sun jima akan hanya yana tauna abinda zaice da ita,don a taqaitaccen saninsa da ita.....mutum ce me matuqar tsari,nutsuwa da aje komai a bisa gurbi da muhallinsa. Bayaso ya kwafsa kaman waccan karon,bayaso damarsa ta sake kubce masa,duk da cewa har kawo yanzun baisan me ya aikata daya rasa wancan damar a wancan karon ba.
Yaji babu dadi ainun saboda ya qwallafa rai sosai a kanta. Ta yiwa zuciyarsa wani mahaukaci kamu a ganin farko. Yayi tsammanin kudinsa da ajin mataki na rayuwa zai saya masa ita cikin qanqanin lokaci,sanin da ya yiwa 'yammata kenan a yanzun,ballantana ita dake da kyau da aji irin wannan.
Sanda yake wannan tunanin nata nazarin da karatunsa duka a kansa yake. Yadda yaketa rejecting kiran dake fama shigowa wayarsa a jejjere. Duk kiran da zai shigo sai ya katseshi. Tuni hankali da kuma jikinta ya bata wanda ke kira.
Idanunta tadan lumshe,koda yaushe su dinne dai,cikin wahala,qasqanci,tozarta da kuma wulaqanta zaune cikin gidajen aure. Ko meye kuma zai fito yaje yazo su din yake afkawa.
"Zan iya cewa wani abu?" Ya tambaya a ladabce yana murza steering motar cikin qwarewa
"Kafin sannan ya kamata ka daga wannan kiran ko?" Ta fada idonta akan fuskarsa.
Motsawa kadan yayi yana duban wayar ta qasa idanu,bai zaci ma ta lura da hakan ba. Haushi ya soma kamashi akan kiran da take masan babu qaqqautawa. Yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,tunda bai jima da fita a gidan ba,yasan kuma abinda ya fito ya baro a gidan
"Tarin damuwa ce da matsaloli kawai take dauke dashi" Ya furta yana jan siririn tsaki.
Har tsakiyar ranta taji saukar maganar,ta lumshe ido kadan tana budesu. Yana nan din a haka,yana nan yadda ta karanta. Tayi qoqarin tureshi daga shiga layikanta,tayi qoqarin hanashi shiga cikin tarkonta don baya cikin irin mazan data zana bisa layi da gurbin rayuwarta,taso ta barshi ya samu me hukuntashi a gaba.....amma tunda har ya sake dawowa cikin rayuwartata cike da karsashi da zumudi,to tayi imani hukuntashi yana cikin qaddararta ne. Ba kuma zata qyaleshi ba,a wannan karon saita hukuntashin yadda ta saba hukunta maza irinsa. Maza irinsa basa tsira daga tarkonta......basa tsira daga kamunta,hakanan basa tsira daga hukuncinta.
Cikin salo na dabarar da yake gani kaman ba zata gane ba ya latse wayar,ya kuma jefo mata maganar da tafi damunsa
"Hanan.......wannan karon bazan bari ki kufcemin ba"
"Nima bazan bari ka tafi ba" Ta furta,a bakinta bisa mizanin ma'ana qwaya daya tak da hankali zai iya fahimta,amma kuma an aje ajjiyayyar ma'anar da ake nufi da maganar can qasan zukata.
Wani irin dadin daya sabbaba masa lafiyayyen murmushi ya ziyarceshi. Bai taba kawowa ko kusa a ransa samun wannan gwaggwabar nasarar a kurkusa haka ba,amma kuma,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa
"Duk kyau ko matsayinta zata sauko......a yanzun fa mata ke neman mazan aure idanu rufe" Hudubar data shiga kunnensa kenan,kuma ya yarda da hakan dari bisa dari.
"Amma hanan banga alama ba......bansa inane mazaunin da kike rayuwa ba,gida unguwa da sauransu"
"Gaggawar me kakeyi?,kada ka samu damuwa" Ta amsa masa tana jin ya ginsheta gaba daya,tana jin ta damu qarshen zamansu yazo,ta qagu su isa SAMHG store ya ajeta ya bata sarari.
A hankali ya kutsa motar babbar harabar kantin saida dukkanin kayan buqatar rayuwa,wanda zaifi kyau ka kirashi da kasuwa a sauqaqe amma kuma a zamanance. Ba abinda basu hada ba na kayan buqatu,tun daga tufafi zuwa kayan masarufi. Wajen nada matuqar girman da idan ka kirashi da duniyar siye da siyarwa. Girmansa ya sanya yake da mashigu daban daban da kuma guraren fita mabanbanta.
Cikin tafkekiyar harabar wajen ya aje motarsa,ya kasheta cikin mutuwar jiki da kasala yana waiwayowa inda take zaune tana qoqarin rataya jakarta gami da daukar wayarta ta riqe wadda ke aje saman cinyarta.
"Idan ban damuwa zan dan tayaki tattaki zuwa ciki......don naga wajen kamar cike yake da maza da yawa......ni kuma ina kishin na barki ki fita ke daya a kallemin ke" Ya furta cikin kulawa da wani irin narkakken so dake ragargazar zuciyarsa.
Da wani sassanyan kallo ta jefeshi,qawataccen murmushin nan dake qawata fuskarta da kuma labbanta ta sakar masa. Ta rausayar da kanta gefe tana juya idanunta. So take ta sallameshi a iya haka,bata buqatar doguwar damuwa. A lokaci irin wannan da takai qarshen mission dinta,ko fita unguwa ba kasafai take damunta ba sai idan buqatar haka ta taso. To amma hakanan taji akwai buqatar ta fita din,akwai kuma buqatar ta fita tayi musu siyayya.
"Baka da damuwa akan duka wannan......wannan hanan din ba komai idanunta ke kalla ba ballantana su burgeta" Ta bashi amsa a nutse.
Murmushi ya saki yana qara narkewa a sonta,yana ji cewa zai iya yin komai don ya mallaketa,yana jin cewa muddin ya sake barinta ta subuce masa a wannan karon ya tafka babbar asarar da bazai iya maida madadinta ba,baya jin ma zai bari hakan ya faru dashi sam sam.....kai koda tuna hakan na iya faruwar bayason yayi.
"Na ga zahiri......na kuma tabbatar wannan halittar ta daban ce......gamu cikin neman sa'ar kasancewa da ita" Ya fada yana lumshe idanu. Kai ta kawar amma tana murmushin yaqe. Ya numfasa bayan ya gama qare mata kallo cikin shauqi ya dauki wayarsa dake aje tun sanda ya maidata silent ya bude.
Tarin miscall a qalla guda goma kyawawa daga gareta. Ya jawo maballin sama ya sharesu yana sakin tsaki can qasan ranshi tare da wucewa mobile app na banking da yake ajiyar kudadensa.
Sosai ta jingina da makarin motar idanunta a lumshe sosai,sai kayi tsammanin bacci ko kuma gajiya ne sukayi mata yawa,saidai a cikin biyun duka babu ko daya a ciki.
"A taimaka a karantomin account number na dan bada wani tukuici" Idanunta ta janye daga saman wayar nasa,saita tashi ta zauna sosai tana dan sakin murmushi
"No need" Ta amsa masa a yangance kaman yadda ta saba magana
"Please.......ba wani abu bane me yawa.....just tukucin bani damar ganinki da kikayi a yau ne" Bata sake ce masa komai ba,sai ta zura hannunta cikin jakarta,wani dan siririn card me ruwan zaibar gold ta ciro ta aje a gefansa. Ta dauke kai tana qoqarin bude murfin motar wanda ita kanta tasan ba zata budu ta sauqi ko dadin rai ba......ta kwana da sanin meta aiwatar mata.
Cikin qasa da minti daya taji ya furzar da iska daga bakinsa gami da cewa
"Done.....ina fata zakiyi appreciating"
"Why not?,godiya me kima......godiya nake qwarai......but motarka tana nema ta riqeni fa"
"Da zatayi hakan data taimakeni ai" Ya amsata yana sake lafewa jikin kujerar. Kyawawan sexy eyes dinta ta waro waje kadan,sai kuma ta daga hannunta tana duban agogo
"Akwai alqawari da nayi,bana so kuma na saba......idan ka sani na saba kuma......next time kafin na baka daman sake haduwa dani....." Katseta yayi yana dariya ta hanyar hada hannayensa biyu waje daya sannan ya saukesu ya juya yana buda side dinsa
"Lemme check meye ya riqemin amaryata haka".
Da lumsassun idanunta ta bishi da kallo har zuwa sanda yake zagayawa gaban motar zuwa daya side din da take zaune. Yayi dukan dabarunsa amma hakan baiba,don haka ya zagayo yana fadin
" Bansan me yake faruwa,lafiya lau qofar yake,bari nasa a duban.....am really sorry" Ya sake apologizing yana hade hannuwansa.
taka Kai kawai ta daga masa tana irgen lokutan cikar target dinta. Cikin saa kuwa ya juya ya fara takawa yana barin wajen,wanda hakan ya bata damar janye kallonta sannu a hankali daga kansa,ta kuma maida saman wayarsa dake ajiye a wajen tana bada haske,tabbacin yunqurin hanata komawa key yayi daidai kenan,saita katse kiran da takeyi daga tata wayar zuwa tasa don sanya wayar awake.
A nutse ta jawo wayar ta wuce zuwa ga maballin kira.
Tarin miscall dinne kuwa ta samu kamar yadda tayi zato,dukka kuma daga number dake ajiye cikin wayar da sunan MOM SUHAIL.
"SUHAIL" Ta ambata a fili,idan har bawai ta manta ba suhail din shine sunan first born dinsa kamar yadda T.j ya tabbatar mata.
Wani irin tausayin matar da batasan ko wacece ba ya fara ratsa ta. Tana shirin karkata akalar binciken nata zuwa wani sashe na daban saqon SMS ya shigo wayar.
MOM SUHAIL kamar yadda yake a rubuce ta bangaren kira. Bata tsaya dogon jinkiri ba ta bude,gajeran saqo ne kamar haka.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 18
_Nayita kiranka baka dauka ba,kome meye mukayi da kai kafin ka baro gida ai ya kamata ka tsaya kaji dalilin kiran da nake maka babu qaqqautawa,bayan ka fito ciwon suhail ya tashi,a yanxu haka muna asibiti,amma babu ko sisi a hannuna,baka barmin komai ba,already kuma account dina yana buqatar naje banki na gyara bare nayi hidimata da kudina yadda na saba_.
Wani abu me tauri taji ya tsaye mata a wuya,ta zura hannu a jakarta ta ciro wayarta,tanason taga nawa ita ya kashe mata?,nawa ya saka mata alhali ko sisi matarsa bata amfana dashi ba?.
Naira dubu dari ta tarar. Wani matsiyacin tsaki ta saki,cikin dukkan arziqinsa ya rasa da meye zaiyi mata kyauta sai naira dubu dari?. Bata tsaya batawa kanta lokaci ba ta sauka ta koma mobile app dinsa da bai jima da fita a kai ba.
Daga password har username dinsa fes cikin kanta,tamkar hadaka ko gamayya sukayi dashi wajen creating dinsu a sanda zai bude manhajar. Cikin qasa da second goma komai ya bude,tarin miliyoyin kudaden dake kwance cikin account din nasa suka bayyanarwa idanunta,sai ta koms ta jingina da kujerar motar tana kallonsu,kamar ma bata tsoro ko shakkar dawowarsa.
Numfashi take fitarwa d'ai d'ai qirijinta na sake quntata. Tarin zallar rashin imanin maza yana sake tabbatar da kansa a zuciyarta.
"Yana da wannan kudin ya fita yabar matarsa babu ko sisi?,yana da irin wadannan kudaden yabar yaronsa cikin halin ciwo?,yana da wannan kudin ya gaza siya masa abun hawan da idan lalura irin wannan ta taso baya kusa zata kaisu zuwa ga asibiti cikin gaggawa?.
Tsanar MAZA tsanar SOYAYYA da kuma tsanar AURE suka sake linkuwa cikin ranta. Irin wannan shaidojin na gani da ido ta din saidai ta bada labarinsu. Shi din ma ba komai bane a cikin maza......bata kuma san namiji na nawa bane shi din da a yau xai shiga makarantarta.......a yau zata sanyashi ya koyi darasi kaman sauran,saidai nasa darasin yazo ne a gaggauce saboda gamawa da babinsa da tayi,da kuma dadewa da tayi da sanin shi din wayeshi?.
Beneficiaries dinsa ta duba,cikin sa'a tun batayi nisa ba taci karo da sunan da yayi daidai da sunan matar
*ameena mu'azzam*.
Kai tsaye ta saka amount din da yayi mata ta kuma karkatasu zuwa ga account din.
Daidai lokacin data hangi tahowarsa,ta daga hannunta ta zare wania abu daga jikin qofar,sannan ta maida hankalinta kan wayar kamar ba me wayar ne yake dosota ba.
Hankali kwance ta koma ta goge alert massage din da kamfanin sadarwa suka aiko,ta kuma koma zuwa ga email a gaggauce ta goge nashi tayi minimize ta maida wayar mazauninta tana karanta sunan banking da yake amfani dashi,sannan ta zaro tata wayar tana duba ma'ajiyar lambobi dake cikin wayar.
Sunayen dake ajjiye cikin wayar ta fara bi,cak ta tsaya saman wani suna da yayi daidai da sunan banking nasa,ta danna malatsi na tura saqonni,ta kuma aika da saqon a gajarce
"Done" Ta jefa wayar a jaka daidai sanda ya iso bakin window din suna sake yunqurin buda motar.
Ja daya bakaniken ya yiwa murfin ya bude,sai ya waiwaya yana dubansa cikin mamaki,wanda shima cikin manakin ya iso
"Oga ina tunanin kaine baka jawo ta da kyau ba"
"Kai amma nayi mamakin faruwar hakan" Ya matsa yana kama hannun motar ya matsashi har sau uku. Mamaki yadan sake kamashi,amma kuma kiransa da tayi d nuryarta me laushi ya dauke hankalinsa daga nan.
"Okay na gode to" Ya fadiwa bakaniken yana cirar wani abu a aljihunsa adan gaggauce saboda kiran nata.
Bude mata qofar yayi,ta sako qafafunta ta fito tana gyara zaman abayar jikinta. Cikin nuna kulawa yake fadin
"Da alama motar bata gaji dake ba,kamar yadda me motar shima bai gaji da kallin wannan kyakkyawar surar ba......don Allah ayimin lamuni a bani exact gurin da zan sameki.......da gaske nake,banzo da wasa ba,ni din ba irin sauran samarin yanxu bane......da niyyar aure nazo" Ya qarasa maganar yana lanqwashe murya.
A nutse ta watsa masa idanunta da suke sake narkar dashi. Batajin daga rana irin ta yau ma zai sake samun damar tsaiwa da ita a muhalli daya irin yanzun. Wannan itace dama ta qarshe kuma lokaci na qarshe a wajensa tsakaninsa da ita.
"Ba damuwa......ka samu number dina ai.....komai zaizo da sauqi?"
"Are you sure?" Ya tambayeta yana kallonta cikin kokwanto. Saboda shi kansa yasan samunta din abune me wahala.....ta subuce masa wancan karon.....hakanan haka ya qaraci karakainarsa da nemanta amma ko me kama da ita babu ballantana ita karan kanta din. Kai kawai ta gyada masa sannan ta juya ta soma takawa tana barin wajen gami da cewa
"Godiya nake......fatan alkhairi"
"Nike da godiya kyakkyawa" Ya fada murya a lanqwashe yana binta da kallo da zazzafan so,yana jin kamar ya saceta ya gudu da ita ya mallakawa kansa ita.
A nutse take taka kowanne step da zai sadata da ainihin makeken store din. Murmushi ne kwance saman fuskarta ita daya,duk da bata juya ba amma ta tabbatar yana tsaye ne yana kallonta,tana hasaso yadda fuskarsa zata koma a sanda ya laluba asusun bankinsa ya taras da barnar datayi masa,tana hasaso yadda wannan tattausan kallon zai koma zazzafan kallo da kuma zurfin tunanin TA YAYA AKAYI HAKA YA FARU?.
Yadda take daukan hankula da idanuwan wasu daga cikin jama'an dake sabgoginsu a waje da cikin shagon bai dameta ba,don ba wani baqon abu bane a wajen ta. Itadai ta sani,akwai dubbai zuwa miliyoyin mata da suka zartata a kyau.....don bata tana daukan kanta ta sanya a sahu ko jerin kyawawan mata ba,amma batasan mene a tattare da ita me matuqar jan hankali irin haka ba.
K'annenta sune gaba da komai da kuma kowa. Buqatunsu kuma sune gaba da nata buqatun. Don haka duk list na abinda suke buqata ta fara dubawa. Tana tsinta tana jefawa a cart.
Ta kwashi a qalla minti ashirin tana nasu siyayyan sannan ta fara nata. Siyayyarta bame sauqi bane,tana da tsari tana zabi,ba komai yake burgeta ba kaman yadda a rayuwarta na zahiri ba kowa ke burgeta ba,komai nata yana da tsari,don haka ta bata lokaci sosai akan nata kayan,ta saki jiki kuma kamar ba zata bar shagon ba.
Sai data gama tsaf sannan ta gangara bangaren kayan maqulashe. A duk sanda ta samu kudi irin haka bata rabo da siya musu kayan taba ka lashe,harda ajiye wasu ma cikin daki. A duniya idan akwai abinda taqi jini shine taji sunce BABU ko BANI DASHI ADDA....kalma ce da bata yarda a yanzun ta shiga tsari da babin rayuwarsu sam sam.
Sashe ne dake danqare da chocolate kala kala da kuma biscuits. Masu tsananin tsada da kuma masu matsakaicin kudi. Da ido ta dinga bisu daya bayan daya,wani lokaci can baya daya shude bata isa ta sanyasu cikin idanunta ba,wani lokaci can baya daya shude sunfi qarfin tabawar hannuwanta ballantana akai ga batun sanyasu a bakinta.....wani lokaci can baya daya shude saidai ta hangesu......hangema daga nesa.....wannan ya sanya tayi alqawari......ta kuma ci alwashin muddin tana raye ba zasufi qarfin rayuwar 'yan uwanta ba.
Tana cikin dubawar ta hangi favourite chocolate dinta,ta kasa jurewa sai data daukota ta bareta ta jefata a baki,daidai sanda taji anyi kiranta da daya daga cikin sunayenta data mallakawa wani.....sunayen da suke zama tamkar tag ne ga kowanne namiji daya taba shiga rayuwarta.
"Basma" Iya sunan daya kira tun kafin ta waiwaya ya gaya mata waye. Duk wanda ta bawa sunanta wannan sunan nashi ne shi daya,wannan sunan shita mallakawa shi kadai.....wannan kuma ya zame mata stamp kuma alama ta kowanne mutum daya taba shiga DUNIYArta.
Murmushi ta saki tun kafin ta juya tayi tozali da wanda yayi kiran.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 19
________________________
*_Katafaren sansanin UMMUMAHNOOR LUXURY,TA SHIRYA TSAF DON SAMA MUKU TSALA TSALAN KAYAN ADO DA SUTURA NA KECE RAINI IRIN NA 'YA'YA MATA,IRINSU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
___________________________
Iya sunan daya kirata dashi ya bayyana mata kanshi tun kafin takai ga waiwayowa.
Sanda ta juyo din yana tsaye daga bayanta,ya kafeta da wadannan jarababbun idanun nasa data sanshi dasu tun a lokacin,idanuwan data tsana fiye da kowanne ido a duniya,idanuwan da kuma tafi tsana bayan baqin mugun halayen dake rataye da jiki da zuciyarsa.
"Malam nasiru....kana lafiya?" Ta fada calmly tana dauko wani box na chocolate din ta jefa cikin kwando. Takowa ya soma yi yana sake kusantota,har yanzun dai bai dauke idanunsa a kanta ba.
Sake daga kai tayi ta kalleshi,sai ta fara tura kwandonta gaba
"Kana mamaki ne?.....kayi tunanin bazan iya shaida ka ba ko?" Ta tambayeshi da murmushi a saman wannan miskilar fuskar da zaiyi wahala kaga fitar murmushin daga samanta.
"Wannan basman bata manta fuskar mutanen da suka taba shigowa cikin rayuwarta.......hakanan wannan basman bata manta fuskar mutane irinku......hope kana lafiya ko?" Ta sake tambayarsa tana tafiya a nutse,tana kuma ci gaba da zaban abinda yayi mata tana jefawa a kwandon.
Tarin mamaki ne ya lullube masa zuciya ainun......tsahon lokutan yayi tunanin duk ranar da sukayi haduwa ta farko da ita zata razana......zata kuma tsorata,idan da yiwuwar ma ta nemi guduwa duka zatayin duba da girman laifin data aikata masa.
"Tana da wayo......tana kuma da hadari......da alama akwai abinda ta taka" Maganar abokinsa kenan ta dawo cikin kansa bayan wani zama da sukayi dashi,wannan ya sanyashi Maida hankalinsa jikinsa sosai,ya kuma tattaro bacin rannan da ta dasawa zuciyarsa wanda har yanxu a cikin bala'i da masifar data sakashi yake
"Idan kika mantani ai baki cika 'yar halali ba......ai dama idan kere na yawo zabo na yawo dole wataran zasu hadu" Ya farta cikin fushi.
"Yar halak?" Ta furta a sarari,sai ta dakata da abinda takeyi ta waiwayo ta zuba masa idanu
"Akwai bashi ne tsakaninmu da kake nema na har kalmar kere da zabo zata gitta tsakaninmu?" Kansa ya daure tamau,zallar raina masa hankali da tayi yaga ta fito muraran. Ji yayi bashi da sauran abinda ya rage illa ya fiddo mata makamansa.
"Kina iya cewa komai,amma kafin sannan shawara daya zan baki.......ki maido min dukka kudade na da kika samfe daga account dina sawunki a likkafa.....ko kuma hukuma ta matsaki ki fito dasu" Idanunta ta watsa masa tana sakin murmushi
"Kasan a inda kudadenka suke?,za kuma ka iya zuwa karba din idan na gaya maka?" A tunzure cikin fushi da yadda takeson maida maganar wata mara alfanu ko muhimmanci ya kalleta
"Duk duniya akwai wanda ya isa ya hanani karbar haqqina?,akwai wanda ya isa ya cimin haqqina ban karba ba?"
"Kwantar da hankalinka mana...." Tace dashi still tana murmushi,saita dafe kwandonta ta soma takawa tana nufar ficewa daga gidan kuma tana fadin
"Gidan marayun nan......a wannan ranar kowanne yaro ya rabauta da duk wani abu na buqata da bashi dashi,suttura kayan ado na 'yanmatan da kuke sakawa ana musu dauki d'ai d'ai cikin dare ana kai muku su gidajen shaqatawarku da hotels kamar yadda ka gayyaceni nima zuwa naka dakin hotel din......kana iya zuwa ka karbi komai dake hannunsu ka sanyashi a kasuwa ka maido kudinka......muddin kuma ba zaka iya hakan ba,to ina baka shawarar ka fita daga rayuwar SABREEN......ka kuma daina bibiyarta......idan bakaji ba kuma......zan sake sakaka fidda wasu kudaden masu ciwo da baka shirya fitarsu ba kamar dai wancan lokacin" Ta qare maganar tana kaiwa qarshen wajen ta karya kwana tana niyyar bacewa ganinsa.
Daya biyu uku yahada dukka yaga basuyi masa daidai ba. Wani sashe na zuciyarsa ya soma zugashi da
"Ta yaya kana tsaye qaramar yarinya me qarancin shekaru zata nemi raina maka hankali?".
Ya samu kansa da kansa da tuhumar kansa tare da ganin tsananin baike da wallensa. Wannan tunanin kadai ya qara masa qaimi,ya taka qafafunsa cikin azama da qwarin gwiwa ya soma rufa mata baya lokacin da takeji a ranta ta kammala siyan duk wani abu da suke da buqata ita da 'yan uwanta,wanann ya sanya ta nufi gurin biyan kudin kai tsaye
"Inda zan baka shawara......zaifi kyau ka koma ka tafi sabgaka...."
"Saboda ke kike nema na bani ke nemanki ba?,saboda nine mai laifi bake bace?" Hankali kwance ta maqale kafada tana sakin siririn murmushi
"A'aha.....ba don dukka wadannan dalilan bane suka sanya ni na baka wannan shawarar ba......na baka ita ne don gudun kada ALLURA TA TONO GARMA"
"Ni dake zanga wanda allurarsa zata tono garma......"
"Ba laifilaifi malam naseer....." Abinda tace dashi kenan tana ci gaba da tattaki a bayanta. Yau yanason ganin qarshen gudun ruwanta......yanason yasan ita din wace?......da waye take tare?,su waye suka dauki nauyinta?.
Waye ya turota?,maqarqashiya ce ko kuma hadin baki?.
Hakanan yaci gaba da rufa mata baya tamkar me tsaron lafiyarta ko wanda aka bashi aikin kula da ita. Har cikin zuciyarsa yakejin yau zai nuna mata shi waye,zai kuma tabbatar mata tayi mahaukacin gangancin kuskure data shiga hanyarsa.
Mutum biyu suka samu ana lissafa kayansu jikin qaramar na'urar dake da alhakin qididdige fitar kaya cikin katafaren shagon.
A hankali ta tsaya daga bayan matar wadda bata iya ganin ainihin fuskarta,saidai shigar atamfar chiganvy gold mix match da wani irin danyen lafiyayyen lace da aka yiwa qawataccen dinkin buba da zani ya fito da kamalarta da kuma cikar siffarta. Tsaye yake daga gefanta,matashin da duka duka shekarunsa ba zasu haura ashirin da takwas ba. Ya bata dukka hankalinsa yana sauraren maganar da takeyi dashi cikin muryarta dake bayyanar da tsantsar kamalarta da cikakkiyar nutsuwar ruhi data halitta. Yanayin yadda ya rusuna ya bata hankalinsa yana saurarenta kadai zai bayyana maka zallar ladabi da kuma ganin girmanta da yakeyi,akwai kuma tag idan ka lura sosai daga gaban aljihunsa dake bayyanar da cewa shi din ma'aikaci ne a wani guri na daban.
Mai matsakaicin tsaho ce,hakanan me jiki ce saidai ba qiba me yawa cancan ba,ta lullube saman kanta da 4D Vail me asalin kyau da aka zubawa duwatsu masu daraja akayi adon jiki dasu.
Sassanyan qamshinta ya dinga tasowa a hankali daga jikinta zuwa hancin sabreen dake tsaye daga bayanta tana kallon tulin kayan siyayyar da aketa jera mata cikin ledar dake dauke da tambarin store din.
Hannunta dake dauke da wasu kyawawan banguls masu sheqi ta miqawa ma'aikacin gurin tana cewa
"Bansan me yasa suke son mu'amala da wannan katin bankin ba,duk sun lalace da lamarin cashless" Murmushi ma'aikacin ya saki cikin tsananin girmamawa
"To ai hajiya yafi sauqin sha'ani ne" Kai ta gyada a hankali tana furta
"To Allah ya kyauta". A nutse ta maida dubanta ga saurayin,tun kafin tace wani abu ya sake matsowa a ladabce yana bata hankalinsa
"Ka kiramin wancan yawalen da kuma wancan acicin suzo mu wuce kafin rana ta sake dagawa"
"Okay to in sha Allah" Ya amsa mata yana zaro wayarsa daga gaban rigarsa,yayin da ta fara takawa cikin nutsuwa tana ficewa daga gurin hadi da gyara yafen mayafinta dake qoqarin zamewa.
Wucewar tata ya bawa sabreen damar matsowa gaba don a lissafa mata nata kayan
"Ji mana.......zaki dawomin da duk abinda kika san kin sace ko kuma saimun dangana da hukuma?" Hannayenta ta goye a qirjinta tana kallon qofa yadda mutane ki shige da ficensu hankali kwance. Yana da ban mamaki......saidai ita din ta fishi abun mamaki. Inda yasan meta taka a kansa......inda tasan cewa kafataninsa.....zahirinsa da badininsa a tafin hannunta yake da baiyi gigin matsawa rayuwarta ba har ya matso gareta har haka ba.
A nutse ta waiwayo ta zube masa farare tas din idanunta masu matuqar jan hankali da fusgar tunanin me tunani
"Kana sha'awar yin gaba da gaba da hukumar ne?" Ta masa tambayar idanunta a tsaye car tsakiyar nashi. Idan ya kira kansa gogaggen cikin duniya baiyi qarya ba.....muddin kuwa ya kasance hakan yana ganin mugun ganganci ne zaiyi ya gaza samun fikirar karantar mutum daga yanayin kallo zuwa lafuzan bakinsa ba.......
"Kina tunanin abune me wahala a gareni?" Ya amsa mata yana mamakin yadda wannan mugun kwarjinin nata yake taka masa burki,kaifin idanunta ke hanashi daukan mataki tare da aiwatar da abinda yayi niyya.......abinda zuciyarsa ke shawartarsa.
"Ko daya....daidai ne kuma" Ta amsa masa tana dauke duba da hankalinta daga kanshi tana maidawa ga ma'aikacin wanda ya kammala lissafin yana gaya mata adadin abinda zata biya.
"Okay" Ta furta hankali kwance tana maida dubanta ga daya daga cikin ma'aikatan dake taimakawa da wadanda sukayi siyayya me yawa kamarta
"Ko zaka fitamin dasu gate na biyu?"
"Okay hajiya" Ya fada yana ajjiye qaramar calculator dake hannunsa yana qarasowa gurin tare da jira a gama sanya dukka kayan cikin leda.
Sake Waiwayowa tayi gareshi karo na biyu. Kallon da tayi masa ta fahimci yakai matakin qarshe a iya haqurinsa
"Malam naseer......ka shirya biyan duka bill na siyayyar sabreen ko kuwa tunda kai ka kawo qafafunka duk da gargadinka da tayi?"
"Sabreen?" Ya maimaita sunan yana kallon idanunta. Kiran sunan sabreen da tayi a maimakon basma shi ya batar masa da tunani cikin taqi qanqani.
"Zai biya duka bill din.....na gode sosai" Ta fadiwa ma'aikacin
"Naga uban wanda zai sakani biyan kudin nan......na fahimci na sakar miki fa da yawa" Ya furta da zafi sannan a zafafe ya biyo bayanta. Ya tsammaci zata nemi guduwa ko ta gudu dinma,amma ga tarin mamakinsa tun bai qarasa isowa gareta ba taja cak ta tsaya tana sauraron isowarsa.
"Ka samu aminci game da haramtattun kayanka da aka aiko maka dasu ta cikin jirgin ruwan dake tsakanin River Benue da riba niger?.......ko kuma ka shirya aci kasuwar wannan sirrin da jami'an tsaron dake neman kayan tamkar yadda mutuwa ke neman ruhi?".
Kamar wanda aka sanyawa sasari akan tsaida haka yaja wani wawan burki. Kallonta yakeyi da madaukakin mamaki. Wanne irin hadari ne da ita har haka?. Wanne nisan ji da gani ne da ita?,nisan binciken da ya bata damar gano birnannen sirrinsa da ko matarsa da suke kwana daki daya su tashi daki daya bata sani ba?.
"Ka biyasu kudin siyayyarsu duk yadda suka buqata,na barka lafiya Alhaji Naseer" Ta qarashe maganar tana takawa hankali kwance tana fita kwata kwata daga wajen.
"Malam qaraso ka bada kudin......ta atm ne ko cash zaka bada?" Muryar ma'aikacin ta katseshi daga bin burbushin hanyar data wuce da kallo ya juyo zuwa wajen biyan kudin yana sauke wani irin gauron numfashi me nauyi da zafi cikin tsananin mamaki da tsoro.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 20
________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_ingancin kaya da kwalliyar mata shine muradinmu_*
__________________________
Iya sunan daya kirata dashi ya bayyana mata kanshi tun kafin takai ga waiwayowa.
Sanda ta juyo din yana tsaye daga bayanta,ya kafeta da wadannan jarababbun idanun nasa data sanshi dasu tun a lokacin,idanuwan data tsana fiye da kowanne ido a duniya,idanuwan da kuma tafi tsana bayan baqin mugun halayen dake rataye da jiki da zuciyarsa.
"Malam nasiru....kana lafiya?" Ta fada calmly tana dauko wani box na chocolate din ta jefa cikin kwando. Takowa ya soma yi yana sake kusantota,har yanzun dai bai dauke idanunsa a kanta ba.
Sake daga kai tayi ta kalleshi,sai ta fara tura kwandonta gaba
"Kana mamaki ne?.....kayi tunanin bazan iya shaida ka ba ko?" Ta tambayeshi da murmushi a saman wannan miskilar fuskar da zaiyi wahala kaga fitar murmushin daga samanta.
"Wannan basman bata manta fuskar mutanen da suka taba shigowa cikin rayuwarta.......hakanan wannan basman bata manta fuskar mutane irinku......hope kana lafiya ko?" Ta sake tambayarsa tana tafiya a nutse,tana kuma ci gaba da zaban abinda yayi mata tana jefawa a kwandon.
Tarin mamaki ne ya lullube masa zuciya ainun......tsahon lokutan yayi tunanin duk ranar da sukayi haduwa ta farko da ita zata razana......zata kuma tsorata,idan da yiwuwar ma ta nemi guduwa duka zatayin duba da girman laifin data aikata masa.
"Tana da wayo......tana kuma da hadari......da alama akwai abinda ta taka" Maganar abokinsa kenan ta dawo cikin kansa bayan wani zama da sukayi dashi,wannan ya sanyashi Maida hankalinsa jikinsa sosai,ya kuma tattaro bacin rannan da ta dasawa zuciyarsa wanda har yanxu a cikin bala'i da masifar data sakashi yake
"Idan kika mantani ai baki cika 'yar halali ba......ai dama idan kere na yawo zabo na yawo dole wataran zasu hadu" Ya farta cikin fushi.
"Yar halak?" Ta furta a sarari,sai ta dakata da abinda takeyi ta waiwayo ta zuba masa idanu
"Akwai bashi ne tsakaninmu da kake nema na har kalmar kere da zabo zata gitta tsakaninmu?" Kansa ya daure tamau,zallar raina masa hankali da tayi yaga ta fito muraran. Ji yayi bashi da sauran abinda ya rage illa ya fiddo mata makamansa.
"Kina iya cewa komai,amma kafin sannan shawara daya zan baki.......ki maido min dukka kudade na da kika samfe daga account dina sawunki a likkafa.....ko kuma hukuma ta matsaki ki fito dasu" Idanunta ta watsa masa tana sakin murmushi
"Kasan a inda kudadenka suke?,za kuma ka iya zuwa karba din idan na gaya maka?" A tunzure cikin fushi da yadda takeson maida maganar wata mara alfanu ko muhimmanci ya kalleta
"Duk duniya akwai wanda ya isa ya hanani karbar haqqina?,akwai wanda ya isa ya cimin haqqina ban karba ba?"
"Kwantar da hankalinka mana...." Tace dashi still tana murmushi,saita dafe kwandonta ta soma takawa tana nufar ficewa daga gidan kuma tana fadin
"Gidan marayun nan......a wannan ranar kowanne yaro ya rabauta da duk wani abu na buqata da bashi dashi,suttura kayan ado na 'yanmatan da kuke sakawa ana musu dauki d'ai d'ai cikin dare ana kai muku su gidajen shaqatawarku da hotels kamar yadda ka gayyaceni nima zuwa naka dakin hotel din......kana iya zuwa ka karbi komai dake hannunsu ka sanyashi a kasuwa ka maido kudinka......muddin kuma ba zaka iya hakan ba,to ina baka shawarar ka fita daga rayuwar SABREEN......ka kuma daina bibiyarta......idan bakaji ba kuma......zan sake sakaka fidda wasu kudaden masu ciwo da baka shirya fitarsu ba kamar dai wancan lokacin" Ta qare maganar tana kaiwa qarshen wajen ta karya kwana tana niyyar bacewa ganinsa.
Daya biyu uku yahada dukka yaga basuyi masa daidai ba. Wani sashe na zuciyarsa ya soma zugashi da
"Ta yaya kana tsaye qaramar yarinya me qarancin shekaru zata nemi raina maka hankali?".
Ya samu kansa da kansa da tuhumar kansa tare da ganin tsananin baike da wallensa. Wannan tunanin kadai ya qara masa qaimi,ya taka qafafunsa cikin azama da qwarin gwiwa ya soma rufa mata baya lokacin da takeji a ranta ta kammala siyan duk wani abu da suke da buqata ita da 'yan uwanta,wanann ya sanya ta nufi gurin biyan kudin kai tsaye
"Inda zan baka shawara......zaifi kyau ka koma ka tafi sabgaka...."
"Saboda ke kike nema na bani ke nemanki ba?,saboda nine mai laifi bake bace?" Hankali kwance ta maqale kafada tana sakin siririn murmushi
"A'aha.....ba don dukka wadannan dalilan bane suka sanya ni na baka wannan shawarar ba......na baka ita ne don gudun kada ALLURA TA TONO GARMA"
"Ni dake zanga wanda allurarsa zata tono garma......"
"Ba laifilaifi malam naseer....." Abinda tace dashi kenan tana ci gaba da tattaki a bayanta. Yau yanason ganin qarshen gudun ruwanta......yanason yasan ita din wace?......da waye take tare?,su waye suka dauki nauyinta?.
Waye ya turota?,maqarqashiya ce ko kuma hadin baki?.
Hakanan yaci gaba da rufa mata baya tamkar me tsaron lafiyarta ko wanda aka bashi aikin kula da ita. Har cikin zuciyarsa yakejin yau zai nuna mata shi waye,zai kuma tabbatar mata tayi mahaukacin gangancin kuskure data shiga hanyarsa.
Mutum biyu suka samu ana lissafa kayansu jikin qaramar na'urar dake da alhakin qididdige fitar kaya cikin katafaren shagon.
A hankali ta tsaya daga bayan matar wadda bata iya ganin ainihin fuskarta,saidai shigar atamfar chiganvy gold mix match da wani irin danyen lafiyayyen lace da aka yiwa qawataccen dinkin buba da zani ya fito da kamalarta da kuma cikar siffarta. Tsaye yake daga gefanta,matashin da duka duka shekarunsa ba zasu haura ashirin da takwas ba. Ya bata dukka hankalinsa yana sauraren maganar da takeyi dashi cikin muryarta dake bayyanar da tsantsar kamalarta da cikakkiyar nutsuwar ruhi data halitta. Yanayin yadda ya rusuna ya bata hankalinsa yana saurarenta kadai zai bayyana maka zallar ladabi da kuma ganin girmanta da yakeyi,akwai kuma tag idan ka lura sosai daga gaban aljihunsa dake bayyanar da cewa shi din ma'aikaci ne a wani guri na daban.
Mai matsakaicin tsaho ce,hakanan me jiki ce saidai ba qiba me yawa cancan ba,ta lullube saman kanta da 4D Vail me asalin kyau da aka zubawa duwatsu masu daraja akayi adon jiki dasu.
Sassanyan qamshinta ya dinga tasowa a hankali daga jikinta zuwa hancin sabreen dake tsaye daga bayanta tana kallon tulin kayan siyayyar da aketa jera mata cikin ledar dake dauke da tambarin store din.
Hannunta dake dauke da wasu kyawawan banguls masu sheqi ta miqawa ma'aikacin gurin tana cewa
"Bansan me yasa suke son mu'amala da wannan katin bankin ba,duk sun lalace da lamarin cashless" Murmushi ma'aikacin ya saki cikin tsananin girmamawa
"To ai hajiya yafi sauqin sha'ani ne" Kai ta gyada a hankali tana furta
"To Allah ya kyauta". A nutse ta maida dubanta ga saurayin,tun kafin tace wani abu ya sake matsowa a ladabce yana bata hankalinsa
"Ka kiramin wancan yawalen da kuma wancan acicin suzo mu wuce kafin rana ta sake dagawa"
"Okay to in sha Allah" Ya amsa mata yana zaro wayarsa daga gaban rigarsa,yayin da ta fara takawa cikin nutsuwa tana ficewa daga gurin hadi da gyara yafen mayafinta dake qoqarin zamewa.
Wucewar tata ya bawa sabreen damar matsowa gaba don a lissafa mata nata kayan
"Ji mana.......zaki dawomin da duk abinda kika san kin sace ko kuma saimun dangana da hukuma?" Hannayenta ta goye a qirjinta tana kallon qofa yadda mutane ki shige da ficensu hankali kwance. Yana da ban mamaki......saidai ita din ta fishi abun mamaki. Inda yasan meta taka a kansa......inda tasan cewa kafataninsa.....zahirinsa da badininsa a tafin hannunta yake da baiyi gigin matsawa rayuwarta ba har ya matso gareta har haka ba.
A nutse ta waiwayo ta zube masa farare tas din idanunta masu matuqar jan hankali da fusgar tunanin me tunani
"Kana sha'awar yin gaba da gaba da hukumar ne?" Ta masa tambayar idanunta a tsaye car tsakiyar nashi. Idan ya kira kansa gogaggen cikin duniya baiyi qarya ba.....muddin kuwa ya kasance hakan yana ganin mugun ganganci ne zaiyi ya gaza samun fikirar karantar mutum daga yanayin kallo zuwa lafuzan bakinsa ba.......
"Kina tunanin abune me wahala a gareni?" Ya amsa mata yana mamakin yadda wannan mugun kwarjinin nata yake taka masa burki,kaifin idanunta ke hanashi daukan mataki tare da aiwatar da abinda yayi niyya.......abinda zuciyarsa ke shawartarsa.
"Ko daya....daidai ne kuma" Ta amsa masa tana dauke duba da hankalinta daga kanshi tana maidawa ga ma'aikacin wanda ya kammala lissafin yana gaya mata adadin abinda zata biya.
"Okay" Ta furta hankali kwance tana maida dubanta ga daya daga cikin ma'aikatan dake taimakawa da wadanda sukayi siyayya me yawa kamarta
"Ko zaka fitamin dasu gate na biyu?"
"Okay hajiya" Ya fada yana ajjiye qaramar calculator dake hannunsa yana qarasowa gurin tare da jira a gama sanya dukka kayan cikin leda.
Sake Waiwayowa tayi gareshi karo na biyu. Kallon da tayi masa ta fahimci yakai matakin qarshe a iya haqurinsa
"Malam naseer......ka shirya biyan duka bill na siyayyar sabreen ko kuwa tunda kai ka kawo qafafunka duk da gargadinka da tayi?"
"Sabreen?" Ya maimaita sunan yana kallon idanunta. Kiran sunan sabreen da tayi a maimakon basma shi ya batar masa da tunani cikin taqi qanqani.
"Zai biya duka bill din.....na gode sosai" Ta fadiwa ma'aikacin
"Naga uban wanda zai sakani biyan kudin nan......na fahimci na sakar miki fa da yawa" Ya furta da zafi sannan a zafafe ya biyo bayanta. Ya tsammaci zata nemi guduwa ko ta gudu dinma,amma ga tarin mamakinsa tun bai qarasa isowa gareta ba taja cak ta tsaya tana sauraron isowarsa.
"Ka samu aminci game da haramtattun kayanka da aka aiko maka dasu ta cikin jirgin ruwan dake tsakanin River Benue da riba niger?.......ko kuma ka shirya aci kasuwar wannan sirrin da jami'an tsaron dake neman kayan tamkar yadda mutuwa ke neman ruhi?".
Kamar wanda aka sanyawa sasari akan tsaida haka yaja wani wawan burki. Kallonta yakeyi da madaukakin mamaki. Wanne irin hadari ne da ita har haka?. Wanne nisan ji da gani ne da ita?,nisan binciken da ya bata damar gano birnannen sirrinsa da ko matarsa da suke kwana daki daya su tashi daki daya bata sani ba?.
"Ka biyasu kudin siyayyarsu duk yadda suka buqata,na barka lafiya Alhaji Naseer" Ta qarashe maganar tana takawa hankali kwance tana fita kwata kwata daga wajen.
"Malam qaraso ka bada kudin......ta atm ne ko cash zaka bada?" Muryar ma'aikacin ta katseshi daga bin burbushin hanyar data wuce da kallo ya juyo zuwa wajen biyan kudin yana sauke wani irin gauron numfashi me nauyi da zafi cikin tsananin mamaki da tsoro.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
PAGE 21
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
____________________________
Sanda take sallamewa saita samu kanta da zama sosai a inda ta idar da sallar tana irga tasbihi da yatsun hannunta,yayin da kunnuwanta kadan kadan ke jiye mata tasbihin matar dake yinsa can qasa qasa,saidai lokaci lokaci yana qwacewa ya fito,har zuwa sannan bata waiwaya ko sau daya ta kalli fuskarta ba,amma daddadan turarenta bai fasa silalowa zuwa cikin hancinta ba.
Wayarta ta matsa haske ya bayyana ta duba lokaci. Tasan ko busari bai iso ba to dab yake da isowar,ta maida wayar ta ajiye tana kallon sararin cikin masallacin da babu kowa saisu uku. Daidai sanda zata dauke idanunta dai dai sannan taji matar dake gefan nata taja wani irin qaqqarfan salati numfashinta yana yayyankewa.
A tsorace ta waiwaya gefan damanta... Hannuwanta dukka biyun na tallafe da qirjinta,tana kuma daga kanta sama tare da qoqarin maimaita
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Saidai tana kakkamota ne da qyar saboda yadda numfashin yake son qwace mata.
Da hanzari ta miqe,hanzarin daya sanyata cilli da wayarta dake saman cinyarta. Jikinta dukka yana rawa a gaggauce ta matsa jikin matar
"Lafiya?,me yake faruwa?" Ta furta cikin matuqar tsoro da kuma rudanin ganin yadda take kaman shirin rasa numfashinta.
Bata iya amsa mata ba,wannan ya sanya sabreen zama sosai ta tallafeta da kyau zuwa jikinta tana sake maimaita tambayarta a rude
"Ina ganin kaman asthma attack ne" Mace guda dayan data rage a cikin masallacin ta furta bayan ta iso wajen itama tana dubanta
"Asthma?" Sabreen ta furta a gigice tana jin wani abu yana dukan zuciyarta. Shine ciwo guda daya da kullum taji sunansa sai zuciyarta ya tsinke,ciwo qwaya dayan da kullum takewa mummunan kallo,ciwo guda dayan da yayi silar wasu jigo na rayuwarta,har ila yau ciwo qwaya daya da yake wujijjiga rayuwarsu.
Da sauri ta finciko jakarta bayan da tunaninta ya dawo,ta zugeta da hannu daya daya hannun yana tallafe da ita,ta daga jakar ta zazzage duka tarkacen dake ciki,cikin matuqar sa'a ta hangi inhaler dihta.
A gaggauce ta dauka ta kara mata,hannuwan matar dukka rawa suke sanda ta dora nata hannun saman na sabreen kamar tana son tayata matsa inhaler din,kamar tanason nuna mata tsananin buqatarta da takeyi.
Cikin mintuna qalilan ta fara samuwa,saidai har yanxun bata daidaita yadda ya kamata ace ta daidaita din ba. Oily eyes dinta sun cika taf da qwalla
"Kamar asibiti tafi buqatar a kaita" Ta kasa haquri har sai da bakinta ya furta hakan
"Zaifi kyau dai gaskiya don da alama tana buqatar iska sosai".
Dai dai sannan wayarta data watsar ta dauki ringing. Matar ce ta matsa ta miqo mata,ta sanya hannu ta karba tana fadin
" Na gode" Tana duba me kiran.
Busari ne,ta latse wayar tana karawa a kunnenta
"Na qaraso,ina dab da bakin masallacin"
"Ka karba kayana wajen me gadi,gani nan fitowa asibiti zamu wuce" Bata tsaya sauraren abinda zai fada ba ta katse kiran.
Idanunta ta mayar saman fuskar matar. Wani abu taji ya taba zuciyarta,sai takejin kamar umminta ce ta dawo,sai takejin tamkar lokacin data rasa umminta. A duk sanda take mutum me dauke da irin ciwon tsananin tausayinsa yake kamata,duk da itama abar tausayin ce. Duk sanda taga babbar kaman haka yana fafutuka da wannan ciwon sai ta dinga tuna umminta.
Su biyun suka tallafeta don taji qwarin jikinta,suna takowa a hankali da ita har suka fito zuwa inda Kekenapep din yake
"Zan samu face mask a wajenka?" Ta tambayi busari.
"Eh hajiya" Ya amsa mata da sauri yana bude aljihun motar ya fidda shi sabo fil ya bata.
A kusa da ita ta zauna tana riqe da face mask din,saita sauke idanunta qasa tana jujjuyashi.
"Zan saka miki wannan saboda iskan mota,motan bana gida bane". Idanunta saman fuskar yarinyar,har zuciyarta tana jin qauna da jinjina taimakonta a kanta,ta lura tana d'anjin wani nauyi da kuma rashin sakewa. Qaramar yarinya haka me zuciyar taimako?,sai abun ya qayatar da ita.
Mintuna ashirin daidai suka qarasa private hospital din,wanda a nan file nata dana qannenta dukka yake. Tuntuntuni ta sallama asibitin gwamnati,yana daya daga cikin muhallan da suka samarwa rayuwarta gibi,yana daya daga cikin guraren da suka dasa qaton tarihi a rayuwarta,suka kuma ajiye mata wani tabo na har abada,shi ya sanya daga sanda ta samu dama ta nisanta kanta da dukkaninsu daga asibitin gwamnati.
Private hospital ne daya amsa sunanshi,babu nau'in wata kulawa da mara lafiya baya samunta,saidai kuma kudi ne zasu fita sosai daga aljihun majinyaci ko ahalinsa.
Private room suka bata,cikin mintuna goma sha biyar kacal suka bata dukkan taimakon daya dace,bata samu nutsuwa ba sai da suka shafe awa guda taga bacci sosai ya dauketa tana sauke numfashin a hankali ta cikin oxygen din da suka maqala mata saboda yadda taso galabaita sosai.
Zama tayi kawai gabanta bayan taja kujera,ta maqale hannunta a qirji bayan ta zube idanunta a kanta tana dawo da bayanan da likita yayi mata a kanta.
"Ta samu mummunan attack ne,tana samun kulawa sosai to amma kuma kaman yanayi ya nuna ba'a kiyaye wasu dokoki na masu ciwon,sannan kuskure ne ta dinga fita hakanan ba tare da inhaler ko wani a kusa da ita ba".
Idanunta ta qanqance sosai tana ci gaba da nazarin maganganunsa. Hakanan sai taji ranta yayi matuqar baci,indai har mace me irin wannan shekarun bata samu kulawa ba sai yaushe?,indai har ba za'a kula da dokokin da aka bata ba meye amfanin makusantanta?. Dukkan alamu sun nuna,tun daga suturar jikinta da komai nata ma cikin wadata da sukunin rayuwa take ainun,to meye zai hana su su bata kulawa su ahalin nata?.
Idan zata iya tunawa mutum daya ne ta gansu a tare a tsaye cikin store din,har tana bada umarnin a kira mata wani data kira a cici da kuma yawale. Yawonsu kenan yafi musu kasancewa da ita?,yanzu haka fa mahaifiyarsu ce amma sun gwammaci tafiya yawo akan su bata kulawa?.
Iska me zafi ta sake fesarwa ranta yana sake tunzura musamman bayan data duba agogon hannunta. Aqalla awa daya harda rabi da barowarsu store din amma har yanxun basu biyo address na asibitin data barwa wancan matar sun biyo bayan baiwar Allahn ba?. Sake juya wayarta tayi su huda suna fado mata a rai. Ta tabbatar zuwa yanzun sun dawo gida,suna can kuma zaune su daya a daki. Karon farko da taji kaman ya kamata ta siya waya ko qwaya daya ce ta ajiye cikin dakin saboda lalura irin haka,ko ba komai ba zata barsu cikin zulumi ba,zata kira taji lafiyarsu suma suji lafiyarta,duk kuwa da cewa komai runtsi a gida takeyin magrib.
Daidai sanda tunaninta yakai nan taji an murda handle na qofar. Kyakkyawan matashin ne ya fara bayyana. Dogo me matsakaicin haske. Kai tsaye idan kace masa kyakkyawa bakayi kuskure ba,yana da cikakkiyar suma me santsi tun daga kansa zuwa habarsa.
Yana sanye da dakakkiyar shaddar getzner Neautaral color daketa yauqi da sheqi. Yanayin dinkin da aka yiwa shaddar yayi masifar dacewa da structure na jikinsa. Dinkin zamani dake nuna zallar gogewa da wadatar arziqi na wanda suturar ke kwance a jikinsa. Yadda shaddar ke walqiya hakanan hular kansa,wadda koda ba'a gaya maka kudinta ba zakasan cewa bada qaramin zare aka saqata ba. Qafafun sanye cikin takalmin Batozzi,hakanan cikin qasa da second biyar dakin ya gauraye da sassanyan qamshin turarensa.
"Hamma mun sameta,gata tana bacci" Ya furta da kwantacciyar muryarsa da alama kuma yana magana ne da wani a wayar dake manne a kunnensa,dukka hankalinsa da idanuwansa suna kan matar dake kwance cikin mazari yana d'okin isa gareta.
"Okay hamma......in sha Allah" Ya sake fadi da sauri sannan ya jefa wayar a aljihunsa yana isa inda take kwancen ba tare daya damu ya kashe wayar ba.
Rusunawa yayi sosai a gabanta yana riqe da hannunta da dukka hannayensa biyun. Yayi wani irin laushi,don idan ka kalli hannunsa da kyau kana iya ganin yadda suke danyin rawa.
Dauke dubanta tayi daga kansa haushinsa yana saukar mata,saita maida kallonta akan wanda suka shigo din tare. Shine dai wanda ta gansu cikin store din tare wanda ta bari ya biya kudin siyayyar da tayi.
"Kamar kece kika kawota ko?" Ya fadi saboda hada idanu da sukayi. Maganar tashi taja hankalinsa,yadan sassauta riqon da ya yiwa mara lafiyan ya kuma waiwayo da dukka nasa idanun yana dubansu,don shi sam sam bai ma lura da kowa ba a wajen.
Kamar yayi mata susa ne a inda yake mata qaiqayi,sai ta miqe a nutse tana saqala Jakarta a kafadarta,haushinsu yana sake turniqeta
"Eh nice bayan kun yasar da ita kun kama gabanku ba?,waishin kunsan muhimmancinta kuwa?,kunsan yadda ciwonta ke buqatar a dinga yawan kulawa da ita musamman ita da shekarunta suka fara yawa?.
Ji yayi maganganunta sunyi girma ainun,tasan wace ita din a wajensu har da zataga gazawa da kasawarsu?. Saidai bai datseta ba saboda yadda yaga hawaye suna cika idanunta
"Mutane da yawa basusan muhimmancin iyaye ba sai sanda suka rasasu......amma ku sani cewa......yadda suka baku kulawa a sanda bakusan muhimmancin rayuwa ba.....ba komai bane don kun basu kulawa a sanda sukasan muhimmancin nasu rayuwar......ba kowa a kusa da ita.....ba inhaler.....yanzu inda numfashinta ya katse fa?" Ta qarashe fada adan tsawace hawayen na fara gangarowa ta idonta qwaya daya,sai tayi hanzarin kauda kanta gefe ta dauke hawayen da yatsanta. Su kadai sukasan yanayin da suke shiga idan ciwon ya tasar musu shi yasa babu me fahimtar abun sai wanda ke cikin yanayin
"Kuji tsoron Allah ku kula da ita yadda ya dace,don yadda muke amana a hannun iyaye haka suma amana ne a hannunmu,kuma Allah zai tambayemu game da yadda muka kula da tsufansu" Tana kaiwa nan ta soma takawa tana ficewa daga dakin.
Gaba daya mamakinta ya cikashi,yadda take haqiqancewa ba tare da tasan komai a kansu ba. Mahaifiyarsa itace rauninsa har abada.....wani abu guda daya me matuqar tsada da muhimmancin da ba madadinta. Har ta fice ya kasa tsaidata kaman yadda yaso har sai data bacewa ganinsu.
"Bita ka tsaidata......a qalla ko godiya ya kamata muyi mata,sannan kuma muji yadda za'a maida mata kudaden data kashe tunda na samu an biya bill na komai"
"Okay" Ya furta a girmame yana juyawa ya fice a dakin.
Kamar wayar dake aljihunsa yaji yana motsi,ya dafe wayar sai kuma ya sanya hannu ya fiddota da sauri. Mamaki ya kamashi,ya akayi bai kashe wayar ba. Hamman ne har yanzu akan layi,duka mintunan da sukayin wayar na a kunne,sai ya maida wayar kunnensa
"Waye yake mata fada saman kai?" Ya furta nutse
"Wanda ta kawota ne daga can store din"
"Don ta kawotan take ma mutane fada?" Ya furta adan harzuqe
"No hamma...." Ya fadi da sauri. Numfashi yaja yana ware idanunsa sosai
"Stop......banason a sake mata hayaniya a wajen nan....if not ran kowa zai baci"
"In sha Allah hamma"
"Idan ta farka ta dawo daidai give me a call"
"Done" Ya fada a taqaice kafin ya yanke masa waya,yana gama fadin kuwa yaji qit ya gintse wayar,saiya cireta daga kunnensa yana girgiza kai.
"Hamma.....hamma" Ya maimaita sau biyu.
Koda cewa tayi fada cikin yanke hukunci akan abinda bata sani ba.....bata da yaqini amma shi baiga laifinta ba,ya mata uzuri......hasalima ta burgeshi qwarai,dukkan alamu yana nuna tasan darajar dan adam ne,sai ya maida hankalinsa akanta yana duba shiga da fitar numfashinta.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 22
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
____________________________
Batasan me yasa ba,batasan dalilin da ya sanyata takejin bacin rai sosai akan abun ba. Ta dinga fidda numfashi me dumi a hankali daga baki zuwa hancinta. Cikin nutsatsen takun nan nata take nufar inda tabar busari yana jiranta. Takun da yayi matuqar tafiya da hankali da tunaninsa baya ga zubin mamallakin takun.
"Wai har yanzu akwai irin mata masu wannan ajin?" Ya furta qasa qasa ba tare da yasan a waje yayi maganar ba,tana ta'allaqa dubansa a kanta,yana jin tana tafiya da gaba daya kuzari tunaninsa dama hankalinsa gaba daya.
Tamkar an zungureshi ko kuma anyi masa qaimi,sai ya saka hannu da wani irin hanzari yana bude murfin motar. Sam gaba daya ya manta da dalilin daya kawosu asibitin,ya kuma manta ma da waye yake tare,burinsa guda daya tal! A yanzu,ya samu isa gareta,yakuma samu daman yin magana da ita.
Sallamar tashi ta ratsa kunnenta a sanda take dab da isa wajen da Kekenapep din yake. Ta lumshe idanunta a nutse tana riqe masaqalin jakarta da kyau. Dama tasan hakan zata iya faruwa duba,zaiyi wahala a kallon farko da tayi masa ya iya tsallake halaye da kuma dabi'uj data hanga kai tsaye daga gareshi.
"Assalamu alaikum.....don Allah....." Ya katse maganar tashi da kan kanshi lokacin da yasha gabanta idanunsu suka gauraya waje daya.
Wani kwarjini na musamman,wani yanayi ya tsarga masa irin wanda bai taba jin irinsa ba. Nashi idanun ya janye a hankali yana qoqarin daidaita kansa tare da zallar mamaki yana kuma tambayar kansa
"Meye haka?,ita din wace?". Baisan iya adadin kalar matan daya gani ba tun da ya fara zama cikakken namiji zuwa yau. Baisan adadin matan da yayi mu'amala dasu ba daga jinsin yare daban daban,amma yau daya wata mace da baya tunanin ta rufa shekara ashirin da biyar a duniya na neman yi masa kwarjini?.
"Lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsuke fuskarta tare da sake bada tazara tsakaninsu. Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi,sai ya sake mata murmushi hadi da gyara tsaiwarsa sosai a gabanta,yana jin ba wata mace da zata iya kaucewa tarkonsa muddin ya d'ana shi.
"Ba lafiya ba......maganar gaskiya kenan.......akwai gagarumin tashin hankali" A mamakance take duba fuskarsa tana yamutse tata tare da qoqarin sakeyi masa sabon karatun da baisan tana yi ba
"Amma fa a zuciyata" Ya qarashe maganar yana dafe qirjinsa.
Numfashi taja sosai har cikin huhunta sannan ta fesar tana kauda kanta gefe hadi da juya qwayoyin idanunta. Ba shine mutum na farko data taba gamuwa dashi me irin wannan salon ba,don haka tafiyar dashi bazai bata wahala ba.
Dukkan wani d'a namiji da zai ratso rayuwarta tayi imanin QADDARARSA ce a nan.......da kuma zallar tsautsayi. Mafi rinjaye daga cikinsu kuma SON RAI da SON ZUKATA.
Ba kasafai ta fiya bada kai ta farat daya ba,koda ta tsara amsarka,don tuni ta fahimci duk wani abu da akeson yayi daraja.....kar a bari samuwarsa ta zama ta sauqi. Don haka ta soma tattaki da zummar kubcewa daga gabansa.
A gaggauce ya sake tare mata gaba yana dubanta cikin marairaicewa
"Ranki ya dade.......na tabbatar girmanki yafi gaban a tsaidaki a hanya....to amma muddin na barki kika wuce din nayi imanin sa'ata ta rayuwa ce ta kubcemin gaba dayanta......ki tallafeni ki sammin minti uku kacal" Ya furta yana nuna yatsunsa guda ukun.
Juyowa ta sakeyi a karo na uku tana kallonsa. Ya fiya zaqin baki da yawa,maza irinsa suna da wani hali da dabia da tuni ta gama karatunsa. Tabbas akwai wani abu tattare dashi da wata qila take nema......tana hasashen yiwuwar samun wata qaruwa me girman gaske. Taga irinsa ba daya ba.....ba biyu ba....ba uku ba,har ba zata iya tantance adadi ba.
Duk da wannan hasashen amma bata yarda ta nuna masa komai ba. Sai ta sake kau da kanta tana yamutsa fuska
"Matsawarka daga hanyata kamar zaifi zame maka alkhairi akan ci gaba da tsaiwar......ina da tarin abubuwa a gabana....."
"Bansan ko me ke jiranki ba......amma na tabbatar koda baikai wannan tsaiwar tamu alkhairi ba bazai wuceta ba" Ya fadi a zaqe da fatan samun nasara
"Na roqeki kada ki watsan qasa a idanu,ki wofantar da wannan kyakkyawar damar a garemu gaba daya" Ya fadi yana marairaicewa tare da miqa mata wayar hannunsa yana kasheta da idanu gami da karyar da wuya da raunanar da idanun nasa.
A nutse ta sauke kallonta akan wayar ta kalla. Tsaleliyar iPhone 16 wadda kana dubanta zakasan bata wani jima da baro dumin kwalin da aka qerata ba. A yangance ta dauke kanta daga kai ta sake maidawa gefanta bayan.
Wani numfashi ya fusga da qyar bayan ya gama sauraren jerin lambar wayarta data karanto masa. Sautin muryar nata yana masa wani irin amsa kuwwa a kunnensa. Karon farko daya yadda cewa muryoyin wasu matan kadai suna iya haddasa fitina a zukata da gangar jikkunan maza. Sai yakejin yana sake zurfi ason ya kasance a tare da ita
"Sai nakega kaman girma da martabarki ya dara kihau napep.....da zai yiwu da kin sadaukarmin da wannan tsadajjen lokacin na saukeki a gida....." Yana ajewa tana daga masa hannunta,sannan ta fara takawa tana wucewa cikin abun hawan da busari ke jiranta.
Har ya bawa napep din wuta suka fice daga harabar asibitin yana tsaye a gurin. Sai daya tabbatar sun qwacewa ganinsa sannan ya buga qafarshi yana yarfar da hannunsa,wani shu'umin murmushi yana kubce masa. Ba shakka ita din ME ZAFI ce,ta kuma cancanci dukkan wannan dagawar da kuma jan ajin. Yana da makamai a hannunsa masu tarin yawan da zai iya yaqar zuciyarta yakuma yi nasara ba shakka ko kokwanto. Makami guda daya da dukkan namijin daya mallakeshi yake iya sanya kaza ta kwanta ta yanka masa kanta ta gasa ta kuma kawo kanta da kanta har inda yake don biyan buqatar ranshi.
Iya wassafa samuwar nasara kadai a gareshi ya sanya murmushi ya subuce masa. Ya sake buga qafa yana wassafa irin yadda zai tsikari rayuwarsa da tsinke yadda ya kamata
"Dole na qarawa kaina kusanci da dukkan qofofin da zasu budemin manya manyan qofofin taskokin da zan miki hidima dasu don mallakar muradina" Ya furta a sarari yana qanqance idanu,muradinsa yana sake ninkuwa,burikansa suna sake fadada.
Daidai qofar gidan nasu busari ya ajiiyeta bayan ya fiddo mata dukan kayan daga cikin motar. Cikin farfajiyar gidan ya ajiiyeta mata kayan sannan ya juya yana komawa ciki.
Tsaye tayi a farfajiyar gidan da iskar la'asar ke kai kawo. Ba wadatar yara sam,wanda koda ace akwai wadatar nasu tasan cewa ba kowa ne a cikinsu ke aikuwa ba. Kayan sun mata nauyin da ba zata iya dauka ba,tana tsaka da wanna tunanin ta hangi fitowarfitowar nadra,haneefa na biye da ita.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 23
___________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
__________________________
Nadra,haneefa na biye da ita
Dukansu suka watsar da abinda ke hannunsu sannan suka nufota. Fuskokin dauke da madaukakiyar fara'a wadda har tsakiyar zukatansu ta ratsa. Ita daya ce HASKE GIDANSU.....ita daya ce FARINCIKINSU hakanan ita kadai ce BAQINCIKINSU. Rashinta a kusa dasu yakan debe dukkan wata walwala da sakewa tasu,duk da tarin jamaar dake rayuwa a gidan amma duk sanda bata nan din suna jin gidan kamar babu kowa a ciki saisu.
Cikin jikinta ta rungumesu kaman yadda ta saba,sannan nadra din ta soma jan daya daga cikin ledojin. Duqawa haneefa tayi itama zata dauki guda daya nadra din ta tsaidata
"Bafa zaki iya dauka ba" Cak ta tsaya tana turo baki
"Anty wai da gaske bazan iya ba?" Murmushi ya qwace mata saboda hangen farincikin da tayi daga idanuwansu.
"Zaki iya auta" Ta furta tana bude ledar,jakankunan maggi da suka qarawa ledar nauyi ta ajjiye a gefe sannan ta daure mata ledar tana cewa
"Bismillah auta aiba raguwa bace" Hakan ya faranta mata rai,ta sukunya ta dauki ledar tana cewa
"Ita yaaya nadra kullun komai sai tace bazan iya ba,batasan na fita qarfi ba" Daga sabreen din har nadra data riga tayi gaba suka saki dariya.
Idonta a kansu har suka mata nisa sannan ta tsugunna a nutse ta kwashe maginta,ta fara takawa tana binsu zuwa Qofar da zata sadasu da babban tsakar gidan nasu. Zuciyarta a karye tana hangen haneefa daga nesa. Ta sake sakin boyayyen murmushi,akwai jarumta me yawa dangane da yarinyar,da alama zuciyarta dakakkiya ce kuma a tsaye take.
Dab da zata shiga din su kuma suna yunqurin fitowa su biyu. A hankali taja da baya tana basu hanya bayan ta sauke idanunta qasa,saidai duk da hakan da tayi bai sanya ta tsira daga garesu ba.
Qasan ranta akwai haushi takaici da kuma fushin rashin samun nasarar da batayi ba a safiyar dazu.
"Ke ya kamata mu bawa hanya ta wuce ai......gagara" Ta furta tana qanqance idanu idanun nata fes akan Fuskarta da kuma abinda ta riqo a hannayenta.
A hankali daada dake tsaye daga bayan bibo din ta gewayo ta gefanta tana cewa
"Muje mana bibo,yamma tana sakeyi"
"K'nnnn,gaskiya dai,fitar dare ai 'yan kwalta" Ta fada tana zakudawa tare da bin bayan daada bayan ta waiwayo ta ajewa sabreen wani kallo.
Da kallon itama ta bisu,sam ko kadan daada bata nuna ta santa ko tasan da zamanta......nata da sauqi don kome za'ayi a kansu baka taba jin ta tofa nata........batasan wanne matsayi zata aje daada ba a kanta cikin gidan,ta bibo kuwa fitacciya ce ainun,muddin magana ce a kansu,Ala cuta ala magani har abada bare ya fiye mata su,koda kuwa wanne irin nau'in alkhairi zasuyi mata ko zasu kowa cikin gidan.
Ajiyar zuciya ta saki tana ci gaba da kutsa kanta cikin gidan tana ta qoqarin kauda abinda takeji a yau yana taso mata qasan zuciyarta. Abune da take ganin bai kamata ta damu ba......ita din dai tasan kanta,ta yarda da kanta,sannan tasan wacece ita?,to me ya rage?,me take nema da shaidar mutumin yau?,mutanen dake rayuwar a DUNIYARta sam basu cancanci ta basu damuwarta ko tayi yunqurin gamsar dasu game da WACECE ITA?.
Da sallama a bakinta ta sanya qafafunta cikin falon nasu,komai a tsaftace a kuma tsare,madaidaiciyar iska me dadi tana kai kawo tsakanin falon ta wutar sola dake maqale a dakin.
Sanda take zubewa saman kujera daidai lokacin haneefa ke isowa gabanta da school bag dinta da wani.littafinta a hannu
"Anty munyi C.A,a cikin talatin na samu ashirin da takwas......sannan an bamu assig....."
"Kai haneefa haba" Nadra ta fasa tana hade fuska. Murmushi ta saki,saita dagawa nadra hannu
"Qyaleta,zo.nan auta" Ta kirata sanda huda ke qarasowa ta aje mata ruwan pure water me sanyi guda biyu
"Ki aje komai sai zuwa anjima zan duba,duka yau tare zamuyi assignment din kinji?" Kai ta daga tana murna ta cilla da gudu ta koma bedroom dinsu da jakar.
Sai data bula ruwan sannan ta kalli huda
"Me yasa baku wuce islamiyya ba?" Gyara zamanta kadan tayi sannan tace
"Jiran dawowarki mukeyi" Rabi tasha ruwan ta ajjiye tana sake karantar wani yanayi na daban daga huda din
"Sai na dawo sannan zakuje Islamiyya huda?,yaushe aka fara wannan tsarin a dakin nan?" Tadan furta a zafafe tana dubanta. Qasa da kant huda din tayi,ba kasafai take ganin fushi ko fada dava Fuskarta ba,to amma duk sanda tayi din ya tabbata laifi sukayi mata babba.
"Kiyi haquri.na tsaya dora abinci ne" Sassautowa tayi kadan tana sauke boyayyen numfashi. Bata qaunar abinda zai zaunar dasu cikin gidan ko kadan ballantana idanuwa ko kunnuwansu suji ko suga abinda rayuka zasu baci. Hakanan koda wasa bata qaunar suyi wasa da makaranta. Tana jin ciwo idan ta tuna iya inda matakin karatunta ya tsaya a shekaru ashirin da daya hudu da take dashi a duniya,wanda a yanzun kimanin shekaru hudu kenan rabonta da wata bawa wai makaranta.
"Ku shirya ku wuce,duk da lokaci ya fita amma baiyi nisa ba ai" Ta fadi tana duba agogon hannunta sannan ta fara zareshi daga hannunta.
Tana zaune dukansu suka gama shiryawa cikin fari qal din uniform da baqar doguwar riga daga sama. Hankalinta bai dawo daidai ba sai data tabbatar sun fita a gidan.
Kai tsaye ta rage kayan jikinta ta zura sassauqar riga sannan ta wuce kitchen din dake falon tana duba girkin da huda ta fara yi.
Komai yayi daidai,dole ta sanya huda ta koyi girki tun batakai minzali ba. Tana fita ta bar mata nadra da haneefa,tun bata san ya zata kula dasu ba har ta koya. Ko a yanzun idan huda tayi girki,itama tayi sai na huda ya dara nata.
Sai data kammale komai sannan ta daura alwalar sallar la'asar,sanda ta idar idanuwanta sun fara nauyi,tana zaune daga saman abun sallar tana dan murxa idanunta. Ba baccin take buqatar yi ba a yanzu,tana son magana da jib ne. A yawancin lokuta a irin wannan lokacinne take samun tattauna maganganu ire iren wadannan,sam bata yarda tayi komai bisa idanunsu,bata taba bari ta rab'a lamarin rayuwarsu da nata rayuwar,komai tana tsaidashi ne iya muhallinsa.
Hakanan tana hamma ta miqe ta koma daki. Locker gefan gadonta ta jawo,ta fidda madaidaiciyar baqar jaka dake dauke da mini laptop dinta,sannan ta zaro wayarta dake cikin jaka ta sake dawowa cikin falon.
Kalmomin sirri ta sanya ta bude laptop din,sanna ta maida hankalinta akan wayarta tana barin laptop din ta daidaita. Maadanar lambobi ta shiga bincikawa har ta kawo kan sunanshi,ta danna masa kira tana aza idanunta akan screen na laptop din tana duban hoton daya mamaye fuskarta. Hoto ne da bata gajiya da kallonsa,duk sanda ta dubi hoton sai taji kamar tana tare da ita,kamar zata kirayeta ta amsa,kamar zata iya jin kadan daga radadin da take fuskanta,kamar zata damqi hannunta su fuskanci wannan JUYAYAYAR DUNIYAR su kuma kutsa cikin birkitacciyar rayuwarta su kawo daidaito.
Daga wayar da akayi shi ya katse mata tunaninta,ta daidaita idanunta da suka fara zugi kadan kadan da alamun son tara ruwan hawaye
"Aikin jeeb ya taso?" Boyayyen murmushi ta saki tana gyada kai
"Sosai......ka zama kusa da na'urarka......inason sanin wayeshi"
"An gama" Ya fada a taqaice
"Aikin dazu fa?" Ta sake tambayarsa
"Adda ya zama tsohon tarihi......bashi ba......ko bankinsa basu isa susan ya akayi kudin sukayi fiffike ba bare inda suka sauka"
"Yayi" Ta amsa masa a taqaice tana sauke wayar daga kunnenta.
Sake duba bagaren kira tayi a nutse har ta iso number wayarsa. Ta tsaya kadan tana kallon numbers din. Daga yanayinsa da yanayin shigarsa ta tabbatar ba qaramin mutum bane. Amma ko daya batajishi koda a gefan zuciyarta bama bare a shiga wani batu na daban. Hasalima yadda yaso bata mata lokaci ne yafi bata haushi,kalaman bakinsa kuwa aqalla taji masu kamanceceniya dasu a bakin gomman maza......maza iri daban daban,masu mabanbantan halaye da dabi'u.
Tana jan system din kira yana sake shigowa. Ta dora zagayayyun idanunta ga fuskar wayar tare da zubawa numbers din idanu kamar me nazari. Batasan wadanne irin zukata suke dasu ba.......a sanda sukaso abu suna zamewa tamkar wadanda ba zukata a qirjinsu,tamkar wadanda hankulansu ke zamewa daga gangar jikinsu,idanuwansu da dukka kunnuwansu suna rufewa ruf izuwa ga cikar muradinsu.
Dukka layukan da tasan zasu zame mata damuwa ta ciresu kwanaki biyu kenan,ta kuma tabbatar akwai masu nemanta da yawa.
Qaramin tsaki taja ta saka hannu ta jawo wayar,ta daga tana karawa a kunnenta
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 24
____________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
____________________________
"Ranki ya dade.....girmanki ne ai" Idanunta ta lumshe sannan ta budesu,shima dai kaman sauran,gwanayen dadin baki da iya tsara mace,abinda basu da masaniya akai....ya zuwa yanzu babu wani d'a namiji da yake burgeta duk duniya. Sunan soyayya kawai da labarinta tana daukanshi a mazaunin wani wasa ne.....wasa da qwaqwalwa da wani salo na batawa kai lokaci.
Ya'aqoub,daya daga matasan mazan dake sharafinsu,kuma giyar soyayya da ta sha'awar sabreen suka yiwa qawanya. Daya daga cikin mazan da sukejin zasu iya kashe komai......zasu iya bada komai,hakanan zasu iya salwantar da komai saboda ita
"Ayimin afuwa nasan wataqila nazo da takura......ba wani abu nake bida ba illa a bani dama zan turo dan saqo da aike"
"Ka wuni lafiya?" Ta katseshi ya hanyar tambayar lafiyarsa. Wani boyayyen numfashi ya aje,daya daga cikin dabi'unta da suka banbanta dana sauran matan da ya sani wadanda suke rayuwa shigen tata......dabi'arta guda daya dake tsundumashi a kokwanto da tunanin WACECE ITA?,YADDA ZAHIRINTA YAKR HAKA BADININTA YAKE?.
Yana da tarin buqatu da yakeson gabatar mata dasu,saidai kwarjininta da wani irin shakkarta yakan daki zuciyarsa a duk sanda yayi yunqurin hakan. Ta sha bashi damar haduwa sama da damarmakin da take bawa kowa......hakan kuwa baya rasa nasaba da yadda yake kame kansa a gabanta
"Lafiya qalau.....saidai tsananin kewarki......na iso qasar nan da burin ki zama mutum ta farko da zan fara tozali da ita....... Amma inajin nauyin tambayar hakan don kada na aza miki abinda ranki baiso"
"Banayin abinda baniso......hakanan bana yin abinda zan takura" Ta fadi mishi kai tsaye kaman yadda halayyarta take.
"Na sani nadeeya" Ya amsa mata da karsashinsa,har sai da boyayyen murmushi ya kubce mata. NADEEYA shine stamp din ya'aqoub,kaman yadda muhseena yake stamp din MASHKUR,mashkur din da tayi imanin zuwa yanzun qila ya kusa zaucewa da rashin samunta a waya da bayayi. Shi kansa ya'aqoub din wata irin saa ya taka a sanda yayi katarin samun number wayarsa. Dashi da mashkur dukkansu ta hadu dasu ne a rana daya,saidai kuma a mabanbantan gurare da lokuta.
"Zaa yimin wannan alfarmar?" Ya tambayeta yana langabar da kansa tare da sassauta muryarsa da kyau
"Zan duba"
"Zuwa yaushe please......zuciyata a jigace take nadeeya.....i beg you karki sakamin lokaci da nisa....."
"Baka da damuwa" Ta sake bashi amsa a gajarce
"Dan saqo na yana iya isowa?"
"Sharada yahaya gusau road,najbil road" Ta fadi a nutse tana yanke kiran.
Wayar ya cire a kunnensa yana binta da kallo. Ya zaci inda yayi mata aike wancan karon wannan karon ma can za'a kai mata?. Iska ya furzar daga bakinsa,bata da wuyar canzawa tamkar waya hawainiya. Har yanzu bashi da wani yaqini ko tabbaci a kanta. Baisan komai a kanta ba banda suna da kamanninta. Yana da buqatar abubuwa masu yawa game da ita amma bata bashi dama ko qanqani a kanta ba.
"Allah yakai damo ga harawa" Ya fadi yana furzar da iska daga bakinsa. Ya miqe a hankali yana ture kyakkyawan mulmulallen table na glass dake gabansa cikin qawataccen falon nasa da ya tanada domin hutawarsa yana laluben number wayar babban yaronshi. Yanason saqon ya isa gareta da wuri,don yanason ya sanya qaimi ya matsa da kyau don samun kyakkyawan kusanci tare da ita.
A yadda ya ganta baiyi tsammanin za'a dauki wani dogon lokaci ba tare da ya samu abinda yakeso ba. Saidai duk sanda ya tuna yanayin jin kanta,miskilancinta da shariyarta,sai yaga eh.....ba abun mamaki bane,mata irinta daban Allah yake halittarsu.
Baki ta tabe tana ajjiye wayarta a gefe,sai kuma taja dan siririn tsaki tana sake bada duka hankalinta akan system din.
Folder da takanyi rubuce rubuce ta adana a duk sanda zuciyarta ta buqaci abokin hira ta shiga,ta budeta,sannan ta fara rubutun daga dukkan abinda taji tana da buqatar amayarwa.
Wata irin rayuwace da babu qawa ko aminiya......babu aboki ko amini......qawayenta sune qannenta da suka fito daga tsatso guda......saidai har kwanan gobe bata bari sun zame mata aminai ba.......saboda batason tunaninsu da hankulansu su gurbata ya zuwa wani tunani na daban. Tana jin itace dole.....kuma tilashin daukan alhakin komai yana a wuyanta.
Awa guda harda qarin wasu mintuna ta dauka kafin ringing na wayarta ya janye hankalinta. Ta dauke idanunta da suka dan sauya launi tana mayarwa kan wayartata,daidai sanda take iya jiyo hayaniya da ifce ifcen wasu daga cikin jikoki da yaran gidan. Bame son hayaniya bace sam,zata iya rayuwa cikin muhallin da babu motsin kowacce halitta sai ita......tana da wannan damar ta samarwa kanta irin wannan muhallin da kuma wannan rayuwar......amma qaqqarfan dalili guda daya tal zaya hanata kaiwa zuwa ga wannan burin nata,tna buqatar tsira da sauran burbushin MUTUNCINTA tana son ta sake tabbatarwa da kowanne me zargi abinda yake zargi a ransa yaji haka ne?,ko kuma ya sauya bigiren ra'ayinsa a kanta.
A nutse ta karanta sunan dake saman screen din,sai ta tattara dukka hankalinta akan kiran ta ture system din tana jingina sosai da makarin kujerar tata.
A nutse tayi mata sallama
"Wa'alaikumussalam" Aka amsa daga daya bangaren cikin matuqar nauyin jiki dana murya.
"Lafiya kike titi?" Sabreen din ta tambaya murya a sanyaye itama. Tana jin dukka wata gaba ta jikinta tana yin sanyi
"Alhamdulillah sabreen.....,saidai......"
"Aisha ko?,ayshatu?" Kai titi take jinjinawa tana qoqarin hadiye abinda yake taso mata. Saita kass cewa da sabreen din komai,bataso ta bijiro mata da abinda take da tabbacin itama yafi qarfinta......bataso ta bijiro mata da abinda zai hautsina nutsuwarta,duk kuwa da tarin qoqarinta.....sadaukarwa da tsaiwar dakanta akan yarinyar
"Titi ki fadamin me ya faru?" Ta sake jefa mata tambayar tana jin kamar ta tashi a daren ta iskesu a inda suke
"Ki nutsu sabreen.....Allah yana sane da halin da take ciki......kinyi iya yinki......kinyi kuma iya abinda zaki iya,mu barwa Allah komai"
"Titi ki fadamin!" Ta furta adan tsawace,tsawar ma da batasan ta yita ba
"Sabreen.....naira million takwas suke da buqata wajen aikinta" Wani qaramin jiri taji tana niyyar kayar da ita tana daga zaunen. Tayi luuu da idanunta tana son furta addu'a ko qwaya daya ce amma bakinta ya kasa lalubota.
"Tabbas titi akwai abinda kika boyemin......baya rabuwarmu wani abu ya biyo baya amma titi baki gayamin ba......tabbas" Ta fadi muryarta tana rawa. Tana ji har tsakiyar zuciyarta da ruhinta tausayin aisha kamar zai kasheta.
"Wannan wacce irin DUNIYA ce dake cike da al'umma masu tsananin son kansu?,duniyar da kowa kansa ya sani?" Ta fadi a sarari tana iya jiyo kukan titi wanda takeson boyewa.
Kasa riqe kanta itama tayi,sai kawai ta tsinke wayar,ta dora Fuskarta saman hannun kujerar da take kai. Ba zata iya riqe quncin da takeji saman qirjinta ba,ciwo nauyi da kuma radadin ya mata yawa. Abinda ta saba kamar kullum shi tafi buqatar yi a yanzu wato KUKA. KUKA abu guda daya daya zame mata solution na dukka matsalolinta,duk da ta dade da sanin kukan baya maganin komai.
A hankali take rera sirin kuka wanda take kokawa rayuwar su da rayuwar aisha. Tsananin talauci da rashin galihu ya sanya ta tsinci kanta a halin da take ciki yanzu. SON ZUCIYA da rufewar idanuwa da tsananin zallar rashin imani ya sanya yayi mata silar zamowa daya daga cikin mutanen dake ziyartar asibiti domin ganin LIKITAN ZUCIYA.....ciwon da yakai minzalin da take buqatar TIYATA don ceto rayuwarta
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 25
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
____________________________
Ita kanta batasan yawan lokacin data dauka a wajen ba,batasan kuma ta jima a wajen ba sai data fara jiyo muryoyin yaran gidan cikin wadanda ke zuwa islamiyya sannan ta tuna da HUDA NADRA DA HANEEFA.
Ta tabbatar muddin suka shigo suka sameta a irin wannan yanayin sai hankulansu ya tashi. Wani irin soyayya da kulawa suke mata,wadda sam sam basa qaunar abinda zai tabata komai qanqantarsa.
Da azama ta miqe tana leqa fuskarta tsakanin labulen falon zuwa filin tsakar gidan. Tanaso ta fita ta wanke fuskarta ta kuma daura alwala,amma bataso taci karo da kowa ballantana su tunzura hali da yanayin da take ciki.
Idanunta ta maida ta lumshe muryar titi tana mata amsa kuwwa a kunneta. Cikin duhuwar idanuwanta tana hangen aisha da wannan innocent face din nata. Har yanzu bata huce ba daga abinda azzalumin ya aikatawa aishan ba.....duk da burinta ya cika na danganashi da gidan kaso da tayi. Har yanzu tana jin kamar hukuncinsa yafi qarfin wannan hukuncin da akayi masa a yanzun.
Lokaci guda taji hankalinta yana neman tashi
"Million takwas" Sautin adadin kudin ya ratsa kwanyarta. Ta ina zata soma nema?,ta ina kuma zata samu?.
"Mashkur" Zuciyarta tayi mata hasashenshi farat daya. Tsam tayi da ranta tana juya sunan cikin zuciyarta. A hankali sai kuma ta dinga gyada kanta,tana bawa kanta da kanta tabbacin yes......a jikin mashkur yafi cancanta a hada wadannan kudaden,iya wannan tunanin ya sanyata juyawa zuwa dakin nasu da gaggawa tare da mantawa da niyyar fita zuwa tsakar gida da takeson yi.
Zama tayi sosai saman gadon daga gefe. Locker gadon dake hannun damanta wadda ba kasafai ta fiya budeta ba ta bude. Tarin tarkace ne a idanun mai kallo,amma a wajen sabreen wasu ajiyayyun abubuwa ne dake da tarin muhimmanci da amfani a wajenta a mabanbantan lokuta. Har ma idan ka tambayeta a wani lokacin tana iya ce maka SUNE SABREEN.
mitsitsiyar akwati ce wadda bata fi girman akwatin sanya zobe,ta saka hannu ta daukota sannan ta bude. Wani qaramin layi ta ciro ta rufe akwatin ta maidata,sannan ta dauki wata farar qaramar Samsung's ta bude gefanta ta zura layin ta maida wajen ta rufe sannan ta danne madannin dake gefen damanta. Take ta kawo haske,bayan bayyanar tambari da sunan kamfanin komai ya dawo daidai yadda ya dace.
Batakai ga danna komai ba saqonni suka fara turmutsutsun shigowa. Tsai tayi da idanunta tana kallon notifications din har suka gama jerin gwanon shigowarsu suka qare. Kaman ta sharesu ta isa kai tsaye ga abinda zai sadata da mashkur sai kuma ta sauya tunani.
Ma'ajiyar saqonnin ta shiga,ta fara bin sunayen mutanen da suka aje mata saqon daya bayan daya don bata jin tana da isashen lokacin da zata tsaya budewa da karantawa.
Kamar yadda ta zata,ta samu saqonnin mashkur da yawa fiye dana kowa,saita wuce kowanne saqo ta tafi saqon daya tura mata na qarshe kwanaki biyu da suka wuce.
Sallamarsa kadai ta amsa,ta tura masa ta maida wayar ta aje saman locker tana bin fuskar wayar da kallo,zuciyarta na shirya mata yadda komai zai tafi.
Ta jima da ajjiye mashkur saboda yadda zalamarsa ta fito a fili. Ta jima da ganin ta barshi a gefe saboda yadda halinsa yasha banban dana kowa cikin mutanen da ta taba tarayya dasu cikin rayuwarta. To amma yanzu silar matsalar aisha tana ganin wannan shine right time da zata koya masa darasi shima yabi sahun sauran mazan da suka shude cikin rayuwarta.
Agogon dake manne saman kanta ta kalla tana qoqarin dawo da nutsuwarta waje guda. Zuciyarta ke wani irin rawa tamkar dai ta soma gajiya da al'amuran da suke tunkarota cikin rayuwa. Wasu su shude,wasu kuma suna ci gaba da fuskantarta da babbar BARAZANA.
kamar mintuna goma sha biyar sun qaru akan lokacin dawowarsu daga islamiyya na ainihi. Aje dubanta tayi saman hijabinta na sallah,saita miqa hannu ta dauka tana miqewa da zummar duba inda suka maqale. Bata wasa da duk wani abu da ya shafesu musamman fita da dawowarsu gida. Duk da su din kwata kwata basu san ko ina ba idan ka dauke hayoyi da layukan dakan sadasu da makarantarsu.
Kaman jira akeyi tayi taku uku daidai wayar ta dauki ringing. Duk da ta jima bataji ringing din wayar ba amma babu abinda ta manta daga sautinta.
Taku ukun ta sakeyi ta dawo tana duban wayar bayan zuciyarta ta gama ayyana mata waye din me kira
"Mashkur" Kaman yadda ta aje number dinsa. Siririn murmushin da bata shirya ba ya subucewa labbanta. Tana tsaye tana ci gaba da duban wayar har ta qaraci burarinta ta yanke. Bata da niyyar daga kiran kwata kwata a yanzun,don ba tsarinta bane samun komai daga wajenta cikin sauqi ba. Ta yardarma kanta tana da tsada,tsadar data sanya kowanne namiji da zai ratsa ta cikin DUNIYARTA yarda da hakan,ya kuma bita da tsarinta a yadda ya sameta.
Kaman yadda ta zata bazai kira sau daya ya bari ba haka taji wayar ta sakeyin qara,salin alin ta koma ta maidata silent,sannan ta jawo Locker ta wurgata ta rufe ta kuma soma takawa hanyar falonsu tana zura hijabin saman wuyanta. Shimfidadden kwarjinin dake boye bayan fuskarta ya sake bayyana sosai tamkar ta sanya hijabin ne don ado ba domin biyan buqatarta ba.
Slippers dinta masu taushi ruwan hoda dake daga bakin qofar da zura ma fararen qafafunta,ta murda handle din qofar ta bude ta tura ta fito.
Fayau tsakar gidan nasu yake da wadataccen filin nan da baya rabo da tsafta duk da iyalin da gidan ke qunshe dashi. Kamar kowanne lokaci kamar kuma yadda suka maidata ABUN KALLO. Kowanne motsinta yana saman idanun mafi yawa daga cikinsu,bawai don su bata kulawar data dace ba....bawai don suyi mata gyara idan tayi kuskure ba......badon kulawa ta qauna ba.......saidai don wani radin kansu da biyan buqatar qashin kansu.
Tana da wani irin kaifin nazarin fahimtar meke kai kawo a kewayenta. A zaune take ko tafiya take?. Wani yanayi da a baya baya cikin dabi'unta,kuma bata dashi,amma yanayi da salon rayuwa ya tilastata kasancewa hakan.
Dab da rijiyar gidan wadda daga ita sai hanyar da zata sadaka da ainihin farfajiyar gidan ta ganta. Tsaye gaban rijiyar dauke da cup da alama ruwa ta gama sha.
Sanye take da atamfa classic da aka yiwa dinkin zamani riga da skirt daya zauna daidai jikinta. Kanta ba dankwali wannan zai baka damar hango baqar sumarta me sulbi da suka gada ainihi daga mahaifinsu.
Idanunsu cikin na juna na wasu sakanni,sai ta fara janye nata duban daga kanta tana ci gaba da nufar soron.
HADIYYA......Idan har a baya za'a gaya mata rayuwa zata ajeta a bigiren da suke kai a yanzun ita da ita zata qaryata......idan har a baya za'a gaya mata rayuwarsu zata koma kaman yadda take a yanzun zatace mummunan mafarki ne mara ma'ana....wanda bashi da tushe ballantana makama.
Hadiyya 'yaruwar haihuwarta,wanda mahaifi yayi silar zamowarsu jini daya......hadiyyan da suka taso qarqashin rainon mahaifiyarta......cikin daki guda saman shimfida guda,duk da murdadde kuma zazzafan kishin da mahaifiyarta ke bazawa.......amma hakan bai sauya komai ba na kusancinsu.
Sai gashi a yanzun sunyi irin rabuwar hannayen riga. A yanzun haka tana nata karatun cikin makarantar koyon aikin jinya bisa daukar nauyi da kulawar yayan mahaifiyarta......yayin da tata rayuwar tayi matuqar shan banban da ta hadiyyan.......take neman ta nutse cikin neman dauki da tallafin data gaza me kawo mata,har sai da tayi wani irin wawan tsalle da batasan zata sauka a daidai ko kuma garin saukar tana iya gamuwa da karaya da tarin raunukan da zasu zamewa rayuwarta tabo?. Takai qarshen tunanin sanda takai bakin qofar farfajiyar gidan ta farko,saita aza tafin hannunta saman fuskarta tadan shafi fuskar. Tasan bawai kuka takeyi ba,don a yanzun batajin cikin qwayar idanunta akwai sauran ruwan hawayen da suka rage da zasu bata hadin kan yin kuka. Kawai huci da dumin da fuskarta ya dauka takeso taji ya huce,idanunta sake mata dan zugi zugi tanason rage musu adadin iskar dake shiga cikinsu.
Karo sukayi da huda sanda take shirin fita shigowa su suna shirin shigowa. Suka ja baya dukkansu hudan tana dan riqe goshinta
"Ke kuma ina kuka tsaya haka dukka ku ukun har ana shirin kiran salla?" Ta jefa mata tamabayar tana tsareta da ido. Kafin huda tace komai haneefa ta tsinke da dariya
"Anty.......yaa nadra muka tsaya jira......bata bada hadda ba sai malam ya tsareta" Idanunta ta mayar kan nadra wadda fuskarta ke a daure
"Garin yaya?,kin soma wasa da haddar ne?" Kai ta girgiza da sauri,tana shirin magaa hudan ta rigata
"Kallo suka tsaya yi jiya da daren bayan kin kwanta" Fuska a daure ta sake maida kallonta a kansu
"Ashe?,yau zaku jawa kanku,sai na tsinke kowanne cable na kallo dake dakin nan"
"Ah wai.......ni abunnan yana dauremin kai?,wai lalatacce shike tarbiyya" Murya bibo ta ratsa kunnuwanta sanda take dubansu nadra.
Dukansu ido suka azawa bibo din lokacin da take kutsowa cikin gidan. Kaman yadda suka fita ne dazu,ita da daada,saidai kaman dazun ma daada ratsewa tayi ta wuce abinta ba tare data tsaya yiwa bibo tayin su wuce ba kamar dazun.
Motsawa kadan huda tayi wanda motsinta kadai ya sanar da SABREEN abinda take shirin yi. Yatsarta ta kada mata sautin da ya sanyata tsaiwa can tare da hadiyar wani abu me tauri a wuyanta
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 26
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
__________________________
"Ku wuce muje" Sabreen tace dasu,suk sai sukayi gaba tana biye dasu a baya. Nadra ta hadawa kayan duka ta wuce musu dashi daki. Ita tayi tsaye dasu kowacce ta gama buqatarta suka daura alwala suka wuce daki.
Sallah sukayi bayan sun sauya uniform. Har a sannan tana ankare da yadda huda din keta hadiyar zuciya. Ta sani muddin tace zata saki huda tayi abinda takeso zaman bazaiwa kowa dadi ba......tafi huda zuciya nesa ba kusa ba......tafi huda dabi'ar take yanke.....amma me?,daga baya ta fahimci me irin wannan dabi'ar ba kasafai yake nasara ba.
Sai data kammala sallar magariban sannan tabi takan wayar. Ta samu miscal biyar hade da wasu saqonnin daga gefe. Tabi number tasa da kallo,sai a yanzu takejin ta shirya saurararsa. Kamar yasan tana riqe da wuyar saiga wani sabon kiran ya sake shigowa,don haka ta miqe a nutse ta koma daki tana matsawa daga inda su nadra dake cin abincin dare suke.
"Laifin me nayi dana cancanci wannan uqubar fateema?" Numfashi ta saki wanda sautinsa ya isa har kunnensa
"Ki gayamin ko meye nayi a shirye nake da na nema afuwa" Shuru ta sakeyi tamkar bata layin,saidai tana sauraren dukka maganganunsa
"Fateema" Ya sake kiranta da sunan da shine nasa STAMP din,sunansa ne shi daya,duk duniya shi ta mallakawa wannan sunan
"Naam" Ta amsa a karon farko tunda ya fara maganar
"Kinsan irin rayuwar dana tanadar miki?,kinsan irin gatan da nakeson miki?,kinsan yadda nakeson maidaki tauraruwa a cikin mata?,kinsan yadda nakeso ki koma tamkar sarauniya?"
"Dukka wadannan dama abinda ka lissafa basu nake da buqata ba"
"Me kike da buqata fateema......ki gayamin,a shirye nake na mallaka miki su......"
"Zamu iya haduwa?" Ta jefa masa tambayar
"Ko a ina nake a duniya a yanzun haka kika ce kina buqatar ganina zan wanzu a gabanki" Maida idanunta tayi ta lumshe sannan ta budesu
"Mu hadu yanzu fateema?,ko dan kadanne inaso naga fuskarki"
"Alright" Ta amsa masa a taqaice,abin da yazo masa a bazata,don haka a rude yace
"Venue?"
"Zan gaya maka,i will call you" Bata sake bashi daman cewa komai ba ta yanke kiran.
Wayar ta riqe a hannunta tana juyata a hankali bayan ta zubawa guri daya idanu. Lissafi ne fal Qwaqwalwarta,dole kafin ta samu abinda take nema saita yi haquri ta sake masa,dole ta dinga bashi mabanbantan gurare har zuwa sanda tsarinta zai fada aikinta zai cimma nasara.
A nutse ta miqe tana wassafa yadda zata fita yau din da dare,abinda sam ba dabi'arta bane saiya zama mugun dole,ba kuma zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ya taba faruwa da ita ba,amma yanzun dole ta fitan,tanason ta amintar dashi sosai a kanta.
Kai tsaye ta wuce ma'ajiyar kayanta tana duba suturar da zata dace da ra'ayinta a wannan lokacin. Da idanu ta gama qare musu musu,daga qarshe ta tsaya saman wasu Turkish dress masu strip skirt long sleeve shirt da doguwan kinomo sai madaidaicin veil da zai lullube saman kanta.
Sam bata da ra'ayin sutura me matse jiki duk kuwa da yadda mutane da yawa suke kallon ita tafi dacewa da irin wannan shigar.
Tsaf ta shirya cikin kayan kalolin navy blue da gray color. Sanda ta gama nada veil din a kanta sai data sake duban kanta sosai ta cikin madubin. Tayi wani irin sassanyan kyau me matuqar daukar hankali. Ta miqa hannu a nutse ta dauki turarenta ta feshe jikinta can qasan ranta tana jin fargaba kadan kadan kan haduwarta da mashkur,saidai kuma wani sashe na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwar ba komai,wannan ne haduwan farko,nothing will happen.
Asalin wayarta ta jawo tana lalubar number JIB. bugu daya tak ya dauka,tadan motsa bakinta a nutse
"Ina fatan kana available kuma free"
"Ko ba hakan bane ai ya zama dole nayi creating time wa ke.....me kike buqata?"
"Connection" Ta fada a gajarce
" A daren nan?"
"Haka abun yazo,mashkur......mashkur alqali abdulkreem"
"Done.......wancan aikin ya kusa kammala......akwai ragowar information dana kasa accessing.....but...."
"Karka damu.....mu sanya wancan a mala.....wannan din shine yafi muhimmanci a yanzu"
"An gama.....bani code......let me write it" Ya fada yana dan riqe wayar kadan kafin yace
"Okay.....karanto" A nutse ta karanta masa wasi gajerun lambobi guda uku sannan ta katse kiran. Ta jawo locker madubinta ta ciro Bluetooth tayi danne danne saman wayar tata ta bada wasu sakanni sannan ta maqala a kunnenta. Saita aje wayar,ta dauki wancan Samsung din ta kunnata sannan ta fara yunqurin kira.
Bugu daya tak tayi aka daga,ta kalli wayar da mamaki sanda yake cewa
"Am ready to go princess......ina zaune a mota nida driver a parking lot na gida"
"Yayi.....but if possible ka taho kai daya mana"
"An gama" Ya amsa mata cikin farinciki hankali kwance.
Tana kammala saka takalma huda na shigowa dakin. Kallo daya tak tayi mata taga yanayinta ya sauya. Hudan tadan ritsata da idanu tana dubanta,saidai tun kafin takai ga tambayarta ta bata amsa
"Zan dan fita kadan amma yanzu zan dawo" Iya abinda ta gaya mata kenan ta fara takawa zata fice.
A jikinta taji yarinyar kallonta take,a jikinta taji tana tsaye ne kawai har yanzu,don haka ta tsaya cak sannan ta waiwayo. Ido suka hada,sai a sannan hudan ta kauda kanta. Iya hakan ya gayawa Sabreen maganganune sosai cikin zuciyarta,wataqila girma da kimarta kadai zai hanata ta furta mata su. Taku hudu tayi ta iso gaban hudan
"Dole ce ta saka zan fita huda......amma bazan wuce awa daya ba,idan na dade biyu"
"Amma anty...." Hudan ta furta fuskarta fal damuwa.
Yatsanta ta dora saman lips tana duban hudan,sai kuma daga bisani ta dauke yatsan tana aza dukka hannuwanta saman kafadarta,ta kuma zaunar da ita saman stool na madubin dakin
"Ke daya ce tal cikin mutanen da sukasan wace Sabreen gaba daya baya,kada kiyi tunanin na canza......ban canza ba huda.....kuma har abada bazan canza ba.....nayi alqawari......mommu da abba dake qarqashin qasa bazan bari suyi kaico dani ba" Kai ta gyada a hankali tana kallon Sabreen kamar yadda itama ita din take kallo. To amma a hankali tana rasa wannan yardar wanda tasirin maganganu daga kowanne saqo da lungu na layinsu dama unguwarsu ke kai kawo a kunnuwanta
"Don't lose hope huda......alqawari na.....bazan karyashi ba,ki kula da nadra da haneefa" Ta fadi mata daga qarshe ta juya tana fita a dakin. Nata ruhin yana motsuwa.
Har abada ba zata daina zargin maraici ba......har abada ba zata daina kuka dashi ba......a wani sashen na duniya,a irin wannan lokacin,diya kamarta tana qarqashin kulawar mahaifanta ne guda biyu.......ko kuma qarqashin kulawar wasu amintattun mutane da zasu zame mata makwafin iyayen.......sai gashi tata DUNIYAR ba haka bane,dukka kafadunta dauke suke da wani irin nauyi dakeson fin qarfinta ya kaita qas.
Daga baya baya ta sanya busari ya ajeta kafin akai ga shiga gurin a yanayi salo na kula da takunta kanta dama dukka wani motsi nata.
Sallamar busari tayi tace zata nemeshi idan hakan ta taso,sannan ta fara takawa a hankali tana nufar wajen.
A hankali take ratsa wajen cikin nutsuwa data zame mata dabia,tana takawa a hankali qamshinta da kuma yadda shigar ta amsheta kadai suka soma jan hankulan matasa da yawa wajen. Guri ne da yakan hada matasa maza da mata,wayayyu da suke da gogewa a fannin rayuwa kudi da kuma ilimi. Wajene kebantacce da yawansu suka maidashi gurin nishadi da kuma debe kewarsu,wasunsu a duk daren duniya,wasu kuma jifa jifa.
Yadda take daukan hankulansu haka kwarjininta ke dukansu,wannan ya sanya duk wani dakeson kawo mata caffa ya gaza yin hakan,saidai tazo ta ratsashi ta wuce shi kuma ya bita da kallo.
Tun daga nesa ta hangeshi,ya fita yayi tsaf cikin wani lafiyayyen jeans da shirt da suka dace da takalmin qafarsa. Kanshi pcap ce daya sauko da ita tadan rufe masa fuska. Hannunsa dauke da wayarsa yana latsawa a hankali ba tare daya damu da abinda ke kai kawo a wajen ba.
Ta sani,hankalin gomayyar 'yan mata dake wajen tabbas suna kanshi. Mashkur din ba irin mazan da mace me muradin jinsin maza irinsu zata kall sau daya bane ta iya kauda kai kota wofantar,kusan zata iya cewa ya hada dukkan komai,abubuwa da dama da mazan da suka taba ratsa rayuwarta ba wanda ya gama cikasu irin haka. Yana da kyau daidai gwargwado wanda kudi suka sake qawatashi,yayi karatu har zuwa matakin degree,hakanan dan wulaqanci ne shi,wulaqancin daya zame masa ado a idanun mata marasa kamun kai. Idanunsa a bude suke tarwai,yana da wata irin wayewa data zarta shekaru da kuma iliminsa,wanda hakan baya rasa nasaba da fita qasashen waje da yake yawan yi,musamman qasashen turawa.
Dab da zata iskeshi ya daga kansa sai suka hada ido. Zumbur ya miqe yana zube mata idonshi,har cikin zuciyarsa yana jin wani abu daya qarasa mamaye gangar jikinsa.
Karon farko daya soma jin ra'ayinsa akan mace na neman canzawa. A yanzun kallo daya tak.....cikin qasa da minti daya kacal ya soma ji a ransa kamar ya aureta shine abinda yafi dacewa dashi da ita gaba daya. Kamar alaqar daya shirya da dangantakar daya shirya ginawa a tsakaninsu ba ita ta dace ba,duk da har yanzu gaza fuskantar AINIHINTA....a wanne mataki na 'yammatan wannan zamanin take?. Wasu abubuwan nata na masa kama da dabi'un mace ta musamman.....amma wani motsin nata a wani lokacin sai ya sanya masa shakku akan haka. Kamar dai yanzun,yadda duk da duhun dare ya lullube sararin subhanana amma hakan bai dasa mata shakku ko ya zama dalilin qin fitowa su hadu ba.
A maimakon kujerar daya ja mata don ta zauna saita matsa kujera ta gaba,saidai kuma fuskarta a sake tana maida masa martanin murmushinsa.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 27
_________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
_________________________
Duk da a qasan zuciyarta ba haka bane.
Idanunsa a kanta kaman bazai iya daina kallonta ba yana nashi seat din ya zauna
"Finally dai after wasu watanni......har na debe tsammani sai gashi......" Ya fada yana dan watsa hannayensa irin na gogaggun samari
"Me ma bahaushe yake cewa?.....me haquri ko?" Ya aza mata nauyin amsa tambayar ta hanyar kallonta da idanunsa.
Qaramin murmushi kawai ta saki tana maida bayanta ta jingina sosai da kujerar da take kai din,yayin data daba hankalinta gida biyu. Wani a gurinsa,wani kuma yana kan yanayin wajen dake cike da 'ya'ya mata. Tayi imanin dukkaninsu uwaye ne suka haifesu,koda ace akwai na gaba da fatiha to kadanne. Son rai son zuciya kwadayi su sukayi musu jagora zuwa ga turbar da suke kai a yanzu?. Ko kuma suma kamar ita dinne?.
"Yauwa......thanks" Taji ya furta,saita maido dubanta kanshi.
Idanu ya kashe mata cikin salon jan hankali me zafi,ya kuma sake matsowa sosai har yana rungumar table din da suke kai zuwa qirjinsa,sannan ya aje manual din da aka kawo ta hannun waitress.
"Choose babe" Ya fadi yana lanqwashe murya kamar wani mace gami da kanne mata idanu. Manual din da ya tura mata ta sauke idanu a kai. Tarin abinciccika ne iri daban daban,wanda ko kaffara ba zatayi ba idan ta qiyasta maqudan kudaden da za'a lasa ta sanadiyyar cinsu. Sai data qare musu kallo gaba da baya,yayin da shi da waitress din ke jiransa ba tare da sun qosa ba,saita maida ta ajiye saman table din. Ta motsa bakinta zatayi magana kenan sallamar da akayi da wata raunanniyar muryar taja hankalansu.
Dukkansu shi da ita suka maida dubansu ga wajen. Matashiya ce mai matsakaicin haske wadda idan ka kalleta a qiyasin da zaka fara yi mata duka duka shekarunta ba zasu haura ashirin da bakwai zuwa da takwas ba da haihuwa. Sanye take fallen zanin atamfa da kai tsaye zaka kirata da atamfa leda ko roba,duba da yadda ta cukuikuye a jikinta saboda tsufa da rashin quality da kuma yanayi na dan busawar iska data hadu dashi. Qasan zanin a cinye yake abinda zai wassafa maka kenan shekarun da atamfar ta dauka a duniya ana amfanarta. Hijabi ne a jikinta daya fara gajiya da rayuwa,tsananin sussuqewarsa ya sanya ya baiwa me kallo daman hango yaloluwar rigar dake a jikinta.
"Ke kuma fa?,daga ina wa kike nema?" Mashkur dake dubanta sama da qasa da wani irin qasqantaccen kallo ya jefa mata tambayar.
Rusunawa qasa tayi cikin matuqar taushi da karyar dakai ta hade hannuwanta biyu waje daya
"Taimako nake buqata yallabai......don Allah ka taimaka min da duk abinda Allah......"
"Wait.....wait mana" Ya fada a tsawace har hakan ya sanyata miqewa ta tsaya saman qafafunta. Waiwayawa yayi zuwa ga waitress din
"Yaushe wajen nan naku ya lalace?,yaushe kuka fara bawa mutane irin wadannan daman shigowa gurin nan.....wait.....wai bakusan kowa na zuwa irin nan bane don ya huta ya kuma yi uzurin gabanshi ba tare da kowa da komai yayi disturbing nashi ba?".
Duk joint din da basusan fuskar mashkur ba to tabbas ba cika joint ba......imma darajar wajen tsada da kuma darajarsa batakai ba......ko kuma dai kawai wajen bai cikin tsari da ra'ayinsa. Wannan abun ya sanya cikin rudewa ta soma bashi haquri tare da qoqarin nesanta matar daga wajen,duk da yadda kuwa take roqon su taimaka mata.
A nutse Sabreen ke kallon matashiyar zuwa ma'aikaciyar ma gaba daya. Yar uwarta nace ke qoqarin rabata da gurin don dai kawai kada ta batawa customer rai ta hanyar da babu girma arziqi ko darajta dan adam. Yanzun inda ace cikin kyakkyawar shiga take.....inda ace cikin dressing me kyau take......inda ace jikinta a gyare yake......inda ace zata koma hakan tabbas basai ta tsaya bagging a taimaketa ba. Ta cikin ruwan sanyi matasa dama manyan ire iren wadanda ke zaune yanzu haka a wajen zasuyita miqo mata buqatunsu,wanda yadda ta karba da hannu bibbiyu......kwatankwacin hakanne zata samu nata biyan buqatar.
"Dakata......barta ta dawo" Sabreen din ta samu kanta da furtawa idanunta da suka canza launi suna saman fuskar waitress din.
"Kamar yaya?,ki barta......" Mashkur ya furta yana maida idonsa ga matashiyar data fara takowa a hankali zuwa inda suke din
"Nooo" Ta amsa masa da wani sauti da yake tafe da wani irin zafi da ya motsa mata zuciya. Ganin matar kawai ya tuna mata abubuwa masu yawan gaske,ganinta ya fama mata wani babban ciwo,sai ta sanya hannunta cikin mitsitsiyar handbag dinta sannan ta zaroshi da dukkan kudin dake cikin jakar ta miqa mata.
Cike da mamaki take kallon fuskar sabreen din. Saita motsa kanta tana mata nuni da kudin. Wani irin karyewa zuciyar matar tayi,sannan ta sulale da wani irin qarfi ta tara hannuwanta tana amsar kudin. Jiki da muryarta dukka rawa suke sanda ta fara jera mata addu'a da godiya
"Ya isa jeki" Mashkur din ya fada yana fatan ta gusa ta basu waje ba tare data bata masa budget ko ta bata masa lokaci ba.
Cikin jikinta taji cewa ita din mashkur yake kallo. Ta lumshe idanunta tana qoqarin daidaita mode dinta,sai kuma daga bisani ta sauke mata wannan kallon nata dake saurin waftar hankali
"Are you okay?" Ya jefa mata tambayar cikin matuqar nuna kulawa. Sai da ta danyi gyaran murya sannan ta gyada kanta
"Am okay....."
"Am sorry ko?,irin wadannan mutanen dear ki daina gaggawar amincewa dasu ko basu taimako.....they are wicked wallahi at so many times......yanzun kalli yadda ta bata mode dinki gaba daya?" Gyara zamanta sosai tayi tana maida qafarta daya ta dora saman dayar,sannan ta sarqafe yatsunta saman qafarta tana sake zuba masa idanu. Rashin tausayi rashin imani da kuma rashin bawa dan adam darajarsa yana fita fes a tare dashi,wanda hakan ya sanya taji a ranta yayi deserving ayi punishing dinsa qwarai da gaske fiye da yadda ta shirya yi a baya.
Ya daddage yana sharhi akan baiwar Allahn da baisan wacece ba?,meye matsalarta?,meye damuwanta cikin sararin subhana?.
"Is okay ya wuce" Ta amsa masa a taqaice tana kallon agogon da yake daure a tsintsiyar hannunta.
Hankalinsa yadan dauko kadan,a duk sanda yaga tayi hakan alama ce dake nuna tana dab da yin layar zana,layar zanan da idan tayin baka isa bincikota ba sai sanda taga damar bayyanar maka.
"Times up?" Ya fada yana qureta da ido. Kadan ta saki murmushi
"Eh.....kusan haka ne"
"Ban yarda ba.....dole kici wani abu"
"Nop......banjin wannan.......zan wuce.....but soon zamu sake haduwa"
"Am......bamu tattauna komai bafa......if possible a qaramin minti goma kacal.....in sha Allah bazan haura haka ba" Hannuwanta ta aje daga daukan handbag dinta da tayi niyya,ta koma ta sake harde qafafunta tana kallonsa.
Shima idanun ya zuba mata yana jin yadda kowanne sashe na jikinsa yake da buqatarta
"Wai sai yaushe zaki soni kaman yadda nake sonki fateema?" Ya tambayeta bayan ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya. Dukka girarta guda biyun ta dage tana sake nazarinsa ta cikin qwayoyin idanunsa
"Ta yaya zaka zargeni da abinda ba haka bane?"
"U mean......kina sona kaman yadda nake sonki?" Sai data lumshe ido kadan as usual sannan ta gyada kai
"Okay,prove it" Ya fada da wani irin zumudi yana gyara zamansa sosai tare da rinjayar da gangar jikinsa zuwa zuwa mazauninta.
Ido tadan juya,reaction na fuskarta na nuna masa bata fahimta ba,a nutse ta motsa labbanta
"Like?....."
"Dis week nakeson zuwa dubai nayi annual leave dina......zanji farinciki fiye da yadda baki tsammani.....zanyi alfahari dake zan kuma mallaka miki komai da kike buri cikin rayuwarki......." Sai ya bude wallet nashi dake aje gefe,ya zaro wani qaramin littafi me abun rubutu a gefansa,ya buda tsakiyar littafin ya sanya biron,sannan ya aje mata shi a gabanta yana cewa
"Write it down.....,ko meye.....komai girmansa kada ki gaza rubutawa,and zai kasance ne as you wish" Fararen idanunta ta dora akan littafin kamar me nazarin launin takardar
"Musayar mutunci" Zuciyarta ta raya mata hakan. Wani zafi taji har cikin qwayar idanunta,saita dauke idanunta dama kanta daga wajen ta maidasu gefe. Cikin qasa da second biyar zuciyarta ta gama tsara komai,don haka ta waiwayo ta fuskanceshi sosai sanda yake fadin
"What happened fateema?....." Yana leqen fuskarta. Murmushin da ta fuskanceshi dashi ya sanya yaji relief,fatan samun nasararsa daya soma zagwanyewa duk sai yaji yana dawo masa.
"Nothing......kawai gani nayi kazo da qaramar buqatar da bata buqatar dogon sharhi da roqo har haka......kaman ma bata buqatar tafiyarmu wata qasa......nan ma zata iya zama dubai dinmu"
"Really?" Ya tambayeta da wani irin excitement a jikinsa dama fuskarsa.
"Yes" Ta amsa tana daga masa kai da nata guntin murmushin daya tsaya iya labbanta.
"Thank god.....thank you fateema......ban taba tunanin it gonna be easy kaman haka ba"
"Why?" Ta tambayeshi tana dubansa
"Ba zaki gane ba.....your are so unique fateema......alright.....now"
"Not now......am tired.....inason na koma gida na kwanta.....see you next time saimu qarasa tattaunawa"
"When?,ina gudun ki kufcemin fa?" Bata amsashi ba sai data gama gyara zaman rolling dinta
"Wannan ma kai kayi finding dina out ko nice"
"You are the one"
"Tom" Ta fada kawai tana shirin daukar jakarta,saidai kuma shi din ya rigata ta hanyar jawo jakar gabansa.
Duk da bata saka ido da kyau ba,amma idanunta sunga tamkar takardun kudin waje ya saka mata
"Thanks" Ta furta a gajarce ba tare da taga qima ko farinciki da kudin ba ko qanqani.
Ya sani,daya daga cikin rules nata shine baa yi mata rakiya idan zata tafi,don haka a nan yayi tsaye goye da hannayensa yana kallom nutsasen takunta har ta fice daga gurin.
Ko daya bata jin me busari yake fadi sanda suke tafiya a hanya. Gaba daya tunaninta yayi nisa zuwa wata duniyar ta daban.
Lissafe lissafe ne fal kwanyarta,tama rasa da wanne zata fara?,daga ina zata fara?,a ina kuma zaren lissafin nata zai katse. Zuciyarta da idanunta sunason zuwa ganin aishatu,to amma kuma bata so taje ta ganta a halin da take ciki alhalin bata tanadar mata da komai da zaya fiddata daga wannan yanayin ba. Jib ya kirata,ya tabbatar mata aiki duka ya kammalu daga bangare biyu,amma ta gaya masa ya saurara ta isa gida tukunna.
Goma saura busari ya ajiyeta daga gaban gidan nasu,ta sauke hand bag dinta ta zuge don masa ihsani kaman yadda ta saba,duk da shi din bai kawo komai cikin balance din da ha kamata ace ya kawo din ba amma bata damu ba. Sai data zura hannunta a jakar ta tuna bata da komai sai irin kudin da mashkur ya zuba mata. Tadan jawo kudin gaba kadan tana dubansu,sabbin US dollar ne qar dake qyalli da qamshin sabunta,saita maida dubanta a kanshi
"Zan saka maka wani abu busari ta account,ka bayarma inna kace tayimin addu'a,saida safe"
"Kinfi gaban haka......Allah ya bamu alkhairi" Ya fada yana dan bin bayanta da kallo. Yana mamakin kirki irin nata......duk da ita din zuma ce a wani lokuta idan bataso ba,ga zaqi ga kuma harbi. Ya tayar da napep din yana janyeshi da qofar gidan,qasan ransa kuma yana qididdige adadin alkhairinta a tattare dasu.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 28
Sanda ta isa falon dukkansu ta samesu qudundune saman kujera,kowacce nannade da blanket dinta. Huda ce kadai zaune saman carpet nannade da hannayenta tana kallo a tashar Arewa24.
Tayi mata sannu da zuwa ta amsata tana wucewa ciki don rage kayan jikinta ta sauyasu zuwa da na bacci,gashinta ta kama ta daureshi waje daya ba tare da tasa komai ba,don bata fiya son abinda zai takurata ba duk sanda zata kwanta,ta shafe jikinta da daddadan turarenta me sanyin qamshi data wareshi ne kawai don kwanciya ta dawo falon.
Tsam huda ta miqe ta gabatarata da abinci,saidai bat jima da fara cin abincin ba wayarta ta dauki tsuwwa. Jib ne,qaramin tsaki ta saki,a lissafinta ta gama amsa kowanne kira don bacci take da buqatar tayi,tanaso gobe ta shiga wajen aysha taga yadda jikinnata yake. Abun ya tsaye mata a rai,tana jin cewa idan tana da dama a rayuwa zata sauya rayuwar Yarinyar ne gaba daya.
A kasalance ta kara wayar a kunnenta bayan tayi sallama ya amsa
"Ya akayi?" Ta tambayeshi
"Komai ya kammalu" Ya gaya mata kai tsaye. Dan shuru tayi tana saurarensa,daga yadda yake mata magana ya tabbatar mata fuskarshi qunshe take da fara'a duk kuwa da bata iya ganinsa.
"Okay.....meye result?"
"Bari na fara da abinda yafi damuna yafi kuma yimin dadi......da farko dai zan iya ce miki congratulations.......ina kyautata zaton indai zakiyi amfani da damarki sosai yadda ya dace,kin kusa fara shiga jerin sahun mata masu arziqi......kawai dai" Ya fada yana dan sauke qaramin numfashi
"Wani lokaci duk wani opportunity sai naga kamar kina shuresu ne da gangan......"
"Jib...." Ta ambaci sunansa
"Ina tare da ke,sai na yita tunanin fa me yake damunki?" Yadda yayi maganar a wani sanyaye ya sanyata murmushin dole. Tasan me yake buqata a nashi son rai ace tana yi
"Ka rasa wani abu ne?" Kai ya girgiza
"Ko kadan.....kawai daman da kike samu ya zarta yadda kik amfani da ita......"
"Bani labarin aiki na" Ta zabi shafe wancan maganar gaba daya,don ba me amfani bace a wajenta kamar yadda nashi hasashen yake bashi.
Ajiyar zuciya ya sauke,har tana iya jinsa ta cikin wayar
"Congratulations once again.......daga mashkur har mika'il.....suna daya daga cikin mutanen da suka mallaki manya manyan dukiya........sunyi tarayya ta wajen hali da dabi'a.........amma ta gurin source of income nasu sun sha banban"
"Ehnnnn" Ta fadi tana juya abincin gabanta da spoon ba tare da takai ko loma guda bakinta ba tun bayan kiran nata da yayi
"Mashkur dan kasuwa ne kamar yadda yace.....yana aiki tare da mahaifinsa......mika'il kuma wani babba ne a wani babban kamfani daya boye sunansa......don kamar yana cikin policy na kamfanin ma'aikata irinsa su dinga exposing kansu da rank dinsu cikin company din......saidai iya abinda hangena yakai......company ne babba dake samu da kuma biyan kowanne ma'aikaci albashi me matuqar tsoka" Yakai qarshe yana sauke numfashi tare da sararawa.
Ajiye spoon din tayi tana gyara zamanta, bayanan sun mata dadi sosai,kuma su suka haska mata akwai nasara akan mission nata. A hankali tadan aza dubanta akan huda,duk da hankalinta yana ga kallo,to amma kuma bata bari tayi dukkan wata magana data shafeta a gabansu
"Good job......na gode.....akwai sauran bayanai nasan,ina da sauran tambaya da qarin haske.......amma......bari zuwa gobe mayi waya"
"Alright.....to hakan yayi"
"Allan ya tashemu lafiya" Ta fada tana gintse kiran.
Wayar ta sauke tana bin fuskarta da kallo,tunani ne cinkus cikin zuciyarta. Fuskar matar dazu kawai ke mata yawo a idanu
"Meye amfanin dukiyar da bazaka bayar da ita ba fisabilillahi saidai qarfi ya qwata?" Ta furta a qasan ranta tana tambayar kanta da kanta. Daga mashkur har mika'il tayi imanin cikin budin da Allah yayi musun,inda zasi fidda abinda suka mallaka su dinga narkasu cikin nutsuwa a hanyar data dace......dubban jama'a zasu samu sauqi da radadin da yake damun zukatansu da gangunan jikinsu.
"An kawo miki saqo" Taji muryar huda daga gefanta tana fada. A nutse ta daga kai tana duban hudan kafin ta maida dubanta ga akwatin data jawo gabanta.
Zuba masa idanu tayi tanason tuna daga ina?. A hankali sai kuma abun ya fado mata,ita sam ta manta sunyi dashi ma zai bada saqon
"Kaishi daki" Ta fada tana maida kanta ga waya. Wata number ta lalubs a gajarce kuma ta tura mata gajeran saqon karta kwana
"Received......thanks".
Shi daya ne cikin qawataccen falon da aka qawatashi da dukkan wani nau'in kayan alatu da qawa na rayuwa. Madaidaicin falone wanda ke da saurin janye idanun me kallo da kuma sauqin shiga rai lokaci daya ya kuma dace da kowanne mode da mutum yake ciki.
Shi daya ne tal cikin falon,sanye yake da shirt me gajeran hannu sky blue,sai gajeran wandon da duka duka iyakarsa gwiwarsa.
Yana a tsaye ne yana fuskantar qatuwar t.v plasma dake zaune dirshan saman kyakkyawar tv stand suna haska wasan qwallon qafa,saidai fiye da rabin hankalinsa baa wajen yake ba.
Bayan gilmawar kowanne minti ko second sai fuskarta ta dawo masa. Ya lumshe idanunsa sanda aka buga qwallo na qarshe cikin tazarar bada sa'a game rabo wato penalty,ya daga ragowar tsadajjiyar giyar data rage a qasan glass cup din hannunsa ya qarasa kurbeta,ya dire cup din yana fidda iska daga bakinsa.
Tsakanin awannin daga dazu zuwa yanzu ya gama tsara yadda zai baibaye rayuwarta da tsadajjiyar rayuwa......yadda zai narkar mata da zuciya da masu gidan rana......yadda zai maidata tashi shi kadai......yadda kuma zai siye mata zuciya da kuma rayuwa da kudi wadanda yayi imanin a wannan lokacin da muke ciki sune maganin kowacce matsala.....suke iya siya maka dukka nau'in macen da kakeson ka mallaka.....don babu yaren da matan sukafi ganewa irin yaren LUXURY LIFESTYLE.
Kallonsa ya mayar saman system dinsa dake kunne,yana jiran kirane daga wajen CEO na JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES (JDCR).
A duk sanda sunan ya fado masa a rai,ba abinda yake fara zuwa ransa sai GIDAN KUDI. wanna shine sunan da yafi kiransa dashi......wannan shine full definition nashi da yake ganin ya dace dashi gaba da baya.
Sake matsawa yayi ya gani koda ya nemeshi?,amma ba wani saqo ko kira kai tsaye ta yanar gizo. Mamaki yadan kamashi,saboda sanin da yayi masa na zamantowarsa mutum me girmama lokaci tare da bawa lokaci muhimmanci,yasan tabbas akwai abinda ya riqeshi ne hala.
Baiso yasha komai ba har sai sun kammala duka maganganun da zasuyi through video call. Yasan halinsa,yana da tsananin zafi yana kuma da masifar kaifin karantar mutum,wanda banda shima ya zama mutum me tsananin iya takunsa yayi imani da tuni labari ya jima da shan banban.
Yaci wuya ya kuma tsallake turaku gwaji da jarrabawoyinsa sosai kafin yakai matsayin da yake kai a yanxun. Saidai kuma tsakanin jiya zuwa yau burinsa ya fara fadada. Ya fara jin cewa yana buqatar budawa a harkokinsa fiye da wannan da yake ciki a yanxu,yana buqatar qarin kusanci da CEO fiye da wannan kusancin........yana so matakin da suke kai sufi haka shi da shi na qullewa da kusanci tare da sakar masa ragamar komai na kamfanin fiye da yadda yake kai a yanzu.
Sai ya zagayo saman kujera ya zauna saboda yadda yaji jikinsa ya fara week,alamu dake nuna abinda yasha din ya fara tasiri a jikinsa,duk da giya ce me tsadar gaske da yake kashe kudade masu kauri wajen siyota,bata bugar dashi buguwar da zata sanyashi fita daga hayyacinsa gaba daya.
A sannan sai yaji bashi da wani sauran muradi daya wuce yaji muryarta,gaba daya taswirar qwaqwalwarsa ita take hasko masa cikin shiga da dressing daya dinga ji kamar yayi fiffike ya kamo ta,don haka ya jawo wayarsa ya fara gwada number dinta. A karo na uku kenan daga dazu zuwa yanzun da ya fara kiran nata bai samu isa gareta ba,saidai a yanzun cikin sa'a......har ya fidda rai da tsammani......dab da zata tsinke sai aka daga.
"Kin barni da kewarki ko?" Ya fada murya can qasa. Shuru tayi tana sauraren yadda muryar tashi ke fita kafin ta motsa bakinta a hankali
"Ka wuni lafiya?"
"Ba lafiya ba......nayita kewarki ne kamar na zauce.....don Allah.....ki bani daman ganinki koda zuwa gobe ne MEENAL".
Wani siririn murmushi ta saki,irin wanda take saki din a duk sanda wani cikinsu ya kirata da stamp name dinsa
" Ba yanzu ba" Ta bashi amsa,amsar da a zahiri da gaske take,ta fito ne daga qasan zuciyarta. Ba kasafai take baka damar ganinta ba a sanda ka damu da ka ganta din,muddin akwai mission a kanka saita kaika matakin da take da buqatar kaje din.
"Zan katse kiran,bacci ne a kaina,zan sauka saida safe?" Tayi furucin da sigar tambaya,bawai don tana da buqatar amsa ba.
Bai samu sararin cewa komai ba t gintse kiran tana aje wayar a gefanta tare da bin wayar da kallo
"Mika'il" Ta sake maimaita sunan tana gyada kai.
Shima bin wayar yayi d kallo kaman sakarai
"Zatayi girman kai,zatayi izza tun a ganin farko na sani......amma kuwa zuwanki hannu bazaiyi wahala ba 'yammata" Ya fada a sarari yana lashe baki hadi da sakin wani shu'umin murmushi.
Yana shirin aje wayar wani kiran ya shigo masa. Mato sunan dake rubuce da number dake kiran nasa.
Wani zunkudawa yayi sanda ya gama hada haruffan me kiran nasa saboda yadda kanshi ya fara nauyi,ya daga wayar ya sakata a hands free ya ajiyeta,sannan ya koma da baya ya jingina yana saurarensa
"Sai ogaaaaaa.......sai bosssss"
"Ya akayi mato......nasan kiranka alkhairi ne da kuma samuwa"
"Ba kadan ba kuwa.......na samo mana wani sabon zone na caca.......harka ruwa ruwa.......kudi faca faca.......A wanki gara......abun kuma babu kama" Gyara zamansa yayi sosai yana bashi hankalinsa. Baya wasa da harkar caca kwata kwata,suna daya daga cikin abinda ke kawo masa maqudan kudade bayan kamfanin jadda DIAMONDCHORE da ya zame masa lamba daya
"Kaman yaya?,yimin dalla dalla,don wutata ta kusa daukewa" Ya fada muryarsa tana dan rangaji.
Yasan waye ciki da bai dinsa,tunda ya fadi hakan kuma ya gama fahimtar abinda ke faruwa,don haka ya tattara bayanansa ya gyara zamansa yana cewa
"Wani gurin caca wanda na tabbatar a wajenka me gida local ne......akwai 'yan wasa na haqiqa amma kuma kai tsaye na fahimci cewa gidadawa ne.......basu da wani wayewa kwata kwata a cikinta.......akwai kudade amma fa a qasa,na tabbatar a bugu daya zaka tarwatsasu ka kuma yi gaba da duk wani abu da suka shigo cacar dashi" Wata shu'umar dariya ya saki
"Mato nawa" Ya furta maganar mato din na masa yawo saman kai,saidai gajimaren da yahau ya hanashi tsaiwa su qarasa maganar,don haka ya sanya hannu ya katse kiran kawai yana furta
"Munkaila bisa kansu" Cikin mutuwar jiki da kasala.
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
_________________________
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 29
*SOUTH KOREA*
*_THE CAPITAL OF SOUTH KOREA (SEOUL)_*
*_Yanghwa-ro to hongdae geori_*
Yanghwa-ro daya daga cikin lafiyayyun street dake da wani irin daddaden yanayi a kowacce safiya cikin anguwar hongdae dake tsakiyar south Korea. Yanayi ne me me dadi dake wanzuwa a kowacce safiya cikin street din dake da wani irin shuru da nutsuwa gami da nisanta da kowacce irin hayaniya daka iya damun ruhi ko matsantawa nutsuwar dan adam.
Ga duk ma'a bocin fitowa da sassafe tsakanin yanghwa-ro zuwa hongdae geori zai zame masa abu me wahala baisan baqin fuskar matasan Nigerians din guda biyu ba. Zaratan matasa masu wani irin kyan zubi na halitta da kuma ajiyayyen kwarjini da kuma haiba. Yaya da qaninsa wanda fitowa jogging kusan kowaccw safiya ya zame musu kamar al'ada.
Muhammed FU'AD,da kuma musaddiq hamza kibiya wanda yake daga gefan Muhammed FU'AD din. Idan yayi kamar zasu daidaita wajen sassarfa me kama da gudun da sukeyi sai ya zame har sai FU'AD din ya wuceshi yana fadin
"Eheennn......don't stop.....don't stop" Da wata iriyar husky voice da Allah ya huwace masa wadda ke cakude da nishi kadan na gudun da suka dauko.
Yayi kaman zai tsaya din ya kusa sau biyar......hakanan shima yake zaburar tashi har zuwa sanda suka iso daidai wani guri. Guri ne da kusan kowacce unguwa take da nata wanda aka tanadeshi aka killaceshi domin hutawar jamaar unguwar cikin wasu kujeru da shimfidaddun tsirrai da suka wadatu da tsafta suke kuma samun kulawa yadda ya kamata.
Ruku'u musaddiq yayi yana cakewa a wajen,ya kama gwiwoyinsa da hannunsa yana sauke nishin wahala gumi yana fita daga sumarsa zuwa goshinsa.
"Oh shit" FU'AD ya fada yana jan birki,sannan yayi reverse yayo kwana da hanzari yana dawowa daidai inda musaddiq ya cake.
Baice masa komai ba ya kama wuyansa ya cafka yana tadashi tsaye sosai saman qafafunsa,abinda ya sanyashi sakin wata qaramar qara yana matse kafadunsa
"Sorry hamma......am really tired wallahi......i try hamma......kusan minti talatin tunda muka fito muke wannan gudun.....ko doki hamma sai haka"
"Shut your mouth.......malalaci kawai......da wanna halin da dabi'ar naku meye marabarku da mata?,inajin mun kusa baku jilban da dankwali kuna daurawa ko?". Sosai dariya taso murqushe musaddiq,amma yasan bai isa ya yita a gabansa ba. Duk wani training nasa suna shanyewa amma yanzun don ya gaza cikashe mintunan gudunsa shine ya zama malalaci har zasu fara dauka zani?.
Zanin da ya sake tunawa ya sanya dariyar da yake boyewa ta qwace masa da gaske,don ba wanda ya hango daure da zani sai saddiq.
Sakin qeyar nashi FU'AD yayi yana watsa masa wani irin kallo da lumsassun idanunsa dake da wani irin kaifaffen kallo me kashe duk wani zarra ta mutum
"Are you laughing?,da gaske baka gaji ba......zamu qarasa gida a haka,ko sau daya kuma ka sake tsayawa kasan sauran......salary dinka na wannan watan zan saka abba yayi sadakarshi" Ya fada yana gyara doguwar socks din qafarshi daya rufe mass har gwiwarsa. Kayan motsa jiki ne a jikinsa,amma yadda sukyi masa kyau zata tsammaci ya sanyasu ne don ado. Sun fidda duk wata qirar qarfi da Allah ya bashi,murdaddun muscles dinsa zuwa shaffen cikinsa da qirjin yafi cikin dagowa.
"Hamma......wallahi Allah ba abinda kake tunani bane" Ya fada cikin karya wuya da sanyaya murya
"......Allah hamma kawai musaddiq na hango daure da zani da dankwali......" Sai ya qarasa fadi yana bushewa da dariyar data sanyashi ya murmusa dole. Dariya yake sosai yana kuma kallon fuskar fu'ad din.
"Iyakarshi kenan" Ya furta a ransa. Murmushi shine maqurar dariya a wajensa ko yaya kuwa abu yakai. Kai ya girgiza kawai qasan ransa yana tuno wasu abubuwa na sadiq da musaddiq din. Suna da wani irin wasan da inda ace shima irin farouq ne baya jin yaran zasu shuka abun arziqi idan ba shiririta ba. Har kullum abba na jin dadin jajircewarsa a kansu,don shima din sun maidashi kakansu qarfi da yaji,yayita masifa yayita masifa amma a banza,maganae mutum guda ce take ratsasu.....zancan mutum daya ne yake zama daram saman kansu shine zancan muhammad fu'ad.
Bai sake ce masa komai ba sai ya miqe yana zaro wayarsa dake aljihun wandonsa. Iphone 16 sabuwar qira wanda babban hoton wata kyakkyawar matashiya ya mamaye ilahirin fuskar wayar. Kyakkyawar bafulatana me wani sassanyan kyau,cikin kamilalliyar shiga data qarawa hoton da Fuskarta kwarjini. Dududu shekarunta da suka nuna cikin idanunta da kuma fuskarta goma sha takwas ne.....sha takwas din da aka soma gangarawa cikin sha tara.
Kalmomin sirri ya sanya ya bude wayar,sannan kai tsaye ya tafi zuwa ajiyayyun lambobin da basu da yawa cikin wayar. Akan wata number dake dauke da sunan ABBA NA ya tsaya,ya danna kira sannan ya maidata aljihunsa yana gyara zaman Bluetooth guda daya dake manne a kunnensa yana bada hasken qyallin wuta time to time. Sai kuma ya fara takawa a hankali ba tare daya cewa musaddiq komai ba,wannan ya bawa musaddiq din daman biyo bayansa a nutse can qasan ransa yana murnar yadda aka haqura da jogging dinnan haka.
"Shi ya dauka kowa kamarshi ne me jikin qarfe da baya gajiya da motsa jiki......idan na hada qarfi ina zan kaishi" Yayi gulmarsa a ransa yana biye dashi tare da qare ma bayansa kallo.
Shi kansa yadda yake da ginannun muscles yana burgeshi yana kuma bashi sha'awa,amma bashi da juriya da qarfin halin da zai building muscles ma jikinsa kamar nashi.
"Abba ka farka?" Ya fada cikin matuqar nuna kulawa bayan yayi masa sallama.
"Okay gamu nan qarasowa" Sai ya katse kiran ta jikin Bluetooth din nasa sannna ya dan soma sassarfa yana cewa musaddiq
"Oya.... Mu qarasa gida" Kaman zaiyi kuka hakanan ya taka ya soma bin bayansa. Kafin su qarasa gidan sai da yaji kaman zai zube,cikin ransa yake ganin gaskiyar sadiq ashe da yakanyi ciwo ko ya qirqiro uzurin qarya duk sanda ya tasheshi ya rakashi jogging. Har gwara ku shiga gym room dashi,wannan idan suka faki idonshi sai su zabi machine daya su haye su kasheshi ko su rage gudunsa sosai.
A hankali suka qarasa hongdae geori cikij estate din dake unguwar. Gida me lamba ashirin,yayi tsaye yana danna bell yayin da qirjinsa ke dagawa sama da qasa yana fidda Zazzafan huci daga bakinsa. Ya jiqe sharkaf da gumi,musaddiq kuwa tuni ya zube saman step biyu dake bakin qofar gidan yana numfashi da sauri da sauri.
A hankali qofar ta bude,dattijon mutumin nan Alhaji hamza kibiya ya bayyana cikin wata lallausa kuma kyakkyawar abayar qasar morocco ruwan zuma. Ba abinda ya sauya tattare dashi sai shekaru da suka fara bayyana kansu a jikinsa.....bayyana ba me muni ba saboda daular rayuwa da kuma jin dadin da yake ciki daya zarta ya kuma ninka na shekarun baya ta hannun zaratan yaransa guda hudu dukka maza.
Da murmushi a fuskarsa kamar kullum yake kallonsa
"Ina dayan me babban suna?" Alhaji hamza ya tambaya saboda idanunshi basu hango musaddiq ba sam sam.
Da baki ya yiwa abba cunensa,abban ya dora hannu saman baki yana bushewa da dariya
"Kai......taso dalla.....dama babu me maganinku ai sai me babban suna......tashi nace mace kawai.....koni nan da shekaru suka fara turamin ina gudun nan,kuma ka gani da idanunka.....ina zakuyi qwarin damu uwayenku mukayi?,baku da aiki sai hawa mota sai ciye ciye da shaye shayen banza" Abban ya fada yana wurga hannu. Kai ya daga da qyar yana duban abban
"Abba wallahi.....bazan iya tashi ba da gaske,qafafuna kamar zasu tsinke.....gudun fanfalaqi yau hamma ya saka mukayi" Yadda yace gudun fanfalaqin ya tilastawa abba sakin dariya,yayin da FU'AD ya girgiza kai kawai. Suna ganin iskanci a gidan wajen sadiq da musaddiq,kullum kaman basa girma,kullum kallon kansu sukeyi kaman qananun yara.
"Tunda ba zaka tashi ba ai idan wancan qadangare ya shige maka riga ai ka nema hanyar gida" Wani mugun tsalle ya doka sai gashi a tsaye kyam
"Yauwa.....dan nema ja'iri,zo ka wuce kaji me babban suna" Abban ya fadi yana komawa ciki fuad yabi bayansa yana dariya qasan ranshi. Har yanzun musaddiq yana tsoron qadangare kenan tun yarinta?,abun ya dinga bashi mamaki don shi baiga wani abun tsoro a qadangare ba.
Suna shiga yana biyo bayansu yana dube dube yana fadin
"Wallahi abba ka kusa sakani na saki fitsari a wando......yanzu inda a gaban nasreen......" Tsaf ya kame bakinsa ba tare daya qarasa ba saboda kallon da FU'AD ya jefeshi dashi,ya sosa kanshi ya sauya akalarsa zuwa kitchen da kake iya hangensa tarwai ta falon.
Saman kujera ya zauna a nutse yana warware takalman qafarsa,abban ma ya koma inda ya tashi ya zauna yana daukar mug tare da ci gaba da kurbar zazzafan tea din dake ciki.
"Sannu da gida abba" Ya sake fada yana dan jingina bayansa da kujera
"Sannu fuad shugaban 'yan motsa jiki" Abban ya amsa masa da murmushi tare da maida dubansa ga takalmansa daya cire. Duk abinda ya cire ko yayi amfani ddashi yasan ya killace shi,zaiyi wuya kaga ya watsar da kaya ko wani abu makamancin hakan. Ya tabbatar hakan baya rasa nasaba da matsananciyar tsaftarsa da kuma yadda rayuwarsa ta ginu a shekarun baya,cikin gwagwarmaya da daukar nauyi da lalurar kanshi. Yana da bala'in tsantsami shi yasa abubuwa da yawa ya gwammaci ya tsaya ya yiwa kansa. Idan ka ganshi a kitchen yana hada breakfast ko yana dafa tea zaka rantse da Allah ba shine dan marayan zakin nan ba mamallakin kamfanin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES ba,wanda jaridu zuwa mujallu kullum kwanan duniya ke zumudi da rububin yin rubutu a kansa ba domin samun daukakarsu da qaruwarsu. Duk wani rubutu ko labari da wani gidan tv jarida ko radio zasu fitar akan MUHAMMAD FU'AD tamkar daukaka ce a tare dasu. Matashin mamallakin kamfanin haqar ma'adanai na diamond ne da makamantansu. Kifi daya a ruwa da manyan masu sarrafa gwalagwalai da diamond na duniya suke saka fatsarsu domin kamo kaya daga kamfaninsa saboda inganci da kyansu. Diamond guda daya daya taba tsinta a sanda yake tsakiyar bautar qasa can cikin jahar kogin nigeria.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 30
Dan bautar qasar da bai wuce sati biyu a camp ba.....wanda ya fita yawon ganin gari shida shaqiqin aboki amini kuma dan uwansa farouq hamza kibiya. Haka kawai yayi sha'awar bin daya daga cikin matasan da farouq ya saba dasu a teburin me shayi wanda duk dare sai yaja fu'ad koda kuwa bayaso,suje su zauna su sha hira suga yanayin gari da mu'amalar mutanensu. Da fari fu'ad baya so,daga bisani ne ya sake a hankali bayan da yayi tunanin wannan karin maganar ta bahaushe
"Tafiya mabudin ilimi". Ba yadda zaiyi ya samu ilimin muddin yana nade a camp da kuma dakin. Abinda yafi damunsa yake hanashi fitar yadda 'yammatan camp din nasu harma da cikin garin suke da son wasa da wargi gami da son shigewa mutum. Shi kuma abu guda da yafi tsana kenan kaf fadin rayuwarsa. MACE halitta guda daya da ba kasafai yake mata uzuri ba a rayuwa.....halittar da yayi amanna ya kuma saddaqarwa kansa su da KUDI tamkar rai ne da bugun numfashi. Halittar da ya gama karatunta cewa tafi bawa KUDI muhimmanci sama da komai.....kwadayyar halitta me son kanta.....mara tausayi kuma mara imani koda akan dan cikinta ne kamar dai MAAMANSA.
Farouq yaso hanashi binsu inda suke haqar a sirrance saboda sanin tsananin risk din dake wajen. Bawai iya barazanar fadowar rami bisa kan me haqa ba.....a'ah.....hatta na a tsakaninsu suna iya farde wanda ya tsinta din suyi kashe mu raba da abinda ka samu.
"Farouq......ragon namiji shike tsoro.....faduwar gaba asarar namiji......ba'a haliccemu don mu kwanta ko mu zauna iyayenmu su dinga bamu suna mana wahala ba.....an halicci Muhammad fu'ad don yayi gwagwarmaya ya kuma fuskanci challenges a rayuwarsa.......na fara gwagwarmaya tun daga sanda na fara fahimtar Muhammadu sunana ne......na fahimci kuma MAAMA itace ta haifeni......" Ya qarasa maganar wani abu yana tsirgawa daga tsakiyar muryarsa har cikin qwayoyin idanunsa
"Wai anni bata hanaka zancan maama dinnan ta haka ba?" Farouq yace da fu'ad a sanyaye. Wani malalacin murmushi ya saki ya sunkuya yana ci gaba da daura boot din qafarsa da kyau. Ta yaya MAAMA zata bar zuciyarsa wai?,ta yaya?har abada sai randa qasa ta cike idanunsa.
"Na shirya zan wuce sai na dawo" Ya fada yana miqewa tare da zube hannayensa a aljihun wandonsa yana duban farouq. Harara ya watsa masa sannan ya miqe da hanzari
"Ina zan barka ka tafi kaje ka bace ka jamin jarfa a wajen abba......qafata qafarka.....idan ma zamu bata mu bata tare" Yayi maganar yana miqewa.
Miskilin murmushinnan nasa ya saki ya juya yana kada kai. Ya sani shine dai kawai a gaba kafin abba da yake qorafi akai,kawaidai bazai iya barinsa ya tafi bane ya barshi,wanda wannan daya daga cikin danqon qauna da 'yanuwantaka dake a Tsakaninsu.
Yana shiryawa yana mita har ya kammala suka sulale suka fice daga gidan da aka musu masauki ba tare da kowa ya sani ba.
"Ni bansan me zakayi da wata mahaqa ba.....dukkanmu abba jira yake mu kammala wannan service din ya bude mana namu kasuwancin"
"Ta yaya zaka zama cikakken dan kasuwar da yasan daraja da kimar dukiya baka iya gwagwarmaya ba?.kana daga zaune ba tare da ka tara komai ba?" Fu'ad ya masa tambayar yana kallon hanya kawai ha tare daya kalli farouq din ba
"Gwagwarmaya cikin wadannan qedarun?,don kawai Samuel ya gaya maka za'a je da kai?,suna da hadari fa fu'ad?" Murmushi ya kuma saki hankali kwance,har yanzu kuma bai kalli farouq din ba ya sake bashi amsa
"Muhammad fu'ad dan arewa.....ya fisu hatsari.....zaka gane hakan idan sukayi yunqurin yin wani abu". Maganarsa ta tabbata kuwa a wajen farouq.
Tun isarsu gurin komai ya fara bayyana. Da wani irin kallo ayarin suka fara binsu saboda ganinsu baqin fuska kuma 'YAN AREWA dake yara yaran hausa. A haka aka soma tafiyar har zuwa kebantaccen wajen da suke haqar ba dare ba rana don samo ma'adanai. Samuel shi ya dauki dukkan wani risky ya shige gaba aka barsu har suka isa gurin cikin wadanda aka aminta da shigarsu wajen.
Duk inda fu'ad zai motsa farouq yana biye dashi,sam wajen shi baiyi masa ba,hakanan a tsorace yake da wajen,shi sai ya zamana kamar me gadin fu'ad ne a wajen. Duk wani motsi da za'a yi a wajen ko wani da zai tunkarosu hankalinsa yana wajen.
A hankali ya tura kansa ramin da fu'ad ke ciki wanda yayi zurfi
"Mutanen nan fa hankalinsu a kanmu yake,duk wani motsinmu suna ankare dashi"
"Karka damu" Kawai yace dashi saboda wani abu daya fara hanga wanda ya dauki hankalinsa matuqa.
"Farouq" Fu'ad ya kirayeshi da wani sauti me jan hankali wanda yaja hankalin wanda ke ramin daura dasu ya kumayi tsai yana jiran jin dalilin kiran.
Tura kansa farouq din yayi yana cewa
"Menene"
"Na samo.....na samo" Ya fada da wani irin excitement,yayin da zuciyarsa da kwanyarsa suka cika da mamakin samun abinda bai taba zaton zai samu ba koda kuwa a mafarki. Har a qasan zuciyarsa ya gwada zuwa wajen ne kawai don samun experience da karantar yanayin yadda irin rayuwar yake.
"Duba ka gani farouq" Ya fada yana miqo masa. Farouq din da hanzari ya dira ciki yana toshe bakin fu'ad
"Keep quit fu'ad.....ka tono masifa" Ya fadi a tsorace. Da wani kallon mamaki yabi farouq din
"Kaman ya?"
"Kamar yadda ka sani.....kowa dake nan wajen abinda yake zuwa nema kenan kwana da kwanaki.....kana baqo wanda aka yiwa alfarma.....zuwan farko kayi kacibus da abinda yake dukkansu shine burinsu?. Akwai shugaba a cikinsu wanda duk wanda ya samo sai yabi qarqashin umarnin shugaba......zai kuma danqashi a hannunsa....." Tsaki fu'ad yaja saboda dokokin rainin wayo da yaji farouq yana karanto masa wanda shi baisan dasu bama,don ya fishi zama da hira da Samuel
"Su sukamin wahalar?,ko an gaya maka nazo nan dinne don na yiwa wani qaton zindiqin arne aiki?.....let's go mu wuce gida" Ya fada yana kama ramin tare da nufar hanyar fitowa.
Sanda yayi tsalle ya qarasa fitowa baima lura da wadanda suka kewaye ramin ba,har sai daya gama karkade jikinsa yaji sadiq daya fito daga bayansa ya zungureshi.
Lafta laftan yare masu mummunar siffa tun daga halitta zuwa zuciya. Mutumin da alamu suka nuna shine shugaban yana tsaye a gaba. Ya sake matsowa gaba kadan ya miqawa fu'ad hannu..
Sarai ya fahimci abinda yake nufi,amma yadda yake kallonsu da dukkan wani motsi nasa cikin izza da nuna isa ya sanyashi jin har cikin ransa bazai taba iya bashi abun ba. Ballantana abinda yake wahalarsa kuma guminsa ne. Ko daya babu me haqqi a ciki bare yayi tunanin cinyewar zai zama laifi har a wajen Allah.
"Ban gane ba" Fuad din ya furta cikin dakiya da jarumta
"Ka miqo diamond din daka samu aka ce...!" Daya daga cikin wadanda ke daura da ogan ya furta murya a kausashe yana sake matsowa dab da fuad din saboda nuna masa tsananin buqatar abun da suke da,da kuma nauyi da girman abinda yake dauke dashin.
Cikin qasa da second biyar ya gama fahimtar motsi da niyyar kowa. Tabbas!.....tabbas babu abinda yafi dacewa dasu muddin yana da buqatar tsira da wanann abun face tserewa
"Ka shirya farouq.......ka shirya gudun tsira da rai.....ko mu ko su,ka qarfafa zuciyarka da gangar jikinka" Ya furtawa farouq qasa qasa tare da damqe hannunsa da kyau.
Kaduwa sosai farouq yayi da abinda yaji fu'ad din yana fada.....yasan halinsa muddin ya fadi sai ya cika.....amma kuma abinda zasu aikata din mugun ganganci ne da zai iya zama ajalinsu.
Bai gama sauke wannan tunanin ba yaji qarar wani abu timmmm sannan yaji an finciki hannunsa. Sanda zai duba sai ya samu fuad dinne ya kaiwa ogan nasu mummunan naushi har sai da yakai ga zubewa qasa war was,da wannan ya janye hankalinsu suka tsallakesu,saidai ko taku uku basuyi ba aka samu wadanda suka rufa musu baya bayan fusatacciyar tsawar da ogan nasu ya buga musu wadda har yanzu yana zaune a qasa
"Catch them!!" Ya fada qarajin hasaso asarar dake tallafe dashi tare da tsoro da razanin rasa abinda yake tamkar shine cikamakin burin rayuwarsa.
Wani irin gudu tamkar a indian film fu'ad ya dinga yi,abun har yaso yafi qarfin farouq banda shi dinma yaci sunan me sunan.
"Mu tsaya fu'ad.....harbi sukeso su fara"
"Wa ya gaya maka ana gudu da waiwaye?......just run!!,run kawai.... Kada ka sake waiwayawa". Ganin kamar farouq din ya fara karaya ya sanyashi yin wani juyi ya maida farouq din gaba shi yana biye dashi.
Da gaske dai suka fahimci zaratan samarin 'yan arewan guda biyu na niyyar kufce musu,sai kawai suka fara harbi,harbin da ya gigita farouq qwarai da gaske ya kuma dinga kiran sunan fu'ad akan su maida musu abinsu.
"Basu isa ba....don ba abinsu bane,arziqi ne na ubangiji daya shimfida a qarqashin qasa saboda bayinsa,ba don su kadai Allah ya ajjiyeshi ba" Ya fada a zafafe cikin yanayin gudun yana sake fusgar hannun farouq da kyau. Wani irin samfurin gudu da fu'ad din keyi riqe da hannun farouq sai daya zama abun kallo a wajen farouq din. Bai taba tsammatar iyawa ko qwarewa haka a tare dashi ba wajen sanin kurdawa tsakanin manyan dutsuna da qananunsu ba sai a sannan. Bayan shafe dogon lokaci suna fafatawa Allah ya basu nasarar kufce musu
"Park zamu wuce mu kwana a can daga can muyi gida......ba park na kusa da nan ba,ta gaba da nan" Fu'ad ya fadi yana kallon farouq
"Ya zamu bar camp kuma bamu dauki komai namu ba......sannan kuma......"
"Kana tunanin sun qyalemu ne?,kana zaton idan muka koma can din zasu barmu mu kwana da ranmu?" Fu'ad ya tambayi farouq wanda da alama baisan girman ta'addanci irin nasu ba.
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
________________________
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 31
___________________________
Wani murmushi ya saki
"Ai basu ba,ko jamaa da muke tare dasu sukasan abinda muke dauke dashi sunanmu matattu......maganar diamond da gold akeyi farouq.......kasan nauyi da girman ma'adanin dake jikinmu?......mutanen nan sun wuce duk sani da tunaninka.....ni kaina da na yarda mubi Samuel da shirina,na san kuma cikin su waye zan shiga,kaine nake zaton bakasan irin girman wajen da muka shiga ba.....banda saa tana tare damu bamu isa mu shiga wannan wajen bama bare akai ga samun abinda muka samu kuma har mu gudo lafiya lau dashi......daga yanzu har zuwa sanda zamu koma qasarmu rayuwarmu na cikin hadari......take care dude...." Ya fada yana bugun kafadar farouq da ya gama mutuwar zaune.
Bin fu'ad kawai yakeyi da kallo yana mamaki. Yasan girman hatsarin fiye dashi amma yayi kaman bai sani ba?,ko a yanzun wannan uban wahalallen gudun ceton ran da sukasha shi kaman ma baiyi ba?. A yadda ya sanshi da I don't care manner da rashin shiga abubuwan rayuwa sosai bai taba zaton ya iya daukar risk da tarar aradu da ka ba sai a yanzu.
Tun daga tashar da suka samu mafaka sukasan lallai an baza nemarsu,a daren suka haye motocin kaya dake lodin arewa suka wuto gida.......wanda sai daga bisani abba yasan komai.
Yayi fada yayi fada kaman zai ari baki......ya kuma yi musu fadan da bai taba musu shi ba,musamman me babban suna da yake girmama sunansa yake kuma qaunar yaron har cikin ransa. ANNI ce ta sanya baki aka samu ya lafa sannan aka fara tunanin yadda zaa yi da abinda ya haqo din,tunda ya riga ya shigo hannu ba batun ace za'a maida musu.
Bisa dukkan dokoki da tsare tsare kan tsaftatacciyar hanya aka tsara komai ya zama dukiyar da a yanzun suke juyata shida farouq dinsa. Abban kuma ya zame musu jagora madubi.....ma'adanin kuma ya zama shine kasuwancinsu.....babbar masana'antar karbar haqaqqun ma'adanai su tace su gyarashi su fiddashi xuwa manyan qasashe,irinsu china,south Korea japan UK da manyan qasashen dake hulda da cinikayyar ma'adanan qasa masu tsada da daraja.
A nahiyar africa JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES ya zama kamfani na daya da qasashen ke rububin karbar kaya a hannunsu bayan doke Coregeo mining company din da yayi. Kamfanin daya jima yana murza zarensa da kyau,sai gashi rana tsaka JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES yazo yasha gabansa ta ba zata,al'amarin daya haifar da takun saqa me girma a zuciyar kamfanin. Duk da fu'ad yasan da wannan......amma ya dauka normal competition da kishi ne da kan iya faruwa tsakanin kowanne kasuwanci,saidai ga mamallakin kamfanin JOE abun ba haka bane.
*_D A W O W A_*
Dubansa abba yayi bayan ya aje mug din hannunsa
"Kwanaki nawa ya rage mu tafi ne me babban suna?" Zama yayi sosai yana goge gumin fuskarsa da dan qaramin towel din da magaji(hadiminsa) ya miqo masa.
"Ba zamu wuce sati daya ko kwana biyar ba abba,hankalina yana kan anni......jikintan nan ya fiya matsawa da yawa" Yayi maganar alamun abun yana tabashi ya bayyana har saman fuskarsa. Idanu abban yadan zuba masa,har a ransa yana cike da zallar mamaki na yadda me babban suna ke damuwa da anni da rayuwarta fiye da dukkansu su ukun. Annin da abban yake ganin ba itace halitta ta farko data cancanci samun wannan qauna da kulawa daga gareshi shi din ba......annin da yake ganin kulawar da yake bata baifi ya bata kaso hamsin cikin dari ba.......ita kanta wasu lokuta tana sanya damuwa a ranta game da inda yafi karkatar da kulawar tasa sama da daya bigiren da shine dolensa,.....kuma akafi buqatar hakan daga gareshi.
"Yanzun haka ma nan da awa daya zan fita,zamu gana da ceo na Labrilliante company,zan miqa musu iya abinda zasu samu.....don abba wannan karon tunanina ya fara sauyawa" Maganar fu'ad cikin tatacciyar nutsuwar nan tasa da wani irin jan aji kamar mace ya dawo da Alhaji hamza daga tunaninsa
"Wanne tunani ne fu'ad?" Zamansa ya gyara sosai yana bawa abba dukkan kallo da hankalinsa
"Abba......a yadda mutanen nan daga kowacce qasa suke rububin siyan resources namu da muke fiddowa daga qarqashin qasar da Allah ya shimfida mana kadai ya isa ka fahimci suna amfani damu ne suna kuma amfani da damarsu......yanzu haka a daren jiya kafin na kwanta sai dana karba kira daga wani company dake japan bayan ainihin kamfanin da muke kaiwa kaya......suna taya kayanmu akan farashin da wancan kamfanin basa bamu......wannan shi yasa nayi wani nazari......abba ya kamata qasarmu ta amfana da wadannan ma'adanai masu tsada da daraja,wanda mu Allah ya mallakawa su.....abba inda a qasarsu wadannan ma'adanai suke,babu wani baqar fata daya isa ya sameshi.....it's hardly ka iya isa wajen......nayi tunanin bude babban company da zai dinga sarrafa wadannan ababen zuwa kayan qyale qyale na mata.....don dama company daya muke da na alhaji rayyan(dangantakar zuciya),shi kuma duwatsu masu daraja suke sarrafawa ba gold ko diamond ba".
Shuru abba yayi yana girgiza kai. Tabbas fu'ad din yazo da tunani me kyau daya kamata ace tuntuni sun yishi
"Na yarda da wannan tunanin naka.....to amma fu'ad qarqashin haka akwai tarin matsaloli da qalubale......"
"Na sani abba......insecurity na qasarmu ma kawai qalubale ne......amma a hakan.....ya zama dole mu raya qasarmu da kowanne qaramin chance da muka samu a rayuwarmu......tsoro da tunanin asara ko faduwa shine abinda zaici gaba da kasheta kowacce rana......bayan tsoron dauko shi akayi aka dasa mana shi a zukatanmu......kuma ake da buri da fatan ganin ci gaba da wanzuwarsa har zuwa rayuwar na bayanmu"
"Best son ever" Abban ya furta yana sakin wani irin murmushi tare da jin qarin alfahari da fu'ad din,gefe guda kuma yana taya ainihin mahaifinsa murnar samun nagartaccen yaro mara tsoro irin muhammad fu'ad din.
Qas yayi da kansa cikin girmama abban
"A tayamu da addu'a abba"
"Kullum cikinta muke"
"Allah yaja kwana,ya qara lafiya me amfani" Ya masa addu'ar da yake jinta har cikin zuciyarsa.
Agogon dake manne a bango ya kalla,sai ya miqe a nutse yana cewa
"Zan qarasa ciki abba na shirya kada na sabawa lokaci"
"Hakan yayi kyau" Abba ya fada fu'ad din yana sake burgeshi saboda yadda ya dauki alqawari da matuqar muhimmanci kaman yadda yake girmama lokaci.
A nutse ya tura qofar dakin da sallama a bakinsa,duk kuwa da yasan ba wanda zai taras a ciki. Dakine da duka duka basufi sati guda a cikinsa ba......amma har ya kama ya kuma rine da sassanyan qamshin nan nasa dake iya bawa zuciya nutsuwa da kwanciyar hankali koda cikin radadi da qunci take.
Towel din hannunsa ya rataye,ya kuma matsa gaba kadan ya ajjiye takalmin motsa jikinsa wanda daga ranar da suka tasamma barin Korea sunansa shara. Baya yawo da kaya,kowacce qasa zaije,koda kwana nawa zaiyi single yake tafiya abinsa,saidai yana sauka a qasar komai da zai buqata na amfani zai sanya a tanadar masa,yana gama amfani dashi kuma a nan zai barshi ya qara gaba.
Matsawa gaba kadan yayi gaban wata mini dispenser da tafi kama da tulun zamani wadda ke zaune saman wani kyakkyawan table kusa da mirror,ya dauki disposable cup ya matsi ruwan dake da madaidaicin yanayi ya fara sha a hankali bayan yayi tsaye gaban madubin idanunshi a kai kamar me karantar yadda yake zuqar ruwan zuwa cikinsa.
Ya gama ya ajiye saman madubin yana fidda siririyar iska yana ci gaba da kallon fuskarsa a madubin. Kyakkyawar sumar kansa data wadatu da tsafta ya taba sannan ya gangaro zuwa madaidaiciyar qasumbarsa data hade da gemunsa wadda ta zamawa fuskarsa wani lafiyayyen ado daya qara fidda zahirin kyawun fuskarsa,ta kuma qara masa wani mahaukacin kwarjini. Gemun da qasumbar daya zama topic of discussion a wajen 'yammatan da suka marmace a kansa. Kusan kowacce tana gayawa kanta namiji babu gashi a fuska ai mace ne,bata taba ganin qasumba da gemu da yakai kyan nasa ba......tsabar macewa a soyayya ne.....ko kuma zallar tsagwaron gaskiya suka fadi?.
Rigar jikinsa ya yaye zuwa sama sannan ya zareta ya ajjiyeta saman gadon,wannan ya bawa Ginannun muscles din jikinsa bayyana muraran. Muradden jikin da zai gaya maka adadin lokutan da aka bata ana bashi kulawa ta fannin lafiya da cin lafiyayyen abinci me gina jiki. Yayi taku daya don dauko bath set nashi zai wuce toilet sai ya fasa,ya dawo da baya ya dauki wata farar samsung dake ajjiye saman mirror din.
Yaga miscal amma sai ya fara maida hankalinsa ga dalilin daukar wayar,ya latsa ya fara lalubar magaji. Umarni ya bashi na abincin da zai hada masa kafin ya fito,saiya maida wayar yana shirin ajeta kira ya shigo wayar.
Cak ya tsaya yana kallon sunan dake tsalle saman wayar. MOM kaman yadda farouq ya dauka da hannunsa yayi masa saving. Kafe sunan yayi da idanuwa,wayar tana kadawa hade da zuciyarsa. Sunan yake tuna ma'anarsa da kyau cikin kwanyarsa.....wadda aka maqalawa sunan ta cancanci wannan sunan kuwa anya?......ta dace data karbi sunan?,nata ne sunan da gaske?.
Kamar bashi da idea akan yadda ake daga waya,haka yaci gaba da kallon wayar har ta qaraci ringing ta katse. Ya sake daga qafarsa zai wucs kiran ya sake shigowa. Kamar dai dazu a yanzunma haka ta gama kadawa ta katse,kira na uku kuma ya sake shigowa immediately,saidai akasin dazu,yanzu sunan daya fito akai ya banbanta dana dazu.
Lovy dovy shine sunan daya bayyana,sai ya saki qaramin murmushi yana dawowa baya kadan. Kafin ya daga sai daya kalli lokaci,tabbas ya tsaya saurarenta ya tabbatar saita kwakwashe masa duka mintunan daya tsara zaiyi a gidan ya fice zuwa Labrilliante amma hakan bai sanya ya fasa dagawa ba,ya sanya wayar a kunnensa.
Da siririyar baby voice dinnan nata tayi masa sallama. A nutse fuskarsa a sake ya amsa
"I will call you back habibty.....nan da one hour haka?"
"Yes habibee.....byeee" Ta fada cikin rashin damuwa da kuma fahimtarsa a duk sanda ya sako mata uzurinsa. Wayar ya mayar ya ajjiye yana murmushi,daidai sanda a daya BANGAREN.........
Ta daga kai ta kalleta sanda take zaune a gabanta
"Waya yake amsawa hajiya" Ta fadi tana sauke wayar daga kunnenta bayan computer ta gaya masa ana amfani da layin ta hanyar amsa wani kiran
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 32
___________________________
“Waya kuma ake amsawa?” Ta tambaya cikin wata irin isa sa ginshiri tana qanqance idanunta,qwayar idanun nata suna kan wadda tayi maganar. Kai ta jinjina mata cikin bata tabbaci
“Eh haka ne”. Juyawa tayi ta zauna sosai tana fesar da iska me zafi daga bakinta. Ta qanqance idanu sosai tare da zubawa guri daya idanu,abinda zai baka tabbacin akwai wani radadi me yawa da take ji daga cikin zuciyartata
“Alamu kenan suna nuna yaga kiran,nice dai…….nice dai da bazai amsa wayata ba,nice dai da bazai saurareni ba sai a sanda yaga dama ko kuma aka bashi umarni?” Ta qarashe maganar ta hanyar yiwa kanta da kanta tambayar. Tambayar da bata haifar mata da komai ba sai qarin qunci da bacin ran da ya sanyata miqewa tsaye.
Hannunta ta dunqule ciki juna,ta fara kai kawo tana naushin tafin hannunta da daya hannun data dunqule waje guda. Ba shakka tayi sake ba dan qarami ba,ba shakka kuma hajiya mariya tana son jefa kanta tsakiyar shingen da ba nata ba. A baya tayi tarin ayyuka game da hakan,amma idan har tace taga nasara tattare da hakan to tayi qarya me yawa ma,zata iya kiran ayyukanta na baya da JIYA I YAU,tana tsaye a waje daya babu sauyi ko qanqani,zata zuba idanu ne abubuwa mafiya daraja da kima a rayuwarta…..kuma mallakinta amma ace suna ci gaba da subuce mata?,suna ci gaba da zama haramiya a gareta?,shin zata yarda da zamowa ‘YAR RAKIYA ko kuma taci gaba da wanzuwa a mazaunin ‘yar kallo?.
“Ba zata sabu ba!” Ta furta a zabure sannan ta juya da sassarfa tana daukan mayafinta dake yashe saman kujera
“Tashi samira muje” ta bawa hadimar tata umarni,wadda ke zaune tun dazu guri daya tana duban kai komo da maganganun da takeyi ita daya
“Ina hajiya?” Ta tambayeta murya a lanqwashe. Tayi imanin tunda har ta buqaci fita irin wannan afujajan ba shakka ba alkhairi a cikinta sam
“Gidan alhaji hamza!” Ta bata amsa a tsawace da salon abun nan da ake cewa haushin kaza huce kan dami. Tsam ta miqe tana gyara daurin zaninta sannan ta wuce da sassarfa zuwa shiyyar dakunansu don dauko hijabi.
Cikin jerin amintattu kuma lafiyayyun dakunan da mansion house din na alhaji hamza kibiya ya mallaka. Zaune take tsakiyar wani lallausan rug dake a gefe daya na dakin wanda aka masa rukuni da lausasan sofas qwaya uku da suka zamewa wajen tamkar wani dan qwarya qwaryar falo ne na cikin bedroom. Wani irin lafiyayyen daki ne da ba zai barka kasan safiya ko dare ba,zafi ko sanyi,damuna ballanta rani ba muddin ka kasance wanzajje a dakin.
Daga saman rug din take zaune saman abun salla da zai baka tabbacin bata jima da kammala sallar walaha ba. Salla ceda bata taba wuceta a rayuwa muddin ba wani qaqqarfan dalili ya gifta ba,tun zamanin quruciyarta har kawo yanzu da girma da shekaru suka hau kanta. Shine kuma ya same mata sila da tsani na dawowa rayuwa hamza a shekarun baya,a sanda ta yanke zato da tsammani daga sake rayuwa dashi da kuma yaranta da suka zame mata sanyin idaniyarta.
Wataqila nutsuwa da kamalar da fuskarta ta wadatu dashi yana da alaqa da wannan din,yawan ibada,yawan bautar Allah,yawan azumin tadawwu’i da babu wanda yayo gadonta a wannan fannin qafa da qafa irin muhammad fu’ad.
Akwai haske sosai saman fuskarta,tana saye da atamfar chiganvy gold mekauri kyau da asalin tsada. Jikinta lullube da mayafi me kauri,yayin da yatsarta ke maqale da qaramin carbi irin na ma tsawa.
Daga gefanta saitin kafadarta shine a kashingide,kana kallonsu zakasan magana sukeyi,magana kuma irin ta da da uwa,hira cikin nutsuwa qauna da kuma kulawa
“Nikam saddiq……sake kiramin wayata mana,jakata tun ranar da akayi asibiti dani ban sake ganin gilmawarta ba,akwai muhimman abubuwa a ciki,harda kudaden Amna data bani ajiya” idanu ya zaro sannan ya miqe yana zama sosai
“What?,anni?,dollars fa?”
“Wallahi sadiq” ta fada a nutse.
“To Allah ya tsananta rabo,don auta ta saka buri akan wannan ajiyar,naji tana lissafin abinda zatayi dasu idan ta dawo” ya fada yana cusa hannunsa a aljihu yana laluben wayarsa. Fuskarta anni ta shafa tana fadin
“Idan har ba’a gansu haka zata haqura ai,tsautsayi da qaddara tana wuyan kowane bawa”.
Shuru sukayi dukkansu suna saurareb sautin din…..din,sautin dake gaya musu lallai kiran ya isa ga wayar anni dake tare da documents dinta da kuma sauran kudade masu kauri cikin jakar.
Kamar cikin mafarkinta ta dinga jin wani sauti mara qarfi yana ratsa kunnuwa zuwa kwanyarta.
Shuru tayi ba tare data motsa ba,daddan ring tone din mara hayaniya yana tasowa can qasa qasa,da alama akwai abinda ya sake rage kaifin sautin.
Sai data fahimci ba cikin bacci bane sannan ta qarasa bude fararen idanunta da suka qara girma saboda bacci. A hankali ta yamutsa fuskar tata sannan ta sanya hannunta ta maida lallausar sumarta me tsaho data rufe rabin fuskarta baya,ta juya daga rub da cikin da tayi zuwa rigingine sannan ta miqe ta zauna sosai tana wuwwurga idanunta zuwa kowanne sashe na dakin don gano ainihin ta inda sautin yake fita.
Ba kowa a dakin,don tuntuni su huda sun gama shiryawa sunyi abincin safe kaman yadda suka saba sun wuce makaranta,don ko idanunta bata iya budewa tace dai kawai su buda jakarta su dauki kudin makaranta su kuma ja mata qofan idan sun fita.
Fes dakin yake kamar kullum kamar kuma ko yaushe,sai ta saka hannunta ta tattare gashinta ta qulleshi tsakiyar kanta idanunta ta tsaiwa kan medium luggage din dake cike da tsarabar da aka kawo mata,wadda ko samun damar budeta batayi ba.
Tayi matuqar gajiya a jiyan,tana fita kusan kowacce rana.....amma bata yin awanni masu yawa kaman haka a wajen. Komai nata yana da lokaci tsari da kuma iyaka. Ta zube fararen qafafunta saman qaramin carfet data sanya musu daga gaban gadajen nasu saboda sanyin tile,ta jawo dankwali me santsi ta daura sannan ta miqe tana isa gaban luggage din.
Sai a sannan ta kuma gasgatawa daga cikin qaramar handbag dinta sautin ke fita,jakar ma da gaba daya ta mance da ita tun ranar data je musu siyayya ta dawo,ko tarkacen ciki bata kwashe ba. Hannu ta zura tana laluben meye yaketa qara din haka cikin jakar,sai kawai ta wuce gaban gadon ta zazzage jakar gaba daya saman gadon.
Kyakkyawar purse baquwa ta gani cikin jerin tarkacen dake cikin jakar wanda ta tabbatar duka nata ne. Onion color me ratsin maroon a jiki. Hannu ta miqa ta jawota,ta dagata a hannunta tana jujjuyata cikin mamakin a ina ta samo ta?,kuma ta waye?,tun yaushe take cikin kayan nata?. Kamar anason sanar mata da amsar duka tambayoyinta ne sai wannan siririn sautin da ya tasheta a bacci ya sake kadawa daga cikin jakar.
Kai tsaye ta zuge jakar,ba wani ba wata ta sani waya ce. Wayace qila da take da alaqa da mamallaki ko mamallakiyar jakar.
Wata siririyar Samsung ta gani,ta sanya hannu don cirota da gaggawa gudun kada kiran yanke,take sabbin dollar din dake maqale a zip na daban na jakar suka biyota suka fada saman cinyarta hade da qananun hotunan passport. Ba wannan bane a gabanta,don haka batabi ta kai ba ta fara duba sunan dake yawo saman screen din wayar
MUSADDIQU NA....shine full name din dake jikin number. Tadan tsaya tana sake duba sunan da kyau tare da bitar karantashi,sai kuma tadan tabe baki kadan sannan ta daga kiran ta Kara wayar a kunnenta
"Alhamdulillah.....an daga anni" Musaddiq ya fada yana sanya wayar a kunnensa.
Shuru tayi tana sauraren motsin dake fita daga daya bangaren,kafin daga bisani sallamarsa ta maye gurbin shurun. Muryarsa a nutse dake dauke da kamala yayi cikakkiyar sallama data sanyata motsa bakinta da tata siriryar muryar tana amsa sallamar.
"Barka da warhaka" Ya fada a nutse.
"Yauwa.....barka" Itama ta amsa masa a taqaice
"Don Allah idan ba zaki damu ba zan iya tambayarki wayar nan ta waye?" Banbarakwai taji tambayar tazo mata,har sai data sake duba sunan dake jikin wayar,amma yanayin yadda muryarsa ke nuna kamalarsa da nutsuwarsa ya sanya tayi gyaran murya daban
"Kaman sunan me kiran dana gani akan wayar yana da alaqa me qarfi ko kuma mafi kusanci dame wayar ko?". Murmushi ya saki,yadda tayi maganar cikin fasahar harshe da tsari sai yaji ya burgeshi,hakanan kuma a karon farko ya gano muryar,yakuma dago ko wacece
"Hakane ranki ya dade.....idan na canka dai dai.....kamar mutuniyar kirkin nan kuma baiwar Allahn nan data ceci rayuwar mahaifiyarmu ko?" Dan jim tayi tana son gano ma'anar zancansa,don tuni rayuwarta taci gaba daga inda ta tsaya,tuni ta shiga wani babin kuma na daban,ta manta abinda ya faru dazu jiya bare shekaran jiya.
Haka policy na rayuwarta yake. Ba kasafai take bawa komai gurbi cikin rayuwarta ba bare ta hadu da traffic akan dukka plans nata da kuma tunaninta ba.
"Dattijuwa me asthma a masallacin HGMS store?"
"Oops....." Ta furta a hankali,yanayin daya sanya musaddiq sakin murmushi don ya fahimci abun ya kwanta mata
"Kayi haquri don Allah,ka kuma nawa mama haquri,na hada da purse dinta ne a cikin kayana bisa rashin sani,bansan ma da ita din ba sai yau da aka kira"
"No....karki damu......mune ma muke fata Allah yasa bamu takuraki ba....."
"Zaku iya karbanta a jambulo third gate.....link 5" Abinda ta furta kenan ta yanke wayar,daidai sanda anni ta miqa hannu da zummar karbar wayar su gaisa.
"Ya ka katse wayarwayar inaso mu gaisa nayi mata godiya da ban gajiya"
"Daga canne anni ta yanke......" Ya bawa anni amsa yana duban wayar tare da mamakin yadda take magana da bada amsa haka cikin taqaice komai
"Babu matsala.....amma zanso sake ganinta ko magana da ita......zanso nayi mata godiya sosai,dukan wanda yayi saving rayuwarka ai baka da sama dashi.....mutum ne me matuqar kima da martaba cikin rayuwarka.....har yanzu ina iya jin sanda ta rungumeni sosai a jikinta kamar ta sanni......sai na dinga jin kamar amna ke riqr dani......ta damu sosai kamar mahaifiyarta ce a cikin halin" Ta qarasa maganar tana duban fuskar musaddiq,fuskarta kuma na nuna abubuwa da dama da zuciyartata taji. Zamanshi sosai ya gyara yana murmushi.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
PAGE 33
"Ni kaina anni ina iya hango sanda taketa masifa da fada da gaske wai mun banzatar da rayuwarki,bamusan illa da kaifin ciwon ba......amma fa anni kaman ina zaton.....anya bata da ciwon itama ko wani nata?" Yayi tambayar yana duban anni kamar annin tasan zahirin maganar.
Cikin isa izza da jin cewa takai kowanne qololuwar mataki na rayuwa ta ratsa babban falo kuma na farko na gidan,ta ratse dukkan wasu hadimai da kuma masu aiki na farkon gidan,falon farko har ta dangane da falo na biyu.
Kowanne taku idan tayi idanunta suna sauke zazzafan kallo ne akan kowanne alatu da kuma jayan jin dadi na rayuwa dake kowanne muhalli na falon. Kowanne abu da idanunta zaya sauka akai tana debe kallonta ne daga kanshi cikin jin wani irin zafi da quna gami da radadi idan ta tuna cewa MUHAMMAD FU'AD ne ya yishi tare da gumin dan uwansa MUSADDIQ.
Da wannan tunanin ta tsaya tsakiyar falo na biyu hannayenta riqe da qugunta tamkar qaramar yarinyar da take ganiyar fitsara da kuma jin cewa tana daidai da kowa.
Ko ita dinma a yanzun kusan hakan take. Tsaiwarta a falon qiris ya rage dukkan wani ganuwar haquri nata kawaici da yakana da takeyi su qare,haquri da kawaicin da take ganin tunda tazo duniya bata taba yiwa wata halitta irinta ba
"Amina nakeson nayi magana da ita" Ta fadi kanta tsaye sanda daya daga cikin hadiman dake da alhakin kula da wannan sashen ta qaraso.
"Eyeee?" Me aikin ta tambaya cike da mamakin yadda ta kirayi sunan dattijuwar data zame musu baya goya marayi haka gatsal,babu sayawa ko qanqani,duk kuwa da cewa zasuyi sa'annin juna,amma a garesu kiran ainihin sunanta wani baqon abune da yake jimawa bai faru ba
"Nace AMINA nake buqatar gani.....uwar farouqu da saddiqu" Ta maimaita a wannan karon da madaukakiyar muryar data sanya hadimar maida hankalinta ta hanyar dubanta da kyau,sai kuma taja baya kadan tana cewa
"Inji wa zaa ce mata?" Ta tambayeta tana sake kallonta sosai
"Kice mata uwar Muhammadu da musaddiqu" Sunayen data furta din ya saka hadimar sake dubanta da kyau,saidai bata ce komai ba don bata da hurumin cewa komai din,ta taka a hankali ta kama stairs tana hawa a hankali don isar da saqonta ga anni.
Kafin anni ta furta nata hasashen knocking dinta ya dakatar da firar tasu. Firace da yawancin lokuta musaddiq din yakan qaraso har quryar bedroom din anni ya tayata don debe mata kewa lokaci lokaci da hanata zaman kadaici. Duk da cewa gidan cike yake da hadimai wadanda suka aiki qarqashinta ta kowanne fanni da take da buqata na rayuwa. Hatta hirar akwai masu tayata cikin masu aikin,wadanda aikinsu kenan,gwanaye ne wajen iya hira da mutum,debe masa kewa da sanyashi nishadi......musamman FU'AD ya daukesu aiki saboda haka kawai,amma ko kusa ko alama hira dasu bai kama qafan hira da yaranta ababen soyuwarta ba.
"Waye?" Musaddiq ya riga anni tambaya
"Badawiyya ce"
"Bismillah qaraso" Anni ta bata umarni tana gyara zamanta saman lallausan abun sallarta.
A nutse kuma cikin girmamawa ta qaraso cikin dakin. Ta tako a hankali zuwa gaban annin ta tsugunna
"Baquwa kikayi anni" Ta fadi kanta a qasa
"Baquwa kuma?,daga ina?" Tayi tambayar cikin dan mamaki,saboda yau din ba ranar ganin baqi bane,tana cikin ranakun hutunta,sannan tun bayan dawowarta ma daga asibiti fu'ad ya hana kowa ganinta,yace saita murmure ta huta tukunna.
"Ban dai kai ga gane fuskarta ba.....tadai ambaci asalin sunanki,tace kuma a gaya miki babar fu'ad da musaddiq.......kuma...." Tadan fadi tana daga kai kadan ta dubi fuskar musaddiq da ya tattara dukka hankalinsa akan waya,har sai da yaji sunansa ya fito cikin zancan
".....suna dan yanayi da yallabai musaddiq kadan". Dukkaninsu daga ita har musaddiq din kowannensu ya fahimci wace......kowannensu ya gane wace take nemanta.
Fuska annin tadan saka kadan tana murmushi
" Banda abun badawiyya,ai ba baquwa bace 'yar gida ce itama.....ki gaya mata ta hauro.....ta qaraso zuwa falon sama".
"To anni" Ta amsawa anni din a ladabce tana miqewa don isar da umarninta,saidai kuma a can qasan tata zuciyar mamaki ne kwance. Mamakin yadda annin ta bada umarnin qarasowar matar zuwa falonta na qarshe wanda daga shi sai dakunan baccinta.....matar da sam bataga ruwa ko alamun kirki a tattare da ita ba,tun daga yanayin kallonta har zuwa lafuzzan bakinta,to amma menene ALAQARSU DA YALLABAI FU'AD DA KUMA MUSADDIQU?,tambayar da bata da amsarta kenan daidai sanda ra qaraso falon.
Tana nan a tsaye inda ta barta,kamar dazun ba abinda ya sauya daga yanayin tsaiwarta a cikin falon,zuwaira na daga gefanta bayan tayi amfani da sakannin hawan badawiyya sama da saukowarta ta sake yiwa zuciya da ruhinta wani karatu da sake dorata akan wani bigiren.
"Tace ki qaraso saman" Badawiyya ta furta a ladabce kaman yadda tsarin aikinsu yake cikin gidan girmamawa ga duk wani baqo da zai sanya qafafunsa cikin gidan alhaji hamza kibiya,walau me dogon zangon zama,ko kuma me gajeriyar baquntar da bata wuce awanni zuwa mintuna
Kai ta jinjina,eh yana da kyau hakan,ko ba komai a karon farko idanunta zasu ganeta komai da kyau......idanunta zasu gane mata yadda akayi amfani da kudi da jini da kuma quruciyar d'iyanta don shimfida kyakkyawan rayuwa ga wasu.
Cikin jin isa taqama gami da izza take taka kowanne step na stairs din,idanunta na sake qididdige mata adadin dukiyar da aka narkar wajen ginin gidan tare da qawatashi da kayan alatu dana alfarma na kecewa sa'a. Irin alatun da ita shine nata mafarkin,irin qawar da shine burinta DUNIYARTA. Yau ga komai a kusa......komai a dab da ita da sunan mallakinta.....amma wani taqi da kuma taku kadan sun hanata isa ga wannan bigiren. Iya lallausan carpet din da aka mamaye ilahirin stairs din dashi aka lullube tsadajje marbles din dake shimfide don kada anni taji sanyi cikin jiki da qashinta......duba daya zakayi masa kasan asalin tsadar da yake dashi. Wani abu ya dinga taruwar mata yana tsaya mata a wuya,wutar bacin rai taba taso mata kamar ta hallakata.
Sai da badawiyya ta fice daga dakin sannan anni ta janye idanunta ta maida kan musaddiq. Suna hada idanu sai ya janye dubansa daga kan annin ya mayar ga wayarsa. Ta tabbatar yaji komai kuma shima ya fahimci wacece tazo din. A karon farko kenan data fara tsomai qafafunta cikin gidan tun bayan data sake bayyana cikin rayuwarsu karo na biyu.
Yanayin yadda ya share din kamar baisan meke wanzuwa ba yadan sanyata murmusawa. A sannu a sannu hali da dabi'ar dan uwansa tana masa naso cikin jiki. Saidai bata da tabbas din shima dama yana da dabi'ar ne ta iya shariya dayin kamar baiga abu ba?,ko kuwa kuma daga bayane zama da madaukin kanwa ya sanyashi koya?.
"Musaddiq" Ta kira sunansa kai tsaye
"Na'am anni,akwai wani abu da kike buqata ne?" Yayi tambayar badon haka bakinsa yakeso ya fadi ba. Kai ta girgiza har yanzu tana duban fuskarsa. Cikin ranta tana jin inama wannan dukka tarin kulawar,.....wannan nuna damuwar da bata muhimmancin zasu rabata ko yaya yake da matar da suke kira MAAMA?. Saidai ta sani,TUN RAN GINI tun ran zane.....bakin alqalami kuma ya riga ya bushe......dawo dashi bisa zarafin aiki da damshinsa don gamsar da buqata kuwa aiki ne ba na yanzu yanzu yau ko gobe ba
"Ba buqatar komai......amma bakaji wadda tazo bane?" Ta sake tambayarsa
"Naji anni.....maama ce" Ya amsa mata kai tsaye. Kai ta sake jinjinawa,ta buda baki zata sake magana amma ya rigata
"Maama ce.....kuma bani da tabbacin alkhairi ya kawota" Ya sake fadi idanunsa na nuna akwai wani abu daya taba zuciyarsa. Fuska annin ta sauya tana rage adadin saketa da tayi a baya tadan tsuketa kadan
"Wato kaima kanason bin sahun dan uwanka kenan musaddiq?" Ta Tambayeshi cikin tsuke fuska. Kai ya jinjina sannan yakai hannunsa ya ture hularsa baya yana shafar sumarshi
"Ba haka bane anni.....akwai wasu abubuwa da wasu lokuta suke iya tasowa dan adam a matsayinsa na dan adam din,duk kuma yadda mutum yaso ya ture ya goge ko ya shafesu ba zasu taba barin zuciya da ruhi su huta ba".
" Ya isheni......tashi muje" Ta fada tana yunqurawa sannan ta miqe tsaye tana gyara lullubinta.
Tana sanya qafarta cikin falon qofar bedroom din anni dake falon ya bude. Anni ce a gaba musaddiq da ya bude mata qofar yana daga bayanta.
Kyakkyawan kallo ta sauke musu a sanda take tsaye tsakiyar falon tana kallon yadda dukiya ke magana da kanta cikin falon. A iya rayuwar da tayi.....a iye shige shige gami da fadin tashin da tayi cikin duniya tasan abu me daraja......tasan abu me tsada kamar yadda tasan abu me aji,don haka bata buqatar batawa kanta lokaci wajen sake nanatawa kanta a nan dukiyar da yaronta ya mallaka take tafiya,da gaske ne.....ba sharri bane.....hakanan ba cikin labarai na qanzon kurege bane.
Sanda suke takowa zuwa falon yana biye da anni saita gaza dauke idanunta a kansu. A hankali taji tashin hankalinta yana sake qaruwa. Kana musu duban farko a yadda suka fito shi da anni din baka isa duk masifarka kace ba diyan cikinka bane. Musaddiq ne.....musaddiq din da tun farar safiyar jiya bata sake sanyashi a idanunta ba bayan zaman jiransa data dinga yi na yazo suci abincin rana ko dare tare,abincin da ta yiwa tanadi na musamman,ta barar da kudade sosai a kanshi duka zai gashi ya tashi a tutar babu,sai gashi a yanzun tare da matar ya zame mata tamkar wani body guard a sanda nata idanun suke mararin son ganinsa tun jiya.
"Bismillah mana maama ku zauna" Anni ta fadi fuskarta lullube da murmushi sanda musaddiq yake dauke mata pillows din dake saman kujerar saboda taji dadin zama.
Tana jin kamar ba zata zauna ba,to amma kuma wani sashe na zuciyarta idan bar bata zauna daidai da nata zaman da tayi saman kujerun da tayi imani da dukiyar d'anta aka siyesu ba....lallai ta sake zama me daraja a kanta.
A nutse ya qaraso gabanta ya kuma rusuna har qasa a ladabce yana gaidata
"Barka da safiya.....mun tashi lafiya?"
"Lafiya qalau......ya mukayi da Kai jiya?" Ta jefa masa tambayar tana son boye fushinta don kada amina ta fahimci tarin galabarta a kanta ta kuma karanci rauni da ciwon da ta haifarwa zuciyarta.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 34
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 34
"Kiyi haquri......jiya mun fita da hamma farouq ne,mun samu baqi masu yawa a company,so kuma nike kula da fitar da kayan da kamfani ya sarrafa dole na tsaya har dare muka kammala muka sallamesu". Dubansa take sosai,sam harkar kayan gona da kayan abincin da yakeyi batayi mata ba,gani take kamar akwai wata maqarqashiya da shiri cikin abun. Taso ace shima kamar dan uwansa harkar diamond da gold yakeyi......ga kayan masarrufi da ma'adanai me zaa tsinta a kayan abinci?.
"Kai wai me ya hanaka bin sawun dan uwanka ne ma?,bayan duk duniya kaine mutum na biyu bayanni da bashi da kamarka?,don me zaka tsaya kamfani harkar kayan abinci?,kana zaune a Nigeria ya dauki bare ba dangin iya bana baaba ya tsallaka dashi yana nuna masa manyan harkoki kai kana zaune kana fama da sabgar shinkafa?". Boom yaji furucin nata ya masa tsawa saman ka,sai yakejin kamar ta samu ruwan zafi tana kwarara masa tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafukan qafafunsa..
A dabarance ya jefa idanunsa sashen da anni take,sai yaga kwata kwata hankalinta da idanunta baa kansu yake ba,ta aza dukka idanunta ga makekiyar tv plasma din dake aiki suna watso labaran abinda ke faruwa da mutanen Palestine. Yasan sarai taji,tana da wani irin matsanancin kara,ba sanin jiya ko yau ya yiwa anni ba......ballantana tana zaune a falon.....da zazzafa kuma kakkaifar muryar da maama take magana zaiyi wahala ace koda a bedroom dinta take ace bataji komai ba.
"Kalleni nan" Ta fadi cikin nuna zafinta ainun tana karantar yadda yake kaffa kaffa da kunnuwan anni
"Ka tashi ka bani guri,kuma indai ni na dauki cikinka.....nayi naqudarka,na kuma haifeka to tabbas anjima inason zama dakai.....dole nasan me kuke ciki don ba wani ya haifamin ba"
"Wannan gaskiya ne.....ai ita uwa tafi gaban komai" Zuwaira ta fadi tana satar kallon musaddiq daya miqe. Kallo daya yayi mata ya wuce yana yin gaba don bashi da lokacinta,hasalima baisan fuskarta ba baima gane wacece ita ba.....duka bama wannan ke damunsa......zafafan kalaman da ta soma fesarwa gaban anni su sukafi sanya masa damuwa,tun yanzu kenan?,me zata fada a gaba?,me kuma tazo dashi?.
Wannan tunanin ya tilasta masa jan burki akan rukunin kujerun dake dab da qofar sauka daga stairs din. Yana jin kamar ya zama dole ya tsaya din,kamar idan ya tsaya din zai iya tsaida wata barnar da dukka zata fito daga bakinta.
"Musaddiq......sauka zuwa qasa" Anni wadda tana kallonsa cikin qasa da second biyar ta karanci abinda yake shirin aikatawar. Idanunsa ya zubawa anni,ta karanci yana roqon ta barshi ne amma saita wofantar da roqon ta sake maimaita masa
"Ka wuce zuwa aikinka.....Allah ya bada sa'a,ka dawo lafiya" Ta furta a nutse kaman yadda ta sabawa kowannensu addu'a a kowacce rana,a fili ko kuma a boye.
Idanuwan mutum uku ne suka rakashi har sai daya kufcewa ganinsu. Nata idanun ta janye tana jin suna mata yaji yaji. Wato abun har yakai matakin da ita bata isa ta basu umarni ba subi?,abun yakai lalacewar da maganar wata itace gaba da tata maganar?.
"Barka da shigowa mariya.....fatan mun tashi lpy". Anni ta furta fuskarta qunshe da murmushi.
"Ba gaisuwa ce ta kawoni ba.....zuwa nayi na tambayeki sai yaushe zaki sakarmin yara na su dawo gareni kamar kowacce UWA?" Sautin kalmar uwa din yadan bada amsa kuwwa kadan cikin falon yayin daya dauke kowanne motsi da yake gilma falon na wasu sakanni. Tamkar me nazari haka anni ke kallon fuskokinsu ita da zuwaira,sai kuma ta gyara zama tana cewa
"Gwara da kika ce UWA baki ce MAHAIFIYA BA......wanne abu aminatu tayi kuma?" Tayi tambayar hankalinta kwance,tamkar yau ce rana ta farko data fara sanin wata me suna mariya kaf rayuwarta.
Idanu ta zuba mata kamar yadda itama ta zuba mata nata idanun. Babu komai cikin tambayar annin face zallar rainin wayo da kuma rainin hankali. Tana cewa yanzu yanzu tayi mata tambayar amma buqatar maimaici takeyi kenan?.
Tattara dukka nutsuwarta tayi da kuma tarin kalaman dake cike fal a bakinta,tanaso a yau ko yaya ta fanshe haushi da takaicin anni dake kwance a ranta.....haushi baqinciki da kuma Takaicin da suka jima suna ci mata rai.
"Zuwa yanzu ya kamata ace kinsan cewa da Muhammadu da musaddiq nice na haifi abuna ba kece kika haifamin su ba......zuwa yanzu ya kamata ace kin warware duk wani qulli da kikayi a kansu....kibarmin yara na na moresu kamar yadda kowacce uwa ke morar 'ya'yanta......yanzu har takai matsayin da ni zan daga kira na kira fu'ad yaqi dagamin kira saboda baqin kilbibinki da qullinki ameena?" Qaramin murmushi anni ta saki tana dan motsa idanunta sannan ta waresu akan maama. Tana mamakin maama din sosai a yadda take da qarfin halin lissafo abubuwa irin haka. Kamar ma dai ta manta ita din WACECE. Kamar ta manta su waye yaran da take ikirari gami da!kiransu da sunan 'YA'YANTA.
A dukka zancanta babu wani abu daya dameta ko ya bata mata rai,don bawai yau ko jiya tasan mariya ba,ba kuma shekaran jiya ko waccan shekaran jiya ta gama fahimtar duk wani karkataccen saqo shagube da jirwaye da kamar wanka da mariya ke aike mata a fakaice ba. Saidai ko da wasa bata taba daga mata hankali kota dadata da qasa ba,tunda ta sani cewa tun ran gini tun ran zane......hakanan mariya din ta riga tabar kari tun ran tubani,duk wani da zatayi a yanzu bazai zame mata damuwa ba,don akwai idanun data sanya take kallonta dasu.
Abu daya ne da taji bataji dadinsa ba shine abinda fu'ad din yayi. Qin daga kiranta,wanda ita kanta ba zata daga masa qafa ba akan hakan,kuskure ne babba wanda yana daya daga cikin abubuwan da take yaqi dasu da son canzasu akai zuwa wani abu na daban,saidai akance mahori ya riga mabada hali.
"Wannan tsohon zance ne da duniya ta riga ta shaidashi......meye abun daga hankali,tada jijiyar wuya ko wahalar da baki wajen maimaitamin shi mariya?,fu'ad danki ne halak malak da ya fito daga tsatsonki,haka ma musaddiq.......qaddara ta jefosu hannuwana da taimakon salon taki rawar da kika taka,shin meye laifin ameenatu a ciki?,rubutacce ne wannan,duk wanda yayi lissafinsa ba daidai ba dole idan yazo kwashewa ya diba ba daidai ba......ba wanda ya tayaki lissafin bare kiyi tunanin shi ya miki dungushe" Sosai martanin anni ya tabata. Ta sani magana ce take maida mata a kaikaice wadda bata buqatar dogon bayani ko kuma fashin baqi.
Murmushi maaman ta saki tana kada qafarta
"Shi lissafi idan akayishi ba daidai ba......akwai hanyoyin gyaransa don a samu a diba yadda ya kamata,akwai rance akwai ciko akwai kuma bashi.......mariya nake har yau har gobe ameena" Idanunta anni ta janye daga kanta tana sakin murmushi. Mariya na daya daga cikin halittun dake bata mamaki a rayuwarta kaf.....saidai ta wani fannin sai taga lamarinta ba abune daya cancanci a tsaya ana masa mamaki ba. Landline dake kusa da ita ta jawo ta soma latsa wasu lambobi wanda bugu biyu kawai aka daga.
"Kiyimin kiran amna kice ta kiramin yayansu tace ya kirani yanzu yanzu"
"An gama" Aka bata amsa a gaggauce cikin zaquwa da son isar da buqatarta.
Kife wayar tayi tana duban maama hankali kwance
"Kada ki tsananta sanya damuwa a ranki mariya......komai juyin lokaci da zamani fu'ad da farouq ba zasu taba canzawa daga sunan 'ya'yanki ba......"
".....na jima da sanin hakan" Ta katsi numfashin anni tana miqewa
"Kada ki tsammaci cewa gazawa kasawa ko kuma rashin isa ta sanyani bi ta hannunki don nayi magana da fu'ad......a'ah.....nayi hakanne don ki sani.......daga rana irin ta yau hakan ba zata sake faruwa ba.....don zaki rasa dama irin wannan ne har abada.........a sannu zaki manta da cewa kin taba sanin wani me suna fu'ad ko musaddiq......wannan saqon nakeson isar miki".
Yadda bata motsa ba hakanan bata ce da ita komai ba,har zuwa sanda ta juya tana ficewa zuwaira tana biye da ita a baya.
Duk da ranta baqiqqirin yake amma ta wani fannin tana jin wani farinciki yana shigarta. Ko banza,ko kuma yaya ne ta amayar mata da wani sashe na maganganun da suke cizo zuciyarta. Cikin miliyoyin maganganun da take buri da fatan amayar mata yau din ta fesar mata da kadan daga ciki,saidai kuma ta kasa samun salama ko qanqani cikin ranta,musamman sanda take ratsa stairs tana saukowa tana ratsa falon farko na anni din.
Bata da wani buri a rayuwa daya wuce dukka wannan daula dukiya da kuma mulki su dawo qarqashin kulawarta,su dawo qarqashin mulkinta,su dawo qarqashin umarninta.
Tunda ya sauko ya kasa wucewa yabar gidan kamar yadda anni ta umarceshi,kawai sai ya samu kansa da samun waje ya zauna saman tsadaddu kuma lafiyayyun sofas din da suka zamo ado wa falon. Kujeru ne na musamman kaman yadda kowanne falo na gidan ke qawace da nashi kalar kujerun.
Ba komai yakeyi ba,kawai yana zaune ne hakanan,saidai kuma zuciyarsa tayi nisa da gangar jikinsa. Tun yana da shekaru biyu a duniya yasan wacece ita,yasan abune me matuqar wahala ta iya zama da anni ta sauko lafiya qalau ba tare data gasa mata maganganu masu ciwo ba. Damuwar anni damuwarsu ce,sukan gwammace ciwo bacin rai damuwa ko jarrabawa ta samesu amma tabar musu anninsu ta zauna lafiya.
Motsi da alamun takun mutum da yaji yaja hankalinsa,ya waiwaya da sauri daidai sanda ta kammala sauka daga stairs din take doso ainihin falon ta yadda zata cimma qofar fita waje.
Da idanu ta kafeshi har zuwa sanda ta cimmasa a inda yake tsaye goye da hannayensa.
"Ka gaza tafiya ko saboda kada kabar wajen na bata ran qanwa ko yayar ubanka!" Ta furta a zafafe. Kadan zuwaira ta matsa hannuwanta
"Da ruwan sanyi ma saika dafa dutse......kiyi a hankali" Ta furta mata qasa qasa. Kalamanta sun samu gurbi a zuciyarta saidai basu samu damar sauketa daga fushinta ba gaba daya,don haka taci gaba da kallonsa a sanda yake tsaye a gabanta ba tare da yace komai ba. Kimanin mintuna biyu kafin ta furxar da iska daga bakinta sannan ta juya tana barin falon zuwairan na biye da ita.
Sanda suke ratsa farfajiyar farko ta gidan zuwa na biyu.....duk da maganganu da zuwaira keyi wanda duka akan abinda ya faru cikin gidanne amma hakan bai dauke hankalinta daga tarin zalla zalla kuma galla gallan motocin dake ajiye qarqashin sashen ajiyar motoci na gidan ba.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 35
Ta sauke wata qatuwar ajiyar zuciya me nauyin gaske
"Bugatti,rolls Royce,Lamborghini Aventado,Brabus G_wagon,Mercedes Benz,BMW......zuwaira?" Ta qarashe lissafin jerin motocin da idanunta suka gani din tana waiwaya ga zuwairan
"Na'am?"
"Kinsan adadin lissafi da qiyasin kudaden wadannan motocin kuwa?,kinsan waye da waye matsayi da matakin rayuwa suke cillashi zuwa ga mallakarsu?,kinsan wanne me tsananin sa'ar ne cikin duniya yake da rabon samun wadannan motocin?.....zuwaira ace d'ana keda su amma ya rasa a gidan da zaya barni sai a wannan wulaqantaccen gidan?" Ta fadi da mugun zafi tana nuna gidan da suke tsaye a gabansa da yatsa.
Kamar yau ne zuwairan ta saba ganin gidan,kamar ba cikinsa take kwana take tashi ba,ta daga kai tana duban gidan da maama din ke kira da wulaqantacce.
Kyakkyawan gini ne da aka yishi madaidaici me dauke da madaidaiciyar harabar dake dauke da mota qirar range Rover guda biyu duka don biyan buqatar matar gidan. Wadatacciyar haraba dake dauke da dogayen katangu da kuma yalwataccen gate dake qarqashin kulawar mutum daya wato malam saidu. Akwai qaton kitchen da aka zuba masa dukka kayan tasarrufin girki kamar kitchen din 'yar bana bakwai,kitchen din dake maqale da store dake danqare da kayan abincin da yafi qarfin cikin mutum ashirin da zasu shekara kullum suna ci kuma ana kyauta dasu.
Babban falo me dauke da dining area......bedrooms guda hudu da kowanne aka qawatashi da kayan gado 'yan turkey masu asalin kyau da tsada,kaman yadda aka qawata falon da kayan turkey din hatta da curtains da carpet kuwa. Wuta 24hrs,engine wanki dana guga,Ac hade da fanka,me aiki guda daya a cikin gida,da kuma me kula da farfajiyar gidan namiji baya ga me gadi malam saidu. Albashin naira dubu dari duk wata ga mamallakiyar gidan.
Nisan buri......zurfafa da kuma zarmewa a son zuciya.....take laifuka,dannesu da manta abinda baya ta haifar ya lullube idanunsu su dukka biyun
"Indai zaa yi qiyasi bisa irin nau'in arziqin fu'ad.....idan dai zaa yi duba da gidan daya sanya wadancan mutanen wanda idan aka sanya gidanki cikin nasu baifi matsayin boys quarters na gidan ba......tabbas ya wulaqanta haqqin haihuwa......hakanan ire iren wadannan gidajen kinfi qarfin zama a cikinsa saidai kiyi kyautarsa ga irinmu"
"Zuwaira" Ta kira sunanta cikin jaddadawa
"Na'am"
"Ki rubuta ki ajiye.....muddin ban raba tsakaninsa da aminatu ba tabbas ban haifu 'yar halak ba...." Maganarta ta qarshe kenan da tayi ta kutsa kanta cikin gidan tana jin gaba daya gidan tafi qarfin wanzuwa a ciki.
"Subhanallah......innalillahi wa'inna ilaihi rajiun" Malam saidu ya furta yana dire qaramar radio din dake hannunsa yanata kokawar kunnata.
Sake maimaita salatin yayi,kansa yana sake daurewa sosai.
To amma meye ya kawo wannan cin ALWASHIN?. Me ya kawo wannan CIN BURIN. Saita rabashi da anni?,rabuwa ta har abada?,sai ta mallakeshi?,MALLAKA kamar wani miji?. Shin me ya kaita alwashi akan DAN DA BA NATA BA?,wanne rashin imani ne zata tasamma shiga tsakanin UWA da D'A?,shin mene ne alaqarsu?,wacece ita a tsakaninsu?.
Kasa kunna radio din yayi,yayi shuru tamkar yana nazarin wani abu dake shirin tunkarowa. Ya gaza fahimtar tsakanin ita da ANNI WACE MAHAIFIYAR?,WACE KUMA UWAR?.
Cikin nutsatstsen takunsa ya miqe daga zaman da yayi saman sofa bed yana sanya rufaffun takalmansa na fata berluti brand da suka dace da suit da lafiyayyen suit dinsa *hugo Boss* brand da sukayi fice wajen fidda luxury suit daga zare da yaduka gami da auduga mafi daraja a duniya.
Tsaye yayi gaban mirror yana cirar madaidaicin comb da yake amfani dashi wajen taje kwantacciyar sumar dake fuskarsa qasan habarsa da kuma kansa. Sumar da ko yaushe cikin sheqi take da asalin santsinta da wani irin darkness da gashin yake dashi nuturally. Sosai fuskarsa ta sake fresh,cikakkiyar eyebrows dinsa da eyelashes dinsa masu baqin gashi sun sake fidda ainihin kyawun fuskarsa,sun kuma sake taimakawa kyakkyawar qasumbarshi wajen sake qawata fuskarsa da wani irin ajiyayyen kwarjini.
Sai daya feshe jikinsa da sassanyan turarensan nan na din din din sannna ya kalli lafiyayyen agogon fatar dake kwance luf saman fatarsa. Lokaci ya cika daidai kamar kullum da zaici wani abu,ya taka a nutse yana isa inda dan kyakkyawan silver tray din ke ajiye wanda komai ke ajiye samanshi bisa tsarin da akasan wanda zai mu'amala da tray din yake dashi.
Har ya miqa hannu zai dauki glass mug din dake da murfi sai ya dakata saboda qarar wayarshi dake side pockets na suit nasa.
Hannu ya zura ya zarota yana duba me kiran. Sunan nan dai na dazu ya sake bayyana
"Amna....amna" Ya fadi sau biyu a hankali yana motsa jajayen labbansa da sukayi wani fresh suka sake fidda red color nasu kamar me amfani da wani kebantaccen abun shafawa labba
Sai daya koma a nutse ya zauna saman sofa sannan ya daga kiran
"Hamma......"
"Amna......i will be busy today fa"
"I know fa yaaya......anni ce kawai tace na gaya maka ka kirata"
"Lafiya dai ko?" Ya tambaya yana dan motsa fuskarshi
"Hamma......waye yasan tsakaninka da anni kuma?" Wani qaramin qasaitaccen murmushi ne ya subuce saman labbansa,wanda ya fidda kyawun fuskarsa sosai
"Jealous girl" Ya furta a hankali. Siririyar dariya ta kufcewa amna din,ya latse wayar yana laluban number annin. Tunda ya tashi da sassafe kafin ya fita yayi kiran layin nata har sau biyu saidai ba'a daga ba,sai ya bada uzurin banbancin tazarar lokuta dake tsakanin nigeria da South Korea din wala'alla tana nata baccin ko don yanayin jikin nata ma.
Tana gaban mirror tana fama da tazar doguwar sumarta. Wani abu guda daya da taqi jini shine duk abinda zai taba mata kai. Tun tana qarama daya daga cikin dabi'unta bata qaunar kitso kwata kwata,wannan ya sanya har sai da ummunta ta taba aske gashinta,saidai kowanne bawa da irin halittar gashinsa,don babu jimawa wata sumar ta fara taruwa ta kuma sake cika kan da yalwarta da santsinta har taso tafi ta baya da aka aske.
Sake runtse idanunta tayi sanda ta sanya comb din a tsakanin gashinta,daidai sanda ta sake jin daddadan sautin nan irin na dazu. Ta wurga fararen idanunta saman purse din dake ajjiye saman madubin.
Idanu ta zuba mata,kaman zata dauka sai kuma ta share taci gaba da abinda takeyi,wannan ya bawa wayar daman ci gaba da kadawa har ta gaji ta tsinke.
Wayar ya sauke daga kunnensa yana duban fuskar wayar. Sai ya sake gwada kira yana mamaki kadan cikin ransa,don tunda yake da annin bai taba kiran wayarta sau biyu ba ba tare data daga ko ta biyo kiran ba,sai gashi yau kira na biyar kenan zaiyi mata,duk da annin da kanta tace ya kiratan zasuyi magana. Kodai akwai laifin da yayi mata?,ya tambayi kansa duk kuwa da yasan ba haka bane. Abune mawuyaci ka batawa annin rai,musamman su din sanyin idaniyarta guda hudu.
Sake leqa fuskar wayar tayi a karo na uku kenan da ake kiran wayar. Suna daya ne dai MUHAMMADU. Siririn tsaki taja tana jawo wayar gabanta,cikin tarin abubuwan data tsana harda maimaita kiranta a waya koda kuwa kiran me muhimmanci ne. Ba wayarta bace amma ranta taji ya baci data duba taga miscal shida kenan harda na dazu,don haka dab da wayar zata katse ta daga adan zafafe ta karata a kunne.
Karamar ajiyar zuciya ya saki Lokacin daya fuskanci an daga wayar,a hankali ya maida hankalinsa ga daukan kiran da akayi,cikin jikinsa sai ya dinga ji kaman ba anni bace. Koda cikin bacci anni ta daga kiransa zaya fahimta ballantana idanushi biyu.
Kamfanin wayar ya fara irga sakannin da akayi ana riqe da duka layukan biyu,mamaki yaji yadan fara kamashi,yayin da a nata bangaren kuma ranta ya ninka baci akan na dazu. Ansan ba'a da abun fada aka addabi mutane da kira ba qaqqautawa?,an daga kuma zaa bar mutane da riqon waya a hannu?.
"Idan ba wani abun fadin zaa ajjiye wayar" Ta fada tana cije lips dinta na qasa saboda haushin da takeji cikin ranta.
Daga wayar yayi daga kunnensa yana duba number still duk da yasan number anni ce ba kuskure a ciki. Amma baquwar muryar me kama da muryar babies itace ta daure masa kai. Sai ya dakata daga takun da yakeyi don dauko mug dinsa,ya soke hannunsa a aljihun trouser na suit dinsa tamkar me jin sanyi
"Who are you?" Yayi tambayar kai tsaye
"Ina me wayar?" Ya sake jifanta da tambayar
"Bansan me wayar ba.....koma wace me wayar wayan baya hannunta......ka jira idan ya koma hannunta ka sake kira" Ta amsa masa a taqaice tana gintse kiran.
Sautin Din din din na yankewar kiran ya sakashi janye wayar a kunnensa mamaki yana kashesa
"Who's she?" Ya furta a fili yana trying na sake kiran layin,saidai ya taras da na'ura tana gaya masa wayar a kashe take.
Sosai ransa yayi qololuwar baci,wacce irin yarinya ce haka mara kunya wadda bata iya magana dana gaba da ita ba?. Maida akalar kiran nasa yayi ga musaddiq zuciyarsa na masa wani irin zafi. Bayan magana da take fadi kanta tsaye harda katse masa kira?,wayan nata ne?,ko itace tayi kiransa da zata katse masa waya?.
Daidai sanda yake zaune a falon tun bayan wucewar maama da zuwaira kiran muhammad fu'ad ya shigo masa. A kasalance ya zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa,yana tsammanin driver manu ne ya gaji da jiran fitowarsa yayi kiransa. Sunan da ya gani a rubuce jikin wayar ya sanyashi sauke ajiyar zuciya gami da daidaita zamansa. Ya jingina bayansa da kujerar yana kara wayar a kunnensa. A ladabce yayi masa sallama
"Wa'alaikumussalam.....wace mara kunyar kuka bari wayar anni taje hannunta.....har tana katsema mutane kira?"
"Turqashi!.....anzo wajen" Musaddiq ya fada qasan zuciyarsa. Ya sani kowanne bayani zaiyi masa ma ba lallai ya fahimta ba. Ya tsani ya kiraka ka katse masa waya har sai idan shi ya buqaci hakan. Bashi da abun ce masa don haka muryarsa a raunane wadda tayi laushi saboda tarin tunane tunanen dake kanshi yace
"Kuskure aka samu hamma......kayi haquri....bari na hadaka da annin" Ya fadi yana miqewa tsaye.
Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,ya koma saman sofa bed din ya zauna yana jawo mug din yana duban dafaffiyar tumeric fresh milk din ciki kamar yau ya saba ganinta.
Da sassarfa ya soma kowawa ciki,dab da zai isa stairs din yaja ya tsaya saboda annin dake saukowa a nutse zuwa qasa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
Page 36
"Dama baka tafi ba?" Anni ta jefa masa tambayar a nutse tana jifansa da kallon tuhuma. Kalar tausayi ya koma yana karya wuya
"Bazan iya tafiya bane anni na barki"
"Saboda kana tsoron kada ta cinye nama na?" Ta sake tambayarshi cikin salo na gatse.
Ya gama fahimtar gatsen take masa amma sai ya basar yana binta da wayar lokacin data wuceshi tana zarcewa saman kajurun falon ta zabi daya ta zauna
"Anni......hamma ne yakeson magana dake" Ya furta yana rusunawa a gabanta
"Kiraminshi......wataqila yayita kiran layina bai sameni ba" Ta fada tana daukan remote hadi da sauya tashar dake aiki cikin tvn.
Sipping yakeyi na madarar yana irga yadda agogon dake facing dinsa yake bugawa. Ranshi a bace yake amma yana qoqarin danne hakan. Qarar wayar ya sanyashi waiwayawa inda ya gangarar da wayar yana kallon kiran musaddiq. Yasan ba kiran qashin kansa bane.....na anni ne,don haka bai barta tana burari ba ya jawota ya daga yana sakata a kunne.
Da wannan calmness din nashi yayi sallamawa anni. Itama ta amsa masa har cikin zuciyarta tana jin wani farinciki yana saukar mata da jin tasa muryar dake bayyanar mata lafiya qalau yake.
"Barka da warhaka anni" Ya fada yana dan rusunar da kanshi tamkar yana a gabanta. Yana jin wannan respect din har cikin zuciyarsa
"Barkanka me babban suna....."
"Kin tashi lafiya?,ya jikin naki anni?.....ina fatan ba wani matsala ko damuwa?" Ya tambaya cikin kulawa. Ajiyar zuciya ta sauke hade da furzar da numfashi
"Ba ciwo,sai damuwa da kukeson sakani kai da musaddiq". Maganar ta dukesu duka su biyun,har musaddiq dake zaune a gefe ta sanyashi daga kai cikin hanzari yana dubanta.
" Subhanallah......subhanallah anni kiyi haquri.....me mukayi?" Ya furta yana jin damuwa sosai cikin ranshi tare da tuhumar kansa akan sanya damuwa ga ruhin da kullun burinsa ya kyautata musu?.
"Fuad.....yau ka gaida maama daga safen nan zuwa yanzu?" Ta jefa masa tambayar data sanyashi dauke wuta,sannan a hankali ya hade labbansa guri daya ya kuma amsa mata a hankali da
"A'ah".
"Me yasa?"
"Ba komai" Ya amsa mata kai tsaye,saboda shi din mutum ne da bai iya qarya ba sam komai girman laifinsa kuwa
"Me ya hanaka daga wayarta sanda ta kiraka?"
"Anni......fargaba kiranta yake sanyamin,anni banason ganinta tana kirana.....anni bana buqatar mu'amala da ita......nafiso taci gaba da nisantarmu anni kaman yadda tayi a baya......bama buqatarta......duk sanda zan ganta anni sai naji wani abu a kanta.....inama zaku fahimci laifi mafi girma data aikata mana wanda yafi tafiya ta barmu girma muni ciwo da kuma girman zunubi?" Wadannan sune abinda so samu ya kamata ya cewa annin,amma kuma bakinsa ya gaza furta hakan,sai shi kadai daketa jujjuya maganganun cikin zuciyarsa. Ya rasa waye zai zayyanawa su,ANNI dince,to amma bayaso yabar mata wani abu da zaya yi mata tsaye a zuciyarta ko kuma a rayuwarta. Damuwa itace abu na qarshe da yayi alqawarin tarewa anni shigarta,kamar yadda ta sanya duk wani qarfin iko na jiki dana aljihunta ta tare ma rayuwarsu kasancewa da wanzuwa cikin damuwa har kawo bigiren da suke kai haka a yanzu. Wannan tunanin ya sanya ya zabi bawa anni amsa ta hanyar cewa
"Ba komai".
" Ban tsammaci haka daga gareka ba Muhammadu,kanaso abbanku yaji ba dadi a ransa shima kamar yadda naji?" Ta fadi cikin tausa murya tamkar tana magana da qaramin yaro.
"Ko kadan anni.....kema da muka sanya kikaji ba dadin yanzu haka kiyi haquri ki yafe mana......za'aci gaba da kokawa da zuciya,kuma zaa gyara in sha Allah". Murmushi ta saki tausayinsu yana narka mata zuciya. Lallai duk dan da baiyi sa'a da dacen uwa ba abun tausayi ne shi.
"Bakuyimin laifi ba muhammad.....illa dai lahirarku da kuma fagen rayuwarku da nakeson na sake share muku ita tas". Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa ta karaya......inama ana canjen uwa?.......inama ace anni ita ta haifesu kamar yadda ta haifi Sadiq da farouq?.
" In sha Allah anni bazai sake faruwa ba"
"To Allah ya yiwa rayuwarku albarka,ya tsaremin ku daga dukkan sharrin me sharri"
"Kinyi addu'a me kyau anni" Ya furta qasan ransa,don sai yaji kaman ta nemawa kanta tsari ne daga dukkan wani matakin da maama keson kutsawa dashi cikin rayuwarsu.
Ya jima yana juya wayar a hannunsa,tunani da dama suna kutsawa kwanyarsa. Sai yaji gaba daya madarar da duka breakfast din da aka kawo din ya fita a ransa,don haka ya maida mug din ya ajiye,ya miqe ya jawo bedside drawer ya zari dukka abinda yake da buqata ya taka a hankali yana fita a dakin jiki da zuciyarsa duka babu walwala da karsashi.
Sannu a hankali motar dake dauke dashi zuwa companyn ke tafiya busa qa'idoji da dokokin qasar,yayin da shi kuma yake kwance jingine sosai da back seat din na motar. Wayarsa ya sake cirowa cikin rashin walwala ya budeta,bangaren kira ya shiga yana duba adadin miscals na wayar nashi. Miscall dinta shine na qarshe a jerin kiraye kirayen daya rasa cikin wayarsa. Ya bude numbers din yana kalla tamkar me qoqarin haddace numbers din. Tsahon wasu sakanni sai ya dauke duban nasa ya mayar ga titi da yake ita hangowa tarwai ta glass. Haka kawai yake jin bayason kiran,gaba daya bashi da wani hope ko marmari akan dukka wani abu da ya shafeta,ta kashe komai ta kuma qonashi murqus tun a shekarun baya da suka shude,ME YAYI SAURA?. Amsar da kullum take biyowa baya shine BABU.
Da wani dan qaramin hanzari ya danne zuciyar tasa ya danna maballin kira,kiran kuwa ya tafi direct kai tsaye,wanda cikin qasa da sakan goma kiran ya isa ga wayartata.
Duk da jerin dinner abincin daren da me hidima da ita keta faman jere mata a gabanta amma ba wani abu daya daya burgeta ya ko ya bata sha'awa. Sai yanzu ta fahimci dawowa DUNIYARsu da kuma shiga DAULARSU ba shine kadai iya abinda take buqata ba. Ba shine kadai iya abinda ruhinta da zuciyarta suke da muradi ba. Lallai tana buqatar wani abu da yafi wannan muhimmanci a tattare da ita.
Ta juya a hankali tana duban zuwaira data cika plate da pepper chicken tana ci hankali kwance. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana kallonta
"Zuwaira....."
"Asama'u" Zuwairan ta amsa mata da bakinta daya cika da zallar tsokar kazar gwamnati(broiler).
"Me yake faruwa dani ne?......wa kaman ba nice ma'u ba?,kamar ba nice asama'u ba?,koda karin maganar nan da hausawa keyi ne yakeson tabbata a kaina?,lokaci shekaru da zamani suna son maidani wata lusara?......indai hakan ta kasance bazan taba yafewa kaina ba......bana ma fata hakan ta kasance,dole yarana su dawo qarqashin iko na kamar kowacce uwa.....dole su kasance qarqashin shimfidaddun dokokina.....suyi abinda nakeso na sakasu....su kuma bar abinda na hanasu......suso wanda nakeso.....suqi wanda bana so.....su kyautatawa wanda naso su rabu da wanda bana so.........dole na rabasu da aminatu.......dole Alhaji hamza ya zame musu babban abokin gabar da babu irinsa......zuwaira.....wannan karon burina da muradina me girma ne.....inaji kuma ina ganin kamar girman buqatata a wannan karon ya shallakewa aikin MADUGU.....Ina buqatar wanda yafi madugu zafi.....ina buqatar aiki da zafi zafinsa" Idanun zuwaira suna kanta har ta kammala,sai zuwairan ta nisa ta ajiye plate din naman hannunta ba don ya isheta ba,sai don gano damarmarki masu girma da yawa a gabanta.....da wata siririyar qofa da take hangota da fadin gaske daga can ciki.
"Akwai BAHAGO bayan madugu din......bani da kokwanto ko tantama a kansa.....tun ba yau ba......tun kina kogi na miki sha'awar zuwa wajensa amma kika qi bada hankali.....na tabbatar inda kin aminta da hakan da yanzu ba wannan matsalar a gabanki.....da tuntuni kin jima da tsallake wannan babin.....saidai kina da buqatar kudade..... Kudade masu kauri.....kaman yadda aikinsa yake da zafi haka yake da karbar kudi,saidai ribar da zaki samu yafi abinda duka zai amsa daga gareki".
Zamanta ta gyara sosai tana duban zuwaira. Ta sani ita din gaba take da zuwaira ta fannin abubuwa masu tarin yawa.....zuwaira bata isa ta hada kanta da ita ba indai ta wannan bangarenne......amma kuma komai qasqancin bawa akwai ta inda yake iya wuce maka
"Tunanin da ya fara zuwa kaina kenan.....abun nan yana min ciwo.....kamar ni zuwaira?" Ta fadi tana nuna qirjinta da yatsanta
"D'ana......mamallakin jadda diamondchore resources amma bazan iya kallon mutum nayi masa kyautar million biyu zuwa sama ba?,zaman me nakeyi a duniya zuwaira?" Ta qarashe fada da wani irin zafi da take jin ya ishe mata har qasan zuciyarta
"Komai ya qare idan kinbi a sannu.......idanma baki da wannan jumurin zirga zirgar ai kina dani,driver kawai zaki yiwa umarni......fu'ad kuwa danki ne.....muddin kuma yana neman albarka.....dole ya biki" Ta fadi tana tallafar farantin namanta da nufin ci gaba da kaiwa cikinta. Daidai Lokacin kiran ya iske wayar dake yashe a gefe guda.
Tare suka kalli wayar,sai zuwaira da tafi kusa da ita ta miqa hannu ta jawota tana dubawa. Baki ta tabe sannan ta furta
"Tabdijan" Ta matsa gaba tana ajewa maahmah a gabanta
"Qarshen sakaci......qarshen toxarci......tabbacin akalar duka yaranki suna hannun aminatu.....tabbacin steering dinsu yana damqe a hannunta kenan......sai yadda taga dama zata juyashi......an bada umarni kuma ya karba da gaggawa gashi ya zartar" Maganganun zuwaira kamar saukar ruwan dalma tsakiyar tsokar zuciyarta take jinsu. Tamkar tana yiwa ciwonta fami ne,sai ta gaza cewa komai,ta ja wayar tana daga kiran ta sakashi a hands free ta ajiye saman cinyarta
"Assalamu alaikum" Nutsatstsiyar muryarsan me nuna zallar kwarjini da nutsuwar mamallakinta ta bayyana tana karade falon
"Amen......sai yanzu kaga damar kirana bayan da aminatu ta baka umarni ko?" Tayi maganar cikin tsananin daci da bacin ran dake damfare a zuciyarta.
Idanuwansa ya lumshe kana ya budesu duka Lokaci guda. A duk sanda yaji sautin muryarta abubuwa da dama take tunasar dashi wadanda suka jima da shudewa. Yana jin kamar tana bankada babi babi na wata rayuwarsu ta baya da a yanzu yaketa kokawar binneta tana sake boqarewa gami da son bayyana kanta.
"Am sorry" Ya tattara kalmar da qyar yana gaya mata.
Shuru ne ya wanzu a tsakaninsu,kowa da abinda zuciyarsa ke raya masa,kowa kuma yana qoqarin controlling kansa ya fuskanci dan uwansa
"Barka da dare.....kin yini lafiya?"
"Da ban wuni lafiya ba zaka ganni fu'ad?,ko kana jiran labarin baqincikinka kai da Musaddiq ya kwantar dani ya kasheni?"
"Ya salam" Ya furta a hankali har kalmar ta shiga kunnuwanta da kyau,abinda yada karya lagonta kenan tayi shuru bata sake cewa komai ba. Shurun da tayi ya bashi damar sake cewa
"Am really sorry.....naso kiranki to amma kuma ban samu zama ba......" Qaramin tsaki taja me sauti,ita sam a yanzun ma ba wannan bane a gabanta,kiransa ko akasinsa......hanyoyin biyan buqatarta sune abinda take da muradin riska
"Ba wani matsala ko?,ba abinda kike da buqata?" Yayi mata tambayar data zama lazeem a kansa a duk sa'ilin da zaya kirata ta waya ko zaiyi tattaki zuwa inda take
"Akwai matsala......kuma ina da buqatun da zasu zama tamkar abun kunya a tattare da kai ace uwa ta mutum irinka sunfi qarfinta" Murmushi yaso qwace masa,duk da koda a gabansa kake ba zata fahimci hakan ba.
Ya riga ya fara harbo layin da ta soma hawa,don haka furucinta bai dagi hankalinsa ba ko kadan. Ya bata dukkan wani jin dadi ta fannin sutura.....muhalli abun hawa lafiya,abinci da abun shan da kaf gidan daga ita har masu aiki a qarqashinta babu wanda ke ta'ammali da wani ruwan sha idan ba ruwan gora ba. Ya bata kulawar da babu yadda za'a girka abinci cikin gidan ba tare da nama ko kifi ba. Ba irin nau'in nama ko kifin da babu shi cikin gidan muddin musulunci ya halasta cinsa.....hakanan babu nau'in cima da babu ita a gidan muddin halas ce cikin addininsa.....kamar yadda abun sha ba nau'in da babu.......ana kuma sake shiga da wani duk qarshen kowanne wata ba tare da damuwa da cewa akwaisu bila'adadin ba bash kuma qare ba
"Maahma?......wanne abu ne yafi qarfinki?" Ya tambayeta murya a tausashe yana son ya kaita muhallin da yayi imani can takeson zuwa
"Kudi fu'ad.......a matsayina na mahaifiyarka......bani da wani abu da zai shiga tsakanina da kai sai dubu dari a wata?" Ta furta tana jin ciwon abun sosai cikin zuciyarta.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 37
Ya riga ya sani tun kafin ta fadi,yasan abinda zata fada din shine burinta na qarshe da zai kaita ga cikar muradinta. Yana da cikakken sani na haqqin uwa.....yana da cikakken sani na duk wani haqqi da yake wuyansa daya zamewa rayuwarsa tilas ya saukeshi......a ciki kuma babu wani abu guda data rasa sai KUDI. Kudin kuma da yakejin ba zaya iya mallaka mata sama da abinda yake bata din ba saboda wani babban dalili. Inda zai yiwu cikin abinda yake batan ma zayaso ya zama qasa da hakane ke shiga hannunta. Barin kudi a hannunta GANGANCI NE. Barin kudi a hannunta KUSKURE NE da ya tabbatar aikatashin zai zamana babu wani abu da zai goge wannan kuskuren.
"Am sorry maahma....." Ya fadi da lallausar muryarsa data karye. Shi daya yasan abinda yakeji a qirjinsa idan ya daga idanu ya kalli maahma a matsayin mahaifiyarsa.....shi kadai yasan abinda yakeji idan ya tuna dalilin da yasa take neman kudade haka masu yawa daga hannunsa.
"Idan akwai wani abu ba wannan ba da kike buqata.....ko musaddiq kina iya shaidawa.....am sure zaiyi handling komai.....na barki lafiya" Ya qarasa maganar yana zame wayar daga kunnensa.
Zazzafar iska ya fitar a bakinsa sanda ya zubawa titi idanu......ya tabbatar duk yadda ubangiji ya ni'imta rayuwarka.....tabbas akwai jarrabawa da ba'a raba ruhi da rayuwa dasu.
"Sadiq" Ya kira sunansa a hankali,sai sadiq din dake zaune a gaban motar yana fama shirya bayanai kan yadda ganawar su da kamfanin zata kasance yadan waiwayo
"Na'am"
"Banaso mu wuce awa biyu a kamfanin nan.....inaso kome mukeyi cikin satin nan mubar Korea......gida nima nakeso mu koma"
"In sha Allah hamma" Ya amsa masa cikin girmamawa sannan ya daidaita zamanshi yana ci gaba da aikinsa.
Sai data tabbatar ta kammala gyara gashin tsaf,ta saka siririn ribbon ta daureshi. Sosai fuskarta ta fita tarwai,silky skin din nan nata kaman tana amfani da wani abu daban na gyaran fata.
A nutse ta taka don dauko wayarta dake saman gado,idanunta ya sake sauka kan luggage din da har yanxu ta kasa budewa,sai ta koma ta zauna sosai saman dan madaidaicin rug na gaban gadonta,ta jawoshi jikinta ta soma zugewa
Tsala tsalan abayas ne suka fara mata sallama. Abayas masu tsananin kyau da tsadar da suka amsa kudinsu na qasashen dubai da oman da Morocco. Kowacce abaya da shoe din daya dace da ita wanda yawanci takalman kamfanin Gucci Hermes kitton da tom Ford ne. Tsala tsala agoguna na kerewa sa'a data tabbatar kudade ne ba qanana ba aka zuba aka siyesu. Sai wasu siraran abun hannu masu shining da sukafi mata kama da na gold,daga gefensu kuma turaruka ne turmus masu mabanbantan qamshi da kuma tsada. Dan aljihun dake jikin luggage din ta zura hannunta,sai ta fiddo kyakkyawan kwalin,ta juyashi kadan a hannunta,tun bata bude ba ta fahimci kwalin waya ne,saita zazzage ledar kwalin ya fado. A nutse tayi unboxing wayar data jima da sanin kudinta. Aqalla kudin wayar ya tasamma miliyan hudu,sabuwar Samsung 3screen da bata gama fita hannun jama'a ba. Ta riqe wayar a hannu tana juyawa tare da duba qaramin takardar dake nuna a qasar da aka qerata da zafi zafinta acan Ya'aqoub ya siyeta.
Ajiye wayar tayi a gefe tana bin kayan da idanu,kaya ne masu tsada dukansu,siyayya ta masu aji masu ji da naira. Babu abinda baiyi kyau ba a ciki amma sam ba abinda ya burgeta. Idanunta ta lumshe zuciyarta tana motsawa. Ta tuna mata da yawa,a daidai yanzun 'yammata nawa ne kamarta suke can suna neman yadda xasu tsira da mutuncinsu?,'yammata nawa ne suka rasa darajarsu saboda neman yadda zasu rufawa kansu asiri?,mata nawa ne suka hadu da abubuwa marasa dadi saboda an rasa me taimakonsu?,bayan al'ummarmu cike take da mawadata irinsu Ya'aqoub din,wanda kyautar dubban daruruwa zuwa miliyoyi ba komai bane don su fita da aljifansu?.
Zuciyarta ta tabu sosai,ta shiga tuna wasu shekarun baya da suka shude da rayuwarta,shekarun da sukaso girgiza duniyarta,sukaso jefata wani baqin duqununun ramin da inda ta afka babu rana ko wata na fita daga ciki ko tsere masa?.
Sautin qarar daya daga cikin wayoyinta ya katse mata tunaninta,ta bude idonta tana wurgawa inda wayar take,ta miqa hannu a kasalance ta jawota.
Mk kamar yadda tayi saving number dinshi haka ya nuna mata.
"Mika'il" Ta furta sunan muryarta qasa qasa,yayin da zuciyarta ke wassafa abubuwa da dama a kanshi.
Ci gaba tayi da kallon wayar,batayi yunqurin dagawa ba har zuwa sanda wayar take dab da tsinkewa.
A kunnenta ta kara wayar,sannan ta maida idanunta ta rufe gami da jan bakinta ta tsuke.
"Hi" Ya furta cikin zamudi tamkar ya mance gurin da yake a zaune. Qaramin tsaki taja qasan zuciyarta,ta motsa labbanta a hankali
"Assalamu alaikum" Ta fadi a nutse.....sallamar da ta sanyaya masa jiki,ta kuma jefa shakku a cikin zuciyarsa. Itace macen da yakewa kallon bariki ta farko da take matuqar masa kwarjini. Itace ta farko da yake hangen wasu kalan dabi'u da suke jefa shakku da kokwanto cikin zuciyarsa. Baisan kala da adadin matan da yayi mu'amala dasu cikin rayuwarsa ba,amma sai take neman zame masa ta daban.
Dan gyaran murya yayi sannan ya amsa mata da
"Wa'alaikumussalam.....afuwan.....banyi sallama ba ko?,na matsu da naji muryarki ne.....na kwana da kewa na kuma tashi da ita......ina fatan kin tashi lafiya?" Sai da tasha qamshin nan nata da yake a halittarta sannan ta amsa masa
"Lafiya qalau......"
"Naji dadi dajin hakan.....yaushe za'a bani damar sake ganinki?" Yayi mata tambayar abinda yafi damunsa kuma cikar burinsa a kanta.
"Sai lokacin yayi......idan yayin da kanshi zai kawoka gareni". Sam ba haka yaso ba,sai kuma yake ganin kaman daga gareshi ne,ya kamata ya gyara wasanshi.
"Zan iya haqurin jiranki koda na shekara nawa ne......amma inaso kisan akwai zuciyar da tayi matuqar mutuwa a kanki take kuma da buqatar soyayyarki....."
"Mika'il......" Aka kira sunanshi daga gefe,muryar ta fusgi hakalinsa,yadan waiwaya kadan ya dube kamilar fuskar nan,daya daga cikin fuskoki biyu dake masa kwarjini cikin kamfanin
"Am sorry......zan yanke kiran,ina fatan samun wayarki a bude zuwa anjima,ba kamar yadda nasha wahala jiya ba" Boyayyen tsaki ta saki tana yanke kiran hadi da zame wayar daga kunnenta. Ta wurga fararen idanunta gefe tana sauke qaramar ajiyar zuciya. Wato namiji akan mace tamkar mayen qarfe ne da qarfen kansa?,musamman idan zaki bashi abinda yakeso?,ko kuma yana hasashen samun wata riba ko ganima a kanki?.
A nutse ya zuba masa idanunsan nan yana kallonsa lokacin da yake jefa wayarsa a aljihu yakuma iso bakin zagayayyen table din da yake zaune a kai.
Muhammad fuad jadda CEO abinda ke rubuce kenan jikin wani dan siririn katako dake zaune sosai saman table din daga gaba gaba. Saidai a maimakon muhammad jaddan,farouq hamza kibiya ne zaune saman kujerar yana duban mika'il da kyau har ya zauna kujerar dake fuskantarsa.
"Sassaucina fiye da oganku kamar yana son jawo sakaci da aikinku ko?" Ya jefawa mika'il tambayar yana debe dukkan wani wasa da haba haba da ya saba yi dasu dake saman fuskarsa. Shafar kansa kadan mika'il yayi cikin rusunawa
"Sorry sir.....urgent call ne shi yasa....but hakan bazai sake maimaituwa ba"
"Mituna nawa nayi ina kallonka ba tare daka sani ba,hankalinka baya jikinka?,ka kuwa san girma da matsayin position da kamfani ta baka mika'il?" Ya sake masa tambayar yana riqe habarsa da yatsarsa guda gami da kafeshi da idanunsa sosai. Yanayin ya tabbatarwa mika'il na gaske ne,a irin wannan lokacin da yake buqatar kusanci na sosai da JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES bai kamata ya bari BOSS muhammad ya dawo ya samu wani shaidan banza a kansa ba
"Sorry sir.....it will never happen again" Kaman bazai daina kallonsa ba sai kuma ya fesar da iska daga bakinsa,ya tura masa wani folder yana cewa
"Ruwanka ka riqe aikinka da kyau,ruwanka kayi wasa dashi.....daga rana ita yau ba zaka sake ganina a company dinku ba,wataqila saidai ziyara......ka kuma fini sanin waye boss dinka" Ya qarashe maganar yana tashi daga saman kujerar.
Yadda hankalinta yayi kan zuwa duba aysha yasa gaba daya ta manta da batun wayar da ta bada address din aje a karba. Gaba daya ta manta ma da zaman wayar cikin dakinta. Sai data tabbatar su huda sun dawo daga boko sun wuce islamiyya sannan ta shirya cikin wani dinkin atamfa doguwar riga data bude sosai daga qasa ta zauna mata daga sama cas jikinta,ta kuma lullube kanta da Chantilly veil,takalmi da jakan D&G su suka zama cikamakin adon nata.
Kamar ko yaushe tsakar gidan nasu zuwa farfajiyar gidan bata rabo da kai kawon jama'a jifa jifa. Kamar kullum haka ta ratsasu a nutse ta fice ba tare data damu da idanun dake zube a kanta ba.
Kamar dai kowanne lokaci,abinda ta baro cikin gidan shine a waje. Yawan idanun jama'a dake kanta ko kadan basu dadata da qasa ba. Tun asali mutum ce me damuwa da lamarin gabanta.
Abubuwa da dama da suke cikin zukatan mutane a kanta bata isa ta gogeshi ba. Abune da tun yana damunta ya zame mata jiki. Suna mata kallon biri ne tana musu kallon ayaba. Anyi walqiya me hasken data haska mata abubuwa masu tarin yawan da suke boye cikin hijabin idanuwan jama'a da wani irin shamaki da tsinkaye da idanuwa basu kaiwa wajen.
Wasu mutanen a riga kawai suke mutane.....wasu dattawan a suna ne kawai kuma a baki.......wasu jama'ar da ake tunanin suna gyara ko bada gudunmawar gyaruwar al'umma su din GUBA ne,guba ce wadda bata da magani,guba ce me d'aid'aita komai da wargaza komai.
Daidai sanda takai qarshen tunaninta sai ta fidda eye glasses dinta da ba kasafai ta fiya amfani dashi ba ta manne qwayar idanunta. Daya daga cikin abinda ya sanya suke mata mummunan kallo da mafi munin fassara. Eye glasses ne me duhu dake qarawa fuskarta kyau da kuma kwarjini,yake kuma iya hana mutane ganin ainihin qwayar idanunka.
A nutse takai bakin titi,saidai yanayin kai kawon abun hawa kadai zai gaya maka akwai qarancin motocin haya
"Ki siya mota kawai ki huta sabreen" Ta tuna kalamin qawarta qwaya daya da take da ita duk duniya wato haseena. Karon farko tun wayewar garin ranar ta saki murmushin da batayi niyya ba,abinda ya sanyashi tsaiwa da motarsa cak. Duk da cewa ta daki zuciyarsa tun daga nesa daya hangeta,amma sai gashi farat daya ta sanyashi tsaiwar da baiyi niyya ba.
Taga gilmawar farar motar amma saita dauke dukka wani hankalinta zuwa wani sashen,qasan zuciyarta tana fatan bawai ya tsaya bane saboda ita,don a yanzun bata da buqatar qaruwar kowanne namiji cikin rayuwarta. Tana da tarin matsalolin da takeson ta kammala dasu tukunna,mazajen dake cikin rayuwarta kuma a yanzun ta sallami kowa da kalar sallamar data dace dashi kafin ta sake sabon zubi.
A hankali motar ta dawo daidai gabanta ta kuma tsaya cak,sannan aka sauke glass din motar,abinda ya bawa sassanyan sanyin ac din dake gauraye a motar damar fitowa waje ya kuma daki fuskarta.
Sallamar da yayi mata ta tilastata waiwayowa ta dubeshi. Nutsatse kuma kamili a ido,wankan tarwada wanda ko bai miqe tsaye ba ta tabbatar dogo ne. Zagayayyar Fuskarshi da gemu ya yiwa qawanya,sai idanunsa dake saye a cikin glass.
"Bai dace ace zafin rana yana dukan wannan kyakkyawar fuskar ba.....shigo don Allah na rage miki hanya". Jin kai da miskilanci cikin jininta yake,duk daga yanayin kamalar data gani a fuskarta ya mata kwarjini amma saita sake dauke kai ba tare da tace masa kanzil ba.
Murmushi ya saki,ya miqa hannu yana bude mata motar
"Ki shigo domin Allah". Ya furta yana tsareta da idanu har zuciyarsa yana jin tayi masa. Duk da cewa akwai wani irin kwantaccen kwarjini akan fuskarta wanda bayajin cewa ita kanta tasan tana dashi.
Kaman yadda magiyarsa ta dauki hankalinta haka bullowar kawu ta dauki hankalinta. Duk da cewa daga nesa yake amma ta zuba masa idanu da kuma wannan komar tata dake saurin karanto lissafin me lissafi. Cikin qasa da minti daya ta gama karantarsa,zaiyi wuya ace ba ita yaje nema gida ba bai sameta ba ya fito. Batayi shawara ta biyu ba ta juya a hankali ta kama murfin motar ta bude ta shige ta maida ta rufe,daidai sanda motar ke tashi ya iso gurin.
"Kaga shegiyar yarinya?,ni zaki gudarwa?,don ubanki ai duk tantirancinki dai idan dare yayi gidan adamu kike dawowa ki kwana ko?,to mu zuba dani dake.......meye amfaninki muddin ba za'a moreki kudi ba?,ai amfaninki kiyita kawo mana kudi tunda hanyar da kika zabawa kanki kenan" Ya fada yana yarfe hannuwa shi daya a gefen titi,kai kace ya samu matsalar kwanya.
Juyawa yayi da zummar barin wajen,saidai taku biyu rak yayi wayarsa keypad dake aljihunsa ta dauki kururuwa.
"Kai jama'a......Allah yasa ba bala bane.....kash.....shine wallahi" Ya fada yana qoqarin danna madannin wayar da yayi tsananin tauri saboda ganin rayuwa da yayi.
"Hel.....helo bala.....don Allah kar ka damu.....ai in sha Allahu ina me tabbatar maka damu za'a shiga wannan cacar.....yo ta ina zamuyi wasa?,bayan kai da kanka ka tabbatar min mutumin nan attajiri ne......ai ina maka rantsuwa da Allah baka bina bashin rantsuwa wannan karon arziqi ne yake kiranmu....inata buga buga naga na samu adadin abinda akeso a shiga cacar dasu....kada ka damu,zuwa nan da dare in sha Allahu zaka jini,yauwa na gode" Ya fada yana sauke wayar,ya soma laluben aljihunsa don maidata ciki yana sake magana a fili.
"Idan ma Allah ya taimakeni na haye da wadannan kudaden ina zaki sake jina?,ai nima na zama attajirin kaina don ubanki" Sai yaja qwafa sannan tsaki ya biyo baya,ya juya yana sauya hanya.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 38
Sau biyu yana sake juyawa yana kallonta. Tun bayan sallamar da tayi yayin shigowa motar bata sake cewa wani abu ba.
A nutse take da dukkan nutsuwarta,nutsuwar data sake janye ra'ayinsa a kanta matuqa.
"Erhmmm" Ya danyi gyaran murya kafin ya dora da
"Na gode qwarai da baki wofantar da magiyata ba.....hakan ya nunamin kinsan darajar dan adam....." Maganarsa ta sanyata dawowa tunaninta tare da tunasar da ita a inda take. Batace masa komai ba,tadan dai motsa kadan alamun tana saurarensa,hakan ya bashi damar ci gaba da magana.
"Da farko dai sunana alhassan.....ko zan iya sanin sunan malamar?" Sunan daya kira kanshi dashi ya sanyata juyawa kadan ta kalleshi sannan ta maida dubanta ga kwaltar da suke bisa kanta. Kaman ba zatace komai ba sai kuma ta motsa bakinta
"Sunana....." Sai tayi hanzarin dakatawa. Shima kaman sauran?,yana buqatar a bashi stamp?,yana buqatar personal suna nashi tamkar dai sauran 'yan uwansa jinsinsa?. Eh yana buqata,saidai shi din bata jin zatayi wani doguwar mu'amala dashi da har zai buqatu ya zuwa stamp na musamman
"Da alama sunan nan me tsada ne ko?,sai na siyeshi?" Ya fadi yana dan satar kallonta kadan fuskarsa dauke da murmushi. Kai ta girgiza a hankali
"Sunana sawwama"
"Nice and good name.....me azumi kenan?" Ya fadi yana dubanta kadan. Kafada ta daga,koma meye ma'anar sunan bai zame mata damuwa ba,kawaidai ta bashi sunan ne don shine sunan da yazo kanta.
"Ma sha Allah......gashi mun iso inda kika cemin,kuma ina da tarin abubuwan fadi don inason alaqar tamu tayi nisa,tafi haka zurfi,za'a bani wani abu kaman number waya ko adress nazo na sameki?"
"Wayata bata da guarantee adress kuma bani da" Ta bashi amsa ta kai tsaye daidai sanda yake tsaida motor din a inda ta nuna masa.
"Waya ba guarantee adress aishi zai zama babban guarantee ko?....me yasa kikace baki da adress?"
"Saboda bamu da gida" Ta sake bashi amsa kai tsaye sanda take dubansa da fararen idanunta masu sheqi da hasken rana ya qara musu qyalli,abinda ya sake daukan hankalinsa kenan. Murmushi ya saki yana jin tana sake burgeshi
"Alright.....nasan dai ba dan adam din dake rayuwa a titi.....amma bazan takurawa zabinki ba......zaki iya bani dama ta uku?,damar yin magana dake a nan?" Numfashi ta sauke a hankali tana jin ya takurata da yawa,ta daga hannunta dake daure da agogo ta kalla sannan ta sauke tana juya idonta daya sashen alamun qosawa
"Mintuna biyar kawai"
"Na gode" Ya fada yana gyara zamansa sosai.
"Bari na tafi kai tsaye kada na cinye mintunana ko?" Ya furta yana sake sakin murmushi. Batace masa komai ba still,saidai ta kafe idanunta ne saman qofar gidan dake gabansu kadan. Tunaninta yafi karkata akan gidan,tana tunanin me zataje ta taras?,wanne abu zata samu cikin gidan.
"Tunda na ganki sawwama naji zuciyata ta kwanta dake.....ta kuma kamu da sonki......naji kuma a raina na samu matar aure.....ina fatan zaki bani dama....." Statement dinsa na qarshe data samu fahimta kenan.
Waiwayawa tayi ta dubeshi,shima idanunsa yana kanta,da alama ya gama dukkanin bayanansa ita yake da buqatar jin ta bakinta. Dauke duban nata tayi,sannan ta saka hannu ta bude murfin motar ta zura qafafunta ta fito. Da mamaki yake binta da kallo har zuwa sanda ta maida masa murfin motar ta rufe,tadan rage tsaho kadan tana dubansa da shiny eyes dinta
"Na gode da karamcinka......amma kayi haquri.....babu aure a rubuce cikin rayuwata.....na barka lafiya" Ta motsa labbanta a hankali sannan ta janye jikinta daga motar.
Soma takawa tayi a hankali tana barin wajen,AURE na daya daga cikin abinda take mantawa dashi a rayuwarta. Aure yana cikin abinda yake a lissafin qarshe cikin abubuwan da suke ba dole ba a rayuwarta. Aure yana daya daga cikin abinda take masa wani irin kallon da batasan ajin data zubashi ba.....babu shi ko kadan a dictionary dinta,idanma anyi zancensa,tana masa kallon wani baqon abu wanda batasan ranar da zata saba da ji ko ganinsa ba,bare azo da batun wanzuwarsa akan kanta.
Ko kadan bata damu da tsaiwarsa a wajen ba,abu daya ta sani.....kaman sauran mazan,yadda basu da masaniyar daga inda ta fito......hakanan bata basu qofa ko qanqani game da sanin inda zata ko inda zata shiga. Don haka bata kutsa kanta cikin gidan ba sai data kadar masa da hankali,ta kuma tabbatar ya bar layin.
Da sallama a bakinta ta shiga madaidaicin tsakar gidan dake shimfide da sabon simintin da bata jima da sanyawa ayi musi shi ba saboda jin dadinsu.
Yara ne aqalla kusan guda biyar wadanda shekarunsu bazai haura goma zuwa sha uku ba. Biyu daga cikinsu wanki sukeyi,daya kuma tana wanke wanke,yayin da guda dayar take jawo ruwa a rijiya tana zubawa a babban mazubin ruwan da suke amfani dashi a gidan.
Sallamarta ya sanya kowacce ta watsar da abinda takeyi,suka kuma rugo da gudu suna rige rigen isa inda take. Kyakkyawar fuskarta ta fadada da fara'a itama ta buda hannunta tana tarbarsu,daidai sanda muryar matar ta iskesu
"Ku da waye haka?" Ta bayyana tare da qarashen tambayarta tana qoqarin daura dankwali saman kanta.
Murmushi ne ya wadaci fuskarta itama,kakkaurar matar ma'abociyar tsaho da qiba,saidai alamu sun nuna yanayi na rayuwa ya sanya qibar zubewa sai saura data zama halittarta ce ba zata iya rabuwa da ita ba. Baqace wannan ya sanya dukka kamanninta sukafi karkata ga kamannin babarbariya.
"To ku barta ta qaraso mana" Ta fadi tana juyawa cikin dakin da ta fito,dukansu sai suka bi bayanta harda sabreen daketa jefawa yaran tambayoyi.
Tare suka zauna da yaran saman shimfidaddiyar dardumar da matar ta shimfida saboda sabreen din,daya daga cikin yaran ta miqe ta fice sai gata da ruwa adan qaramin jug da cup,yayin da sauran sukaci gaba da zama a kewayenta.
"Ina Ayshatu?" Tambayar farko da sabreen tayi mata bayan sun gama gaisawa,tambayar data sanya yaran suka miqe daya bayan daya suna fita a dakin.
Bata ce komai ba matar saita miqe tana dosar wata qofa dake maqale a falon,itama batace komai din ba ta miqe ta biyo bayanta.
Yalwataccen daki ne dake wadace da tsafts,ba komai a qasan sai wata lamusashiyar katifa guda daya yashe a qasa. Daga samanta idan ka duba da kyau mutum ce a kwance data lulluba duka jikinta. A sanyaye sabreen ta qarasa gaban katifar,ta saka hannu ta yaye rufar bakinta yana rawa ta kira sunanta
"Aishatu?" A hankali ta ware idanunta akan sabreen din,sai kuma wani busashen murmushi ya subucewa kyakkyawar fuskar yarinyar
"Aunty....kece kika zo?" Ta tambayeta da siririyar muryarta. Kasa riqe kanta tayi,sai kawai tayi qasa da kanta hawaye yana diga daga idanunta. Tana jin tausayin yarinyar kamar zai fasa zuciyarta,tana jin kamar zata narke a wajen,tana jin inama ace tana da ikon fidda ciwo ta farat daya daga jikin mutum a yanzu yanzu basai anjima ta cisgeshi daga jikin ayshatu
"Ko baki da ikon cire mata shi yanzu yanzu.....kina iya sama muku dama ke da ita na samo mata lafiya a duk inda lafiyar take a fadin duniya" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsar data motsa mata wani qwarin gwiwa daga can qasan zuciyarta. Wannan ya sanya ta sake daga idanunta tana kallon aysha. Allah ne kadai yasan bila'adadin mata da yaran da suka shiga irin yanayin da ayshatu ke ciki duka sanadin TAIMAKO. Lalacewar al'ummarmu abune me matuqar ban mamaki da daure kai. FYADE ba'a daukeshi da wani muhimmancin da me aikatashi zai fuskanci hukunci mafi tsananu ba a tsarin doka. Tana iya tuna yawan kudaden data kashe,shige da ficenta da kai kawo data dinga yi kafin ta samu ayiwa azzalumin hukuncin da doka ta tanada. A abinda ya yiwa aisha,ba hukuncin daurin shekaru take da buqata ba......lahira yafi kamata ya baqunta yaje ya hadu da hukuncin mafi iya hukuncin masu hukunci.
Sosai ta bawa zuciya da gangar jikinta qwarin gwiwa,ta zauna sosai ta yiwa yarinyar komai. Ta bata abinci ta kuma dinga hilatarta,har suka dinga hira tana saurarensu murmushi yana subuce mata. Hakan ya sanyaya ranta kafin su kebe da ummaa ta sake mata bayanin data yi mata a waya.
"Waje nakeson a fita da ayshatu,inason ta warke sumul taci gaba da rayuwarta,duka duka shekarunta sha uku,ya kamata ta rayu kamar kowa" Ta fada zuciyarta tana mata zafi. Allah ya dora mata tausayin yaran da matar kanta da batasan asalinsu ba,amma dukka dawainiyarsu kusan kaso tamanin cikin dari tana a wuyanta,hatta da hayar gidan da suke zaune a ciki kuwa,banda abinci da ma karantarsu rayuka shida.
Da idanu ummaa take bin sabreen. Tasan cewa dukkaninsu babu wanda suka hada dangantaka a tsakaninsu,amma suna jin juna kamar 'yan uwa,suna kuma ci gaba da tsananin shaquwa da juna.....kuma a yanzun sune 'yan uwan kawunansu.
"Sabreen......kiyi iya abinda zaki iya mu barwa Allah sauran.....samun maganin ayshatu a gida Nigeria ma miliyan nawa ya kama bare ayi batun fita da ita waje?,kinsan miliyoyin kudin da za'a cajemu?,daga visa passport masauki abinci da zaman asibiti zuwa kudin magani?" Shuru sabreen tayi tana saurarenta,tana jin zuciyarta na wani irin ciwo,irin ciwon da mutum kanji a duk sanda yake tsananin son abu amma babu ikon samuwar wannan abun gareshi. Numfashi taja sosai ta aje tana duban maama
"Allah zaiyi cikin iko da isarsa......na tabbatar Allah bazai taba wofantar da bayin da aka zalunta ba" Kai ummaa ke jinjinawa tare da yaba tauhidi da yaqinin sabreen.
Ta jima dasu saidai hankalinta yana kan asibiti,don haka lokaci kadan ta qara akai tayi musu sallama bayan ta aje musu kudi kaman yadda ta saba da basa wuce cefane da zirga zirgar makarantar yaran.
Tana hanya zuciyarta kamar ta fashe,hakanan ta sake jinta a rikice bayan fitowarta daga asibitin bayan taji bayani daki daki na yadda zata fita da ayshatu waje ayi mata aiki.
Kudade ne masu kaurin da a yanzun bata dasu bata kuma bawa wani ajiya ba. Batasan tayi farautar kudi don ta ajiye ta tara abun duniya ba......tana farautarta ne don ta raba a tsakanin mabuqata marasa galihu irinta,yanzun ka buqata ta taso mata wadda take da girma da muhimmanci a rayuwarta. Sai taja numfashi mai nauyi,tabbas a yanzun zatayi FARAUTA ta ainihi,tsakanin MIKA'IL YA'AQOUB da kuma MASHKUR waye zaiyi aman wadannan maqudan?.
_tofa zamuji waye,komarta zatayi kamu ko kuma wannan karon ita zata shiga komar?_
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 39
Tun a hanya har takai gida zuciyarta na karakaina ne tsakanin sunyen mutum ukun MIKA'IL MASHKUR KO KUMA YA'AQOUB.
Da sallama ta shiga parlor din bayan ta tsallake tarin idanun da a kullum suke da tuhume tuhume da zarge zarge a kanta masu tarin yawa. Ta samesu suna hada uniform dinsu guri guda nadra zata wanke. Huda kuma na kokawar kammala abincin dare,don da alama basu jima cancan da dawowa islamiyya ba.
Takan samu cikakkiyar nutsuwa a duk sanda ta dawo gidan ta samesu lafiya lau kaman yadda ta fita ta barsu. Haneefa ta zaburo da gudunta ta daneta tana mata sannu da zuwa
"Auta na gaji.....mu zauna". Ta fada tana direta saman kujera itama ta zauna a gefanta.
Jakarta ta bude ta fiddo alawa cikin wadanda ta siyawa su aishatu ta musu tsaraba ta miqawa nadra da haneefa
"Karbi huda" Ta furta sanda huda din ta gama goge qasan tiles din inda suka zubda ruwa.
A nutse ta tako,ta zauna a hannun kujera ta miqa hannu tana karba din idanunta akan fuskar Sabreen.
"Komai lafiya ko?" Sabreen din ta tambayeta tana kallonta ganin kallon da huda din ke binta dashi.
Kai ta gyada tana kauda dubanta daga kanta
"Lafiya lau anty" Da idanu sabreen din ta rutsata tana kallonta,kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta buda baki a hankali
"Ko yauma kunnuwanki sun sake ji miki wani magana daga bakunan mutanen gidan nan da kika sakashi a ranki?" Ta mata tambayar tana tattara hankalinta a kanta.
A hankali ta girgiza kai alamun aah
"Huda" Sabreen ta kirayi sunanta kanta tsaye. Daga kai tayi ta kalleta sai kuma ta qara sadda kanta qasa
"Dawo nan ki zauna" Ta fada tana nuna mata gefanta zuciyarta tana bugawa fiye da yadda ya kamata ace ta buga din. Ko kadan bata qaunar taga sauyawar yanayi daga motsin kowannensu. Duniya da mutanen cikinta tsoro suke bata matuqa.....irin tsoron da babu shi a cikin FARAUTARTA amma tana dashi cikin DUNIYARTA data 'yan uwanta. Sune dukka rauninta a rayuwa,sune tsoronta kuma sune kwanciyar hankalinta.
Kamar yadda ta buqata haka ta zamo ta zauna a gefanta,saidai har yanzu bata yarda sun hada idanu ba
"Huda.....kalleni nan" Ta fada tana kausasa muryarta. Yadda ta bata umarni kadai ya gaya mata bada wasa take ba,ta furta umarnin ne tun daga tsakiyar zuciya da kuma ruhinta,don haka ta dago din ta dubeta kai tsaye kaman yadda tace
"Zan maimaita tambayar dana miki,kuma ina buqatar ki bani amsarta kafin nadra da haneefa su sake dawowa dakin nan......mene a ranki?,meye damuwarki?"
"So nake ki daina fita yaaya......ki zauna a gida kaman kowa" Ta fadi muryarta tana rawa. Idanunta sabreen ta maida tadan lumshe kana ta budesu. Fargaba tadan saukar mata,yau huda ce ta fara tararta da wannan maganar,gobe sai nadra jibi sai haneefa?. Tambaya ta yiwa kanta amma kuma tana baiwa kanta yaqinin abinda zai faru kenan a zahiri.
"Kina zargi na ne kema huda?" Tayi mata tambayar takai tsaye tana kallon qwayar idanunta. Kamar maganar ta daketa sosai hakan ya sanyata daga kai da hanzari ta kalleta tana girgiza kai,sai kuma ta sake sauke kan nata qwalla tana gangaro mata.
"Yaushe kika soma zare audugar dana baki ki sanyawa kunnuwanki akan zancan mutane?,yaushe kika samu cikakken zaman saurara da fahimtar maganganun mutane?,yaushe hankalinki ya fara kaiwa nan huda?" Ta furta idanunta suna qanqancewa,wanda hakan zai nuna maka zallar radadin da takeji a zuciyarta.
"Ina nan yadda kika sanni huda.....babu kuma abinda zai canzani......gwagwarmaya da fadi tashin da nayi a baya bai sauyani ba bare yanzu dana 'YANTU.....karki bari zargi shakka ko kokwanto a kaina ya ratsa zuciyarki har ya samu gurbi......bazan iya zama ba huda......bazan kuma iya daina fita ba,don haka ki cire damuwar wannan daga ranki" Ta amsa mata tana miqewa a nutse daga saman kujerar,saidai dukka gabbanta sun saki da gajiya da kuma damuwar data saukarwa ruhinta.
Ta qasan idanu take bin sabreen din da kallo har ta shige dakinsu. Ta janye idanunta tana sanya hannunta gami da dauke qwallar dake tsiyaya daga idanunta. Anya ta kyauta idan har ta sanya zuciyar data sadaukar da komai nata saboda farincikinsu da ingantuwar rayuwarsu.....ta kyauta idan tayi silar sanyata a damuwa?.
Babu kyautawa ko kadan,idan har ta aikata hakan kenan bata da maraba da sauran gama garin jama'ar gari?. Bata da banbanci dasu?,tafi aminta dasu kenan akanta?. Nadama taji tana saukar mata a hankali. Bawai tayi komai bane da gangan,kawai ta kasa controlling din kanta ne akan batun,ta kasa jure abubuwan da takeji take kuma gani kulliyaumin,ita daya kuma tasan yadda takeji a duk sanda akayi magana akan yayartata halitta mafi soyuwa a gareta.
Tana zaune a wajen tana feeling guilty akan maganar,har sabreen ta sauya kaya zuwa wasu riga da wando silk me dogon hannu,rigar tadan sauko mata har saman cinyoyinta,yayin da wandon ya sauka har saman qafafunta. Tayi alwala ta dawo ita da haneefa,nadra na daga waje bakin fanfo tana dora nata ta kalleta
"Ki tashi kiyi alwala,ko kina fashin sallah ne?" Tayi mata tambayar cikin basarwa tana qoqarin zura jilbab dinta. Kai ta girgiza,ta miqe tana takawa a sanyaye tana ficewa. Sanda nadra ta shigo sai tace ta sanya hijab su jira huda din ta shigo sai suyi jam'i kamar yadda sukeyi lokaci lokaci. Zama tayi gefan kujerar falon kafin shigowar hudan tana duba saqonnin cikin wayarta. Tana jimawa bata duba saqon sms ba don bata fiya bashi muhimmanci ba.
Sama sama ta fara jiyo hayaniya daga tsakiyar gidan nasu,saidai bata wani bada hankali ba,don ba baqon abu bane cikin gidan nasu musamman lokaci irin wannan. A hankali hayaniyar ta fara yin yawa,sai kuma ta fara jin kamar muryar huda cikin hayaniyar. Abinda yaja hankalinta kenan,ta daga kanta daga wayar tana duban nadra da itama tayi kasaqe tana sauraro,saidai batace komai ba,ko wala'alla itama tanason gane cewa muryar hudanne ko ba ita bace. Baqon abune ga dan dakinsu wato yin hayaniya ko daga murya kaman haka. Basu da abokin fada ko adawa,kamar yadda har mahaifiyarsu tabar duniya bata da abokin fadan,saidai kai kayi dasu idan kaso hakan. Hudan ce ma mai dan zafin rai wani lokaci da kuma rashin dagawa duk wanda ya shiga gonarta. Sabreen ta shafeta sosai......amma yana da wahala ka gano haka saboda miskilanci da rashin son shiga shirgin mutane.
A sannu ta tanqwarata ta koya mata hadiye fushi,a dole kuma sukaci gaba da tafiya kan wannan bigiren har kawo inda yanzu rayuwa ta ajiyesu.
"Dubamin.....kamar muryar huda nakeji" Sabreen ta fadi tana duban nadra. Da hanzarinta nadra din ta miqe,don dama abinda take jiran ji kenan daga sabreen. Bin nadra tayi da kallo har ta fice,saidai kafin dawowar nadra dakin kunnuwanta sun bata tabbacin huda ce,saita ajiye wayarta gefe tana duban haneefa
"Auta qarasa karatunki.....kada ki fito ina zuwa" Kai haneefa ta daga idanunta a raunane tana bin sabreen da kallo har ta fice.
Kusan duk wani ahali na gidan dake cikin gidan yana tsaye a tsakar gidan banda mace qwaya daya.....mace guda daya tak da koda mutum zaa dafa a gidan sai tayi niyya ko ra'ayi zaka ga gilmawarta a shiyyar tsakar gidan ma bare akai ga farfajiyar gidan.
Tun kafin ta qarasa idanuwanta suka gane mata da wadda akeyi. Huda da hadiyya......suna tsaye tsakiyar mutane kowaccensu tsamo tsamo a jiqe da ruwa,ruwan da bata raba dayan biyu ruwan wankin da hadiyyan takeyi ne da kuma wanda ke zuba yanzu haka daga famfo.
Kwalar huda na hannun hadiyyan cikin zafi da zafafa
"Zanga uban daya tsaya miki cikin gidan nan.....kibar ganin kamar kun isa kun bunqasa......kun riqar da ba'a saku ba'a kuma hanaku......ni bariki da duk wanda ke cikinta baya bani tsoro wallahi" Ta fada tana waro idanunta waje.
Idanu sabreen tadan runtse kadan tana jin wani abu me zafi yana saukar mata. Ta sani yau Allah kadai yasan adadin tarin maganganun da kunnuwansu zasu amsa cikin gidan. Maganganu ne da aka tarasu cikin qiraje ana neman ranar zubda su,amma ba'a samu ba saboda kiyayewarsu da shiga hurumin kowa sai nasu......yau kam da dama ta samu ba shakka sai iya abinda sukaji.
Bata cewa kowa komai ba sai kutsa kai cikin mutanen data dinga yi a nutsenta sanye da hijabin sallarta,abinda ya dinga jan hankalin kowa da fitowarta kenan.
Bata tsaya ba har sai data isa tsakiyar inda suke abun,a sannan ran huda yayi bacin da itama ta cakume hadiyya. Abinda ya tunzura hadiyya kenan ta daga hannunta a zafafe ta saukewa huda lafiyayyen marin daya sanya huda din sakinta ba shiri.
Cikin tsananin fushi hudan ta zabura don maida martani sabreen ta iso tsakaninsu
"Karki soma" Sabreen din ta fadi duk da ita kanta tasan marin da hadiyyan tayi shiryayye ne da ko waye aka yiwa shi sai yaji matuqa a jikinsa.
"Barta.....barta.....ta tsammaci ni din sa'arta ce,batasan ko yayartata da take kallon kanta jan wuya ba ni nasha gabanta wallahi faufau"
".....yaaya.....kina jin abinda take fadi?,kina ganin abinda tayimin?" Huda ta fadi muryarta na rawa,kuka yana shirin qwace mata amma bataso tayi kukan don bata shirya yinsa a gaban wadannan azzaluman ba. Mutanen da babu rahama tausayi jin qai ko imani a zukatansu a tattare dasu. Mutanen da d'ai basa kallon maraicinsu basa kuma kallon komai a tattare dasu face zallar sharri da mugun fata tare da mummunar makoma.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 40
Idanunta ta lumshe tana gyada kai
"Ya isa huda.....ki wuce daki.....karki sake tsaiwa a nan" Ta fadi tana duban idanun huda. Kai hudan ta jinjina,da alamu umarnin sabreen din ya mata nauyi da yawa,da alama a yau ta bata umarnin da takejin matuqar nauyin bi da dauka.....umarnin da zuciya ke raya mata kamar ta takeshi
"Aikin banza aikin wofi.....ni wallahi na riga na tserewa mutum.....duk iya barikinsa saidai ya ganni ya qyale,ba wanda nake tsoro ko shakka,hakanan babu wanda zan dagawa qafa" Hadiyyan ta fadi tana jujjuya jiki cike da jin taqamar ta daki hudan a bulus.
"Ke meya kaiki ma kulasu?,mutumin da yake kan hanyar samun kwalin degree a fannin likitanci?" Cewar bibo tana bin bayan sabreen da harara wadda tuni ta fara takawa tana barin wajen
"Qyaleno bibo....wani lokaci ajjiye karatun akeyi ai ka nunawa mutum kaima fa ka iya barikin nan ehe...tarbiyya ke sawa kake dage qafa"
"A'ahhh.....akul,zuba ruwa ki kurkure bakinki,'yar nan meye hadinki da bariki?,bariki fa?,suma jaza musu akayi.....don ko yaya ka taba bariki dai dole a samu me gado kota nono sa zuqa" Cak ta tsaya daga tafiyar data fara yi zuwa daki,bugun zuciyarta nason qara yawa dajin lafazin bibo
"Aikuwa dai an tafi lahira an bar musu gado mara amfani wallahi" Hadiyyan ta fadi tana gyara daurin zaninta tana gatsina fuska.
Lafazin hadiyyan ya sanyata waiwayowa,wani irin zafi takeji yana sauka mata a qirji,ranta yana wani irin mummunan baci
"Akul hadiyya.....kul dinki......hawainiyarki ta kiyayi ramar iyaye na...." Kammala daura zanin tayi da gaggawa ta maida hannunta ga qugunta duka tana riqe dasu,fuska da bakinta cike fal da isgili rashin mutunci da wulaqanci,idanunta tsakiyar na sabreen
"Idan naqi ji fa?,kina da sauran wani abu da zakiyimin ne sabreen?". Kai ta dauke sabreen din,tana hadiyar wani yawu me tauri tamkar dunqulallen dan waken da ya tsaya a maqogaro. Kamar ba zata tanka ba kafin ta waiwayo,a nutse ta kalli idanunta tace
"Ki gwada qinjin gargadina mana hadiyya koda na minti guda ne kiga abinda zaya faru?" Ta qarashe maganar cikin jin zuciyarta da ruhinta sun taurare. Akan batun iyayenta kuma komai tana iya aikatashi muddin hakan zai sanya ta kare mutuncinsu daga baki da aibantawar mutanen da basusan me ake nufi da daraja da kuma kimar dan adam ba
"Hadiyya.....rabu da ita.....karki sake ce mata komai don ke din tsatson mutunci ce......kuma muddin hassada tana dawainiya da mutum akan ci gaban daka samu da kulawa ta iyaye komai ma zai iyayi maka don ganin kun dawo daya kai dashi" Kalmar HASSADA ta sanya sabreen waiwayowa ta kalli hadiyyan da bibo din gaba dayansu. Banda yadda ranta yakai maqurar baci da babu abinda zai hanata murmusawa. Wata kalma ce da take daidai da hali da kuma abinda ke cin zuciyarsu a kanta,shine sukeson sanya dukkan qarfinsu su juyar da ita zuwa kanta.
Tana jiyo bibo tana ci gaba da soki burutsunta,sai bata bi takai ba,ta dinga takawa a hankali abinta har ta wuce zuwa dakin su.
Wani zafi da zugi zuciyarta takeyi mata. Wani irin radadi data jima bata ji irinsa ba saboda kawar da kanta daga harka da sabgar kowa a gidan. Tana kallon yadda huda ke zaune tana kuka amma batace mata komai ba. Tasan kukanta guda biyu ne,na tadda hadiyyan taci mutuncinta dasu gaba daya amma sabreen din ta hanata maida martani.
Ita nadra da haneefa sukayi sallansu,don har suka idar huda din tana zaune tana kuka. A hankali ta maida idanunta kan hudan,tana jin tausayinsu dukka yana kamasu. A hakan a sanda rayuwa ta fara musu kyau. A hakan a sanda ta jajirce akansu.....a sanda basu nemi komai a gurin kowa ba......a sanda asirinsu yake a lullube ba tare da sunyi ROKO ko bara ba.....ba kuma tare da sun nema komai a wajen kowa ba......ya rayuwa zata kasance musu a sanda dukka babu wadannan ababen data lissafa?.
"Ki tashi ki dauki pure water kiyi alwala cikin kitchen" Tace da ita tana ci gaba da sauke kanta qasa. Abubuwa ne cunkus masu yawa qasan ranta. Har tayi sallar nadra ta zuba musu abinci daga ita har hudan ba wanda ya samu damar sanya komai a cikinsa. Ta kama haneefa ta tsefe mata kanta,don ba abinda take bari suyi cikin unguwar,bata bari kowacce kalar mu'amala ta hadasu da kowa,tana kaffa kaffa da komai nasu,ta nesanta su da mu'amala da kowa don kiyaye jinsu da kuma ganinsu,tana dubansu tace musu
"Gobe zamu fita kitso,ke nadra kece me nauyi,bazanyi jira ba me yawa don da wuri zamu dawo gida in sha Allah".
"To" Suka amsa mata gaba daya. Ta miqe a nutse ta barsu a falon,don tasan ba zasu kwanta yanzu ba har sai sun gama kallon film din da ake haskawa.
Numfashi ta sauke me nauyi sanda ta zube ruf da ciki saman gado tana lumshe idanunta,sai takejin fitar numfashin tamkar raguwar radadi ne daga zuciyarta. A haka idan ka kalleta zaka dauka bacci takeyi,amma idanunta biyu tana ci gaba da sauraron motsin su nadra jifa jifa daga falon. Radadin da rayuwa ke tafe dashi take tunawa daki daki. Ba wani majibancin al'amari da zata sanya kanta saman kafadunsa tayi kuka.....ba wanda zata amayarwa da irin radadin da takeji.....ba abokin shawara.....ba abokin raba dadi da akasinsa,sai nauye nauye dake aje saman kanta masu tarin yawa.
Har suka kammala komai sukayi shirin bacci suka kwanta tana jinsu,sai da kusan bacci ya daukesu sannan ta miqe don samawa kanta abinda zataci,daidai lokacin taga motsawar huda.
"Huda?" Kai tsaye tayi kiran sunanta don ta tabbatar batayi bacci ba kenan. Abinda kuma ke alamta mata bacin ran da take ciki ne har yanzu yake nuqurqusarta.
Qasa qasa ta amsa mata,sai ta umarceta ta tashi ta zauna. Ba musu ta yaye abun rufar ta miqe ta zauna tana dubanta. Takawa tayi zuwa gaban gadon ta zauna idanunta a kanta. Ta zuba mata idanu na wasu mintuna ta zuba mata,abinda ya yiwa hudan nauyi tayi qasa da kanta,ta buda bakinta a hankali tana jin tsanar gidan dama duka mutanen ciki
"Kiyi haquri adda"
"Yanzu meye ribarki huda?,wace riba kikaci bayan kin tsaya kin biyewa hadiyya?,shikenan kalaman da kunnuwanki keson ji daga bakinsu kinjisu hankalinki ya kwanta?". Hankalinta taji yadan tashi,tsanar rayuwar gidan tare da ci gaba da rayuwa ma a cikin gidan duka tana saukar mata. Ta girgiza kai idanunta suna tara qwalla me yawa
"Ba haka bane adda......bakiji abinda suke fada a kanki bane?,bakiji mummunan jifa da qazafin da sukeyi miki ba?" Ta fada hawaye na saukar mata.
Yawu itama ta hadiya tana qoqarin hana nata qwallar fita,duk da ba qaramin abu bane yake sanya fitar hawaye daga idanunta ba
"Ki barsu suyita fada mana huda?,meye zai gutsireni?,mene ne kena zai gutsireki?......shin kin manta su din su waye?,ko kin manta ne huda?" Kai ta girgiza qwaqwalwarta na tunano mata abubuwa da dama daga halaye da dabi'un mutanen gidan.
"Wannan ya zama lokaci na qarshe da zaki sake maida kai cikin shirginsu"
"Kiyi haquri" Ta fada bayan ta gyada kai
"Ya wuce......ki kwanta hakanan" Ta fada tana dan taba kafadarta.
Dukka wayoyinta ta dauka harda ma wadanda ta basu hutu na satittika dana watanni,sannan a nutse ta wuce zuwa falon. Bata zauna ba sai data zuba abinci,duk da cin abincin nata har kullum tamkar wasan yara yake. Takan tuna umminta duk sanda ta zauna irin haka zataci abinci
"Kedai saidai addu'ar shiriya sabreen.....yarinya kamar mage?,ki dinga lasar abinci?,zakici ba zakici ba?,shi yasa kikejin jiki idan ciwonki ya tashi". Numfashi ta sauke,ta saka hannu tana goge qwallar data cika mata idanu.
Babu wani lokaci ko yanayi da zaizo bata tuna umminta ba. Ba wani dan qaramin sakan ko minti da zaizo ba tare da tuna umminta ya sanyata zubda hawaye. Bangwaye guda biyun da zubewarsu ya sauya rayuwarsu daga wani abu izuwa wani abun na daban.
Kunna wayoyij tayi gaba dayansu ta kuma jeresu a gabanta,ta jawo abincin tana qoqarin tilastawa kanta ci,idanunta na yawo tsakanin fuskokin wayoyin. Haske kusan dukansu suka dinga yi alamun shigowar saqonni zuwa gareta kena. Ta saba da irin hakan duk sanda ta baiwa wayoyinta hutu toba shakka zata samu saqonnin da basu da adadi. Da yawansu tana gogesu ne ba tare da tako duba ba,d'ai d'aiku daga ciki take tsaiwa dubawa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*_Arewabooks:@Huguma_*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
__________________________
PAGE 41
Kusan a tare wayoyi uku suka dauki ruri dake nuna alamun ana kiranta.
Mashkur mikail da ya'aqoub,abubuwan farautarta da batasan waye a ciki zai fada komarta ba. Ta dinga bin sunayen da wayoyin da kallo cikin canki cankin wanda zata fara daga wayarsa a ciki har sai da suka katse,sai ta barwa ranta wanda ya soma sake kira. Saidai kuma cikin rashin sa'a sai ga mashkur da mikail suna kiranta lokaci guda. Plate din hannunta ta ajiye,ta sanya hannu tana daukan kiran mikail. A lissafinta shine mutum na farko da takeson saukewa daga layinta. Dukka wani binciken halayya nasa suna gwada mata tsantsar dacewar ya karbi sakamako da horo yadda ya dace. Ita kanta batasan adadin abinda zata diba daga gareshi ba,saidai ko banza ta sanya zata sanyasu a muhalli da guraben da suka dace.
A jirkice yayi mata sallama da muryar data sanya ta saka masa ayar tambaya. Ta daga wayar daga kunnuwanta ta duba fuskar wayar tana mamaki
"Bayan neman mata harda caca da harqallolinsa harda shaye shaye?" Ta tambayi kanta cikin mamaki,sai ta maida wayar kunnenta kawai tana saurarensa.
"Sai yaushe zaki bani dama ne?......ina tsananin kewarki......ina son kasancewa dake" Abinda ya fada kenan yana jin kamar ana fusgarshi zuwa gareta. Katse wayar tayi tana jan dogon tsaki. Baci kawai takeji ranta yana yi kota ina tare da azalzala mata akan mikail. Sai ta jawo wata qaramar waya daga gefanta wadda bata hasken komai ba ta turawa JIB qaramin saqo. Tana jin ya kamata aikinta ya fara ta kansa.
Yadda mashkur yaketa kiranta ba daga qafa ya sanya ta share kiran ya'aqoub ta daga nashi. Kiran ya'aqoub din ma bata mata rai yakeyi,ta tabbatar dukkan wani magidanci me mata irinsa a yanzun yana cikin gidansa ne koda a dakinsa ko a sassan yake. Taga maza da yawa da halayensu,daya daga cikin halayyar tasu kuma da tafi baqanta mata rai take tunzurata shine wannan. Wai ta yaya ma zatayi Aure?,bayan bataga komai ba a tattare da mazan sai munanan dabi'u dake girgiza zukatan matan su haifar musu da muguwar illar hawan jini ko ciwon zuciya?,ko mummunan zawarcin da har ki mutu bazai fita a tarihinki ba?. Har abada tana kallon zaman 'ya mace me cikakken 'yanci a yayin da ya kasance babu igiyar wani a kanta.
"Saura kadan ki kashemin raina muhseena......hala bakisan girman soyayyar da nake miki ba har yanzu?......kinsan Allah?,banqi a daren nan ace an daura aurena dake ba?"
"Aure?" Ta furta a hankali tana jin kalmar tayi mata girma da yawa.
"Yes aure muhseena....." Ya maimaita fada yana gyara zamansa cikin tattausar sofa din da yake kai. Yana fatan samun gamsashen amsa tare da mamakin kansa yadda yarinyar ta sauya masa tsari gaba daya.
"Gaskiya ne" Ta amsa masa a taqaice tana aje numfashi.
Hira ya dinga qoqarin janta dashi,duk da ita din bame doguwar hira bace amma ta dan sake masa,don itace hanya guda daya da take dashi da zata haska mata hanyar gano gurbin da zata dasa bomb dinta.
"Kiyimin alfarma daya mana......ki gaya min credit dinki na yimin rakiya dubai for just one week......ni kuma nayi alqawari zan biya ko nawa ne" Ya fada yana sake jin kowacce gaba tasa tana narkewa da sha'awarta da sonta. Yanajin koda bata shirya aurensa ba......zai kashe mata ko nawa ne suyi irin rayuwar da yake muradi......idan da yiwuwar ta zama tashin a gaba sai ta zama.....idan ma hakan bata samu ba yana ganin duk inda ta kwana sha ne muddin ya tsira da abinda yake qulafucin samu.
"Zan baki dama kiyi tunani......sannan ki yanke ko nawa kikeso muhseena.....ko nawa ne muddin raina zaikai ga muradinsa".
Maganarsa t qarshe kenan data sake sanyawa sabreen mummunan zato ga maza......maganarsa ta qarshe data sanyata ta kusa raba dare tana kuka......ta kuma dinga godewa Allah ta wasu fannin.
Mashkur din data tura masa mabanbantan mabuqata da buqatar neman tallafin da duka duka baikai ko digo cikin abinda ya mallaka ba yasa aka koresu?......yace bashi dashi?.....yace bazaya bada ba?......wannan mashkur din yau shike bada damar a nemi ko nawa ne zai iya mallaka mata bisa rashin sanin WACECE ITA?.
Hakan tamkar wata dama ce a gareta kenan da zata samu dukka kudaden da takeso......amma bisa sharadin sadaukar da abinda yafi komai mutunci a tare da ita?.
Koda ta saba ko tana da damar accepting masa abinda yazo dashi.......tabbas ba zata lamunce ba......tanaso ta debi kudadensa ta hanyar data saba azabtar da sauran.......tanaso ta debesu ta hanyar da zaiji ciwon da bazai kankaru ba a zuciyarsa.......tanaso ta debi kudin da zai tsaye masa a rai......yayi masa ciwo fiye da yadda rayuwa da zukatan matan da ya fadawa mutuncinsu sukayi musu ciwo......tanason bashi darasi me girma a rayuwa.......tanason shima ya girgiza girgizar da zata tsaida masa komai na rayuwarsa cakkkkk koda ba tsaiwa bace ta har abada......to amma kuma ta sani.......babban plan da yake buqatar nutsuwa da tsare tsare masu yawa. Don haka da safiyar washegari ta tura JIB wani saqon da sunan mutum biyu.
Tana tsaye tana shan ruwan dumin da takesha duk safiya kafin shigarta wanka saqo ya shigo wayarta. Sanda ta duba sai ta samu alert na kudi daga wajen ya'aqoub. Five hundred thousand ce,sai ta gyada kai a hankali tana sakin murmushin takaici. Don kyauta yana da kyauta ya'aqoub ba daga baya ba......abinda bata da yaqini shine haka yake a cikin gidansa?,ko shima fankan fayau ne?.
Saqon godiya ta tura masa a gajarce,ta aje wayar tana shirin wucewa wanka wani saqon ya sake shigowa
"Patiently waiting for you" Share saqon tayi hade da sauran. Tasan me saqonsa ke nufi a gajarce. Kowacce safiya izina ce a gareta,kowacce rana kowanne sati da kuma kowanne wata cikin rayuwarta yana bude mata babi na abubuwa da yawa cikin rayuwarta. Waishin akwai ragowar NAGARTATTUN MAZA kuwa?,tambayar da kullum idan ta yiwa kanta ita take bawa kanta da kanta amsa da BABU.
Kanta tsaye take takawa cikin tsakar gidan nasu ba tare data daga kai ba bare ta lura da waye a hagunta ko damanta?. Ba tare data damu da kallon nan nasu data tabbatar a safiyar yau zai ninka ko ma ya canza salo saboda abinda ya faru a jiya.
Dab da zata sanya qafarta a qofar toilet din nasu dake da sassa biyu bathroom da toilet ta jiyo muryarsa yana koda sallama. Sallamar da muddin ya yita duk wani dake da hadin kai dashi take masa dadi......duk wani wanda yake da qulli dashi Kuma yake neman yin ta kansa,mutane kuma kamar ita sukejin kamar su turashi ya koma muhallin da ya fito.
Koda taso tayi shigewarta toilet din ta tabbatar sai ya ganta don ya iso dab da wajen. Don haka ta tsaya a nutse tana bude toilet din ta hanyar murza handle,abinda ya bashi damar qarasa shigowa farfajiyar tsakar gidan.
Da ita ya fara hada idanu kamar yadda nata idanun suka zube a fuskarsa. Kamanni dai da mahaifinta har kullum sune,bata kuma fasa ganinsu shimfide a fuskarsa,saidai nisan tazarar halayya da dabi'un sun kai girman tazarar dake tsakanin sama da qasa.
"Yauwa alhamdulillah......ai gwara dana sameki cikin gidan.....zuwan dama naki ne" Kallonsa kawai tayi ba tare da wani mamaki ba,dama wanne zuwa ne zaiyi gidan ba nata ba?,koda yayi zuwan daba nata ba to lallai daga qarshe sai ya zama nata ko kuma ya hado da ita a abinda bai zama damuwarta bama bare y shafeta. Amma tun a jiya tasan tabbas dama zayazo,shi yasa taso su fice kitso da wuri yazo ya taras da sararinsu kawai.
"Ina kwana kawu?" Ta fada cikin girman nan da bata fasa bashi shi kaman yadda kowa cikin gidan ke bashi duk kuwa da farin sanin da tayi na waye shi?,sanin da kaf gidan tayi yaqinin ba wanda ya masa shi......sanin da a qa'ida ya cancanci ta rainashi......amma sai kuma batayi hakan ba.......sanin da ko yaushe ta tunashi dashi take jin kaico da bacin rai da rashin sanin son ganin gilmawarsa.
"Lafiya qalau......idan kin baro bandakin ki sameni a dakin bibo" Ya fada yana saba babbar rigarsa yana wucewa ciki tare da jaddada sallamarsa.
Da kallon takaici ta bishi,tasan dama zaa rina,ba wani abu da zai fari cikin gidan ya kwana ya hhantse baije kunnuwansa ba.......yana kuma zuwa kunnuwan nasa ne ta hanya guda daya rak wato BIBO. Idanma akwai ta biyunta to bata bayyana ba tukunna. Cikin rashin damuwa da lamuransu gaba dayansu ta kada kanta ta wuce bandakin.
Babu wani abu da zai sanyata gaggawa a zuwa kiran data tabbatar babu alkhairi sam sam a tare dashi. Wannan ya sanya ta kammala wankanta a nutse,takuma tsaya gaban madubi ta shirya tsaf kamar yadda ta saba. Tun bata kammala ba ya aiko kiranta ya kusa sau biyar. Ana shidan ta tsaida nadra da taji tana gaya musu cewan kaya take sanyawa
"Kace gani nan zuwa" Ta fadima usman daya aiko. Rigar lace tayi niyyar sakawa,don haka ta fara sanya 'yar cikin rigar ta yane kanta da mayafi ta zura slippers dinta tana cewa
"Ku kammala shiryawa ina dawowa zamu wuce" Ta qarasa fada tana sanya qafafunta a waje,huda kuma ta bita da kallo. Sam bataso ace sabreen din taje da kanta kamar yadda kawu ya buqata ba,ta tabbatar da cewa ba wai wani abun arziqi zai aiwatar ba face tsantsar son zuciya da son rai kamar yadda suka saba. Ba wani lokaci da abu irin haka zai taso cikin gidan ya zamana anyi hukunci cikin adalci da sanin ya kamata.
Hankali kwance ta daga labulen dakin bibo gami da sallama. Su uku ne cikin falon,kawu bibo sai hadiyya dake zaune saman daya daga cikin kujerun. Qafarta daya saman daya tana kadata a hankali. Tako ina tana jin kishin wanzuwar komai dake tattare da sabreen din. Kowanne abu tana yinsa ne don kawai ta samu daqile sabreen din. Ba haka takeso ta bude idanuwa ta ganta ba. Wani qaqqarfan abu ya dasu a ranta game da sabreen din.
A haka mutane ke raina matakin da take kai.....suke mata kallon wadda ke tafiya bisa baragurbin bigire......amma ita a nata idanun ta sani cewa sabreen din tayi mata wani irin nisan tazara me tarin yawa. Bataso ta ganta a haka.....ba'a haka take da muradin ganinta ba,tana son ta sauya daga matsayin da take kai a yanzun,shine abu daya da zai gamsar da ita.....
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*_Arewabooks:@Huguma_*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
________________________
PAGE 42
Janye dubanta tayi daga kan hadiyya,sai ta nemi hannun kujerar dake daga bakin qofa ta zauna akai,wayarta a hannunta tana qoqarin sakata a silent. Ta manta yaushe ne lokaci na qarshe data shigo wannan dakin,bama shi ba,dukkan wani daki dake cikin gidan ba muhallin shigarta bane.
"To da kika shigo kikayi mana derere saman kujera ai sai ki sauko ko?" Muryar bibo ta rasa kunnenta. Dauke dubanta tayi daga saman wayar ta aza a fuskarta. Abubuwanta sun fara mata nauyi akai,tanason ta fara shige huruminta. Tana ganin kima da martabarta a matsayinta na macen data taba kasancewa mata a wajen mahaifinta,amma ta lura da sam sam bata kula da wannan.
Dauke idanunta tayi daga kan bibo din,tana ji a ranta lokaci ya kusa da zata sassauta wannan girma da martabar da take bata,tunda har ita din ta gaza riqo dasu yadda ya kamata
"Gani" Ta fadi kai tsaye tana duban kawun. Zamansa ya gyara yana wani hakimcewa. Jira yake su kammala da maganar da aka tattagoshi a kanta ya gabatar da nasa batun wanda shine yafi damunsa
"Yanzu ke......wani irin baqin hali gareki ne?.....kin fita ZAKKA ke kadai?,kin addabi kowa kin damu kowa?,a gidan nan kaf babu wanda yake da matsala sai ke?" Duk da tasan qarshen zancan,ta kuma san abinda ya sanyashi debo dogon zance har haka amma sai maganganun nasa suka bata mamaki. Banda tsabar rashin son zaman lafiya na mutanen gidan......a yanayin yadda ta tsara rayuwarta dana 'yan uwanta,ya kamata ace tana cikin sahun jerin mutanen da za'a mance da wanzuwarsu cikin gidan. Zaka jima baka ga gilmawarta ba,zaka jima baka ganta zaune a farfajiya ko filin tsakar gidansu ba.....zaka jima baka ganta a tsaye tana magana da kowa ba,to wai shin me ta tsarewa bibo da ire irenta cikin gidan?.
"Wani abu akace maka ya faru?" Tayi tambayar tana tsareshi da idanu. Fada yakeso rufeta dashi kamar yadda bibo ke buqata.....amma kuma yana duba da tunanin kada hakan ya sarayar da samuwar tashi buqatar.
"Yo har sai ance miki ma wani abu ya faru cikin gidan nan banda raini?.....me ya kaiku shiga hurumin yarinyar nan banda neman tada zaune tsaye?,yarinyar da babu abinda ta sanya a gaba banda karatunta?,inajin kaf cikin yaran marigayi babu kamarta ko akwai?" Ya qarashe tambayar yana maida dubansa kan bibo da taketa cika tana batsewa. Dukka salon fadan daya dauko babu wanda yayi mata
"Ina fa?.....mu irin karatu ne,kuma karatu shine a gabanmu" Ta fada tana gyara daurin dankwalinta.
Da idanu kawai take binsu tamkar bata fahimtar koda kalma daya daga cikin maganganunsa,har zuwa sanda yakai qarshe ya kuma jona da tambayar bayyana fifiko me yawa tsakaninsu da hadiyya.
Tsam ta miqe tana duban kawun
"An gama?,inaso na fita ne" Ta fadi kai tsaye ba tare da tayi duba ga sashen da bibo ke zaune ba. Dukkaninsu idanu suka zuba mata su ukun,yayin data juya a hankali tana nufar qofa ganin kawun bai iya cewa komai da ita ba.
Cikin tsananin jin zafi gami da yunqurowar wani boyayyen zazzafan kishinta a kanta ta sauke qafafunta tana aje wayar hannunta gefe
"Kin gani ko bibo?,ai dama na gaya miki......wallahi bata kunya ko shakkar kowa......ni nasan kawu ba matakin da zai iya dauka a kai....."
"Ke!.....yimin shuru,rashin kunya zakiyimin?" Ya fada cikin fadan nan nasa yana rarraba idanu. A duniya idan akwai abinda ya tsana itace kalmar YA KASA KO YA GAZA
"Aah dakata sule......" Bibo ta fada tana daga masa hannunta daidai sanda kunnuwan sabreen sukayi nisa daga jin cecekucensu.
"rashin kunya har takai wadda waccen figaggiyar gantalalliyar yarinyar tayi maka.....tambadaddiya da ka kasa saitota cikin yaran dan uwanka......kaf dinsu yara mata goma sha tara amma ita daya ta fita ZAKKA?,to kada kazo kace zaka zaqemin akan yarinya......me laifi daban wanda za'a huce a kansa daban?". Ransa ya baci sosai,don shi din irin mutanen nan ne da basa son raini ko wargi ko qanqani. Banda ma bibo din da taga wallensa......kaf yaran gidan tsoro da shakkarsa suke idan ka cire SABREEN din
"Ke hajara......dakata,hawainiyarki ta kiyayi ramata......kibar ganin ina daka ta taki.....wallahi ina nan yadda kika sanni......kawai ina duba wasu abubuwa ne nake rama miki halacci da halacci......amma tunda iskancin naki a kaina zai sauka a gaban qaramar yarinya irin wannan......to shikenan......ni na zare hannuna daga sha'aninki cikin gidan nan......" Ya fada yana miqewa cikin hargagi gami da kakkabe babbar rigarsa.
"Haba sule.....zauna mana kaji......ba haka nake nufi ba.....ni dadina dakai wannan masifar taka da jarabar". Tsaiwa yayi yana hade rai gami da dubanta
"Ba haka kike nufi ba hajara gayamin abinda kike nufi". Sai kuma ya waiwaya sashen da hadiyya ke zaune
"Tashi ki bawa mutane guri kin zauna kina raba idanu a gabansu" Ya fadi mata cikin tsawa kamar zaibi ta kanta. Wayarta ta dauka sumi sumi tana yin hanyar shigewa bedroom din bibo din,qasan ranta cunkushe fal da baqinciki. Baiyi mata yadda takeso ba,ba kuma haka takeso ya yiwa SABREEN ba. Batasan dame sabreen din ta fisu ba da har tauraruwarta tafi tasu haske cikin gidan,duk da tayi yaqinin ko meye sabreen din zata juya ta kuma nunawa duniya shi to ba shakka ya samu ne daga dattin ZINA da kuma dattin BARIKI. Ba abu mafi daure kai irin mazan dake karakaina a kanta tamkar su sadaukar mata da rayukansu......amma ta gaza cafke koda guda daya ta maisheshi mijin aure?.
"Mazan bariki dama suna auren macen da suka hadu da ita a bariki?,ai saidai su tsotseta tas.....su musaya wannan zaqin da gardin da suka samu daga gareta da 'yan kudaden da zasuyita mata barinsa......daga sanda buqata kuma ta biya su tattarata su watsar su qara gaba zu zabi wata". Sai ta tuna maganar da sukayi taba yi da bibo wadda ke kamaceceniya da kalmomin maleeka roommate dinta. Juyi tayi kadan saman gadon,tana da burika masu tarin yawa akan karatunta,wannan ya sanya ta sadaukar da rayuwarka akanshi. Tana so ta ganta tana fantamawa,tanason ta ganta tana haskawa tamkar sabreen da dukkan wani alatu da jin dadi......tanaso taga maza suna mutuwa a kanta sama da sabreen......amma dukka ta hanyar karatunta da kyawun sura da Allah ya bata. Tana cikin sahun jerin farko farko da 'ya'ya masu kyau a gidan......ta tabbata ko wannan ya isheta jari wajen zaben kalar mijin da take buri da muradi idan aka qara da karatunta da takesa ran kammalashi ta kuma riqi kyakkyawan certificate mafi girman daraja a idanun mutane.
Ta samesu a zaune sun gama shiryawa sanda ta koma dakin. Kai tsaye ta wuce can ciki ta jawo rigarta ta sama ta zura,ta hada igiyoyin ta daureta ta zauna dai dai jikinta,abinda ya bawa rigar daman fidda kyakkyawan shape din nan nata da ba kasafai ya fiya bayyana ba saboda ita din ba ma'abociyar sanya damammun kaya bace. Sai data sake goge jikinta da sassanyan oil perfume dinta sannan ta fara rolling dan kwalinta saman kanta idanunta akan fuskarta data bayyana tarwai ta cikin madubin.
Maganganunsu taketa tattaunawa ita da zuciyarta. Dabiar kawun dama bibo gaba daya. Yadda tsahon lokaci da zamani bai sanya kowannensu ya sauya ba. Ranta da zuciyarta duka ba dadi. Ta iya rigima tuburan idan taso......ta iya surutu har kayi zaton ma ba ita bace......hakanan ta iya fada musu da kuma taurin kai......amma daga sanda rayuwa ta soma Karantar da ita wasu darussa sai ta gane basu take buqata ba,don haka ta tattarasu ta aje a gefe.
Jakar da zata dace da shigar da kuma yanayin ta dauko. Kaman yadda ta saba duba jaka kafin takai ga fita da ita haka ma wanna,a nan taci karo da kudaden da mashkur ya bata. Maidasu jakar tayi da zummar damqawa suraj su,daidai lokacin haneefa ta shigo tana kiranta
"Kizo inji kawu sule"
"Kawu kuma?" Ta tambayi haneefan tana duban idanunta
"Eh" Kamar ba zata mata komai ba,sai ta fesar da iska daga bakinta. Tasan dukkan abinda zai sanyashi shigowa wajenta baya taba zame mata abun alkhairi face tarin matsaloli fadace fadace da fadin maganganu barkatai da zasu yamutsa DUNIYARTA tana zaune salin alin
"Kice masa gani nan" Ta bata amsa tana juyawa sashen ajiye takalmanta ta fara dubawa. Takalma ne kala kala masu mabanbantan shape kudi da kuma kaloli. Wani adadi ne me yawa ma'ajiyar takalman taci,wanda dukkansu idan ka kalla babu takalmin qasa sa dubu goma.
A duk sanda ta kalli sashen suturar data mallaka a yanzu,a karan kanta mamakinta yana sake ninkuwa ne. Suturu na alfarmar da yaran masu hannu da shuni ke taqamar mallaka ko jin isar cewa sun kai. Daya daga ciki ta zaro,ta aje a qasa ta zura a qafafunta sannan ta debi wayoyinta ta jefa a jaka tayi hanyar fita tana ji a ranta ko sisi a yau din bazai samu daga wajenta ba muddin abinda ya shigo dashi kenan.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 43
___________________________
GROUP 1
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
*_assalamu alaikum warahmatullah_*
*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_*
*_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_*
*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_*
Shadda
Laces
Atamfa
Kayan yara English wears dana jarirai
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Huluna na maza da mata yara da manya socks
Takalma na maza da mata yara da manya
Lafayas
Sarqoqi agoguna banguls da rings
_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_
_bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*
*_masu manyan qarfi da matsakaita?_*
*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_*
*_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_*
*MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA*
*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
*_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_*
*_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
GROUP 2LINK
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
_________________________
Samunsa tayi zaune dirshan saman carfet yana karakaina da kwanukan da suka gama breakfast. Ya buda flask din da suka zuba dafaffen naman kai wanda sukaci suka bar sauran sai zuwa dare. Yana cikin ire iren siyayyar da take musu lokaci bayan lokaci dukka a qoqarinta na ganin basu rasa komai ba......basu nema komai sun rasa ba......hakanan komai din bai gagaresu ba. Tana da buri me yawa akansu,tana da mafarki mai fadi......tana kuma fata da sanya ran wataran zata basu rayuwa fiye da wadda sukeyi a yanzu haka.
Daga kai yayi yana dubanta sanda yake tauna naman,zaqin maggi yana ratsashi.
"To zauna mana banda abinki,kikayi wani dogogo saman hannun kujera?" Ya fadi saboda yadda ta kame a hannun kujerar rungume da hannayenta. Sam batason ya bata mata lokaci ta kuma fahimci zuwa yayi yaci mata lokacin
"Kawu ai ina tunanin wancan maganan mun gama da ita ko?,fita nakeso nayi ne ana jira na" Ta fada tana duba agogon hannunta.
"Kefa kin fiya tsiya da hurwar banza da wofi,ayita tattaroki kina wargajewa?,har sai kin jawo magauta sun jimu?" Shuruuuu tayi tana me zuba masa idanu tare da mamakin fitar kalamin daga bakinsa. Wai magauta,ji kuma na nawa?,ko yana tunanin cikin gidan yana da wani magauci a tsakaninsu da ya wuce shi karan kansa?.
"Tunda sauri kike bari nayi a gaggauce" Ya fada yana sude hannunsa daya nado romon naman kan,ya gyara zamansa sosai yana kallonta.
"Kinsan hausawa sunce ko kana gudu haifi ka yar.....kuma ita haihuwa rana gareta" Yayi maganar cikin sigar kwantar da murya da jan hankali. Bata ce masa ta tafasa ya sauke ba,tadai ci gaba da kallonsa yana bayanansa tare da son jin inda zantukansa zasu tuqe
"Wato wata gwaggwabar mu'amala ce ta taso mana,wadda cikin ikon Allah take buqatar adam zuba wasu kudade kuma a kwashe da riba me tarin yawa.......to kinsam harka ta samu dai ba'a wasa da ita a lokaci irin wannan,duba da yadda al'amuran qasa suka yamutse....to na duba na dubo......na laluba na lalubo kaf 'yan uwa na kusa dana nesa......ba wanda zai rufan sittira ya bani kudin nan aro ko bashi banda ke diyar albarka" Ya qarasa maganar yana addu'a qasan ransa. Ya santa sarai.....yasan aikinta,yasan kuma abinda zata aikata da wanda ba zata yi din ba. Ya jima baiga yarinya mai zubin matsorata ba,wadda kuma a zahiri zuciyarta a tsaye take carrr babu tsoro ba irin sabreen din.
Tsam ta miqe abinta bayan data fahimci cewa yakai aya a maganarsa
"Bani da wasu kudade kawu.....zan fita sai na dawo" Ta fada kanta tsaye tana gyara chain din hand bag dinta. Daga zaunen ya tada kai yana dubanta
"Wai baki fahimci abinda nake magana bane akai sabreen?" Qaramin murmushi ta saki. Ta sani,idan tayi rantsuwa ko kaffara ba zatayi ba,zaije yayi caca ne.....abar da ya jima yana tabawa da taimakon mahaifinta ta soma sakinsa,sai gashi a yanzu gushewar me masa saiti ta sanya ya dawo da dukka wasu tsaffin dabi'unsa da ake sanya ran yayi adabo dasu. Duk da hanyar da take samar da kudadenta.....amma tayi imanin ba zata iya diba ta bashi ya buga caca ba. Inda wajen wata lalurar dabanne,ita a karan kanta lokaci bayan lokaci tana miqa mass,shi kansa yasan tana sahun mutane na farko farko da hannunsa ke yawan amsa daga garesu koda bataso haka ba.
"Naji kawu...kayi haquri bani dasu" Ta sake fada hankalinta kwance,don sam case dinta bai daga mata hankali ba,don abu daya data sani shine,ko sama da qasa zasu hadu ba zata iya bada silai tata ya sanya a caca ba,bayan tarin buqatu da lalurori dake zayyane cikin littafin ayyukanta da takeson wanzarwa. Tana da babban mafarki akan mutanen da take rayuwa dasu,tana son kowanne ta daukeshi ta dora rayuwarsa bisa wani gurbi ko matakin da koda bayan ta gushe tasan tayi dashen daya baza rassa sassa da kuma jijiyoyi masu inganci da qarko.
"Bari dai na miqe don kiga iya adadin tsahona,sannan ki tabbatar da gaske dai nake" Ya fada rai a bace yana miqewar kamar yadda yace. Kallonsa ta sakeyi sosai,a nutse tsaf ta janye iidonta. Ranta yana baci mamaki yana sake mamayarta. Bai taba nuna damuwa ko yaya akan yadda suke rayuwarsu ba,sunci?,basuci ba?,lafiya suke ko akasin haka?,yaya karatunsu lafiyarsu da sauransu,amma a yanzu qarfi da yaji so yake ya dinga qaqaba mata lalurorinshi wanda koda ya sauke su baya gani baya kuna darajta hakan bare ya qimanta su.
Fara takawa tayi a nutse tana dosar qofar waje
"Idan ka gama zan rufe dakin kawu,dukkanmu zamu fita ne" Ta fada masa a ladabce tamkar ba ita ta hana masa abinda ranshi yakeso ba tana qarasa fita a falon,don ta tabbatar idan ba haka sukayi dashi ba zai yita zama yana jawo zantuka kala kala da daga qarshe zai barta da qunar zuciya da zubar hawaye mai zafi.
"Indai ni kika tozarta sabreen zaki gani......na tabbatar inda ubanki ne yazo da buqatarsa ba zaki taba tozartashi ba,ba komai,badai ni kika wulaqanta ba?,to in sha Allah......in sha Allah,sabgar dai da bakiso za'a yita,kuma sai ta kawo arziqin da baki tunani mara mutunci kawai" Ya fada daidai sanda yake sanya qafarsa a waje. Baya taja kawai batace masa komai ba,har ya zura takalmansa yayi gaba yana sababi kamar ya ari baki.
A hankali take takawa huda na gefanta,haneefa na daya gefan tana riqe da hannun haneefan cikin nata,sai nadra dake a gabansu da yake tana da sauri a tafiya ba laifi.
Dukka su ukun sanye suke da atamfa iri daya kamar yadda mayafansu suke iri daya. Duba daya zakayi musu kasan suna samun kulawar rayuwa daidai gwargwado. Ba yunwa wahala ko jigata a tattare dasu,wanda duka hakan ya samu garesu ne ta sanadiyyar YAYA ME KAMA DA MAHAIFIYA da suka samu.
Kaffa kaffa take dasu da rayuwarsu sosai tun daga lokacin da duniya ta gama bude mata dukka fuka fukai da lokunanta da saqonta.......tun daga sanda duniya ta soma yi mata wani karatu wanda a sannan ba'a taba yi mata karatun da yakai gefan wannan ba.....tun daga sanda ta fahimci DUNIYA cike take da ababen tsoro da mutane MAFARAUTA masu banbancin hali da dabi'a cikin abun farautarsu.
A haka suka kai qarshen layinsu suka kuma sada kansu da bakin titin unguwarsu. Tsaiwarsu da duka mintunan da basu haura uku ba motar ta karyo daga cikin layinsu da yunqurin hawa bisa babbar kwalta,idanunta suka sauka akan matuqin motar. Za'a iya cewa ido hudu sukayi,shi ya fara gaggawar janye nasa idanun yana gabansa yana faduwa,sai itama ta janye nata tana jan wani dogon siririn tsaki. Bata jin har abada......har numfashinta yabar gangar jikinta zata iya manta wannan fuskar tasa.....yana daya daga cikin mutanen da ba zata taba iya mancesy ba bare akai ga mance fuskarsa......mutumin da had kullum idan ta tunashi take gayawa kanta shekaru hamsin da takwas dinsa a duniya ya yita ne a banza da wofi ba tare data qara masa komai ba......hakanan arziqinsa bai qareshi da komai ba sai dulmiya cikin sabon Allah kaca kaca.
Da wannan tunanin ta sanya hannu ta tsaida musu empty keke napep me tahowa,don zai yi wahala ta fita ta hada abun hawa da wani ko wata,ta saba da daukan drop duk inda zata muddin ba busari zai dauketa ba. A mu'amalarta da 'yan uwanta kuwa bata lamunci susan kowa ba ko kuma kowa ya sansu ba,duk fita indai dasu ne abun hawa na haya take dauka duk da aminta da tayi da busari din dama JIB,amma ta sanya a ranta kowanne cikin su akwai iyakarss,aikin da yake mata kuma sam bai shafi 'yan uwanta ba,basu da alaqa sam dasu,ko fuskokinsu cikin su ukun babu ta guda daya da zasu iya shaidawa.
Cikin motar dake girke daga nesa kadan daga shagon. Motar da aqalla ta dauki tsahon kwanaki tana sintiri a titin,tana kuma daukan dukka sa'o'in a wanni a fake a wajen ba tare da kowa ya damu da su waye a ciki ba?,meye kuma yake kawosu ba?.
Dai dai sanda suke sauka daga napep din,ta biyashi ta kuma sanyasu a gaba suna nufar babban shagon wankin kan gyaran fuska da kuma yin kitso na noor's beauty parlor,daidai lokacin ya dauke idanunsa daga kan wayar hannunsa,idanun kuwa sukayi kyakkyawar sauka a kansu su dukka hudun.
Da wani irin hanzarin samun damar cimma abun FARAUTAR ya tabo dan uwansa dake kashingide yana lumshe idanu,da alamun gajiya ta fara sanyashi jin baccin dole.
"We found her......" Ya fada da wani irin karsashi da qwarin gwiwa,wanda bai bashi damar jiran abokin nasa ya kammala zama gaba daya ba yayi swapping da sauri zuwa kakkaifar camera dinsa ya soma daukan hotonsu bayan zooming camera din da yayi daga bakin window din,ya kuma bada hoto me kyau duk da 'yar tazarar dake a tsakaninsu. Kafin su shiga ya samu hotuna guda uku kyawawa da suka yalwata farincikinsa. Yayin da abokinsa dake zaune daga gefe bakinsa ya kasa hutawa daga furta
"Well done" Ba. Harara ya juya ya watsa masa bayan ya tabbatar ya adana hotunan
"Dole kace well done tunda ka kwanta kana shirin yin bacci" Ya fadi masa da gurbatacciyar hausarsa da zata gaya maka shi din ba ainihin bahaushe bane. Dariya ya saki yana cire hular kansa tare da karkadeta ya maida saman kansa
"Da gaske na cire tsammani duba da satittikan da muka shafe muna zuwa wajen nan babu wani alamun nasara ko alamun ganinta.....amma yau dai komai ya fara hawa saiti,meye target na gaba?" Ya tambayi abokin nasa yana kallonsa.
Haka kawai ta dinga jin wani yanayi yana mamayarta na rashin sukuni da kuma sakewa tun daga sanda suka sauka daga motar har zuwa sanda take zaune saman kujerun da aka qawata wajen ana kitse lallausar sumar nadra da haneefa me tsaho da santsi wadda dukka da tsahonta batakai tata yawa ba. Wayarta ce a hannunta tana duba wasu bayanai da JIB ya tura mata......amma sai takejin kamar akwai wata mantuwa ko kuskure da tayi.
A karo na kusan shida ta daga kanta tana duban nadra da fuskarta t fito tayi kyau sakamakon kitson da aka kusa gama mata. Cikin qasa da minti biyu gabanta ya yanke yayi wani mummunan faduwa
"Nayi kuskure.....nayi ganganci" Ta fadawa kanta da kanta can qasan zuciyarta tana jin wata qaramar fargaba tana mamayeta.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 44
________________________
GROUP 1
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
*_assalamu alaikum warahmatullah_*
*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_*
*_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_*
*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_*
Shadda
Laces
Atamfa
Kayan yara English wears dana jarirai
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Huluna na maza da mata yara da manya socks
Takalma na maza da mata yara da manya
Lafayas
Sarqoqi agoguna banguls da rings
_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_
_bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*
*_masu manyan qarfi da matsakaita?_*
*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_*
*_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_*
*MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA*
*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
*_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_*
*_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
GROUP 2LINK
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
__________________________
Duk wani da zatayi mu'amala dashi......yadda bata yarda yasan daga inda take ko inda zata......hakanan take nesanta tare da barin duk wani muhalli da suka taba haduwa ko ya taba ganinta a can din. Cikin tsarinta bata sake mu'amala ko huld da gurin......tana kuma nisantar wajen da duk abinda zai sanya ta ratsa wajen ko tayi hulda da gurin.
Wannan gurin shine guri na qarshe da suka hadu da alhaj naseer.......shine kuma gurin data sauya saboda wankin kai wankin qafa da gyaran fuska da takanyi time to time.
Batasan me ya dauke hankalinta ba ta sake dawowa gurin ba,ta karya dokarta da kuma tsarinta da kanta,ya akayi tayi mantuwa irin wannan?,haka kawai saita kasa samun nutsuwa,ta maida wayarta jaka ta ajeta gefe,ta hada hannayenta guri daya sannan ta harde qafarta daya saman daya tana sauraren gilmawar kowanne motsi dake kewayen wajen,tana kuma karantar kai kawo da aikin kowa dake wajen cikin nutsuwarnan tata da kaifin sansano abu.
Yawan rashin nutsuwarta ya qara yawa,tilas ta miqe a hankali sanda aka kama kan huda wadda ita daya ta rage sai ita din karan kanta da zaa wankewa kai
"Madam saura ke" Daya daga cikin ma'aikatan ta fada tana kallonta sanda take takawa a hankali tana nufar bakin qofar wajen
"No......inajin sai zuwa wani lokaci ni na dawo,a kammala dasu dai"
"Okay to" Ta amsa mata tana tattare kayan gyaran gashin data baza.
Cikin tsanaki ta riqe curtain din wajen. Ta sanya idanunta a nutse tana qarewa titin kallon cikin nazartar kowanne abun hawa dake kai kawo a wajen. A qalla ta kusa kashe mintuna goma a tsaye ta cikin shagon wanda babu lallai kai da kake waje ka iya ganinta.
Idanunta basu iya gani ko hangen komai da zata iya sanyashi cikin zargi ba,zargin da zai iya alaqantuwa da wala'alla yanayin da takejin jikinta da zuciyarta a ciki ba.
Ajiyar zuciya ta sauke tana matsawa da baya a hankali cikin ainihin shagon. Ranta yana raya mata wala'alla don ta fito ne da dukkansu shi yasa ta kasa sakewa,sai taji gaba daya ta qagauta a gamawa hudan su wuce ba tare data damu da cewar ita din ba'a yi mata komai ba.
"Ta koma?" Ya tambaya daga daya sashen cikin tsananin farinciki,hankalinsa kwance a yau din saboda samun damar kama bakin zarensa da kyau
"Eh,ta koma" Suka bashi tabbaci daga inda suka janye motartasu suka ajeta. Wani shu'umin murmushi ya saki,yayi taku biyu yana jan wata dunqulalliyar kujera ya zauna akai
"Na gaya muku....tana da matuqar wayo fiye da zaton me zato.....amma ku sani....muddin aikinku ya tafi da kyau.....ya kasance kamar yadda na tsara.....ina me muku albishir din qari akan abinda mukayi yarjejeniya daku"
"Aikinka kamar anyi an gama shi ne" Ya maida masa amsa cikin zallar nishadi
"Take care.....ina sake maimaita muku.....ku kula" Daga haka ya yanke sadarwar dake tsakaninsu,don baya yarda suyi wayar data wuce minti daya dasu.
*******Sanye take cikin daya daga cikin suturu na alfarmar da suma zame mata abun sawarta. Walau fita zatayi?,ko kuma tana zaune ne kawai a gida saboda gwada qarfin izzarta tare da son nunawa duniya matsayinta da kuma kashe qarfin kwadayin izza da kwadayin sauran kayan qyale qyale na rayuwa.
Ni'imtaccen falon nata da takejin qarfin iko da isarta sun zartasa a killace yake tsaf kamar yadda dabi'arta take na mace da batason qazanta sam sam,yana gyare ne tsaf bisa jagorancin masu aikin da suke duk wata hidima ta gidan ba tare da tayi cas ba bare as idan ka dauke bada umarni.
Ta kasa hankalinta ne gida uku,daya yana ga bada umarnin yadda takeso a tsara table din don zuwan musaddiq cin abincin dare gidan,daya yana ga duban cikar lokacin da zai iso din,yayin da dayan yake kan zuwaira tana sauraren zantukanta da a mafi yawan lokuta sukafi gama da banbadanci.
Sake gyara zamanta tayi tana daidaita zanin embroidery vlisco atamfa din dake jikinta wadda kudinta ya tasamma dubu sittin. Ta zube idanunta akan zuwairan karo na uku
"Duk yadda zanyi zuwaira.....kome meye ne zai faru dole zan dauki mataki fa.....ba irinmu ake zuwama da irin wadannan abubuwan su bari ba.....komai tsiya musaddiq da fu'ad 'ya'yana ne halak malak,babu wanda ya isa duk duniya ya kankare wannan matsayin" Ta fada har cikin zuciyarta tana jin zafi tsana da qyamar anni......tana jin a duniya ita da alhaji hamza sune manya manyan maqiya kuma abokan gabar da bata da sama dasu. Sake duba agogo tayi,yadda taga lokaci yana ta ja ya sake sanyawa ranta ya baci
"Zuwaira yanzu haka yana can ta riqeshi har sai sanda tayi masa izini zai taho gurina?" Kyabe baki zuwairan tayi tana tallafe kanta da hannunta tare da dogarashi jikin kujera,sannan ta karkatar da kanta tana kallon wani sashen,tabbacin abun yana mata matuqar ciwo kenan
"Kema ai kinsan kwanan zancen.....ai kinyi sake maryam ba dan qarami ba kuwa". Maganganun zuwaira suka sake zame mata tamkar allura,taja wata doguwar qwafa bacin ranta yana ninkuwa,a take taji duk wani danshi na maqogaronta ya bushe ruwa take da buqatar sha. Kamar ko yaushe a tsawace tayi kiran sunan me aikinta,ta nufota a gaggauce,ba tare data bari ta qaraso ba tace da ita
"Koma ki bani ruwa......banason kowanne sai swan.....karki maimaita kuskuren jiya". Jikinta yana ruwa ta amsa mata
" In sha Allah ba za'a samu matsala ba" Ta juya da hanzari hanyar kitchen.
Su biyu ne kadai zaune saman lafiyayyen dining din na wata iriyar mulmulalliyar kwalba me garai garai. Komai na gidan an zubashi ne bisa nunawa kudi iyakarsa,komai me kyau ne me kuma asalin tsada,kamar yadda komai aka zubashi bisa tsari.
Anni ce saman daya daga cikin kujerun,jikinta sanye da wata sassauqar cotton abaya 'yar asalin moroco wadda ta dace da jikinta da kuma shekarunta. Kanta sassalkan dan kwali ne da yazo da rigar,tana riqe da waya da alama wani kira take amsawa da ya janye hankalinsu su duka ita da musaddiq dake zaune saman kujerar dake fuskantar tata. Idanunshi akan annin yana dariya saboda yana iya sauraren abinda siririyar muryar ke fadi ta wayar. Jikinsa na sanye da yadin senate me asalin tsadar. Sosai yadin ya kwanta masa a jiki ya kuma dace da kyakyawar hularsa dake aje saman table din daura da plate din abincin da yaci rabi yana riqe da cokalin yana sauraren wayar anni.
"Don Allah anni kice mata ta zauna kin yafewa nanna ita" Ya fada qasa qasa yana boye dariya da muryarsa don bayaso ta jiyoshi. Annin ta jishi sarai,murmushi me sauti ya kubuce mata,saita cira wayar daga kunnenta tana cewa
"Ga qaramin yaaya zai baki saqo" Ta aje masa wayar a gabansa taja nata plate din a hankali taci gaba da diban abincinta tana ci tana kuma saurarensu.
Idan daru ne tsakanin amna da musaddiq a gidan ba wanda baisan da zamanshi ba. Saidai kuma akwai shaquwa me tsananin qarfi tsakaninsu da ba wanda ya isa ya taba daya a gaban dayan. Wani sabo da 'yan uwantaka ce me zurfi a tsakaninsu wadda tadan sha banban da wadda ke tsakaninsu da FU'AD da kallon UBA kusan sukeyi masa.
Tana jin yadda suke fafatawa da yace mata an barwa nanna ita,ya dinga kwasarta yana dariya anni na zaune kawai tana murmushi har sai daya tabata sosai sai ya yanke kiran,daidai sanda farouq ke shigowa falon.
Sassanyan matashi,cikamakin barin zuciya ruhi da rayuwar mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources muhammad fuad jadda. Kaman twin brother dinsa fu'ad yadda ake kallonsu kenan,illa banbancin career da kowanne yake dashi.....yana da wani ajiyayyen kyau nutsuwa da haiba. Su biyun kam sun zamewa duniyar 'yammata da yawa jarabawa,ba'a maganar 'yammatan da karansu baikai tsaiko ba.....yammatan da basu da damar nuna yatsa ko tsaiwa a dandamalin da kowacce diya da take ji da gata da kudi zata tsaya......yammatan da saidai su gansu jikik TV mujallu da jaridu da kuma sauran kafafen sadarwa......aah.....wannan fagen na 'YA'YAN GATA ne,yaran da iyayensu da kuma su kansu suka ci suka kuma tayar da kai,yaran da suke da chance 50 to 60 percent na ganinsu,walau a gidajensu ko a guraren ayyukansu,ko tafiya ta hadasu a filin tashi da sauka na jirgin sama a kowacce jaha dake Nigerian,ko kuma su hadun cikin qasashen da aiki ko kuma hutun da sukan tafi dukka family din alhaji HAMZA KIBIYA zuwa wasu daga cikin kebantattun qasashen da sukanyi quri'ar zuwa.
Wata irin nutsuwa suke da ita,wanda kwata kwata harkar mata bata gabansu. Har gwara gwara farouq din,akwai wasu banbance banbancen dabi'u da kuma halaye tsakaninsu da fu'ad. Tun asali farouq mutum ne meson comedy ko yaya ne,abinda zai sakashi dariya da nishadi,yanason yaga ya tsokani mutum abinda ya sanyashi yasha wahala qwarai a hannun mariya......sabanin sadiq da yake da tsoro da kuma tsantseni. Saidai dukkansu a yanzun girma ya sauya wasu daga cikin halayensu. Raino na uwa da Allah yayi musu alfarma suka sake samu,sai dukka wannan tsoron na sadiq ya gushe,ya koma tsaiwa da jajircewa akan komai,saidai kuma ua biyo halin fu'ad na matsanancin miskilanci shariya da kuma maida kansa kamar baya fahimtar abinda kake aiwatarwa. Dauke kai da banzatarwa akan abu idan baiso ba,zaman kadaici da rashin son hayaniya ko doguwar magana. Farouq yana nan da halinsa,saidai ya ragu sosai,kusan dukka sakewarsa cikin gidan ne,idan ya fits waje ya koma boss saidai cikin abokai kuma. Shi dinma ya samu abokin tayi wato musaddiq,wanda shine copy dinsa,idan suna a gidan maida anna suke kamar kakarsu,abu daya ne yake bata salama idan fu'ad yana nan,tofa nan daya,sunsan qaryarsu tasha qarya,dole su shafa mata lafiya subar bakinta ya samu salama.
A boye musaddiq da sadiq suka fara zuwa zance abinsu. Ba wanda ya sani sai ranar da fu'ad ya fahimta. Da wannan salon hukuncin nasa ya ritsasu a falo,kowanne ya rasa da bakin da zai masa bayani,amma koda anni ta iskesu ana shari'ar goya musu baya tayi
"Ba wanda bazai iya riqe mace ba a cikinsu,tunda sama ta kasa,ai bai kamata qasa ta gaza ba" Ta bawa fu'ad amsa. Ya fahimceta sarai,ya kuma fahimci anni dasu take shida farouq......kai tsaye ma idan an tashi shi din za'a ce,don dama farouq din dab yake da bayyana nemansa gasu annin,shi dinne bashi ga tsuntsu bashi ga tarko,bai kuma san ranar da zaiyi tsuntsu ko tarkon ba,don a yanzun baya jin duk yarinyar da yace zaya aura din zai iyayi mata adalci,don a qasan ransa ko digo baya jin marmarin aure,baya ma taba hange ko hasashen gashi da macen auren ko gashi a sunan magidanci......duk da cewa shi kansa shaida ne akan jikinsa yakai geji yakai iyaka ya kuma kai maqurar buqatuwa zuwa ga diya mace......duk da tarin yanayin da yakan tsinci kansa a ciki.....shi kansa yasan kowacce irin lafiya ake da buqata yana da ita,don ba'a maganar cikakkiyar lafiya ma ga mutum ma'abocin motsa jiki. To amma baisan dalili ba.....ko kadan sabgar bata gabanshi,hasalima!,zai.iya cewa bai taba jin soyayyar wata 'ya mace a zuciyarsa ba......bai taba daga idanu ya kalli wata mace yaji ta burgeshi ba......bai taba zama koda da minti daya ba....kaf rayuwarsa tunda ya mallaki hankalinsa wai yayi imagining aure cikin rayuwarsa ba. A yanzu ya sake gina rayuwarsa bayan ginin da yayi mata shi yafi sawa a gaba,aikinsa kasuwancinsa da sana'arsa sune budurwarsa kuma matarsa,baya da wani buri a yanzun illa ya sake zama gwani ta fannin ayyukansa gaba daya.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 45
________________________
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
*_assalamu alaikum warahmatullah_*
*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_*
*_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_*
*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_*
Shadda
Laces
Atamfa
Kayan yara English wears dana jarirai
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Huluna na maza da mata yara da manya socks
Takalma na maza da mata yara da manya
Lafayas
Sarqoqi agoguna banguls da rings
_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_
_bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*
*_masu manyan qarfi da matsakaita?_*
*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_*
*_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_*
*MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA*
*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
*_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_*
*_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
__________________________
Yana da matuqar karsashi da qarfin zuciya......da kuma fuskantar dukkan wani goal nashi har sai ya cimmasa ya kaishi qasa. Baya taba bari buri tsoro ko fargaba suyi masa iyaka ko shamaki......faduwa kuma bata sanyashi yayi giving up,wannan shine sirrin nasarar da kullum yake dada samu.
Za'a iya cewa kai tsaye farouq hannun damanshi ne,don haka ba wani motsi ko mission nasu da dayan bai ganewa koda bai gayawa daya ba,duk da cewa ma babu boye boye gaba daya a tsakaninsu. Wannan ta sanya farouq ya jima da fuskantar fu'ad,idan magana kake ta aure ko soyayya to kada ma ka fara kiran sunanshi a ciki,domin baya gane komai ta wannan bangaren. Yakan jima yana dubansa cikin mamaki,ya bawa kasuwancinsa lokacinsa da rayuwarsa fiye da komai baya ga familynsa,wato shi sadiq musaddiq anni da abba,kullum lissafinsa da target dinsa moving forward.....moving to the next step. A hankali ya fara zolayarsa don gane gejin yadda idanunsa basa gane kowacce halitta da ake kira da DIYA MACE,sai ya sake karatun nasa da kyau yadda ya kamata,har daga qarshe ranar yakai kusan biyu na dare saman system yana duba wasu sabbin diamond da aka samu nasarar cirowa,yadda zasu sarrafashi da kuma kamfani mafi dacewa da zasu kai.
Shi kam har yayi bacci ma kai na biyu ne,ya fito main parlor na sassansu ya sameshi zaune dungurgur saman sofa yana fama da zazzafan coffee don hana idanunsa kamuwa da bacci. Farouq din da mamaki yake kallonsa,saidai baice masa komai ba har sai da yaje fridge ya ciro ruwa me sanyi ya dawo gefansa ya zauna
"Sannu bawan kasuwanci" Ya fada cikin gatse,gatsen da bai damu fu'ad ba saima maida idanunsa kan ruwan hannun farouq din da yayi. Har ya dauke idanunsa kamar bazai magana ba cikin dabi'ar nan tasa ta shariya da banzatar da abu,sai kuma ya dawo da dubansa kanshi.
"Kana da jarabar son aure.....amma kana kashe kanka da abubuwan banza da wofi.....kana namiji me yake hadaka da kayan zaqi da sanyi?" Yayi masa tambayar fuskarsa a hade yana duban idanunshi.
Qaramar dariya farouq din ya saki yana qoqarin bude gorar hannunsa
"Kasan me?,nifa bazan iya rayuwar da kakeyi ba,duk wani abu me dadi ka haramtawa kanka ci sai d'ai d'aiku,ka tattaro abubuwan da sam basu da dadi ko dandano a harshe kullum dasu kake mu'amala......yanzu kalla don Allah" Ya fada yana nuna tray din gaban fu'ad da awannin baya kadan ya gama amfani dashi.
"Gasashen zaitun.....hadin salad me man zaitoon,shayin ginseng,wolf Berry smoothie.....meye mai dadi a ciki?" Ya fada yana yamutsa fuska.
Idanu kawai fu'ad ya zuba masa har yakai qarshen zancan. A nutse ya saki wani qaramin murmushi da bai bayyana ba yana dauke idonsa daga kan farouq
"Dukka abinda ka lissafa yanxun kaje kayi binciken amfaninsa ga jiki da lafiya" Ya amsa masa yana jawo wata takarda dake aje a gefansa yana son hadesu waje daya da stapler.
Kai ya girgiza yana tabe baki
"Wanne amfani zan tsaya dubawa abinda basu da dandano ko kada......kaifa a taqaice ko?,bakasan meye dadi ba kwata kwata wallahi"
"Tashi don Allah ka tafi mr ciye ciye karka cikamin kai da bayanai.....kaci gaba da ciye ciyenka yadda kake da hazaqar son kayi aure,auren zai baka amsarka". Dariya ta kubcewa farouq din harda buga qafa tamkar ba dare ba
" To mijin aljana.....don dai na tabbatar zaiyi wahala kaidai idan aka kira me ruqiyya yayi maka ruqiyya inajin mata hudu gareka cikin jinsin aljanu".
Duk yadda yakai ga pressure dinsa hade rai ko salon miskilancinsa farouq kadai ke saukeshi. Ya addabeshi wasu lokutan har yaji kamar ya makeshi amma ba yadda ya iya dashi,don kaf duniya baya gashi ba wanda yake masa karan tsayen da yake masa irin haka. Ko a yanzun ma sai da yayi silar fitar murmushi daga kyakyawar fuskarsan nan ma'abociyar tsukewa da ba kasafai ta fiya fidda fara'a
"Kaga bakina alaikum na huta ai.....don wadannan matan na bil'adama......." Sai kuma yayi shuru ba tare da ya qarasa fade ba. Ba kasafai ya fiya son tona abinda ke danqare a zuciyarsa ba,baisani ba ko Allah ya nufeshi da rahama daya zare son aure ko son mallakar mace kwata kwata daga zuciyarsa ba?.
Dan kadan farouq ya kalleshi ta gefan idanu ganin ya dauko magana ya kuma katseta,sai shima yayi shuru kawai bai sake cewa dashi komai ba.
Tun daga wannan lokaci idan yaso masa tsiya da shaqiyanci yakan kirashi da mijin aljana. Anni tayi tayi ya daina amma ina,lamarin farouq sai a hankali,mugun shakiyyi ne idan yaso,idan kuma ya sakaka a gaba ka saku kenan......amma kuma tamkar hawainiya yake,idan yaso canzawa zaka rantse da Allah bashi bane matsokanin nan ba.
Kusan a tare suka amsa sallamar farouq din
"Kana nan dama?" Farouq din ya fada sanda ya qaraso dining din yaja kujera dake tsakiyarsu ya zauna yana tattare long sleeve din shirt din jikinsa sama.
"Yana nan sunatayi shi da mutuniyar" Anni ta bashi amsa tana dariya qasa qasa.
Baki ya tabe yana bubbude warmer din dake jere kan dining din
"Wannan autar taki anni taci kai wallahi.....wai ita an gaya mata zama zamuyita yi da ita a gidan nan?,baka gaya mata gaskiya wallahi" Ya qarasa maganar yana duban fuskar musaddiq cikin salo na harara.
Dariyar ta kubcewa musaddiq ya kalleshi da kyau yana daidaita zamansa idonsa akan farouq
"Yanzu don Allah BB(big brother suke masa abbreviation),so kake ayita kada mata hanjin ciki?,duka duka amna nawa take?"
"Allaaaaahu akhbar.....kaga masuyi don Allah,dama kana cikin masu lalatata a gidan nan......don Allah kayita gaya mata damu zata rayu.....Allah ka sakata ne kawai a keken bera......itafa har yanxu bata da hankali na lura......na godewa abba ma da yace sai taje ta raka nanna......tafiya duka duka sati biyu kawai amma ta cika mutane da qorafin yhan yhan yhan......itafa gida zata dawo waye ya mutu waye ya tashi.....shi kuma wancan mijin aljanar yana can yana sake daure mata qarqashi...."
"Farouq?" Anni ta tsaidashi tana dubansa
"Sunan nan bazai fita a bakinka ba ko?" Ta sake jefa masa tambayar tana dubansa.
Gyara zamansa yayi yana wani tsuke gira,shi ala dole yana son zama serous.
"Allah dai ya bada haquri anni......amma shima ai anni ba sunan da yafi dacewa dashi sai wannan.....banga alamar lafiyarsa qalau ba" Ya qarasa fada qasa yana fara serving kanshi da abincin da yafi so. Idanu anni kawai ta tsura masa tana kallonsa ba tare da tace komai ba,ita kanta yadda fu'ad keyi da lamarin yana tabata,ko a fuska ko kuma a aikace bai taba damuwa da ganin dukansu su ukun suna shirin yin aure ne su barshi ba,yana shiga dashi akayi dukka maganganun da zaayi da iyayen yara,amma shi yana zaune ba wani damuwa a gabanshi,saima lissafin yadda zaici gaba da juya kwabo ta koma dari.
"Kaga MAN.....ka koma gaya mata gaskiya,aurar da ita zamuyi da wurwuri.....ba zancan yin PHD a gidan nan.....munason ganin jikokin 'yar uwarmu mace". Daga anni har musaddiq ba wanda farouq din bai bawa dariya ba ganin yadda yayi maganar da gasken gaske har yana tabo hannun musaddiq din don ya jishi da kyau,ya kuma basar ya soma cin abincinsa.
Na anni kawai idanu,tana tsarkake girman ubangiji da yadda yake halittar bayinsa da mabanbantan dabi'u da kuma halaye. Yara hudu,mace cikon ta biyar amma kowanne da nasa halin da dabi'ar. Ta sauke boyayyar ajiyar zuciya kunnuwanta suna sauraren hirarrakinsu. Bahaushe yayi gaskiya da yake cewa DA D'A DA DUKIYA BA'A YI MUSU MUGUNTA,DON BA'ASAN ME MORARSU BA SAI ALLAH. tana tuna wani lokaci can baya.....shekaru da suka shude,sanda ta tsoma qafafunta da sunan kome gidan tsohon mijinta alhaji hamza. Yadda tasha baqar wuya kafin ta daidaita lamuran gidan ta kuma maida kowa cikin hayyacinsa. Me babban suna tafi shan wuya akansa akan kowa,tasha gwagwarmaya kafin ta samu nasarar cire wannan fushin baqin rai da kuma mummunan fenti da ya yiwa kusan kowa da yake kewaye dashi idan ka dauke 'yan gidan nasu. Rashin yarda da rashin sakewa da jama'a wanda har yanzu tana fuskantar ragowa da kuma tasirin wannan dabi'ar tattare dashi da bata gama barin jikinss ba. Wani irin yanayi me ban tausayi da har yaso taba karatunshi.....boyayyen kuka duk dare da rashin bacci. Ta dauki dogon zango cikin musu addu'a da neman daidaitar rayuwarsu. Tofi rubutu da addu'a dukka kafin lamuransa su fara daidaita. Sai ta fuskanci kyara tsangwama ga duk macen da zata dososhi koda qanqanuwar yarinya ce. Bata fuskanci yadda abun yayi musu!mugun tasiri ba sai bayan wasu shakaru data haifa musu Aminatu amna me sunanta kenan.....haihuwar data tabbatar matsanancin rabo ne,don ko a wasa bata taba tunanin wai zata sake wata aba wai ita haihuwa ba.
Da fari tsakaninsa da amna idanu ne kawai,baya ma zama.inda take bare daukarta,ta fahimci kaman wata kakkaifar gaba ce tsakaninsa da jinsin mata,ita kadaice mace cikin miliyoyin mata da take samun kulawa da qauna daga gareshi wanda ita dinma sai da suka debi shekaru yana dari dari da ita. Bata tsananta tuhuma ba,tasan incident din daya faru dashi a baya akan mariya da mariya sune suke hunting dinsa.
Wannan abun bai karye ba tsakaninsa da amna din har sai sanda ta fara laulayin haqori. Kashin haqori matsananci daya sanya mata amai da zawo da yaso wucewa da rayuwarta. A ranar a kuma daren har sun fidda rai da ita,tayi wani suma a hannunsa. A ranar taga gigicewa mai tsanani a tattare dashi,shi daya ne yake da qwarin gwiwar daya dinga mata wasu abubuwa don dawo da mumfashinta,sai gashi cikin ikon Allah ta dawo.
Tun daga wannan ranar kulawarsa a kanta ya zama na dabanne,sabo ya shiga tsakaninsu,ta tashi ta ganshi a matsayin yaya kuma uban da bata da kamarshi.
"Kamar akwai inda zakaje ko?" Anni ta tambayi musaddiq da suke hira da farouq
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 46
____________________________
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
*_assalamu alaikum warahmatullah_*
*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_*
*_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_*
*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_*
Shadda
Laces
Atamfa
Kayan yara English wears dana jarirai
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Huluna na maza da mata yara da manya socks
Takalma na maza da mata yara da manya
Lafayas
Sarqoqi agoguna banguls da rings
_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_
_bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*
*_masu manyan qarfi da matsakaita?_*
*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_*
*_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_*
*MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA*
*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
*_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_*
*_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
_____________________________
Tana tsareshi da ido. Duba daya ya yiwa annin ya fahimci tambayar ta yita ne kawai bawai don tana son sanin amsa daga bakinsa bane....aah,ta yita ne don tanason tunasar dashi wani abu
"Kamar zan fita din......amma kuma banason fitar" Ya fada yana kallon qatoton agogon dake manne a bango.
"Amma dai ina fata kana sane da girman umarnin uwa ko?,sannan kana sane da girman alqawari......haka kuma uwa uba baka manta dashi ba?" Dukka jikinsa ne yayi sanyi,sai yadan sadda kansa qasa kadan. Lallai ba shakka inda ace dukka iyaye haka suke tamkar anni da zaiyi wuya.....za'a tirza,hakanan za'a sha fama kafin a samu baragurbin yara cikin al'umma.
Kai ya jinjina,sai ya soma ture plate din gabansa,ya dauki wayarsa ya sanya gaban aljihunsa ya miqe yana fadin
"Sai na dawo"
"Allah ya kiyaye......" Anni ta bashi amsa tana satar kallonsa. Tako ta ina ba alamun jin dadin zuwan da zaiyin,ba wani sukuni walawala ko farinciki irin na da a sanda zai hadu da iyayensa.
Da kallon tausayi ta bishi dashi har ya bacewa ganinta. Ta janye idanunta tana sauke zazzafar ajiyar zuciya,sai suka hada idanu da farouq dake zaune yana cin abinci a hankali.
"Daga musaddiq har muhammad tausayi suke bani har yanzu,har yanzu wannan tabon da aka barwa rayuwarsu yana tare dasu bai goge ba". Kai farouq ke gyadawa yana duban anni
"Gaskiya kika fada anni......musaddiq nashi me sauqi ne,ba wanda abun ya yiwa illa matuqa yake kuma taba halayensa da dabi'unshi har yanzu irin fu'ad......akwai fushi saurin daukan zafi da yawa cikin halayensa......shariya rashin son yin magana ko hira da kowa,wanda yawancin lokuta idan irin hakan ta faru nasan abinne ya motsa masa,shi yasa sau da dama nake maida kaina wani iri a wajensa saboda na sama masa farinciki duk qanqantarsa". Kai kawai anni ke jinjinawa,har cikin zuciyarta tana jin ba dadi,abun kuma yana tabata.
Wani gauron numfashi ta sauke tana ajiye wayarta data dauko wadda ta kasa juriya tana shirin kiranshi kenan. Kacokam ta aza idanunta ga bakin qofa tana tsumayin qarasa shigowarsa tana jin yadda yake gaisawa da ma'aikatan gidan faran faran. Irin sakewa da ta tabbata idan ya shigo ciki baya iya irinta da ita.
Da sallama ta yaye kakkauran curtain din dake bakin qofar ya shigo. Ganinsa kawai da tayi,zuciyarta kuma na ayyana mata cewa wannan din d'anta ne halak malak sai taji wata izza ta sake daduwa cikin kanta
"Kina da wannan kadarar.....kina da wannan damar don me yasa zaki bari a qwace miki su cikin sauqi haka?" Ta yiwa kanta da kanta wannan tambayar.
Gyara zamanta tayi sosai sanda ya iso ciki,ya zauna saman daya daga cikin kujerun yana dan tsagaita dubansa daga inda take
"Barka da dare" Ya furta a nutse,har yanzun baya jin wani sabo shaquwa ko soyayya nata a tattare dashi,yana jinta kamar kowacce baquwa......yana kuma jinta kamar kowanne baqon abu na rayuwarsu.
Qoqarin wadata fuskarta da fara'a tayi kaman yadda zuwaira ta shawarceta don samun isa ga burika da muradanta cikin sauqi
"Ai na cire tsammani da zuwanka musaddiq......wai dama haka duniya take?,......na zaci komai girman laifin uwa d'a yana iya yafeshi ko?" Ta fada murya a sanyaye. Idanunsa kadan ya daga yana kallonta,ya kasa gamsuwa da ita har yanzu,yana jin inama ace yadda ta furta wadannan kalaman a bakinta haka suke har cikin zuciyarta?.
"Kibar wannan maganar maamah,abune daya riga ya shude,kin wuni lafiya?" Ya maida maganar da tambayar lafiyarta
"Alhamdulillah.....saidai yayanka ya watsar dani musaddiq,ya barni cikin buqatar rayuwa da abubuwan da a zahiri ya cancanci ace nafi qarfinsu amma suna neman fin qarfina" Ta fada a karye.
Mamaki sosai ya sake lullubeshi har ya gaza jurewa sai daya daga idanunsa ya qarewa suturar jikinta da kuma falon da take ciki kallo. Tana cikin ni'ima da wadatar da babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa amma tana kiran abubuwa da dama sunfi qarfinta?. Anya kuwa da kyakkyawa da kuma tsakakkiyar zuciya ta dawo cikin rayuwarsu?,anya wannan tsohon maqalallen halin baya tare da ita?. Shine mutum na farkon da yafi kowa sanin cewa hammansa baya wasa da ci sutura sha muhallinta da lafiyarta,bayan ya dauke duka wannan kuma da wani ajiyayyen salary na dubu dari duk wata,duk da aqa'ida ba wata qwaqwarar buqata guda daya da ashekarunta ta yima rayuwarta saura. Hatta da man fetur da ake zubawa motocinta guda biyu bai daukewa kansa ba,to me take nema sama da wannan cikin dukiyar da aka sameta a sanda ta nisancesu?,cikin dukiyar da aka sameta a sanda ta gujesu?,cikin dukiyar da aka sameta a sanda take can cikin duniya tana kalar rayuwar data zaba?,kalar rayuwar data fifita sama da ta rayu dasu?.
"Bana jin akwai sauran abinda hamma ya rageki dashi maamah" Ya gaza jurewa sai daya fadi mata idanunshi tsar a kanta zuciyarsa kuma cike da mamakin furucinta. Idonta itama takai kansa tana kallonsa
"Yanzu a naka tunanin a matsayina na mahaifiyar mutumin da ya mallaki kamfanin sarrafa diamond......mutumin da yake da harqalla da manyan kamfanoni da suke a qasashen waje.....qasashen wajenma manyan qasashen da suka tumbatsa ta fannin tattalin arziqi da qarfin mulki da iko.....mutumin da yake noma kaso mafi tsoka na dukka abincin da Nigerian dama Africa gaba daya suke ciyar da al'ummarsu amma ace abinda zai iya cira ya bani na zallar kudi shine dubu dari?" Ta aje masa tambayar ranta yana fara mata zafi amma tana danneshi.
Ci gaba yayi da kallonta yana fahimtar abubuwa da dama tattare da ita,a yau kuma a yanzun sai yaji shima ya shirya tambayarta
"Idan har ya miki kadan kuma hamma bai kyauta ba......wacce buqata kike da ita da zakiyi da kudi?" Tambayar sak irin ta dan uwansa kenan......amsar kuma da ba zasu taba samunta a bakinta har abada
"Musaddiq......yanzu bayan ci sha sutura da biyan duka sauran buqatu da zasu taso Shikenan iya abinda nake da buqata a matsayina na 'yar adam?,bayan ina da d'an da a kullum idan zai bani kyautar million daya bazaiji komai ba a jikinsa daga abinda ya mallaka?"
"Maamah......kin taba zuwa da wata buqata kinaso ayi miki kaza?,ko a yiwa wane kaza wanda ba zallar kudi zaki amsa ba da hamma ya taba qinyi miki?" Ya jefa matar tambayar yanason gane ainihin gaskiyar da takeson lullubewa
"Kai musaddiq.....kalleni nan......dukkanku ke da fu'ad nina haifa abuna......banyi lalacewar da don zaku yimin wani abu sai na zama tamkar almajira a wajenku ba....."
"Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki" Ya fada kawai don kawo qarshen zancan. Can qasan zuciyarsa babu gasgatawa ko yarda da ita ko kadan. Idan yayi rantsuwa ko kaffara bazaiyi ba,ba haka siddan hammansa yaqi yarda ya sakewa maamah tsurar kudi ba,ya yadda dashi dari bisa dari,yana komai bisa bayyananniyar hujja da kuma dalilai. Kawai dai mutum ne shi me tsananin zurfin ciki da miskilanci,wannan ya sanya idan ya aiwatar da abu babu lallai ka fahimci don me yayin?,kuma bazai taba zama yayi maka wani bayani ba game da hakan.
Shuru ne ya biyo baya na wasu mintuna,tanata qoqarin controlling kanta don har yanzu bata kai ga cimma burinta na abinda takeson taji ba. Ta furzar da iska kadan sannan ta fara kiran daya daga cikin masu aikinta.
Kamar ko yaushe da sassarfa ta iso saboda tsoro da gudun sabawa umarninta.
"Ki sauke kayan abincin nan a nan....ko dining din zaka hau kaci?" Ta tambayeshi tana dubansa.
A zahirance so yake ya gaya mata ya qoshi,baya buqatar cin komai,amma ya tabbata fadin ba abinda zai haifar sai wani rigima da tashin hankalin,don haka yadan gyara zamansa
"Ta kawo nan din" Sai ta juya ta watsa mata kallo
"Kinji ai abinda yace". Suna zaune ta dinga sauke kwanukan abincin. Warms na alfarma masu tsananin tsadar da ko a gidajen masu sukuni sai wane da wane.
Da kanta maamah din tayi serving nasa don buqatarta shine ya saki jiki yaci sosai ta yadda zata samu daman yin magana dashi ta kuma samu duka information din da takeso.
"Bismillah sauko" Ta fada da salon bada umarni nakai tsaye. Bai musa mata ba ya zamo ya sauko din,sai ya fara kai hannunsa ya dauki glass cup na lemo yana juyashi a hannunsa.
Spoon ta dauko ta qara a plate din,ta kalleshi da murmushi
"Muci tare ko?" Kai ya gyada kawai yana duban kwanon. Komai yayi masa banbarakwai. Ko a shekarun baya da suke da qananun shekaru ya iya abinda qwaqwalwarsa zata iya riqewa baya jin sun taba zama kwano daya,sai yanzun da ya zama cikakken mutum?. Ko a baya sanda bai kammala iya cin abinci ba idan ta zuba musu ta tura musu ta shiga sabgar gabanta hamma ne ke zama ya bashi komai zafinsa har sai ya qoshi.
Hira take sako masa a hankali a hankali,tana cin abincin yana juya cokalin kawai a ciki bayan ya dire cup din lemon.
Sai bayan data soma karantar kamar sakin jiki tattare dashi sannan ta aje nata spoon din tana dubansa cikin murmushi
"Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma ka nesanta
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 47
"Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma ka nesanta kanka da kalar sana'arsa ka maida kanka baya ta hayar sanya jikinka a al'amura ta harkar gona?,bayan sana'ar ba taka bace,gadon gidan Alhaji hamza kibiya dinne zasu daukeka su cusa ka?,sannan su raba dansu da fu'ad kai su tsigeka daga gareshi?,wanne irin ragon azanci ne wannan shirme da shashanci?,sannan wannan kadai ya isa ya nuna akwai mummunar manufa da qulli cikin zuciyar amina da manufa aka shirya wannan".
Maganganunta sunyi masa girma qwarai,mamaki kuma ya lullubeshi har sai daya tsaya kawai yana duban yadda maamah din ta haqiqice.
".....bazan yarda ba a rabamin kan yarana,bayan a mahaifa guda suka kwanta......don wannan zalunci ne kawai,duk yadda zakayi ka nema komawa sashen da dan uwanka yake aiki,shima kuma zan masa magana kaji?" Sai ta qarashe kuma cikin kwantar da harshe saboda magana ta gaba da takeson yi.
"To" Kawai ya iya cewa da ita,ya sani basai an gaya masa ba,maamah din tayi nisan da batajin kira,hakanan dukkan wani bayani da zaice zaiyi mata yana zaman bata lokaci ne kawai a wajenta.
"Yanzu bayan kamfanin diamond ai ina sanya ran zuwa yanzu addu'ata ta cicciba Muhammad izuwa mallakar wasu boyayyun mafanunnukan ko?" Ta fada tana murmushi tare da tsare musaddiq da kallo.
Dubanta yayi sosai,yana ji har cikin zuciyarsa da gangar jikinsa bai gamsu xa yanayin tambayar tata ba,don haka girgiza mata kai kawai yayi
"Bansan komai a kanshi ba maamah tunda ba sashe daya muke dashi ba" Wani abu ne ya tsaya mata a wuya,amma sai tayi qarfin halin danneshi ta amsa masa da
"Haka ne......amma dai baka ce bakasan qarfi da nauyin kudaden da suke shigo masa ba ko?" Sake daga kai yayi yana dubanta zarginsa yana sake tabbata
"Bana ce ba maamah.....abune da ya shafi sirrinsa kuma ba a qarqashinsa nake aiki ba.....ni ina qarqashin farouq"
"Eh to.....maganar gaskiya sai yanzu na fahimci kimiyyar da ta sanya amina tayi kutin kutin din cusa danta wa Muhammed kai kuma ta rabaka dashi.....kana jininsa wanda bashi da na biyunsa a duniya amma bakasan komai nasa ba?.....wanda ni nayi imanin a yanzun inda zan zaunar da shi saddiqun nayi masa ire iren tambayoyin da nayi maka din yana da amsar kowacce fes?.....wannan itace hanya mafi sauqi da zata samu salwantar da fu'ad da dukka abinda ma ya mallaka". Idanunsa ya runtse yana jin zafin mummunan zaton da maamah din ke jifar 'yar tahalikar dashi.....matar data zame musu bango majingina,matar data zabi farincikinsu akan nata.....matar da silarta ne a yau suka zama dukkan abinda suka zama din.....suka kawo izuwa matakin da suke kai a yanzu......matar da banda ita da yanzu shi da muhammad din duka da take taqama dashi ba'asan a wacce shiyya nahiya ko yanayi suke ba.
"Maamah..." Ya fada yana bude idanunsa a kanta ba tare da ya shirya tsaida maganarta ba.
"Duk yadda kike tunanin anni fa ba haka take ba.....idan baki godewa anni ba bai cancanci ki jefeta da mugayen zato ba......kamfanin nan da rayukanki suke baci akai asalin diamond din da aka samu ba hamma bane kawai ya sameshi ba.....a lokacin suna tare da BB farouq......"
"Amma shi ya haqo shi kuma ya samu nasarar tsira dashi.......ka dauka bansan dukka wannan ba?" Tayi maganar tana tsareshi da idanunta da suka cika da bacin rai. Lallai sai sun nuna mata fifikon matar can akanta?,bayan bata da masaniya akan sanda ta dauki cikinsu bare kuma haihuwarsu?.
"Eh hakane.....amma shi BB farouq baida sha'awar harkar diamond noma yafi so shi yasa......"
".......shi yasa aka fidda haqqinsa aka bashi nasa kason......dukiya ta zama ta muhammad sh kadai......amma duk da haka basu qyaleshi yana amfana da abarsa shi kadai ba.....saboda nasa kason da nasa bangaren na haqar ma'adanai yafi noma albarka da kawo samu,shi yasa suka tattare shi suka kuma dora masa dukan lalurarsu suna zuqeshi sannu a hankali.....suka kuma nesantaka dashi.....suka haramta maka sanin komai daya shafeshi ta cusa danta" Ta qarashe maganar da wani irin ciwo da emotiona daga zuciyarta
"Maamah....." Ya kira sunanta yana son dakatar da ita. Baya qaunar ko kadan wadannan kalaman marasa dadin sauraro suna fita daga bakinta zuwa kawunan mutanen da suka yiwa rayuwarsu tsaiwar da babu wani mahaluki daya taba yinta
"Ni na zabi fannin noma da kayan abinci......basu suka sani ba....ba wanda ya bani shawara....."
"Musaddiq!.....ina fada kana fada duk akan mutanen can?,to waishin ko zaka koma cikin aminatu ta sake haifarka a matsayin danta bani mariya ba?". Maganar yaji tayi tsauri da yawa,kuma ya sani uwa uwa ce komai lalacewarta,hakanan ba'a canzawa tuwo suna,don haka ya miqe tsam,don dama a qagare yake da wannan zaman da baiga ma'anarsa ko alfanunsa ba. Ya dauka zasuyi hira ne irin ta d'a da uwa?,ya dauke zata tambayeshi bayan ta barsu yaya suka rayu?,ya dauka zata nuna nadaman barinsu da tayi sun basu gama zama mutane ba?,sai gashi gaba daya hasashenta da hangenta ba'a nan yake ba?,da gaske ne abinda zuciyarsa take raya masa ta biyo DAUKAKARSU DA DUKIYARSU NE?.
"Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki,sai da safe.....na barki lafiya" Ya fada yana juyawa a hankali yana fita daga falon zuwa farfajiyar gidan.
Da kallon takaici ta bishi,shi kansa me sukuni da wadata ne wanda zai iya kashe mata ko nawa take buqata ballanta a gangaro kan muhammad,mahaukatan kudade ke shigo musu daga harkar noma kayan abinci da sauran kayan masarufi da sukeyi,kuma su rabasu cikin qasashen Africa dama qasashen qetare. Tana da dukka information daidai gwargwado a kansu.....amma sai gashi wadatar kowannensu yanason zame mata hoto.
Yadda ranta yake a bace sai zama ya gagareta,takai ta kawo kusan sau uku tana ji har cikin zuciyarta ya dace ta gaggauta daukan mataki,ya kamata tayi wani abu akai kada komai yaci gaba da tafiya a haka. Daidai sanda takai dab da qofar taji horn na mota da kuma shigowarta farfajiyar gidan,bata bi takai ba amma zuciyarta tana mamakin baqon daren da sukayi.
Mintina uku kawai tayi sallama cikin falon. Sallamar data sanya maamah din waiwayowa tana amsa mata fuskarta babu walwala.
Sanye take cikin wani lafiyayyen lace ruwan zuma. Kallo daya tak zakasan cewa ba na qananun mata bane,ba kuma qananun kudi aka sanya aka mallakeshi ba haka dinkin boubou din da aka zuba masan. Zagayayyen dauri ne saman kanta da zai gwada maka adadin wayewarta da kuma zurfinta a sanin data yiwa duniya. Mayafinta na yafe a kafada daya,daga hannayenta har zuwa wuyanta adon sarqa zobe da bangles ne da babu ko tantama da shakka na gold dinne. Ita din idan ka kalleta baifi ka bata shekaru arba'in da biyar ba,saidai kuma ta dara hakan,don a yansu tana dosar cika shekaru sittin ne a duniya.
Daga bayanta wata macece wadda duka ba zata haura shekara arba'in ba. Riqe da wata kyakkyawar handbag wadda babu ko tantama jakar matar dake gaba ne saboda dacewa matuqa da tayi da kayan jikinta.
Maimaita sallamar tayi a karo na biyu tana duban maamah fuskarta a sake. Wannan ya sanya maamah din tayi qoqarin sakin tata fuskar gami da sakaya damuwarta a gefe,cikin mamaki da tarba me kyau ta matsa gareta tana tararta
"Hajiya......isowar yaushe?" Ta tambayeta tana murmushi
"Tun shekaran jiya fa?,gajiya nayi ma na gudo,amma ason dan ahalan sai farkon sabon wata zamu dawo" Ta furta tana neman wajen zama.
Zaman itama tayi a kujerar dake fuskantar tata
"Da kyau.....ai ya kyauta wallahi,ko yanzu aikin huta ko?"
"Yadda ya kamata kuwa.....wai nikam musaddiq nake gani yana fita sanda nake shigowa da mota?". Dan tabe baki kadan maamah din tayi sannan ta amsa cikin salon rashin bawa maganar muhimmanci
"Shine mana"
"Hala bai ganeni ba,don baiyimin magana ba"
"Ko ya ganekin ma babu lallai ya miki magana ai harira" Ta amsa mata boyayyar damuwar fuskarta tana bayyanar da kanta.
Kallon tsanaki hajiyar mamallakiyar sunan harira ta yiwa maamah kafin tace
"Ban gane me kike fada ba mariya" Qarasa bawa sauran boyayyar damuwarta qofa tayi ta fallasa kanta,don tambayar sa harira tayi mata ta zama tamkar susa ce tayi mata akan ciwonta
"Ina da damuwa harira.....ina da damuwar da har kwanan gobe na gaza gano maganinta".
A nutse hajja harira ta waiwaya ta dubi 'yar aikinta,wadda ke tsaye daga gefe,tunda suka shigo taketa faman gaida maamah din amma bata ma jita ba bare ta amsa
" Ajiyemin jakar ki fita daga waje ki jirani" Ta fadi mata. A ladabce ta ajiye jakar sannan ta juya da hanzari tana ficewa,abinda ya bawa hajja harira damar maido hankalinta ga maamah
"Nayi tunanin kawo yanzu kinyi nisa daga dukkan wani abu me suna damuwa daga randa dan cikinki ya zama mamallakin kamfanin diamondchore?"
"Daga sannan sabuwar damuwa ta fara hajja harira" Maamah din ta furta ranta yana matuqar quna
"Idan na kalli yadda kike fantamawa hajja sai na sake tabbatarwa kaina lallai akwai aiki a gabana......aikin kuwa shine YADDA ZAN MALLAKE 'YA'YANA". Wani irin duba hajja hariran take mata,sai kuma ta kyabe baki
"Keda wanne baccin kikeyi da baki aikata hakan ba mariya?,wanne gangancin ya kaiki?,bakisan daga ranar da Allah ya yiwa 'ya'yanki arziqi ba.....akwai tarin mutane da dama da suke marmarin juye matsayinki su haye kai ba?.......kin ganni nan mariya?,kaf 'ya'yana babu wanda ya isa ya aiwatar da wani abu komai girmansa kuma komai qanqantarsa ba tare da sanina ko yardara ko sahalewata ba.....ke koda matansu ko 'ya'yansu zasu yiwa kuwa sai da sanina da yardaya,a cikinsu babu wani gida da bansan me yake gudana a cikinsa ba 24hrs......yanzu haka katafaren gini na sanya sukeyi na bai daya duka zamu zamana a muhalli guda....." Kai kawai maamh ke gyadawa,a yau ta yarda ta miqa wuya ta kumayi surrender kan cewa harira ta fita shu'umanci,iya yadda tae bada.labarin cike da izza da alfahari kawai ya isa gaya maka gaskiyar haqiqanin zahirin abinda ke faruwa kenan......jikinta ya isa ya sake qarfafa maka zancanta.....tsanin alfahari da takeyi yayin bada labarin kuma zai gaya maka yadda take jin dadin yadda take tafi da rayuwarta.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 48
"Inaso na zama uwa mafi gata a duniya harira,inason na zama uwa mafi izza akan yaranta......inason na zama uwa mafi zama abar alfahari abar nunawa a duniya....inason 'ya'yana su dawo qarqashina.....na mulkesu kaman yadda ubangida yake mulkar bawansa......su zamana a tafin hannuna kamar yadda jariri sabuwar haihuwa yake zama a hannun mahaifiyarsa".
Wani murmushi hajja harira ta saki tana duban maamah
"Lallai mariya burinki me girma ne......amma dai kinsan ki baro kari tun ran tubani ko?,ko mu da muka raini yaran har suka girma muka aurar dasu,bamu gusa ko nan da can ba muna gabansu suna gabanmu sabunta ayyukanmu mukeyi akai akai.......munayi matansu sunayi,wanda keda nasara shike samun rinjaye.....ballantana ke,yaranki ina da tabbacin suna buqatar gagarumin aiki kafin samun saituwarsu akan bigiren da kikeso".
"Abinda ya wuce ya wuce hajja harira.....yanzu meye abinyi?" Gyara zamanta tayi sosai tana bawa maamah dukkan hankali da nutsuwarta
"Akwai plans guda biyu,plan A da plan B......idan A baiyi aiki ba zamu wuce zuwa na biyu"
"Kamar?" Ta tambayeta cikin matsuwa da jin bayanin komai
"Yauwa......na farko akwai wajen mutumina da zan kaiki wanda shi yakemin aiki akan komai da kowa......"
"Kai....kai.....amma kin gama min komai" Maamah ta fada tana gyara zamanta da kyau fuskarta na washewa da madaukakiyar fara'a,saboda ta hangi zuwan nasararta a nan kurkusa......ta hangeta tana fantamawa fiye da yadda hajja harira ke fantamawa din.
"Ba komai fa.....zaman tare ai ba qarya bane....zaki zayyane masa dukkan abinda kike da buqata wanda nake da imani a kansa mallaka sai yadda kika juyasu.....akan mansur ya fara yimin aiki,lokacin da yayi aure sai na fuskanci wani abu,maganata qasa take da maganar matarsa,dukkan umarni da zabi nata ne sai abinda taga dama sai kuma abinda tace.....a sannan na farga,amma in gaya miki inayi yarinyar nan tana nata har daga qarshe na hadu da DAN DUMA....tuni na saka ya qara mata wuta a gidan,mansur ya saketa tayi gaba,tun daga ranar dukkan wanda zaiyi aure a cikinsu nice nake zaba masa yarinyar da nakeso ya aura din,wadda zan cimma buqatuna ta hanyarta,wadda zan juyata ba musu ba kuma damuwa......to kema wannan shine plan B dinki idan na farko yaqi aiki"
Shuru maamah tayi tana jinjina kai,lallai duk iya yadda take ganin mulki da isa da kuma izzar hajja harira ta wuce nan. Wannan shine cikakken ma'anar HAMSHAQIYAR UWA ko kuma CIKAKKIYAR UWA. Idan so samu ne tana son kamar haka ko sama da haka
"Amma banajin musaddiq zai qara watanni shida ba tare da yayi aure ba"
"Ko yau yau zaa daura auren kina iya ruguzawa,ki maye gurbinta da wadda kikeso" Ta fada kanta tsaye cikin confidence.
"Waye babbar damuwarki a cikinsu?,muhammadu?" Kai ta jinjina. Tafi damuwa da kamashi a hannu fiye da musaddiq. Tasan waye fuad din,yana da tsauri da tsananin da ita kanta tayi imanin mafi rinjayen aikin a kansa zaa gabatar
"To ki manta da batun musaddiq me sauqi ne"
"Haka ne wannan" Ta fada tana murmushi,tana jin cewa qarshen matsalarta yaxo,tana jin cewa lokaci yayi da zata cika muradanta
"Yaushe zamu tafi zuwa wajen DAN DUMA?,kinsan ba'a bori da sanyin jiki" Ta karkata tambayarta ga hajja hariran cikin zumudi da farinciki,tana jin bacin ranta yana zagwanyewa.
Tunda suka fito daga wajen a cikin jikinta kawai takejinta uncomfortable. Haka kawai take jin kamar akwai wani abu,tayi dukkan research da idanunta hankali da kuma tunani bata ga wulgin kowa ba,hakanan bataga alamun ana bibiyarsu ko wani abu da yayi kama da hakan ba. Saidai har suka soma nisa da wajen bata samu nutsuwa ba,abinda muddin ta soma jinsa a jikinta zaiyi wahala idan baby afkuwar wata matsalar.
"Me napep idan zaiyuwu ka kaini madabo.....zan qara maka wani abun" Tacewa me abun hawan. Malam ne yaketa fado mata a rai,dattijo kuma kamilallen mutumin,ma'abocin nutsuwa karamci da kuma ilimin addini.
Asalin haduwarsu ta fara ne a ranar da zasu rabu da ameen,daya daga cikin mazan da suka taba shiga rayuwarta dama tarihinta. Abun yaso ya kwabe mata har ameen din yaso fahimtar ainihin wace ita ba tare da takai ga fita daga layin ba. Ya sanya aka biyo sahunta tiqa tiqan qattin dake gadin qofar gidan nashi harda rakiyar karensu guda daya.
Malam din shi ya musu kaca kaca,ya kuma hada harda ameen din daya tako da kansa,ya nuna masa daraja da martabar mace,sunaji suna gani yayi saving nata a hannunsu ya wuce da ita sukaci gaba da takawa a qafa har titi.
Ita dinma a hanya bai qyaleta ba,ya dinga yi mata fada bawai don ya fahimci wacece ita ba?,ko ya fahimci ainihin abinda ya hadosu. Donme tana diya mace zata bari takai gefin magriba a irin wannan unguwannin?. Haka kawai taji ranta ya nutsu da dattakonsa da kuma addininsa,rana ta farko da wani ya taba yi mata fada irin wannan tun bayan shudewar iyayenta. A daren ranar tayi kuka tayi kuka,kukan kuma kukan dadi ne na yadda yau aka samu mutum qwaya daya daya tsaidata da zuciya daya yana mata fada kanshi tsaye. Tun daga wannan ranar malam din ya zame mata daya daga cikin mutanen da suke da martaba a idanunta. A duk lokacin da kudi suka samu takan dauki wani abu tayi tattaki taje ta gaidashi,ta kuma bayar wa almajiransa tace ayi ma iyayenta da suka rasu sadaka.
Matarsa tana da matuqar kirkin da ta dauketa kamar diya kaman yadda malam ya dauketa diya a wajensa. Duk sanda zataje gidan bata gaza fahimtar wasu abubuwa daga sabreen. Macace mai matuqar hikimar da sai da takai daga qarshe ta karanci wace sabreen din,sai ya zamana itama bata fiya boyewa inna komai ba muddin ta tambayeta din,gidan sai yake zame mata wajen samun nutsuwa a wadansu lokutan.
Unguwar madabo,daya daga cikin tsaffin unguwanni dake birnin kano,wadda take da dadadden tarihi. Hakanan ta tara malamai da masana addini masu yawan gaske.
Tsukukun loko ne da ko adaidata sahun a matse yake shiga,wannan ya sanyata ta nemi ya ajiyesu daga bakin babban lokon da zaka karya ka shiga qaramin. Ta bude jakarta ta sallameshi,sannan suka fara takawa ita dasu zuwa ciki.
Tun a rumfar dake qofar gidan ta tabbatar malam baya nan,don babu tabarmin karatu,hakanan daliban nasa sai jifa jifa kowa yana sabgar gabansa,don haka kai tsaye suka wuce zuwa ainihin cikin gidan.
Da sallama a bakinta suka kutsa kai,gidan yana nan kamar kullum cike da tsafta. Ba kowa a filin gidan sai hayaqi dake fitowa daga kitchen da alamu ana gab da kammala tuwon dare. Yaransu bakwai da malam,maza hudu mata uku kuma dukkansu sun aurar dasu,don haka inna ce kadai ke rayuwa cikin gidan,sai babbar jikarta da aka kawo mata don ta tayata zama.
Sake sallamar tayi,kusan lokaci daya aka amsa mata daga kitchen din da kuma rumfar dakin inna. Cikin qasa da second daya wadda ke kitchen din ta fito. Matashiya ce da duka duka bata wuce sa'ar huda ba,murmushi sosai take saki,ta baro cikin kitchen din tana goge hawayen fuskarta da hayaqi ya sanya mata tana takowa
"Adda sabreen.....kece yau a gari?" Miskilin murmushin nan nata ta saki
"Inji maqi baqo ko rumasa'u?" Sai ta saki 'yar dariya tana kamo haneefa
"Muje yau inna taga su auta,tanata zancanku tace kwana biyu shuru,gashi batasan muhallinku ba bare ta binciki ko lafiya?,layinki Kuma kwata kwata baya shiga" Ta qarasa maganar tana riqe da hannun haneefa wanda tuni sukayi gaba zuwa dakin innar.
Sai a sannan da rumasa'u tayi zancan layinta baya shiga ma ta tuna yana daya daga cikin layukanta da suka tafi hutu,sai ta taka a hankali tana bin bayansu zuwa ainihin falon innar.
Dare dare ta samu haneefa gefan cinyar inna. A duniya gidan yana daga cikin gidan dasu haneefa din keson azo,don sai ya kasance musu kamar wani gida daya qwaya tak na 'yan uwansu da suke iya ziyarta su kuma sake,sakewar da basa iyayinta cikin ainihin gidan mahaifinsu.
Da murmushin tambayar da taji innar na yiwa haneefa ta qarasa shigowa ciki
"Wa'alaikumussslam.... .ina nan ina tuhumar amaryata me takeci naga tana ta tsaho?,kunyi nisan zango wannan karon AMEENATU(real name dinta kenan)". Murmushi ta kuma saki,a duk sanda innan ko malam sukayi kiranta da sunan ba wanda ke fado mata a rai sai mahaifinta. Shike yawaita kiranta da sunan,sunan da ya kasance na qanwa ga mahaifinsu guda daya tak da aka haifa a tsakanin su maza su uku,tazo kuma ta rigasu rasuwa a wajen haihuwa tabar nata yaran mata duka su uku.
"Kuna raina inna....abubuwa ne suka sha kaina" Ta fada tana zama itama.
Gaisawa sukayi sosai ta tambayeta malam
"Malam yau duka bai zauna ba,ya tafi kasuwar qauye,amma yana hanya nasan in sha Allahu".
Kamar kusan kowanne lokaci idan sunzo gidan,komawa take 'yar kallo,nadra haneefa harma da hudan suke sabgoginsu.
Lumshe idanunta tayi tana sauke boyayyar ajiyar zuciya. Ta tabbatar yau ta faranta musu ta kuma rage musu kewa qunci da takurar zama waje daya. Tana so ta dinga kaisu guraren da zasu dan sha iska,amma tana tsoron koda da kuskure suga wani abu da zai iya affecting tunaninsu.
Suna matuqar son a zo gidan,amma kuma duk dadewar da za'ayi ba'azo din ba ba zasu taba tada mata zancan ko suyi qorafi koda kuwa sau daya ba,har sai ranar da sukazo din.
A nan sukayi sallar magariba,sukaci kuma tuwon dare. Suna haramar tafiya malam din ya dawo.
Sosai shima yaji dadin ganinsu,ya bude kuma duk abinda yazo dashi din kama daga rake,gyada,quli kabewa,dinya da sauransu ya diba musu. Walwalarsu ta dadu sosai a sannan,duk sai da suka fice da zummar zasu tafi ya rage saura Sabreen din,ta xuge jakarta ta fiddo kudi ta aje gaban malam
"Malam ayimin sadaka,sannan ayi mana addu'a". Kudin ya kalla sannan ya kalleta.
"Zan miki addu'a aminatu koda baki bada komai ba....."
"Malam bakai na bawa ba,yaran malam na bawa"
"Idan kin fita waje ki raba musu da kanki kamar yadda aka saba" Ya tareta
"Malam don Allah kayimin alfarma ko rumasa'u ta raba musu,tabbas don dare yayi ne da bazan karya maka tsarinka ba,malam kai kemin fadan kaiwa dare a waje" Ta fada murya a karye. Tanason masa ihsani,amma mutumin yana da wani irin kamewa da gudun duniyar data tabbatar bazai karbi komai nata ba
"Shikenan,Allah ya karba.....kici gaba da kula da qannenki da kanki"
"In sha Allah malam" Ta fada tana yin qasa da kanta kunya da nauyinsa suna kamata. Tana jin kamar inna ta gaya masa wani abu a kanta ko zata gaya masa,saidai ta sani ko daya innar nada cikakkiyar kamalar da bazata taba fadin sirrin wani ba.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 49
Tunani ne kala daban daban cikin kanta sanda suke abun hawa har suka isa gida.
Banda hadiyya data samu tana zance a farfajiyar gidan nasu bata hadu da wani babba ba sai yara dake dan kai kawo a tsakar gidan nasu. Zuciyarta a karye take bude musu qofar dakin. Wannan shine tabbacin basu da wani sauran gata.....ba wani wanda ke tsaye yana jiran dawowarsu......babu wani da zai tambayi ina sukaje?,me yasa suka dade wuni sur a waje?,ba wani me musu barka da dawowa,dasu dawo da kada su dawo duk daya.....ire iren wadannan abubuwa ke qara mata wata qaqqarfar zuciya tare da jin cewa.....ZATA SADAUKAR DA TATA RAYUWAR don samarwa rayuwar qannenta gobe me kyau.....zata zame musu makwafin uwa da uba,dukkan wuya da dadi.....zata hanasu dandanar duk wani kalar baqinciki na rashin gata dama rashin abun kulawa da rayuwarsu.
Dukansu a qoshe suke kuma a gajiye,don haka basu jima ba kowacce ta nema wajen kwanciya,don dama ita haneefa suna shigowa ta bingire a wajen.
Sau biyu tana yaye labulen tana duban tsakar gidan nasu. Wanka takeso ta fita tayi saboda yadda gajiya kebin jikinta,uwa uba ma kuma ita din tun asali mutum ce data saba da yin wanka da dare kafin ta kwanta,saidai kuma daga baya abun ya zame mata qalubale babba,saboda kallon da ake mata da wasu idanu na daban.
Yadda ta fita dinnan ta wuni a waje ba zata iya kwanciya haka ba,don haka taci gaba da dabuwa. Akwai daukewar qafafu sosai,wanann ya bata daman cire kayan jikinta ta daura zani ta kuma lullube sassalkan gashinta da babban towel,ta dauki kayan wankanta.
Tana shirin fita nepa suka kawo wuta,don haka ta tsaya ta kashe solar din dakin ta maida musu nepa sannan ta fito.
Ta tsaya daga bakin famfonsu tana tarar ruwa. Tsakar gidan tarwai da haske,kuma tsaf tsaf dashi,dabiar gidan qwaya daya tal dake burgeta,wanda idan ka dauke wannan babu wani abu dake burgeta cikin gidan dama jama'ar gidan gaba daya.
Allah yasa har ta gama tarar ta wuce wankan ba wanda ya fito. Ta kammala ta nade jikinta da zanin ta dauro towel din a sama ta fito.
Tana duqe baqin famfon tana daura alwala. Bude toilet din wankan da akayi ya sanyata daga kai. Sukayi idanu hudu da ita,saita miqe sosai ta tsaya maimakon dazun da take duqe tana daura alwala.
Kallon bibo din takeyi kamar yadda itama ita take kalla,tun daga qafafunta har zuwa kanta da yake lullube da towel.
"Ha'illallahu.....mahammadurrasulillahi......ke duniya ina zaki damu?,aah?yanzu wankan ma sai kinzo gida?" Bibo taja qaramin salati sannan ta kama haba tana sake qarewa sabreen kallo.
Wani abune yazo ya yiwa sabreen tsaye a wuya,ta lumshe idanun takaici. Ta gama fahimtar zahirin abinda bibo ke nufi......ta kuma gama fahimtar abinda inda ta dosa,saidai kafin ma ta sake daga qafarta ta sake jin muryarta
"Kiji tsoron Allah 'yar nan......ki daina sanyawa mala'iku suna tsaida iyayenki cak cikin kabarinsu......yanzu wannan wankan....." A fusace da kuma wani irin zafin nama ta waiwaya tana duban bibo,abinda ya sanya towel din kanta zamewa sumarta ta fito.
Bata qarasa ba itama sai tabi kan nata da kallo. A bushe yake ba kuma alamun damshi ko lema,hasalima ta nannade doguwar sumar tata da tayi gado ta uwa da uba a tsakiyar kanta ta cusata guri guda,wannan ya sanya bibo din hadiye abinda taso fada din.
"Ke zaa cewa kiji tsoron Allah,kuma zan maimaita miki kiji tsoron Allahn" Ta fadi da ita a nutse sannan ta fara takawa tana dosar dakinsu.
Idanma tace zata riqe zafin da qirjinta yakeyi da suya to tabbas ta yiwa kanta qarya,don haka ta sulale saman kujerar falon ta saki wani marayan kuka.
Bibo na daya daga cikin qalubalen rayuwarta,bibo na daya daga cikin mutane na gaba gaba da suke mata wata irin adawa mara fasali ba tare da tasan meye ne ta tsare musu ba. Ta jima a wajen tana kuka har sai da fuskarta tayi wani pink pink,sannan ta samu ta sauya kaya taja jikinta zuwa kan gadonta ta kwanta tana rufe idanunta tare da sauraron bugawar jini daga kanta wanda keson komawa ciwon kai.
Sassanyan ringing dinnan shine ya sakata bude idanunta. Shaf ta mance da batun wayar sai yanzu da tayi kuka. Tunawa tayi tayi alqawarin kai wayar a yau,kada ma su tsammaci ko ta gudu da sune,wannan ya sanya ta miqa hannunta qasan pillow din data ajeta dazu ta dauko da nufin dagawa ta basu uzurin gobe in sha Allah aje a karba.
Bata wani tsaya bata lokacin duba me kiran ba,tunda tasan koma waye zai kira a irin wannan lokacin tabbas makusanci ne,don haka ta shafa ta daga ta kuma Kara a kunnenta.
"Assalamu alaikum anni?" Ya furta cikin husky voice dinsa dake cakude da wani irin nannauyan sauti dake nuna izza da zatin mamallakin muryar. Yayi sallamar a sanda yake tsakiyar system da kuma tarin tarkacen takardun dake dauke da plan na ginin sabon kamfanin samar da kayan qyale qyale na mata mafi tsafa da daraja da za'a dinga qawatashi d wani yanki na diamond d gold.
Wani yankewa gabanta yayi ya fadi,zuciyarta kuma ta buga sosai har tana jin sautin bugun cikin kunnuwanta. Batasan dalili ba batasan kuma me yasa taji hakan ba,sai ta buda bakinta a hankali da muryarta da tayi nauyi saboda nauyin dake cike a qirjinta
"Ba ita bace". Shuru ne ya biyo bayan fitar sautin nata. Ita tana bawa kanta tabbacin wancan mutumin ne daya kira duba da shurun da aka sakeyi mata kaman dazu,shi kuma kwanyarsa tana son alaqanta sautin da muryar mara kunyar yarinyar nan data dag masa waya.
Kusan a tare suka daga wayar daga kunnuwansu. Ta samu tabbacinne ta hanyar karanta sunan dake yawo saman screen din.
Sauke wayar yayi daga idanunsa,yaja siririn tsaki yana kashe wayar. Sautin tsakin yakai mata har kunnenta,wani mummunan baci taji ranta yayi. To ita meye nata a ciki da har zai bita da tsaki?,waye wannan daya cika izza haka?,wanne irin mutum ne me izgili da rashin sanin daraja da martabar dan adam?,don kawai a bisa kuskure wayarsu ta fado cikin kayanta sai ta zama abar wulaqantawa?. Samun kanta tayi da latse wayar kawai ta kasheta gaba daya ranta yana suya,cikin ranta kuma tana yiwa kanta alqawarin a gobe wayar ba zatakai sha biyu na rana ba a hannunta zata kira busari yakai musu duk inda suke.
"Wanne irin wulaqanci ne da rashin sanin abinda kukeyi da zaku ci gaba da barin wayar anni a wani wajen?" Fuad din ya furta daidai sanda ya kira musaddiq.
"Kayi haquri hamma,ta fadi inda za'a karba anje ba'a samu ba,anyita kiran wayar kuma ba'a dagawa".
"Koma meye banason na sake kira naji muryarta.....kuyi magana da ita idan wayar takeso ta sauke layin daga kai,ka sanya ayima annin swapping a dauki wata wayar a hada mata".
" Ka kwantar da hankalinka me babban suna,banjin yarinyar tana da niyya ko nufin riqe wayar nan,akasi kawai dai aka samu da ajizanci irin na dam adam......tana da kirki qwarai,ita ta kaini asibiti ta kuma zauna dani har sai da musaddiq ya iso". Wata sassanyar iska ya saki daga bakinsa,sai yanzu ya tuna inda yasan muryar
"Itace mara kunyar yarinyar nan data tsaya tana yiwa mutane fada akai don ta kaisu asibiti?" Ya jefawa anni tambayar da nutsatsiyar muryarsan nan.
Murmushi ne ya subucewa annin. Tasan halin fu'ad qwarai da gaske. Yana da tsananin kamewa da rashin son shiga sabgar kowa
"Ba rashin kunya tayi ba muhammadu......fada ta yiwa musaddiq,kuma ai ta fadi gaskiya ne,ta kuma yi daidai,sun tafi yawonsu sun barni,a jikina kuma babu inhaler kwata kwata,a nata ganin indai hakan taci gaba da kasancewa komai ma yana iya faruwa". Shuru ya ratsa tsakanin bayanin anni,yana ji kawai annin tana son bata kariya ne saboda halinta na bawa kowa uzuri komai girman laifin da ya aikata mata
"Is okay....." Ya fada yana sauke siririyar ajiyar zuciya a qoqarinsa na fesar da bacin da ranshi yayi
"Ya jikin naki anni?"
"Jiki alhamdulillah na warware"
"Suna kula dake kuwa?" Ya sake tambayarta da wannan seriousness din nashi. Murmushi ta saki kadan
"Qannenka suna qoqari sosai,ina samun kulawa tamkar kana nan.....saidai kewarku,ina fatan komai yana tafiya kaman yadda aka zata?,kowa kuma yana lafiya?" Murmushi ya saki,wanda mutum uku keda wannan baiwar sakashi murmushin koda baiyi niyya ba,anni abba da farouq kada ma farouq din yaji labari. Abune me wahala ka tsinci murmushi akan fuskarsa,akwai mutane da yawa dake da tambayoyi da yawa a kansa
Anya kuwa ya taba dariya?
Wannan kuwa yana murmushi?.
Wasu tambayoyin na isa kunnensa ta harshen farouq,wasuma kam baisan ana yinsu ba.
"Ba zamu wuce kwanaki hudu ba anni in sha Allah". Farinciki ya wadaci fuska da zuciyarta
"To ma sha Allah.....amma baka shaidamin ba me babban suna?,banda na tambayeka da ba zaka gayamin ba ko?".
"Aah anni......banason na sanyaki wannan hidimar me yawa" Murmushi ta sake saki
"Hidima ai bata qarewa Muhammadu muddin akwai rai a jikina.....fatan da zakuci gaba da yi mana shine Allah ya qara mana lafiya....."
"......da nisan kwana me amfani" Ya qarashe fadi. Qaramar dariya ya sanyata a wannan karon
"To da nisan kwana me amfanin mu daku gaba daya".
Koda suka gama wayar baiko motsa ba a wajen,yayi zaune da wayar kawai a hannu yana juyata. Duk yadda zai fasalta anni a rayuwarsa da zuciyarsa bazai kwatantu ba. Ita din uwa ce data amsa sunanta na uwa. Wadda tayi sadaukarwa da yawa cikin rayuwarsu,sadaukarwar da tayi musu ba qarama bace,sadaukarwa ce da UWA kadai ke iyayi wa danta.
Asthma dinta bata taba hanata taba ruwa saboda su,asthma dinta bata taba hanata sammakon tashi koda da sassafe ne a lokacin da hazo da sanyi suka lullube sararin samaniya......a yanayin da kuma yafi zama barazana ga masu lalurar......asthma dinta bata hanata tsaftace musu muhallin kwanansu......bata hanata dafa musu abinda zasuci
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 50
koda ita din bataci ba,bata kuma hanata kulawa da lafiyarsu koda ita din bata da cikakkiyar lafiya. Har tsakiyar zuciyarsa yana jin wata qauna me girma tana tabashi game da anni,tayi musu abinda baki bazai iya fadi ba,zuciya da ruhi ba zasu iya mancewa ba. Ta musu hidima da jikinta da kudinta da lokacinta harma da lafiyarta,irin hidimar da ya debe tsammanin zasu sameta,irin hidimar da suka buqaceta a yunwace daga wajen wadda tayi silar zuwansu duniya amma ta gagaresu.....kulawar da baiyi tsammanin zasu sameta ba daga gurin kowacce mace a duniya. Baiga abinda zai samu a duniya ba da zai manta da anni.....baya tunanin akwai abinda anni zata nema daga gareshi ta rasa.
Yana shirin sauke wayar tasa don ya tattara tarkacensa ya wuce daki ya samu bacci koda na awa biyu ne kafin zuwan lokacin sallar asuba sai kiranta ya shigo.
Kamar ko yaushe ya zubawa kiran idanu,a duk sanda zata kirashin sai ta tuna masa da abubuwa masu yawa. Aduk sanda kiranta zai shigo wayarsa saita tada masa wani abu daga can qasan zuciyarsa.
Bashi da wani zabi da ya wuce ya daga din,sai ya sake zama sosai ya ya dauki wayar yana karawa a Kunnensa,
Cikin jin isa da izzar cewa ta haihu.....cikin isa da jin izzar ita din a yanxu wata abace cikin duniyar.....cikin jin izzar ta isa takai qololuwar gata a cikin jerin iyaye mata ta amsa sallamarsa.
"Barka da dare.....an wuni lafiya?". Maimakon ta amsa masa saita sake daidaita kanta,a dake take masa magana
"Yanzun ace bankai kima da martabar da a kullum zaka kirani kaji ya na kwana ya na tashi ba?" Ta maida masa gaisuwar da qorafin abinda me masa suya a qirji.
"Afwan.....kiyi haquri" Ya zabi furtawan. Har cikin zuciyarsa,har kuma tsakaninsa da Allah kirantan kaman yadda take buqata wani baqon abune cikin rayuwarsa dama lokutansa. Yadda ta zamewa rayuwarsu baquwa haka dukkan wata mu'amala da zaiyi da ita take zama baquwa a wajensa. Koda yayi niyyan yin hakan saboda sauke nauyi da haqqin haihuwa dake wuyansa sai ya manta sam sam,tunda abune da aka fareshi bada dadewa ba,sabo dashi kuwa zai dauki lokaci kafin ya shiga jiki da zuciya,bayan haka ma......kwata kwata mu'amalar dake a tsakaninsu wata irin tattaurar mu'amala ce da babu taushi a jikinta bare ta shiga zuciya da kyau ta tsayema tunani.
"Koda baka nemeni ba ni bazan zubewa duniya ku ba.....ku zama inuwar giginya na nesa kasha dadi...." Ta fadi tana watsa hannuwa ba tare data tuna da kuskuren rayuwarta na farko ba.
Numfashi ya aje,maganartata ta zama tamkar wani tuni ne daya dace ace kanta da kanta ta yiwa shi
"Ba zata zubewa duniya su ba....." Baisan zubewa ta nawa ya rage tayi musi ba,kalamanta a kullum sake haska masa ita yake,yayi imani yana kuma sake samun gamsuwa da dalilai masu tarin yawa dake bayyana masa lallai AKWAI DALILIN dawowarta cikin rayuwarsu......lallai ta dawo ne bawai da sunan nadama ba ko gyaran kuskure......AKWAI DALILI AKWAI KUMA HUJJA.
Wasu yana kallonsu shimfide a zanen tafin hannun qaddararsa,wasu kuma baisan daga inda zasu soma bullo musu ba.
"Ba'a canzawa tuwo suna Muhammad,kuma ko ma meye ka zama sai dana haifeka sannan ka zama din......mahaifiya daya ce kuma ni dince dai". Idanunsa ya lumshe na wasu sakanni kafin ya samu budesu. Ba abinda maganganunsa ke haddasa masa sai sake jagula duk wata qanqanuwar nutsuwa tasa da yake qoqarin samarwa kansa.
"Kiyi haquri" Ya sake maimaita mata kalaman da ta dade da haddacesu daga bakinsa.
"Yaushe zaku dawo?,idan ba nan kusa bane dawowar taka ka sanarmin......don nasan sai yadda akayi dakai,sai kuma abinda aka shimfida maka".
Yaji saukar kalamanta sosai har saman zuciyarsa. BATA SON AHALIN ALHAJI HAMZA KIBIYA ya dade dayin wannan karatun a qanqanin lokacin data duro cikin rayuwarsu......ya kuma san halinta tun daga sanda ya fara rarrabe abubuwa har zuwa sanda ta fice daga rayuwarsu. Idan batason abu bata sonshi kenan......dadi ko wahala basa sauyata akan abun. Idan taqi taqi kenan.....hakanan idan taso taso kenan......bata ja da baya akan duk abinda ta sanya a gaba......bata rasa ABUN HARINTA komai dadewar lokaci.
Wadannan abubuwan ya sanya ya sanya dukkan wata nutsuwa da karatu nasa a kanta......ya sanya duk wani nazari da dogon hange da tsinkayensa a kanta,yasan wacece......sanin da ita kanta batasan bata kuma yi zaton yakai zurfin haka ba.
"Ba zamu wuce satin nan ba in sha Allah" Ya amsa mata kamar yadda ya amsawa anni a dazun.
"Har sai ankai sati?" Ta masa tambayar a zaqe,har abun yadan so bashi mamaki,don sam salon tambayar nata baiyi kama da ta zaqu ko tsahon kwanakin sun mata yawa da zasu bayu ga ganinsa ba,tabbas yasan akwai dalilin tambayar a qasa.
"In sha Allah" Ya bata tabbaci yana jiran dalili na gaba
"Kudi nake buqata ka turamin ta account dina akwai amfanin da zanyi dasu......kada suyi qasa da million daya" Tayi maganar kanta tsaye cike da karsashi da qwarin gwiwa kaman yadda hajja ta kwatanta mata.
Mamaki kadan ya kamashi.....saidai ya ajeshi a gefe
"Akwai abinda baki dashi?,cikin gidan ko sutura ko wani abu makamancin haka?,ko akwai wanda kike da buqatar ayi masa wani abun?"
"Duka babu ko daya.......shin waima sai ina da wannan buqatun zan buqaci kudi daga wajenka?,yarinya ce ni qarama ko kuwa?,ko banyi isar da zaa dauki tsabar kudi a bani ba har sai akwai dalili ko hujja?"
"A'ah......"
"To dakata......ba sharhi nakeso ba......kayi abinda nace daga yau zuwa gobe". Sai yaji alamun yanke kiran,abinda ya tilasta masa sauke wayar daga Kunnensa yana binta da kallo.
Yatsunsa kawai ya dora saman goshinsa yana murzasu a hankali,kadan kadan yake furzar da iska me zafi daga bakinsa. Tabbas yasan da akwai wani abu......akwai wata a qasa......
Wanzuwar kudi a hannunta kwata kwata ba alkhairi bane,kuma ko yanzun bayajin alkhairi ne ya sanya ta nema.
Cikin lokaci qanqani yaji jijiyoyin kansa sun qara adadin gudunsu da kuma harbawarsu,abinda ya haifar masa da fara jin alamun ciwon kai. Bayason hayaniya......bayason matsala kwata kwata,wannan ya sanya yake nesa da mutane da al'amuransu,banda kasuwanci daya daukoshi tsundum ya jefa cikin mu'amalantar mutane qarfi da yaji.
Ba wani karsashi ko qwarin gwiwa ya dauki dukan abinda yasan yana da buqata,a maimakon tattare takardun nasa gaba daya da yayi niyyar yi ya kuma shiryasu kamar yadda ya saba. Yana da wani irin tsafta da duk abinda yayi amfani dashi zai wahala ka sameshi ba'a killace ba.
Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya tura qofar dakinsa idanunsa akan dakunan abba da saddiq daya tabbatar zuwa lokacin sun jima da yin bacci,wani lokacin sai ya dinga ji kamar su kadai ne basuyi sa'ar rayuwa ba.....sai ya dinga ganin kamar kowa ya dace da rayuwa me kyau amma banda su. Duk sanda irin wannan tunanin ya fado masa yakanyi qoqarin korar shaidanne daga ransa.
A gefan gadon ya zauna,ya miqa hannu ya kunna bedside lamp,dan siririn hasken da baida takura da yawa ya bayyana. Hannunsa ya zura qasan drawer din da fitilan take kai,ya ciro wani mini wallet dinsa,ya bude ya sake zaro wani qaramin hoton dake ciki.
Duk da hoton baida cikakkiyar kala amma fuskar mutumin ta fita sosai,kamannin nan nasa da murmushinsan nan da idan ya kalla sai yaji kaman idan ya kirashi zai amsa.
Wani abu ya tsaya masa a wuya,yayin da idanunsa suka sauya launi,gefe daya wani qaqarfan abu da ya jima yana kokawa dashi akan maamah din ya fara taso masa,sai ya fara hadiyar zuciya kadan kadan yana qoqarin hadiye bacin ranshi,tamkar me hadiyar lomar abinci,don daga inda inda kake kana iya hangen Adams Apple dinsa daya zamewa wuyansa dama fuskarsa ado yana kaikawo daga sama zuwa qasa.
A duk sanda ya kalli fuskarsa cikin hoton sai yaji duk duniya ba wanda ya kaisu maraici......a duk sa'ilin da zai kalli wannan jarumar fuskar sai yaji zuciyarsa ta cika da qiyayyar kowacce d'iya mace a duniya idan ka debe anni da manal......wata irin wuta ce take ruruwa a zuciyarsa a kanta......har yakanji kamar bazai iya sake kusantar muhallin da take bama ballantana yaci gaba da accepting nata ko kyautata mata a matsayin uwa.
Fuskar abban wata fuska ce da a kullum take tunasar dashi gwagwarmaya da ainihin ma'anarta.....fuskar tasa fuska ce dake karanta masa tare dayi masa bitar cusgunawa....uzzurawa da azabtarwa irin ta diya mace. Kowanne hoto nasa da abinda yake karanta masa.....hakanan da abinda yake tunasar dashi. Ko kusa ko alama....ko sau daya.....hakanan koda wasa bai taba sha'awar aure ba ballantana wata diya mace. Yana kallonsu a wasu halittu ne na daban da babu imani ko tausayawa cikin lamuransu.
Sanadin ciwon abban....da silar data sanya ya dinga ci gaba abune da bayason tunawa,abune dake dake tilasta zuciyarsa juyawa MAAMAH baya da dukkan abinda ya danganceta. Koda ya tuna da abin a sanda take daura dashi yakanji baya buqatar kallon fuskarta ko kuma sauraren muryarta,yanaji cewa ba abinda zai bashi sukuni face yayi nesa da ita.
*_AKWAI WANI SIRRI.....AKWAI WANI BOYAYYEN SIRRI CIKIN DUNIYARSA_*
*******Sannu a hankali take tafiya cikin daya daga cikin layukan da suke zame musu turba kuma hanya ta isarsu gida a duk sanda suka rasa samun abun hawa ko kuma kawai jin rikici irin na dalibin dakan qirqirarwa kansa tafiyar qafa haka siddan.
Ita daya a hanya amma tanata mamakin yadda yau aka raba musu lokacin tashi daga makarantar alhalin tunda suka fara tsahon shekarun tare ake tashinsu. Ta cika tayi fam akan yadda nadra din da haneefa sukayi gaban kansu suka taho gida abinsu ba kamar yadda suka saba ba abinda basu taba yi ba.
Gefe daya kuma na zuciyarta ya cika da saqe saqe tare da tunanin yadda zata qarqare haddace ayoyin qarshe na shafin da a yau zata bada haddarsa a islamiyya. Kaman daga sama,babu zato kuma ba tsammani taji an finciki qaramar jakar da take dan cillata a hannunta wadda ke dauke da muhimman abubuwa da dama. Sanda ta daga kai kuwa a firgice barawon ya soma nisa da ita yana gaya mata
"Idan kina da gata,ko kina da me qwatoshi ki turo shi" Sai ya juya cilla sassarfa ya fada wani lokon dake daura dasu.
Ko wanne sashe na jikinta rawa yake,tayi wata irin tsorata da bata taba yin irinta ba.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 51
Abune da bai taba faruwa da ita ba koda wasa,ta waiga gabas da yamma kudu da arewa,ba kowa a layin,babu gicci ko wulqawar kowa,ko cutas da ita zayayi zaiyi ne hankali kwance,abinda ya sake kada mata hankali kenan,ta soma yunqurin tattara dukkan qoqarinta wajen ganin tabar layin.
Taku uku tayi ya shawo kwana. Hannunsa riqe da jakartata da yanzu yanzu aka wafceta. Birki taja ta tsaya,gudun zuciyarta yana sake qaruwa kaman zuciyarta zata fito ta bakinta. Ta qura masa idanu tana kallonsa kaman yadda shima ita yake kallon. Guduwa takeson tayi amma ta kasa kaman an kafeta a wajen.
Duk taku daya da zaiyi yana sake ganin kamanni na jini da kuma yanayinta da SABREEN din. Yana mamakin yadda ta iya boye komai nata,yadda ta iya bad da bami,ta iya nutsewa da narkewa cikin sararin duniya ba tare da ka iya gano daga ina take fitowa ba ina kuma take komawa?.
"Karkiji tsoro......ni ba cutar dake zanyi ba.....jakarki na karbo miki,nazo wucewa naga abinda ya faru,karbi jakarki" Baya taja kadan,bata jin aminta dashi sam sam a zuciyarta. Wani irin raino da horo sabreen ta yiwa kowannensu na rashin yarda da baquwar FUSKA muddin sunanka NAMIJI.
"Da gaske nake miki.....ba cutar dake zanyi ba,idan kuma baki yarda ba ga jakarki nan" Ya fada yana ajiyeta a tsakaninsu sannna ya juya ya fara takawa yana barin wajen fuskarsa shimfide da murmushi,qasan zuciyarsa kuma fes cike da murnar samun CIKAKKIYAR NASARA da kuma tabbacin DAUKAN FASA mafi ciwo a gareta.
Sai data tabbatar ya bada tazarar da koda ya juyo zuwa gareta zaiyi wahala ya cimmata sannan ta taka ta isa ga jakar,ta tsugunna ta dauka,ba tare data damu da datti da qurar data debo daga qasa ba ta rataya tana maida idanunta kansa.
Tafiyarshi yakeyi baiko waiwayota ba,ta kalli jakar ta kuma kalleshi,sai ta buda bakinta a hankali tana furta
"Na gode". Cak ya tsaya tamkar dama yana dakon martaninta ne,sai ya waiwayo yana sake fadada fara'ar fuskarsa
"Nima na gode.....sunana....." Dakatawa yayi kadan saboda tuna wani abu da yayi
_"Tana da wayo,tana da hadari.....da alama kuma akwai abinda ta taka_ kalaman suka dawo masa kai fes
"Sunana BASSAM....kefa?" Ya furta yana murmushi tare da samun gamsuwar lallai sunan zaifi saurin isar da saqo a maimakon ainihin sunansa na NASEER. Bashi da buri baya kuma fatanbta fahimci komai har sai zuwa sanda komai din ya kammala......har sai zuwa sanda shi da kansa zai mata bayanin komai. A lokacin da yake buri da kwadayin jin sheshsheqar kukanta......a yanayin qunci baqinciki da kuma tarin damuwa da yake fatan ta hallakata......koda bata hallakata ba yana fatan tayi mata mummunar illar da koda gaba ba zata qara gigi kasada ko gangancin shiga shingen mutane irinsa ba.
"Kefa 'yammata?" Ya tambayeta cikin lanqwasa murya da tausasa harshe gami da sanya wani amo me sanya nutsuwa ga duk me saurare.
Lokaci daya ta danji ta samu nutsuwa kadan,sai ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ta bashi amsa
"Huda" Ta furta a nutse tana jin wani iri da kiranta da sunan 'YAMMATA da yayi,karo na farko cikin rayuwarta da wani ya taba kiranta da wannan sunan.
Murmushi ya sakar mata yana gyada kanshi gami da lumshe ido yakuma budesu a lokaci guda
"Nice name.....duk wanda ya baki wannan sunan ya iya zaben suna". Maganar tasa ta sanya fitar murmushin dole a saman fuskarta. Tadan murmusa kadan,abinda ya sake sanyashi ganin kamanninta muraran da sabreen. Wutar daukan fansanshi ta sake ruruwa cikin ransa.
Kai ta jinjina a nutse tana dan sadda kanta qasa kadan
"Autyna ce" Ta samu kanta da bashi amsa
"Antynkin nan tana ja da yawa.....ta iya zaben sunaye" Ta fada da ma'ana biyu,a zahirance kuma da harshen da ba kowane zai fahimci boyayyen sirrin dake qasan zuciya ba.
Dagowa tayi a karo na biyu ta sake kallonsa,sai taji wani dadi zuciyarta tana saki kadan. Duk wanda zaya so sabreen a wajensu basu da kamarshi......kaman yadda suke nisantar wanda zai kawo suka a kanta ko wanene.
"Nadan rakaki kadan ko?,ki fita daga layin nan,don har yanzu ban gamsu da sahihancinsa" Ya fadi yana duban gefe da gefansa bayan ya zube dukka hannayensa cikin aljihu.
Tayashi duban itama tayi gabanta yana dan faduwa,ta yaya zata iya jerawa dashi wai?. Amma ko kafin tace komai ya fara takowa zuwa inda take tsayen yana jifanta da murmushi,tadan ja baya kadan dole ta fara takawa ya rufa mata baya
"Kada ki damu,bawai zamu jera bane,ba wanda zaisan tare muke......kawai dai zanyi gadinki har ki aminta" Kalmar aminci daga bakinsa ta sanya taji ta sake,sai taci gaba da tafiya,shi kuma yana biye da ita da 'yar nisan tazara a tsakaninsu.
Duk wani taku nata guda daya yana lasafta yadda komai zai wakana......a yanzu bayan wutar daukan fansa dake ransa,wata wutar daban ta soma rura kanta da kanta a zuciyarsa.......bayajin koda ba komai tsakaninsa da sabreen zai iya qyale wannan danyar 'yar shilar ta wuceshi. Duk da bata qarasa 'yar uwarta ba a komai.......amma zata sama masa nutsuwa yayi yaqinin hakan ko yaya take kaman yadda ya dade yana tsara zai samu daga yayartata.
Bai tsaya ba har sai da qafafunta suka isa babban qofar gidan nasu,sai ya samu waje nesa kadan saboda gudun bacin rana da bacin aiki,ya tsaya kawai yana jifanta da wani mayataccen kallo tamkar mayunwacin zaki.
Har ta sanya qafafunta sai ta dakata ta waiwayo,suka hada idanu abinda ya bashi damat jifanta da wani shu'umin murmushi. Itama murmushin ne ya subuce daga bakinta tana jin cewa ya kyautata mata matuqa,abinda ba kasafai suke samunsa daga wajen al'ummar da suke kewaye dasu ba,don haka wannan din ya qawatar da ita. Bakinta ta bude a hankali ta furta kalmar
"Na gode sosai". Duk da tasan ba lallai ya iyajinta ba,amma zai karanci bakinta. Ya kuma karanta din,sai ya daga mata kai don haka ta juya tana shigewa cikin gidan.
Haka kawai murmushi ke fita a fuskarta tana tuna yadda komai ya kasance. Badan shi ba Allah ne kadai yasan abinda zai faru da ita a wannan qonannen layin da babu kowa. Ba yadda kuma zatayi,nan dinne dai hanyar wucewarsu tilo guda daya,inda da wata hanyar tabbas ba abinda zai sanyata ta sake bi ta nan wajen.
"Ke dawa kike murmushi ke daya?" Sabreen dake tsaye gaban fridge dinsu tana duba adadin pure water da lemon daya rage musu a ciki ta fada hannunta dafe da murfin fridge din. Cikin sauri ta gyara yanayin fuskarta tana qoqarin adana takalmanta data shigo dasu
"Ba kowa adda...." Idanunta ta zube mata sosai tana son karanto wani abu amma bata samu nasarar gano komai ba,saidai duk da hakan haka kawai takejin bata nutsu da irin amsar huda din ba. Emotions ke sauya yanayin fuskar mutum,walau na farinciki ko baqinciki,dole idan ya nuna saman fuska to akwai wani labarin a qasan zuciya.
Sakin fridge din tayi bayan ta rufeshi tana takowa tsakiyar dakin
"Wacce irin tafiya kukayi ne yau ke dasu nadra?,kinsan dai banason kuna raba tafiya ko?" Ta fadi tana zama idanunta still akan fuskar huda din.
Fuska ta bata ba kaman dazu ba tana duban sabreen
"Wallahi dama nace zamu hadu dasu.....kawai adda ina fitowa na samu wai sun wuce gida?,yau bansan me yasa aka rarraba mana lokacin tashi ba" Ta qarasa maganar fuskarta a bace da gaske. Idanunta tadan dauke daga kanta tana sauke numfashi
"Banason irin wannan tafiyar,kome raba lokacin su dinga jiranki" Cikin ranta tana jin abun kwata kwata baiyi mata ba.
Qaramar dariya ya sakarwa kansa bayan ta shige gidan. Fara takawa yayi hankali kwance yana barin layin. Tabbas shima zai buga nasa wasan yadda ya dace,zaiyi wasa da rayuwarta da kuma hankalinta yadda ya kamata......zai gigita mata rayuwa ya dagula dukkan wani lissafi nata......zai guntule dukkan wani farinciki nata kaman yadda ta gurgunta ta kuma dagula rayuwa da nutsuwarsa. Yanaji a ransa abun zai bashi nishadi qwarai,zai kuma qarasa goge baqinciki qunci da takaicin data qunsa masa.
********Cikin nutsuwar nan tasa yake saukowa daga matakalar jirgin riqe da kyawawan briefcase guda biyu. Tasa data Alhaji hamza kibiya.
Biye yake da dattijon,yana aje tasa qafar a duk muhallin da ya cire. Kamilallen dattijon da adadin furfurar dake baibaye a fuskarsa da kuma gashin kansa suka sake tabbatar da dacewar sunan dashi. Cikin kamala yake komai nashi,sanye da shadda dinkin babbar riga da maroon hula dara sak ainihin shigar marigayi malam aminu kano.
Muhammad fu'ad jadda,mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources wanda ke biye dashi a baya. Sanye cikin dinkin kaftan da yayi matuqar qara masa kwarjini da wani irin haiba me cika idanun me kallonsa. Idan ka kallesu shida Alhaji hamza kibiya din zakayi tsammanin shine ainihin mahaifi gareshi saboda yadda tsahonsu yake kusan daya da kuma murjewar jikin. Bayansa kuma sadiq ne janye da luggage dinsu. Shikam t.shirt ne jikinsa da trouser,ya lullube qafafunsa da lafiyayyen boots ba kaman fu'ad ba dake sanye da wani lafiyayyen halfcover ba dan qasar itali da aka samar dashi da dinkin hannu(sau da dama mu a nigeri muna raina takalman hannu,amma a qasashen qetare babu takalma masu daraja da tsada irin handmade shoes,wani ma kana ce masa handmade ne ka bata show din😂,nija my nation 🫡😂).
Tare suka jero kafada da kafada shi da Alhaji hamza din zuwa muhallin da farouq yafi tsaiwa a duk sanda yazo daukosu daga tafiya irin wannan. Ko a yanzun da suke nufar mota don isa gida ma duk hirar akan kasuwanci ce. Abun yana bawa Alhaji hamza mamaki. Duk qwarewarsa da qaunarsa da kasuwanci fu'ad din ya shallakeshi. Kowacce rana kowacce safiya,kowanne dare da wuni plan din rayuwarsa da komai nasa yana kan kasuwanci. Me za'a bunqasa?,me za'a qirqira?,me kuma za'a gyara?,ina ne nasara take a bunqasata?,ta ina faduwa take ayi hanzarin bawa gurin kulawa da kariya?.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 52
Yana jingine da motar yana kallonsu,idanunsa fes a kansu. Yana masa dadi yana kuma sanyawa ya manta cewa fu'ad ba dan uwansa bane na jini a duk sanda ya ganshi kamar haka da Alhaji hamza din. Yana alfahari yana kuma qara ninka alfaharinsa akan muhammad fu'ad din. Shi kansa ya sallama......jajirtaccen mutum ne da jajircewa take a cikin jinin jikinsa.
Ya maida idanu a hankali akan yanayin takunsa. Tafiya ce me cike da ginshira gami da cikakken kuzari da karsashin da zai bayyana maka adadin cikakkiyar lafiyar da yake da ita.
Daga abban har fu'ad din hankalinsu baya wajen,yana duba wani qaramin takardu da suke dauke da bayani da taswirar burinsa na gaba wato ginin katafaren kamfanin samar da kayan ado na sarqoqin mata da zai dinga amfani da wani sashe na ma'adanan da yake haqowa.
Tun daga fitowarsu gaba daya security guards dinsa da ya bari a gida kowanne ya koma kan aikinsa. Dukan inda ya ajiye qafarsa nan suke maida tasu.
Murmushi ya subucewa farouq,ya dawo kenan,kuma yanzun za'a fara. Bayaso abba ne ya tilastashi daukan guardsmen duba da yanayin qarancin tsaron da ake fama dashi. Uwa uba ma zaiyi wahala a nasibin rayuwa daya samu......da irin mu'amalarsa ace ya zauna haka gayansa yana yawo babu masu tsaron lafiya tattare dashi.
Wani lokacin idan yaso yana kubce musu ne yayi fitarsa shi kadai a mota yasha iska ya dawo. Ba kasafai ya fiya son fita qasashen waje sai idan harka haka ta taso takai kayan da sunyi yawan yayi wakilci......amma yanzun ya koyi fita din lokaci bayan lokaci haka siddan ma don ya samu ya sarara yayi rayuwarsa shi kadai. Mutum ne da bayason matsi,bayason takura,zai iya rayuwa me dogon zango shi kadai a wani muhalli na daban,shi yasa ko a yanzun a sassansu gini ne me zaman kansa dake dauke da bedroom and parlor da toilets kowa shi kadai. Saddiq da musaddiq sun hade dakunansu saboda kowa nashi apartment din ya masa girma. Amma oga fu'ad shi daya ne a nashi,hakama farouq,sai shi farouq din da lokaci bayan lokaci yakan dawo sassan fu'ad din yayi kwanaki yana kwana a nan sannan ya koma wajensa.
Kullum ya hangi fu'ad din daga nesa ba abinda yake tunawa sai wannan matashin dan bautar qasar,mara tsoro kuma mara shakka,cikakken jarumin daya shiga yankin daba nasa ba,yayi abinda koda haifaffen yankinne ya aikata bazai sha ba.....ya kubuta da tarin nasara. Farouq yadan sake murmusawa yana tuna yadda yaci wahala bayan uban gudun da sukayi,ya tuna yadda fu'ad din yayi jinyarsa tamkar ba dashi akayi gudun ba
"Ba abinda nakeji man.....ni dakai ba daya bane,sau nawa ana gaya maka ka dinga gym saboda yuwuwar samuwar irin wadannan lokutan na qwatar kai?,sai kuyita zama kaman mata,baku da wani banbanci dasu?" Ya tambayi farouq din a wancan lokaci yana dage masa dukka girarsa bayan ya bashi maganin ciwon jiki yasha.
"Yanzu wannan pain killer din da kake fana dashi......da warm water da fenugreek kake sha da yafi maka amfani". Harara ya balla ma fu'ad din yana dubansa
"Ba zaka qarasa kasheni ba da wadannan home remedies din naka ba" Sai ya juya ma fu'ad din baya yana sauke numfashin wahala yabar fu'ad din da sakin siririn murmushin nan nasa me tsada. Miqewa yayi yana dauke cup din
"Idan home remedies bai kasheka ba......son jiki da rashin exercise....aci a kwanta duka ya kasheka......naga wanda zai aureka da qaton tumbi" Ya qarasa maganar yana jefa kwalin lemo a dutsbin. Duk da farouq na cikin yanayi a sannan saida murmushi ya qwace masa.....fu'ad mahadin rayuwarsa ne kuma mahadin zuciyarsa ne kaman yadda ya tabbatar a wajen fu'ad dinma haka yake.
Kafadarsa y
Ta dama yaji an daka
"Murmushin me kake kai kuma?" Sassanyar muryar nan tasa sake cakude da wani deepness ta shiga kunnen farouq. Kallonsa ya dora saman fuskar fu'ad din yana jin yawan kewarsa da yayi
"Ina nan ina kallon gujajjen dan bautar qasar nan da bai kammala service dinsa ba sai a garin kano". Murmurshin nan da shi daya ke iya fidda masa shi daga kan fuska ya saki kadan yana sake kaiwa kafadarsa duka. Dariya kadan ya saki shima farouq din
"Ina hasaso yadda zasu cinye namanka danye duk sanda suka fahimci daga ma'adanin qasarsu ne aka samar da attajirin nan mamallakin jadda diamondchore company........" Murmurshin ya sake sanyashi saki,sai ya saka tafin hannunsa saman wuyansa yana dan karyar da wuyan kadan
"Naman muhammad jikan jadda yafi qarfin cinsu umaru...." Ya bashi amsa da anihin sunansa,abinda ya sanya farouq din sakin dariya sosai. Kafadar fu'ad din yadan bubbuga
"Na sani.....nafi kowa sanin wannan dan uwan nawa wanne iri ne......tun daga ranar da mukayi temple run dinnan na sake yadda da hakan..."
"A nan zaku gama hirar ne?,idan ku baku gaji ba ku tallafa ku kaini naga aminatu na" Muryar abba ta sauka kunnuwansu.
Fu'ad ne ya waiwaya don farouq yana fuskantar abban ne. Dan murmusawa kadan fu'ad yayi ya matsa yana yunqurin budewa abban qofa,amma farouq ya rigashi
"Dukkanku kai da abban yau qarqashin hidimata kuke....baqinmu ne ku daga South Korea".
"Sannu sarkin noma.....godiya muke" Shima abban ya fada cikin barkwanci bayan ya shiga motar.
Dashi da farouq din baya suka shiga bayan ya bawa shugaban security dinsa umarnin su bisu a baya.
Kusan duka a hanya ma dai tattaunawar ta kasuwanci ce. Farouq din yana bawa abban labarin yadda abubuwa suka kasance bayan tafiyarsu
"Amma tabbas sai ka sake sanya idanu akan mika'il.....ina suspecting wani abu tattare dashi,duk da bana ce gashi ba,amma nasan kai din zaka fini fahimtar komai" Farouq din ya furta.
Idonsa fu'ad ya dauke daga kan wayar hannunsa,wanda saqon mika'il dinne ya shigo,mutum na farko daya fara masa saqon barka da dawowa kafin kowa. Bai cewa farouq komai ba,amma kuma maganar tasa ta samu gurbi sosai a zuciyarsa ta zauna,sai ya gyada kansa a hankali yana sake maida dubansa ga wayar.
**"Anni an gama komai" Ta furta sanda take saukowa daga saman tsararren dining area din daya dauki kyakkyawan family dining table na wani mulmulallen tangaran kai kace an samar dashi ne daga burbushin diamond ko gold da kamfanin jadda ke wankewa su fiddashi. Fara ce tas,mai matsakaicin tsaho,saidai bata da qiba ko qanqani. Yanayin sumar gaban kanta kawai zai fada maka akwai suma me yawa a saman kanta wadda bata da duhu ta danyi brown kadan bame yawa ba. Yanayin yadda ta datsi daurin dankwalinta daga tsakiyar kanta shi zai baka daman ganin hakan sosai. Straight gown ce a jikinta ta atamfa me igiyoyi hagu da dama wadda ta daureta daga gefen qungunta guda daya.
"Ma sha Allah.....sannunku da qoqari....sun wuce ne?" Anni data daga kanta daga tab din hannunta da take duba wasu addu'o'i ta fada.
Fuska tadan yamutsa kadan tana zama kujerar gefan annin gami da ajiye qaramin towel din hannunta a side table sannan ta dauki wayarta dake ajiye akai tana qoqarin budeta
"Kowa ya wuce......yanxun abba da hamma kawai muke jira" Ta qarasa maganar murmurshi yana subuce mata.
"Umhummm......wato shi saddiq shine marainin wayonki da baki ta tasa ko?" Anni ta fada tana maida idanunta ga addu'o'inta . Fuska ta yamutsa,duk da bata kalli annin ba amma ta amsa
"Bar wannan anni,wa yake ta tasa,ba abinda ya iya sai takurawa mutum ba dalili......hamma takurawarsa me dalili ne idan bakayi abinda yace ba ko baka kiyaye dokarsa ba......amma yaa saddiq.....hmmmm....ko wayar nan yanzun ya shigo yana ina dannawa sai yayi challenging dina" Ta qarasa maganar tana zamewa ta kashingida saman kujerar tana maida hannunta kan shafinta na X.
Ita da annin kowa ci gaba yayi da uzurin gabansa,wannan ya bawa falon daman daukan shuru na wani lokaci kafin ta daga kanta. Haka kawai ta qarewa anni kallo sai ta saki dariya
"Anni.....kinsan tsadar kayannan?" Ta fada tana kallon kwantaccen lace din jikin annin dake wani yauqi da santsi duk kuwa da cotton ne. Peach color da ratsin green,bashi da nauyi ko kadan
"Saikin fada 'yar kasuwa......" Ta amsa mata ba tare data dubeta ba
"Anni Allah hamma yana shagwabaki......ki zauna da kaya me tsada haka a gida duk dogayen rigunanki?....amma dai....to,hala abba aka yiwa kwalliya?" Ta fada qasa qasa tana qunshe bakinta da hannu. Kadan ta dubeta ta harareta
"Akwai kayan da sukayi tsadar da zan kasa yiwa abban kwalliya dasu?" Kai ta girgiza tana qoqarin maida kanta ga wayarta tana qoqarin boye dariyarta
"Babu anni.....anni ta abbanmu".
"Amna.... Qoqarin maidani kakarki kike ko?"
"Aah anni wallahi" Ta fada da sauri tana duban anni still tana son shanye dariyarta
"Kici gaba.....inajin zan dauki shawarar farouqu ne,zaki komawa nanna ne kiyi zamanki a can". Kyabe fuska tayi da kyau tana aje wayarta gefe kaman zata saki kuka
"Dama haka yaa farouq din yace?,duk haqurin zama cikin mazan da nakeyi ban da sister?....."
"Oho koma.meye gwara ki koma can,tunda kinga can dinma akwai mata 'yan uwanki sai kinfi jin dadi". Sosai ta sake kwabe fuska tana duban anni
"Da gaske anni zaki iya bayar dani?" Daga kai tayi ta dubeta
"Ba mace bace ke?,wataran ba aure zakiyi ba?" Ta tambayeta,ai kuwa saira soma matsa hawaye tana juyawa annin baya
"Ai dama na sani......gidan nan babu wanda yake sona sai hamma da abba na......shi dama yaa farouq kaman ya bayar dani kyauta yakeji.....ni bazanyi aure ba.....dake zan yita zama". Yadda tayi maganar zata yita zaman da ita sai ya bawa anni dariya amma ta dake
"Sai kiyi kuma" Tace tana ci gaba da scrolling sama tana duba adduo'inta.
"Kinga.....ki daina biyewa ta BB farouq.......indai ina nan ba wanda zai matsa miki.......i swear" Muryar musaddiq ta biyo bayan sallamarshi. Tuni ta miqe ta zauna sosai tana qoqarin goge hawayenta.
"Kaima kana biye musu yaa musaddiq wani lokacin.....amma dai ka fisu" Ta fada tana daidaita zamanta saman kujerar.
Qaramar dariya ta qwacewa anni tana qoqarin ajiye tab dinta a gefe
"Uhumnnn..... Ai dama ba kasafai akewa amna abun arziqi ba.....wanda ke mata abun arziqi kai tsaye a gidannan Muhammadu ne......har kun dawo?" Ta tambayeshi tana duban musaddiq dake dariya qasa qasa.
"Eh anni.....su abban basu iso ba?"
"Sun sauka amma basu qaraso gidan nan ba.....amma na tabbata suna dab da isowa don tun dazu suka tafi daukosu". Ta amsa masa tana miqa hannu ta karbi purse din nata da yake miqa mata.
Tana yunqurin budewa su kuma suna magana tsakaninsu shi da amna. Ta zuge jakar cikin rashin tabbas da yaqini,ta bude ne kawai don taga meye yayi saura a cik,me ta samu?,amma ga mamakinta sai ta samu komai a muhallinsa ba tare da an canzawa komai waje ba bare a cire wani abu,sai wayarta data nuna low battery da alama ba'abi ta kanta bama bare a sakata a charge.
"Ikon Allah" Ta fada,abinda yaja hankalin amna da musaddiq kanta
"Ba abinda aka rasa a ciki musaddiq.....ba abinda ta taba kota dauka" Ta fada da mamaki idanunta cikin jakar
"Nima dana bude nayi mamaki,amma nace bari na kawo miki ki duba komai bansan ko akwai wani abun daban ba"
"Aiko yadda na zuba kudin a jere ba'a canza tsarinsu ba" Ta fada tana sake fiddosu
"Amma dai ka yiwa yarinyar godiya ka karbamin number wayarta ko?,ko mamarta na sake yiwa godiya?"
"She's not natural fa anni" Ya fada a taqaice
"Kamar yaya?" Ta tambaya cikin rashin fahimta.
"To nidai anni ko qyallinta ban gani ba,a bakin wani waje wani ya tareni ya bani,baicemin komai ba ya juya,nima haka na juya da kan motata na dawo gida"
"Ikon Allah......gashi bata bari ko sau daya na mata godiyar alkhairin data yimin ba.....na kasa manta damuwa da kulawar data nunamin" Annin ta fadi tana juya abun a ranta.
Bai samu ce mata komai ba saboda qarar bude gate da shigowar motocin da suke da tabbacin baqinsu sun iso
"Alhamdulillah" Anni ta fada tana murmurshi gami da ajiye wayar da jakar a gefe.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 53
Dukkansu da sallaman a bakunnasu suka shigo. Suka amsa musu suna miqewa tsaye tare da dakon qarasowarsu cikin falon,saidai amna ta kasa jurewa. Da sauri ta taka zuwa bakin qofa ta riqe abbannata da kyau tana dariya idanunta saman fuskar fu'ad
"Abba sannu da zuwa....hamma....hamma sannu da zuwa" Ta furta matsanancin murmushi yana subuce mata
"Sannu 'yar abba qanwar hamma.....hamman dai aka matso a tarba aka fake da abba". Abban ya fada yana lakuce mata kumatu. Dariya suka saki fu'ad yana tayasu da murmushinsa
"Amnee......barkammu" Ya amsa mata cikin kulawa. Sakin abba tayi ta matsa dab da fu'ad din tana karbar briefcase dinsa
"Su amna an iya munahirci" Muryar sadiq ta shiga kunnenta,sadiq din dake tsaye ta bayansu abban. Gotasu tayi kadan tana leqensa,sai ta bata fuska
"Duk abinka bazanyi welcoming naka ba.....abba me yasa baku samu wata bolar South Korea kun yar dashi kun gudo ba?" Ta qarasa tambayar tana kallon abba a shagwabe. Ba wanda maganar bata bawa dariya ba a cikinsu
"Idan muka yar dashi ke zaki fara qorafin muje mu dauko miki shi ai"
"Allah bazan nemi wannan ba....."
"......me qarya?" Saddiq ya datsi numfashinta yana fadi idanunsa a waje
"Dan aljanna" Ta fadi tana juya idanunta abinda zai sake tabbatar maka da sauran quruciya a tare da ita,hakanan kuma tana fama da sakalcin auta da gasken gaske.
Kasa jiran isowar abban tayi,sai ta taka ta ruskeshi a tsakiyar falon. Ta rusuna tana masa sannu da zuwa gami da gaidashi duka tare da qoqarin amsar qananun tarkacen dake hannunsa. Cikin nashi tsananin kulawar da kallon kewa yake amsa mata,fuskarsa ta wadatu sosai da fara'a yana tambayar lafiyarta dama ta jama'ar gidan gaba daya.
Hankalinsa yana kansu,qauna da kulawar dake tsakanin anni da abba sune abu guda daya tak da suka rage wadanda suke bashi hope din wataran qila zai iya aure. Soyayyar da sukema juna wani irin dasashen abu ne da har yanzu yake tasiri a tsakaninsu,babu alamun gushewa sam sam. Yanayin rayuwarsun yana burgeshi,wata irin mu'amala annin kewa abba,irin mu'amalar da bai taba ganinta ba tsakanin MAAMAHnsa da ABBEY dinsa ba. Mu'amalar da bai taba zaton akwaita tsakanin miji da mata ba sai a wajen annin.
Gabanta ya qarasa shima kaman ko yaushe,cike da ban girman nan da yake jinsa har cikin ruhinsa ya tsugunna yana gaidata. Bata iya tsaiwa saman kanshi ba saboda girman shima da take bashi sakamakon sunan MUHAMMADU da yake dashi......da wata ajiyayyar kima da martaba da take ganinsa dashi saboda dattakon halinsa data sani tun bai cika shekara sha takwas bama a duniya.......uwa uba yadda yake tattalin farincikinta kadai ya sanya kowanne lokaci takejin tamkar jikinta ya tsaga ya fito.
"Lafiya alhamdulillah me babban suna.....jiki na warware tun tuni......dama ta jima bata tashi ba,akasi kawai aka samu a ranar,nafi tunanin kuma matar da mukayi salla tare ne turarenta yayimin qarfi da yawa".
Dan qwarya qwaryar zama sukayi cikin falon na duba lafiyar juna,qananun zolaya tsakanin amna farouq da musaddiq abban yana shiga yana raba gardama kafin daga bisani anni tayi umarni
"Abinci ya zama ready.....zaku shiga ku watsa ruwa tukunna ko?" Ta fada tana duban abba me gayya me aiki
"Hakan yana da kyau ko me babban suna?" Ya maida tambayar ga fu'ad. Murmushi kadan ya saki,suna girmama ra'ayinsa qwarai,sunan da yake dauke dashi ya bashi wannan girman a iyalin da suka san girma da martabar sunan. Wani abu da sam sam bai gani ba ga maamah,tana iya kiransa a lokacin quruciya da sunan ta kuma zabga masa zagi fada da sauransu
"To abba" Ya amsawa Alhaji hamza yana miqewa. Farouq ne ya miqe ya dauki luggage din fu'ad din yana nufar qofa
"Muje na taka maka badon halinka ba......don wallahi ka shiga uku duk sanda mukayi aure muka barka kai kadai a gidan nan". Yayi maganar qasa qasa yadda su abba ba zasuji ba.
Harara fu'ad ya zabga masa yana jan qaramin tsaki
"Sannu tattabara sarkin aure?,yanzun ma idan kaga dama ka koma mana ka gani?......ni gwara fa ku qara gaba ku barni daga ni sai anni ko mayi kumari". Dariya ya fashe da ita harda buga qafa kadan
"Kayi asara wallahi.....kai ta qara qiba ma kake,kaci gaba da gandamewa a gaban annin?,idan bakayi wasa ba gaba gaba sadakarka za'a bayar Allah......"
"Munyi asara dai ni dakai mayen aure......idan kun tashi kuyi shelata a masallacin juma'a".
"Basai munkai ga nan ba......owner na diamondchore resources company guda.......ko a sirrance akayi shelarsa mugun ciniki zamuyi Allah,a zaba maka guda hudu qwarara......matsalar kawai har yanzun ni kaina bansan color na macen da kakeso ba.....". Shammatar farouq din yayi yakai masa wani wawan duka sai daya qame,don maganar ta fara isarsa,yasan kuma farouq baisan bari ba,baisan ya isa ba.
"Kaci bashi......sai na dauki fansa.....ka qarasa cikin da kanka na fasa rakiyar" Ya fada yana jingine masa luggage dinsa daidai qofofin sassansu
"Tafi nono fari" Fu'ad din ya fada yana zura key ma qofan sassansa yana budewa,saidai fuskarsa kwance take da murmushi yana juya halin farouq din. Shi daya farouq din yakewa haka.....kamar yadda shima farouq din kawai ke akwai 'yar hakan a tsakaninsu.
"Alhamdulillah" Ya furta a sarari murya can qasan bayan ya isa ainihin bedroom dinsa,yana jin ma'anar godiyar daga qasan zuciyarsa. Tarin godiya ce fal zuciyarsa game da ubangijinsa,godiyar da har wani lokacin ya dinga jin baisan ta yadda zaiyiti ba takai gurbin da akeso. Ubagijinsa ya gama masa komai.....ya kyautata rayuwarsa fiye da yadda yake tsammani.
Komai na sashen nasa a killace a kuma tsaftace akan tsari fiye ma da yadda yakeso. Wani irin qamshi ke tashi,abinda ya sanyashi sakin wata nannauyar ajiyar zuciya data sanya yaji wani nauyi ya ragu sosai daga saman zuciyarsa. Yana yiwa qamshi wani jarababben so,a duniya qamshin yana daya daga cikin jerin abubuwan da yafi qauna. Qamshi yana sanyashi maqalewa waje,kaman yadda akasinsa ke sanyashi rabuwa da waje.
Yana iya baiwa farouq dinsa komai amma indai ta fannin abinda ya shafi turare ne to zaka iya jin musunsa dashi. Bai yarda ba a taba masa turaruka,gwara ka zaba ko na nawa ne ya siya ya baka kyauta.
Kayan jikinsa ya dinga zarewa har sai daya rage saura fara qal din vest din jikinsa da gajeran wandon da bai qarasa gwiwarsa ba. Muradadde kuma ginannen jikinsan nan dake dauke da wasu lafiyayyun muscles dake alamta ainihin qarfi na siffa ta zahiri da badini ya bayyana,lullube da wadatattun gargasa ta ko ina. Wankan yakeson yayi amma shigowar kira ya hana masa hakan,tilas ya samu saman sofa bed ya zauna yana amsa kiran.
Amsa kiraye kirayen ya daukeshi lokuta masu tsahon da har musaddiq ya dinga zuwa dubashi zasuci abinci. Daga qarshe ya basu excuse akan suci din idan ya kammala zai fito.
Fitowar da bai samu daman yi ba kenan,don sanda ya fito a wankan gaba daya kasala da tsohuwar gajiya ce ta saukar masa,dole ya haye gadonsa bayan ya maida da dakin dark ta sakin dukka manya manyan curtains dinsa,ya kuma kashe kowacce fitila da zata iya bashi haske don baya son bacci a duhu sam sam. Koda baccin yakeyi kana kunnata ka tasheshi. Sunsha fafatawa da farouq akan hakan,don shi mutum ne da kwana cikin haske bai dameshi ba. Wannan dalilin yasa ko a yanzun yafi sha'awar kowa ya zauna a sassansa,ba kasafai ya fiya son takurawa mutum da salon tsarin rayuwarsa ba.
*****Su biyun dukansu suna zaune ne saman buzu na fatar dabbar da basusan wacce iri bace. Kaman yadda dukkaninsu jikinsu ke sanye da sutura ta alfarmar da zaka fahimci rayuwa ta basu sukuni yadda ya dace,saidai tasu salon miqa godiya wa mahaliccinsu da suka munana hanyarta.
Daga atamfar jikin hajja har lace din da maahma ke sanye dashi wanda ya darawa atamfar hajjan tsada isashen jari ne ga mutane masu yawan gaske. Kaman yadda jakar maahma din da takalman data sanyawa qafafunta suke wani jarin me zaman kansa ga wasu mutanen. Takalmin da fu'ad din yayi mata order dinsa da kanshi tun daga qasar Italy.
Kusan yadda ta bawa mutumin dan duqurqushi me zubin wada hankalinta hajja bata bashi nata haka ba.
Daya daga cikin qoqunan gabansa da suke kife ya daga,qoqon da babu komai amma saiga haske ya cikashi. Tafukan hannayensa ya saka yana rufe qwayar da hannunsa nasa. Idanunsa ya runtse,wasu irin maganganu ya dinga furtawa da ba'a gane abinda yake fadi,tun yana fada a hankali a hankali har ya fara furtawa da sauri da sauri da kuma qarfi har muryarsa tana amsa kuwwa. A hankali jikinsa ya fara wani irin kakkarwa tamkar wanda aka jonawa shocking. Da wani irin sauri yan fusge hannayensa daga saman qwaryar yana yarfar dasu kamar wanda wuta ta taba,sai kuma ya sake maidasun yana canza salon yaron da yakeji ba irin na dazu ba.
Ya kusa minti biyu a haka,wata irin zufa da basusan daga ina take ba ta gama jiqeshi sharkaf.....a hankali a hankali ya soma sassauta muryarsa sannan ya fara daidaita yanayinsa kafin ya bude idanunsa da suka ninka ja akan asalin jan da suke dashi.
"Matso!" Yace da maamah a tsawace. Tsoro ba kalma bace da ta santa ba kaf ray uwarta......qafafunta sun taka gurare da dama amma a yanzun saita samu kanta cikin shakka da d'ar d'ar har ta matso zuwa inda yake mata nuni
"Ba shine wannan ba?" Ya fada da qarfi yana nuna mata qoqon.
Fu'ad ne kwance saman gadonshi yana baccinsa hankali kwance kaman yadda ya kwanta a ainihin dakinsa dake gidan Alhaji hamza kibiya. Mamaki ya qarasa cikata,ba shakka fu'ad ne,kuma dakin ya mata kama da dakunan gidan Alhaji hamza,sun dawo kenan kaman yadda yake shaida mata dazu da sassafe kan suna hanya?.
Daga ita har bokan ba wanda ya samu cewa wani abu dif hoton dake cikin qwayar ya bace kaman an dakeshi harda tartsatsin wata wuta.
"Kin gani ko?,ba mutumin da muka sha wahalar kawoshi zuwa garemu saishi......baya ga haka kinga yadda surarsa ta dauke da gaggawa......abinda ke bamu tabbacin aikinsa yasha banban da dukka ragowar aiki da muka taba yi a baya......akwai tashin hankali......akwai wahala.......akwai kuma qalubale!!!" Ya furta da kakkausar muryarsa mara dadin amo da sauti bare sha'awar saurare.
Dukkan kayan aikin nasa ya tattara ya zuba cikin qwarya daya daga cikin qorai biyu dake gabansa,take suka bace bat tamkar ba'a taba halittarsu ba a wajen.
Jajayen idanunsa da babu rahama,musulunci ko imani a ciki ya daga ya kalli maamah dake dubansa babu ko qiftawa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 54
Idanu yadan zuba mata na wasu mintuna da har sai data dan sha jinin jikinta. Sai kuma ya saki wani busashen murmushi da yafi kama da kukan jaki yana kallonta
"Ba shakka kin haifi jarumi......kin haifi yaron da taurarinsa suke da tsananin hasken da ba kasafai ake samun galaba ayi kutse a cikinsu ba ko asha kansu.......yaronki yana tattare da abubuwan al'ajabi da baiwarwarki masu yawan gaske wadanda ko ke uwar da kika haifesa bakisan yana dasu ba......cikin mutane dubu guda daya ake iya samu irinsa......". Kai kawai take jinjinawa tana sauraronsa. Tun sanda ta haifi fu'ad din tasan daban yake da sauran yara,to amma a yanzun kalamansa daga mata hankali sukeyi,kamar sunason shinshina mata rashin nasararta ne......kamar suna shinshina mata rashin yiwuwar aikinta?.
Maganarsa ta gaba ta bata amsa ta kuma yanke mata dukkan zatonta
"Aiki a kansa ba qaramin abu bane me girma......akwai tsari a jikinsa......yana da addu'a sosai tare da kare kowanne abu da musulunci yayi umarni akai.....baya shan giya.....baya zina.......baya kallace kallacen abubuwan haramun......hasalima azumin da addininku yace a dinga yi litinin da alhamis baya wuceshi.....abinda zai bada mamaki banda wannan uwar goyon nasa da uban goyonsa ba wanda yasan yanayin wannan azumin koda farouq makusancinsa......."
"Kana nufin yanzu mallakar da nakeso ayi masa.....da shiga tsakaninsa da iyayen goyonsa bazai yiwu ba kenan?" Ta dawo dashi zuwa ga ainihin amsar da takeso taji.
"Zaki iya samun biyan buqata.....zaki kuma iya samun faduwa......biyan buqatarki ya ta'allaqa da adadin sadaukarwar da zakiyi da kudaden da zaki ajiyewa shaqiqanmu don suyi miki yadda ya dace......amma fa....." Ya fada yana daga yatsa
"Tabashi abune da zai iya zuwa da hadari......mafi qarancin sakamako shine a gaza yin nasara a kansa......muddin rashin nasarar ta zarta haka kuwa.....dani da dukkan wani shaqiqi da mukayi aiki dashi zamu iya samun nakasa,harda shudewa daga rayuwa ma idan ta dauro,saboda haka......aikinki aikine me tsadar gaske " Yayi maganar yanayin muryarsa daga qarshe yana canzawa alamu dake nuna saukar mutanen boyen da yake aiki tare dasu a kansa.
Tsoro yadan shigeta kadan amma ta dake
"Kamar nawa zai kai?" Ta fada a dokance
"Kalli nan!" Taji an furta daga bakin mutumin amma da mabanbantan muryoyi marasa dadi da batasan mutum nawa bane suka hadu suke maganar.
Waiwayawa tayi tana duban inda ya daka,saiga lambobi a jere wanda data dubesu da kyau suka bayyana kansu a matsayin million goma.
Sosai adadin ya daketa,duk da tasan a qa'ida tana cikin arziqin data bawa wannan adadin baya amma kuma batakai ga samunsu ba zuwa yanzu. Ta waiwaya ta kalli hajja dake zaune tana kallon komai,don dokarsa shine me matsala dashi yake magana. Da idani ta mata tuni da tsarinsa,baya yanka kudi a nemi ragi.....daya daga cikin kusakuren da zaka iyayi wanda zai tunzurashi kenan.
Kamar wadda wuyanta ya qage ta maido dubanta gurin,saidai zuwa sannan lambobin da hasken da suka nuna mata yawan abinda zata biya din ya shafe daga wajen ba komai. Ta maida kallonta ga duqurqushin bokan da kamanninsa suka juye,saita gyada kanta
"Na karba na aminta"
"Karki qara minti daya a wajen nan......kizo da sadakin aikinki kuma nan da kwanaki uku kacal" Daga haka ya bace shi da dukkan sauran tarkacen dake wajen,sai gurin ya rage daga ita sai hajja din. Zumbur suka miqe kaman yadda ya umarta,suna riqe da hannun juna suka fara fitowa daga sarqaqiyar har suka cimma inda suka faka motarsu.
Sau biyu hajja tana juyawa tana kallon maamah wadda ta kafe kwaltar da driver ke zabga gudu akai. Tunda suka fito daga wajen bata ce komai ba,magana bata hadasu da kowa ba. Tun a dazun ta fahimci tayi nisa ne qwarai a tunani,kaman ta qyaleta amma sai ta kirayeta don tanaso taji ta bakinta
"Banji kince komai ba tunda muka fito?" Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke sannan ta dora idanunta akan na hajja din
"Daga yanayin ayyukansa,da kuma bayanansa kawai na gamsu cewa aikinsa me zafi ne......abinda kawai ya tsayemin a rai yanzu shine ta yadda wadannan kudaden zasu samu" Tayi maganar alamunta suna nuna lallai lallai a matse take da buqatar mafita
"Danki ne,dole ki bashi umarni yabi don babu wata uwa sama dake......idanma hakan bai yiwu ba,cikin kadarorinki ki saida wani abu.......ko kice masa wasu zaa yiwa wani abu da kudin da zarar yasa anyi abun ki saida abun kiyi zarafin gabanki". Ajiyar zuciya ta sauke ranta yana mugun baci
"Yanzu har takai idan ina da buqatar abu a wajen dana saidai nayi qarya ko na biyo ta wata hanyar?" Ta yiwa hajja tambayar.
"Biyan buqata ai yafi dogon buri,kome ya faru.....kuma kome kika saida,wuyarta aiki yayi yadda akeso......sai kin maida ninkin baninkin da bakisan adadinsa ba......sai kin karba kin gaji......saikin tara fiye da yadda kike buri......saikin zame musu tamkar abun bautarsu wajen yi miki biyayya.....a yanzun da zan kira auwal dake wata qasar,nace masa ya dawo nigeria yau yau inason ganinsa.......na rantse miki da Allah a qasar nan zai kwana,koda babu jirgi bazai kwana a gida ba saidai a airport.......saidai idan nice nace masa ya koma gida ya kwanta ya taso gobe......koda ya koma bashi da cikakken nutsuwa har sai gari ya waye ya kawo kansa gareni......bari yau zan nuna miki qarfin ikona ki gani da kanki" Ta fada tana fiddo wayarta daga jakarta.
Kai ta jinjina kawai tana dubanta,tana jin inama ace itace hajja?.....tana hasashen ranar da wannan damar zata samu a hannunta?.....tabbas saita sanya aminatu kuka da idanunta........sai ta sanya zuciyar aminatu da hamza sun buga da qasqancin da zasu gani daga yaran da su suka rainesu har suka zama abinda suka zama a yanzu
(Tabbas gaskiya ne da akace ka guji sharrin wanda ka kyautatawa.......me makon jin dadi kyakkyawan fata da kyakkyawan mu'amala ta shiga tsakaninsu da mutanen da suka maida mata 'ya'ya mutum.....amma ga nata salon sakamakon,Allah kayi mana tsari daga sharrin dukkan wani abu me sharri mutum ko aljan,me rai ko maras rai ameen ya hayyu ya qayyumu).
Bugu daya tak aka daga kiran da hajjan tayi,muryarsa ta fito tarwai yana gaidata. Cikin kulawa ta amsa masa sannan tace
"Kaga yahaya.......naje unguwa ne sai na sallami driver da xummar zan tuqo kaina na dawo gida......."
"Me yasa hajja?,ta yaya zakiyi tuqi da kanki?" Ya fada a tsananin firgice kaman wanda akace masa ta hallaka. Murmushin qasaita ta aje
"To ai yanzu ma gashi na kasa dawowa din da kaina duk kasala ta rufeni...."
"Bari na kira driver din ya dawo ya maidaki" Ya furta da hanzari
"Kaga dakata.....wanne irin driver?" Ta fada tana bata rai
"Yi haquri hajja,me kk so?" Ya sake fada a rikirkice
"Matarka nakeso ka turomin ita zata maidani......kace ta kirani na bata kwatancen inda nake yanzu haka ina jiranta......kada kuma ta batamin lokaci" Ta fada tana bata rai
"An gama" Ya fada zuciyarsa na rawa.
Ta rigashi ajiye wayar ta waiwaya tana kallon maamah cikin murmushi
"Kinsan matar da nace a kiramin?" Kai maamah ta girgiza tana shakkar yiwuwar wanzuwar umarmin da hajjan ta bada yanzu yanzu
"Matarsa ce......itace taso dagamin yatsa taso tayi fito na fito dani,a zatonta tana da malaman da xasuyi mata aiki fiye da nawa......tanaso ta mallaki yahaya ta mallakeni.....har na sanya ya saketa na sakashi ya dawo da ita don tazo taga iyakarta......taga iya mizanin nawa aikin.....don tazo ta banbance tsakanin aya da tsakuwa,ta sake kuma fahimtar da gaske fa shi ruwa ba sa'an kwando bane......ita kanta a yanzun sai yadda nace mata,duk dana fahimci kanta yana fusga wani lokaci kaman wasu abubuwan idan nayi mata tana jin ciwonsu,shi yasa nakeson na qarasa horata da kyau" Kai kawai maamah take jinjinawa,abun yayi mata da kyau.....salon kuma ya burgeta yahau mizani da gwargwado na abinda take hasashen shimfidawa kanta. DA FUAD DA MUSADDIQ DAMA MATAYEN DA ZASU AURA SU ZAMA QARQASHIN IKONTA. wannan shine cikakken iko da isar UWA. Ta fada a ranta
"Wannan shine cikakken iko da isa.....ki katange komai kaman yadda sanda kk sha wahalar komai din ke daya kk sha" Hajja ta fada tana jinjina kai
"Indai ni na haifi fuad ya zama tilas ya fidda kudaden nan ya bani.....zan motsa masa qwanjina.....zan kuma banbance masa uwa da mahaifiya a wannan lokaci karo na farko" Maamah ta sake fada a ranta.
Ya jima riqe da wayar bayan gama waya da mahaifiyar tasa yana juya wayar a hannunsa. Sassa biyu na zuciyarsa kowanne na qalubalantar dan uwansa.
"Tayi daidai,ko mutuwa hajja tace muyi daidai ne......ai ta isa....girmanta yana da yawa,to laifin me ma tayi?,koni ta kira zuwa zanyi bare matata,komai tayi a kowanne lokaci ko yanayi daidai yake" Daya sashen yake fadi,yayin da daya sashen zuciyarsa yake cewa
"Ta yaya tana tsaka da hidimar gida,ya tabbatar yanzu haka tana can tana yiwa hajjan girkin rana daya zama wajibi aka kowacce matar danta tayi mata shi kulli yaumin rana da dare ba fashi......(tsarin girkin abincin gidan tsarin girki ne na bai daya,duk da irin girma da wadatar gidan tukunya daya ake dafa abincin safe rana dana dare,raba girki ne a tsakanin faccaloli tamkar kishiyoyi,kowacce zatayi kwana biyu 'yar uwarta ta karba,hakanan a tattare a babban dining room dake dauke da family dining table akecin dukka abincin. A nata fadin don a tattala mata dukiyar 'ya'ya,kuma dukkansu zasu samu sauqin kashe kudi a gidajensu,tunda kome zaa siyo hadin gwiwa zaayi a kawo......amma kuma ta gefe daya.....tsabar nuna isa izza da mulki ne,da kuma dabarar karantar motsin kowa cikin gidan ba tare data shiga sashen kowa ba don ta tattaro kowa din waje daya.
A yanzun ya tabbatar tana can tana wannan hada hada.....bama wannan ba......fita haka katsam a lokaci guda ba shiri?. Wannan sashen dake hango masa rashin dacewar shine sashe mafi rauni a zuciyarsa,don haka wancan bangaren ya rinjayeshi ya danna mata kira kanshi tsaye.
Sanda maamah ta bude baki da zummar sake magana kira ya shigo wayar hajja. Ta daga wayar tana kalla,sai ta sake wani murmushi me sauti
"Naja'atu ce" Ta fada cikin nishadi,saita daga wayar tana sanyata a hands free
"Salamu Alaikum hajja......daddynsu arfat yace kina buqatar nazo daukarki......kina daidai ina?" Fuska ta tsuke tamkar ba itace ta gama dariya yanzu ba
"Ke banason hauka......haka akeyi daga kiran waya ba gaisuwa ba komai?,duk kinzo kin gaidani dazu da safe amma yanzu mecece?,la'asar fa muke dosa?" Shuru yadan biyo baya kafin muryarta ta sake bayyana a karye
"Kiyi haquri,ina wuni?.....kin yini lafiya?"
"Lafiya lau" Ta furta a dake
"Ina 'yan kaba,kizo daidai bakin kasuwar turawa ki jirani" Daga haka ta katse wayar.
Dubanta maamah tayi tana mamaki
"Hajja me kuma zai kaimu 'yan kaba?,ai sam ba hanyarmu bace" Zamanta ta gyara tana sake sakin shu'umin murmushi
"Eh mana.....ai so nake ta sake gane girman izzar tawa......sai bayan mun isa gidan ki zaki fahimci sauran aikin". Sosai maamah ke duban hajja din,lallai dole tasha kan kowa da komai,dole ta murxa kambunta yadda takeso. Sai yanxu take tambayar kanta ya akayi tayi sanyi haka ta sake?,hajjan da a baya a wajenta take daukan courses na abubuwa amma yanzu nema take ta zama malamarta qarfi da yaji?.
"Kina mamaki ne mariya?" Ta tambayeta tana kallon hanya
"Ai duk wanda yayi bacci a wannan zamanin zaiga bacci.....ba yara na ba ba surukaina ba.....hatta da jikokina.....yara da manya dukka sai abinda hajja ta shimfida"........
Ji yayi tamkar an daka masa tsawa tsakiyar baccinsa ana kuma masa umarni da ya farka. A nutse ya farka saidai kuma yanajin wani irin sauti mara dadi yana amsa kuwwa cikin kunnuwansa tamkar dai a mafarki akayi masa tsawar. Idanunsa ya lumshe a hankali yana son tuna abinda ya faru din,amma kansa blank bai iya hasaso komai ba
"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwhuw,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ya furta a hankali bakinsa yana motsawa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 55
Tsam yayi da ransa yana jin yanayin jikinsa yana sauyawa daga ainihin yadda ya kwanta din a dazun. Numfashi ya aje a hankali ya yaye blanket din ya miqe,ya zauna sosai saman gadon. Duk da knocking din da akeyi din hakan bai hanashi hada hannuwansa guri guda yayi addua ba,ya shafa saman fuskarsa a nutse sannan ya zuro qafafunsa qasa ya miqe.
A nutse yake takowa zuwa ainihin falon nasa dake cike da nutsuwa,shuru tamkar ba cikin gidan yake ba,komai komai cikin matsananciyar tsafta a killace kamar yadd yakeso koda yaushe ya dinga ganin komai a hakan.
Yana ci gaba da jin jikinsa da wata 'yar maqalalliyar kasala har ya isa qofar falon,ya murza key ya bude qofar amma bai murza handle ba,ya barta a haka yana komawa da baya hadi da bada umarnin a shigo.
Tun bai zauna ba ta sako qafafunta falon,dauke da wani kyakkyawan kwando me qananun tayoyi,yana da mariqi tamkar na luggage ko trolley da zaka iya rageshi ko ka qarashi sannan ka jashi yadda kakeso.
Da sallama a bakinta da qanqanuwar nutsuwar nan da take samar da ita a gabansa.
"Wa'alaikumussalam" Ya amsa yana zama saman daya daga cikin qawatattun sofas din da suka yiwa falon qawanya masu tsananin taushi da kyau na gaske,yasa hannunsa yana lalubem remote na A.c din falon don ya rageta. Shi din ba kasafai ya fiya son ac ba ko ya qureta har haka ba,wannan din sai oga farouq,a nan ma zaka iya jin kansa dashi.
"Hamma barka da warhaka". Ta fada cikin shagwabarta da marairaitar nan tata data zama a halittarta. Labbansa ya motsa kadan da wani yanayi da yafi kama da murmushi
"Habibtyn hamma" Ya furta a nutse kaman yadda tsoron qarewar haruffan bakinsa. Sunan daya kiratan dashi ya sanyata ta sake rakwarkwabewa. Ta tabe fuska tana kallonsa
"....hamma na dauka ka daina yayi na......BB farouq yacemin ka samo wadda ta sace zuciyarka.....tunda ta sace zuciyarka wai kuma tayi snatching naka a wajen kowa....she owns you ita kadai". Qaramin murmushi ya sake subuce masa wanda yafi na baya. Rigimar amna yawa ne da ita,har yau bata girma baisan kuma sanda zata girma din ba,yafi tunanin aure ne kawai zai kawo mata wannan hankalin da girman. Gefe daya farouq,shikam a duniya yanaso yaga ya tubura amna din,wani lokacin yana yi ne kaman hankalinsu daya,abinda kuma bazai taba zama hakan ba
"Zo nan" Ya fada yana yafitota da hannu gami da nuna mata gefansa. Sai ta tako din a hankali ita da kwandon nata har ta iso gabansa ta zame ta zauna sosai
"Baki gaya masa tare zaku zabi mata da hamma ba?,baki gaya masa sai wadda kikace tayi kinaso sannan hamma ya aura ba?" Yayi mata tambayar yana kallon qwayoyin idanunta abinda ya qara mata karsashi da qwarin gwiwa. Murmushi ya subuce mata data tuna da wannan
"Na gaya masa hamma sai ya tabe baki,kasan me yace?" Kai ya girgiza yana qara girmama quruciyar amna din,tabbas auta ba wasa ba,ko yaya sai wannan quruciyar ta tabashi
"Wai ita soyayya ba ruwanta da jiran lokaci ko dacewa,sace zuciya takeyi ko an shirya ko ba'a shirya ba....." Ta qarasa maganar daidai sanda farouq din yayi knocking hadi da turo qofar yashigo gaba daya,don yaji muryarta alamun suna zaune daga falonne.
Tsaf kalaman nata da suka fito daga bakin farouq din duka zauna masa akai,sai ya daga kai yana dubansa sanda yake takowa falon. Ya bude baki zai fara mata tsiyan nashi fu'ad din ya tari numfashinsa
"Kai kakeso ka lalatamin kunnuwan qanwa?.....kai kake karanta mata yadda soyayya take ko?".
Wani dariya ya saki yana saka hannu ya dauki green apple guda daya cikin apple din dake ajiye cikin wani dan kwando nan saman fridge din dake kusa dashi yana takowa falon
"Har yanzu kallon jaririya kuke mata ba?.....zakusha mamaki sanda ta kawo wani tace itace shi takeso,aure takeso kuyi mata".
"Hamma....." Ta fada idanunta suna yin rau rau tana duban fu'ad. Hannu ya daga mata alamun tayi shuru kada tace komai,sai ya maida dubansa ga farouq din
"To sai me?,idan ta fada dinma ai daidai ne". Yana zama a gefansa yace
"Ni zanfi kowa murna da hakan ai......tashi ki bamu waje" Farouq din ya fada yana komawa serious dinsa. Duk sanda yayi irin hakan ta tabbatar Lokacin wasa ya fita kenan,don haka bata musa ba ta tsugunna tana rage plates da bowls din da tasan fu'ad ya gama amfani dasu saboda ta sanshi bai fiya son tarkace a waje ba,yanzun saisu sanyashi fasa cin abincin gaba daya.
Spoon ya dauka kawai ya saka a plate din fu'ad din bayan fitar amna,wannan din ba wata sabuwar dabi'a bace,kusan sun saba cin abinci kwano daya,tun daga wancan lokacin da suke fafutukar rayuwa da samarwa kawunansu 'yanci,har zuwa yanzun da suka zama cikakkun mutane kuma 'yantattun 'ya'ya.
A nutse suke cin abincin kuma ci gaba da tattaunawa akan tafiyar tasa. Har suka kammala basu tashi a gun ba,sai da kiran anni ya shigo masa waya.
"Ka shiga wajen maamah kuwa?" Tambayar data fara yi masa kenan
"Zan shiga dai anni....."
"Kome kake ka barshi,ka shiga ka gaidata tasan da dawowarka"
"In sha Allah anni" Ya fada a nutse,sai ta katse wayar shima ya sanya hannu yana sauka daga bangaren kiran gami da fidda siririyar iska daga hancinsa.
Miqewa farouq yayi abinda ya sanya fu'ad din daga kai daga zaune ya kalleshi. Kafin yakai ga tambayar shi ya rigashi magana
"Na jima ban shiga abuja ba,ina jin gobe ko jibi zan shiga din......."
"Safe journey" Fu'ad din ya fada a taqaice yana miqewa shima. Siririyar dariya farouq din ya saki yana tsare fu'ad din da ido wanda alamu ke nuna yana Neman hanyan wucewa ne daga wajen
"Kar muyi haka dakai.....karka canza kuma daga yadda na sanka......ko da da sau daya baka taba yimin kara ka rakani wajen fannah ba.....kayimin alqawari next time idan na tashi zuwa tare zamuje......."
"Yanzun daga daukomin dogon sharhin nan farouq.....cewa nayi bazani ba?.....kawai dai kasan ba abu bane me sauqi gajimare ya gama yawo dani na sake komawa wani tsakanin kwana daya ko biyu kawai......infact ma kasan yanzun shirye shiryen dake gabanmu ai.......ba cikakken lokacin batawa a irin wadannan abubuwan.....but duk da haka bazan karya alqawari ba.....if zaka iya jirana na kammala sai muje din". Dariya ce taso qwacewa farouq din amma ya maze,ya san dama zaa rina,kuma wannan dogon bayanin da yakeyi duka yana neman hanyar guduwa yaqi zuwa ne.
Bai taba ganin mutumin da soyayya bata taba burgeshi ko d'ad'ashi da qasa ba ko yaya takai ga bawa jama'a sha'awa ba irin fu'ad din. Bawai ya tsani mata bane......aah......amma yadda yake nesa qwarai da al'amuransu kai tsaye idan kace bai jituwa da shirginsu bakayi laifi ba.
"Kanka tsaye kacemin yanzun ma ba zakaje ba.....kacemin ka shirya nunawa fannah iyakata....ni din ba kowan kowa bane a wajenka" Ya fadi yana hade rai sosai idonsa akan fuskarsa. Kallon idanun farouq din yayi,bai wani damu ba yasan halin kayansa sarai,yasan ya fada ne don ya motsashi,don haka ya daga kafadunsa
"Ka fada soyayya ne at wrong time......har yanzun kana da sauran lokaci da ya kamata ace kana gina kanka ne bawai soyayya ba......ita soyayya idan lokacinta yayi zata kawo kanta da kanta"
"Kaiii.....inaaa......a wannan lokacin da mutum ke bacci da qyar?,am against you fa har abada indai ta nan wajen ne.....kaidai da waccan aljanar tayi maka shigar sauri zamu ci gaba da nema maka magani......" Bai qarasa ba yaji saukar spoon a kafadarsa,ya goce spoon din ya fadi qasan marbles,sai ya soma sauka daga dining area din yana dariya abinsa gami da cewa
"Tafiya abuja dole ce......zan siya ticket harda kai......alfarma daya zan maka zan daga zuwa next week cikin weekends din" Yana kaiwa nan ya fice abinsa daga parlor din.
Kai kawai ya girgiza yana murmushi qasan zuciyarsa. Bazaice ko sau daya ga sanda suka taba samun sabani da farouq ba ko wani ya bata ran dan uwansa. Wani hadi ne daga buwayi gagara misali,idan kaga musaddiq da Sadiq zakayi tunanin sune uwayensu daya,kaman yadda da yawa ake tunanin shi da farouq din twins brothers ne da suke da kamanni daban daban.
Baiyi mamakin jin ba ruwan zafi a toilet kaman yadda ya saba samu koda yaushe ba,don dukka ma'aikatansa da sauran masu masa hidiman sassansa ya basu hutu na satittikan tafiyarsa south Korea,don haka ya kunna heater ya dawo cikin bedroom din sannan ya wuce kai tsaye yana fita daga ciki.
Qofa ce qwaya daya tak wadda batakai duka sauran doors din falon fadi ba,ya budeta ta hanyar key din dake maqale a jiki ya turata a hankali ya shiga.
Dakin yana da dan duhu don haka ya laluba makunni ya kunna fitila take haske ya gauraye dakin
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 56
A yadda qofar dakin take daga waje,ba zakayi tsammanin taras da yalwataccen daki me wani irin tsari da kyau ba kaman haka. Ci gaba yayi da kunna kowacce fitila ta cikin dakin,kama daga ta bango zuwa kyawawan table lamps masu wani irin kyau me daukan hankali. Wani irin guri aka tsaga daga sashen nasa da yayi Linkin da ainihin farfajiyar gidan bangaren da duk yawan taro ko hayaniyar jama'a da gidan zaya tara zaiyi wuya ka iya jinta muddin kana wajen. An qawatashi da wasu irin shelves da drawers masu mugun kyau da daukan hankali da aka tsara takardu documents zuwa litattafai nau'i daban daban daga yarukan duniya daban daban da yake iya fahimta yake kuma iya magana da wasunsu.
Ragowar bangunan kuma manyan frames ne masu asalin kyau da tsada na qasar turkey da dubai da aka kashewa kudade masu ciwo aka tsara sunayen Allah da ayoyin qur'ani masu girma da wani irin ruwan gold daya sake baiwa frame din kima kyau da daraja. Akwai kyakkyawan table din daya zama cikon ado wa home office din nashi da yake hade da kujerarsa,sai kuma wasu cushions da aka zuba gajajjeru da ba zasu bata tsarin wajen ba,daura dasu kadan kuma wani board ne dake dauke da rubuce rubuce barkatai da baya rasa alaqa da tsare tsare na abubuwan da ya sanya a gaba zaiyi.
Komai na room din neutral color ne kaman yadda dayan bedroom dinshi yake,abinda zai bayyana maka kenan normally bayason kaloli masu hayaniya can can can.
Da gaske a yanzun target dinsa shine bude kamfanin......babban burin da a yanzun bashi da wani sauran abu daya rage masa kamar shi,saidai abune daya tabbatar yana buqatar qarin jajircewarsa da kuma aiwatar da komai cikin sirri har sai an kai gabar da ya kamata komai din ya bayyana.
Ba alaman qura ko datti ko qwalli daya,don duk wanda ke aiki dashi yasan tsarinsa da kuma dokarsa. Waje ne da ba wanda yake bari ya shigar masa sai family dinsa,anni farouq amna saddiq sai musaddiq......sai kuma amintaccensa mutum guda daya me sunan malam.
Ya bude lockers da yawa,ya kuma jona abubuwa da yawa kafin ya daidaita komai ya juya yana fita a dakin da zummar zuwa sanda zai dawo komai ya zama normal,don yau din aiki yakeson yi sosai kafin ranar Monday ya isa kamfani ya duba yadda ya barsu.
Fes ya fito a shirye,sanye da lallausan yadin filtex fari qal mai qarancin nauyin da har kana iya hangen farar vest din jikinsa data lafe takuma saje da yadin sosai saboda tsananin haskenta. Sassanyan qamshin nan nasa dake da daukan hankali yake fitarwa sannu a hankali,fuskarsa tayi fresh cikin yanayin da zai nuna maka cikakkiyar nutsuwar zuciya da ruhi da yake da ita. Sabanin wasu lokutan,yanzun kanshi saye yake da hular data dace da yadin jikin nasa,sai half covers din daya sakaye doguwan qafansa a ciki.
Komai rashin nisan waje bazai taba iya taka qafarsa ba tare da ya sanar da anni ba,yanzunma sassanta ya bulla,yana tafe yana amsa waya har ya cimma sassan nata.
Bai iya ci gaba da amsa wayar ba sanda qafafunsa suka shiga ainihin falon,sai ya zare wayar daga kunnensa sakamakon sautin karatun qur'ani dake fita daga speakers din dake daura da qatuwar plasma din dake girke saman mulmulallen tv stand din.
Karatu ne cikin muryar babban malaminsa sheik abdurrahman assudais,qira'ar dake balain kashe masa jiki tare da saukar masa da nutsuwa koda yana cikin bacin rai. Falon anni na dabanne,badai ka shigo ka samu ana kallace kallace marasa ma'ana ba bare akai ga batun jin kida ko waqa,kusan duka haka ta azasu akai,suma kuma haka suka taso.
Lokaci irin wannan magariba ke kan hanyar qarasowa,zaka sameta zaune cikin kamala tana wani abun da zaya amfani lahirarta,imma girkin abba ita da amna,ko ka sameta da carbi,ko tana sauraren wani karatun addinin.
Yanzunma suna tare da amna din,wanda daga gefan amnan kadan wata baquwar matashiyar ce da zata girmewa amna din da aqalla shekaru biyu ko uku.
Yana shigowa ta sanya remote tayi qasa da karatun sosai tana murmushi. Ya qaraso a nutse ya zauna daga gefanta yana tanqwashe qafafunsa tamkar ba wanda yayi shirin fita ba,sai kuwa ta tareshi
"A'ah miqe....ai sai ayi magariba kana zaune a nan.....kaje ka dawo.....don abincin dare ma yau banda kai a gidan nan" Girarsa duka biyun ya daga alamun mamaki,yanayin daya qarawa fuskarsa wani irin kyau,ya kuma fusgi hankalin matashiyar qwarai da gaske
"Anni yau din nayi wani laifi ne....?" Ya fada calmly idonsa akan annin. Kai ta girgiza
"Ko kadan......kawai nasan idan kayi dinner a daya gidan naku hakan zai farantawa maamah sosai,zai kuma sake bada fahimtar juna da shaquwa a tsakaninku". Tayi maganar cikin kwantar dakai itama tare da fatan kaishi zuwa ga abinda takeso din.
Kansa yadan motsa kadan,har yanxu anni kaman bata fahimci daga ina ainihin tushen matsalarsu ya fara ba?,har yanzu kuma kamar annin bata fahimci menene yake riqe da matsalar tare da sake wanzar da ita ba?,wanne fahimtar juna da shaquwa a yanzun ake nema tsakaninsu ne?.
"Saika dawo......kace ina gaidata" Ta fada tana daukan remote zata qara volume,abinda ke alamta masa ta gama fadin bayaninta kuma batason yayi sharhin komai akai
"Hamma....." Amna ta kirayi sunansa tana murmushi idonta a kansa.
"Lovy dovy" Ya fada yana xuba hannunsa a aljihun rigarsa yana jin karsashinsa da duk wani walwalarsa yana ja baya tamkar wanda aka tura gidan kaso.
Murmushi tayi,tsokanarsa takeso tayi amma kwarjinin nan nasa ya taso ya danneta
"In fada hamma?" Tayi masa tambayar tana dubansa
"Say it amna....." Ya maida mata cikin caring din daya kusa sanya matashiyar narkewa. Bata taba zato koda a mafarki yana da wannan siffar ta kulawa haka ba......bata taba hasashen akwai dabi'a ta sauqin kai a tattare dashi har haka ba
"Muhammadu.......yi tafiyarka......ku wuce ciki keda unaisa ku wankemin bottles dinnan,suna kitchen basu da yawa".
Duk da yaso ya wuce din kamar yadda anni tace amma dole sai daya dan tsaya a farfajiyar gidan suka gaisa da ma'aikatan gidan,sannan kuma me sunan malam yayi masa tattaki suka fice daga gidan bayan ya shaidawa security dinsa ba nisa zaiyi ba baya buqatarsu.
Yana takawa a nutse yana sake fuskantar gidan wani yanayi yana riskarsa,abubuwa masu tarin yawa da suka saba dawo masa a duk lokacin da zai gifta ko ya shiga gidan.....al'amura masu nauyin dake iya motsa zukata qwarai da gaske. Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya yake janye jiki da rayuwarsa sosai daga gidan. Duk da komai na fasalin gidan ya canza,ba wani abu da yayi saura dangane da ainihin ginin gidan na baya,to amma dai wannan filin....wannan gurbin da wannan muhallin da aka aza tubalin ginin gidan har yanzu dai shine a wajen. Har yau har kwanan gobe idanunsa basa mantawa da tsarin gininsu na asali,wannan ya sanya idan ya kalli wasu guraren sai ya tuna da JADDA sai kuma ya tuna da ABBANSA,duk da guraren a yanzun sun sauya sun koma wasu abubuwan na daban,amma tambarinsu yana nan kafe qasan ransa da zuciyarsa.
Cike da girmamawa,martabawa tare da kallon Cikakkiyar kima da darjtawa malam sa'idu yake miqewa sanda ya fuskanci dosowarshi gidan.
"Barka da zuwa yallabai.....sannu da zuwa" Malam sa'idu yake fadi cikin mutuntawa.
"Barkanmu da warhaka baba.....mun sameku lafiya?" Fuad din ya furta shima cikin tsananin bada girma. Malam sa'idu bawai me gadi bane kadai a gareshi,yana da wani role da yake takawa da kuma wani ajiyayyen matsayi da fuad din ya bashi ba tare da sanin kowa ba.
Malam sa'idun da asalinsa me saida kayan marmari ne a bakin titin tsohon layinsu,wanda a yanzun layin ya koma tacan katangun gidansu yake,qofofin sun dawo bayan gidansu na asali,inda kusan gaba daya fuad din ya siye layin sai tsirarun gidajen da suke mazauna ciki suna da buqatar zama a ciki. Tun asali bayan layin nasu suna kiransa ne dama da layin 'yan gayu,don kusan manyan gidaje ne ata wajen,kamar yadda kusan mafi rinjayen unguwar tasu layinsu ne kadai keda qananun gidaje jifa jifa. To a yanzun layin duka ya zama qarqashin kulawar fuad da wani irin kwalta da aka zuba,gate a farkonsa da qarshensa da manyan fitilu jere reras.....cctv cameras da masu gadin layin saboda tsaron dukiyar mazauna layin da rayukansu.
Bayajin malam sa'idu zai iya ficewa daga tarihin rayuwarsa ko zuciyarsa. Yadda mahaifinsa baya iya cin komai haka malam sa'idu zai hada fruit ya bashi daidai qarfinsa lokaci bayan lokaci duk sanda Allah yakai wucewar fuad ta wajen,ana tsaka da haka malam sa'idu yaje ganin gida,bai kuma dawo ba har sai bayan wasu shekaru. Bai manta da yadda malam sa'idu ya nuna jin ciwon rasuwar abbansa ba,wannan ya sanya ko da rayuwa ta kawosu inda suke a yanzun ya nema malam sa'idu. Kyautata rayuwarsa yayi da gasken gaske ba tare da mutane sunsan da hakan ba......amma sai ya ajeshi a mazaunin me gadi bisa shawararsu da amintarsu shi da malam sa'idu din,kuma hakan bai hana ya bashi albashi ba duk wata,saidai ba irin albashin da ake jifan gamagarin masu gadi ba. Malam sa'idu baisan wace maamah ba bare anni,tun a baya wajen sana'arsa yake lazimtar zama,bai tara jama'a bare gulma dayi da gidajen alumma ya shigo ciki har yasan abinda gidan wani ke ciki,abu daya ne dai da har yau bai fahimta ba,jaddada gadin gidan da kula da shige da ficen matar gidan daya kasa tantance matsayinta a wajensa. Da yake bame damuwa da abinda bai shafeshi bane bai taba tambaya ba,yana dai aikinsa yadda akace,duk kuma abinda muhammad din yake da buqatar sani yana sanar masa.
"Mu zauna daga nan" Fuad ya fada yana neman wajen zama saman bencin da malam sa'idun kan dan kashingide akai wani lokaci.
"Aa haba yallabai.......ai sai ka bata kayanka kuma......bari a dauko maka kujera daga cikin gida kafin mutanen gidan su qaraso"
"Yi zamanka" Ya fada cikin ko in kula. Mamaki ya sake kashe malam sa'idu. Duk uwar dukiyar daya mallaka,kyau....ilimi duk basu sanyashi jin ya bambamta da sauran jama'a ba.
"Ita kadai ta fita?" Fuad din ya tambayeshi yana zaro wayarsa
"A'ah....su biyu ne" Ya amsa masa kai tsaye,don ba tambayar da zaiyi masa da zai boye masa wani abu. Kai ya daga yana duban malam sa'idu din jin ya ambaci ita da wata.....Allah yasa abinda yaketa qoqarin kaucewa da fatan kada ya faru ba shine ya soma faruwa ba
"Sun jima da fita?"
"Eh ya kusa awa biyu zuwa uku haka" Ya sake amsa masa. Idanu yadan zubawa malam sa'idu din kamar yanason fahimtar wani abu daga gareshi,sai kuma ya janye idon yana fesar da iska daga bakinsa,sai ya samu kanshi da Maida wayar aljihunsa kawai ya miqe daga zaman da yayi niyyar yi da,ya dawo gaban gidan ya tsaya sosai jikin realer da aka yiwa gaban gidan adon flowers da ita,idanunshi bisa hanya zuciyarsa na karanta masa abubuwa iri daban daban.
Tun dazun tunani da hankalin maamah yana kan hajja,har zuwa lokacin da mintuna kadan suka rage musu su isa ga unguwar
"Yarinyar can fa hajja kin kaita wata unguwar tana jira". Murmushi hajja ta saki da qaramin tsaki a hade
"Bari ki gani" Ta fada tana daukan wayarta daga saman cinyarta.
A hands free ta saka wayar,bugu daya ta daga. Akwai qaguwa sosai cikin muryartata,amma kuma bata isa ta nuna hakan ba koda da wasa kuwa
"Hajja na qaraso"
"To yayi.....na bar wajen,zan turo miki address na inda zaki sameni,na gaji gida nakeso na wuce,kada ki wuce minti biyar baki iso ba"
"To hajja" Ta amsa mata a sanyaye. Katse kiran tayi,murmushi na subuce mata ta kalli maamah
"Yanzu nan zata zo cikin minti biyar?" Maamah ta tambaya cikin mamaki
"Kuma mijinta shi zai maidani gidanma a gabanta ba....da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne". A gajarce ta tura mata adress din,sannan ta fara qoqarin kiran yahaya daidai sanda suke karyo kwanar da zata sadasu da shimfidadden jadda street din dake rubuce jikin wani qaramin allo dake kafe a farkon layin.
Tunda ya hangi motar ya ganeta kafin takai ga isowa. Yaci gaba da bin motar da idanu har ta qaraso qofar gidan,tayi kuma yi tsaiwar bawa malam sa'idu umarnin bude mata hanyar shigewa,sai a sannan ya sauke hannayensa yana duban tayoyin motar da sukayi bududu abinda zai shaida maka ba qaramar tafiya akayi da motar ba,tafiya me tsaho kuma cikin guraren da basu da shimfidadden titi ya saka kai yana wucewa ciki kafin malam sa'idu ya kammala bude musu gate din.
Kansa a qasa yake takawa cikin gidan,haka kawai zuciyarsa yakejin bai gamsu da yanayin fita da kuma shigowar motansu a yanzu ba. Cikin falon ya yiwa kansa gurin zama. Ba kowa a ciki,don dama muddin idan bata nan din bata aminta da masu aikin nata su kusanci falon har sai ta dawo.
Tun tsaiwarsu bakin gate din ta ganshi,wannan ya sanya driver yana aje motar qasan rumfar aje motocin ta bude ta fito
"Ya da sauri haka ko duk gajiyar ce?" Hajja ta tambayeta sanda take tattaro jakarta
"Yaroncan Muhammadu na gani,yana ciki yana jira,bansan tun yaushe ya shigo gidan ba.....banyi zaton jirgin safe zasu biyo ba" Ta fadi hankalinta yana yin cikin gidan. Da kallo hajja tabi maamah din ganin yadda duka hankalinta yayi cikin gidan,sai kawai ta jinjina kai ta soma yunqurin fita a motar itama tabi bayanta.
Qafafunsa na harde cikin juna yayin daya jingina bayansa da makarin kujerar,ya zube idanunsa duka a bakin qofa yana jiran ganin shigowarta. A wannan yanayin ta murda qofar ta shigo,tanata qoqarin azawa fuskarta rashin sukuni da gasken gaske. A wannan karon batajin zatayi masa da wasa akan dukka buqatun da zata bijiro masa dasu.....dole yayi yadda takeso wanda shine zai zama cikamakin burin MALLAKAR 'YA'YANTA.
Duk yadda taso tayi diban watsin tsiya dashi amma sai kwarjininsa yakeson bugar da ita. Hausawa sukace kuma wanda yayi me kyau ya sani haka wanda yayi maras kyau. Idanun da yake binta dashi sai ta dinga jin kamar yanason karantar daga ina take?,me kuma taje yi?.
"Sannu da zuwa" Ya fada a nutse yana zare qafafunsa daga cikin na juna daidai sanda take aje mayafinta da jakarta
"Ai kaine da sannu" Ta fada a taqaice tana ta tattalin fushinta da bacewar fara'a daga fuskarta,saidai kuma wani bangaren na zuciyarta yanata saka mata tsarguwa da kuma shakku.
Hada ido sukayi a karo na uku,sai ta kasa jurar kallon da yake binta dashi din
"Kana mamakin na baka umarni baka bi ba kazo na sameni a raye ban mutu ba ko?" Ta fake da wannan,don batasan da abinda zata iya qalubalantar kallon nasa dake mata wani irin nauyi da kwarjini ba. Idanun nasa ya sauke a qasa yana girgiza kansa,baikai ga cewa komai ba ta sanyo kai da tata sallamar.
Ita dinma dashi suka fara hada idanu,saidai nata kallon yafi na maamah tsini a nata idanun da zuciyar. Kwarjininsa ya cikata fal,hakanan alfaharin ganin farko wa mamallakin jadda diamondchore resources ya cikata.
Sunansa ya jima da shiga kundin nata lissafin,saidai a dukka hasashenta bata taba tunani ko zaton samunsa a nan kurkusa ba.....bata taba kawowa cewa yana da wata alaqa ta jini me kusanci irin haka da tsohuwar qawa kuma aminiyarta mariya ba.....bata taba hasashen mariyan tana da nasibin haifar babban mutum har kamar Muhammad jadda ba.
"A'ah.....yaron namu ya iso kenan......maraba" Ta fada tana sauya reaction na fuskarta cikin qasa da second biyar tare da takowa cikin falon a hankali. Akaikaice yake dubanta da wani irin kallo,sam baisan fuskarsa ba......bai kuma tuna ko yaya a inda ya santa ba,ta yaya ita din akayi tasan wayeshi?,yaya akayi tasan daga tafiya ya dawo?.
"Bana jin zaka iya shaidani.....shi ya sanya banyi mamakin musaddiq daya kasa ganeni ba.....ga yayansa ma ya gaza shaidani?" Ta fadi tana sakin fara'ar da bata kai ga qarasawa ainihin zuciyarta ba,yayin da kwarjininsa ke barazanar hanata samun abun fadi. Still dai baice komai ba yana ci gaba da dubanta. Ko dis baiji matar tayi masa ba,bai hangi dattako ko kamala da sukayi daidai da shekarunta ba a tattare da ita,sai kawai ya dauke kallonsa daga kanta don baiga amfanin maida hankali tare da son qoqarij fahimtar abinda ya tabbatar daga qarshe bame amfani bane,amma ina suka fita har na tsahon awannin ita da maamah din?. Tambayar data maqale masa kenan,bashi kuma da amsa.
Qafarsa kawai ya miqa ya zira takalmansa ya miqe
"Lokacin sallah ya kusa,zanyi salla na dawo" Ya fadi yana juyawa a nutse yana fita a falon.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 57
_________________________
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
Assalamualaikum
Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule??
Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen??
To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen.
Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki.
Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina.
Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
____________________________
"Yaa huda.....yaa huda?" Muryar haneefa ta ratsa kunnuwanta dai dai sanda take kwance qudundune cikin bargonta. Kusan idan bawai dare ne yayi ba hakan ba dabi'arta bace,amma a yanzun yana neman ya zame mata dabi'ar da sabreen ta fara karantar hakan.
Batakai ga ce mata komai ba,don ba abinda ta gani behind kwanciya din da take yawan yi,sai ta barshi kawai a zuwan yanayi ne da yakan sauyawa kowanne dan adam. A yanzu ma gaba daya hankalinta yana kan ayshatu.....ciwonta gaba yake qara yi,ga mika'il a gefe,ga mashkur shima daya sanya wuta da yawa a kanta. Ya'aqoub ne kawai me dan sauqi saboda bai cika zafafawa ba. Dukkansu batason kowa ya subuce mata a daidai wannan lokacin da shirinta ke qara zurfi a kansu,kuma tafi hangen samun nasara da wuri akan mika'il da mashkur,don shi ya'aqoub a yanzu tunaninsa yafi karkata kan yadda zai shawo hankalinta ta aminta ta aureshi,abinda kuma bataga ranar yiwuwarsa ba. Wai mema zata tsinta ne a auren?,bayan tana ganin yadda su mazan suke?,tana ganin kuma yadda matan ke komawa?,ko hanyan aure yanzu mutum yayi mata ai bai qaunarta ballantana ace mata tayi. Duka tsari da halayyar mazan baiyi mata ba ballantana ta cusa kanta a sabgarsu da nufin zama tsakaninta da waninsu zama na din din din?.
Miqewa tayi a dole tana duban haneefa,sai haneefa din ta miqo mata takarda tana cewa
"Wani ne wai a waje yace a baki...." Da sauri ta fiddo mata idanunta waje sanda muryar sabreen wadda ke amsa waya take dosowa cikin dakin. Yadda suka daga kai suka kalleta duka su biyun ya sanyata janye wayar daga kunnenta tana kallonsu
"Lafiya?" Tayi tambayar tana sauya yanayin fuskarta. Wani faduwa gabanta yayi,cikin tsoro tsoro ta girgiza kanta tana qaqalo murmushi tace
"Ba komai.....ina kwance haneefa ta tsoratani,na dauka wani abune da naji tanata tashina". Idanu ta sake zuba mata na daqiqu sannan ta amsata tana zama gefan nata gadon
" Ko bata tsorataki ba dama ai yaci ace kin tashi,an kusa kiran sallah.....uniform dinku nadra ta wanke tunda kin koyi laziness......kije kiyi alwala ki dawo ki kwashe abincin tukunya a flask a wanke sauran abinda ya rage".
"Tom" Ta fadi tana matse takardar a tsakiyar hannunta tare da tunanin yadda zata miqe da takardar ba tare data lura da ita ba,to amma kuma ci gaba da zama dinma tunanin mafita tamkar tana bata damar dora ayar tambaya ne a kanta.
Aljihun skirt dinta ta tuna dashi,cikin dabara ta cusa a ciki,sannan ta zame ta sauko tana gyara inda ta kwanta din,ta daura dankwali saman doguwar sumarta ta juya tana fita a dakin. Dauke idonta tayi daga kan tab dinta ta bita da kallo. Haka kawai ta gagara samun nutsuwa kwanaki biyun nan,duk motsinsu a kan idanunta yake,kuma da gaske tana ganin dan sirkawar wani abu kadan tattare da huda din.
Bandaki kawai ta wuce kai tsaye tana fata da zumudin budewa taga meye a takardar?.
Sai data samu guri cikin toilet din ta zauna sannan ta ciro takardar ta kuma warwareta.
Kaman yadda ta zata shi dinne,sunansa kawai data gani sai bugun zuciyarta ya qaru da kaso hamsin cikin dari.
Yau kwanaki uku kenan,ya rakota daga hanyar makaranta har dab da gidansu kamar yadda ya saba a kowacce rana......tun tana gocewa har ya fara zame mata sabo ba tare da sanin nadra ko haneefa ba wadda yanxun aka banbanta musu lokutan tashi qarfi da yaji ba tare da kowa yasan dalili ba. Ya zame mata kamar abokin rakiya a yanzun.....tun tana dari dari da tsoro har hakan ya fara gushewa daga zuciyarta.
A ranar alhamis tayi matuqar mamaki yadda ya tsaya suna tsaka da tafiya,ya kuma kafeta da idanu
"Lafiya kake?" Ta tambayeshi da mamaki
"Ke kyakkyawa ce" Ya fadi yana jin wutar sha'awarta na ruruwa a ransa tamkar yadda ya dinga jin ta 'yar uwarta. Yana jin kamar ya dauketa a yanzun ya wuce da ita ya aikata abinda ya tanadi aikatawa,saidai kuma bazaiyi haka ba,yanason komai ya kasance a daidai sanda zatafi jin ciwo da radadin da zai iya zama ajalinta,ya kuma tarwatsa farincikin da take musu tattali. Yanason idan ya tashi ya tarwatsata tarwatsewar da ba zata taba dawowa ta gyaru ba ballantans ta koma yadda take.
Idanu ta waro tana dubansa,yadda yake yawan kambata da kurantata ya sanya kusan kullum sai ta kalli madubi......kusan kullum sai ta kalli kanta da kanta taga wannan kyan da yake magana a kai......wannan budurwar da yake yawan kiranta dashi. Tun bata ganin abinda yake fada din har ta fara ganin,amma tana ganin kaman bata ca canci kowacce rayuwa ba a yanzun......karatu shine yafi da cewa dasu kamar yadda yaa sabreen ke gaya musu
"Ina sonki huda.......ina tsananin qaunarki tun daga ranar dana fara ganinki.......zuciyata tana miki wani mahaukacin so da bansan iya adadinsa ba......wallahi inaji a zuciyata tamkar zanyi hauka saboda ke huda......ki soni don Allah......ko baki sona ni zan koya miki yadda zaki soni din". Kalaman da suka tsoratata suka kuma razanata kenan. Kalaman kuma da Naseer din ya shiryasu ne kawai don ya soma wasa da tunaninta da qwaqwalwarta,plan na biyu kenan daga cikin tsarikansa.
Baya taja tana girgiza kai,tana jin tsoro yana shigarta. Wacce irin soyayya a shekarunta?,duka duka nawa take?,koda yaa sabreen bataga ta kawo kowa tace shi zata aura ba,bataga wani yazo qofar gidan da sunan zance wajenta ba.....koda abinda ake maganarshi a kanta da nasu idanun basu taba ganinta cikin motar wani ko tsaye da wani ba har zuwa yanzun da take tsaye a gabansa. Ko rakota da yakeyi kullum kwanan duniya a tsorace take......wani lokaci zuciyarta tana raya mata idan sukayi kacibus da yaa sabreen fa?,sai kuma zaqin bakinsa da daddadar hirarsa ta yaudare tunaninta da kunnuwanta.
Tayi mugun tsoratar data dinga ja da baya da baya tana girgiza kai. Yana tsaye ya kafeta da idanu,abun yana masa sugar sosai. Irin hakan yafi buqata don ta haka ne sabreen din zata fuskanci girman nasa aikin. Ya samu sabon ruhi sabon gangar jiki da baisan komai ba game da rayuwa......zai hurewa zuciyar kunne,sannan ya mori gangar jikin yadda yaso ya kuma watsar da ita tamkar wani yasashen abu maras amfani. Yana tsaye harta gudu a layin ta bacewa ganinsa,sai ya bushe da dariya.
Hakan da tayi ya tabbatar masa qwaila ce,ya kuma bashi tabbacin baa taba gaya mata kalmar so ba sai a kansa
"Allah sarki......gashi baki fara da jin kalmar ba a sa'a......anyway......ko mene ya faru dake 'yar uwarki ce taja miki" Ya fada yana juyawa don barin layin ya qarasa inda yaransa ke cikin mota suna jiransa.
Hannunta har rawa yake sanda take warware takardar. Tsakanin alhamis jumaa asabar da kuma yau lahadi ba wasu mintuna biyar kyawawa da suka wuce ba tare da tunanin abinda ya faru tsakaninsu ya dawo kanta ba. Duk juyin da zatayi sai kalamansa sun dawo mata,kallonsa murmushinsa da kambamawarsa. Fuskarta kam ta kalleta yafi sau adadi tana sake duba kyawun surarta da yake yawan jaddadawa. A yadda take gani ba mace me kyan yaa sabreen dinsu......ashe itama to tana da kyau dinne da gaske?,ko kuma yana fada ne kawai?.
*_Hello me kyau,fadin azabtuwar da idanuna da zuciyata sukayi saboda rashin tozali dake ba abu bane me sauqi......ina fata zaki daure a gobe ki barni naga wannan kyawawan idanun da zuciyata ta mutu a kansu.....idan ba haka ba.....zan iya rasa numfashina_*
Da sauri ta duqunqune takardar ta kuma jefa a toilet ta bita da flushing zuciyarta na bugawa sosai. Tsoro zumudi fargaba da mamaki dukka suka hade mata har ta rasa wanne tunani ma zatayi.
Bugun qofar bandakin da akayi ana jiranta ya sake rudata,sai kawai taja qofar ta bude ta fito ba tare da tayi komai ba,taja burki bakin famfo ta daura alwala tayo dakin nasu.
Gaba daya tunaninta ya karkata ga saqon,har ta mance da batun kwashe abinci tayi zaune saman kujera tana bitar saqon da ya riga ya rubuta kansa da kansa a kwanyarta. Fitowar sabreen din ya sanyata tunawa,ta miqe da hanzari ta nufi kitchen.
Yanzunma da kallo sabreen ta bita har ta shige kitchen din. To wai me yake samun huda take wasu wasi haka?. Bata sani ba,sai ta girgiza kai ta taka hannun kujerar tana dauko babbar dardumar da sukan shimfida suyi magariba da ishai akai suyi bitar karatun makaranta ta taimaka musu da wanda zata iya.
Da ruwan zafi sosai tayi wanka bayan wucewar hajja saboda ciwo da jikinta yake mata sakamakon zaman mota data jima batayishi kaman haka ba. Ta shirya kanta cikin fafi indian abaya me laushi,ta yane kanta da mayafin abayar daya kasance medium cotton kaman yadda jikin dogon rigar yake.
Cikin falon tayi zaune bayan ta kirayi me aikinta ta canza mata channel. Qafafunta a miqe saman side glass table din,hannunta dauke da glass cup dake cike da lemon raspberry tatacce me asalin tsadar. Babu wani abu da zata ci ko tayi amfani dashi cikin gidan da yake da qaramin kudi. Komai nata me tsada take zaba,hatta da ruwan da zata sha kuwa ballantana akai ga sutura ko wayar hannunta.
Ko a yanzun haka ta gaya masa tana buqatar ya sauya mata iPhones din hannunta guda biyu. Iphone 15 da wata tsaddadiyar waya sabuwar qira da kamfanin Samsung's. Duka duka wayoyin ba wadda tayi wata uku,to amma garin gane ganenta ta hangi wasu sabbin fitar,su kuma takeso ta riqe.
A komai tafison ta zama cikin sahun mutane na farko da ake ganin komai sabo a wajensu. Inda tana da iko komai zai zamana ana ganinsa ne ta wajenta,sanda zai soma zagayawa hannun masu kudi irinta ita ta dade da cin zamaninta. Ta sani,a dukiyar da d'anta yake dashi yana da qarfin kudi da mulkin da zai iya sanyawa a qera mata duk abinda take buqatar ya kasance nata ita kadai daga kowanne kamfani a fadin duniya,to amma ta fahimci rayuwarsa baya daidaitata dai dai data sauran masu kudin irinsa. Ba kuma haka takeso ba.....ba haka take muradi ba......tanaso ta gansu suna rayuwa daidai da matakin arziqinsa. Ta fahimci yana cikin sawun mutanen da ba kasafai suke bayyana arziqinsu ba,sai abinda ya riga ya bayyana ba yadda zasuyi dashi.
Aka idar da magariba akayi ishai shuru. Tun tana tattalin maganganun da zatayi dashi har wasu suka fara bace mata. Ta daga kai ta kalli agogon dake shirye saman tv din falon takwas da rabi na dare,to shin sai yaushe zai shigo?,sai yaushe wannan abun zaizo qarshe?.
Sannu a sannu sanda taga an doshi tara na dare babu alamunsa,wayoyinsa dukka a kashe shida musaddiq din da zata sanya ya kira mata shi a duk inda yake.
A ranta ta dinga jin cewa hadin baki ne......a ranta kuma ta dinga ji aminatu ce ta hanasu.....a yanxun haka qila suna can gabanta......ta zaunar dasu sai abinda tace musu.
Wannan tunanin ya dugunxuma mata zuciya,har taji bata da wani sauran zama cikin gidan. Dakinta ta wuce kawai bayan ta ajiye kofin lemon,ta shiga zaro takalmi cikin jerin takalman alfarma dake adane a shoe rack dinta. Cikin zuciyarta takeji yau din Alhaji hamzan zata tunkara......tanaso taji shine yayi mata cikin yaran ko ubansu?,tana so taji da ita dasu wai waye ahaqqu dasu?.
"Nazo muje ne?" Zuwaira ta tambayeta sanda taga tana dosar qofar fita daga falon
"Zauna basai kinje ba" Ta amsa mata a gaggauce tana fita a gidan.
Mugun bugun da takewa tafekeken gate din gidan ya fusata securities din gidan,saidai kuma lokacin da suka duba wadda ke bugun ta na'uarar tsaro dole kowannensu fusatarsa tayi nata guri.
Basusan ainihih matsayinta ko ita wacece ba......amma yadda suka fahimci girmamawar da take samu daga mazauna gidan ya basu alamar cewa tana da nata matsayin na daban.
Ko kallo security din daya bude mata qofar bai isheta ba ballantana tabi takan welcoming nata da yakeyi tare da bude mata qofa ta biyu da zata sadaka da farfajiyar gidan. Daga nan wasu security din su sake marabtarka kashi na uku kenan kafin kakai ga ainihin cikin gidan ka zarge qofar da zata sadaka da babban falon anni na farko.
Bata taba tunanin zata sake takowa cikin gidan ba karo na biyu.......don duk lokacin data tako din alatun gidan yakan zame ma idanu da zuciyarta barazana. Tana jin kamar kowanne abu idan ta kalla a gidan yana mata izgili ne tare da gaya mata da dukiyar danki aka samar dani......baki kuma da wata izza ko power ta mallakata.
Kowanne taku daya idan tayi cikin gidan ranta quna yake......sak fasalin yadda takeso gidan da zata rayu ya kasance sai gashi kacokam a yau din irin wannan dream house din nata mallakin aminatu ne.. Wasu mutane da basu da masaniyar sanda ta dauki cikin fuad har ta haifeshi.
Qofa ta qarshe da zata bata daman shiga falon annin nanma sai data jinkirtawa na'ura sannan ta bata izinin shiga,ta dauke kanta ranta yana suya da wani irin fushi. Tafi qarfin ta tako gidan alhaji hamza har abada.....inda sun bata girma da martabarta da a yanzun ba shakka ita ake zuwarma haka neman gindin zama.
Tana sane da yadda mabuqata ke yawan ziyartar gidan karbar taimako a duk sati......taimakon da ta tabbatar daga fuad ake rabashi.......sai gashi ita duk yadda taso ta dinga cina farfajiyar nata gidan da mabuqata,tana raba musu kudi a envelope yadda taso abun bai samu yadda takeso ba. Bai hana taimako,amma saidai ta rubuta list na mabuqatan ya hadasu dana gidan alhaji hamza a raba musu taimakon tare.
Bata samu yin sallama ba,sai Allah ya sanya tana sanya qafafunta a falon idanun anni dake kashingide cikin lausasan sofa ya sauka a kanta.
"Ikon Allah" Anni ta furta tana miqewa daga kashingidar da tayin tana sauke qafafunta qasa idanunta akan maamah
"Da kinyi zamanki ma.....don ni ba wajenki nazo ba kaman yadda na alqawarta zuwa na na qarshe gidan nan......wajen hamza nazo" Maganar tata tazo qarshe dai dai sanda amna ke fitowa daga kitchen ta zuba abincin dare,don tace yau zaman cin abincin abban yayi dare da yawa,ba zata iya jiransa ba da wuri takeso ta kwanta.
Kallon kallo sukayi tsakanin maamah din da amna. A kallon farko ta fahimci wacece duk da wannan shine karon farko da ta fara ganin yarinyar ido da ido. Autar alhaji hamza kenan,yarinyar da ake gaya mata irin sabon dake tsakaninta da fuad......yadda take ji dashi da yadda shima yake ji da ita
"Idan har kikayi da wasa kina zaune zakiji ance 'yar gida akayi.....wannan matar zata aura masa autarta..... Kinga shikenan komai ya qarasa watsewa" Muryar hajja ta dawo mata akai cikin tattaunawar da sukayi da hajjan a dazu dazu kan hanyarsu ta dawowa gida.
"Ke amna......dubamin abbanku idan ya kammala,kice maza maza yayi baquwa"
"To" Ta fada tana ajiye plate din sannan ta miqe tana nufar qofar da zata sadata da sassan abban nasu ba tare da tabi ta ainihin farfajiyar gidan ba. Tana tafe tana waiwayen maamah,itama ta lura da hakan,sai taja wani tsaki me matuqar qarfi abinda ya sanya amna din maida kanta tana yin gaba.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 58
___________________________
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
Assalamualaikum
Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule??
Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen??
To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen.
Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki.
Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina.
Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
_________________________
Farfajiyar gidan ba kowa sai qofar dakin malam saidu da yake iya hangowa wanda yake a bude. Juyawa yayi zuwa sassan da spare din famfo dake bawa shukokin gidan ruwa yake,ya xame takalminsa,ya kuma xare agogon hannunsa ya jefa aljihu sannan ya matsa ya kunnashi. Dukkan hannayensa ya tara yana kallon saukar ruwan,sai yaji wasu kalamai suna dawo masa a ka
_"ka mutu mana......ai ba a kanka aka fara mutuwa ba,kuma ba'a kanka zaa daina ba......talauci da fatara tafi mutuwarka yimin barazana......ta kuma fi mutuwarka dagamin hankali"_
Wani abu yaji ya tsaye masa a tsakanin numfashinsa daya sanya ya cire hannayensa daga famfon. Wasu daga kalaman maamah kenan a can shekarun baya a bakin famfo tamkar irin haka,daidai sanda abban nasu yake daura alwalar sallar magariba. Takalmansa kawai ya mayar yana jin bazai iya ci gaba da xama a cikin gidan ba. Ire ire wadannan abubuwan da ba wanda ya sansu saishi,.....koda musaddiq kuwa......suna sanyashi yana jin kamar numfashinsa zai fita a wasu lokutan.
"Ko buta zaa baka ranka ya dade" Muryar malam saidu ta ratsa kunnensa sanda yake dab da qofa. Kansa kawai ya gyada masa yaja ya koma ya zauna,ba jimawa ya dawo da butar,ya karba ya fara dora alwalar a gaggauce,ya gama ya bashi ya karba ya maidata wajenta
"Zo muje malam said" Fu'ad ya fada yana ware hannun rigar sa.
Tare suka jera shida malam saidu din,duk da yadda yaso ya zuqe saboda girmamawa,me sunan malam kuma yana daga bayansu kadan ta yadda bazaiji wani abu da suke tattaunawa ba
"Magana zamuyi" Ya fada a nutsensa
"To....to" Ya fadi da hanzari
"Tambayoyi ne amma sai bayan mun idar da sallah zan saurari amsoshinsu"
"To ba laifi ai" Ya amsa masa,don ya saba lokaci lokaci dama yakan masa tambayoyi game da gidan ya kuma buqaci amsarsu.
"Waccan matar da suka shigo da hajiya meye sunanta?,wace ita a wajenta?,yaushe ka fara ganinta a gidan?,sannan kamar sau nawa ta taba zuwa ko take zuwa?,ita kadai ce koda wasu?,tana dadewa cikin gidan?,suna yawan fita tare ko aah" Yakai qarshen dukkanin tambayoyin nasa sanda suka kai bakin masallacin,don haka yayi shuru yana adduar shiga masallaci a madadin tarin tambayoyin.
"Lallai na sake yarda da maganar bokan can.....lallai akwai aiki qwarai akan yaronkin nan" Hajja ta fada duk da nata yaron da matarsa data shanya a waje kowanne cikin motarshi yana jiran fitowarta.
Labba maamah ta cije kadan sannan ta saki sanda take maida riga maras nauyi a jikinta
"Ni kuma cewa nayi miki zan qyale wannan aikin ya cimmani?,na zuba idanu naga iya gudun ruwansa na yau kawai......amma duk abinda yakai gobe zakiji kirana......a gobe nakeso mu koma a fara aikinnan"
"Ai da zafi zafi akan bugi qarfe....." Hajjan ta fadi zuciyarta na saqa mata abubuwa masu yawa.
Har bakin gate din farko ta tako tana yiwa qawartata godiya da ban gajiya. A nan suka gaisa da yahaya da matarsa. Yadda ta samesu a jere kowanne da mota yana jiran dakon fitowar hajjan ba tare daya isa yabar wajen ba ba bisa umarninta ba ya sake ninka kwadayinta itama na kaiwa wannan bigiren,sai taji kamar ta jawo wadannan kwanakin da tayi imanin suna dab da zuwa......ranar ea zata nunawa aminatu da hamza cewa ruwa ba sa'an kwando bane.....hakanan koda giwa ta fadi tafi qarfin wawa.
Haka siddan?,daga maqotaka?,ba sidi ba sadada a kama mata yara a musu muguwar mallaka?,bayan ko sanda ta tafinma suna da wayon da zasu iya kula da kansu?. Da wannan qananun mitocin ta isa cikin gida.
Ya kusa minti ashirin yana fuskantar gate din gidan,harde da hannayensa kawai yana duban qofar kwanyarsa tana digesting maganganun da sukayi da malam saidu daga hanyar masallaci zuwa dawowarsu. Baisan a wanne matsayi zai ajjiye maamah din ba.....karo na uku da wani abu ya sanya yake tunanin ANYA ITA DINCE TA HAIFESU?,anya ita din UWACE?,akwai zuciya irin ta uwaye a qirjinta kuwa?. Me yasa kullum DUNIYA itace a gabanta sama da komai?,yayi tunanin shi da kowa ma zata canza ko kuma ta canza din.....amma sai kuma akasin tunaninsu ya biyo baya.....akasin tunanin da shi kadai gani na zuciya da lura da bin takunta sannu a hankali suke karanta masa komai a kanta....karatun da idanuwa kadai sunyi kadan su iya fahimta ko ganeshi.
Hannayensa ya sauke jikinsa a mugun mace,baya jin zai iya komawa cikin gidan nan,idanma yace zai koma din abinda zai wanzu tsakaninshi da ita bame dadi bane. Ko haduwarsu na 'yan mintuna kadai ya sake wani karatun. Ya dawo lafiya?,wacce nasara ko qalubale ya riska?,duka ba damuwarta bane......damuwarta shine KUDI.....me yasa bai turo ba?. Abu guda daya da bai taba faruwa tsakaninshi da anni ko abba ba......basu taba neman anini taro ko sisi daga hannunshi ba.....a hakan take neman kudin da zata rabashi da Alhaji hamza da aminatu?,mutanen da su suka bashi RUHI na rayuwa da yake yawo a jikinsa a yanzu?.
Kansa ne yaji ya sara,sai ya sake qara azamar barin qofar gidan ya juya zuwa nasu gidan. Gidan da a baya shine gidan maqota a wajensu amma a yanzun basu da gidan daya kaishi.
Tun a gate ya sallami kowa,ya gaya musu da wuri zai kwanta don gobe zasu fita da wuri,duk da baida yaqinin goben a yadda zai tashi saboda wani nannauyan ciwon kai daya saukar masa yanzu yanzu.
Tun bai qarasa sassansa ba ya kashe duka wayoyinsa,yabi ta qofar baya don bayason kowa yasan ya shigo din ya wuce sassansa.
Bai kunna kowanne fitila na sassansa da zai bada alamar yana ciki ba,sai ya wuce a hankali kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki zuwa study room dinsa,ya tura qofar ya shiga ya maida ya rufe.
Zaune kawai yayi saman sofa idanunshi a kulle,yayi nisan nazarin da shi kansa baisan wane zare a tunanikansa zai kama ba. Abu daya ne da yafi daure masa kai da dagula masa lissafi,qoqarin da takeyi da gaske na sai ta raba tsakaninsu,indai haka ne wannan fitar tasu tana da alaqa da qudurinta.....indai haka ne kudin da take nema lallai yana da alaqa da qudurinta......indai kuma haka ne tabbas wannan BAQUWAR FUSKAR akwai tata rawar cikin mission din......duk da yasan wannan din tsohon quduri ne dake ranta.....amma dukkan alamu sun nuna ta samu MAKAMASHI.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 59
Shuru ne ya biyo baya tsakaninsu,babu wanda yace da dan uwansa komai tsakanin ita da anni din. Daga yanayin tsaiwarta da yadda take bin komai da wani irin kallo ta tabbatar ba alkhairi bane ya kawota,don haka taci gaba da abinda takeyi din ba tare data ce komai da ita ba.
Baifi minti biyu ba kacal sai ga amna ta dawo
"Yace gashi nan...." Ta bata amsa tana sake binta da kallo tamkar a tsorace,sannan ta qarasa ta dauki plate dinta ta koma kusa da annin ta naniqe ta zauna tana ci gaba da satar kallon maamah din.
Da sallama ya shigo falon cike da kamalar nan tasa dake shimfide saman fuskarsa,sanye yake da jallabiyya ruwan qasa,kansa sanye da qaramar hula tashi ka fiya naci.
Amna da anni ne suka amsa sallamar tashi,yayin da maamah ta dubeshi kadan kafin ta dauke kanta
"Mariya ce?,....bismillah......zauna mana" Ya fada yana zama kujerar dake daura data anni. Kamar tace ba zata zauna ba,to amma kuma zaman yafi kamata tayin,don tanason daga qarshe ta gasa masa maganganun da indai ya haifu zai fara janye jikinsa daga dukkan wata mu'amala ta fu'ad dama rayuwarsa gaba daya,yabar mata 'ya'yanta kamar yadda kowacce uwa keda iko da nata yaran.
"Muna lafiya.....ina fata kuma lafiyar ko?" Gyara zamanta tayi sosai tana dora qafarta daya kan daya,sannan ta saka idanunta sosai cikin nasa
"Wajenka nazo hamza" Ta fadi kanta tsaye,abinda yaja hankalin anni kenan tadan daga kai ta dubeta,sai kuma ta saukar tana son kwashe hankalinta sam sam daga kansu.
"To ai gani.....Allah yasa lafiya" Fuska ta qanqance tana dubansa idanunta a ciki.
"Al'amarinku yana bani mamaki hamza yana kuma dauremin kai.........duk duniya ban taba ganin inda ake irin haka ba sai a kanku,hankaka mai da dan wani naka?......amma mu ajjiye wannan batun......tunda kun zab lallai sai na zama maqasqanciya a gabanku akan 'ya'yana?......ba laifi don komai da ka gani a rayuwa lokaci ne.....kuma iyaka gareshi......" Ta furta qasan ranta tana hangen iya adadin lokacin da ya rage musu wanda alaqar uwa da uba zata wanzu a tsakaninsu.....da tazarar lokacin da alaqar zata juye zuwa alaqar gagarumin abokin adawar da duk duniya fuad din zai wayi gari bashi da abokin adawa irinsa. Burinta shine ta bude idanu taba tsabtsar gaba da adawa mai qarfin gaske ta qullu tsakaninsu......irin adawar da zata bawa kowa mamaki ta kuma shiga sahun tarihi......tabbas saita fanshe dukkan wani baqinciki da suma cusa mata......hakanan ba zata qyale ba sai sunyi aman duk wani da sukaci daga cikin arziqin fuad......koda kuwa wannan gidan da suke ciki yana cikin jerin sahun mallakar fu'ad din.
"Wai nikam hamza.......ban sani ba ko cikin duhu ne a sannan?......hadaka da kuma gamayya kukayi da ubansu fu'ad yayin samuwar cikinsu?,ma'ana tare kukamin cikinsu ko kuwa?" Ba alhaji hamza kibiya kadai ba,hatta anni dake zaune daga gefe ba tare da shiga shirginsu ba sai data cira kanta da sauri maganar tana dukanta
"Subhanallahi.......innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Alhj hamza ya fada zallan mamaki yana saukar masa,idanunsa akan fuskar amna wadda ta yunqura tana miqewa ba tare data tsaya daukan plate din abincin ba saboda yadda maganar ta girmimi kunnuwanta.
"Mamaki kukayi?,to ai ba abun mamaki bane duba da yadda kuka qanqame min rayuwar 'ya'ya hamza" Ta kuma fadi cikin izza ba shakka ko d'ar a cikin idanunta.
"Mariya cikin hankalinki kike kuwa?" Anni ta gaza jurewa ta fada tana kafeta da idanunta. Wurga kallonta tayi zuwa ga annin
"Kinga ina iface iface ne ko yage yage da zakiyimin wannan tambayar?"
"Shin mene marabar dambe da fada mariya?,ai hauka nau'i nau'i ne.....nakin ina kyautata zaton ta wannan fuskar yazo"
"Kamar yadda cutarwarku tazo da sigar yaudara da damfara ba.......na rantse da Allah a yau inda fu'ad yana a faqirinsa bashi da komai da tuni kun watsashi shi da dan uwansa........."
"Kaman yadda zamantowarsu halittar da zaki iya mora ta sanya kika dawo cikin rayuwarsu ba?....bayan kin watsar dasu a sannan kina zaton su din ba masu amfani bane,nauyi ne kawai a wuyanki?". Anni ta maida mata amsa ta hanyar katse numfashinta bacin rai yana fara nuna alamun tasiri cikin muryarta
"Ya isa aminatu......ban yarda ki sake cewa wani abu ba" Alhaji hamza ya fada yana daga mata hannu. Ya gama karantar akwai abubuwa masu tarin yawa a bunne cikin zuciyar maamah din,biye matan da annin zatayi shi xai bata damar furzar da maganganun da idan suka qyaleta basu tanka mata ba har ta mutu saidai ta mutu dasu a cikinta.
Dole ta ninke dubban maganganun da suke tsinkulinta a rai kawai don ta bawa abban girmansa,amma bawai don abinda take da shirin furtawa itama ya qare ba,ta kauda kai tana hadiye fushinta ba tare data sake jefa baki a maganarsu ba
"Ka gaya masa ya bini.....domin kuwa duk duniya ba wanda akace aljannarsa tana qarqashin qafarta face ni.....komin lalacewata......ka taimaka ka sakar masa mara ya rabu dani lafiya kaman yadda na tabbatar ka rabu da naka lafiya......ka shaida masa yazo ya bani kudin dana buqata a hannunsa.......bawai alfarma nake nema ba......ka gaya masa dole ne yayimin...." Tana kaiwa nan ta miqe tsam,idanunta akan anni da tayi kaman batasan da wanzuwarta a wajen ba. Taso ace annin taci gaba da ja,don tana da tarin maganganun da takeso ta amayar mata
"Wallahi duk d'an da ya hana uwarsa bacci.......shima bazai huta ba" Ta furta tana juya hankali kwance tana barin falon.
Shuru ne ya biyo baya,duk kuwa da cewa ta gama ta kuma fita daga gidan ma gaba daya
"Hasbunallahu wani'imal wakil" Alhaji hamza ya furta gauraye da wata ajiyar numfashi me nauyi idanunsa na kallon waje daya.
Baisan wanne irin abune yake dawainiya da mariya ba......baisan kuma wanne girman laifi sukayiwa rayuwarta haka da take musu kallon wasu manya manyan abokan adawarta ba. Anni batace komai ba kaman yadda shima bai buqaci tace ba,tanata qoqarin sarrafa bacin ranta da ganin ta hadiyeshi ba tare data barshi ya mata tasiri ba
"Ina muhammadu?" Alhaji hamza yayi tambayar yana duban annin
"Bansan ina yayi ba.....mun rabu dashi a dazu kan zai shiga wajenta" Ta amsa masa a taqaice. Karkacewa yayi ya ciro wayarsa daga aljihun jallabiyyarsa ya soma trying number din fuad din.
Sosai yayi nisa cikin tunani,a haka idan ka ganshi zaka dauka bacci yakeyi,saidai ba ko guda daya. Wasu mintina ne daketa wulga masa tsakanin bacci da ido biyu wanda a ciki baisan ainihin abinda yakeyi ba
A silent wayar take,amma hasken da take fitarwa ya ratsa rufaffun idanunsa a cikin duhun dakin.
Kamar bazai bude idanun nasa ba amma sai ya budesun a hankali yana saukesu akan wayar. Yayi tsammanin ya kashe duka layukan,sai a sannan ya lura guda daya ya kashe. Sunan daya gani saman wayar ya sanyashi sauke qafafunsa a hankali yana maida hankalinsa a kanta,ya miqa hannu ya daukota daga inda take ajiye yana qoqarin dagawa.
Sallama yayi amma muryarshi ta maqale,yadanyi gyaran murya sanda yajiyo muryar abban yana masa sallama
"Ina ka shiga ne?" Alhaji hamza ya tambayeshi
"Ina cikin gida abba"
"To fito......inason ganinka.....ka sameni falon anninka"
"To abba" Ya amsa masa a ladabce. Remote ya laluba ya dauko ba tare daya tashi a gun ba ya maida hasken dakin. Take yayi tarwai da haske kaman yadda ainihin dakin yake
"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla.....wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" Ya furta muryarsa can qasa,yana jinsa gaba daya ba kuzari,tun daga zuciyarsa har zuwa gangar jikinsa.
Bai wani bata lokaci ba ya sauya kayan jikinsa sannan ya wuce sassan annin. Sallama yayi hankalinsa na kaiwa fuskar anni. Tun bai zauna ba jikinsa ya bashi akwai wani abu,don ba kasafai kake ganin fuskar annin a haka ba. A nutse ya qarasa shiga ciki,kai tsaye kuma ya nufi inda Alhaji hamza yake,wanda bai motsa ba daga wajen tunda maamah din ta fita ta barsu.
"Bismillah.....zauna" Alhaji hamza din ya masa nuni da kujerar dake kusa dashi. Sanda ya zauna din ita kuma anni ta miqe da zummar barin wajen,abban ya maida dubanshi kanta
"Zama kema zakiyi......ina zakije?" Duban abban tayi,kaman zatayi magana sai kuma ta fasa,ta koma ta zauna ba tare data sake cewa komai ba.
"Muhammadu" Abba ya kira sunanshi kai tsaye,abinda ba kasafai hakan ke kasancewa ba. Mamakin ya hanashi amsawa saidai ya daga kai kawai yana duban abban.
"Muhammadu ya ina yabonka sallah zaka kasa alwala?" Abban ya sake fada idanunsa still akan fu'ad din,tausayinsa kuma yana ratsa zuciyar abban.
"Abba....." Fu'ad ya motsa labbansa a hankali da zummar yin magana
"Me dame mariya tace maka tana da buqata wanda bakayi mata ba?" Ya masa tambayar Kai tsaye don sauqaqe masa wahalar tunani.
"Abba.....ba wani nauyi ko haqqi daya kamata na bawa maamah wanda bana bata shi......bana tunanin akwai wani abu da ya zama nauyi ko haqqi da ubangiji ya doramin wanda na gaza dauke mata shi". Har cikin zuciyarsa abban ya gamsu da wannan,saboda shi kansa ganau ne bawai jiyau ba akan hakan
"Na sani Muhammadu......amma don me yasa idan tana da buqatar kudi daga hannunka kake hana mata?". Sam baima kawo wannan zancan bane,sai ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana sauke kanshi qasa.
Rashin amsawarsa ya bawa abba amsar tambayarshi
"Me yasa kusan ko yaushe matsalarka da ita akan tana neman kudi ne ka hanata?,bayan Allah yayi maka wadatar da zaka iya bata ko nawa ne Muhammadu?" Ya qarashe maganar ta sigar tambaya idanunsa a kanshi,can qasan ransa yana mamakin abinda ke kawo musu matsala akan abinda yasan ya jima da fin qarfinsa. Km
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 60
"Ka sani cewa......duk d'a aljannarsa tana qarqashin qafar iyayensa?,kuma haramunne jayayya dasu bare su buqaci abu aqi ayi musu?"
"Na sani abba.......amma bazan iya bawa maamah ko sisi ba". Sosai maganar ta bawa abban mamaki,har anni dake zaune daga gefe itama ta daga kai tana kalleshi
"Akwai abubuwa masu yawan da baka gama saninsu ba abba akan maamah......akwai boyayyun sirrikan dana ajewa cikina abba.......akwai wasu abubuwa masu yawa wadanda ba zasu fadu ba......amma koma meye cinta shanta lafiyarta dama suturarta wani abu ne da bazan taba iya hana mata su ba ko don albarkacin haihuwa da Allah ya bata........amma batun kudi abba........bazan iya bata ba"
"Dalili?,dalili nakeso naji Muhammadu" Abba ya sake tambaya cikin tsananin mamaki. Bai taba umartarsa da abu ba ya saba.....sai gashi s yau yana qoqarin bijire masa.......tabbacin akwai wani qaqqarfan dalili da kuma hujja kenan
"Abba...." Ya kirayi sunansa yana jin nauyin abinda zai furta din. Shurunsa ba abinda zai harfa tsakaninsa dashi sai gurguwar fahimta,bayaninsa din kuma bawai abu bane me dadin ji ko sauraro ba.
"Kasani Muhammadu.....koda baka bayar ba ni zan dauka na bata da kaina"
"Zan bayar abba.....zan bata amma bawai don zuciyata tana so ba......"
"Zuwa yaushe kenan?" Ya sake tambayar sa
"Zan yiwa sadiq magana,zai saka mata"
"Kirashi yanzu yanzu" Ya sake bashi umarni kai tsaye. Dole ya fidda waya ya turawa sadiq din saqon umarnin fidda kudaden,sannan ya aje wayar yana duban abban
"Zai sanya mata in sha Allahu". Ajiyar zuciya abban ya sauke. Shi kansa yasan akwai qalubale masu tarin yawa cikin rayuwarsa,to amma ko meye zaiyi yana yine saboda kyautatuwar rayuwa da kuma gobensu.
Kamar yadda ya saba lokaci bayan lokaci baya gajiya da yi musu nasiha dukkaninsu,yanzunma nasihar ce dai yayi masa.
Haka kawai sanda yake barin falon yaji hankalinsa bai kwanta ba. Muddin maamah tazo gidan to ya tabbatar akwai wani abu maras dadi daya biyo baya. Ko mene kuma ya farun yasan babu me gaya masa cikin gidan,daga amna sai musaddiq wanda baya gidan.
Yana takawa a farfajiyar gidan yana lalubar number amna din. Bugu daya ta daga tana amsa sallama a nutse
"Fito waje inason magana dake"
"To hamma" Ta amsa masa tana sauke plate din hannunta data gagara cin abincin ciki. Wayar tabi da kallo har yanzu muryar matar tana amsa kuwwa a kunnenta. Maganganunta sun girmi kunnuwanta,batasan komai a kanta ba amma tana ganin rashin kirki qarara daga dukkan wani motsi nata.
A tsaye ta sameshi idanunsa saman qananun shukokin dake bawa wajen iska me kyau da yanayi me dadi
"Zauna" Yace da ita yana nuna mata kujerar dake gabansa tare da qoqarin karantar fuskarta. Ba musu din ta zauna tana jin jikinta yana qara sanyaya daga kallon da taga yana yi mata
"Akwai baquwar da tazo gidan nan dazun?" Ya tambayeta yana kallon tsakiyar idanunta. Kallonsa itama tayi sai tayi qasa da kanta tana tuna gargadin da anni tayi mata
"Ba ruwanki da abinda tazo ta fadi,wannan ba abinda ya shafeki bane.....ba'a gaban kowa kuma akayi ba saike kadai...... Kada na soma jin zancan nan ya fita" Gargadin annin kenan bayan ta bar falon ta isketa a kitchen.
"Ehnnnn......kina nan sanda ta shigo na tabbatar......akwai wasu abubuwa data cewa anni da abba?" Ya sake tambayarta yana kallon fuskarta. Ba zata iya kallonsa kuma tayi masa qarya ba......hakanan ba zata iya saba maganar anni ba,don haka ta zabi sunkuyar da kanta ta kuma girgiza masa kai. Qaramin murmushi ne ya subuce masa wanda ba komai cikinsa sai bacin rai
"When kika fara yiwa hamma qarya amna?" Tambayar tasa saita rudata gaba daya,taji bata da sauran zabi illa ta shaida masa gaskiya.
Tambayar farkon data jefawa abban ita ta sanya fuad jan kujera shima ya zauna wani nauyi yana saukar masa. Ya ilahi.....wannan wacce irin jarabawa ce?,me yasa UWA take jin tasu jarabawar rayuwar?.
"Tashi kije" Ya bata umarnin daya sanyata miqewa da sauri tana barin wajen.
Tafin hannunsa ya sanya yadan daki goshinsa yana lumshe ido. A mizanin hankali da tunani da sanin ya kamata......yayi zaton maamah zata kasance ne cikin sahun farko na mutanen da ko kansu sukan sanya a gaba suka yanka ba zata ce komai ba.
****A hankali take takawa cikin layin zuciyarta na bugawa a hankali a hankali. Bugun zuciyartata ne batasan meye ainihin dalilin faruwarsa ba. Tsoron ganinsa takeyi ko kuma shauqin ganin nasa?.
Tun daga wancan ranar daya aike mata wasiqa ta qarshe bata sake jinsa ko kuma ganin motsinsa ba,har kawo yau da suke shirin cinye satin gab daya a kuma shiga sabon sati.
"Assalamu alaikum" Sautin sallamar daya sanya zuciyarta wani irinn bugawa ta ba zata,mamaki kuma da tsoro suka hanata amsawa saboda yadda taji alamun muryarta a shaqe take. Kasa waiwayawa tayi har zuwa sanda ya tako yana cimmata a inda take,ya zagaya kuma yana yiwa kansa matsaya a gabanta dab da ita. Yanayin kallon daya rutsata dashi ya hanata janyewa baya kaman yadda takeyi a duk sanda ya tsaya kusa da ita kamar haka
"Banga alamar kinyi kewata ba......inacan soyayyarki zata kasheni?" Ya furta yana karyar da wuya tare da komawa kalar tausayi ainun.
Idanunta ta fiddo waje tana dubansa
"Me ya sameka?" Ta samu bakinta da subucewa gami da tambayarsa kai tsaye.
"Ciwon sonki" Ya fada wani mayaudarin murmushi yana subuce masa. Nasararsa yake hange muraran daga idanun yarinyar,ya tabbatar yana dab da cika burinsa......yana kuma gab da daukan fansa.
Wata ajiyar zuciya taja tana sauke numfashi
"Bakiyi kewata ba huda sam sam" Ya sake fadi yana kalmashe wuya idanunsa cikin nata,yanason ya sake dasa mata dafin da zaiyi wahalar gogewa daga ranta. Yanason ya cimmata sosai,ya kuma nutsar da ita cikin tafkin qaunarsa fiye da yadda yayarta ta jefa masa qugiyar da har yanzu ya gaza zameta daga ruhinsa. Baya jin akwai wata mace da zata iya kashe masa qishirwarta. A kanta yakejin komai kuma ita kadai zata iya sama masa da wannan nutsuwar.
Saidai kuma ya karanci hakan wani abu ne da bazai taba samunsa ba.....don haka gwara yayi daukan fansan da zata gwammace bashi rayuwarta yayi yadda yaga dama da ita.
"Don Allah me kyau kice wani abu mana" Ya fada yana marairaice mata
"Nayi kewarka mana....." Ta samu kanta da furtawa. Yadda ya fidda idanu yana gwada mata mamakinsa ya sanyata jin kunya gami da mamakin kanta. Wani abu ne da yake faruwa da ita karo na farko a rayuwarta da bata taba tunanin zuwansa a nan kusa ba
"Da gaske kike?" Ya fadi har yanzu idanunsa a waje,sai tasa hannunta kawai ta lullube fuskarta dasu tana sakin qaramin murmushi,abinda ya sake fidda kamanninta sosai da sabreen.
"Don Allah yau daya ki bani aron mintunanki biyar" Ya fadi yana hade hannayensa waje guda. Mintunan biyar din da yake sanya ran a cikinsu zai qarasa dashen da ya dauko.
"Don Allah karkice aah,bazan sake neman wata alfarma ba daga wajenki ba daga wannan" Ya sake maganar yana qara marairaicewa da kyau.
Rabuwa biyu zuciyarta tayi,wani sashe na zuciyar tata yana cewa ta bashi damar.......yayin da wani sashen kuma yake cike da tsoro,tsoron da kusan kullum a cikinsa take.
Batasan yadda akayi ya shammaci rayuwarta har ta soma sabo dashi take kuma jin wasu baqin abubuwa a kansa ba,irin abinda bata taba jinsa akan kowa ba,koda kuwa cikin duniyar mafarkinta ko kuma hasashe.
Cikin qasa da mintuna biyar din daya dauka ya qarasa wargaza duk wani tunani nata. Sanda take takawa zuwa gida dauke da kalamansa masu nauyi.......ji ta dinga yi duniyar tamkar ita daya ce mace a ciki......dama haka zukatan dake da masu furta musu kalamai masu dadi sukeji?. Yau daya ta gasgata kalaman daya taba furta mata
"Har yanxu ke yarinya ce.....ba zakisan dadin rayuwa ba sai kinso kin kuma bada dama an soki......kowacce rai tana da buqatar wanda zai sota.....a lokacinne zaki karanci martaba da darajarki da kuma zamowarki cikakkiyar mace duk da qarancin shekarunki.
Hannunta takai tana shafa qaramar wayar daya bata wadda ke dauke da layi da kuma number dinsa. Ita kanta batasan adadin yawan roqon da yayi mata ba kafin ya karya zuciyarta ta aminta da karbar wayar ba
"Zanyi tafiya me nisan xango,a qalla zanyi watanni biyu ban saki a idanuna ba......bazan iya jurar rashin ganinki ba......" Kai take girgizawa a tsorace
"Yaa sabreen......"
"Ita kike tsoro?,zanje na nema dama a wajenta,kada ta rabani da abinda raina yakeso,zan roqeta ta barni na dinga jin muryarki....."
"Baka da hank......" Taji bakinta ya subuce da fadi.....sai kuma ta yiwa kanta waigi daga furta abinda tayi niyyar fada din a mugun tsorace. Yaa sabreen din da kullum kwanan duniya cikin kwatanta mata ta kaucewa sauraren kowanne d'a namiji har sai ta isa minzali?,yaa sabreen din da bata lamuncewa kowa mu'amala dasu ba komai kusancin dake tsakaninsu?,shine a yanzun yake neman kai kansa da kansa gabanta?.
"Huda......zan iya komai a kanki.....zan kuma iya komai saboda ke,ni kadai nasan zafin sonki da nakeji a raina.....don Allah ki karbi wayar nan......muryarki kawai xanji,daga gaisuwa idan kinso ki kashe wayar" . Ido ta zuba masa a mamakance jikinta kuma yana yin sanyi,wai dama haka soyayyar take?. Qwallar data gani shimfide a idanunsa suka karya duk wani qwarin gwiwa nata,kafiya da kuma dagiya,ta karbi wayar ba tare da tana da masaniyar ta karbi shiryayyen abu da zai wargaza musu rayuwa ba dukkaninsu......
Sake dafa wayar tayi sosai,qasan ranta tana jin qarin tausayinsa yadda yake faman marairaice mata,da alama soyayya ba qaramin kamu tayi masa ba. Dama wannan itace soyayyar?,dama haka akeji?,dama haka take iya canza mutum daga ainihin yadda ka sanshi?.
Ita kanta mamakin kanta takeyi yadda ya iya canzata gaba daya cikin qanqanin lokaci haka,amma kuma hakan fa yana nufin nan da shekara daya ko biyu kenan aure zatayi?. Tayi aure kuma yana nufin tabar yaa sabreen?,tabar nadra tabar haneefa?.
To wai ta yaya ma zata fuskanci yaa sabreen din da shi?,tace mata me?,bayan tsahon tasowarta idanunta basu taba gwada mata yaa sabreen din tana soyayya ba da kowa ma ballantana aure?,kullum zancanta yadda zasuyi zuzzurfan karatu kuma su zama wasu a gaba......wannan qudurin zai cika kuwa?.
Eh.... Wata zuciyar ta bata amsa daga wani gefan
"Shi karatu ai baya hana aure......kaman yadda aure baya hana karatu" Ta tuna da wata hira data jiyo 'yammatan ajinsu sunayi,abinda ya sanyata sakin murmushi kenan dai dai sanda take sanya qafarta cikin falon nasu.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 61
Dai dai lokacin sabreen din ke aje wayar mashkur wanda ya sanyata a lissafin yadda komai zaya kasance.
Shine mutum na farko daya matsanta mata da son ta bishi wani guri wajen garinsu. Da fari yaso ace dubai suka wuce,saidai tayi duk wata hikima tata ta kansile tafiyar da a baya ya tayar dayi musu shirinta gadan gadan. Baisan wace ainihin sabreen ba.....shi yasa ya gaza fahimtar dukka wadannan shirmen basa gabanta. Taqi kadan take jira ta yasar da qwallon mangwaro ta huta da quda.
A matse take.....kuma cikin matuqar buqatar kudaden saboda aikin ayshatu data tabbatar gab zuciyarta take ga kaiwa ga matakin da zata daina moruwa. Ko a jiya data ziyarci gidan jikinta yayi sanyi.......ta kuma sare sosai da yanayin jikin nata,har sun fidda rai da ita a wunin ranar,amma da yake shi rai idan yana da sauran shan ruwanshi a gaba to tabbas fa sai ya sha.
Motsin shigowarta ba tare da sallama ba ya sanyata daga fararen idanunta ta zubesu a kanta.
"Meye hakan kuma yau?" Tayi mata tambayar tana duban fuskarta wani abu yana darsuwa a ranta.
Fuskarta da fara'a ta juya tana fadin
"Au.......mantawa nayi wallahi" Saita tsaya daga qofar tana yin sallamar kamar yadda suka saba.
Sai data danyi jim kadan sannan ta amsa mata,ta bude labulen ta shigo,sabreen ta bita da kallo can qsan rabta wani abu yana kai kawo
"Sannu da gida" Ta fada tana nufar hanyar dakinsu,don sam ba'a sake take ba,Allah Allah take ta samu waje ta yiwa wayartata ajiya me kyau. Tasan halin yaa sabreen din qwarai da gaske,tana da mugun fikira da saurin dago wani abu dake a boye,a yanzun haka kallonta da takeyi din gani takeyi kaman tana kallon wayar ne tarwai bisa idanunta.
Bata iya amsa mata ba,tadai bita da kallo har zuwa sanda ta wuce dakin. Janye dubanta tayi daga bakin qofar dakin tana sauke numfashi. Bataso taji kokwanto ko shakka ko kadan akan 'yaruwarta......to amma haka kawai jikinta yake bata wani yanayi daban wanda bata saba jinsa ba akan huda din.
Duk da tasan ba kowa a dakin amma hakan bai hanata kallon gabas da yamma hagu da dama na dakin ba kafin ta ciro wayar daga aljihunta,ta kuma daga katifarsu daidai inda tafi kwanciya ta jefa wayar. Tana dagowa sabreen na daga labulen dakin ta shigo hade da sallama.
Wani mummunar faduwa gabanta yayi,ta amsa da sauri tana kuma waiwayawa,sai suka hada idanu da ita. Tsoronta ya qaru,ta dinga ji kamar ta ganta ne sanda take ajiyar.
Kanta da taga ta dauke shine abinda ya bata relief,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya ta fara fidda uniform din jikinta.
"Huda" Tayi kiran sunanta sanda ta zauna bakin gadonta.
"Na'am" Ta sake amsa mata tana sakin rigar uniform dinta data kama zata fidda.
Idanunta ta zube mata,kafin tace komai haneefa da nadra sun shigo,wanda already sun rigata dawowa harma sun sauya uniform dinsu zuwa kayan gida
"Gashi yaa" Nadra ta fada tana miqa mata Leda
"Kuje falo a samu plate a juye yasha iska,gani nan fitowa" Ta amsa musu tana binsu da idanu har suka fice kafin ta maida dubanta ga huda
"Zo nan huda" Ta umarceta tana ci gaba da karantarta. Ba musu ta ajjiye dan kwalin hannunta sannan ta tako ta zauna a inda sabreen din tayi mata nuni.
Zuba mata idanu tayi tamkar yau ta fara ganin fuskarta,abinda ya sake sanya ma huda fargaba da shakku
"Kinsan na tsani nayi tambayar meke faruwa?,akwai matsala?......a bani amsa da babu komai....bayan kuma da matsalar.....akwai kuma abinda yake faruwar" Ta qarashe maganar idanunta har yanzu cikin na hudan.
Har cikin qashinta taji tambayar tata tamkar taba hango komai tar tar,saidai kuma wani sashe na maganarsa ya bata qwarin gwiwa tare da hikimar kaucewar tuhumarta
"Tunda har akwai tsoron yaa sabreen a ranki,bai kamata ki bari a yanzu tasan muna tare ba,har sai mun sake shaquwa da junanmu.....ta yadda koda ta tashi rabamu,tausayin yadda mukeson junanmu zai sanyata ta haqura......akwai lokacin da na ware da zamu sanar mata......kinga koda kuwa na girme mata nesa ba kusa ba.....amma dole nayi mata biyayya kema na tayaki yi mata biyayya ko ba haka ba?" Wasu daga cikin kalamansa da a yau suka sake sanyawa ta sake masa. Yadda ya mutunta mata yayar da duk duniya bata da abu mafi girman daraja irinsa.....bata jin zata kasa sonshi a ranta.
"Me yake faruwa huda......kome qanqantarsa kada ki boyemin" Ta furta tana kallonta.
Kanta ta girgiza tana narke fuskarta
"Me kika gani yaa sabreen......?" Itama kanta ta kada zuwa gefe guda gami da cije lips dinta na qasa,daga qasan zuciyarta ana gaya mata lallai akwai wani abu da ba dai dai ba.
"Canji nake hangowa dan kadan huda......wanda kowanne canji cikin rayuwa daga kadan kadan yake farawa" Ta amsa mata kai tsaye ba wani kwana kwana.
Zama tayi sosai hudan tana dubanta
"Ba komai yaa sabreen fa.....idan ma akwai din ni bazan boye miki ba"
"Kin tabbata?" Ta jefa mata tambayar da wani nannauyan sauti dake tabbatar mata tambayar me girma ce dake dauke da tarin fassarori da ma'anoni.
Kalamansa sukaci gaba da bata confidence,har ta daga kai cikin tabbatarwa
"Na tabbatar" Ido ta lumshe tana gyada kai
"Shikenan" Sai ta miqe itama tana daukar daya wayar tata wadda ita ta shigo da ita dakin.
Mika'il takeson tabowa.......tana da buqatar fara kawar dashi daga layin,koda kudin visa passport da bill na asibitin ta samu daga gareshi,idanma so samu ne ya zamana komai ya fita daga jikinsa,ta yadda duk abinda zai samu daga bangaren mashkur din zai zamana tamkar ribar qafa ce.
Akwai abubuwa da yawa da yake list dinta wannan karon da takeson yi,wanda kuma yana da buqatar muquden kudade. Akwai mutane da yawa data kwana biyu bata gansu ba,tanason a wannan karon ta jiqa kowa yadda ya kamata.
Kaman yadda ta saba kebe kanta a dukkan lokaci irin haka da ya shafeta. Yanzunma can farfajiyar gidansu ta wuce bayan ta rabbatar ta sallamesu da dukkan abinda ya kamata. Me home work yana yi,me bita da hada haddar da zaya bayar a islamiyya ma yana nashi.
JIB ta kira,kamar ko yaushe layinta layine na musamman da ita kadai ke kiransa dashi,hakan ya sanya baya missing call,don muddin yaga kiran yasan akwai abu me muhimmanci.
Gaisuwar ban girma yayi mata kaman yadda suka saba sannan suka shiga tattaunawa kai tsaye akan ayyukan da takeso ta gama dasu
"Ka sani,ba kasafai nakeson dadewa da mutum ba.....nafison nayi na gama a wuce gurin ya sake sabon lale.....ciwon aishatu shine abinda yafi dagamin hankali najeeb......banason sanadiyyar wani ayshatu ta rasa ranta......inason sama mata lafiya tare da mata tanadin rayuwa da zata manta abinda ake kira da tsanani talauci ko wahala". Can qasan ransa yake hadiye wani abu,yana cika da mamakinta ako yaushe,tana yawan sanya ranta da kanta a risk,bawai don saboda jin dadinta ko walwalarta ba......aah......tana yin komai ne kawai don jin dadin wasu.
"Zamu kammala da izinin Allah......amma a wannan karon indai komai yayi kyau,adadin kudaden an samesu daidai ya kamata kema ki inganta rayuwarki sama da yadda kike a yanzu". Dan qaramin murmushi ne ya subuce mata,har jib yana iya jiyo sautinsa kadan
"JIB.....kune a gabana......har yanzu inajin mutanen dake tare dani ban kaisu matakin daya dace sukai ba". Zuciyarsa ce ta karye girmanta na dada qaruwa a ranshi
"Ko yanzun ma me ya rage?,kinyi mana komai,tunda muna iya tsaiwa da qafafunmu......mu ya kamata mu tallafeki kikai inda ya dace kikai din.....kusan dukkanmy burinmu ki samu nagartaccen miji......"
"Mubar wannan maganar jib yanzu" Ta katse numfashinsa. Murmushi kadan ya saki,shima kansa yasan ya taba inda batason aje. Sau tari yakanyi mata uzuri......koda shine yaga abinda ta gani,yaji kuma abinda taji ba shakka iya hukuncin da zaima rayuwarsa shine nisantar kowacce diya mace,saidai kallo daga nesa,indai ba qaddara me qarfi da zata hada tarayyarsu guri guda ba.
"Zakibi mashkur abuja bayan mun gama da mika'il" Ya furta a nutse bayan shurun daya gifta a tsakani na wasu 'yan mintuna
".....banason tafiyar nan jib"
"Itace hanya guda daya mafi sauqi da zamu kammala komai hankalinmu kwance......na sani baki taba bin kowa ko ina ba......amma a yanzun zakije,na miki alqawarin ba abinda zai faru,zan baki kariya da support harki dawo,zan bi bayanku idan ta kama......kwana daya tal zaki bani zan kammala aikinsa.....mashkur din nada tsananin wayo fiye da yadda kike tunani......amma kuma kinsan kutsa kai asusun mika'il yafi na mashkur hadari da kuma tsauraran matakai da sai an masa shiri na gasken gaske?" Shuru tayi tana son fasa maganganunsa daya bata su a cure. Kanta har ya soma dan hargitsewa,sai ta gyara zamanta kadan tana cewa
"Ka rudar dani jib......mashkur nada wayon da lallai sai an bishi qafa da qafa kafin cimma nasara......mika'il sassauqan wayo ne dashi......amma nasu account din yana tattare da tsaro sosai haka ne?"
"Exactly boss lady" Ya fada yanason jefa raha cikin zancan. Ya jefawa fuskarta murmushi kadan kuwa,sai taja dan qaramin tsaki
"A ajjiye wasa jib.....na soma gajiyawa da wadannan hadarurukan......inason muyi babban aikin da zan huta nima hakanan na kula da rayukan dake gabana da kyau"
"Haka nakeso miki nima......bari na qara miki wani bayani kadan......mika'il yana riqe da ragamar babban account din dake mallakin wani kamfanin sarrafa diamond......kamfani ne ne matuqar qarfin jari da huldodin kasuwanci da qasashe daban daban.......kusan rabin kudin wannan kamfanin asusunsa mika'il yana da access dashi.....hakanan duk wani kudi da zai shiga ko ya fita yana da access da hakan.....a bincikena na lura yana wadaqa da kudin yadda yakeso,saidai kuma yana bi ta hanyar lura da saka tsantseni ta yadda ba lallai a gane hakan ba,saboda mahaukaciyar riba da matsiyatan manya manyan kudaden da kamfanin ke samu a kowacce rana....."
"Matsiyata.....manya manya?" Ta jefawa jib tambayar. Qaramar dariya ya saki
"Sorry......maqudan kudade"
"Okay......naji kana amfani da wasu kalmomi ne.....eheeen......kaga kenan komai zaizo mana akan daidai?"
"Haka nake tunani......amma ki bani kwana uku,zan duba yadda zamu kutsa cikin asusun.....amma shima dole ku hadu a ranar Koda na awa daya zuwa mintuna talatinne......ki sassauta riqon tsaurinki kiyi kaman kin sakar masa komai....."
"Mtseewww....ya isa don Allah" Ta dakatar dashi,don zuwa yanzun abubuwan sun fara barin kanta,tana ji kawai lokaci ya tunkarota da zata maida kai sosai ga 'yan uwanta. Dukkansu girma suke qara yi,kuma suna da buqatar attention dinta sosai fiye da wanda take basu a baya.
Jib na 'yar dariya yace mata
"Shikenan......cikin kwanaki ukun zaki iya jina koda wanne lokaci,kibar wayar a bude,ki kuma fara shirin zuwa abujan.....nima zanyi nawa shirin"
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 62
"Yayi" Ta amsa masa a taqaice tana katse kiran.
Shuru kawai tayi tana jin yadda iska ke kai kawo a farfajiyar wajen. Yadda iskar ke kadawa sai take jin kamar kwatankwacin yadda tata rayuwar ke garawa kenan,daga hagu zuwa dama,daga dai dai zuwa rashin daidai,amma a yanzun cikin ranta takejin lokaci yayi da zata tsaida komai.....ko a iya haka ta tabbatar tayi qwarin da rayuwarsu ba zata tagayyara ba.
Tunda ta tabbatar ta fita zuwa farfajiyar gidan ta rufe qur'aninta,ta kuma miqe da hanzari ta wuce zuwa cikin dakinsu.
Cikin mintuna qalilan ya cire dari darin da take na amsa wayarsa da takeyi cikin dakin. Tun tana a tsaye tana kai kawo da kuma leqe tsakanin labulayen dakin har ta koma ta zauna sosai a gefen gadon tana sauraren kalamansa dake da wani irin dadi suke kuma sake samun matsugunni me kyau a zuciyarta.
Yadda dukka kalamansa suke a tsaftace,ba wani kalma ko furuci maras kyau ya sanya take sake jinsa sosai cikin ranta,wani bangaren na zuciyarta kuma yana yabawa kamalarsa da kamewarsa.
Ba wani abu me muhimmanci da zaman zaiyi mata,don haka ta yanke duka tunanin tana miqewa daga inda take din tana nufar cikin gida don komawa dakinsu.
Tun daga nesa kadan dab da qofar da zata sadaka da ainihin tsakar gidansu ta hangi hadiyyan. Ta ganta sarai zance takeyi,wanda dama takanyi din lokaci bayan lokaci.
So samu tabi ta wata hanyar da bazata hada numfashi da ita ba,to amma kuma babu hanyar,saidai tabi zabi guda daya daya rage mata,ta koma ta zauna ta jirata har ta gama zancan tabar wajen. Wannan abunne kuma takejin ba zata iya ba,duk abinda ta niyyaci ko nufaci yi ba kasafai take bari dalilin wani ko wata ya sanyata ta juya da baya ba.
Tunda ta doso gurin ta fuskanci hankalinsa ya dauku a kanta. Ba baqon abu bane a wajenta saurin gane motsi ko manufar d'a namiji a kanta daga kallo daya tak. Dauke hankalinta da idanunta tayi daga wajen kamar bata san da zamansu ba tana wucewa ciki.
"Wannan 'yar gidanku ce itama kenan?" Ya maida hankalinsa ga hadiyya yana tambayarta wadda tuntuni idanunta suna a kanshi,cikin wani irin banzan kallo da bacin ran yadda yake kallon sabreen din
"Eh 'yar nan dince.....sai akayi yaya kuma?" Ta bashi amsa a matuqar fusace har sabreen dake gab da wucewa tana ita jiyota.
Kanta ta girgiza kawai tana sakin siririn murmushin nan nata maras sauti me dauke da tarin ma'anoni masu yawa. Itakam daga hadiyya har dukkan wani gajan baqo da zayazo wajenta bata tunanin akwai wanda ya isheta kallo a cikinsu.
"Ina kuma hudan?" Sabreen ta tambaya tana kallon sararin da tabar hudan a zaune kafin fitarta
"Ta shiga daki" Haneefa ta bata amsa. Labulen daya sakaya qofar shiga dakin tabi da kallo
"Daki kuma?,me takeyi a ciki?"
"Ban sani ba wallahi.....naga dai ta shige" Nadra da aka miqawa tambayar ta amsawa sabreen cikin rashin taqamaimen amsa
"Tun yaushe ta shiga din?" Ta sake tambayar nadra wannan karon qasa qasa.
"Baki jima da fita ba" Ta bata amsa itama da yanayin yadda tayi mata tambayar. Bata son saka ko darsa wani abu a ransu,don haka tadan sake rantabrana kallon nadra
"Rufe littafin data bari a bude din" Batayi gaggawar shiga dakin ba don kada ta barwa zuciyar yaran wani hasashe,saita koma ta bude fridge ta dauko ruwa,ta qarasa gaban first aid box dinsu dake ajiye cikin falon t dauki paracetamol ta taka zuwa dakin.
Daidai sanda ta shaqi wani sassanyan numfashi daya cika fal da farinciki da kuma shauqin soyyayya,daidai lokacin ta daga labulen dakin tana takowa zuwa ciki.
Mutuwar kwance tayi sanda idanunta suka ga shigowarta,sai ta kasa ci gaba da maganar da taso ci gaba da yi. Tana iya jinsa yana cewa
"Hellooo.....my love.....hello" Amma ta kasa kowanne motsi. Duk sautin maganarsa qwaya daya ji takeyi kamar zata saki fitsari,don tana ganin yadda sabreen din ke matsowa tsaf zata iya jin sautinsa.
"Me kikeyi a kwance bayan sallar magariba?.....kuma na barku ne kuna karatu?" Ta mata tambayar tana kafeta da idanu,gami da zama saman drawer dake tsakanin gadajen nasu. Shuru yayi daga inda yake zaune yana bin sakannin da suka kwashe da ita akan waya suna qara gudu,yana kuma sauraren sautin muryar sabreen dake ratsowa ta cikin wayar zuwa kunnuwansa tare da sake tuna masa abubuwa masu yawa da suka shude tsakaninshi da ita.
Numfashi taja ta sauke,lokaci daya yadda zata sauya daga ainihin yanayinta yazo mata,saita bata fuska
"Banajin dadi ne". Inda hankalinta cikin jikinta yake a lokacin ba shakka babu abinda zai hanata jiyo sautin fitar murmushinsa.
Ko iya hakan yana gwada masa samuwar matakin nasara daga gareshi. Ta yadda ya bibiyi diddigin rayuwarsu.....a yadda bincike ya fito masa.....basa iya boye mata komai.....komai girman laifinsu ko gaskiyarsu.....komai tsanani ko maslaharsu.....ba wani abu da suke iya lullube mata shi,yau gashi ya fara taka matakin nasara......ta koya qarya saboda shi.
"Me yake damunki haka nan da nan?" Cikin qwarewa wajen iya bankado abinda ke lullube ta tambayeta. Tambayar data sanyashi jingina bayansa da kujera yana jiran jin amsa ta biyu
"Kaina ne yake ciwo" Sai ya tsinci muryar sabreen din tana bada amsar da hudan ce ya kamata aji haka daga bakinta.
Yadda ta bada amsar ya sanya huda daukewar numfashi daga jikinta na wucin gadi,tare da sanya Naseer tattara hankalinsa akan wayar,kadan kadan fargabar kada ya zamana ta gano meke lullube tana son saukar masa.
"Ga magani tashi kisha" Ta sake cewa da huda tana miqa mata kofin ruwan dake hannunta tare da satches na maganin.
Ruwan da maganin duka tabi da kallo,ta fara motsawa kadan sannan ta miqe da sauri ta zauna tana sakin wayar. Santsin pillow din ya sanya ta zame ta kuma sulale ta sauka a gefen cinyarta saita matsa kadan tana qarasa danneta.
Ci gaba tayi da dubanta har zuwa sanda ta balla maganin tasha,sai ta miqa hannu ta karbi rayuwar ruwan da maganin itama ta balla ta sanya a bakinta tabi da ruwa
"Ba abu mafi sauqin fade irin ciwon kai.....amma ki sani,yawan kiran sunansa yana iya jawoshi koda babu shi a wajen" Ta fadi tana qarasa sauke idonta a kanta.
Tsoro da fargaba ya sake cikata,saita lumshe idonta tana son dasa gaskiyarta a zuciyarta
"Nima zamana kenan na jishi ya saukar min,na dauka nadan lokaci ne xai sauka idan na kwanta"
"Allah ya sawwaqe" Ta fada a taqaice tana takawa a hankali hadi da ficewa daga dakin.
Wata ajiyar zuciya ta sauke tana fidda idanunta waje,tana iya jin yadda bugun zuciyarta ke kai kawo wanda ta tabbata tsoro razani da kuma firgici ne ya haifar mata dasu.
*****Tsakanin asabar da kuma lahadin yana da isashe lokacin da zaiyi shirin komawa bakin ayyukansa zuwa litinin,wannan ya sanyashi maido da dukan ayyukansa da suka tsaya sakamakon tafiyar da yayi.
Shi kansa yasan satin da zasu shiga din ba satin zama bane,babu hutu sam a tattare dashi. Aikine me yawan gaske,don bayajin zai zauna ya huta har sai yakai ga gacin kammala komai ya kuma bude kamfanin da a yanzu shine cikar burinsa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 63
Sassanyan yammaci ne dake bada wata irin iska me dadin shaqa da samar da nutsuwa ga zukata,hakan ya sanya zaman wajen yayi masa dadi ,wanda tun bayan sallar azahar ya zauna a nan din. Yau din zama sukayi sosai da mu'allim,wanda shi yake kula da bangaren masu buqata ta musamman da kuma neman taimako. Ya karba list na mutane masu yawa,ciki harda list din anni dana maamah wanda ya jima yana kallonshi.
Sunaye na mutane barkatai,wanda yafi kyautata zaton an shirya sunan ne kawai an kuma shigar. Ya karba takardar da zummar zai duba din,don hatta da numbers na wayoyinsu dake a jiki kallo daya yayi musu yaji sunfi masa kama da lambobin bogi.
A yanzun ya gama shigar da komai cikin laptop dinsa da kusan zaiyi wahala ka ganshi ba ita. Tana dauke da muhimman bayanansa da kuma sirrika sosai a ciki.
A yanzu da yake zaune yana karbar kira ta kai tsaye ta cikin system dinsa. Video call ne da daya daga cikin kamfanin narka gold da wankeshi daga qasar china,farouq ya tako yana isowa farfajiyar.
Kujera yaja ya zauna,sannan ya fidda wayarsa yana duba saqonnin WhatsApp da tun daxun ya sauka da zummar zai koma din. Hira sosai suka shiga yi da fannah,don kusan duka saboda ita din ya hau. Jifa jifa yana mata gajeran voice note don kada ya janye hankalin fu'ad da baqonshi.
A nutse ya kammala amsa kiran,yayi disconnecting sannan ya maida dubansa ga farouq. Idanu yadan zuba masa,yana mamakin yadda yakejin dadin soyayya gaba daya,wai shin mene a cikinta har haka da take iya maida mutum wawa ne?.
"Ya dai?" Yaji muryar farouq din yana katse masa tunaninsa
"Am just wondering...."
"For what?" Farouq ya katse masa magana yana maida masa tambaya murmushi dan kadan yana fita a fuskarsa
"Yadda mutum me hankali yake komawa kaman soko.......wannan abar farouq It doesn't make sense wallahi" Ya fadi iya gaskiyarshi,gaskiyar da har saman fuskarsa zaka hangeta kwance quru quru.
Dariya ce sosai ta qwacewa farouq har yana duqawa,abinda ya sanya fu'ad tsaiwa ya zuba masa ido yana kallonsa.
"To abun kuma ya fara cin qarfina,to be sincere ka fara bani tsoro sama dana baya.......nafi tunanin kuma yanxun bawai aljana bace ta aureka ba,tunda koda aljana ce saida soyayya ai ko?"
"Kai ka sani qaton banza" Fu'ad din ya fada yana jifansa da wata harara data sake sanyawa farouq ya fashe da dariya,don irin wannan hararar kawai yake iyayi masa idan ya quleshi ya kaishi bango.
Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi don kada ya jawowa kansa jagwal ko yaqi bashi hadin kai akan batun da yazo masa dashi,ya sani sarai kadanne daga aikinsa ya murje idanunsa,musamman yanzun da har ya shiga gonarsa ya kuma tsokaneshi.
"Mu ajjiye wannan batun.....ina nan dai inayi maka addu'a.......na saka a duba mana ticket zuwa abuja Saturday in sha Allah......already ma nayi payment zai mana printing ne kawai"
"Bazanje ba" Ya bashi amsa kai tsaye yana qoqarin shutting down system dinsa idanunsa saman screen din.
Fuska farouq din ya narke yana koma masa kalar tausayi
"Sai na tafi ni kadai.....amma kuma idan ta tambayeka,zan bata labarin ka saba Alqawarin da mukayi da kai ne" Yakai qarshe yana zuba ma side na fuskarshi idanu.
Shuru yayi kawai bai sake cewa komai ba,wanda alamu ke nunawa farouq zaiyi wahala yace bazaije din ba. Sau tari shuru a wajensa alamu ne na accepting abubuwa,idan baya so kai tsaye zaice baiso kuma bazaiyi ba kaman yadda yanzu ya fada mishi da farki,yana sane kuma ya sanyo zancan cika alqawarin......don ya sani shi din mutum ne da ba abinda ya tsana irin qarya sam sam,idan kanaso kaga tunzurarsa ko fadansa to kayi masa qarya.
"Ya ake ciki maganar ginin?" Farouq ya sanyo masa maganar da yasan yanzun itace a gabansa sama da ko wacce. Sai kuwa ya qarasa kashe system din ya rufeta yana dora fararen idanunsa akan farouq din.
"Ending month dinnan nake sanya ran gini zai kammala,sai preparation kawai na budewa wanda shima banaso ya wuce watanni biyu.....duka engines da sauran kaya next week zasu iso in sha Allah" . Kai farouq yake jinjinawa,yana matuqar yabawa da hazaqa da qoqari irin na fu'ad din.
Tun farko yasan idan don ta shine bazai iya ba......don haka ma ya saki wannan ragamar kawai ya miqawa fu'ad din,don tunda shi ya faro barota shine zai iya. Qaramin murmushi farouq din ya saki,fu'ad ya dage masa gira alamun tambaya
"Ba komai.......kawai na tuna temple run dinka ne......rigimammen dan bautar qasar da yaje garin wasu ya musu barna.....ya kuma gudo da abinda suke ta buri da nacin samu......Allah inda a zamanin yaqe yaqe ne zakayi barna da yawa fa" Maganar dole ta sanya murmushi kubcewa daga fuskar fu'ad,ya zauna sosai yana sake duban farouq
"Mazantaka a zuciya take farouq......sannan dukkan namiji muddin zai amsa wannan sunan dole kalmar TSORO ta fita daga dabi'arsa......bai halatta ba sam sam namiji ya zama me tsoro ba..... Idan hakan kuwa ta kasance a matsayinsa na shugaba kuma jagora,dole al'amura su lalace..... Adinga ganinsu kuma ba'a yadda suke ba".
Duk da tsananin gajiyar dake a jikinta bayan dawowarsu daga wajen boka DURGUJI amma hakan bai sanyata zama ta huta ba bare akai ga batun kwanciya. Kai kawo kawai takeyi tsakanin kitchen da dakunanta cikin sabgar dafawa da saukewa. Wani tsari da takeson fara qirqiro dashi a yau din,don shine hanya guda daya da zata samu ayyukan da aka tsara mata su tafi yadda takeso.
Ta bata lokaci sosai tana son tuna wanne abinci da wanne abinci sukafiso ta dafa musu lokacin quruciyarsu?. Da qyar ta dinga tuna wasi abubuwan da suma shafesu saboda yadda ruhi da zuciya suka jima da yin nisa daga rayuwarsu dama komai daya shafesu.
Tayi lissafin abubuwa guda hudu duk da tasan sunfi hakan,saidai sauran ta barwa ranta zata nemi ganin ma'aikatansa da yake yawan rayuwa dasu don samun wasu amsoshin. Anni ce tasan wadda zata samu amsar kai tsaye daga gareta,saidai zuwa yanzun tana jin cewa tafi qarfin anni ballantana ta sake neman wani abu daga wajenta akan 'ya'yan da ita tayi cikinsu ta kuma haife abinta. Alwashi taci......tana nan kuma riqe dashi......hakanan ba zata runtsa ba ba kuma zata huta ba har sai ta samu cikar wannan alwashin nata.
Tana aikin masu aikinta suna mamakin shigarta kitchen yau da kanta. Duk kallon da suke binta dashi bata samu nasarar tantancewa ko kuma kula ba,saboda hankalinta yayi matuqar nisa akan maganganun da suka tattauna da durguji.
_"sau daya nakewa mutum aiki na gama dashi.....muddin kuma nayi aiki baici ba yana da wahala na sake na biyu indai ba sa'a ka taka ba......aikinki me hatsarin gaske ne......duk abinda kikaji ko kika gani kada ki wuce wata guda kacal baki dawomin ba"_
Ita batun sake aiki da rashin sakewar duka ba damuwarta bane,tunda ta riga data sani kudi suke juya akalar kowa su kuma sauya tunaninsa. Muddin zata zube masa kudi ta tabbatar duk taurin kansa sai ya sake waiwayarta. Kawai abinda yake damunta a yanzu shine yadda zata samu dawowar hankulansu a kanta,ta yadda cinsu da shansu zai dawo qarqashinta,wanda wannan shine abu guda daya tal da zai sanya aikinta ya tafi yadda ya dace.
Tana kammala white rice sai ta kasa haquri ta fita a kitchen din. Dakin gadonta ta wuce ta samu saman sofa bed ta zauna tana latsa wayarta. Number fu'ad din ta fara kira,daidai sanda yake zaune suka ci gaba da tattaunawa da farouq yana nuna masa tsarin taswirar ginin kamfanin.
Fararen idanunsa ya daga yana azawa saman wayar. Zubawa wayar idanu yayi yana kallon yadda sunan ke wucewa ta saman screen din. A duk sanda zaiga shigowar kiranta sai yaji wani abu tun daga qasan ransa har tafin qafafunsa. Inda yana da iko bazai daga wayar ba sam sam,to amma wata fuskar tafi gaban mari
"Ina zuwa" Yace da farouq yana daukan wayar ya daga ya saka a kunnensa.
Cikakkiyar sallama tayi da kwantacciyar murya da zai iya cewa ya manta rabon da yajita daga bakinta,wani abu guda daya sake jan hankalinsa,saidai bai hanashi amsa sallamartata ba hadi da dorawa da fadin
"Barka da yamma" Dan murmushi ta saki kadan
"Yauwa barka kadai Muhammadu" Ta fada cikin nuna kulawa
"Ka wuni lafiya kai da dan uwanka?,tunda har yanzu ban cancanci a kullum naga lafiyarku ba......hasalima kamar kuna mantawa ne da rayuwata" Yadda tayi maganar ya taba ransa kadan,yaji sautin da amon da ya jima baiji daga gareta ba
"Kiyi haquri ba haka bane" Ya maida amsa wani abu yana kai kawo a ranshi
"To idan ba haka bane yaya ne Muhammadu?,kamanhar yanzu kun kasa manta abinda ya faru ne kawai" Idanunsa ya lumshe kawai yana saurarenta. Zuciyarsa nadan qara bugun da takeyi yana jin wani abu sosai can qasan ransa da kuma wani sashe na zuciyarsa
"Idan zaku iyayimin alfarma,inaso ana gama sallar ishai ku shigo kai da musaddiq....inason ganinku duka ku biyun"
"In sha Allah" Ya amsa mata kai tsaye. Wayar na a kunnensa har ta yanke Kiran,sai shima ya zame wayar daga kunnensa yana kallon screen din.
Sanda ya daga idanunsa sai suka hada ido da farouq,murmushi farouq din ya sakar masa kawai. Har yanzu bai taba saka baki ko shiga lamarinsa da maamah ba,infact ma shi bai taba masa magana a kanta ba,ko yaushe shida sadiq suna qoqarin kiyaye iyakokinsu ne.
Wani irin murmushi ta saki bayan ta ajiye wayar idanunta akan qofa tana jin wani farinciki yana shigarta. Nasara ce a kusa take shanshanarta......kuma jikinta yana bata komai yana kusa da qofarta.
Plan dinta guda uku ne qwarara,ta fara da wannan na farkon,idan yayi aiki shikenan,idan baiyi ba zata wuce plan B,idan shima yayi aiki shikenan,idan kuma shima baiyi ba tana da plan C......wanda shine tsororuwar shiri mafi tsauri da tauri.....plan din data tabbatar zai yamutsa hazo iya yamutsawa........ita kuma zata saki dukkan wata iyaka da ikon da Allah ya bata don ganin tabbatuwar plan din da kuma wanzar dashi.
Ranta fes,Zuciyarta wasai ta ajiye wayar ta koma kitchen tana shirye shirye shirye gadan gadan.
Haka kawai yakejin yanayinsa wani iri,jikinsa da zuciyarsa dukka ba'a sake suke ba,a haka ya shirya cikin Moroccan abaya ne sulbi ya wuce zuwa sallar magariba.
Kafin ya isa masallacin suna hanya shi da farouq musaddiq da saddiq suka biyo bayansu. Wannan din wata kyakkyawar al'adarsu ce da anni ta renesu a kai. Muddin suna garin ko suna qasar,hakanan ba wani babban uzuri ko aiki bane ya riqesu a kamfani,to zaka samesu a gida duk inda magariba tayi. Kwata kwata basusan yawon dare ba,farouq ne ma medan sha'awar fitan daren,to sukan fita jifa jifa su zaga a mota su dawo. A nan zasuyi sallar magariba suyi ishai,suyi dinner tare me uzuru ya wuce nasa uzurin.
Sanda yake sabule tattausan flip flops din qafarsa yace da musaddiq ba tare daya waiwayo ba
"Bayan ishai ku shirya kaida saddiq zamu shiga wajen maamah" Dan kallon yayan nasa kadan yayi,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya amsa da to.
Tun bayan magariba ta sallami kowa tare da kafawa kowa sharadi da dokar bataso kowa ya sake tako mata parlor sai gobe idan Allah ya kaimu.
Ta duba doormat din bakin qofar falon yafi sau goma daga zamanta,ta kuma tabbatar komai yana nan intact kamar yadda ya kamata ace ya kasance din,sai ta koma ta zauna tana sauya tashar Tv din zuwa mbc Bollywood bawai don tana jin dadin kallon ko yana burgeta ba,dukkan hankalinta yanzu da nutsuwarta shine takowarsu cikin falon,su zauna kuma su cika cikin su da abinci da abin shan da ta tsumashi ta kuma tanadashi musamman saboda su.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 64
Saddiq da musaddiq dinne a gaba shi kuma yana biye dasu a hankali a hankali,hakan ya sanya suka dan masa tazara kadan. Wayar Mika'il yake amsawa,wanda yakeso ya tabbatar komai ya zama daidai zuwa ranar Monday da zai koma office. Yanason ya gabatar masa da dukkan wasu mu'amala na kudi da banking ya samu bayan tafiyar tasa,komai na shige da ficen kudi.
Yana wayar ne amma hankalinsa yana kan saddiq da musaddiq,tamkar 'yan biyu kamar yadda kowa yake musu kallo hatta da makarantun da sukayi. Suna hira abinsu ne cikin wani irin shaquwa da jituwar jini. Malam saidu ne ya bude musu qofan da kanshi,ya rusuna kuma yana miqa masa gaisuwa sai ya gyada masa kai hadi da daga masa hannu saboda wayar da yakeyi din,ya taka a nutse yana bin bayansu.
Dab da zasu isa steps din da zasu sadasu da ainihin falon yaji gabansa yayi wani mummunar faduwa
"Zamu qarasa anjima" Yace da Mika'il a gaggauce yana katse wayar ba tare daya jira amsarsa ba
"Kai saddiq" Ya furta da muryar da taja hankalin maamah dake falon,wadda dama dukkan tunaninta yana fa farfajiyar gidan tana sauraren kowanne motsi.
"Saddiq kuma?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance,sai ta tuna kuma bata da sauran lokacin batawa,don muddin ta bari wani bayan yaran nata ya taka wannan shirin akwai matsala,don haka ta zabura tayi zumbur ta miqe ta kuma nufi bakin qofar falon da sassarfa.
Wancakali tayi da doormat din,ta sanya hannu ta dauke abun da yake qasan,sannan ta finciki tsintsiya dake ajiye a can wani gefe daban ta fara tattara sauran abubuwan da suka rage.
"Kunyi addu'a ne?" Ya fada yana tsaresu da idanu duka su biyun. Juna suka kalla shi da musaddiq din
"Hamma ai daga masallaci muke" Saddiq din ya fada dukkaninsu suna sauke qafafunsu daga saman steps din da suka fara dorawa
"Kuyi addu'a kafin ku shiga.......haka musulunci ya koyar damu,kome zakayi akwai addu'ar da akeyi masa" Ya fadi idanunsa akan musaddiq
"To hamma" Suka fadi sannan suka maida qafafunsu kowa bakinsa yana dan motsawa.
Da kallo ya bisu zuciyarsa cike da wani wasi wasi da baisan daga inda ya samo asali ba. Sosai hankalinsa yana kan musaddiq da ya tabbatar baisan komai akan shirin maamah nason raba tsakaninsu da iyalin alhaji hamza ba. Shi kansa abban baisan komai ba akai,shi daya yake juya maganar tsakanin qirjinsa da zuciyarsa.
Dan ja sukayi suka tsaya sanda suka sameta duqe tana tattare wani abu da basusan meye shi ba. Ta daga kai tana dubansu,wani irin bacin rai ya cika mata zuciya fal.
Ta yaya banda sun raina umarninta zata ce tana buqatar ganinsu su biyu su rakito mata wani?. Fushin yanason yayi galaba a kanta amma tanata qoqarin danneshi. Yanzun ba lokacin nuna fushi bane ko fada..... Lokaci ne na sauke kai da maida komai ba komai ba muddin nasara take da buqata,wannan shine abinda hajja ta gaya mata.
Dole ta qirqiro murmushi tana cewa cikin nuna kulawa a garesu gaba daya
"Maraba da 'yan samari na" Saita zubda abun cikin kwandon shara ta kuma taka zuwa ciki tana fadin
"Ku qaraso mana". Sai da suka fara shiga sannan yabi bayansu yana kula da hagu da damansu
"Ina ma'aikatan suka barki kina shara?" Fuad ya furta da nutsatsiyar muryarshin nan yana zama hannun kujera hannunsa goye a qirjinsa yana kuma qoqarin karantar komai dama motsin komai dake a falon.
Dan murmushi ta saki tana zama saman daya daga cikin kujerun alfarma dake falon
"Ina buqatar kebewa da 'ya'yana,nayi sirri dasu irin na uwa da 'ya'yanta,shi yasa na sallamesu yau da wuri". Maganar tata sai ta kasance kamar ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse guda,don haka saddiq sai ya rusuna kawai yana gaidata.
"Lafiya alhamdlh saddiq......ya mutanen gidan?"
"Suna lafiya maamah"
"Ma sha Allah,don Allah kace ina gaidata da kyau da kyau"
"Zataji in sha Allah......hamma zan qarasa,saikun fito" Idanu fuad din ya zube masa,yayin da maamah ta bata fuska tana cewa
"Ina kuma zaka daga shigowarku ko zama bakayi ba?". Dan murmushi yayi yana saukar da kansa qasa cikin girmamawa
"Gida zan qarasa,jibi zamu koma company ban kuma gama shiryawa ba,kinsan kuma hamma......bazai dagan qafa ba idan aka samu kuskure" Tabe baki tayi kadan ta yadda ba lallai bane su fuskanta,qasan zuciyarta kuma cike fal da baqinciki da bacin rai,amma kuma a fili saita saki murmushi
"Gaskiya ne,to Allah ya taimaka,ka gaisheta"
"In sha Allah" Ya fadi yana waiwayawa gefan musaddiq ya bashi hannu yadda suka saba yana yin gaba.
Shiru falon ya dauka sanda saddiq ke ficewa,cikin ranta take gayawa kanta da kanta saura kadan komai yazo qarshe.... .watan watarana saidai ya gifta katangun kamfanin ya ratse ya wuce ta bayansu,komai na wata dama ta shiga cikin kamfanin baida ita.
Sai daya kammala ficewa tsaf sannan ta maida dubanta garesu,dukansu ta fahimci kamar hankalinsu baya tare da ita,don haka ta danyi gyaran murya,gyaran muryar daya sanya dukansu suka dubeta,sai ta saki musu murmushi.
Amsa gaisuwarsu dukka su biyun tayi,a yau sai take jinta kamar a aljannar duniya,sai takejin kamar burinta ya gama cika duk da an samu matsala a karon farko,amma akwai tafiya ta gaba,ta tabbatar ba zasu tsallakewa abincinta ba.
Tanaso a yau tasan abubuwa masu yawa game da rayuwarsu,tanason tasan adadi da zurfin dukiyar da kowannensu ya mallaka,koda batasan duka ba,tanason ta karanci kaso me tsoka.
"Ina fata dukkaninku kuna lafiya"
"Alhamdulillah" Suka fada kusan a tare kowa ba karsashi a tattare dashi.
Ta fahimci hakan,don haka ta gyara zamanta tana fadada fara'ar fuskarta
"Ina fatan zaku cire komai daga zuciyarku,kuci gaba da kallona a matsayin mahaifiyarku,komai zai wuce mu fara gina sabuwar rayuwa tsakanina daku.....ina buqatar 'ya'yana a kusa dani kamar yadda kowacce uwa take da buqatar 'ya'yanta. Inaso na kasance daku tamkar komai bai faru ba,nayi alqawarin baku farinciki da kariya kaman yadda kowacce uwa ke bawa 'ya'yanta" Ta qarashe maganar cikin matuqar raunin zuciya da karyewar murya kamar wadda ke shirin sakin kuka.
Dukkaninsu dubanta suke,kowannensu da mabanbancin feeling a zuciyarsa,saidai kuma dukkaninsu akwai mamaki danqare qasan ransa.
Ci gaba da dubanta fu'ad yayi mamakinsa yana qaruwa. Tunda ta fara magana baiji inda tace tayi nadama ba......nadama koda qwaya daya akan abinda ta yiwa abbansu ba,su din basu da buqatar ta nema yafiya ko afuwarsu,tunda itace ta haifesu,tayi silar kowasu duniya.....ba wani abu da zasuyi mata wanda zasu saka mata da iya wannan aikin......amma kuma abban fa?,kota manta cewa itace silar komai?,ta manta itace silar faruwar komai?. A yanzun ya Fatimid tafi buqatar hankalunsu a kanta da abinda suka mallaka sama da nadama neman afuwa ta zahiri da yafiya daga mutumin da aka zalunta wanda yanzu haka yake kwance a qarqashin qasa.
"Banaso ku dinga nesa dani suka nesanta kanku dani,bani da wani abu dana mallaka a yanzu sama daku.......ina zaune ni kadai,idan mutuwa ma nayi kenan saidai kuji labari daga wajen bare?" Ta maida tambayar kan fuskar musaddiq. Kanshi ya girgiza mata yana sauke kan nasa qasa. Har yanzu idanunsa da sauran tunaninsa sun kasa goge masa komai,ballantana hammansa daya tabbata komai yana rubuce ne a allon zuciyarsa. A duk sanda ya kalleta sai ya tuna ruwan data watsa saman fuskar majinyacin mahaifinsu sanda ya buqaci ta bashi ruwa,shine ya zame masa rumfa yaje ya kwanta a samanshi da zummar kareshi saboda sanyi da yadda ya jiqe din sosai,a sannan ta taka ta fice a dakin hankalinta kwance tana waqe waqe abinta.
"Don Allah koda abincin dare ne ku kasance tare dani ko na safe... Ku bani koda awa daya kowacce rana mu zauna ni daku nasan na haifi 'ya'ya nima kamar kowacce uwa.....don Allah" Ta sake fada da muryar roqo sosai,raunanniyar muryar daka iya sauko da tausayi a zuciyar wanda baisan manufar me magana ba.
"In sha Alla" Kawai fu'ad din ya furta. Ya sani koma me zaice yanzu ba maslaha zai kawo ba,ba kuma zata taba fahimta tunda akwai banbancin manufa a tsakaninsu. Kowanne a cikinsu abinda ya ajjiye a zuciyarsa daban.
"Muje ga abincin dare can na shirya muku.....abinda nasan kunfi so sosai" Ta fada tana murmushi ranta yana mata dadi da yadda suka karbi request dinta suka amince da xuwan nasu.
Ba wanda ya musa mata,suna dai binta da ido da kuma hankulansu har xuwa sanda ta jawa kowannensu kujerar zama tana fadin
"Bismillah" Inda ta kasance daga kujerar dake facing dinsu.
Serving nasu komai da komai tayi,tana yi tana jansu da hira tare da qoqarin tuna musu wani abu na daga quruciyarsu. Shidai fu'ad idanu ne kawai nashi ba tare daya iya maida komai ba,har ta kammala tana fadin
"Gashinan kowa ya dauki nasa". Duban abincin yayi da kyau,gaskiya ta fada batayi kuskure ba,a baya baida abincin da yakeso irinsa,amma tun daga ranar data dafa abincin cikin gidansu,ta kuma yiwa mahaifinsu haramiyar abincin a sanda yake kwance yana jinya.....yunwa take sake take rawa wajen galabaitar dashi,ta hana masa abincin,abinda yayi silar kwanansa da yunwa,tun daga ranar har kawo yau bai sake saka irin abincin a bakinsa ba,daga ranar ya fita a ransa,fita ta har abada wadda har yau bai sake dawowa zuciya da rayuwarsa ba.
"Shikam hamma ai maamah yanzun wannan ba cimarsa bane......nima kuma kin manta dama ba kasafai na fiya ci din ba?" Musaddiq ya fada yana shafa kanshi idanunsa cikin na maamah din.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 65
Wani abu ne yaso ya tsaye mata a rai,tunzura takeso tayi amma kuma tana gayawa kanta ba yanzu ba......idan ma basuci na yau ba ai na gobe yana nan,muddin kuma zasu ci gaba da taka qafarsu cikin gidan yau ko gobe nasara tana nan tare da ita.
"Yaushe Muhammad ya daina ci?" Ta yiwa musaddiq tambayar sai kuma ta maida dubanta ga fuskar fu'ad din a mamakance,saidai kuma sanda suka hada idanu dashi sai komai daya faru a wancan ranar ya dawo mata a take,amsar tambayarta ta fita kamar budewar shafukan littafi.
Wani abu taji me nauyi wanda sam baiyi kama da kunya ko nadama ba,tabbas a baya din don ba cikin daidanta take ba.....ba yaran bane a gabanta ballantana abinda ya shafesu da har zata lura da meye ya damesu da wanda bai damesu ba.....amma tabbas sai yanzu ta tuna,tun daga ranar yake bar mata kwanonta gaba daya yadda ta zuba.
"To amma bai kamata ace bakuci komai ba koda lemo ne" Ta sake fadi tana jan jug din gabanta tare da qoqarin raba kofunan ta zuba musun kada ya zamana komai da komai ma tayi asararsa a yau din.
Idonsa still a kanta,ya miqa hannu ya jawo gorar ruwan daya tabbatar a kulle take ya soma budeta,qarar budewar ya sanya ta daga kanta zuwa gareshi tana dubansa
"Ruwa kuma muhammadu?,ga lemo dai" Ta fada tana tura masa wanda ta zuba
"Maamah dare ya soma yi.....idan kuma dare ya fara bana iya cin komai...." Dubansa ta sakeyi kadan sai kuma ta dauke kanta tana qirqiro murmushi
"Kowa time table zai bani na abinda yakeso yaci kullum har sati guda koma sati biyu.....masu girki na musamman zan ajiye muku.....burina naga kun kusanta dani......na maida tsohuwar alaqar dake a tsakaninmu" Ta qarasa maganar tana duban cikin idanunsu.
"Fu'ad" Ta sake kiran sunansa,ya daga fararen idanunsa da suka fara rusuna saboda gajiya da zama a wajen,sam baya jinsa comfortable sam sam
"Me yasa kabar musaddiq tare da farouq......duk da ba laifi bane.....amma kaman zaifi cancanta ya kasance tare dakai qarqashin naka kamfanin" Shuru ya biyo baya na second uku,sai ya maida idanunsa ya kulle yana jan boyayyen numfashi. Shikam yayi imanin ba zata canza ba,ya tabbatar abune me wahala da girman gaske da zai sauya mata hali farat daya. Wannan ya sanya kowanne taku ko motsi nata yake sanya masa ayar tambaya,wani lokaci idan tayi wani move din sai yaji gaba daya kanshi ya juye yana tambayar kansa anya da gaske maamah din itace uwa ta asali a garesu?.
"Kowanne bawa da abinda yafi shaawar yi yafi qwarewa a rayuwarsa......yadda abba ya ginemu shine kowa ya dauki zabinsa da ra'ayinsa a rayuwa muddin bai kaucewa hanya ba....inda kikaga farouq da musaddiq su suka zabi wannan sashen duk kuwa da cewa tare da farouq mukayi gwagwarmayar samar da abinda na gina din a yanzu.....ba wanda ya zaba masa ko ya tursashi gashinan maamah ki tambayeshi" Juyawa tayi tana duban musaddiq ranta duka a jagule,bata son kowa ya rabi fu'ad a duniya idan ba dan uwanshi ba,batason kowa yasan sirrin dukiyarsa idan zaiyuwu sai ita daya,wannan tunanin ya sanya ta yanke shawarar sanya ido me tsananin a alaqar fu'ad din da amna......don ba zata taba yarda amina ta dauki d'iyarta ta qwaquma masa ba su qarasa nadeshi.
"Shikenan,Allah ya taimaka" Ta fadi tana sauke numfashi bawai don ta haqura a zuciyarta ba. Kawai tana ganin tunda komai yana kan turba bai kamata ta bata lokacinta tana dogon zance dasu ba,lokaci kadan take jira ta soma bada umarnin wanda zai shiga ko ya fita daga rayuwarsu.
"To yaya sunan surukar tamu musaddiq?....koda wasa baka taba attempting kawota ta gaida mamarka ba?" Ta yiwa musaddiq tambayar tana dubansa da murmushi,cike da zaquwa da son jin kalar matan da suke shirin kawowa rayuwarsu. Wani babbab abu da yake cikin tsarin abubuwan da takeso ta yiwa garambawul idan damar da take tsimayi ta samu,tanason surukanta su zama qarqashin ikonta fiye da yadda hajja ke juya nata mulkin a gidan.
Murmushi kadan ya saki,karon farko da yaji 'yar kunyarta ta sauko masa
"Minal bata iya zuwa ko ina,daga makaranta sai gida.....zata zo wataran in sha Allah". Ba haka takeson ji ba,don haka ta gyara zamanta tana sake sakin fuskarta
"Aah wataran yaushe kenan?,ina buqatar ganinta mu tattauna ka shaida mata mamarta nason ganinta......" Ta fadi din don da gaske tanason ganin wace ita?. Zuwan nata kuma a nan ne zata samu amsoshin tambayoyib data tabbatar ba zata samesu daga bakin musaddiq ba.
"In sha Allah" Ya fadi a taqaice yana auna yadda abun zai kasance.
"Kai kuma fa?" Ta waiwaya tana duban fu'ad daya tattara hankalinsa duka saman wayarsa tamkar ma baya jin abinda suke fadi. Gajiyayyun idanunsa dinnan ya daga ya kalleta,sai kuma ya maida dubansa ga musaddiq. Kan musaddiq din a qasa yana satar kallon fu'ad din ta qasan idanunsa,boyayyan murmushi nason qwace masa.
"Me maamah?" Ya tambayeta da sautin muryarsa da tayi laushi sosai.
"Wa ka daukomin a matsayin suruka?" Ta sake maimaita tambayar tata.
"Babu fa maamah...." Musaddiq ya fadi muryarsa na nuna murmushin da ya boye.
Debe kallonta kacokam tayi ta maida kan musaddiq tanason sake samun tabbacin hakan
"Kamar yaya kenan?" Satar kallon fu'ad yayi sannan ya dubi maamah,yayi qasa sosai da muryarsa,duk da yasan dole ya jishi don yana da wannan baiwar ta kaifin ji
"Ba wata budurwa.....tsoronsa ma suke......ba wadda take iya tararsa maamah tace tana sonshi"
"Very good" Ta fada qasan zuciyarta. Tsananin farincikin da taji ya bayyana har saman fuskarta,tadan danne tana hada rai
"Garin yaya?.....har yanzu halinka dinnan bai canza ba?" Ta watsa masa tambayar . Karon farko kenan da magana kwatankwacin wannan ta taba hadasu,don haka ya rasa ma da abinda zai bata amsa illa cewa da yayi
"Ba yanzu ba....lokaci baiyi ba.....in fact ma da sauran lokaci"
"Lokacin lokaci na ne,yana kuma tafe" Ta bawa kanta da kanta amsa a zuciyarta,amma a fili sai tace
"Allah ya nuna mana lokacin".
Duka hirar ba wani armashi gareta ba,amna haka suka sadaukar da lokacin har zuwa sanda ta basu izinin tafiya sukayi mata sallama suna ficewa.
Suna tafe ne kawai suna dosar gidan,daga shi har musaddiq din ba wanda yace da dan uwansa komai. Sai da sukazo mabanbantan qofofin sassansu,fu'ad din ya murza key yana bude qofarsa yace da musaddiq
"Shigo ciki ka zauna muyi magana" Ba tare daya dubeshi ba,ya gama budewa ya shige musaddiq din yabi bayanshi.
Zaune kawai tayi tana duban kwanukan abincinta da suka barta dashi,banda ruwan gorar dukkaninsu ba abinda suka taba ko qanqani. Lemon data zuba ta turawa musaddiq din ma tana saka ran zaiyi koda kurba daya ne amma baiyi din ba shima sai ya buge da shan ruwa. Ta fahimci yana bin sahu tare da matuqar kwaikwayo ga fu'ad,iya wannan ya isa ya bata amsar cewa,muddin ta samu fu'ad ta samu musaddiq......wanda kuma wannan din shine babban qalubalen da aikin data sake amanna ba qarami bane.
Furzar da iska tayi me zafi daga bakin ta,kusan komai data tsara ya wargaje babu shi,dan abinda ta amfana dashi daga zuwan nasu bai taka Kara ya karya ba.
Akwai damuwa sosai a ranta da take da buqatar abokin tattaunawa,don haka ta sauka daga dining area din zuwa ainihin falon ta dauki wayarta ta lalubo hajja.
"Musaddiq" Ya kira sunanshi kai tsaye sanda yake zaune saman wata qawatacciyar kujera da irinta qwaya daya ce tal cikin falon.
"Na'am" Ya amsa masa. Shuru kaman bazaiyi magana ba,sai kuma ya zauna sosai yana goye hannuwansa a qirji
"Inaso ka zama me takatsantsan sosai......inaso kuma ka zama me kula.....bazan hanaka zuwa gidanmu ba duk sanda kake da muradin hakan......amma kayi aiki da hankalinka da kyau......yanzun kai ba yaro bane.....ba wannan musaddiq din da ko yaushe sai hammansa yana gefansa bane don ya kula da abinda zai cutar dashi ko ya amfaneshi bane.....abubuwa sun yiwa hammansa yawa......kula da rayuwarsa yana hannunsa".
Wadannan kalaman na hamman su suka dinga juyawa cikin kanshi. Duk da bai fito qarara ya masa bayani a bayyane ba,amma kamar yadda yace din shi ba yaro bane yanzun,hakanan shi a karan kansa hankalinsa ya fara dauko masa wasu abubuwan a iya zuwansu gidan yau kawai.
Haka kawai ya kasa bacci a daren,har yanzu musaddiq baisan ainihin wace maamah din ba. Iya matakin da idanuwan basira da hankalin musaddiq kadai ya kaishi bai sadar dashi da ainihin wacece maamah ba........meye zata iya yi?,da wanda ba zatayi ba.......dole koda a fakaice ne ya sake nesantashi da tunkudeshi daga dukkan abinda yake ganin zai iya zama cikas a rayuwarsa.
Bugu biyu tak hajja ta dauka,hakan ya yiwa maamah dadi,sai ta miqe da wayar tana nufar bedroom dinta
"Na zaci kinyi bacci ai"
"Aah inadai shirin tashi.....labaran ne ya zaunar dani muna lissafin abinda kamfaninsa ya samu na shekara". Ido maamah tadan fiddo cike da mamaki
"Kamfaninsa fa?,yanzu lissafin shima tare kukeyi?". Dan qaramin murmushi me sauti hajja ta fidda tana aza hannunta saman kan budurwar dake kwance saman cinyarta tana amsa waya itama
"To meye a ciki?,nice uwarsa fa?,akwai wani abu da suka isa su boyemin?,koda cikin gidajensu akayi abu koda da darene da safe kuwa rana bata bullowa bansan komai ba......ke banda ma ina taka birki ma wasu abubuwan......ai hatta sunnar aure da matansu sai sanda na bada iznin a yita,kuma idan anyin sai an fada min"
"Innalillahi......ke hajja?" Maamah ta furta cikin tsananin mamaki
"Ke?.....zauna kina wasa da lamarin yaran yanzu,kina sake musu hanya sai linzaminsu ya koma hannun matansu,keda wahalar raino da daukan ciki amma wata ita keda d'an,kin zama 'yar kallo,sai abinda tace a tsakuro a sammiki.....tun daga kan yahaya na fara daukan izina.....ban kuma zauna ba har yau har magajin gobe" .
Duka mamaki ya gama kashe maamah,amma kuma bayanan hajja din sai suka gamsar da ita,ta kuma yarda cewa gaskiya ta fadi,gashi yanzun ita tana fafutukar karbar 'ya'yanta daga hannun wata ma tun basuyi aure ba?.
"Yanzun ya ake ciki?,komai ya tafi dai dai ko?" Ajiyar zuciya maamah ta saki tana maida hankalinta ga hajjan
"Hajja ba abinda sukaci fa?.....duk wahalar nan kin ganni da kayana suka barni....."
"Karki gaggawa,idan ba yau akwai gobe,idan ba gobe akwai wani satin"
"Haka nake gayawa kaina......kana iya target din abu amma shekara goma gaba kake hangowa.....zamu zuba dasu in sha Allah......wannan karon banga abinda ya isa ya hanani ko ya dakatar da burina ba" Ta fadi har qasan zuciyarta tana jin confidence akan wannan.
"Sirrin samun nasararmu dama itace jajircewa naci da kafiya". Hajjan ta qara mata qwarin gwiwa.
Sun tattauna sosai har na kusan mintuna talatin kafin su yanke kiran. Hajjan ta sauke wayar wani murmushi na fita daga fuskarta,tadan tsuke bakin ta lissafinta yana tafiya da nisa sosai.
"Mommy ga adeel zaku gaisa" Budurwar ta fadi tana daga kanta daga saman cinyarta hadi da miqa mata wayar. Sai data kalleta sannan ta amsa wayar ta sanya a kunnenta.
Ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar nashi,ba jimawa sukayi sallama ta miqawa yarinyar wayar tana kallonta. Kallon hajja kawai a garesu yana da fassarori,don haka tayi masa sallama ta katse wayar ta ajiyeta a gefe tana kallon hajjan
"Momy lafiya?" Numfashi ta ajiye tana dubanta duba na kai tsaye
"Ina sake gaya miki......nayi miki tanadi,kada ki kuskura ki zurfafa a soyayya da kowa....don kowa a cikin rayuwarki temporary ne......akwai target dina.....kuma bazanyi missing target dina ba tabbas" Tayi maganar da sautin da zai gaya maka tayi maganar ne da gasken gaske daga zuciyarta,ta kuma yi maganar tana kafe autartata da idanu don ta sake jaddada mata girman maganar.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 66
Itama duban momyn nata take yi,ta sani tabbas momy din nata tana matuqar ji da ita.....kaman yadda ta sani taci buri sosai a kanta. Duk da hakan tana da buqatar qarin haske a maganarta,don haka ta motsa kadan
"Momy.....wanne irin buri ne?,ta yaya zan iya sallamar dukkan kuma wadanda muke tare dasu yanzu?"
"Bance ki sallamesu yanzu ba,tukunna dai.....amma dai abune da kika sani cewa.....ke din ba kalar qananun maza bace....ban haifeki don wani me jaririn arziqi a hannunsa ya aureki ba.....plan dina kuma idan lokaci yayi zakiji....don ku yaran yanzu kwata kwata bakusan me ake nufi da sirri ba".
*****Ta jima zaune gefan gadonta tana juya wayarta a hannu. Mikail takeson kira,ta kuma shirya haduwarsu kaman yadda ta tsara zata kammala da babinsa ta kuma rufeshi kwata kwata cikin shafukanta kamar yadda ta binne maza masu yawan gaske. To amma haka kawai duk sanda tayi attempting na kiran nashi sai taji kaman kada ta kira din.
Wani sashe na zuciyarta na bata qwarin gwiwar ta kira
"Ya cancanci ya fuskanci komai......ya kuma cancanci kowanne irin hukunci,jin kunyar mara kunya asara ce!" Ta sake jin wani sauti daga can qasan zuciyarta yana rada mata maganar har zuwa kunnuwanta.
Danna kiran tayi,ta kuma tattara dukka nutsuwarta akan wayar tana sauraren yadda Kiran ke tafiya kai tsaye zuwa layin mika'il din.
A kasalance yake shiryawa,kasancewar daren jiya ya shawu. Duk da ya tsagaita shan ma,bai wani sha yadda yakeso ba,saboda ya sani safiyar yau din litinin tana cikin ranaku masu muhimmanci da zai gana kai tsaye da CEO. Mutum na farko kaf rayuwarshi dake masa wani irin kwarjini,kwarjinin daya tabbatar yana da alaqa da kamewarsa......da yadda fara'a ko murmushi sukayi nesa da fuska dama rayuwarsa gaba daya.
Ya jima yana so ya shiga rayuwarsa fiye da matsayinsa,amma kuma ya gaza samun wannan fuskar. Mutum ne da idan ya zauna aiki kawai,baya daukan wata magana da ba cikin aiki take ba,kamar yadda baya daukan wasa ko kuma wargi.
Yadda dukkan ma'aikatan dake aiki qarqashin kamfanin suke da iyakoki......haka nan dukkan wata magana da zaiyi dakai akwai iya adadin lokacin da yake baka.
Qarar wayarsa ta ja hankalinsa sanda take saka links na rigarsa,sai ya dakata cak daga abinda yakeyi din cikin tsananin mamaki yana kallon wayar.
"What a wonderful day" Ya fada qasa qasa yana daukan wayar ya zauna gefan kujera. Wani mamakin yana sake kasheshi da idanunsa suka tabbatar masa eh itace take kiransa
"Yau kuma da kanta?,da wanne irin sa'a na tashi?" Ya yiwa kansa tambayar yana daga kiran ba tare daya tsawaita dogon tunani ba.
Kamar kowanne lokaci tayi masa sallama wadda shikam ba kasafai yake iya tunawa da ita ba. Sai yadan daburce kadan kafin ya amsa sallamar ya dora da fadin
"Good morning queen....nayi kira nayi kira har na gaji anqi a dagamin waya.... Kwatsam sai gashi na tsinci wani abu da ban taba kawowa zai faru ba".
Murmushi ta saki kadan wanda ko kusa da gefen zuciyarta bai kai ba,yayin da shi kuma kunnuwansa yaji kaman zasu narke da fitar sautin sassanyan murmushin nata. Kowanne tsiga na jikinsa sai ta shiga tashi
"Ka sani ko yanayin alaqa da dangantakarmu ne suka dauko hanyar sauyawa?"
"Da gaske!" Ya fada da wani irin murna daya kasa boyuwa yana fidda idanunsa waje
"Eh mana....." Ta amsa masa a taqaice.
"Yes!" Ya sake fadi da wani irin dadi yana mamayarsa
"Indai haka ne kiyimin proving mana......"
"Kamar?" Ta jefa masa tambayar da zazzaqar muryartan nan,don wajen da takeso azo kenan tana tunanin kuma ana gab da zuwa din,saidai ita ba zata iya requesting ba har sai ya nema da kanshi
"Mu hadu yau.......don Allah kada kicemin aah". Shuru tayi cikin salon jan aji,kaman bataso
"Please mana.....please,kice to" Ya fadi murya a raunane cike da fatan samun amincewarta
"Shikenan"
"Oh god......" Ya sake fadi yana dukan kujera da hannunsa,yana kuma ji duk duniya ba wani d'a namiji da yakaishi sa'a yau dai a duniya. Yana nashi bidirin amma nata qasan zuciyar a quntace. Wani mugun tsanarshi take ji da haushinsa. Da gaske wannan din dabi'arsa ce bazai kuma taba canzawa ba,ko shin mata nawa ya lalata da kalar wannan mummunar dabi'ar tasa?.
"Bansan da wanne irin yare zan gode miki ba....amma zakiga godiya a aikace har saikin rasa da meye zaki maye min gurbin hidimata a gareki......tabbas zan ninka darajarki.....zan daukaka martabarki a idanun duniya......zan maidake tauraruwa cikin mata....zan miki ado da gold irin adon da sai 'yar gata...."
"Thank you......thanks" Kawai tace dashi don tanaso ya dakata daga zubo wannan dogon sharhin nasa. Tana tausaya masa a daren yau irin barnar da zatayi masa,ta tabbatar wadannan maganganun da yake jerowa a yanzu saisun koma sumbatu.
"Zan shiga company akwai lissafin da zamuyi da boss dina.....duk inda la'asar yayi koda bamu gama ba zan dauki excuse......zan kama mana daki a Bristol,zan tura miki details da komai da komai".
Baki ta tabe tana jin wani haushi yana cikata. A daren yau bashi ba,hatta da boss din nasa saita sakasu a lissafin da babu fita. Tanaji a jikinsa ma shi da boss din basa zaiyi wahala idan ba zamuje ta tadda muje mu ba. A yadda yakan bata labarinsa lokaci bayan lokaci......irin kudaden da yake wasa dasu da kuma shekarunsa talatin da bakwai a duniya amma ace ba macen aure?,to idan ba sheqe ayarsa yakeyi ba me yakeyi kenan?.
Ture wannan tunanin tayi daga zuciyarta don a halin yanzu bashi da amfani,abu guda daya ta sani ba sassauci,kuma a yau din takeso mika'il ya zama tarihi cikin rayuwarta,shi kuma ta bashi darasin da zai sanya rayuwarsa tayi laushi da kyau.
"Ba laifi...." Ta amsa mass,bata kuma jira cewarsa ba ta dora
"Ina fata kasan rule din.....zaka rigani isa gurin da wasu mintuna......kuma bana buqatar kowa yasan muna tare ne da kai"
"Dukka dokoki da qa'idojinki kisa a ranki an gamasu......ranki ya dade.....da zaki bani dama da kin fadi inda zan aiko driver ya daukomin ke.....don bana buqatar kiyi wahala" . Wani sirrintaccen murmushi ta saki
"Na maka uzuri saboda baka jima cikin rayuwata ba bare ka fahimci wacece ni......zanzo da kaina,bana buqatar kowanne driver"
"As you wish.....saidai zan saka kudin transportation.......please karkice min aah" Idanunta ta lumshe sannan ta budesu,har ta fara gajiya da dogon hirarsa
"Alright....byee" Ta furta a taqaice tana tsinke wayar.
Ajiyeta tayi gefe tana furzar da iska daga bakinta. Inda ace dukka haka mazan aure suke ba shakka a jiya da kunnuwanta basu jiye mata abinda taji ba saman dogon layin masu lalurar ciwon zuciya dake dakon ganin likita......tabbas da idanunta basu gane matan auren da hawan jinin bacin rai da baqincikin d'a namiji ya jefa musu hawan jinin daya juye musu zuwa ciwon zuciya ba......da bataga matar data yanke jiki a wajen ta fadi ba......wadda daga qarshenta gawarta aka fitar a asibitin 'yaruwata na kuka dukka sanadin baqinciki namiji.
Ita kuwa me zatayi da aure?......wanne tsautsayi ne zai kaita damqa rayuwarta hannun d'a namiji guda daya yayita hajijiya da rayuwarta ba gaira ba dalili?.
Abubuwan data gani din dasu ta kwana,su suka yita yiwa kunnuwa da idanuwanta gizo,kuma suka hanata komawa duba ayshatu.....suka kuma sanyata jin ta matsu ta kora mika'il mashkur harma da ya'aqoub din daga rayuwarta gaba daya.
Kafin tabar wajen taji alamun shigowar saqo. Koda ta duba alert ne daga banki da sunan mika'il wanda ya sanya mata 1mil a matsayin kudin mota kawai. Ta juya wayar a hannunta,ta sake juyata,sai kuma ta saki siririn tsaki tana ajeta a gefe.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 67
Kamar kowanne lokaci,yakanyi breakfast dinsa ne a sassansa,saboda duk wani abu da zaiyi breakfast dashi yasha banban da cimar mutanen gidan. Wannan ya sanya ya aje cook dinsa daban wanda yasan tsare tsare na cimarsa. Koda a ranar baida ra'ayin cin abincin cikin gidan,nashi cook din zai masa irin abincin da yayi dai dai da ra'ayinsa,zai shiga ne kawai ya taya anni zaman cin abincin.
Yau din ranar litinin ne daya tsara abubuwa da yawa da zaiyin. Bakwai da mituna goma sha shida ya murza handle na bedroom dinsa ya soma takowa a nutse zuwa ainihin parlor dinsa.
Yayi wani sassanyan kyau cikin tsadajjen yadin Qiviut fabric me tsananin taushi da kuma rashin nauyi,daya daga cikin favourite yadiddikansa duk da tsadar da suke dashi amma baya jin wannan. Metro blue ne da yayi matuqar haska fatarshi,ya kuma fidda sura haiba da cikar kamalarshi.
Fuskan nan a dinke kaman ko yaushe,wanda kusan duka safiya anni ko abba ne ke jefa murmushi a kanta,sai kuma fitinannenshi farouq musamman idan a sassan ya kwana,to fa kafin su rabu kowa ya wuce wajen aikinsa sai ya addabeshi har ya zare wannan yanayin daga kan fuskarsa din..
Yau din budadden takalmi ya sanya,abinda ya bawa zara zaran yatsunsa daman fitowa kenan cif da cif cikin takalmin da ya soma zareshi daga qafansa sanda ya iso dining area dinsa.
"Good morning sir" Cook din nasa daya kasance yaren igala ya furta cikin girmamawa yana rusunawa
"Morning ameh.....how are you?" Yana jan kujera zai zauna
"Fine sir...." Ya amsa masa yana matsowa da sauri gami da kama aikinsa na serving nasa komai. Wannan kuma shine ya bashi daman duba wayarsa da yaji tana vibration,wanda kusan koda yaushe idan zai kwanta bacci yana barinta ne a hakan gudun takura.
Sunan daya gani ya sakashi dan furzar da iska kadan daga bakinsa. Duk da cewa a yadda suka rabu jiya bayajin yau zata kira ta assasa wata matsalar ko damuwar,shidai baisan me yasa duk sanda zaiga kiranta hakanan ba sai wani abu ya tsirga masa ba.
Daidai sanda Ameh yake barin gurin ya daga wayar,ya ajeta daga gefansa bayan ya sakata a handsfree yana jawo mug din da ya zuba masa dafaffiyar madarar da aka watsa mata turmeric guda guda,wannan yadan sauya mata kala zuwa yellow kadan.
"Barka da asuba" Ya fadi cikin nutsuwar nan tasa. Murmushi ta saki daga daya sashen,cikin son nuna zallar kulawa tace masa
"Barka kadai.....kira nayi naji lafiyar d'ana ya ya tashi?,na kira dan uwanka wayarshi a kashe,ina fatan komai lafiya?" Kaman ko yaushe,duk wani motsi nata yana masa banbarakwai,yanzun ma haka ne,sai ya aje mug din yana hade hannayensa waje daya
"Mun tashi lpy alhmdlh.....da fatan kema haka......musaddiq ban fita cikin gidan ba tukunna,bamu hadu dashi ba". Fuska tadan yamutse,amma bata bari sautin muryarta ya canza ba
"To yayi ba damuwa.....amma ya kamata dai ace kasan kwananshi da tashinsa......banason yadda kuke nesa nesa da juna fa?".
Sai yaji maganar kamar ta saukar da murmushi cikin zuciyarsa,murmushin dake nannade da mamaki,amma sai ya basar
"In sha Allah"
"To hakan yayi.....nace ba?" Ta fada don janyo hankalinsa
"Ina tare dake maamah" Ya amsa mata tana duba agogon hannunsa da kuma qaramar wayar dake ajiye a gefe,wanda kiran saddiq yake shigowa
"Cewa nayi bari nayi muku tuni,dinner by 8pm yau......ina fatan zaku cikamin burina na kasancewa tare daku duk dare?". Idanunsa ya sake lumshewa,tsananin rashin gamsuwa da tsarij yana tsarga masa. Da can da waye da waye taci gaba da kasancewa duk daren a sanda ta tattarasu ta baiwa duniya kyautarsu?. Bayajin a stage din da ake kai yanzun zai yarda da ita ko ya gasgatata. Furucinta da kuma alaqarta da hajja harira ba zasu taba barin zuciyarsa ta nutsu da ita ba
"Okay.....we will be there in sha Allah"
"To yayi na gode.....sai na ganku" Ta fadi tana yanke kiran. Wayar yabi da kallo,har tayi maganar da tafi damunta,ta fadi kuma dalilin da ya sanya ta kirashi suka kammala wayar baiji addu'a guda daya daga bakinta ba.
Yaja numfashi me nauyi yakaishi xuwa cikinsa,ya tabbatar babu yadda za'ayi anni ta kirashi......walau yana qasar nan ko yana wata qasa su kammala maganar su bata bishi da kyawawan addu'o'in da ko yaushe yake jinsu har cikin tsakiyar zuciyarsa ba. Addu'a da tsaftaccen niyya da kuma manufa na alkhairi.
Hasken wayar ya sanyashi maida dubansa gareta,sai ya daga itama ya sakata a handsfree yana sake janyo mug dinsa yaci gaba da kurba
"Saura mintuna goma lokaci ya cika hamma"
"Gani nan......Moses ya qaraso?" Ya tambayeshi yana bude daya plate din dake gabansa
"Muna tare dashi"
"Okay.....get ready" Ya fada yana katse kiran tun kafin saddiq din ya katse nasa.
Kamar kowacce safiya,ya shiga wajen annin cikin nutsuwa mutuntawa da kuma qaunar daya tabbatar daga ubangiji take....irin qaunar da yayi imanin Allah ne ke sanyata cikin zukatan bayinsa aduk sanda yakeso. Ta gyara lullubin laffayarta tana masa addu'a,addu'ar data sanya rauni me yawa a zuciyarsa,raunin da yaso nunawa har sanda yake cikin motar da dagashi sai saddiq sai driver,sauran guards suna gabansa wasu a bayansa cikin wata motar ta daban.
Wacce irin rayuwa ce hakan wai?,wanda zai hafoka daban?,wanda zai gina maka rayuwa da kyakkyawan fata da kuma addu'o'i daban?. Wannan shine abinda ya dinga yi masa yawo akai,har daga qarshe ya samu ya yakice komai a ransa kafin su isa kamfanin.
Kamar kowanne lokaci isowarsa cikin kamfanin kadai yakan sanya kowa shiga hankalinsa. Hakan kuma yana da nasaba da rashin daukan wasansa da yadda yake daukan komai da muhimmanci. Wannan ya sanya duk wanda ke aiki dashi yake shiga taitayinsa yake ajiye komai a gefe sai idan ka fita wajen kamfanin.
Babban office ne dake dauke da kusan sashe biyu a cikinsa,wanda kusan kowanne sashe zaman kansa yakeyi. An qawatashi cikin tsari da nau'in kalolin da yafiso ya kuma fi ta'ammali dasu. Komai cikin tsari yake da tsananin tsafta tamkar wankewa da gyarawa kawai akeyi ba tare da ana shiga ba.
Yadda mamallakin office din ya zama na daban,haka office din nasa ya zama na musamman.
Hularsa ya zare ya ajiye su saman mulmulallen table din yana hadawa da wayoyinsa da system dinsa daya karba daga hannun ahmad,wanda shike jigilarsa tun daga sanda zai shigo kamfanin har ya fita.
Idanunsa na ga wasu files daya tarar saman table din,amma kunnuwansa na sauraren bayanin taheer.
Baice komai ba sai da ya gama sannan ya kalleshi
"Ina mika'il?" Yayi tambayar hankali kwance yana daga wasu takardu dake gefe
"Bai qaraso ba tukunna" Saddiq dake qoqarin kashe tab din hannunsa ya bawa fu'ad amsa.
"Alright.....trading manager da laboratory technician.....su da sauran staffs dake qasansu dukka ka shirya mana meeting.....one hour thirty minutes kawai,akwai meeting da zanyi da sababbin ma'aikatan da muka dauka kafin nayi wannan tafiyar"
"Done" Ya fadi cikin rusunawa da girmamawa.
Daya bayan daya yake duba duka aikin daya bari da wanda suke zaman jiransa. Wadanda yake buqatar qarin haske ya turawa saddiq komai ta email nashi,don shine yake da alhakin kula da komai daya shafeshi,kaman yadda komai din sai ya biyo ta hannun saddiq din kafin ya iso gareshi.
Duk da cewa yasan shi din mutum ne da baya saba lokaci ko karya magana,amma hakanan ya samu kansa da duba agogonsa.
Yau din gaba daya hankalinsa baya a jikinsa,yana jin cewa yau zata kasance babbar rana a gareshi wadda zata kafa tarihi cikin rayuwarsa da kyakkyawar yarinyar da ya tabbatar koda cikin bariki samun irinta abune me wahala.
Duk da 'yar hira da tattaunawa dake gudana tsakanin ma'aikatan hankalinsa shi ba'a wajen yake ba yayi nisa wajen wassafa yadda zai rayu da ita,yayi nisa wajen tsara yadda zai more rayuwarta da kyau.....ya kuma yi nisa wajen tsara yadda zai jiqata da kudi.....yadda zai sake maidata tauraruwa.....da kuma yadda zai maisheta abar kallo.
Muddin ya sameta yayi imanin zaiyi zarra cikin duniyar bariki,zai kuma tayar da hankulan abokan adawa da yawa,hakanan zai zama wani na daban daya mallaki babe din da baijin akwai sauran irinta.
Miqewar da ma'aikatan sukayi daga saman kujerun zamansu dake zagaye da kyakkyawan table ya sanyashi dawowa hayyacinsa. Miqewa ce taban girma ga CEO din nasu,wanda yake takowa cikin hall din cike da takunsa dake sake nuna zallar kamala da nutsuwar da Allah S W T ya hore masa.
Lafiyayyen kwarjinin nasa dake sake saka kowa shiga taitayinsa yana kwance saman fuskarsa. Basu zauna ba har sai daya basu izinin zama sannan shma ya zauna din.
Yadda suka saba gabatar da meeting irin wannan haka suka fara yanzun ma. Mataki bayan mataki,matsayi bayan matsayi. Yana biye da bayanan kowa ta sigar da idan ka kalleshi a haka zata tsammaci kaman baya fahimtar bayanan,don babu system ko abun rubutu ko daya a hannunsa,illama yatsun hannunsa daya sarqe cikin juna yana kallon duk wanda bayani yazo kansa.
A gaban mika'il din akwai mutane da sai sun kammala miqa nasu bayanan kafin azo kanshi. Duk sai yaji ya matsu,tamkar ya nemi a daga masa qafa tukunna ya fara gabatar da nasa bayanan. To amma ko giyar wake yasha yasan hakan bame yuwuwa bane,don waje ne da ba'a daukan irin wannan wargin.
"Ina neman afuwa,lokacin da na tsara zamu zauna din ina ganin kamar sai mun wuceshi.....zamu sake qara awa daya zuwa biyu......akwai me wani uzuri kaman na abinci?,shiga bayan gida da sauransu?". Yayi maganar cikin harshen turanci da wani irin daddadan accent,karyewa da lanqwashewar halshensa kawai ya isa ya gaya maka gwani ne wajen iya yaren.
Cikin rashin jin dadi mika'il din ke rarraba dubansa akan fuskokin staff's din,yana cike da fata da burin samun wanda zaice yana da uzuri shima ya zama na biyu da zai furta haka. Saidai kaman yadda zuciyarsa ke raya masa ba wanda ya nemi wannan excuse din,hasalima daya daga cikinsu cewa yayi
"Koda duka awanninmu na yau zaka qarar sir mun sadaukar maka dasu" Sauran suka shiga gyada kai. Kowannensu da wani irin qawa zuci da qauna ta gaske yake zaune dashi,duk da ba'a rasa qananu matsaloli da kowacce tafiya bata rabo dashi,amma ya gina wani irin qaunarshi a zukatansu da sadaukarwa me tarin gaske,wanda shi kansa baisan ya gina din ba. Saidai kuma abune sananne,duk wajen da ake samun kulawa tausayi da kyautatawa dole qauna ta biyo baya. Fada ce ta ma'aiki,an gina zukata abisa son wanda ke kyautata musu da qin wanda ke munana musu.
"Alright.....na gode" Ya fada da salon daya sake sanyawa kowa nutsuwa da qaunarsa a zuciya.
Boyayyar ajiyar zuciya mika'il din ya saki,gumi yana fara tsatsatsafo masa. Yafi kowa son samun kusanci da jadda......yafi kowa son ganin yafi kusancin dashi,yanaso yafi kowa samun fada da dama,don haka shi yafi cancanta ya nuna zallar biyayyarsa ga boss din ba wasu ba,don haka ya saki wani murmushi
"As you wish sir.....mu duka muna qarqashin cewarka ne". Kadan fuad ya waiwaya ya kalleshi,sai ya gyada masa kai ba tare da yace komai ba.
Gyara zamansa yayi saman kujerar kamar tana mintsininsa ne,yana jin kamar babbar asara tana shirin samunsa ne,kaman zai rasa wannan babbar damar ne a yau,wadda muddin ya rasata din baisan ranar da zai sake samunta ba. Sake danna wayarsa yayi ta kawo haske,lokacin da suka tsara zasu hadun yana dab da cika.
Wajen SMS ya shiga,ya rubuta gajeran saqo ya tura mata,idanunsa suna kan wayar yana fatan samun amsa daga wajenta,duk da kuwa yasan abune me wahalan gaske.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 68
Tunda suka dawo daga makarantar hankalinta yana kan wayar,dama kawai take nema da sabreen din zata fita ta samu ta fidda wayar. Ta tabbatar yayi kiranta har ya gaji,yanzun haka qila yana cike ne da kewarta.
Sunyi hira me tsaho dashi jiya cikin toilet,wanda ta dinga mamakin yadda yasan wasu abubuwan a kansu,saidai amsar daya bata ta cire dukkan wani zargi nasa daga ranta
"Indai zakiyi mamakin yadda akayi nasan rayuwarki huda ashe son da nake miki ma baikai nan ba......kina wasa da kalar soyayyar da nakeyi miki ko?" Idanunta ta lumshe har cikin zuciyarta tana jin a yau din bayan yaa sabreen din ta sake samun wani barin zuciyar wanda ya damu da rayuwarta ya kuma damu da damuwarta. Har yake iya sanin wacece ita a rayuwa ba tare data sani ba saboda tsananin son da yake mata
"Inason na daukeki daga gidanku huda.....na killaceki daga rayuwar da kike ciki......na hana kunnuwa da idanuwanki ji ko ganin duk wani mummunar kalma duk don saboda yaa sabreen....". Ta riga tayi amanna yasan komai kawai a kansu har akan sabreen din,don haka sai ta lumshe ido zuciyarta tana karyewa
"Ba rayuwar da tafi rayuwar aure daraja da martaba a wajen mace.....qila idan yaa sabreen dinki taga zakiyi aure itama tayi" Ya fada cikin salon karya harshe dason nuna yadda zuciya ta karye,saidai a gefe guda yana sone kawai ya cusa wani kakkaifan abu a zuciyarta.
"Banji dadin shaidar dana ji daga bakunan mutane a kanta ba.....don nima a yanzun ina daukarta kamar yaya take a gareni".
"Hameed....." Ta katseshi cikin rauni.
"Muyi kowacce magana dakai amma banda ta yaa sabreen,don zuciyata me rauni ce a kanta,ita din komai namu ce....."
"I know huda.....i know,but inason na killaceki huda na daukaka darajarki.....inason ta silarki ya sabreen dinki ta zauna waje daya,ta samu martaba irinta....." Sai kuma yayi shuru bai qarasa ba,shurun da itama hudan da zuciyarta ke mata zugi ta zabi yinsa.
"Zamuyi waya anjima idan kin samu lokaci.....i so much love you....please take care" Ya fadi yana katse kiran ya barta da yawa a hannu.
Zare wayar tayi daga kunnenta jikinta yana yin sanyi. Kenan kowa ma yana dora tuhuma akan yaa sabreen?,kowa ma yana da zargi a kanta?. Idan dai har Hameed da yake baqo a unguwar dama rayuwarsu gaba daya zai iya samun wani abu a kanta to ya kenan sauran jama'a suke kallonta?.
Shin gaskiya Hameed yake fadi?,tayi aurenta kawai ko hankalin yaa sabreen dinta zai dawo daidai?. To shin me yasa yaa sabreen din ba zata zauna kaman kowacce mace ba?. Me yasa bayan ta samu kudaden da sun isa ta riqe musu rayuwa?.....me yasa ba zata haqura ba?....me yasa?,meye dalilinta?,idan a baya tana da hujja tana da dalili yanzun meye dalilinta?.
Wadannan tarin tambayoyin su suka dinga yi mata kai kawo,sannu a hankali sai taji kaman tana da ja akan sabreen din,tana kuma qalubalantarta duk da harshe ko aikinta bai nuna ba....... Amma tun daga sannan can qasan zuciyarta wutar hakan tana ruruwa sannu a hankali.
Kamar wadda ke ciwon jiki haka ta dinga aiwatar da komai. Duk da tana da daukan lokaci wajen wanka da shirinta amma a yau din sai abun ya sake ninkuwa.
Ta gyare gashinta ta kuma dameshi cikin band madaidaici,ta gama shafa cream dinta na musamman dake qarawa fatarta glowing cikin kowanne yanayi,amma kuma saita kasa ci gaba da yin komai.
Bata taba ayyukan da suka tsaye mata a rai takejin ta takura ba irin aikin Mikhail dana mashkur da cikin qarshen satin nan zata yishi. Batasan dalili ba......amma ta alaqanta hakan da canzawar salon aikin. Ma'ana kowannensu zata kasance dashi cikin dakin hotel daga awa daya har zuwa sanda aikin zai kammala. Shin tana da tabbacin kubuta daga hannun miyagun kurayen da dama dama suke nema irin wannan?,mutanen da suke kallon diya mace cikin idanuwansu da wani irin duba kwatankwacin duban da mayunwacin zaki kewa nama a yayin da sukayi arangama?.
Tana zaunen amma tana lura da yawan shige da ficen da huda keyi tsakanin falon zuwa dakinsu. Kaman zatayi mata magana sai kuma ta basar,don tana da wani irin dabi'a nabin komai da idanu har sai sanda ta samu cikakken hujja ko makama a kanshi.
Qarar yar siririyar wayar da tasan kiranta na dabanne shine ya dauki hankalinta. Wanda ta zata din shine kuwa,Jib ne,sai ta daga kiran tana rage volume na kiran.
"Hello jib?" Ta furta daidai sanda huda ke ficewa a dakin. Samun kanta tayi da jan qaramin tsaki can qasan ranta. Jib?....ko waye kuma da wannan sunan?,zai iya yiwuwa wannan shirin da takeyi ma fita zatayi,kuma wajensa zata je,idan mace da namiji suka kebanta a waje daya kuma me zai biyo baya?,idan taje gurinsa me zasu aikata?..... Tambayar data yiwa kanta kenan ta qarshe data sanya bugun zuciyarta qaruwa,saita samu kanta tana saurin dakatar da kanta daga wannan tunanin tana furta
"A'uxubillah" Wani sashen na zuciyarta kuma yana gaya mata
"Yaa sabreen ce fa?" Idanunta ta lumshe tana son sake jaddadawa kanta eh.....ya sabreen ce,amma wani sashen kuma yana qoqarin maidata baya.
"Yadda kika tsara abun bazai yiwu ba sister.....dole ya kasance kuna tare nan da awa guda......mafi kyau kuma ku isa wajen tare koda xaku shiga ta qofa daban dabanne......don na bincika a yanzun kamar suna dakin meeting da boss dinsu..... Meeting din kuma zai zamana sun tattauna muhimman abubuwa.....na lissafa zasu soma lissafi na kudaden da company ke dashi a qasa......zasuyi musayar documents da bayanai,zaa tashi ba tare da sun kammala ba don bayanan yana da yawa,kuma owner na kamfanin jadda baya saba lokaci......wadannan bayanan da zasu kasance tare dashi ina da buqatar wasu abubuwa a ciki da zasu sauqaqamin kutsa kai cikin account din muyi aikinmu da wurwuri mu gama.......inaso kuma aikin na gamashi ne a daidai lokacin da masu kula da komai nasu suka tafi hutun fitowa daga meeting din....idan zaiyiwu ki samu kaiwa office dinsa,akwai wani ajiyayyen code cikin files na office din da zaki ciromin,kin fahimta?"
Dukkanin bayanan sa ta fahimta ta kuma gamsu,to amma kimarta fa?. Bata saba yin magana ta dawo ta warware ta ba
"Kada kiyi tunanin komai.....wannan ce rana ta qarshe tsakaninki dashi.....kuma wadannan sune awannin qarshe da aishatu keda chance na tsallakewa siradinta".
"Ba damuwa" Ta bawa jib amsa a taqaice tana yanke kiran.
Wayar ta aje a gabanta kawai tana kallonta tare da tunanin da yadda zata sake requesting wa mika'il din su kasance tare tun yanzu?. Kaman ana jira ta yiwa kanta tambayar saiga shigowar saqonsa.
Tana duba saqon tana jin sanyi da yadda komai yazo mata a sauqaqe. Duk da hakan ya faranta mata amma saita ajiye wayar bayan ta gama dubawa,ta miqe kawai ta isa wardrobe dinta tana laluben suturar da zata dace da jikinta da kuma yanayin.
Shurun nata da rashin samun amsarta ya qara masa yawan rashin sukuni. Ya dinga duba wayarsa duk bayan wucewar wasu mintuna,har sai daya kasa jurewa ya sake tafa massage dij har sau biyu ya tura mata a jere.
Saqon ya shigo mata sanda take daura agogon hannunta ne,tun taga sunan tasan shine,bata bi takai ba sai data gama daurawar,ya qara barima a kunnenta tayi Rolling mayafin Turkish dress din,ta kuma jawo kimono din kayan da suke zuwa tare da shirt me dogon hannu da skirt din ta aza saman kayan sannan ta dauki wayar ta bude tana maida masa amsa
"What's the adress?.....zan taddaka har inda kake don farincikinka".
Sai data maimaita karanta saqon kusan sau hudu,tana mamakin yau itace da kanta zata turawa wani d'a namiji saqo da yayi kama da wannan?. Ji tayi kaman ba zata iya turawar ba,ta aje wayar saman madubi tana furzar da iska daga bakinta
"No way out" Taji zuciyarta na gaya mata,dole ta tura muddin tanason cika mission din. Tana so ta rabu ne da mikail.....ba kuma zata iya barinsa salin alin ya wuce hakanan ba,sai ta miqa hannunta ta sake bude wayar,ta danna send sannan ta maida wayar ta ajiye.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 69
Bayan maimaita karanta saqon da yayi,har sai data kaishi ga murza idanun nasa don ya tabbatar daidai ya gani ko kuwa akasin hakan?.
Jikinsa har rawa yake wajen maida mata reply,har bai lura da yadda Muhammed jadda ya zuba masa idanu ba yana karantar yanayinsa.
"Mr mika'il" Ya kirayi sunansa da husky voice dinsan nan dake ratsa zukata su kuma maida hankalin mutum zuwa jikinsa.
"Yes.....yes sir" Ya fada adan daburce yana qoqarin tattara masa nutsuwarsa bayan ya tabbatar da isar saqon zuwa wayarta. Bawai address kawai ba,harda code da zata samu zarafin bude office dinsa ta shiga ta zauna tayi tsimayensa.
Murmushine ya subuce mata da ganin yadda ya bata komai in details. Ba wani shakka ko kokwanto. Wato shi namijin bariki akan mace susutacce ne?.....sannan fiye da rabin maza ta fuskanci ba kasafai suke iya mallakar kansu ba idan batu ake na mace. Wani zaka hangi fuskarsa cike da kamala amma muddin aka raba masa mace a nan dukka rauninsa yake bayyana. Bai tsoro shakka ko kwanton ita din fa baquwa ce cikin rayuwarsa gaba daya?.
"Good job mika'il" Ta fadi murya can qasa tana forwarding ma JIB komai.
"Kana tare damu?" Muhammad jadda ya sake jefa masa tambayar yana dage girarsa dukka biyun
"Yes.....yes sir" Ya fadi yana sakar masa murmushi don ya amintar dashi. Idanu yadan tsareshi dashi kaman meson karantar wani abu,wanda duka duka cikin mintuna biyar ya dauke idanun yana cewa
"Bismillah" Tare da maida idon nasa saman farar takardar gabansa da daya daga cikin ma'aikatan ya gabatar.
Sai da yayi namijin qoqarin daidaita nutsuwarsa sannan ya fara gabatar masa da komai daki daki.
Sai data buda qaramar handbag dinta ta tabbatar ta sanya komai a ciki sannan ta fiddo dubu biyu a ciki ta miqawa huda dake tsaye a gabanta
"Masu kamfanin pure water zasu kawo ruwa....ki basu wannan idan sun kawo.....naso saikun wuce islamiyya kafin na fita.....amma it's urgent.....kiyi qoqari ku fita da wuri kada kuyi latti"
"A dawo lafiya" Ta fadi bayan ta karbi kudin. Qasan ranta fal farinciki,a yau din zatayi hira da hameed yadda ranta keso,don zata saitawa su nadra hanya zuwa islamiyya ne ita kuma ta baje kolin soyayyarta yadda ranta yakeso.
Gaban haneefa ta qarasa tana sakin murmushi,itama haneefa din murmushi ta saki,hannunta ta dora saman sumarta data cirewa dankwali. A kullum fuskar haneefa ba wanda take tuna mata dashi sai umminsu. Akwai shaquwa da sabo me tsanani tsakaninsu.......amma duk da haka saida mutuwa tayi aikinta ta raba tsakaninsu.
"Ayimin addua auta....zan kawo miki abun dadi"
"A dawo lafiya yaa sabreen........amma yau kam sabuwan teddy nakeso ki sayamin"
"Ke kuwa ki rasa abinda zaki zaba sai Teddy?" Nadra ta fada tana qyalqyala dariya
"To madam tsokana.....ba ruwanki" Sabreen tayi hanzarin katse nadra data wuce daki tana ci gaba da dariyar tsokana din hadi da yiwa sabreen a dawo lafiya.
Tana takawa don fita daga layinsu ta isa bakin titi amma tunanin qannen nata ne a ranta. Batason ko kadan yadda kullum sai ta fita ta barsu,wani lokaci su fita tare saidai su rufe dakin,harma wasu lokutan su rigata dawowa. A yanzun huda tafi tsaye mata a rai,tunda har ta cika shekara sha biyar ta shiga ta sha shida tana da buqatar sanya idanunta a kanta,don mataki ne da komai daga nan yake farawa daga rayuwar yarinya. Duk da inda ace ita din me gata ce,ita dinma tana buqatar kulawa ne tare da qarasa rainon tarbiyyarta.
Ko kusa ko alama bata lura dashi ba,don tayi nisa a tunaninta,sai muryarsa taji daga gefanta.
"Um uhmmm......sai ina kuma haka?" A nutse ta waiwaya tare da sake rage yanayin tafiyar tata tana kallonshi.
Tsaf yake kallonta,ya turo hula gaban goshinsa yana mata wani irin kallo. Idanunta ta dauke don bata buqatar yanayin kallon da yake binta dashi. Ta sani haushinta yakeji qwarai,tun waccar ranar data hanashi kudi. Wannan duka ba damuwarta bane,don idan da sabo ta saba,sai ta watsar da wannan batun kamar kullum tace dashi
"Barka da warhaka kawu.....an yini lafiya?"
"Ras na wuni.....ko kin dauka zan mutu ne saboda kin hanani kudinki?,to kisha kuruminki 'yar nan......cikin satinnan da yardar me duka arziqi zai fashemin......sunana zai fantsama a duniyar masu arziqi......daga sama'ila zan koma alhaji ismai'il sha maka Allahu". A mamakance take kallonsa,tadai sani bashi da wata sana'a data wuce caca,kuma muddin ka jishi yana lissafin maquden kudade irin wannan to wata caca za'a buga kuma yake sanya ran zai cinye.
"Allah ya bada sa'a.....amma dai kawu.....caca"
"Akul naji bakinki.....dani dake ai dan juma ne da dan jummai... Ke har gwara ni duk tsiya".
Kanta ta dauke tana hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya,bata sake tanka masa ba sai ta fara takawa tana barin wajen. Har tayi taku hudu qwarara ya qwala mata kira da ainihin sunanta
"Aminatu" Dakatawa tayi don ba zata iya ci gaba da tafiya ba,ba'a canzawa tuwo suna,duk duniya kawu sama'ila ubanta ne.
"Ke wato baki jin ko dar idan an miki gugar zana ko?,to miqomin wani abu nan,ki rubuta shi a lissafi duka cikin satin nan zan biyaki" Ya fada yana miqa mata hannu tamkar ya bata ajiya. Idanu ta xuba masa,sai kuma ta sanya hannu tana sauke jakarta daga kafada,ta zuge ta fidda dubu dubu guda hudu ta miqa masa.
Karba yayi yana juyasu alamun a raine suke a wajensa,sai ya yatsina fuska
"Ki rasa abinda zaki ban sai wannan?,kai Allah ka dawo mana da arziqinmu za'a sha kallo wallahi......" Daga haka ya juya yana cusasu a aljihu tare da barin gurin bai kuma sake bi takan inda zataje din ba.
Kasa ci gaba da tafiya tayi har sai daya bacewa ganinta,ta kada kai ta na yin gaba kamar kullum zuciyar nan cike da nazarin rayuwa . Tun daga rasuwar mahaifinsu har ta mahaifiyarsu bai taba miqo komai yace musu gashi ba wai don su rayu.....amma ita ba zata iya qirga ko lissafa adadin sau nawa ya karba daga hannunta ba,kuma a raine,ba godi bare na gode.
Ya riga ya bata shaidan da zata nuna na cewa shi take nema,wannan ya sanya bata samu matsalar shiga kamfanin ba tun daga gate din farko gate na biyu,ta zarce zuwa main entrance,ta ratsa reception da sauran guraben da kamfanin yake dashi kai tsaye kuma ta isa ga office din.
Tayi amfani da code din ya kuma bude mata successful. Ta tura qofan a hankali kamar me tsoron shiga qaramin murmushi na sauka saman fuskarta
"Quda a wajen kwadayi akan mutu" Ta furta qasa qasa tana sanya qafafunta cikin office din. Har ta fara takawa sai kuma ta tsaya cak tana wurga idanunta sassa sassa na qawataccen office din da aka narka kudi akayi masa wani irin lafiyayyen tsari me daukan hankali. Tabbas tasan babu yadda za'ayi guri irin wannan ya rasa CCTV camera,indai kuma hakanne ta yaya zata iya gudanar da komai ba tare data samu wata matsala ba?.
Dan wani abu cikin kunnenta ta matsa,muryar JIB ta bayyana,sai ta danja da baya kadan ta raba qafa tsakanin office din da veranda din da jerin gwanon office din yake don bataso ta fito gaba daya ko ta shiga gaba daya don kada camera din ya samu damar nunata
"Ni dakai duka bamuyi tunanin CCTV ba jib?".
"Ya salam" Ya fadi yana aje wani numfashi
"Haka ne......wasu lokuta dama kece ke mana hasshen irin wadannan abubuwan......ba matsala bane,manyan kamfanoni irin wadannan akwai irin cameras din da suke amfani dasu,katseshi ba zaiyi wahala ba nasan takan irinsu sosai......yanzu ki tsaya daga nan inda kike...kafin ki shiga ki gano mana daga wanne saiti camera din yake shikenan kawai"
"Okay....."
"....karki datse connection daga nan har mu gama aikin"
"So kaji komai tsakaninmu kenan bayan sirri ne?" Ta fada cikin dan salon zolaya da wani lokaci takeyi masa. Dariya ya qyalqyale da ita kadan yana fadin
"Tuba nake....Allah yabar soyayya". Sai kawai ta saki murmushi kadan tana tura qofar hadi da sake qarewa office din kallon tsaf.
Cikin qasa da minti goma ta gano komai suka kuma katse sadarwa da tsaida aikin camera din. Da dan hanzari ta ajjiye hand bag dinta. Tanaso tayi komai ne ta gama kada damar ta subuce mata yazo ya shigo.
Sai data tattara dukka hankalinta da nutsuwarta ta karanci inda komai yake ajiye a office din,gudun kada ta taba wani abu ta kasa maidashi daidai inda yake hakan ya nuna masa alamar tayi masa bincike. Hatta da biro dake ajiye qwaya daya tal saman teburin sai data karanci a yadda yake ajiye din,ta dauka ta kuma gwada maidawa ta tabbatar ya zauna kaman yadda aka ajiyeshi. Wayarta ta fidda,ta sake yiwa office din qaramin video komai da komai sannan ta maida wayar jakar,ta kuma shiga aikin bincika komai daki daki.
Baya ga abinda suke nema taga abubuwa da yawa cikin office din,irinsu condom dake nuna mata lallai riqqaqqen dan bin mata ne,taaba irin masu tsadar nan da sauran abubuwan maye. Abinda ya sake darsa mata mugun tsanarsa kenan,wutar kuma ta tabashin ta hanyar kwakwashe masa komai tana sake ruruwa cikin ranta. Ya zama dole ta durqusar dashi,durqusarwar da bazai sake tashi ba.
Maida komai tayi kaman ba wani abu daya faru a office din,ta tattare duk abubuwan da take nema din tayi musu ajiya ta musamman cikin jakarta. Hatta da wani qaramin ledar cake da akaci aka barshi sai data tabbatar ta maidashi yadda yake,ta gyara rolling dinta da kyau tana sauke numfashin samun nasarar kammala komai ba tare daya dawo ba.
Maqoshinta taji ya bushe tana da buqatar ruwa,sai ta taka tana nufar kyakkyawan fridge din dake girke waje daya.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 70
Turus tayi tana kallon yadda aka maqare gidan farko na fridge din da wasu kalan kwalabe da bata saba ganin irinsu ba. A hankali take dubasu har ta fahimci kwalaben na meye?.
Kwalaben giya ne tabbas,ta maida idanunta ta lumshe tana furta
"Innalillahi" Can qasan harshenta. Sai kuma taja jikinta baya a hankali tana matsawa daga jikin fridge din don batajin zata iya shan wani abun sha daya fito daga fridge din komai halascinsa.
Zuciyarta ke qara bugawa da tsanarsa haushi da kuma takaici. Shikam mikail dame zaiji?,abubuwan ai sunyi masa yawa,sun masa yawan da batasan wanne a ciki zai iya dauka ba. Kaman ana son bata amsar tambayarta sai qofar tayi qaramar qara alamun ana budeta ne,ba jimawa ya bayyana cikin office din yana dubanta da murmushi
"Am so sorry dear......ina fata banyi keeping naki da yawa ba......boss ne idan ya tashi aikinsa tamkar engine.......baya gajiya,na samu na kubota da qyar".
Idanunta ta dauke daga kan files din da yake rungume dasu,wanda ta tabbatar a cikinsa sauran bayanan da take nema suke. Ta kalato dukkan dauriyarta ta jefeshi da qaramin murmushi
"You deserve it ai....."
"Wow......serious?" Ya fada da wani irin zumudi da zakwadi yana qarasowa gabanta dab da ita ya zauna har yana neman hade gwiwoyinsu guri guda. A dabarance ta miqe da sauri,sai ya bita da kallo. Taji a jikinta yana kallonta ne don haka ba tare data juyo ba tace
"Bari nayi fitsari kadan"
"Oh....okay to dear" Ya fada yana dora files din saman table din cikin ransa yana qissima yadda a yau din zai gwangwaje,a yau din zai kashe duk wata qishirwa tasa dake damunshi a rai.....a yau zaiyi morewar da bayajin ko daren amarcinsa zaiyi wannan.
Gaban madubij toilet din ta tsaya tana sauke numfashi idanunta akan fuskartata. Muryarta can qasa tace
"Please jib.....muyi komai mu gama da sauri......banason ganin fuskarshi kwata kwata"
"I know.....zanyi iya qoqarina......amma please kada kice zakiyi halin hawainiyar nan taki" Dan murmushi ta saki,yasan halinta sarai,koda nawa aikin zai basu idan ta motsa mata tana iya cancel dinsa
"Zanyi qoqarin nima" Ta amsa masa tana kunna famfo sai ta bige da daura alwala.
Mutum hudu ke biye dashi sanda yake takowa cikin veranda din idanunsa saman takardar dake hannunsa yana sake karanta abinda take dauke dashi. Can qasan zuciyarsa akwai wani kokwanto da mamaki,kusan zaman yau da suka fara yi da mikail wanda ba'a qarqareshi ba saboda quracewar lokaci ya karanci kamar hankalinsa ba gurin yake ba sam sam. Yana karance da kuma bibiye da motsinsa. Duk muhimmanci da girman takardar a wajen kamfanin gaba daya amma har ya iya mantota cikin dakin taron,wannan ya sanya ya yanke biyoshi da kanshi ya kawo masa don ya sake alamta masa muhimmancin takardar.
"Wait here" Ya fadi a nutse ga mutanen dake bayanshi yana sanya code na qofar office din Mikhail din ta bude ya murza handle din yana turawa can qasan ransa yana jin kamar bai kamata yayi hakan ba ba tare daya nema izinin shigar ba. Duk da kowanne office a qarqashinsa yake amma bai shiga office din kowa,hakanan baya taba bada damar a bude maka office muddin baka nan,amma haka kawai yau din yaji yayi hakan.
Sanda ya murda handle din yake shigowa da sallama cikin husky and deep voice nashin nan,dai dai sannan itama ta bude qofar toilet din ta fito tana qoqarin maida rolling na mayafinta.
Idanunsa kan mikail daya miqe a rude cike da tsananin mamakin ganin boss din nasa yau da kanshi a office dinsa gabansa yana faduwa,yayin da nata idanun suke kan fu'ad fuskar fu'ad din tana dubansa qasan ranta tana jin kamar tasan wannan fuskar.
Baikai ga lura da ita ba ya miqa masa takardar
"Keep it......." Ya furta da wani irin yanayi idanunsa cikin tsakiyar qwayar idanun mikail wanda hakan kadai ya isa ya gaya masa wani gargadi yake aika masa da kuma muhimmancin da takardar ke dashi
"In sha Allah sir" Ya amsa yana karbarta da hannu biyu. Juyawa yayi da zummar ficewa a office din,dai dai sannan idonsa ya sauka a kanta. Idanunasu suka gauraya waje daya,sai tayi saurin zare dubanta daga kan fuskar tashi gabanta yayi wani irin faduwar da batasan meye dalili ba.
Dan zuba mata ido yayi na sakanni tamkar zaiyi magana,sai kuma ya fasa,ya juya ya kalli mikail sannan ya maida dubansa kanta sai kuma ya juya yana ficewa a nutse daga office din.
Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke. Allah ya sanya ba zuwa yayi ya samesu cikin wani yanayi ba da dukka sauran gaskiyarsa da yakeson tabbatarwa boos din a yau babu ita.
Yasan an jima ana kai masa tsegumin halinsa,amma kasancewar shi din ba mutum bane me daukan qananun maganganu ya sanya abun bai wani tasiri ba.
A yadda yake jinsa a dan rude sai yaji yana buqatar giya don daidaita nutsuwarsa. Ya tafi zuwa fridge din yana fadin
"Boss......bashi da sauqi kwata kwata,idan har wani kuskure ya faru tsaf zaka rasa aikinka,a wajensa wannan din ba wani abu bane me wahala".
Batace dashi komai ba kaman yadda bata kula da abinda ya dauko yakw sha ba,ta qarasa wani sashe na dakin ta tayar da sallah kawai don lokacinta ya shiga.
Tunda ta tayar da sallar har ta idar yaba zubawa cikinsa barasa. Sanda ta sallame din saita kafeshi da idanu kawai. Ranta cike fal da mamakin yadda dan adam da hannunsa zai dinga durawa cikinsa abinda yasan zai cutar dashi?.
Waiwayowa yayi sai suka hada ido. Ta hade fuska da kyau tana miqewa
"Banason wannan abar sam... Muddin kanason mu kasance tare kuwa saidai ka rabu da ita" Tayi maganar duka tana jin wani iri har cikin ranta
"Am sorry dear.......indai wannna ne kada ki damu na ajiye".
Tana maida takalmin qafarta tana tunanin yadda zata samu ta duba takardar da boos din nasa ya kawo masa yanzu?.
Ta kalleshi tana gyara zamanta bayan ta gama saka takalmin
"No water no drinks?" Murmushi ya sake mata
"Akwai mana.....gasucan a fridge sai kalan wanda kikeso" Kai ta girgiza
"Ba wani abu da zai fita a fridge dinnan na sha shi"
"Why?" Ya tambayeta yana zare ido
"Na tsani shaye shaye" Ta bashi amsa kai tsaye,amsar data sakashi sake zaro idanu
"Duk kyan nan naki babe?,kinsan yanzun macen bariki bata gama cika ba sai ta hada da cakewa?". Ido ta dan rufe kadan tana budesu,kalmar MACEN BARIKI da yayi amfani da ita a kanta tana mata quna sosai cikin rai
"Cikar wannan kyan naki babe ki dinga taba wani abun da zai sanya ki dinga jin kanki very high......Ni zan dauki nauyin baki komai mai tsada wanda ba kowacce yarinya ce ta isa ta samesu ba......sai irinku matan da kuke da gata a wajen partner dinsu......like kaman wannan giyar.....bata bugar dani,saidai nayi bacci na awa daya shikenan idan na farka zan jini fresh......please ki koya sha ko kadanne akwai dadi,saikin gwada zaki gayamin" Yayi maganar yana qoqarin sake zuba wata a cup da alama kuma ita yake da niyyar baiwa idan ya zuba din.
Tsam ta miqe tana jawo jakarta dake a gefanta tana ratayawa
"Ya haka kuma?" Ya tambaya yana dubanta
"Zan wuce gida" Da sauri ya diro daga saman kujerar da yake kai
"Haba babe.....me yayi zafi?,bayan baki cikan alqawari na ba......kinsan dakin nawa na kama mana a Bristol kawai saboda yau?" Idanunta ta juya tana ajiye numfashi
"Banga alamun ka dauko wannan hanyar ba......kana yimin maganar abinda babu shi a tsarina.......baka iya saukar baqo ba sam......na nema abun sha kana min sharhin da lokacinka yake ci maka......idan lokacin dana diba ya cika zan tafi koda ba komai daka samu"
"Ba za'ayi haka ba" Ya fada da hautsine jin zaiyi asaran abinda ya qwallafa rai a kai,ya ajjiye komai na hannunsa ciki harda takardar da yanzu yanzu aka jaddada masa muhimmancinta yayi hanyar fita daga office din.
Wannan shine ya bata cikakkiyar damar qarasawa,ta fidda wayarta tayi snapping takardar ta turawa JIB kai tsaye ta share komai ta koma mazauninta tana jiran dawowarsa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 71
Kai tsaye ya wuce saman sofan dake ajiye bangare daban na office din yana zame takalman qafarsa. Already sunyi sallan azahar bayan fitowarsu daga hall din,don haka ya maida bayansa kadan ya jingina da sofa din.
So yake ya huta kadan kafin ya fita yaje yaga baqinsa,to amma tunani ya hanashi hutawar,don maamah ce ta fado a ransa,sai ya fidda waya yana kiran musaddiq idanunsa akan agogo yana qirga yawan awannin da suka rage da zasu maidasu gida su duka. Ko kadan bazai bari musaddiq yaci gaba da mu'amala da gidan maamah haka kai tsaye ba,ko mu'amala da dukkan wani abu daya shafi gidan game da abinci ko abun sha ba. Don sam hankalinsa bai kwanta ba bazai kuma taba kwanciya ba,don ta kashe dukkan wani abu da zai bashi nutsuwa tattare da ita.
Bugu daya ya daga,muryarshi ta fita cikin girmamawa.
"Qarfe nawa zaku bar company yau din?".
"Zamu dan jima yau,saboda akwai sabbin fertilizer da aka muka fitar,zamu gabatar dashi ga manoma"
"Yayi kyau,idan kun kammala kafin ka fita a company din ka sanarmin"
"In sha Allah" Ya fada a girmame.
Katse wayar yayi yana sanya hannu zai jawo file din daya shigo dashi sai kuma abun ya fado masa. Ya tsaya cak yana juya ganin da yayi mata. Daga toilet ta fito,jikinta duk damshi da lema da yake nuna ta taba ruwa,to me yakai mace office din mikail?.
Ya jima yana jin maganganu iri iri akan mikail din,to amma shi din ba mutum bane ke daukan qananun maganganu shi yasa bai taba bi takai ba. Hakanan bai fiya zafafa bincike da bin al'aurar mutum ba. Amma yau haka kawai yaji maganganun da yakeji a kanshi din yana dawo masa.
Muqamin da Mikhail yake dashi a company din bashi da alaqa sam da hada hadar jama'a karbar baqi ko mu'amala dasu ballantana yace harkar kasuwanci ne ya kawota wajensa.
Qaramin tsaki yaja yana qoqarin watsar da maganar. Ta iya yiwuwa irin watsatsun 'yammatan nan ne dake yawon bin maza office office dinsu don kawai son abun duniya. Muddin ko haka ne shi bazai bari wannan ta faru cikin kamfaninsa ba. Dukiya yake nema ta halal me cike da albarka,dole duk wanda yake qasansa ya kiyaye dokar Allah lokacin mu'amalarsu,bayan kuma mutum ya fita daga kamfanin saura ya rage nashi.
Zancen ya maqale a ransa duk da ya bude file yana dubawa,qananun shekarun daya fuskanta tana dasu su sukafi tsaye masa a ido duk da ba qare mata kallo yayi ba,yana tsoron kada ya zamana yaudarota yayi ya kawota office dinsa?. Wayarsa ya zaro ya laluba number saddiq da ya baro a first floor yana ganin ma'aikatan da suke da buqatar dauka kafin shi ya gansu yayi final interview dasu.
Ringing biyu ya daga,sai ya zauna sosai ya sake tambayarsa inda yake duk da yasan a inda yake din
"Muna qasa.....na kusa kammalawa dasu"
"Alright......kasan me nakeso da kai?" Ya tambayeshi yana shafa baqar kwantacciyar sumar dake gefan fuskarsa zuwa habarsa
"Aah hamma"
"Mikail......ina buqatar kowanne motsi nasa daga yanzu ya zama ana min monitoring nasa"
"Done hamma" Saddiq din ya fada cikin qwarin gwiwa.
Sosai wannan aikin da hamman ya bashi yayi masa dadi,don ya jima yana ganin abubuwan zargi masu yawa tattare da mika'il din,to amma baida cikakkiyar hujja da zai gabatarwa da hamma,shi kuma hamma koda kana da hujja sanda zaka gaya masa magana sai ya bincika ya tabbatar da gaskiyar maganarka.
Minti talatin ya sake duba agogonsa. Yana shirin miqewa saddiq din ya shigo,ya gabatar masa da komai ya ajiye masa duka takaddun
"Well done" Fu'ad ya fadi bayan ya tabbatar da komai ya tafi daidai.
"Kira me sunan malam.....wanne time ya bawa mutanen nan?" Ya gayawa saddiq daya kasance executive assistant dinsa wani lokaci ya juya ya zama P.A dinsa,har muqamin me sunan malam dinma yana hawa wato scheduling coordinator ma gaba daya.
Hularsa ya dauka da agogonsa daya jiye a gefe,ya qarasa ya sanya takalmansa daidai sanda executive Porter dinsa ya shigo
Shi ya dauki sauran kayan da yasan zai iya fita dasu din,yabi bayansa,yayin da musaddiq ya tsaya don ya qarasa killace komai ya kashe sauran electronics dake kunne,don yasan ba lallai su sake dawowa ta kamfanin sai kuma gobe.
Yana fita suka hadu dame sunan malam din,sai yabi bayansa suna takawa a nutse yana gaya masa sauran schedule dinsa na yau duka
"Amma sir.....sai nakega kaman abubuwan sunyi yawa.....ko akwai abinda zaa rage ko a sauyashi a kaishi gobe?".
Kansa ya girgiza sanda saddiq ya matso yana scanning keycard jikin designated elevator din da shi daya yake amfani dashi cikin company din.
"Kada ayi cancel komai.....zamu kammala in sha Allah komin dare.....make sure kowanne ka sanar masa da exact time da zamu hadun"
"Yes sir" Me sunan malam ya fada yana bawa guards dinsa waje,daya daga cikinsu yayi gaba don tabbatar da lafiyar elevator din duk da anyi keeping nata waje daya kuma don saboda shi,muhammad jadda yabi bayansa sauran guards din suka shiga hadi da saddiq.
Cikin ransa ya shirya sake maida kanshi busy fiye da kima,bama wai shi kadai ba,hadda musaddiq don kaucema duk wani tsari da plan na maamah har sai yaga iya inda gudun ruwanta zai kaisu. Ya shirya sadaukar da dukka lokacinsa ya tafi dashi a aiki fiye da yadda yakeyi a baya,duk da ko a bayan shi din ba wani cikakken lokaci gareshi ba. Sau tari anni tana yawan yi masa fadan yana tsaurarawa rayuwarsa da yawa,ya kamata ya fiddawa kansa lokaci da zai dinga hutawa. Bashi da wani time qwaqwara daya ware don yaje hutu,idan ka ganshi yana hutawa to tabbas umra yaje wadda duka duka baya haura sati daya yake dawowa.
Suna yawan ware qarshen kowacce shekara suje dukansu suyi umra,daga nan abban ya zaba musu qasashe guda biyu dake da wani tarihi cikin addini ko rayuwa suje su qarashe qarshen shekararsu a can. Sau tari shi din baya tafiya tare dasu,saidai ya biyosu daga baya,wanda ana kammala umra dinsa yake dawowa kan kamfaninsa,bai fiya binsu tafiye tafiyensu da suka tsara ba.
Direct suka nufi private parking garage dinsa wanda aka tanada kawai saboda ajiye motocin da yake kai kawo da kuma hidima dasu. Wajene da yasha banban da sauran duka parking lot na company din,wanda aka qawatashi aka kuma cikashi da tsaro na cctv da kai kawon security.
Dukka sauran guard nashi suna tsaye suna jiran qarasowarsa. Isowar nashi yasa da sauri CSO dinsa ya qaraso ya bude motor din da zai tafi a cikin ta ya matsa yana bashi guri,ya shiga saddiq yabi bayansa.
Sanda motocin ke motsawa suna barin wajen zuwa ainihin hanyar da zata sadasu da gate na farko na kamfanin,daidai lokacin ya gyara zamanshi yana bude wani guri a side na kujerar da yake kai don ciro earpiece da zaiyi using nasa wajen amsa kiran daya shigo wayarsa.
Kaman fitar kibiya idanunshi suka fada parking lot na sauran staff da suke da matsayi na biyu cikin kamfanin. Kan mikail idanunshi suka fada,ya bude mata murfin motar yana jifanta da wani mayen murmushi,yayin da nata fuskar yake kadaran kadaham tana sanya jikinta cikin motar
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 72
Zare Idanunshi yayi daga kansu yana jin wani quna a ransa.
"Tun yaushe mikail yake irin wannan abun?" Yayi maganar a hankali ba tare da yayi tunanin saddiq zai jishi ba. Dan dubansa sadiq din yayi kafin ya rusunar da idanunsa
"Hamma yana dan taba harkokinsa dama,amma kuma banajin a cikin company,yanayin komai ne a wajen company"
"Idan har a wajen company yakeyi in zanyi wani abun bazai wuce tunasar dashi kawai da gyara masa kuskurensa da take wuyan kowanne musulmi,ya kuma wajaba a kansa ya zama dole a addini da wajen ubangiji yayi akan dan uwansa musulmi a sanda ya fahimci kuskure ko gyara cikin al'amarinsa.....amma kuma muddin yana shigo min da wasu abubuwa da basu dace ba muhallin neman halal dina.....lallai lallai zan dauki mummunan mataki ne a kansa". Yayi maganar da sound din da zai nuna maka da gasken gaske yake.
Tunda suka shiga motar take jifanta da wani irin narkakken kallo. Yanaji jikinsa yana macewa kasala yana saukar masa kamar ko yaushe idan yasha barasa,shi yasa yaso ta bashi hadin kai ko hannunshi yadan fara kaiwa jikinta guraren da suka tsone masa idanu amma ta qiya. Yana kuma tsoron suna isa Bristol zaiyi wahala baiyi baccin nan nasa ba na wajibi,wanda muddin baiyishi ba bazai iya hasala komai ba yadda ya kamata.
Ta gaya masa tana da qa'ida da kuma dokokin da dole ya kiyayesu muddin yanason rakiyarsu tayi tsaho. To sai yaga hanzarin ma na meye?,ya qyaleta mana?,don dai jiran awa daya kacal me zai cishi?,shi da ta tabbatar masa a yau din wuni guda tana tare dashi?.
"Babe......muddin a yau kika bani hadin kai yadda na jima ina mafarki.....zan baki fara sheet da ba komai a ciki ki rubuta komai da yazo kanki kike burin mallaka......idan nace komai ina nufin komai fa,komai tsadarsa ko yawansa.....ina tare da lalitar jadda diamondchore" Ya fadi yana sakin qaramin shu'umin murmushi,don ya hango irin barnar da ganimar da kwasa cikin account din.
Kadan tadan dubeshi sai ta dauke kai,tana maimaita sunan kamfanin da tun shigarta ta tabbatar ba qaramin kamfani bane gama gari da kowa ya saba gani ba......to amma sai taji ba abinda ya burgeta tattare dashi. Ta tabbatar tunda har mamallakin kamfanin zai danqawa mutum irin mika'il ragamae tasarrufi da dukiyar kamfanin duk kanwar ja ce,ba yadda za'ayi mikail din ya dinga irin wannan fantamawar yana wasa da kudadensa ba tare da masaniya ko daurin gindinsa ba.
Ta yaya ma cikakken namiji kamar wannan daya mallaki dukiya ke dimbij yawa,kadarori kala daban daban ciki harda private jet amma ya gagara aure?,bayan a shika shikan aure bai rasa komai ba?.
Qaramin tsaki taja qasan ranta hoton fuskarsa yana dawo mata tana jin kimarsa da haushinsa suna kwaranyewa daga idanunta,saboda haka batajin daga shi har mika'il sun cancanci tausayawa.
Saidai ta sani,kudaden da suke da zummar kwasa din ba qananun kudade bane.....kudade ne da ta tabbatar ita kanta sunfi qarfinta dama duk wanda yake tare dasu,saidai kuma yawan masu buqatan kudi da muke dasu suke kuma kewaye da idanunta sun isa su lashe komai cikin zama mawadata da zasuci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin salama,ta soma hango wasu daga cikinsu suna rayuwa irin rayuwar da takeson ganinsu sunayi,wannan tunanin ya sanyaya sakin sassanyar ajiyar zuciya.
"Bakice komai ba" Mikail ya fadi yana dan waiwayowa ya dubeta kadan,don tsananin rudewa da firgicewa cikin farinciki da dimuwa da yake ganin wasu matan a ciki idan ya musu irin wannan albishir din sam sam baiga koda kamannin haka a wajenta ba
"Idan kuma hakan baiyi miki ba ki zabi kome kikeso a rayuwa......indai zaki bani rayuwarki zan baki komai da kike da buri" Ya sake fada cikin qoqarinsa nason gamsar da ita kalamansa.
"Baka da damuwa" Ta amsa masa cikin salon miskilancin nan nata,don maganganunsa sun fara isarta,bata fiya son doguwar magana ba.
Juya kalmar ta bashi rayuwarta takeyi cikin ranta. Har yanzu ta kasa sabawa da kalaman maza 'yan bariki,har yanzu mamakin wannan halittar ta d'a namiji ta kasa sakinta,su koda yaushe kansu sukeso?,kansu suka sani?,ko yaushe yaya zasuyi su samu jin dadinsu daga wajen 'ya mace?,ba tare da sun damu da yadda tata rayuwar zata kasance ba?. Basu da wannan asarar,suna iya sanya qafa suyi fatali dake duk sanda wannan halin nasu ya motsa na BUTULCI,aurenki sukeyi ko zaman bariki kuke?.
Tayi imanin halin D'A NAMIJI A JININSA YAKE,dan kunama ne shi da gaske,tana kyautata zaton babu wani d'a namiji da bashi da wannan halayyar,saidai na wani ne ya d'ara na wani kamar yadda take gani take kuma kan gani din. Wannan hasashe da karatun da tayi musu shike nesanta zuciyarta kullum daduniyarsu,takejin ba abinda yafi dadi a wajen mace irin ta rayu ita kadai ba tare data raba kowanne namiji cikin rayuwarta ba bare ta bashi wani matsayi da zai zameta lalura qunci ko quna nan gaba cikin rayuwa.......gwara ta rayu ita daya shine zata zama me cikakken 'yancin da bata dame bata mata rai.
Nisa da zurfin da tayi a tunani ya sanya har suka iso Bristol bata sani ba. Yayi parking na motar ya fito yana takawa da qyar saboda yadda jikinsa yake qara nauyaya,ya zagaya side din da take zaune ya bude mata qofar sai ya miqa mata hannu alamun ta taho.
Hannun nasa ta kalla sannan ta kalli fuskarsa. Ta gama ganin zallar mayen giyar da yasha yana narkewa a jikinsa
"No need" Ta fada tana girgiza kai sannan ta dauke dubanta daga kanshi.
Baya yaja kadan yana furzar da iska daga bakinsa. Gulmarta yakeyi a ranshi,jin kanta yayi yawa,tana da wata izza da wani irin jan aji da kamewar da bai taba gani a wajen matan titi ba sai a kanta,amma ba komai,yaci alwashin a yau dinnan sai ya banbance mata aya da tsakuwa,dukka wannan jan ajin garawar da wahalar dashi data dinga yi sai ya fansheshi a yau.
Tana gaba yana bayanta kamar ma ba tare suke ba har suka wuce ciki. Bata sake gasgata da gaske yayi booking ba......da gaske lamarin namiji abune me bada mamaki da daure kai ba sai da suka shiga babban dakin daya kama musu,wanda duk kwana daya a yadda ta gani cikin jadawalinsu naira dubu tari takwas da hamsinne. Komai an jere na kayan abinci,isowarsu kawai ake jira. Ya fada saman lafiyayyen gadon da yafi kama da gadon da ake shirin cin amarci a kai yana dubanta qasa qasa.
"Komai da kike buqata akwai an tanadeshi.....amma inajin sai kinyimin alfarma na matse baccin nan ko na awa daya ne cakal.....kiji dadinki yadda kikeso.....idanma akwai wani abu da kike da buqata ga waya can ki musu magana zasu kawo miki" Yayi maganar muryarsa tana maye ita kanta,da alama baccin yayi mugun cin qarfinsa.
Sanda ya miqe yana shirin sabule wandonsa da riga sai ta kau da kanta tana jin yadda zuciyarta tayi wani irin bugawa. Irin wadannan abubuwan take gudu shi yasa bata taba yarda ta biyo kowa wani kebantaccen waje ba,sai gashi haka kawai jib ya takura mata sai tabi mutum biyu don samun cikar aikinsu.
Yif taji ya koma ya fada saman gadon,koda ta maida dubanta sai taga bai iya cire komai a jikin nasa ba,kawai kokawar banza ya gama yi ya koma ya fadi cikin bacci.
Minti goma qwarara ta bashi sannan ta taka ta isa gabansa. Yayi sadidan a baccinsa,taja da baya a hankali tana jin faduwar gaba tace
"JIB yayi bacci"
"Good" Ya fada yana jawo dukka kayan aikinsa.
"Stay tuned.....minti talatin ya wadatar......ki kula da duk abinda zanyi requesting"
"Okay" Ta fada tana jin sanyin jiki da faduwar gaban da batasan dalilinsu ba.
Ganin mintuna arba'in suna niyyar shudewa ba wani labarin nasara,ga mikail yana motsawa lokaci bayan lokaci ya sanyata magantuwa
"Jib.....ya ake ciki?"
"Wannan aikin yayi tsauri da yawa adda.....akwai tsauraran matakai da shinguna masu zafi a kai,yanxun haka abinda na soma fahimta kamar wani abu ya fara alerting nasu anason musu kutse cikin asusun nasu" Ya fadi shi kansa kamar yanajin qarfin gwiwarsa yana son sarewa. Duk inda ya zaci zai samu nasarar balla account din nasu da dukkan hanyoyi da dabaru amma sai yaga abun kamar ya wuce nan.
Daidai lokacin da yake tsaka da meeting da investors din da suka jima suna da shaawar sanya hannun jarinsu a kamfaninsa na jadda diamondchore resources da yake a lagos da kano.....da kuma sabon kamfanin da yakeson yabude din a yanzu na jewelry da sauran dangin kayan ado da qawa na mata.
Daga saman system dinsa wani abu ya fara harbawa. Alamace da take nuna masa DANGER. Sosai ya zubawa alamar idanu,sannan da hanzari ya jawo system din gabansa ya soma bibiyar abun
"What?,scammers?" Ya furta qasan ransa,sai ya kalli baqin nasa yana miqewa tsaye gami da daukan wayarsa
"Excuse me" Yana daga musu hannu tare da takawa a hankali yana matsawa nesa dasu. Sadiq dake can nesa dashi ya kira
"Call the security team na kamfani......ka gaya musu akwai alamun shirin yin kutse su kula".
"Done" Ya fada kaman yadda ya saba gaya masa. Juyawa yayi yana komawa wajen baqinsa,ya koma mazauninsa ya zauna yana jawo system din gabansa.
Hankalinsa ya raba biyu,yana saurarensu yana kuma duba yadda suke samun progress na sake kutsa musu. Alama ta qarshe daya gani ta sanyashi lumshe idanunsa hadi da ture system din gefe kadan ya maida dukka hankalinsa dari bisa dari akan baqinsa.
"Done adda!......done,millions of naira sunyo dropping" JIB ya fadi da wani irin sautin farinciki,yana jin sukuni yana ratsashi na samun cikar mafarkin mutanen da suke rayuwa ruhinsu a jikkunansu.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
Page 73
"Zan iya tafiya?" Shine abu na farko data tambayeshi ba tare da tabi takan adadin kudin da suka samu cira ba
"Yes adda.... Zaki samu me napep a corner farko na street din yana jiranki gudun samun delay". Katse kiran kawai tayi,ta miqe tana daukar jakarta ta jefa wayar hannunta da sauri tana dan duban yadda mikail yaketa motsawa,alamar koda kowanne lokaci yana iya farkawa,saita wuce kai tsaye ta bude qofar ta fice.
Sai data tsaya da lobby din ta daidaita nutsuwarta da kyau gudun zama suspect a idanun security na hotel din,sannan ta fara takawa a nutse tana qarasa ficewa.
Hankalinsa a tashe yake dawowa wajen fuad din,yama gaza kiransa a waya kaman yadda shi ya kirashi a daxun.
Ta bayansa ya qaraso,yadan rusuna don sanar dashi halin da ake ciki
"Na sani.....jeka jirani mu qarasa mu wuce gida" Ya dakatar dashi ba tare da ya barshi yace komai ba. Da dan mamaki sadiq yake dubansa ganinsa zaune hankali kwance. Duk da yasan yafi gaban hakan amma wannan din ba qaramin abu bane da ya kamata ya ganshi haka a zaune calmly ba yana tattaunawa da investors,to amma bashi da sauran zabi illa juyawa ya tafi din kamar yadda ya buqata.
Tana tafe a hanya tunane tunane cinkus cikin kanta da qwaqwalwarta. Haka kawai taji ta kasa isa gida,sai kawai ta bawa me napep din umarnin suna da wajen da take so ya kaita.
Guri ne very quite,ba cikar jamaa,kuma kowa sabgan gabanshi yakeyi. Hakanan gurin yana da yalwa da fadin da zaka zauna a guri wani ma da yake nemanka bai ganka ba. Order din lemo da ruwa kawai tayi don batajin zata iya cin komai. Batasan me yasa ba.....ba yaune karon farko da haka ta fara faruwa ba amma wannan din yanason tsaye mata gami da sanyayar mata da jiki.
"Eh ba shine na farko ba......amma kuma yafi kowanne nauyi da girma......baki taba samun kudade masu tsananin kauri da yawan wadannan ba,sannan kamar an shiga lalitar wadanda baki taba koda magana dasu ba.....kaman akwai nasu haqqin a ciki". Wani sashe na zuciyarta ya fara tunasar da ita. Wanda qarar ring na wayarta ya katse mata tunanin.
Sunan titi data gani shi ya dauke hankalinta daga dukkan tunanin komai,ba jinkiri ta daga wayar suka fara magana
"Da sauqi.....amma sumanta biyu yau"
"Komai ya qare in sha Allah" Ta bawa titi amsa a taqaice saita katse kiran. Dukka karsashinta taso dawo dashi,ta fara lalubar wata number da jib ya bata.
Ayyuka biyu tayi a wajen da suka qara kashe mata kusan awa daya da rabi. Ta tura dukkan abinda mutumin ya buqata don yiwa titi aishatu da dan rakiya daya visa na fita qasar india da ita da komai da komai da zaa buqata na asibiti lafiyarta da sauransu wanda ya lashe maquden kudin da suka ninka kudin da akayi hasashen zaa kashe din. Abu na biyu kuma ta zauna ta datse ta share ta kuma sake toshe kowacce hanya ko kafa da zata sake sadata da mikail.....sai data tabbatar ta sanya kowanne shinge da zai nesantata dashi nisa na har abada sannan ta tattare komai nata tana fita daga wajen.
_hmmm,anya kuwa kayan Muhammed fuad jadda zasu tabu 'yammata?,to muje zuwa dai muga yadda wasan zai kaya FUAD dinne keda nasara?,ko SABREEN?_
Karo na farko a rayuwarta da taji shigowar sabreen cikin gidan dama dakin gaba daya amma ta shareta kamar ma bataji ba. Tayi lakur saman gadon tana ci gaba da kwanciyarta.
Hirarsu da hameed yau ta dasa mata abubuwa da yawa cikin zuciyarta dangane da yayartata. Tayi amanna ta kuma yarda hameed mutumin kirki ne na qwarai,daga yadda yake yawan mata nasiha da wa'azin ta kare mutuncinta......ta guji yawace yawace da yawan fita barkatai.....don duk yarinyar data fiya fice fice,qafafunta basa zaman gidan tabbas akwai ayar tambaya a kanta ko taqi ko taso,alamar kamewa ga mace shine ta lazimci zaman gida.
A yau din ayoyi qwalli biyu da hadisai guda biyu suma daya karanto mata sunja hankalinta. Itakam hameed yayi mata,a yanzu dukka burinta shine tayi aure......tayi aure ta matsa daga rayuwar da take sake Fahimtar yaa sabreen din tana yi.....ta auri hameed tayi nesa daga cakwakiyar gidansu.....baqaqen maganganu zallar gori da habaice habaice. Ta tabbatar zata samu irin rayuwar da takeso daga wajen hameed,zai killaceta kaman yadda yake fadi din.
Tayi mamaki sosai da taga qofar tasu a bude,sanda ta shiga kuma falon sai ta tabbatar akwai wani a ciki,sai ta aje jakar hannunta ta kutsa uwar dakin.
Gaban gadon hudan ta qarasa tana kiran sunanta. Da farki sai tayi banza kamar bataji ba,har sai data saka hannu ta yaye bargon da take ciki
"Lafiya huda?" Ta tambayeta tana qoqarin son ganin fuskarta
"Lafiya qalau" Ta samu kanta da bata amsa kai tsaye. Wani irin mamaki yaso kasheta a tsaye,amma sai ta cinye wannan. Hudan a yanzun ta fara zama budurwa,shekara sha biyar ta fara hawa bigiren kaiwa yammatanci,tabbas zata iya faskantar canje canjen halaitada dabi'u a tattare da ita kaman yadda ta tabaji mamanta ta fadi a sanda take cika tata shekara sha biyar din,wanda a yanzun shekara biyar daidai kenan
"Idan har lafiya lau huda me zai hanaki zuwa makaranta kuma uhmmm?". Kamar ta bude bakinta ta gaya mata aure takeso,kamar ta bude baki tace ta bawa hameed ita,kamar tace mata ta gaji da ganinta kullum tana fita babu sahihin inda take zuwa,ba makaranta ba ba kasuwa ba,amma sai tace
"Gajiya nayi,amma zani gobe"
"Gajiya?" Ta maimaita qasan ranta,amma a sarari sai tace
"Allah ya kaimu" Ta juya zuwa sashen kayan sawarta tana fidda kayan jikinta don sauyawa da wasu. Can qasan ranta zuciyarta ta kasa samun nutsuwa,sake gaya mata takeyi
"AKWAI MATSALA.....DOLE KI NINKA SANYA IDANUNKI" da wannan tunanin ta kammala canza kayan sannan ta juya ta koma falon don duba me dame akayi da bata nan.
Da kallo ta bita har ta fice,sai taja qaramin tsaki qasan ranta zuciya da shaidan suna ayyana mata ko dame dame ma tayi sanda ta fitan?,caraf kuma wani sashe na zuciyartata ya kwabeta
*D U N I Y A TA*
*_H U G U M A_*
PAGE 74
Kaman kowanne lokaci ya bawa kowa daman yayi order na abinda yakeso qarqashin kulawar sadiq da shike handling kusan komai.
Shi daya ya ware kansa a wani table da corner na daban,ya fidda system dinsa da ya sanya sadiq dauko masa ita. Ranshi a tsananin bace yake,amma kuma yana da wani irin abu,ya iya boye fushinsa idan yaso,ya iya kuma danne abinda yake damunsa,dole da rayuwa sun sanyashi iya controlling anger dinsa.
Yana da matuqar sani da zafi gami da kaifi ta bangaren computer.....ya koma da baya daga baya cikin karatunsa,ya zabi computer science ya kashe lokaci akai har sai daya zama qwararre kuma cikakke akan fannin,saidai ba kasafai ayyuka da cushewar abubuwa ke bashi daman practicing karatun nasa ba,amma komai nasa zaka sameshi a tsare da burbushi da alamu dake nuna yasan kan computer sarai.
A nutse ya soma bin komai daki dai cikin matuqar qwarewa tare da sanin makamar komai. Ba jimawa musaddiq ya iso wajen,sai yayi masa alama yayi joining sadiq kawai. Juyawa yayi yana matsawa daga wajen don tunda ya ganshi a hakan ya bawa system nutsuwarshi yasan akwai abinda yakeyi me amfani.
Ya samu sadiq din yana waya wanda ya kasa jurewa ya kira security team din da kansa. Ranshi a bace shima yake wayar,duk da abincinsa dake ajiye gabansa baiko bi ta kansa ba. Dan zuba masa ido musaddiq yayi kafin ya zauna,jikinsa kuma yana bashi lallai akwai wani abu. Jawo tray din yayi yana bude komai tare da warware spoon da fork din dake nade cikin tissue,ya sanya musu cikin abincin ya saita musu komai saidai still hankalinsa yana kan saddiq din.
Kusan mintuna goma sha biyar da isowarsa kafin ya kammala wayar,ya kasheta ya ajiye yana jan tsaki.
"What's going on?" Musaddiq ya jefa masa tambayar yana dage giranshi. Cup din daya zuba musu ruwa ya jawo yana kurba
"Scammers......hackers.....me ma zance ne musaddiq?". Idanu musaddiq ya waro waje yana kallon sadiq
"A'ina?Meye ya faru?"
"Sun diba maquden kudade daga cikin asusun company dazu........security team dinmu sun kasa aiwatar da komai......hamma fu'ad kuma baisan wanne matsaya ya dauka ba.....duk da nasan bazai qyale ba amma sai naga kaman ya dauki abun da sanya.....ina dai kyautata zaton yanzun yakebin kadin abun kamar ba kudi masu yawa aka diba ba" Saddiq yayi maganar yana maida hankalinsa ga fu'ad dake dan nesa dasu wanda baya iya ganinsa sosai da sosai
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Musaddiq ya soma maimaitawa yana rasa abun fadi kwata kwata.
Sannu a hankali ya soma bude idanunsa har ya gama budesu gaba daya
"Wayyo......." Ya furta yana miqewa sosai saman gadon yana jin yadda kanshi da idanunsa sukayi fresh. Komai ya sakeshi kenan,babu wani sauran burbushin giyar a tattare dashi,komai kuma zai tafi daidai yadda ya dace.
Idanunsa ya fara wurgawa cikin dakin bai ganta ba,sai ya barwa ranshi tana toilet ne tana shiryawa,don haka ya jawo wayarsa yana yana duba time
"Kai!" Ya fada a mamakance ganin irin baccin da yayi na kusan awa uku maimakon awa daya kacal kaman yadda yace zaiyi. Jikinsa ya danyi sanyi ganin yadda baccin yayi tsaho,zuciyarsa ta raya masa yarinyar nada wani irin aji da wahalar samu tamkar tarwada cikin ruwa,anya zata zauna duka wadannan awannin tana jira?.
"Da kuwa na tafka babbar asara" Ya furta a sarari gabanshi yana faduwa,sai ya jiye wayar ya miqe da hanzari ya nufi toilet din.
Duka bandakin ya duba ba ita ba alamar ta,sai ya fito ya soma duba dakin har zuwa balcony dake gaban dakin,lobby da sauran gurare,hakanan ya dawo zuciyarsa na harbawa da tsananin baqincikin kufcewar wannan damar a garesa
"Wai me yasa ma nasha barasa duk da sunan farinciki?,wannan tsinannen baccin......" Ya katse zancan bayan ya zauna gefan gadon yana dafe kansa da hannayensa bibbiyu.
Yadan jima a haka yana karatun asarar da yayi,da kuma wassafa yaushe zai sake samun irin wannan damar?.
Tsaki yaja sanda yaji wayarsa tana qara. Ya waiwaya yana duban me kiran,john ne chief of security team.
"Ubanshi zan masa......ya barni naji da asarar da nayi" Ya fada a sarari yana rejecting kiran.
Sake kira yayi bayan sakanni biyar kacal,hakan ya sake qufular dashi,don daga yanzu har wayewar gari har kwana uku bayajin zai huce daga asarar da ta sameshi.
Sake rejecting yayi,bai haqura ba ya sake kiransa a karo na uku. Wannan karon da niyyar cuccusa masa ashar ya dauki wayar,tunda a tsakaninsu kar tasan kar ne,saidai yana dagawa ya jefeshi da tambayar data sanya ya shiga tunani
"Kana tare da wayarka kuwa?,kasan me yake faruwa?,bakasan anyi kutse account din kamfani ba?". Dif wuta ta dauke masa,sai kuma ya bude bakinsa
" Kai john banason iskanci.....ka sanni na sanka,idan giyarka ka shawo ka daina gigin kirana ka bari ta sakeka tukunna,wayata tana hannuna......kuma ba wani abu daya faru,na sani fa ka dade kana harin muqamina,to qaryarka tasha qarya......in kanaso sai ka jira sai sanda matsayina ya qara daukaka a jadda company sai ka shiga takarar neman tsohon matsayi na" Daga haka ya katse kiran yana mitar shi baisan abinda yake damunsa ba zai qara masa damuwa.
Yankewa yayi kawai ya kirata ya lallasheta ya kuma sake shawo kanta,tunda kudin kwana biyu ma ya biya,ya samu ko wuni dayan gobe tayi masa tunda ya tabbatar ba zata taba dawowa a yau ba.
Saqon da idanunsa suka gane masa daga banking da kamfanin nasu ke ta'ammali dashi ya kusa sanya gudawa da fitsari duka yanke masa lokaci guda. Yayi wani mugun gigicewa sanda ya shiga saqon idanunsa suka haska masa adadin kudaden da aka zare daga asusun.
Wani irin abu yaji yana tsirga masa daga kowacce kafa ta gashi dake jikinsa. Gangar jikinsa yakejin kamar ba tashi ba ballantana ayi batun qafafunsa su samu daman iya daukansa,don haka sai kawai ya sulale ya zube ragwab a wajen yana jin kamar numfashinsa zai qwace masa.
Meye ma zaiyi ne?,ihu ko kuka?,hauka zaiyi ko mene?,kudade maqudai?,kudadenma kuma na kamfanin jadda?,kudaden da akansu yau suke lissafi zasu kuma gama lissafinsu a gobe?. Shin waye ya aikata hakan?,waye yake da alhakin aiwatar da hakan?. Yaushema abun ya faru?,wa zai soma kira ya tambaya bayan daga bakinsa ya kamata a fara ji?,wai yaushe ma abun ya faru ne?.
Ko sanda ya duba time na faruwar abun,da sanda John ya fara kiransa sai kawai ya saki wayar ya dora hannu saman kai yana fadin
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da qarfin gaske,wanda kalmar ma sam batazo bakinsa ba sai sannan. Yana dire kalmar farko hawaye suka fara bin kuncinsa. Daidai sanda kuma kira ya shigo wayar tasa abinda ya sanyashi zabura kafin yakai dubansa ga wayar.
Sir sadiq daya gani a rubuce ya sanya fitsarin dole kubce masa duk kuwa da yadda yaso ga riqeshi. Ya shiga uku ya lalace,yasan tunda yaga kiran saddiq din magana ya gama isa kunnen boss. Da wanne baki zai kare kansa?,idan suka buqaci kuma ya biya a ina zai samu?,ta ina zai samosu?. Yayi imanin koda danginsa zai siyar bazai hada wadannan kudaden ba.
Zuciyar dake da Allah a cikinta......hakanan zuciyar dake da yawan ambaton Allah ce kadai ke samun nutsuwa a sadda bala'i ya durfafo ta,don haka dukka wata dabara da kuma nutsuwa sukayi qaura daga gareshi.
Ya dinga zirya yana kai kawo,ya kasa aiwatar da komai,ya kuma kasa kamo bakin zaren komai. A haka lokutan sallah duka suka shude masa,hakanan qarar kiraye kirayen mutane suka yita shiga kunnuwansa suna fita ba tare daya iya rabar inda wayar take ba.
Duk wani kira da zai shigo wayar tsoro yake bashi,baya qaunar koda rabar inda wayar ma take gaba daya.
Sai kusan bayan sallar ishai ya iya fusgo tunanin baiyi sallah ba,ya miqe yana hada hanya ya nufi toilet don cire jiqaqqen wandon jikinsa daya jiqe da fitsari ya dauraye jikinsa ya kuma daura alwala. Har a sannan sam tunaninsa bai kawo masa sabreen ba,ya mance sam sam da itama saboda tsananin rudanin daya shiga.
"Don't call him again......ka barshi,inason naga iya gudun ruwanshi......kafin sannan ni na gama nawa" Fuad yace da sadiq wanda ke shirin sake kiran mikail din karo na biyu
"Okay" Ya amsawa fuad din yana maida kansa ga titi.
Ring na wayarsa ya katse shurun daya gilma cikin motar. A hankali ya maida kallonsa kan screen din. Anni ce,sai a sannan ya manta bai kira ba bai kuma sanya an kirata ba wunin yau. Zuciyarsa tadan saki daga quntatar da take ciki,ya daga wayar yana sanyata a kunne.
Kusan tare suka yiwa juna sallama ita dashi,sai suka amsawa juna sannan tace
"Nace dai Allah yasa lafiya......daga ku har abbanku yau duka kunyi dare a waje"
"Lafiya lau anni.....ayyuka ne suka riqemu,wasu al'amura kuma suka taso wadanda su suka shagaltar dani daga kiranki"
"Babu komai......kada ka damu,tunda dai dukkaninku kuna lafiya to alhmdlh......farouq yace min kuna tare da musaddiq ko?"
"Eh muna tare anni"
"To Allah ya tsare,ya dawo daku lafiya"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ya amsa mata zuciyarsa na sake cika fal da qaunarta da qarin ganin kimarta. Tana taka muhimmiyar rawa qwarai da gaske wajen cike musu wawakeken gibi da ramin dake zukata da kuma rayuwarsu.
Tun da aka kirayi sallar magariba ta gama shirya komai,sannan ta sallami masu aikinta kamar jiya. Tsaf ta shirya cikin embroidery holland gold atamfa da keta sheqi da nuna ainihin tsadar sutturar. Tayi kyau abinta,kai ba zakace itace ta haifi zabgegen saurayi irin muhammad fuad da musaddiq ba. Ita din ba baya bace wajen iya kula da jiki da tattalin fatarta da dukkan abinda zaya qara mata lafiya da kuma quruciya.
Parlor ta koma tayi zaune bayan ta kunna tv ta kuma saita tashar da take ra'ayi. Ta kame saman daya daga cikin sofas din falon tana kallon hagunta da damanta. Kujerun take kallo,a ranta tana wassafa ranar da zatayi gwanjonsu. Duk da tsadarsu da kudaden da aka kashe wajen mallakarsu sam ita bata tuna wannan. Abu daya dake sake tsaye mata a rai shine,labarin katafaren ginin daular data samu cewa yana yi cikin garin abuja. Batasan ainihin wacce unguwa bace,amma me kawo labaran ya shaida mata cikin jerin unguwanni mafi daraja da tsada a garin abuje yake ginin,kamar yadda yakejin qishin qishin din yana nan yana tamfatsa wani a lagos.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 75
K'aramar qwafa taja,muddin da gaske wannan villa din yake ginawa.....indai da gaske hoton da me dauko rahotonta ya nuna mata fuad dinta ke ginawa.....to kuwa koda zatayi yawo tsirara ba zata taba bari ameena da hamza su sanya qafafunsu cikin wannan daular ba.
Wayarta ta dauko ya kira hajja harira,a nan suka bata lokaci me tsaho suna sake tsara yadda komai zaya kasance.
Batasan ma lokaci yaja haka ba sai da suka gama waya da hajja harira din. Ta kalli agogo tana mamakin rashin shigowarsu gidan,fargaba na saukar mata na kada fa yau ma a maimaita abun jiya?.
Bata samu fuad ba,amma ta samu musaddiq,ya amsa mata da zasu shigo,don shima baisan fuad din ya gama shirya yadda zasu cinye daren a waje ba.
Ci gaba tayi da duba lokaci mintuna bayan mintuna,saidai duk sanda ta kalli agogon sai ranta ya sake baci,haka ta sake jawo waya da xummar sake trying number musaddiq amma ta kasa samunsa.
Ranta ya sake baci qwarai,dama ta sani samun number fuad ba abu bane me sauqi,sau tari xaka iya kiransa ka kasa reaching dinsa,saboda ba da gama garin wayoyi yake amfani ba don dalili na tsaro da kuma matakin rayuwa da yake kai dole yana buqatar tsari akan komai nashi.
Dukka number dinsa taci gaba da gwadawa,number ta qarshe data kira taji alamun kiran ya soma tafiya,saita samu gefen kujera ta zauna tana furzar da iska me zafi daga bakinta ranta yana tafasa.
Kaman jira ake ya gama wayar wani kiran ya shigo. Kamar ko yaushe bayyanar sunanta saman screen din fargaba da kokwanto yake sanyashi. To amma ba yadda ya iya,dole ya daga kiran ya mata sallama kaman yadda yake a dabi'arsa.
"Wa'alaikumussalam.......me yasa har yanzu baku shigo bane fuad?,ka manta da alfarmar dana nema kenan?" Ta fadi tana qoqarin tausar zuciyarta ta yadda kalaman zasu fita da taushi daga bakinta.
Komai qanqantar motsi tsakanin anni da maamah sai yaga tarin banbance babance. Da fari anni lafiyarsu kawai takeso taji kafin komai......amma ita nata uzurin su shigo suci abinci shi ta fara gabatarwa,abincin da ta tabbatar koda basuci a wajenta ba zasuci ako ina nema,amma kuma lafiya fa?.
"Ayyukane suka tsaremu yau dukkaninmu,yanzu haka ma wani guri zan qarasa......amma in sha Allah i will do my best". Shuru ta danyi wuta tana dauke mata,yanzun qarfe tara harda rabi na dare,yaushe yaje wani waje,yabaro gurin kuma yazo wajenta?.
" Okay,ina jira" Abinda ta fada kenan tana jin kamar ta bude masa abinda ke ranta. Bala'i da masifa takeson lullubeshi dashi,to amma ko dazun suna waya da hajja harira sai data gaya mata
"Me garaje ba kasafai ya fiya cin nasara ba a dukka lamuransa,saikin saka haquri juriya da kauda kai kaman bakiga komai ba". Wayar ta cillar gefe,ta hada tafukan hannayenta cikin fuskarta.
Wata irin tsanar anni da alhaji hamza tana mata masauki a zuciya tana kuma qara samun hauhawa cikin ranta. Inama ace yau zata budi idanu taga babu su cikin rayuwarsu?,da kowacce dama tazo mata yadda takeso.
Iya tafiyar da sukayi cikin motar bawai zaman shuru kadai yayi ba,zuciyarsa ta gama nisa akan matsalar iya balla shingen asusun ajiyarsu har kuma a debi wani abun?. Ba shakka koma waye ya aikata hakan yana da alaqa me qarfi da kamfaninsu,yana kuma da alaqa ta kusa kusa da mika'il. Dole ya zamana yana da alaqa da mikail.....ko shi kansa mikail din ma gaba daya.
Dalili......dukan abinda zai basu daman yin kutse kai tsaye da samun nasara haka a sauqaqe yana tare da mikail din. Dazu dazu ya danqa masa komai,cikin qasa da awa biyu kacal kuma ace komai ya faru?.
"Muje gida" Ya bawa driver din umarni,wanda ba wanda ya binciki dalili tsakaninsu ukun suka sauya akalar tafiyar tasu.
A tsaitsaye ya leqa anni sannan ya wuce zuwa sassanshi. Ya samu sassan nasa neat kamar ko yaushe kaman kuma yadda yake buqata. Ba duhu ba kuma haske me yawa sai matsakaicin hasken da bai fiya takurawa idanuwa ba. Ko ina qamshi yake fiddawa da wani irin moderate yanayi.
Takalmanshi ya sabule daga bakin qofa yana sauya wasu lausasan flip flops,daya daga cikin hadimansa ya sunkuya ya daukesu yana adanasu cikin wani qawataccen ma'ajiyar takalma me daukan hankali.
"Ku ajiye komai ku tafi,na sallami kowa.....sai da safe" Ya fadi musu yana takawa zuwa hanyar da zata sadashi da wani dan corridor da zai bashi daman isa bangaren dakunan baccinsa.
Daga zuciyarsa har gangar jikinsa basu da wani karsashi ko qwari,to amma kasancewar zuciyar jaruma ce ya sanya bata gaza ba,sai daya tabbatar yayi wanka yayi sallah ya sauya kayan jikinsa sannan Kai tsaye ya dawo falon da babu kowa a cikinsa,saidai ya tabbatar security tako ina suna kai kawo cikin gidan dama wajen gidan.
A nutse yake ratsa falon hannunsa zube a aljihun boxers din daya sanya tamkar wanda ya boyeshi saboda jin sanyi ko baya buqatar aga hannun nasa. Light blue kalan kayan sun masa wani irin kyau,saidai kuma fuskarsa tadan fada kadan wanda baya rasa nasaba da stress din yau daya tsinci kansa a ciki.
Dining ya wuce kai tsaye,komai yana shirye cikin tsafta. Bayajin a duniya bayan anni akwai wanda yakai ameh sanin tsarinsa akan abinci.
Yasan duk abinda ya bude cimarsa ce,kuma abinda yakeso ne,saidai kuma bayajin akwai wani sauran space da cikinsa zan dauki abinci,wannan ya sanya ya bude royal glass bowl din da tun bai bude ba yana iya ganin abinda yake ciki.
Lafiyayyen fruit salad ne da aka samar dashi daga dukkan nau'in kayan marmari na nan qasar dama wanda bamu dasu a nan din. Baya rabo da fruit sam,don haka masu shirya masa store da fridge dinsa sunsan duk inda zasu samar masa da nauin fruit da cimar da yakeso din.
Yadan diba da yawa,sai ya sauka a hankali ya duba ma'ajiyar shayinsa.
Bayashan coffee sai idan dole ta kama,amma yasan sirrin shan black tea da ake masa hadi na musamman da abubuwa masu amfani ga lafiya irinsu cinnamon cardamom scent leaves da sauransu.
Da kansa ya shirya komai saman tray ya nufi wata yar kyakkyawar books shelves ta ainihin gogaggen katako dake bangon gabas na parlor din. Hannu daya ya sanya ya murza wani abu da ba lallai ka iya lura da zamansa jikinta ba,sai ya sakeshi yasa hannu ya juyashi take qofa ta bayyana daga baya abinda ba zaka taba tunanin samuwarsa a wajen ba,ya taka ya shiga a hankali yana maida qofar yadda take.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 76
Daki ne da yakan jima bai shiga cikinsa ba sai muhimmin aiki irin haka ya taso. Saidai duk da haka komai a tsaftace yake.
Wani irin table ne na musamman ya jawoshi gaban main table dake dauke da nau'ikan na'urorin computer iri daban daban,ya aza tray din hannunsa a kai,ya taka a hankali ya kunna kowanne lantarki dake dakin,ya bada haske sosai. Komai na dakin bisa tsari yake,da nau'o'in kalolin green masu qarawa idanu qwarin gani.
Idanunsa saman systems din daya kunna guda biyu yana jiran su gama saituwa. Kadan kadan kuma yana kurbar black tea din da qamshinsa ke qara masa nutsuwa,kafin ya ajiye ya soma shan fruit salad din,daidai sanda komai na system din ya daidai ta,sai ya sake jawo kujerarsa gaba yana bata dukkanin hankalinsa.
Cikin tsananin nutsuwa da qwarewa yake bin komai. Ya kusa kashe a qalla awa biyu cikakku kafin ya dakata,ya tura kujerarsa baya yana zubawa allon computer idanu yana duba abinda ya samu a tsahon zaman da awannin da ya kashe.
Iska kawai yake furzarwa daga bakinsa,mamaki yana sake cikashi da samun bayanan duk da bai qarasa samun ragowar baya nan ba,amma ko iya wadannan bayanan da zaman da zaiyi da mikail sun isheshi samun kan komai. Ya dinga murza tafin hannunsa cikin na juna tamka ma jin sanyi,kanshi yana sake cakewa.
"Jibril usman" Ya maimaita sunan idanunshi nakan sunan da bai samu damar samun ainihin fuskar me sunan ba. Tabbas ko wayeshi din mayen computer ne,kuma qwarrare a sanin fanninta,saidai duk da haka qwarewar tasa akwai saura,don akwao gurare da abubuwa daya gani wanda shi Jabril din da ya samu rufesu to ba shakka shi kansa yanzun bazaikai ga isa ga bayanan ba. Qaramin masanin computer zai iya saluting jibril,amma shi da mutane ire irensa zasuyi murmushi ne kawai,a karon farko kuma su fahimci saura taqi kadan yakai inda ya dace yakai din.
Gefe daya ranshi ya sake ninka baci,duk wanda yaga aka zare kudin zaiyi tsammamin manyan hackers gagarumai wanda suka gagari duniya system dinsu ta hadu dashi......wannan kadai ya isa ya sake zaburar dashi lallai lallai yana buqatar yin garambawul wa security team dinsa,amma kafin sannan mikail shine mutum na farko daya dace ya dauki mummunan mataki a kansa,saboda shi da kansa ya yiwa tsaron company dinsu aiki,ya saka abubuwan da duk qwarewarka idan ba samun wani information mutum yayi ba zai wahala ya samu isa ga inda suka samu isa din.
"Ina yaje?,waye ya bawa sirrinmu?" Wadannan sune tambayoyi guda biyu da yake buqatar ji daga bakin mikail din. Kodai yaci amanar company......ko an nemi rayuwarsa an masa barazana....kota dalilin sakacinsa bayanan sun fita.
Washegari kaman kullum,yabi tsarin jawadalinsa na kullum tun daga gida har zuwa office. Qarfe shida da rabi yake kammala motsa jikinsa ya wuce wanka,idan ya fito yakan dan bar bathrobe jikinsa ya karbi newspaper da magazines ya duba,yadan duba saqonnin email da WhatsApp dinsa ya hada da shan ruwan duminsa ko dafaffiyar madarar shanunsa me tumeric. Sai bayan kammala dukka wadannan hidindimun sannan yake shiryawa,yayi breakfast ya wuce office.
Kamar ko yaushe yau dinma bakwai da rabi ya fito daga toilet daure da bathrobe dinsa. Yanaso yau ya fita da wuri ne fiye da yadda ya saba fitan. Don ko da safe daya tashi ya sami missed calls din maama din kusan guda goma,wanda ya tabbatar tun na daren jiya ne.
Yawan kiran nata kadai da takeyi yana sake bashi tabbaci ne a kanta. Ya jawo wayar ya turawa musaddiq text akan zuwa takwas ya shirya zai aikeshi wani guri,sai ya cire toilet slippers din ya sanya wasu tausasan rufaffun takalma ya soma takawa yana fita don riskar parlor ya duba newspapers din yau.
Ba kowa parlor din sai ameh daketa zirga zirgar shiryawa ogan nasa dining,sai me sunan malam dake zaune saman lallausan turkey carpet din da aka qawata tsakanin kujerun. Me sunan malam din na daya daga cikin amintattunsa da basu da shamaki wajen samun daman isowa parlor dinsa.
"Good morning sir" Ya fadi yana rusunar dakai
"Morning me sunan malam.....mun tashi lpy" Ya amsa masa yana zama saman wata sofa guda daya data banbanta da sauran duka kujerun parlor din yana kai hannunsa saman dan qaramin table din da aka zube masa sabbin newspaper din bayan an kwashe na jiya.
"Lafiya alhamdulillah sir"
"Ma sha Allah" Ya furta yana bude page din farko na jaridar ba tare daya tsaya karanta bangonta dake dauke da title na labaran ciki ba.
Labarin farko suka wafci idanunsa. Ya sake dawowa da baya bayan ya karanta layin farko da akayi da manya manyan zane. Bai tsaya bata lokaci ba ya koma bangon don sake duba title din da ya tsallakeshi a dazu. Tabbas duka abu guda suke nunawa cikin harshen turanci
*_GAGARUMAR SATA.....AN WAWASHE KOMAI DAGA ASUSUN JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES/AKWAI YIWUWAR DURQUSHEWAR COMPANY DIN NAN DA WANI DAN LOKACI_*.
Jaridar ya juya tamkar ma ya manta wanne gidan jarida ne suka kafe labarin. Sai ya maidata ya ajiye yana dauko newspaper ta gaba.
Ita dinma kaman wancan,bangon farko abinda yake rubuce kenan a jiki,ya sake juyawa shima ya duba gidan jaridar sai ya maidata itama din ya ajiye,ya sake daukan ta uku.
To ita dinma babu wani canji,duka dai labari guda daya ne,abinda ya bashi tabbaci da yaqinin wannan shine labari na farko da zaiyi trending kenan yau a duniya kasuwanci.
Idanu kawai yaci gaba da zubawa rubutun kamar wanda kwanyarsa ta kasa gano komai,ya daga idanunsa a nutse da suka fara sauya launi ya kalli ameh daketa goge dining din da kyau don kawar da qura datti ko maiqo komai qanqantarsa daga muhallin cin abincin boss din nasa da ya sani da tsananin tsafta da rashin son qura ko datti komai qanqantarsa
"Ameh......dauki waya ka kira sassan saddiq.....i wanna see him yanzu yanzu".
"Yes sir" Ameh ya amsa masa yana sakin komai,sannan ya gangara a hankali yana nufar inda wayar take girke.
Daidai sanda ameh ya gama shaidawa saddiq saqon fuad farouq yayi knocking daga can first door sannan ya turota a hankali ya shigo. Yana sanye da kayan motsa jiki da alama fitowarsa kenan daga dakin motsa jiki na gidan,wanda dama kusan kullum shine qarshen shiga,fuad kuma na farko,saddiq da musaddiq ke binsa daga baya.
Dauke yake da jaridu har guda uku a hannunsa,kallo daya fuad yayi masa ya karanci shima labarin ya gani kuma shi ya shigo dashi. Fuskarsa a dinke ba walwala ya samu kujerar dake fuskantar fuad din,wannan ya sanya me sunan malam ficewa ba tare daya gabatar da abinda ya kawoshi ba,hakanan ameh shima ya wuce ta kitchen ya bulla ta baya yabar sassan.
"Tun jiya naketa qoqarin ganinka.....duk da dare yayi sanda kuka dawo nayita nemanka ban samu ganinka ba........yanzu da safe kuma sai naga wannan" Ya fadi yana zube masa jaridun hannunsa. Binsu yayi da kallo sannan ya maida dubansa kan fuskar farouq
"Nima haka na tashi na gansu farouq"
"How comes fuad?" Ya furta tsananin bacin rai yana cin zuciyarsa. Kanshi ya motsa kawai yana girgizashi kadan
"A lot of things farouq......bansan ma ta inda komai ya fara ba......na kuma rasa ta inda zan kamoshi......inajin kamar ana warwaremin tunani na ne......da farko wawashe asusun kamfani ta sigar da ba wanda zai iya yinta sai na kusa ko wanda yasan sirrin asusun......ina cikin aikin kamo zaren kuma sai ga wannan......wannan fantsamar labaran tabbas shiryayyen abune koda kwashe kudin ba shiryayye bane.......zakafi kowa fahimtar anyi ne don a yiwa kamfanin illa......ta yaya babban kamfani kamar namu da yake da hannuwan jarin manyan 'yan kasuwar duniya ace saboda tsananin rashin tsaro har za'a iya kutsa kai ciki a debe kudin mutane?......wanne tabbacin tsaro muke dashi da zamu baiwa dukkanin wanda yake da buqatar kasuwanci damu?,wannan shine tuhumar da xamu fara fuskanta daga wajen al'umma......waye ya fidda labarin cikin qasa da awanni uku,har ya zamana labarin da kowanne shafin jarida suka maida bangon labarinsu?". Kai farouq ke gyadawa cikin zuzzurfan nazari,ya daga Idanunsa ya sake duban fu'ad
"Shi kansa kwashe kudin nan baka tunanin aike ne?,ture ne?,kuma suna da alaqa da wanda ya fidda labarin?". Mintuna kusan uku fu'ad din baice komai ba,kansa yana sake qullewa,sanda ya bude baki zaiyi maganar sadiq ya shigo sanye da jallabiyya hannunsa riqe da system.
Kallo daya dukansu sadiq din yayi musu ya fahimci sunga komai,tun da sassafe kiraye kirayen wayoyi suka tasheshi,kusan fitar labarin su suka hanashi fita motsa jiki tun daga sallar asuba daya koma. Yana tunanin ta yadda zai iya sanarwa da fu'ad din abun,amma kuma yasan zai wahala awannin safiya su wuce bai sani ba tunda shi din ma'abocin bin shafukan jarida ne.
"I hope abba baiji komai ba ko bare anni?" Fu'ad yayi tambayar tsananin fuskar farouq da sadiq. Junansu suka kalla kafin farouq ya amsa
"Zai wahala abba bai sani ba,tunda kasan yana bibiye da kafafen yada labarai,annin dai ita zaka zatarwa haka" Kai ya girgiza yana yin qasa da kan nashi,yasa hannunsa yadan shafi qasan wuyansa.
"Yanzu mene abunyi?" Farouq ya tambayeshi yana kallonsa.
"Dole komai ya kasance cikin hikima da kuma tsanaki,hakanan for now dole mu zama cikin takatsantsan da sanya ido akan kowa,faruwar wannan kadai ya sake gayamin tabbas akwai wasu qofofi dana bari a bude......akwai wasu bayanai namu tabbas da suke fita.....akwai wanda kuma yake dauka yakai din......sadiq " Fu'ad ya fadi yana dubansa
"Na'am hamma"
"Inaso kabar kowa a haka,kada ka sake amsa waya ko maganan kowa.....amma ka shiryamin meeting na sirri,koda me sunan malam banason yasan da zaman.....ka tsara awannin da zamu zauna din zuwa tashi,zai fara daga goma na safe har sai sanda na buqaci tashi......general meeting nake buqata"
"Okay hamma" Ya fadi yana sauke system din saman cinyarsa cikin qoqarin duba schedule dinsa na yau yayi cancelling wasu ya kuma gyara time na wasu koda akwai yiwuwar zai iya gabatar dasu.
Sun jima da farouq a wajen suna tattaunawa kafin farouq din ya miqe ya wuce nasa sassan da zummar shiryawa,don yanason ya bishi zuwa kamfanin.
Sai qarfe tara saura suka fito,kaman ko yaushe ya taka zuwa sassan anni. Kowacce safiya takan zauna a parlor har sai taga ficewar kowa zuwa wajen sana'arshi. Yau dinma tana zaune cikin riga da zani na lallausar atamfar super exclusive me ruwan sararin samaniya da ratsin ruwan ganye. Ta lullube jikinta da tattausan mayafi dan turkey daya dace da atamfar,dukka hannayenta siraran awarwaro ne masu daukan idanu da suka dace da fatarta da batayi komai na darajar kulawa nutsuwa da kwanciyar hankalin da take ciki.
Kamar kullum kuma kaman ko yaushe ya duqa gabanta suna gaisawa. Yau din bata ja zance dashi ba saboda ta karanci kaman gaggawar fitar sukeyi.
"Muhammadu" Ta kirashi sanda suka gama sallama ya juya zasu fice
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 77
A nutse ya waiwayo sannan ya amsa
"Na'am anni......akwai wani abunne?". Kai ta girgiza tana jin tausayinsa hakanan yana tsarga mata. Tasan cewa akwai abubuwa da yawa da suke damunshi cikin zuciya,amma shi din wani irin mutum ne me masufar zurfin ciki. Zai wahala kaji ya b'ara ko kaji kukanshi.
"Kaman akwai wani abu ko?" Ta jefa tambayar gareshi don batason fitowa kai tsaye ta Qureshi da tambayoyinta
"Ba komai anni" Ya fada cikin bata tabbaci,don yayi imani ya nuna mata akwai damuwar,to yinin yau gaba daya haka zasu barta cikin rashin sukuni.
Kai ta gyada ba don ta yarda ba,sai don tasan koma meye idan ya dace ta sanin shine mutum na farko da zai fara gaya mata
"Ubangiji ya kauda dukkan abunqi,Allah yayi jagora"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu anni,na gode" Daga haka ya juya yana fita. Har cikin ransa yakeji irin wannan addu'o'in nata,duk kuwa da cewa bawai shi daya takewa adduar ba kowannensu ne,amma yakanji a ransa kamar tasa ta dabance.
Bai shiga mota daga parking lot na gidan ba,sai yace su fiddo motocin su sameshi waje. Ya soma takawa a nutse suna jerawa shida farouq suna tattaunawa kadan kadan har suka fito a gidan.
Sanda suka doshi gidan nasu yayi tsammanin farouq zai dakata daga yi masa rakiya amma sai yaga yaci gaba da binsa har suka isa bakin gate. Sun gaisa da malam saidu cikin girmamawa sannan suka kutsa kai ciki,guards dinsa guda biyu dake biye dashi suka dakata suna jiran fitowarsa.
Tunda ta wayi gari ta kasa tabuka komai,tana kwance kawai a daki tana kwancewa da saqawa bayan doguwar wayar da sukayi da hajja harira. Anya kuwa nasarar da take sanya ran samunta zata cimmata?,zata ma iya haqurin kwana ukun da bokan ya deba mata kuwa ba tare data koma ta sanar dashi komai ba?.
Maida tunaninta tayi tana sarrafa shawarar da hajja hariran ta bata. Bata jin cewa shawarar zatayi aiki har ta lanqwaso mata me babban suna yadda takeso?.....anya bazai zama doguwar hanya me wahala ba?.
"Waye ne?" Tayi tambayar cikin izza sanda taji an nace da knocking mata qofar bedroom
"Nice hajiya.....yallabai ne yazo" Me aikin ta furta a qasqance
"Yallabai?,fu'ad kenan?" Ta tambaya a mamakance tana duba lokaci
"Eh shine" Ta sake amsawa a ladabce. Cike da mamaki ta kalli agogo. Wannan ba shine lokacin da suma saba shigowa gareta ba,me ya kawoshi yau da safe?,ko dukka cikin dabaru da salon son kauce mata ne?.
"Ina zuwa" Ta amsa mata sannan ta fara yunqurin saukowa daga saman gadon.
Tun daga nesa ta zuba idanunta a kansu,hira suke qasa qasa da wani irin kusanci da emotion da zaka tsammaci su din tagwaye ne da ska rayu qarqashin mahaifa guda daya. Bata ga wani banbanci ba ko kadan tsakanin danta muhammad jadda mamallakin kamfanin haqa da sarrafa diamond ba.....da kuma farouq hamza kibiya me kamfanin saida tsabar abinci da taki ba!.
Meye ribar suna da yayi?,meye amfanin salon banbancin kasuwanci tsakaninsu muddin a idanu zaka dinga hangar yanayin sukunin rayuwa iri daya tsakaninsu?. Kamata yayi ace ana hangen tazara tsakaninsu,kwatankwacin tazarar dake tsakanin bawa da uban gidansa.
Wani irin abu yayi mata tsaye a wuya,amma dole ta saita yanayin fuskarta sanda ta isa gabansu
"Wato farouq kayi wuyar gani,har gwara sadiq ya fika kirki anfi ganinka" Dukkaninsu ba wanda zancanta ya kwantawa,saidai kawai sun bita da irin yanayin da tazo musu dashi. Wannan faran faran sa sabuwar maraba da iyalan Alhaji hamza kibiya sabuwa a idanunsu da basu taba ganinta ba.....koda kuwa sanda ta dawo ta iske iyalinta cikin kyakkyawan rayuwa qarqashin jagorancinsu da tallafawar rayuwarsu.
"Wanne irin aiki ne ya riqeku jiyan kaida dan uwanka kuka saka halartar kira na?" Tayi masa tambayar daketa cin ranta,don har xuwa lokacin bata gamsu wai aiki ne ya riqeshi ba
Yana murza yatsun hannunsa idanunsa samansu,zuciyarsa na wani irin motsa cikin yanayi maras dadi. Koda yaushe maganarta babu komai ciki sai zallar son kanta a ciki......ba wani sauti alama ko yanayi na kulawa ko nuna damuwa......ba wannan shaquwar da maganadisu dake tsakanin uwa da danta da har zata iya karantar yanayin damuwa walwala ko farinciki da yake ciki,abinda dukka ta rasasu anni kuma ta haye kansu ta zauna sosai.
"Yanayi ne na aiki da zai iya rutsawa dakai ako wanne yanayi ko lokaci" Ya amsa mata a taqaice don bawa kansa kariya .
"Yau kuma fa?" Ta sake fadi tana tsareshi da dukka idanunta
"In sha Allah" Kawai ya fada shima nan a taqaice.
Duka duka zaman bai wuce na mintuna goma zuwa sha biyar ba suka wuce. Mintuna goman da suke da matuqar tsada da daraja a wajensa......don ita din itace.....yana jin ya wajaba ko yaya ya bata wadannan mintunan don tserewa tuhumar ubangiji.
Fadin ma yanayin daya kwana a cikinsa a wannan ranar dare har ya zuwa safiya bata baki ne. Duk sanda ya waiwaya ya sake duba wayarsa sai ya dinga jin abun kamar mafarki......kaman baccin daya kwanta shi yakeyi,kaman har yanzu idan ya farka zai samu komai ba gaske bane.
Daga sallar magariba har ishai saida safe ya hada da asuba ya ramasu. Gaba daya ya wani firgice ya fita hayyacinsa a tsakanin. Ba abinda yake iya tunawa sai wanene Muhammed jadda da kuma irin hukuncin da zai iya dauka a kansa.
Duk yadda yaso ma ya yiwa kansa hasashen ta inda zai fara kare kansa a gaban mutumin da a fagen aikinsa baida maraba da zakin daya fito farauta sai yaga sam zantukan daya tsara ko kadan basu hau kan saiti ba,basu kuma dace da hankali ba. Tsananin tsoron da firgicin ya sanyashi kashe wayoyinsa gaba daya,saishi kadai cikin dakin tamkar tsohon mahaukaci.
Ba abinda kunnuwansa ke gaya masa sai sautin sallamar talauci cikin rayuwarsa,an debi kudin da ya tabbatar baida abun biya koda kuwa zai saida komai daya mallaka shi da danginsa su koma yawo tsirara.
Taku biyu yayi don shiga toilet ya rage gudawar da yake fama da ita tun faruwar abun idanunsa suka fada kan dan kunnen.
Gabansa yayi wani mummunar faduwa sanda kwanyarsa ta haska masa wani abu lokaci guda tamkar haskawar walqiya cikin duhun dare.
Tsugunnawa yayi ya dauki dan kunnen.....sai yanzu ma ta dawo kwanyarsa,sai yanzu tunaninsa ya soma haska masa wani abu
"Fateema?" Ta maimaita ainihin sunan da shine nasa STAMP din data bashi.
Komawa yayi ya zauna saman kujerar dake daura da qofar bandakin yanason tuna yininsu na jiyan a tare.
Yayi dukkan wani flash back daga qwaqwalwarsa zuwa zuciyarsa da kuma idanunsa,ba wani motsi nata guda daya daya bashi alamun rashin gaskiya a tattare da ita
"To amma me yasa na farka na nemeta na rasa?" Ya jefawa kansa tambayar data sanyashi miqewa ba shiri,ya jawo wayarsa da baiyi shirin kunnuwa ba ya kunnata,cikin ransa yana jin gamsuwar tabbas ita ta aikata ko kuma tana da hannu wajen afkuwar komai.
Sanda wayar ta daidaita sai ya fara yunqurin kiranta,saidai a duk sanda zai kirata din sai computer ta datse kiran ba tare da an masa bayanin komai daga danganci network ne babu a area din da take?,ko kuma wayarce dungurun gum a kashe?.
Ci gaba yayi da gwada kiran babu qaqqautawa,har sai daya sare,energy dinsa yayi qasa,ya tabbatar bazai cimmata a waya ba.
"Sai kayi tattaki ka sameta a inda take" Wannan shawarar ta sakashi zabura ya miqe,ya zura takalman qafarsa a gaggauce,saidai yana daukan key din motarsa komai ya tsaya masa cak
"A ina take?,a ina kuma zaka sameta din?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar data kusa tsaida numfashinsa
"Na shiga uku" Ya fada yana jin dukka jikinsa yana rawa
"Bansanta ba,bansan komai a kanta ba" Ya fadawa kansa da kansa idanunsa suna tara hawayen da babu makawa sai da suka yiwa kansu qofa
"Garin ya akayi haka?" Ya sake tuhumar kansa da kansa,abinda ya sanyashi sulalewa ya zauna a wajen.
Yafi qarfin awa biyu zaune ya kasa hasalawa kansa komai,kafin daga baya wata zuciyar ta bashi wata guntuwar shawarar data dan bashi nutsuwa kadan,har ya iya miqewa ya gyara rigar jikinsa ya maida hularsa ya lalubi qofar fita.
Dukkan wani muhalli da yasan sun taba haduwa,cin abinci,shan ice cream,shopping da sauransu ba wanda baije ba. Saidai duk inda yaje din dogon bayani ne maras fa'ida ko kuma alfanu,domin ba wanda ya ganeta. Abinda bai sani ba shine......ita din tamkar tarwada take a cikin ruwa......tana da matuqar santsi da idan taje waje zai wahala ka sake samunta a nan... Muddin taje waje dakai sau daya ta kansile wajen kwata kwata cikin jadawalin rayuwarta,ba guri bane da take mu'amalantarsa ba a koda yaushe ballanta fuskarta ta zama sanniya a wajen mutanen dake yawan xiyartar wajen ko kuma ma'aikatansu ba.
Tun yana zagayawa da qarfin gwiwarsa har ya sare. Zuwa sannan yanajin zai haukace ne idan bai gayawa kowa halin da yake ciki ba,don haka yana isa Bristol baiko koma dakinsa ba ya kira mato a waya.
Tazarar minti ashirin kacal ya iso,ya shigo dakin yana cewa
"Kai matsala ne dakai,wani lokacin sai ayita faman kiranka baka dagawa,tun jiya nake danna maka kira kaqi dagawa......gobe ne za'a zauna cacar nan fa......"
"Shut up mato!" Ya dakawa mato din tsawa,don maganarsa a sannan daidai take da yana buga masa abu me qara a kunne.
"Lafiya uban gidana?,me kuma ya faru?"
"Mato na hadu da 'yar damfara......na hadu da gagarumar barauniyar data yasheni tas......bama ni ta yasheba tukunna......ta taba dukiyar kamfanin jadda ne!".
Zaro idanu mato din yayi waje yana janye jikinsa baya da sauri kaman yaga wani abun tsoro tattare da mika'il din
"Anya yau bakasha barasar da kanka baya dauka ba?,kasan maganganun da kakeyi?,barauniya fa kace,kuma macace?,sannan data tashi dukiyar Muhammed jadda ta kwashe?" Ya qarasa maganar kaman zaiyi ruku'u. Ba kuma ruku'u din zaiyi ba,kawai yayi hakanne don ya samu damar ganin fuskar mika'il dake zaune sosai,yanason kuma samun tabbacin maganar haka take ko kuma akasinta.
"Duk yadda kaji ka sake kuma fada hakanne" Ya fada a galabaice yana tsananta fatan samun mafita daga wajen mato.
Ga mamakinsa sai yaga mato ya juya yana neman hanyar fita daga dakin. Da wani irin hanzari mikail ya miqe ya damqo rigarsa yayi qarfin halin jawoshi baya sannan yasha gabansa
"Ina zakaje kuma?" Kicin kicin yayi da fuska
"Ka dauko bala'in da yafi qarfinka ai me gida,ni kuma bani da wani gatan da zan iya tareshi,kaga gwara na yiwa kaina qiyamulallaili nasan nayi". Sakinsa mikail yayi har yana taga taga kaman zai fadi. Cikin fusata da fushi yake duban mato,yayi taku biyu a gabansa sannan ya tsaya yana sake kallonsa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 78
"Kai butulu......na dade da sanin alaqar bariki bata da riba.....kuma bata wanyewa lafiya qalau.....amma inaso ka sani.....ni mikail baka isa ka gwadamin wannan halin ba saboda yadda kaci a jikina,komai ka zama ta silata ne.....to ga hanya nan......kana iya tafiya......amma ka sani,wallahi.....wallahi duk abinda zan shiga zan bada sunanka da tabbacin tare mukayi komai".
Ji mato din yayi kaman ya debo qarfe ya jibga masa saman kanshi,sai ya koma ya sulale ya zauna
"Ya zakayimin haka oga?,kasan tun safe naga qishin qishin abun?,ya baza jaridu da jafafen yada labarai?,amma ban taba tunanin kaine a ciki dumu dumu ba?"
"Mune dai a ciki,kuma zanyi maka haka muddin kaima kayimin hakan". Ya bashi amsa kai tsaye yana duban tsakiyar idonsa.
Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana yin collapse. Nadama da dana sanin taba sanin mikail a rayuwarshi tana sauko masa. Shikam ina zai iya tarar case da Muhammed jadda?,wanne ganganci ne ma zaiyi saken da koda sunansa zai shiga list na sahun wadanda ake tuhuma.
Shuru yaci gaba da wanzuwa a dakin tamkar dukkaninsu ba xasu sake magana ba kafin mato ya magantu
"Ita yarinyar wacece ita?,zaifi kyau kabi sawayenta ka bincikota ka damqawa jadda ita a sauqaqe su tuhumeta". Wani banzan kallo ya watsawa mato
"Inda nasan ita din wace da ta yaya ma zan batawa kaina lokaci ina neman shawarar butulu irinka?......tun haduwata da yarinyar na karanci tasha banban da sauran yammata dama mata gaba daya.....tun daga yanayin kyau siffa da kuma jan ajinta......bata sake shallake tunani ba sai a yau dana karade dukkan guraren da muka saba haduwa ko na saba ganinta amma na kasa zaqulota,......ta shafe dukkan wani footprint nata,bani da sauran hanyar da zan iya lalubota".
Shuru mato yayi abun yana tsimashi shima. Duk iya yawan duniyarsa bai taba cin karo da abun mamaki irin wannan ba.......duk budewar idanunsa da kuma son duniyarsa baiga gangancin da zai sanyashi tunkarar fada ko jayayya da mutum irin muhammad jadda ba.....hakan daidai yake da saida rai.....daidai yake kuma da Rungumar mayunwacin zaki. Amma irin wadannan maquden kudaden kuma ace diya mace ce ta diba?.
"Me afkuwa ta afku yallabai.......yanzu lokaci ya qure ya kuma matse da zaka tsaya nemanta da bayyanar da gaskiyarka.....don koda ka samota dinma ka gabatar musu da ita to ba shakka dole saika rasa aikinka.....na tabbatar zasu sallameka ne". Wannan maganar ta mato ta sanya gumi tsatstsafowa mika'il. Ya koma baya yana zama sosai tare da kamo habar rigarsa yana sharce gumin goshinsa.
"Don ubanka mafita nace ka bani bawai ka dinga haskomin makomata ba" Ya fadi da mugun tsaron ci gaba da jin sautin xai rasa gurbin aiki da kamfanin jadda diamond rashi na har abada,bayan a nasa mafarkin yana hangoshi ne wataran a kujerar CEO din ma gaba daya yana juya nasa kamfanin diamond din.
"Mafita kam na samota......amma sai idan ka amince.......zaka juya hankalin kowa kayi wasa dashi.......ka kuma binne batun kwashe kudin asusu ba tare da kowa ya fahimta ba".
Kaman an watsa masa ruwan sanyi haka yaji rahama tana sauka a zuciyarsa,baisan sanda ya kama hannun mato ya riqe qam qam ba abinda bai taba yi ba tsakaninsu
"Dama za'a samu irin wannan hanyar na kasa yarda da ita mato?,maza gayamin......gayamin don Allah".
Hannunsa ya zame yana mamakin yadda yau masifa da bala'i suka sanya ubangidan nasa zama maqasqanci a gabansa.
"Caca......a caca ne kawai zaka ciyo maquden kudaden da zaka iya cike babban gurbin da zai sauke fushin me jadda daga kaso dari zuwa ashirin". Ido ya zubawa mato alamun me gama Fahimtarsa ba.
"Nasan baka gane ba ko?,me gida......kana da nasibin da muddin ka zauna teburin caca saidai ka kwashe badai a kwashe ka ba,tunda kake baka taba zama teburin caca an cinye ka ba tsahon shekarun daka dauka,saidai ma ka tashi da gwagwabar ribar dake lunka arziqinka.......wannan zaman da za'ayi a gobe babban zama ne......akwai manyan gidadawan masu kudin da basu gama wayewa a sabgarba.....basu kaika qwarewa ba,sun sanya mugayen kudade masu nauyi cikin cacar saboda romon bakan shigowarka cikinta da nayi musu da yawan kudade masu nauyin gaske.......kudin da kowanne zai zuba ba qarami bane me gida......kuma ina da tabbacin kaine zakayi nasarar wawashesu......ka zuba kudade sosai ka saki jiki don ka sarqafo dukkan abinda zasu zuba.....bana jinka.....nasan da qwarewarka.....na kuma yarda dakai".
"Nima na yarda da kaina" Ya fadi kai tsaye cikin confidence da kuma yarda da cewa lallai ba shakka waraka tazo. Rungume mato yayi yana jin tsananin farinciki kafin ya sakeshi yana cewa.
"Muddin muka gama da wannan,na rantse da sarki Allah saina nemo yarinyar nan......saina nuna mata cewa ita din ba komai bace cikin duniyar bariki,sai na bar mata tarihi,saina sanyata tayi danasanin zuwanta duniya!!".
Tunda gari ya waye yake kwance kawai lamo,ita bame bacci ba hakanan ita ba idanunta biyu ba. Su biyu ne a dakin tun bayan wucewar nadra da haneefa makaranta,tana daga parlor huda na cikin uwar dakin qudundune a bargo da sunan bata da lafiya ba zata samu daman zuwa makaranta.
Ta shirya hakanne don tana sanya ran sabreen din zata fita ta barta a dakin kamar jiya,tasha hirar soyayya da hameed dinta,wanda a yanzu duk duniya bata jin akwai sauti ko muryar da takai tasa dadi da daraja.
Amma ga sabanin mamakinta yadda taga sabreen din kwance yana gaya matane ba lallai bane ta fita ba yau din. Tayi tsaki cikin bargon yafi a qirga,tayi juyi daga hagu zuwa dama sau ba adadi. Tana iya ganin yadda wayarta dake qasan filo keta haske alamun kiran hameed wato naseer ne yake shigowa amma tsoro ya hanata dagawa.
A hankali a hankali ta dinga jin duk wata juriya tata tana qarewa,muradinta da burinta kawai shine yadda zata samu taji muryar hameed dinta. Sannu a hankali ta dinga jin hirarsu ta jiya tana dawowa
_akan sonki bana tsoron kowa,zan kuma iya komai a gaban kowa saboda ke....zan iya sadaukar da komai a kanki,zan kuma iya rabuwa da kowa,kefa?,zaki iya?,ki gwadamin wataran_.
Kalaman Hameed kenan ko yaushe a kanta. Muddin zai sadaukar har haka ita me zaya hanata ta sadaukar?. Tambayar data yiwa kanta kenan,abinda kuma ya cire sauran dan tsoron dake ranta ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta.
Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sakar mata kamar qaramin yaro
"Har na fidda rai.....huda kina azabtar dani,kullum kafin na samu jinki sai nasha baqar wuya?,sai na shafe awanni ina lalubenki?,bayan ni ko agaban waye bana iya wofantar dake huda?,koda waye a wajen zan ambaceki zan kuma yi waya dake.....me yasa huda ni bazakimin wannan sadaukarwar ba?". Yadda yayi maganar sai ya bata tausayi sosai,harma taji tana zargin kanta daqin daga wayar tasa tun dazu
"Allah huda idan aka wayi gari na mutu sonki ne ya kasheni" Duk wata tsiga ta jikinta sai data zuba......son da yake mata wai da gaske ne har yakai haka?.
"Kina mamaki kuma kina musu ko?,kinason tabbatarwa?" Cike da quruciya da rashin sanin kan rayuwa ta furta masa
"Eh"
"Nan da kwana uku xan dawo ya kama ranar Monday,zaki yarda na shigo makaranta na daukeki?.....zan kaiki inda zan nuna miki zallar soyayyata a gareki ki ganta quru quru.....kin yarda kinaso ki gani tawan?". Sai ta narke wuya zuciyarta na karkata gason ta gani din. Can qasan ranta kuma fal mamaki,tadai kusa ganin wannan soyayyar da yaketa faman zuguiguita mata ita......ta kusa ganin soyayyar nan dai da takeji anata magana a kanta.
"Zan miki tanadi na musamman,zaki gani da idanunki.....daga ranar nasan ba zaki sake musu shakka ko kokwanto ba". Janta yayi zuwa cikin hirar sosai duk da sama sama take amsa masa a darare amma hakan bai dameshi ba,sake jan ra'ayinta kawai yakeyi,yana kuma sake dulmiyata cikin kogin qaunarsa.
Kadan kadan takejin motsi daga dakin,to amma sai kunnuwanta sukafi tafiya zuwa tsakar gidan gidan nasu. Don ta tabbatar huda bacci takeyi ko sanda ta fito,ta share wannan maganar tana dauko wayarta ta lalubi number jib.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 79
"Allah dai yaja kwana hajjaju......our young hajiya" Jib din ya fadi cikin fara'a.
Karamin tsaki taja tana kauda zancan,haka kawai ita batajin komai akan kudin,bata kuma jin wata walwala. Duk wani tsari da jib din yakeyi mata tana jinsa ne kawai,don nata lissafin duka ba'a wannan bangaren yake ba.
Uwa uba shi Kansa jib din bataji ya tsarawa kansa komai ba,ita kuma yanzu su dinne a gabanta da sauran yara marayun nan da take kwana dasu ta kuma tashi dasu cikin ranta.
"Ka sameni gidan marayun nan,zamu qaraso nida busari" Ta bashi saqon a taqaice
"Okay to ba damuwa.....amma ke me kika warewa kanki?"
"JIB....ajiye maganarnan haka a gefe,kada kabarmu mu jiraka please"
"In sha Allah" Ya fada mamakin halayenta suna sake ninkuwa a ranshi.
Kafin ta ajiye wayar tahau ta daya sim din data saba neman busari,ta tura masa saqo sannan ta ajiye wayar tana dan furzar da iska daga bakinta gami da zubawa labulen qofar falon idanu kamar me nazari akan yadda aka sarrafashi.
Kadan kadan ta dinga jin kamar dai motsinne daga dakin da kaman sautin murya a can qasa. Tun tana basarwa har ta miqe,ta taka a hankali ta soma nufar dakin.
"Eh" Kalmar da aka fadi qasa qasa ta shiga kunnenta sanda ta yaye labulen dakin. Hasken daya ratso falon zuwa uwar dakin ya ratsa blanket din da take ciki ya kuma alamta mata wanzuwar wani a dakin,sai tayi wata mutuwar kwance zuciyarta tana tsananta bugawa ta latse wayar tana turata tsakanin katifar da bagon gadon. Daqyar take iya hadiyar yawu saboda tsoro,tun yaushe nema aka shigo bata sani ba,kada dai ace ta jima a tsaye tana jinta?,wannan tunanin kadai ya sanya jikinta jiqewa da gumi kamar an watsa mata ruwa.
Hannu ta sanya ta yaye bargon,sai ta runtse idanunta
"Keda waye kike magana?" Sabreen ta jefa mata tambayar tana zube mata idanun nan nata masu kaifi.
"Magana kikaji yaa sabreen?" Shuru tayi dajin tambayar datai matan,sai ta girgiza kai alamun aah bayan ta gama qare mata kallo
"Wannan gumin fa?,ko zazzabi kikayi ya sauka?" Ta sake jefa mata tambayar amma wannan karon da salon son kamo abun farauta
"Eh.....eh nima haka naji" Idanunta ta maida ta lumshesu sannan ta bude. Ta gama bata hint,ta kuma gama hada dukkan wasu abu da takeso,ta sanyata a ajujuwa kuwa tun daga sauyawarta zuwa yau,kuma ta fadi a kowanne aji......tana jin sunzo matakin qarshe ita da ita,sai ta sake mata blanket din,ta juya tana takawa a nutse zuwa inda take adana kayan wankanta ta diba tana fita a dakin.
Da wani malalacin kallon ta bita har ta gama ficewa,haka kawai taji kaman akwai wani abu ba daidai ba
"Idan ma akwai.....idanma kuma ta gane aiba wan sabon Allahn kikayi ba" Wannan tunanin ya bata qwarin gwiwa ta tabe baki,ta maida kanta filo tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sosai,daga bisani kuma ta koma tunanin hirarrakinsu da hameed kaman yadda ta saba.
Cikin qanqanin lokaci suka isa babban gidan kula da marayu,wanda yana cikin gidajen da suke karban kaso mafi tsoka daga dukkan abinda ta samu.
A yau din kabakin arziqin data kai musu ya faranta ran kowa. Hakanan list da tayi na abubuwan da zata aiwatar musun ya sanya kowa kokwanton anya da gaske take?. A duka shekarunta ina taga adadin wadannan kudaden?. Ayyuka ne da zasu canza fasalin gidan gaba daya ya canza cimarsu harma karatun yaran gidan. Tsari ne kuma data dauki sunayen 'yammatan ciki da suka isa aure suke da buqatar tallafin kayan daki da kayan kitchen harma da suturar fitar biki. A ranar gaba daya gidan a yamutse yake da tsananin mamakin ayyukan da tace zatayi din. Saidai daga bisani shigaban gidan ya basu nutsuwa ta hanyar fadin
"Ta iya yiwuwa 'yar wani hamshaqin attajirin ce mu bamu sani ba ta bad da sawu,ko daga suturar jikinta da fatarta zakasan cewa kaman hakan zai yuwu,kudai godewa Allah daya turo me dauke mana damuwarmu koda yaushe,gashi a wannan karon bayan tallafin data saba bayarwa zata mana aikin da mutanen dake da ikon yi masu yawan gaske suka gaza yi mana......zata mana aikin dana tabbata muddin ya tabbata matsalolinmu masu yawa zasu kauce".
Ta yita share qwalla me yawa a hanyar komawa gida,yaran suna mata gizo cikin idanuwanta. Wato maraya a wannan zamanin daidai yake da wani abu maras alfanu cikin al'umma muddin ba dukiya aka mutu aka bar masa ba?,hankula da idanuwan al'umma duka sun toshe?,me arziqi shine mutum?,me arziqi shike da amfani?,idan yau kana da abun hannu kowa qoqarin rabarka yakeyi?,kowa so yake ya hada dangantaka dakai komai qanqantarta?,kowa so yake ace kuna da alaqa kunsan juna?.
Anya mutane a yau kuwa sunsan iya adadin bala'i da masifar zubar ruwan hawaye a idanun maraya qwalli daya tak a garesu?,anya suna tunawa da girman haqqinsa da ma'aiki yayi gargadi da jan kunne akai?. Bibo ta fado mata a rai,saita dinga juya kai kawai,matar tana daya daga cikin mutanen da zasu azabtar dasu tsananin azaba inda Allah ya qaddari mutuwa ta dauke ummeensu a sanda suke dukkaninsu qananu......arrahmanu arraheem ubangiji da baya hadawa bawa abu biyu......sai ya dauke musu sanyin idaniyarsu a sanda ita nata hankalin da qarfin ya fara kawowa. Ya sanya mata qarfin zuciya da kuma qarfin halin iya tare musu tashin hankali da masifa komai girmanta,ya sanya rainonsu da kulawa dasu a hannunta tun bata wuce itama a raineta ba.
(YAKE BAIWAR ALLAH!....tabbas riqo yana da wahala.....riqo yana da daci yana da nauyi,amma kisani......DA KI RIQE YARO KI AZABTAR DASHI GWARA KI TUN FARKO KICE BA ZAKI KARBA RIQON BA yafi miki sauqi da mafita har a wajen Allah muddin kikasan zuciyarki ba zata iya jure da kiyaye wannan amanar ba.....AMMA WALLAHI
WALLAHI
WALLAHI kikayi kuskure kika karbi riqo don ki burge ko kada a zargeki,to wallahi idan nace KINA CIKIN MASIFA ma kadan ne.....ba zaki san girman bala'i da kike ciki ba sai ranar gobe qiyama......hatta ubangiji bayason kuka maraya shi da yayi kowa yayi komai ya kuma qaddara hukuncin maraici a kansa
IDAN KINSAN akwai maraya yanzu haka da kike banbanta riqonsa dana 'ya'yanki.....to ki gaggauta yiwa kanki hisabi tun kafin ranar zuwan hisabin na gaske.......idan har kinsan akwai maraya yanzu haka a hannunki.....to ki gaggauta gyarawa kafin ki barwa 'ya'yanki masifa da bala'in da zaiyita bibiyar rayuwarsu,kiyi qoqari kifi qarfin wannan tsokar dake qirjinki wadda ake kira da ZUCIYA.....kiyi qoqari kifin qarfin wannan maqiyin naki wato SHAIDAN.....Allah ya bamu ikon fin qarfin wadannan ababe guda biyu ameen summa ameen).
"Kaini gidan malam" Ta fadiwa busari a nutse,wanda bai musa ko ya tambayi ba'asi ba ya karkata akalar motar. Zuciyarsa shima cike take da farinciki,don yana cikin alherin tashi daga dan adadaita sahu,zuwa mamallakin shago sukutum da guda a babbar kasuwar kantin kwari nan da sati uku kacal.
Kusan duk wanda ya kwana ya tashi a kamfanin yasan da faruwar komai. Yayin da sake fitar labarin boyayyar badaqalar data afku qasa da wasu awanni ya sake sanya mutane da yawa na kamfanin mamaki musamman wadanda basu san komai ba,basusan kuma abinda ake ciki ba.
Kowa da kansa da kansa ya yiwa hisabi,don shigowar boss Muhammad kamfanin ya sake sanya kowa shiga taitayinsa. Masu zuba kunnen abinda zai faru da kalar matakin da zai dauka suka ci gaba da sanyawa,yayin da a nasa bangaren ya nutsa cikin bincike tare da tattaunawa da taimakon dan uwansa kuma shaqiqinsa farouq.
Ganawa ce takai tsaye kuma da mutum na farko bayan shigarsa kamfanin da sukayi da manager din banking da yake mu'amala dashi,wanda suka iso su uku da biyu cikin nasu ma'aikatan. Hankalinsu kusan yafi na fuad tashi,don sun sani ba qaramar nasara bace ace kamfani kamar wannan yana da asusu dasu,hakanan kuma....gagarumar asara da faduwa ce ace a yau ya rufe account dinsa dasu sanadiyyar wannan.
"Baku da laifi sir......coz kusan sai aka shigar da komai da ake buqata da zai bawa mutum damar accessing da account din sannan kuka bada damar fitar kudin......inda kuskuren yake shine......amount din da aka fidda din ya cancanci ace anyi alerting namu kafin a bada daman fiddashin.....saboda akwai hanyoyin da mukebi wajen fidda kudade masu nauyi irin haka........kuma kun san da hakan......anyway...sakacin security team namu yafi na kowa.......sai kuma ma'ajij company da yake number one" Ya qarashe maganar yana komawa ya zauna sosai yana gyara wuyan suit nashi.
Matsowa sadiq yayi dab dashi a nutse ya rada mishi
"Hamma......mun gaza samun mikail har yanzu mu shaida masa zaman da za'a yi yau din". Kansa ya gyada
"Kar damu dashi......idan inason ganinsa ko ina ya shiga zan sanya ne a kawomin shi.......but nafison ya kawo kansa da kansa in a legal way.....ka rabu da nemansa"
"Okay" Ya fadi cikin gamsuwa. Ya yadda da hamman nasa,ya sani ba ordinary mutum bane tuntuntuni......bayajin a yanzu ko farouq zai gaya masa wayeshi saboda kaf gidan yafi kowa kasancewa dashi cikin awanni masu yawa. Fara aiki dashi ya sanya kullum kwanan duniya yake sake shiga ransa. Baisan haka hamman nasa yake da shiga rai ba sai yanzu......baisan haka kyakkyawar mu'amala take yawo a jininsa ba sai yanxu da aiki yake hadasu adadin awanni masu yawa.
Hannu ya miqa ya karba file din da suka iso masa dashi na dukka bincike da nasu bibiyar da sukayi. Kusan wasu guraren abubuwan da suka bincika yazo daidai da nasa,wani gurin kuma sun kasa accessing information din jibril wanda shi a yanzu haka yana da komai. Abu daya ya kasa yarda dashi shine......jibril bashi kadai yayi wannan aikin ba.....dole akwai wani a tare dashi......wanin kuma yana qarfafa zargin muddin ba mikail bane da kanshi ya dauki duka information din ya miqa musu da zummar cin amana ba......to na jikin mikail ne wanda yake tare dashi.
Hannu ya bawa manager din sukayi musabaha
"Mr Joshua mamallakin bankin yana miqa jajensa......yanzu haka yana hanyar zuwa kowanne lokaci,da fatan zaa karbi baquncinsa". Wani abu me kama da murmushi kawai yayi yadan dage kafadarsa,sukayi sallama dashi ya fice.
Iska me zafi ya fitar a bakinsa,ya miqe yana zare suit din jikinsa na saman ya ratayeta a muhallin da aka tanada don ratayewar. Ya duqa yana zare takalmin qafarsa hadi da magana da saddiq
"Awa nawa ya rage mu shiga meeting?"
"Thirty minutes hamma"
"Good......yanzun security team kawai nakeson gani,kayi cancel sauran staffs......infact ma banason susan da zaman.......ina da buqatar binciken sirri a kansu don dole mu nemo me fidda mana information......ka gayawa me sunan malam immediately after meeting inason ganinsa"
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 80
"Done" Ya fada kaman yadda ya saba. Daga kai farouq yayi ya kalli saddiq din
"Kalleshi kaman mutumin kirki........ya addabemu cikin gida......sai yazo company sai ya zama wani me biyayya.....thank god da Allah ya hadaka da fu'ad......da nine da tuni ka kusa sakamin hawan ruwa" Ya qarashe maganar yana daukan gorar ruwan da fu'ad ya dauko musu saman table yana mamakin yadda qananun hidima na cikin office yake yi da kansa,duk da cewa yana da qarfin ikon da ko taka qasa yace bazaiyi ba akwai masu yi masa.
"Bakasan mutane da yawa da suka fiya wasa ba suna da wani boyayyen talent?".
"Talent a wajen wa wai?,wannan?,kawai dai Allah ya tattaro mana shi da taimakonka" Ya fadi yana bude murfin ruwan. Bai amsa ba fu'ad,yadai saki siririn murmushin da ba lallai ka iya fahimtarsa ba yayi bismillah can qasa ya soma zuqa a hankali.
Kafin yakai ga dire cup din kira ya ratso wayarsa,saddiq yafi kusa da ita don haka yace
"Hamma amna ce"
"Kai dauki kace mata lokacin aiki ne yanzun" Kai fu'ad ya girgiza da sauri yana aje ruwan. Wayar ya miqa masa,ya sake duba kiran sannan ya daga
"Good morning hamma"
"Mornin lovy dovy". Qaramin murmushi ta saki
"Hamma ka tashi lafiya?,yau ka fita early kuma anni tace baka tambayeni bama" Ta qarashe fada da shagwabar nan tata data zame mata jiki. Murmushi ya saki
"Ban tambayeki ba amma kina raina amna.....wani muhimmin abune ya taso.....kiyimin addua,ki gayawa anni ma idan tazo sallan dhuha tayimin addu'a.....but karkice mata wani abu ne ya taso,just kice munyi waya nace tayimin addu'a during salat of dhuha".
"In sha Allah hamma.....Allah ya kula ya tallafa" Ta fada cikin kulawa
"Ameen autan anni" Murmushin jin dadin sunan ta saki
"Hala rival dina baya kusa hamma......yaji da kunnensa sunan dai nawa ne"
"Karki bari na dawo gida na iskeki....." Saddiq dake gefan fu'ad ya fadi da sauri. Kai ya daga fu'ad din ya jefa masa harara
"A gaba na?"
"Sorry sir" Ya fadi yana shafa kansa. Abun ya yiwa amna dadi,yana iya jiyo qaramar dariyarta har ya katse kiran.
"Baka hasko komai game da mikail ba?" Farouq ya jefa masa tambayar sanda yake qoqarin duba wani saqo daya shigo system din nasa daga department na wanke dukka diamond din da aka haqo don tabbatar da kyansa da ingancinsa.
Fararen idanunsa kewayayyu da hasken system din ya qara haskewa ya daga ya dubeshi na wasu sakanni sannan yace
"Kai me ka hango?".
"Guy din bashi d gaskiya kwata kwata.....and ina kyautata zaton yana da masaniya akan komai koda bada saninsa akayi ba".
"Na fahimci haka......but akwai wani abu ko wani behind him....."
"It's true.....ni tun tafiyarka South Korea na karanci abubuwa masu yawa game dashi,bamu samu zama bane yadda naso har wannan abun ya faru......amma bari mu fita a meeting dinnan"
"Yayi" Ya amsa masa yana duba lokaci.
Wata irin zazzafar tattaunawa ce ta wanzu tsakaninsa duk wani dake under security team. Jiki da zukata sunyi laqwas da wani irin tsoro da kuma firgici. Bacin ran da suka gani a fuskar boos din nasu ya sanyasu cikin tashin hankali,domin kuwa wani abune da basu taba ganinsa a tattare dashi ba.
Dukka bayanan da suka bashi kusan yazo iri daya akan nasa da wanda baki suka bashi,saidai akwai wasu sauye sauye cikin nasu
"Na baku 2days to find full details na dukka team din da sukayi wannan aikin......na tabbatar ba aikin mutum daya qwal bane......team work ne tabbas!" Ya fadi yana doka file din saman table din da yake kai.
Zuciya da qwaqwalwarsa duka a zafafe ya dawo office,yayi nufin yin alwala don yayi salat dhuha kaman yadda ya saba sai yaga lokaci ma duka ya qwace,duk da haka bai fasa daura alwalar ba saboda ita kadai tana saka masa sanyi cikin zuciyarsa
"I need rest please.....duk meson ganina ka gaya masa sai after one hour......kayi shutting komai saina nemeku" Yayi magana da mutanen dake tare dashi. Da daya da daya kowa ya fice har saddiq. Farouq ya miqe a hankali
"Ina zaka kai kuma?"
"Zan bar CEO ya huta haka nan......da gaske brain dinka yana buqatan shuru na wasu lokuta".
"Ko zan huta da ganin kowa banda kai farouq" Ya amsa masa yana jingine bayansa jikin sofan da ya canza mata siffa daga kujera ta koma qaramin gadon hutawa cikin sakan talatin.
Murmushi farouq ya saki,sai ya kalli agogonsa sannan yace
"Na sani.....but now dai dole farouq yadan matsa kadan Shima.....zanje nayi waya da fanna......yau duka ban kira naji lafiyarta ba". Kiran sunan fanna kawai da yayi ya sanya ya daga masa hannu ba tare da yace masa komai ba,sai ya sake sakin qaramar dariya yana takawa
"Anyi zancan SOYAYYA zaka birkice.....bari na qara matsawa da hanzari......hala daya cikin matan naka ne ma zasu kawo maka ziyara". Yayi zancan yana kaiwa qofa.
Maganarsa ta sanya fu'ad sakin murmushin dole duk da bai shirya ba,sai ya bude idonsa a hankali yana bin bayan farouq da kallo har ya qarasa ficewa,ya maida idon ya rufe bayan ya saita security na qofan nasa da wani qaramin remote a gefansa ta yadda babu me iya damunsa,duk da ya bada warning ma reception nasa da kuma saddiq. Shi a wannan ire iren situation dinma idan har yace soyayyar zaiyi baisan ta yadda zai fuskanceta ba.....baisan ma ta inda zai kwasota ba. Yasha ji daga bakin farouq rashin bada kulawa da bada lokaci yana kawo macewar soyayya.....shi kam ya tabbatar wannan shine dalili na farko da zai saka tasa soyayyar mutuwa murus. Ya tuna 'yammata biyu da farouq ya takura ya hadasu.....abinda dukka ya rabasu dashi shine lack of caring. Sometimes ma mantawa yakeyi da babinsu,koda kuwa ta hanyar tura tex bare kira bare aje gayin tattaki zuwa gidajensu. Da kansu suka fahimta baida lokaci,suka kuma samawa kansu salama zancan ya mutu murus,shima suka shafa masa lafiya.
A hankali kekenapep din ke gangarawa da ita layin gidan malam din,ya kuma tsaya daidai gidan.
"Na gode......kana iya tafiya,gobe idan Allah ya kaimu zan nemeka saimu qarasa komai,ka gaida ummaah da kyau"
"Zataji in sha Allah....tace zatayi tattaki da kanta don miki godiya". Murmushi kawai ta saki tana sauka daga napep din,idanunta kan muhallin da malam ke bada karatu. Ba jamaa wajen,ta kalli agogon hannunta,da sauran lokaci akan lokacin daya saba xama,sai ta taka a nutse tana wucewa cikin gidan.
Kamar kullum ta taras da rumasa'u tana aikace aikacen gida,matar malam na daga rumfarta a zaune tana tsince busashen zogale.
"Maraba da diyata" Ta fadi cikin fara'a da murmushi tana sauke farantin zogalen daga cinyarta gami da karkade zaninta da ya d'an baci da kadan. Har qasan zuciyarta kuma tana jin dadin dawowarta da wuri,ba kaman wancan karon ba data tafi ta jima bata waiwayosu ba.
Itama tata fuskar da murmushi tare da jin dadin yadda aka samu wasu halittu da suka damu da rayuwarsu ta qarasa shiga cikin rumfar,bayan ta zame halfcover din qafarta
"Aah.....ina sauran jikokin nawa?" Ta furta tana duban bayan sabreen. Murmushi ta saki tana zama saman shimfidaddiyar daddumar da matar malam din ta shimfide mata
"Ba daga gida nake ba gwaggo" Ta fada Kaman yadda taji rumasa'u tana kiranta wani lokaci.
"Kash.....to ai naso ganin kishiyata haneefa ne ai" Ta furta tana dariya tare da yunqurin miqewa
"Itama kullum zancanta kenan.....amma zan kawosu na kusa in sha Allah"
"To Allah ya yarda" Ta amsa mata tana bude fridge din dake ajiye a rumfar gaban falonta ta ciro mata ruwan pure water me matsakaicin sanyi da lemon zobo,rumasa'u ta hado da kofi ta shigo mata dashi.
"Nima inata sanya ido naga huda" Ta fada tana murmushi. Kiran sunan hudan ma ya sanya hankalinta dawowa kan huda din data barosu gida.
"Zasuzo in sha Allah rumasa'u" Ta amsa mata cikin kulawa.
Zama tayi suna dan taba hira,tana son su sabreen yarinyar,wanda su kansu basusan dalili ba,saidai ba ruwan ubangiji shi yakan sanya qauna da jituwa tsakanin bayinsa a duk sanda yaso hakan ya kasance.
"Hala malam baya nan?" Ta tambayi gwaggo
"Yana nan,yadan fita ne kasuwa,amma da wuri yau din zai dawo,yana da karatun dare na manya da yakeyi". Kai ta jinjina,tana jin dole zata jirashi har ya dawo,duk da tanason komawa gida da wuri,don a yanzun hankalinta bai bata ta dinga nisan kiwo ba.
Jikinta da zuciyarta sun gaza samun nutsuwa sam sam akan huda,cikin jikinta takejin akwai wani abu ba daidai ba.
Iya yadda tayi magana da ita dazun kawai ya isa gaya mata akwai wani abu,saita rufe babin wannan tunanin tana maida hankalinta tsakar gida hadi da taya su gwaggo amsa sallamar malam din.
*Tsaye yayi kawai gaban madubi yana duban fuskarsa da kyau tare da son bawa kansa qwarin gwiwa. Yana buqatar cikakkiyar nutsuwa da kuma qarin tattara dukkan wani tsohuwar fasaha da qwarewarsa wajen ganin ya cimma nasara a cacar. Tunda yake bai taba caca mafi hatsari ba irin wannan. Caca ce da zata iya zuwa masa da sakamako guda biyu......nasara wadda zata wankeshi daga dukkan wani rudani da tashin hankali.....ko kuma faduwa wadda daidai take da daukan guduma ta kuma tarwatsa rayuwarsa gaba daya.
Hasashen sunan faduwa kawai sanyawa zuciyarsa wani irin mugun bugu yakeyi,tuna sunan FADUWA kawai sai yaji kaman qirjinsa zai tarwatse,don haka a yanzu da yake tsaye gaban madubin ya daga murya don baiwa kansa da kansa tabbaci tare da qwarin gwiwa
"Ba faduwa a hanyata,tabbas nike da nasara......ni zan cinye!" Ya fadi da wani irin qaraaji yana sake sanyawa ransa nasarar da gaske tasa ce.
Qofar aka dan qwanqwasa,ko ba'ayi magana ba yasan waye,don haka ya waiwaya yana fadin
"Gani nan,tayar da mota" Sai ya juya ya dauki waya da maqullansa ya fito.
Baice da mato komai ba ya bude gaban motar ya shige,mato kuma ya bawa motar wuta,ya danna hon me gadi ya dage musu gate din suka fice.
"Ina fatan yau baka shawu ba" Mato ya fada yana sake bawa motar wuta saman kwalta. Harara ya waiwaya ya maka masa kafin yace
"Mahaukaci ne ni?,idan nasha ta yaya zan samu isa ga abinda nakeso?,......zan shawu iya shawuwa bayan mun dawo da talin himilin kudin da zan cike gibin asarata". Kai mato ya jinjina yana dan dukan steering
" Inaji a jikina kam wannan nasarar tana hannuwanka......munkaila me da'ira?.....ka manta sunan naka ne?". Wata wawiyar dariya ya saki,sunan da mato ya tuna masa ya sake jinsa cikin alfahari......wani rubutaccen suna ne daya samoshi daga wajen abokan cacarsa. Muddin zai hau tebur din caca to ko kai waye ka zama nama,baisan iya adadin abinda ya tara ba da dukiyoyin al'umma shekara da shekaru,sai yau gashi dare daya wata qaqqarfar guguwa tanason yin gaba da tsohon arziqinsa?......inaaaa......ai bazaya bari ba,sai inda qarfinsa ya qare. Iya sunan da mato ya gaya masa ya sanya masa qarin karsashi tare da jin dokin isa wajen.
"Ni kaina inaji a jikina lokacin nawa arziqin ya gabato,don gagarumar caca ce ina gaya maka me gida.......tsaffin 'yan caca za'a zuba wadanda suka sanya kudi masu ciwo......don Allah banda ganganci ina tsohon hannu zai kara da sabon jini?,yaro masanin dabaru da siddabarun kayar da mutum?"
"Tsautsayi ne mato" Ya bashi amsa wani murmushi yana subuce masa,don nasararsa kawai yake hanga muraran.
Tafiyar mintuna kadan suka isa gidan cacar,tun daga waje ya fahimci gidan a cike yake,abinda ya sake tabbatar masa da maganar mato. Ya fito a motar yana murmushi suka jera da mato zuwa ciki yana sake bashi bayani akan komai.
"Amma me gida......nayi mamaki da me jadda bai nemeka ba".
"Har gwara ya nemeni da wannan shurun da yayimin......shirunsa yana nufin komai mato......shi yasa nake bidar nasara a wannan karawar.......daga nan wajensa zankai kaina ayi a gama......bani da tabbacin a yanzun baida masaniyar inda nake.......tsaf yana sane da motsina duka zai iya yiwuwa". A mamakance mato ke duban mikail,tsoron girman izza da qarfin ikon Muhammed jadda tana sake saukar masa,saidai bai samu cewa komai ba suka qarasa ciki.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 81
Daga yadda yaga wajen ya sake amanna da maganganun mato din. Duba daya ya fahimci tabbas masu tsohon arziqi da kudin caca ne,kuma da alama a yau din kowa cikin buri yake,hakanan kowa yayi guzurin dukka wata dukiya da yake alfahari da ita.
Saura kadan dariya ta fashe masa,don dukkaninsu shi a nasa idanun kallon gidadawa yake musu,kuma cinyayyu da zasu qare wasan cikin hasara da rashin nasara.
Su biyu rak ke zaune daga wata kwana cikin farfajiyar wajen. Kawu kenan,wato kawu sama'ila shi da nasa aminin barau.
Cikin nutsuwa da shegen kwanyar da yake dashi yake karance mikail da idanunshi sunkai kan kawo amma banda kan kawu din. A nutse yake karantar mukail,har zuwa sanda suka zauna da'irar da za'a zuba caca ta farko.
"Me ka karanta ne sama'ila?,kayi shuru ko ka fasa ba zaka buga wasan ba?" Murmushi kawu ya saki yana tura hularsa gaba.
"Tun bayan mutuwar yaya daya haramta min yin caca,ban qara zama gagarumar caca irin wannan ba.....inaji a jikina silar arziqina ne yazo.....bazan zauna ba har sai naga iya nashi takun......baka ruftawa wasa baka san yanayin hannun kowa ba"
"To me ka fahimta sama'ila?" Barau ya sake tambaya idanunsa akan yadda wasan ya fara tafiya
"Dan zamani ne fa wannan da zai kara da tsaffin 'yan wasa......gogagge ne kana kallonshi,kuma shima qwararre ne da irin tasa qwarewar,wanda idan kowa baiyi takatsantsan ba komai zai iya faruwa"
"Shege sama'ila" Barau ya fada yana qyaqyacewa da dariya
"Ka zuba ido kawai kayi kallo" Ya amsa masa yana maida hularsa daga gaban goshi zuwa qeya.
A duk sanda yakeson samun nutsuwa ta qwaqwalwa da ruhi sararsa shine kwanciya,ya rufe idanunsa yayi kuma shuru a waje da muhallin da ba hayaniya ko kuma motsin kowa. Ko yanzun hakan yayi cikin office din,saidai qarar wayarsa ya sanyashi miqa hannu ya lalubota don yasan ring din na daban ya sakawa kiran don kirane da yake buqatarsa
"Sir........yana gidan caca na green card"
"Good" Ya fada a nutse yana bude idanunsa
"Don't let him go.....ina buqatar information na wuninsa na yau gaba daya"
"Yes sir" Ya furta cikin girmamawa. Wayar ya ajiye,sai ya miqe a nutse ya zauna ranshi na wani mahaukacin baci. Ga wani zargin ya sake shigo kasa akan mikail yanason kore uzurin da zuciyarsa keson bashi. Muddin ya kuskura bincike yazo masa caca yayi da kudinsa na halal tabbas!,zai nuna masa ainihin kalarsa......zai gane waye zahirin muhammad jadda. Dukiyar da aka tarata da gumin halak?,dukiyar da ake takatsantsan wajen jefa haram a ciki komai qanqantarsa?,kudin ruwa da ruba dukkaninsu haramtattu ne a cakudasu cikin dukiyarsa,amma yau din zanyi ganganci ko kuskuren zarar halalinsa ya jefa a qazantaccen guri irin wannan?.
Tsam ya miqe,sai ya koma saman table dinsa ba tare daya sanya takalma a qafarsa,ya kunna system dinsa ya tattara hankalinsa akai.
Karo na kusan goma barau ya kalli kawu sama'ila kaman yadda mato ke zaune yana murmushi daga gefan mikail yana kuma tayashi lissafin maquden kudade da dukiyar da yaketa cinyewa ta abokan bugunsa.
"Sama'ila?,dama wannan shine hasashen naka?". Murmushi kawu ya saki yana karkacewa kaman abun ya masa dadi
"Gaskiyar kenan barau.....amma barshi ya gama iya tasa dabarar......uwayensa na nan zuwa su koyar dashi darasi" Wata dariya barau ya saki bayan ya gama fahimtar abinda kawun yake nufi
"Yanzu naji batu,amma ta yaya muna da kai zaka bari wannan jaririn yazo gidanmu ya cimu wasa?" Murmushi ya sake saki idanunsa akan mikail daidai sanda ya cinye alhaji wada miliyoyin kudi
"Talala ce me kaman sake.....barshi ya gama karbarmin kudaden tukunna da gidajen" Dariya barau ya sake saki harda buga qafa.
Cikin awa uku ya daurewa kowa jijiya a wajen. Cikin tumbatsa da izza mato ya miqe
"Akwai wani sauran wanda zai kara da sarki?" Yayi shela yana ji a ransa sun gama da kowa,babu me sauran motsi. Shuru ne ya biyo baya,sai ya sake maimaita tambayar yana duban kowa d'ai d'ai
"akwai" Barau ya fada da qarfin murya. Mato da mikail din duka suka waiwaya suna duban kawu dake qurya,sai suka dubi juna tsakanin mato din da mikail
"Waye kenan a cikinku zai shiga?" Tsam kawu ya miqe yana nuna kansa
"Nine" Ido suka hada sai suka bushe da dariya tsakanin mato da mikail
"Qaraso mana dattijo....koda yake ba dattijo a nan......inajin akwai rabona a jikinka ne kaima.....ko giya ta kwana daya na sha da canjinka". Boyayyen dariya kawun ya saki,ya fara takowa zuwa wajen kowa ya zuba masa idanu yana mamakin qarfin halinsa,kamar ba'a gabansa aka cinye kowa ko ba amma shi zai jefa kansa?.
"Dame zaka shiga?" Ya jefa masa tambayar a raine. Karkacewa yayi ya zaro wasu takardu yana dubansu. Takardun dake dauke da sunan alhaji aliyyu ahmad zaki......mahaifi ga sabreen..... Takardar dake matsayin mallakin magadan kuma marayan yaran da yayi Qundumbalar shiga cacar da ita,cikin jin cewa zata ciyo masa tarin maquden kudaden da zasu zame masa silar arziqinsa gaba daya.
Saman teburin ya aza takardar yana kallon mikail,hannu ya sanya ya dauka ya duba ya karanta ya kuma tabbatar original ce wanda gidan ya haura miliyoyin kudi
"Ashe.....kudinka baaba ai ya haura 'yan canji ma ai.......idan na samu nasarar cinye gidan nan ko?,rusheshi zanyi na maidashi gidan shaqatawa,ayita shigomin da 'yammatan unguwa ina hutawa dasu ina biyansu".
Wani abu ne ya cakewa kawu a rai,ya tsani zina,ya tsani harkar neman matan banza,kaman yadda ya tsani shaye shaye,barshi kawai da cacarsa data zame masa masifa wanda dama tana da shiga jiki. Kai tsaye yaji tsantsar cin fuska ce ya tanadeta zaiyi musu wannan ya sake aza wutar qaimi a zuciyarsa,ya karkace kaman yadda yakanyi a yanayi irin wannan,ya kalli Mikhail da kyau
"Idan dai har ya zama mallakin naka kana da wannan damar" Ya bashi amsar da wani irin kakkaifan kallon dake gaya masa kai tsaye na SAI NA BAKA DAMAR CINYE GIDAN SANNAN ZAKA AIKATA HAKAN.
Izza da jin cewa zai samu nasara akan kawun ya sanyashi ninka abinda kawun ya zuba shima ya zuba cikin cacar aka fara buga wasan. Tashin farko kawun ya maido takardun gidan yayi tafiyar ruwa da kudaden da mikail ya zuba,abinda ya jawo hautsinewar wajen,hankula dukka suka komo wajen,aka fara yo dafifi,wadanda aka cinye suke alhini dukansu karsahinsu ya dawo,sai aka fara zuba sabon wasa.
Da daya da daya ya dinga zuba abinda ya ciyo kawu sama'ila yana kwashewa. Duk abinda ya zuba kawun ya cinye shaidan zuciya da kuma mato saisu gaya masa ya sake zuba wani,zai iya yuwuwa ya samu nasarar dawo da abinda aka cinye masa a baya.
Tafi tafi cikin qasa da awa biyu sai gashi yana tashi daga Mikhail me manyan kudi yana komawa asalin mikail dinsa kaman yadda ya shigo wajen. Cikar awa biyu cif komai ya qare!.kawu sama'ila ya wawushe duk wata kadara daya cinyo daga wajen wasu ya zuba!,ya koma tsurar yadda ya shigo musu a wajen!.
Sowa ihu murna da tafi ya cika wajen,ainihin sunan kawu sama'ila na teburin ya soma dawowa bakunansu wato DA BANBANCI!.
Kowacce tsiga ta jikin mikail zubawa takeyi. Idanunsa sun kada sunyi jazur,jijiyoyin kansa sun fito rada rada. Sosai yakejin ya muzanta,ya toxarta. Ta yaya zai bari wani qaramin alhaki tsohon daya bashi shekaru masu tazara ya kafa tarihi a kansa?,tarihin da muddin ya bari ya tabbatu a haka.....to ko shakka babu ya xubar da kimarsa da kwarjininsa a idanun abokan cacarsa dake bashi wani irin girma. Karon farko a rayuwarsa da wani yayi nasara a kansa,shi kuwa ta yaya zai bari haka ta tabbata?.
"Ga wasu kudaden na zuba.....azo a sake zama!!" Ya furta da qarfi,sautin daya sanya wajen yin dif aka zuba masa ido.
Da sauri mato ya kalleshi,ya kuma ja hannunsa da qarfi yana dubansa qasa qasa
"Wanne kudi kuma ya rage maka indai ba motar da mukazo a ciki ba zaka saka?"
"Qyaleni mato.....bakajin habaicin da suke yada min?,dole na aje musu tarihi,dole sunan mikail suma yaci gaba da wanzuwa a kunnuwansu da bakunansu da wajen cacarsu".
"Wanne kudi ya rage maka?!"
"Ragowar abinda aka bari a asusun jadda" Ya fada yana jin zuciyarsa ta qeqashe,kuma tabbas wannan kudin xai dawo da sauran kudin da duka narke,duk kuwa da yasan mugun gangancin dake cikin aikata haka.
"Kada kayi haka!" Mato ya fadi a gigice.
"Anma yi" Ya amsa masa ba fargaba ko shayi saboda ya bawa kansa tabbacin shine keda nasara.
Wayarsa ya fidda yabi dukkan process yayi transfer kudin da suka rage zuwa account din wanda zai ajiye kudin,idan nasara tasa ce ta dawo masa,idan ta kubce kuma dukka kudi sun tabbata mallakar KAWU!.
Daidai lokacin da akayi alerting mutum biyu fitar kudin,sai fuad dake zaune yana bibiyar komai ya lumshe ido yana sauke siririyar ajiyar zuciya,daidai sannan kuma kira ya shigo masa. Ko daya duba sai yaga daga department din da aka kira ya daga yana cewa
"Just keep an eye on it,naga komai" Sai ya kife wayar yana maida dubansa ga allon system din yana qoqarin tracking account na wanda aka sanya kudin.
*_TURQASHI....QAQA QARA QAQA,BAZANCE KOMAI BA😂😂.....amma akwai ZAZZAFAR TURKA TURKA FA.....MUJE ZUWA_*
*HUGUMANKU CE*
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
Page 82
A wannan karon......daga shi har kawu samaila sai da aka basu hutun mintuna ashirin,don kowannensu yayi iya shirin da zai qara yi. Magoya baya kuma jingima kawun ya samu,wanda kusan dukkansu suna murna ne da nasarar daya samu,don sun tabbatar cewa koda basu maida dukkan abinda Milakil yaci nasu ba,to tabbas kawun zai maida musu wasu abubuwa kasancewar shi din nasu ne.
"Me gida......ka tsaya iya waccar asarar da kayi......kada kayi kuskuren sake yin wani ganganci......ka fini sanin waye muhammad jadda"
"Sosai kuwa mato.....amma jikina yana bani nasarata tana tare dani wannan karon......bazan bari nayita asara ba" Ya amsawa mato cikin yanayin da yake alamtawa mato cewa mikail din yayi nisan da bazaiji kira ba.
Cikar mintuna ashirin aka sake zama,zaman daya dauki sabon salo ya kuma dauki hankulan kowa dake wajen. Tsahon wasu mintuna ana fafatawa,inda daga qarshe komai yazo qarshe. Kawu samaila ya sake wawushe kudin,ya kuma bar mikail cikin wani irin yanayi tsakanin mutuwa da rayuwa.
Dukka kururuwar murna da muryoyin abokan kawu samaila dake tashi a wajen baya iya fayyace komai. Abu daya kwanyarsa ke iya fahimta gami da maimaita masa
"An qarasa cinye kudin jadda diamond resources,ba abinda yayi saura".
Kowanne sashe na jikinsa ya dauki rawa da wani irin kalar tashin hankali mara misali. Yana jin komai ne tamkar yana mafarki.....yana ganin kamar xai farka ko zai tashi,yana ganin kamar ba haka bane har sai daya damqi hannun mato
"Mato da gaske ne?,ko mafarki ne?"
"Da gaske ne maigida......ai na gaya maka dama". Taga taga mikail din yayi zai fadi mato ya taroshi,jama'an dake kusa suka kuma karanci hakan suka kawo masa dauki ta hanyar tallafe masa mikail din suka zaunar dashi suna masa sannu
"Kaima banda abinka oga ai kayi wauta.....hausawa sukace idan bakasan gari ba saurari daka......na tabbatar rashin sanin waye sama'ila ya sanyaka sakin jiki dashi kan teburin caca......amma ita dama yau gareka ne gobe ga dan uwanka,idan an sake wani zaman ta yiwu ka samu nasarar maido wani abun naka"
"A wajen wa?......lallai garba ka manta waye sama'ila ne" Dan uwansa da suka kawo daukin tare ya fadi yana murmushin aikin gama ya gama.
"Kaini gida mato.....mu fita daga nan" Mikhail ya fada kaman wanda ya hadu da ciwon makanta,don gaba daya sai yakejin wajen ya matse masa ainun,kai......kamar ma baya shaqar numfashi yadda ya kamata a wajen.
Tsoro fargaba da mutuwar jiki suka saukarwa mato sanda ya tayar da motar da yake tunanin ita daya ce Allah ya mantar da Mikhail bai sanyata tsaiwa takarar na ciyo ko a cinyeni ba wato caca. Kuka rurus mikail ya fashe dashi. Yana ji har a cikin zuciyarsa bashi da wani sauran abinda ya rage masa,to wai shin idan baiyi kuka ba me zaiyi?.
Yana hango kawai yadda zai qare sauran Rayuwarsa ne a gidan kaso......yana hango yadda me jadda zai qarasa murqusa Rayuwarsa bayan rasa dukkan wata dama daya fara jiyo qamshinta a baya. Ba shakka fateema ta cuceshi.......har a zuciyarsa yana jin inda zai iya ido hudu da ita a yanzu babu abinda zai hanashi hallakata.
Sun dan dauki lokaci da malam suna hira tana ta juya yadda zata gaya masa batun tallafin data kawowa dalibansa da rabon jarin da takeson yiwa duk wanda ya isa munzali a cikinsu. Cikin kudaden tanaso ta yiwa malam din alherin kudaden da zasu taba rayuwarshi sosai. Sosai mutumin yake burgeta........namiji na farko baya ga mahaifinta da taji dabi'u da halayensa sun mata,namiji na farko da takeji nagartarsa ya mata......kuma namiji na farko da idan ta zauna suna magana dashi takejin kamar wani sashe na mahaifinta ne ya dawo duniya.
Duba da yadda lokaci yake qara tafiya,ta tabbatar qanqanin lokaci ya rage ya fita don yin sallar magariba. Sai ta daure ta gyara zamanta.
"Magana nazo muyi malam,saidai bansan yadda zaka karbi abun ba" Ta fadi kanta sunkuye a qasa.
"To ina jinki mana aminatu.....lafiya dai ko?" Zamanta ta gyara tana jin nauyinsa da kuma kwarjininsa yana ratsata
"Eh lafiya malam......akwai tallafi ne da wata qungiya ta sa kai ta kawo don a rabawa makarantun tsangayu..... To banyi qasa a gwiwa ba na sanya sunan makarantarka a ciki,don nasan akwai dalibai da qarfinsu ya kawo kuma suke da buqatar sana'a......hakanan kaima malam na saka naka sunan a ciki......an kuma dace sun bada kaso me tsoka"
"Toooo.......ikon Allah" Ya fada a tsanake yana nazarin abun
"To sannu da qoqari,Allah ya saka da alkhairi......to sudai yara ba za'a hana raba musu jari ba......saidai komai zai zama bisa tsari don kada su saka a gaba su cinye.......kuma tallafar Rayuwa ne don bakasan ta sanadin jarin abinda Allah ya hukunta wani zai zama ba......amma zaki raba musu da kanki......hakanan zaki rubuta da kanki......batun sunana da kika saka ni na yafe....na gode miki da dukka qoqarinki a kaina.......amma basai kin bani komai ba".
Shuru gurin yayi,qasan ranta tana jin wani abu maras dadi. Har ga Allah malam uba ta daukeshi........tana masa kallo ne irin na d'a da uba......to amma kuma tasan halinsa,ba kasafai yake canza hukunci ko magana ba idan ya zartas
"Lokaci yana gabatowa,zan fita na shaida musu su zama cikin shiri.....wanda kuma yasan baida sana'a kar ya shigo ciki"
"Hakan ma yayi malam" Matar malam din ta amsa masa,sai ya dauki butarsa da rumasa'u ta cika masa da ruwa yana ficewa.
Yammaci lokaci ne da kowanne ma'aikaci yayi handing over aikinsa na ranar......ya kuma tattara ya nasa ya nasa yayi guda ko kuma guraren da mutum keda ra'ayin zuwa.
Company din yayi tsit.....don hatta da masu danyin late kafin subar office din a yau sun fice,ba kowa sai muhammad fuad......saddiq da musaddiq ke zaune saman sofa,jifa jifa yana daka kansa ya kalli muhammad fuad da yaketa aiki haiqan saman system tamkar a nan zasu kwana ko bashi da niyyar barin office din a yau.
A hankali ya zare idonsa daga system din ya maida saman agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Mikhail ya fado masa a rai,sai ya jijjiga kai a hankali ya maida dubansa ga musaddiq. Idanu yadan zuba masa kadan yana jin tausayinsa yana saukar masa. Ya tabbatar a gajiye yake,kuma bashi da burin daya wuce ya wuce gida,saidai kuma komawarsa gidan a yanzu babban hadari ne ga lafiyarsa dama rayuwarsa.
"Mu qarasa gidan malam muyi sallar magariba a can" Ya fada yana dan ture table din gabansa ya kuma miqe yana ware hannun rigar suit shirt dinsa daya nannade,sannna ya juya yana dauko suit din yana qoqarin maidawa.
Suna hanya kadan kadan yana jin saddiq da musaddiq din suna hira abinsu jifa jifa.....yayin da shi kuma ya tattara nasa hankalin kan wayarsa yana rage saqonnin da bai samu dubawa ba.
A zahirin gaskiya ya gaji,yana kuma buqatar hutawa ne daga gangar jikinsa har ma qwaqwalwarsa,to amma ya sani.....a cikin matsalolin dake cunkushe cikin kansa,muddin zai zauna na second biyar shuru tunanukane zasu addabeshi,wanda yayi imanin zasufi jigatashi fiye da gajiyar da yakeji yanzu haka a jikinsa.
Kamar kowanne lokaci malam din bai taba karbar komai a hannunta ya eabawa daliban da kanshi ba,yau ma ita da manyan dalibansa ya bawa dama suka tattauna,ta kuma rarraba kudin da zata raba musun sannan aka tsimayi sauran wadanda basu kusa suka dawo aka soma hawa layin karbar tallafin.
Har qananun cikinsu bata tsame ba,saidai kowanne tayi kudin girma girma,adadin na qananu daban,na manyan daban.
Ita da rumasa'u suka fito zuwa rumfar gaban gidan malam din,rumasa'u na riqe da jakar tana miqo mata,ita kuma tana miqa musu. Duk wanda ya karba sai ya balbaleta da adduar data dinga sanyawa tana jin saukar wani irin sanyi cikin ranta,wannan ya qara mata qwarin gwiwa taci gaba da binsu da kudin daya bayan daya.
Kaman yadda ya saba a kowanne lokaci ya sanya mota uku cikin motocin dame tsaron lafiyarsa tsaiwa su kuma jira fitowarsa daga ainihin bakin titin unguwar,motoci hudu harda tasa suka fara gangarawa zuwa ainihin layin gidan.
Suna shiga yana ci gaba da duban tsari da yanayi da banbancin unguwanni da al'umma ke rayuwa a ciki. Unguwannin da suke buqatar tsari me yawa da kuma tallafi don samun daidaiton rayuwa.
Kusan dukkan guard's dinsa har yanzu suna mamakin yadda yake zuwa unguwar lokaci lokaci. Ko tsoron lafiyarsa baya yi baya kuma duba girman matsayin da Allah ya bashi?. Saidai a nashi bangaren malam din tamkar wani jigo ne a rayuwarsa.......ya zame masa fitila me haska masa duhu.....domin shine mutumin daya shayar dashi ilimin addinin da a yanzu haka ya zamewa rayuwarsa haske da kuma garkuwa.
Silalowar motocin da kuma nishin isowarsu wajen yadan dauki hankalin da yawa daga cikin almajiran. Saidai da yake daliban malam auwalu daban suke da sauran almajirai ba wanda yayi wani motsi na hayaniya ko fita daga tsari,saidai idanu da suke bin motocin dashi wanda ke qoqarin gyara parking a muhallin da suke ganin zasu iya tsaiwa. Idan ka duba da kyau fuskokin manyan cikinsu murmushi ya sake wadata,domin sun sani mutum daya ne tak me irin wadannan motocin sak....dake zuwa wajen malam,wanda duk ranar da yazo kuwa kakar kowa ta yanke saqa,duk da cewa qalilan daga cikinsu ne suka samu nasarar shaida fuskarsa.
"Bari hamma na fita na duba ko yana ciki" Musaddiq ya furta yana duban fuad da ko sanda motar ta tsaya bai daga kanshi ba,hankalinsa still yana kan waya
"Okay" Ya fada a hankali kaman wanda bayason yayi magana.
A nutse ya bude motar ya fiddo qafarsa dake cikin rufaffen takalmin kamfanin Hermes. Ya qarasa fitowa daga motar yana gyara hannun rigarsa sannan ya fara takawa a nutse yana dosar rumafar malam din daya daga cikin guard yana biye dashi.
Daga shigowar motocin har tsaiwarsu a wajen bata wani basu muhimmancin da zasu dauke hankalinta daga aikin da take ba,don Allah Allah take ta kammala ta wuce gida saboda yadda tunanin huda yaketa mata yawo saman kai abinda bata taba tsintar kanta a ciki ba kenan.
"Hamma malam fa idan ba da gaske akayi ba bazai koma sabon gida da makarantar daka gina masa ba" Sadiq da idanunshi kekan almajiran ya fada yana leqo kansa first set din da fuad ke zaune.
A nutse ya zare lumsasssun idonsa akan wayar yana waiwayawa gefansa ya kuma aza idanunsa a muhallin da yake kyautata zaton a kanshi Sadiq yake magana. Saidai kuma duk da tarin almajiran daketa miqa hannu suna karbar wata takarda idanunsa basu sauka a ko ina ba sai a saman fuskarta.
"Yanzu banda abun malam.....ga gini can a wadace,ga makarantar zamani amma yace sai yayi shawara?,har yanzu kuma bai gama shawarar ba?" Sadiq ya sake fada yana dariya qasa qasa,dariyar da bata samu isuwa ga kunnuwan fu'ad ba duk kuwa da cewa yana wajen.
Sosai ya zuba ma fuskartata idanu bawai don tayi masa kyau ko kuma taja hankalinsa ba......aah.....sai don tuna a muhallin daya soma ganin fuskar duk da ba wani kyakkyawan kallo yayi mata ba.
"Office din mikail......a ranar da incident din zai faru" Sashe mafi saurin harbawa cikin kwanyarsa ya bashi amsa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 83
"Exactly....." Ya furta har labbansa suna motsawa,yayin da wani qaqqarfan tunani ya darsu a ransa.
Bai dauke idanunsa daga sashen ba musamman ganin musaddiq ya doshi inda take kai tsaye......amma kuma kafin ya qarasa din ta juya tana takawa zuwa cikin gidan malam din,abinda ya sanya musaddiq da bai kula da fuskarta ba ya soma tambayar wanda yafi kowa girma a wajen kan ina malam?,kafin ma ya bashi amsa muryar malam din ta ruskeshi yana basu umarni su fara daura alwalar sallar magariba.
"She's a suspect" Ya fadi a hankali yana zare idanunsa daga kanta sanda ta kammala shigewa malam ya bayyana. A nutse ya waiwaya ga sadiq yana kallonsa.
"Kiramin jordan" Ya furta a nutse yana qoqarin bude side din da yake zaune. Baiyi wahalar komai ba ya janye dogon hannun rigarsa ya danna wani abu,cikin qasa da minti daya hotonsa tsaye jikin motar ya bayyana ta qaramin allon computer dake maqale a set din gaba fu'ad
"Ka fita ka cewa malam gani nan shigowa.....ka cewa jordan din ya shigo". Ya danyi mamaki kadan da hakan,amma bai damu ba ya amsa masa yana bude murfin motar sannan ya fice yana gayawa jordan saqon boss din nasu.
"come in" Yace ma qaqqarfan mutumin da yayi tsaye bakin motar cikin rusunawa.
Cikin jin nauyin hada mazauni daya da boss din nasa ya shigo. Sai fu'ad din ya bashi umarnin rufe motar. Yayi kaman yadda yace din yana maido dubansa ga fu'ad din yana satar kallonsa.
Duk yadda yakejin qarfi a ginannun tsokokin jikinsa a yanzu da yake zaune kusa da boss din nasa sai yaga ashe bai fishi da komai ba.
"Kayi noticing wata girl a cikin yaran can tana raba musu wani abu?" Yayi tambayar kanshi tsaye,don yasan mutum ne shi me tsananin kula da motsin kowa
"Yes sir" Ya gyada masa kai cikin qwarin gwiwa da confidence
"Good.......i want every single details of her.....but don't forget.....make it secretly"
"Done sir" Ya fadi a yanayinsa da muryarsa suna bawa fu'ad din tabbaci.
Tun daga fitarsa a motar ya soma aikinsa,tun tana daga cikin gidan malam din fitowarta da tafiyarta hankali kwance saboda tasan bata da wani issue da kowa a nan area din......hasalima ba wanda yasanta a yankin don haka take tafiyarta a tsanake.......ya riga yayi waya da duk wanda ya kamata,don haka qarqashin kulawarsa take,tun daga abun hawan data samu zuwa isarta gidansu.
Can qasan ran malam din yake mamakin dan dadewarsa wajensa a yau,duk da cewa ya maisheshi tamkar uba kaman yadda ya daukeshi d'a. Tun malam din yana tsoron asan cewa fitaccen mutum kuma attajiri irin muhammad fu'ad na zuwa wajensa har ya soma sakewa.
Duk zuwan da zaiyi din kowa yana tsaiwa a waje ne amma shi da Sadiq ko musaddiq ko farouq idan tare sukazo suna zama ne tare dashi.
Magariba dama ishai duka tare sukayi da malam din. Duka yana sane yana yi yana duba agogonshi bayan ya sanya musaddiq ya kashe wayarsa,tasa wayar kuwa dama shigowar kira yana bisa qa'ida ne so baida damuwa. Yadda zaman yaga ya miqa malam din yasa aka fito musu da tuwon dare daga cikin gidan. Yace a fito dashi dinne kawai saboda karamci irin nasa,bawai don yana sanya rai zasu iya ci ba. Saidai ga mamakinsa Sadiq da musaddiq din cin abinsu sukayi sosai,daidai lokacin shi kuma suke tattaunawarsu da fu'ad.
Kudin daya saba bayarwa malam ya rabawa mabuqata duka wata ya ajiye,ya bada na malam din wanda kamar ko yaushe sai yayi kaman bazai karba din,yakance
"Muhammadu......nikam bani da matsala ci sha sutura ko.muhalli,ina ganin a baiwa bayin Allah dake da tsananin buqata mana". Ko yaushe shi kuma yakan maimaitawa malam din.
"Koda kullum zaka rubuta adadin mutanen da idanunka suke gani suna da buqata ta aikemin dashi malam za'ayi musu komai kuma hakan bazai hana ayi maka ba......a duk sanda ka hadu da mabuqaci kada kayi shayi ko shakkar alqawarta masa taimako,tabbas za'ayi masa dukan abinda ka buqata". Ko yaushe ya fadi haka malam ka jinjina kai. Girma da kimar malam a idanunsa tana da dimbin yawa,ya taka rawa me yawa a rayuwarsa,ya kuma tallafeshi da abinda baida abinda shi din zai iya saka masa dashi.
Sai daya tabbatar tara na dare tana musu sallama sannan sukabar gidan malam din.
Sanyin Ac din dake kadawa cikin motar ya sake saka masa kasala tare da taso da gajiyar jikinsa,saidai shi kuma ba wannan bane a gabansa yanxu. Gaba daya hankalinsa ya karkata gason jin komai daya shafi yarinyar,yana ji a jikinsa kamar akwai wani abu a qasa,kamar akwai wani abu.
Ko sanda suka isa gida ma goma ta gota,saidai ya samu abba da anni zaune a falo da alama hira suke,duk da abban akwai takardu da yawa a gabansa yana rubuce rubuce.
"Jiya da yau dai duka ba zama.....yarona ya rantse sai ya zama mutumin arewa na farko daya bawa 'yan kasuwa da masu arziqin arewa sample na kishin yankinsa" Anni ta fada tana murmushi. Shima murmushi ya saki,a koda yaushe yana alfahari da anni da kalamanta da suka zama sune qarfinsa. Bata tsareshi da yawa ba haka shima abban suka sallameshi ya wuce sassansa.
Ta isa gidan bayan magariba da kadan,sanda tsakar gidan nasu ke cike da hada hadar ahalin gidan. Masu wankin uniform sunayi,masu zaman hira na zaune,masu kwashe tuwo da abincin dare kowa yana sabgar gabansa. Koda tayi sallama ba ta tabbatar babu wanda zai jita bare ya kalleta,idanma sun kalletan......zasu kalleta ne da mummunan kallon nan da tasan babu wanda ya isa ya wankeshi daga idanunsu sai randa ubangaji yaso,don haka ta zabi wucewa ciki salin alin ba tare data tankawa kowa ba,saidai duk da hakan bata tsira ba daga jiyo kalaman nan masu muni daga kunnuwan bibo
"Hala yau barikin batayi ribaba.....dawa kuma batayi nama ba.....naga fuskar ba fara'a bare walwala......."
"Ita bariki daman ai alalan gero ce......idan baka iya ba ta kwabe maka.......ta fara hangen wannan din inaji shi yasa ta soma yiwa 'yar uwar training......gashi an fara da fitar dare?" Yabi ta taya bibo din fada.
Wata mummunar faduwa gabanta yayi,jikinta ya dauki rawa da jin kalamansu na qarshe,ta sanya hannu tana dauke hawayen daya silmiyo mata sanda taga daada na dauke flask din abincinta tana wucewa dashi dakinta. Hakan ya tuna mata da rayuwar gidansu,duk da yawansu abinci baya daya daga cikin matsala ko damuwar rayuwarsu,abinci na daya daga cikin abinda muddin kai haifaffen jinin gidanne ko maqoci ko abokin huldar arziqi tabbas kafi qarfinsa!. Abinci me kyau bawai irin abincin da za'a ci ba kawai saboda kore yunwa ko babu yadda za'ayi,yau sai gashi abinci ya zama matsalar gidan ta farko!,abinci ya zama damuwar gidan.....abinci kuma ya zama abu mafi wahalar samu garesu haka abu mafi daraja da tsada a gurinsu.
Ji take kaman iska ke tafe da ita har ta sanya qafafunta cikin falon nasu
"Ina huda?" Ta jefawa nadra da haneefa tambaya wanda suke zaune qasan carfet kawai. Sun tasa litattafansu a gaba bayan gama sallar magaribarsu kenan da alama.
"Muna dawowa islamiyya ta ajiye jakarta ta fita" Nadra ta fadi da karyayyar murya tana tuna yadda ta daka mata tsawa sanda taga tana shirin fita din ta tambayeta
"Inda kika aikeni makira sarkin tambaya!" Daga haka ta zuba mata manyan idanunta tana kallonta har ya fice.
Ji tayi qafafunta kaman suna lanqwashewa don haka ta samu ta lallabo ta zauna kusa da haneefa da take kallonta da idanunta da tasha jin ana cewa irin nata ne sak,sai ta jawota jikinta tana duban nadra tare da qoqarin rarrashin zuciyarta
"Bata gaya muku ina taje ba?" Kai nadra ta girgiza
"Bata fada ba"
"La haula wala quwwata illa billa" Ta fada muryarta nadan rawa kadan. Cikin qanqanin lokaci zuciya ta fara sawwara mata abubuwa masu yawa akan huda. Ina huda ta sani?,ina zata je?. A iya saninta huda bata da wata qawa illa nadra da haneefa,bata da wani wajen zuwa sai inda ita ta kaisu,bata da wajen zama idan ba dakinsu zuwa tsakar gida da farfajiyar gidansu ba.....to ina huda ta tafi?.
Zame haneefa tayi daga jikinta ta miqe tana qoqarin saita kanta,ta wuce kitchen ta duba abinda suka dafa ta zuba musu
"Kuci bari na shiga toilet" Saita fice zuwa tsakar gidan nasu.
Dariya taji qasa qasa daga shiyyar da mutan gidan ke zaune,bata waiwaya ba haka batace komai ba,saidai jikinta ya bata tabbas da ita ake.
Da qyar ta saita kanta ta cire pad din jikinta ta sauya wata sannan ta fito. Tana saka qafarta waje tana ganin shigowar huda wadda ta zarce dakinsu kanta tsaye. Tayi namijin qoqari qwarai da gaske wajen saita kanta ko don idanun jama'ar dake wajen tabi bayan huda a nutse zuciyarta kaman zata fado daga qirjinta.
Sanda ta tabbatar sun isa falon dukkaninsu sai saitinta ya kwance gaba daya. Ta miqa hannu ta finciko huda dake qoqarin wucewa daki kai tsaye
"Dawo nan......daga ina kike?" Ta jefa mata tambayar a tsawace tana dubanta da kyawawan idanunta da suka qara girma a yau.
"Gid.....gidansu qawat...." Sai ta kasa qarasawa saboda tsoron daya kamata na ganin Sabreen ta daga hannu tabbacin lafiyayyen mari tayi nufin sauke mata.
Tsit dakin yayi,a hankali ta maida dubanta sassansu nadra,saitaga sunyi tsumu tsumu suna kallonsu. Wani abune ya daki zuciyarta ya kuma karyata,abinda ya sanyata ja da baya wannan ya baiwa huda damar shiga dakin da sauri sauri.
"Kuci abincinku ina zuwa.....babu abinda zai faru" Sabreen din ta fadi wani madaukakin tashin hankali yana saukarwa zuciyarta amma tana qoqarin tausar kanta,ta kuma taka da dan hanzari ta wuce dakin itama.
Hijabin uniform dinta take qoqarin zarewa,sumarsu me tsaho da sulbi ta gado ta kwance,daidai sannan sabreen din ta miqa hannu ta sake jawota.
Jikinta ta fara duddubawa,sannan ta sanya hancinta ta fara sansana jikinta,abinda ya sanya huda mutuwar tsaye zuciyarta tana wani irin bugawa tana bin sabreen din da idanu kawai ba tare da tasan ainihin ma'anar abinda takeyi ba. Bakinta ta kama ta matse tana duba harshenta,sanna takai hancinta tana shanshana labbanta.
Bataji sauyin komai ba daga gareta,amma yadda zuciyarta ke bugawa ya tabbatar mata lallai akwai alamun rashin gaskiya a tare da ita,sai ta sanya hannu ta tunkudeta,kai tsaye ta fada saman gadon tayi zaman 'yan bori,tayi taku biyi sabreen din ta tsaya a kanta gab da ita
"Ki gayamin daga inda kike tun muna mu biyu kafin duniya ta jimu!" Ta sake fada mata tana fidda idanunta da a yau suka qara girma saboda tashin hankali.
"Ni fa ba inda naje adda......gidansu qawata"
"Wacce qawar?,yaushe kika yita?,kuma a ina take?"
"A islamiyya muka hadu...." Ta fadi tana jawo qarfin gwiwa bayan ta tsinto wasu maganganu daga kalaman naseer da yake a matsayin bassam a wajenta.
Yadda tone din ta ya sauya farat daya yaja hankalin sabreen,saita gyara tsaiwarta
"Islamiyya?.....inane gidansu?,me yasa ni bansanta ba?" Tashin farko sai taji ranta ya baci,karon farko kuma a rayuwarta taji kaman yau yaa sabreen ta raina mata wayo
"To ai kowa ma yana da mutanen da yake mu'amala dasu,ba lallai sai uwa ko uba ko 'yan uwa sunsan da zamansa ba" Tayi maganar kai tsaye abinda ya zowa sabreen din a wata gigitacciyar ba zata
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 84
Dukkan wani motsi nata ya tsaya cak......cikin wani irin madaukakin mamaki take duban huda bugun zuciyarta yana canzawa da wani irin yanayi taji yana saukar mata na sanyin jiki tun daga saman kanta har qafafunta,wani irin sanyi jikinta yayi saidai duk da haka ta dawo da hayyacinta cikin jikinta
"Huda?......" Ta kira sunanta da sautin mamaki. A wannan karon sai hudan taji abun yadan mata nauyi,ta kasa hada idanu da sabreen din,ta juya tana son qarasa cire uniform dinta.
Kanta tsaye ta nufi gadon huda din,ta soma janye zanin gadon zuwa katifar tata. Sannu sannu a hankali ta soma birkice duk wani kaya na huda dake dakin,zuciyarta na raya mata akwai wani abu da huda kesha tabbas wanda shi ya canzata. Muddin kuwa hakan ta kasance batasan meye abu na gaba da zai faru tsakanin tata rayuwar data hudan ba.
Cikin abinda ta tsana mafi girma da muni shine shaye shaye,bata samu relief ba sai data tabbatar bata samu komai daya danganci maye daga fannin huda ba. Hudan da tayi tsaye kawai tana bin yayar tata da kallo. Wato a yadda ta yiwa dakin nasu a yau tayi imanin banda takai wayar an canza mata babba,kuma data shigo da ita tana jikinta a maqale babu abinda zai hanata ganin abinda take boyewar.
"Ki gyara dakin,idan kin shirya gayamin inda kikaje ki sameni a falo,idanma baki shirya ba duk daya" Ta bata umarni nakai tsaye tana takawa tana barin dakin. Qasan ranta ta riga ta gama yanke komai.....ta riga kuma ta gama yanke hukuncin da zata dauka akan huda din.
Har suka gama dukkan wani sabgarsu a falon ko leqowa batayi ba ballantana ta fito har ta sameta da wani batu,ko abinci bataga tazo ta diba ba. Wanna ya sake qona ran sabreen matuqa da gaske,ya kuma sake bata tabbacin eh lallai da walakin goro a miya.
Koda suka shiga dakin sanya nadreen da haneefa tayi suka kwanta,itama tabi sahunsu a nata gadon ba tare da ko tabi takan huda ba. Saidai a nata salon kwanciyar ta kwanta dinne bawai don tana da niyyar yin bacci ba,ta kwanta ne tana monitoring dukkan motsin hudan.
Har ta gama juye juyenta,ta fita falo sha biyu saura na dare,shigarta kitchen da zaman cin abincinta ta gama ta maida kwanon tana jinta.
Har zuciyarta tana son jin muryar bassam dinta.....amma wata zuciyar tana kwabarta,yau din bai kamata tayi waya dashi ba,don gaba daya jikinta da zuciyarta babu qwari.
Sha biyu na dare yana zaune cikin kebantaccen dakin nasa,gaban system da tarin cups na shayi da yake canzawa daga wannan zuwa wancan. Aiki yakeyi sosai,aikin kuma yana tafi masa yadda yakeso,don yana sake samun wasu bayanai da yakeso.
Wayarsa tayi qara alamun shigowar kira. Waya ce daya ware musamman saboda waya tsakaninsa da gurd dinsa musamman idan basa kusa ko basa tare. Jordan ya gani,sai ya dakata daga dukkan abinda yakeyi din ya daga wayar yana relaxing bayansa jikin kujerar da yake zaune akai din,don dama yana expecting kiransa daga wannan lokaci har zuwa asuba zuwa safiya.
"Barka da warhaka sir" Jordan ya fadi da hausarsa da bata gama tsaiwa tar ba
"Barka dai jordan......how far?"
"Fine sir.....duk wani information ya kammalu"
"Very good......" Ya fadi da nutsuwar nan tasa data sake qaruwa sakamakon bacci dakeson fara kamashi.
"Tell me jordan......"
"Immediately sir" Ya fada yana sake tattara hankalinsa akan boss din nashi.
Idanunshi a lumshe sanda jordan ke sakar mishi bayanai dalla dalla akan sabreen din. Bayanai ne na bincike da yayi a kanta ta hannun mutane daban daban da suke da jibi da Rayuwarta.
Ba abinda yake sauraro illa muryar jordan yana masa bayani dalla dalla har yakai qarshe.
"Good job jordan......na baka hutun gobe.....ka kwanta ka huta sosai.....but idan ina buqatar wani abu daban zan kiraka"
"As you wish sir" Ya fada cikin girmamawa.
Da wani irin cakudadden yanayi na ajiye wayar gefansa yana furzar da iska me dumi daga bakinsa. Ba abinda yafi riqewa saman kansa irin kalaman jordan na biyun qarshe
"A taqaice dai sir ana kyautata zaton KARUWA Ce ko kuma mayaudariyar maza......wadda maza da dama ke sonta suke kuma kashe mata kudade masu kauri,kuma daga qarshe abinda yake faruwa ba'a jimawa take rabuwa dasu......tana rayuwa ne ba uwa ba uba.....amma tsarin Rayuwarta da yadda takema kanta komai da 'yan uwanta.....koda d'a me uba da kuma tsananin gata sai haka......bata nemi komai ta rasa ba......sir......akwai wanda ya gaya min tana da hatsari.....tana da hatsari.....tana kuma da mabanbantan sunayen da ita kanta batasan adadinsu ba".
Ajiyar zuciya me nauyi ya sauke yana jin wani abu yana tokare masa a qirji. Ya miqe qafafunsa sosai tamkar zaiyi miqa yana jin wani irin ciwo a zuciyarsa. Qoqari yake ya sake tuno fuskarta ko zai iya banbance shekarunta da yayi imanin ba zasu wuce ashirin ba tsanani da daya.
Abinda yaqi jinij yaji ko ya gani kenan koda cikin labarai diya mace ta lalace har haka. A dukka qananun shekaru irin nata ta iya zama mace me hadari har haka?,har ta iua bada jikinta zuwa ga wasu mazan don ta mallaki abun duniya?,har ta iya yaudara da damfarar wawayen maza irin Mikhail?. Wannan kadai ya isa ya bashi tabbacin tabbas ita ta shirya ko ta tsara ko ta jagoranta ko kuma ta bada gudunmawar faruwar badaqalar cikin kamfaninsu.
"Ya Allah.....how?......diya mace da wannan aikin?,aikin fashi da makami fa kenan a miqaqqiyar hausa,fashi da makami na yanar gizo.
Shi a yanzun ma idan yace zai kamata yace ya kama wa?,ya gayawa duniya kamfaninsa na tuhumar mace da kitsa shiga na'urarsu kuma suka kwashe kudaden asusunsu?. Tabbas ya bari hakan ta faru ba komai bane ga kamfaninsu face zallar faduwa da kuma sake nunawa duniya rauninsu muraran. To amma idan ya qyaletan kenan taci bulus?.....jadda company ya zama marainar wayonta?.....jadda company ya zame mata abun wasa?. Ya kamata ya dauki mummunan hukunci a kanta,irin hukuncin da ko sunan jadda kadai taji zai gigitata ya dimautata ya kuma sanyata a fargaba....ambatar sunan kadai ya zamowa kwanyarta da kunnuwanta baraza.
Sai yaji gaba daya tunaninsa ya karkata kan fitar kudin kamfanin karo na biyu. Idan wannan ita ta aikata ya tabbatar ba zata sake dawowa ba a karo na biyu gudun kada a kama na'urarsu har a samu isa ga inda suke,tabbas wannan karon mikail shi ya aikata haka da kansa,don haka ya bude idanunsa yana sake jawo system dinsa. Yanaso ya sani,yanason yayi bincike ta yadda komai zai tafi masa a daidai.
Cikin qasa da awa daya komai ya fito masa yadda yakeso. Ainihin wanda kudin suka koma account nashi daga account din wanda aka bawa ajiyar sunanshi ya fito baro baro da taimakon shigabannin bankunan da dukka suke amfani dashi,wanda yakan nemesu idan buqata irin haka ta taso
"Rufa'i ahmad mu'azzam" Ya mamaita sunan yana zuba masa idanu.
"Wayeshi?" Amsar da bashi da ita,babu kuma me bayar da ita sai mikail,kasantuwar hakan kuwa ya zama tilas a gobe mikail ya miqo kansa ko kuma shi yasa a kawo masa shi.
Kadan yadan daki table din,sannan ya sake jawo wayar gefansa ba tare da duba da yadda dare yayi ba. Duk da daren hakan bai hana a daga wayar ba da bugu daya tak.
"Barka da dare sir" Aka furta da muryar dake nuna kiranne ya tasheshi daga bacci
"Barka abdus_samad....i have a work for you"
"Okay sir...." Ya fada yana watsakewa daga baccin nasa.
"Zan tura maka through email then sai muyi magana.....but ina buqatar bayanan as soon as possible"
"Yes sir" Ya furta cikin matuqar bada girma.
Kiran ya katse don duk wani abu me muhimmanci ba kasafai ya fiya magananshi ta waya ba,duk da layinsa yana da tsaro sosai......to amma ya sani a kowanne motsi akwai maqiya abokan gaba da abokan burmi.
Komai ya tura masa,sai a sannan yaji idanunsa sun fara yaji yaji alamun suna da buqatar bacci,dole ya tattare komai ya tafi ya kwanta don yana da buqatar ya qarasa hada abinda dukka ya rage masa a gobe tunda jumaa bai fiya fita office ba,koda ya fitan baya dadewa sosai,ga kuma alqawarin tafiya abuja da ya yiwa farouq. Bayason ya sake karya alqawarin,duk da yasan farouq zai fahimceshi zai kuma bashi uzuri fiye da yadda yake buqata ma.
A wannan yanayin kawai yaji ya kamata ya fara amfani da private jet dinsa,sai ya lalubi me haqqin kula da zirga zirgarsa ya tura masa bayanai sannan ya ajiye wayar yana nufar qofa bayan ya kashe komai ya kuma kwashe komai da yake da buqatar fita dashi.
*******Duk wani motsi nata saman idanun sabreen din take yinsa. Tana sake karantar duk wani yanayi na huda din. Zuciyarta na sake tsinkewa yana kuma saukar mata da fargaba hakan. A duk sanda zatonta da zarginta ya bata akwai wani ne a rayuwar huda din?. Abu daya dake sake gigita tunaninta da sanyata jin ya zama tilas ta nuna nata salon maganar nan da ake cewa duk wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 85
Ba wata kalma data sake hadasu da ita,har suka kammala shirin makaranta,ta dauki jakarta kaman kullum,ta kuma fidda kudin transport dana break. Wannan karon nadra ta miqawa a maimakon huda
"Ki kula sosai nadra......ana tashi kada ku tsaya ko ina"
"to adda" Ta amsa mata tana kama hannun haneefa suka fara takawa zasu fice.
"Nifa?" Huda da ta kasa fahimtar abinda sabreen din tayi ta tambayeta. Kai ta daga a nutse ta watsa mata kallo. Sai ta janye idonta daga kallon da takewa sabreen din saboda yadda idanun sabreen sukafi nata kaifi.
"Na dakatar da zuwanki makaranta" Amsar data bata kenan ta miqe,amsar kuma data girgiza huda din.
Ta dakatar da zuwanta makaranta kamar yaaya?. Dakatar da ita daga zuwa makaranta fa kenan yana nufin yankewar ganinta da bassam?. Idan haka ta kasance kenan sunyi bankwana da bassam?,saidai ta zauna ta zuba idanu tana ci gaba da rayuwa cikin wannan quntataccen gidan nasu da babu farinciki ko guda daya a cikinsa?.
Bata sake bi ta kanta ba,dole kuma data gaji da tunanin taja qafarta tana komawa cikin dakin,yayin da sabreen taci gaba da kai kawo tsakanin falon da dakin,tana shirya zata kasance da huda a dakin tsahon wuni da kwanakin da zasu biyo baya. Ta tabbatar idan ta lazimci hakan dole koma meye huda take boyewa ya fito fili.
Tayi juyi tayi tayi juyi har batasan iyaka ba. A duka hukuncin abinda yafi damunta shine yanke mata qofar fita. Fitar da itace hanya guda daya da zata bata damar samun bassam ta kuma shaida masa sabon dokan da adda sabreen din ta kafa mata. Ta yita zuba ido taga ko zata fita?,saidai yau qiyau miyau,banda toilet data fita tayi wanka ta dawo ba inda taje,haka suka wuni tana sabgoginta don ko tayin abinci batayi mata ba,sai data gaji don kanta tana rara gefe ta fada kitchen din ta diba taci ta koma taci gaba da kwanciyarta.
Ko da akayi sallar isha'i tana jiyosu a parlor suna assignment da sauran bitocin karatunsu kaman yadda suka saba. Ba wanda yabi ta kanta a tsakanin su ukun. Gaba daya dakin dama gidan ya sake gundurarta ya kuma fice mata a kai. To wai shin ita adda sabreen dakeyi mata haka?,ita waye ya takurata haka?,waye ya dameta haka?,kullum Allah shike da kullum sai ta sanya qafa ta fita waye ya taba dakatar da ita ballanta ya sanya mata dokar fita.
Miqewa tayi ta zauna bakin gadon nasu tana jan qaramin tsakin baqinciki. Tana masifar son gadonta da jin dadin kwanciya akai,amma yau gaba daya sai taji ta tsaneshi ya kuma fice mata a kai.
Wayarta dake haske ta jawo ta buda tana dubawa. Wayar na cikin personal wayoyinta da ba kasafai take bari saqo ko kira a ciki ya wuceta ba.
"Kina da tafiya on Saturday da mushkur......ina fata baki manta ba?" Saqon da jib ya tura mata kenan.
Yatsunta ta cusa cikin sumarta tana yamutsawa kadan kadan. Har cikin jininta taji batason tafiyar,komai kuma ya fice mata a kai,to amma batasan dalilin da ya sanya wani sashe na zuciyarta ke zugata yana gaya mata BAI KAMATA TA BARI MASHKUR YACI BULUS BA,KODA DAGA KAN MASHKUR TA RUFE QOFA YA KAMATA YA DANDANI DACIN QWACE ABU DAGA HANNUN ME SHI.
Idanunta ta juya ta kalli sashen dasu nadra ke zaune. A irin wannan yanayin ma da take qoqarin fuskantar inda rayuwar huda ke neman dosa,sam sam bata qaunar tayi nesa da kowannensu don sanya ido akan motsinsu
"Ko ta buqaci friday?,gajeriyar rana ce......sannan kuma tana da tabbacin zai wahala ta rasa ticket din juyowa a ranar" Tayi zancan cikin ranta,don haka ta soma rubuta tex tana turawa kowa tsakanin mashkur da jib da zai kula da komai.
Kamar jira akeyi ta kammala muryar ta mamaye ilahirin tsakar gidan nasu. Da wannan madaukakin sautin nasa da babu komai ciki face takura wulaqanci da kuma saukar azal akan duk wanda ta ratso dashi.
"Yau kuma akan waye da waye ta fada?" Ta fada qasan ranta,don tasan wajibi sunanta a sahun farko. Bai taba shigowa gidan ya fita salin alin ba tare daya takalo wani abu da ita ba,wannan ya sanya ko yaushe take shiryawa zuwansa da ko wanne irin yanayi ma zayazo dashi.
"Kowa da kowa ya fito,maza da mata,yara da manya,yau dai Allah yayi arziqin me arziqi ya dawo......rabon bawa da arziqi mutuwa......Allah ya lamuncemin nima......ku futo yau arziqin rufa'i ya dawo,wanda yayi biyayya aci dashi,wanda kuma ya bijire saidai yaga ana ci" Ya qarasa maganar yana bin dakunan da qofofinsu suke a rufe yana bubbugawa.
A nutse ta maida idanunta kan su nadra da suma ita suke kallo. Tana iya hangen wani boyayyen murmushi akan fuskar nadra din,da alama idan so samu ne tanason fita ta ganewa idanunta kamar yadda ya gayyaci kowa ta kuma fara jin alamun suna fita din,don muryar bibo har nan inda suke muryarta zaqwai tana karadi. Batasan me yasa duk gidan nadra tafi kowa maidashi kaman kakanta ba. Ada muguj balain tsoronsa sukeyi,amma yanzu kwata kwata bata tsoronsa. Duk sanda ta kwasheshi idan yana tambotsansa ya dinga zaginta kenan amma ita ko a jikinta,hasalima dariya take binsa da ita,yayi dukan yayi dukan sabreen tayi fadan amma ko a hancin takalminta
"Kada wanda ya motsa,ku gama aikin da yake gabanku" Ta dan hade rai tana fada. Idanunsu suka maida kan litattafansu suna ci gaba da aikinsu,saidai daga ita harsu kunnuwansu yana tsakar gidan suna tsintar wasu daga kalaman kawun.
A qalla ya kusa mintuna arbain da shigowar gidan kafin suji an banko qofar dakinsu.
"Barin hali sai mutuwa,miskili kafi mahaukaci ban haushi....halin ne ya motsa ko baqinciki ake da komawata mawadaci?" Ya qarasa maganar sanda yake sako jikinsa cikin falon yasha shadda dinkin babbar riga da 'yar ciki yanata bazata.
"Ko daya kawu......ina maka murna.....amma Allah dai yasa ba daga aikin da abban ya hana bane...." Tayi masa shaguben data tabbatar kaf jama'ar gidan ba wanda ya isa ya gaya masa hakan,wasu saboda tsoronsa wasu kuma saboda kwadayin abun duniya.
"Sannu ja'ira maras kunya.....ke harni zaki gayawa haka?,yo dani dake waye zaiwa wani gori?,Allah na tuba ba har gwara nawa kudin ba gwagwarmaya da fargaba nasha na kuma zuba nawa jarin kadan suka jawomin masu yawa?,ke nawa kika zuba kike samun naki kudin?" Ya fada cikin bambamin daya sanua huda dake daki kwance yin bakam tana jinsu,maganar kawun kuma ta sake tsaye mata a rai tare da sake jin wani baqon yanayi akan sabreen din da yafi kama da haushi haushi da son shinfida tata rayuwar......ita da aure ma zatayi?.
A hankali ta sauke idanunta zuwa wayar hannunta,maganganun kawun suna mata wani irin daci cikin zuciya har zuwa saman harshenta. Ba wannan bane karon farko daya jefeta da magana irin wannan ba muddin zata sako masa zancan caca.....amma wannan din yayi mata zafi ne saboda ya ambata tsakanin su nadra da huda da taketa qoqarin gano bakin zaren matsalarta.
"Kome meye dai sama'ila ya shallake......ba kuma zai sake zuwa tambayar komai a hannun kowa ba.....kuma daga yau har na mutu sunana mawadaci.....munyi hannun riga da talauci" Ya qarasa maganar yana wara hannayensa kaman me jiran wani yazo ya rungumeshi.
Sai daya gaji ya sauke sannan ya gyara zamansa yana sake kallonta
"Yauwa......batun kudadenki.....zuwa nayi muyi lissafin abinda kk taba bani na rage.....don bazan iya biya duka ba domin kuwa tattalin dukiya akeyi yanzu......yauwa". Badon yanayin daya jefa zuciyarta ba tabbas murmushi ne zai qwace mata,amma a yanzun sai kawai ta dubeshi ta dauke kai
"Bana buqatar komai a ciki.....hasalima dama kyauta na baka ba bashi ba" . Washe baki ya fara yi yana shafa habarsa
"Aah......kaga farar diya irin albarka.....diyar da babu kamarta kaf haife haifen da ahmadu yakeyi baiyi kamar taki ba har yabar duniya.....Allah dai yashi miki albarka" Ya fada yana sake sakin dariya.
"To ni zan wuce......sai kunzo ganin hamshaqiyar fada ta tarewa nan kusa da kuma qarin auren mata ta biyu". Kadan ta dubeshi,saita kasa cewa dashi komai,har ya juya ya fice yanata sakin qarin bayani.
Hannu ta sanya ta dafe goshinta kadan,abubuwa da dama suna mata kai kawo saman zuciyarta. Kwata kwata DUNIYARTA bata jinta daidai bata kuma kallonta daidai da duniya kowa. Akwai abubuwa da yawa da takejin suna ba daidai ba cikin rayuwarta......WAI SAI YAUSHE KOMAI ZAI DAIDAITA?.
_Tambayar data yiwa kanta kenan da bata da amsarta,wadda batasan wannan din shine MAFARI na komai ba_
*******K'arfe goma na safe ne sanda yake takawa cikin farfajiyar gidan nasu. Sanye cikin farin lallausan yadi daga lallausar auduga mafi tsada da daraja.
Fari ne qal yadin maras nauyi dake iya bayyana shatin fara qal din vest din jikinsa sama sama. Kusan komai da yayi amfani dashi a yau din fari ne,tun daga sutura takalmi da agogon fata me tsada dake daure a tsintsiyar hannunsa. A irin wannan rana ma ta juma'a motor din hawansa yakan canza zuwa fara duka don sabunta sunnar ta'ammali da farin abu.
Hularsa tana hannun me sunan malam dake tsaye daga gefe bayan ya karbi news paper din daya kammala dubawa. Ameh ya sallama daya biyoshi da tray din teen da zaitun da kuma jan inibi da bai zauna yaci ba,ya juya yana duban me sunan malam
"Ka shiryamin zama da shugaban gidan jaridu a gobe.....don yau din zamuje abuja.....but zuwa yammaci zamu juyo"
"Okay sir" Me sunan malam ya furta,sai fu'ad din ya sanya hannu ya karbi hular ya juya yana nufar qofa,abinda ya sanya duka guards dinsa tsaiwa don sunsan inda zashi,mutum biyun daya saba tafiya dasu sukabi bayansa.
Dab da zai fice a gate din farko yaji tana qwala kiran sunansa da shagwabar na tata
"Hamma......hamma na". Tun kafin ya waiwayo murmushi ya subuce masa duk da bai shiryawa hakan ba. Yasan zaisha qorafi saboda haduwa da tayi wahala a tsakaninsu a kwanan nan.
Barin hali inji hausawa sai mutuwa,tana isowa taja tunga kuwa tana tura baki gaba
"Hamma.....kace kada na yarda da abinda BB farouq ya fada......kuma ni Allah alamun nake gani". Wani lafiyayyen murmushi da ba kasafai ake katarin ganinsa saman fuskarsa ba ya saki yana juya fuskarsa dama da hagu kafin ya tsaida dubansa saman fuskarta.
"Amneeen hamma amneen anni......zaki yarda magauta su rabamu?" Kai ta girgiza da sauri tana sake fuskarta qasan ranta kuma tana fata inama saddiq yana kusa yaji yadda hamma yake ji da ita.
"Kwana biyun nan school ya saki gaba.....nima duka aikace aikace sun tasomin......ko bakison mu bude company n jewelry sample din farko da zamu fara fiddawa ya zama naki......kinsan sunan da zamu bawa brand din?" Kai ta sake girgizawa cikin tsananin jin dadi
"To sai kin kawo cin hanci zan gaya miki" Yayi maganar yana juyawa tare da ci gaba da tafiya.
Da hanzari ta tattaka ta cimmasa sukaci gaba da tafiya tare
"Please hammana.....ka gayamin cin hancin me kakeso?,kome kakeso hamma zan bayar"
"No....ki canka da kanki kawai ki bada din sai na gaya miki" Shuru tayi tana zurfafa nazarinta na abinda ya dace ta bashin,dab da zasu fice a gidan tace masa
"Yauwa.....hamma........zanyi maka mata ka huta da gorin yaa farouq akan kaqi nemo mata......na baka friend dita nasreen...." Dan rage speed na tafiyanshi yayi ya waiwayo yana jefa mata harara da fararen idanunsa.
Ya yarda autanci da kuma quruciya suna damun amna din da gasken gaske,da alama fa da gaske take,don daga yadda tayi masa maganar tana zumudi tare da jij ta masa bajinta kadai zai gaya maka iya gaskiyarta kenan.
"Wannan ba cin hanci bane......saidai ma ki jawo komawa ta biyu da za'a bawa product din" Hannu ta sanya tana rufe bakinta gami da zaro ido. Sai yanzu ta gane tayi wautar,ta tuna sunanshi da farouq ke gaya masa,ta kuma tuna shi lamarin yin budurwa ko zancan aure abune da bata taba gani ya zauna ya bashi muhimmanci ba.
Kunnenta ta kama daidai sanda suke isa qofar gidan wanda sam bata ma kula da gidan da suke nufa din ba saboda yadda hankalinta ya dauku
"Am sorry hamma.....please,wallahi idan ka fasa yaa saddiq zaiyimin dariya".
"Ki canza wani abun.......but this" Sai ya girgiza mata kai yana maida dubansa ga muhallin malam Sa'adu wanda bai ganshi wajen ba da alama ko ya zaga ne.
Tun daga shigowarsu gidan har takowarsu farfajiyar gidan idanunta yana bisa kansu. A yadda tasan hali da dabi'arsa ya akayi yarinyar ta samu sakewarsa har irin haka?,anya abinda take tunani kowanne dare kuwa bazai afku ba?.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 86
Ita kuwa ta yaya zata bari wani abu ya hada zuri'arta data hajiya amina?. Muddin da rai da ruhi da kuma numfashi a gangar jikinta.... Koda zata rasa komai data mallaka.......koda shine abu na qarshe da zata aiwatar cikin rayuwarta ba zata taba bari wannan tunanin ya wanzu a kwanyar kowa bama bare akai ga haifar tunanin a zahiri.
Labulenta ta saki zuciyarta na mata wani irin suya. Kwanaki biyu kenan suna sanyata yin asarar komai data shirya domin su. Yaune cikar kwanakin da bokan ya diba mata,muddin a yau ma nasara ta qwace mata to lallai zancan bokan ya tabbata na cewa aikin aiki ne......muddin a yau bata samu yadda takeso ba batajin gobe warhaka zata kasance a bigiren da take tsaye akai a yanzu......dole ta tafi plan B da zafi zafinta kuwa.
"Zuwaira.......maza leqa ki gaya masa ya qaraso ciki amma shi kadai......bana ko qaunar kallon fuskar yarinyar ballantana gangar jikinta ya shigomin cikin gida".
Sosai zuwaira taji nauyin aiken saboda ba qaramin kwarjini fu'ad din yakeyi mata ba,amma ba zata iya musa umarnin uwar dakin nata ba.
Da bismillah a bakinsa yake shirin sanya qafarsa a step na farko da zai sadaka da qofar falon zuwaira ta fito. Kai ya daga ya kalleta a nutse ganin kamar an jehota,sai tayi qas da kanta cikin tsananin qanqan da kai ba tare data iya hada ido dashi ba tace
"Maamah tace ka qaraso ciki.....amma so samu tanason ganawa da kaine kai kadai". A nutse ya waiwaya ya dubi amna,suka hada ido sai ya zare idonsa daga kanta,ya miqa mata hularsa yana cewa
"Riqemin yanzu zan fito" Bata musa ba ta sanya hannu ta karba,ta koma daga gefe ta zauna kawai jikinta a sanyaye,don inda ya barta gida zata koma,sai yanzu ta tuna gidan waye ta biyoshi?. Matar da totally ita tsoro take bata tun ranar data shigo gidansu ta kuma ga abinda tayi musu.
Bai fasa duka addu'anshi ba kafin ya sanya qafarsa cikin matuqar kula da takatsantsan. Tana zaune saman sofa qafarta daya saman daya tana kadata a hankali. Ciki ciki ta amsa masa sallamar ba tare data masa wani dogon kallo ba. Ya qarasa ya tsugunna cikin girmamawa yana fadin
"Barka da safiya.....kin tashi lpy?"
"Koma ka zauna muhammadu" Ta furta kai tsaye wanda baice komai ba ya miqe din ya koma ya zauna sosai.
"Wacece mahaifiyarka ne muhammadu?" Tayi masa tambayar da wani sauti dake cike da izza da kuma bacin rai. Kanshi ya daga ya kalleta suka hada idanu,ta tsareshi da ido sosai da kuma tarin abubuwa daya gansu kwance cikin idanun nata.
"Kece" Ya amsa mata a gajarce.
"To amma banga alama ba.......banga alamar hakan ba......yanzu ace samuwar farincikina daga gareku sai ya gagara?,yanzu ace samun kulawa da danuwarku a kaina sai ya zamemin aiki?" Ta jefa masa tambayar da ba abinda tayi tasiri a kai sai tuna masa da baya da tayi. Ta tuna masa sanda suke da tsananin buqatarta a daidai wannan lokacin ta tattara hankalinta zuwa ga wani waje daban. Ya tuna tun shekarunsa basu kai ya koyi wasu abubuwa masu yawa harda ma wadanda sukafi qarfinsa saboda rashin samun kulawarta. Ya tuna yadda yake kasa yiwa mahaifinsa dake jiyya abubuwa da yawa saboda bashi da qarfin da zai iya dagashi zuwa toilet da sauransu,saidai su zauna shi kuka shima kuka. Sau tari maganganunta da lafuzzanta sunfi masa kama da na mutanen da idonsu ya rufe......mutanen da buqatar gabansu kawai suka sanya a gaba,mutanen da ba ruwansu da damuwar kowa sai tasu......mutanen da ba wani burbushi na nadama a tare dasu ballantana dana sani.
"Kiya haquri" Ya jefeta da kalmar da yakejin iya ita kadai kawai zai iya furta mata don bashi da wani sauran abun fada.
Sake zube masa idanunta tayi tana sake jaddada zallar miskilanci da taurin fu'ad din. Ba wani alamun sarewa ko saukowa a tare dashi?,tamkar ma an sanya fetur da ashana an qone dukkan wata qauna ta mahaifiya dake zuciyar kowanne d'a. Anya ba zancan hajja harira bane akan hanya da take hasashen hadda farraqu hajiya ameena ta sanya akayi musu?.
"Zanje abuja yau din.....nace bari na sanar miki,sai mun dawo" Ya furta bawai don yana sanya ran zata masa addu'a ko wani abu daya dace ba,don yana kaiwa qarshe ya miqe yana gyara hannun rigarsa.
Dan runtse idonta kadan tayi tana hasashen yau dinma kenan babu nasara?. Da qyar ta iya controlling kanta da fadin
"Sai ka dawo" Duk kuwa da tarin tambayoyin da takeson masa akan me zaije yi abuja?,yaushe zai dawo?.
Binsa tayi da kallo har ya fice daga falon,taja wani mataccen numfashi idanunta na qanqancewa saboda bacin rai.....dole suje plan B bata kuma fatan su isa plan C don zaifi kowanne mataki wahala a gareta dasu gaba daya
"Yaro baisan wuta ba sai ya taka.......yaro man kaza......idan kasan wata bakasan wata ba" Dukka ta furta a sarari tana daukan wayarta gami da kiran hajja harira.
Cikin wani iri ya dawo cikin gidan. Saidai yayi qoqarin daidaita yanayinsa lokacin daya isa parlor din anni.
Can babban dining area din dake parlor din ya samesu saman dining. Anni abba da farouq suna breakfast,yaja kujera kusa da anni ya zauna yana gaida abba da basu samu haduwa ba sai sannan.
"Abba.....nace ya kamata ace tare muka fara hawa jet dinnan". Dan murmushi ya saki yana ciro tissue cikin tissue box.
"Nikam wannan jumaar a kibiya zanyita me babban suna......indai muna da rai ai za'a yita hawa ko don zuwa ibada qasa me tsarki.......yanzu kam ku wuce sabgar gabanku.....saidai kads ku manta da addu'a,Allah yasa a shiga a sa'a,ya kauda dukka abunqi"
"Allah yasa a fara hawa cikin sa'a,ubangiji yasa rai aka yiwa" Anni itama ta furta tana murmushi. Har qasan ranta tana jin dadi gami da jin alfaharin kasancewarta uwar goyo a gareshi. Koda muhammad bai kasance me dukiya da arziqi kaman haka ba.....shi din abun alfahari ne ga dukka uwa me hankali......yana da wasu nagartattu kuma kebantattun halaye na daban da ba kowanne dan adam yake samun baiwar mallakarsu ba.
Da dukka zuciya da idanu ta takawa hasken idaniyar tata har zuwa sashen da kowannensu zai hau mota tana rakasu da addu'o'i na neman kariyar ubangiji da kuma tsarinsa. Abban yau sunyi kibiya shi da musaddiq,wanda dama kusan kowanne qarshen wata ko sati idan ya samu chance acan yake sallar juma'arshi,hakanan yakan tafi musu da tarin alkhairai daga arziqin da Allah ya wadatashi dashi bayan wasu daga cikin 'yan uwan da suke zaune a gidan. Wannan din wata dabi'a tasa ce dake qara masa farinjini da soyayya wajen al'ummar garin,domin kuwa alkhairinsa ba wai iya ga 'yan uwansa kadai ya tsaya ba......ya kewaye kowa da kowa.
A saman idanunta dukka motocinsu suka tashi,sai gidan ya rage daga ma'aikata sai ita sai musaddiq.......sai mutanen dake can boys quarter da ba kasafai suke iya jiyo motsin abinda ke faruwa cikin ainihin gidan ba ko kuma su aji nasu.
Idanunsa lumshe cikin jirgin,sanda yake lulawa dasu sararin subhana daga abujar birnin tarayya zuwa kanon dabo. Abujan da duka duka awa biyar sukayi cikinta suka fito. Acan sukayi sallar jumaa cikin centra mosque abuja,daga nan suka wuce unguwarsu fanna.
Rashin sabo da wannan sabgar ya sanya mintuna talatin kawai yayi gidan ya cewa farouq zan dan kama masauki na wucin gadi da yafi kusa da airport.......zai tura masa location din sai ya sameshi a can su wuce.
Shigarsa masaukin yayi arba da abinda ya sake tsuke tunaninsa ya kuma sake dora masa mamaki me azabar nauyi......ya shiga daidai sanda mashkur ne gangarowa daga sama riqe da wayarsa a mugun gigice yana cigiyar hotonta daya buda cikin wayarsa. Hoton da yakebin duk wanda ya gani da tambayar
"Don Allah kaga wannan?,yanzun nan ta sauko daga dakina fa.......ta yasheni ta kwashemin komai daga accounts dina guda biyun". Da irin wannan bayanan ya tareshi sanda yake yunqurin kiran elevator ya haura dashi zuwa sama bayan yabar guards dinsa guda cikin reception din.
Duba daya tak ya yiwa hoton ya dauke idanunsa a hankali ya maida fuskar mashkur da tayi wani irin hautsinewa.....da alana ta zare masa kudi masu yawan da tsaf zai iya taba rayuwarshi. Wacce irin hatsabibiyar yarinya ce wannan?,fu'ad ya yiwa Kansa da kansa tambaya sanda elevator din ya qaraso ya bude ya soma shiga. Har a sannan yana jin muryar mashkur dake bulayin neman wanda ya ganta.
Lumshe idanunsa yayi yana jin wani mummunan bacin rai yana saukar masa. Yana buqatar qarin information a kanta abinda ya raya kenan a ransa,ya fiddo wayarsa yana neman Jordan,sukayi maganganun da zasuyi,dab da zai ajiye wayar kuma kiran abdus_samad ya shigo masa.
Dukkan wasu bayanai ya karanto masa akan rufai ahmad mu'azzam.
"Caca" Shine alaqar data hadasu da mikail?,ta yaya zai zama mutumin banza yana zaune kudinsa ya tafi ta qazantacciyar hanya irin caca?.
"Thanks for your effort" Ya amsa masa yana gintse kiran. Still yana shiga dakin daya kama din kiran saddiq ya shigo masa
"Hamma......mikail keta neman haduwa dakai......" Idonsa yadan lumshe kadan kana ya bude kaman yadda ya saba a duk sanda ranshi ya baci yake kuma qoqarin hadiyewa
"Ya samawa kansa mafita.....koda bai kawo kanshi ba tabbas zan sanya a kawomin shi.......bani da time na ganinsa yanzu......sai zuwa Monday......ka tuntubi Easter kan investigation da na saka suyi cikin company"
"Itama tayi dropping min massage.....tace in sha Allah zuwa Monday din komai zai kammala"
"Alright" Ya amsa a taqaice kanshi yana sake shiga rudani.
Wannan din shine abinda ya zurfafa tunaninsa cikin jirgin,har sai da farouq ya magantu
"Wani abu ya sake faruwa ne?" Idanunshin da suka sauya launi ya bude a hankali sannan ya girgiza kai
"Nothing.....kawai dai kaman akwai abubuwan da nake ganin ba haka ya kamata su tafi ba.....but everything will be fine". Kai farouq ya kada masa yana dubansa da kyau
"Whenever you need assistance........kada ka manta farouq na side dinka.....am ready to be a good partner". Dan qaramin murmushi ya sakar masa yana gyada kai
"Na sani tuntuni".
Tun kafin sabreen tayi nisa da gida ta zura hijabinta zuwa gurin daya gaya mata ta duba zaya ajjiye mata sabuwar waya torch. Yadda ya kwatanta matan haka ta sameta a wajen,ta dauketa cike da murnar zataji muryar da tayi kewa qwarai ta wuce zuwa gida.
Murmushi ya saki bayan informers dinsa dake wajen ba dare ba rana sun shaida masa abinda ya faru
"Yadda zaki bare sabuwar wayar nan yarinya haka zan bareki nan da kwanaki uku kacal masu zuwa" Yayi maganar cikin shauqi da wassafa ta yadda a ranar zaici karensa babu babbaka,ya dauki tiyo dake maqale da bututun tukunyar shisha ya zuqi hayaqin har cikinsa ya fesar,sannan ya kalli matashin dake gefansa.
"Aikinka na yau tunda ta dauki wayar zai fara da tura mata zazzafan saqo da zai nuna asalin kewa da shiga rudani da rashin jin muryarta"
"An gama oga" Ya fada yana bude wayar ya fara abinda aka umarceshi,shine kuma kwangilar daya dauko takanas zai yiwa naseer din.
Jikinta har rawa yake sanda ta kunna wayar saqon ya shigo. Tana gama karantawa taji idanunta sun cika da qwalla,tausayinsa ya cikata.
"Allah sarki bassam.....bazan sake yarda adda sabreen tayi silar yin nesa dani ba" Tayi maganar yana yunqurin kiransa saiga nasa kiran ya shigo.
A yadda ya marabceta a yau din sai da zuciyarta tayi narkewa da qwalla ta fita.
"Tun daga ranar bani da lafiya huda.....fargabata na mutu ba tare dana cika muradan zuciyarmu ba....baqincikina kuma sai na jima a kushewata qilan kafin labarin mutuwata ya riskeki....."
"Allah ya kiyaye.....in sha Allah ba zaka mutu ba" Ta fada muryarta tana rawa tana tuna yadda ta rasa abbanta da umminta,yanzu kuma sai ace shi?.
"Ganinki ne kawai zai sanya na warke huda.....ki taimkeni muddin kinaso na farfado naci gaba da rayuwa kizo na ganki"
"Bansan gidanku ba.....bansan inda zan ganka ba"
"Indai zakizo din huda zan tura miki da adress....ki taimakeni kizo......amma karki takura kanki daga nan har zuwa litinin,har sai kin gamsu da kanki na cancanci kizo din na ganki.....".
Ko kusa ko alama bata ji saukar damuwa saman zuciyarta akan mashur ba,wanda ta tabbatar ta masa gagarumar barnar da zaiyi wahala ya maida gurbinta.
Wani tabbataccen labari data samu a daren jiya akan mashkur shi daya ya qara mata qwarin gwiwa da jin cewa ya cancanci ta rabashi da komai da yake sanya shi jin xai iya shiga ko bata rayuwar dukka diya macen da yaso a sanda yaso.
Da confidence dinta take takowa zuwa cikin gidan nasu. Kamar ko yaushe bata damu d kallon me kallo ba......bata damu da hasashen me hasashe ba......hakanan bata damu da zunden me zunde ba,ta keta a hankali har ta isa qofar dakin nasu da tayi tsammanin samunshi a bude saboda lokacin lokaci ne da tasan suna makaranta a irinsa.
Da mamaki hadi da wata cakudaddiyar fargaba ta murxa qofar ta tura ta bude tana shigewa,saita samu kanta da takawa a hankali har zuwa qarshen falon.
Ba kowa,kuma wajen yana tsaftace kaman kullum,don haka ta juya tana sanya kanta cikin dakin tana mamakin waye yake magana haka kaman masu gulma?.
"Nayi maka alqawarin xuwa ka ganni muddin ba'a wata qasa kake ba.....zanzo har inda kake don ka tabbatar da ingancin son da nake maka!". Qididdigaggun jimlolin da suka zamewa sabreen tamkar saukar aradu a tsakiyar kanta.
Wuta ce gaba daya taji ta dauke mata sanda take iya hasken waya a kunne huda.
"Anya huda ce?,meye hakan yake shirin faruwa?,d waye take magana haka?.
"Waya" Taji an rada mata cikin kunnuwanta,abinda ya sanyata xabura ta kuma sanya hannu ta yaye blanket din da hudan ke ciki,take ta bayyana kwance maqale da waya tana ta doka murmushin samun abinda zuciya takeso.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 87
Bayyanar haske cikin duhun blanket din ya sanya huda zabura,haduwar idanunta kuma dana sabreen ya sakata miqewa cikin matuqar kaduwa da zabura har wayar na neman subucewa,saidai kuma kafin yakai qasa sabreen din ta sanya hannu da zummar tarota,abinda ya bawa huda qaimi itama takai nata hannun don bawa wayar kariya.
Sabreen din ta rigata samun nasara,batayi wata wata ba ta sanya wayar a kunnenta,lokacin da Naseer keta faman maimaita kalmar
"Hello......hello baby?" Wani abu taji ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafafunta. Wannan muryar ba baquwa bace a wajenta da zata iya bacewa daga kwanyarta.......ba muryar naseer ba......maza da dama da suka taba shiga qaddarar rayuwarta,suka kuma ratsa ta DUNIYARTA bata wasa da komai daya shafesu bare ta bari ya bace mata
"Nnn......" Tayi niyyar furtawa,sai kuwa ta dunqule maganar ta hadiye ta maidata cikinta,ta sauke wayar tana katse kiran sannan ta maida dubanta ga huda dake tsaye tana fuskantarta idanunta fes kan fuskar sabreen.
"Ki bani wayata adda" Ta tattaro dukka qwarin gwiwar daya rage mata ta furta tana miqawa sabreen hannu. Saidai maimakon ta bata wayar yadda ta buqata sai ta maye gurbin hakan da ajiye mata lafiyayyen mari saman fuskarta,sanda take yunqurin maido hayyacinta cike da matsanancin mamaki ta sake sauke mata wani marin a daya kuncin nata. Gigicewa tayi duka ta sanya hannayenta ta dafe kuncin nata gaba daya,wannan baiwa sabreen din ba cikin matsanancin fushi ta turata ta koma saman gadon tayi zaman dabaro sannan ta bita tayi tsaye a kanta tana damqe hannunta a cikin matuqar dimuwa da gigita.
"Kinsan waye wannan?,kinsan waye kike tare dashi huda?....kinsan hadarin da kike shirin jefa rayuwarki dama mu gaba daya?,kinsan waye Naseer?!" Taqarasa fada idanunta a waje sosai suna nuna girma da yawan bala'in data tarko musu.
Gaba daya ido ta zubawa sabreen din tana mamakin maganganunta
"Wayeshi din?" Hudan ta fada zuciyarta a tsaurare.
"Ba sunanshi naseer ba,sunanshi bassam". Ta sake fada tana ji a ranta ya kamata itama tayi tsaiwar daka har sabreen din ta fuskanci nata zabin.
"Basma......bassam.....innalillahi" Sabreen ta furta duka a tare tana komawa qasan dakin gaban hudan ta zauna jabar.
"Tun yaushe kuke tare?,kun taba haduwa?,shine ya baki waya?,dame dame yake gaya miki?,tun yaushe kike waya dashi?!" Tayi maganar wani irin zafi yana taso mata daga qasan zuciyarta. Iya kallon da huda ke mata.....iya abinda take gani daga idanun hudan kawai sun isa bata amsar zuciyarta ta fara soyewa.
"Dake nake magana huda!" Ta furta da wata gigitacciyar tsawa data ratsa hudan ainun ta cakude da radadin marin da baibar fuskarta ba har yanzu.
"Ki barni yaa sabreen.....ki barmin zabina......bassam ya cancanta,shi nakeso kuma yayimin alqawarin bani kulawa kaman yadda iyaye ke bawa 'ya'yansu......banyi wani abu da ba daidai ba fa,kema kin tsara rayuwarki ne daidai yadda kikeso......kina kuma abinda kk ga dama a sanda kikeso.....ni ko nadra ko haneefa akwai wanda ya taba tsaidaki ko ya hanaki?,ni mene ma nayi?,abinda ban taba wuce layin bayan gidanmu ba?,ban taba zuwa hotel ko joint joint ba.....ba'a taba ganina da wani d'a namiji a cikin mota mun kebe b.......".
Sake saukar wani lafiyayyen marin da yafi na dazu shi ya daukewa huda dukkan wata kalma da zata ci gaba da fita a bakinta. Marin da wannan karon ya jawo digar jini daga hancin hudan,muryar sabreen din kuma dake shaking tace
"Huda?.....kinyi hauka ne?,eh idan ma haukar kikayi kisan wadanne kalamai zaki gayamin.......nice sabreen da na baki tazarar shekara kusan biyar cikin rayuwarki.....nice sabreen da na sadaukar da walwalata farincikina da martabata saboda kuji dadi!....nice sabreen dana hana muku kuka......nice sabreen dana hana muku jin yunwa da wulaqanta.....nice sabreen dana zame muku garkuwa......nice sabreen dana maye muku gurbin uwa da uba wanda kece ta farko daya cancanci ta zama shaida akan hakan......na zame miki garkuwa a sanda baki da wani abu na shaawa ko burgewa a jikinki da d'a namiji zai gani ya burgeshi......na zame miki garkuwa a sanda baki da wani abu da zaki amfana mini face zallar qauna da 'yan uwantaka fa fisabilillahi......wanne sauran kulawa kike buqata da ban baki ba?,wacce sauran qauna ce da tafi wannan girma da fadi?......soyayya huda?.....kin san wanne abune da yafi tarwatsa rayuwar diya mace?,kinsan wanne abu ne yafi zama girman nadama cikin rayuwar 'ya mace?,kinsan mene ne mabudin nadama......wahala da azabtuwa da zuwa da qaddarar da bata sauyuwa cikin rayuwar mace?......ba komai bana face SOYAYYA kuskure na gaba da rayuwar kaso casa'in dake afkawa shine AURE......namiji!.....bashi da imani......bashi kuma da tausayi.....namiji BUTULU ne dake iya bijirewa halasci komai girmansa.......namiji halittar data fi kowacce halitta son kanta cikin duniya.....halittar da babu imani cikin ruhinta ta fannin azabtar da ruhin diya mace.......samun salamar rayuwaki ki rayu ke daya.....baki saka kanki cikin sabga ko sha'anin kowanne d'a namiji ba......wannan wani karatu ne da rayuwa tayimin bayan gushewar abba da ummina.....mutum na farko da ya fara qoqarin bata rayuwata shine ALHAJI LAWAN......" Da wani irin kallo huda ta dubi sabreen,saidai ta kasa furta komai
"Eh....alhj lawan maqoci kuma aboki ga mahaifinmu,......tun daga wannan rana na fara karatun waye namiji?,daki bayan daki kinsan komai kafin na fara sakaya wasu al'amuran daga idanunki saboda samun damar saituwar tunaninku.....huda!......dago kanki ki kalleni da kyau!" Ta furta da gasken gaske,abinda ya sabbabawa hudan duban nata da idanunta da suka hada hawaye masu yawan gaske
"Ba suna kirana karuwa ba?,ba cewa suke ina yawon ta zubar ba?,ba cewa sukeyi nayi cikin shege yafi sau a qirga ba?,ina bin maza?,ina sata?,ba haka suke bada shaida ba?......to na barsu da Allah na kuma barsu da ranar da zasu tsaya gaban Allah su baida shaida akan hakan......ni aminatu ahmad na rantse miki da girman Allah ban taba bawa kowanne d'a namiji kaina ba.....ban taba sanin d'a namiji ba ban taba kwanciya da kowa ba,idan kuma na taba....."
"Aah yaa sabreen" Huda da kuka ya kecewa ta fada da hanzari tana dora hannunta saman bakinta yayin da dukka hannayenta ke rawa.
Wani qauna da tausayi na 'yan uwantaka ke tsirgawa kowannensu. Daga ita har huda din hawaye ne da kuka ya ballewa kowannensu har zuwa wani lokaci
"Me yasa kika boyemin wani abu daya shafi rayuwarki huda.....bayan hudubata kullum a kanku itace.....komai girman matsala ko qanqantarta.....kome girman abu da qanqantarsa da kukaga alamun zai afka cikin rayuwarku.... Alkhairi ne a idanunku ko sharri ban yarda a boyemin ba?.....kinsan wayeshi?". Kai kawai huda ke kadawa ragowar hawayen idanunta suna sauka tana jin wani abu maras dadi cikin qirjinta
"Sunansa na asali shine naseer bawai bassam ba......yayi amfani da sunan bassam ne saboda sunan dana bashi nawa shine basma a madadin sabreen......dila ne na qwayoyi da cocaine da dukkan wani nau'in kayan maye,yana dillancinsu da safararsu zuwa qasashe masu yawa ta wannan qazantacciyar hanyar ya tara duk wata dukiya da yake qafafa da ita. Ya qware ainun wajen ta'ammali da mata duk kalar wadda ranshi yayi mishi.....yarinya ko babba musulma ko Christian,koda kuwa ba harkarki bane idan wani abu a kanki ya darsu zai sanya a dauko masa yarinya yayi mata fyade......a irin haka muka hadu,kuma na zama sanadiyyar daya buga gagarumar asarar da har yau ya kasa murmureta bayan kuma ba haka ya tsara ba......yayi zaton ya samu irin matan barikin da zai kashema kudi ya gama da tenure dinsu ya sallamesu........tashi d'aya na bace masa bat......yana da balain naci da bibiyar da nayi imani ita ta bashi daman gano ni wace da inda nake......yayi nufin yin ramuwar gayya ne a kanki huda....saidai kuma naci alwashin sai nayi silar qarar da ragowar rayuwarsa a gidan maza tunda har bai daddara ba ya dawo cikin hurumina.......yaso kuma taba killataccen gold din da hannu vai isa yakai gareshi ba".
Ta sani ta kuma dade da sani zantukan adda sabreen kamar rubutu ne saman dutse.......bata qarya komai runtsi komai wahala,don haka maganganunta akan waye bassam naseer sukayi matuqar tsoratata. Jikinta ya sake daukan rawa.....wannan shine dalilin da ko yaushe yake qoqarin yadda zai shirya haduwarsu tana rushewa?.
"Ki rabu dashi don Allah adda.....kada ki sake jefa kanki cikin hadari.....". Bata saurareta ba ta jefa mata wayartata zuciyarta na mata wani irin ciwo da kuma son daukar fansa
"Bakin alqalami ya riga ya bushe......kirashi ki jaddada masa zaku hadu da yammacin litinin,saidai kice kina tsoron kada a gane kin fita a gida.....kuna da event a wani guri dab da wajen acan kikeso ku hadun" Tayi maganar tana qoqarin yago paper cikin wani memo dake saman bedside din hudan tana rubuta mata sunan wajen.
*_LITININ DIN DA MUTANE DA YAWA SUKA CIWA BURINTA.....LITININ DIN DA ZATA ZANA QADDARORI CIKIJ RAYUWAR WASU,WASU QADDARORIN KUMA DA SUKE ZAMA MABUDIN QOFOFI MASU TARIN YAWA GA RAYUWAR WASU.....MABUDIN FARA GWAGWARMAYA DA TIRKA TIRKAR DA ZATA JA MANA RAGAMA HAR ZUWA QARSHEN LITTAFIN NAN.....ZAMU GANI WAYE LITININ DIN ZATA ZAMEWA FARAR RANA KO AKASIN HAKAN?_*
_KUCI GABA DA BIBIYAR 'YAN MUTAN HUGUMA_🥰🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*_Matsalarki inda zaki samu ingantattun kayan kitchen na kece raini cikin farashin rangwame da rahusa me kama da KYAUTA?_*
*CHINA*
*DUBAI*
*INDIA*
_Duk kasu a sanqame a waje daya,amintattun kaya nau'i daban daban masu daukar hankali don qawata kitchen,siyan daya ko sari_
*_Ko damuwarki kayan kitchen DESIGNERS na alfarma da kece raini?_*
*_maza garzaya cikin gidan HUGUMA UTENSILS UNIVERSE,domin kuwa ta shirya tsaf dom share muku hawayenku da galla gallan kayan kitchen cikin qanqanin farashi_*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EzM8Qst8A2XAevw3akx5ub
__________________________
PAGE 88
Lokacin da motarsu ke shan kwanar layin nasu wayarsa ta dauki tsuwwa. Kaman bazai dauka ba amma sai ya miqa hannunsa,saboda duk kiran daya shigo ta wannan wayar yana da tabbacin yana da alaqa me qarfi dashi.
Sunan Musaddiq ne ke yawo saman screen din. Ya sake zama sosai yana daga wayar sannan ya karata a kunnensa.
Kafin yace komai muryar Musaddiq din da sautin sallama ya ziyarci kunnensa. Ya amsa masa a nutse.
"Hamma kun dawo ne?" Ya tambayi fu'ad din
"Muna dab da shiga gida.....wani abu ne?" Siririyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
"Hamma muna asibiti" Yanayinsa ne yadan canza kadan ya bude baki yana tamba cikin fargaba
"Asibiti?,kai da wa?,waye ba lafiya?"
"Maamah ce hamma......muna dawowa nida abba saiga kira da asibiti.....wai an kai ta ta fadi"
"Ta fadi?" Ya maimaita kalmar cikin mamaki
"Eh hamma" Shuru kaman bazaice komai ba,sai kuma ya sauke ajiyar zuciya
"Me ya sameta?,ko kuma me sukace yana damunta?". Kai Musaddiq ya girgiza yana sauke idanunsa akan hajja harira,sai ya miqe kuma a hankali yana tura qofa ya fice daga dakin.
"Wasu bayanai likitan ya fara,saidai yace yana da buqatar ganinmu ni dakai a tare don yayi mana gamsashen bayani"
"Alright.....zan shigo" Ya amsawa Musaddiq yana sauke wayar a kunnensa.
Guri daya ya zubawa ido yana kallo qwaqwalwarsa na tafiya zuwa wani nazari. Ya bude bakinsa a nutse da zummar bawa driver umarnin wucewa asibitin,sai kuma ya lumshe idonsa yana tuna wani abu daya faru a shekarun baya wanda sai daya sanya shi sauke wani numfashi me nauyi,kana a hankali ya hadiye kalmarsa yana maida idanunsa ga gate din gidan da suke dosa.
"Waye a asibiti ba lafiya?" Farouq da yake amsa waya sanda fu'ad ke wayar ya tambaya bayan ya kammala wayar yana duban fu'ad
"Maamah ce" Ya bawa farouq din amsa a gajarce ba tare daya kalli farouq ba.
"Maamah kuma?,amma inaga ya kamata ace mun juya akalar tafiyar tamu zuwa asibitin ko?"
"Ba yanzu ba farouq.....na gaji,sai na huta tukunna......kaina kaman zai tsage da abubuwan dake cushe akai".
"Duk da hakan bai zama hujja na kasa zuwa dubata ba.....ka huta din idan mun dawo......janar....." Ya qwallawa driver nasu kira wanda ya rage gudun motar saboda kawowarsu tafkeken gate din gidan alhaj hamza kibiya
"Sir" Ya amsa masa a a ladabce
"Juya motar nan mu koma titi" Ya bashi umarnin idanunsa saman wayarsa yana lalubar number wayar Musaddiq don yaji a wanne asibiti suke?,don ya tabbatar yace fu'ad zai tsaya tambaya zai bata lokacinsa ne kawai.
"SAMHG hospital kuke?" Ya tambaya Musaddiq ga zaton suna can din. Kebantaccen asibiti ne da ake duba iyalin gaba daya bayan asibitinsu na cikin gida da fu'ad keson maidashi babba ya fadadashi sosai cikin sabon ginin mansion house din da yake musu yanzu haka
"Okay.....turon address din" Ya fadi yana kashe kiran.
A haka zakayi zaton kunnuwa da hankalinsa basa tare da farouq din,saidai kuma har yayi wayar ya gama yana saurarensa. Ta yaya za'a kaita wani asibitin da ba nan ne asalin inda kowa yake zuwa ba?. Tambayar da ya samu wani guri na musamman cikin kwanyarsa ya adanata.
Kira farouq din ya sakeyi,a wannan karon anni ya kira. Dab da zata tsinke ta daga da cikakkiyar sallama da muryar nan tata ma'abociyar kwarjini da nutsuwa.
"Mun dawo anni.....amma mun wuce asibiti dubiya,kada ki jimu shuru"
"Waye ba lafiya?" Ta tambaya cikin kulawa
"Maamah ce" Ya amaa mata kai tsaye
"Subhanallahi......amma ba wanda ya sani cikin gidan nan......ince ko jikin nata da sauqi?"
"Ban sani ba anni,sai munje yanzun zamu gani"
"To don Allah kuyi mata sannu,idan akwai wani abun kuyi gaggawar sanar mini"
"To anni" Ya amsata yana sauke wayar. Dubansa yakai ga fu'ad,har yanzu waje daya yake kalla,yadda yayi dif kaman baya wajen,haka fuskarsa ta nuna kaman baisan me ake magana akai ba.
"Fu'ad" Farouq ya kirayeshi sanda suka isa farfajiyar asibitin,guards dinsa kuma nata kai da kawowa wajen tabbatar da tsaron wajen kafin fitowarsa.
Idanunsa dinnan masu bala'in kwarjini ya daga ya zubewa farouq su. Yanayin kallonsa yana da matuqar kaifi da saukar da dafi,idanun suka so yiwa farouq din kwarjini,saidai wannan din ba baqon abu bane a wajensa,abune da ya riga ya saba dashi tuntuni.
"Ako yaushe ka dinga tuna cewa taci albarkacin kalmar UWA.....zata kuma ci gaba da cin wannan Al Farmar koda meye tayi maka" Idanunsa yadan ragewa kaifi kaman zai lumshesu sai ya fass,ya sake budesu sosai saman fuskar farouq din. Wannan maganar inda farouq din yasan mugun famin da ya yiwa ciwonsa da baiyita ba,har maqogoronsa sai da yaji yawu yana neman daukewa,ya tattara dukka wani yaqi da yakeyi da yanayinsa sannan ya bude bakinsa
"Inda ace a yau za'a zare wannan kalmar tsakanina da maamah......da har abada ba zata sake ganin fuskar muhammad fu'ad ba muddin kuwa ya haifu daga tsatson jadda.....a lokacin daya miqa mata dukkan soyayya da yarda......a lokacin ta nuna masa cewa DIYA MACE MAYAUDARIYA CE.....BA KUMA ABAR YARDA BACE,bata barshi haka ba har sai da tayi silar......." Ji yayi bazai iya qarasawa ba.....ji yayi wannan sirrin bazai iya furtashi ga kowa ba,sai kawai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya zura qafafunsa yana fitowa ba tare daya jira me budewar ya bude masa ba.
Tun bai qaraso bakin qawatacciyar balcony din da aka yiwa dakin ba musamman saboda shan iska da hutawar me lalura da me jinya ba ya hangeta zaune ta hasken fitilun da aka wadata wajen dashi. Kanshi ya dauke sarai,yana jin har qasan ransa ya washi matar. Ba zaya gaya mata gogayya da duniya ba.....kaman yadda bazai gaya mata sanin takan duniya ba. Bata tunanin akwai wani yanayi da zai nuna mata a yanzun da zai tunzurata ta janye rayuwarta daga cikin tasu har sai ta cimma nata gacin.
"Sannu da zuwa.....ashe ka qaraso" Hajja harira ta furta cikin tsananin nuna kulawa tana miqewa daga saman kujerar da take kai.
Kanshi ya dauke yana maidawa ga Musaddiq daya taroshi tun daga farkon balcony din
"A nemo likitan......yazo da gaggawa don ina da abunyi" . Sosai maganar ta daure kan hajja harira wadda kwarjininsa ya hanata sake cewa komai. Lallai ya kamata kafin ta zurma kanta da yawa ta sake karantar kowanne taku da motsi nasa domin samun isar muradinta cikin sauqi.
"Waye a cikin dakin?" Ya sake jefa tambayar ga Musaddiq. Saidai kafin wanda aka yiwa tambayar ya amsa hajja hariran ta rigashi amsawa cikin matuqar alhini
"Basu barin kowa ya shiga don har yanzu ma bata farfado ba". Duba daya tak ya yiwa hajjan yayi taku uku ya isa gaban dakin,ba tare da jiran umarni ko bada dama ga kowanne likita ba ya murza handle din ya tura kansa ya shige.
Daga bakin qofa ya fara tsaiwa,ya harde hannayensa a qirjinsa yana qare mata kallo. Tana kwance cikin lallausan blanket da aka rufeta dashi har zuwa qirjinta. Ba qarin ruwa babu na jini.....baiga oxygen ba,saidai akwai canola daya kula da ita a hannunta.
Idanunta a rufe suke,a haka tafi kama da me bacci. Sake nutsa idanunsa sosai yayi saman fuskarta yana karantar fuskar bayan wucewar kowacce daqiqa har ya samu matsaya cikin zuciyarsa dangane da ita,ya sauke hannayen nasa yana sake qarasawa ciki,takun likitan kuma sai ya biyo nasa takun.
Fasa qarasawa yayi bakin gadon,ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa ya waiwayo a nutse yana amsa sallamar likitan gami da zube masa idanunsa.
Dan tsamurmurin likita sanye da lab coat,hannunsa kuma riqe da wani file,yayin da wuyansa ke rataye da abun auna gudun zuciya.
Ta cikin farin gilashin idanunsa ya kalli fu'ad. Kallo qwaya daya tak daya mamayi zuciyar likitan da wani irin mahaukacin kwarjini tare da zallar mamakin wanzuwar muhammad jadda cikin asibitinsu.
"Meye ya kawo mamallakin jadda diamond chore resources asibitin?" Ya tambayi Kansa da kansa tsoro da kwarjini suna cikashi.
"Kada dai ace da gaske suke da suka gaya masa ita din mamarsa ce?" Wannan maganar ta sake tsarga masa wanda hakan ya sake sakashi jin rudani yana mamayarsa. Yasan waye muhammad jadda,bazaiso kuma fadawa matsala dashi ba,ba zayaso fadawa hurumin da ba nashi ba da karatunsa daya samu yake riqe kansa da iyalansa.
"Shine likitan?" Fu'ad daya gama qarewa likitan kallo ya furta yana duban musaddiq daya qaraso daga ciki yayi tsaye gefan fu'ad din
"Shine hamma" Ya amsa masa shima yana maida dubansa kan likitan.
Duk wani qoqari nasa ya tattaro,ya kalato yawun bakinsa yana dora murmushi saman fuskarsa
"Barka da zuwa asibitinmu yallabai.....munyi farinciki da shigowarka yau asibitinmu......hakan ba qaramin qarin kima da martaba bane ga asibitinmu damu kanmu gaba daya". Hannayensa zube a aljihun wandonsa,kamar yadda idanunsa suke a Kan likitan.
"Madalla.....inason magana dakai if possible"
"To......ba damuwa.....ba matsala hakan,muje ne ko a nan zamuyi?" Yayi tambayar yana raba idanunsa tsakanin fu'ad din da musaddiq.
"Qaraso ka duba patience dinka".
"Aah yallabai..... Ai ba za'a barka a tsaye kana jira ba.....hasalima ban jima da fita a dakin ba ai". A nutse ya debe dubansa daga kan likitan,sannan ya fara takawa a nutse yana fita a dakin musaddiq ya mara masa baya.
A hankali yaci gaba da takawa yana fita a asibitin. Bai dakata ba har ya isa inda motarsa ke ajiye. Kafin ya qarasa daya daga cikin guard din ya zabura ya bude masa sannan ya jira isowarsa
"Kada ka rufe.....zanga baqo"
"Yes sir" Ya fadi yana barinta a bude kaman yadda ya buqata. Budewar data bash daman kallon likitan da kuma karantar kowanne motsi nasa cikin wani kallo da ba na kai tsaye ba wanda ke cike da hikima.
Wani irin bugu zuciyarsa keyi musamman sanda ya tsinci kansa tsamo tsamo tsakanin Jordan da abdulbasit da suka kusa rufa tsahonsa. Ya daga kansa yana duban fuskokinsu da suke manne da baqin gilashin idanu.
*D U N I Y A T A*
*_D U N I Y A T A_*
Page 89
________________________
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
*_assalamu alaikum warahmatullah_*
*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_*
*_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_*
*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_*
Shadda
Laces
Atamfa
Kayan yara English wears dana jarirai
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Huluna na maza da mata yara da manya socks
Takalma na maza da mata yara da manya
Lafayas
Sarqoqi agoguna banguls da rings
_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_
_bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*
*_masu manyan qarfi da matsakaita?_*
*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_*
*_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_*
*MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA*
*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
*_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_*
*_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
_________________________
PAGE 89
"Enter" Jordan yace dashi yana jiyowa sosai gareshi gami da nuna masa cikin motar. Bashi da abunda zai ce don shi kansa yasan nan din ba wajen wasa bane,ya daga qafafunsa da yaji sun fara masa nauyi yana sanya jikinsa cikin motar,yana kuma jin yadda gumi yake tsargo masa daga kowacce kafa ta jikinsa.
Set din dake opposite nasa ya masa nuni,hakanan ya zauna yana qoqarin gyara lab coat dinsa yana hadiye wani miyau me kauri. Idanu kawai fu'ad din ya sake zuba masa duban daya sanyashi kasa nutsuwa ya dinga gyare gyare,daga gyara agogo zuwa gyara rigar jikinsa da kuma hannun rigar.
A nutse ya janye masa idanun,sannan ya motsa bakinsa
"Ya sunan doctor din?"
"Ni....Dr kamal......sunana Dr kamal". Kai fu'ad ya jinjina yana lumshe ido gami da budesa sanan ya maimaita sunan a hankali
"Good Dr kamal,ina maka murnar samun damar zama likita ga mahaifiyata......am.....inaso nasan da meye da meye suka ce ka gaya mana a matsayin cutar dake damunta?". Sosai maganar ta rudashi saboda tazo masa a bazata,ya dubi fu'ad yana qoqarin nuna masa gaskiyarsa
"Su waye?.....Ni ba wanda yacemin ga abinda zan fada sai abinda bincikena ya gano".
"Kamal!" Fu'ad ya kira sunansa da wata irin deep voice dake dauke da amo me tsoratar da wanda ake magana dashi.
"N...na'am"
"Lookat me......" Ya sake fadi masa yana tsareshi da idanunsan nan da suke sanya Dr kamal jin kamar zaya narke.
"Kayi haquri yallabai" Dr din ya sake fada kansa tsaye ba tare da fu'ad din ya sake cewa komai dashi ba. Wani irin rudani da firgici suna ratsashi.....gaba kura baya sayaki,yasan hajja harira ba sanin shanu ba,amma ta yaya zai yadda yayi jayayya da mutum irin muhammad jadda din?,wanda yayi imanin ita kanta inda hajja harira ta gama sanin wayeshi da kyau ba zata saka kanta cikin wannan wasan ba.
"Yallabai......sunce zasu biyani bayan barazana da hajja harira tayimin......sunce na kwantar da ita kawai na saka mata ruwa wanda zai qara mata kuzari ne kawai...........sunce tabbas zakazo...idan kuma kazo din na kambama ciwo da kyau,na nuna muku zaman kadaici da kewa ce take damunta,wanda muddin ba'a kula da ita da kyau ba.....an samu wani cikin wadanda sukafi kusa da ita take kuma yawan ambatarsu su zauna tare da ita ba to tabbas zuciyarta zata iya bugawa ayi hasararta......sunce idan.....". Dakatawa yayi ba tare daya qarasa fadin abinda zai fada din ba saboda daga masa hannu da fu'ad yayi. Shuru ya ratsa motar,abinda ya sake ruda Dr kamal,ya sanya hannun rigarsa yana goge gumin fuskarsa bayan ya cire gilashin idanun nasa.
"Sauka kaje....kaci gaba da riqeta.....zaka sallameta,but sai daidai lokacin da na baka umarnin yin hakan"
"Okay sir" Ya fada da gaggawa yana juyawa gami da laluben hanyar fita daga motar,don zaman motar duk da laushin kujerunta da sanyin Ac da wani ni'imtaccen qamshi da yake fita......amma ji yakeyi kaman yana zaune ne cikin qabarinsa.
"Dr" Ya sake kiran sunansa dab da zai sanya qafafunsa a qasa. Adan zabure ya waiwayo yana qoqarin saita kansa.
"Banda wannan harqallar.....ka tabbatar babu wata sauran haramtacciya ko miyagun harqalloli da kakeyi a boye......don idan hakan ta kasance ka tabbata ba zaka tsira a hannuna ba"
"Wallahi ranka ya dade ba ruwana......ni din mutumin kirki ne ka tambayi kowa ma"
"In kuwa hakane ka kyautawa kanka".
"Sauko malam" Jordan yace da Dr kamal din a dake cikin rashin son wasa.
Jinsa ya dinga yi kaman zai kifa sanda yake komawa cikin asibitin. Inda ace yasan da gaske take ita din mahaifiyarsa ce ta yaya zaiyi wannan kasadar?. Fadan giwa da damusa waye yake shiga?,sai wawa sai mahaukaci,shi kam qaura zaiwa asibitin bazai sake shigowa ba sai gobe,duk da yasan bashi da inda zaije yace ya guje masa.
Duk wani mamaki da maamah zata bashi a yanzu ya biyo bayan wanda ya gani a yanzu da shekarun rayuwarsa ta baya. Ko daya bai sake komawa asibitin ba,saidai kuma bai hana kowa zuwa ba. A kwanakin ma gaba daya yana qoqarin ganin ya gyara wasu abubuwa da yake ganin suna qoqarin tasowa can qasan kamfanin,wanda idan har ya bari matsalar tayi girma zata iya jawo asara mafi muni fiye data kudadensu da suka zirare.
A cikar ranar lahadi kusan kowanne bayani ya kammala samunsa,ya shigar da komai cikin documents,sai la'asar ya kammala,don haka daga nan alwala yayi ya wuce masallaci. Daga masallacin ya sake dawowa gida,ya leqa anni da bata jima da dawowa duba maamah ba,sai ya zauna falon bayan ta sanya amna ta dama masa yoghurt da fura.
"Muhammadu" Anni ta kirasa,sai ya dauke idanunsa daga tasha alhadath dake nuna yadda bani Israel ke dake ragargazar Palestinian,hankalinsa ya fara nisa kan hanyar da zai aika musu tallafi ya kuma isa garesu kai tsaye
"Na'am" Ya amsawa annin yana dubanta
"Jiya abbanku ke complain....ko sau daya ance ba'a ganka a asibiti ba......ni kaina ko sau dayan banji kace zaka je ba,sai zama da kaketa yi a sassanka?".
Hannu ya sanya ya karbi kyakkyawan tray din da amna ta jero cups da bowl me kyau dake dauke da dammen yogurt din,ya aje gabansa yana cewa
"Thanks lovy dovy". Qaramin murmushi ta saki,ta juya tana komawa kusa da anni ta zauna.
"Jikin nata da sauqi ai anni......infact ma tun ranar ta samu lafiya.....yau ma zasu sallameta". Ya amsa ba tare daya kalli annin ba,don yasan yana yin hakan zata dago wani abu
"Duk da haka muhammad wannan din baiyi kyau da tsari ba....."
"Yanzu daga nan can zanyi anni kiyi haquri". Kalmar haquri idan ya fadeta da gaggawa haka to tabbas baison bacin ran annin ne,ta gama karantar hakan.
Jujjuya furar yayi sannan yayi bismillah yakai bakinsa. Fuska yadan bata ya daga kai yana duban amna
"Yaushe kika koma sakamin sugar a abin sha?". Kai tadan langabe
"Hamma.....kadan fa na saka maka wai don bakinka yayi taste"
"Zoki dauke abarki" Ya fada yana dan ture bowl din. Da sauri ta miqe tana fadin
"Ayyah hamma.....kayi haquri kada magauta suji kanmu....bari na hada maka wani wannan sai BB farouq yasha"
"Kayi zaton amnan taka tayi hankali ne?,kaima kai ka sowa kanka wannan gallafirin......wai sai yaushe zaka fidda mace ne Muhammadu?,bakasan duk girman namiji aure shike cikashe wani gibi ba?,gibin da babu abinda zai cikeshi face auren?......ita kanta amna yaushe ta fara iya riqe abinda ya dace da itama ballantana ta riqe abinda ya dace da waninta?". Waiwayowa tayi tana duban annin kamar zata saki kuka
"Wayyo anni.....yanzu duk qoqarin da nayi baiyi ba?,hamma don Allah ban canza ba?" Wani sassanyan murmushi ya kubce masa,ya maida kallonsa ga anni
"Tsokanarki fa anni takeyi.....kin canza sosai amna ta,kinyi kuma hankali,yauma nasan akasi aka samu,ki dama min wata ki sakamin apple a ciki da grapes ki ajiyemin,idan na dawo zan sha".
Tabe baki anni tayi tana kauda kanta
" Ai daman.....indai abu da laifin amna duk girmansa saika maidashi qarami......da tashi kayi kaje ka shiryadinma da zaifi maka". Murmushi ya saki ya miqe a nutse. Duk wani jini na anni girmansa yake gani martabarsa yake gani hakanan qaunarsa yakeyi.
"Hamma na shirya na rakaka?" Ta fada tana tallafe da tray din.
Bayason zuwa da ita,saboda ya tabbatar ba zata samu marabtar data dace da ita ba,amma bazai iya cewa bazaije da ita ba,don haka yace
"Ki shirya.....but be fast....banson jira"
"Yanzun nan hamma" Ta fadi tana qara hanzarin barin wajen.
Suna hanya tana cikashi da labarai kala kala wanda hakan yake masa dadi da debe masa kewa. Don amna din wajen quruciya da sakalci irin na autanni ba daga baya take ba.
Koda suka isa cikin asibitin sai ya kalleta
"Ko ki zauna a nan,ko na yiwa Jordan magana ya kaiki ki zabi duk abinda kikeso.....kina da 30 to 40minutes"
"Yay!.....thank you hamma na" Ta fada da tsananin murna.
Zaune take daga bakin gadon da kwata kwata cikin kwanaki ukun a duniya taji ba abinda ta tsana sama da kwanciya a kansa. Kwanciyar da babu alamun nasara a tattare da ita,kwanciyar da bata amfaneta da komai ba saima sake haska mata rashin nasararta muraran da ake sakeyi.
"Ba alamun nasara hajja......zuciyata tafi karkata akan na tafi plan C.....a plan C ne kuma nakejin cewa koda sharadina zai zama silar rugujewar fu'ad wannan karon basan sassauta masa ba......a wannan karon a shirye bake na gindaya masa sharadin da nayi imanin bazai iya tsallakeshi ba.....a wannan karon hajja......ban yarda koda da darsawa a rai ba zuciyata ta darsamin wai bazanyi nasara ba.....dole dole dole nasara ta kasance a tsagina.....hajja a yau zan bar asibitin nan,ina da buqatar na huta saman gadona nayi bacci me lafiyar da zai bani damar tsara komai da kyau cikin kwanyata.....na kuma wayi garin litinin da wannan shirin".
Kai hajja ke gyadawa tana kuma sake juys Plan C din maamah data tabbatar zaiyi wahala idan ba abinda take hasashe bane ba.
"Hakan ma yayi,abun ni kaina ya soma shallake tunani na.....amma mariya anya shima baida hatsabiban da suke masa aiki?" Shuru maamah tayi,ko qwalqwalwarta bata kama muhammad yana biye biyen nan ballantana hankalinta. Tun daga haihuwarsa zuwa tasowarsa kawai tasan ya banbanta da sauran yara,quruciyarsa ma ta daban ce a cikin yara,zuwa sanda ya cika shekara goma cas a sannan ta sake ganin banbanci mabayyani a kanshi.
Shigowarsa dauke da cikakkiyar sallama sai ta zama tamkar amsa ga tambayoyin hajja harira. Bakinta yana dan rawa tana kamo amsar sallamar da qyar ta hada kalaman tana amsa masa.
A nutse ya tako ciki idanunsa akan maamah din data dauke kanta daga gareshi gabanta tana ji yana faduwa. Haka kawai ita kanta sau tari sai taji ya mata kwarjini,fargabar kada dai ace yaji wani sashe na tattaunawarsu yana cikata.
Duk yadda hajja ke qoqarin ankarar dashi tana wanze a dakin ta hanyar jera masa sannu da zuwa amma ta gaza samun hankalinsa. Bawai kuma don baijita ba,aah haka kawai yakejin wani abu na daban game da matar,sannan kuma kwanyarsa a kullum idan ya ganta takan yawaita qoqarin tunata cikin jerin sahun mutanen da yaga gilmawarsu a shekarun da abbansu yake raye.
Kaman bai lura da sauyawarta ba,yaja kujera gaban gadon ya zauna yana gaidata. Ta amsa masa tana hadiye bacin ranta. Fada takeson masa sosai ko zata samu sassauci amma kuma idan ta tuna a gobe akwai nata plan din dai ta danni zuciyarta,saidai duk da hakan sai data b'ara
"Kasan ina nan amma fu'ad ka banzatar dani?,ko ka manta ba'a canzawa tuwo suna?"
"Kiyi haquri" Ya jefeta da kalmar nan da har ta fara tsanarta saboda yawan fitarta daga bakinsa.
Shuru yaci gaba da ratsa dakin ba tare da kowa yace da dan uwansa komai ba,kafin daga bisani aka turo qofar.
Dr kamal ne,ya qarasa shigowa cikin takatsantsan da tsantseni,wanda dukkan me hankali yana kallonsa zai fahimci hakan.
"Kwanciyar haka ta isa?,xaki iya komawa gida?" Ya tambayeta a tausashe saidai kuma kalamai ne masu harshen damo da yawa a ciki.
Juyowa tayi tana dubansa maganar tana qoqarin fassara kanta da kanta cikin qwalqwalwarta. Ta zargi wani abu,amma kuma yanzun ba muhallin wannan bane,don haka ta dauke dubanta ta maida kan Dr kamal
"Ina buqatar sallama Dr,naji qwarin jikina".
" Yanzu in sha Allah" Ya fadi yana bude file dinta. Hannunsa yana dan rawa yayi rubuce rubuce ya maida ya rufe,sai fu'ad ya miqa masa hannu Kai tsaye,yadan kalleshi sannan ya miqa masa file din salin alin.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 90
*_MONDAY_*
*_Tushen aiki,ko nasara na tsoronki_*
Cike da confidence take shiryawa cikin tsadaddiyar dubai abaya budaddiya data lullube jikinta ainun.
Wine color wadda aka qawata qasanta da kuma qasan wandon abayar da wasu irin stones da zare ruwan gold masu daukan hankali.
Gaban madubi ta matsa tana saka brush tana sake kwantar da doguwar sumarta me yauqi da rashin cika sannan ta ware madaidaicin mayafin abayar tayi rolling dinsa saman kanta,abinda ya bawa kyakkyawan fuskarta daman fita tarwai ta kuma haska da wine color din abayar jikinta.
Siririn agogo ta sanya gold me dan adon wine,wanda yake suwa set da komai nasa,ta taka a hankali ta matsa ta dauki purse dinta da wayarta ke ciki tanata haske.
Kiran ta daga ta sanya a kunnenta tana aza idanunta kan huda dake zaune gefan gadon,kai kace mata ket ta zura da gudu
"Okay.....gani nan fitowa" Ta furta tana maida wayar jaka sannan ta maida kallonta kan huda. Suna hada idanu boyayyun hawayen dake qasan idanun hudan suka yiwa kansu hanya.
"Adda.....ina tsoro" Ta fada tana jin zuciyarta tana nauyi. Taku biyu Sabrina ta isa gabanta,ta kuma kamo hannunta
"Duk duniya.....duk wanda yace zai tabaku bazan qyaleshi ba muddin ina da iko da qarfin hakan......ba yau ba,ba kuma sau daya ba ina jan kunnen Naseer yayi qoqarin fidda rayuwarsa daga kaina......ya sanyawa ranshi bai taba haduwa da wata basma ma ba amma baiji ba........a wannan karon ya kamata nayi masa general hukuncin da zai sanya a rage ire irensa baragurbi cikin mutane......kada kiji tsoro,babu abinda zai faru" Ta bata tabbaci tana matsa hannayenta.
Iska me zafi maamah ta furzar daga bakinta sanda suka kammala zama saman qawatattun kujerun da aka zuba saboda zaman cin abinci ko shan wani abu ga baqi maziyarta wajen.
"Wai nikam mariya.... Meye hikimar tattaunawarmu a nan?" Hajja harira ta tambayi maamah tana kallonta.
"Harira.....gani nakeyi kaman akwai wani information nawa da yakeyin leaking.......yadda fu'ad yake samun damar kaucewa kowanne tarko nawa abun yana da matuqar daure kai......inaso mu koma gida da wuri don a yau nakeso A YITA TA QARE!"
"Ina saurarenki" Hajja ta furta tana hade yatsunta guri daya tare da bawa maamah hankalinta.
"Hajja......aure zanwa fu'ad!" Sosai maganae ta zowa hajjan a bazata,wanda hakan yaso hautsinata tare da haifar mata da fargaba......fargabar yiwuwar rushewar plan nata da rashin cimma interest dinta tsakanin wasan da ake murzawa yanzun.
"Aure kaman yaya mariya?,ya samo matar auren kenan?" Kai ta girgiza tana sake matsowa kaman hajja din bata jinta sosai
"Ya akayi kanki ya kulle hajja?,zanwa fu'ad aure da yarinyar da duk na zaba masa don ta zamemin tsanin MALLAKARSA".
Shuru hajjan tayi wuta tana neman dauke mata. Ba wai kuma mamaki ta shiga ba,aah tanason adan taqin tayi tunanin amsar da zata bawa maamah wadda zata bayu ga tafiyar lissafinta daidai. Duk yadda taso kuma ta kwalkule maganar ta fiddata a daidai ta gaza,don harbuwar maganar zuwa kwanyarta tazo mata ne da wani irin katsuwar hanzari da gajere kuma tsukakken lokaci
"Yimin bayani dalla dalla qawata".
"Yanzun nan" Cewar mamah tana komawa ta zauna sosai.
"Zan nema yarinyar da na tabbatar babu soyayya a zuciyarta sai soyayyar kudi......zan nema yarinyar da zata iya aikata komai indai akan kudi ne.....zan nema yarinyar da ba kasafai namiji ke burgeta ba kaman yadda kudinsa yake burgeta ba......za muyi contract da ita na auren fu'ad zuwa wani lokaci.......zata shayarmin dashi ta ciyarmin dashi daga dukkan wani abu da akeso yaci ko yasha da zai jawo min hankalinsa.......daga sanda buqata ta biya zan sallameta daga dukkan adadin kudaden da takeso tayi kuma nesa da rayuwarsa.....a sannan ne kuma tayimin tawa shimfidar da zan soma tawa tafiyar".
Idanu hajja ta zubawa maamah sosai.....ga bikin zuwa kuma babu zanin daurawa.....tabbas wannan tsari nata yayi.....kuma komai zai iya tafiya ya kuma wanzu kaman yadda ta tsara din muddin akayi katari da kalar yarinyar da zatayi aikin.
A jikinta takejin wannan aikin nata ne,wannan kuma su za'a yiwa.....wannan aikin JANAN dinta za'a yiwa ba kowa ba......zata soma tata shimfidar ne itama a sanda mariya ke tunanin zatayi tata.....a sannan zata wanzar da nata tsarin da zai kauda na mariya,dole ta tsaya kai da fata ta taya mariya fafutukar wannan tsarin ya tabbata,to amma ta yaya zaiyi accepting?. Yaron da yake da tsananin kafiya da tsaurin da bokansu ma ya gaza juya akalarsa?.
"To amma ta yaya kike zaton zai karbi maganarki ta sauqi irin haka?" Hajja ta yiwa maamah tambayar da taketa cin ranta.
Wani murmushi maamah ta ajiye tana goye hannuwanta a qirji,daidai sanda sabreen ke shigowa wajen tana takowa cikin nutsuwar nan tata me fusgar hankali,sai maamah din ta dauke idanunta daga kanta ta maida ga hajja ba tare data bawa ganin data yi matan muhimmanci ba,amma abu daya taji ya darsar mata a rai
"Da mata masu kyau irin haka ya kamata ta yiwa fu'ad din fatsa.....domin su din suna da saurin kama zukatan mazaje".
"Komai lalacewar uwa uwa ce.......hakanan komai lalacewar d'a yasan me ake nufi da uwa.....ballantana fu'ad da nasan me na haifa?,nasan iya matakin kaifinsa da kafiyarsa......wannan ba wani abun damuwa bane".
Ba tare da jira ko neman izini ba taja spare kujerar dake gefansa ta zauna. Shimfidadden kyan nan dake fusgar zuciyarsa tunda can baya wanda ya jashi zuwa ga wanzuwar alaqa tsakanin su a yanzun sai yakega ya ninka yadda yake a baya. Fuskarnan a rubuce da dabi'ar miskilanci baro baro samanta.
"Zuwa da kai ai yafi saqo ko?......ka nema qanwar ga yayar tazo da kanta.....zaifi kyau a sauka ta inda aka hau". Tayi maganar a jejjere da wani irin aji da kintsi daya qara kwarjantata a idanunsa.
Zuciya da ruhinsa suna masa d'ari d'ari gami da gargadinsa a kanta,to amma kuma wani sashen na zuciyarsa na bashi tabbacin tabbas yaci wasan ne......lallai ta fuskanci cewa shike da nasara wannan dalilin ya sanya tsananin wayonta ya bata shawarar tayi gaggawar bada kai.
Wata irin dariya ya kece da ita yana kallonta gami da gyara zamansa sosai
"Haba 'yammata?,irin wannan karaya haka da sauri?"
"Karaya kuma?......sabreen bata taba karaya ba.....hakanan ba zata karaya akan wulaqantaccen mutum maras daraja irinka ba". Mamaki ne ya lullube farincikinsa,a hankali yanayin fuskarsa ta sauya.
"Daga yanzu zuwa sanda zaka isa gidan birsin ka fara qididdige yawan adadin haramtattun kudadenka da zasu salwanta bayan cafke jirgin da aka boye cocaine me nauyi,wadannan kudaden an samesu ne ta hanyar maida mutane zuwa dabbobi wajen basu gurbatattun magungunan bugarwa da sanya maye.....kaga kuwa garin banza a farau farau din banza yake qarewa".
Wani irin shock ya shiga saboda kiran sunan jirgin da ayau yake sanya ran isowarsa. Ya lissafa yau a ranar sa'a a gareshi.....zai aike mata da sakamakon abinda tayi masa ta jikin 'yar uwarta......hakanan kuma zai maida gurbin hasarar da yayita jiran cikewar gurbinta.
Bai qara koda motsi daya ba sautin takun ma'aikatan cikin sassarfa da hanzari ya karade gurin. Hankalin kowa dake wajen ya tashi yayin da aka soma kallon kallo a tsakanin juna.
"Kada wanda ya motsa.....munxo kama me laifi ne.....kowa yana cikin aminci.....amma kada ku motsa har sai mun gama mun bada umarni" Daya daga cikin ma'aikatan da ba'a iya ganin fuskarsa yayi maganar a gaggauce.
Ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yakeyi......wannan ya sakashi miqewa da zummar samun hanyar fecewa,saidai kuma tuni suka ankara suka masa qofar rago gami da fadin
"U are under arrest!". Wadannan din ba irin ma'aikatan daya saba gani bane,rana dubu ta barawo,ya tabbatar idan har ya saba kubce musu to a wannan karon babu wannan damar,don haka ya tsaya kyam jikinsa yana kyarma har suka gama.
"Koda ka sake samun rayuwa a nan gaba.....kayi komai da lura" Ta furta tana nuni da gefen kanta,sannan ta juya a nutse ta fara takawa
"Thanks for the information" Daya daga cikin ma'aikatan ya furtawa sabreen din da ta fara barin wajen. Murmushi ta saki kadan
"Wannan aikin kowanne dan qasa na gari ne"
"Gaskiya ne" Ya furta yana saluting nata,yayin da suka waiwaya zuwa ga Naseer suka riqeshi sosai suka sanyashi a tsakiya suna fita dashi ta daya qofar cikin hararrami da tsaurara masa tsaro.
"Keep calm......you're safe guys.....kowa yaci gaba da sabgarsa". Mutumin da yayi musu jawabin farko a yanzu ma ya fadi sanda yake bin bayan abokan aikinsa da sassarfa.
"Tabbas akwai wata boyayyar fuskar a bayan wannan" Muryar hajja ta daki kunnen maamah wadda idanunta ke kan hanyar da sabreen ke wucewa.
Dauke kallonta maamah tayi zuwa kan hajja
"Kada dai ace tunaninmu yazo daya?"
"Me kenan?" Hajjan ta cewa maamah tana dubanta
"Na samota.....inaji a jikina zata iya.....inaji a jikina ba iya fuskar da muka gani yanzu ce kadai a tattare da ita ba.....zo muje" Maamah ta fada tana jan hannun hajja zuwa hanyar da sabreen tabi.
"Inason insan wacece.....inaji munzo nan ne a yau domin cikar burina" Maamah ta fada tana jin wani irin nutsuwa da fuskar data gani din.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 91
Agogon fatar dake daure a hannunsa ya duba bayan yadan gyara shirt din jikinsa. Lokacin da yake hutu na mintuna ashirin zuwa talatinne a yanzu.
Iska ya furzar daga bakinsa yana duba adadin mutane da jerin sunayen wadanda keson ganinsa ta qaramar computer gabansa wanda mutumin da yake kula da sashin da zaka soma tsaiwa kafin ka samu damar ganinsa ya tura masa wato mr abdulhaleem.
Mikail shine mutum na farko cikin jerin sunayen,to amma baya buqatar ya fara da ganinsa,don hakan zai iya hasala fushinsa ya gaza ganin sauran mutanen dake da muhimmanci su ganshi din.
Me sunan malam ya kira,ya bashi apple da strawberry sai ruwan dumi. Mintuna goma kacal ya bawa kansa sannan ya fara bada umarnin shigowar baqin.
Duk wani mutum me muhimmanci sai daya kammala da ganinsa kafin ya bada umarnin shigowar mikail,wanda zuwa sannan yayi imanin inda za'a auna jininsa yakai dari biyi qila harda talatin ma.
Sanda yake shigowar fu'ad din yana tsaye daga bakin book shelve din da aka yiwa wani kyakkyawan tsari cikin office din. Dukkan documents din da suka shafi case din yake cirowa a nutse yana qoqarin danne yadda ranshi yakeyi yana baci.
Ba kaman kwanakin baya kadan da suka shude ba.... Lokacin da yake da daraja da martaba ta gaba gaba cikin kamfanin......a lokacin da zaiyi sallama cikin girma da mutunci cikin office din,ya tako kaman kowanne ma'aikaci da Allah ya tarfawa garinsa nono yake iya idanu biyu da muhammad jadda din kai tsaye ba tare da shamaki ba. Akwai dubban ma'aikatan dake kamfanin wanda basu taba idanu biyu dashi ba......amma shi yana cikin wadanda zasuyi tattaki har zuwa cikin office din su zauna saman kujerar da ake bawa kowa don ya tattauna da CEO din.....a yau din sai gashi a matsayin qasqantacce,me tarin laifukan da baisan ta inda zai fara kare kanshi ba. Ya fadi gaskiya?,wadda ya tabbatar fadar nata wata faduwa qasa ce wanwar......yayi qarya?,ita kuma ta zame masa alaqaqai da babbar matsala a duk sanda me jadda din ya gano ainihin matsalar.
A nutse ya juyo abinsa ba tare daya kalli sassan da mikail ke gurfane saman gwiwoyinsa ba. Baice komai dashi ba sai daya koma saman kujerarsa sannan ya motsa bakinsa a nutse
"Tsugunna kazo kayimin ko bayyana min gaskiya?....idan kuma duka ba wannan ba ka shirya amsa tambayoyin muhammad fu'ad?" Ya qarashe qarshen maganar yana dauke idanunsa daga kan file din yana zube masa su.
Kallonsa kadai ka sanya razani a zuciyar mutum,ballantana ma mutum irinsa maras gaskiya ko qanqani?.
"Na shirya sir.....don Allah kayimin rai"
"Gaskiyarka kadai ita zata fiddaka.....am listening" Ya furta yana dora qafarsa daya kan daya,sannan yayi relaxing bayansa sosai da fuskar kujerar tana juyata a hankali,wanda banda motsa kujerar da yakeyi idan ka kalli kyakkyawan fuskarsar nan me shimfidadden kwarjini zakayi zaton bacci yakeyi.
Bai boye masa komai ba......ya gaya masa komai yadda ya wakana......saidai statement dinsa na qarshe da harshensa yaso sarqafewa
"Saidai.....daga b.....dag.....ga baya na gano da ita da wan....."
"Da wancan tsohon dan cacan UBA NE DA 'YARSA BA ka gayyatosu suka taba dukiyar da gumin halal ya tarata?!" Ta furta da wata irin tsawar da hatta mutumin dake qofar farko bama reception na office dinsa ba zai iya jiyo tartsatsinta,bayan dukan table din da yayi da hannunsa abinda ya sanya wasu files din da takardun misplacing daga inda suke.
Har cikin tsokarsa yake jin fushin yana masa tasiri.....bai taba ganin an raina masa wayo kaf rayuwarshi irin wannan lokacin ba. Sanda yake kammala binciken da sakamakon daya karba daga hannun wadanda yasa suyi nasu binciken ya duba yaga conclusion nasu yayi daidai da nasa.....saidai duk da haka zuciyarsa tana masa kokwanto.
Ta yaya 'ya zata zama KARUWA?.....yar fashin YANAR GIZO.....MAYAUDARIYA ME SACE XUKATAN MAZA DON KAWAI TAYI AMFANI DASU?. Sannan kuma ace uba ya zama DAN CACA?,WANDA ZAI IYA ZUBA KOMAI A CACAR NAN DON NASARA TA ZAMA TASA CIKI HARDA TAKARDUN GIDAN DA MARAYU KE ZAUNE A CIKI?.
Dukka jikin mikail bari yake kai kace wanda aka watsawa ruwan qanqara ne cikin hunturun matsanancin sanyi.
"Kayi haquri yallabi.....tuba nake.....kayimin gafara kayimin aikin rai....wallahi banci komai a ciki ba sir.....ko sisi sai nawa kudaden ma da suka narke!"
"Will you shut your mouth or not?!" Ya sake fadi da wata gigitacciyar tsawar data sanya fitsari balle ma mikail din,ya kuma koma yayi zaman dabas a qasa don ya gama sarewa.....ya kuma yi imani bashi da sauran mafita.
"Ni zaku mayar dan iska?,dukiya ta halalina a gidan caca?,a wajen karuwai?,a wajen sabon Allah?.....ko an gaya maka ni ban san dadin rayuwa ba?,sai kai?......to daga kai har su wannan shine zai zame muku aikin ashsha na qarshe da zaku aikata.....daga kaina ba zaku sake marmarin sake aiki irin wannan ba......ka tashi ka fita ka bani guri.....zan nemeka.....idan kaso ka gudu duk inda kakeso" Ya fadi yana huci idanunsa da suka sauya launi akan fuskar mikail da yayi jalaf da gumi da fitsarinsa.
"Na roqeka sir......kayimin duk kalar hukuncin da zakamin a yau basai wani lokaci ba......amma ka yiwa Allah kada ka koreni daga bakin aiki koda zaka sauyan matsayi".
"Naci gaba da biyanka albashi kaci gaba da shan barasa da neman mata.....ka bacemin a wajen tun ban gama tunzura ba!' Ya amsa masa yana sake jin zuciyarsa tana hasala.
Ajiyar zuciya gami da iska zazzafa ya dinga fesarwa bayan fitar Mikhail din. Ya sake komawa yayi relaxing sosai yana jin wani irin huci yana fita daga fuskarsa. Ya tsani dukkan wasu ayyukan ashsha......mikail yayi masa abu mafi muni....abu mafi munin koda dashi kadai ya kamashi cikin company dinsa zai iya zama silar korarsa ko rasa aikinsa....NEMAN MATA.....zina itace abinda yafi qyamata cikin rayuwarsa bayan shaye shaye,dukka rayuwar mikail ta dagula ta kuma gurbata cikin wadannan ayyukan. Wata qyama ta mikail dama yarinyar gaba daya suka sake kamashi,ya waiwaya fannin caca......abar data tabbata da nassi cewa haramun ce itama qarara.....
"Wadanne irin ahali ne wannan?" Ya furta a fili qasa qasa zuciyarsa na masa wani irin ciwo. Baisan girman tsanar da ya yi musu ba....ko don ya taso ya samu nagartaccen mahaifinsa ko yaushe yana jaddada musu su guji su kuma nisanci wadannan abubuwa iya gudunsu?.
Wanne hukunci ya dace yan yankewa mikail?,tsohon dan cacar da kuma 'yar kwaltar Yarinyar?. Wannan tambayar ce har ya gama zamansa a company na wunin ranar bai samo amsarta ba.
Yau koda ya koma gida sai yaqi zaman sassansa.....ya zauna sosai sunyi dinner dukkansu kaman yadda suka saba a duk sanda dama ta basu irin haka dukansu su shidan. Sun jima suna hira tsakaninsa da abba,wanda anni na gefe tana jin gwarazan 'ya'yan nata. Qauna da kuma wani alfahari dasu yana ratsata.
Sha daya saura ya sanya qafafunsa a sassansa,wanda kamar tunanin yana tsaye daga bakin qofa yana jiransa ya mamayeshi. Yaja dogon tsaki kamar zai tsinke harshensa......ya taka a hankali yana zarcewa toilet bayan ya sanya me sunan malam ya sallami kowa,masu kwanciya sun kwanta,masu kwana bakin aikinsu sun kama wajen tsaiwarsu.
Shafa'i da wuturi yayi a kebantaccen wajen daya ware saboda ganawarsa da ubangijinsa. Koda ya idar sai yayi zaune saman abun sallar. Yana jan hasbunallahu da duk dare bata wuceshi qafa dubu da la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin. Iya wadannan abubuwa guda biyu ya tabbatar suna taka rawa me yawa cikin rayuwarsa,sun kuma zame masa mabudin sirrin nasararsa.
Har ya kammala ya kasa tsaida hukuncin da zaiwa kowannensu,har sai daya hau saman lalallausan gadonsa,ya dauki qaramin remote yana sauke rumfar gadon da ke tattare ba lallai ka lura ma da ita,kyakkyawan net din ya sauko ya lullube gadon ruf yana bada wani dim light da ke bawa bacci nutsuwa.
Numfashi me zurfi ya sake ja yana jingina bayansa da pillow hadi da lumshe idanunsa kana ya budesu. Kamar wannan kawai ake jira yayi qwaqwalwarsa ta fara aiki.
"Mikail ya dade da zama korarre daga dukkan wani aiki da yake da nasaba da jadda diamondchore resources company......kamfanin dake kano ko lagos.....koda kuwa aikin shara ne cikin kamfanin........mutumin da ake kira da samaila fa?,idan yace ya dawo masa da dukkan abinda yaci nasu horo ne me sauqi.....dole ya hada masa da wani abun....YARINYAR KUMA FA? .
Jan duvet dinsa yayi yana lullube fuskarsa har zuwa kanshi. Koda a qasan zuciyarsa bayason tunata. KARUWA wani suna ne daya samu gurbi cikin kunnuwansa tun yana da shekara goma sha uku a duniya.
_"mariya......bansan me yasa idanunki suke makancewa ba da barin daidai.......kina matsayin matar aure.....wadda ke auren sunna da yara har guda biyu,me zai hadaki alaqa da qawance da karuwai?"
"Karuwai?,hmmmm.....bakasan a yanzu babu wanda yakai karuwa mutunci ba?,saboda zaunannun kudi gareta da zata yiwa duk wanda taso ihsani.....kyautar ban girma da ban mamakin da ke da kike qarqashin inuwar aure baki isa ki sameta ba.....kaga kuwa karuwanci ai ya biya su".
Muryoyin dukansu su biyun da irin zancan da sukayi a sannan ya dawo masa tarwai cikin kwanyarsa abinda ya sake qarawa zuciyarsa wani irin zafi da radadi. Abbansa dake kwance a qarqashin qasa yanzu......da kuma maamah din da take rayuwa dasu a yanzun hakan itama. Wani yanayi ne da bayason tunashi......wasu abubuwa da binnesu yafi zama alkhairi a gareshi duk da yadda kullum suke qona masa zuciya da mafi zafin ciwo da suka.
"Dole ta fuskanci hukunci me girma....." Ya fada yana bude idanunsa,ya dauki wayarsa ya aika gajeran saqo sannan ya koma ya kwanta yana qoqarin tilastawa kansa yayi bacci.
Kwanaki ukun da ya dauka yana dakon jiran kira daga wajen Muhammed jadda sai suka zame masa tamkar me jiran ranar mutuwarsa ne. Komai ya tsaye masa cak.....wata iriyar nadamar sanin sabreen dake a mazaunin fateema a wajensa tana mamayarsa irin nadamar dashi kansa baisan yawanta ba.
Ranar da saqo daga kamfanin jadda din kwana yayi yana zawo. A gobe jumaa....juma'ar da baisan yaya zata kasance masa ba.
****takardun gabanta ta jawo ta rufe a nutse tana maida dubanta kan fuskar hajja dake shan lafiyayyen nonon da aka zubawa madara aka kuma niqeshi cikin 'ya'yan itace masu dadi.
"Na gode sosai qawata.....na gode qwarai da gaske......tabbas banda ke koda komai zai tafi zai kasance me wahala a wajena..... Banda abinda zan iya biyanki dashi,kedai Allah ya bawa autarki miji na gari". Wani qasaitaccen murmushi hajja ta saki tana Ajiiye mug din dake cike da furar idanunta akan fuskar maamah. Ita daya tasan me take tsarawa cikin zuciyarta,ita kadai kuma tasan me ke kai kawo a ciki
"Ameen mariya......banda abinki mene ne amfanin amincin?,mene ranar amincin?......yanzu kawai abinda ya rage shine.....muyi tattaki har zuwa cikin gidansu don mu sake tabbatar da komai a kanta.....daga nan sai mu saka rana ta daban da zamu tunkari yarinyar.....komai ina ganin bazai mana wahala ba......ina ji a jikina zata karbi komai cikin sauqi da hanzari,tunda kudi ta fito nema......mu kuma biyan buqata kawai mukeso". Kai maamah ta jinjina farinciki yana lullubeta. Hasken nasararta da dukkan wata lamba ta nasara tana walqawa cikin idanunta.
"A shirye nake na rasa komai don wannan abu ya tabbata" Maamah ta furta
"Ba zaki ma rasa komai din ba.....don komai zai fito ne daga jikin wanda ake abun don shi" Hajja ta fadi tana sake sakin murmushi.
"Ina jin me zai hana yau mu shiga gidan nasu?,tunda ga adress nan da komai jikin takardar?" Maamah dake sake duba takardun ta fadi
"Da zafi zai haka?......"
"Bakiji abinda bahaushe ya fada ba?,da zafi zafi ake dukan qarfe?" Maamah ta katse maganar hajja,sai kuma suka saki dariya dukkaninsu.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 92
Cikin wani dan banzan lace peach colour da torches na purple maamah din ta shirya,sannan tayi amfani da wani irin luxury veil me wani irin lafiyayyen jiki ta lullube jikinta dashi. Tun daga takalmi da jakar hannunta zaka sallamawa shigartata,ballantana azo ga sarqa da awarwaraye zuwa zobunan gold data sanyawa yatsunta guda hudu kowanne hannu bibbiyu.
Cikin motocinta ta sanya driver ya fidda wadda bata fiya shiga ba,aka gogeta tas ainihin kyawunta da qyallinta ya sake bayyana.
"Gaskiya kin fini gaggawa mariya" Hajja dake shiga cikin motar ta furta tana 'yar dariya.
Ajiyar zuciya maamah ta saki tama girgiza kai
"Mariya kenan,ba zaki gane yanayin da nake ji ba,saboda ke komai ya miki daidai cikin rayuwarki,yara biyu?,amma ba guda daya wanda zaka juya yadda kakeso?......zaiyi wahala idan har yarinyar tana cikin gidan ma ban nemeta ba......gwara mu yita ta qare hajja.....idan na samu yadda nakeso ma zuwa qarshen watan nan a gama komai ta tare na fara aiwatar da aikina.....don na samu labarin dab yake da kammala ginin wannan gidan da nake burin kasancewa a ciki ni da duk wanda naso naga dama". Kai hajja ta jinjina tana sauke boyayyar ajiyar zuciya. Tafi kowa buri da kwadayin wannan gidan,saboda bahaushe yace gani ya kori ji.
Tayi yawo da qafafunta tsakanin katangun gidan,ta kuma samu ganin iya abinda Allah yayi tana da rabon gani,don hatta ginin da akeyi qarqashin kulawar security ne,so shiga ko fita din yana qarqashin kulawa.
"Karki damu.....komai zaizo yadda muka tsara qawata"
"Haka nake fata" Dukkaninsu sukayi maganar cikin ransu suna gamsar da kansu tasirin tasarrufinsu ba tare da sun tsarma kalmar IN SHA ALLAH a ciki ba.
Idanunsu kaf cikin layin lokacin da motarsu ke gangarawa,suna lissafe da kowanne gida da suke giftawa har suka qaraso babban qofar gidan
"Yauwa......tsaya a nan,shine wannan da alama" Hajja ta fadi tana baiwa driver din umarni.
Tare suka fito kowa ta qofa daban daban,maamah ta soma gyara lullubin kanta tana duban gidan. Gida ne da kana masa kallon farko zaka fahimci a wani zamani da can mamallakin gidan yana cikin sahun masu arziqin wancan lokacin,to amma duk da hakan data fuskanta sai tadan tabe baki
"Banda lalura da neman biyan buqata babu abinda zai sanya na nemawa fuad aure a irin wannan gidan........bari amma ba komai.....ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba,muddin komai ya kammala,xan sanya binciken qwaqqwafi sai na nema masa auren yarinyar da tafi kowacce 'ya gata a al'ummarmu.....sannan kuma wadda zata dace da tsarina". Murmushi hajja ta saki tana jin maamah tana motsa mata wani abu cikin ranta.
"Qwarai kuwa qawata......dan gata ai sai 'yar gata,amma naji dadi da kika fahimci nema masa wannan ba matsala bace.....tunda AUREN WUCIN GADI NE AUREN BIYAN BUQATA".
Ranta a sake tana murmushi suka fara kutsawa gidan suna magana da juna qasa qasa.
Har suka dangane da babban tsakar gidan gidan basu hadu da kowa ba. A irin wannan lokacin lokaci ne da yara da sauran wadanda suka tasa cikin gidan suka jima a makaranta har wasu ma suna dab da tasowa,don haka ba kowa din sai tsakar gidan dake a tsaftace kamar kullum.
"Salama alaikum.....gafaranku dai mutanen gida" Hajja ta ware muryarta ta kwarara sallamar idanunsu yana yawo bisa tsaftataccen tsakar gidan.
A hankali ta bude idanunta dake a lumshe,kimanin awa guda tana kwance a haka saman doguwar kujerar falon tun bayan kiranta da JIB yayi ya shaida mata an rarraba wasu cikin kudaden a account din mutum dubu d'ari tsaffin 'yan pension da suka rasu da bashin banki,wanda hakan ya sanya ake cirewa daga cikin abinda gwamnati ke bawa iyalansu duk wata. Hakan ya tagayyara iyalai da dama,domin basu da qarfin biyan kudin bare su tsira daga zari d'ai d'ai da banki yake musu. Cikin ranta da jikinta takejin wani irin sanyi kamar ta aiwatar da wani wajibi da yake kanta. Ta zame ta kwanta cikin mutuwar jiki tana tuna yadda bashin bankin ya zamo silar shigarsu halin ni 'yasu bayan rasuwar abbansu,duk da cewar bashi yaci bashin ba ci masa akayi babu saninsa babu kuma yardarsa,rayuwar ta dinga qwallo dasu har zuwa sanda tasu mahaifiyar ta sake tafiya ta barsu da tsanani da uqubar rayuwar. A yau tasan iyalai da yawa zasu kwana cikin farincikin da take fata ya zama sanyi da haske cikin qaburburan mamatansu ciki harda iyayenta.
Ta jima a kwancen tana tunanin me gobe zata haifar mata?,a wanne gurbi zata dora rayuwarta wadda daga rana irin ta yau takeso ta koma aminatu dinta ba sabreen fateema minal da sauran tarkacen sunayen data yita rabawa maza ba. Ta zauna taci gaba da kula da rayuwar qannenta dake da matuqar tsada da muhimmanci a gareta.
Tanaso subar gidan,tanaso su bar kano ma gaba daya idan zaiyuwu,saidai kuma tana hasaso irin qalubalen da zata iya fuskanta a sanda ta koma rayuwa cikin wata al'ummar da basusan ainihin wacece ita ba. Wanne kallo zasuyi mata sanda take zaune cikin gidan da daga ita sai qannenta mata?,wannan ne kadai abinda yake sake taka mata burki,sai kuma ga sallamar ta ratso har dakinta.
Sallama ta uku taji an sakeyi,dole ta miqe daga kwanciyar ta sauko da qafafunta qasa ta miqe tana takawa a hankali don amsa sallamar da kuma duba waye. Don tasan lokaci irin wannan da yawa cikin matan gidan suna bacci.
Har ta sanya hannu zata yaye labulen muryar daada ta dakatar da ita,sai ta koma a hankali ta zauna a inda ta tashi tana jawo wayarta ta bude.
"Wa'alaikumussalam" Ta amsa tana binsu da kallon rashin sani. Saidai kafin ita ko su su sake cewa komai bibo ta bankada nata labulen ta fito da buta a hannu.
Itama sakin bakin tayi tana kallonsu,saidai ita tana musu duban farko ta karanto zallar wadatar da suke ciki da kuma arziqi. Atamfar jikin maamah ta kalla,saitaga tana mata kama da atamfar da sabreen ta saka rannan har musu ya barke tsakaninta da hadiyya,inda daga qarshe hadiyyan ta tabbatarwa da bibo kudinta ya kusan kaiwa dubu sittin da biyar idan ma baifi haka ba.
Wannan abun data tuna ya sanyata saurin ajiye butar hannun nata sannan ta kawo fara'a da murmushi ta aza saman fuskar tata. Idanma arziqi ne kamata yayi ace kai ka fara tararsa a dakinka ya fara sauka
"Marabanku sannunku da zuwa lale" Ta fadi cikin haba haba da tsananin kulawa.
Hausawa sukace shimfidar fuska tafi shimfidar tabarma,wannan da suka gani ya sanya suka karkatar da hankalinsu akan bibo suna amsa mata,wannan ya sanya daada salin alin sakin labulenta ta koma ciki don ba kasafai ta fiya shiga shirgin da ba bata ba,musamman kuma data ga bibo din ta zaqe.
"Ku shigo ciki mana,kwa tsaya daga nan?,ai baqonka annabinka" Ta fadi da sauri tana juyawa ciki.
Idanu suka dinga bin rumfar bibo din dashi sanda take rawar jikin aje musu ruwan sha,akwai wadatar tsafta amma ba wadatar arziqin da yakai koda quarter din nasu.
"Bismillahir rahmanirrahim" Ta fadi tana zama a gabansu.
"Mu sake gaisawa ko?,ina wuninmu zaa ce?" Tayi zancan tana sake fadada fara'arta.
Hajja da tasan takan duniya ta washe mata bakinta tana amsa mata itama cikin madaukakiyar fara'a da nuna sakewa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 93
itama,tana hango qishi qishin halayen bibo da kyau daga yanayinta da idanunta dake nuna zallar wayo.
Itama maamah data zurfafa a tunani ta sake waiwayawa suka gaisa,sai kuma dan shuru ya biyo baya na wani lokaci kadan kafin bibo ta kasa daurewa
"Kuyi haquri fa bayin Allah,abubuwan da yawa,ban shaida ku ba" Tayi maganar tana basu hankalinta sosai.
Murmushi hajja tayi tana gyara zamanta
"Eh ai gaskiya ba zaki shaidamu ba,don bana jin mun taba gamuwa kam.....mu din baqi ne,sunana hajja harira.....wannan kuma mariyatu amma muna kiranta da maamah" Hajja ta fadi tana nuna maamah din da hannu
"To....to ma sha Allah,ni hafsatu nake.....kuma nice mace ta uku cikin gidan nan.....duk da me gidan Allah yayi masa rasuwa,ya rasu ya bar kowaccenmu da 'ya'ya". Fuskokinsu suka nuna jimami suka masa addu'ar samun rahama sannan hajja ta dora
"Muna tambaya ne akan wata yarinya da muke kyautata zaton itama 'yar gidan nan ce" Sake daidaita zamanta bibo tayi,zuciyarta tana zillo da fatan jin wacece
"Mun sanya an biyo mana sawunta ne saboda muna son nemawa d'anmu ita". Murmushi bibo ta tsinke dashi hade da faduwa kuma da gabanta yayi. Wannan dan mutanen ko makaho ya shafasu yasan cewa tabbas masu arziqi ne,masu dukiya ne,ba kuma qananun mutane bane,akwai arziqi daula da dukiya a wajen,iya zamansu a wajen kawai qamshin turarensu ya cika wajen,wannan kawai ya isa ya gaya maka matsayinsu a rayuwa.
Zuciyarta cike fal da fata take dubansu,don tana kyautata zaton ba wanda za'a nema haka cikin gidan cikin dattako haka irin d'iyarta dake karatun kiwon lafiya.
"To......to ma sha Allah,ai kowa kukeso a gidan nan 'ya'yanmu ne dai.....wacce ce a ciki?,hadiyya?". Kai hajja ta girgiza tana kallon bibi
"A'ah,Sabrina ce".
Tamkar hajja ta kawo ruwan zafi ta watsa ma bibo a sassan jikinta haka taji,ta dinga jin wani abu yana tsarga mata tun daga saman kanta har tafin qafafunta.
Wacce Sabrina din ga nasu 'ya'yan a zazzaune kamammu?,wadannan mutanen masu alamu na damshin arziqi sune za'a ce sun tattako neman auren Sabrina din?,wacce daraja ko kamala take da ita data cancanci wannan?. Ji tayi ba zata iya daurewa ba,tako wacce fuska sai ta barar da dan guntun mutuncin da qila dansu yaje ya musu qarya ya labarta musu tana da shi yarinyar,dole ta farke mata laya don ba zata iya bari wannan abu ya faru ba.....idan ma Allah ya bata sa'a ta musu nuni da tata kamilalliyar d'iyar.
"Tofa......amma dai hajiya d'anku ya rufeku gaskiya,duk da bansan ko irin cikin mutanenta shima yake ba?".
" Kamar yaya kenan?" Maamah ta jefa mata tambayar cikin fargabar kada ta kasance an kusa aurenta ne da wani,wanda muddin hakan ya faru sai inda qarfinta ya qare wajen baza dukiya har sai an fasa an dawo da abun kan fuad din.
"Abinda nake nufi shine maganar gaskiya baku yiwa yaronku zaben macen aure ta gari kaman yadda addini ya shardanta ba......ni da kuka ce Sabrina ma abun mamaki ya bani,waye zai nemi auren wannan idan ba asharari ba?,danku dan gidan girma da dattako bai cancanci auren mace irin Sabrina ba......yarinyar da duk cikinmu ba wanda yasa sana'arta data wuce KARUWANCI.....sam bata kwana cikin gidan nan sai anci sa'a qwarai....ni nan da hannuna nasha tsareta amma ta tsallake ta gudu,rubutun shiriya ba irin wanda bata sha ba,fada duka ba wanda ba'a yi ba......ga sata kaman bera,yanzu haka kwanaki muna kyautata zaton cikin shege taje ta zubar,ba wanda take ganin mutuncin sa ballanta ta raga masa,dan tsoro irin na diya mace fa sam ita bata sanshi ba,gaba gadi take komai cike da rashin kunya da rashin albarka......son abun duniya a wajenta abun har ba'a magana......zata iya komai akan kudi.....idan nace komai ina nufin komai da komai fa......har kisa...."
"Wadannan dabi'un su suka sanya mukeson aurenta da yaronmu". Maamah da dogon sharhinta ya fara isarta ta fada tana kallon bibo,dogon sharhin da yayi Mata dadi ma,don ya qara tabbatar mata da cewa tabbas zata iya.....Sabrina din ita tafi dacewa ta kuma fi cancanta da deal din.
Idanu bibo ta gwalalo tana kallonsu maamah cike da zallar mamaki.
"Amma ta yaya za'a aikoku neman aure kuje ku nema musu irin wannan baragurbin diyar?, bayan ga gaskiya kun gani daga bakin iyayenta sun gaya muku ba'a rufeku ba?,anya ku din ba kishiyoyin uwa bane zaku rufi uwarsa ku cutatar mata da d'a?,ku nema masa auren tantariyar hatsabibiyar KARUWA ba tare da saninsu ba?"
"Ni nan nice uwarsa kuma mahaifiyarsa data dauki cikinsa wata tara ta kuma haifeshi ba tare da taimakawar kowa ba.....a haka nakeso ta zamewa d'ana matar aurensa,wannan din zabina ne!".
Dukka sai aka gogewa bibo hadda,sun sanyata a rudani gaba daya ta rasa fahimtar komai. Uwa kuma?,uwa da kanta?,anya da gaske uwar ce?.
Tana tsaka da wannan tunanin ta tsinkayi miqewarsu suna aje mata wasu adadin kudin data tabbatar ba 'yan kadan bane.
"Ga wannan ki soma riqewa......ki nuna mana kawai dakinsu ko dakinta cikin gidan nan" Maamah data qagu ayi komai a wuce wajen ta furta tana duban bibo
"Daki me kallon wannan dab da matakalar bene" Ta furta a sanyaye.
"To mun gode fa" Hajja ta fadi tana bin bayan maamah da tuni ta fice.
Zumbur ta miqe tabi bayansu tana leqensu ta tsakanin labule,salati da sallallami kawai takeyi zuciyarta na wani irin bugawa. Tunda take a rayuwarta bata taba ganin baragurbin iyaye ba irinsu,shin anya ma da gaske kuwa suke?.
Tsaf nutsuwarta ta dauke,tana jin ba zata iya zama haka ba tare data labartawa kowa wannan zancan ba. Balaraba bata nan tun dazun ta fita.....bata jin kuma zata samu cikakken hadin kan yin magana da daada,don tasan ba kasafai ta fiya shiga shirgunan da ba nata ba,ballantana ma kuma lamarinsu Sabrina din.
Wuf ta fito ta kuma fada dakin daada hankalinta a kansu sanda suke cire takalmansu suna shiga parlor dinsu Sabreen.
"Lafiyarki meye haka bibo?" Daada dake zaune tana gyaran zogale cikin rumfarta ta fada idanunta akan bibo.
"Muhammadur rasulillahi daada.....zo kijimin wata lalacewa....zo kiji wata almara,wai zuwa akayi neman auren yarinyar nan Sabrina?". Tayi zancan tana zama d'aid'ai a gaban daadan.
"Wa'alaikumussalam" Sabreen ta fada a hankali tana daga idanuwanta zuwa ga bakin qofar falon nasu.
Idanu ta zube musu sanda suke shigowa cikin falon,haka kawai taji gabanta yana faduwa akan baqin fuskar da batasan su waye ba. Sai ta samu kanta da miqewa tsaye tana fadin.
"Sannunku da zuwa"
"Yauwa sannu 'yar nan" Maamah ta furta cikin murmushi yayin da hajja ke qarewa sabreen din kallo wadda ke sanye cikin soft Egyptian bubu me mayafi,amma madadin mayafin sai ta sanyawa kanta hula wadda santsin gashinta ya hanawa hular zama daidai,kaman ma ta mata kadan sakamakon nannadadden gashin data daure a qeyarta.
A nutse ta taka zuwa ga fridge dinsu tana lalubar musu ruwa,yayin da su kuma suka dinga bin dakin da kallo suna ganin zallar banbanci tsakanin falon da sauran falukan gidan,wanda hakan ya sake jaddada musu zarginsu.
A hankali idanun maamah ya fada kan babban hotonsu guda daya dake kafe a falon. Sabreen a tsaye huda a zaune a gabanta,nadra da haneefa suna zaune daga dama da hagunta. Idanu ta tsura musu tana kallon yadda suke kamanceceniya da juna,tana mamakin kuma yadda sam sunan yaran bai fito cikin bincikensu ba.
Gabansu ta ajiye ruwan sannan ta koma da baya ta zauna a nutse tana kallonsu.
"Barka da warhaka" Ta fadi tana qoqarin karantarsu,don ta fahimci akwai wani kallo na daban qasan idanunsu da sukeyi mata ita da falon.
"Yauwa sannunki 'yammata.....ya kike ya garin?" Hajja ta fada da murmushi
"Alhamdulillah.....wa kuke nema?" Ta tambayesu kai tsaye,don itadai tasan dukan wanda yake alaqa ko mu'amala da ummensu na kusa kona nesa ya jima da sanin rasuwarta,tun suna zuwa wadanda basu sani ba daga baya har labarin ya game ko ina,kuma an jima sosai da sunan anzo wajenta.
"Ke muke nema wajenki mukazo" Hajja ta sake fadi har yanzu tana murmushi
"Ni kuma?" Ta tambayesu a mamakance
"Eh ke" Hajjan ta jaddada mata
"To gani,Allah yasa lafiya"
"Lafiya qalau sai alkhairi......yaronmu mukazo nemawa yardarki ki zame masa matar aure" . Tamkar tana karanta tatsuniyoyin gizo da qoqi haka taji zuwan zancen kunnenta,daga inda take zaune ta daga idanu tana kallonsu,kalmar aure tana maimaituwa a kunnenta.
"Aure kuma?,bam fahimta ba,ya sanni ne?,idan ya sanni munyi jarjejeniyar aure dashi?"
"Kwantar da hankalinki,baki sanshi ba bai sanki ba.....hasalima mu muka shirya abun". Idanunta ta sake azawa sosai a kansu tana musu kallon masu tabin qwaqwalwa a wannan karon,kamar wasu qananun yara?,hadin aure kaman wasan 'yar tsana?.
" Eh.....zakiji abun wani iri ko?...."
"Da zaki daure ki tafi bayaninki kai tsaye da sai nafi fahimta" Ta furta a gajiye da zamansu a wajen,don bata fatan su huda su dawo su samesu cikin falon.
"Dalla dalla zan miki yanzu yammata......auren KWANGILA ne,shi mukeso kiyi da d'anmu..... Wanda dukanmu mu dake zamu amfana gaba daya,zaku fimu samun moriyar abun ma,don ke da kanki zaki yanks adadin kudin da kikeso kafin aikin da kuma bayan aikin......ga mahaifiyar yaron da kanta zata tsara miki yadda takeso abun ya kasance".
Da wani irin madaukakin mamaki ta maida idanunta kan fuskar maamah,uwa kuma?,uwa da nemawa d'anta auren kwangila?,wacce irin uwa ce wannan?.
Mutuwa tayi murus a zaune sanda maamah ke karanto mata qudirinta,har ta kammala ta kasa janye idanunta a kansu.
"Muddin komai ya tafi yadda nakeso......zaki zama wata abun kwatance cikin ahalinku......hakanan zaki gane a baya wahala kawai kikeyi.....zakiyi arziqin da me kamoki cikin danginki sai yayi da gaske,zaki samu kudin da rayuwar wadannan zata zama rayuwa mafi gata" Maamah tayi zancan idonta akan sabreen hannunta kuma yana nuni da hotonsu dake bango tanason ganin reaction din sabreen akan hoton.....don ta fuskanci wani abu kadan daga gareta.
"Basu da alaqa da dukka wani aiki ko kwangila......ki sauke hannunki daga saman hotonsu" Sabreen ta furta da wani irin emotion idanunta itama tsaye cikin na maamah.
Wani shu'umin murmushi maamah din ta saki,sai ta sauke hannunta a hankali,ta samo abinda takeson samowar,kuma tabbas lallai komai zaizo da sauqi.
"Aure na gaske ko na wasa,na kwangila ko wanda bana kwangila ba baya cikin tsarina hajiya,bama wannan deal din ba.....koma meye a yanxu bani da sha'awarsa......bana buqatar komai bana buqatar kowa!" Tayi zancan da wani fushi fushi da kuma dakewar zuciya.
"Koda wannan shine aiki na qarshe da zakiyi sai kin mana wannan yarinya......ina me baki shawarar ki kwantar da hankalinki kibi kawai......cikin sati daya ko biyu ma zuwa wata daya idan buqata ta biya kina iya tafiyarki.....kada ki yarda akan wannan ki jefa rayuwarki cikin hadari".
"Bazanyi ba" Ta furta idanunta a lumshe kuma a nutse,saidai kuma batasan me yasa zuciyarta take wani irin tsananin bugu ba. Bawai barazanarsu bace ta tsoratata kota dameta ba,don ba kalar barazanar da bata gani ba,to wadannan su ko nasu qalubalen yasha banban da sauran?.
"Zata iya yiwuwa" Zuciyarta ta gaya mata kafin muryar maamah ta sauke a kunnenta.
"Kwana daya kacal kike dashi kan bayyanar yardarki......idan kika haura haka kuwa.....zamu tilastaki ki yarda koda baki so ba" Ta qarasa maganar tana matsawa gabanta ta ajiye kudi masu yawa da rubutacciyar number wayarta,sannan suka juya suna fita daga dakin salin alin. Dole ta bude idonta ta rakasu da kallo,ta rasa abinda take ji a qasan ranta,tsoro ko fargaba?,wanda dukkansu bata sansu ba,ko kuma shakka ce ko kokwanto?.
Suna shirin sanya takalmansu su huda suka shigo,kallon kallon sukayi a junansu su hudan na mamakin ganin fitowar baqi daga dakinsu,abinda suka manta rabon dasu gani,ganin yadda baqin ke kallonsu sai suka gaidasu,suka amsa kuwa cikin fara'a,su suka wuce suma suka fada dakin.
"Ban taba zato ku tunanin yarinyar nan zata watsar da damar samun kudade masu kauri irin haka ba" Hajja ta fada sanda driver ke tuqasu don maidasu gida.
"Na fiki mamaki hajja,anya bayanan da muka samu a kanta babu na bogi?"
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 94
"Nima na fara wannan shakkar,saidai kuma na yarda da aikin hidima.....ya iya aiki fiye da zatonki,wannan ya sanya bamu rabu ba tsahon shekaru" Kai maamah ke jinjinawa
"Ta yaro kyau take bata qarko.....a wannan karon zata fahimci duk wanda ya rigaka kwana sai ya rigaka tashi".
**Duk wata jijiya dake harba jini a jikinsa kyarma take,kaman yadda ya jiqe jalab da gumi a sanda yake zaune saman kujerar cikin shaddarsa dataji aiki,kadan daga shigar yiwa talauci jan kunne daya fara yi a kwanakin kenan a cewarsa.
Zaman MUHAMMAD JADDA a gabansa a yanzu sai yakeji kadan yake da banbacin zaman mala'ikan mutuwa a gabansa. Ya tsinewa Mikhail dake zaune a qasa da mato yafi sau shurin masaki,hatta da wanda ya shirya cacar ya tsine masa a ransa har baisan adadi ba.
Wallahi inda yasan akwai wani daya jibanci muhammad jadda ma sam da baiyi kuskuren hada caca dashi ba ballantana akai ga karbar dukiyarsa,bai sani ba.....qaddara kuma ta rigayi fata.
"Dukka wannan abubuwan daka lissafo malam rufa'i matsalarku ce.......abinda nakeson tambayarka shine.......nawa ta raba ta baka kayan ta qwamushe kudade daga account na kamfani na?" . Gigicewa ya sakejin yayi da saukar tambayar da baiyi zatonta ba ballantana tsammani.
"Sabrina?" Sunan da yazo masa a cikin zuciyarsa kenan,saidai abinda bai sani ba ya zarce har zuwa saman harshensa sautin sunan kuma ya bayyana a kunnen fuad da Mikhail dake zaune a wajen.
"Yes" Fuad ya furta yana yin relaxing bayansa a jikin kujerar yana kuma qarewa kawu rufa'i kallo tare da karantar duk wani motsi nasa.
Salati kawun ya dinga debowa a tsakanin rude,daga sama zuwa qasa,daga qasa zuwa sama. Wani irin tashin hankali yakeji yana saukar masa,wacce irin masifa ce Sabrina din keson jefasu?.
"Wannan yarinya anyi 'yar Allah bani......yallabai....wallahi wallahi bansan da komai ba.....gagararriya ce dama ta fitinemu,tunda uwarta ta sanya qafa tabar duniya shikenan yarinyar ta zama kangararriya........wannan aikin nata na kwashe kudaden akawunt na al'umma dama na jima inajin qishi qishin dinsa......batun zamowarta karuwa kuwa na jima da sani......"
"Dakata" Ya tsaida kawun ranshi yana tsananin baci. Dukka komai ma akan yarinyar gaskiya ne kenan?,komai da komai ya gama samun tabbatattun shaidu da hujja.......a nata tunanin har takai riqar da zata shiga gonarsa?,idan har ta saba shiga shirgin wadannan tarkacen maza.....tana tunanin muhammad jadda zai tabu?.
"Ba kowanne namiji take saurara ba......tana da girman kai da izza......sai namijin da taso tayi alaqa dashi.....koshi dinma yana gwaruwa kafin ya samu ta fara saurarensa......amma ni yallabai,ba abinda ya taba faruwa tsakanina da ita duk da naso hakan ya faru,amma aurenta naso yi,saidai kwata kwata aure baya gabanta,shine cikin jerin sahun lissafin abu na qarshe da take tunanin wataqil watan watarana idan tana raye zatayi,hasalima zancan aure dana fara mata dashi ya kawo rashin samun cikakkiyar fahimtar juna a tsakaninmu.....hakanan da sunan FATEEMA NA SANTA". ya tuna maganarsu da Ya'aqoub kenan a jiya bayan ya sanya an kawo masa shi a wani kebantaccen guri.
Tashi yayi ya zauna sosai yana harde yatsunsa cikin juna gami da zube idanunsa akan kawun idanunsa a samansa,fuskar nan shimfide da wani lafiyayyen fushi daya cakuda da izza da kuma miskilanci. Yanaso ya tuna hukunci guda daya mafi tsaurin da zai musu......yanason ya musu hukuncin da zasuji a jikin su,saidai kuma yanaso hukuncinta yafi zama mafi tsaurin da ba zata sake gigin maimaita kusakuren data aiwatar a baya ba.
"Rufa'i kake ko?" Ya jefa masa tambayar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa.
"Na'am yallabai.....labbaika" .
"Inason kai da d'iyarka ku hadamin kudina nan da awa ashirin da hudu,ficika a ciki banaso tayi ciwo,naira biyar idan babu a ciki zata iya zame muku matsala..... Muddin kuwa ba haka ba......" Kawai sai ya girgiza kai ba tare daya qarasa fadin abinda zai fada din ba,ya maida bayansa ga kujerar yana jawo wayarsa ya fara latsawa hadi da bawa banza ajiyarsu shida Mikhail din.
Yadda cikin kawo ya karta ya bada wani sauti zata zaci zai tsinke da gudawa ne,cikin kwanakin yaci kudin da baisan iya adadinsu ba,wanda maidasu a yanzun wani gagarumin tashin hankalinne da baisan ta ina zai tarosa ba. Uwa uba sabreen.....yarinyar dake da matsiyacin taurin kai da daukar kasadar da yasan ko sama da qasa zasu hade ba zata fidda abinda ya shiga hannunta ba.
"Tana da taurin kai da kasada......wonderful" Ya qarasa maganar yana maida idanunsa saman fuskar kawu rufa'i ba tare daya motsa daga yadda yake a zaune ba.
"To me zai hana ku bani aurenta a madadin kudin da kuka cimin kai da ita?". Tsananin mamaki da rudu ya sanya kawu rufa'i rikitowa daga saman kujerar sai gashi ya zube a qasa a gaban muhammad fu'ad
" Wallahi tallahi yallabai mun baka.....na yarda munci sadakinta harma da sauran kudin hidimar aurenta....."
"Oh.....da kana tunanin wani kudin daban zan lissafa na baku?" Fu'ad ya fada very calm yana dage dukka girarsa idanunsa akan kawun.
"Inaaa yallabai.....wane mutum?,wane aikinsa?" Ya fada yana jijjiga kai da kalar mamakin daya kasa sakinsa.
"Oya.....kaje ka shaida mata ka bada aurenta nan da sati biyu kacal masu zuwa"
"An gama ranka ya dade" Kawu rufa'i ya miqa kaman babbar rigar jikinsa zata tadeshi ya fadi ya durfafi qofa,jordan ya bude masa ya fice babu ko waiwaye bare ya tuna da Mikhail daya bari a ciki.
🔅Idanun bibo akan su maamah har suka fice daga gidan,saita dawo a gaggauce ta sake zama gefan daada
"Kin gansu can daada......don girman Allah daada ki dubamin zancan nan fa?". A karo na biyu daadan ta sake dubam bibo bayan ta dauke kai daga farantin zogalenta
"To wai ke meye naki a ciki bibo?". Kaman ta harari dadar sai kuma ta daure
" Haba mana daada,don ke yaro daya Allah ya baki yana can saudiyya baisan me ake ciki a qasar nan ba?,fisabilillahi ace duk kamammun 'ya'yanmu a rasa wanda zaa zo neman aure cikinsu sai wannan tambadaddiyar?"
"Duk tambadar tata kin gaya musu,kuma sunce sunji sun gani,ke meye yayi miki saura a ciki?" Daada ta sake jefawa bibo tambayar. Bata da amsa amma kuma bata gamsu har yanzu da cewa ta zuba idanu wannan abun ya tabbata ba. Iya leqen da tayi qofar gida taga motar da sukazo a cikinta ya sake dasa mata kwadayin duk yadda zatayi ta tabbatar likita hadiyya ce ta shiga wannan ahalin,saita miqe ta fita da sassarfa zuwa dakin Sabrin.
Duk su huda sun wuce ciki sunata qoqarin sauya uniform dinsu zuwa kayan gida,su kuma killace sauran. Tana nan zaune inda suka barta ta kasa koda motsawa wanda ita kanta batasan dalilin mutuwar jikinta da fargabarta ba.
Ciki ciki ta amsa sallamar bibo din,don duk sanda ta ganta a dakin ba wani ba wata,ba tantama ba alkhairi bane ya kawota.
"Ashe sun tafi.......lalatattu mutanen banza da wofi,haka ake zuwa neman aure?,mata ma da zuwa neman auren idan banda lalacewa?" Saita soma sakin kuka tana matse hawaye
"Allah sarki rayuwa......Allah ya jiqan alhaji da rahama,mutuwa me tonon silili,banda baka wai yau shine har wasu matan ke takowa gidansa da sunan nemawa diyarsu auren dansu?,yaron da ba'asan asalinsa ba?".
Idanunta sabreen ta lumshe sannan ta budesu lokaci guda,tana jin muryar bibo har tsakiyar kanta ne
"Don Allah ki fita.....banason hayaniya" Tayi zancan a nutse tana yamutsa fuska.
Haba bibo ta kama,yarinyar dake da wannan halin tun yanzu inaga ta shiga gidan arziqi har haka?,tabbas ba shakka sai inda qarfinta ya qare
"Wato abun arziqi ma bai karbi kare ba ko?,don inason kare haqqin zaman tare?,a gidan waye ya shigo miki bandani?,to kuwa muddin na haifu ga cikin sahura da labaran bazan sake shiga shirginki ba"
"Da dai yafi miki" Sabreen din ta furta qasa qasa tana jan qaramin tsaki sanda bibo ke fita a dakin gwiwa ba qwari. Taso taji sauran bayani daga bakin sabreen din yadda suka dade a dakin,taso kuma taji meye matsayar yarinyar akan mutanen.
𝗗 𝗨 𝗡 𝗜 𝗬 𝗔 𝗧 𝗔
𝙃 𝙐 𝙂 𝙐 𝙈 𝘼
𝙋𝘼𝙂𝙀 95
Wani zuzzurfan numfashi sabreen ta sauke,tana jin yanayinta gaba daya yana sauyawa. Tun daga tunaninta bugun zuciyarta dama komai nata. Zuwan mutanen ya kasa barin zuciyarta da idanunta har ma da kwanyarta.
"A ina suka sanni?,su waye su din ma tukunna?" Wadannan sune tambayoyi masu ban tsoro da kuma qara sanya mata firgici. Qasan ranta kuma zuwa yanzu takejin ya kamata tayi qaura daga ainihin inda aka Santa,ta koma wani bigire na daban wanda ba kowa yasanta a wajen ba don sake lullube kamanninta dama komai nata,tare da sake bad da sahu da dukkan wata alama da zata alamtawa masu farautarta inda take.
Saidai kuma......wani hanzari ba gudu ba,har yanzu tana tattalin MUTUNCI,har yanzu kuma tana matuqar girmama kalmar MUTUNCIN MACE.....kalmar da tayi imani tayi adabo da ita daga idanun mutane da yawa.
******Dukkaninsu shuru sukayi kai kace ruwa ya cisu. Ba abinda kawu rufai yakeyi sai sharce zufa tare da mutsu mutsu kamar wanda wani abu yake cizo. Gefe guda mutumin dake kusa dashi ya sake sauke zuzzurfar ajiyar zuciya,ya kuma miqe ya zauna sosai yana tura hularsa baya.
"Rufa'i.......baka da wata mafita akan buqatar muhammad jadda......"
"Ina naga mafita rabi'u?.....aini godewa Allah kawai nakeyi nake kuma sakeyi.....don na tabbatar inda wa'adin biyan kudinsa ya sanya mana da mun bushe.....wallahi bani kadai ba ba kuma Sabrina ba......dukkan danginmu qwanmu da kwarkwatarmu......waye zai iya fada dame kudi?,wa ya isa yaja dame kudi?,wahala ma kenan rabi'u" . Kai babban aminin kawu rufa'i yake jinjinawa,banbancin ra'ayi wajen sana'a shi ya kawo nisan alaqa kadan tsakaninsa da rabi'u din. Sam rabi'u baya hanyar caca ballantana yayita,suna kuma yawan samun sabani da kawu rufa'i akan hakan,wannan ya sanya indai kaga kawu rufa'i yayi shawara da rabi'u to babban al'amarine dake neman nutsuwa da hankali irin wannan.
"Yanzu abinda kawai yake damuna rabi'u......yarinyar nan Sabrina,bansan ta yaya zan bullo mata da batun maganar na bada aurenta ba......yarinyar ta fita zakka a cikin dangi kamar wadda akayi tsugunnon haihuwarta tsakanin fukafukan shaidan....."
"A'uzubillahi" Rabi'u yayi saurin fada yana dakatar da kawun
"Haba rufa'i......Sabrina fa 'yarka ce halak malak...."
"Na sani rabi'u.....na sani,Kai dai kawai ka barni......na fika sanin wacece ita,wallahi duk taqadirancina ta dameni ta shanye yarinyar nan......yadda kasan me gani har hanji akan maza.....tana iya zuqe tattalin arizqin kowanne d'a namiji idan taso tana zaune daga gida.......ka bani shawara rabi'u,yau daya sai nakejin ina shakkar tunkararta". Shuru rabi'u yayi na wani dan lokaci sannan ya gyara zamansa
"To a zahirin gaskiya dai aurar da Sabrina ba wani abu bane mummuna,asalima yin hakan tamkar taimako ne ka baiwa rayuwarta.....kuma a addinance kai din uba ne a wajenta da zai iya zaba mata mijin aure,to abinda nake ganin yafi kawai ka tunkareta da zancan.....sannan kabi dukkan hanyoyi na hikima ka kwatanta mata aure shine babban rufin asirin mace".
Shuru kawu rufa'i yayi tamkar me shakka ko kokwanto akan shawarar rabi'u.
"Har yanzu rabi'u bakasan yarinyar nan ba,kafaffiya ce me shegen taurin kai da rashin tsoro,idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya tanqwarata,bata tsoro shakka ko kuma shayi.....ba irin Sabrina bane ake zuwa musu da magana haka kai tsaye a hada da wa'azi da shawara ba kuma su dauka.......Sabrina rinduna ce da sai an fuskanceta da gayyar jama'a....amma dai kafin sannan zan gwada wannan din rabi'u "
"Zata aminta in sha Allah,kuma komai zaizo da sauqi"
"To Allah yasa" Kawu rufa'i ya furta ajiyar zuciya tana subuce masa. Shi kadai yasan kalar tashin hankalin da yake ciki,yayi nadamar sanin duk wani dan caca tun daga haihuwarsa kawo yau bare kuma har ta zame masa sana'a.
*****Shi daya ne tal tsaye cikin kitchen din,sanye da fararen tanks top da joggers masu taushi. Kunnensa daya yana maqale da earpiece yana amsa waya. Daga gefe guda kuma yana tsaye ne gaban wani qaramin cabinet yana ciro ganyen zaitun,ginseng wolfberry da zai dafa tea dinsa na musamman dasu,sannna ya jawo wai qaramin plate din daban ya zuba dabino teen da busashen inibi da ake kawo masa shi tun daga china bayan anyi packaging nasa a wata jar leda mai kauri.
Hankalinsa yayi nisa sosai wajen amsa wayar da dafa tea din,har baiji shigowar farouq ba,wanda ta qaraso dab dashi ya kumayi tsalle ya haye saman kitchen cabinet din kusa da plate din da fuad din ya zuba friut din,ya soma miqa hannu yana tsinta daya bayan daya yana jefawa a bakinsa gami da cilla qafafunsa yana duba wayarsa rabi da rabi,yayin da kuma lokaci bayan lokaci yakai kai dubansa ga fuad din.
Daidai sanda ya gama amsa wayar tea din nasa ya gama dahuwa,ya jawo kebantacciyar ma'ajiyar kyawawan kofunan shan shayi na tangaran.
"Nayi zaton baka shigo ba ai". Fuad dake zuba musu tea din ya furta ba tare daya kalli farouq ba.
"Na shigo tun dazu......na tsaya duba wasu baqi ne da abba yace na sauraresu don yayi nisa". Kai kawai ya jinjina,yayin da farouq ya maida dubansa kan cups din da fuad ke zuba tea din
"Amma dai bani ka zubawa ba ko?" Ya fada yana dan yamutsa fuska. Sai a sannan ya daga kai ya kalli farouq din.
"Ba dole bane sai ka sha......" Yayi maganar shima yana hayewa saman kitchen cabinet din tare dakai cup din bakinsa a nutse hankali kwance yana sipping.
Sosai farouq yake kallonsa kafin murmushi da yafi kama da dariya ya subuce masa
"Ina mamaki idan na ganka a kitchen......zai zamewa 'yan jarida babban labari idan sukasan muhammad jadda dinnan yana shiga kitchen da kanshi time to time"
"It's my hubby.........inason dafa tea dinnan da kaina.......na tabbatar bakasan amfanin wadannan ganyayyakin a jikinka ba da bazakayi wasa dasu ba". Yakai qarshen maganar yana sake maida cup din bakinsa.
"Inaso na koya......but bakina yanason dadi.....harshena ba irin naka bane" Yayi maganar yana nuna damuwa akan fuskarsa. Sake cire cup din yayi yana balla masa harara
"Ka zauna dadi ya kasheka......you know baka fini son girki me dadi ba......but lafiyanka a matsayinka na d'a namiji sama take da komai.....wait.....wai meyasa ma zan zauna inatayi maka wannan bayanin,do what you want,amma sanda kayi aure kada ka nemeni da shawaran komai". Murmushi ya sake kubcewa farouq,yana so yana kuma farinciki yaga ya sanya muhammad magana har haka,wannan dalilin ne ya sanya baya gajiya da tsokananshi,duk da ba kasafai yake biye masa ba.
"Kaine na hannun daman ango.....so that kai ya kamata na fara nema kuwa......"
"Baka da wani abu me muhimmanci ne da zaka fada?" Fuad din ya fadi yana kafe farouq da idanu. Dariya sosai farouq ya saki harda sunkuyawa kadan
"Da alama aljanar amaryarka ta iso,taji batun aure....."
"Farouq" Fuad yadan kirashi da husky voice dinsa.
"Times up" Farouq ya furta yana daga hannayensa sama
"I have something to talk about.......very serious" Farouq din ya fada yana gyaran murya kadan sannan ya maida fuskarsa serious,abinda ya sanya fuad shima ya bashi hankalinsa ganin ya koma umarul farouq dinsa na asali.
"Tun jiyan zuwa yau nake zuba ido da kunnen ka nemeni ko kayimin qarin bayani...."
"Akan me?" Fuad din ya tari numfashinsa.
"Akan yarinyar daka nema aurenta ta hannun kawunta a office dinka......kwata kwata ban fahimci meye shirinka ba......in fact ma duk wanda ya sanka dole abun ya sanyashi mamaki......how and when ka fara sassautawa ra'ayin riqau akan aure?,when kasan yarinyar har soyayyar da za'a iya aure ta shiga?,.....anya auren tsakani da Allah zakayi kuwa dude?"
Sassauta zamansa fuad din yakeyi,baisan murmushi ya subuce saman kyakkyawar fuskarsa ba. Murmushin da ya sanya farouq ya sanya masa qatuwar ayar tambaya ya sabbaba masa kafe fuad din sosai da ido.
Bayaso fu'ad din yaje ya aikata wani kuskure,yanason koma meye su bishi a sannu
"Banda kai dan rainin hankali ne dama ana auren wasa ne?.....da gaske aurena zaa daura mata,aure zan nema kaman yadda kuka nema kuke kuma neman naku....already ma gayawa wancan tsohon nata...two weeks ma nace masa badon ina nufin nan da 2weeks din nake buqata ba,zan daura mata igiyata kaman kowanne mutum......but....." Ya katse maganar yana durgowa daga saman cabinet din,sannan ya fara takawa zuwa bakin sink din kitchen din ya kunna tap yana wanke cup din. A mugun qagauce farouq yake kallonsa yana son jin qarshen labarin,ya sani tsaf zai iya qin qarasa masa ya barshi da guntuwar magana a ciki
"But what fu'ad......tell me mana?" Farouq ya furta cikin damuwa,danuwar data taba zuciyar fu'ad din har ya waiwayoshi bayan ya gama wanke cup din.
"I want her to lern the hard way.......she made a mistake data zabi taba kudin jadda company"
𝗗 𝗨 𝗡 𝗜 𝗬 𝗔 𝗧 𝗔
𝙃 𝙐 𝙂 𝙐 𝙈 𝘼
𝙋𝘼𝙂𝙀 96
Yayi maganar yana zube idanunsa akan farouq da mamaki ya fara saukar masa
"To learn what?fu'ad?......sai ka aureta ne sannan zata koya darasin rayuwa?". Wani dan qaramin murmushi ya saki,ya miqe tsaye sosai yana goye hannayensa har yanzu idanunsa akan farouq din
" Ba wata hanya me sauqi da zan sanyata ta barwa sauran mata masu irinta darasi sai ta wannan hanyar.....dole ta fuskanci hukunci.....dole ta gane yadda ta dauki kanta batakai can ba......dole ta karbi sakamakon mutanen data dinga sanyawa a masifa saboda rabasu da dukiyarsu data dinga yi ba dalili.....inason ta san meye rayuwa......tasan kokai waye kana da iya limit dinka a rayuwa.......abdus salam na tura mata amma tayi avoiding nasa........kaga inda tayi accepting dinsa da hukuncin zaizo da sauqi" Yakai qarshen zan can yana sakin hannayen nasa gami da juyawa yana nufar inda ya ajiye wayarsa.
"Let her fu'ad......"
"Am sorry bro....Definitely sai na nuna mata kuskurenta......na dauki wannan alwashin" Ya sake fada yana bude wayarsa.
Shuru farouq din yayi yana wani gajeran tunani.....yafi kowa sanin waye fu'ad.....yafi kowa sanin halin tsaiwarsa da kafiyarsa akan komai ma.....idan yace zaiyi ba gudu ba ja da baya
"Amma ta yaya zaka tunkari su abba da wannan maganar?".
" Kaman yadda kowanne me neman aure yake sanar da iyayensa mana......akwai wani abu sabo ne a ciki?" Yayi zancan kanshi tsaye hankalinsa kuma kwance ba wani haufi.
Duk da yasan waye fu'ad amma wannan karon mamaki yake sake bashi,yayi tsai da ranshi yana kallonsa kamar yadda shima shi yake kallo.
"Da wani abu?" Fu'ad ya furta yana dage dukka girarsa biyun. Kai farouq kawai ya girgiza,yama rasa me zaiyi?,murmushi ko takaici?.
"Idan naji wani abu daban daga wajen anni ko abba tabbas kaine" Fu'ad ya fadi ba tare daya kalli farouq ba daya sauko daga saman cabinet din shima.
Harara ya watsawa fu'ad din kaman zai idanunsa zaso fado
"Saika hanani fada din" Daga haka ya soma tattaki zai fice daga kitchen din
"Karka damu,koda ka fada din ai ba wani abun bane.....zan koya mata tarbiyya ne na kuma koya mata wadatar zuci da kame kai daga dukiyar al'umma......kaga ko ba komai zan samu ladanta ko?"
"Kai ka sani" Farouq ya fada yana qarasa fita a kitchen din,yanayin yadda yayi magana kuma ya sanya fu'ad sakin wani lallausan murmushi.
*****Tamkar tsakanin hajja da maamah din babu wani me sauran abun fada sanda driver ke wulwula saura dasu cikin baqar range Rover din mallakin maamah.
Ba wanda yace komai din har zuwa sanda maamah ta gaji da shurun ta gyara zamanta.
"Amma hajja abun yazomin a bazata,ya kuma dauren kai matuqa". Juyawa gefanta hajja tayi tana duban maamah data tsinke mata zaren nata lissafin da take hadawa tare da qoqarin ganin amsar lissafin ya fito daidai.
" A yadda bayaninta ya nuna......zata iya aikata komai muddin akan kudi ne.....hakanan kudin sune abu mafi daraja cikin idanunta......ya akayi ta wofantar da buqatarmu ta watsa mana qasa a ido?......duk da cewa ido ba mudu ba ai yasan kima.....duk wanda ya kallemu zai shaida irin daula da ni'imar da muke ciki". Wata ajiyar zuciya hajjan ta saki itama,ta zubawa waje daya idanu kafin tace
"Ni kaina abun ya dauren kai,kuma iyakar tunani na bamu shiga mata da wani abu da ba daidai ba" Tayi maganar cikin 'yar damuwa. A wannan gabar ita kanta nasara take buqatar a samu.....nasara takeso tazo musu......yarinyar zata zame mata tamkar wani tsani me tsananin sauqin da zai ciccibata ya zuwa matakin tata nasarar.
"Ba wani abun damuwa bane ba hajja......ita iya nata hasashen ta dojewa buqatarmu.....kina tunanin zan barta?" Ta jefawa hajja tambayar.
Duk yadda hajja ta saka idanunta cikin na maamah din don hango plan dinta akan yarinyar ta gaza ganowa,don haka ta dora da tambayar
"Wanne mataki kenan zaki dauka?".
"Matakin da shine mafi dacewa da ita,ki zuba idanu kawai ki jira cikar kwanaki ukun dana bata.....da kanta zata budi baki tace ta amince" Ta furta sanda motar ke tsayawa a farfajiyar gidanta,don haka ta saka hannu da kanta ta bude murfin tana fita hajja ta mara mata baya zuciyarta cike da wasiwasi.
Sun samu zuwaira ta kammala komai,ta cika table da kalolin abinci iri iri na alfarma,wanda duka cikin izzar maamah dince. Ba'a abinci kala daya a gidan,bata yarda wannan ba,daga breakfast lunch har zuwa dinner ana mata varieties of food ne taci wanda ranta ke ra'ayi tabar sauran.
Daki na musamman da aka kebe ta sanya aka shigar da hajja don ta huce gajiya kafin itama ta watsa ruwa ta sauya wasu kayan ta fito. Kamanninta da musaddiq suna fitowa sosai sanda take fitowa daga dakinta sanye da wata bubu gown me tsananin laushi.
"Yau nake sake ganin kamanninki da musaddiq fa...." Hajja ta fada tana murza awarwaro hannunta.
Murmushi kadan ta saki tana jan daya daga cikin Kujerun dining din ta hau ta zauna
"Tun duniya na kwance akance kamannina da musaddiq yafi yawa......shi wancan babanshi ya dauko.....ni kuwa ba?" Maamah ta hade zancan duka tana qoqarin daukan cup da zuwaira ta fara zuba musu lemo
"Uhmmm" Hajja ta fada tana kallon maamah,can qasan ranta tana jin wani abu.....tana kwatanta irin izza gadara da mulkin da maamah din zata zuba a duk sanda haqarta ya cimma ruwa
"Waya sani ma ko ta rufe idanu ta manta dake ta canza qawaye?" Wani sashe na zuciyarta ya jefo mata wannan tunanin.
"Ni kuma bari zanyi hakan ta faru?" Ta bawa kanta da kanta amsa
"Kinsan wani tunani da nayi" Maamah ta sake fada tana juya cokalin cikin abincin bayan barin zuwaira waje. Zuwairan da a yanzu tsananin kishi da tsanar hajja ke ruruwa qasan ranta,ganin farat daya hajjan ta rushe gwamnatinta,gwamantin da da ita aka fara fafutuka aka kuma dasa harsashin gininta.
"Zanyi magana da fu'ad a yau ko gobe.....zan sanar masa ya fara shirin aurensa nan kusa". Kallo hajja ta bita dashi
"Da wuri haka?,har yanzu bamu samu tabbacin amincewar yarinyar ba". Wani murmushi maamah ta saki tana saka lomar abinci na farko a bakinta.
"Sabrin qaramar alhaki ce a wajena.....bata isa ta tsallakewa tarko na ba......amincewar fu'ad tafi zama abu me wahala a gareni akan amincewar sabreen.....na rantse miki da Allah.....muna nan zaune dake zata kira da kanta ta furta ta amince". Maganganun maamah din a yanzu daure kan hajja sukeyi. A kafe yarinyar take,ba wata alama ta amincewa a tattare da ita har suka baro gidan,to wanne abune haka zai sakata sauya ra'ayi da gaggawa?.
"Indai kina da wannan tabbacin to tabbas tsarinki yayi". Hajja ta bata qwarin gwiwa,daga wannan kuma sai suka zarce da wata hirar ta daban.
******A hankali suke takowa ta tsakanin kyawawan shuke shuken da aka qawata kusan kowanne sashe na gidan. Baqin wando ne a jikinsa wanda bai qarasa idon sawunsa ba da kadan,sai shirt itama baqa me gajeran hannu,hakan ya bayyana murdadden damtsensa,kalar rigar kuma daya kasance baqa ta haska farara lafiyayyar fatarsa dake sulbi tamkar ta mace. Kadan kadan iska ke wasa da sumarsa daga hagu zuwa dama,wani lokaci yasa hannu yadan shafeta kadan. Ko daga ina kake muddin a daura dasu kake to tabbas hancinka zai iya dauko maka lallausan qamshinsa daya zauna sosai a jikinsa,ya kuma kama komai da yake mu'amala dashi,kama da wayarsa keys dinsa briefcase da sauransu.
Shi da farouq ne bayan fitowarsu daga ainihin parlor din abba wato alhaji hamza kibiya. Karo na farko kaf tsahon rayuwarsa daya gabatar da wata d'iya mace a matsayin macen da yakeso ya aura. Har a sanda suke takawa yanayin anni ya kasa barin idanunsa,can qasan zuciyarsa sai yakeji anya ya kyautawa wadannan dattawan guda biyu da suka karbi lamarin auren hannu bibbiyu da zallar farinciki?.
"Alhamdulillah.....alhamdulillah,Allah na gode maka daka gwadamin wannan ranar da raina da lafiyata.....wacce me sa'ar ce?,a ina take?,ya kuma sunanta?" Anni da qananun hawaye suma maqalewa ta fada tana kallonsa.
Sunkuyar da kansa yayi,sam bai dauka lamarin aurensa ya zaune musu a rai ba har haka saida wannan maganar ta taso,ko da wasa bai taba qiyasta zasuyi farinciki har haka da zancan aurensa ba,tunda duk sanda farouq ya sanyashi a gaba game da lamarin auren cewa anni take
"Ka shiga hankalinka fa......matar mutum kabarinsa.....komai komai nada nasa lokacin.....kar ka sake kiransa mijin aljana......yarona yana da ibadar da ba wata halitta data isa ta cutatar min dashi".
"Sunanta sabreen......kuma marainiya ce" Abinda yaji kawai farouq ya fada kenan. Kallon gefan ido ya yiwa farouq din,a nasa zaton zai tona asirin plan dinsa......sai baiyi hakan ba......amma ya jishi kuma yana isar da wani zance da baisan sanda suka yishi da farouq din ba.
"Dukkaninmu ya fimu iya shiri anni......yanason aje nema masa auren,kuma sati uku kawai yake buqata". Shuru suka danyi dukansu,don abun yazo musu a bazata. Sun dauka zaya jera ne tare da 'yan uwansa ayi komai lokaci guda?.
"Anni......komai na gininku ya kammala......da bude company da tarewarku duka duka sati biyu ne ya rage......ayimin afuwa idan abun yazo muku a gaggauce......inason ku zama wakilai akan komai kafin mubar nan din". Yayi maganar cikin sunkuyar da kai tare da mamakin me yasa farouq yin hakan?. Bazai iya qaryata farouq din ba ko yace ba haka bane a gabansu annin,dole ta sanya ya dora da nasa bayanin. Baida wani plan na a daura auren sam a yanzu,yanason ya fara sanya mata shamaki ne ta hanyar maidata property dinsa. Shiga ko fita saida izininsa,hakanan yana buqatar kowanne motsi nata ya kasance qarqashin umarninsa,matakin quntatawa na farko kenan da yakeso ya fara aiwatar mata wanda zai sanyata jin ta qasqanta,kuma ita din batakai inda take tsammanin ta kai ba.
Murmushi abba ya saki yana cewa
"Banda abinka ko a yau iyayenta suka baka ita ai bai haramta a daura muku aure da ita ba......zan samu mamanka a sanar mata ko akwai wanda zai zama nata wakilin wajen zuwa neman auren......zanyi magana da bangaren mahaifinka suma,in sha Allah bazai wuce wadannan satikan ba".
Har suka isa sashensa baice da farouq ci kanka ba,sai da suka isa falon. Qarasawa yayi gaban freezer a nutse ya bude,ya ciro ruwa me sanyi abinda yadan jima baisha ba,yau dole zaisha din saboda yadda tsarin farouq yazo masa a bazata,ya kuma busar masa da maqoshinsa.
Sai daya gama sha ya dire robar saman dining,ya kuma fara saukowa daga steps din dining din cikin tafiyar nan tasa me cike da ginshira.
Ba zato ba tsammani farouq yaji saukar waya sama cinyoyinsa,sannan fu'ad din ya tako gabansa ya tsaya hannunsa zube a aljihun wandonsa.
"Tunda kai ka tsara komai ai sai ka qarasa aikinka......ka kirayi wancan tsohon ka gaya masa yadda ka tsara din,don bani da lokacin masa bayani......lokacin kawai nace ka shaida masa.......sadakin aure kudin sanya rana da sauran bidi'o'i ya lissafa ya cire cikin kudadena da suke kwasa,canjin ya rubutasu aci gaba da lissafi har zuwa ranar da zan fashesu gaba daya......don ba wanda zaici kudin jadda ta wannan hanyar ya tsira".
Da idanu farouq yake binsa,dariya nason kamashi amma yana dannewa
"Amma malam ya kamata ka koyi ladabin magana zuwa yanzu,ko ka manta yanzun suraki yake a wajenka?" . Harara ya watsa masa da fararen idanunsa yana zama saman sofa
"Kaci gaba da gayamin haka,wataran zaka wayi gari da haqoranka a hannu" .
"Zaka aikata.......ai gwara da aka saka ranar auren 3weeks,kafin aljanarka ta dawo ta sanyaka kace ka fasa.....kaini koma wanne irin aure ne fa gwara kayishi,a qalla addu'ata bata fadi qasa banza ba,zaa yiwa aljana kishiya.....naci nasara" . Duk da baijin dariya ko wani raha sam a ransa.......amma saida maganganun nan na farouq suka sanyashi sakin wani miskilin murmushi kafin kuma ya waske kaman bashi ba.
Yana tsaka da cin abincin dare kiran ya shigo masa,ya daga wayar ya sanyata a hands free yana adduar koma waye ya kirashi Allah yasa alkhairi ne.
Tunda farouq ya gabatar masa da kansa gumi ya fara yanko masa,gaba daya yaji abincin ya gundureshi ya fita a kansa,sai ya tsame hannunsa daga ciki ya miqe tsaye yana sauraron farouq jikinsa yana kyarma
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 97
"To.....to shikenan......in sha Allahu zan shaidawa dangin uwarta.....to Allah ya nuna mana....to godiya nake a gaida alhajin". Ya qarasa fada jikinsa yana rawa wayar kaman zata sulale ta fadi
" Na shiga uku na lalace ni rufai" Ya fadi a sarari yana zama dabar saman Kujerun da kwana uku kacal da zubasu sumame daga jadda company ya riskeshi. A da mugun laushin Kujerun yake ji,amma a yanzu yana jjnsu tamkar kujerun da aka sarrafa da bishiyar qaya.
Kansa kawai yake mirginawa daga hagu zuwa dama. Duk da ya iya tijira ya kuma iya tubura,amma wannan karon sai ya tsinci kansa da tsananin shakkar yadda zai tunkari sabreen din ya gaya mata ya bada aurenta a madadin kudin cacar wasu da yaci,da kuma nata kudaden data kwasa.
Bata iya doguwar magana ko rashin kunya irin na 'yan uwanta ba.....amma idan tayi maka wani abun har sai ka gwammace baki ta bude ta gasa maka rashin kunyar.
"Yanzu meye mafita?" Ya fada a sarari yana juya hannaye irin na wanda ya banu ya lalace,daidai nan matarsa umma asabe tayi sallama ta shigo dakin.
Kusan duka wayar da farouq din keyi da kawu nashi hankalin yana kan news da suke hasko faduwa da tashin hannuwan jari a kasuwa a yau din. Yaji suna sallama da kawu rufai din,sai wayarsa dake ajiye a gefe ta dauki ruri.
Kamar kowanne lokaci da bayyanar sunanta saman fuskar wayarsa ke sanyashi jin wani iri haka ma yanxun. Ya miqe ya zauna sosai yana sauke qafafunsa dake harde a dazun,ya daga wayar ya saka a kunnensa yana yin sallama.
"Wa'alaikumussalam..."
"Barka da dare" Ya fadi a nutse yana qoqarin saita kanshi.
"Barka kadai......idan kana gida ka shigo yanxu inason yin magana da kai". Dan shuru yayi kafin ya amsa a taqaice da
"Okay" Amsawar tasa ya bata daman katse kiran,ta ajiye wayar tana sake hada kalaman da zata tunkareshi dasu.
Kaman bazai motsa ba sai kuma ya miqe,farouq ya miqa masa dayan wayan tashi
"Mun gama magana......"
"Ba wani abu me muhimmanci a ciki da saika sanarmin......ka riqe duk bayanansa zasuyi maka amfani wajen qarasa plan din daka tsara". Dariya farouq ya saki yana lumshe idonsa,ya kuma sake relaxing abunsa sosai cikin kujera
"Hakanma ni yayimun.....zakaga kalar tawa ja'irartar". Bai amsashi ba ya soma wucewa inda flip-flops dinsa ke jere nau'i daban daban cikin wata ma'ajiyar takalma dake bakin qofar shigowa falonsa,ya miqa hannunsa kan wanda ya fara gani,ya zarosu ya sanya a qafarsa ya buda qofa ya fice yana jin wata fargaba haka kawai tana saukar masa wadda baisan dalilinta ba.
Yau ma gidan ba kowa,banda malam saidu daya bude masa qofa suka gaisa ya wuce ciki.
Ita daya ce hakimce saman lafiyayyun kujerunta,falon bai cika hask sosai ba sai haske fitilun da aka qawata ginin POP din dake saman falon.
Da murmushi a Fuskarta ta amsa sallamarsa tana tashi daga kashingidar da tayi ta zauna sosai. Ya zare takalmansa ya barsu daga nan sannan ya qaraso ciki.
Kaman kowanne lokaci,ba kasafai ya fiya zama saman kujera ba idan ya shigo falon yauma haka,sai ya samu daura da inda take zaunen ya zauna yana tanqwashe qafafunsa kamar me shirin fara cin abinci.
"Bari na samo maka ruwa tukunna". Ta fada tana miqewa sannan ta wuce cikin kitchen. Bai dakatar da ita ba don gudun ballo wata rigimar daban kuma,saidai bayajin ko a gabansa akayi aikin ruwan zai iya aminta yasha shi. Kansa ya daga kadan yana kallon falon da ainihinsa nan din dakine na mahaifinsu ciki da falo......dakin da ya rayu yasha jiyya a cikinsa har ya koma ga mahaliccinsa.....dakin da nan ne waje na qarshe data sanya qafafunta ta tsallakesu ta fice......dakin da anan sukaci gaba da zama shi musaddiq da jadda cikin talauci har itama jadda ta tafi ta barsu. Yau ga dakin ya zama wata qawatacciyar duniya.....saidai wadanda suka cancanci suci arziqin abun sunyi qaura sun barwa wani sashe da basu da alhakin samun gajiyar abun.
"Bismillah" Ta fada tana dire masa tray din sannan ta koma saman kujera ta zauna. Idanunsa ya lumshe da suke masa wani irin radadi sannan ya budesu,ya miqa hannu ya dauki gorar ruwan swan ya balleta ya tuttula a cup ya dauki cup din kawai ya riqe a hannunsa
"Tashi ka koma saman kujera ka zauna sosai magana nakeso muyi dakai me matuqar muhimmanci" Tayi maganar tana soke yatsunta cikin na juna tana sassauta sakin Fuskarta zuwa daurewa.
Kallo daya tak yayi mata,sai ya dire ruwan ba tare daya ce komai ba ya miqe din ya zauna saman kujerar dake fuskantarta.
"Muhammadu" Ta kirashi kai tsaye da zallar sunansa,kiran da ya saka gabansa faduwa abinda ya mance rabonsa da yajishi
"Na'am" Ya motsa tausasan labbansa ya amsa da wata murya can qasa.
"Wacece ni a wajenka?" Ta jefa tambayar a gareshi tana kafeshi da idanuwa.
Jin abun yayi yayi masa banbarakwai kawai,yana ganin amsace bayyananniya ai da ba sai anyi dogon neman amsa ba.
"Mene ya kawo wannan tambayar maamah?" Ya fada a sanyaye
"Akwai.....amma kafin sannan inaso naji amsa daga bakinka.....don komai da zai taso daga baya din yana da alaqa da kalar amsar daka bani" Qasa yayi da kansa ransa da zuciyarsa suna sake jaddada masa tabbas akwai wani abu.
"Mahaifiyata ce ke" Kai ta jinjina tana jin alfahari,tana jin kalmar har tsakiyar ranta,zamowa mahaifiya ga mutum irin Muhammad jadda ba qaramar takar sa'a bace ga kowacce mace.....ba qaramin zamowa riba bace ga kowacce uwa me haihuwa.....ribar qafa ce ta kowacce bangare.
"Shikenan......akwai buqatar da nake da ita daga gareka.......kuma umarni ne zan baka,bawai roqo ko neman alfarma nakeyi ba......ina magana ne da harshen uwa kuma mahaifiya........ba me cin alfarma ko darajar kowa ba cikin duniya......ina magana ne da baki na uwa wadda haihuwa ta karramata da wannan darajar..." Tayi maganar a jere cikin sauti da yanayin da ya sanya yaji kowanne noti na jikinsa ya qarasa kwancewa
"Wacce irin nannauyar buqata ce haka?" Ya samu bakinsa da subucewa yana tambayarta ba tare daya shirya hakan ba don dai kawai kunnuwansa sun kasa jumurin jiran jin me zai fito daga bakinta.
Gajeran murmushi ta saki tana gyara zamanta
"Na godewa Allah da tun yanzu ka gane girman buqatar uwa akan d'anta.......muhammad" Ta sake kiransa da sunan nan dake masa girma da nauyi.
"Ka jima kana bijirewa umarni na.....kana sabawa Maganata......ka dade ina fadin magana kana taketa,kana mata riqon sakainar kashi......ina dauke maka kai,ina maka kara ina maka alkunya......ina maka sassauci irin na uwa......ina da tarin buqatu......ina da tarin burika.....ina da mafarkai da yawa da nakeso na cikasu amma dukka ban samu wannan damar daga gareka ba.....a yanzu ina da wani babban mafarki akanka na samu macen auren dake sonka ba don dukiya ko abinda ka mallaka ba,macen auren data dace dakai ta gari wadda zata zauna da kai da zuciya daya......wannan damar da ita nayi amfani na laluba na kuma zaba maka nagartacciya guda daya......wadda nakeso kai tsaye ka karbeta saboda umarni ne nakai tsayen daga uwa zuwa d'anta!" Ta qarashe maganar da kakkaifan harshen daya sanyashi wata matsananciyar faduwar gaba da bai taba jin irinta ba
"Ya ilahal aalameen" Ya furta a zuci da bakinsa murya can qasa. Wanne irin lamari ne haka katsam lokaci guda?. Matar aure fa take magana maamah din......maamahn da bata gama zama nagartacciyar uwa cikakkiyar garkuwa ga 'ya'yanta ba ta kowacce fuska?,yaushe zata samu nagarta fahimtar nagartacciya cikin mata?.
"Maamah......aure ba abun wasa bane,aure ba tafiya ce ta yau kuma a kammalata gobe.....aure abune da akeso mutum biyu su gani su kuma aminta......"
"Dakata Muhammadu!!!" Ta furta a tsawace tana daga masa hannu.
"Ka manta a farkon zance na?,na gaya maka ba neman shawara nake ba?,hukunci na yanke ina gaya maka hukincin ne saboda kasan da wanzuwar abun.......zan nema dangin mahaifinka koda mutum qwara daya ne,da nawa ahalin mutum uku a ciki,su kadai sun isa suje neman auren.......bana buqatar komai naka a ciki......bana buqatar sisinka,zanyi komai.....abu guda daya tal nake buqata" Tayi maganar tana daga yatsanta dan manuni.
"Ka kula da ita yadda zaka kula dani mahaifiyarka......ka bata kulawa ka tattalata kamar yadda kowanne d'a namiji yake tattala mahaifiyarsa da 'yarsa da matarsa......idan kanaso ka hadu da mummunan fushi na kuma kalar wanda baka taba gani ba......ka gwada tsallake wannan dokar" Wani irin mawuyacin hali yaji yana neman fadawa,lokaci daya taji tamkar an daga duniyarsa ne an kifata daga sama zuwa qasa,yayi qoqarin tattaro muryarsa a raunane yanason sake fahimtar da ita,don shi ba abinda ya fahimta a wannan abun face wani kitsatse kuma shiryayyen al'amari da muddin ya rufta ciki rayuwarsa kaf yana hango rugujewarta
"Amma maamah......"
"Muhammadu.......muddin kace zaka gwada bijiremin.... To ka jira tsinuwa daga gareni da zata biyo baya......zan daga maka nono......zan maka Allah ya isan nonona daka sha?!!". Qas yayi da kansa yana jin wata zufa tana keto masa,duk kuwa da wadatar ac dama pan dake kadawa a hankali.
Jin jikinsa da kansa yakeyi gaba daya kaman ba nashi ba......yanajin kaman gini me hawa goma ne ya lafto saman kansa. Bakinsa yayi nauyi qwarai,yaji bashi da wata sauran kalma data rage masa.
"Kiyi haquri" Ya fada a mugun raunane.....raunin da a sannan idan abokan adawar kasuwancinsa suna wajen zasu rantse da Allah ba muhammad jadda bane.
"Naji......tashi kaje ka fara shiri" Abinda tace dashi kenan wani dadi yana ratsa qasan zuciyarta ganin alamun nasara baro baro a tare da ita. Zuciyarta fari tas sanda yake fita,tana jin wannan karon sa'arta ce,lokacin sa'arta yazo,sabreen kawai ta rage mata,sai kuma ta koma wajen boka ya hada mata dukkan kayan sa'a,ya bata kuma manya manyan bomabomai din da zata bawa sabreen ta shiga gidan dasu masu qarfin da sa'arta zata qarasa cimmata nan da nan.
Da qyar yake jefa qasarka gaba yana nufar gidan ba tare da cikakkiyar fahimtar inda yake sanya qafar tasa ba.
"Wannan wanne irin tashin hankali ne?,wanne irin shiri ne kuma daban wannan bayan shirinta nason ciyar da su da shayar dasu da kayan tsubbu da suka kaucewa hanya sunna da kuma koyarwar musulunci?" Ya yiwa kansa da kansa tambayar sanda yake zubewa saman kujerar falon kowanne sashe na jikinsa yana mutuwa.
"Wanne shiri ne daya wuce ta ajiye maka wadda zata baka komai kaci ka kuma sha kai tsaye ba haufi?,wadda zaku rayu tare qarqashin rufi daya?,ta yadda komai zaifi sauqin kama ka?"
"Yes!" Ya samu kansa da fada bayan dogon nazarin da kwanyarsa ta tafi me dogon zango.
Ba shakka kusan duk wanda ya sani tare da maamah babu wani halin dattako ko na alkhairi sam sam tare dasu,ta yaya maamah din har zata iya cimma MAR'ATUSSALIHA da irin wannan halaye da dabi'u nata?. Tsaftatacce sai tsaftatacce fa haka qur'ani ya fadi Allah da kansa kenan yake bamu labari.
"Wacce yarinya ce ke shirin jefa rayuwarta tsakanin runtsin da yafi qarfinta?,wacce yarinya ce wannan?" Yayi tambayar a fili yana qanqance idanunsa.
Anaso ayi amfani da maamah ne ko kuma maamah din keson amfani da wasu?. Ya sake tambayar kansa da kansa yana sake zurfafa nazarinsa wanda yaji kaman kansa zai tarwatse,sai yaji me yasa bai tsaya ya nema cikakken sani akan wacece ba?,sunanta?,d'iyar wace?,a ina take?. Yanaso ya sani da gaske.......yana buqatar sani,amma kuma bayaso yayi kowanne motsi ko taku da zai sanya maamah ta sake tsaurara aqidarta a kansa.
Tana a wajen tana juya girman nasara takun farko data fara samu ita da matar da takewa kallon aminiya wato hajja,ta kuma neman alfarmar ta shirya don rakata wajen boka nan da kwanaki biyu ko uku kafin masu neman auren sabreen sukai ga magabatanta saiga zuwaira ta shigo.
"Alhaji hamza ne yake son magana dake". Sosai zancan ya bata mamaki,ta dauke wayar daga kunnenta tana kasheta gaba daya cike da madaukakin mamaki. Alhaj hamza yau a gidanta?. Bai taba tako koda qofar gidan ba koda kuwa da wasa tunda ta dawo gidan da zama karo na biyu......ko a baya ma ba zata iya tuna sanda irin haka ta faru ba sanda marigayi yana da rai ballantana yanzu.
"Alhaji hamza kuma?" Ta sake jaddada tambayar ga zuwaira.
"Eh shi".
"Ce masa ya qaraso ciki,faduwa tazo daidai da zama......nima nemansa nake" Tayi maganar tana hade ranta da kyau tun Alhaji hamza din bai kai ga shigowa cikin falon ba,zuciyarta tana raya mata indai har daga fitar fuad ne yaje yakai masa qararta lallai sai ta saka sunyi nadama daga shi har fuad din. A wannan karon zata nuna masa shi da munafukar matarsa.....dama sauran dukkan munafukan dake gefe suna kallo cewa,itace fa ta haifi fuad harma da musaddiq......babu wani da yayi mata wahalarsu.......babu wanda kuma yasan ciwo da zafinsu sama da ita.
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
̶H ̶U ̶G ̶U ̶M ̶A
◦•●◉✿PAGE 98✿◉●•◦
Cikin sallama da kuma cikakkiyar kamala ya shigo falon. Kujerar da tafi kusa da bakin qofa ya zauna tare da bismillah a bakinsa.
Ciki ciki ta amsa tana gyara nata zaman gami da harde qafarta ta dorata daya bayan daya don nuna izza da tata isar.
Bata jin zata iya gaidashi ko gabatar masa da wani ruwa ko lemo wanda mutumin dake da kima da martaba kawai akewa haka,sai ta jefa masa tambayar
"Ina fata lafiya ce ta kawoka.....sannan ina fatan alkhairi ne ya sanyaka takowa cikin gida na?". Wani murmushi ya sake dake cike da kamala da dattako. Shi ba mace bane,saboda haka bayajin yana da wani lokacin bata lokacin gutsi gutsin maganganu
"Batun d'anki kuma d'anmu shine ya taso dani....."
"D'ana dai....."
"Hakanma yayi.......jiya ya sameni da zancan samun matar aure da yake buqatar aje nema masa ita,kuma cikin qasa da sati uku yakeso a kammala komai".
Wani murmushi ta saki tana kada qafarta,shuru na kusan minti daya sannan ta soma magana cike da izza.
Malam hamza......ita kuma wacece?,a ina take?,shi yace yanaso ku kuma aura masa akeso ayi?.....koda yake duka wadannan tambayoyin basu da wani amfani......na yiwa d'ana mata.....kuma nan da sati uku in sha Allah ya zama magidanci,saboda haka ba wani batun wata yarinya da zan karba" Tayi zancan tana sauke qafafunta data harde.
Cikin son hadiye dafin maganganunta ya dubeta da duba na tsanaki
"Kin manta cewa a addinij islama muke ba wasu addinan na daban ba?.....laifi ne idan kin aura masa wadda yakeso shima ya auri wadda yakeso duka a lokaci guda mariya?". Yayi maganar hankali kwance yana tsareta da ido.
Kallonsa takeyi itama,saidai kaifin nasa idanun ya shafe nata,don haka ta nanye dubanta a kansa tana jin sam sam bata aminta da wannan zancan nasu ba. Zuciyarta kawai tana bata wata qulalliyar ce.....sun nemo masa mata ne kawai bisa hadin baki suna son cusa masa don a samu damar cin dukiyarsa da lasisi (ni kuwa nace uhmmmm.....idan mutum yana aikata abu sai ya dauka kowa ma haka yake?🤔🤔....kaico da uwa irin maamah).
"Koma wacece ni uwa ga Muhammed fuad ban karba ba ban aminta ba". Ta fada tana tura dankwalin kanta gaba.
Shuru ya ratsa na wasu mintuna,tamkar bazaice komai ba sai kuma ya miqe tsam
" Zai auri zabinki.....kamar yadda ba wanda ya isa ya hanashi auren zabinsa......abu daya ya rage miki ki bada komai akan yarinyar zamu binciki waye mahaifinta......idan har ta cancanta.....zai auri mata biyu a rana guda.....zabinsa da zabinki.....komai bazai wuce kwanaki hudu ba,don haka ki sanar da iyayensa bangaren danginki don a fita haqqin kowa dake kansa". Daga haka ya juya yana takawa a nutse yana fita a falon.
Miqewa tayi tsaye tana bin bayan nasa da kallo,Zuciyarta na wata irin tafasa,ta yaya kansa tsaye da wannan confidence din yakeson nuna mata qarfi da iyakarta akan abinda duk duniya tafi kowa iko dashi?.
"Ba zata sabu ba" Ta dauki wayarta da sauri tana kiran hajja.
"Daga hankalin na meye?,koma wace muna da boka,fiddata bazai zama wani abu me wahala ba.....ki bashi kwatance gidan da sunan mahaifinta na ainihi.. ..kibi a hankali ki zuba masa idanu......wannan karon harshi sai munyi maganinsa"
"Na gode aminiyata......duk duniya bani da masoyi kamarki"
"Yiwa kaine ai" Ta fada da binnanniyar ma'anar da ita daya ta barwa kanta saninta.
*****A mamakance yake riqe da takardu biyun a hannunsa yana dubansu. Gyara zamansa ya sakeyi sosai sannan ya daga kansa ya kalli anni dake zaune a gabansa
"Abunne yaketa bani mamaki aminatu.....yarinya daya ce shi da mahaifiyarsa duka ke fatutuka fa". Dan muskutawa kadan anni tayi tana daidaita zamanta.
"Ina cikin damuwa abba tun randa kace maamah ta zabawa fuad matar aure......bamusan ya zata kasance ba yarinyar.....to amma yanzu kuma na shiga rudani ne,ya akayi dukansu suke neman yarinya daya cikin rayuwarsa?". Shuru abban ya danyi,sannan ya ninke takardar ya ajiye a gefansa yana sake dubanta
"Ina aminatu?" Dan murmusawa kadan tayi saboda shi kansa yasan wannan sarar tasa tana bata dariya
"Gani abba"
"Yauwa.....abu na farko da nakeso ba gaya miki shine......ki dinga tunawa mariya itace mahaifiyar Muhammadu na ainihi,ita ta dauki cikinsa tahaifeshi ta kuma reneshi na wasu shekaru kafin ya dawo hannunki.....dole haqqin dake wuyansa nata yafi naki.....sannan so na uwa daban yake,duk yadda kikeso ki kawar masa da abu me cutarwa akwai guraren da ba huruminki bane shiga cikinsa"
"Abba nafi mariya qaunar me babban suna....." Wani murmushi ya saki yana girgiza kai
"Kin fita sanin ya kamata ne,kin fita kuma tausayin dan adam da qaunar yara koda ba naki 'ya'yan bane.......mu ajiye wannan.....abinda nakeso dake......a baya kafin bincike ya zamaya ya fito daga gida daya nima ina da wannan shakkar da kokwanton,saidai kuma ba hurumina bane na hana.....bugu da qari na samu relief da naji shima itace yarinyar da yake nema din,koda mariya da tata manufar na hadashi da yarinyar.....to shi ba yadda za'a yi ya cutar ai da kansa da kuma tasa rayuwar......abun tambayar qwaya daya ne kawai dana gaza banbancewa........ya akayi dukkaninsu sukasan yarinyar?,kuma dukkansu suka afu a kanta?,wanda samun amsar shima na huruminmu bane.....don muhammad yakai munzalin baligi kuma aqili da bazai dauko abinda zai cutatar dashi ba".
Kai kawai anni ke kadawa,maganganun abba suna gamsar da ita,daga bisani da saki nannauyar ajiyar zuciya
"Haka dukka maganganunka suke abba....daga yau in sha Allah bazan gushe ba ina adduar idan akwai sharri cikin lamarin.....ubangiji al'arshi ubangijin sammai ya juyar dashi ya koma alkhairi,ya kuma tsare dukkan wani sharri"
"Yau aminatu na......yanzu kikayi magana me kyau" Sai ta saki murmushi tana jin kunya tana dan kamata,don har yanzu girma tsufa ko shekaru basu sanya wannan kunyar dake a tsakaninsu ta gushe ba.
****Shudewar awanni uku kenan da wata murya tayi kiranta,ta kuma shaida mata cewa kirane nakai tsaye daga gurin hajiya mariya akan batun neman aurenta,ta aminta ko aje zuwa mataki na gaba?.
Duk da batasan meye ainihin abinda suke nufi da mataki na gaba ba,amma hakan bai hanata sauke saqo da kakkausar murya ba.
"Idan tana saurare shikenan.....idan kuma saqo zaki isar mata ki tsaya ki saurari komai dakyau don kada kiyi batan koda harafi daya wajen isar mata da saqona......ni aminatu sabreen ba haja bace a kasuwa da kowa zai iya tayata da farashin da yaga dama ya kuma siya,'yantacciyar diya nake ba baiwa ba wadda keda daman zabawa kanta komai da kuma kowanne yanayi na rayuwa......da ita da d'anta dama dukkan dukiyar da suka mallaka basa gabana koda kuwa zasu mallakamin dukkan abinda suka mallaka din.......ki gaya mata kada ta sanya ran wataran akwai abinda zai canza ni......ba wani abu da zai sauya tunani na akan maza......ba d'anta bama kawai.......har yau ba'a samu nasarar Haifa min wanda zai janye ra'ayina naji ina da niyya ko sha'awar ya zama mijina".
Sosai kalaman suka daki maamah wadda ke zaune a gefe tana sauraron komai. Ba zata iya jurar jin wadannan nauyayan kalaman ba,don haka ta miqa hannu ta gintse kiran cikin wani matsanancin fushi,sannan ta dauki wayarta tana laluben wata number tana cewa
"Zaki fahimci cewa komai yana da nasa iyakar".
Numfashi ta zuqa tana duban agogo,sai tayi zumbur ta tashi ta zauna. Batasan yaushe lokaci yaja har haka ba,batayi sallar azahar ba don haka ta miqe tana sanya slipper ta nufi tsakar gidan nasu.
Yadda taga kusan kowa da kowa cikin yara da jikokin gidan sun dawo sai ya dauki hankalinta. Su huda kusan sune sahun farko da sukafi kowa dawowa gida akan lokaci,ya akayi yau suka zama na qarshe?. Tun tana daura alwala take sanya ran shigowarsu amma shuru,ta kammala ta wuce daki,ta tayar da sallah ta kammala,sai tayi zaune a wajen tana zuba kunnuwa.
Shuru maqatau,abinda ya sanyata miqewa kenan gabanta yana faduwa. Basu taba kai warhaka a makaranta ba,har gashi masu zuwa islamiyya cikin gidan sun fara wucewa,sai kawai ta dauki wayarta da key din dakin ta fito.
Layukan nasu ta duba amma babu su,abinda ya tsananta faduwar gabanta kenan. Ta dauki wayarta zummat nemo busari yazo ya dauketa suje makarantar sai gabanta yayi wani mummunar faduwa sanda idanunta suka sauka kan number wayar da aka kirata dazu. Tunanin ya sake bnagazar Zuciyarta abinda ya sanya qafafunta yin sanyi qalau,ta sulale tana zama saman dakalin dake daura da ita hannunta yana yin sanyi qalau.
Wayarta taci gaba da kalla tana kuma taya agogon dake fuskar wayar irga wucewar kowanne second,har zuwa sanda ya nuna mata qarfe biyar daidai harda rabi na yammaci sai kawai ta danna kan number ta kira.
Kira ta dinga yi ba qaqqautawa amma ba'a daga ba,yayin da duhun dare yake sake kusantowa,yan islamiyya da wadanda na sukaje kasuwa sunata dawowa suna giftata kowa idanunshi a kanta don bash saba ganinta haka zaune a waje ba,wanda ita sam bata damu da hakan ba,har zuwa sanda kallon da yawan kiran suka soma quntata rayuwarta,saita miqe tana komawa cikin gida afujajan cikin matsanancin tashin hankali.
"Indai tayi kuskuren sanya min 'yan uwa cikin harqallar da daga ni sai ita......tabbas sai na shayar da ita mamaki koda hakan shine abu na qarshe da zanyi a rayuwata" Ta furta a sarari ganin yadda duhu ke sake kutsowa ba'a daga wayar ba ba'a kuma biyo kiran ba.
Sanda ake haramar kiran sallar ishai,sanda take zaune kan abun sallah ta bada faralin magariba cikin rashin nutsuwa da tashin hankali tare da zurfafa tunanin inda zata kamo bakin zaren kiran ya shigo wayarta.
Duk da kirana ne da take ta dakon shigowarsa amma bata daga ba sai dab da zai tsinke.
"Ki sakesu.....don su din basusan komai akan rayuwata ba".
"Good......naji dadi nayi kuma farinciki,haka kwanyarki take ja da wuri?" Hajja harira ta fada cike da mamakin gaske kan yadda ta dauki haske da wuri. Lalle da gaske ne da akace musu tana da basira tana kuma da hadari.
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
̶H ̶U ̶̶G ̶U ̶M ̶A
◦•●◉✿PAGE 99✿◉●•◦
Idanunta ta lumshe tana jan wani numfashi har cikin hunhunta,tana jin wani zafi baqinciki da radadi suna ratsa zuciyarta.
"Ina sake maimaitawa.....kada kuyi involving innocent lives a cikin wannan deal din......ku sakesu safely".
"Karki damu yarinya.....qannanki zasu dawo hannunki cikin aminci..... Munyi hakanne kawai don mu gwada miki banbancin tazarar dake tsakanin sama da qasa......don kuma mu nuna miki girman wutar da kikeson wasa da ita kike kuma tunkara ta hanyar bijirewa umarninmu"
Sake lumshe ido tayi,maganganun hajja suna ratsata ranta yana sake baci
"Ku sakesu" Ta sake maimaitawa muryarta cike fal da bacin rai. Ta nason fadin abubuwa masu yawan gaske,saidai kuma tana qoqarin tausar zuciyarta. Ta sani ta riga data shiga hannunsu,sun mata shigar sauri,sunyi mata kuma shigar ba zata,dole tabi komai a sannu,dole itama ta shammacesu kamar yadda sukayi mata suma.
"Zamu sakesu amma bisa sharadin kin amince da buqatarmu?......"
Wani yawu me tauri ta tattaro a bakinta ta hadiyeshi da qyar. Baya cikin tsarinta QARYA amma yanzu ya zama dole ta fara gwadata akan mutanen
"Na yarda" Ta fada kanta tsaye. Murmushi hajja ta saki sannan ta sake cewa
"Kada fa kiyi tunanin kin amince don ki yaudaremu mu sakar miki yan uwa haka siddan.....lalala.......kina iya karya alqawarin,amma ki sani daga wannan lolacin daga kuma rana irin ta yay rayuwarku tamu ce,ba wani motsi ko taku da zakiyi ba tare da munsan ina zaki ko ina kika nufa ba.....ko yaya muka sameki da laifin yunqurin karya wannan amincewa da kikayi daga yau har zuwa ranar da zaki kammala aikinki.....hukuncinki abune da bazai fadu ba,na barki lafiya" Daga haka kiran ya yanke.
A hankali wayar ta sulale daga hannunta,wanne irin abune kuma ke shirin tunkaro rayuwarsu bayan tarkuna data tsallake masu tsananin girman hatsari?,su waye ne wadannan mutanen?,me suke nema da rayuwarta?,me yasa basu hango kowa ba sai ita?. Take idanunta suka sake dawo mata da fuskokinsu.
Fuskar hajja a farko,ta tabbatar a yanzu haka ita uwar wasu ce......me yasa duniya ta cika da masu son zuciya da masu son rai?,a yadda take uwa tayi imanin ba zata taba bari wani aibu ko abu me cutarwa ya samu yaranta ba..... to amma me yasa su take qoqarin ingiza rayuwarsu zuwa ga wani bigire?,don ba itace ta haifesu ba?,kenan kowa dansa ya sani?,wai shin a duniya WAYE ZAI RUNGUMI MARAYA IRIN RUNGUMAR DA UWA KEWA DANTA NE?.
A hankali kuma sai tunaninta ya hasko mata fuskar maamah. Har yanzu bata yarda ita din uwa bace ga yaron da take nemawa aurenta.......idan kuwa har hakan ya kasance da gaske ita uwarsa ce?tabbas tata lalacewar ta dara ta hajja. Me yasa take mata famfo akan danta ba zata tayata ta inganta masa rayuwa ba?,me yasa idanunta suke rufe akan cikar qazamin burin da batasan inda zai kaita ba. Wadannan tarin tunane tunanen su suka zaunar da ita adadin lokacin da bata sanshi ba.
******Dukkaninsu ta sanyasu cikin jikinta ta rungumesu tana sauke ajiyar zuciya a tare da hadiyar wani abu wani yanayi yana tsargawa a dukka sassan jikinta washegarin ranar da tayi zaune tana dakon ta inda zasu shigo. Dukkaninsu cikin abaya masu tsananin sulbi da tsada. Nadra da haneefa sun kasa daina bata labari tamkar wadanda sukayi balaguron alkhairi. Da alama zuciyarsu da hankulansu basu riski wani abu mara kyau ba a zahiri da zai ankarar dasu hadari suka fada ba.
"Suna da kirki adda.....wannan kayanma su suka siya mana fa bayan kowa ya zabi irin wanda yakeso" Nadra da kanta ke jikin Sabreen ta fada
"Munci kayan dadi sosai adda.......dakin da muka kwana me kyau sosai shima,harda Ac da komai da komai" Haneefa ta fada cikin zumudin gaske tana riqe box na chocolate dinta da kyau farinciki muraran cikin muryarta.
Idanunta ta mayar kan huda,ita daya ce kawai a zaune ta zubawa Sabreen idanu,tunda kuma suka shigo itace bata ce komai ba a cikinsu. Duban tsakiyar idanun hudan tayi ta karanci lallai nata feeling din akan mutanen yasha banban dana 'yan uwanta,zataso taji meye a zuciyarta?,meye nata hasashen. Zataso tayi magana da huda koda ba zata fahimceta gaba daya ba,aqalla ta rage wani nauyi daga zuciyarta dama qirjinta.
"Ku shiga ciki ku canza wasu kayan.....kema haneefa ki ajiye wannan chocolate din" . Tare suka miqe nadra tayi gaba haneefa tabi bayan ta suna maganganunsu.
Da hannu Sabreen ta yafito huda,sai hudan ta taso tsam ta dawo gabanta ta zauna. Dukka hannuwan huda Sabreen ta kama ta sanya cikin nata hannun,suka fara kallon kallo a tsakaninsu,kafin wani lokaci idanun Sabreen din suka cika taf da qwalla. Tana jin kamar ta gaza.......tana jin kamar ta kasa basu kariyar data dace dasu,tana jin tausayinsu matuqa da gaske,tanaso suyi amintacciyar rayuwa yantacciya kamar kowanne yaro. Tana qyamatar dukka abinda zaya tabasu,to amma da alama a dan tsakanin nan wata qaqqarfar guguwa ke shirin tasowa,wanda bata sani ba zasu kubuta daga azabarta da kuma qurarta ko kuma dukkaninsu zasu fuskanci wani sakamakon da ubangiji ne kawai yasan yanayin qarshensa.
"Inaji kamar na gaza huda.....kamar banyi aikin daya dace ba......" Tayi maganar qwalla cike a idanunta,muryarta kuma tana rawa sosai kamar zata saki kuka.
Damqe hannunta hudan tayi tana girgiza kai
"Kinyi dukkan qoqari adda.....kin bamu kowacce irin mafaka da kariya a rayuwarmu.....tundaga sanda suke daukemu jikina ya bani akwai matsala,duk kuwa da bamu fuskanci komai ba sai haba haba da maraba,sun bamu kowacce irin kulawa.....amma bamu sansu ba,bamusan su wayesu ba.....adda,abu daya suka gayan shine,dansu sukeso ki aura......me yasa ba zaki aureshi ba adda?,kaman alkhairi sukeson hadawa......me yasa bakison aure?". Kai Sabreen ke kadawa da sauri da sauri.
"Ban shirya aure ba huda.....ban shirya auren kowa ba,koda zanyi aure sai na aurar daku gaba dayanku a hannun nagartattun mazaje.....saina aurar daku a muhallin da nasan koda mutuwa nayi bani da haufi......bani kuma da kaico....amma ba yanzu ba,ba a irin wannan yanayin ba huda....idanma auren zanyi.....bazanyi auren cutatarwa ba,dansu baimin komai ba,ta yaya zan aureshi kawai don na zama silar da mallakarsa?" Maganganunta na qarshe ne hudan bata gane ba,sai ta zuba mata idanu tana kallonta.
Duk da tarin fargaba da yake ciki yake kuma kan fuskanta akan yadda zai tunkari Sabreen da maganar bada aurenta.....to qarshen tika tika tik inji bahaushe.........a yau shi rufai ahmad ya karbi komai na auren Sabreen din hatta da sadakinta bisa yanayin da bai taba zata ba.
Abinda yasha kwana yana mafarki shine......daga shi har Sabreen din sun cinye dukiyar aurenta da hannunsu,tun daga kudin aure kayan lefe sadakinta dama komai da komai na kudin baki. Sai gashi a yau ya wayi gari da baquncin wasu attajiran mutane dauke dakkan wata dukiyar aure. Kama daga sadakin aure daya tasamma naira miliyan biyar.......maqullin mota qirar Ferrari da baisan inda ma zasu ajeta ba........da tarin goro daya kusa huhu talatin,kwalayen alawa da suka kusa kaiwa kwali hamsin da tarin dabino da baisan ina zai ajiyeshi ba. Ga wasu uban kudaden da shi kansa baisan miliyan nawa bane na amarya kyauta ta daban,shi kansa ga wata dukiyar da aka mallaka masa a mazauninsa na uban amarya,abinda ya sanya jikinsa dukka ya dinga bari......Allah yasa komai ya tafi a tsari bisa taimakon kamilin amininsa.
Qarfe uku na yammaci motar da yasanya ta jido komai da komai ta tsaya a gaban gidan daya kasance gida ga d'an uwansa kuma uban riqonsa da yayi masa alkhairi masu tarin yawa a rayuwarsa.
Yara masu wucewa ne suka fara tsaiwa kallo ganin mota shaqe da kayan kwali kamar ana shirin bude provision. Wannan ya bashi damar kiran yaran,kafin wani lokaci sai gasu sun cika wajen harda wadanda ba'a kira ba,suka fara hidimar diban kayan suna shigewa cikin gidan dasu.
Hadiyya na daga bakin qofar famfo tana wanke uniform dinta na school of nursing,tazo gida ne weekend anjima kuma takeson komawa,yayin da bibo ke zaune saman kujera 'yar tsuguno daga qofar kitchen dinsu tana gyaran wake suna taba hira da shalelenta.
Daada ce ta fito a daki dauke da buta don kama ruwa gami da daura alwalar sallar la'asar. Daidai sannan yaran suka fara layin shigowa
"Kai.....kai daga ina?,ko.izzatu ce tazo?,izzatun alkhairi,don ita daya ce kaf gidan nan ke iya shigowa da kabakin arziqi haka" Bibo ta fada tana sakin murmushi
"Kawu ne yace mu shigo dasu,ku gyara waje don suna da yawa,a ina za'a ajjiye?" Wani yaro cikin yaran wanda shekarunsa suka dan dara na sauran ya fada yana sauke kwalayen hannunsa.
"Wai kana nufin rufai?" Bibo ta tambaya
"Indai shine aje masa inda yace,kada yazo ya yiwa jama'a tijara,bansan ma masifar data sakashi kawo mana kaya gidan nan ba,shi abinsa da baya tabuwa,tunda kudin cacar nan suka samu mu kuma bamu da kwanciyar hankali". Taja qaramin tsaki daada na gaban famfo tana tarar ruwa wanda suka kusa daukeshi don haka da qyar yake zuwa.
Tun tana irga adadin kwalin har suka fara yawa suka fara kuma shallake tunaninta. Tun daada na bandaki har ta fito tana daura alwalarta,sai bibo ta ajiya farantin waken tana cewa
"Wai rufai sai ya cika mana gida hankalinsa zai kwanta?,wanne irin kwalaye ne haka na alawa da biscuit masu tsada kuma?,ko kantin siyayya zai bude ai sai haka ko?......hadiyya tsame hannunki ki leqa ki ganemin". Zubda ruwan kurkurar bakinta daada tayi,a karon farko tayi magana
"Ke kin fiya ci da zuci wallahi.....wai shinma a kanki kayan zasu zauna?,koma meye ai zaiyi bayani ko?,tunda shima kinsan bakinsa baya shuru".
"Adai dubo din daada abun ya fara wuce lissafi". Ko kafin hadiyya ta fita ta dawo kwalayen sun sake yawa,sai gata tana zare mayafinta
"Aida saura bibo.....shikam yana can yanata bawa yara umarnin aci gaba da shigo dasu". Wannan karon har daada tsaiwa sukayi suna kallon ikon Allah,zuwa wani lokaci da faffadan tsakar gidan nasu yayi hani'an da kaya,muryar nan tasa dake iya tada mutum a barci ta karade tsakar gidan,ta kuma ratsa har kunnuwan Sabreen da haneefa dake riqe da hannun juna a daki.
"Me bacci ya tashi......wanda kuma idonsa yake biyu ya bani hankalinsa ta nan......me aiki ya ajiye aikinsa saina kammala bayani na" Ya qarashe maganar yana saba babbbar rigarsa gami da jawo botikin fenti ya haye sama yana harde qafarsa daya kan daya.
"Lallai ba'a daya a dangi.... Kuma gado ba karambani ba......yau ta tabbata cikin diyoyin dan uwana akwai wadda tayo gadon arziqi irin namu.....ta fita zakka diyar albarka haihuwar asuba" Yayi zancan yana dukan tafin qafarsa daya dora saman gwiwarsa.
Harara bibo ta galla masa tana jan qaramin tsaki
"Kai ka fiya sarqa zance,ba yadda za'a yi kayi magana miqaqqiya......akan meye kake magana?akan kuma wace?" Tayi zancan gabanta yana faduwa,saboda tsoron kada zuwan matan nan a wancan kwanakin yana da alaqa da wannan uban kayan da kwatankwacinsu basu taba shigowa cikin gidan ba.
"Akan waye kuwa nake magana idan ba'a kan Sabrina ba?......akwai wata me qashin arziqinne sama da ita cikin gidan nan?". Sosai takeso ta rufe kawu da balain yadda yake ware 'ya'yansu,yana abu kamar su ba haifarsu sukayi ba,to amma kuma tana buqatar taji kan zancen sosai.
"Sabrina kamar yaya?"
"Sabrina?" Huda itama dake daki ta maimaita sunan tana maida idanunta akan fuskar Sabreen din data tabbatar itama taji sautin futar sunanta daga tsakar gidan nasu da yake tamkar sansanin yaqi wasu lokutan.
Wuf tayi zata miqe,Sabreen tasan fita zatayi taji ba'asin sunanta da aka kama,don haka ta jawota ta zaunar da ita tana girgiza mata kai idanunta cikin nata.
"Sabreen fa......cikin ikon Allah yau na bada aurenta ga hamshaqin attajirin nan da basai ba gaya miki sunansa ba.....zaki gani cikin IV" Baki duka suka saki suna dubansa,banda daada data nufi dakinta tana cewa
"Allah ya tabbatar da alkhairi"
"Ameen hauwa'u....ke da yake baki iya doguwar magana ba" Fara takawa yayi yana nufar dakinsu Sabreen din yana cewa
"Bari naje na fito" Yayi maganarsa gaba gadi yana dosar dakin.
Page 100
Yau din da cikakkiyar sallama ya shiga falon,wanda duba daya Sabreen tayi masa qirjinta taji yayi wani mummunan faduwa. Ta dauke idonta a kansa tana amsa sallamar ta dubi huda.
"Ki wuce ciki ku zauna keda su nadra.....kada ki bari haneefa ta fito" A sanyaye huda din ta miqe,tana jin kamar ta zauna taji da meye kawun yazo dashi. Abune me wahala ya shigo dakinsu da alkhairi,koda yaushe idan kaga ya shigo akwai wani tashin hankalin da yake tafe dashi.
"Yar arziqi......yarinyar kirki,haihuwar albarka,kedai Allah yayi miki albarka,farar haihuwa,ubangiji ya jiqan mahaifinki da mahaifiyarki,ba abinda zamuce da haihuwar diya irinki sai sambarka,kin zame mana marufar asiri,kin zama kuma silar kawo mana hamshaqin attajiri cikin salsalarmu" . Dukka yayi maganar ne yana kallonta,bakinsa cike fal da fara'a.
Wani irin duba take masa,don gaba daya bata fahimci inda maganar sa ta dosa ba.
"Nasan ba zaki fahimci komai ba,amma yanzu zan miki bayani......ungo wannan" Yayi maganar yana ajiye damin sabbbin 'yan dubu dubi din a hannun kujerar da take kai
"Duba tsakar gida daga nan idan zaki iya hangowa....goro alewa da biscuit din na aurenki......wannan kuma" Yayi maganar yana nuna kudin dake kusa da ita.
"Ki cire million biyar kudin aurenki kenan,sauran kuma kyauta suka baki tukuicin auren dansu da zaki yi,kome kike buqata kuma ki samu takardar kiyi list......karki cuci kanki idan da hali ki siyo full scape masu yawa ki raba dare kina lissafawa ba abinda zaifi qarfinsu don akwai.abun fiye da tunaninki".
Cikin kanta da zuciyarta taji tana tantama,anya mafarkin yin arziqi bai soma haukata kawu rufai ba?. Kaman yaji me take tunanin,cikin murmushi yace mata
"Kina kallona kamar na tabu ko?,to wallahi koke na gaya miki wanda ya biya sadakin aurenki saikin zabure.......da farko dai kuma a taqaice na bada aurenki ga Muhammad jadda......mamallakin jadda diamond chores resources LTD....ga sadakinki nan......sati biyu masu zuwa zasu zo da waliyyansa da naki a tara shaidu kowa ya shaida".
Wani wawan duba take masa a kaikaice kamar taga wani tuburarren mahaukaci,yayin da gagarumar jayayya da yaqi ya barke tsakanin bangarori biyu na zuciyarta.
Sashen farko ya cika da fargaba da kuma zulumin komai fa kawu yana iya yi indai akan kudi ne.......kada ya zamana zancansa gaskiya ne.......yayin da wani sashen na zuciyarta kuma kewa abun kallon zancan shifcin gizo ne kawai. Ta yaya zai bada aurenta haka?,sai kace wata diyar 'yartsanar roba ko abun wasan yara?,a haka ake bada aure bada masaniyar kowa ba sai tasa masaniyar shi kadai?. Sam sam kanta ma bazai dauki wannan shirin film din na kawu ba,saidai batasan me yasa takejin muguwar faduwar gaba da wani irin tashin hankali dake cakude da fushi ba,ta zuba masa idanu yayin daya ci gaba da zuba mata bayanan da sam ita bama fahimtar me yake fada takeyi ba. Abu na qarshe data fahimta shine,wayarsa daya ciro yana cewa
"Kawunki na senegal abdulk'adir ya bani damar karba.....yace kuma idan na shigo na hadaku kuyi magana".
"Uncle abdulk'adir?......tashin hankali!" Maganar tayita qasan zuciyarta zuciyartata na wani irin bugu mara misali.
Uncle abdulk'adir.....zazzafan mutum me tsananin tsauri da kafiya......me zafin zuciya da kafewa kai da fata wajen gaskiya.....mutumin da ako da yaushe take kaucewa haduwarsu......mutumin da ko yaushe take qaranta yin waya dashi,mutumin da har yanzu bata yarda yasan ainihin number wayarta ba gudun bin diddigi tsanani takura da kuma sanya idanu......yau shine kawu rufai ke ambata a gabanta?. Da gaske bakin alqalami ya riga ya bushe tunda har sunan kawu abdulk'adir ya fito cikin batun!!!!.
"Kinga ban sameshi ba,dama dazun yacemin yau jumaa sai yammaci yake fita a masallaci.....qila ya kashe wayar da zai shiga,amma ba matsala anjima saina dawo na hadaku".
Batasan takai hannu ta watso kudin qasa daga hannun kujerar ba saida taga kawu na binsu yana tarosu.
"Yaushe mukayi dakai zaka aurar dani ga wani da bansan waye ba?,saboda son dukiyarka da kwadayin abun duniyarka kawu?......" Saita saki wani murmushi daya sanya hankalin kawu ya tashi
"Bari na baka shawara......tunda wurwuri.....tun komai da duminsa kaje ka warware abun nan.....wallahi wallahi wallahi ba wanda ya isa ya auraminshi ko wayeshi kuwa,bansan da wannan zancan ba haihata haihata,ba kuma abinda ya shafeni bane"
"Za kuwa kiyi kaffara aminatu......" Muryar kawu ta isa kunnenta sanda take yunqurin shigewa daki abinta don batason taci gaba da zama awajen.
Yadda yayi furucin da wani qwarin gwiwa ya sakata waiwayowa. Yana tsaye kawun riqe da kudaden
"Zakiyi kaffara.... Don baki da kudin da zaki iya biyan me jadda kudaden kamfaninsa da kika sace......hakanan bani da kudin da zan biyashi kudinsa da na ci a caca cikin rashin sani......ke din fansar kudadensa ce......cikin dattako da kuma alfarma irin tasu duk da haka suka sake biyan wasu kudaden saboda aurenki.......kin shirya yaqi da fito na fito da mamallakin diamond gold da azurfa?".
Qafafunta taji suna yunqurin kayar da ita,maganganun kawun suna mata girma akai dama sassan jikinta tamkar bata da jarumta da qwarin gwiwar iya dauke dukkan bayanansa.
𝙈𝙪𝙝𝙖𝙢𝙢𝙖𝙙 𝙛𝙪'𝙖𝙙
Idanunsa zube cikin na farouq sanda yake masa bayanin yadda komai ya kasance. Yayi relaxing sosai abinsa,yayin da ya miqe dogayen qafafunsa saman table din glass dake gabansa yana sipping ruwan wolf berries da wasu daga cikin 'ya'yansa cikin qaramin cup na glass.
A nutse ya ajiye cup din,me sunan malam ya dauka yana ficewa dashi daidai sanda farouq ya kammala duka bayaninsa. Yatsunsa ya sarqafe waje guda idonsa akan farouq
"Duka wannan hidimar wa ya aikeka tsarata?.....bakasan already ta debi kudin aurenta ba?". Qaramar harara farouq din ya watsa masa yana dora qafarsa shima daya saman daya
" Duka wannan kai ka sani......abu daya nake da matsaya akai......daga gidan dattako muka fito....so dole neman aurenmu da kuma matayenmu susha banban da na kowa......that's all" Kai fuad yake jinjinawa da wani qaramin kwantaccen murmushi can qasan fuskarsa.
"Tunda kuka sake basu dukiyata dole na tsaurara matakan tsaro.......kuma tamkar kun sake lafta musu bashi ne.....don already na sallamesu,nace su lissafa cikin abinda suka dauka su zare kudin komai da komai". Girgiza kai farouq yayi,wai me yake damun fuad ne akan wannan batun?. Duka duka abinda aka basun ma baikai koda kaso daya cikin goman abinda yake fiddawa kusan kullum ana rabarwa mabuqata ba. Gyara zamansa yayi ya sako masa zancan da yafi damunsa tunda suka dawo din......ya kuma tsaye masa a rai.
"Abu mafi muhimmanci da kuma ban mamaki ma.....kai da maamah ashe gida daya.....kuma yarinya daya kuke nema". A nutse ya daga idanunsan nan da wani lokaci suke fita gada gada,wani lokaci kuma su kasance lumsassu kamar wanda bacci ya kama ya zubawa farouq su
"Ba wadannan idanun nace ka watsamin ba......na gaya maka wani abune da yaban mamaki". Dan murmushi yaja kadan,idan bai manta ba farouq ya taba gaya masa bai fiyason ya watsa masa idanunsa ba,don wani lokaci suna masa wani iri da dan sakashi jin kamar ba me babban sunansa ba.
"Maamah tana da nata plan din......kamar yadda nima nake da nawa plan din......so an samu haduwar target duka akan abu daya". Zuba masa ido farouq yayi yana jin zuciyarsa na sake cika da shakkar halin matar,duk kuwa da cewa mahaifiya take a wajen dan uwan nasa kuma rabin jikinsa. Saidai duk inda akaje aka dawo shi din me qoqarin saita fuad ne,musamman akan mahaifiyar daya fahimci shi da ita duka zukatansu sunyi nisa akan abinda suka saka a gaba.
"Kada kayi mummunan zato ko zargi akan yarinyar daka zaba don ta cikashe maka rabin addini da rayuwarka.....hakanan kada ka dora zargi akan mahaifiyar da tayi silar shigowarka duniya".
Wani murmushi ya saki yana sauke qafafunsa qasa,sannan ya miqe ya zauna sosai yana duban farouq
"BB farouq.....har yanzu sai nake ganin kamar baka gama sanin waye Muhammad fuad jadda ba.....any way......komai ina sane dashi,zan kuma ji dashi daidai da yadda ya dace...."
"But....."
"But what?" Ya katsi numfashin farouq.
"Don't make....."
"Ba abinda zai faru dude" Ya sake fadi kawai yana miqewa daga zaman alamun yakai qarshen maganarsa dama hukuncinsa.
Yaji wani irin abu tun daga saman kansa har tafin qafarsa a sanda ya kammala bincikensa kan wacce maamah keson hadasu. Kenan ba wani guri daya kuskure wajen fahimtar hatsarin yarinyar?,zallar rashin tarbiyyarta?,qwarewa wajen iya taku tare da buga kowanne irin wasa da qwaqwale zuciya dama dukiyoyin jama'a?. Kenan ya tabbata itama jan wuya ce tunda ga hadin gwiwa nan ya tabbata tsakaninta da maamah?. Abu daya ne tak! Da baikai ga ganowa ba.....hakanan duk wasu 'yan bincikensa suma basu kai ga ganowar ba shine.....KAN WACCE IRIN KWNGILA SUKA GINA ALAQAR?......MEYE LULLUBE QARQASHIN BATA AURENSHI?. Shidai yasan tasa agenda din.....TO MECECE TASU?.
"zaki gane baki da wayo.....i will teach you a lesson........ You'll learn through experience" Yayi zancan yana fitar da wani siririn murmushi.
Cikin ranshi yake tsara wanne hanya zaibi don ya fara gwada mata nashi salon izzar?,tasa isar?....da kuma qarfin ikonsa tun daga yanzu?". Dakatawa yayi daga tafiyar da yakeyi,yadan waiwaya kadan sashen da farouq yake
"Kace ba?,kunkai sadaki ko?" Ya yiwa farouq tambayar data dan sashi maida hankalinsa akanshi
"Yes.....haka na bawa abba shawara kuma hakan akayi".
"Good boy" Ya fada yana dan murmushi
"Ka gaya musu.....cinta shanta dama fitarta dukka yanzu suna qarqashina......kada ta sake fita muddin ba da sanina ba".
" What kind of madness......"
"Tell them ko ni na kirashi da kaina....you know ina da number wayarsa ko?".
"Oh sheet" Farouq ya fada yana kama goshinsa.
"Wai meye damuwanka?......bakason komai.....but kana bibiyan komai why?" Juyowa yayi sosai yana duban farouq din,wannan karon murmushinsa yadan bayyana
"Wickedness" Ya amsa masa a taqaice.
"Bai kamata a dinga qyale irinta ba haka suna ci gaba da abinda sukaga dama......punishing nasu ya kamata ayi ta hanyar da zasu ji har cikin tsoka da jinin jikinsu"
Balcony dinsa ya isa kai tsaye hannayensa zube a aljihun wandonsa,yana bin dukka tsirran dake shuke daga gaban wajen da ido. Haka kawai yakejin interest dinsa yana qaruwa akan ya hora yarinyar. Abinda ya karanta maza sun badasu da har ta raina ajawalinsu haka da yawa,so dole ta fahimci nata kuskuren.
*_SABREEN_*
Jadda wani dadadden suna ne daya jima yana shiga kunnenta lokaci bayan lokaci,saidai ta tantance wayeshi yadda ya kamata abune da bazata iya ba. Tun daga fitar sunan daga bakin kawun har zuwa shudewar daqiqa sittin kallon kawu din kawai takeyi,kafin daga bisani qarar wayarsa ta katse wa kowa saqar da yakeyi cikin zuciyarsa.
Sau da dama bayyanar number farouq cikin wayarsa wani abune dake zame masa kama da ZAK'I DA MADAC'I,daidai ga gaurayar farinciki da kuma dimuwa a lokaci guda a kuma muhalli guda.
"Ga iyalin gidannan.....bismillahir rahmanir rahim" Ya ambata kafin daga wayar kaman yadda amininsa ya bashi shawarar yi domin amintar da kunnensa daga jin abinda zai dinga daga masa hankali har a samu a qare maganar auren.
Sai daya zauna sosai sannan ya daga kiran,ya bada kunnensa yana sauraren bayanin da farouq ke masa,wanda duka bayanin yana yinsa ne yadda kawun zai fahimta.....ya kuma gwammace ya dinga isar da saqon fuad ne gudun kada ya bayyana halinsa.....ko aljanar daya sake haqiqancewa akwaita ta sanyashi yin wani baqon halin da mutuncinsu zai zube idanun surukai,duk kuwa da cewa shima dama a karan kanshi dan kai tsaye ne,dan gaba gadi.Page 101
"To.....to in sha Allahu ranka ya dade.....godiya muke qwarai da gaske....Allah ya qara arziqi" Yayi zancan yan a kashe wayar,sannan ya maida dubansa ga sabreen da tuntuni baqinciki ya qarasa kasheta a wajen,ta kuma koma ta zauna tun kan ya gama wayar,badon bata gaji da zamanta a wajen bane.....aah....don tana da sauran abun gayawa kawun,saidai kafin ta fara nata jawabin shidin ya rigata
"Saqo ne daga mijinki......yana me umartarki daki lazimci zama a gida......yace a gaya miki baya buqatar daga yau har zuwa randa zaa tara shaidu a shaida daurin aurenki ki sake leqawa ko ina.....amma dan uwansa yace idan kina da buqatar fita ki sanarmin a kawo mota da masu tsaron lafiyarki......zasu kaiki duk inda kikeso a qasar nan ko a wata qasarma idan kina buqatar haka" Yayi bayanin fuskarsa wasai farinciki yana nuna kansa muraran a fuskar tasa.
Idanunta ta lumshe tana son tilastawa kanta fahimtar ma abinda kawun yake cewa. Shigar maganar kunnenta daidai take da wasan kwaikwayon yara.
"Miji?,ita sabreen?,mijin kuma yana iqirarin hanata fita saida izininsa?,wai shin yaushe ma akayi daren har garin zai waye?,yaushe ta yarda da wannan wasan kwaikwayon nasu da har zai tunanin ta amsa sunan MATARSA?. Shi a matsayin wa da zai tilasta ta aureshi?".
"Ko baka qarasa bayanin komai ba tsaf na fuskanci dalilin da ya sanya ka bada amanna qulla auren nan......kawu......har yanzu ba'a haifi me arziqin da zan aureshi don dukiyarsa ba koda ina da manufar yin aure......ballantana sam sam aure shine abu na qarshe cikin jerin lissafin wajibai na rayuwata.......kawu......ka rubuta ka kuma ajiye,wannan abu tamkar sabreen bata taba sanin ya wanzu ba......ba wani qato daya isa ya hanani fita a sanda naso a kuma duk lokacin dana ga dama.....ruwanka kawu ka maida musu dukiyarsa ruwanka ka riqe......abu daya na sani....kudin dani sabreen na taba na tafi dasu ta hanyar da nake ganin tayimin daidai.....kuma yayi adabo dasu har abada saidai ya sake sabon zubi da lale" Daga haka ta miqe tana yunqurin shigewa daki tana jin kwanyarta kaman zata birkice.
Me yasa qaddarorin qulluwar aure suke ta yawo a kanta cikin qasa da sati daya kacal?. Ta gama laluben hanyar gamawa da issue din wadancan matan?,yanzu kuma sai ga wannan?.
"Idan dai har kina ganin zaki iya ja dame jadda ga fili game doki nan" Abu daya da kawu yace da ita kenan ya miqe yana ficewa abinsa yana barin sabbin kudaden dake a mazaunin sadakinta yashe a qasa.
ᎷᏬᎻᎯᎷᎷᎯᎠ ᎰᏬ'ᎯᎠ
"Hamma?......hamma?" Ya jiyo muryar amna dake cike da shagwaba tana kiransa da alama nemansa takeyi. Wata iska ya zuqa me yawa yana dauke dubansa daga saman furannin da yake kalla cikin balcony dinsa tun dazun,ya juya a nutse yana fadin
"Am here lovy dovy". Dan murmushi ta saki tana qanqame paper din hannunta da wani tsadajjen biro me garai garai,ta taka a hankali ta isa balcony din inda yayi tsaye goye da hannayensa a qirji yana jiran isowarta.
"Hamma wajenka nazo" Tayi maganar hannunta boye a bayanta. Murmushi ya saki yana mata nuni da daya cikin lausasan kujerun dake ajiye a wajen. Ta taka a hankali ta zauna tana kallonsa da murmushi,fuskarta na nuna wani irin excitement
"Hamma.....zuwa nayi ka gayan favourite colour da kakeso a sawa matarka a lefe......and then ka fadi dame dame zaa zuba?,lissafin anni ya qure,tace nazo na sameka naji naka ra'ayin". Ido ya lumshe yana sakin murmushi,ya fuskanci sun daukaki abunnan,da gaske suka dauki komai,kuma da alama gagarumin shiri sukeyi.
Dukkan abinda suka aiwatar shi ko daya ma baizo kansa ba,ya manta dasu cikin ma hidimar neman aure,ko ita kanta yarinyar yana mantawa da zamanta sai idan wani abu ya gilma ko sun tada zancan.
"I don't have anything to say......the choice is yours" Ya fada da tsararren accent din nan nasa dake nuna gwanancewa wajen iya sarrafa harshe.
Murmushi sosai amna ta saki tana gyara zamanta cikin nuna doki
"Thanks hamma......bari na zabawa addana classy kaya" Ta dora hannunta saman paper din ta soma zana list.
Da sauri yaja baya sanda yake yunqurin fitowa daga dakin,idanunsa akan bibo wadda ta afko dakin kamar an tunkudota. Fadowarta dakin bai hana sabreen maida kanta taci gaba da takawa zuwa cikin dakin a nutse ba.
Maganganun bacin rai ne fal zuciyarta da zataso amayarwa da kawu rufai din,to amma tanata dannar zuciyartata saboda yiwuwar wanzuwar tata manufar. Sassauta fuskarta tayi tana fuskantar kawun sosai idanunta cikin nashi
"Banda abun rufai......ai ba'a yiwa 'ya'yan yanzu dole......tunda dai yarinyar nan tace batayi bataso ka qyaleta mana,gida cike fal da 'ya'ya......nan nan hadiyya idan kace ita zaka bashi.....wallahi tsaf zaa katse karatun nan duk da muhimmancinsa.....duk kuma yadda take sonsa....ai aure shine gaba da komai a wajen yarinya". Tayi zancan tana jaddada masa muhimmancin maganar da kuma gaskiyar abinda take fada. Hannu yasa ya kama habarsa yana dubanta
"Wato har yanzu dai ba zaki daina hali ba bibo?,kin saurari komai kenan?"
"Kaga rufai kada kayimin mummunar fassara.....saboda Allah don kawai yarinya ta nuna batayi......na bada shawarar kada a shiga haqqinta saika nemi canzamin magana?". Karon farko kawu rufai din yaji jikinsa ya sanyaya da bibo din,ya kalleta sosai cike da mamaki
"Bibo"
"Rufai" Ta amsa masa da sunansa kamar yadda shima ya kirata da sunanta
"Bari kiji na gaya miki......sabreen suka nema ba wata 'ya cikin gidan nan ba..."
"Suka nema ko kuma ka nemo Mata?" Tayi zancan tana yada kanta gefe cikin salo na watsa habaici.
Wata dariyar takaici kawu rufain ya saki
"Gwara ki fito kai tsaye ki fadi abinda yake ranki bibo......ki saurareni da kyau kiji.......sabreen bani na nema mata miji ba.....farinjininta da qashin arziqinta daga Allah ne,don haka bani da hurumin musanya musu da wata.....saiki dage da addu'a kema Allah ya azurta taki 'yar da koda yaron mijin Sabrina ne". Maganar tayi masifar sosawa bibo rai,harta kasa masa shuru sanda yake qoqarin fita daga dakin. Ta saki shewa ta daki cinyarta
"Ahayye......lallai sai yau na sake yarda kai din dan kunama ne.....kuma ka cika cikakken butulu......to bari kaji,ka tsallake yaranmu kaf ka tafi nemowa wancan tsintacciyar magen miji saboda tsabar qwarewa wajen munafurci da tsugudidi.....wallahi indai ina da rai na ci maka alwashin sai hadiyya ta auri mijin daya kerewa na sabrin"
"Allah ya bada sa'a......ko mafarki kikayi hakan ta faru lallai kin cika me sa'a" Ya bankada labulen ya fadi mata sannan ya juya abinsa zuwa tsakar gidan don ya sarrafa kayan da aka shigo dasu din. Ta gefe daya ya dauki dukka maganganun sabreen ya azasu akan mizanin abinda baida muhimmanci sam sam,saboda shi din yasan waye muhammad jadda.....kuma duk inda takai ga kafiya da jin kanta to la shakka daidai yake da zamaninta.
Idanunta ta lumshe tana qoqarin daidaita fitar numfashinta,yayin da idanuwansu dukka su ukun yake zube a fuskar yayar tasu.
"Kiyi haquri adda" Haneefa dake tsaye sosai a gaban sabrin din ta fada fuskarta kamar zata saki kuka. Duk da ba komai ta fahimta ba,amma kusan ta saba da hayagagar kawun,wanda duk sanda ya yita cikin falon nasu to wani fada ne ko tashin hankali......tun bata fahimta har ta gane komai sannu a hankali.
Cikin zuqar numfashi daya ta dawo da dukka jarumtarta tana sake gayawa kanta. Ita din 'yantacciyar 'ya ce.....ba property din kowa ba ballantana a ajiyeta a sanda akaga dama a inda kuma akaso.....sannan a janyeta ko a sauyata a duk sanda buqatar hakan ta taso.
Murmushi ta saukewa fuskarta,ta miqa tattausan hannunta tana shafar kumatun haneefa din
"Komai bai faru ba auta.....ku koma parlor ku kunna tv,nasa an gyara muku receiver din". Kai ta gyada a sanyaye,ta waiwaya ta kalli nadra da huda,sai ta juya tana ficewa suma suka bi bayanta,duk kuwa da cewa fuskokinsu sun nuna sam zuciyarsu bata gamsu da abinda ta fada ba.
Kanta ta cusa sosai cikin lallausan pillow dinta,ta shaqo qamshin ciki tana fesarwa ta baki. Wacce irin qaddara ke bibiyarta haka?,ta kowacce fuska barazana rayuwa takeyi mata da lamarin aure?,tabbas ko sama da qasa zasu hadu ba zata taba aminta da wannan shirin wasan kwaikwayon na kawu ba......kamar yadda ta gama shirya komai don bacewa wadancan azzaluman matan.
Kamar ana jira takai nan wayarta ta dauki qaramin sauti tana haske......ta daga kanta a nutse ta zubawa wayar idanu. A nata zabin bata da sauran wani dangantaka ko dalili naci gaba da sauraronsu.....to amma yaqi dan zamba ne.....wannan wata rubutacciyar magana ce data jima da haddaceta tare da adanata cikin dictionary dinta.
Sai data zauna sosai sannan ta daga wayar ta sanya a kunnenta tana cije labbanta.
"Salamu alaikum" Tayi sallama da muryar nan tata da tun randa ta fara furta mata manufarta a kanta ta haddaceta tsaf......sannann ta sakayata a gurbi na musamman da take ajiye dukkan wasu abubuwa da suka zame mata dole takatsantsan dasu.
Cikin wannan miskilancin nata daya zame mata jinin jiki ta amsa mata. Hakan sam ba damuwar maamah bane.......tana da tarin abubuwa da takeson sake sani tsakaninta da fu'ad.
"Ina fata zuwa yanzu dukiyar auren d'ana ta ruskeki?". Tadan shiga mamaki kadan,kamar zata tambaya amma miskilanci ya hana,sai ta zabi ci gaba da yin shuru har zuwa sanda maamah ta fahimci ba zatace komai ba.102
"Magana nakeso nayi dake masu tsananin muhimmanci.....naso ta kasance fuska da fuska.....to amma inason dauke idanu da hankulan mutane daga kan plan da dukka ma wani tsare tsare namu......na tsinci cewa yarona da nake nemawa ke shima ke yake nemawa kansa......abune me matuqar mamaki da daure kai.....nayi mamaki kaina ya kuma daure akan ya akayi hakan ta faru?.....ban samu wani tsoro ko kuma fargaba ba......saboda dukkan wata alama da zata bani cewa auren soyayya ne ake shirin qullawa babu shi......ya akayi kikasan muhammad jadda?.......meye naku shirin akan aurenku..... Duk da ba lallai ne na sani ba......amma zan gaya miki abu guda daya a taqaice......koma meye kuka shirya ke dashi ki tabbatar shirinku baici karo da nawa ba".
Sosai kanta yayi wani irin daurewa,sai taji kamar ta fara daina gane komai. Tana nufin ita din mahaifiya ce ga.......ya salam......." Ta furta cikin zuciyarta da murya qasa qasa. Wai su din wadanne irin mutane ne wadannan?,da d'a da uwa dukkaninsu kowa da irin kalar tasa alqiblar?,da d'a da uwa kowannensu nada karkatacciyar manufa?,kuma duka ba'a kan kowa ba?,a kanta?.
"Ina fata kin fahimta?" Maamah ta tambayeta ganin koda tarinta bataji ba.
"Akwai wani abu me muhimmanci daya dace ki fadan ki fadi ba?" Ta motsa labbanta a nutse tana tambayar maamah duk da yadda kwanyarta da zuciyarta suke cakude da rudani.
"Shikenan.....qaramar magana ce kuma gajeriya,amma me matuqar muhimmancin daya kamata ayi mata riqon tsauri" Qaramin murmushi ta saki me sauti,sautin daya ratsa ta wayar ya isa kunnuwan maamah. Wai ta yayama ita zata tsaya a dinga tambulin da rayuwarta tsakanin UWA da DANTA?. Ta yaya ma zata tsaya ta zuba musu idanu suna yin yadda sukaga dama rayuwarta?,rayuwartata da ba mallakin kowa bace ba kuma wanda yake da iko da ita?. Rayuwar da aka fusgeta da qyar?,tsananin kuma nisan kwana ya kawota inda take zaune a yanzu?.
Isar murmushin kunnuwan maamah ya haifar mata da 'yar fargaba kadan,saidai kuma lafazin sabreen din ya danne dimuwar
"Baki da damuwa.....ki qirga kwanakin kawai da kike jiran komai ya kasance"
"Da kyau.....naji dadi dana sameki ame saurin cika alqawari.....sati uku.... Sati uku kadai ya rage ki zama daya daga cikin familyn jadda......nasan kuma bakisan wanne irin family zaki shiga ba......cikin qasa da sati daya kafin sannan ina buqatar ganawa dake don ki karbi jadawalin tsarin yadda nakeso komai ya kasance". Idanu ta lumshe ta kuma budesu lokaci daya tana gyada kai. Karon farko a rayuwarta da tasan murmushi yana iya fita daga fuskar dan adam a yayin da yake cikin bacin rai.
"Baki da matsala" Ta furta da ma'anoni daban daban.
"Okay.....inason ki saki jikinki.......bayan hidimar dashi da uban goyonsa zasuyi miki......karkiji nauyin tamabayata komai......ko nawa kike da buqata a shirye nake dana kashe miki shi......inaso surukata tafi kowacce suruka daga cikin surukan sanannu kuma attajiran families.....biki zamuyi na kerewa sa'a.....irin bikin da zai kauda zato da kuma dukkan zargin me zargi a kanmu".
"Ba damuwa bane....na fahimci komai,amma ina buqatar hutu........zamuyi magana wani lokacin" Ta qarasa fada tana yanke kiran ba tare data jira cewar maamah din ba. Gefe tayi jifa da wayar tana nutsa hannunta cikin sumarta
"Ya ilahi.....ya akayi dukka haka ta kasance?ya akayi komai yazo a daidai?" Tayi zancan a fili
"Kiyi aurenki adda......kiyi aurenki" Taji muryar huda dake rawa,wadda ke tsaye daga gefanta.
Hannayen nata ta zare daga sumar,ta daga kanta a hankali tana duban huda dake tsaye. Idanunta cike fal da hawaye,ta qaraso da sauri ta tsugunna gaban Sabreen gami da riqo hannayenta
"Adda....."
"Shshsh" Ta dakatar da ita tana dora yatsanta akan lips dinta.
"Nayi aure a wannan situation din kike fadi huda?.....na kaiku ina?.....waye zai kulamin daku?"
"Allah......Allah ne adda" Ta amsa mata har yanzu muryarta na rawa.
"Na sani huda.....na sani,amma kinsan wanne irin aure ne wannan auren nawa?.....rayuwar addanki sukeson jefawa cikin wani game da ake bugashi tsakanin D'A da UWARSA.game din da ba wanda yasan meye ainihin ma'anar bugashi,zasu tsoma rayuwar aminatu a ciki bayan bata cancanci ta fuskanci raba uqubar rayuwar kowa ba.....me nayi da zasu nemi na zama silar cutar da dayansu?". Tana kaiwa nan sai ta samu kanta da kecewa da kuka,wani nannauyan kuka me siririn sauti,irin kukan data dauki sama da shekara shida tana tarashi a qirjinta,don bata da kafadar da zata kwantar ta fiddashi ta rage wannan radadin.
A yau hudan ta zame mata wannan kafadar,har ta zama jarumar data dinga sharewa sabreen hawaye dukka jikinta yana rawa
"Daga yau zamu dinga raba wannan tsananin da quncin adda......ba zaki sake kuka ke kadai ba....kiyi haquri kada su nadra su jiyoki"
"Ba wanda zai rabamu huda.....dole na nemana muhallin da zamuyi nisa da dukkan wannan qullin.....bazan fuskanci wannan abun ba". Tayi maganar tana zare kanta daga kafadar hudan,ta miqe tsaye kai tsaye tana dosar bakin gadonta.
𝙒 𝘼 𝙎 𝙃 𝙀 𝙂 𝘼 𝙍 𝙄
*******Daidai lokacin da su huda suka wuce tahfeez a safiyar asabar din. Ta shirya kanta tsaf cikin turkey dress da suka maidata tamkar daya daga cikin kyawawan 'yammatan turkey din.
A nutse take rufe qofar parlor dinsu,ta zuge qaramar jakar hannunta ta jefa key din duk da yadda takeji a jikinta akwai idanuwa masu yawa a kanta cikin jamaar dake zazzaune a tsakar gidan.
Tsakanin jiya da yau din ta karanci an samu yawaitar jama'ar dake zama a tsakar gidan nasu. Wani irin zama da yake kama da zaman gulma tsurku da kuma zunde.....a wani yanayin kuma yafi kama da zaman jajantawa da kuma jimamin da batasan ma sunayi ba. A nata ganin dukkan kai kawonsu bazai wuce akan tatsuniyar qirqirarren aurenta da kawu ya gabatar cikin gidan ba,labarin daya girgiza kowa cikin gidan harda 'yan uwanta da suke uba daya wanda suke aure a wani gidan.....lamarin da inda suna da yadda zasuyi suka tsige mata shi me yiwuwa ta sanyasu cikin jerin masoyanta da bata da kamarsu.
Idanuwa sunyi yawa a kanta sanda take ratsawa tsakar gidan,idanuwan dake cike da hassada da jin haushinta,sannu a hankali ta samu ta isa ga soronsu ta bulla farfajiyar gidan da zata danganata da gate na qarshe na gidan.
Motar dake lullube cikin tempol qarqashin rumfar data kasance ma'ajiyar motor mahaifinsu sanda yake raye idanunta suka fada.....
Ido ta dauke daga kanta tana jin wani zafi yana ratsa zuciyarta. Da gaske yake kawun kan lallai saita karba komai harda motar da anata idanun daidai take da motar daukan gawa.
"Komai ya kusa qarewa" Ta fada qasa qasa sanda take gifta motar,tana buqatar isa inda tayi niyya don shirya yadda zata nesanta kanta da qannenta da wannan Cakwakiyar da ake shirin tsomata.
"Ke.....ina zuwa?,ina zaki haka?" Muryar kawu rufai ta ratsa dodon kunnenta,kawun dake tsaye qofar wani daki dake can qarshen katangar gidan. Dakine da ashekarun baya mahaifinsu kr jibge kayan abinci a ciki.
Duba daya tayi masa ta kauda kai taci gaba da takawa abinta don fita. Ya fahimci maganarsa sam bata dadata da qasa ba,hakanan sautinsa bazai taba dakatar da ita ba,don haka ya saki aikin gyara kwalayen da yasa akeyi ya tako da sassarfa cikin burin cimmata.103
Har ta murda hannun qofar ta bude sai kuma ta dakata saboda wani tunani da yazo mata. Tsaf kawun zai iya binta waje ya tara mata jama'a,don shi din bai ita magana qasa qasa ba.
"Ina zaki nace ke aminatu" Yayi tsaye a gabanta yana fada idanunsa a kanta yana daure fuska.
"Kin tambayi mijinki?,da izininsa koda saninsa zaki fita?" Ya sake jefa mata tambayar da gaske yana adan tsorace.
"Mijinki" Kalmar tayi wani amsa kuwwa cikin kunnenta. A duk sanda taji ya ambaci wannan Kalmar sai abun ya zame mata wani irin baqon abu.
"Bazan hanaki fita ba.....amma sai na tabbatar da izininsa kika fita din,don a yanzu ke amana ce a hannunmu,bazan Kuma yi wasa sa wannan amanar ba har sai na tabbatar ta fita daga hannu na".
A nutse ta daga ido ta kalleshi,abun yana bata mamaki gaba daya,wai yau kawu shike haqiqancewa haka akan lamarin da ya shafeta?,wai yau shike tambayarta ina zata fita?,lallai kudi sun zamewa rayuwar wasu bayin jarabta. Abune da bata taba sanyawa cikin kanta ba......wai akwai wata rana da zata zo har wani ya damu da inda ta fita ko kuma ina zata je?.
"Ki sanar dashi sannan kije duk inda kikeson zuwa din" Ya same maimaitawa yana tura qofar da qafarsa.
"Oh......inda ranka kasha kallo....duniya juyi juyi wai kwado ya fada ruwan zafi......dama idan bakayi sharar masallaci ba ai kayi ta kasuwa,kudi shu'umai......iska kuma na wahal dame kayan kara.....ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta". Wannan jerin gwanon habaicin suka fito daga bakin bibo wadda ta iso daura da wajen don zubda sharar sa ta kwaso daga dakinta.
Waiwayawa kawu rufai yayi yana dubanta
"Wai dukka wadannan gayyar gamayyar haibaicin akan waye kike?,indai da Sabrina kike aikin banza kikeyi,kinfini sanin halinta,uwa uba kuma a yanzu ita din me arziqi ce.....me arziqi kuwa baya fada da talaka......ni kuwa kinsan warki nike daidai qugun kowa.....to saiki banbance".
Tsaiwa tayi sannan ta waiwayo tana zabgawa kawu harara,wani irin tsanarsa da haushinsa suna cikata
"Magana kakeyi ne ko bakinka ne a haka?,aini rufai na jima da sallamaka cikin lamurana.....ashe da gaske aboki yana iya juyewa ya koma maqiyi?,dadin abun ba'a fimu iya 'yan shige shigen nan ba,to na meye ma zan damu banda abinka rufai?" Ta qarasa maganar tana yarfe hannu cikin son boye damuwarta da lamarin.
"To barkanki.....gwanda da kika gyara zancanki kika samawa kanki salama....".
Kunnuwanta ba zasu iya ci gaba da sauraron wannan quruciyar ta kawun da bibo ba,wanda har yanzu suka kasa dainawa,duk kuwa da cewa kansu da bakinsu a hade yake,yanzun ne abun duniya yake shirin hadasu,don haka suna tsaka da sa'insarsu ta tajuya tana takawa da nutsatsiyar tafiyarta dinnan da 'yan bani na iya suka sawa suna
"Maciji me tafiyar mutuwa" Nutsuwarta a tafiya a cewarsu sam bai dace da halinta ba a tasu fahimtar.
A falo tayi wurgi da jakarta ranta yana susa,tun komai baiyi nisa ba har kawun ya soma!shiga gonarta da kuma nuna mata iyakarta?. Dankwalin kanta ta zame sassalkar sumarta ta zare daga ribbon din data matse gashin,ta koma da zafi zafi ta zauna saman kujerar tana furzar da iska daga bakinta
"Ta yaya ma zata zauna a maida rayuwarta haka?,ya zata zauna ta rayu kaman haka?,dole ta matsa qaimin tattare komai dama kowa nata zuwa bigiren da zata ci gana da gudanar da rayuwarta cikin 'yanci kuma a yanayin duk da takeso.
Idanunta dama kunnuwanta gaba daya suna a tsakar gidan nasu,tana bibiye da kowanne motsi na gidan. Jira takeyi kawai kawun ya matsa daga gidan ya tafi tashi sabgar itama ta fice nata. Kaman yadda takeji koda sama da qasa zasu hade ba zata taba daga waya ta kirayi mutumin da bata taba jin burbushin muhimmancinsa cikin rayuwarta ba......hakanan fitarta a yau ta zama wani abu na tilas don laluba yadda zasu gusa daga wannan muhallin zuwa wani 'yantaccen gurin.
Tana ji a jikinta idan bata aiwatar da hakan ba a yau tamkar bata da wani sauran lokaci da ya rage mata,kamar lokaci ya riga ya qure mata,kamar yaune kawai damar data rage mata.
Saidai duk yadda take zirga zirga da sanya idanu,kowanne motsi sai ta juyo muryar kawun ko gilmawarsa. Tun lokacin dawowar yara daga makaranta baiyi ba har yayi. Ba nutsuwa a tattare da ita sanda suka shigo,don ko abinci bata dora musu komai ba,burinta kawai kawun ya matsa ta samu ta fice,amma qemem wunin gaba daya yau a gidan ya yishi.
Bata samu ya bar gidan ba sai kusan biyar na yammaci,tasan kuma yayi hakanne saboda yasan ita din bamai fitar dare bace,saidai a wannan rana ta karya record dinsa,ta shirya a gaggauce ta fice abinta.
Cikin nasara ta kammala komai,saidai hakan ya dauketa har zuwa bayan sallar ishai,tanata fargaba ta shigo gidan,ta wuce kai tsaye cikin dakinsu,wanda tana sanya qafa shima ya sako tasa qafar,saita zarce bedroom kawai,don tasan dole zai fahimci ta fita,koda bai fahimta ba a cikin gidan nasu ba zaa rasa masu gaya masa ba,a yadda suka canza su kansu,komai yana shirin canzawa gaba daya.
*******K'arar wayarta shine abinda ya farkar da ita daga nannauyan baccin daya dauketa,hannunta daya mata nauyin ta miqa ta jawo wayar tana duba me kiran. Ganin sunan titi ya sanyata miqewa ta zauna sosai tana amsa wayar.
"Anjima da yammaci jirginmu zai tashi zuwa qasar India,najeeb ya gama komai"
"Alhamdulillah" Ta furta a sarari tana jin kamar an cire mata daya daga cikin nauyayan duwatsun dake danne saman zuciyarta. Ciwon aishatu shine cikar burinta na farko da take fatan gani kowacce rana.
"Zan shigo naga aishatu.....zan shigo da wuri titi in sha Allah" Ta fada tana jin farinciki yana ratsata . Murmushi titi din tayi
"Koda baki shigo ba sabreen kin gama yiwa aishatu komai ai,tsakaninmu dake sai fatan alkhairi".
Idanunta ta maida kan agogo bayan sun gama wayar,takwas saura na safe. Tayi mamaki da motsinsu huda bai tasheta ba,suma kuma cikinsu ba wanda ya tadata,sai ta jawo dan qaramin farin hijab dinta data cire sanda zata kwanta ta aza saman kanta ta zuro qafafunta qasa ta sauko tana fitowa falon.
Dukansu sun gama shirinsu,kowa sanye da uniform,fitowar tata taja hankalinsu,suka soma gaidata sanda take zama kusa da haneefa,saita karba saka mata socks din tana cewa
"Auta ta daina neman me saka mata socks yanxu ko?,girma yanata zuwa" Dariyar jin dadi tayi tana cewa
"Amma adda kullum ya nadra cewa takemin yarinyar nan...."
"Rabu da ita,harda ke za'a raba aiki idan muka koma sabon gida" . Furta sabon gidan da tayi sai dukansu suka zuba mata ido,bata bada hankali ba sai data gama sawa haneefa socks din.
"Adda......wani gidan zamu koma?" Haneefa ta riga 'yan uwan nata tambaya fuskarta na nuna farinciki sosai.
"In sha Allah.....gobe.....kaman ko yaushe bana buqatar masaniyar kowa,idan an tashi daga school yau ba islamiyya.....koda kun dawo baku sameni ba zan shiga duba aishatu,ku fara shirya kaya huda cikin manyan bags din can kafin na dawo"
"Tom" Huda ta amsa mata saidai nata jikin a sanyaye yake. A nata hasashen tana ganin kaman idan addan nata tayi auren shine zaifi dacewa da ita......auren zai zama wata hanya ta wanketa daga dukkan zargi da mummunan kallo da society din da suke rayuwa a ciki suke mata,bataga alfanun ture wannan auren ba.....duk da tayi mata nata bayanin gwargwadon yadda zata fahimta.
Addua ta musu na dawowa lafiya,saita jawo wayarta tana son taba JIB ya qara mata bayani akan wanda titi tayi mata,sannan shima suyi handing over akan komai.....tana buqatar sabuwar rayuwar da babu kowa cikinta daga ita sai qannenta da kasuwancin da takeso ta fara wanda shi take sanya ran zai zame musu madogara
_ni kuwa nace ummmm inji me ciwon haqori,anya kuwa sabreen?,haka siddan zakici bagas?😂,to bari dai mu gani_
Wayar bata shiga ba saiga nadra da haneefa sun dawo cikin dakin,ta ajiye wayar ta maida hankalinta a kansu tana shirin tambayarsu lafiya huda itama ta shigo. Tsoro sosai saman fuskarta,ta qaraso cikin falon tana dubanta.
"Adda.....ina tsoron faruwar wani abu"
"Me kenan?" Sabrin ta tambayeta tana tattara hankalinta sosai a kanta
"Wasu manyan qatti ne guda biyu a qofar gidan nan.......duk wanda zasu shiga ko zai fita su zasu bude masa qofa.......nayi qarfin halin tambayarsu su waye amma ba wanda ya amsa min a cikinsu". Shuru sabreen tayi tana qanqance idanunta cikin alamun zurfafa a tunani. Kwanyarta ta gaza cafko komai,sai ta maida dubanta kan haneefa.
"Akwai wani alamu na cutarwa a tare dasu?,hayaniya tsawa ko wani abu daban?". Kai ta girgiza
"Ba daya,kawai zasu kalli fuskarka ne sannan su bude maka qofar"
"Haka kowa yake fita daga cikin gidan?.....akwai wanda kukaga sun hana fita?"
"Kowa yana fita,amma cikin tsoro,ba kuma wanda suka hana".
Sosai ta jijjiga kanta zuciyarta tana d'arsa mata wani abu,saidai kuma bata tunanin hakan zata kasance.
" Ba damuwa,ku wuce kuma ku fita kaman kowa,basu da alaqa daku". Cak sukayi suna kallonta,da alama dukkaninsu itace damuwarsu,kada ma huda taji labari saboda sanayyarta da abubuwa da yawa da sauran basu sani ba.
Tattausan murmushin nan nata dake tsananin qara mata kyau ta saki tana girgiza kai
"Karku damu......muna da yawa a gidan,ba abinda zai faru damu,a dawo lafiya" Tana ganin yadda suka kama hannun juna da kyau kaman kowa na shirin karewa dan uwansa wani abu me cutarwa,wannan sai ya tsinka mata zuciyarta sosai,ta sake jin ruwa da iska zata ci gaba da zamewa rayuwarsu garkuwa har abada.
Tana dauke idonta daga kansu kankatsin salatin bibo ya rusketa
"Daada.......tani......wai bakuga yau kuma bala'in da muka wayi gari dashi bane yau?,karta kartan garada sun tsare mana qofar gida kamar gidan tsaffin 'yan damfara.....koda yake biri yayi kama da mutum.....kuma sai da karen gidanka kake ganin na wani gidan......wannan masifa da take shirin afko mana gida ya ubangijin Allah ka tsaidata iya kan wansa ya jajibota....."
"To wannan balai mudai bamu taba ganin irinsa ba tsahon rayuwarmu da mijinmu sai a wannan karon" Tani da suke dan juma da dan jummai wani lokaci ita da bibo kafin su hautsine kuma ta fada tana tafa hannuwa
"Yo kome zamu gani aisaidai mu nemi tsari.....wanna masifa duk yadda akayi silar wannan gafalallen auren ta samemu.....wai daada ba zaki fito bane sai an cimmaki?".
"Me zan fito nayi?,ina ruwan biri da gada?,tunda dai basuce ni suke nema na ina ruwana ni dasu?,maza ku zafafa damuwa dasu sayi awon gaba daku idanma zuwan nash ba naku bane ku jawa kanku da shegen bakinku"
"Bakinki ya sari danyen kashi wallahi,.....saboda abun arziqi bai karbi kare ba,daga abun arziqi sai ki juye mana da fatan tsiya?,sha zamanki idan an cimmaki wani cikinmu aka cimmawa"
"Ke kika sani" Daada da bata fiya jurewa dogon cece kuce ba ta fada.
Tana danna number jib kunnuwanta suna saurarensu. Wannan dabiar tun bata mallaki hankalin kanta gaba daya ba tasan bibo da ita,har kwanan yau kuma ba abinda ya canza a tattare da ita.
Waya sukayi da jib din ta minti talatin kacal,daga nan sai ta soma shirin shiga wanka. Ta dawo daki ta tsane jikinta da towel,ta shirya cikin glitter wax me tsananin kyau data dace da kalar fatarta da kuma yanayin qirar jikinta,dinkin half bubu da straight skirt da aka tsaga bayansa,ta dauki Chantilly veil me asalin tsadar peach color adon jikin atamfar,ta hada da plate shoe da hand bag dinsa bagco.
A tsaitsaye ta hada tea da biscuit tasha,ta yafa mayafinta ta daura agogon hannunta don buri take taje taga farincikin dake kwance fuskar aishatun.
Hankali kwance take takawa a harabar gidan nasu tana nufan qofa,tana jin ta gama da dukka wata matsala yanxu dake gabanta,so saura ya rage na wadanda suka gayyatota cikin matsalar susan yadda zasu warware qullinsu.
Tana taba handle din qofar taji an budeta,sai ta daga kanta a hankali ba kaman dazu da yake a qasa ba tana kallon gabanta.
"Good morning madam" Kakkaurar muryar ta fada cikin tsananin girmamawa har yana rusunar da kansa duk kuwa da cewa ya ninkata a tsaho da shekaru,girman jiki kuwa sam ba'a maganarsa don bata kawo koda gefansa ba.
"Good morning madam" Ta sake jin wata muryar ta daban a daya gefan nata shima ya fada a girmame.104
Da idanu ta sake binsu,murdaddune a tsaye,wanda babu alamun tsoro ko shakka a tattare dasu,zubin tsayayyun masu damarar nan da akan samu akan hanyar shiga fadar shugaba wasa,wanda rana ko ruwa basa sanyasu motsawa ko canzawa daga muhallin tsaiwarsu.
Sosai ta tattaro dukka dauriya da qwarin gwiwarta,ta azawa fuskarta wani mugun daurewa,tasa hannu tadan tura qofar tana amsawa ciki ciki da
"Morning" Tana sanya qafarta zuwa waje
"Sorry maaa........kiya haquri ki koma ciki..... Isn't allowed maaa". A mamakance ta dakata gami da ja baya saboda yadda yayi bake bake a gabanta,bataga ma hanyar wucewar ba komai qanqantarta
" Isn't what?......waye kai?" Tayi masa tambayar kai tsaye saboda bata da lokacin batawa tayi wani dogon nazari.
"My name is abdulgafar......ni da abokin aikina kuma duka munzo ne don tsaronki" Ya fada da matuqar girmamawa kansa a qasa,baya iya wani cikakken hada ido da ita. Haushi da mamaki duka suka hadu waje daya suka tsaya mata a wuya
"Tsarona like how?.....ni na buqaceku?"
"No maaa.....bake bace......umarni ne daga wajen boss" Dayan da baiyi magana ba sai yanzu ya fada da tasa girmamawar
"Who's boss?" Ta fadi da mugun fusata saboda ta fara shanshano wani abu
"Sir muhammad jadda....."
"Enough......ya isa.....ku bani hanya na wuce,daku da boss din naku da gadin nawa duka matsalarku fe ba tawa ba".
Rusunawa kadan yayi yana hade hannayensa waje daya
"Am sorry maaa......ba'a yarda mu barki ki fita ko ina ba har sai boss ya dawo". Kadan ya rage bakinta ya furta kalmar ashar saboda tsananin mamaki,sai tayi tsaye kawai tana kallon baqar fuskar mutumin mamaki yana zagayawa da ita duniyar tunani,yayin da shi kuma yake ci gaba da furta mata kalmar rarrashi da kuma ban haquri duka a cakude cikin harshen hausa da karyayyen turancinsa.
A wannan karon tana jin tura takai bango,ta inda kuma aka hau ta nan ake sauka,bata kuma da sauran lokacin batawa tayi sa'insa da yaranshi,don haka ta juya a mugun fusace zuwa cikin gidan. Tana tafe da dan sassarfa tana neman number kawu Rufai,abinda ta manta rabonta dayi kenan,saidai shi ya kirata idan neman abun duniyarsa ya motso,shima din ba kasafai ba,don yafi ganewa yayo tattaki suyi ido da ido.
Wata muguwar guda taji an sake mata data ratsa har tsakiyar kanta sanda take taka tsakar gidan nasu,ta runtse ido gudar bibo tana sake birkita mata kwanya,tana so taji da matar nan,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata tukunna dai ba yanzu ba,wannan qurar data taso miki a yanxu ita tafi cancan ta a kasheta.
"Yar arziqi irin albarka......kiranki alheri ne.....yanzu haka ina cikin layin naku ai,gidan zanzo akwai bayanin da zan miki"
"Basai kazo ba kawu... .Amma inaso ka kira wancan mutumin da kake iqirarin ka bashi aurena......ka shaida masa yayi gaggawar janye wadancan gumakan daya dasa mana a qofar gida da zummar hanani fita sabgogina"
"Kajimin shashasha.....macen da aketa tattali amma ta kasa gane hakan......banda abun ki wacce macace kaf unguwar bama gidan ba ta samu darajar samun masu tsaron lafiyarta idan bake ba?,ke wannan kawai bai isheki alfahari ba?"
"Kawu!" Yau din ta kirashi da dan tsauri a muryarta saboda yadda ranta yakai maqura a baci
"Fadi abinda kikeso ki fada......gani nan ma na shigo gidan" Ya qarasa fada yana datse kiran.
Da kallo bibo data maida yanzu zaman tsakar gida sana'arta qarfi da yaji ta bishi dashi
"Allah ka rabamu da mutuwar zuciyar da 'ya'yan cikinmu zasu dinga juya mu" Ta fada qasa qasa,yaji tana magana amma bai fahimci me take cewa ba,don shi a yanzu hankalinsa nakan lamarin sabreen da me jadda,bazai samu cikakken bacci ba sai ranar daya tabbatar an miqa musu ita.
A tsaye take don ta kasa zama,ba abinda zuciyarta ke maimaita mata sai kalmar
"Wai waye wannan muhammad jaddan?,me ya dauki kansa?,wa yafi?,wa ya damu dashi?".
Koda kawu ya shigo kallo daya yayi mata ya tabbatar lallai abubuwa sun fara cabewa. A yadda yayi mata farin sani fuskarta kawai ta gaya masa lallai ta fara cika,kuma dab take da fashewa,fashewar kuma da yayi imanin ba zata taba zame masa alkhairi ba musamman shi,bata da tsoro,tana iya yin komai idan har ta tsara zatayin,gwara tun wuri yayiwa tufkar hanci......ya gayyato masu tayashi yaqinnan don ya samu ya tsira da mutincinsa da sauran 'yan canjinsa.
"Ka kirashi ka gaya masa......idan ba haka ba zan gaya masa ta hanyar da bazata yiwa kowa dadi ba kawu!" Ta sake maimaita maganar da sautin da zai tabbatar maka kai tsaye daga zuciyarta maganar ke fita.
"Oh.....Allah na gode maka" Abinda kawai ya iya fada kenan. Tako ina yana jin gumi yana tsatsafo masa,tsakanin me jadda da sabreen baima san wanda yafi wani sakashi a masifa ba.
Hannun kujera ya samu ya zauna yana share fuskarsa da hannun babbar rigarsa,yana jin gaba daya duniya ta juya masa baya cikin qanqanin lokaci. Number da a kullum kiranta yake yawan sakar masa da fargaba da kuma faduwar gaba ya kira,duk da ya fuskanci cewa mamallakin number mutum ne me tsananin sauqin kai da kuma fahimta qwarai,hakanan kiran number wayarsa yafi masa sauqi akan kiran wancan mutumin da yake jinsa tamkar wani mala'ikan daukan rai a wajensa.
Daidai lokacin da yake tsaye cikin malam aminu kano international airport,zagaye da guard nasa,gefe daya kuma farouq ne da yayo masa rakiya.
Kusa da kusa suke tsaye sosai shi da farouq din,da alama akwai magana me muhimmanci da sukeyi shi dashi din. Hannunsa ya zura kawai cikin aljihun kaftan dinsa ya zaro wayar,ya maida dubansa ga fuskar fuad dake qoqarin sanya wayarsa a silent,don ba kasafai ya fiya son kiran waya ba
"Surukinka ne yake kira" Yayi maganar qasa qasa ta sigar zolaya da muryar da iya su kadai zasu iya jin maganar. Kadan yadan daga fararen idanunsa ya jefa masa harara,sannan ya maidasu kan wayar yana ci gaba da abinda yakeyi din ba tare daya ce dashi komai ba.
Idanunta suna lumshe,amma kuma yadda kawun yake wayar cikin matuqar girmamawa kai kace sune sama dashi sai bacin rai ya sake zuwa mata wuya......ba wannan bane a gabanta,abu mafi muhimmanci shine ya sanya wannan qattin su janye daga qofar gidansu,don haka ta saka kunne sosai tana sauraron muryar farouq dake fita tar tar ta speaker din wayar kawu,wanda ya sakata ne a speaker don ta samu tabbaci kan duka hukuncin da ya yanke a kanta.
Haka kawai cikin ranta takejin bashi bane yake magana,daga yadda farouq din ke magana adan sake ya sake baya yaqinin haka.
"Yallabai din yana kusa?,akwai saqo da aka bani zan isar masa....."
"Yana jinka uncle......bari na saka a speaker......though dai zaiyi kusan two weeks idan ya wuce.....zai dawo one week before the wedding". Kansa fuad ya sake dagawa ya watsawa farouq wata harara,don me zai zauna yana bayani musu akan abinda shi kadai ta shafa
"To ma sha Allah......ma sha Allah.......dama sabrina ce ke neman izinin rage masu tsaronta......sannan kuma a yau din tana buqatar ya bata izinin fita.....".
"Ban yarda taje ko ina ba....koda kuwa qofan gida ne". Wannan dakakkiyar muryar tasa dake cike da ginshira ta ratsa wayar ta kuma samu kyakkyawan damar isar da saqo ga kunnuwanta.
Kaman ya yarfa mata ruwan zafi haka taji. Tsam ta samu kanta da miqewa,ta zauna sosai tana zubawa kawu rufai idanu wanda zuwa sannan har ya fara haramar rufe maganar hanyar fadin
"To in sha Allah.....in sha Allahu ba damuwa......". Bai ankara ba,baisan kuma ta yaya ba sai tsintar wayar yayi a hannunta,kai tsaye ta zare wayar daga hannun kawun ta maidata kunnenta cikin wata fusatacciyar murya
"Ina fatan kana kan waya!" Sautin da yaja hankalin farouq da wayar ke hannunsa,da kuma shi kansa fuad daya soma takawa zai wuce ciki don ya isar da saqon da yakeson isarwa din.
Taku uku farouq ya cimmasa,sai ya zura masa wayar kawai a aljihun gaban rigarsa yadan matsa gefe yana karantar yanayin fuad din
"Ban nema izini ba......hakanan bance a nema min izinin komai daga wajenka ba......umarni ne kawai kan ka janye wadancan halittun da babu sanin kimar dan adam ko daya a tattare dasu......kafin su tafi kuma ka tabbatar sun karbi komai naka daka bada da sunan dukiyar aure"
"Au haba?" Ya fada da wani irin calmness zuciyarsa da kwanyarsa na qidddige wasi cikin halayenta.
"Ashe bayan qwamushe girman kai harda rashin kunya kika hado?.......abun yayimin daidai......i salute you ma'am........zaki ci gaba da zama cikin gida har na tsahon sati biy cur ba tare da kin taka koda qofar gida ba.......wannan shine punishment mafi sauqi a gareki".
"But....who are you?" Ta tambayeshi a zafafe tana jin zallar rainin wayo cikin maganganunsa.
"Relax mana.......so soon haka?,saurin me kikeyi nason jin waye muhammad fuad?,bayan sanin nasa suine babban barazana a rayuwarki?". Yakai qarshe yana ajiye numfashi,bai kuma barta ta sake cewa komai ba yace
"Kina zaton zan barki ba masu tsaremin ke.....don nasan kadan daga aikinki ki fecemin da dukiyar aure na.......wannan wasan zaiyi dadi sosai.......but......kisan dawa zaki bugashi......idiot!". Qit ya katse wayar,ya kuma zarota a gaggauce daga aljihun nasa. Abu daya zai sanya ya buga wayar a qasa,ta fito daga wajen mutum me matuqar girma da mutunci a rayuwarsa.
"Don't ever never try it.......kasan bana shiri ko jituwa da mara kunya......wayarka taci saa data kasance taka ce,da daga yau ba zata sake amsa sunan waya ba" Sai ya sake masa wayar shi kuma ya cafe,yayin da ya qara gaba yana wucewa cikin kaman yadda yayi niyya.
Yadda ya qara zafin nama cikin tafiyarsa kadai zai gaya maka zuciyar 'yan maza ta motsu sosai,ya bishi da kallo sosai. Yadda yayi doguwar magana haka yau cikin fada,ya tabbatar koda ya bishin bazaice komai dashi ba.
Kasa bawa kawu wayar tayi har sai daya sake kwatsa mata tsawa
"Bani wayata nace!" Saita miqa masa wayar wanda miqawar ya hadu da silalowar siraran hawaye daga fuskarta. Da gudu gudu ta qarasa shigewa dakin,tana jiyo sababin kawun da yaketa yarfa ruwan masifa kamar xai ari baki
"Kinsan wayeshi?,kin kuma san matsayinsa da har kika gaggaya masa magana haka?,kinsan idan ran mutumin nan ya baci ya kama duka danginki ya kulle basu da saidan me fiddasu?".
Maganganun kawu ba sune suke dawo mata akai ba,yadda ya dinga yaba mata magana kalma bayan kalma kuma murya a kwance.....hankalinsa ma a nutse shine yafi mata matsanancin ciwo.
Wunin ranar haka ta dinga juyi cike da baqinciki da takaici,tanaso tayi kuka amma tana hana kanta,tana ganin tafi qarfin tayi masa kuka(ni kuwa nace anya sabreen?,ba girin girn ba tayi mai).
Tana daga kwancen tana irgen yadda awanni suka shuda suka kuma zama silar tafiyar ayshatu india ba tare data yiwa yarinyar kallon qarshe kamar yadda taso ba. Da wannan juyin ta qarar da wuninta kaf da tunaninta na yadda zata samu zullewa tsakanin qattan garadan nan ta fice a gidan,ta kuma nisanci kowa ta yadda zai kasance kafin zuwan sati biyun da ya ambata saidai ya dawo ya tarar ta zama tarihi a garesu gaba daya.
********"kai jama'a,qalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un,mudai mun hadu da masifa,wannan bala'in har ina?,kai da gidan mijinka amma duk shiga ko fita wani qato yana tsaye,shi xai bude maka qofa shi xai rufe maka?". Muryar bibo kenan dake sakin buhun data dawo dashi daga kasuwar saitin dakinsu sabreen din,don tana so dukka maganganun da zata fada ya samu wajen zama na din din din a kunnenta.
A kwanakin sam bata da aiki sai fadin baqaqen maganganu da kuma tarin habaice habaice,tana neman duk wata hanya ne da sabreen zata kulata ta lanqaya mata sharrin da har masu gadin nata zasuji su kuma isar dashi ga uban gidan nasu,wataqila hakan ya zama silar fasa auren. Sosai auren ya tsaye mata a rai,ta laluba ta kuma bincika inda zata sake ganin matan nan don ta sake jaddada musu 'YAR BARIKI fa dansu zai aura.....amma bata samu ma wanda ya gansu ba ranar da sukazo unguwar ballantana ya tayata neman su. Ita din a yanzu tsoron taba sabreen din takeyi,duba da iya mutanen da suke gadin gidansu ma gaba daya ba ita sabreen din ba,wannan dalilinne kawai yake taka nata birki akan abubuwan data qulla aiwatar mata. Abu daya take jira shine ranar da zaa ce zaa kawo lefe,tana sanya ran ranar ta zame mata ranar nasara tunda ba wani daya danganci sabreen,a ranar sai tayi mata tonon silili cikin jamaar kawo lefen,ta tabbatar za'a tafi da ita a baki,kuma dole saqo zaikai kunnen wadanda suke da iko da hana abun ko aiwatar dashi.....randa zasuzo karbar kayan aurensu kuwa tasan dukka yadda zatayi.....koda tsiya koda bala'i ta juya abun ya koma kan hadiyyarta.105
A wannan lokacin sabreen din na kwance saman doguwar kujerar falon nasu,a kwance take rigingine tana kallon ceiling,saidai kuma manyan idanunta dukkabiyun a rufe suke kai kace bacci takeyi.
Banda yar qaramar fankar dake bada iska me dadi a falon ba zakace akwai wutar nepa ko sola cikin dakin ba. Ta kashe tv ta kashe dukkan wani qwai da zai iya bada haske.
Kwanakinta shida kenan tana irin wannan kwanciyar,musamman lokaci irin wannan da yara suka wuce makaranta. Zuwa yanzu kwanyarta da tunaninta dukka sun gajiya kan yadda zata sanya wadannan qattan subar qofar gidan,abinda zai bata damar sakewa kenan ta qarasa aiwatar da plan dinta. Ta lura daidai da second basa gusawa daga qofar gidan bare ta samu wata qaramar dama ma da zata gifta. Dukkan wani tunani nata ya soma gajiyawa,hakanan ta fara gajiya,bataga wani alamu na samun cikar nasararta na nesantasu da wannan gidan ba.
Kulli yaumin Allah shine da kullum sai kawu ya shigo dakin ya sameta a haka,qarfi da yaji ya zama me wa'azi yayin da ita kuma ta zama kurmar dole. Ta sake qaranta magana da wawalwalarta,ta sake zama miskila sosai,sai yayi maganarsa ya qare ya tashi kan wa'azin biyayyar na gaba da muhimmancim aure bata ma bude idonta ba bare tace dashi ta tafasa a sauke ba.
Wannan abun da take masa yana sake razanashi,yasanta cikin miskilai ma nata halin na daban ne,wannan ya sanya ya dauki matakin da bata taba zato ko kawo cewa zai dauka din ba......don a daidai sannan kunnuwanta suka jiyo mata sallama da wata murya da take kyautata zaton ta santa......ta mata kyakkyawan sani ba in general.
Daga sallamarta ta farko har zuwa ta biyu dukansu suna ji,amma tsananin mamaki ya saka suka kasa amsawa har sai data sake bayyana sosai a gabansu.
Bahijja........matar da a yanzu haka suka shafe shekara goma sha daya basu sanyata a idanaunsu ba.....haihuwar haneefa......haneefa daa yanzu girma da shekaru suke bayyana kansu a tattare da ita.
Kasa kowanne motsi tayi,saboda tana jin komai ne a mazaunin mafarki,sai kawai idanuwanta data bude ta zubawa qofa idanu tana sauraren isowarta don taga da gasken itace?.
Daga cikin al'ummar gidan da suka shaidata suma kallon mamaki suke binta dashi. Fuskar da ta bace musu tun wani zamani baya. Da idanu take qarewa gidan kallo kawai tare da al'ummar gidan da ba wanda ya iya fusgar sunanta sai daada.
"Ikon Allah.......kina nan bahijja?". Murmushi ta saki
"Ina nan daada...." Ta amsa mata dashi tana ji a jikinta lallai akwai tarin qalubale masu yawa.
Kasa daidaita nutsuwarta tayi lokacin da take sallama zuwa cikin falon nasu. Ta sauko gaba daya daga saman kujerar cikin wani irin hanzari tana dosarta. A murya tana jin tamkar ummenta ce ta dawo,haka nan wani sashe na kamanni,duk jikinta rawa yakeyi,hawaye kuma suka balle mata,irin hawayen nan da suke zama tilas zubarsu a idanu. Cak komai nata ya tsaya sanda ta fada jikinta tana sakin kuka lokacin da muryar uncle abdulk'adir. Muryar data sake sanya kowanne sashe na jikinta rawa,ta zare jikinta daga na bahijja ta daga kanta kaman me ciwon wuya tana ware fararen idanunta da suka sauya kala akan uncle abdulk'adir din dake takowa zuwa cikin dakin.
Yana nan dai kaman yadda suka sanshi,giant dashi me yawan daurewar fuska. A wancan lokutan basu da shekaru sosai,wannan ya sanya basu fiya fahimtar rashin sakin fuskar nasa ba saboda yana da fara'a ga yara. Sai ta riqe bahijja sosai wadda suke kira da didi,itama ta kama nata hannun tana shirin zaunar da ita.
◦•●◉✿ "Oh.....Allah na gode maka" Abinda kawai ya iya fada kenan. Tako ina yana jin gumi yana tsatsafo masa,tsakanin me jadda da sabreen baima san wanda yafi wani sakashi a masifa ba.
Hannun kujera ya samu ya zauna yana share fuskarsa da hannun babbar rigarsa,yana jin gaba daya duniya ta juya masa baya cikin qanqanin lokaci
✿◉●•◦𝘽𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙖𝙬𝙖 𝙪𝙠𝙪 ✿◉●•◦
Dukkanin wani kuka a yanzu a kuma wannan lokacin ta yishi,kukan faduwa da rashin nasararta da kuma rashin hango galaba qarara daga kaucewa wannan birkitaccen auren da yafi kama da auren bauta.
"Ba abinda zaki mana.....ba abinda zakiwa kanki ki kyautatawa kanki da rayuwarki sai aure......a wannan shekarun zaman me kike tunani zakiyi?,har kice bakison aure?,idan bakison aure me kikeso sabreen?.....kisa a ranki idan har bakiga afkuwar auren nan ba to daya ne a cikin ku biyu ya mutu.....ko ke ko shi".
"Ya Allah......kasa ya mutu.......ya Allah ka sanya wannan tafiyar da yayi ya yita kenan" Ta samu kanta da furtawa a zahiri. Adduar data baiwa kowa mamaki a wajen banda kawu rufai dake zaune daga gefe. Gigitacciyar tsawar da uncle abdulk'adir ya sake mata ya sanyata runtse idonta kawai ba tare data motsa ba tana sauraren bugun zuciyarta,ko qas zuciyarta bata rusuna ko ta canza ba game da adduar data masa,saita dinga ninks wata can qasan zuciyarta tana maimaitawa akan Allah ya kawo duk wata sila ko hanyar da zaiyi nisa da rayuwarta ya barta ta huta kamar kowacce 'yantacciyar d'iya.
"Wai ina amanar da nake yawan tambayarka akai rufai game da yaran nan?,ya akayi ka bari sabreen ta zama haka?". Wani lafiyayyen gumi ne ya yanko masa,baisan iya adadin qaryar sunan nan lafiya qalau da ya yiwa abdulk'adir ba......baisan iya adadin saqon da ya aikowa yaran ya handame ba ba tare da yabar kowa yasan ma anyi aiken ba.
Idanunta kawai taja ta rufe lokacin da didi keson jin ko tana da wata matsala ko kuma damuwa ne game da auren bayan kasancewar ita ce batason mijin?.
"To ta cewa didi me?,ta gayawa didi mamarsa tana da manufar aurawa danta shi?,while shi kansa batasan me yasa ya nemi aurenta ba da kanshi?. Tana jin bata da sauran option a yanxu illa ta tsaya ta zuba idanu kawai a buga wannan wasan da ita.......waye zai zama WINNER?.....WAYE KUMA LOSER a tsakanin mutum ukun?.
𝐒𝐚𝐛𝐫𝐞𝐞𝐧
𝐌𝐮𝐡𝐚𝐦𝐦𝐚𝐝 𝐟𝐮𝐚𝐝
𝐌𝐚𝐚𝐦𝐚𝐡 𝙜𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖
𝐇𝐚𝐣𝐣𝐚 𝐡𝐚𝐫𝐢𝐫𝐚
Daga gefe da nata shirin da KO MEYE SHI?.
Abu daya ne zata ce ya sanya wani dan siririn haske da sanyi cikin mummunan yanayin da take jin kanta a ciki.....shine samun wani haske a dakin da ya zama tamkar makwafin uwa a garesu. Yadda haneefa huda da nadra suka sanya didi a gaba tamkar ummensu ce ta dawo. Ita kuma tana tsakiyarsu,hira sukeyi tamkar xasu kwana a zaune ita dasu,su din kamar zasu koma cikinta,yayin data rungumesu da kyau itama kasancewar Allah bai bata haihuwa ba.....dangin mahaifinsu ko a wancan lokacin na rasuwar yayarta musamman kawu rufai su sukayi tsayin daka suka hanata koda haneefa da take qarama a sannan,sai haqura tayi badon zuciya bata so ba.
Kwana da wunin da sukayi da sabreen ba wani abu daya canza daga yanayinta. Ta riga tayi giving up tun bayan da kawu abdulk'adir ya wuce yabar didi bahijja da zummar zata zauna dasu a nan har sai lokacin biki yazo za'a share biki da ita sannan ta koma.....komai ya qare kenan!,abinda ya rage mata daya ne shine......ta maida kanta kan tsara yadda zata maidawa kowa aniyarsa......amma har yanxun tana jin abun kamar ba gaske bane.....tana jin kamar a mafarki ne.....yaya akayi wadannan mutanen suka mamayeta har haka?,suke shirin juya rayuwarta dare daya daga wani bigiren zuwa wani......bigiren da bata taba tunanin zata tsinci kanta a ciki ba har abada.
✿◉●•◦𝙎𝙖𝙣𝙣𝙪 𝙨𝙖𝙣𝙣𝙪 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙣𝙖 𝙯𝙪𝙬𝙖......✿◉●•◦
Isowar akwatinan auren muhammad jadda zuwa gidansu sabreen ahmad kadai ya sake gigitar da tarin jama'a na cikin gida dana waje. Wasu irin qasaitattu kuma lafiyayyun luxury akwati kala daban daban da suka tasamma jimillar akwatuna talatin da shida wato dozen hudu dalla dalla inji munafukai da 'yan gaza gani akwatina d'ai d'ai har arba'in da takwas kenan.
Iya kwati set qwaya daya tal kawai idan aka fiddata aka saidata banda kayan cikinta sun isa musulmin jarin cikakke ga mutum a qalla goma sha kyan kyan. Wasu sabbin designers akwatuna da sabreen din ta zama mutum na farko cikin jerin ahalin iyalan masu arziqi data mallakeshi.
Fadin irin tarin dukiya da suturun alfarma dake ciki ma bata baki ne. Lefe ne da aka zubawa kayan ado na gold da diamond a ciki kamar yadda yake shine ainihin sana'ar muhammad jadda,wanda duk wanda ya gani sai ya tabbatar lallai sun cika kayan aure daga wajen mamallakin kamfanin diamond da gold.
"Anya bayan wannan sana'ar kuwa baya yankan kai?,suna kyautar mota kaman suna kyautar sweet.....bayan motar da aka hado mata da ita a kayan aure yanzun guda biyu suka sake sakawa akai kayan lefen fa,wai kyautar uban ango da uwar ango.....nabeela wannan wacce irin baqar rana ce?" Hadiyya da labarin lefen ya hanata zaune ya kuma hanata tsaye cikin dakin hostel din nasu ta fada da idanunta da sukayi jajur don kuka.
Wadda ke zaune a gefensu ta saki murmushi
"Kina wasa da bariki.....ai indai kin cika macen bariki me wayo to tabbas kafin ta bare dake kike kama kanki.....ki samu wani alaj din kiyi wuf dashi ki shige daga ciki abinki....."
"Muffy.......motocin millions of naira fa kaman ana bada biscuit?" Hadiyya ta sake maimaitawa. Tsaki wadda suka kira da muppy din ta saki tana jawo kwalbarta
"Har yanxu na yarda da sauranki baki waye ba.......wai shin kinsan waye muhammad jadda kuwa indai da gasken shi zata aura?.....to bari kuji.....ni ina samun labarinsa ta bakin mata da 'yammatan dake cudanya cikin manya manyan Billoniers din da muke dasu.....kusan burin kowacce mace a cikinsu ta samu kutsawa koda gefen inda yake......amma inaa....saidai hange daga nesa,baya shan koda taba ballantana akai ga giya......bai daga idanu ya kalli d'iya mace ballantana har ta burgeshi akai ga batun nemanta.......abu me tsananin daure hankali da tunani kenan. Koda kyau ne da namiji a yanzun irin na jadda zai wahala kaga baya neme nemen mata ko shaye shaye.....ballanta shi ya hada duka,ga kyau ga masu gidan rana baja baja tamkar ganyen bishiya.......bai shaye shaye ba neman mata,ya rufe wadannan hanyoyin guda biyu wadanda sune suke saurin sawa a cimma d'a namiji.......budaddun qofofi masu saurin isar da sharri rayuwar d'a namiji" Tayi zancan da confidence dinta ganin yadda dukkansu suka bata hankalinsu. Ita kanta tana jin dadin106
Ita kanta tana jin dadin bayar da labarin qwarai.....don har a qasan zuciyarta tana jin muhammad din winner ne na gaske daya tsallake tarakunan da matasan masu kudi da yawansu basu iya tsallakewa,idanma basa yin duka to zaka samu sunayin daya daga ciki tabbas!.
"To.....ko muna da rabon samun irin wannan mazan ko sai a aljanna?" Maganar daya daga cikinsu kenan data bawa kowa dariya duk da suns taya 'yar uwarsu ne jimami. Su kansu a karan kansu sun sani.....samun irin muhammad din sai mace me tsananin sa'a,kowacce cikin zuciyarta kuma ba tare data bayyanawa hadiyya ba ji takeyi dama itace sabreen din,duk da cewa hadiyyan ta gaya musu cikakkiyar KARUWA CE.
Duk yadda bibo ke fama da habaici a ranar kasa komai tayi. Wani irin baqinciki ke nuqurqusarta kaman ta hadiyi zaciya. Inda tasan lalacewar sabreen ba wani abu bane da zai zame mata illa ba ya hanata auruwa da tuntuni ta dade da sanya hannu a lamuranta ta kadata tayi nesa dasu bare yau taga wannan abun takaici. Lefe ya kasa dauke qasan?,sai babban falon marigayi mahaifinsu na sama aka kaishi aka zube a can?. Didi ta sanya muqulli ta rufe don sunyi yawan da za'a ce wai anzo kallo an zauna an bisu daya da daya an kalla kamar yadda aka saba ganin lefe. Wanda gulma ta qarewa kuwa saidai ya leqa ta windo ya kalla,iya Kalllon bayan akwatin kawai ba tare da ankai ga budesu ba wani abu ne me qayatarwa a idanun me kallo.
Tana kwance kamar kullum har akayi didifniyar ajiye lefen dama komai da komai,idanu take budewa kawai lokaci bayan lokaci ta kalli su huda.
Ba wata damuwa sam sam a tattare dasu,sai take hangowa ma kamar farinciki suke ciki. Sun samu didi da yanzu duk inda ta motsa suna wajen ta zame musu uwa na wucin gadi. Tausayinsu takeji qwarai,a ina zata barsu randa aka maqala mata wannan maqalallen auren?. A yanxu kam akwai walwala me yawa tare dasu saboda qishirwar UWA da suke kasheta tare da didi din.
"Anata hidima anata hidima......amma mu har yanxu bamuga qyallin ango ba,bamuga yazo gaisuwa ko ganin amaryarsa ba bare akai ga batun gaidamu iyaye" Irin lafazin da ya fita daga bakin me biwa bibo kenan bayan ta yaye labulen dakin suna gaisawa da didi.
Dan murmushi didi da tasaki,duk da itama abun yana ranta,bata taba ganin ya kirayi sabreen din ba duk da tasan zai wahala ta daga wayar a yadda ta kafe dinnan bataso......bata taba jin ance gashican yazo ba koda ba zata fita ba
"Danku ne fa?,me kike ci na baka na zuba?,ai har sai kun gaji da ganinsa"
"Aiyo to......naga mun aurar amma ba haka mu muka saba gani ba,koda yake sha'ani me arziqi daban dana talaka" Daga haka ta saki labulen tana wucewa don saqo ne takeson ta isar ta kuma tabbatar ya kai inda take da muradi.
Sanda didi ke zaune saman kanta tana jefa tambayar kanta,sai ta mayar da idanunta kawai ta rufe tana cewa
"Ki tambayi kawu" Tana ganin shike da cikakkiyar amsar bada ita ga wulaqantaccen aure irin wannan. A duniyar auren hadi.....a kuma duniyar auren dole bata taba ganin kalar nata auren ba......ki sau daya bai taba tako qafarsa unguwarsu bama bare akai ga isowarsa qofar gidan mahaifinta da zummar nemawa kansa ita kamar yadda kowanne d'a namiji yakeyi. Sai damunsu akeyi da kawo dukiyar data tabbatar tamkar magana ce a fakaice ake gaya mata na sun zabi kudi ga kudi nan.......kawu yayi mata abinda ba wani mahaluqi daya isa yayi mata shi,hakanan ba wanda ya kwatanta yi mata hakan sai shi. A kullum kalmar UBA da Allah yabashi wannan take dubawa take dauke masa qafa da idanu akan wasu abubuwan,banda haka bata tunanin akwai wanda zai mata hakan ta lamunta.
𝘼𝙡𝙝𝙖𝙟𝙞 𝙝𝙖𝙢𝙯𝙖 𝙠𝙞𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙤𝙡𝙙 𝙧𝙚𝙨𝙞𝙙𝙚𝙣𝙘𝙚
"Alhamdulillah" Ta samu kanta da furtawa tana shafa hannunta saman fuskarta bayan ta kammala sallar ishai a ranar. Rana ce data zama ta hidima sosai a garesu kai kace bawai lefe kadai aka kai ba......tamkar bikin ake gudanarwa a ranar. Gefe guda kuma cikin hidimar tashi suke daga gidan,akwai 'yan uwa sosai da abokan arziqi da kowa ke zaban furniture din da yakeso a sassan nata.
Har qasan ranta takejin farinciki idan ta tuna kwanaki bakwai kacal suka rage muhammad dinta ya zama magidanci kamar yadda kullum take da mafarkin wannan ranar. Abu daya ne ya tsaye.mata a rai,yake sake sanyata a shakka da kokwanto duk kuwa da abba hamza yayi qoqarin nusasheta tare da yi mata bayanin ta fidda abun a ranta wato batun mariya.
Komai da mariya akeyi,ayyukanta duka suna gwada yadda take dama dama da auren nan. Ta yiwa mariya farin sani,ba sanin jiya ko yau ba kawai......banza bata kai zomo kasuwa,hakana nan mariyar ungulu ce bata jewar banza......ta kasa aminta da haka siddan mariya keson abun nan ba wata adawa kaman yadda ta saba.....uwa uba kuma neman yazo daidai dana fuad din. A haka dai take kallon abubuwa amma kuma tanata qoqarin gamsar da kanta all is well kaman yadda abba ya shawarceta.
Sallamar musaddiq da farouq bayan sunyi knocking ta basu izinin shigowa su saka sanyata gyara zamanta yadda qafafunta zasu miqe sosai. Kaman ko yaushe tana dubansu bisa alfaharin samun 'ya'ya irinsu suka qaraso.
"Larai keson magana dake akan dakincan,tana tambaya shima zaa fitar da kayan ciki?,nace mata dai su kwashe kawai" Farouq ya fada yana shafar sumar kansa hadi da zama gefan annin musaddiq kuma ya yiwa kansa mazauni saitin qafafunta. Haka suke duk sanda suka sameta zaune koda su hudunne sai su sakata gaba a tsakiya kamar wasu yayayyu ko masu shan maama,sa. Basa ganin girmansu gaba dayansu indai suna gabanta ne.
"Eh yayi hakan....tashin nan ina jinsa kamar wasa wallahi" Anni ta fada tana alhinin bari muhallin da suka dauki shekaru a cikinsa,duk da cewa bawai sun barshi kenan ba.....nan dinma zaa sake zuba sabbin furniture da komai da komai cikin satin nan,idan sun gaji da waccan unguwar sai ta taho nan ta zauna......saidai ko kusa ko alama wannan gidan bai isa ya hada kafada da wannan din ba.
"Lokaci anni.....zakiso wancan gidan fiye da wannan fa" Kai ta kada
"Kayya.....ku yara kune qyale qyalen rayuwa ke mugu gardi.....faruqu......inason magana da surukata,ko zaka kiramin ita?" Ta tambaya farouq.
Zamansa ya gyara ya ciro wayarsa yana budeta
"Banajin ina da number surukar nan taki anni...." Ya fada a ransa yana tunanin fuad dinma baida ita,bayason kuma su fahimci hakan
"Amma bari nasa a turo sai na kira miki".
Kawu kawai ya kira kanshi tsaye ya nema number daga wajensa.
𝙎𝘼𝘽𝙍𝙀𝙀𝙉𝙉
Jujjuya wayar kawai takeyi a hannunta tana cije lips dinta zuciyarta na sake quntata. Tunda suka gama waya da matar da har yanzu ta kasa yarda wai ita din mahaifiya ce ga wancan dan rainin wayon ma'abocin girman kan mamaki yake sake cikata. Wayar mintuna talatin amma ta sanyata zaman minti ashirin tana tariyar kowacce magana data fita daga bakinta
"Duk abinda kikaga baiyi ba kiyi magana.....duk kudin da kike buqata ki nemesa a wajena zaki sameshi........burina guda daya tal shine ki cikamin burina da kuma manufar da ta sanya na nema miki auren d'ana.......wannan shi zai baki damar zama cikin jerin sahun masu kudi masu arziqi.....kuma shine zai zama kariya daga rayuwar 'yan uwanki.....domin har yanzu suna a hannun mu duk da kuwa mun sake miki su".
Kai ta jinjina tana sake cije lebe.....har yanxu matar bata santa ba......batasan wacece Sabrina da iya adadin abinda zata iya aikatawa ba......inda ace ta sanya harsashin wasan tsakanin ita da ita ne data nuna mata tata zallar qwarewar......to amma inaaaa......bisa rashin sa'a ta sanyo da rayukan da suka zama sune K'ARFINTA kuma sune RAUNINTA dole tayi komai bisa lura da kuma tsari.
Bataji nauyin gaya mata kai tsaye ba.....ta shaida mata cewar
"Bani buqatar ku nunawa duniya ni.....duk wani events bani da sha'awar zuwa.....koda kin tsara hakan dani ki cireni a ciki" Amsar data bawa maamah sanda ta bata daman shirya duk kalar events din da take da buri ko mafarkin gudanarwa koda kuwa wasu qasashen take so ayi jigilar qawayenta don gudanar da komai a can. Ta bude mata komai ne don a nata karatun.....gogaggiyar mace kaman sabreen da tasan dadin kudi da bariki.....tabbas zataso cikin manyan burika dama mafarkanta tayi kalar bikin daya zarce na kowacce yarinya dake tashe ko kuma take jin kanta ko ubanta wani ne.
"Ma sha Allah.....alhamdulillah,to Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa....gata bari na bata" Muryar didi kenan data shigo dakin riqe da wayarta
"Ga surukarki.......karbi mana" Didi ta fada tana miqawa sabreen wayar. Kanta ya daure,wacce surukar tata kuma?,wata dabance bayan wadda ta gama tumasanci yanzu ko kuwa?. Yadda didi ta tsareta da ido......ba wani sauran abinda zatayi saita saka hannu ta karba din.
"Assalamu alaikum warahmatullah" Anni tayi cikakkiyar sallamar da wannan muryar tata data cika da nutsuwa da dattako,muryar data tsarga tun daga zuciyar sabreen din ta sace wani nauyi da fushi daketa kai kawo a qirjinta cikin mintuna qalilan ba tare data ankara ba
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Ta samu kanta da amsawa da wata nutsuwa data sameta ba tare da tasan daga ina bane.
"Allah yasa zaki iya shaida wannan mamar taku,ina fatan ya gaya miki komai a kaina?" Anni tai maganar da sautin murmushi a muryarta. Dif tayi don batasan me zatace mata ba.....me zai gaya mata mutumin da ko fuskarsa bata gama tantancewa ba bare duk wani abu daya shafeshi.
A taqaice anni ta yiwa sabreen bayanin matsayinta. Bayanin daya dinga zillo saman zuciyar sabreen yana sake rikita mata lissafi,iyayensa biyu?,masu mabanbantan dabi'u da halaye,wadannan sune kawai abinda tafi riqewa tanason kuma tantancewa amma kawo yanzu kanta ya tsuke gaba daya.
"Ki daukeni tamkar mahaifiyarki sabreen.......duk wani abu da uwa kewa 'yarta zaki sameshi a tare dani in sha Allah". Kalmar data daki qirjinta ta kuma saukar da wani abu me sanyi saman ranta
"Suna da banbani" Taji ana gaya mata daga can saman kanta bayan ta sauke wayar da suka gama da ita. Tana tariyar maganganun data gaya mata cike da harshe me hikima da fasaha.....sam babu hadi ko a iya kalamai tsakaninta da waccan dake iqirarin ita ta haifesa
"Zanso nasan wacece uwar ta gaske" Ta fada qasa qasa tana duban didi dake shigowa.
"Saiki kintsa kanki.....don tace zatayi aiken me gyaran jiki da zasu fara aikinsu daga gobe har zuwa ranar da zaa daura aure.......amma sabreen" Didi ta fada tana neman wajen zama gefan sabreen din ba tare data damu da damuwar da batun gyaran jikinta ya saukar mata ba.
"Mamarsa nada kirki har haka?.....me yake tsananta damuwarki......duk wani motsi nasu yana alamta su din mutanen kirki ne.......wanda dukiyarsu bata rufe musu idanu ba.....don Allah ki kwantar da hankalinki......tabbas ina kyautata musu zato"
"Ba zaki gane ba didi,abinda kike gani a zahiri ba shine a badini ba.......to waima wanna jikin zaa gyara?" Tayi dukka maganar ne idanunta a kulle,amma wannan ta qarshen ta ware idanunta ne akan didin.
Kallonta didin takeyi tana jin kamar sabreen din bayan matsalar miskilanci da yake damunta harda matsalar jinnu.
"Wanne jikin kike dashi bayan wannan nakin?,ko kinaso kiyi ma dattijuwar matar me tsananin karamci gardama?" Ido ta tsurawa didi tana jin kamar fa bai kamata tace mata bataso ba ko?,to amma ai sam gyara jiki ma baihau ba a wannan bigiren da take kai ita,don haka ta mayar da idanunta ta rufe tana motsa labbanta
"Da zaiyiwu shine abunda nafiso ta janyemin". Didin ta jima a zaune tana kallonta mamaki yana sake kamata,sai data gaji don kanta kawai ta miqe tana cewa
"Allah ya kyauta" Ta fice a dakin.
"Anni da suruka.......Muryar nan kamar na santa anni" Musaddiq ya fada yana kallonta. Sai a sannan ta iya dauke kanta daga fuskar wayar kamar sabreen dince a gabanta,batasan me yasa ta jarabtu dason yarinyar da bata taba ganin fuskarta ba hakanan
"Ba mamaki ka taba rakiyar zance a boye ko jinsu suna waya da hamman naka" Dariya ta subuce masa
"Anni wannan soyayyar waye yasan sanda aka qullata?,banda ansan gidan su da sai nace mijin aljana ya bishi da gaske aljanar xaya aura"
"Ungo nan.....wato wannan dan kaniyar yayan naka ya koya maka ko?,maza ka fadi yaji,idan shi yasha a hannunsa kaidai kasan sauran"
"Tuba nake" Ya fada yana rufe bakinsa da hannunsa yana qoqarin boye dariyarsa.
********Tana kukan zuci qwarai da gaske wanda ke tattare da zargen abubuwa masu yawa data tanadi tunkarar kowa da komai......amma hakan bai hana zuwan me gyaran jikin da take aikinta da wata irin qwarewa tamkar zata sauya fatar jikin ta ta ainihi da wata ta daban ba.
Komai ta kawo idanu ta xuba masa kamar dai komai nata ya daina aiki.....saidai fa wannan kwanyar......wannan zuciyar suna nan suna aikinsu daidai.
A daidai sanda komai yake tafiya,shirye shirye suna nisa,kwanakin qulla auren da zai zamewa rayuwarsu 𝙈𝘼𝘽𝙐𝘿𝙄n tafiya bisa wata turba da basu taba kawowa zata bude musu......a wannan lokacin shirye shiryen maamah sukayi nisa itama.
Ta narka kudaden da batasan adadinsu ba wajen bokanta.....wanda ta saida tsaffin kadararrta ta narkasu zuwa kudin da zasu isheta aiwatar da komai.
Kowacce rana da gari zai waye,yana waye mata ne da tsananin farincikin ganin kusantuwar cikar burinta........sanin wacece yarinyar wacece SABREEN adan gamayyarsu ta qididdigaggun lokuta ya sanya ta gabatarwa da boka SUNANTA don tana buqatar aiki a kanta na musamman.
𝙏𝙪𝙧𝙦𝙖𝙨𝙝𝙞......𝙞𝙙𝙖𝙣 𝙠𝙞𝙣𝙖 𝙩𝙪𝙣𝙖𝙣𝙞 𝙝𝙖𝙣𝙜𝙚 𝙠𝙤 𝙝𝙖𝙨𝙖𝙝𝙚𝙣 𝙖𝙗𝙞𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙪 𝙥𝙖𝙧𝙩 2 𝙣𝙖 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙣𝙖𝙣 𝙩𝙤 𝙠𝙞 𝙜𝙖𝙜𝙜𝙖𝙬𝙖𝙧 𝙖𝙟𝙞𝙮𝙚 𝙝𝙖𝙨𝙖𝙨𝙝𝙚𝙣𝙠𝙞.....𝙙𝙤𝙣 𝙗𝙖 𝙡𝙖𝙡𝙡𝙖𝙞 𝙗𝙖𝙣𝙚 𝙘𝙖𝙣 𝙢𝙪𝙠𝙖 𝙣𝙪𝙛𝙖 😁😄
𝙄𝙙𝙖𝙣 𝙗𝙖𝙠𝙞 𝙨𝙖𝙢𝙪 𝙠𝙖𝙧𝙖𝙣𝙩𝙖 𝙥𝙖𝙧𝙩 𝙤𝙣𝙚 𝙗𝙖 𝙠𝙞𝙮𝙞 𝙝𝙖𝙣𝙯𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙠𝙖𝙢𝙖𝙨𝙝𝙞 𝙠𝙞 𝙗𝙞𝙗𝙞𝙮𝙚𝙨𝙝𝙞 𝙙𝙖 𝙠𝙮𝙖𝙪......𝙙𝙤𝙣 𝙜𝙪𝙣𝙙𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙮𝙖𝙣𝙖 𝙖 𝙜𝙖𝙗𝙖
𝙕𝙖𝙯𝙯𝙖𝙛𝙖𝙣 𝙩𝙪𝙜𝙜𝙪
𝙈𝙖𝙠𝙞𝙧𝙘𝙞
𝘿𝙖 𝙬𝙖𝙩𝙖 𝙞𝙧𝙞𝙣 𝙗𝙖𝙝𝙖𝙜𝙪𝙬𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙗𝙞𝙧𝙠𝙞𝙩𝙖𝙘𝙘𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙨𝙤𝙮𝙖𝙮𝙮𝙖
𝘼𝙠𝙬𝙖𝙞 𝙡𝙖𝙨𝙩 𝙥𝙖𝙜𝙚 𝙙𝙖 𝙣𝙖𝙠𝙚𝙨𝙤 𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙠𝙖𝙧 𝙢𝙪𝙠𝙪 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙞 𝙭𝙖𝙢𝙖 𝙢𝙪𝙧𝙛𝙞 𝙜𝙖 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞𝙣
𝙏𝙤 𝙖𝙢𝙢𝙖 𝙞𝙙𝙖𝙣 𝙙𝙖𝙢𝙖 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙗𝙖𝙣𝙞 𝙙𝙖𝙢𝙖 𝙗𝙖 𝙯𝙖𝙢𝙪 𝙝𝙖𝙙𝙚 𝙗𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙨𝙖𝙡𝙡𝙖𝙝
𝘿𝙪𝙠 𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙣 𝙦𝙤𝙦𝙖𝙧𝙩𝙖 𝙣𝙖 𝙝𝙖𝙙𝙖 𝙢𝙪𝙠𝙪 𝙨𝙝𝙞 𝙞𝙣 𝙨𝙝𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝,𝙙𝙤𝙣 𝙯𝙖𝙞 𝙯𝙖𝙢𝙚 𝙢𝙪𝙠𝙪 𝙈𝘼𝙉𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼.
𝙃𝙐𝙂𝙐𝙈𝘼𝙉𝙆𝙐 𝘾𝙀.