Gaban Nana ya faɗi, cikin tsoro da razani ta ce "Waye? Waye a nan?" Sai dai shiru ba a yi mata magana ba.
BUZU BOOK 3 HAUSA NOVEL
78 Gaban Nana ya faɗi, cikin tsoro da razani ta ce "Waye? Waye a nan?" Sai dai shiru ba a yi mata magana ba. Ta kunna fitilar kawai ta ga Imam Hammad a tsaye a cikin ɗakin. Ja da baya ta yi a razane tana toshe bakinta saboda ihun da take shirin kurmawa saboda razani da tsoro. "Idan ki ka yi ihun da Asal ta ji ki, za ki yi mata bayanin abin da ya kawo ni ɗakin nan, kuma duk hukuncin da ta zartar a kan ki sai an yi miki shi, komai tsaurin sa." Ta marairaice ido tana kallon sa cike da tsoro. Ya tako a hankali ya ƙaraso gabanta, ya zuba mata idanunsa da suka ƙara rikita ta, jikinta har tsuma yake yi. "Wace ce ke?" Ya yi maganar yana kafe ta da idanunsa. "Ni ba kowa ba ce" Ta furta jikinta na tsuma cike da tsoron ko yana hayyacinsa jiya da ta je turakarsa. "Ki gaya mini wace ce ke? Kuma da wace manufar ki ka zo gidan nan?" Ta rintse idanunta tana girgiza masa kai ta ce "Wallahi ni ba kowa ba ce ba, Matarka ce ma ta kawo ni nan" "Kin sa…