CANJIN RAYUWA CHAPTER 19 BY HALIMA A K/MASHI

CANJIN RAYUWA CHAPTER 19 BY HALIMA A K/MASHI

 

yi. A kan Zainabu kuma tace kar ya damu, kila ita din ba alheri ba ce a gare shi. Ta ce, in da zai yarda ma da ya koma makaranta don zurfafa iliminsa gaba daya a fannin bokon da kuma Islamiyyar. Ya ce, shi ma tunaninsa ke nan a yanzu. Sukayi

bankwana, bayan ta ba shi wani turare mai kamshi. Ya fito Mahmud ya kai shi tasha.

Bai samu motar Abuja kai tsaye ba, don haka sai ya hau ta Kaduna. Suka miki hanya, zuciyarsa da rauni, bai san lokacin da zai warke ba.

Hajiyar Mardiyya, matar Alhaji Isa Mani, abokin Alhaji Bashir ita ce ke kwada: sallama a falon Hajiya Sauda. Hasina ce ta fito daga dakinsu ta ce, “sannu da zuwa Maman su Nabila.” Ta ce, “yawwa Hasina.

Hajiya fa?” Ta ce, “bari in duba ta.” Nan Hajiyar Mardiyya ta zauna kan kujera.

Hasina ta fito ta ce, “tana wanka ne. ” Hajiya Mardiyya ta mike, “bari in shiga cikin dakin.” Kawaye ne sosai, har yanzu ba su yada juna ba, don sun fi mazan nasu

zumunci, har da matar Alhaji Kabiru, Hajiya Ramatu, abokansa na tun ana talakawa.

Kan gado ta zauna tana ‘yan dube-dube. “Ke kullum aka zo dakinki kal, sai ka ce Amarya.” Daidai lokacin ta fito tana cewa, “me kika ce?” Hajiya Mardiyya ta maimaita. Hajiya Sauda ta yi dariya, to ni ke gyara dakina da kaina. Ku ko kun fi son na ‘yan aiki.” Ta ce, “to meye aikinsu, in ba shara da wanke-wanke ba?” Hajiya Sauda ta ce, *ku dinga duba masu. Kullum ina fada muku, suna yi kuna dubawa, kuma

gyara musu.

Hajiya Mardiyya ta ce, “ke ni zuwa na yi in ji dalili ko kuma laifin da nai miki ba ki fada min biki ba, sai dai in ji a gurin Alhaji.” Hajiya Sauda ta yi tsaki, “Kin san Allah, ban san komai a kan bikin nan ba. Ke in takaice miki, yanzun Alhaji fushi yake yi da ni.” Hajiya Mardiyya ta ce, “a kan me?” Hajiya Sauda ta ce, “kin san ba ta son auren, shi ke so. Ya kira ni wai in tursasa mata ta yi abin da yake so. Sai na nuna masa cewa ba ruwana, yanzu ne aka san da ni? To ni shawara zan ba ta, ba tursasawa ba. Kar ki dada, kar ki raga. Daga wannan shi ne laifina. Wai nice ke zuga ta. Har yau bai sake ce min Kala a kan bikin ba. Na’ima take fada wa su Hasana ta waya wai Nafisa ta je Dubai siyan kaya. An kawo lefe, an yi kaza, an yi kaza.

Hajiyar Mardiyya ta ce, “amma

Alhaji bai kyauta ba. Ko da ke ke zuga ta, ai

kamata ya yi ya ba ki hakkinki na haihuwa.

” hajia Sauda ta ce, ni ma dai shi na gani. Don haka nasa musu ido. Ya ma ki zuwa garin nan sam. Ko kiran waya ya yi, sai ya yi ta wani dake-dake yana magana a cije.Hajia Mardiyya ta ce, amma da

kin yi masa magana da kanki, ki yi masa bayanin nufinki don ki amshi ragamar auren ‘yarki.” Hajiya Sauda ta ce, kin san Allah ba zan kula auren nan ba. Kuma ba zan taba yi masa magana a kan wai ya fahimci ban zuga Mimi ba. Mu je a na zuga tan. Saboda ita ma ba halin kirki gare ta ba. So nake su gane kurensu, dukkansu shi da ita.” Hajiya Mardiyya tace, “shi ke nan, Allah ya kai mu. Mu dai za mu je biki. In Abuja din ne, in nan ne ma dai duk da mu za a yi.” “Allah ya taimaka,” in ji Hajiya Sauda.

Ana saura sati daya bikin ne, Alhaji Bishir ya zo Katsina. Bai ko sanar da zuwansa ba. Barcin rana takeyi lokacin da ya iso. Yaran suka yi masa sannu da zuwa.Kai tsaye ya nufi dakinsa, ya bude ya shiga.

Ya zuba jakar hannunsa da hularsa zuwa wayarsa a kan kujera. Shi kuma ya zauna a bakin gado.

Husna ce ta shiga dakin Hajiya

Sauda ta tashe ta, tana sanar mata zuwan Dady. Ta sha mamaki sosai, domin sai ya sanar kafin ya iso. Ta kalli Husna, “shi ne ya ce ki kira ni?” Husna ta ce, “a’a. Ya shiga dakinsa ne kawai• Hajiya Sauda ta ce, “to

je ki ina zuwa. Har ta mai da kanta ta kwanta, a zuciyarta ta ce tunda da abin da ya zo gidan ke nan ba za ta kula shi ba.Amma sai wata zuciyar ta ce, “mijinki ne, kina kasansa ki je.”Ta same shi yana cire safar kafarsa.Ta yi sallama, ta shiga. Daga bakin kofa ta-tsaya tana fadin, “sannu da zuwa.» Alhaji a

ciki ya amsa da cewa “yawwa.”Ta zauna a

hannun kujera; na ji mamaki, ba ka ce min kana zuwa ba, kamar yadda ka saba.” Ya dago ya dube ta “laifi ne?” Ta lumshe ido, cikin takaici ta ce, “a’a babu laifi.” Ta mike tsaye, “me kake bukata? Ina nufin abin da za ka ci ko sha?” ba na bukatar ko Ya mike, “alhamdulillah daya.Ta ce, “har wanka?” Ya dan yi tsaki, “kin ga na yi datti ne?” ta kautar da kai gefe, sannan ta yi dan huci, sannan ta mike. Har ta kai bakin kofa, ta kasa jurewa, ta dawo, “Alhaji wai laifin me na yi maka da duk ka canza min?”

Ya kalle ta, “ba ki san kin yi laifi ba ko?” Ta ce, “wallahi ban sani ba. Ka sanar da ni mana. Ba sai in ba ka hakuri ba.” Ya ce, “ban zaci zan ce ki yi abu ba, ta.” Ta katse shi, “na zuga ta kuma? In ji ta ne ta ce na zuga ta? Shawara na ce zan ba ta,- kuma na ba ta. Ka tambaye ta wace irin shawara na ba ta? Zan yi mamaki sosai in ka ce ka mance halina. A tunanina mun kai: matsayin da za ka san abin da zan iya da kuma wanda ba zan iya ba. Don ni yanzun zan iya rubuta kundi a kan halayyarka.

Haka kuma in an fadi wanda ba za kaiya ba, zan ce sam ba za ka iya yin haka ba.

Kansa yana kasa, ya yi shiru, domin ya san cewa gaskiya ta fada. Can ya dago kai, “me kika ce mata?” Ta mike ta koma kusa da shi. Bayan ta dauki wayarsa, ta soma latso lambobin ta kai kan lambar

Mimi ta danna kira,sannan ta latsa

‘handsfree’. Sai da ta soma ringing sannan ta mika masa, “ina son ka tambaye ta, mu

Ya ce, “Mimi, in tambaye ki?” Ta ce, eh Ya ce,

Dad.” Ya ce, “me Mamarki ta fada miki game da auren Abbas?” Ta ce, «wace Maman, Momy Nafisa?”

ya ce, “Mahaifiyarki.” Ta tura baki, “Dad cewa fa tayi wai in hakura in bi abin da kake so, ko

* don irin kaunar da ka nuna min. Wai shawara ta ba ni.

“Yace, “shike nan.”

Yana kashe wayar, Sauda ta mike. Ya kamo hannunta, “kar ki yi fushi matata, ki yi hakuri, na fahimce ki. ta danyi jim, sannan ta ce, “shi ke nan ya wuce.” Ya ce, “to zauna mu yi maganar auren Mimi.” Ta ce, “ba ni da ta cèwa game da auren Mimi, face Allah ya ba da zaman lafiya.

Yanzu ka hakura za ka ci abincin?” Ya girgiza kai, “a’a, sai in kin zauna.” Ta lumshe ido, sannan ta zauna.

Ya ce, “ni mana yi miki laifi ban fada miki komai ba. Yau saura kwana bakwai.

Kuma za a yi bikin ne a can Abuja.” Hajiya

Sauda ta ce, “babu damuwa. Allah ya sa a yi lafiya.

* Ya ce, “ameen. Me kuke bukata a

‘cikin bikin ke da yaranki?” Ta ce, “ba ma bukatar komai. Bikin da ba a nan za a yi shi ba. Mu ma fa ‘yan gayyata ne.Yace, “ba na son kina fadin haka. Ba za ku yi Ashoben ba?” Ta ce, “a’a, ba za mu yi ba.” Ya ce, “don me?” Ta ce, “ba za mu samu dinki ba.

Karka damu. Yace, “shi ke nan.”Ya kwana, washegari ya wuce Malumfashi. Ya koma Abuja saura kwana biyar biki. Kuma ranar ne aka yi jeren Amarya a gidan Angonta.

Ismail ya isa Abuja’ yammacin magariba. Maigadi da ya soma ganin sa ya sha mamaki. Ya ce, “Malam kai ne ka dawo?”‘ Ismail ya ce, “ni ne. Daga kiran

“sallar magariba da ya yi, ahalin gidan suka san Malam Isma’il ya dawo. Bayan sun fito sallar Isha’i ne, Alhaji ya bukaci ganin Isma’il a kebe. Bayan, sun gaisa ne Alhaji ke tambayar Isma’il lafiya ya dawo da wuri?

Ismail bai boye masa komai ba. Ya fada masa abin da aka yi masa. Ya ji ya tsani garin Katsina. Alhaji ya ce, “kar ka damu.Allah ya sa haka ne mafi alheri a gare ka. Isma’il ya ce, “amin. Na gode.”

Washe gari saura kwana hudu biki, Amarya ta sha gyaran jiki, ita da Na’ima.Duk abin da aka yi mata, an yi wa Na’ima.Mai gyara ta musamman Momy Nafisa ta dauko. An zuba musu zanen lalle har ba za ka iya bambance Amarya ba. Kawayen Mimi su’ Mina suna ta kai koma don ganin shirye-shiryensu sun kayatar.

Yammacin Laraba za su yi family night. Na’ima ta yi zaton zuwan ‘yan Katsina, amma shiru. Mimi ba ta damu ba, don ta san ita ba zama za ta yi ba. Rashin zuwansu ma zai fi mata. A ranar Alhamis kuwa za su yi ‘Mothers day’, wanda Momy Nafisa ta shirya. Kuma a ranar ne Mimi suka shirya guduwa, ita da Khalil dinta.

Amma Momy Nafisa a nata tsarin, sai daren Juma’a, in an dawo daga kumbo, an yi kamu ke nan, sai ta sa Mimi ta tubure. Daga nan sai ta tura Na’ima ta ce wa Dad din su ita ta yarda a daura da ita.

Anyi Mothers day lafiya an tashi ana, ta daukar hotuna, Mimi ta daga wayarta ta kira Khalil ta ce su zo, shi da wani abokinsa.

Kamar za ta yi magana da wani ta fita wajen hall din ta nufe su. Da mota suke, don haka ta shige. Kai tsaye gidan su Mimi suka koma. Babu kowa, duk ana gurin biki, amma Dad yana nan. Da ta dauko jakarta za ta sauko sai ta ji shi yana waya. Tana fitowa ta ji ashe a falonsa yake, amma daf da babban falon nasu. Sai ta yi sanda ta fice.

Da gudu ta ja mota suka tafi.

Ta dubi Khalil, *Yanzu ina muka nufa?” Yace Kaduna. Don in muka ce za mu kwana a Abuja, da safe za a kama mu.

. Haka cikin daren nan suka dauko hanyar

Kaduna. Gudu suke yi sosai, ga shi lokacin sanyi. Ga Mimi ba ta son sanyi, kuma kayan jikinta irin na Amare ne, ba na dumi ba. Ta kudundune duk da cewa Khalil ya cire T-shirt din sa ya ba ta ta dora a kan kayan jikinta. Shi kuma ya zauna da singileti. Zuciyar Mimi ta kasa natsuwa, wani gefen yana fada mata cewa ba ta kyauta ba, za ta yi nadama, ta kunyata mahaifinta. Wata zuciyar kuma tana zuga ta da cewa ke ki tafi kina kan daidai.

Al’amarin dai ga shi nan.

Dayan dare suka shigo garin

Kaduna. Sadau abokinsa shine ya kawo shawarar su shiga cikin wata unguwa su

Hmmm