da fada maka, laifinka ne kai da Nafisa ba.
Kun gina ta a kan yi mata duk abin da take so. Ya kamo hannuwarta, na yarda laifina ne. Nafisa ta biye min ne don ganin hakan nake so. Abba ya ce, to Dady ka ce ta dawo mana. In yaso ka ba ta shi wanda take so din, tunda Na’ima za ta auri wanda ba ta so din.
Ya kalli Abba, ba canji ke nan. Zan ci gaba dayi mata abin da take so ke nan? Ai yadda ba ta yi min abin da nake so ba, haka nan ba zan tabayi mata wanda take so ba. Ai ta yar da wannan gatan da kanta. Ita ma zan mata abin da ba za ta manta ba, kamar yadda ni ma ba zan manta da abin da tayi min ba. Hajiya Sauda ta ce, yanzu a ina take? Oho! in ji Alhaji. Jiya dai an ce
suna Kaduna. Hajiya Sauda ta ce, Allah ya kauta.
Daidai lokacin wayarsa ta yi
ringing, sannan Momy Nafisa ta shigo tana cewa, Alhaji kana da baki.Duk tare suka fito. Hajiya Sauda dasu Hasana saman Mimi suka nufa saboda gidan da mutane. Har an soma cin abinci. Dangin Momy Nafisa sun fi yawa. Usaina ta kalli Hajiya Sauda bayan sun zauna, Hajiya ki kira ta mana a waya, ki ce ta dawo. Ni na ga Na’ima kamar tana murna da hakan. Ta ja mu tana nuna mana lefen Sis Mimi, wai nata ne. Ga mota can a gare ji, sannan an zuba dukiya a gidanta.
Abdulkarim ya ce, ai ni na yi murna da faruwar hakan. Shi Dad din yanzu yayi nadama ai. Abba ya ce, ni zan zo ma in ma koma ne fa Hajiya. Don ba zan kwana Abuja ba. Gaskiya tunda ya samu sauki, ga shi ma sai bikinsu suke yi. Sai ga masu aiki da kulolin abinci, wai a kawo musu. Hasana ta tashi ta shige dakin barcin Mimi. Usaina ta biyo ta. Hasana ta kalli Usaina, gaskiya Sis Mimi ba ta duba wa kanta ba. Kalli fa dakinta. Dubi duk nan bangaren ta ne, ya fi ko’ina kyau a gidan nan, amma ta kasa yi wa Dad biyayya. Allah ta ban kunya. Usaina ta ce, ai ga shi nan Na’ima ta yi abin da ita ta kasa. Na san ko Momy Nafisa za ta iya sa ta, ko don su birge Dad.
Hasana ta ciro wayarta, mu gwada kira mu gani ko za ta daga. Nan suka soma kiran layinta. Yana ta ruri yana tsinkewa, ba ta daga ba. Daidai wannan lokacin Mimi tana gadon Asibiti kwance. Damuwa ce ta sa take jin ta babu wani sauki. Duk wanda ya kira, ‘tana kallon kiransa. Yanzu haka tana kallon lambar Usaina, hawaye suka soma zubo mata. Yaran da ba ta damu da su ba, ashe suna son ta. Ita yanzu tana jira ne ta ji kiran Momy Nafisa don ta san matsayin da take. In Dad dinta ya yarda, kai ko bai yarda ba, yadda take jin zuciyarta za ta koma gida ne kawai
Khalil ya dauki wayar, bayan ya ji shigowar sako. Ya ce, sako ne Dear. Ki duba ko Momy din ce ko? Cikin sauri ta amshi wayar. Usaina ta gani. Har ta ajiye wayar sai kuma ta bude. Ga abin da Usaina ta ce: Sis Mimi don Allah ki dawo Dad ba lafiya ya fadi saboda jin cewa kin gudu ne, ba sace ki aka yi ba. Sannan anjima za a daura auren Na’ima da Abbas.
Ihun da Mimi ta yi ne ya sa Khalil mikewa. Tambayar ta yake yi,me ya faru? cikin kuka take fadin, Dad ba shi da lafiya. Ni zan koma gida ne kawai. Khalil hankalinsa ya tashi. Ya shiga lallashin ta. kiyi hakuri mana dear. Za mu koma ai.
Amma bari su neme mu. Ta ce, ba ni wayata. Bari in kira Dad din. Ya ce, a’a kar ki kira shi. Tsaya ki ji. Mimi ta tsaya tana kallon sa. Ya ce, ki kira su Usaina din ki ji komai daga bakinsu.
Nan suka kira layin. Hasana ce ta daga wayar.
Mimi, cikin kuka ta ce,
Usaina! hasana ta ce, nice ba Usaina bace.
Ta ce, yanzu wane hali Dad yake ciki? Hasana ta ce ya ji sauki, babu laifi, amma ya kwana a Asibiti ne. Ya ji zafin sakon da kika turo masa cewa kin tafi saboda wani.Usaina ta amshi wayar tana cewa, Sis Mimi ki dawo kawai zai fi miki.
Saboda Dad ya ce, ba zai damu da ki dawo ko kar ki dawo ba, don Na’ima ta gama fitar da shi kunya, ta amince anjima za a daura aurenta da Abbas. Mimi ta kasa magana, kuka kurum take yi. Suka nufi Hajiya da wayar. Usaina ta ce, ga Sis Mimi a waya.
Mimi tana jin lokacin da Hajiya take fadin me za a yi mata don ga ta a waya? Abin da ya kamata ta yi ta kasa. Don haka ba ni da lokacin sauraron ta. Ubanta ma da ya nuna mata so, ta yi masa butulci, bare wani. Da Allah kashe wayarki! hasana ta katse wayar.
Kuka sosai Mimi ta dinga yi. Tun Khalil yana ba ta hakuri, har ya yi shiru ya tsaya yana kallon ta. Sai da ta gaji don kanta, sannan ta kalli Khalil Ni zan koma gida.Ta sauka ta soma duba jakarta. zan koma gida Khalil in yi wa Dad dina biyayya. Amma har abada ka sani ina son ka a cikin zuciyata.Ya ce, ki tsaya ki ji
sauki mana. Ba a sallame muba. Tace, ba na bukatar sai na samu sauki zan tafi. Ka zo ka kai ni gurin da zan hau mota.Tana daukar jakarta, ya nufi ofishin
Likitan, ya sanar da shi cewa wai tana son ta tafi. Lokacin da Likitan ya fito, ta kai harabar Asibitin. Suka sha gabanta, Khalil ya ce, Mimi ki saurari Likitan mana.
Ta ce, Likita ka yi min afuwa, awanni suka rage a daura min aure. Ka san cewa guduwa na yi? Babana ya fadi sabod na gudu.
Likita ya ce, naji za ki koma, amma ki bari ki gama karbar allura. Mimi ta ce, bari in tafi. Nayi nadama sosai da na bijire wa Mahaifina. Zan koma in ba da hakuri, in nemi ya yafe min. Sannan ya aurar da ni ga ko waye yake so.Dole Likitan ya ce, ka bar ta ta tafi kawai. Ba shi da zabi, dole ya koma ya dauko tasa jakar, suka je titin Bypass don samun motar zuwa Abuja. Suna cikin motar ne ta sake kiran Usaina,
karfe nawa za a daura auren? Ta ce,
bayan azahar ne a babban masaliaci. Muma Hajiya tace, da an gama daura aure za mu koma gida. Ta ce, shi ke nan sai na iso. Ta kali Khalil. ina za ka tsaya? yace zan je har gaban Mahaifinki, ya yi yadda ya ga dama da ni.Amma na gama hango mutuwata, in har na rasa ki. Ta kalli agogo,yanzun sha biyu da wani abu, kana ganin har za mu je Abuja ba a daura da Na’ima ba? Ya ce, zan fi kowa so in hakan ta kasance. Kiyi addu’ar Allah ya sa ni ne mijinki.
Daya saura Alhaji ya shigo gidan don shirin zuwa masallaci ko kuma in ce gurin daurin aure. Daidai lokacin ne kuma Hajiya Binta ta shigo, ita da yaranta. Mamakinta da tunaninta Alhaji ya rasu ne? Ko ko an ga amaryar ana ci gaba da, biki, shi yana Asibiti? Ta ga harabar gidan an zuba kujeri da rumfuna, sannan ga mutane da yara.Suka’ shiga falo. Nan ma duk jama’a. Dakin Nafisa Hajiya Bintar ta nufa. Cike da manyan Kawayenta, tana zaune a gaban madubi, ta yo wanka ana yi mata kwalliya.
Hajiya Binta ta ce, Nafisa wai biki ake yi ne? ta mike da sauri, sannun ku da zuwa. Kun iso?
Eh, kin san tafiyar mota, tun
bakwai muka fito. Ban gane ba, wai bikin ake ‘yi ne?
Eh. Bikin Na’ima. Cikin
mamaki, Hajiya Binta ta ce, Na’ima kuma? Momy Nafisa ta karaso gurin ta.:
•Cikin murmushi, eh, kin san Mimi ta gudu. Shi ne Na’ima ta zabi ta ‘fitar da
Mahaifinta kunya. Hajiya Binta ta ce, to shi Alhaiin wane Asibiti yake? ta ce, ya shigo yana gefensa, zai yi wanka. Tun jiya aka sallamo shi. Yana jin Na’ima ta yi wannan furucin, sai ya gyare. Wata daga cikin matan da ke zaune a kan gadon ta ce, wannan yarinya
*ai ta share wa Ubanta hawaye. Wata ta ce, ai ko ta yi sa’a. Jiya Maigidana ke ba ni labarin irin gudummawar da abokan kasuwancin Alhaji suka yi ta ba Amarya.
Babban dan kasuwan nan wanda ya fi kowa shahara a Afrika an ce zunzurutun kudi Miliyan ashiri ya ba da, banda motoci.Hajiya Binta dai ta ce, bari in duba
Alhajin. Momy Nafisa ta ce, to, ki duba shi. Yawwa Hajiya Sauda ma suna saman Mimi.
To, kawai Hajiya Binta ta ce, ta nufi sasan Alhajin, cikin al’ajabi. Gani take yi Momy Nafisa murna take yi da auren ya juye a kan “yarta.
Ta kalli yaranta, ku hau saman Sis Mimi, Hajiya Sauda tana nan. Da farko har za su noke, don suna tsoron Mimi, tunda ba ta kula su. Amma jin cewa Sauda tana nan, sai suka-nufi saman cikin mura.
Suna son Hajiya Sauda don in sun z0 hutu ba sa son tafiya. Ta iya tafiyar da yara sosai.
Ta samu Alhaji ya fito wanka, ya ce, a’a ku ma kun iso? Ta ce, eh, alhamdulillah. Sam ban zaci zan samu jikinka haka ba. Na ji an ce sugar, mene ne, mene ne. Ya ce, da sauki. Da ma karin damuwar kunyar da Mimi ta so ta ba nice.
Sai kuma Na’ima ta zo ta tare matsalar.
Yanzun dai burina a daura auren nan. Zan
•koma asibiti, Likita ya duba ni yadda ya kamata. Ta ce, Allah ya sawwake. To, yanzu mene ne labarin Mimi? Ya kalle ta.
Bayan ya gama saka wando, yana tura singiletinsa, bani da labarinta, kuma ba na bukatar in sani. Hajiya Sauda sun zo da su Abba. Ina zaton suna sama. Hajiya Binta tace, to bari inje gurinsu.
Ta samu su Abba za su fito. Nan suka tsaya suka gaisa. Sannan suka ce bari su fita su yi salla. In an daura aure za su wuce.
Hajiya Binta ta ce, wai ni Hajiya yaya lamarin ya zama haka? Ba kya tunanin cewa Nafisa ta san komai a kan gudun Mimi ko bijirewarta?. Ba na tunani, in ji
Hajiya Sauda. Ba na zargi a kan abin da ban, ji ban ‘gani ba. Abin da na sani kawai Alhaji shi ne silar komai. Haka nan kullum ina cikin addu’ar Allah ya shirya Mimi. Ya ba ta miji na gari. Ban yi fushi ba ko: da aurenta bai kasance da dan gidan Minista ba. Kila ba alherinta.
Hajiya Binta ta ce, haka ne. Allah zai amshi addu’arki, domin bakin mahaifiya yana da karfi a kan yara.
Hajiya Sauda ta kalli Usaina wadda ke dube-dube a kan kwamfutar Mimi, ta ce, kú sa wa yaran nan abinci ga shi nan. Hasana ta sa wa Hajiya Binta. Hajiya.Binta ta ce, ni duk damuwata ta a ba na jin yunwa.
Hajiya Sauda ta ce, damuwar me, bayan ga jikin mijinmu da sauki? Hajiya Binta ta ce,
Satan Mimi ai abin tunani ne.Ko kusa,
in ji Hajiya Sauda, guduwa ta yi, ba bata ta yiba.
Kin ga kwanukan da su Abba da Abdulkarim suka ci? Cewa suka yi tunda
Hmmm