AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 2 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 2 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

 

 

Kai Yaya ya more”. Ta ce, “Aunty Bahiyya, in kin tashi haihuwa ki haifar min irin ki komai da komai, ni kuma sai na haifa masa mata”. Azima tayi ta mana . dariya. Su hudu suka zo Kannensa ne Jamila da Azima, Laila da Mabaruka, gaba dayansu suka zauna muna hira.

Sai da suka yi wanka sannan suka ci abinci, hira muka yi tayi, tunda dama na san su ni Adnan ne ban sani ba, kasancewar shi ba a nan ya yi karatu ba, amma zumunci ne me girma a tsakaminmu da su, du kuwa da cewar mu yanzu babu abin. Jamila mate dina ce.

Na ji dadin zama dasu sosai, dan suna girmama ni.

Sai dai Adnan ba shi da kirki, abu kadan ya zagen ko ya yi min tsawa, Karshe ya ce min “Shi me zai yi dani, yana da dubuna suna jiransa”. Na kanyi mamakin me yasa bana birge shi? Me ya sa ba ya kaunata? Saboda auren biyan bashin da aka yi dani. Wai yaushe zan rayu kamar sauran mata, kwalliyata, daukar magana, girki mai kyau, duk na yi banyi nasara ba. Shi wanne irin mutum ne? Na tattarashi na watsar.

Satin su Jameela hudu suka shirya suka koma

Zaria. Tunda su Jamila suka zo Adnan ya sake, dani ya dawo aiki a nan zai zauna, daga Karshe sai na gano yarinyar da yake haukan so ita ce ta zo yi masa hutu, daga London ta zo. Na gane haka ne ta hirarsa a waya da yake yi.Ina daki ina bacci naji ana ta noking din dakin na fito, wata kyakkyawar halitta na gani a tsaye, ‘yar gayu ce sosai, duk da kasancewata me kyau naga kyan, itama ta razana dani, wato duk mun razana juna. Maganarta ma da gayu take, “Am, Adnan baya gida ne?” Na yi mata kallon up and down na ce, “Wace ke?” Wani irin kallon da na yi mata tayi min, “So in yana nan ki min magana da shi, in kuma baya nan kar kisa min ciwon kai”. Na ce,Sai ki Kara gaba baya nan

Waya ta dauko,Darling kana ina? Ina cikin

gidanka”. Ina kallo ta kashe wayar ta juya, nima na bi bayanta, muka yi isaye a falo. Ya shigo kamar an jehoshi, ya ce,

“Sweet heart!” Ya kamo hannunta ta

kwace tana kallona, kishina karara a fuskarta, tace, “Na gane abin da yasa baka so in zo gidanka, wanna ita ce zabin iyayenka wacce kake ikirarin auren biyan bashi aka yi muku, ban yarda ba”. Adnan ya jata ta Karfi suka fice.

Takaici ya kamani, me wannan ta fini? Me zata nuna min? Bani da ra’ayin zama da Adnan, dan bana son sa. Amma dole in nuna masa tsakanin namiji da mace akwai banbanci. Na juya a hankali, tunanin Sageer ya soma damuna, na dauki wayata in kira shi, zuciyata na hanani da yin hakan, na ringa kuka saboda ina takaicin duk kyauna, duk haduwata, duk da cewa a duniya irinmu ake yayi, amma abin da Adnan ya yi min kenan.

A ranar bai kwana a gidan ba, na san haka ta rashin ganinsa da ban yi ya karya ba, saboda na san kullum takwas zan same shi a falo mu gaisa. Ina zaune har karfe hudu, kwayar idona ta yi fari sol saboda kuka, na ringa jin ciwon kai na damuna. A daddafe na yi wanka, na saka rigar bacci na kwanta. A haka ya shigo ya same ni ina cikin bargo a nade, ya shigo ya janye bargon, yadda ya ganni ya sa shi sakin bargon ya soma kiran sunana, Bahiyya! Bahiyya!!” Na bude ido na ja bargo na rufe

fikina.”Ya ya dai?” Nace, “Kaina ke ciwo”. Ya kai hannu ya ji kan zafi zau. “Ki shirya na kaiki ki ga likita”. Na ce,

« N’а,Kyale ni bana bukata, na gode”

“A’a, Bahiyya ba a wasa da lafiya  Na ce, “Bana zuwa ka Kyaleni, ita ka san matar biyan hashi bata da daraja, kuma ka san auren biyan bashi ba cikakken aure bane, aure ne wanda aka yi shi cikin  da yadda za ka yi”. Gaba daya jikinsa ya yi sanyi ya kada ya raya tace bata zuwa. Fita ya yi ya je ya kawo mata magani, dan dai ba yadda za ta yi ne ta sha.

Kwanan ta biyu a kwance, Adnan na kula da ita.

Rana ta uku Amla tazo suna falo na zuba mata ido ina kallon tace darling ya za ka ajiye ni shiru?” Ko ya manta ina gurin, ne gaba  daya ta rikita shi da kissa, na ringa jin wani abu a raina, ya zan yarda in rayu da Adnan. Kuka na saki sosai, naji a duniya na dena faranta masa, ba zan rayu dashi ba, zan zauna da shi.

Sageer ne ya dace dani, Sageer nutumin da ko wanne uba zai so ya rayu dashi, na barshi kwance asibiti soyayya na wahalar da shi. Na yi biyayya da in faranta masu rai, to ni yanzu me nake a gidan nan?

Baiwa ce ni, tunda dani da wace aka siya duk daya. Na yi kuka kamar raina.zai fita

•Wayata na ji tana Kara na dauka, shikura ke sanar dani zatazo cikin satin nan. Nayi murna kwarai, wani abu da yake damuna, na kula Amla dawo cikin gidan da zama, na san Amla me kyau ce to me tafi ni hardaya zabi su ringa sabon Allah da ita mai makon ni da komai zamuyi lada ne Adnan da Amla suna cutata sosai, dan ina jin ciwon abin da suke yi har na kasa hakuri. Na shiga dakin Adnan, na yi nasara baya nan sai Amla tana barci cikin bargo, zuciya ta ciyoni na yi tsalle kanta ta tashi, tana ganina tsa Kara tana kiran Adnan, amma baya nan, kuma ba ta da Karfi. Na yi mata duka ko sau daya kasa ramawa ta yi, sai kuka tana bani hakuri, ni kuma takaici yasa na yita jibgarta.

Yana shigowa ya ga yadda na yi mata, hanci da baki duk a kunbure. “Bahiyya ba ki da hankali?” Na ce,

“An dake ta din, mene ne amfanin irinsu matan banza wadanda basu daraja kansu ba bare su daraja wani? Kai kuwa ka kiyayi kanka, hakkina ma kawai ya ishe ka.

Wallabi ba zan yarda ka ringa kawo irinsu gida ba, bari in fada maka, ban shirya zama da kai ba, a shire nake ka bani takadda in amshe ta’. Na yi waje ina masifa.

Ina falo zaune ya taitayeta zuwa asibiti, har ranar ban sake sata idamuna ba, na san ba ta Kara zuwa gidan.

Abin da na kula da shi, Adnan kunyata ma yake ji.

Saboda na samu fada a gidansu, iyayensa na sona, haka Kannensa, ina samun alheri da su kwarai. Ni kuma ganin haka ya sa ni nuna masa halin ko in kula da shi.Ke to ki kawo min ruwa in sha”.Nace, “Ban iya ba”. Yace. “Kar ki manta matsayinki a gidan nan baiwa ce ba wata ba, auren biyan bashi aka yi min dake, kefa ba ki da ‘yanci a gidan nan, ina fata kin gane?”

Hawaye ya zubo mata. Yace Gidan nan gidana ne, abin da nake so za’a yi, ina so inyi miki last warning. babu ruwanki da duk macen da zan kawo, saboda ko dai kingi min tsararo, dan ni ba halin mu daya da sauran maza ba. Amla nake so, da ita kadai zan iya rayuwa, duk wani fiflika da kike yi ina raga miki ne. saboda mahaifina, saboda ma ga yadda yake girmama mahaifinki, amma da tuni na yi maganin ki. Ba ki san Adnan ba bush girl’.

Haka kawai ina jin shakkar Adnan yana yi min wulakanci san ransa, na shirya ramawa saboda ba zan bari ba. Shukura ta iso gidana, farin ciki ya cikani, na cikata da kayan cima iri-iri. Muna zaune falo muna hira, na ce, Kwana nawa zaki yi min?” Ta ce, “Allah ya tsareni kwana gidan amare inga abin da zai daga min hankali”Kai! To in za ki kwana?”Ta ce, “Gidan Aunty Suwaiba”.Na ce, “To gidan man duk girmansa sai kinje wani guri” Ta ce, “Allah ba zan kwana ba”.

Kullum za tazo mu yini sai dare ta tafi. Rannan na cewa Adnan, zan bi Kawata gidan yayarta in gani. Ya ce,

“‘a”a. Nace, “Tunda nazo ban fita ba”. Ya ce, “Ba za ki ba”Shukura ta yi sallama ta shigo, na tare ta. Ya juyo suka gaisa, ya ce, “Shukura ashe, ma kece Kawar tata?* Ta ce, “Adnan kenan, rai kanga rai?” Ya ce, “Ga shi kuwa”. Ta ce, “Ashe kana Nigeria?’ Ya ce, “Kawarki tasa aka cicciboni ta Karfi, nike kula da kamfanonin Alhaji na nan”. Tace Ina Amla?’ Ya ce, “Ke zan tamhaya tunda kuwa kawarki ce”. Ta ce, “A’a, kaima ka sán ba halinmu daya ba”. Ya tashi yana fadin sai hali yazo dai-dai ake abota”. Ta ce. “Ban yarda ba”

Hira suka yi sosai, daga Karshe ya yi mana sallama ya fita. Na tsare Shukura da ido na ce, “Dama kin san Adnan?”Na san shi mana tun a London, abokin Amla ne”Ta ce, “Abokinta ko kuma saurayinta?”

Shukura ta sosa Keya ta ce, “A’a, nifa babu ruwana, duk ku biyu kawayena ne, ko wacce ina sonta”

“Amma dai Shukura ki taimake ni ki fada min gaskiyar wacce Amla, saboda zuciyata tana ciwo”. Tace min, “Kin san ‘yar hutu kuwa? Amla a buce take, irin

‘yan gayun nan ne. Amma bari in tsokano miki ita”. Ta dauki wayarta ta kira ta, ta kunna hansfree. “Yello, ya aka yi ne sai yau kika tunani?”Haushi kika bani”

“Na je Nigeria”.Yaushe?”Abuja na sauka, na je gidan Adnan ne”.Kai!”Ta ce, “Allah, gaskiya Adnan na so ya zabe ni ya bar matarsa. Kin kau ga kyan matar? Ba fa shi ya ce yana sonta ba, biyan bashi aka yi masa da ita”Ta ce, “Kai!” Ta ce, “Allah, kuma fa kar ki ce ba ta da kyau, ta hadu sosai. Ta ce, “Ke ai ban gaya miki ba, muguwa ce dukan tsiya ta yi min, kin sanni hutu-hutu”.

“Ki ce kin ci duka?”Sosai ma”.

“To Allah ya sauwake. To yanzu me ya yi mata?”

“Oho, ni dai na tabbatar masa zan aure shi a haka, yanzu so nake in gama shiri To a ina zaku zauna??’

“So nake ya hada mu, domin sai na nuna mata ni

‘ya ce ba biyan bashi aka yi dani ba”.

Suka yi sallama. Shukura tace, “Kin ji shirmen Amla ko?” Ta ce, “Ba shirme gaskiya ne duk abin data fada”. Hawaye ya zubo min, na durkushe gaban Shukura ina kuka. Ta ce, “Adnan bai kyauta ba, ya zai fada mata abin da ya shafe ki, dake da ita duk kalarku ake yayi, babu abin da za ta nuna miki, ke kin fita abubuwan da zai so ki, kin fita tarbiya, kin fita ilimin islama, kin fita asali me kyau. Uwa uba aurenki ya fi nata tsarki, mijinki bai sanki tun a waje ba, na yi imanin shi ya yi disbaging dinki. Takamar me zata yi miki, bashi kuwa hanji ne cikin kowa, ki godowa Allah da kina da baiwar kyau da za’ayi biyan bashi dake, Kila da mahaifinki na daure ko suna kotu Kuka take yi sosai,Ina son ki taimaka ki sa Daddyn ki ya sama min aiki”. Ta ce,

“A gaskiya na san Adnan sosai, wallahi ba zai barki ba, ki yi hakuri”

“Amma ki gwada”. Shukura ta yi dariya, tace,

“Bahiyya ba ki san Adnan ba, ko laifi ya yiwa Amla tana hukunta shi ne ta hanyar kula sauran samarinta, dan ba zai jura ba, bai son kowa ya rabi abin da yake so. Ki tambaye shi, in ya amince za’a samar miki”. Washe gari muka yi sallama da Shukura, na yi mata alheri sosai.

Ina goge falo ya shigo ya tsaya, ya ce, “Yau Shukura batazo ba?” Nace, “Ta tafi tun jiya”. Ya kalle mi, “Saboda me ta tafi ba tayi min sallama ba?”

“Ai ba gurinka tazi ba”Na fi ki sanin Shukura”

Hmmm