MUSABBABI CHAPTER 13 BY HAJ HABIBA

A hankali garar da Malam Mahmud ya yima Afrah suka Kare, ya zamana abincin da Afrah za ta ci ya fara yi mata wahala, tunda Musaddik baida inda zai sami abinda zai ciyar da ita, idan ma ya samun, su

kan Kare ne a wajen shaye-shayensa.

Ta bangaren Hajiya Kilishi kuma ko faranti daya na abinci ba ta iya ba ta balle har ta sa ran za ta taimaketa da wanda za ta dafa.

Ba ta iya taimaka mata da komai, sai wulakanci da cin zarafi, shi ya sa gaba daya ma ta daina shiga cikin gidan Hajiya Kilishi. Amma duk da haka, duk ‘yan aikin da Hajiya Kilishi take da su, haka nan za ta aiko Afrah ta je ta sa ta aiki kuma ko a gabanta aka gama abinci, ba ta yarda a zuba mata ta ci. Haka za ta gama aikin, ta koma bangarenta da yunwa.

Wani lokacin ne ma idan ta je Islamiyya. Ya Sayyadi kan ba ta kudi, su ma da kyar take amsa, don kudin daya ba ta gudunmawa da ta yi niyyar ta. yi sana’a da su ne.

Amma tuni suka kare, saboda zararsu da take tana yin hidimar gidan. Da kuma Musaddik ya fahimci akwai dan wani abu a hannunta, gaba daya ya amshe sauran ya je ya yi sha’ aninsa.

Lamarin Musaddik kam! A yanzu gaba daya ya koma ba Afrah tsoro, domin duk inda take tsammanin lamarin, ya wuce nan, ta kuma cire ran samun farin-ciki daga Musaddik, domin dai har yanzu ba ta san tayi aure ba. Ga jarabawarta tuni ta fito, duk kuma ta cinge ba ta fadi ko daya ba, sai dai ta san mafarkinta na ci-gaba da karatu ba zai tabbata ba.

Abu biyu ta maida hankalinta akai yanzu, shi ne yi ma Musaddik nasiha da kuma yi masa addu’a, domin kullum sai ta yi tsayuwar dare, musamman dominsa, kullum addu’arta ba ta wuce Allah ya shire shi ba, sai dai abu daya ke daure mata kai.

Shine a duk lokacin da take masa nasiha, ya kan nuna mata shi ma fa ba haka ya so ba.

Duk abinda yake yi, ba’a son ransa yake ba.

To amma don me ya kasa yaki da zuciyarsa ya daina ya natsu? Wannan ita ce tambayar da kullum take neman amsarta.

Ta bangaren Malam Mahmud kuwa kullum ya samu haduwa da Afrah yana Kara karfafa mata guiwa tare da yi mata addu a. Hakan shi kadai ke sanyaya ran Afrah tare da Karfafa mata guiwar ci-gaba da zama da Musaddik cikin aminci. Zabe ya gabato, hakan ya sa gaba daya Musaddik ko kwanan gida bai cika yi ba, sai ya kwana daya kwana biyu baya gida. Ran Afrah da hankalinta yana matukar tashi akan wanna bangar siyasar, domin ta san hatsarin da ke ciki.

Ta yi nasihar har ta gaji, amma Musaddik ya riga ya rufe kunnensa, sai dai a duk sanda ya kwana baya gida, idan ya dawo, ya kan dawo da kudi.

Domin har dubu biyar yana ba ta, ta rike ta ci abinci, a wanna tsakanin abinci baya yi mata wahala, duk abinda take so, shi take ci, da yake tana da hankali, ta kuma san samun na dan lokaci ne, ba me dorewa ba, shi ya sa idan ya ba ta, ta kan kasa uku ta aje kashi biyu, ta ci abinci da kashi daya, da dan sauran hidimominta na yau da kullum, amma duk da haka Afrah babu farin-ciki a rayuwarta.

Alhaji Hamza Sarkin yakin kamfen din Hajiya Hudah ne, wacce take neman takarar zama ‘yar Majalisar Wakilai, watau (House of Rep Abuja).

Yana zaune a katon falonta a gidanta na ganawa da baki. Gefe daya Musaddik ne a zaune yana Kare ma falon kallo, cikin kaguwa ya dubi alhaji Hamza ya ce “Alhajin Allah, ni fa duk a rayuwata ba abinda na tsana irin jira, ina mutunta lokaci, shi ya sa ba na Kara lokaci akan wanda aka ba ni”

Alhaji Hamza ya yi dan murmushi ya ce

“Mazaje, ayi hakuri, na san hakan, it ma na tabbata akwai abinda ya tsayar da ita, amma na san tana hanya, bari na Kara kiranta”

Ya tura hannu a’aljihunsa ya ciro waya, ya danna kenan, ya jiyo hon din motan Hajiya Hudah, ya yi murmushi gami da kallon Musaddik, a yayin da yake maida wayar cikin aljihunsa ya ce.

*Ga ‘yar hala din nan ta iso”. Musaddik ya

•gyada kansa yace Ya dai kamata”. Yana rufe bakinsa. Hajiya Hudah ta danno kanta cikin: falon, kyakyawar bafullatar mace ce, fara ce, amma ba irin farin nan me daukar ido ba, tana da matukar kyawun fuska hade da kyawun diri.

* Tana sanye da kaya na alfarma, kallo daya za ka yi mata, ka san goggaggiyar mace ce, wacce ta mallaki masu gidan rana. “Alhaji Hamza kuyi hakufi, na zaunar da kü ko? Kun san abubuwan da yawa ne, babu zama”

Ta fada tana zaunawa. Alhaji Hamza ya Kara yin dabi’arta sa ta murmushi ya ce “Da girman kujerarki, barka da isowa”.

Ta amsa “Yauwa Alhaji”., Ta fada tana kallon Musaddik, wanda yake zaune baida ko alamar gaisheta. Musaddik ya yi matukar yi mata kwarjini, haka nan kuma ta ji ya burgeta, ta dawo da kallonta ga Alhaji Hamza ta ce.Shi ne wannan wanda yakeyi mana. Kökarin nan?’Alhaji Hamza ya dube shi ya ce “Eh, shi ne Musaddik kenan, ku gaisa mana mazaje”.

• Ya dan dauke kansa ya ce “Ki na lafiya Hajiyar Allah?” Ta yi murmushi ta ce “Lafiya Kalau, ya hakuri?” Bai amsa ba, illa kallonta da. ya ci-gaba da yi.

Alhaji Hamza ya fara magana. “Hajiya. Kamar yadda ki ka sani da wanda ba ki sani ba, amma na gaya miki Musaddik shi ne wanda yake mana kokari a wajen matasa, to kamar yadda na fara gaya miki a waya, kika kuma bukaci na taho da shi. ku ga juna.

*Yan-uwan aikin nasa suna da bukatar kudin kayan aiki, tunda zaben nan jibi ne, don haka suna bukatar kayan maye da makamai, wadanda za su sha a yayin tashin hankulan mutane a lokacin zabe, sai kuma kudade wadanda za su. sa aljihunsu,

domin jin karfin gudanar da aikin.

Don haka a matsayinsa na ogansu wanda kuma da shi na ke mu’ amala, kuma duk jama’ar nan shine ya nemosu, shi ya sa suka wakilta shi akan komai.

Hajiya Hudah ta gyara zamanta, gami da Kara kallon Musaddik, wanda duk kallon da za ta yi masa, ta kan sami zuciyarta da bugawa, yana kuma matukar Kara yi mata Kwarjini. Ta ce Musaddik ba dai matsala a can

bangaren naku ko?”Ya Kara dubanta yace

“Matsalar kenan ta kudi da kayan maye, in dai da su, to za ku ga biyan bukata, ta bangaran mu, kuma jama’ar tawa korafi suke yi min suna ganin kamar ana ba ni wasu makudan kudi ne, ina cinyewa to a yadda na fahimce su, suna iya yi min bore a ranar zaben, don haka sai ku san yadda za kuyi da mu.

Alhaji Hamza ya ce, “Ba ku da sauran matsala, ga ka ga Hajiya Hudah nan, gani kuma a tsakiya, duk abinda ku ka nema, za ku samu”.

Hajiya Hudah ta muskuta tana dan murmushi tace

“Babu damuwa”

Ta dauko jakarta ta bude, ta dauko Naira dubu dari uku ta mika ma Musaddik ta ce “Wannan ka je ka raba masu, su sa a aljihunsu”. Alhaji Hamza ya wage baki, yana mamaki.matsolancin Hajiya Hudah da tsoron fitar da kudinta, ta ba Musaddik dubu dari uku ba tare da ta ga jama’arsa ba. Wanda ba ta yin hakan ga wani, sai ta ga zahiri. In dai kudi za ta bayar, lalle

Musaddik yau ya taki sa’a.

Musaddik ya sa hannu ya karbi kudin, ya juya su ba tare da ya ce uffan ba, ta kuma mika masa dubu dari ta ce “Wannan naka ne kai kadai”. Alhaii Hamza ya zaro ido cike da mamaki

A yayin da Musaddik ya karba, lokaci daya yana godiya, ta ce “Wannan dubu dari ukun, kamar yadda na gaya maka, ka rarraba masu, na san a ciki za su sami wanda za su sayi kayan shaye-shayensu, ni dai burina a ranar duk akwatin da ku ka ga, ba zan kai labari ba, ku far masa, ko ku dauke shi koku Talata shi. Idan kuma duk babu dama, to ku tada fitina a wajen. Taimakon da na ke nema kenan a gareku”.

Musaddik ya ce “Kada ki damu, duk abinda ki ka lissafa za mu yi, sai dai wani hanzari ba gudu ba.” Tace “Ina jin ka?. Ya ce “An dade ana amfani da mu a wanna harka, amma daga baya mu kan tura mota ne ta tashi, ta bulbulemu da hayaki.

•Ma’ana, da zarar kun sami biyan bukatarku, sai ku manta da mu, ku kyamace mu, a lokacin ne za ku san mu ba mutanen kirki bane, sai ku kulle alaka da mu.

Wannan babban kuskure ne ku ke yi, domin muna yi maku abinda ko ‘ya’ yanku ba su iya maku, don haka bai kamata ku dinga mantawa da mu ba, bayan kun kafa gwannati ku dare madafun iko”

Hajiya Hudah ta dubi Alhaji Hamza da har yanzu yake yi mata kallon mamaki, sannan ta yi murmushi ta ce, “Ka kwantar da hankalinka, za ka ga bambanci a wannan karon, domin in dai na haye, to da kai za’a tafi gwamnatin, kada ka kara sa wannan matsalar a matsayin damuwarka, domin zan yi maganinta, da zarar na haye”.Tun zamansa, sai yanzu ya yi murmushi ya ce. “To godiya na ke ranki ya dade”

Daga nan ya mike, yana kallon Alhaji Hamza ya ce. “Alhajin Allah taso ka aje ni inda ka dauko ni

. Yana magana yana dauko leda a aljihunsa, ya zuba kudin, ya daure. A lhaji Hamza ya ce «Yanzu fa.”

Ya mike yana kallon Hajiya Hudah ya ce.

“Gari fa ya yi zafi, ga abubuwa sun mika, jibi za’a fita fagen fama, ko zan sami na fetur?” Ta yi masa wani irin kallo, amma Alhaji Hamza bai san tunanin da ta yi ba, bayan ta dübi Musaddik, sai ta janyo jakarta ta Kirga dubu talatin, ta mika masa.

Ba yabo, ba fallasa ya karba, yanzun nan ta bada dubu dari hudu. Amma shi da kullum yake wahala akan lamarinta. Ta Kirgo dubu talatin ta ba shi, ba tare da godiya ba ya ce “Mun barki lafiya”

Tare suka jera da Musaddik suka fice, yayin da Hajiya Hudah ta bi su da kallo har suka bace ma ganinta. A zahiri ta ji dadin haduwa da Musaddik, domin ya yi mata matukar kwarjini kuma bai yi kama da irin iskancin da Alhaji Hamza yake kira masa ba.

•Alhaji Hamza kuwa suna fara tafiya, ya dubi

Musaddik ya ce “Gaskiya ban san irin sa’arka ba Mazaje”. Ya dan dube shi ya ce “Na me fa?” Ya ce

“Na yadda Hajiya Hudah ta ba ka wadannan makudan kudin ba tare da ta ga jama’ar da za ka raba ma ba, ta yarda da kai cikin kankanin lokaci.

Sabanin ni da na yi shekara da shekaru tare da ita, amma idan maganar kudi tazo to fa sai ta ga komai da idonta, duk da tana haukar son wannan kujerar, za ta iya yin komai, domin hawa kujerar. To fa duk da haka, ba ta kwasar kudi irin haka tana bayarwa. Sai ta ji, ta kuma gani. Shi ya sa yadda ta ba ka wanna kudin abin ya yi matukar ba ni mamaki. Don mace ce me son abin duniya.”

Musaddik ya yi murmushi ya ce “To ai komai ya zo gat! Kila ta yi tunanin idan ba ta bada kudin ba, za su yi boren ne, kamar yadda na gaya mata”.

Alhaji Hamza ya nunfasa ya ce.

“Allah shi ya san dalilinta na yin hakan, sai kuma ita kanta, kana ji?”

Ya juyo ya kalle shi ya ce. “Ina jin ka.” Ya ce

“Dan yago min wani abu, don wannan dan kudin da ta ba ni, ba abinda za su yi min.’

» Musaddik ya bude ledar, ya dauko dubu dari da ta ba shi, ya mika masa. A gaggauce Alhaji Hamza ya ce “Dubu dari ne fa mazaje?”

Ya gyada kai ya ce. “Ina sane, wadannan sun isa mu raba ko dubu biyar-biyar ne, ba damuwa, na san kai ba za ka kashesu ta hanyar da za mu kashe ba, za ka yi amfani da su a inda ya dace ne, tunda kai ka ji dadi ka mori rayuwarka, babu shashanci a ciki. Idan na tafi da dubu darin nan, ni a banza zan kashesu akan abinda ba zai taba amfanar rayuwata ba”

iyalinka fa??Cike da tausayinsa. Alhaji Hamza ya ce “To• Ya girgiza kai “Ko na kai mata, ni ne

zan koma na karbesu na kashesu a banza, a duk sanda kuma na je amsa, ranta sai ya baci, domin ta san abinda zan yi. da su, amma ba za ta tada nuna

• min bacin ranta ba, za ta dauka ta ba ni, to gara ma kada na kai mata.”

Alhaji Hamza a sanyaye ya karbi kudin, hakika halin Musaddik, ba irin halin da yake aikatawa bane, kwarai yana da kyan zuciya, tausayi da kuma imaninsa, wannan halin da yake ciki, ba nasa bane, bai kuma dace da shi ba, ga kwarjini da dadin mu’ amala. Karo na farko kenan da Alhaji Hamza ya fara yi masa addu’ ar shiriya. Ya kirga dubu ashirin ya mika masa ya ce.

“Ga shi ka kai ma matarka, na tabbatar kafin ka waiwayesu, sun Kare, tunda babu yawa, don Allah ka kai mata.” Ba tare da musu ba, ya karba, ya tura a’ajihunsa har suka kai inda ya aje shi.

Alhaji Hamza fatan shiriya yake masa, tare da yi masa addu’a, ya kuma sa a ransa ba zai taba mantawa da abinda Musaddik ya yi masa ba a rayuwa, tare kuma da alkawarin sa shi a cikin addu’arsa, a duk sallolinsa na farilla.A daran ranar da wuri ya koma gida, hakan ya: faranta, ran Afrah, ta kawo masa abinci ya ci, ya koshi. Tabbas yana jin dadin abincin matarsa, ba tun yau ba, domin ta iya girki.

Ta kai, ta dawo yana kallonta, haka nan yake jin kunyarta, a duk lokacin da take hidima da shi.

Lokaci daya kuma tausayinta yana kama shi. “Zo ki zauna”. Cewar Musaddik. Afrah ta koma a. hankali ta zauna, tana kallonsa ya ce

“Zauna haka nan ki huta ma kanki, na gode kwarai da gaske.” Ta dan yi murmushi ta ce “Haba Yaya Musaddik, wai sai ka dinga yi min godiya akan abinda ya kamata na yi maka?”Ya ce “Na sani, duk da haka dai na gode”. Ya ciro dubu ashirin a aljihunsa, ya mika mata, ta karba cike da mamaki tana kallonsa. “Na meye wannan kudin? Ya ce “Na ki ne, wani abokin harkar siyasata ne ya ba ni, ya ce in kawo miki”.

Ta yi dan murmushi ta ce “To sai ka dauka duka ka ba ni, ka diba mana.” Ya girgiza kai ya ce.

“A’a na ki ne, ba zan dauki ko sisi ba”

Za ta yi magana kenan, ya mike. “Ni zan fita”.

Nan da nan Afrah ta gintse fara’ar fuskarta ta ce

“Ina kuma za ka tafi?” Ya ce “Wace irin tambaya ce wannan Afrah? Yanzu sai na gaya miki inda zan je, idan zan fita?

Ta girgiza kai ta ce. “A’a ba sai na sani ba, tunda matsayina bai kai na in sani ba, sai dai ba zan gaji da rokonka ba, don Allah Yaya, don girmansa da kuma darajarsa, ka yi ma kanka fada, ka natsu,. ka san rayuwar da ka ke yi, ba ta dace da kai ba. Ka yi ma kanka fada, tun kafin ka fara haihuwa, a fara gorantar ma ‘ya’yanka”.

Juyowa kawai ya yi ya kalleta, ba tare da yace komai ba, ya fice, a hankali ta koma ta zauna akan kujera, hawaye na malala mata, ko Musaddiq ya fara ba ta farin-ciki, sai ya kan koma bakin-ciki, kwata-kwata baya kaunar su zauna suna hira, saboda ya tsani yawan nasihohin da take masa a matsayinsa na magidanci. Lokacin da kowane Magidanci yake dawowa gidansa. Shi a lokacin yake fita. A hankali ta daga hannunta sama tana addu’ ar neman shiriya ga mijinta. A ranar sai tsakar dare Musaddik ya dawo gidan, tana sallar nafila ya dawo cikin maye, don haka ko ta kanta bai bi ba, ya wuce ya yi kwanciyarsa da takalmi a kafarsa.Sai da ta idar da addu’o’ inta ta zo kwanciya, sannan ta cire masa takalman. Amma irin warin da Musaddik yake yi, ya hanata kwanciya kusa da shi, sai falo ta dawo ta kwanta akan kujera, tana zubar da hawaye

Kullum. Musaddik bata mata rai yake yi da dabi’o’insa, amma har yanzu zuciyarta ta kasa tsanarsa, maimakon haka ma tausayinsa ta fara haifar mata da kaunarsa, domin tabbas ba don wannan halin ba. Musaddik mutum ne.Tun safiyar ranar da za’ayi gudanar da zaben.Afrah ta sami kanta da matukar faduwar gaba da kuma damuwa, domin gaba daya ba ta gamsu da yanayin da mijinta ya fita ba, dón haka bakinta ya kasance cikin addu’a. Ta bangaren Musaddiq kuwa, yana can tare da mukarrabansa suna bin mazaba- suna aikata abinda aka umarcesu da aikatawa, inda suka ga Hajiya hudah za ta ci. Su kan daga ma wajan Kafa, inda ko ba za ta ci.ba, da sun ga alamar haka. To su kan tada fitina a wajen. Ta hanyar dukan mutane da kuma kone-kone, a yayin da duk bayan mintina.

Alhaji Hamza da Hajiya Hudah suna buga masa waya, domin jin halin da ake ciki. Abu ya kai matuka, fitina ta yi Kamari, domin har an fara rasa rayuka. Jama’a sai gudu suke yi.

Domin tsira da rayuwarsu. Nan da nan kafin ka ce meye wannan? *Yan sanda sun cika wajen.

Haka nan suka shiga kama jama’ar wajen a kokarinsu na kawo karshen fitinar.

Cikini wadanda aka kama kuwa har da

Musaddik da kuma tsirarun abokan aikinsa.

Wanna kamun ko a kwalar rigar Musaddik, domin dai ya san yana da wadanda za su fito da shi, don ya san Alhaji Hamza ba zai taba barinsa a hannun

‘Yan sanda ba, don an yi hakan ya fi a kirga.

Tunda Afrah ta fahimci fada ake yi, domin yadda garin ya yi shiru, sai warin tayoyin da ake konawa; ka na daga cikin gida ka na hango inda wuta ke tashi, tana rimi, tuni hankalin Afrah ya yi mummunan tashi, fatanta daya. Allah ya sa fitinar ba ta rutsa da Musaddik ba. Ta kasa zaune, ta kasa tsaye. A yayin da ta kira wayarsa ya fi sau talatin, amma wayar na kashe, tun daga lokacin hankalinta ya Kara tashi, har dare ba Musaddik, ba alamarsa kuma a lokacin gaba daya abubuwa duk sun lafa, komai ya dawo dai-dai. Tana ganin zuwa lokacin ya kamata ace Musaddik ya dawo gida.Amma har gari ya waye, bai dawo gida ba.

Zuwa. yamma damuwar Afrah ta Kara fadada, a daddafe gari ya Kara wayewa, kwana biyu kenan ba duriyar mijinta, hakurinta da dauriyarta sun kare, don haka ta fito daga bangarenta zuwa cikin gidan, kai tsaye falon Hajiya Kilishi ta nufa.

Ta tadda ita tare da Hajiya Rakiya suna zaune suna hirar hatsaniyar da ta faru shekaranjiya. Yadda Afrah ta fado falon a gigice, ya sa Hajiya Kilishi ta dubeta a firgice ta ce,Ke lafiya za ki fado ma mutane falo haka? Menene?”Afrah ta ce “Ki yi hakuri Hajiya. Ina cikin matsala ne, na san kuma za ki iya taimakawa”

.Ta dubi Hajiya Rakiya da take yatsina fuska ta ce. “Me ya faru? Afrah ta dan gyara tsayuwarta, sannan tace.

“Hajiya, tun shekaranjiya da Yaya Musaddik ya fita wajen zabe bai dawo gida ba, shine na ke cikin fargabar ko hargitsin daya faru ya rutsa da shi ne.

To shi ne ki ka zo guna na yi maki me?” Cewar Hajiya

Kilishi.Afrah ta ce cikin marairaicewar murya, “Shine na zo ki tamaka min, tunda hannu daya baya iya daukar jinka, ki tayani binciko inda yake.

“Tunda ni gidan Rediyo ce ko? Ina ruwana da rashin dawowarsa gida, kuma ke akan lamarin Musaddik, ai kin wuce hannu daya, hannu dubu-dubu ce, ba kin ce kin ji, kin gani ba.

Kuma banda ma iya yi da neman magana, yau

Musaddike ya fara fita ya je ya kwana bai dawo gida

• ba? Dan iska har wani damuwa za ayi da halin da yake ci, bayan yana can wajen iskancinsa”

Hajiya Rakiya tayi tsaki ta ce “Ni ba karamin firgita ni ta yi ba, meye wani Musaddik da za ki tashi hankalinki, don kawai bai dawo gida ba, sai ka ce yau ya saba. Don Allah ki sassautawa kanki wannan wahalar”

Hajiya Kilishi ta ce “To a ni ban ma gane

• hausar wai na taya ki binciko inda yake ba, to ni ina da abin yi, ba zaman banza na ke yi ba, balle ki ce kin ga ina zaman banza ne, ki ka ba ni aikin yi.

Musaddik Allah ya dawo miki da shi lafiya, amma ni babu abinda zan iya yi miki.”

Afrah da tashi tsaye, zafin maganganun su

Hajiya Kilishi ya tilasta ma idanunta fitar da

• hawaye. Hajiya Kilishi ta juya gun Hajiya Rakiya

• suka ci-gaba da maganganunsu, suka bar ta nan tsaye.

Hmmm