CANJIN RAYUWA CHAPTER 16 BY HALIMA A K/MASHI

CANJIN RAYUWA CHAPTER 16 BY HALIMA A K/MASHI

irin shi ne masu yin magani ba.” Ta ce, bari ka ji abin da ya ce min. Nan ta fada masa yadda suka yi. Ya ce, “ok, ki kira shi yanzu.
Sai dai ina son ki sani ba mu da isasshen lokaci, saboda kullum kwanakin aurenki
Kara kusantowa suke yi.” Ta ce, “to bari in kira shi. Zan fada maka duk yadda muka yi.’
Ba tare da wani dogon nazari ba,
Mimi ta soma kiran layin Isma’il. Ya gama shafa’i da wuturi ke nan, yana kwance kan dardumar duk hankalinsa ya koma.
Katsina, gani yake yi kamar akwai abin da Mahmood yake boye masa. Yana ganin cikin satin nan zai koma gida. Karshen wata ya yi masa nisa, duk da saura kwanaki takwas watan ya kare.
Ringin din wayar shi ne ya katse masa tunani. Cikin sauri ya duba, bai san lambar ba, amma yadda ya ga lambobin ya san cewà na musamman ne. Ya daga tare da sallama, ‘yar siririyar murya ce ta amsa da
“Hello!” Ya sake yin sallama, ta ce, “nice Mimi.” Ya ce, “ba ki amsa sallamata ba, wanda ya kasance amsa sallama wajibi ne a cikin addini.” Cikin kosawa ta amsa, sannan ta ce, “ka san dalilin kiran ka?” Ya ce, “a’a.” Ta ce, “kace, “za ka ba ni maganin bakin ciki da yaye damuwa. Sannan ka ce zan iya cimma burina.” Isma’il ya yi dan murmushi tamkar yana gabanta, sannan ya ce, “Kwarai kuwa.
” Ta ce, “to don Allah ka
taimaka min. Ina cikin damuwa, Mahaifina ne.” Ya ce, “dakata! Ba sai na ji damuwarki ba, ko abin da kike ciki ba, sannan zan taimaka miki.” Ta ce, “na sani Malam. Ina so ne kawai in fada maka, kila za ka tausaya min don ka taimaka min cikin gaggawa.” Ya ce, “Allah ne mai taimako. Tunda kin zabi ki fada min, ina sauraron ki.”Ta ce, “Daddy na ne zai min auren dole. Ina kuma da wanda nake so. Wallahi Malam ni da shi muna cikin wani hali. Shi ne muke son mafita.” Isma’il ya ce, “mafita dai ita ce komawa ga Allah. Za ki iya tashi cikin dare?” Ta ce, “zan iya komai Malam don in cimma burina.” Ya ce, “ki tashi karfe ukun dare ki yi alwala, ki yi salla raka’a biyu ko sama da haka, ki fada wa Allah damuwarki. Insha Allahu Allah zai yaye miki halin da kike ciki. Sannan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur’ani mai girma. Ba wai sai can cikin Alkur’ani ba, ko kananan surori ne ki yi ta karantà su, za ki samu waraka.”
Mimi dai shiru ta yi, yana magana. Ita Kuwa tana tunaninta daban. To, shi wannan Malamin da yake cewa ta yi salla, ba ya ganin cewa da ba ta damu da yin sallar ba, yanzun da matsala ta same ta, sai kuma ta waiwayi sallar? Tamkar ya shiga zuciyarta, ya ce,

SAIFUDDEEN COMPLETE By Billy giro

«kar ki dubi yawan zunubinki, matsawar kika tuba, Allah zai tafe miki kurakurankin. Sannan yana da kyau kiyi addu’ar istihara, wato neman zabin Allah kafin ki kizabin Mahaifinki.Ta ce, *to Malam ai ni ban iya ba. Duk abin da ka ce min inyi din nan ban san ta inda zan fara ba.
” Ya ce, “in kin amince sai
in fada miki yadda za ki yi.” Ta ce, “to, amma ka bari zan kira ka.
Khalil ta kira ta fada masa komai yadda suka yi da Ismail. Ya ce, “Mimi mi yi mai yiwuwa, nasan yana bukatar dogon lokaci.” Ta ce, «ya za mu yi?” Ya.ce,’
“nawa tunanin mu gudu kawai.” Ta dan yi shiru, cikin sanyin murya, ta ce, “zuwa ina-
Khalil?” Ya ce, , “ko ina ma, mu boye na wani dan lokaci. In sun rasa mu za suyi ta neman mu. Sai mu fito daga maboyarmu.
To, za su yi mana aure, gudun kar su rasa mu.” Zancen ya shiga Mimi. Ba tare da wani tunani ba, ta ce, ya shirya musu yadda za su gudu din.
Kamar yadda Abbas yace, minti biyar ce ta karu kan lokacin da ya ce, za su zo. Suka iso. Na’ima ta shiga, Mimi tana nade a gado. “Sis ga Abbas ya iso fa. Dad ya ce ki fito, wai ni ma in shirya muje.” Tsaki ta ja, sannan ta tashi ta shiga wanka. Sun yi
Jira tsawon sa’a daya da rabi, sannan ta sauko sanye da jallabiya, wadda ta kama mata jiki, ba komai ratsin blue, sai dan kwalin rigar da ta rataya a wuyanta. Bai boye gashinta ba. Duk da ba ta shafa mai ba, bare hoda ko turare, amma hakan bai hana ta Kamshi ba. Ta isa gurin Dad, wanda ke zaune yana jiran fitowarta, ta gai da shi.
Cikin fara’a ya amsa tare da cewa ki saki ranki, duk kin tsai da mu. So nike ku fita, sannan ni ma in fita. Ta kalli Na’ima,dauko min wayata na manta.
Na’ima ta koma sama ta dauko.
Sannan taje ta canza kaya, ta sha kwalliya, wai ko za ta ja ra’ayin Abbas. Mimi ta kalle ta, “Na’ima Sarkin kwalliya. Kin fada wa Momy za mu fita?” Dad ya ce, “na fada mata. Tace ku tafi!?
.Sai lokacin Mimi ta kalli gurin da su
Abbas suke. Su uku ne. Ta sake kau da kanta, sannan ta mike, su kuma suka yi wa Dad sallama.
Cikin katuwar CRV din da suke tafiya, Mimi da Abbas sune a tsakiya, Munnir ke jan motar shi da Hafiz a gaba.Can baya kuma Usman ne shi da Na’ima.
Abbas ya ce, “abokaina ba su yi miki laifi ba, amma kin kasa gai da su.” Ta yi banza da shi. Ya ce, “ko ba ki ji ba mai sona?” Ta dago fararen idanunta ta kalle shi, “kar ka matsa cewa ‘sai na yi magana, domin kalamaina yau dük ba masu dadi ba ne na tánada.”
Bai sake magana ba, sai ya waiwaya, ya kalli Na’ima, “Sis ina ne unguwar su Amina Kawarta, ko ita ma a nan Maitama suke?” Tace, “‘a suna Asokoro ne ko Sis?” Mimi dai ba ta tanka su ba.* Ya dauki wayarta ya nemo lambar Amina ya kira ta Ya ce ta shirya ga su nan, shi da su Mimi za su fita. Ita ce ma ta taimaka masa da kwatancon gidansu, sukaje.
Amina dai ba ta ga laifin Abbas ba, kuma ta ba Mimi shawarar cewa ta hàkura ta aure shi. Ta ce, “daga gani shi ma dan rayuwa ne. Kin ce Khalil ya iya soyayya, shi ya sa kike son shi, to ki ba Abbas dama ki ga irin tasa.” Mimi ta ce, “ke yanzu za ki So a raba ki da Faisal?” Ta ce, “a’a. Amma in ta kama zan iya sadaukarwa. Ina nufin Dad dinki ya cancanci sadaukar da soyayyarki don ki faranta masa rai.”
Mimi ta ce;nayi yunkurin haka,
amma na kasa. Don haka yanzu mun tsai da shawara ta karshe, ni da Khalil. Kuma ita ce mafta.”
Mina ta ce, “me kuka yanke?”
Mimi ta ce, “kar ki damu, ba sai kin ji ba.” Suna yin zantukan nan ne a inda suka kee kansu lokacin da Abbas da abokansa suka je gurin Manajan Hall din da su Mina suka ce ya yi musu.
Duk komai Mina da Na’ima suka, zaba, Mimi ko kallon su ba ta yi. Sai kusan daya saura suka nufi gidan da za su zauna.
Ba su da nisa da gidan iyayen Mina. Sai murna take yi, wai za ta dinga zuwa a kai, a kai, sannan ga shi gidan ya burge ta. Ko Mimi ta yaba gidan a zuciyarta, amma ba ta nuna ba.
Abbas ya zo kusa da ita, “Dear ya kika ga gidan naki? Saman nan naki ne ke daya, falulluka uku, duk naki ne: Da na lura kina son zama a sama, shi ya sa kike abar so kamar tsuntsaye.” Mimi ta kau da kai, “*ina

CIN AMANAR KAUNA CHAPTER 2 BY ZUWAIRA ISA

A SANADIN MAKWABTAKA BY OUMMU IMAM*

DABI’AR ZUCIYA BY HUGUMA

Auren Katin Kasa By QueenMarh

Ta ce, “a’a ba na cin abincin ko’ina, sannan ba komai nake ci ba.? Ya ce, “shi ke nan bari mu fara kai Mina ko?” Ba ta tanka ba, ta nüfi fita.
Sun fara sauke Mina wadda take ta yaba wa Abbas, har Mimi ta soma jin haushinta, sannan ya sauke abokansa gidan cin abinci, ya ce bari ya kai ta gida ya dawo, zai same su a nan. Duk zantukan da yake mata tun sadda suka taho ba ta tanka shi ba, har suka zo gidan, yana yi mata magana, ba ta tanka shi ba. Ta sauka ta nufi ciki.
Ko da ya koma, abokansa Korafi suka yi masa a kanta. Munir ya ce, “don tana da kyau sai ta hada da iskanci? Don wannan ya wuce jan aji, tana kallon mu sai ka ce ta ga kashi.” Ya ce, “ku yi hakuri abokaina. Tana cikin fushi ne, amma lokaci kadan za ku ce ta fi kowa kirki a nan gaba.
Dariya suka yi masa, don sun gane ya yi nisa a soyayya.
Ismail yana murna zai soma cusa tauhidi a zuciyar Mimi, sannan ya tanaji abubuwan da zai fada mata don kara cusa mata. Allah a cikin lamurranta. Ya yi ta jiran kiranta, amma shiru. Bayan la’asar sun fita shi da direban yara, Hamisu ke nan, don in an aike-shi ko zai kai yara wani gurin, Isma’il kan bi shi don ganin gari. Ya kosa su dawo don ya kira ta. Haka kuwa aka yi.
Suna dawowa ya shiga daki, sai da ya zauna tsakiyar katifa sannan ya nemi layinta ya kira. Gab da za ta tsinke, sannan ta daga. Ya yi sallama. A kagare ta amsa. Ya ce, “Ya ranki ya dade naji shiru ne?” Ta ce,
“Malam ka bar shi kawai. Mun canza dabara. Khalil ya ce naka zai ci lokaci »Isma’il cikin sauri ya ce, “amma nawa shi ne mai tabbas, In kin yi sabanin abin da na fada miki, Karshe ki yi nadama. Sannan ba Talle ba ne addu’arki ta dauki lokaci, domin Allah Mai jin kan bayinsa ne. Ba ki da wata dabara sabaninyi masa biyayya.
* Ta yi jiM, sannan ta ce, “don Allah ka bar shi kawai Malam.” Sai ta yi tsaki, ta kuma kashe wayarta.
Ta ko’ina abubuwa sun dauki zafi, domin ko can Katsina tuni an daura auren Zainab da Alhaji Lawal. An kuma kai ta gidan. Matansa uku ga yara nan kwatsam. Gidan bene ne hawa daya. dakinsa ne a saman, sai matarsa ta ukun, sai kuma’ dakin Zainabu. A kasa matansa biyu ne da
‘ya’yansu da kuma ‘ya’yan wasu matan da suka fita.
Tunda aka kai Zainabu take cikin kuka. Bayan kowa ya kama gabansa, ta tashi ta datse dakin. Alhaji Lawal ya taho misalin karfe sha daya da tsarabar kazarsa da abin sha. Ya murda kofar Amarya, ya ji ta gam. Yayi ta bugawa tamkar zai balla Kofar, ta Ki budewa.
“Ba Zainabu ba, ina
zaton duk matan gidan suna jin irin zagin da yake surfa wa Amaryar tasa. Fadi yake, “ni za ki kawo wa rainin wayo don ubanki? ‘Yar matsiyata, ba za ki bude ba? In kika bari na balla kofar nan na shigo, sai na karairaya ki, ko in sa a daure iyayenki har sai sun biya ni abin da na kashe.” Ita dai Zainabu jikinta sai bari yake yi, tana ta kuka. Alhaji cikin takaici ya nufi dakin matarsa ta ukun ya sauke mata wahalar da ya debo ta magungunan da ya dankara.

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 9

FETTA CHAPTER 26

Zainabu har goman safe ba ta bude kofa ba. Sai da ya bar gidan, sannan Uwargidan ta zo ta buga, ta ce, “bude yarinya ni ce, shi ya fita.
‘ Matar ta shiga dakin, tana kallon Zainabu cikin tausayi, ta ce, “Allah Sarki, ashe yarinya ce karama.
Ke ko me ya kai ki auren Alhaji? Cikin kuka, Zainabu tace, dole aka yi min. Kudi ya nuna wa iyayena. Ina da wanda nake so, yake so na.Ta ce,”
“amma iyayenki ba su
bincika ba ne?” Ta ce, “ni fa ban san komai
a kan auren nan ba.Ta ce, “Kai iyaye da
yawa suna yin kuskure. Da zaran sun ga kudi, sai su tura ‘ya’yayensu kawai, babu bincike.” Zainab cikin tsoro tace dan Allah hajiya me yake yi tace “ba
komai, kar ki damu. Shawarar da zan ba ki, kar ki sake rufe masa kofa. Sannan duk abin da ya ce, ki yi, kar kike yi masa gardama.
Hakan zai fi miki alheri, ke da iyayenki. In kuma kin ki, to zai tozarta ku gaba dayanku.”
Zainabu, cikin kuka ta ce, “na shia uku! Hajiya to ke ‘yar uwarsa ce?” «A’a, ni Ta mike, “bari in sa a kawo miki abin kari.” Zainabu ba ta ce a’a ba, don tana jin yunwa. Rabonta da abinci tun jiya da safe.
Koko ne da kosai, duk sun huce. Yarinyar da ta kawo za ta kusan sa’arta. Zainabu dai haka ta tuttura.
Da rana Inna Yalwa ta zo, aminiyar Innarsu ce. Zainabu cikin kuka ta fada mata komai. Inna Yalwa, ta ce, “da Allah, can, duk karya ta fada miki, kika kama. Kishiya ce har za ta ce miki ga laifin miji, ki hau cikin fushi. Kuka ta ci gaba da yi. Ya kashe ta da mari, “nine Babanki? To, bari in nuna miki cewa ni mijinki ne, ba ubanki ba!” Da karfinsa ya yi amfani, ya raba ta da tufafinta, sannan ya jefa ta kan gadon. Duk
‘yan gida da yaran suna jin ihunta. Da ma ya yi mata nata shiri na musamman. Don kansa ya bar ta, ba don rokon da take masa ba, ko don wahalar da ta sha. Sannan ya bar ta yashe ba kulawa bare. tausayawa, ya nufi dakinsa.
Haka ta kwanta babu barci sai kuka take yi. Ya fita da wuri, don haka Hajiya Indo ce Uwargidansa ta zo ta duba ta, ta dafa ruwan zafi ta taimaka mata, sannan ta ba ta abin kari. Tsawon sati guda da yayi a dakinta bai raga mata ko sassauta mata ba.
Haike mata kurum yake yi. Don haka ta sha azaba. Tsoronsa da tsanarsa sun dasù cikin zuciyarta.
Khalil ya yi nasarar goge dan imanin
Mimi da dan tauhidin da Ismail ya soma cusa mata. Ta zuwa ‘yan kwanäkin da suka biyo baya, sun yi nisa cikin tsarin yadda za su gudu. Ko yanzun da suke yin waya fada mata yake yi, ta nuna cewa ta amince sai daf da auren sai su gudu. Sannan suna da bukatar kudi kafin ranar. Ya ce, “zan dauki sarkar Mamana in kai kasuwa in sai da, saboda Dad dinmu ba shi da kudi a gida saboda siyasarsa din nan.” Mimi ta ce, “kai ba ka da naka kudin ne?” ya ce, “account dina babu kudi, bai fi dubu ashirin ba. Dad bá ya zuba mana kudi sosai yanzu saboda siyasa.
Ta ce, *ka bar shi, ina da kudi a cikin karamin account dina. Kamar nawa za mu rike?” Ya ce, “muna bukatar kudi sosai, saboda za mu kama guri mai kyau ne a wani state din wanda ba za su yi tunanin za mu je ba.” Mimi ta ce, “ok, ka samo, ni ma zan samo, sai mu hada.” Ya ce, “shi ke nan sai mun yi waya.
Bayan sun yi bankwana ta soma tunanin yadda za ta kwashe duk wani abu nata mai amfani. Matsalarta daya, kudinta masu yawa suna cikin babban account dinta. In kuma ta taba dole ne Mahaifinta

 

 

 

Hmmm