CANJIN RAYUWA CHAPTER 11 BY HALIMA A K/MASHI
CANJIN RAYUWA CHAPTER 11 BY HALIMA A K/MASHI ,shi, ai ba ki rama ba, sannan kin shirya me za ki ce ma Hajiya? Kar ki manta dai da ta gargade ki sosai sannan aka turo mi ki shi. A fili ta ce, to me zan mishi in huce? Ta kalli wayarta, yawwa bari in kira Mina Dakingari. Bakin gadonta ta shiga, bedroom ta zauna, Mina ta daga tare da fadin Khadija Masari ya? Mimi ta ce, lafiya Dakingari, kin san mene ne? (ta ci gaba) Mom dita ce in fada miki ta dage sai wani malami ya koya min karatun islamiyya. Mina ta ce, mene ne laifi? Mimi ta ce, dan rainin wayo ne, kinga yanda ya ke son nuna min iyaka ta? Nan ta kwashe komai ta fada mata, Mina ta ce, kin san me za ki yi masa? Mimi ta ce, a’a, Mina ta ce, in Dad din ki ya dawo ki sa a kira shi, sai ki ce kina son a ware lokacin karatun ku minti talatin ko awa daya, yanda dai ki ka zaba, king ba zai taba tashi daga gurin karatun ba sai lokaci ya cika, Mimi ta ce, yawwa kin kawo shawara, kin ga sai in yi masa duk cin mutumcin da na so na tsawon lokacin, k…