Haqiqa akwai abinda Kawunka ya hanga yake son ya hada ka da Afrah aure, domin tabbas! Aure a yanzu bai dace da kai ba, illa iyaka wata manufa da yake da ita, idan yana tunanin dan abinda ya rage maka na daga gadonka ne yake son ya had auranka da ‘Yarsa, don su kwashi rabonsu.
Ai ya kamata ka yi masa bayanin cewa ba ka da sauran komai, domin abinda ya ragen ka dade da dagawa ka sayar, ka yi shaye-shaye da kudin, babu abinda yarsa za ta aura, sai Musaddik da
wahalarsa. Hankalin Musaddik ya tashi ko kadan baya jin dadin maganar da Hajiya Kilishi take yi ta cin fuska da wulakanci, ya yi Kasa da kansa, ransa na Kuna, a yayin da ta ci-gaba da magana.
“Ni wannan yarinyar ko kadan ba ta burgeni ba, ba ta ba ni sha’awa, don haka ba na murna ko maraba da auranka da ita Ya dago ya kalleta sosal
sannan ya ce.Hajiya ke ce mutum na farko a duk duniya da na taba jin kin ce Afrah ba ta burge ki, domin Afrah tana burge kowa, ko ba don kyawun fuskarta ba, don kyawun halayenta da natsuwarta, dole ta burge kowa Hajiya Kilishi ta ce tana yi masa wani mugun kallo
*Wato ka na son auranta ne Musadik, ba shirin Kawunka bane kadai, kai ma ka na so.” Musaddik ya hadiye bacin ransa yace “Aure baya gaba na, ba na kuma yi ma kaina sha awar zama shugaban kowace mace. Domin na san ba zan iya yi mata adalci ba, amma zuciyata na sameta cike da dokin. auran Afrah, don haka ke ma ki amince da ita, domin alfarma za tayi min na aurena.” Yana gama fadin haka, ya tashi ba tare da ya saurari komai ba daga gareta, ya fice ransa da hankalinsa a tashe.
Bakin-ciki da tsananin damüwa suka Kara cika zuciyar Hajiya Kilishi. Ta tashi ta ‘shiga kai gauro ta kai mari a tsakiyar falon, ko kadan ba ta bukatar Musaddik ya kara yin aure, domin tana da tabbacin idan ya vi aure.
Dole ya rage wani abu daga cikin ta’asar da yake yi, wanda ba za ta taba son hakan ba, kuma auran nasa zai zama sanadiyyar da zai samú shi ma ya kafa tasa zuri’ ar, sannan ko yaya ne za°a dinga ganin mutuncinsa, tunda yana da iyali, hakika auran
Musaddik fitina ne a gareta, don ranta baya so.
Kuma abu ya z0 gaba daya cikin kurarren lokaci, amma gaskiya dole tayi wani ho66asa akin kokarin watsa auran tun kafin ayi, gara Musaddik ya zauna yaci-gaba da gurbatacciyar rayuwarsa, ta yi imanin kuma babu mace da za ta tattago ma kanta auran shashasha irinsa, in dai ba irin wannan auran zumuncin ba. Babu ta inda za’ ayi Musaddik ya sami auran wata mace a irin lalatacciyar rayuwar da yake a. ciki, shin ya aka yi Malam Mahmud ya yi tunanin yi ma Musaddik aure da ‘Yarsa, kuma meye manufarsa?
Domin dai ta fi kowa sanin cewa Malam Mahmud ya san Musaddik bai aje ba, bai ba wani ajiya ba balle ta yi tunanin don abin duniya yake son. ya hada auran nasu, hakika wannan abu bai yi mata dadi ba kwata-kwata. Hakan ya sa gari na yin sanyi, karfe biyar da rabi dai-dai motarta ta tsaya a kofar gidan Malam Mahmud, ga sa’arta kuma Malam Mahmud din yana gida bai dade da dawowa gidan ba,A’a
Hajiya Kilishi ce da yamman. nan? Cewar Mama Hauwa, tana kokarin aje tsintsiyar hannunta.
Hajiya Kilishi ta ce “Ni ce Hauwa”. “Shigo daga daki mana.” Ta girgiza kai ta ce “A°a ba zama na zo yi ba, sauri na ke na koma gida, wajen Mai-gidan na zo, ina fatan yana nan”
Mama Hauwa ta yi murmushi, domin ta fahimci Hajiya Kilishi bada arziki ta zo ba, ta san kuma dama ba wata jituwa ce tsakaninta da Malam Mahmud ba.
Don haka ta ce “Eh, yana nan”. Kafin ta yi magana. Malam Mahmud ya fito daga dakin sa yana kallon Hajiya Kilishi “Sannu da zuwa”. Ta juyo ta kalle shi ta amsa “Yawwa, ina gajiya?”
“Lafiya Kalau, hala dan naki ya gaya miki sakona
ne?” Ta ce “Eh dalilin zuwa na ma kenan.” Ya ce
“Toh”. Hajiya Kilishi ta gyara tsayuwarta, sannan ta fara magana “Yanzu tsakani da Allah wannan abin anyi dai-dai kenan?”
•Yace “Kamar yaya?” Ta ce “Kamar na yadda za’a gaya mana magana daga sama, ni dai a’iya sanina Musaddik da Afrah ba sa soyayya, haka zalika bai taba yi min maganar yana son ya Kara aure ba, tun bayan rabuwarsa da Hannatu, don haka na yi mamakin jin lamarin.
Kuma wane abu ne ya sa ka tunanin Kulla wannan auran? Bayan ka na sane da halin da yake. ciki, auran ma ba zai iya rikewa ba. Don haka ina ganin maganar auran nan a bar ta kawai har zuwa lokacin da zai sami natsuwa, ya nemo ‘yar da yake so da kansa”
Malam Mahmud ya jinjina kai ya ce “Kilishi wace irin magana ce wannan ki ke yi, shin meye amfani sanya ma Musadik ido ya ki aure, don kawai ana kallonsa a matsayin dan iska wanda ke kin sani, ni na sani jama’ar ma da sukeyi masa kallon hakan sun san cewa da ba haka yake ba, kaddarar rayuwa ta maida shi haka.To don me ba za mu taimake shi ba, ni
Zumunci na ke ma, domin Musaddik ba shi da bambanci da dan da na haifa, tunda ‘Yar-uwata ce ta- haife shi, don haka ko ta wane hali, dole na taimaka ma rayuwarsa, zan kuma aura masa Afrah ne, domin ya samu mai kulawa da shi da kuma rayuwarsa. Don haka maganar a janye wannan auran ba za ta yiwu ba, domin mun riga mun gama yanke magana.
Hajiya Kilishi ta yi tsaki ta ce “Ka na wani daga murya sai ka ce wanda aka zo yin fada da shi, ni ba fada ya kawoni ba, rayuwar *yarka da na ga ka. na so ka lalata, shi ne na ke son na fahimtar da kai kuskuran hakan, idan kuma da manufarka ta daban ne to ka yi ganganci.
Domin ka fi kowa sanin Musaddik baida ragowar komai na gadonsa, ina tsammanin wuri zama ma, sai dai idan na ga dama na ara masa, do haka idan ka na tunanin abin duniya ne, ya sa ka ke kokarin cuso *yarka, to ka yi kuskure.
Ya dakatar da ita rai bace matuka ya ce “Kada ki Kara yi min wannan maganar, wane arziki za ki gaya min, kece ke hadamar arzikin Musaddik tunda kuma kun gama cinyewa ke da *Yar-uwark Hannatu, ba shi kenan ba, ku je ya yi maku arzif duniya da lahira, yadda kuma Hannatu ta bar shi shi ne ku ke tunanin ba wacce za ta iya auransa, kun yi kuskure.
Auran Afrah da Musaddik ko bayan raina ne, sai anyi shi, kuma za ta zauna da shi ko da shi ya fi kowa talauci da lalacewa, domin na isa da ‘Yata.
Hajiya Kilishi ta ce. “Eh, Hannatu ta bar shi, don bai dace da ita ba, dukiya kuma da ka ke magana da kansa ya bayar, ka san haka, don haka ba dalilin maimaita
maka, ‘yarka ko ka yi ta aura masa, ina kuma taya
‘«yarka murnar auran Musaddik”. Daga nan ta juya a
fusace za ta tafi. Dai-dai zaure suka ci karo da
Afrah, ta tsaya ta yi mata wani mummunan kallo,
sannan ta fice.
Jikin Afrah a sanyaye ta shigo cikin gidan,
ganin fuskar mahaifinta a dagule ya tabbatar mata
da cewa ba abin arziki ya kawo Hajiya Kilishi
gidansu ba, ta kalli Mama Hauwa ta ga sai fara a take, tana harkarta. Afrah ta dawo da kallonta ga
mahaifinta ta ce a sanyaye “Baba make faruwa ne, na ga Hajiya Kilishi a fusace ta fita?”
Malam Mahmud ya yi gaggawar boye
damuwar fuskarsa ya ce “A’a ba ki dai fahimta ba ne, lafiya lau, na kirata mun yi magana ne akan auranki da yayanki.”
Mama Hauwa ta yi karaf! Ta ce “Me ya sa baza ka gaya mata gaskiyar cewa Hajiya Kilishi ba ta
son auranta da Musaddik ba, kuma ta yi maka
maganganu na wulakanci da batanci”
A.Kidime Afran ta dubi mahaifinta ta ce
“Wulakanci da batanci akan me? Wace ce ita da har take da dama da garantin tsayawa a gaban
mahaifina ta yi masa wulakanci?” Malam
Mahmud ya dubi Mama Hauwa ransa a Gace zai yi magana kenan, ta riga shi.
“A’a ai ba ta da laifi, don kawai ta zo ta tunatar da shi cewa Musaddik baida sauran ko kwandala na gadonsa, don haka idan don kwadayin dukiyar ya sa zai aura masa ke, to ya fa tuna baida komai, kuma ni ban ga laifinta ba. Don ta yi tunanin hakan, don kowa ma hakan zai dauka, don idan ba hakan ba, ba dalilin aura ma Musaddik ke a irin muguwar rayuwar da ya dora kansa a kai.
Cikin fusata Malam Mahmud ya daga ma
Mama Hauwa hannu ya ce
“Idan ki ka kara yin
magana akan batun da ya shafi Afrah da Musaddik ko auransu ko akan abinda ya danganci Hajiya Kilishi.
Ki rubuta ki aje, zan yi matukar ba ki mamaki, domin zan yi miki abinda mafarkinki bai taba nuna miki zan yi miki ba, zan aje duk wata alaka da ke tsakaninmu, naci miki mutunci”.
Mama Hauwa tá bude baki za ta yi magana, ya Kara dakatar da ita “Kada ki yi min wata magana, ki wuce ki tafi, ki ba ni waje.”
Tabbas Mama Hauwa ta ga bacin rai a fuskar mijinta me tsanani, don haka jikinta ya yi sanyi, a hankali ta juya ta shige dakinta, a yayin da Malam Mahmud ya dawo da kallonsa ga Afrah wacce take tsaye tamkar an dasa ta. *Baba abinda Mama Hauwa ta fada gaskiya ne? Zan dauki komai, amma banda wulakanta min kai, don ka fi karfin komai a gareni.” Malam Mahmud ya yi dan murmushi cike da kaunar
‘Yarsa yace Haka ne Afrah, amma ba na son ki sa wannan a ranki balle ya dameki, tunda domin Allah muke yi, duk abinda muke yi, kuma dama ai bai kamata Hajiya Kilishi ta so duk wani ci-gaba da
Musaddik zai samu ba.
Tunda ba ta sonsa ba ta kaunar sa, ba kuma ta kaunar duk wani ci-gabansa, shi kadai ne bai gane hakan ba, yake daukarta a matsayin mai kaunarsa, don haka ko kadan kada ki sa damuwa akan lamarinta”
Afrah ta numfasa ta ce “Haka ne Baba, amma ci maka mutunci shi ne abinda zuciyata ba za ta dauka ba”. Yace “Ki yi hakuri *Yata, ki sabar ma kanki kauda kai akan duk wani da zai ci a gareni, mece ko namiji, bare ko dan gida ki sa ma kanki hakuri, kada kuma ki nuna ma kowa, taba ni shine nakasunki, don idan makiyi ya gano inda lagonki yake, to za ki sha wahala, don ya sami hanyar bata miki rai kenan.”
Afrah ta dan samu natsuwa sannan ta ce “Na yarda da maganarka Baba, na gode kuma da fahimtar da ni da ka yi?. Ya yi murmushi ya ce “Ba damuwa. Ki je ki yi sallah, ni ma masallaci zan tafi, ga shi can ana shirin tayar ma da sallar.” Ta gyada kai, lokaci daya ta wuce zuwa dakinta, domin ta aje
• jakarta ta makaranta. Zuciyarta cike da tsanar Hajiya Kilishi. Domin duk wanda zai tada mata mahaifi, to bata da makiyin da ya fi shi.
Karfe daya da rabi na rana Hajiya Kilishi ta tsayar da motarta a kofar gidan Hajiya Rakiya, lokaci daya ta janyo wayarta da ke dore a saman motar, ta dannan ta kira wayar Hajiya Rakiya. Bugu daya ta dauka. “Hajiyar Allah.” Hajiya Kilishi ta amsa “Ga-ni a kofar gidanki, ki yi sauri ki fito don Allah”
Ta ce “Toh, ga-ni nan fitowa yanzun nan”.
Mintina uku tsakani Hajiya Rakiya ta fito a gaggauce, ta bude gaban motar da sauri ta ta shida, ta harba titi. Sun yi tafiya me nisa, sun fito daga cikin garin Minna har zuwa wata ‘yar karamar rugar fulani, kafin su karasa rugar. Hajiya. Kilishi ta tsayar da motar, suka fito da kafa suka Karasa rugar. A dai-dai gaban wata ‘yar karamar bukka suka tsaya, gaba dayansu.
Hajiya Kilishi- ta ce “Ahuwonka.” Daga cikin bukkar aka amsa “Lale, shigo.
” Nan da nan suka
cusa kai cikin bukkar, wani bafullatani ne mara kyan gani a zaune akan wani buzu.
Gabansa duk tarkace ne na kayan tsubbu, yana ganin Hajiya Kilishi, ya washe baki, ya hau fara’a, ya ce. “Ashe Hajiya ce?” Ita ma ta yi dariya ta ce
“Ni ce Mai Rakwacam!
Bayan sun zaunane, Mai Rakwacam ya bukaci jin abinda ke tafe da Hajiya Kilishi, ta gyara zamanta tana kallonsa sosai ido cikin ido, sannan tace.
“Na zo hankalina a tashe ne, Mai Rakwacam.
Akan maganar Musaddik ne, aure zai yi, ni kuma ko kadan ba na bukatar ya yi auren, domin aurensa hanya ce ta arziki, kuma hanya ce da za ta iya kai shi ga samun canjin rayuwa.
Ni kuwa ka fi kowa sanin duk wani ci-gaba na Musaddik ba na maraba da shi, kuma yarinyar
• Yar-uwarsa ce ta can dangin mahaifiyarsa, auransu ina da tabbacin zai Kara kusanta shi da dangin mahaifiyarsa”.
Mai Rakwacam ya dubeta ya ce “Yanzu me
• ki ke bukata Hajiya?” Ta ce “Kamar yadda ka saba taimaka min kuma na ke ganin haske, shi ne na zo gareka, abinda na ke bukata, shi ne a lalata maganar auran, kada ya yiwu, a bata komai da komai, a bar shi a yadda yake, ya ci-gaba da gararambarsa ta lalacewa.”
Mai Rakwacam ya janyo wani katon tulu ya shiga surkullansa, ya dauki tsawon lokaci yana aikin tsubbunsa, sannan ya dago ya kalleta, yana girgiza kai, sannan ya ce.
Hmmm