MUSABBABI CHAPTER 3 BY HAJ HABIBA
Zuciyarsa cike da tunanin maganganun da suka gama tattaunawa da Innarsa. Washegari da yamma dawowar Afrah daga makarantar Islamiyya kenan, tare suka jero da Sayyadi Habibi, hira suke cike da annashuwa da kaunar juna har zuwa kofar gidansu. ‘Anan suka tsaya, domin su yi sallama, dai-dai lokacin Musaddik ya tsaya shi da dan acaba, daga shi har wanda ya goyo shi, babu mai kyan gani, idanu jajir! “ “Ka jira ni yanzu zan fito”. Musaddik ya gaya ma abokin tafiyar ta sa, sannan kai tsaye ya nufi cikin gidan, murya a sanyaye Afrah ta gaida shi, ya amsa yana kallonta “Afrah ya gidan?” Ta ce “lafiya lau”. . Malam Habib ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya shige cikin gidan. A yayin da Malam Habib ya dawo da • kallonsa ga Afrah, wacce duk fuskarta ta canja ta shiga damuwa, ya ce “Afrah me ya faru ki ka canja fuska? Ta yi dan yake ta ce “Ba komai Ya Sayyadi.” Ya girgiza kai ya ce “Hmmm! Da komai mana, Afrah duk abinda ki ka ga ya faru da bawa, to rubutacce ne akan allon Kaddararsa, ko kadan kada ki sa d…