CANJIN RAYUWA CHAPTER 7 BY HALIMA A K/MASHI
CANJIN RAYUWA CHAPTER 7 BY HALIMA A K/MASHI wannan wulakancin, don Allah ka yi zuciya ka bar mata yarinyar ta. Isma’il ya ce, hmm ka san na sha yunkurin yin haka, amma sai in samu kaina cikin tashin hankali, ban san lokacin da na soma son ta ba. Ka yi hakuri Mahamud ban ki batunka ba, abin ya wuce duk yanda ka ke tunani. Kai dai ka gode ma Allah, tun da ba ka da matsala da iyayen Rabia. Mahamud ya ce, ko da ina da matsala da su ba zan dauki haka ba, sai in bar su da ‘yarsu. Kaima ina mamakin duk zuciyar da ka ke da ita, ya dafa Mahamud kar ka ji komai, ka sa ni cikin addu’arka. Mahamud ya ce, ka binciki asalinsu? Isma’il ya ce, Yaya Amina ce ta binciko, ranar take gayamin wai Ubansu bakano ne. dan wani kauye wai shi Kurje keya. Ita kuma Uwar ‘yar Ruma ce, can wajen Safana. Ya auro ta lokacin yana da abin hannunsa. ‘Ya’yansu shida maza uku mata uku, mazan ne manya matan kuwa Zainab ce babba, tunda arzikinsa ya karye sai buga- buga sai ta raina shi, ‘ya’yan ma suka raina shi, sai abinda ta c…