UMM ADIYYAH CHAPTER 91 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 91 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng “Zan fadawa Maami ta dauke, na san ba ta san kin boye ba. Yaushe za mu tafi, gidan can ba dadi.” Ya fada fuska a yamutse, “Yaushe muka zo? Cab! Ai sai mun kara wata daya kafin nan sun yi kwari. Yanzu fa ni kadai, sai Innayo, idan na koma zan yi kara- mar hauka.” Amma dai wasa kikeyi ko? Wata daya? Kin san kwananki nawa rabonki da gidanmu?” “Ba yawa, Na ga alama barci ne ya yi makka yawa, muna zuwa sai ka gwammace zamanmu.” Ba lsaifi, bazan damu ba, saboda haka ku fara shiri kawai zan yi wa Maami magana, idan ma nauyi ki ke ji ke.” Ya fada yana mata dariya kasa-kasa. Kallonsa kawai take yi yana bidirinsa, bai yi kasa a gwiwa ba ya fadawa su Maami za ta koma aka kammala duk shirye-shiryen komawarta, har gidan an je an gyara mata. Ranar farko da suka koma a tsaye, suka kwana, don kukan yaran, ba dabarun da ba su yi ba, amma abu ya gagara. Sai da suka kai wurin watanni uku. Sannan suka fara barcin dare. Girmansu har mamaki yake…