UMM ADIYYAH CHAPTER 90 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 90 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng murmushi. Daya bebin na cikin Cot din da ke gefen gadon. “Sun ce da kai suka yi kama. Na ce masu ni ma da kai na yi kama.” Umm Adiyya ta fada tana kallon yadda ya kurawa Baby idanu. Juyowa ya yi ya bar dariyarsa, ya tsuke fuskarsa, ya ajiye baby din. Zai mike ne, ta yi saurin riko hannunsa, “Ka yi hakuri.” “Laifin me ki ka yi?” Rufe idanunta ta yi ta bude, “Don Allah kar ka hukuntani haka kawai dai ban fada bane ganin yadda akan daya ma ka damu sosai bare idan ka san biyu ne hankalinka sai ya fi haka tashi. Shi ya sa ban fada maka ba.” “Uhm! Ya yi kyau Allah ya rayasu.” Abinda ya fada kawai kenan ya daga baby B daga dan katifar jariran ya sumbace shi, san- nan ya ajiye shi, shi ma. “A huta gajiya, bari na bar ku, ku samu barci. Sai da Safe.” Baki ta bude da idanu cikin mamakin fushin Zaid, dama yanzu hakan zai bata masa rai? “Please, Noorie kar ka tafi da fushina.” Ta fada a marairaice, hakan ya dawo da hankalinsa kanta, ya…