UMM ADIYYAH CHAPTER 88 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 88 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 88 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  mushi, sannan ya ce, “Shi kenan hankalinki ya kwanta?” Ita ma murmushin ta yi a kunyace. Take Dr. Yusuf ya san lamarin nasu ya wuce basaja. Haka yana ji yana gani suka fice a ofishin din ka na ganinsu, ka ga wadanda suke matukar son juna, daga kallon da suke yiwa juna, zuwa yadda suke magana da juna kadai ya isa shaida. Ajiyar zuciya ya yi, ya daga aikin da ta mika na Project din da suka bari. A bangarensu kuwa, tun suna tunanin abin na dan lokaci kadan ne za ta daina, amma gadan-gadan! Wannan cikin sam baya son kamshin Zaid, sai daga baya suka fahimci ba turaren bane ma baya so, shi karan kansa ne, daga nan kuwa ya nisanci shisshige mata da yake yi, sai in ya kama dole. Wataran sai ya yi kamar zai riketa yadda ya saba zama kusa da ita, sai ya tuna. Har tausayi yake ba ta, amma ba yadda ta iya. Haka dole suka raba sabogoginsu. Wannan al’amari ba karamin damun Zaid ya yi ba, amma dole ya hakura saboda ya san halin da take shiga, muddin ha…