RAYUWAR IRFAN CHAPTER 3 BY (UMMU KHAIRIYYA)

RAYUWAR IRFAN CHAPTER 3 BY (UMMU KHAIRIYYA)
RAYUWAR IRFAN CHAPTER 3 BY (UMMU KHAIRIYYA) Www.bankinhausanovels.com.ng  Aikin Shine Kawai Sa idone inaso kasamin Ido Akamfani na da nake Sarrafa shinkafa ta yadda Zan kaika A Matsayin Me gadi Amma duk wani Shige da fice na kamfanin inaso ya kasance Atafin Hannuna Sannan Akwai Babban Yaro na Salim shine wannan danace ya bamu guri d’an Uwan Matata ne Shike rik’e da komai na kamfanin inaso duk wani Motsin da zaiyi ya kasance Akan idonka Yan zu Ina wayarka? Sosa Kai Irfan ya yi yace “Ranka ya dad’e Ai banida waya” “yawwa Koda kanada waya yazama lallai na can za maka ita Saboda Aikin da zakayi Ina buk’atar video Acikinsa Kuma inaso ya fito yadda Zan Ganshi tar tar” waya ya D’auko Samsung Galaxy note 10 Sabuwa dal Akwali ya mik’a Masa karb’a ya yi yana jujjuya wayar Alh. Sa’id ne ya d’ora da cewa “A wurin kowa bani da wata Alak’a tsakanina dakai Kuma wannan ya Zama Sirri tsakaninmu zakaje kamfani A Matsayin Me gadi duk da cewa Ina da Me gadi Zaka Zama matai makinsa wajan gabatar da Aikin ka…