RANA DAYA CHAPTER 16 KARSHE BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 16 KARSHE BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Wanka ya fada, da ya fito yayi sallah tun daga lokacin ya fara nuna shi ango ne. Gizna ce ya sha fara sol sai aikinta mai ruwan kasa da ratsin gwal.Aka soka hula kube takalmi. Turare kuwa yanda ka san zai yi magana. Ya sakko suka hadu a falo. Hajiya tana aiken Direbansu, ta tsaya tana kallonshi. Yayi mata kyau sosai. Ya ce, “Hajiya sannu da fitowa.” Ta ce, “Kai ne da sannu Ango, wannan irin wanka haka?” Ya ce, “Ai karamin wanka ne wannan sai ma anjima.” Ta ce, “To zo muyi magana mana.” Dakinta suka shiga ta ce, “Naji Alhaji yana cewa wai za a daura aure da safen nan?” Shatima yace “Na Kano ne?” Ta ce “A’a Idan da na Kano tunda asubahi fa naji yana ta waya wai saboda abokanka ko mene ne?” Shatima ya ce, “Ok, na Aliya ne za’a daura yanzun da safe, saboda ‘yan nesa, in mun yi walima za su tafi.” Hajiya ta fadada fara’a “Ayya, na gane. To ya za ayi da abincin daurin auran tunda ba mu san za’a zo da zancen ba?” Ya ce, “Ba akwai snacks da nama ba?” Ta ce, “Eh …