RANA DAYA CHAPTER 15 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Ya ce “Iso mana, sauri nake yi.” Ta durkusa ta gaida shi, ya ce “Mike muyi magana.” tashi. Ya ciro katuna daga mota ya mika mata. “Ta “Na daurin aure ne kawai babu na dinner. Sannan ya bata dubu talatin “Wannan koda za ki yi walima da kawayenki.” Ta ce “Sun yi yawa Yaya.” Ya ce, “Haka na ba sauran.” Ta kalle shi zata sake magana ya ce, “Ki je gida ina sauri ne naga bakinki da magana, lokacin yinta yana zuwa amma ban da yau. Bai saurari abin da zata ce ba ya shiga mota, ta juya ta shiga gida. Biki saura sati daya aka je aka yi wa Nafisa jere itama. Aliya kuma washegari ana saura kwana shida. Duk kowace an yi mata bakin rabonta. Nafisa itama dakunan nan an zuba gadaje, sannan kicin da falo suma an yi babu laifi, don yafi na Aliya tsada ita gado biyu ne, dayan dakin aka sa katifa. Amma duk ba wadda ta kama kafar Amna. Ita ko Salma daidai wannan lokacin suna can Www.bankinhausanovels.com.ng suna ta ganganda yanda za a sai kaya. Gidan Gaje Dillaliya suka je …