RANA DAYA CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI  Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Shatima ya ce, “Yau za su zo karfe takwas na dare Sannan kuma Inna bikin yau saura kwana ashirin da biyar.” Inna ta ce, “Kamar ya ya?” Ya ce “In sun zo iyayen namu za ku ji komai.” Ta ce. “To shi kenan, Allah Ya kawo su. Shi kuma Kawun nasu za a je a zo da shi.” Da zai tafi ya ce Salma ta zo, a zauren gidan suka tsaya. Ya kalleta yana murmushi. “Kin shirya aure nan da kwana ishirin da biyar?” Ta dan juyar da fuskarta cikin kunya ta kalli bango. Ya ce, “Kiyi magana.” Ta ce. “Zan yi mana.” Ya ce “To juyo ki kalle ni.” Ta juyo ta dube shi. Ya ce, “Kina sona?” Ta zaro ido cikin tsananin mamaki. Ta murtsuke idanunta wai ta ga ko mafarki take yi. Ta sake kallonshi a gabanta. Ta cce “Nasan kana tsokanata ne, ni ban fi yar wanke-wanken gidanka ba.” Ya ce, “Ni fa na tambaye ki ne kawai, kina sona?” Ta durkusa kasa, “Don Allah kada ka cutar dani, wallahi na dauke ka na musamman a rayuwata, na soma tsoron ka.” Haway…