RANA DAYA CHAPTER 13 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA CHAPTER 13 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Sai ta ce, “Kaka ina ruwanta da ni, ni fa ban kula kowa ba tunda nazo.” Shatima ya dubeta fuskarshi babu walwala, “Kije gida na gode kawai.” Mamanta ta ce, “Ai ita sakarya ce, shegen kishi ta dora ma ranta.” Hajiyarshi ta ce, “Nafisa ai dole kuwa ki koyi hakuri da danne kishi tun da Allah Yasa ba ke kadai ce za ki zauna ba.” Fuu! Ta fice ta nufi gida. Su Amna suna dawowa suka soma shirin.. tafiya. Shatima ya ce, “Ni dai ba ni ki ka zo dubawa ba.” Ta ce, “Waye ne nazo dubawa?” Ya ce, “Kin zo danna waya ne da zama a waccan kujerar.” Ta ce, “To ina zan zauna?” Ya nuna bakin gadonshi. “Ga guri nan.”Ai tafiya zamu yi, tunda ka ji sauki. Haka ma ya yi min dadi.” Ta fada cikin yake. “Ban gaji da ganinki ba.” Ya fada yana kallonta. Ta ce, “To kayi ta kallona na minti biyu.” Anty tayi dariya ta fita. Kaka ta ce, “Ikon Allah! Yaran yanzu ba kara.” Amna ta ce, “Kaka ban ce komai ba.” duk suka sa dariya, sannan su…