RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  tun a jiya ta gano matsayin waccan Mahaukaciyar yarinyar, don ita minti shidda ya dauka a gurinta. Sai dai har karfe takwas bai shigo ba, gashi ta kasa tashi ta nemi koda abin kari, sai wani bakin ciki da taji yana yi mata tukuki a zuciya. Amna ya soma kira don layin Aliya ya ki shiga. Ta dauka da fadin “Hello honey!” Ya ce, “My honey na makara office yau, ban shigo ba ina fatan kina lafiya?” Ta ce, “Ina lafiya zumana.” Ya ce, “Kin ci abinci ko?” Ta ce, “Yanzun na tashi, zan sha tea ne da Indomie yau.” Ya ce, “To ki sha da yawa. Ta ce, “Jiya mun yi waya da Mom dinmu, ta ce za a kawo min mai aiki yau ko gobe.” Ya dan yi jim, me hakan ke nufi, shi zai biya ‘yar aikin? Ta ce, “Hello kana ji na kuwa?” Ya ce, “Ina jin ki.” Ta ce “Kaga na huta.” Ya ce, “Haka ne, to sai na dawo.” Yayi shiru yana juya wayar hannunshi. Kenan ana nufin sai ya dauki ‘yan aiki hudu ko ko me? Ya juya ya shiga kiran layin Nafisa.…