RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Bayan ya sa ta ta rufe kofa, ya nufi dakin Aliya yayi wanka yasha sabbin kaya, ya dauki makullin mota ya fita. Kajin Amarci ya siyo da madara mai sanyi, da sauran kayan zaki, don ya lura Amna tana son shan zaki ko ya ce an saba musu da shan zaki. Kai tsaye gurin da motocin ta suke ya wuce, ya saka tashi. Sannan ya fito da ledojin ya nufi falon Amna. Yana shiga ya kulle kofar, don yasan ba zai fito ba sai gobe. Dakin da ta sanar da shi cewa nan ne nashi, nan ya nufa. Karan ruwan da ya ji daga cikin bandakin shi ne yasa shi tunanin tana ciki. Sai ma ya ga kayanta da ta cire a kan gado. A ranshi ya ce, “Wannan yarinyar wanka a gurinta ko kifi sai haka.” Ya cire hularsa ya ajiye a kan durowar da ke gefen gado. Tana fitowa daure da babban Tawul, ta rufa da karami tana goge jiki. Ya sakar mata murmushi, tare da cewa, “Koma kiyi alwala muyi wa Allah godiya.” Dan jim din da tayi sai ya ji tsoron kar dai itama…