RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Yana gaida Hajiya, Mustapha ya shigo. Ya gaishe shi, Shatima ya ce “Don Allah Mustapha ka hada min duk kayana. Sannan kuma in an gama zirga-zirga ka dauki motar nan tawa ta da.” Dadi ya rufe Mustapha, ya shiga godiya. Hajiya ta ce, “Kafar yawo ta karu, ai dole kayi murna.” Mustapha yace Ai na huta, in na ari motarki, ko ta Alhajinma, sai a kira ni a ce dawo min da motata yanzun nan.” Ta ce, “Ai dai tayi maka amfani.” Ya ce, “Sai dai za ki dinga taimakawa da na mai ko Hajiyarmu?” Ta ce, “A’a wanda ya baka motar sai ya hado maka da na mai, ko kuma duk lokacin da zaka fita sai ka kira shi ya turo maka da na man.” Suka sa dariya. Bai baro Zariya ba sai da ya tabbata duk abokan shi na nesa sun wuce. Kusan karfe biyar ya shirya kayanshi a motocinsa guda biyu. Ya ce, Mustapha ya tuka masa motar suje, sai ya hau ta haya ya dawo. Yana cikin tuki ya tuna ashe fa zai bada abincin rana a gidansa, gashi tun da …