RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya kunnansa daidai bakinta “Me ki ka ce?” Ta ce, “Tsawona ba zai kai ba.” Ya ce, “Zan taimaka miki.” Ta matso ta dan yanki kasan, ta kalle shi a zatonta zai durkuso ne tasa mishi, sai kurum taji caf! Yayi sama da ita, ya rike kugunta. Ta kalmashe kafafunta tamkar masu rawar turanci, sannan ta saka mishi a baki. Gurin ya dauki sowa. Maimakon ya dire ta sai kurum ya shiga juyi da ita. Guri kuwa ya dauki ihu da sowa. Sannan ya sauke ta, kowa ya koma mazauninshi, aka shiga ci da sha. Ba a tashi ba sai sha biyu da mintuna. Tun da aka dawo daga Dinner Salma ke zaune a barandarta, ga makulli a hannunta amma bata iya bude kofar ba, don tun kafin su Yaya Hadiza su tafi suka kulle suka bata makullin tasa a jaka. Domin babu wanda yaje a cikinsu. Ranar dama yinin yunwa suka yi tunda ba a kawo musu abincin. ‘yan jere ba, wa ma yasan sun zo wani jere? Shi yasa suka ce ba za su je wata Dinner ba. Tana shawarar yanda zat…