RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng RANA DAYA 2/4 Mun tsaya Daga nan sai aka ce Ango ya zo ya ba matanshi abin sha ko naci. ‘Yammata masu sanye da kaya iri daya su uku, su ne suka zo suka kawo wani dan tire. a rufe, daya da ‘yan kofuna guda uku, dayar kuma da hankici na share baki. Www.bankinhausanovels.com.ng Ta bude dan tire din, nakiya ce guda uku, ya dauki daya ya ba Aliya ta gutsura, aka yi tafi gami da rangada guda. Mai kofunan ta matso, ya dauka madarar shanu ce wadda ba a jima da tatsowa ba, ya kurba mata, sannan me hankici ta kawo ya dauka ya share mata. Duk su ukun hakan ya yi musu. Shima haka aka umarce su su ba shi daya ta bashi nama, daya ta ba shi ruwa, daya ta ba shi tataccen ‘ya’yan itatuwa. Tsarin bikin ya birge mutane sosai, daga nan aka shiga daukar hotuna. Tsakiyar Aliya da Amna ya zauna, sannan ya rungumo su duka. Ya sake dawowa tsakiyar Amna da Nafisa, ya sake rungumo su. Sannan yayi da kowacce rungume da ita. Daga nan …