RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI  Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Munnir ya ce, “Wai don Allah Shatima lafiya ka ke tsaki?” Ya ce, “Ina tunani ne, yarinyar nan Salma tana can cikin damuwa, koma ayi mata wani abin tun da na san ba a sonta Munnir ya zabga ma Shatima wata harara, sai ka ce irin yara kanana din nan, sannan ya ja dogon tsaki ya ce, “Ka san Allah har na soma tsanar wannan Salmar, duk ka bi ka zama wani soko a kanta.” Ya ce, “Munnir ba zaka gane ba ne, da dai na sani da na ce ma Anty Momiyo a hada ta da Aliya nasan zata kula min da ita.” Ya ce, “To ka kira mana ba ga waya a hannunka ba, ka dame mu da tsaki.” Shatima ya fita ya kira layin Anty Momiyo, sai a kira na uku sannan ta daga. Ya ce, “Haba Anty, kin ki daga wayata.” Ta ce, “Wallahi na gaji ne, na fara bacci.” Ya ce, “Anty don Allah Salma ita da wanene?” Ta ce, “Oho ban duba ba, ‘yan uwanta dai sun fito sun tafi.” Ya ce, “Ya ya za’ayi don Allah ki hada ta da Aliya.” Anty Momiyo ta ce, “Babu ruwan…