MALIKA MALIK CHAPTER 20 KARSHE JANAFTY MALIKA MALIK CHAPTER 20 KARSHE JANAFTY *KAR’SHE…*??? …..”Full Address Din da Saleema ta Turo mata tabi da kuma tambaya sai gata abakin makeken get din gidansu Malika tana zuba hon da hanzari megadi yazo ya wangale mata get yana mata barka da Zuwa,yana zaton kawar Hajiya Malika ce. Aparking space ta adana motarta kafin ta Fito tana Sanye da abaya doguwar riga baka ta kamfanin Armani Wacce ta yane kanta da karamin bakin gyalenshi, Kafarta Sanye da Cover baki,mai wani Fulawan baki Ajikinsa,sai karamar bakar jakarta dake hannunta Hade da key din motarta cikin Sha”awa take bin gidan da kallo kafin tafara taku Zuwa Wata kofar glass din da zai sadata da cikin Babban Falon gidan. Tana sa kanta Falon Cikin Sallama Da karamar muryanta kamar ba Zahra ba, babu kowa a makeken Falon,sai karar Talabijin din da ta kusa cinye bangon Wajen Saboda Girma,tana kokarin sake Maimaita Sallaman nata ne Sai ga Merry ta Fito dauke da Aryan ahannunta yayinda Dose ke Tura Ayyan a wani karamin keke da…