MALIKA MALIK CHAPTER 16 BY JANAFTY MALIKA MALIK CHAPTER 16 BY JANAFTY Www.bankinhausanovels.com.ng Hajiya Binta tayi matukar Murna da ganinsu sosai haka ta Shiga Dawainiya dasu Ayda ko Ram ta goyeta bisa bayanta tana jijjigata saboda yau tatashi da Rigima ne. Koda suka iso katsina Malika ta nemi Saleem awaya ammh bai Daga kiranta ba,sai tamai Uzuri ko yana Wani Abu ne,ammh Abunda ya bata mamaki har Washegari bata ga kiransa ba,kuma harda zasu Wuce malumfashi da Hajiya ,ta kirashi taji yayi hanging din kiranta A Number Busy kuma daya gama bai kirata ba,Abun sai ya bata mata rai Taga toh metamai Ammh ya Dau Wannan Fushin da ita,Tunda ga lokacin itama Tayi alqawarin Fita batunshi. Duka gidan suka Tafi,sai aka bar Dose da Wata yar aiki da Hajiya ta Dauka sai sauran ma’aikatan Haraban gidan da megadi,Koda suka isa malumfashi a family House din Su Daddy Su ka yada zango wanda dama Tun Daddy na Raye ya gyarashi Sosai Adakin Hajiya Innaro suke sauka in sukazo wanda Shima yake gyare tsaf Duk da Wacce ta Haifi Hajiya Binta tana…