ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 20 KARSHE BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 20 KARSHE BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 20 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Haana. Ta yi masa alkawarin za ta je har gida ta sa su hadu. Da sidin goshi ta yarda suka hadu ba wani lokaci ta ba sa sosai ba. Yadda ta gan shi ta tausaya masa sai dai ta ɓoye tausayin a kan fuskarta. Cikin rauni ya ce, “Raihana me yasa za ki yi min haka bayan kin san ke ce rayuwa ta ke ce farin cikina, shin ba kya tausayin halin da zan shiga idan na rasa ki, ba kya ganin abin da Abba Aminu ya yi min mugunta ce, ki daure ki je ki ce kin fasa auran ni ki ke so.” “Malam M.J ina son ka ina son rayuwa da kai ina son ganin farin cikin ka, kai komai naka ina so ai dai bani da ikon hana auran nan don Abba Aminu ya wuce komai a gurina dole hakura za muyi mu karbi kaddarar da ta zo mana.’ Tana gama fadin haka sai hawaye. Wani irin farin ciki ne ya kama shi ya ce, Raihana-tunda kina sona to ki ce kin fasa auran.” “Ba zan iya ba hakurin kawai shi ne abin yi.” “Shi ke nan ki je ki yi auran,amma ni ba z…