ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 19 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 19 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 19 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Gajeriyar hira suka yi bayan ya gabatar mata da kansa ya ce mata yana aiki a PHCN. Bai wani jima ba ya tafi ita a takaice ta gabatar da kanta gare shi. Zaune suke ita da Muhammad Bashir a farfajiyar gidansu gurin da aka tanada don hutawa, tunda ta hango shi ta ji gabanta ya fadi, yadda ya nufo su kamar wani mawiyacin zaki da ya kwana ya wuni bai ci komai ba. Ko sallama bai musu ba ya maida kallonsa ga Haana ya ce, “Ke na gaji da wannan rainin hankalin da ki ke min ya zama dole ki sallami mutumin ta karfin tsiya ko kina so ko ba kya so kin ji na fada miki.” Cikiin bacin rai ta mike, cikin tsiwa da masifa ta ce. “Ba ka isa ba ba ka da huromin da zai sa ka yi min dole tunda ba a karkashin ka nake ba, a’a wai me ye haka ne ka ki ka bar ni na huta a gida fitina haka makaranta fitina, da wanne ka ke so na ji ne?” Kafin ya ba ta amsa Muhammad Bashir ya ce, “Malam wai me ye haka ne ka zo ko sallama ba ka y…