ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 16 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 16 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Cikin farin ciki da dariyarta ta ce, “Ya Abba ka yi min alkawari?” “Na yi miki Haana.” Dariya ta yi ta ce, “Na gode Ya Abbana daga yau ka dinga ganin farin ciki a fuska ta na kuma yafe maka duk abin da ka yi min na samu sauki yau cikin zuciyata nauyin da ta yi min na ji ta yi sauki na gode Ya Abbana na gode sosai. Ina son yau ka je gurinta ku daidaita kan ku don haka Ya Abba ina son kamar yadda ka ke taimaka min a can baya ina son yanzu ma ka taimaka min, domin na kawo nima farin ciki a rayuwar Haaya da Fadeelah ina son kowa ta samu abin da take so ka yi min alkawari za ka taimaka min. “Na yi miki alkawarin zan taimaka miki da iya dukkan karfina da kuma tunauina. ‘Good Ya Abbana na san dama za ka yi min duk abin da nake so dama wancan wanda ya sani kuka da damuwa ba Ya Abbana ba ne wani Ya Abban ne daban, yanzu nawa ya Abban ya dawo wancan ya tafi.” Www.bankinhausanovels.com.ng Duk da yana cikin dam…