ZAFIN RABO CHAPTER 9 BY SAKIEYY ZAFIN RABO CHAPTER 9 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng Bayan sun idar da jam’in sallar azahar, kamal ya gama add’oin shi a niste, ya mik’e ya fito daga masallacin a hankali yake tafiyar shi, cikin nutsuwa da kasaita, yaso ya tsaya har ayi sallar la’asar yadda ya saba a kullum amma yaga yau bazai iya tsayawa ba, shima kanshi baisan mai ya saka ba kawai dai yana so ya koma gida, haka ya tsallaka titi ya nufi hanyar makeken gidan shi da yake tsallaken masallacin, yana knocking gate d’in bai dad’e a tsaye ba mai gadi ya taho da sauri ya bud’e mishi, yana mik’a gaisuwa, kamal d’aga mishi hannu yayi, tare da yin cikin gidan, bai tsaya danna doorbell ba ko knocking kawai ya saka muk’ullin shi ya bud’e k’ofar, bai yarda da ita ba soboda haka ko da wasa bai bar k’ofar a bud’e ba, Baiyi mamaki ba da yaga parlor din wayam dan yasan bazata tab’a fitowa ta zauna a ckin shi, amma abunda ya bashi mamki da yaga ba kowa a dak’in ta, ko a bathroom d’inta da ya lek’a, haka ya k’ara fitowa ya lek’a d…