ZAFIN RABO CHAPTER 7 BY SAKIEYY ZAFIN RABO CHAPTER 7 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng Tana zaune akan katifa da had’a cinyoyinta da k’irjinta, ita kanta bata san awani nawa ta shafa tana yin abu d’aya wato kuka kenan, yanzu kanta ba irirn sarawar da baya mata, jin da tayi an bud’e k’ofa ya saka ta saurin mik’ewa, ka ganta gaba d’ayan ta a tsorace take, duk ta birkice bayan fargabar da ta cika mata ciki, ummeeta da sisi ta gani a tsaye, sakeena jikinta ne ya hau rawa ganin irin kallon da suke mata, hantar cikinta ta k’ara kad’awa,+ “Mik’a mata kayan” Sisi da fad’a a gadaran ce, haka ummeeta ta ajiye mata su a kan katifar, sakeena kuma ba abunda take in ba binsu da kallo ba, idanunta d’auke da alamun tambaya “Ki kintsa cikin kayan nan dan nan da k’aramin lokaci zakiyi bak’o” Zuciyarta wani mahaukacin bugawa tayi, tare da fara harbawa kamar zata tsage daga k’irjinta, yanzu idanunta sun k’ara cika taf da k’walla, tayi zuru zuru da ita ba abinda take sai bin tsinaniyar rigar baccin da take a ajiye akan k…