ZAFIN RABO CHAPTER 6 BY SAKIEYY ZAFIN RABO CHAPTER 6 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng Ita kuma ta kasa gane lamarin gaba ki d’ayan shi, me ya saka yayi mata abinda yayi mata, ita da ba abinda ya tab’a had’a ta dashi, duka duka yau ce rana ta biyu da ta fara ganin shi, sai d’azu ma ta tuna ashe fuskar shi ita ce wacce ta gani a gaban cilantro ranan nan, wani irin fad’uwa gabanta yake tunda ta iso garin kano, ga yarda taga mijinta na yi mata, it tasan ba haka akeyi ba ranar farkon aure, tasan ba santa yake ba dan had’a su akayi, ta wani b’angaran ta gane b’accin ranshi dan itama basan auran take ba, amma ya kamata yayi mata abunda yayi mata? Tana ganin bata cancanci haka ba, ita wallahi mutuk’ar tsoron shi take ji, duk bakinta yau ta neme shi ta rasa ta kasa mayar mishi da murtani, in ka ganta ta canza a d’an awani kawai, dukan ta a birkice take, bayan ja wur da idanunta sukayi tsabar kuka, jin tab’a tan da akayi ne ya saka ta saurin dawowa daga tunanin ta,1 “Nace muje ko” Datijuwar ce tayi mata magana, sakeena ku…