ZAFIN RABO CHAPTER 11 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 11 BY SAKIEYY
ZAFIN RABO CHAPTER 11 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng  Ko da ya shigo parlor d’in baiga kowa ba, ba sakeena, ba kausar ba kamila, baisan me ya saka abun yayi mishi dad’i ba dan yau baya san had’uwa da matar shi, bedroom dinshi yayi, yana shiga ya fara cire kayan shi tare da fad’awa bathroom sai da yayi wankan shi sosai sannan ya fito, k’ugun shi d’aure da towel, yana fitowa yaji hayaniyar su a waje, gabanshi ne yayi wani irin fad’uwa, barin ma jin muryar sakeena da yayi, a hankali kamal yayi wurin closet d’inshi ya samu jallabiya ya zura bayan ya gama gera jikin shi da feshi shi da turare masu mugun k’amshi, sai da ya d’aure fuskar nan tashi tamau sannan ya fita daga d’akin. + Dukkan su na zaune tv a kunne, murmushin da ya gani a fuskar ta ne ya saka shi tsaywa cak, binta ya fara yi da kallo yana mamakin kamar ba ita bace jiya hawaye suka cika fuskar ta, yafi mintina yana kallanta, suma na parlor d’in basu san yana wurin ba, sai can kamar daga sama kamila ta juya ta ganshi, “Lah ya…