UMM ADIYYAH CHAPTER 87 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 87 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng dawo ba ta kiransa hakan. “Na’am Twinkle me ya faru?” “Ina tsoro…” “Wani abu ki ka gani?” Wuyanta ta shiga shafawa kamar tana goge wani abu. Ya san tsigar jikinta ne yake tashi. “Fada min me ki ke so na yi miki?” “Uhm! Za ka iya canza daki?” Fuskarsa ce ta tattare cikin mamakin kala- manta. “Me ya faru da nan din, bai miki bane?” Rarraba idanu ta yi ta ce, “Uhm… Ya yi min kawai ina so ka canza daki ne, ka bar ni a nan.” Kallonta yake yi kamar ta sha omo ko giyar wake. “Yaya ki ke tsammanin na raba daki da ke? Sannan a garin da ba namu ba cikin otel? Me ya faru?” Idanunta ta sauke, “Ba na son… Ehm. Ba dai kai bane, amma ba na son ganinka.” Shiru Zaid ya yi, ya kura mata idanu wani iri. “Umm Adiyya, yau kin yi karatun Azkar dinki?” “Na yi mana, kawai ka yi hakuri. Wallahi tun shekaranjiya ba na son ganinka.” Tashin hanakali! Mikewa ya yi daga kan gadon, ya yi zirya a dakin ya je ya dawo cikin tunanin abinda ya yi mata ba daid…