UMM ADIYYAH CHAPTER 85 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 85 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 85 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari da safe ya tashi da shirin zuwa wurin aiki. Ta tashi latti wannan ya sa ta yi tunanin yin wanka tukun, saboda ba ta cika son shiga kicin ba ta shirya ba. Ta dade da sanin kuma Yaya Zaid baya son mu- tum ya tashi busu-busu ya wuce kitchen, amma kallon agogon da ta yi, ya sa ta canza shawara ta shirya cikin doguwar riga, sannan ta sauka ta hada masa abincinsa. Ta koma sama don ta yi wanka ne, ta tsaya ga- ban kwabanta don cire kayan da za ta sa, lokacin Zaid ya shigo cikin shirinsa. “Sorry, na yi latti, na sa mana abun karyawwa ka fara bari na shirya.” Tsuke idanunsa ya yi yana kallonta, “Ki shirya zan jiraki.” Har ya kama hanyar fita daga dakin ne ya dawo da baya da ya ga rigar hannunta, daure fuska ya yi ya iso inda take tsaye, “Meye wannan?” “Kayana ne, yanzu zan shirya na sauko, ka yi hakuri yau na makara.” Sa hannu ya yi ya karbi rigar hannun nata. “Seriously? Har yanzu ba ki bar sa wadannan kayan ba? Na tsanesu. Da gaske za m…