UMM ADIYYAH CHAPTER 81 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 81 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Suna gama jin bayanin Saadik, Nas aka koma kurawa idanu, “Tana hutawa yanzu, amma za a gyarata a mayar da ita (Side Ward).” Lokacin ne suka sauke ajiyar zuciya. Maami ko ta mika baby wa Babansa, ta duba Zubaidan sama-sama, sannan ta ce da Abba za ta je gida ta ga me suke ciki. “Su kadai ne a gidan.” Kasancewar duk a masauki suka sauka, wannan ya sa kowa ya riga ya wuce ta can daga gun walima. Su Umm Adiyya aka bari don su ga yanayin Adda Zubaidan, kafin Maami ta je gidan. Faruk ne ya tuka Abba da Maamin, aka bar Zaid da Baban Walid a asibitin. Koda Maami za ta taho asibitin ma da su Walid ta taho. Da ta tashi zuwa wurin Www.bankinhausanovels.com.ng Saudah kuwa Umm Adiyya ta ce ta bar su asi- bitin za a sake dawowa da Saudan. Ana mayar da Adda Zubaida dakin gefe, aka ce za su iya shiga su ganta. Baban Walid ne ya yi gaba. Asma da Umm Adiyya aka bari da leke ta karamin tagar kofar dakin da aka kai ta, yana shiga ya rike hannunta a nasa, ya…