UMM ADIYYAH CHAPTER 79 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 79 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng daukeki cikin farin-ciki da komai, na kai mata ke fuska a turbune da busasshen hawaye? Mu je na gyara miki fuskar. “ “An ki din, ka daina min magana, na yi fushi.” Ta fada a shagwabe. Ta kara tsumewa hade da danno bakinta gaba. “Kin san Zan iya sumbatarki tsawon wuni guda, idan ba ki gyara bakin nan ba, zan dauke shi a matsayin gayyata.” “Ya Salaam! Yaya Zaid me ya shiga kanka ne yau?” “Sonki ne kawai.” Ya fada yana dariya. “Don Allah ka mayar da ni gida.” “Na ki din, a nan za mu kwana.” Ba shiri ta sauke goyon hannunta da ta yi, sai ga ta a kan gwiwowinta. Da sauri ya sa hannu ya dagata. “Umm Adiyya, lafiyarki kuwa2” Kai ta gyada masa, “Kawai gida na ke so.” Duk wata alamar raha ta bar fuskar Zaid, ya gyada mata kai. “Shi kenan yanzu zan maida ke, amma ki daina abinda ki ka yi yanzu, kin ji?” “To.” Ganin fuskarsa a daure ne, ya sa ta tsaya a tsakiyar matakalar da suke sauka yana kasanta da matakala biyu juyowa ya yi wannan ya sa tsawonsu …