RAWANIN TSIYA CHAPTER 7 BY FADEELAH RAWANIN TSIYA CHAPTER 7 BY FADEELAH Www.bankinhausanovels.com.ng ASALIN ABUBAKAR SADIQ BUNZA!+ Alhaji Muhammad Bunza asalin mutumin qaramar hukumar Bunza ne a Kebbi state. Yaran shi sun kasance su uku- Sa’ad wanda shine babba, Sai Mariya itace ta biyu sannan Abubakar wanda shine qarami. Alhaji Muhammad a wannan lokacin ya kasance attajiri don haka ne yaran suka taso cikin gata da wadata. Sunyi karatun boko da islamiyya mai zurfin gaske. Sa’ad da Abubakar a turai suka yi karatun su na jami’a. Ita kuwa Mariya dayake mace ce sai tayi nata karatun a nan qasa Nigeria. Sa’ad wanda a yanzu yara suke kira Big Daddy ya karanci Medicine a qasar Germany. A dalilin bala’in qoqarin shi a wannan lokacin ne babban asibitin Berlin suka bashi automatic appointment inda suka dauke shi a matsayin babban likita. Albashi mai yawa suke biyan shi.. Cikin shekaru shidda ya tara kudade masu yawan gaske. Wannan kudaden ne ya dinga turowa nan gida Nigeria inda aka fara gina mishi wani qaton asibiti a cikin garin Abuj…