RANA DAYA CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne ya biya dukkannin sadakin. Anty Saude kanwar Baban Shatima ita ce ta dauki nauyin siyan takalman da za’a zuba musu duka. Don haka ya amso lambobin takalmansu ya kai mata, dama oder take yi. Aliya ta kan tura masa da sakon Juma’a bata mantawa, Nafisa na tura masa da sakon barka da safiya lokaci zuwa lokaci. Amna kuwa ba ta mantawa da tura masa sakon murna da shiga sabon wata a duk lokacin da aka shiga. Tsarin kowaccensu ya birge shi Shatima yana da kaifin basira, da hikimar zama da jama’a, don haka yake ganin kamar cin tuwo ne ko shan ruwa zama cikin mata hudu ma bare uku. Shagali ake shiryawa a kowane bangare musamman gidan su Amna wadda ta kasance ita ce mace ta farko da za’a soma aurar wa a gurin Mahaifinta. Itama Nafisa ana ta shiri don ita ce ‘yar fari gurin Babanta, ga kuma dangi kowa na cin buri, Aliya kuwa suma suna shiri daidai karfinsu, bata shagali suke yi ba su, sun…