RANA DAYA CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Ta ce, “Yaya bari in bi ka ka sauke ni.” Ya ce, “A’a ina Dircbanki? Ta tafi tana cewa, “Wai sai ya kai Yaya Mustapha wani guri sannan zai kai ni. Bai ce komai ba ta fita zuwa dakinsa. Ta dawo dauke da ledojin. Ya ce, “Ba Hajiya nata tsarabar da Amna tayo min daga Umra.” Badi’atu ta soma zazzage kayan iyayen suna kallo. Ledar farko riguna ne masu kyau, dogon hannu da gajeren hannu. Sai gajerun wanduna irin na ciki guda biyu. Daya ledar takalma ne sawu ciki kala biyu, sai turaruka da agogo mai kyau a kwalinsa. Hajiya ta fadada fara’arta. “Lallai abu yayi, masha Allah.” Alhaji ya ce, “An zo gurin, irin wadda ki ke so ko? Ma su kumbar susa.” Ta cc, “A’a Alhaji, ai mu ma ba a tsiyace muke ba.” Ya ce, “Amma tunda a ka ambaci Alhaji Baita ki ke washe baki.” Shatima ya ce, “Badi’atu kwashe ki maida, amma ki bar ma su Hajiya turarukan.” Www.bankinhausanovels.com.ng Alhaji ya ce, “Kwashe masa abinsa kin san dai na m…