RANA DAYA CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya kullum, don da ina tunanin duk su zauna nan Zariya, ni kuma ina Kaduna sai su ke zuwa.” Kaka ta ce, “Hakan shi ne daidai.” Ya ce, “Kaka a taya ni godiya gurin Alhaji, sannan a nema min alfarma, a rubuta takarda na yarda zan ba da cikon amma sai nan gaba, don kudin hannuna zan tada ginin da su.” Ya ce, “Wannan hutun na karshen mako sai muje kaga gurin.” Ya ce, “Allah Ya kara girma da lafiya Alhaji, Allah Ya jikan Mahaifinku, ya raba ku lafiya da Kaka.” Suka ce “Amin.” Nan suka ci gaba da tattauna al’amuran da suka shafe su. Ya idar da Nafilfilinsa na dare ya zauna yana istigfari, sai ya tuna wannan lokacin a Saudiya tamkar rana ce, zai iya yin magana da Amna. Ya tashi ya ciro wayarsa a chaji ya kunna yana neman lambar da Amna ta kira shi shekaran jiya. Ya kira sau biyu bata daga ba, ya mata uzuri kila bacci take yi tunda ba kowa ne ya saba da zama har wannan lokacin ba. Ya sake kira kashi na uku, sai gashi …