RANA DAYA CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Tayi yar dariya tare da sake matse wayar a kunncnta don dadin hira da shi. Ta ce Tun ranar da na kira ka ka ce zaka kira ni in ka samu sukuni, sai yau ka samu sukuni din? Ya canza kunne da ya manna wayar zuwa dayan kunnen don ya ji SOsai, saboda Amna bata magana da karfi ko. kuma ba ta son hayaniya. Wannan tsarin nata yana matukar birge Shatima. Ya ce, “Ba za ki gane ba, amma lokaci ya kusa da zamu zama tare. Ta ce, “Wane lokaci kenan? “Idan mun yi aure mana, kin san fa bana son a dauki lokaci me yawa nan gaba.” Ta ce, “Ban san ya zan ji ba in aka ce yau gashi na aure ka, ina tsananin sonka Shatima.” Sun jima suna hira kafin suka yi sallama da alkawarin zai kira ta gobe kamar yanzun. Lamo ya yi a kwance yana tunanin cikin su ukun nan bai fi son Amna ba kuwa? Wata zuciyar ta ce, ‘Ina ka bar Aliya mai hankali da sanin ya Www.bankinhausanovels.com.ng kamata, ga kuma Nafisa itama ba baya ba…?” Da wadannan tunanikan bacc…