RANA DAYA CHAPTER 3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Ya nuna mata hanya da hannunshi, “Je ki sallami Kaka.” Ta tsugunna a gaban Kaka ta ce, “Zan tafi gida.” Kaka ta ce, “Har kun gama hirar? To Allah Ya tabbatar muku da alkairi.” Har bakin falo ya rakata, sannan ya dawo gurin Kaka. Ya ce, “Kin ga abin Allah ko Kaka!” Ta ce, “Ai ni na zaci ita ce ta biyun.” Nan ya bata labarin Amna. Ya ce, “Goyon bayankı kawai ni ke nema.” Ta ce, “Shatima nemi komai gurin Allah. ni ai in hudu za ka yi ina murna, don bana son ragon namiji. Shatima mai sunanka gwarzo ne, mu hudu ya aje, ba dai rana daya ba. Amma tsakaninmu babu nisa. Duk ciki ni ce kararmu, yau ina abokan zaman nawa? Ina shi Maigidan namu? Duk sun amsa kiran Ubangijinmu. Mun zauna da dadi-ba-dadi, kuma an yi zaman mutunci, kullum ina yi musu addu’ar samun rahamar Allah, kuma. Allah Yasa tawa tayi kyau irin tasu. The de jah manch slara ar Tilb 2 Ya ce, “Amin Kaka.” Ta ci gaba da fadin, “Mata hudu ba matsala ba ne …