RANA DAYA CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Munnir ya ce, “Allah Ya tabbatar mana da dukkan alkairi.” Ya ce, “Ameen.” Kofar gidan su Munnir ya sauke shi, sannan ya nufi gidansu da ke Kwarbai a garin Zaria. Www.bankinhausanovels.com.ng Damfareren gida ne mai girman gaske, wanda daga gani ka san ma su gidan da kunbar susa, kila ma da jibin sarauta. Ya nufi ɓarayinsu ya aje motar ya kwashi wayoyin shi ya nufi cikin dirkeken falon. Tana zaune a kan kujera Badi’a tana shafa mata man zafi a kafa. Ya zauna kan Dardumar da ke gabanta tare da fadin “Sannu da hutawa Hajiya. Badi’a ta tashi da sauri tare da fadin “Sannu da zuwa Yaya. Ya ce, “Sannu Badi’a.” Hajiya ta ce, “Sannu Shatima, har ka dawo?” Ya ce, “Na dawo Hajiya. Akwai aikin da zan yi “a gida ne.” Ta ce, “To, cikin laptop din taka za ka yi kenan?” Ya ce, “Eh.” Hajiya ta ce, “To bari in sa a kawo maka abinci daki, gashi kuwa abin da ka ke son aka yi. “Burabusko ke nan?” Ta ce, “Eh, kuma akwai farfesun ka…