RANA DAYA CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Salma ta ce “Ya tafi ne?” Yaya Auwal ya ce, “Yana waje cikin motarsa.” Ta saka takalmi ta fita. Gaban motar ta gani a bude, daga gani ta samu matsala ne, shi kuma yana tsaye yana waya. Ta tsaya daga inda take, tana iya sauraron abin da yake fadi. Ta fahimci da Bakanike (mai gyara) ya ke magana. Don taji yana cewa “Zafi take yi, kazo ka same ni a nan Tudun Wada…” Ya ci gaba da yi masa kwatance. Da ya gama ya tsallako suka tsaya a inuwa inda “yan zaman makoki suka watse. Ya ce. “Salma! Tace. “Na’am! Yaya.” Ta tsugunna ta gaida shi, ya amsa tare da fadin “Mike.” Ta mike tsaye tana wasa da gefen hijabinta. “Ya karin hakuri?” Ta ce “Alhamdulillah.” Ya ce, “Kin daina kuka ko?” Ta ce, “Ai tun da ka hana ni ban kara ba.” “Yauwa, ki dangana. Yanzu wace shawara ki ka yanke, ko in ee me ki ke so in yi miki?” Ta kalle shi tayi dan guntun murmushi, sannan ta sunkuyar da kai. Ya ce, “Ki fada ni na baki zaɓi kuma na dau…