RANA DAYA CHAPTER 1 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA CHAPTER 1 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng **FARKO ** Tana fitowa daga dakin ta soma rera kuka kallon dakin da Mahaifinta ke kwance a cikin. Kafadarta taji an dafa tare da kiran sunanta. “Ummu Salma, kiyi hakuri Allah zai ba mu mafita.” Ko bata dago ba ta san Yaya Hadiza ce. Cikin kuka ta ce, “Yaya Hadiza abin nan da bakin ciki, Naira dubu goma tasa za mu koma da Baba gida a haka?” Yaya Hadiza ta kama hannunta. “Zo muje kafın Yaya ya fito mu ga ya za’ayi.” Www.bankinhausanovels.com.ng A harabar asibitin suka tsaya can in da ba kai kawon mutane, sai motoci da ke aje a gurin. Suka jingina da wata mota ba tare da sun damu da zafin da jikin motar ya yi radau ba. Yaya Hadiza ta ce, “Salma yanzun ke nawa ne a gurin ki?” Ta ce, “Jarin Awarata gaba daya Naira dubu ne da dari bakwai, kuma kin ga dai kullum in nayi za a samu dari bakwai, dari shidda. Da shi fa muke cin abinci, in kuma an kwashe an ba da ina zamu samu na cin abinci, har ma a kawo asibiti?”Yaya Hadiza t…